Ba jimawa Mamie ta fito ta sameta a mota, suna fara tafiya ta kalli Mamie tace "kin fad'i gaskiya, Aqilu yace baya sona yanzu."
Kallonta tayi tace "Khairat karfa ki fahimcini ba daidai ba."
Murmushi tayi kawai ta fito da abin sauraronta ta manne kunnuwanta suka ci gaba da tafiya, suna isa gida ta nufi d'akinta bata kuma sake fitowa ba sai da aka fara kiran sallah magrib, har tayi zaune Mamie tace "ki tashi kiyi alwala kizo muyi sallah."
Cike da nuna rashin jin dad'i tayi shiru, a tsawace Mamie tace "dake nake magana kina jina kinyi shiru."
Ganin ta tashi ta wuce cikin kasala Mamie ta dora da fad'in "kuma wallahi ya zama na qarshe da zan miki magana akan sallah, inba rainin wayo ba kamarki shekara ashirin da biyar amma ba zaki iya gaishe da unangijiki ba sai kinga dama."
*Wallahi a zamanin nan da muke ciki, matasanmu musamman yan mata bamu cika tsayar da sallah ba, musamman idan sunyi kwalliya a fuskarsu ba'a son asa ruwa a wanke, ya kamata muji tsoron Allah mu gane saida sallah ne muke iya banbanta kanmu da kafirai, Allah ka bamu ikon kyautata ibadunka, Allah kasa mu zama masu tsayar da sallah domin samun sassauk'an hisabi, Allah kasa mu tsayar da sallah domin ta zama abokiyar zamanmu a qabari dan haskaka makwancinmu.*
*Da sallah ne muke cika cikakki musulmi, idan sallanmu tayi kyaune ake kyautata mana zaton sauk'in hisabi, sallah itace take tayamu zama a qabarinmu kafin lokacin da za'a tashi qiyama, sannan mai tsayar da sallah ko a cikin al'uma zaka ga fuskarshi na annuri, sannan hadisi ne ingantance cewar wuta bata tab'a duk wata gab'a da take samun ruwan alwala, wannan 'yar qaramar tunatarwa ce badan na fiku sani ba.*π
Babu wata matsala a game da alwalarta sai dai a game da sallah kam akwai yar mishkila, saboda cikin minti biyu ta gama sallah ta fito falo, hakan yayi daidai da fitowar Papa zashi makaranta, ganin littafi a hannunshi yasa tace "Papa sai ina kuma?"
Kallonta yayi yace "majlisin malam zani d'aukar karatu."
"Toh , Papa karatu aka koma?"
"Eh 'yata, kuma kema kin kusa komawa insha Allah."
Wata dariya tayi ta nufi fridge tana fad'in "wasa kake Papa, haka dani na shiga makaranta."
Papa ma wucewa yayi dan lokaci nayi yana fad'in "ba'a girma da neman ilimi, tunda ki kaga na fara zuwa to kema ki shirya dan kin kusa."
Yau ma dai kamar kusan kullum ita kad'ai taci abinci bayan iyayenta sunci, tana kammalawa ta koma d'aki tana chat tana sauraron waqoqi har dare yayi sosai tana bacci cikin kwanciyar hankali.
Mamie ce ta shigo d'akin ta zauna kusa da ita, ta jima tana kallonta tana murmushi kafin ta tofa mata addu'a ta sumbaci goshinta, zani taja mata ta rufeta ta tashi saida ta kashe mata wutar d'akin kafin ta fita, tun fil'azal Khairat bata bacci da duhu a d'aki hakan yasa ma bata kashewa.
Kusan abune daya zamar mata jiki mafarkin abinda ya faru da ita, kamar a zahiri haka ta dinga tuna lokacin da take kokawa da Musa har lokacin da yayi nasarar kutsa kanshi a tsakiyar matancinta, razananniyar qarar da tayi a mafarkinta itace ta bayyana har a zahirin baccinta.
"Ahhhhhhhhh, Mamiena, Papa wayyo Allah, Papa, Papa zasu kasheni, Papa gasunan fa, zasu sake min fyad'e, dan Allah kuzo ku taimakeni, Mamie, wai baki jina ne? wallahi gasu nan."
Wannan duhun d'akin shi ya qara firgitata haka ta dinga kiran su Mamie da Papa, kasancewar d'akinsu a qasa yake hakan yasa basu ji da wuri ba, Mamie ce ta fara ji ta tayar da Papa, a sukwane suka shigo d'akin nata Mamie ce ta kunna wuta Papa kuma ya tunkareta, tana ganin haske ya mamaye d'akin tayi saurin rarrafowa ta nufo Papa, fad'uwa tayi wajen tahowa Papa ne yayi saurin tashinta ya rumgumata a jikinshi yana shafa kanta yana fad'in "shiiiiii, shalele, gani nan Papanki ne kinji, ya isa haka."
A haka suka taka ya qarasa da ita bakin gado suka zauna yana ci gaba da fad'in "ya isa kinji gimbiya, ba kowa anan, d'ago idonki ki gani, nine Papanki da kuma Mamienki, ki nutsu kinji."
A hankali kuwa ta daga ta kalli Papa sannan ta kalli Mamie dake gefenshi, da sauri ta kamo hannun Mamie ta sake fashewa da kuka tace "dan Allah Mamie ki kwanta anan, wallahi zasu iya dawowa su sake min fy......" Mamie tayi saurin rufe mata baki.
A haka suka ci gaba da rarrashinta har Mamie ta d'ora kanta a qafafunta bacci ya d'auketa, a zaune Mamie ta kwana tana shafar kanta tare da mata addu'a.
Suna a haka Papa ya shigo ya tashesu suyi sallah asuba, tare da Mamie sukayi sallah sannan Mamie ta sauka ta shiga madafa, Papa na zauna yana hutawa a lambu tare da linttafinshi yana bitar karatu wayarshi tayi qara, ganin mai kira yasa ya rufe littafin ya d'auka, bayan sun gama a sukwane ya shigo cikin falo yana kiran sunan Mamie.
Da sauri ta fito tana fad'in "gani Alhaji, lafiya dai irin wannan kira haka?"
Cikin karsashi yace "lafiya lau, albishirinki?"
"Goro." ta fad'a tana masa kallon tuhuma.
"Yanzu mukayi waya da shugaba, kuma tabbatar min suna so ayi komai a gama, dan haka goben nan zasu kawo lefen Khairat."
Cike da tsantsar farin ciki tace "kai, Alhamdulillah, amma naji dad'in wannan albishir, Allah ya nuna mana goben yasa alkairi."
"Ameen, yanzu kije ki lissafa mana duk abinda za'a buqata dan tarbar bak'i, tunda kinsan fa harkar babba ce."
"Ah sosai kam, kar kaji komai, ba buk'atar kashe kud'inka, ni zan d'auki wannan nauyin insha Allah."
"Kenan dai bikin Khairat na nad'e hannayena nasha kallo?"
Cikin dariya tace "a'a ba duka ba, dole ai kasan zamu shiga cikin aljihunka idan biki ya matso."
"To shikenan, Allah ya kaimu."
πππππππ
Misalin 11:35 Khairat ta tashi ta fito falo, Mamie na madafa tare da masu kama mata aiki, cikin takon mai nuna magagin bacci ta shiga madafa, ma'aikatan ne suka gaisheta amma babu wanda tako kalla bare ta amsa, wajen kayan lambu ta nufa ta d'auki kokomba ta wanke ta fara kaiwa bakinta, sai lokacin ta kalli Mamie tace "ina kwana Mamie."
"Lafiya k'alau, kin tashi lafiya."
"Um." ta fad'a tare da fito ta koma d'akinta tayi wanka ta shirya cikin riga da siket na kanti kanta ba d'an kwali ta fito falo ta zauna, 12:30 su Mamie suka kammala abincin rana, jerawa sukayi a dinning sannan Mamie ta shiga wanka, 13:00 Papa ya shigo gidan tare da sabin masu tsaron lafiyarsa su biyu, suma da qyar ya yarda aka had'ashi dasu.
"Sannu." cewar Khairat.
Kallon teburin yayi sannan yace "sannu shalele, an gama abinci."
Tana kallon wayarta tace "umm , sun gama."
Hannunta ya kamo yana fad'in "muje ki zuba min naci gimbiya, yunwa nake ji sosai."
Itama cewa tayi "amma ai ban iya zubawa ba, bari na kira Biba ko Saude su zuba maka."
"A'a nike nake so ki zuba min." ya fad'a yana zaunawa.
Kallonshi tayi ta kalli kwanukan abincin ajiye wayarta tayi a gefe zata d'auki plate wayar Papa tayi qara, d'auka yayi yana fad'in "hello, manager har kun karaso ne?"
Jim yayi na d'an lokaci kafin yace "to ku shigo kawai ina ciki nima yanzu na shigo."
Aje wayar yayi ya kalli Khairat yace "wallahi wani hazik'in matashi ne aka samu a masana'antarki, baifi wata biyar zuwa shida da fara aiki ba, amma harya fito da sanfirin takalmin da suka karb'u a duniya, shine nace manager ya kawoshi nan mu gaisa na kuma masa godiya, sannan zan shirya masa qarin girma a ma'aikatar."
Ko qala ba tace ba, kwanon farar maca ta bud'a wacce tasha kwalliya da waken gwangwani, cokali ta d'auka ta fara k'walbatowa rabi na zubewa qasa rabi na shiga plate d'in, da qyar ta zuba a plate d'in har Mamie ta fito ta samesu, kwanan miya ta bud'e wacce tasha kaji daga-daga, (πmutuniya ba) tana saka cokalin miyar ta fallatso mata sai a ido, qara ta saki tare da sakin cokalin a miyar, sake fallatsowa yayi sai kuwa a fuskarta da jikinta, zafin da taji yasa ta dinga tsala ihu tana fad'in "na k'one , na k'one, zafi Mamie ki goge min."
Mamie da hankalinta ya koma kan manager da matashin saurayin nan, Umar Faruk daya tsaya ya kasa gudawa yana kallon Khairat na tsalle tsalle duk jikinta na kadawa, da qyar ya had'e yawu suka fara takawa suka zauna inda Papa ya nuna musu, sai lokacin Khairat tayi shiru ta sauke idonta akan Umar Faruk.
Kallonshi take sosai shi kuma ya d'auke idonshi daga kanta, Mamie ce ta katseta da fad'in "ki zuba musu abinci mana shalele."
Da sauri ta kalli Mamie, da ido ta mata alama ta zuba musu, turo baki tayi gaba tace "nifa Mamie ban iya ba, kina gani abinda ya faru yanzu na k'ona kaina."
Wayarta ta d'auka ta juya zata bar wajen Papa yace "gimbiya baki zuba min ba."
Lokacin data juyo idonsu suka had'u dana Umar yana mamakin abinda ta fad'a wai bata iya zuba abinci ba, to kenan ya zata dafashi??? ya tambayi kanshi.
Zagayawa tayi wajen da yake zaune ta mik'a masa hannunta tace "zo."
Da mamaki yake kallonta yana mamakin fitsararta, kallon Mamie da Papa tayi wanda suma ita suke kallo tayi murmushi tace "kunyarku yake ji fa."
Kallonshi tayi tace "kaga ka taso magana za muyi da kai."
Tana fad'a ta ja hannunshi suka nufi d'akinta, tana shirin bud'a k'ofar d'akin ta tsaya cak saboda ji da tayi ya qara matse hannunta, kasa juyowa tayi saboda yanda taji tattausan hannunshi ga kuma gabanta daya fad'i, a hankali ta fara zame hannunta daga nashi shi kuma baisan ya akayi ya kasa rik'e kanshi ba harya qara matse hannunta, saida ta raba hannunta da nashi sannan ta ta bud'e d'akin ta shiga, kallonshi tayi ganin yaki shigowa, alama ta masa da ido akan ya shigo, a hankali yake takawa yana jin bugun zuciyarshi na k'ara tsananta, da sauri ya juya ya kalleta saboda ganin ta rufe k'ofa.
Gabanshi ta tsaya tace "ranar na tambayeka amma baka bani amsa ba, amma daga baya sai nayi tunani naga cewa, ai ko ban tambayeka nasan kai kana daga cikin mak'iyana, kuma kayi farin ciki da abinda ya sameni, kuma nasan ko kai ka samu dama zaka iya yin abinda wad'ancen sukayi."
"To ba komai, kuma ku sani ni Khairat ba zan nuna gazawa ba, ba kuma zan nuna bana da daraja ba, kamar yanda ba zan saka damuwa a raina ba, dan haka duk mai bak'in ciki sai dai ya mutu."
Wucewa tayi ban d'aki tana fad'in "zaka iya tafiya."
Shi kuma ya kasa komai gaba d'aya ji yake yayi sanyi ya rasa duk kuzarinshi, binta yayi da kallo ya kasa fita, Khairat ce daga ciki ta jefo da gaba d'aya kayanta data cire harda qananan ciki saboda bata tunanin yana nan har yanzu, yana ganin haka yayi saurin juyawa zuciyarshi kamar zata fito daga qirjinshi, saurin fita yayi daga d'akin hannunshi a kan saitin zuciyarshi a hankali yake takawa yana tambayar kanshi.
_Me yasa nake jin haka idan na ganta?_
_Me yasa na rasa duk wani k'arfi na dana tsaya gabanta?_
_Me yasa gabana ke fad'uwa idan na tuna koda sunanta?_
_Me yasa nake jin daban a tare da ita?_
ππππππ _no amsa._
Khairat na sakar ma kanta ruwa ta lumshe ido, da sauri ta bud'e idonta saboda ji da tayi kamar hannun Umar Faruk a nata hannun, ajiyar zuciya ta sauke ta sake rufe ido saboda yanda ruwa ke sauka a kanta, Umar Faruk dai ta sake gani yana mata wannan kallon da fassararshi sai _my aunty Aishan Umma_, haka ta fito daga wanka wannan tunanin ya kasa barin qwaqwalwarta harta d'auki riga da wando ta saka qanana sannan ta sake fitowa.
Tare suka ci abinci dasu banda Umar Faruk da ruwa kad'ai yake d'an kurb'awa suma sai Papa ya mishi magana, anan Papa ya masa godiya tare dasa albarka sannan yace "kaci gada da k'wazonka, insha Allah za kayi nasara a duk inda ka samu kanka, Umar Faruk..ko?"
Cikin murmushi yace "eh, *Umar Faruk Ahmad Adam*."
Da mamaki Papa ya kalleshi yace "Ahmad Adam, kai d'an malam Ahmad ne?"
Shima da mamakin ya kalleshi yace "eh ni d'ansa ne."
Mamie Papa ya kalla yace "Allah sarki, kinga fa yaron nan d'an malamin da nake d'aukar karatu wajenshi ne, haba shi yasa ka zama mai hazak'a da basira."
Dariya Mamie tayi tace "yaron kirki ne kam, Allah ya maka albarka."
Kiran daya shigo wayar Khairat ne yasa ta tashi daga wajen, Mamie ce tace "baki ci komai ba fa tun safe."
Juyowa tayi tace "Muzaffar ne yake kira, ina zuwa."
Mamie da Papa ne quka kalli juna suna murmushi, sabanin Umar Faruk da gabanshi ya buga ranshi kuma ya b'ace, cup d'in ruwa ya d'auka ya kifa saida ya shanye sannan ya mik'e yace "ni zan wuce, na gode."
Ficewa yana jin tsanar Muzaffar a zuciyarshi ba tare da sanin shi Muzaffar d'in ba, kasa jiran manager yayi dan haka ya tari taxi ya mayar dashi ma'aikata, haka ya isa ya zauna yana kallon tafin hannunshi da Khairat ta rik'e, wani hamshak'in murmushi ya saki saboda tuna da yayi lokacin da take tsalle tana ihu, sake fashewa yayi da dariya haka kawai ya rasa dalili amma farin ciki yake ji har k'ark'ashin zuciyarshi, Ishaq daya lura da hakane ya tab'oshi ta gefe yana fad'in,
"Da alama fitar nan tayi kyau ko?"
B'ata fuska yayi yace "ban gane ba, kai baka san ina muka je bane?"
"Na sani mana, amma naga ka cika dariya kai kad'ai."
"Son gulma ko? to ba zaka ji ba."
Dariya Ishaq yayi ya maida hankalinshi ga aikinshi yana fad'in "da alama ka fad'a soyayya abokina."
Da k'arfi ya kalleshi yace "me? soyayya fa kace? to aini dama ba sabon shiga bane, ko ka manta ina da Zuby?"
Saida Ishaq ya kalli k'wayar idonshi yace "watak'ila yanzu ne ka fad'a soyayyar gaskiya kuma wacce ta dace, idan kuma ba haka to zai iya yiwuwa yanzu ne zuciyarka ta kamu da so."
"Son wa?"
"Son Khairat mana." Ishaq ya fad'a.
Sake kallonshi yayi dan baiyi tsammanin yaji abinda yace ba a fili, zunbur ya tashi daga wajen ya fita filin ma'aikatar, maganar Ishaq ce kawai ke dawo masa a qwaqwalwa ta cewa "son Khairat mana."
A zafafe ya furta "ina, hakan ba zai yiwuba, bata dace dani ba, zuciyata ba zata tab'a min wannan rashin adalcin ba."
_Aikin gama ya gama_π.
*Team Khairat, ku fito muyi rawa*πππ
Daga yanda Muzaffar yake wa Khairat magana yasa ta fahimci akwai wani dake faruwa, musamman da yace ya matsu gobe tayi a kawo kaya a tabbatar mishi ita tashi ce, kashe wayar tayi ta dawo falon lokacin manager ma harya tafi, tsaye tayi gabansu tana kallonsu tace "me yake faruwa? me Muzaffar yake fad'a?"
Papa ne yace "kinga shalele ki zauna kici abincinki , an jima za muyi magana."
Cikin d'aga murya tace "wane naci abinci bayan abinda wannan mahaukacin yake fad'a, kawai ku fad'a min koma miye naji."
Mamie ce ta d'aga murya itama ta tashi tsaye tace "Khairat!!! mu kuke d'agawa murya? kece kika haifemu ko mune muka haufeki? idan bamu fad'a miki ba me za kiyi?"
Kallon Mamie tayi fuska ba annuri tace "maganar aure yake, kuma nasan kinsan babu wanda zai min aure ba tare da ina so ba, idan alk'awarina kuka mishi to ku janye danni ba 'yar roba bace da za'a min haka."
Zata wuce Mamie ta fizgota da k'arfi za tayi magana Khairat ta fizge hannunta da k'arfi tana fad'in "ki sake ni, karki sake tab'ani, ki fita a harkarta."
Duk da qoqarin b'oye hawayenta kasawa tayi saida kukan ya k'wace mata ta fara magana cikin kuka "na sani kuma dake iyayena kuna ganin yanzu bana da wata kima da daraja ta 'ya mace, inba haka ba babu ta yadda zaku fara min maganar aure ba tare da sanina ba.:
Wucewa tayi ta barsu nan Papa kuma ya kalli Mamie cikin b'acin rai yace "....π
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Wallahi har qasan raina ina jin dad'in addu'arki sister Alawiyyah, gaskiya ke ta dabance, samun fan's irinki abin alfahari ne kuma burin kowace marubuciya, duk da soyayyar da kike nuna min bata isa ba saida kika nunawa my Heenat d'ina itama tata soyayyar, lallai muna yinki over, luv u dear.π_
_My aunty *Aishan Umma* ina mik'a godiyata sosai a gareki, kinsa naji cewar ni mai sa'a ce a rayuwaπ muna alfahari dake a matsayin shugabar k'ungiyarmu._
*Welcome Back my π
±K.*π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣6⃣
"Wai me yasa kike wa yarinyar nan haka, akan me zaki dinga d'aga mata murya, me yasa kika cika b'acin rai ne Na'ima?"
"Au, nice ma na daga mata murya kenan? kai yanzu baka ga abinda tayi ba? wai me yasa kake hakane? Khairat fa 'yarmu ce mu muka haifeta ba ita ta haifemu ba, to akan me zata dinga tsaya gabanmu haka tana fad'a mana abinda ranta yake so?"
Tsaye ya mike yace "koma dai miye kinsan muna da laifi, kamar Khairat ace mun tsayar da maganar aurenta ba tare da saninta ba a wannan qarnin da muke ciki, kinga dole ranta ya b'ace."
D'akin Khairat d'in ya nufa yana ci gaba da mita, tundada ta shiga d'aki ta kwanta kan gado tana kuka, jin kanta na sarawa yasa tasan yanzu zai fara mata azababben ciwon daya saba, tashi tayi da nufin d'auko magani tasha amma bata kai ga wajen ba jiri ya d'ebeta ya yadda, rintsegudu ido tayi ta dafe kanta sosai tana fad'in "wayyo Allah kaina, kaina zai fashe, kaina Papa ciwo yake, dan Allah kazo kai kad'ai ke sona, Papa kaina zai fashe, wayyo, ahhhh, wash."
Papa na shigowa ya ganta kwance a qasa, da gudu ya k'arasa wajenta yana tambayar "shalele lafiya, meya faru, kanne ke ciwo halan?"
Kamata yayi ta tashi ya taimakata ta zauna akan gado yana fad'in "wallahi shi yasa bana qaunar abinda zai b'ata miki rai saboda irin haka."
Da sauri ya nufi wajen maganinta ya d'auko ya kawo mata tare da ruwa ya taimaka mata tasha, kwantar da ita yayi yana fad'in "kwanta ki huta kinji."
Kai ta girgiza har yanzu hannunta na saman kanta tana matsewa tace "dan Allah Papa ka d'aure min kaina fashewa zaiyi, ka taimaka ka d'aure min dan Allah."
Ya tashi kenan zai bud'a kayanta Mamie ta shigo d'akin, wata harara ya dalla mata dan ranshi ya b'ace sosai, kayan ya bud'a ya d'auko wani qaramin gyalenta ya dawo ya zauna kusa da ita ya d'aure mata kan sosai, sake cewa tayi ya d'aure mata sosai, shi kuma yana ganin ya d'aureshi qwarai haka ya sake tamke mata kan, duk da haka ba sauk'i Mamie dake tsaye tana kallon yanda jijiyoyin kanta suka fito sai harbawa suke kai kasan ba qaramar azaba take ji ba, cikin muryar kuka tace "dan Allah Alhaji ko zamu fita da yarinyar nan waje ne, kasan fa babu kyau ciwon kai ga 'ya mace? gaskiya ni ina jin tsoro."
Wata tsawa Papa ya daka mata ba tare da saninshi ba "dallah rufe min baki, duk waya janyo yanzu in ba ke ba, ke wai har abada ba zaki iya mu'amulantar yarinya da kyakywar mu'amula ba, sai hushi kawai na banza da wofi, to idan kika kasheta ai kinga saiki huta, kinsan dai ba zaki sake haihuwa ba har abada dan mahaifar ma baki da ita, ni kuma wallahi aure zanyi da ba zan zauna ba magaji ba."
Kasa hak'ura tayi da abinda ya fad'a saida tace " to kayi auren mana saime? nace saime idan kayi aure? namiji goma aiba uba goma bane, wato ka lalata min rayuwa yanzu kuma burinka kenan na rasa 'yar tawa guda d'aya kai kuma kayi aure, to wallahi baka isa ba, yanda ka b'ata min rayuwa kaima a haka zaka tabbata ba d'a ba jika."
Tsaye ya mike "ni kike fad'awa haka Na'ima, waike me yasa baki da kunya? yanzu a gaban 'yarki kike fad'a min haka? kenan tarbiya ce kike so ta d'auka a haka?"
"Kai tarbiyarce kake so ta d'auka daka fad'a min abinda ka fad'a min, kasan kaine silar lalacewar mahaifata, to miye na fad'a min wai zan kashe 'yata?"
"Dallah ni kimin shiru a wajen nan kona tattakaki."
"Naki nayi shiru, kayi abinda za kayi mana, an fad'a maka tsoronka nake ji? aini dama nasan ba tuban gaske za kayi ba, kawai dai parpaganda ce irin taku 'yan siyasa."
Tatsssss, Papa ya d'auketa da gigitancen mari yana fad'in "ke har kin isa kici mutunci na, wallahi bari gani ina d'aga miki qafa, ruwane suka daki babban zakara wallahi, idan kuma kinfi son in dawo Mani na nada to mu zuba dani dake."
Dauke hannu tayi daga kunci tace "ka dawo Mani mana dama ai baka canza ba, kuma da kake maganar mutunci, kai har mutuncine da kai da za'a ci? kuma wallahi ka sake dukana ramawa zanyi, tunda ni ba jaka bace."
Nunata yayi da hannu yace "kici albarkacin 'yarki dake kwance a wurin n...." bai k'arasa ba saboda ganin Khairat zaune tana kallonsu kamar ba mai ciwon kan nan ba.
Kunya ce ta tureshi dan baiji dad'in abinda ya faru ba ko kad'an, kawai ta kaishi bangone, zai zauna a kusa da ita kenan ta fashe da kuka tace "karka zauna, dan Allah ku fitar min daga d'aki, ku barni zanci gaba da ratuwata a haka, ba zaku tab'a sauyawa ba saboda ya riga daya zama jikinku, ba zan iya zama daku na minti d'aya ba ba tare da kun samu sab'ani ba, ku fita dan Allah, zan kula da kaina ko bakwa nan."
Papa ne ya sake marairaicewa yace "shalele ki saurare ni kiji."
"Bana son jin komai, ku fita kawai."
Jiki a sanyaye suka fita, amma tana jinsu ko nisa ba suyi ba Papa ya fara tuhumar Mamie akan ita ta janyo komai, haka suka jima suna wannan fad'an harya fita ya bar gidan, Khairat kam turmutsutsu ta dinga yi saman gado tana tusa kanta pillow saboda rad'ad'in da yake mata.
*Wallahi yan uwa akwai iyayen da basa iya rik'e b'acin ransu, ko a ina ko a gaban waye idan ransu ya b'ace sai suyi musayar yawu, wallahi iyaye muji tsoron Allah, dan dole zamu tsaya a gabansa kuma mu amsatambayoyi.*
*Yana da kyau ace ke uwa mace kina da hak'uri fiye dana namiji , domin kece mai tarbiyar yara maza da mata, idan ranshi ya b'ace ke kiyi hak'uri ki taushi naki b'acin ran, yara tun suna qanana suna lura da zamantakewar iyayensu kuma hakan nada tasiri a rayuwarsu sosai, wannan d'an qaramin jan hankali ne, Allah ya bamu ikon kiyayewa, ameen.*
*****************
Umar Faruk ne da Zuby suke waya, amma shirunshi yayi yawa ba kamar kullum ba, tunanin Khairat da lokacin data rik'e hannunshi kawai yake yi, ga kuma tuna abinda Ishaq ya fad'a, a hankali ya saki wani tattausan murmushi daya bayyanar da kywunshi, sannu sannu ya bud'a bakinshi ya furta kalmar " *shalele*".
Wani murmushin ya koma saki, muryar Zuby ce ta katseshi da tace "yau kuma sabon sunan na samu?"
Dawowa yayi tunaninshi, cikin rashin gaskiya yace "e..e...eh mana."
Shi kuma harga Allah sunan daya ji Papa y kira Khairat dashi ne ya maimaita, cikin sauri yace "am kina ji? zan sake kiranki."
Yana fad'a ya kashe wayar tare da fad'awa duniyar tunani, ya jima a wannan halin kafin ya fara magana da kanshi "haba Umar Faruk, ka dawo hankalinka mana, wannan fa bata dace kai ba ko kad'an, me yasa kake damun kanka a kanta? ko ka manta wacece ita? kai da ita fa kamar mota da jirgin sama ne."
"Kai kana son mace mai kunya, ita kuma bata da kunya, kai kana son mace mai kamun kai da aji, ita kuma sai ajin amma ba kamun kai, kana son samun mace wacce zata kula maka da mutuncinta ko bayan idonka, amma ita ko a gaban idonka ma zata zubar maka dashi bare kuma bayan idonka, kana son mace mai ilimin addini, amma baka da tabbacin sahihancin addininta, kai namijine mai kishi, ita kuma ta riga da tayi tallar surar jikinta a waje kowa ya gani, bugu da qari baka da tabbacin ita d'in saliha ce tun ma kafin a mata fyad'e, dan haka ka fita a harkarta daga tunaninta ma haka."
π€Έ♂π€Έ♂π€Έ♂π€Έ♂π€Έ♂π€Έ♂π€Έ♂
Sai dare ciwon kan ya lafa mata amma kuma bata fito ko falo ba bare farfajiyar gidan, tana d'aki zamanta tana sauraran waqoqinta, Papa ma yayi yayi ta fito taci abinci amma tak'i, dole sai nan aka kawo mata shima bata ci wani mai yawa ba sosai kamar yanda ta saba, daga nan kuma bacci ya d'auketa.
*Washe gari* gidan an tashi anata qoqarin shirin tarbar bak'i, Khairat na bacci Papa yasa Mamie ta tasheta, dan dole tasan halin da ake ciki, tana bud'a ido taga Mamie kawai ta tashi ta shiga ban d'aki tayi wanka, ta jima kafin ta fito ta shirya cikin rigar shadda dan fita take so tayi daga gidan, falo ta fito da gyalenta a kafad'a da jakarta a hannu, tana shirin kaiwa k'ofa Mamie ta fito daga d'akin Papa, a hanzarce tace "Khairat."
Tsayawa tayi amma jiyo ba, Mamie ce tace "Papanki ke kiranki?"
Saida ta sauke ajiyar zuciya sannan ta juyo bata yarda sun had'a ido da ita ba kawai ta nufi d'akin Papan.
Kamar yanda bata saba ba haka yanzu ma ta shiga d'akin ba sallama, zaune tayi bakin gado saboda Papa na zaune a d'aya daga cikin kujerun d'akin, kallonshi take tana jiran taji me zaice Mamie itama ta shigo ta zauna gefenta, babu wanda ya kalli wani bare suyi magana har Papa ya gyara murya yace....
"Khairat."
Jin yanda ya kira sunanta kuma yayi shiru yasa dole ta amsa da "na'am."
Kallonta yayi yace "waye ni a wajenki?"
Da mamaki ta kalleshi tace "mahaifina."
"Da kyau."
Nuna Mamie yayi yace "wannan kuma wacece ita?"
Kallon Mamie tayi tace "mahaifiyata ce."
Nan ma jinjina kai yayi yace "yayi kyau."
Sannan ya d'ora da "a tunani da hankalin da Allah ya miki Khairat, nasan kinsan iyaye suna da daraja sosai, hakane?"
"Hakane."
"Shin kina ganin mun kai matsayin da zamu iya yanke miki hukunci daya shafi rayuwarki ba tare da saninki ba, ko kuwa dai dole sai mun nemi izininki kafin mu nuna mu iyayenki ne?"
"Zaku iya mana, idan ba zai tauyeni ba."
"Ba wannan nake son ji ba Khairat, zamu iya ko ba zamu iya ba?"
"Zaku iya."
"To Alhamdulillah."
"Khairat, yau za'a kawo kayan lefenki daga gidansu Muzaffar, mun amince a matsayinmu na iyayenki, kuma muna da yak'ini akan ba zaki bamu kunya ba."
Tsaye ta mik'e tayi wata dariyar yan daba tace "nasan dama za ayi haka, yanzu me kuka daukeni da har zaku yanke wannan hukuncin a kaina? taya zaku had'ani da mutumin da tsarina da nashi ma daban ne? ni bana son Muzaffar kuma ba zan aureshi."
Jakarta ta dauka zata fita Papa ya daka mata tsawar da tasa ta tsaya wuri d'aya "ke Khairat, ina magana kina magana, maza wuce ki zauna magana nake dake."
Sum sum sum ta koma ta zauna Papa ya dora da "a tunani mummunar kalma bata tab'a shiga tsakanina dake ba, amma ki sani Khairat idan har kika shirya bani kunya da tozartani, to hakika zaki fara jin kalma marar dad'i ta fara fitowa daga bakina kuma a kanki, bana fatan na tsine miki albarka, amma dai ba zaki ji dad'in abinda zai fito daga bakina ba, ke ba yarinya bace kin isa aure har kin wuce ma, burinmu shine mu kaiki d'akin mijinki kema."
"Khairat, dubi mahaifiyarki ki gani."
Kallon Mamie tayi ta kalli Papa shi kuma yace "burinta kawai taga aurenki, kullum cikin fargaba take a kanki, saboda yanda take son taga kinyi aure Khairat har rabuwa tayi dani kuma ta dawo, yanzu haka mahaifiyarki wata d'aya ta bani dan na aurar dake, idan kuma ba haka ba to zamu rabu kuma rabuwa ta har abada, yanzu ki fad'a min Khairat."
"Shin kina son muci gaba da zama ni da mahaifiyarki, ko kuma kinfi son mu rabu?"
Shiru tayi tana tunanin mafita, tabbas bata son Muzaffar saboda basu dace ba, amma kuma ba zata yarda iyayenta su rabu ba saboda maganar aurenta, dan haka ta samawa kanta mafita, a hankali ta kalli Papa tace "in dai wannan shi zai saku farin ciki, tona amince."
Tana fad'a ta sake d'aukar jakarta zata fita Mamie tace "da gaske kike Khairat?"
Kura mata ido tayi tana kallon tsantsan farin cikin dake fuskar Mamie kafin tace "eh Mamie, na amince."
Juyawa tayi Papa yace " ina zaki je kuma?"
Danne zuciyarta tayi ta qaqaro murmushi tace "yau fa za'a kawo kayana Papa, ai bai kamata na zauna gida ba har sai kowa ya ganni."
Dariya suka saka mata dukansu itama ta wuce tana dariyar, yayin da suka bita dasa albarka, tana fita motarta ta shiga ta fara tuk'i kuma Mamie ta kirata, tana d'auka tace mata "shalelen Papa, dama cewa nayi me zai hana kije gidansu *Hibba*, kinga saiku zauna acan tunda mahaifiyarta ma nanan zuwa nan d'in."
"Ok, zanje." tana fad'a ta kashe wayar Mamie kuma tayi murmushi.
A hanya ta kira k'awayenta *Rashida, Sarina, Farida, Mamy* akan su sameta gidansu Hibba, duka suka amsa kiranta dan sun san akwai labari, hannun riga sukayi da Mamar Hibba hakan yasa basu gaisa ba, kafin su Rashida suzo ta fad'a mata abinda ke faruwa, dan ita kad'ai ke bata shawarar data dace, yanzu ma sake jadadda mata tayi tabi iyayenta, sannan ta nunawa Muzaffar kamar tana sonshi har tayi nasarar samun soyayyarshi ta gaskiya, tunda shi ya fad'a da bakinshi ko da ranar darensu na farko ne bai damu ba dan sun rabu, haka ta bata shawarwari masu kyau, sannan su Rashida suka zo.
Tana fad'a musu za'a kawo kayanta suka saka shewa da murna dan sun san babban bidiri ne, nan suka wuni har Muzaffar ma ya kirata yana tambayarta abubuwa da zasu shirya, kamar yanda Hibba ta bata shawara akan tayi dan ta b'oye sirrin zuciyarya sosai, ta fad'a mishi bata gida za suyi shawara da k'awayenta idan taje gida saita fad'a masa yanda sukayi dasu, a haka sukayi sallama su kuma suka ci gaba da shirye shiryensu.
*A gida* kuwa Mamie farin ciki take sosai hakan yasa suke ta kujuba kujuba, 'yan uwa mak'ota da mutanen arzik'i tuni suka cika gidan, hada hada kawai ake an soya na soyawa , an gasa na gasawa , an dafa na dafawa , an motsa na motsawa haka ma na jik'awa an jik'a.
*16:35* unguwar ta shaida bak'i sun shigo cikinta, jiniya kawai kake ji na motocin matan manya uwa uba ga mahaifiyar Muzaffar da kanta tace ba za'a barta a baya (abinka ga 'yan bariki.π), motoci ne ba adadi suka tunkaro k'ofar gidan kama daga na matan manya da abokan arzik'i, sai kuma na abokan Muzaffar duk da baya gari amma sun masa kara, abinfa ba'a cewa komai ba'a kuma ga komai ba, saida masu tsaron lafiya suka fara bud'e motoci manyan mata na fitowa daga ciki.
Dala tayi kuka a wajen harka ta girma ce akayi sosai, sai dai wata matashiyar mota kyakyawa wacce aka shiga da ita har farfajiyar gidan, masu tsaronne suka dinga fito da akwatina kowace mak'il da kaya d'aya d'aya har dozin biyu da rabi, ga kuma wannan mota da aka azo akan lefan.
Ciki aka shiga masu gulma nayi masu saka albarka na sakawa masu d'aukar photuna suna d'auka, acan kuwa na hango muku Mamar Mujaheed π€£ta rumgume jakarta tana kallon manyan mata suna yagar kaji da qafafun rak'umi π, haka dai aka ga abin arzik'i tari guda sannan aka sake tsayar da ranar kwana ashirin da biyar ya rage.
**************
Tunda Khairat ta dawo gida taga kayan ita kanta taji dad'i, dan burinta kenan ta samu babban mutum ta aura, bata wani kalli kayan duka ba kwai ta shiga d'aki tayi wanka tasa kayan bacci sannan ta kwanta dan bacci take ji.
*Washe gari* da safe kiran Muzaffar ne ya tasheta, cikin magagin bacci ta d'auka ta aza a kunne da fad'in "hello."
"Amaryata, kuma uwar gidana, ina fatan kin tashi lafiya?"
Sai lokacin ma ta tuna shine fa wanda zata aura, zaune tayi tace "lafiya lau, ya kake?"
"In dai kina cikin k'oshin lafiya, to ai nima haka nake."
Tashi tayi ta fara rage kayan jikinta tace "ok, to yanzu zaka min uzuri na shiga bayi, dan tashina kenan."
Cikin shagwab'a yace mata "amma fa muryarki nake so naji."
A hassale tace "muryar lafiya, tashina fa kenan, so kake nayi fitsarin anan? haba nifa bana son irin haka."
Ji tayi ya fashe da dariya yana fad'in "ashe fitsari kike ji, kinga kuwa da zaran munyi aure, da kaina zan dinga jaye miki fitsarin nanπ."
Da sauri ta wani qaqaro amai tana fad'in "kai, wannan qazamtar fa? kaga sai an jima."
Kashe wayar tayi ta cilla saman gado tayi bayin da gudu, ko wanka ba tayi ba ta fito kai tsaye falo ta nufa, binsu take da kallo ganin mata zaune suna kallon kayan lefen, cikin risunawa suka ce "sannu da fitowa Hajia."
Kai kawai ta daga musu ta nufi madafa, had'uwa sukayi da Mamie da kula abinci a hannunta, "yawwa dama yanzu zanje na tasoki , zo muje to ga abincinki."
Hannunta ta kamo suka dawo falo suka zauna, buda kula tayi wani b'ata rai Khairat tayi tace "wannan fa? Mamie karfa zaki fara min wannan tashin hankalin ne? wallahi ba zan iya ba."
Dariya sukayi Mamie kuma tace "kwanciyar hankali dai Khairat, wannan shine gudumuwar da zan iya baki, dan nima shi kakarki ta bani."
Diba Mamie tayi tasa mata a baki, da qyar ta had'e tana b'ata rai sannan tace "haba Mamie ba dad'i ba."
"Yi hak'uri kinji shalelen Papa, ki saba da cinta kullum, kuma wannan fa had'in tattabaru ne, sai an jima zan miki na kaza."
Haka Mamie ta dinga bata tana rarrashinta har saida ta cinye wanda aka zuba mata sannan ta tashi ta shiga wanka.
*Tofa daga wannan rana* Khairat aka shiga sahun masu kurbe kurbe da tamne tamne, duk abinda Mamie zata had'a mata baya wuce na kayan itatuwa saboda sunfi lafiya, wannan kazar da tattabaru namiji da mace kad'ai ake hadawa da wasu sinadarin wajen dahuwarsu, abinka ga lafiyayya sai hakan ya d'an fara damunta saboda wasu itatuwa sun k'ara mata k'arfin sha'awa wanda da bata da ita, wasu kuma suna saukar mata da ni'ima.
Kowace safiya take jan foyer wajen gyaran jiki cikin k'ank'anin lokaci ta koma kamar sabuwar haihuwa, kuma haka ake kullum ba'a daina ba, yan mata da samari sun had'u sun tattauna abinda zasuyi, daga ciki akwai arabian night wanda ango yake bala'in son partyn , sai indian night wato b'angarenmu ba yan indiaπ, sai kuma party wanda za'a gayyaci kowa da kowa, sai cocktail daya zama kamar al'ada.
Kasancewar Khairat ta karanci zane hakan yasa ma ta zana kalar abayar da zata saka a arabian night d'in, amma kayan indian night Mammie tawa magana aka fara aiko mata da photuna ta zaba sannan Mammie zata taho dasu.
*Shirye shirye sunyi nisa sosai, kuma ango ya dawo sai dai Khairat tak'i yarda su had'u, hakan kuma ya dameshi dan haka ya fara tunanin ko da matsala ne.
Yau ta kama ranar *Asabar* kwana bakwai ya rage a daura aurensu, shiryawa yayi kawai yace shi zai tafi ya gant, mamarshi ce tace "Allah ya kiyaye hanya, amma dan Allah banda saurin hushi."
"Haba Mama, ina kusan zama angonta kuma zanyi hushi."
Yana fad'a yasa kai tare da rakiyar masu tsaron lafiyarsa sai gidansu Khairat....
_FAN'S JIHADI, ku kawo kud'in ankonku , dan yau zan siyo tawa, kuma babu wanda za muma alfarma ya shiga idan baya da anko musamman 'yan team d'in Umar Faruk, dan zasu iya b'ata mana taro.πππ_
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣7⃣
Babu kowa a falon kasancewar sanyin safiya ce, Mamie yau bata fito wajen girki ba, sai masu aikin kad'ai suke abinsu, ganin babu kowa yasa shi sallama da k'arfi, da sauri Saude ta fito ganin ko wanene yasata zube qasa tana gaisheshi, saida yayi qaramin tsaki sannan yace "ina Mamie?"
Murya na rawa tace "tana d'akinta bata fito ba."
"Khairat fa?"
"Itama bacci take."
Kamar mai ciwon baki yace "ok, jeki."
Tashi tayi ta nufi madafa tana fad'in "ikon Allah kenan, sai kuma Allah ya had'ata da daidai ita."
Shima sama ya haura d'akin Khairat, a hankali ya bud'a k'ofar yana kallon gadon da yake da tabbacin tana nan, (kunsan mutuniyar dama ba kwana take da manyan kaya ba) hakan yasa Muzaffar ya kusa kallon rabin sadakinshiπ, saboda wata irin riga ce bata da maraba da bras, sai kuma wandon rigar kad'an ya wuce mazaunanta, takowa yayi harya tsaya gaf da ita yana had'iye yawu masu nauyin gaske, da qyar ya lumshe idonshi sannan ya sake bud'ewa ya saukesu a kanta, hannu ya kai zai daddab'ata ta bud'e ido tare da juyawa, karaf idonsu suka sark'e dana juna, a zabure ta tashi zaune taja dara ta rufe jikinta tana mashi kallon tuhuma.
"Wannan wane irin jahilci ne, miye haka Muzaffar, ya zaka shigo min har cikin d'aki kana tab'ani?"
K'ara matsowa yayi yana fad'in "kinga Khairat dan Allah kiyi shiru, karki tara min jama'a, wallahi bada wata manufa na tai tab'aki ba."
"Dallah ni kamin shiru, ka fice min daga d'aki."
"Haba Khairat w...." katseshi tayi da fad'in "dallah ni nace k...." kuma sai tayi shiru saboda tuna abinda Hibba tace mata.
Hararanshi tayi ta turo baki gaba tace "to dan Allah kawai ka shigo min haka duk ka bani tsoro."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "kiyi hak'uri kinji. "
"To naji, wai mema ya kawoka nan? bayan nace maka ba zamu had'u ba har sai an fara shirya shiryen bikinmu."
"Kiyi hak'uri my Khairiri, wallahi na kasa hak'ura ne shi yasa, matuk'ar so nake na ganki sosai."
"To naji ni dai yanzu ka fita ka jirani falo zanyi wanka na fito."
Cikin wani shu'umin kallo yace "to muje na miki wankan mana."
Pillow ta dauka ta jefa masa tare da masa kallon kai shashasha kuma hamago ne, amma da yake hamagon ne na gaske saiya kasa fahimtar kallon, hannu ya mik'o mata tare da sake fad'in "kizo na rakaki to idan ba zaki yarda na miki wankan ba."
Saida ta had'e fuska sannan ta mik'a masa hannunta ta sauko daga kan gadon, ci gaba yayi da k'arewa surarta kallo ita kuma ko a jikinta, har saida ya kaita bakin ban d'akin sannan yayi murmushi yana cewa "insha Allah nan da rana kamar ta yau kin zama tawa, kuma daga wannan ranar ni zan dinga miki wanka."
Itama murmushin tayi tace "zaka dinga min, ko zamu dinga yi tare?"
Sunkuyawa yayi yace "yanda kike so gimbiya."
"To ka jirani falo ina zuwa."
Tana shiga shima ya bar gidan gaba d'aya ba tare daya jirata ba dan akwai abubuwa gabanshi, itama kuma ta jima bata fito ba bayan ta shirya ta fito falo, bata sameshi ba kuma bata damu ba, harkokin gabanta ta shiga yi bayan Mamie ta had'a mata kayanta tasha nasha taci naci, foyer ta nufa wajen gyaran jiki kamar kullum.
***************
Cikin farin ciki ya fito daga gida zuwa wajen aikinshi, tunda ya shiga yaga gungun su Ishaq sunata hira, saida ya tsaya bayanshi bai sani ba ya kai masa duka yana fad'in "iskancin banza, wajen neman kud'in naku kuka mayar kamar kasuwa?"
Dariya Ishaq yayi lokacin daya juyo ya kamo hannunsa yace "kai haba zo ka gani kaima."
Matsowa yayi shi kuma ya d'auko wata had'add'iyar shadda gizna kalar ruwan qasa ya bashi, hannu yasa ya karb'a yana kallo yace "na miye wannan?"
Saida ya kalleshi yace "ankon Hajia Khairat ne ta aiko manager ya kawo, kuma tace duk wanda bai siya ba to yasan sauran, dan tace tana buk'atar ganin kowa dake wajen nan ya hallara duka shagulgulan da za ayi."
D'orawa yayi da "kuma kasan halinta dai, k'aramin aikinta ta tsige mutum daga aikin nan, dan haka kayi sauri ka siya dan kwana hud'u ya rage a fara shagulgulan bikin."
Wata uwar harara ya zabga masa tare da jan tsaki ya cilla masa shaddar a qirji ya fita ya bar wajen, saida ya hau mashin d'inshi ya tambayi kanshi "ina kuma zaka je?"
"Gida." inji wata zuciyar.
Ai kuwa gida ya nufa da tunanin samun sauki, yana shiga a soro ya aje mashin d'in ya shiga ciki, duk da mutanen daya gani a farfajiyar gidan bai kula kowa ba yana shirin shiga d'aki mahaifiyarshi tace...
"Kai Umar faruk, lafiya ka dawo gida yanzu?"
A wahalce ya kalli Mamar yace "ba komai Mama, bana jin dad'i ne."
Zai wuce ta sake cewa "Umar faruk, ashe yarinyar nan za tayi aure wacce kuke aiki a masana'antarta, shine kuma baka fad'a ba, kuma kaga ko mahaifinka bana tunanin ua sani dan daya fad'a min."
Rai b'ace ya kalli Mamar yace "Mama kuma waya fad'a miki maganar nan?"
Kallon budurwar dake gefenta tayi tace " *Ruk'ayya* ce."
A zafafe ya kalleta yace "ke kuma gidan uban wa kika ji?" ya tambaya a harahen zarma.
Tuni Ruk'ayya ta fara rawar jiki saboda tsoro tace "wallahi yaya Umar nima a Whatsapp ne na gani ana d'ora photonta da akwati talatin da makullin mota,amma ni bansan komai ba."
Sama da qasa ya harareta ya rangada dogon tsaki sannan ya kalli Mama yace "wallahi shi yasa banso aka bar yarinyar nan ta rik'e wayar nan ba, kawai salon yara su lalace."
D'akinshi ya wuce zuciyarshi kamar zata kama da wuta, wani irin haushin kanshi ne yake ji daya takura kanshi akan tunanin wata banzar Khairat (a cewarshi), bai sake fita ba har saida Ishaq yazo gida ya sameshi da yamma.
Gaishe da matan gidan yayi kafin ya d'ora ma Mama da "Mama mutumin kuwa yana ciki?"
"Yana ciki Ishaq, yana sabon d'akinshi."
Dariya yayi ya mike yana fad'in "mutumin fa ba dama, kamar gobene auren nan."
Itama dariyar tayi tace "ka barshi kawai, a doleshi k'uryar d'aki yake so a fitar masa, kuma wuri ba zai isa ba, in dai baso yake na fita daga d'akina ba dan yayi k'uryar d'akin."
"A'a Mama ki barshi, dole zai hak'ura ai."
Yana shiga ya sameshi cikin falon d'akin wanda ke shafe kayane kawai babu, falon babba ne sosai amma babu wani d'aki a ciki, d'an k'aramin kewayene daga waje sai matsakaiciyar ban d'aki , gaisawa sukayi Ishaq ya d'ora da "kai haka ake? kawai saika sa kai kayi gaba kuma baka komawa, shi yasa ai na fad'a musu wallahi son yarinyar nan kake, dan inba...."
Katseshi yayi da fad'in "kai kai kai, dakata dan Allah, wacece nake so d'in?"
"Khairat mana."
"Mtssss, yanzu wannan sakaryar kake had'ani da ita, wannan mahaukaciyar yarinyar? gaskiya ka cuceni Ishaq, wallahi da zan san zuciyata na sonta, toda babu abinda zai hanani hukunta kaina ta hanyar da tafi kowace hanya zafi."
"Wace hanya kenan?" cewar Ishaq.
Shiru ya masa ya ci gaba da kallon d'akin shi kuma yace "to aini banga wani aibunta ba yarinyar, kaifa kasan *wacece ita*."
"Sanin wacece ita yasa ba zan iya yarda na bari zuciyata ta fara sonta ba, da bansan ita yar d'an giya bace ko kuma manemin mata, da ace bansan ita fiysararriyace wace bata d'auki cud'anya da maza ba a bakin komai, da ace bansan ita mai wulak'anta mutane bace, da ace bansan tana soyayya da arne ba, sannan da bansan itace yarinyar da namiji majiya k'arfi guda biyar suka sauke sha'awarsu a kanta ba, to da zan iya tunaninta."
Da mamaki Ishaq ke kallonshi dan b'acin rai ne kawai ya gani a idonshi da tafasar zuciya, girgiza kai yayi yace "wallahi wannan ba Umar Faruk d'ina bane, tabbas akwai abinda ke damunka kuma baka shirya fad'a min ba, Umar d'in dana sani yana da ilimin addini dana zamantakewar rayuwa, wannan maganganun bai kamata su fito daga bakinka ba, amma saboda b'acin ran da kake ciki yasa ka fad'esu, amma duk da haka ni ban yarda baka son Khairat ba, sai in har ka siyi ankon bikinta kuma ka halarci taron sannan na yarda."
"Wannan shi zai tabbatar maka bana sonta?"
"Sosai ma."
"Muje, muje ka rakani na siyo yanzun nan."
Kamar wasa Umar faruk ya shiga d'akinshi ya k'wamuso kud'ad'enshi suka fita, tare suka siye kuma suka biya suka bada d'inki, Umar harda siyan takalmi πkaji sai kace shine angon.
Saida dare yayi suka dawo gida, dama kuma gida biyu ne ya raba gidansu, k'arar mashin d'inshi yasa Baba dake zaune a d'akinshi dake farkon shigowa gidan yasa ya kira sunansa , bayan ya shigo nan ma dai maganar d'aya ce akan aure Khairat ne, sai dai shi Baba Papa ne yazo da kanshi ya gayyaci malaminshi a matsayin wanda zai wakilceshi ya bada auren Khairat, a tsorace Umar Faruk ya d'ago kai yace "Baba, wai kai zaka d'aura auren?"
"Eh, da wata matsalane?"
"A'a, zan iya shiga ciki? kaina ke ciwo."
"Ba damuwa kaje, amma ka sani dole zaku je wannan d'aurin auren, na fad'awa duka yan uwanka maza masu wayo , zamu tafi tare daku."
"K....kkk....kuma dai?" cewar Umar faruk.
"Eh, akwai damuwa ne?"
"A'a, saida safe."
Da qyar yakai kansa d'aki yayi kwance yana ji kamar yayi kuka, amma kuma yana tambayar kansa to kukun me kenan zaiyiπππ.
*****************
*Komai* na tafiya yanda suke tsarashi a haka kuma Khairat ta fara d'aukan haske saboda k'unshi da gyaran kai mai masifar kyau da aka yanyara mata gwanin sha'awa, ranar *laraba* aka fara da indian night, a ranar an rak'ashe sosai shagali yayi shagali, yayin da ya tara dubban mutane manyan yara da manyan mata, kusan kowa yayi qoqarin yin shigar indiawa, amma kana ganin amarya zaka ganeta saboda kayan data d'auka jar kala da golden, riga da siket ne hannayenta sun sauko akan damatsenta amma ta kamata sosai, sai k'aton siket d'in da yake jan qasa yasha duwatsu ga walk'iya, mayafin kayan ne aka d'ora mata akai, ba laifi gana gani zasu birgeka dan had'insu yayi, sai dai duk kyan Muzaffar Khairat ta takeshi ta shanye, haka akayita walima har aka buk'aci da amarya da ango su shigo fili su d'an taka, sai lokacin kad'ai nida ma chΓ©rie Hakeema da sister Chappa muka tsagaita da rawa muka ba Khairat d'inmu fili dan munsan tanan b'angaren gwanace ta qarshe.
Ai kuwa bata bamu kunya ba, dan kuwa wata waqa ce aka baza mata d'aya daga cikin film d'in *dilwale* mai taken *janam janam*, Muzaffar tsaye yayi amma fa amarya ta taka ba laifi sai lik'i da tafi da aka dinga mata, a haka aka tashi taron ango ya maida amarya gida shima suka wuce gida kowa yayi baccin gajiya.
_Har yanzu kunkumina ciwo yakeπ can naga yan team d'in Umar faruk ta taga suna lek'enmu muna yagar kaji, ah to ai dama na fad'a muku dan babu alfarma a wannan ranar_.
*Washe gari* ma sabon shiri aka d'auka na arabian night, abayar da Khairat ta zanawa kanta ta saka, sosai rigar ta dace da ita, dogayen hannuwa kuma matsatsu hakama ta kamata wajen qirki abinda yayi kunkuminta, sai dai daga nan kuma saita bud'e sosai har tana jan qasa a baya, kwalliya akama rigar sosai ga d'an kwallinta ma, tana d'orawa ta fito kamar balarabiyar gasken, dogayen takalmi aka d'auko mata zata saka kawai taga ba zata iya ba, in da take ajiyar takalmin ta bud'a sai idonta ya sauka akan wasu tapet masu kyau masu kamar na maza , murmusawa tayi data tuna ranar farko da manager ya shigo tare da Umar Faruk suka gabatar mata da takalmin kuma tace su bar mata su, tana sawa suka tsaya a qafarta d'aram gwanin sha'awa dasu, haka suka nufi hall d'in taron amma idon Khairat sun kasa barin takalmin nan, yau ma haka akayi wannan taro aka ci aka sha baja baja (an samu na banza ba), 22:15 kowa yasan in da dare ya masa, sai dai tun kafin abar taron photon amarya da ango suka rigasu fita daga wajen, masu d'orawa a fecebook, Whatsapp, Instagram, kai da sauransu, cikin qanqanin lokaci sai photunan suka shiga duniya, maganganu iri iri wasu na yaba dacewarsu, wasu na yaba kyawun matar, wasu na yaba kyawun namijin, wasu na fad'in ai an mata fyad'e, yayin da maza suka fara tabka mahawara a shafukan sada zumunta iri iri, wasu na cewa ya kyauta kuma yayi jarumta tare da *Jihadi*, wasu kuma suna ganin ba zasu iya ba kuma shima da yayi bai birgesu ba.
*Al'amarin aure kenan, dole sai ace nan yayi daidai, nan baiyi daidai ba, mutum d'ari na iya maganar aurenka, amma da wuya ka samu goma da zasu ce Allah dai ya sanya albarka, kashi saba'in masu kushewa ne, ashirin masu yabawa, goma ne masu addu'ar fatan zaman lafiya, Allah ka rabamu da sharrin mutane da aljanu , Allah ka bamu ikon yin komai da kai.π*
A cikin haka Allah ya had'a Umar Faruk da videon Khairat a Indian night tana rak'ashewarta, wanda anan ma mahawarar ake , wai idan kaine ya za kayi azo party amaryarka na wannan rawar kamar baindian gaskiya, wasu na fad'in kafin a d'aura auren zasu ce sun fasa, wasu kuma na cewa aiba komai bane zamani ne, yayin da Umar Faruk ya sake jin haushin Khairat sosai a zuciyarshi, tunanin yake yanda zaije partyn gobe da aka ce dole suje kuma gashi manager ya rok'esu akan suje danshi.
Photo d'aya ya zubawa idanu shine in da take cikin abaya ta yane kanta, meuk-up d'in da tasha ta sake canza mata kammani tayi bala'in kyau, saika santa zaka iya ganeta abinka ga farar fata, da alama bata san an d'auki photon ba saboda babu murmushi a fuskarta kuma bata kallon mai d'aukarta, kanta na kallon qasa baka iya ganin idonta sai golden da pink d'in eyshadow d'in dake saman idon, zoom d'in photon yayi yana kallon kyawun fuskarta, a hankali furta "dama labarina dake gajere ne, gashi ya datse tun bamu kai ko ina ba." da kallon wannan photo har bacci ya d'aukeshi.
A b'angaren Khairat kuwa har tayi shirin kwanciya bacci Mamie ta shigo da 'yan tame tamenta, tun kafin tayi magana Khairat tace "ohh Mamie, wai dan Allah abun nan ba zai qare bane? nifa wallahi na gaji da shan kayan nan suna takura min."
Cikin dariya Mamie tace "kiyi hak'uri kinji, keda nake tunanin na had'a miki su idan ki kaje can kiyita anfani da kayanki."
"Wa, ni? ba zan iya Mamie, na yanzu ma wallahi komawa za kiyi dasu."
Kafad'arta ta dafa tace "Khairat, burin kowace uwace, taga yarta tayi rayuwar farin a gidanta, kiyi hak'uri nasan ba zaki ji dad'i ba amma ya zama dole na tuna miki, 'yata, akwai wani abu mai mahimmaci da kika rasa wanda ba zaki iya yiwa mijinki tink'aho dashi ba, amma duk da haka ina so naga kin samu kyautar da ake samu a daren farko."
"Kinsan wace irin kyauta ce?"
A hankali Khairat ta girgiza kai alamar a'a, murmushi tayi tace "wasu na bada kyautar kud'i, kadara ko tasa albarka, amma ni ina so a daren farkonki , mijinki ya mallaka miki kanshi ke kad'ai, ina so ya mallaka miki zuciyarshi ki zama mai alhakin kula da ita, duk abubuwan da kika ga ina baki, wannan ne sirrinsu, ki rik'esu da kyau su zama sirrinki, duk in da mijinki zaije to wallahi zai dawo matuk'ar kin rik'esu, natural ne ga lafiya a jiki ga dad'i a baki, kuma zasu dinga tsumaa jikinki koda kin zama raguwar mace, to zasu jima a jikinki ba tare da kin rage d'and'ano ba, idan kuma kina yi akai akai, to kullum d'and'anonki zai dinga haukata mijinki tamkar qaramin yaro ."
Kumatunta ta dafa tace "kinji ko 'yar albarka?"
Kai ta sake girgiza alamar eh, Mamie na bata ta amsa ta kifa kai saida ta shanye sannan ta ajiye cup d'in Mamie ta d'auka sukayi sallama ta bar d'akin zuciyarta fari qal.
*Mamie nima na rik'e sirrin nan, shi yasa ban fad'a musu baπ, nifa har kyautar yaran da zan haifa aka minπ.*
*Washe gari* haka aka tashi da sabuwar hada hada kasancewar gobe d'aurin aure, bak'i na nesa dana kusa sun hallara kuma kowa na shirin tafiya partyn da za ayi na kowa da kowa, yamma nayi aka fara tafiya bayan wankan da amarya ta d'auka cikin shadda irinta ango, sunyi masifar kyau masha Allah, yau kam hall d'in cika yayi sosai dansu Umar Faruk ma na hangosu da sauran ma'aikatan, da qyar ake iya ganin amarya da ango saboda masu d'auka da waya nayi masu camera ma nayi, haka ake taro har mc ya kira amarya da ango suka yanka babban cake d'in da aka masa siffar amarya da ango , suka ba junansu a baki sannan suka shigo fili suka fara d'an rausayawa, naira tayi kuka domin wasu kamar a cikin shara suka deb'ota yanda suke zubawa ango da amarya, Umar Faruk ya kasa d'auke idonshi akan Khairat amma da kallonshi ya kai ga Muzaffar, π€£sai naga ya bishi da harara da dogon tsaki, wannan tsakin ne ya ishi Ishaq yace su tafi su tafi tunda dai an gama ai, ko ruwa baisha ba bare jus sai Ishaq yayo oder abinshi a leda ya taho dasu.
*Can naga yan team d'in Umar Faruk suna kokawa wajen d'aukar kwalban jus d'aya, amma da yake team d'in Khairat akwai imani, haka muka cika musu jakunkunansu da kayan k'walamπ*
_Grp JIHADI FAN'S._
_Grp Queen Bee_
_Grp Qanin miji fan's_
_Grp Nida yayah Al'ameen 1 & 2_
_Grp Beneficiale writers_
_Grp yan Baiwa_
_Grp sharhi da tambayoyi_
_Grp Na baki rayuwata_
_Grp BK fan's_
_Grp Raheenat m kk fan's_
_Grp Online writers_
_Ummu Fatima conversation_
_Grp Mom sultan novels 1_
_Grp rayuwar gidan kawuna_
*Hak'ik'a kun min kara, dan kun cashe sosai fiye da tunani na.*
π€π€π€π₯° *ANA TARE FAN'S*
******************
Koda ya shigo gida kai tsaye d'akin mahaifiyarshi ya nufa sai dai tuni sunyi nisa a bacci, kamar yanda ya sani dama ko yayi dare to abincinshi na gefen mahaifiyarshi, kwanan ya d'auka ya zauna kusa da ita ya fara ci yana kallonta tana baccinta, sai dai baici mai yawa ba ya barshi ya fito daga d'akin, d'akinshi ya shiga ya cire kayanshi ya fito zai shiga wanka, yayanshi ne *Abbakar* ya shigo shima bayan ya yiwa mashin d'inshi wajen zama, hannu ya bashi suka gaisa yana fad'in "yadai abokina, ina ka shiga ne haka?"
Cikin sanyin jiki Umar Faruk yace "wallahi abokina ina nan, kai dai ka b'ace, waccen matar ta b'oyeka."
Nunashi yayi da hannu yace "kai ka fita idona, ina ruwanta kuma."
Bokitin ya d'auka ya nufi ban d'akin yana fad'in "idan ka shiga kace mata na dawa ta zo ta gaisheni."
"Lallai ma, sai dai ka kama layi to harta gama dani, kasan ance in ana dara fidda uwa ake."
Baice komai ba saboda harya fara cire kayan jikinshi, yana fitowa kuma yayi alwala ya shiga d'akinshi, doguwar riga yasa ya kabbara sallah ya fara nafilfili har saida kiran sallah asuba ya riski kunnuwanshi sannan ya dakata, fitowa yayi saboda jin motsin mutane sun tashi suma , tare suka nufi masallaci da yan uwanshi da kuma mahaifinsu, bayan sun idar da sallah suka dawo gida, kuma kamar yanda mahaifin nasu ya koya musu wasu karatun littafi mai girma suka fara, wasu kuma tasbihi da hailala da kuma istigfari, Umar Faruk ma karatu yayi saida 06:00 tayi sannan ya rufe ya d'an kwanta kafin k'arfe 09:00 auren Khairat.
*Daga gobe ne fa*π
********************
*Yau ne fa*π
Yau ta kama ranar *asabar* ranar d'aurin aure, Umariri ma πbaiyi qasa a gwiwa ba wajen shiryawa kamar yanda yaga yayanshi Abbakar da k'annanshi guda biyu *Usman da Aliyu* suna yi dan cika umarnin mahaifinsu, wani abun mamaki shine, haka kawai Umar Faruk kejin wani nishad'i da farin ciki na baibaye mishi zuciya, ga murmushi mai matuk'ar tsada daya kasa barin fuskarshi, duk da yana d'an jin fad'uwar gaba da kuma tsoro, amma dai yafi farin ciki hakan kuma yasa ya ta'alak'ashi da karatun da yayi ne dan yafi komai samarwa mutum da nutsuwa.
Cikin wata shaddarshi gizna fara ya shirya wacce suka d'inkata a bikin abokinsu , kasancewar ba mutum ne mai sha'awar manyan kaya ba yasa tun ranar bai kuma sawa ba, kamar yau ne ya fara saka shaddar saboda yanda take d'aukar ido, dogayen hannuwa ne da ita da kuma wasu da aka aza daga iya kafad'u hakan zaisa kayi tunanin rigar ninki biyu ce, bak'ar hula takalmi qafa ciki bak'ak'e da agogo ya d'aura kamar dai yanda aikin rigar yake, shi kanshi yasan ya had'u masha Allah sai tafiya kawai.
Yana fitowa ya samu duka sun shirya suna tsakiyar gidan, rufe d'aki yayi ya kallesu yace "muje ko."
Duka da kallo suka bishi saboda ganin bak'on al'amari a tare dashi, ganin kallon yayi yawa yasa Umar faruk sake cewa "muje ko."
Baba ne yace "wai Umar faruk kaine da wani murmushin haka mai tsada, meya faru ne haka kake farin ciki?"
Murmushin kawai ya ci gaba dayi ba tare da yace komai ba, Abbakar ne yace "wannan farin cikin dai akwai wani abu a qasa gaskiya, mutumin da kullum fuska a had'e."
Cikin dariya yace "dan Allah ni ku wuce mu tafi, lokaci fa tafiya yake."
*Saratu* matar Abbakar dake zaune tare dasu Mama a tsakar gidan ce tace "wannan sauri da kake Allah yasa ba wani abun kake shiryawa ba."
Kallonta yayi yace "baki iya gaida miji ba amma kin iya katsa landa, to me zan shirya ni kuma?"
Cike da zolaya tace "tona sani ko amaryar zaka sace , ko kuma kasa a d'aura auren da kai."
Dariya duka aka saka saishi daya ce "wata d'iyar robace da kike tunanin haka ta faru?"
Mama ce tace "yarinya fa tsadane da ita tunda ita ta...." sai kuma tayi shiru.
Ke Ruk'ayya uwar d'umi sai kika ce "ita ta tallabeshi da mari fa duk wannan d'acin da yake mana a gida."
Da gudu tayi d'aki saboda biyota da yayi duk da kiranshi da Mama keyi saida yakai , yana shiga ya tallabeta da marin itamaπ sannan ya kama kunnenta ya murd'e yace "wallahi na sake jin bakinki manya na magana, saina lahira ya fiki jin dad'i."
Kuka take sosai shi kuma yana fitowa ya kalli Saratu yace "ki shirya tarban sabuwar amarya."
Fita sukayi suka hau taxi dukansu suka nufi d'aurin auren, dandazon jama'a manya da qanana masu mulki masu sarauta, masu kud'i na nesa dana kusa ga kuma bak'i daga k'asashe da dama na gida dana waje, ganin irin d'ubbin jama'a yasa Umar Faruk jin haushi ma ya kamashi, haka dai suka samu suka kutsa tare da mahaifinsu harya shiga babban masallacin dake d'an nesa da gidan su kuma suka tsaya daga bakin masallacin.
Unguwar *Presidetielle* tank'am take da mutane har lokacin da shugaban...ya iso wajen, haka aka bud'a masa hanya jami'an dake tare dashi suna kakkareshi harya shiga cikin masallacin, bayan sun gaisa da mutane suka fara qoqarin abinda ya tayasu a wajen, duk da haka Umar faruk baya jin komai sai wannan d'an fad'uwar gaban wanda farin ciki yafi yawa a ciki, Ishaq ma zolayarshi kawai yake manager kuma yana musu dariya.
********************
*A b'angaren* Muzaffar ma farin ciki yake da d'okin zuwa wajen d'aurin auren, ya gama shirinsa tsaf ya d'auki babbar rigarshi zai saka amininshi da suke kira da *Basta* ya kalleshi yace "sai farin ciki kake da zumud'i zaka samu Khairat, amma mu kuma bak'in ciki muke dan koba komai munsan mun kusa rasaka kenan har abada."
Cike da mamaki yace " Basta, yanzu dama bak'in cikin aurena da Khairat kake? amma gaskiya ka bani mamaki."
"Ba haka bane abokina, ina nufin ina bak'in cikin rasaka da za muyi."
"Ban gane ba, rasani kamar yaya?"
"Nasan kasan komai game da Khairat, amma sai gashi ka yarda da aurenta kamar wanda mata quka k'are a gari, baka tsaya kayi bincike ba bare ka tabbatar da lafiyarta, haba abokina kayi tunani mana ka gani, kai da kanka ka fad'a min mahaifin yarinyar nan ne yaje ya samu mahaifinka da maganar aurenku, kenan akwai wani abu a qasa."
Shiru ya d'anyi yana tunani sai dai bai iya tunani komai ba, a hankali ya tambayeshi "kamar me kenan?"
Shu'umin murmushi yayi yace "kasan ko suwaye suka mata fyad'e, ai kuwa ba zata rasa cuta mai karya garkuwar jiki ba, ko kuma dai wata cutar ko kuma ciki."
"Ciki kuma? amma ai ba yau bane aka mata fyad'e, wata nawa aka d'auka da cikin ya kasa bayyana har yanzu?"
"Kai baka san mata ba wallahi, amma idan baka yarda da abinda na fad'a maka ba , to ga wuri nan."
Yana fad'a ya fita ya barshi dan yasan zaifi yin tunani da kyau, haka ne kuwa ya faru ya jima yana tunanin abinda ya fad'a har lokaci ya tafi sosai, agogon daya kalla yasa shi d'aukar wayarshi saboda ganin 08:57, shugaba ya kira yana d'auka cikin sauri yace "Papa an d'aura auren?"
Murya qasa qasa cikin dariya yace "wai saurin me kake? harna bayar da sadakinka fa, d'aurawa kawai za ayi."
"To a dakatar da d'aurin auren."
"Me , kasan me kake fad'a kuwa? akan me za'a dakatar?"
_Hummmmm Haleemat addu'arki ta kama mu._
"Papa kawai a dakatar da auren nan wallahi na fasa."
"Wai kasan me kake fad'a kuwa, baka da hankali ne? yanzu haka fa d'aura auren nan ne za ayi."
"To ni dai nine za'a d'aurawa auren, kuma nace na fasa dan haka ba zanyi ba."
Shugaba ne ya saci kallon Papa da bakinshi ke bud'e sannan tasa babbar rigarshi ya goge zufa, aje wayar yayi yana kallon mutane malam ne yace "to zamu iya farawa yanzu."
Shirun da shugaban yayi yasa aka fara shirin d'aura aure, sannu sannu murya na rawa yace "a dakatar da d'aurin auren."
Kallonshi akayi amma babu wanda yayi magana , "Muzaffar ne ya kirani yanzu, kuma yace a dakatar da auren."
Papa ne da gabanshi ya fara dukan uku uku yace "a dakatar kamar ya, gaba d'aya za'a dakatar ko kuma na wani d'an lokaci?"
"Eh to, nidai yace min a dakatar ya fasa baya so."
Da sauri Papa ya dafe kanshi, yana jin mutanen cikin masallacin na hayaniya amma bai iya cewa komai ba, kusan minti ashirin aka d'auka wasu na waje sun fara qaguwa akan meke faruwa, na cikin masallacin ne da suka tabbatar ba za'a d'aura ba suka fara fitowa, shugaba ma kallon Papa yayi yace "kayi hak'uri Mani, wallahi bansan meya faru ba,amma idan na koma gida zanji meye matsalar."
A wulak'ance Papa ya kalleshi yace "ba damuwa, ba saika takurashi ba, allah zai kawo mana d'auki."
Fita shima yayi ya rage daga Papa da malam sai yaya Suleiman da sauran k'annan Papa, su Umar Faruk dake tsaye k'ofar masallacin ne suka shigo ciki, wajen malam suka nufa suna tambayar lafiya har yanzu ba a d'aura auren ba, a raunane malam yace musu "yaran ne ya fasa."
Kallon kallo suka shiga yi suma har muryar Papa ta daki kunnuwansu yana fad'in "bansan me zance mata ba, tafi kowa damuwa da auren nan, tana matuk'ar son ganin Khairat tayi aure, yanzu gashi ba lafiya ne da ita ba, watak'ila idan na fad'a mata hawan jininta ya tashi, Khairat ma na fama da rashin lafiya, itama zata iya shiga matsala duk da dai nasan biyayya ta mana ta yarda zata aureshi."
A hankali ya furta "Allah ka kawo mana agaji." sai kuma kuka ya k'wace mishi, ganin haka yasa hankalin Umar faruk tashi babba na kuka a gaban idonshi, akan abinda zai iya taimaka masa, dole ne ma yayi wannan *Jihadin* kodan ceton mutunci da rayukan wasu, watak'ila kuma labarinshi da Khairat dama baizo qarshe ba, kuma zai iya yiyuwa akwai wani *b'oyayyen al'amari* dasu basu sonshi ba .
Matsowa yayi kusan Papa ya rik'e hannayenshi yace "yallab'ai, ni ba kowa bane, kuma ba d'an kowa ba, bansan ko zaka iya bani auren 'yarka ba."
Take farin ciki ya lullub'e Papa ya rumgume Umar faruk yana ci gaba da kuka, godiya kawai yake masa yayin da mutane suke mamaki malam kuma yana farin ciki haka ma 'yan uwanshi.
Anan take aka d'aura auren *UMAR FARUQ AHMAD ADAM* da *KHAIRAT MANI BUKAR* Papa da kanshi ya wakilci Umar Faruk, anan ango ya tattara duk abinda yake da aka biya sadaki, malam kuma ya wakilci Khairat.
_Farin ciki_πππ€barkanmu 'yan uwa, musha biki lafiya.
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
*ALHAMDULILLAH KASIRAN, ALHAMDULILLAH ALA KULLI HAL*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣8⃣
Ana gama d'aurin aure sai kuma labari yasha bam bam, amma a wajen Papa farin cikine zalla yake saboda faruwar hakan, Papa ne ya keb'e da ango da Abbakar da kuma Baba yana tambayar lokacin da zata tare, Umar Faruk dai cewa yayi duk lokacin da suka shirya, amma Baba yace a basu sati d'aya, sosai Papa yaji dad'i ya kuma ce ya bawa Umar Faruk kyautar gidan da zasu zauna da kuma mota, murmushi Umar faruk yayi yace "wallahi bana buk'atar komai, shi yasa ma na fad'a maka koni waye dan matsayinmu ba d'aya bane, ba zan bar gidanmu ba, kuma ina da wajen da zan ajiyeta, idan kuma taga hakan bai mata ba, toni banda matsala tun kafin tafiya tayi nisa zan iya sss..."
Bai k'arasa ba saboda taushe mishi baki da Abbakar yayi, Papa ne yace "ba komai Umar faruk, ai ba sai ankai ga haka ba, ko rumbu ka ajeta dole ai zata zauna, mudai muna godiya sosai."
Papa ne yama Umar faruk iso a cikin gida yaga sauran iyaye da kakannin Khairat ya gaishesu, abinka ga idan Allah ya aiko abu, duk uwayen masu hankali idan suka kalli Umar Faruk sai suji ya kwanta musu a rai saboda hankali nutsuwa da kunya, haka suka kamo hanyar komawa gida yana wasi wasi yana ji kamar yayi kuskure hukuncin daya d'auka.
******************
*Khairat* na d'aki tare da k'awayenta tanti (aunty) Safiya ta shigo ta fita da ita bayan ta rufeta ruf da daren amare bleue wacce ta mata kyau, babban falon da Papa ke sauke manyan bak'inshi suka shiga, duk da kanta na qasa kuma cikin dara amma saida taga yawan mutanen dake d'akin, gaba d'aya kannan da yayun mahaifinta ne, Mamie kuma dama ita d'aya ce ga iyayenta, hakan yasa sai Safiya da *Ramlatou* itama cousine d'inta ce, sai kuma matar margayi babansu Papa da kuma Mammie, zaunar da ita tayi a tsakiyarsu sannan itama ta zauna.
*Nan fa* aka fara sambado ma Khairat nasihoji ta ko ina bayan sun fad'a mata yanzu ita ba budurwa bace mai aure ce, kuma ita ba matar Muzaffar bace, matar *Umar Faruk ce*, an jawo mata ayoyi hadisai da kuma karatun *duniya*, sosai nasihar ta shiga jikin Khairat sai gata da kuka tare da bawa kowa dake wurin hak'uri na ayafi juna, dan duk rashin kunyarta bata kai tama mutanen dake wajen ba saboda girma da matsayinsu gareta, haka suka bita da sa albarka bayan ta musu alk'awarin bin Umar Faruk sau da qafa, tanti Safiya ce ta mayar da ita d'akinta.
Tunda ta zauna ta fara wani sabon kuka dan babu yanda za tayi ne kawai ta amsa musu, amma ko kad'an Umar Faruk baya da tsari irin na mazan da take so (a cewarta fa)π, gashi kuma baya da komai hasalima a qarqashinta yake samu, to tayaya zata rik'eshi a matsayin miji, gaskiya zata hak'ura taje gidanshi danta musu biyayya, amma dole zata dawo dan rainine ma a had'ata da wani wai Umar Faruk, haka dai bayan 'yan d'aurin aure sunsha lagwadarsu wasu har sun tafi da guziri, aka fara biki gadan gadan aka sha casu sosai.
Tun yamma mutane suka fara watsewa zuwa dare kuma babu kowa sai bak'i da suka zo, kowa ya kwanta dan yayi bacci ya huta gajiya amma banda Khairat dake tunanin yanda rayuwar aurenta zata kasance, yanda taga safe haka taga rana ba tare data rintsa ba, kiran sallah asuba kad'ai yasa ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta kwanta rama baccin da bata samu tayi ba.
******************
*A b'angaren* Umar Faruk kuma suna shiga gida yanda duk suka shiga da kazar kazar amma banda shi yasa mahaifiyarshi ta fara tambayar lafiya, fad'a mata yayi ita da yan uwanta (matanshi guda biyu) su sameshi d'akinshi, ba b'ata lokaci suka hallara tare da Abbakar da Umaririπ, nan Baba ya fad'a musu abinda ya faru sannan ya d'ora da "wannan na tabbata itace k'addarar yaranku, kuma wannan abun *rubutatten al'amarine* da ubangiji ya rubutashi tun kafin a samar dashi kanshi Umar d'in, dan haka ku shirya tarbar sarakuwarku ban da rana irin ta yau insha Allah, sannan ku saka musu albarka."
Saida suka gama jimami sannan mahaifiyarshi ta sauke ajiyar zuciya tace "gaskiyane malam, kuma insha Allah ba za'a samu matsala daga garemu ba, kuma muna musu fatan alkairi Allah ya basu zaman lafiya."
"Ameen ameen." cewar malam kafin ya kalli sauran yace "ku kuma me zaku ce?"
Tab'e baki *Sa'a* tayi tace "ah to me zamu ce, tunda kun riga da kun gama yanke hukuncinku."
Mik'ewa tayi ta kama hannun *Maimuna* tana fad'in "nifa ba zan iya zama wajen nan ba."
Itama Maimuna saida suka mike ta kalli Umar Faruk da kanshi ke qasa shi abin duniya ma ya dameshi tace "wallahi dai kayi abin kunya, in banda kwad'ayin dukiya ta uban yarinyar nan, ince kaine nan kazo kwanan baya kana huci akan ta mareka kuma ka rama, shine yanzu dan tsabar rashin zuciya wai kai uban taimako ka taimaketa, kai yanzu ba abin kunya bane a wajenka ace ka auri macen da wasu garada suka raga?"
Sa'a ce tace "ke rabu dashi dan Allah, yana tunanin zai samu abin duniya shi yasa, amma ka sani ba lallai ka mori abinda za'a baka ba, dan cutar da waccen ya guje ma kai zata sama, wannan itace k'addararka."
Bushewa sukayi da dariya suka tafa hannu suka wuce abinsu, ba sabon abu bane wannan dan haka babu wanda ya dama a cikinsu, Baba ne yace "Umar Faruk."
D'agowa yayi ido jawur kamar zai fashe da kuka yace "na'am Baba."
"Kayi hak'uri kaji, wallahi Allah ba zai barka haka kawai ba saiya dafa mata, kuma ni nayi farin ciki da abinda kayi, kuma nayi alfahari da kai a matsayin D'ana, Allah ya maka albarka."
"Ameen Baba."
Mama ce tace "to a ina zasu tare?"
Baba ne ya kalli Umar Faruk d'in shima kallonshi yayi, cikin muryar tausayi yace "Mama ba zan iya barin gidan nan ba, idan sunga nan ya musu, to su kawota idan kuma ba haka ba, to gaskiya sai dai mu rabu, danni dama kawai saboda na fitar dasu daga halin da zasu shiga nayi."
Mama ce tace "haba Umar Faruk, me yasa zaka fara maganar rabuwarku tun yanzu, bana so ka daina, kuma ba komai ai sai a qarasa gyara abinda ya rage, idan har ya musu saisu kawota nan d'in."
Abbakar ne yace "Mama, saida fa mahaifinta yace zai bashi gida da mota, amma yaron nan da taurin kai yak'i amincewa."
Umar Faruk ne yace "idan na amince na amsa kenan me nayi? me kake so al'umma suce a kaina? na aureta saboda dukiya? to wallahi babu abinda mahaifinta zai bani a duniyar nan na amsa, ni taimako nayi *jihadi* nayi na auri 'yarsa, dan haka bana buk'atar komai daga gareshi."
Tashi yayi ya fita daga d'akin Baba kuma ya kalli Abbakar yace "nifa naji dad'i da bai karbi komai ba, dan yanayin haka jama'a za suce dama abinda yasa yayi taimakon kenan, duk da bansan yarinyar ba nasan dai tana da rawar kai, kana ganin idan ya amshi wani abu daga mahaifinta zata yarda ya tank'warata a matsayinshi na mijinta?"
A hankali Abbakar yace "kuma hakane gaskiya, zata rainashi ne ma."
Mama ce tace "nidai wallahi a tsorace nake, dan zamanshi da yarinyar nan fa akwai matsala."
"Wace irin matsala kuma?" cewar Baba.
"Kaifa kasan halin Umar Faruk da zuciyar tsiya, ina jin tsoron yanda zasu zauna gaskiya ba tare da sun samu matsala ba."
"Kinga dan Allah, ki cire tsoro a ranki sannan ki bishi da addu'a, insha Allah komai zaiyi daidai."
"To Allah ya yarda."
Baba ne ya sake cewa "yanzu to me zaku shirya? biki za kuyi ko walima."
"Kuma dai?" inji Mama.
Cikin dariya Baba yace "ban gane kuma dai ba? kina ganin zamu zauna hakane ba muyi komai ba bayan amaryar da muka samu a sauk'ak'e, kema kinsan dole za muyi koda walima ce mu godewa Allah."
Abbakar ne yace "ina ga ayi walimar zaifi, kunga sai ayi wa'azi ma tare da musu addu'ar zaman lafiya."
Mama ce tace "gaskiya kam shawarar tayi, to yaushe kenan?"
Baba ne yace "ayi ranar juma'a, tana gobe zata tare."
"To Allah ya nuna mana."
"Ameen." Baba da Abbakar suka amsa.
Suna fitowa Abbakar yaga matarshi a tsakar gidan tana shirin d'ora abincin rana , saida ya tsaya gabanta yace "ashe haka bakinki keda k'arfi, lallai Allah ya miki baiwa, tunda gashi abinda kika fad'a ya faru."
Duk da gabanta ya fad'i dan bata fahimceshi ba haka tace "lafiya, meya faru, mena fad'a kuma?"
Murmushi yayi yace "da zamu fita ba kince Umar faruk zai sace amarya ba ko a d'aura dashi?"
Dafe qirji tayi da k'arfi tace "me Umar d'in yayi?"
Dariya yayi ya nufi kewayensu dake kusa da d'akin amaryar Umar Zubyπyana fad'in "dashi muka d'aura auren."
Wata irin bud'a ta rangada data sashi tsayawa cak yana kallonta, wato ita farin cikinta ma harya kai haka, wucewa yayi ita kuma da gudu ta lek'a d'akin Umar daya cire kayan jikinshi ya kwanta, amma ganinshi ba riga yasa ta dawo baya ta koma ga aikinta.
Umar Faruk kuma in banda tunanin irin kuskuren da yayi babu abinda yake, ji yake kamar fa ya sauke ma kanshi nauyin daya d'auka ya aza ba tare da an tilastashi ba.
Tunda kannanshi suka dawo daga islamiyya aka fad'a musu suma dai murna suke yayansu yayi aure, nan kuma Mama ta siyo goro ta bawa yaran suka dinga rabawa makota ana fad'a musu Umar ne yayi aure, haka ma a waya Mama tasa Rukayya da Ali suna kiran yan uwa suna fad'a musu, wani yaji dad'i wani yaji haushi, dan ma ba'a fad'a musu wacece amaryar, duk da a kurarran lokaci ne amma zama lafiya da mutane da Mama keyi yayi tasiri sosai a yau, dan gidan turuwa aka dinga yi ana zuwa tayasu murna, Umar Faruk kuma ganin ba za'a barshi ya huta ba yasa ya sake shiri ya fita zuwa gidansu Ishaq dake kusa dasu.
*****************
Tunda Ruk'ayya ta kira tanti *Ma'u* (Mamar Zuby) ta fad'a mata ta fara bala'i tun a waya, ganin haka yasa Ruk'ayya kashe wayar taci gaba da kiran wasu, duk da haka bata hakura ci gaba tayi da masifa ita kad'ai Zuby kuma da taji meya faru kuka ta fashe dashi, Mama ko nata bala'i ko sauraronta ba tayi ba, jin kukan nata yayi yawa yasa tace,
"Dan ubanki rufe min baki kafin inci uwaki , yar banza kawai duk bake kika jawo ba, Umar Faruk wace irin jaraba ce baiyi ba ki bari ayi aurenku amma kika k'i yarda, waike sai kin gama jarabawarki, to yanzu gashi nan ya samu dama kuma yayi anfani da damarsa, yanzu kafin wata biyu yayi a d'aura aurenki dashi ita lokacin ta fara laulayin ciki, kinga ta riga ta tsere miki."
Zaby na jin haka ta sake fashewa da kuka tace "na shiga uku Mama, yanzu Umar faruk saiya had'a jikinshi da wannan tsohuwar kilakin."
"To me zai hana, macece fa kuma shi namiji, namijin ma rik'akk'e.
"Wayyo Allah, dan Allah Mama ki taimaka min wallahi ba zan iya jura rasa Umar Faruk ba, Mama kinsan ina sonshi sosai, bana so wata ta rab'eshi ma bare harya had'a jikinshi da wata."
"Uwarki ma, yo wane irin taimako zan miki? ai kin riga da kin cuci kanki."
"Dan Allah Mama kiyi hak'uri." kwance tayi tana kuka hakan yasa taji ba dad'i, tadata tayi ta zauna tace "kwantar da hankalinki kinji, Umar fa d'an uwanki ne kuma naki ke kad'ai, sai kinso ne zaki bashi dama harya kusanci wacce karuwar sauran sojawa (da yake Zuby ta fad'awa Mama komai akan Khairat d'in tun ranar da Umar ya d'aga mata murya akanta.)."
"Kamar ya Mama, ban fahimta ba?"
Murmushi tayi tace "idan da zaki yarda da sai nace a d'aura aurenki dashi ranar juma'a da za ayi walima, to daga nan fa sai labari ya fara shan bambam."
Murmushi ne ya bayyana kan fuskarta tace "da gaske Mama, kina ganin Umar zai yarda ya aureni ranar juma'a?"
"Umar Faruk d'in banza, ni uwanshi nake iko dasu, dan haka kwantar da hankalinki tsaf za'a d'aura aukenku."
"Wallahi Mama na amince, danni bana so na rabu dashi."
"Ba zaku rabu ba, amma fa ki sani ba zaki tare a gidansa ba har sai munga kamun ludayinshi a matsayinshi na me mata biyu, kinga zaki samu damar raba tsakaninsu ta zaman da za kiyi anan, sauran karatun kuma na biya miki shi daga baya."
Alk'awari ta mata gobe za taje gidan ta sanar dasu halin da Zuby take ciki, dan haka kawai a d'aura musu aure.
π€π€π€ _Mata biyu_
*********************
*Muzaffar* manyan duniyaπ wallahi dariya yake bani,π abokananshi na zuwa gidan suka fara balbaleshi da masifa, wannan bai dameshi kamar da wani yace "dallah ku rabu dashi, tunda shi bai aureta ai wani ya aureta ko."
Da firgici ya kalleshi yace "me kace, wani fa ya aureta?"
"Kwarai, wani ne a cikin taron auren yayi *jihadi* ya rufa mata asirin da kai kake kokarin tona mata, kuma yanzu Khairat ta zama *matar Umar Faruk*, dan haka zaifi maka kaje ka samu mahaifinta danya biyaka duk abinda ka kashe a kanta."
"Kutumar uba, wane dan haune ya auri *matata*? wallahi k'aryane , babu wanda ya isa ya auri Khairat ina raye, na riga dana tsara rayuwata da ita kuma ita kad'ai nake tunani, dan haka dole a kwance wannan auren."
Ire iren irin wannan magnganun yake tayi duk suka watse suka barshi yana sambatu, bai tab'a tunanin yana son Khairat haka ba sai yau daya rasata, dafe kai yayi da hannu yace "na shiga uku, Basta ka cuceni, gashi banma san ina kake ba yanzu, Allah ya tsine maka albarka shege tsinanne."π
Yan uwa da iyayenshi takaicine ya hanasu zuwa inda yake, haka baki kowa ya tattara kayanshi ya koma inda ya fito rai a b'ace, shi kuma damuwa ta mishi yawa saida ya zubar da hawaye kad'ai yaji dama dama, haka ya wuni cikin d'akinshi bai fita ba bai kuma cire kayan jikinshi ba har yayi bacci dasu tare da daukar dangana da komai daya kashe akan Khairat amma ba da ita kanta ba, dan har yanzu yana ji zai iya samunta tunda a tunaninshi tana sonshi.
_A banza man kare_π
******************
Umar Faruk na baccin da bai jima da d'aukarshi ba k'aninshi *Sa'ad* ya shigo ya tasheshi wai tanti Ma'u na kiranshi, gabanshi ne ya shiga fad'uwa dan sai lokacin ya tuna wata aba wai ita Zuby, haka ya tashi ya sanya doguwar riga ya fito yana tunanin idan aka daura aurenshi da Zuby ya zama *mijin mace biyu* kenan, zaune ya samesu a d'akin Mama tare da Baba, wata harara masa tace "sannu ango."
K'asa ya zauna yana shafa kansa yace "ina kwana."
"Humm." cewar tantin tana kallonsa.
Gyara zama tayi ta kalli su Baba tace "to ni dama ba wani abu bane ya kawoni sai maganar Umar faruk da Zubeida."
Rudududu yaji kayan cikinshi sun kada , yawu ya had'e ya daga kai ya kalleta, ci gaba tayi da "tun jiya da Zuby taji abinda ke faruwa ta daga hakakinta da nawa, har yau kuka take tak'i ci tak'i sha, daren jiya da zazzabi ta kwana gashi yau ma tak'i hakura, maganarta d'aya shine zata rasa Umar Faruk, shine nace to da a tsaya haka me zai hana a daura musu aure? tunda dai dama an gama komai lokaci kawai ake jira, hakan zaisa ta samu tabbacin ba zata rasashi ba, amma shawara ce ya kuka gani?"
Mama da Baba tausayin Zuby ne ya kamasu saboda dole za taji ba dad'i saboda shak'uwar dake tsakaninsu, da firgici ya kalleta yana tunanin girman maganar data zo da ita, a ranshi ne yace "ni kum gidan uban wa zan kai mace biyu a wannan qarnin, a zanyi dasu?"
_Umariri kenan,πkafi kowa sanin yanda za kayi dasu idan ka gansu gabanka._
Baba ya amshi tayin data zo dashi yace ba matsala, kuma za'a d'aura auren ranar juma'a, ita kuma tace ba yanzu zata tare ba sai bayan ta gama karatun, haka tanti ta koma gida cikin farin ciki Umar kuma ya kalli Baba yace "amma Baba, mata biyu a lokaci d'aya, duka ni d'in nawa nake da zan auri mace biyu, kuma idan suka tare ina zan ajesu? gaskiya Baba nauyin yamin yawa ba zan iya ba."
"Haba Umar faruk, da jarumta fa akasan mai wannan sunan, karka bari mana mata su baka tsoro da wuri haka, zaka iya da yardar Allah, kuma Allah zai baka yanda za kayi dasu insha Allah, zai dubi zuciyarka ya taimaka maka wajen d'aukar nauyin ko wacce."
"Maganar wuri kuma da kake, ai abune mai sauki, tunda itama Zubeida ba yanzu zata tare ba, kaga ita Khairat d'in dake uwar gida saika ajeta acan b'angaren daka gyara, d'akinka na yanzu kuma da muke tunanin saka k'annanka a ciki idan ka tashi, sai a gyara Zubeida ta shiga ciki, abinda zasu ci kuma wannan Allah ba zai hanasu ba, nasan za kayi k'ok'arin yin adalci a tsakaninsu, kuma zamu maka addu'a Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu."
Mama ce tace "Allah ma ya yardar maka kafin lokacin da Zubeida zata tare ka mallaki naka gidan na kanka."
Kallon Mama yayi yace "mallakar gida a wata biyu Mama?"
"Eh mana, kana wasa da yin Allah ne?"
"A'a." yana fad'a ya tashi jiki ba kwari ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin qananan kaya, fita yayi ya gidansu Ishaq ya sameshi kwance yana bacci, ware hannu yayi ya kai masa duka, a tsorace ya farka yana ganinshi yace...
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
1⃣9⃣
"Umar Faruk! miye haka dan Allah?"
"Dallah malam tashi, wato kai duk girgizar qasarnan da ake baka ji kana nan kana bacci, ni ina can cikin ibtila'i kai kuma hutawa ma kake."
Gyara zamanshi yayi yana murza ido yana fad'in "lafiya, meya faru?"
Saida ya zauna shima akan katifa sannan yace "akwai matsala fa mutumina."
"Matsala tame kuma?"
Kallonshi yayi yace "maganar yaran nan ne mana."
Bushewa da dariya Ishaq yayi yace "ai koda kace yaran nan na fahimci da matarka da kuma budurwarka kake, dan kasan mu maza ko mace ta girmemu muna so muce mata yarinya."
Harara ya cilla masa yace "toni fad'a min a cikinsu wacece ta girme min? ka daina ganin wannan da kabri ga kuma tsayi, wallahi ba zata wuce ashirin da uku zuwa da biyar ba."
"Humm, nidai yanzu fad'a min me yake faruwa da kace akwai matsala? danni bana tunanin abin nan zai fara damunka tun yanzu, tunda Zuby nanan tafe."
"To ai akan Zuby d'in ne, tanti fa tazo gida kuma sun gama magana akan za'a sake wani d'aurin auren ranar juma'ar nan."
"Juma'a kuma? amma me yasa zasu mai dashi juma'a? bayan wata biyu ne nan gaba."
"Kaima kasan halin tanti, wallahi ni nasan dagangan tayi haka, kawai akwai bala'in da suke so su kunno min shi yasa tayi haka."
"Ai kuwa in hakane wallahi saika tashi tsaye, ka nuna musu kai namiji ne na gaske, dan inba haka ba sai kazo ka rasa yanda za kayi, wata rana ka kwana d'akina wata rana kuma kaje wajen Mama kana hawaye."
"Wa? ni Umar zanyi kuka akan mace tamin wani abu, ai kaima kasan halina, duk wacce tamin ba daidai ba wallahi daidai nake da ita, tsaf zan zane yarinya."
Dariya Ishaq yayi yace "sai dai Zuby, amma Khairat ba zata daku a hannunka ba."
"Wai wasa kake dani ko? gani kake tafi k'arfina ne? ai kuwa za kasha mamaki, dan sai nasa yarinyar nan tayi laushi fiye da tunaninka."
"Allah yasa, dan in haka ta faru kaine za kafi kowa cin moriyar hakan."
"Kai, karfa ka d'auka wata rayuwar jin dad'i zanyi da ita, taimak...."
Ishaq ya katseshi da "bana son cika baki mutumina, bari ya shigo tukun muga iya gudun ruwanka, nasan mata kuma zata iya canza maka tunani cikin qanqanin lokaci, dan haka bari har naga tafiyar taku sannan."
"Ai kuwa zaka gani."
Tashi Ishaq yayi ya d'auki doguwar rigarshi yasa ya d'auki maclean da brush zai fita yace "ka jira na fito saina rakaka wajen amarsu."
Dan k'uwa ya masa yace "amaryo ba amarsu ba."
Yana ganin ya shiga shima ya fito zai tafiyarsa ya had'u da Baban Ishaq zai fita shima, har k'asa ya zube ya gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska tare dasa masa albarka, sannan ya d'ora "jiya sai mu kaji abin alkairi, gaskiya ka kyauta Allah ya maka albarka ya taimakeka a duka al'amuranka, saura wannan sakaran shima kasa ya samu mata yayi aure."
Dariya kawai yayi ya tashi tsaye shima tsohon ya wuce, saida ya koma gida ya d'auki mashin d'inshi sai dai bansan ina ma zashi ba, yau *lahadi* yau ne dama suke hutu a wajen aiki, mashin d'inshi ya tuk'a bai zame ko ina ba sai gidansu Zuby.
Taji dad'in ganinshi amma kishi yasa ta kasa bayyanawa, d'aki ta shige ta barshi zaune gaban tanti, ganin haka yasa tantin tace "tashi ka wuce ka sameta mana, gidan ai ba bak'onka bane."
Yana wucewa ta bishi da harara, zaune ya sameta a bakin gado ta had'e hannaye, zaune yayi kusanta yana kallon fuskarta, sun jima a haka kafin ya sake kallonta yace "amaryata hushi take dani?"
Da mamaki ta kalleshi tace "lallai ma yaya Umar, yanzu daga d'aura auren naka shine harka kaini matsayin amarya tun ma bata tare ba a gidanka? lallai da matsala."
Shima dai da mamakin ya bita da kallo, taushe zuciyarshi yayi yace "ko da ita ko ba ita, ke amaryata ce kuma kinsan haka."
Hawaye ne suka ciko idonta ta kalleshi tace "wallahi yaya Umar ni dama tun ranar daka d'aga min murya akan banzan yarinyar nan nasan kana sonta, kawai raina min hankali kayi ka nuna ba komai, shine yanzu wai za'a ce ta zama matarka ta farko bani ba, bayan lokacin da muka d'auka muna tare da kai, wallahi kaci amanata yaya Umar, tunda muke da kai ban tab'a kallon wani a matsayin saurayi ba na kare maka kaina,amma shine kai ka kasa hakan, dama ku maza h......"
"Dakata dan Allah." ya katseta.
"Mu maza me? mayaudara ko maciya amana? kinga ki hukuntani ni kad'ai saboda ni miki laifi, amma karya shafi kowa, sannan ni kaina bana jin abinda nayi laifine, saboda ni namiji kuma *mijin mace hud'u*, saboda nayi ta farko kuma zan aureki a matsayin ta biyu ni banga wani aibu a ciki ba."
"Sannan kinsan abinda ke tsakanina da ita, so bashi ya sani nayi abinda nayi ba."
Cike da rashin wayo tace "ba wani nan wallahi, idan da gaske taimakonta kake son yi, meya hana ka rok'i yaya Abbakar ya aureta, ko kuma shi Baban ya aurrr."
Qamewa tayi ta rintse ido tana jiran taji saukar hannun, Umar faruk kam daya d'aga hannu zai wanketa da mari tsayawa yayi saboda tunawa a cikin gidansu yake, nunata yayi da hannu yace "maganar data shafi ni dake, karki sake saka iyayenmu a ciki, idan ba haka ba ranki zai dinga b'acewa."
D'orawa yayi da "karki kuskura kice zaki raina min mata bare iyayena, ita ke gaba dake kuma dole ki bita in har kina son zama dani, in kuma ba haka ba to mu hak'ura da junanmu, dan duk abinda zai shafi mutuncina bana k'aunarshi, a yanzu kuma itace tabbas d'ita tunda ta shiga hannuna , kuma kare mutuncinta yana wuyana ne, dan haka ki kiyaye, sannan idan kin shirya aurena to ki shirya dabarun zama dani lafiya."
Yana fad'a ya fito daga d'akin yayi wa tanti sallama yayi gaba ranshi na quna , wai tun yanzu kenan za'a fara caza masa kai, sai lokacin kuma ya dinga tunano abinda ya fad'a mata akan Khairat, duk da ba sonta yake ba amma yaji dad'i dan ko ba komai dai dole ya kare mutuncin kowace a cikinsu idan har suka zama nasa dukansu.
*****************
Khairat na bacci ka tasheta saboda bak'i na shirin tafiya, sallama suka dinga mata ana sake mata addu'a Allah ya bada zaman lafiya, ita kuma tana yak'e tana amsawa da ameen ameen π, har suka gama tafiya ya rage sai Mammie a gidan, bayan sallah azahar suka tafi da Hibba salon aka cire mata akaihun data saka dogaye da kuma gyaran da aka mata aka aka gyara mata aka mata kitso manya, bayan la'asar suka dawo gida tayi wanka tayi sallah taci abinci, ita da kakarta sai farin ciki suna hira cikin nishad'i.
*Bayan sallah magrib* Papa ya tafi masallaci d'aukar karatu, kamar kullum saida sukayi sallah isha'i aka sallami kowa, anan Baba ya tsayar da Papa ya fad'a masa maganar auren Umar faruk, farin ciki Papa yayi tare dasa albarka kuma yace zasu halarci d'aurin aure insha Allah.
Bayan yazo gida ya fad'a ma Mamie da Mammie, Mamie ce kawai tace "Allah ya basu zaman lafiya ya basu hak'urin zama da junansu, a fad'a mata kawai tasan halin da ake ciki."
"A'a." cewar Papa sannan ya d'ora da "ba hurumin mu bane, ki bari mijinta zai fad'a mata da kanshi, shi yasan ta yanda zai tarota."
"To shikenan, amma ni dai wallahi ina son yaron nan sosai, dan nasan shi kad'ai ne zai iya tafiyar da Khairat a matsayin miji, kuma ina ji a jikina zata gyaru ta dalilinshi ne insha Allah."
Papa ne yace "nima yaron ai ya kwanta min a rai sosai, dan ba kowa bane zai iya yin *jihadin* da yayi."
"Sosai kam, dan da yanzu bamu san halin da muke ciki ba dukanmu, nadai tabbatar bama cikin yanayin dad'i." cewar Mammie.
Dariya Mamie tayi tace "ai yaron kirki ne kuma ya samu tarbiya, tunda ba shine karo na farko ba daya taimakemu."
"Kin sanshi dama? wane irin taimako yayi mana?" inji Papa.
"Shine fa yaron daya je asibiti yana son ganinka, wanda ni na fito na ganshi kuma shiya fad'a min inda aka samu masu laifin nan, kaga ba danshi ba da yanzu muna nan tare dasu."
"Allahu Akbar, lallai ya mana taimako, babu abinda zamu saka masa dashi sai dai addu'a da fatan alkairi, Allah kuma yasa kar yarinyar nan ta bamu kunya."
Mamie ce tace "ameen, amma dai nasan zaiyi wuya a samu sauk'in al'amari daga wajen Khairat."
Mammie ce tace "ba zata bada matsala ba insha Allah."
"Allah yasa."
Suka amsa da "ameen."
********************
*Haka* aka dinga tafiyar da rayuwar ba dad'i ba wuya, Khairat rayuwarta take kamar babu auren kowa a kanta, sai dai Mamie ta hanata fita ko k'ofar gida, itama kuma bata damu ba tunda tana sakewa a cikin gidan, zuwan Mammie ya sata farin ciki sosai kullum suna tare suna shirmensu kamar yanda suka saba.
Sai dai kuma har yau basu had'u da Umar Faruk ba, kamar yanda basa da lambar juna bare wani ya kira wani, sau d'aya yazo da sassafe tana bacci, yace agaisheta kawai zai dawo har yau kuma bai koma ba.
*****************
Umar Faruk ma shirye shiryen wani sabon auren yake tayi hakan yasa ma baya da lokacin kanshi sosai, sai dare yayi kuma sai Khairat ta sallamo mishi ta hanashi bacci, tunaninta na takura masa yana hanashi sukuni sosai, wani lokaci har yakan manta da Zuby a rayuwarshi saboda katutun da Khairat tayi a zuciyarshi.
*Kwana hud'u* yau da auren, Mamie ta tura Mamar Hibba da tanti Safiya gidansu Umar Faruk ganin d'akin Khairat, su kad'ai ne ta yarda dasu da kuma hallayarsu shi yasa ma ta turasu su kad'ai, sunje cikin aminci kuma sun dawo cikin farin ciki saboda tarbar da aka musu, sun fad'ama Mamie komai akan gidan dama d'akin inda tanti Safiya ta qara da cewa "gaskiya rayuwa dai ta mai qaramin k'arfi, to wannan d'akin na Khairat ya ishi bawa rayuwa kuma cikin farin ciki."
Sai dai Mamar Hibba tace "amma ko kad'an kayan da aka saka mata a d'akin Muzaffar ba za suyi a wannan d'akin ba."
Hakan yasa Mamie turawa aka d'auko kayan Khairat daga gidansu Muzaffar aka sasu kasuwa, a take kuma aka siyo mata wasu sabbi yan zamani masu bala'in kyau, *ranar alhamis* aka mata jere a d'akinta, masha Allah yayi kyau sosai duk da d'aki d'aya ne amma zai birge, haka yan gidan suka lek'a suka ga d'aki yayi tsaf dashi, ga kayan kallo da aka lak'a mata panka da k'aramar fridge, matasan kujeru ne aka aza a d'an k'aramin farfajiyar kewayenta , sai babbar kujera a cikin d'akin ta zaman mutun uku, saman wradrob kam cike yake da manyan darori da bargo , ciki kuma bayan kayan jiki sai kwanoni da sauran kayan aikin gida, a kusa da taga ma wasu darorin ne aka jerasu har suna kusan tab'a rufin d'akin saboda yawa, haka aka rufe d'akin ana jiran asabar tayi maishi ta shiga.
Duk wani abu da Muzaffar ya kawo saida Khairat ta tabbatar ta mayar masashi a cikin akwatinshi, duk wani abu data d'inka saida tasa aka nemo irinshi sannan tasa aka mayar masa, kamar dai yanda yayi itama motoci ta samu suka kai kayan har gidansu, had'e kuma da makullin motarshi, tunda yaga haka ya tabbatar da aikin Khairat ne ma'ana tayi hushi kenan, bai k'ara tsinkewa da al'amarin ba saida ya bud'e k'aramar motar ya samu goron daya bada da kuma enveloppe, yana bud'awa yaga kud'i ne a ciki kamar yanda ya bada, sai kuma k'aramar takadar data rubuta wasik'a da harshen french cewar,
_"Bani ba kai, ba kai bani har abada, yunk'urin sake shigowa rayuwata a karo na biyu, daidai yake da yak'in duniya na uku, dan ba shakka yak'i ne zai b'arke tsakanin gidanmu da gidanku, *K'ARAMIN MUTUM* kawai._
Hawayen da yaji suna son zubo mashi yasa ya koma cikin gida ranshi b'ace, hamshak'iyar mahaifiyarshi dake zaune a d'akinta tana waya ya fad'a saman jikinta yana kuka, kashe wayar tayi tare da tureshi daga jikinta cikin jin haushi tace "dallah ni dagani shashasha kawai, kasan kana sonta uban wa ya aikeka d'aukar zigar aboki ana daf da d'aura aurenka? kawai saboda rashin tunani da lissafi saika yarda da abinda ya fad'a, yanzu gashi har yau bai sake zuwa inda kake ba, tunda burinshi ya cika."
Ganin mahaifiyar tashi ma ta d'auki zafi yasa ta tashi ya fita ya koma b'angarenshi zuciyarshi kamar zata buga.
****************
Tun ranar Umar Faruk bai sake zuwa gidansu Zuby ba bai kuma kirata ba, shirin d'aurin auren kawai yake yi amma sam ya daina jinta a cikin ranshi, musamman idan ya tuna abinda ta fad'a masa, haka kawai yake jin ba dad'i idan ya tunata yafi farin ciki kawai idan yana tunanin Khairat wacce yake da yak'inin ko sau d'aya bata tab'a tunaninshi ba.
*Yau juma'a* gidan an tashi da shirye shirye da kimtse kimtse, kamar yanda muka sani lokaci na gudu, dan-danan sai aka fara tafiya masallaci, bayan gama sallah kuma aka sake d'aurawa Umar Faruk wani auren, *Umar Faruk Ahmad Adam* da *Zubeida Hamza*, daga masallaci gidan wani abokinshi *Abdul Azeez* suka wuce inda akasha gara tare da tayashi murna, Ishaq dai dariya yake masa duk lokacin da suka had'a ido dashi saboda tamke fuskar da yayi, bidiri sosai abokanshi suka shirya wanda ya kaisu har magrib, suna sallah kuma suka dawo gida inda aka fara shirin walima.
Shiryawa yayi cikin wata sabuwar shadda ruwan toka had'e da takalma sai dai bai d'ora hula ba, yana fitowa ya samu taro harya fara cika, Abdul Azeez ne ya takura masa ya rakashi asibiti yanzu aka kirashi ankai kakarsu ba lafiya, jin uzurinshi kuma tunda bai nemi kowa ba saishi yasa suka shiga mota suka tafi.
****************
*Amarya Khairat* ce zaune a falo a saman qafafun Mammie tana latsa wayarta, kirane ya shigo ta d'auka da "hello macho."
"Gamu a k'ofar gidanku." cewar Rashida.
"Gidan namu kuma mak'abarta ne da ba zaku shigo ba?"
"Kinga kedai ki fito."
"Wai lafiya, meya faru ne?"
"Kai Khairat, kina b'ata mana lokaci fa, asibiti zamu wuce tare da Farida muke."
"To naji ina zuwa."
Mik'ewa tayi daga jikin Mammie ta d'auki kallabin doguwar bleue rigarta ta d'ora a kai tace ma Mammie "su Rashida ne waje wai asibiti zasu, bara naje naji kiran me suke min."
Tana fita Mamie ta fito cikin shirin tarban Papa, zaune tayi tana fad'in "ina ta shiga kuma?"
"Wai Rashida ta kirata suna k'ofar gida."
Zunbur Mamie ta tashi tace "Rashida? na shiga uku, nifa bana qaunar yarinyar nan, wallahi ita ke qara lalata min yarinya."
K'ofa ta nufa Mammie na kiran "ina kuma za kije? yanzu zata dawo fa."
K'ofa ta nufa tana fad'awa mai gadi "kai duba min Khairat, maza ce nace ta shigo ciki."
A cewar mai gadin "a'a Hajia ai har sun tafi."
"Sun tafi ina kuma?"
"Wallahi Hajia ban sani ba, taxi daice suka shiga."
Dafe kai Mamie tayi tace "na shiga, ina zasu je kuma? me zan fad'awa mahaifinta?"
Dawowa tayi tace "Mama kin gani ko? Khairat bata nan wai sun fita."
Kafin Mammie tayi magana ta d'auki wayarta ta fara kiranta, Khairat kuma da tana fita ta samesu a cikin taxi Rashida ce tace "yawwa zo muje."
Ta fad'a tana matsa mata nufin ta zauna, "ina kuma zanje bayan kinsan ba'a barina fita?"
"Kinga asibiti zamu je k'anan Farida ne ba lafiya, dazu aka kaishi ya k'one da ruwan zafi, kizo muje yanzu zamu dawo daga nan sai muyi magana."
Hannunta ta janyo ta fad'a cikin taxi d'in suka ja suka tafi, ba suyi nisa ba kuma kiran Mamie ya shigo wayarta, tana d'auka Mamie tace "kina ina?"
"Mamie ina bisa hanya za muje asibiti ne yanzu zan dawo."
Da sauri Mamie tace "amma kinsan ba kya fita ko ina ko? me yasa zaki fita haka kawai, idan mahaifinki ya dawo ya zance masa?"
"Dan Allah Mamie karki damu, ba jimawa zanyi ba."
Tana fad'a ta kashe wayar ta kalli Rashida tace "wace magana za muyi?"
Kallon juna sukayi kafin Rashida tace "am Khairat, wallahi mutuminki yana cikin wani hali, yana buk'atar taimakonki sosai."
"Wane mutumin nawa?" ta fad'a tana kau da kai.
Farida ce tace "Muzaffar mana, kinga yanda ya koma saboda damuwa, wallahi sai addabarmu yake wai mu taimaka masa."
"Yanzu dama akan maganar waccen banzan ne kuka saka na baro gidanmu ba tare da izinin kowa ba? kinga tsayar da mai taxin nan na koma gida in dai wannan ce maganar."
Rik'eta sukayi suna fad'in "kinga shikenan to, ba zamu sake miki maganarshi ba, yi hak'uri."
Harara tabi kowace a cikinsu tana fad'in "aikin banza kawai, mutumin daya ci min mutunci har zaku wani zomin da maganarsa , shi bai fad'a muku ba komai tsakanina dashi ba, ko sile baya bina bare ya takura min, mak'uddan kud'ad'e na kashe wajen biyanshi abinda ya min."
Babu wanda sake magana har suka isa asibitin suka duba yaron da qafarshi ce kad'ai ta k'one sannan suka tashi zasu koma, bayan mahaifiyar Farida ta gargad'eta akan ta kula da gida da sauran k'annanta, fitowa sukayi suka tsaya a bakin titi suna jiran samun taxi.
*Umar faruk* ne suka fito zasu tafi suma sun shiga mota suka tayar, bakin titi suka tsaya suna so kai kawon motoci ya tsagaita su samu su hau titi suma, a cikin waige waigen da suke sai kuwa Abdul Azeez yace "masha Allah, abokina da alama nima lokacin aurena ya kusa, domin kuwa naga wacce tamin."
Haka kawai sai Umar Faruk yaji gabanshi ya fad'i, daurewa yayi yace "toh , wace mai sa'ar ce wannan?"
"Gatanan gabanka kan gani."
Sai lokacin Umar faruk ya kai kallonshi ga yan mata ukun dake tsaye, hakan yayi daidai da Khairat ta juyo saboda motar dake bayansu ba haskesu sosai, saida ya rintse ido saboda takaici da bak'in ciki, sam fitowa bada izininshi bai dameshi ba kamar rigar dake jikinta.
Duk da bata kamata ba amma da yake tana da 'yar k'iba kuma yadin rigar yadine mai bin jiki, hakan yasa ya hango shatin kwanciyar pants d'inta da kuma bras d'inta, ga kuma kallabin k'aramin hakan yasa gashinta ya fito har ya kusan rufe shatin bras d'inta, duk da dai baida tabbacin gashin kanta ne, ranshi ya b'ace sosai musamman da abokin nashi ya haskesu da mota yana mata kallon k'wak'waf, dan suma k'awayen nata duk shigar tasu babu mai dama dama a cikinsu.
A fusace ya fita daga motar ya tsaya bayanta ba tare da yayi magana ba, jin kamar mutum a bayanta yasa ta juyo dan ganin wane d'an rainin wayone, a take gabansu ya tsinke ya fad'i sai kallon kallo da sukewa juna, kasa magana tayi dan har cikin zuciyarta taji bata ji dad'in ganin daya mata a haka ba, kasa d'auke idonta tayi daga kanshi shima kuma haka.
Rashida ce tace "macho, kin sanshi ne?"
Had'iye yawu tayi ta kalli Rashida, muryarshi ta dawo da ita da yace "wuce muje."
Kallonshi tayi amma wani irin bala'in kwarjini daya mata sai yasa ta nuna su Rashida da hannu, wani sabon kallo daya mata da idonshi fuskar nan ba hasken annuri ya sake cewa "wuce muje gida."
"Amma ai....."
"Nace ki wuce mu tafi ko." tsawar daya mata yasa ta kama hanya ba shiri , ganin haka yasa yabi bayanta ya bud'e mata bayan motar ta shiga, tana kallonsu Rashida suka wuce suka barsu, su kuma mamaki suke ko wanene shi, Farida ce tace "nifa ina tunanin ko shine mijin nata."
"In kuwa shine gaskiya yarinyar nan mai sa'a ce, danni kin sanni fa ina son namiji irin wacce wallahi, da irinsu sunfi dad'in harka.
Farida ce tace "ki daibi a sannu, dan kinsan yarinyar can ta fiki akuyanci, mijinta kuma yafi k'arfinki."
******************
Tunda suka d'auki hanya babu wanda yace tak , tafiya kawai suke Abdul Azeez kuma da kanshi ke kulle bai samu damar magana, dan yasan tabbas akwai wani abu a qasa saboda yanda yaga Umar faruk ya mu'amulanci Khairat d'in yasan ba sanin yanzu bane a tsakaninsu, Khairat kam tayi iya k'ok'arinta wajen ganin gabanta ya daina fad'uwa amma ta kasa, kamar yanda Umar faruk kejin haushinta da takaicin aurenta da yayi, a haka suka isa gida da kanshi ya fito ya bud'e mata k'ofar ta fito babu wanda ya kalli wani, izuwa yanzu kuma Abdul Azeez ya gane kuskure yayi dan ko ba'a fad'a ba wannan itace 'yar Mani Bukar.
Wucewa tayi zata shiga shima yabi bayanta, tana daf da shiga gidan yace "kina haukane da kika da wannan kayan a jikinki, sannan da izinin wa kika fita?"
A hassale ta juyo tace ".....
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
ππππππππ
_ALLAH KA SHIRYA MANA YARANMU MAZA DA MATA, ALLAH KA BAMU IKON TARBIYANTAR DASU, AL'AMARIN NAN YA FARA BANI TSORO WALLAHI, YARA QANANA SUN D'AUKI D'ABI'A MARAR KYAU, WASU GANI SUKE WASU KUMA YIN KANSU NE KAWAI, ALLAH UBANGIJI KA KARE MANA 'YA'YANMU DAGA B'ATA GARIN ABOKAI, ALLAH KA BAMU IKON KIYAYE DUK WANI ABU DA ZAI HASKU A IDON 'YA'YANMU HAR SUYI SHA'AWAR KWAIKWAYA._ππ
ππππππππ
2⃣0⃣
"Ban gane ba, me kake nufi, me kayan jikina sukayi, wai ikone zaka min tun ban tare gidan naka ba? ina ruwanka da kayan jikina to? kana da matsala da hakan ne? karfa kace zaka rainani saboda kaji ance an daura mana aure, wallahi ba dauka zanyi ba kaji na fad'a maka, haka kawai zaka wani tsareni harda tambayar wai da izinin wa na fita, bayan a gidan mu nake har zaka min wannan tambayar, ko kana ganin iyayena basu da ikon da zasu bani damar fita? to in dai kai zan dinga tambaya kafin na fita da sai dai karna fita har abada, dan ba zan iya qasqantar da kaina har haka ba, kuma wallahi ka fita idona, kar kace zaka sake min irin tsawar da kamin d'azu musamman a cikin mutane, in kuma ba haka ba."
K'wafa tayi mai k'arfin gaske ta juya zata shiga gida, wata fizgowa ya mata saida ta kai mashi karo a qirji, turata yayi ta kaima bango karo ya mata runfa da faffad'an jikinshi, kafeta yayi da ido sunyi ja saboda zafin maganganunta fuska a d'aure ba alamar wasa cikin dakakkiyar murya yace "waye ni?"
Cike da tsiwa tace "waye fa daya wuce d'aya daga cikin gama garin mutane."
Rufe ido yayi ya sake maimaita "waye ni nace?"
Kallonshi tayi da ido tace "Umar....Faruk mana."
"Nace waye ni a wajenki?" tsawar daya mata har saida mai gadi ya leko, amma ganin Khairat da angonta yasa ya koma, ita kam yanda muryarshi ta daki k'ok'on kanta yasa ta zabura da k'arfi tare da fashewa da qara har wayarta ta sub'uce ta fad'i, hannayenshi yasa a jikin bango kamar zai rumgumeta ya sake tsareta da ido yace "ina jiran amsarki."
A hankali ta daga idonta ta kalleshi amma sai hawaye suka zubo mata, kau da kai tayi ta sauke ajiyar zuciya ba tace komai ba, sake matso da kanshi yayi daf da fuskarta yace "zamu kwana anan in har baki fad'a min ba."
Cikin daga murya da jin zafi tace "to waye kai? me kake so nace? so kake nace *mijina*? to naji kaine *Umar faruk mijina*, shikenan? to kauce min a hanya zan wuce."
Wani d'an iskan murmushi yayi mai kama da kuka tare da fad'in "humm." kafin yace "daga yau ina so na dinga jin muryarki k'asa da tawa, idan kuma kika bari k'uruciya da hauka irin naki yasa kika d'aga min murya, to ki kuka da kanki, dan zan miki abinda kaf a tarihi babu wanda ya kwatanta yi miki shi."
Sunkuyawa yayi ya d'auki wayarta ya dangwara mata a hannu sannan ya juya ya shiga mota tana kallonshi har suka b'acema ganinta, juyawa tayi ta shiga gida kamar zata tashi sama, har Papa na falo suna jiran dawowarta, a tare suka mik'e ganin ta shigo da sauri tana share hawaye, Papa ne ya fara tambayar "shalele lafiya, meya faru kike kuka."
Mammie ma d'orawa tayi da "shalele meya sameki, wani abu aka miki?"
Kallonsu tayi cikin muryar kuka tace "karku damu ba komai."
"Ya zaki ce ba komai? bayan kin fita cikin farin ciki kin dawo kina kuka, kuma an fad'a min wad'ancen yan iskan yaran ne suka fita dake."
Ganin zasu takurata yasa tace "Mamie ba komai fa, tare dashi muke."
"Shi wa?" cewar Papa.
Turo baki tayi gaba tace "Umar Faruk."
Fuska kowa ya saki yana murmushi har Mammie tace "to kuma a waje kika baroshi?"
"Harya tafi." ta fad'a tana wucewa d'akinta.
_Abinka ga manya_ duk sai sukayi tunanin ko zaman da tayi na sati d'aya ne yasa ya gagara hak'uri, shi yasa suka fita ya d'an rage zafi, π masu hangen nesa kenan, wannan hasashen naku ba yau ba ba kuma gobe ba.
Cikin b'acin rai da bak'in cikin abinda Umar Faruk ya mata ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin rigar bacci doguwa, dole ta toshe kunnuwanta da abin sauraro danta rage zafi.
*******************
Tunda suka d'auki hanya babu wanda yayi magana, amma saboda ya nuna masa baisan komai ba yasa Abdul Azeez cewa " *wacece ita*?"
Kamar ba zai amsa ba amma kuma ba tare daya kalleshi ba yace " *matata ce*"
Shiru yayi dan duk wata magana da zaiyi yanzu zai iya janyo b'acin rai fiye da yanzu, har suka isa babu wanda ya sake magana, suna zuwa tuni taro yayi taro *ustaz Khalid* nata bada wuta, nan ya fara gaishe da malamanshi da uwaye da kuma kakanni , tare da sake miki gargad'i da nasiha akan rik'e adalci da gaskiya, wuri ya samu ya zauna kamar mai sauraron abinda ake amma a gaskiyar lamarin ba haka bane, harya fara hango irin rayuwar da zaiyi a tsakanin d'akin Khairat da d'akin Zuby, Zuby akwai k'arancin wayo, Khairat kuma da wayonta zata b'ata maka rai, amma dole ya d'auki matakin gyara tun kafin lokaci ya k'ure masa.
****************
Zuby ce tsakiyar aunyt's d'inta guda uku, sun gama zigata tare da hure mata kunne, sun cire mata soyayya da tausayin Umar Faruk a ranta tun kafin aje ko ina, tilasta mata sukayi ta kurashi ta bashi hak'uri akan abinda ta masa, saboda akwai wani magani da suka siya mata, kuma dole aiki dashi sai suna shiri dan suna son ya kusanceta, wayar ta d'auka ta kirashi lokacin yana tsaka da tunani, yayi mamakin ganin kiranta sosai dan abune da bai tab'a faruwa ba suyi fad'a ta kirashi sai dai shi ya kira, dauka yayi baice komai ba, cikin taushin murya tace,
"Amincin Allah ya tabbata a gareka angona yayah Umar."
Nauyayyan ajiyan zuciya ya sauke yace "amincin Allah ya tabbata a gereki."
Cikin shagwab'a tace "kenan ba zan samu ko wane irin suna daga gareka ba?"
Murmushi tayi yace "ina tsoron nace amaryata kuma kiyi hushi ne."
Cike da wayencewa tace "ba komai yayah Umar, ka kirani amarya zan amsa, tunda aunty Khairat ta rigani zama taka."
"A'a, har yanzu fa babu wacce ta shigo hannuna, dukanku dai ina jira ku gama wainani sannan ku shigo gidan."
Haushi ne ya kamata danta lura soma yake Khairat ta shigo gidan bayan yace taimako yayi, shi kuma baya so ne ya bada wata k'ofa da zata sa Zuby ta raina Khairat musamman ace ta dalilinshi, koba komai itama matarshi ce kuma uwar gida, a dak'ile tace "dama na kirane na baka hak'uri abisa abinda ya faru, dan Allah ka yafe min ba zan sake ba."
"Ba komai k'anwata, ya wuce ai."
"Na gode, saida safe, dan naji kana cikin jama'a."
"Saida safe." ya fad'a suka tsinke kiran.
Haka taro ya tashi lafiya bayan addu'o'in da aka zuba musu, dare yayi kowa ya kwanta amma banda Umar Faruk, a qarshema d'akin Khairat ya bud'e ya shiga, fitilar d'akin ya kunna a hankali ya dinga sauke numfashi saboda wani baqaraken k'amshi dake shigar hancinshi, had'e yake da kamshin turaren wuta da kuma turaukan dake zube a saman coiffeuse da mayuka har babu wurin aza wani abun, bin d'akin yake da kallo ko ina yana kallon irin kayan da aka cika d'akin dashi, wai nan danma yana ba'a samu irin wurin da ake so bane, kusan komai na d'akin pink couleur ne hakan yasa yace "da alama shine couleur prΓ©fΓ©rΓ© (best coulor) d'inta."
A sannu yake tunanin ranar daya fara shiga d'akinta yana fad'in "girman d'akinta shine kaso d'aya na bisa ukun gidan nan, girman gadonta kuma d'akin nan ba zai daukeshi ba, duk da banga ban d'akinta ba, amma na tabbata ta kusa girman d'akin nan."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi yace "taya zata iya rayuwa a d'akin nan? bayan gashi tagar dake akwai ma kaya sun rufeta, taya zata iya rayuwa da wannan pankar? bayan acan ac take kunnawa , taya zata iya rayuwa a gidan nan da mutane haka? bayan ita acan ita kad'aice ba k'ane ba k'anwa ba yaya ba aunty."
_Wannan itace rayuwar daya kamata ta fara kota koyi hankali_
********************
*A b'angaren* tunda aka tashi da safe ta tashi jiki ba k'wari, gashi Mamie ta kira mai kitso amma sam tace bata so, ayi juyin duniya tace ba taso dole aka barta, da qyar ta bari aka mata jan lalle tunda waccen ya goge dan jikinta baya da kama lalle, duk da mutanen da suka zo dan rakiyar amarya Papa yace sam bashi ba wannan bidi'a, dan haka da kanshi zai kai yarshi gidanta tare da rakiyar kakanninta.
Abin yama Khairat yawa dan haka tun yamma ta fara kuka, amma sai tace musu kukan rabuwa ne dasu, haka akayi magrib akayi isha'i, ba wani shiri tayi ba atamfa ce ta zabga riga da zane d'inki simple, kasancewar bata tab'a saka zane simple ba saiya mata kyau d'as, Mammie da Hajia *Maryama* ne suka kamata Papa da kanshi ya tuk'a mota suka nufi gidan amarya bayan d'an jan kunne da Mamie ta sake mata, sai bayan fitarsu Mamie kuma ta fashe da kuka saboda tunanin rayuwar da yarta za tayi a gidan yawa.
Kasancewar a gidan Baba Papa ya koyi *sunna* hakan yasa basu tarar da wasu 'yan tarban amarya ba bare abincinsu, mutanen gidan ne kawai kuma yara na islamiyyar dare dan haka sai uwayen, tarba aka musu sosai tare da Baba aka musu iso zuwa d'akinta, Papa ne ya kama hannun Khairat ya zaunar da ita bakin gado sannan ya zauna zauna kujerar dake kallonta, su Mammie ma zaune sukayi kusa da ita kafin Papa ya kalli Baba yace "surukin namu yana nan? ina so zan d'anyi magana dashi."
"Ba damuwa, ina jin ai baiyi nisa ba, bara na dubo muku shi." Baba ya fad'a tare da fita waje.
A gidansu Ishaq aka kira Umar Faruk tun saman hanya gabanshi ke faduwa, haka ya shigo cikin gidan har kuma d'akin, Papa ne ya masa nuni daya zauna kusa da Khairat, kallon Papan yayi ya kalli wajen da zai zauna sannan ya matsa a hankali ya tsoma k'ugunshi, duk da fuskarta a rufe take da mayafi amma sai yake ji a jikinshi hararanshi take, kuma kuwa hakaneπdan bayan harara harda murgud'a baki da gunaguni.
Papa ne ya fara da "Umar Faruk, ga Khairat nan, mun kawo maka ita, kuma amana muka baka, muna fatan zaka rik'e mana ita abisa gaskiya da amana, Umar Faruk na yarda da kai, bana jin akwai ranar da zata zo ka bud'i baki ka gorantawa Khairat akan taimakon daka mana, ka sani Umar Faruk akwai ranar da Allah zai tashemu kuma ya tambayemu yanda muka zauna da iyalenmu , kayi adalci a tsakanin matanka domin hakan ne kad'ai zaisa ka samu rabo a ranar gobe k'iyama, kasan wani abu Umar Faruk, ba wai gaggawar aurar da Khairat bane muke da har yasa muka baka ita a waccen ranar, kawai dai na yarda da tsatson daka fito, kuma ina da yak'ini akan tarbiyar daka samu, ina son Khairat sosai fiye da komai a duniya, domin ita kad'ai na mallaka, bawai ina son zamanta anan bane dan nasan dole kafin ta saba zata sha wuya, amma darasin da zata koya a zamanta anan d'in shine yafi min komai dad'i, dan nasan *tarayyarku* zata zamar mana alkairi."
"Daga qarshe kuma, ina sake jaddada muku da kuyi hak'uri da junanku, Umar Faruk, akwai abinda ya kamata ka sani a game da Khairat, tana fama da wata muguwar rashin lafiya wacce idan ta taso mata takan shiga tsakanin halin rayuwa da mutuwa, duk da ince kusan nine silar wannan rashin lafiyar, amma dai a yanzu ina fatan kai ka zama maganin wannan cutar, wacce damuwa da kad'aici ne suka janyo mata ita, da fatan zaku zauna lafiya, Allah ya muku albarka, Allah ya baka abinda zaka ciyar da matanka, Allah kuma ya baka ikon yin adalci a tsakaninsu."
"Ameen." mutanen d'akin suka amsa dashi.
"Insha Allahu Baba zanyi k'ok'arina wajen kawar da kowace damuwa a tare da ita." cewar Umar Faruk yana satar kallonta.
Murmushi Papa yayi yace "Allah ya baka iko , ke kuma baki ce komai ba?" inji Papa yana kallon Khairat.
A hankali ta d'ago da kanta tana d'aga mayafinta tare da kafe Umar Faruk da ido, shima ita ya kalla amma ganin kallon da take masa bana arzik'i ne yasa ya kawar da kanshi, maida kallonta tayi ga Papa tace "nayi muku alk'awarin zama dashi...." sai kuma tayi shiru ta sake kallonshi, sai dai shima a lokacin ya kafeta da ido yana jiran yaji me za tace, ba tare data d'auke kai daga gareshi ba tace "har abada."
Wani irin farin cikine Umar Faruk yaji ya mamayeshi ba tare da yasan dalili ba, su kaka kuma hak'uri dai suka sake jaddaja musu suyi da junansu, nan suka tashi zasu tafi Umar ma ya mik'e dan rakasu, da gudu Khairat ta k'arasa ta rumgume Papa ta fashe da kuka, nan ya shiga rarrashi da ban magana tare da k'ok'arin yakiceta a jikinshi amma ta cije , a lokacin kuma Mammie ta janyo hannun Umar Faruk ba tare da kowa ya gani ba ta bashi magungunan Khairat tace masa,
"Wannan sune maganinta idan ciwonta ya tashi, ina fata zaka zamar mata waraka , a k'arshe ma ku jefar da maganin saboda rashin anfaninshi gareku."
Kai ya girgiza yana mamakin wane irin ciwo ne, ko dai aljanu gareta? ya tambayi kanshi, murmushi yayi ya rik'e hannun Mammie yace "na miki alk'awarin haka, insha Allah."
Lokacin kuma muryar Baba ta dawo dasu yana fad'in "kai Umar Faruk, kamata dan Allah su samu su tafi."
Kallon Baban nashi yayi yana tunanin ta yanda zai fara rik'eta, wasu yawu ya had'iya tare da yin k'unar bak'in wake yayi kansu zai b'anb'areta, ita kuma tunda taji ance ya rik'eta ta sake sark'afe Papa tare da lab'ewa bayanshi tana fad'in "ni wallahi ba zan zauna, kawai ku tafi dani, wannan fa mugune ba imanine dashi ba."
Papa ne ya kalli Umar Faruk da yayi tsaye yana sauraronta yace "dan Allah ka rik'e matarka kaji."
A hankali ya matso ya fara k'ok'arin b'anb'areta daga jikin Papan, da taimakon Papan ya samu suka rabata dashi, da sauri Papa ya bar d'akin tare dasu Mammie, tana ganin haka ta sake fashewa da kuka tana fizge kanta tana so ta fita, shi kuma rik'eta yayi sosai hakan yasa take k'ok'arin zubawa a guje, da k'arfi ya sake jawota ta fad'o kanshi ya matseta sosai a jikinshi, sake volume tayi tana kukan shi kuma sai wutarshi ta d'auke d'uf , a hankali taji yana shafa bayanta yana fad'a mata wani "shiiiiiiii, ya isa haka to." kamar yarinya k'arama, da sauri ta janye jikinta ta fad'a saman gado ta kwanta tana ci gaba da kukanta , shi kuma tab'e baki yayi ya fita daga d'akin sai gidansu Ishaq.
Umar Faruk bai dawo gidan ba saida *23:30* tayi sannan, yana shigowa ya shiga d'akinshi ya cire kayan sannan ya shiga wanka a ban d'akinsu ta tsakar gidan, yana fitowa kuma ya sake shiga d'akin a shirya cikin doguwar riga fara qal duk kai da kawon nan yayi shine cikin sand'a kar Baba yaji, sannan ya fito ya nufi d'akin amarya.
_Kuzo mu raka ango siyan baki_ππ
Yana shigowa ya sameta yanda ya barta sai ajiyar zuciya take saukewa a hankali alamar bacci ya d'auketa, kashe mata wutar d'akin yayi ya fita ya rufe k'ofar tare da rufe gaba d'aya kewaye sannan ya koma d'akin tuzurai πUmariri kenan.
Ya jima baiyi bacci ba suna waya da amarya Zuby wacce take farin ciki take ganin kamar ta hanashi gabatar da daren farkonshi , nikam nace π _kin rako mata duniya dai, lokacin da zai yishi ma sai kin shigo gidan_, suna gama waya kuma saiya d'auro alwala ya fara jera nafilfili har asuba, kiran farko ya bud'e k'ofa a hankali danya koma d'akin amarya ya tasheta, amma ina duk hanzarinshi Baba ya rigashi , domin kuwa yana bud'e k'ofar sai kuwa Baba a bakin panpo yana d'ibar ruwa a buta , cike da kunya da sanyin jiki ya nufi d'akin ya bud'e ya shiga ciki, tana nan har yanzu kwanciyarta kawai ta gyara, saida ya gama kallon qafafunta da suka sha lalle suka yi tsaf dasu sannan ya tab'a qafar, a hankali ta fara motsawa harta tashi zaune ta wartsake sosai, kau da kai yayi yana shan k'amshi yace "ki tashi kiyi sallah, lokaci yayi."
Wata muguwar harara ta dalla masa tare da juya baki, qasa da sama ya kalleta sannan ya wuce abinshi, har tayi kwance kuma taji gumi ma ya isheta, tashi tayi ta cire mayafin jikinta da d'an kwali sannan ta mik'e ta cire rigar atamfar sannan ta d'auki t-shirt matsatsa mai k'ananan hannuwa tasa, bata cire zanin ba dashi ta fito d'an k'aramin kewayen nata, duk da duhun asuba saida ta gama kallon ko ina, tabb', wai itace zata rayuwa a wannan gidan, hayaniyar da take ji yasa ta lek'a ta gajeruwar katangar saboda ta fita tsayi, kai komo kawai mutanen gidan keyi yara da manya sunata alwala, da mamaki take kallon mutanen da ko ganinta ba suyi ba, a ranta tace "duk mutanen gidan ne wannan kamar ana biki, lallai ma.", a qalla sunkai ashirin kosu haura ashirin, kujerun da aka jera a wajen ta zauna duk da fitsarin da take ji amma tana so ya zo ya nuna mata ban d'akin.
Ana gama sallah suka kamo hanyar zuwa gidan, a hanya kuma Baba saida yama Umar Faruk fad'a akan abinda yayi, anan take ya bada hak'uri tare da alk'awarin kiyaye gaba, suna shigowa Baba ya tsaya d'akinshi na soro, Abbakar yayi kewayenshi dake had'e da nasu Umar, su Usman ma suka shiga d'akinsu dake kusa da kewayen iyayensu mata, saida ya shiga tsohon d'aki ya had'a kaf abin buk'atarshi dan tarewa d'akin amarya sannan ya fito da kaya nik'i nik'i, yana shigowa ya tsaya kallonta ganinta zaune da alama ba tayi sallah ba.
"Kinyi sallah?" tambayar daya wurga mata kenan.
Tashi tayi daga kishingid'ar da yayi ta fara rabka hannuwa tana jujjuyasu tana fad'in "toh malam, ina zanyi sallah? ka nuna min inda zan kama koda ruwa ma bare nayi alwala, naga gidan naku har yanzu bak'in da suka zo biki basu tafi ba, to ina zan fita bansan kowa ba."
Ya gane akwai cin zarafi a maganarta, amma saiya dake ya nuna mata da hannu yace "ga ban d'akin nan."
Yana fad'a ya wuce da kayanshi ya shige d'akin ya ajesu a inda yaga wuri kafin yayi zaune yana tilarwar karatu, tunda ta lek'a taga matsatsan bayin ta fito ta sameshi d'akin tace "wai malam me kake nufi? waccen abar itace wurin wanka, da komai da komai?"
"Itace, idan zaki shiga ki shiga, idan ba zaki shiga ba ki zauna a haka matsalarki ce." ya fad'a ba tare daya kalleta ba.
Cikin d'aga murya tace "inaaa, wallahi ba zan iya ba, to wannan idan na shiga zan iya tsayuwa ma kuwa? tunda ni dai ba gajera bace, uwa uba kuma kai, ya za kayi kenan?"
"Babu ruwanki dani." ya fad'a a daqile.
"To dama me yayi ruwan nawa da kai, ni dai ka samo min gurin da zanyi wanka a wale , amma ba wannan kurkukun ba."
Tana fad'a ta koma gado ta zauna, ganin da gaske take kuma gari na haske yasa yace "ki tashi kiyi sallah, in yaso kyazo kici gaba da zaman har sarkin zama ya sameki."
"Ba zanyi ba har sai nayi wanka."
"Ki tashi nace." duk da jin amon muryarshi ba wasa amma bata tashi ba.
A zafafe ya taso yayo kanta yana fad'in "dake fa nake magana kina jina kinyi shiru, zaki tashi ko saina b'allaki?"
Gabanta ya tsaya yana kallonta itama kuma shi take kallo, tsaye ta mik'e fuska a had'e tace "wai me? dukana za kayi? hahaha, kai dai kasan da ganina wallahi ba zan daku gareka ba, dan ba zan tsaya sanya ba wajen zage k'arfina mu daku da kai ba, idan kuma hakan ya gagara tofa akwai k'ungiyoyi da dama masu kare hakk'in mata, wallahi tsaf zansa a d'aure min kai."
Saida ya shafi kansa yace "idan harna tashi dukanki, to ki sani dukan da zan miki bama zaki iya tuna meya faru dake ba bare har kiyi k'arata ba, shi yasa nake so ki bini a hankali mu zauna lafiya."
"Yanzu wuce kiyi sallah, dan akan wasa da sallah wallahi sai ajimu dake a kaf garin nan."
Ba yanda ta iya dole ta wuce ta shiga ban d'akin ta kama ruwa sannan ta fito tayi alwala ta koma d'akin, saida ta jima kafin ta samu hijab d'in da Mamie ta d'inka mata sabbi sannan ta d'auki sallaya zata shinfid'a ta kallesa da harara tace "ina ne gabas?"
A tunaninshi iskanci ne kawai amma ta sani dan haka yace "ki kalleni kiyi sallahn."
Ai kuwa shinfid'awa tayi tana kallonshi ta kabbara sallah, ganin da gaske take sallaceshi za tayi yasa yayi saurin cewa "wai ke bahaguwar inace, yanzu nan shine gabas? dallah malama can zaki kalla."
Wata hararar ta sake banka masa sannan ta juya ta daidaita ta ci gaba da sallahta, tun daga sallah ya fahimci akwai matsala kuma yayi niyyar gyara mata, tana idawa shi kuma ya shiga wanka kasancewar akwai k'aramin panpo ciki, yana fitowa ya samu ta koma kan gado tayi kwance, gashi yana so ya canza amma ya kasa, lura da tayi da hakan yasa ta tab'e baki ta juya masa baya tana fad'in "me zan kalla a jikin? sai kace wata mayya."
Bai kulata ba harya gama shirinsa cikin jan raiga mai dogayen hannu da bak'in wando da takalma qafa ciki bak'ak'e, yayi kyau sosai sai turarenshi daya fesa sannan ya juya zai fita daga d'akin dan yau babu aiki , saurin juyowa tana fad'in,
"Kaga malam, wannan shirgin kayan naka ka tattaresu daga nan, ka bud'a armoire (drower) nan na qarshe akwai wuri ka zubasu."
Ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi kafin ya fara d'iban kayan yana jerawa, duk kayan saida ya samar musu matsuguni sannan ya rufe, ya sake juyawa zai fita kenan Ruk'ayya ta rabka sallama daga k'ofar d'akin....
*Me kuka ce fan's a game da zaman nan*π
_Ina sonku masoyana , addu'o'inku ma kad'ai sun ishemu farin ciki._ Allah barmu daku.π
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_My π
±K, ina tayaki murnar kammala wannan novel mai suna, π *NA BAKI RAYUWATA* π, wallahi Allah har cikin raina nake ji kamar na gani da idona a lokacin mutuwar Affan, sosai wannan labarin ya shigeni dan saida na zubar da hawaye na gaskeπ, Allah yasa wannan fad'akarwa da ki kayi taje inda muke so kuma ayi anfani da darasin ciki, Allah ya baki ladar tare da sakamakon gidan aljanna, Allah kuma ya qara miki lafiya sai mun jiki a next novel._ *ina yinki tawan.*
_My Seeya, barka da fara sabon novel mai suna *QADDARATA*, daga jin sunan kasan zai bada kala dan kowa da tashi qaddarar, Allah ya baki ikon kammalashi lafiya kamar yanda kika fara lafiya, fatan nasara my see see._π
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣1⃣
"Wa'alaiki salam, Ruk'ayya shigo." cewar Umar Faruk.
Wata sallamar ta sake yi tare da bud'a labulan d'akin ta shigo, saida ta sunkuya ta aje kwanukan dake hannunta sannan ta d'ago tace " ina kwana yah Umar, ina kwana aunty Khairat." ta fad'a tana kallonta.
Umar Faruk dai ya amsa amma banda Khairat da take tunanin itace matar tashi, jin bata amsa ba yasa ta kalli Umar Faruk tace "dama Mama ce tace na kawo muku abin karinku."
Juyawa tayi ta fita Umar Faruk kuma yace "na gode."
Kwanukan ya d'auka a aza saman karamin tebur d'in dake tsakanin gado da doguwar kujerar nan sannan ya zauna yana kallonta, ita kam ta d'aure fuska dan haushin Ruk'ayya taji sosai, ganin shirun ba zai gyarashi ba yasa yace "ki taso ki zuba mana abinci muci."
Cikin jin zafi tace "nice zan zuba maka abincin? to kar Allah yasa kaci, ni kaga nayi kama da masu zuba abinci, ka tab'a jin koda labari cewa an ganni ina zuba abinci ko a gidanmu, ai kaima ka gani ranar, dan haka in zaka zuba ka zuba kaci."
Shiru ya d'anyi na dakiku kafin ya tashi inda yaga tarin kayan anfani ya d'auko plate da cokali guda biyu ya zo ya fara zubawa, saida ya gama ya kalleta yace "ki taso kici."
Sai lokacin ta juyo ta kalleshi, plate d'in ta kalla ganin malku ne (naman kan rago) yasa ta yamutsa fuska tace "wacece? ni zanci wannan abun? bana cin a wannan lokacin, kawai kaci abunka."
Banza yayi da ita kawai ya d'auki bred ya fara ci, yana cikin ci yaji tace "wannan itace matar taka?"
Cak ya tsaya daga kai lomar da zaiyi, cikin rashin fahimta ya kalleta amma sai tace "wallahi ban tab'a tunanin zan iya auren mutumin da bai min alk'awarin zama dani ba ni kad'ai, amma sai gashi wai na auri mai mata, mtssss, rayuwa kenan."
Shi kam tunani yake ko bata san jiya ne aka daura masa auren ba, to kenan iyayenta basu fad'a mata ba kome? ji yayi abincin ya fita a ransa kawai ya fita ya wanke hannu ya dawo d'akin, zaune ya sake yi a inda ya tashi yana kallonta yace "wannan ba *matata* bace, kanwata ce, jiya ne aka daura aurena kuma bata tare ba sai nan da wata biyu."
Kallonshi tayi amma saboda harbawar da zuciyarta keyi yasa ta kau da kai tana guna guni, ganin ba za tayi magana yasa ya mik'e ya d'auki turare ya fesa a hannayenshi sannan ya fice ya barta.
Wani bala'in haushinshi take ji dama matar duk da bata ganta ba, ta jima cikin d'akin har rana ta take sosai sannan ta mik'e ta nufi waje, tana fitowa daga 'karamin kewayen nata ta ja ta tsaya tana 'kerewa gidan kallo, yana da girma amma yawan mutanen gidan yasa duk an matseshi , duk yara na islamiyya sai Ruk'ayya kad'ai dake k'ok'arin hura wuta dan d'ora abincin rana, sai kuma Saratu dake kamata da alama a tare ake girkin , iyayen kuma su uku suna zaune duk da dai biyu sun had'e kai waje d'aya, ta jima tsaye babu wanda ya lura da ita har saida haushi ya kamata yanda Ruk'ayya keson wutar ta kama amma tak'i kunnuwa.
Cikin d'aga murya tace "waike dan Allah ba zaki bar hura wutar nan bane, duk kibi kin cika mutane da hayak'i, wai dama da ice kuke d'ori? tabb'."
Sai lokacin kowa dake wajen ya kalleta, Ruk'ayya ma juyowa tayi sai dai kafin tayi magana ke Mama Maimuna sai kika ce "kaji kuma wani iyayi , to in tabar hura wutar dame za ayi d'orin kenan, ko kin tanadar mata wani abun ne? kiji rashin kunya kai."
Mama Sa'a ce tace "ah to dai ganin min hanya, mu za'a yiwa fitsara anan."
Takowa Khairat ta fara yi saida tazo har gabansu ta tsaya tace "daku nake magana? kunji nace kune da kuka samin baki? to karku sake min irin haka in baso kuke na muku rashin mutunci ba, ku in banda ma qaddara kun isa ku ganni cikin gidan nan bare har kumin katsalandan a harkata."
K'wafa tayi ta juya zata wuce Sa'a tace "ke mu kike wa rashin kunya? kinsan komu su waye? muma fa iyayen Umar Faruk ne."
"Saime? idan ku iyayenshi ne nace saime? na shiga harkarku ne? ko kuma shi yace ku dinga shiga tawa sabgar? to bana so."
Tana fad'a ta juya su Mama da Saratu kam mamaki ma ya gama kashesu daga inda suke, sun d'auka ta tafi ne amma sai suka ga ta sake fitowa da wayarta a hannu da da d'aya daga cikin kujerun nan, ta zauna a bakin k'ofar shiga b'angaren nata, waya take sai dai basa jin me take fad'a, Ruk'ayya dai ta samu wutarta ta kama bayan wuya da tasha ta fara aikinta gadan gadan, su Mama Sa'a kuma sai satar kallonta suke daga nan amma baki ya mutu murus, a qalla awa d'aya aka d'auka tana zaune ta d'auki wayarta ta kara a kunne saboda kiran daya shigo, tana d'auka tace "ok ina zuwa." ta kashe wayar.
Mik'ewa tayi ta nufi hanyar da take tsinkayan mutane na wucewa ba kallabi a kanta sai wannan k'aramar rigar da zane ta fita, a k'ofar gidan ta tsaya wasu samari ne guda biyu, "yawwa ku shigo dashi." ta fad'a tana komawa cikin gidan, Umar Faruk dama ba wane wurin yaje ba suna k'ofar gida shida Ishaq da wasu abokansu su hud'u, ji yayi kamar zai fashe daya tsinkayeta amma ya zaiyi, sharewa kawai yayi ya basar, suna shiga gidan ta kalli Ruk'ayya tace "ki nuna musu inda zasu aje miki."
Kowa da mamaki yake kallonta da samarin nan saboda ganinsu sun shigo da cuisinière mai guda hud'u da kuma butalin gas 5kilo, duk da suna cikin zulumin abinda tayi saida kowa yayi farin ciki, sai dai mahaifiyar Umar Faruk najin d'ard'ar, da ba lallai malam ya amince ba, nan Ruk'ayya ta nuna musu cikin wata rufa suka had'a mata shi sannan suka juya inda Khairat ke tsaye, dama ta shiga d'aki ta fito kudi ta mika musu masu yawa sukayi godiya suka tafi, itama d'akin ta koma tayi kwance Ruk'ayya da Saratu kam ai sai suka mayar da tukanansu sama cikin jin dad'i, ai sai suka manta da rashin kunyar da tayi, yayin da Mama Sa'a da Mama Maimuna suka waro ido suke tunanin sunci arzik'i dan haka su kwantar da kai kawai.
Yara na dawowa kowa baki bud'e sai farin ciki, nan suka rankaya suka nufi d'akin dan ganin amarya, suna zuwa sun sameta ta kasa bacci tunda ta shiga zafi ya dameta duk da pankar data aje gabanta, binsu take da wani kallon tsana da qyama suma yaran kallonta suke saboda kallon da take musu, ganin sunyi zaune wasu qasa wasu akan kujera yasa tace "ku kuma fa daga ina?"
Mai wayon cikin ne yace "ina kwana aunty amarya, mu kannan yah Umar ne, jiya bamu ganki ba kuma kuma da safe muka tafi islamiyya, shine yanzu muka zo mu ganki."
"Tofa." ta fad'a a wahalce.
Sauka tayi daga kan gadon ta nufi wata coffre ta bud'a ta d'auko chocolat tazo ta bawa kowa d'aya d'aya, haba ai da gudu aka fita ana murna ana ji wannan amarya mai ja ce, πhaba kudai baku sani ba, dan ita ta basu ne dansu tafi su barta, suna fita cikin farin ciki suka had'u da Umar ya shigo gidan shima, cike da murna sukayi kanshi Zeinab na fad'in "yah Umar, kalla aunty amarya ta bamu."
Fuskarta ya shafa yace "ince dai kun mata godiya?"
Shiru sukayi suka kalli juna dan sun manta, ai da gudu suka sake komawa shi kuma ya nufi wajen Ruk'ayya da Saratu dake girki baki bud'e har sun kusa kammalawa, "wannan fa 'yan mata?"
Saratu ce ta harareshi tace "na fad'a maka ka daina kirana yan mata fa."
"To naji na daina, ina kuka samu wannan?"
"Aunty Khairat ce tasa aka kawo mana." cewar Ruk'ayya.
Baice komai ba sai juyawa da yayi ya nufi b'angaren nasu ya rasa wane hali zuciyarshi ke ciki, farin ciki ko k'unci, yaran na fitowa shi kuma ya shiga, tana ganinshi ta sauko daga kan gadon tana fad'in "yawwa, dama kai nake jira dan Allah ka nuna min inda zanyi wanka, tun jira rabona da wanka fa."
Kallon kwanukan daya ci abincin safe yayi yace "amma aina nuna miki ban d'akin, watak'ila dama wankan bai dameki ba shi yasa kike so ki d'ora laifin ga ban d'akin."
"Humm, nida nake shiga cikin baho cike da ruwa nayi link'ayata son raina, shine zaka nuna min wannan banzan douche d'in kace wai a ciki zanyi wankan, kaima kasan ba zai yiwu ba wallahi, koka nuna min inda zanyi, ko kuma na tub'e a tsakar gidan nan nayi wanka na dan nan ne kad'ai zai isheni , in yaso sai kace ma kowa ya rufe idonshi."
"Kije kiyi mana ga wajen nan, inkin fasa ba sunanki Khairat ba."
Yana fad'a ya juya ya bar d'akin saboda rashin sanin wacece Khairat, bayanshi ta biyo ya dauka shi take bi hakan yasa ya tsaya yana kallonta, wuceshi tayi ta fito tsakar gidan ta fara kalle kalle, Ruk'ayya ce ta hanga tana kashe wuta da alama ta gama, "ke." ta kira Ruk'ayya dashi.
Kallonta Ruk'ayya tayi tace "na'am."
"Zo nan." da sauri ta taho ta tsaya gabanta, babban bokiti nake so ki cika minshi da ruwa ki aje min nan, saiki fad'awa iyayenku su koma d'aki zanyi wanka."
Da mamaki fal a fuskarta ta kalli Umar Faruk dake bayansu, ce mata yayi "kije kici gaba da aikinki."
Wucewa tayi Khairat kuma ta kalleshi tace "aini ba musaka bace zan iya da kaina."
Kewayen nasu ta shiga ta samu bokiti ta fito da nufin d'ebo ruwa a bakin panpo kawai ya rik'e hannunta yace "ke mahaukaciyar inace ne? me yasa baki da h...."
Bai k'arasa ba tace "wallahi karka kuskura ka k'ara kirana bana da hankali ko mahaukaciya, wai ka mantani ne da kake fad'a min haka, ko dan kaga ana kiranka da mijina shi yasa, to bana so wallahi kaji na fad'a maka."
Fizge hannunta tayi zata wuce yayi saurin tare gabanta yace "kinga saurareni, kiyi hak'uri ki shiga nan kiyi wankan , daga baya zansa a gyara miki tunda ba kya so, kinji?"
Zuyawa tayi ta kalli douche d'in sannan ta kalleshi tace "idan ma baka gyara ba wallahi ni zansa a gyara, kawai douche sai kace gidan b'eraye."
Wucewa tayi ta fad'a douche d'in ta cire kaya ta cillo kamar yanda ta saba, rigar data jefo qarshe sai a fuskar Umar Faruk da zai shiga d'akin, a hankali ya janye rigar ya kalli sauran kayan pants bras da zanin, sunkuyawa yayi ya kwashesu ya shiga dasu d'akin ya aje mata, ruwa ta makama jikinta ta d'auki sabulu ashe bata d'auko ba ta d'auka douche d'inta ce wacce ke akwai komai da komai, cikin d'aga murya tace "ka d'auko min sabulu."
Shirun da taji yasa ta sake bud'a murya tace "ka d'auki min sabulu, kona fito na d'auka."
Tun maganar farko ya jita ya kuma tashi d'auka, jin abinda ta fad'a a qarshe yasa yana fitowa daga d'akin yana b'are sabulun a cikin kwalishin yace "kizo ki d'auka mana."
Yana daf da kaiwa bakin douche d'in ita kuma ta zuro da kai za tayi magana, da sauri ta dage qirjinta saboda bayyanar da yayi tare da komawa ciki tayi shiru, yana ganin haka ya juya bayanshi ya mik'a mata sabulun yana fad'in "gashi."
Amsa tayi sannan ta fara wankan shi kuma ya fita daga gidan, Ruk'ayya ya turo ta d'auki kwanunan ta wanke sannan ta zubo musu wani abincin ta kawo ta aje, duk lokacin Ruk'ayya na mamakin irin wankan da take data jima haka, amma a b'angaren Khairat fad'a da guna guni kawai take rusawa daga cikin douche d'in, sai gashi ta fito ba tare da tayi abinda ta saba yi ba, ta fito daga wanka cikin minti sha biyar zuwa ashirin, d'aki ta shiga ta fara shiri tana ci gaba da masifa akan douche d'in.
K'aramar riga ce mai siraran hannaye ta kamata sosai duk ta fito mata da mamanta , sai kuma jan siket data d'ora a saman rigar har kusa da qirkinta, a bud'e yake siket d'in sai dai iya gwiwa ya tsaya mata, raba gashinta tayi gida biyu tasa k'ananan chouchou (ribom) ta d'aureshi, bata wani kwalliya ba sai turare data shafa ta kuma fesa sannan ta d'auki wayarta tasa takalma ta fito farfajiyar gidan.
Wata kujerar ta d'auka ta aza 'kofar kewayen nasu ta zauna dan zafi ya isheta, daga yaran har iyaye satar kallonta kawai suke babu wanda yayi magana, mahaifiyar Umar Faruk kuma tana so tayi magana amma tana jin tsoron wulak'ancin da zata mata, waqa tasa a wayar ta fara biyarta tana rausaya daga zaune, mak'ota da yan uwa suka fara shigowa ganin amarya, amma duk wanda ya shigo saiya nufi wajen mahaifiyar Umar Faruk ya zauna yana tambayar ina amarya, da an nuna masa Khairat saiya tashi yana addu'a Allah ya kyauta, a qarshe da taga kowa ita yake kallo, aje wayar tayi ta zuba tagumin rainin hankali tana bin kowa da ido itama, hakan yasa gidan yayi shiru sai magana qasa qasa.
Baba da Abbakar ne suka taho zasu shigo gidan ganinsu yasa Umar Faruk ya biyosu suka shigo, da sallama suka shigo amma ta Umar Faruk saita tsaya saboda ganin Khairat da wannan kayan a jikinta, Abbakar ma dai duk'e kai yayi qasa ya nufi inda mahaifiyarsu take zaune ya tsugunna, Baba ma haka ya k'araso jiki ba k'wari saboda ya riga daya shigo, kamar wanda k'wai ya fashema a ciki Umar Faruk ya tako ya nufi wajenta, yana kaiwa cikin zafin nama ya finciko hannunta yayi cikin d'akin da ita.
Qarar da tayi lokacin daya fizgi hannunta yasa Baba ya kalli Mama yace "kinga, tashi dan Allah kira minshi, sai yayi b'anna yaron nan kin sanshi da bak'ar zuciya, karya lahanta 'yar mutane."
Da sauri ta tashi ta nufi d'akin nasu, suna shiga ya jefata saman gado cikin b'acin rai, zaiyi magana ta rigashi da cewa "meye haka wai, kana haukane? ni sa'arka ce da zaka min wannan pigar kazar mahaukaciyar."
"Mtssssss." tsaki tayi ta fito daga d'akin zata sake komawa inda take, shi kuma dama tsakin yafi bashi ma haushi, da azama ya biyota ya cakumo hannunta ya juyo da ita da k'arfi, wani irin zafine daya ratsata saboda rik'on daya mata yasa ta janye hannunta daga gareshi hawaye fal idonta, kasancewar shima yayi niyyar sakinta yasa ta fad'a saman kujerun dake wajen, kuma bata fad'a da kyau ba kawai sai kujerar ta wuntsila da ita ta fad'i qasa, qara ta saki mai k'arfin gaske hakan yasa Baba dake can tsaye hankalinshi ya sake tashi, Mama kuma ta karasa danno kai ciki, samu tayi Khairat na kokarin tashi tsaye hakan yasa ta kamata ta tashi tana kallon Umar Faruk, "meye haka Umar Faruk, kana lafiya kuwa?"
Kallon matar Khairat tayi tace "kece mahaifiyarshi?"
Kai kawai Mama ta d'aga mata, kallon bayan hannunta tayi da har gurin ya karce jini ya fara fitowa saboda hannun ya had'u da bango, maida hawayenta tayi ta fizge hannunta daga Mama kawai ta koma d'aki, Mama kuma harara ta bishi da ita tace "ai saika fito mahaifinka na nemanka."
Juyawa tayi zata fita ya kamo hannunta ya rik'e ya marairaice yace "wallahi Mama ban mata komai ba, dan Allah ki fad'awa malam."
Wucewa tayi ta barshi kawai dole ya biyo bayanta, da hannu Baba kawai ya masa alama ya boyoshi d'akinshi, cikin sanyin jiki ya bishi d'akin suka zauna, cikin hikima Baba ya dinga mashi nasiha da gargadi har a qarshe ya dora da "ba haka ake ba Umar Faruk, a matsayinka na namiji, dole akwai bukatar kafi matanka hak'uri, saboda su matane kuma masu rauni , mace zata iya yin abu, kai a ganinka waouta tayi amma ita sai tace kuskure ne, dan haka dole ka dinga hak'uri wannan zuciyar taka ka dinga tausarta, musamman kai daka fara da mata biyu, duk ranar da Allah ya had'aku zama gida d'aya, dole zaka gane ba kada wayo dan dole sai sun gwara maka kai, nasan ka sani dan kai shedane akan zaman da nake da iyayenku, dan haka dan Allah bana son wannan yawan hushi da zafin zuciya, ka rage kaji ko?"
"To Baba, insha Allah zan gyara."
"To Allah yasa, yanzu kaje ka bata hak'uri dan Allah, sannan ka mata godiya akan d'awainiyar da tayi, dan mahaifiyarka ta fad'a min, tashi kaje Allah ya maka albarka."
"Ameen Baba, na gode ."
A haka ya tashi ya tunkari b'angaren nasu yana tunanin ya bata hak'uri kamar yanda Baba yace, ko kuma dai ya shareta kawai.
_Ya kuka ce? kuna ganin zai bada hak'uri, ko kuma zaiyi taurin kai?_ππ
*Ina barar addu'arku yan uwa, Allah yaba mahaifiyata lafiya, tana jin jiki, yer uwata ma na fama da tasku na rayuwar aure, gidan miji da tsangwamar kishiya , plss ku tayamu da addu'a.*
0 comments:
Post a Comment