Zai kama hannun tayi saurin janye hannunta ta d'aga masa hannu tana fad'in " karka kuskura ka tab'ani, mugu kawai azzalumi, wallahi Allah saika sakeni na koma gidanmu, ba zan iya zaman wannan takaicin ba."
Wani tafarfasa yaji zuciyarshi nayi tare da bugawa da k'arfi, wajen kayanshi ya nufa ya bud'e ya d'auko wani magani pommade ya bud'e ya lak'ata a hannunshi ya matso zai shafa mata, tsaye ta mik'e akan gadon tana fad'in "nace karka tab'ani ko, ko ana dole ne? ban son taimakon naka."
Danya nuna mata ba damuwa yayi da ita ba kawai ya cilla mata maganin a jiki yace "idan kinga dama ki shafa da kanki, yarinya sai taurin kan tsiya."
"Nice yarinyar? Umar Faruk ni kake fad'ama yarinya? lallai *zaka gane kurenka* wallahi."
Zaune tayi akan gado shi kuma ya matso kusanta yace "yaushe aka haifeki to?"
Sama da qasa ta wurga masa harara tare da jan tsaki, bata daidaita bakinta ba ya kama labb'an nata ya matse sosai wanda yayi silar sake fito da wasu hawayen daga idonta saboda masifar zafi, duk da idonta daya ga sunyi ja saida ya qara murd'e bakin yace "zaki sake min tsaki?"
Rintse idonta tayi sosai hawaye na zuba, sake murd'ewa yayi yana fad'in "za kiyi magana ko saina cire bakin? fad'a min naji zaki sake hararata ko tsaki?"
Kasa magana tayi saboda ya rik'e bakin sosai, cikin fashewa da kuka ta girgiza masa kai a hankali cike da takaici, shima harara ya dalla mata ya saki bakin yana fad'in "marar kunyar banza kawai, wallahi ki yarda na sake gani kiga yanda zamu kwashe dake."
Zaune yayi akan kujera ya fara zuba abincin da Ruk'ayya ta kawo ta aje, ita kam hannu tasa ta dafe bakinta gam tana kallonshi, had'a ido da sukayi yasa ta sake banka masa wata hararar, danya tsorata yasa ya taso da azama yana fad'in "baki daddara ba kenan? bari kiga yanda zanyi dake."
Da gudu ta wuntsila daga kan gadon tayi d'aya b'angaren tana nunashi da hannu tace "wallahi ka matso kusa dani zan illataka."
Murmushi kawai yayi ya koma ya zauna ya gama zuba abinci ya kalleta har yanzu tana tsaye yace "kizo kici abinci."
"Ni ba komai nake ci ba, ina da tsari na."
Tab'e baki yayi ya fara cin abincin, amma bai kai ko ina ba sai wata zuciyar tace masa "da safe ma bata ci komai ba, a hakane Umar Faruk zaka tafiyar da iyalinka? kai kaci ita kuma baka damu da taci ko karta ci ba."
Ajiye cokalin yayi ya kalleta yace "ki fad'a min me zaki ci?"
Sai lokacin ta zauna bakin gadon tana fad'in "karka damu dani, ka d'auka zamana a gidan nan kamar naje k'auyen kakanni na ziyara ne, dan haka zan kula da kaina."
" *Khairat*."
Saida taji gabanta ya buga tare da sanyin jiki saboda yanda ya kira sunanta, bata kalleshi sai dai tana sauraro taji me zaice, ganin bata kallonshi yasa kawai ya qyaleta shima, saida ya gama cin abincinshi sannan ya tashi ya fita ko kallonta baiyi ba, ita kuma tana ganin ya fita ta sake kama bakinta saboda har yanzu zafi yake mata sannan ta bishi da harara tace "mugu kawai." sake haye gadon tayi ta kwanta, taso tayi bacci amma ina zafi da matsatsi sun hanata, dole tashi tayi ta sake fitowa farfajiyar gidan, lokacin wasu na d'aki wasu na tsakar gidan, zaune tayi dan har yanzu kujerar na nan inda take.
Usman ne ya doso cikin gidan, da matuk'ar mamaki yake kallonta ganin bak'uwar hallita a gidansu, ko kad'an baya tunanin matar Umar Faruk ta kasance haka, cike da fara'a yace "sannu ko."
Da hannu ta masa alamar yazo, ba musu kam kamar sakarai ya nufi wajenta, tsaye yayi gabanta yayin da mutanen dake wajen kallo ya koma kansu, rik'e hab'a tayi ta tangale hannu da kujerar tana kallonshi tace "kana da abin hawa?"
"Eh, ina da moto."
"Da kyau, aikenka zanyi restaurant ka siyo min abinci."
"Ke kuma awa?" ya fad'a yana mata tuhumammen kallo.
Mik'ewa tayi tsaye tace "ka bari idan wanda nake zaune dominshi yazo ya fad'a maka koni wacece, amma yanzu ka fara zuwa aiken nawa."
D'akin data nufa ya tabbatar masa matar Umar Faruk ce, kuma wannan itace Khairat, kai kawai ya girgiza ya juya ya kalli mahaifiyarshi da yasan sarkin surutu ce amma tayi shiru, tunkararta yayi ya tsugunna gabanta yana fad'in "Mama, ita kuma haka take?"
"Kai, tashi kaje abinda ta saka bana son surutu, kuma kayi sauri ka dawo." cewar Mama Sa'a tana yi tana kallon k'ofar da Khairat zata fito.
Fitowa tayi amma ganinshi gaban wacce take tunanin mahaifiyarshi ce yasa tayi zaune saman kujerar tana jiranshi, da k'arfi Mama Sa'a ta turoshi ya dawo gaban Khairat ya tsaya, jikka goma guda uku ta bashi ta fad'a masa abinda take so, wucewa yayi yana tsananin mamaki akan abincin da zata ci zaka kashe duk wannan kud'in, lallai yaran nan iyayensu sun kwashe mana kud'i suna facaka yanda suke soπ inji Usman faπ.
Ta jima tana jiranshi amma bai dawo ba, har saida ranta ya gama b'acewa taji abinda take so d'in ya fita a ranta, ta tashi kenan zata shiga d'aki Usman ya danno kai cikin gidan, wani wawan tsaki taja tare da nunashi tace "saika zauna kaci ai, ni bana so."
Shigewa tayi d'akin shi kuma ya tsaya da leda a hannu yana kallon k'ofar, da gudu gudu Mama Sa'a ta taso ta karb'i ledar zata shiga d'akin Usman yace "canjin fa."
Dawowa tayi ta karb'a ta wuce d'akin Khairat mahaifiyar Umar Faruk na kallonta tana jin tsoron abinda zai biyo baya, da sallama ta shiga cike da ladabiπ€ sau hud'u tayi sallama ana biyar ne Khairat tace "ki shigo."
Da murmushi ta shigo tana k'arewa d'akin kallo tana ji kamar ace d'akin tane ko kuma na 'ya'yanta mata masu aure, aje wayarta tayi tana kallonta cike da tsana da wulak'anci amma ita bata damu ba, ledar ta mik'o mata tana fad'in "gashi 'yata , kiyi hak'uri kici kinji, kinsan yaran yanzu sai hak'uri, inka aikesu sai sun b'ata lokaci kafin su dawo, amma na miki alk'awarin ba zai sake ba daga yau."
Gatse gatse Khairat tace "baki ji me nace mishi bane? nace yaci idan kuma ba zai ci ba, ke kici ko kuma ku zubar a shara, amma ni na gama da babin wannan kuma, zaki iya tafiya."
Ba tare data damu ba ta sake murmushi ta mik'o mata kud'in tace "to ga canjinki."
"Suma ku rik'e bana so." ta fad'a tana maida abin sauraronta a kunne.
Da dariya cike da farin ciki ta juya ta fita, amma abin mamaki saita d'auki kwano ta juyo abincin ta zauna Usman da sauran yaran dake nan suna kallo da mahaifiyar Umar Faruk ta fara ci tana fad'in "harkar arzik'i aida mutanen arzik'i ake yinta."
Usman da haushi ya kamashi ficewa yayi daga gidan, ita kam ko a jikinta cin abinta tayi tasha ruwa saura ta bawa yara, amma kasancewar sun samu tarbiya sai basu karb'a ba suka ce sun k'oshi, masifa ta fara tana fad'in "yara an koya muku bak'in hali tun kuna k'anananku, to ku aje kar Allah yasa ku ci d'in ."
Kud'inta kuma bata bari ma kowa ya gani ba, ko abokiyar cin mushen nata dan dama tana d'aki tana bacci.
******************
Mamie da Papa sosai suke cikin damuwar rashin 'yar gudaliyarsu, haka duk suke zama shiru kowa da abinda yake tunanin a kanta, haka ma ma'aikatan gidan suna damuwa ta b'angaren kyauta da taimako, amma ta b'angaren wulak'anci da yawan aiki kuma suna farin ciki da hakan, amma dai kam tabbas suna kewarta saboda ita kad'aice 'ya a wajensu.
*******************
Ana gama sallah isha'i Umar Faruk ya shigo gidan danya shirya saboda yace ma Zuby yana nan zuwa, da sallama ya shigo tare da leda a hannunshi, bata amsa ba kuma bata kalleshi ba sai ayabarta data d'auko a fridge take ci tana korawa da fresh milk, aje ledar yayi saman tebur ya d'auki maclean da brush ya shiga wanka, ya d'an d'auki lokaci kafin ya fito sanye da dogon wando fari da kuma towel ya rufe jikinshi dashi, ya jima tsaye yana shafawa yana fesawa kafin ya fara k'ok'arin saka kaya, ganin yana zame wandon daga jikinshi yasa Khairat saukowa daga kan gadon da duk ta ya mutseshi ta fito a d'an kewayen nasu ta zauna, saida ta daidaici ya gama shiryawa sannan ta shigo, gaban madubi ta ganshi yana daidaita hularshi, da kuma waya a kunnenshi ya danneta da kafad'a.
Muryarshi taji qasa qasa yana fad'in "to ki shirya min kanki, dan gani nan zuwa yanzu, kinga tunda aka d'aura mana aure bamu had'u ba."
Shiru ya d'anyi sannan yace "ok to, sai nazo."
Juyowa yayi yaga Khairat tsaye tana kallonshi, wuceta kawai yayi yana sa wayarshi aljihu sannan yasa takalmi ya d'auki leda d'aya a cikin wanda ya aje ya kalleta yace "wannan taki ce."
Juyawa da yayi zai fita yasa Khairat tayi saurin cewa "wannan fa ta wacece?"
"Zubeida, amaryata."
Kai tsaye kuma ya fita daga gidan ba tare daya sake kulata ba, tab'a ledar tayi taji kaza ceπ(ina sonki kaza), a hankali ta fara d'aga qafafunta harta koma kan gado, sai dai ta rasa meke damunta da taji zuciyarta na mata k'unci duk taji ba dad'i, haka ta rasa me za tayi gaba d'aya kalmar Zubeida amaryata ta tsaya mata a rai, daga ta dafe baki saita dafe goshi ko kuma k'ugu, a hankali ta lumshe idonta amma sai tayi saurin bud'ewa saboda jin hawaye sun zubo mata, hannu tasa ta share ta tashi ta shiga 'yar k'aramar douche d'in ta cire kayan jikinta ta jefosu kamar yanda ta saba ta fara wanka, saida ta gama ta fito kuma ashe babu towel, kamar yanda tayi da rana haka ma yanzu tayi, da gudu ta fito ta shigo d'akin sannan tayi shirin bacci, rigace mai 'yan hannuwa sai wandon dogo har qasa amma bai kamata ba sannan ta kwanta, bacci ne ya gagareta saboda zafi fitowa tayi farfajiyar gidan, kowa yayi shinfid'arsa ya d'aura gidan sauro ya kwanta, kewayenta ta koma ta zauna akan kujera tana sauraron waqoqi daga nan kuma bacci ya d'auketa zuciyarta na tsananta bugawa, gashi tunanin Umar da Zuby ya kasa barin qawqwalwarta.
****************
Tunda yace zaizo tanti Ma'u tayi farin ciki Zuby kuma ta shiga wanka, tun kafin ta fito kuma Umar yazo, koda ta fito mahaifiyar tata harta had'a mata 'yan tame tame da tsarabe tsarabe, saida tayi kwalliya sosai ta shirya cikin riga da siket na shadda sannan Mama ta zaunar da ita bakin gado ita kuma tana tsaye ta mik'a mata roba mai cike da nono da magunguna masu k'arfin gaske ta shanye, wani farin magani ta bata tace "tashi ki matsashi a gabanki."
Tashi tayi kamar yanda tace haka tayi sannan ta aje mata kaskon wuta ta zuba wani turaren tace ta sake tsugunnawa, gyara jikinta tayi sannan Mama tace "kina jina ko? kiyi duk abinda kika san zaija hankalinki ya kwanta dake, dan wannan abinda kika gani bana wasa bane, nasan dai duk gaggawarshi bai riga ya kusanci waccen karuwar ba, dan haka kar kiyi wasa da wannan damar."
Ganin Zuby tayi qasa da kanta alamar kunya yasa tace "to kuma miye na kunya? nifa uwarki ce dan haka karki damu."
A sanyaye ta kalleta tace "wallahi Mama tsoro nake ji, gabana ma fad'uwa yake."
"Saboda me? mijinki ne fa, kasheki zaiyi? keni nama ci uwaki idan kika b'ata min rai, to in banda abinki kowace mace ba saida tazo wannan gurin ba kafin nan ta wuce, muma duk bata haka muka sameku ba."
Shirun da tayi yasa tace "maza wuce kije yana jiranki."
Lemon da Mama tasa aka siyo mata ta d'auka ta fito ta shiga d'akin da aka gyara mata ta zauna kafin lokacin tariyarta, zaune yake akan k'atuwar katifar dake tsakiyar d'akin, k'ura mata ido yayi harta zauna kusa daf dashi duk da irin ruwan da take jin gabanta na fitarwa, sosai ta masa kyau kasancewarta siririya kuma kayan sunbi jikinta, ga kwalliyar da tayi sosai hakan yasa ta masa kyau.
Wani kashe ido ne da tayi yasa jin tsikar jikinshi ta tashi had'e da fad'uwar gaba, itace tayi k'arfin halin cewa "sannu da zuwa angona, na barka kana ta jirana ko? kayi hak'uri to na tsaya maka shirine."
Cikin wani irin yanayi da shi kad'ai yasan me yake ji yace "ba komai, ai girmanki ne."
Lemon ta d'auka ta bud'e sannan ta kai masa a baki tana sake rikirkitashi da wani sabon kallon, kurb'a d'aya yayi ya kau da kansa gefe tare da d'auko ledar daya shigo da ita mai d'auke da kaza da kuma lemuka masu sanyi, bata yayi ta karb'a tana fad'in "meye kuma?"
"Ki diba ki gani mana, kazar amarcinki ce."
Ya fad'a yana dariya, ita kam gabanta ne ya fad'i dan haka tace "na shiga uku, nifa bana son cin kazar nan."
"Me yasa?" ya fad'a yana kallonta.
Cikin tsoro tace "wallahi ina ji k'awayena suka fad'a wai duk wanda yaci kazar nan, to shima dole sai an...." kuma sai tayi shiru.
"Ina jinki, kina tunanin na saka wani abu ne a ciki?"
"A'a, kawai dai ance idan kaci kaima zaka biya."
Cike da zolaya yace "ke kuma biyanne kike jin bak'in ciki ko?"
Tuna abinda Mama ta fad'a mata yasa ta fad'a jikinshi tare dasa hannunta ta shafo qirjinshi amma ba tace komai ba, tunda ta fara shafarshi ta kwance masa lissafi ido ya rufe yana sauraronta, bata daina ba saima botir d'inshi data b'alle ta zura hannu tana shafoshi, cikin wata rikitaciyar murya ya kira sunanta da,
"Z..u....beid...a."
D'ago kan da tayi ta kalleshi tana marmad'a ido yasa ya sake fita hayyacinshi, a hankali ya had'a bakinshi da nata ya fara tsotsa, tun yana aika sak'on a hankali harya fara da sauri sauri, sai kuwa ya kwantar da ita akan katifar ya hau samanta ya cire hularsa da riga da.....πBK za tace waya aikeni.
Umar Faruk dai ya manta da ina yake sai faman aiki yake, rana ta farko daya fara sanin 'ya mace kenan, shaye shayen da Zuby tayi yasa Umar Faruk bai sarara mata ba ko kad'an, hakan ya janyo ya mata babbar k'ofaπshiga gari, wacce ba lallai Khairat nada ita ba, ya jima sosai kafin ya d'agawa Zuby k'afa , kwance yayi yana kallon sama yana sauke numfashi duk da gumin daya had'a, Zuby na ganin haka ta yunk'ura ta tashi zaune ta d'auki rigarta ta yab'a tare da saka siket d'inta ta mik'e zata fita, da sauri ya tashi ya d'auki wandonshi qarami ya saka ya rik'ota yana fad'in "ina zaki je haka Zubeida, miye haka?"
Cikin layi da shan wahala tace "dan Allah ka k'yaleni na tafi, wallahi ciwo nake ji, zanje wajen Mama ta taimaka min."
Tare gabanta yayi yace "haba Zuby, ya kike nema ki tona min asiri? ki bari dan Allah ki gyara jikinki, karki fita haka."
Zip d'in rigarta ya saka mata tare da bata d'an kwalinta ta d'aura sannan ya saka nashi kayan shima, sallama ya mata ya bar gidan dan ba zai iya had'a ido da Mama ba, haka ya bar gidan gabanshi fad'uwa kawai yake kamar bai samu nutsuwa ba, a haka harya isa gida.
Zuby na shiga d'aki ta fad'a saman gado, da sauri Mama ta d'auko babban roba da ruwan d'umin data d'ora musu tunda ta kara kunne a k'ofar d'akin taji nishi da sambatun Umar Faruk da kuma kukan Zuby ta dafasu , da taimakonta ta samu ta gasa jikinta sannan tayi wanka kafin baccin wahala ya d'auketa.π
******************
00:30 ya shigo da mashin d'inshi a cikin gidan bayan ya kasheshi yanda Baba ba zaiji ba, yana daidaita zaman mashi d'in yana sad'af sad'af zai shiga ciki muryar Baba ta daki kunnuwanshi da kiran sunan "Umar Faruk."
Rintse ido yayi sosai yana jin bugu zuciyarshi na qaruwa, a hankali ya juyo ya kalli Baba dake qofar d'akinshi, kallon da yake masa yasashi zubewa k'asa ya durk'usa yana sauraran Baba.
"Umar Faruk, ya ina yabanka sallah zaka kasa alwala, kai da kanka Umar Faruk, yanzu ka kyauta kenan? to waima daga ina kake?"
Yana shafa kai cikin rashin gaskiya yace "kayi hak'uri Baba, daga gidansu tanti Ma'u nake."
"Au, yanzu acan kayi dare kenan haka? Umar Faruk yanzu yarinyar mutane daka bari fa? ya kayi da ita?"
Shiru yayi ba magana dan haka Baba yace "to kaje ka bata hak'uri, dan kamar ka d'auki kwananta ne ka kaiwa wata, ko ban tambayeka ba nasan akwai abinda ya shiga tsakaninka da Zubeida, dan yanayinka ya nuna hakan, ka tashi ka ka b'ace min da gani, kuma wallahi ka kiyaye shiga hakk'in matanka, dan mugun kamu Allah zai maka." yana fad'a ya shiga d'akinshi ya barshi.
Jiki ba k'wari haka ya tashi yana k'arewa kanshi kallo dan baya so ya shiga da wannan yanayin da Baba yace ya gani a tare dashi, kallon ahlin nashi yayi da sukayi nisa a bacci, k'ofar kewayen nasu a bud'e take haka ma wuta ba'a kashe ba, yana dosa kai ciki ya tsaya cak saboda ganin Khairat zaune akan kujera harta langab'e kamar zata fad'i, ga abin sauraronta a kunne wayar kuma ta fad'a a d'aya saman kujerar, abinda ya d'aga mashi hankali shine yawan motsin da take saboda sauron dake ta cizonta sai sosar jiki take, a hankali ya sunkuya daf da ita ya saka hannayenshi ya .....
_Kuna ganin d'aukar zaiyi, ko kuma me zai mata.?_
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣3⃣
Hannu yasa ya zare abin sauraron daga kunnenta ya d'auki wayar ya kashe, a hankali ya daddab'a hannunta kafin yayi na biyu kuma ta bud'a ido, zunbur ta tashi tsaye tana zare ido sai kuma ta fara sosar jiki kamar mai k'yaya, jin gaba d'aya jikinta ya d'auki rad'ad'i na cizon sauro yasa ta lab'e baki kamar jaririya ta fashe da kuka tana ci gaba da sosar duk inda take jin kyaikayi, Umar Faruk kuma mutuwa yayi da kallonta cike da birgewa yanda tayi kalar yara, wani murmushi ya saki ya nufi kayanta data jefo lokacin da za tayi wanka ya d'auke ya shiga dasu d'aki, jim kad'an ya fito ya fad'a douche danya tsarkake kanshi, kallon juna sukayi ita kuma ta wurga masa harara da tsaki dan sai lokacin ta tuna rabuwarsu dashi, douche ya shiga ita kuma ta shige d'akin amma ta kasa komawa ta kwanta.
Fitowa yayi cikin doguwar riga ya sameta zaune tana kukan shagwab'arta, zaune yayi akan kujerar yana kallonta, ganin har yanzu sosar jiki take yasa ya taso a hankali ya zauna bakin gadon tare da sauke ajiyar zuciya, waigawa yayi ya kalleta cikin taushin murya yace "Khairat."
Cikin kukan shagwab'a ta fara magana "wallahi Allah ni dai ka mayar dani gidanmu, ba zan iya zama anan ba sauro ma kasheni zaiyi, dan Allah ka taimaka ka bani izini na tafi gidanmu."
Ta sake fashewa da wani kukan, "Khairat." ya sake kiran sunanta.
Kallonshi tayi dan haka yace "tashi kiyi alwala kizo."
"Ni ina maganar ka kaini gida, kai kuma kana maganar naje nayi alwala." ta fad'a a matuk'ar harzuk'e.
"Ki tashi kiyi abinda nace." ya fad'a yana komawa kujerar.
Saboda ibada ne yasa ta tashi ta fita ta d'auro alwala ta dawo ta sameshi, tunda ta fita ya duba ledar daya aje tana nan yanda take, yana ganinta ya tashi ya shinfid'a sallaya yace "kisa hijab d'inki ki tsaya bayana."
"Meye kuma haka?" ta tambaya tana kallonshi.
Kallon daya mata yasa ta d'auki hijab d'in ta saka ta tsaya daga gefenshi a bayanshi, kabbara sallah sukayi, raka'a biyu sukayi tare da jimawa zaune Umar Faruk yana jero musu addu'a, suna sallamewa zaune yayi sosai tare da juyowa ya kalleta, cikin nutsuwa da hikima ya fara magana,
"Khairat, da farko na d'auka labarina dake gajeran labari ne, amma daga ranar da zuciyata ta yanke min hukuncin na amince da aurenki, saina yarda labarinmu dogone, hak'ik'a aurena dake Allah ya qaddara faruwarsa bamu ba, idan har za ayi maganar gaskiya, to kin wuce tsarin aurena, matsayinki da nawa ba d'aya bane, amma duk da haka sai kuma Allah ya hukunta aure tsakanina dake, hakan na nufin akwai abinda Allah ya tsara mana a rayuwarmu, dan haka zaifi mu jira hukuncin ubangiji, amma maganar saki ki daina ba kyau, sannan ina so kiyi hak'uri dan nasan na b'ata miki sosai saboda aurenki da nayi, amma dan Allah Khairat ki bani dama na cika alk'awarin dana d'aukarwa iyayenki ta hanyar samar maki ingantacciyar ruyuwar da suke miki fata da kuma burin samu."
"Khairat akwai tambayoyin da nake son yi miki a game da addininki , kuma ina fatan zaki amsa minsu kamar yanda suke, ina so na d'ora miki daga inda kika tsaya, dan haka ina son fara sanin yanda kike tsarkake kanki, domin kuwa saida tsarki ne zaka fuskanci ubangijinki, idan har kina wankan tsarki kamar yanda aka koyar to alhamdulillah, dan haka ina jinki ki fad'a min."
Hannu ta zura a cikin hijab d'inta ta d'an sosa damtsenta da duk k'urajen sauro suka fito mata, shiru tayi kamar bada ita yake ba, hakan yasa yace "Khairat dake nake fa."
"Toni me zance maka? kana ganin sauro duk ya b'ata min jikina, ya kake so nayi."
Tsaye ta mik'e ta cire hijab d'in tana shirin hayewa gado taji ya rik'e qafarta, juyowa tayi tace "dallah sakeni malam."
"Ki dawo magana muke." ya fad'a ya matuk'ar tsaurare.
Tana turo baki gaba ta koma ta zauna shi kuma yana bin hannayenta da kallo, saiya ji tausayinta saboda duk fatarta tayi ja sai shatin cizon sauro a jikinta.
D'orawa yayi da "ina jinki."
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi tace "bansan me zance maka ba, zan fad'a maka rabona da islamiyya tun ina 'yar shekara bakwai, ko kuma zan fad'a maka ni bansan komai ba, abinda na koya daga wankan tsarki a wa'azi naji a gurin malamai da dama, duk da sunce wankan akwai wanda zaka iya zuba ruwa tun daga samanka har qafafunka tare da cud'a jikinka ma ya hallata , to amma ni hankalina yafi kwanciya ga wanda yake tare da alwala, dan haka ni shi nake yi."
"Ina so nasan yanda kike yinshi."
Kallonshi tayi tace "wai dan Allah ba zaka bari harda safe ba, yanzu bacci nake ji ga wannan masifar sauron."
"Ina jinki." yayi maganar ba wasa.
Hararanshi tayi taja tsaki, da sauri ya kalleta ya kai hannu zai kamo bakinta ta tuno da karonsu da rana, da sauri ta jaye daga wajen tayi baya tana fad'in "to naji zan fad'a maka."
"Nakan fara da niyyar yin wanka sannan na tanadi ruwana masu tsarki da tsarkakewa, sannan na wanke gabana da kyau ta yanda duk wata qazanta zata fita har izuwa gwiwoyina zuwa cibiya, sannan nasa sabulu na wanke hannayena da kyau, sannan na fara d'aura alwala sau d'aya d'aya har saina zo shafar kai, ana so ya samu ruwa sosai sannan na k'walk'wale kunnuwana, daga nan kuma zan fara wanke barin damana tun daga sama har qasa, sannan na koma barin hagu shima tun daga sama har qasa, sannan na wanke qafar dama sai kuma ta hagu, wankana ya kammala kuma idan lokacin sallah yayi ma zan iya yin sallah dashi in dai har banyi wanka da sabulu ba, to yanzu zan iya kwantawa *malam Umar Faruk mai tambayar wankan tsarki*?"
Yaji dad'i sosai da har wankanta ya zamana yanda sunna ta koyar ne, dan haka ya dinga mata tambayoyi tun daga lokacin daka gama alwala har lokacin da zaka shiga sallah, kuma cikin ikon ubangiji ta amsa saboda tambayoyi ne masu sauk'i, abu d'aya shine ko hizib d'aya ba zata iya karanta maka ba daga farko zuwa qarshe, dan haka Umar Faruk yace "karki damu, in dai har zaki bani goyon baya, to kema zaki samu hasken qwaqwalwa dana zuciya, ina so zan fara miki karatu daga gobe daga inda nake ganin ya kamata a d'oraki, kuma ina so kisa abin a ranki ta yanda ko bana nan zaki iya tambayar wani ko wata, a cikin gidan nan Khairat ko *Fateema, da Alqasim* kika tambaya zasu iya d'oraki daga hizib d'aya zuwa talatin, dan haka kije ki kwanta gobe insha Allah zan fara miki da littafin *AL'AKHDARI, HUSNUL MUSLIM, KHAMSUNA HADITH, DA KUMA LITTAFI MAI TSAKI DAGA HIZIB D'AYA ZUWA GOMA*, idan har kika saka abin a ranki to Allah zai taimakeki cikin sauk'i ki dinga fahimtar abinda kike koya, saida safe."
Ya fad'a yana tashi tsaye tare da kabbara wata sallah, duk da taga sallah yake amma bai hanata cewa ba "na d'auka ba zan tab'a samun hasken rayuwa ba, ina son sanin addinina sosai, amma duk lokacin da nayi yunkurin zuwa inda za'a koyar dani, sai k'awayena da zuciyata su nuna min na wuce wannan wurin ko kad'an ba ajina bane, kuma ma ai ina da ilimi na zamani ga wayewa ga kuma kudi, sai dai na manta dashi ilimi ba'a tsufa da nemanshi, kuma wannan ilimi saida shine zan samu tsira ranar gobe qiyama, insha Allah zan koya kuma lokacin ya kusa zuwa da zanje gaban Mamie na karanta mata sura mai tsayi wacce za tasa tayi mamaki harma ta saka min albarka."
Tana fad'a ita kuma tayi kwance a gado sai dai ina bacci bai samu ba, kiran sallah ne ya daki kunnuwansu dan haka Khairat taji wani sabon shauk'i a game da son ibada ya shigeta, tun kafin ya sallame ta tashi ta fita tayi alwala, zata shigo d'aki shi kuma zai fita masallaci, tsaye tayi ta fita sannan ta shigo saida ta fara da *salatul fijir* sannan tayi sallah, tun bata tashi ba bacci ya fara fizgarta daga nan, jingina tayi da gado kawai ta dunk'ule cikin hijab ta fara gyangyad'i, a haka Umar Faruk ya shigo ya sameta, zaune yayi yana tasbihi yana kallon fuskarta, murmushi kawai ke bayyana a fuskar tashi saboda tuna tambayoyin daya mata kuma ta amsa, ga kuma abinda yaji tace a game da son karatun, a cikin ranshi yace "taya zan bata hak'uri kenan?"
Bai samu amsa ba kuma bai daina kallonta ba har gari haske yana kallon yanda take bacci kuma ko motsawa ba tayi ba, a sama sama yake iya jin hayaniya a tsakar gidan, dan haka ya d'auka ko masifa ce dasu Mama Sa'a suka saba da ita, hayaniyar ce ke sake yin sama ga kuma kuka da yake ji wanda yake tunanin na *Yusuf* ne d'an Abbakar, wannan kukan ne yasa Khairat bud'a ido ta sauke akan Umar faruk dake kallonta, zaune tayi da kyau tana mike qafafu tana murza ido shi kuma tuni ya d'auke kai daga kallonta, jin kukan da hayaniyar mutane yasa ta kalli Umar Faruk tace "waiku gidanku ba kwa baccin safe ne? suna damuna fa."
Kafin yayi magana ta mike tsaye ta cire hijab zata kwanta kenan taji ana kiran sunan Umar Faruk, da sauri ya fita daga d'akin tana binshi da harara da jin haushin mutanen gidan da basa barin bacci, da azama ya sake shigowa taga yana lalabar aljihun rigarshi daya cire jiya, yana d'aukar makulli yace "zanje na dawo."
"Ina?" ta fad'a dan taga tashin hankali a idonshi.
Yana barin d'akin yake fad'in "zamu kai Yusuf asibiti."
Jin haka yasa Khairat biyo bayanshi da sauri itama ko kallabi bata d'ora a kai ba bare takalma, Yusuf na rik'e a hannun Abbakar sai kuka yake Umar Faruk kuma yana gaba danya fitar da moto, duk kowa yayi cirko cirko Ruk'ayya ce Khairat ta dafa tace "meya sameshi."
Saida ta kalli kayan jikinta sannan tace "wallahi wata 'yar k'aramar lula ce mai kamar ball ya samu yake wasa da ita, shine ya saka a hanci ta shige masa, kuma gata ana gani amma tak'i fitowa."
Jin haka yasa Khairat rugawa a guje ta tari gaban Abbakar ta finciko Yusuf daga gareshi ta zaune dashi a qasa ba tare data damu ba, ganin haka sai kowa ya matso inda take duka suka rufesu suna kallon ikon Allah, Umar Faruk ma zai fitar da moto yaga kuma an taru dan haka ya dawo shima, amma abin mamaki da bai tab'a tunanin ko a mafarki ya faru bane ya faru, Khairat ya gani duk da hawaye da miyo ga majina data b'ata fuskar Yusuf bai hanata saka bakinta a hancinshi ba a inda babu lular tana busawa, sosai take busawa kafin ta d'ago kai ta kalli Abbakar tace "ace duk yawankun nan kun kasa taimaka mishi, sai wani maganar asibiti kuke."
Sake maida bakinta tayi da k'arfi tana busawa, sai kuwa lular nan tayi b'ul ta fito daga hancin Yusuf, wata irin sa'ida da salama da yaron yaji yasashi saurin rumgume Khairat ya manna kanta a qirjinta dake k'yam dashi yana hararan Umar Faruk daga nanπ, d'an shafa kanshi tayi sannan ta mik'awa Abbakar shi yana amsa ya kalleta sosai yace "mun gode sosai k'anwata."
Mik'ewa tayi amma sai Saratu ta rik'e hannayenta duka biyu ta had'e tana kuka tace "na gode sosai yer uwa, tashin hankalin dana shiga yasa na manta ta yanda zan fara taimaka masa, na gode sosai."
"Ba komai." ta fad'a kamar dai wacce aka saka dole, kakkab'e wandonta tayi ta juya ta nufi kewayenta kowa kuma na binta da kallo saboda abinda tayi babu wanda yayi tsammanin yinshi, saida kowa ya kama harkar gabansa Umar Faruk na tsaye, daga baya yaji an dafa kafad'arshi, juyawa yayi sai yaga Mama ce, murmushi yayi zai wuce yaji Mama tace "zuciyarta mai kyau ce, tana da abinda ba kowa yake dashi ba, wato *tausayi da taimako*, duk wanda yake da wannan halayen to mai imani ne shi, d'an duhun dake cikin rayuwarta nake so naga ga yaye matashi ka mayeshi da da haske , kaje Allah ya muku albarka."
Wucewa Mama tayi shima kuma ya nufi kewayen yana jin wani irin nishadi da farin ciki na lullub'e zuciyarshi, yana shiga ya ganta ta d'ibi ruwa tanata wanke baki wai ita majina, murmushi kawai yayi ya shiga d'aki, tana shiga itama tayi zaune tare da d'aukar wayarta tana aika kira, ba jimawa aka d'auka a daqile tace "ka kawo min mota ina jiranka."
Duk da wanda ta kira yaso ya tambayi gidan nata, amma ta riga data kashe wayar, Umar Faruk kuma tashi yayi ya shiga wanka, koda ya fito ta tashi zata shiga itama tace masa "aiki zanje, idan ka rigani zuwa kace Habiba ta share min bureau (office)."
Tana fad'a ta wuce abinta shi kuma yayi shiru yana tunanin kuma ta yanda zaiyi ya dakatar da ita, harta cire kayan jikinta sai kuma taji wani irin sanyi ya lullub'eta, dafa wuyanta tayi sai taji zafi ruf, tsaki tayi dan tasan sauron nanne kawai ya zuba mata zazzabi dan haka ta d'auko kayanta a hannu ta manta da inda take rayuwa yanzu, duk da ta raumgume kayan amma dai kallo d'aya zaka mata kasan babu komai a jikinta, tana dosowa zata shiga Umar Faruk ya bud'e labule zai fita gaida iyayensu, da sauri ta durk'ushe qasa ta rintse ido tare da rufe fuska da kayan, kasa gaba yayi sai baya da yayi ya dawo cikin d'akin ya fad'a saman kujera kamar an turashi, yana hangenta ta labule bata tashi ba yasa ya tashi ya d'auki towel d'inta daya gani rataye ya bud'e ya cilla mata a jiki, sai lokacin ta mik'e ta d'aurashi sannan ta shigo, zaune tayi ta sake d'aukar waya ta danna wani kiran, kasalance tace ,
"Kina asibiti ne?"
Shiru alamar tana saurare kafin tace "wallahi zazzab'i ne ke son rufeni, zanzo yanzu."
Aje wayar tayi duk yana kallonta amma baice komai ba, tashi tayi ta bud'a kayanta ta d'auko doguwar rigar atamfa ta saka tabi jikinta sosai kuma ta mata kyau, d'an kwali ta d'aura sannan ta d'auki qaramin mayafin daya dace da kayan ta aza a kafad'a, poshet (post) d'inta ta d'auka ta bud'a wata jakar ta d'ibi kud'i ta zuba a ciki sannan ta d'auki wayarta tasa takalmi ta d'auki turare ta feshe jiki dashi, takowa tayi har gabanshi ta tsaya tace "idan driver Mamie ya kawo min motar ka karb'a ka aje min ni zan hau taxi."
Zata fice yace "ki saka hijab d'inki."
Juyowa tayi tace "iko? wai iko kake so ka min? to ban tab'a fita dashi ba ba kuma zan fara yau ba."
Tsaye ya mik'e yana fad'in "kuma dole kisan cewa da dah da yanzu ba d'aya bane, wallahi ke baki isa ki zubar min da mutunci ba, idan kika fita a haka to mamaki da zulumi ne zasu hana mutanen unguwar nan samun shak'at, ace surukar malam Ahmad a haka, ina ba dani za ayi wannan fitsarar ba."
"Wato ma nice fitsararriya ko? to ba zanyi ba naga me za kayi, idan kuma zaka tursasani ne na gani."
Sallamar Ruk'ayya ce yauma tasa ya amsa tare da bata izinin shiga, yau ma gaishesu tayi sai dai Umar Faruk kad'ai ya amsa kamar dai jiya, aje kwanukan tayi ta fita abinta Khairat kuma ta juya har zata fita kuma ta tsaya ta sake kallonshi tace "idan iko kake so kaima a matsayinka na namiji, toka bari har figaggiyar matarka ta shigo gidan saika mulketa, amma bani ba *Hajia Khairat*."
Gyara tsayuwa tayi tace "duk da bana da ilimin addini, amma ka sani na kare mutuncina, kuma duk da bana da sani akai amma nasan abinda kayi jiya baka kyauta ba, ka raba dare a wajen amaryarka, kuma daga yanda ka shiga wanka a wannan tsohon daren ya tabbatar min da wani abu ya faru, amma karka damu na yafe maka badan komai ba saboda ni ba sonka nake ba, kuma bana qaunarka kamar yanda ba son auranka nake ba."
Bakinshi ne ya mutu dan haka dole yayi shiru yana kallo harta fita daga gidan, mutanen dake tsakar gidan kuma kowa kasa motsi yayi yana kallonta harta fita, sai dai Mamar Umar Faruk tayi niyyar fad'a mata gaskiya dan wannan ba abu bane mai yiwuwa, malam ma dake k'ofar gida suna tattaunawa da mak'otanshi yana ganinta ya d'auke kai dan karya nuna ma ya santa, amma dai shima dole yaji a ranshi zai tsawatar mata da kanshi, bata sha wahalar samun taxi ba ta d'auketa kai tsaye sai asibitin kud'i asibitin da suke da familly docteurn su, *Clinique d'an magori* kai tsaye bureaun docteur d'in ta shiga, kasancewar suna ganema juna sosai yasa ta kwantar da ita ta saka mata sΓ©rum (drip), tana kwance amma suna hira baka ce Khairat ce ba mai ganin dama kafin tayi magana.
*****************
Tana fita shima ya fito ya fara shiga d'akin Mama Maimuna ya gaisheta saboda shine farko, kuma an nuna musu duka iyayensu ne dan haka d'aya ne, yana fitowa kuma ya shiga na Mama Sa'a, abin mamaki shine cewa da tayi "Umar Faruk ya 'yata, da fatan dai ta tashi lafiya?"
Kallonta ya d'anyi a fakaice sannan yace "da sauk'i Mama, dan yanzu haka ma ta tafi asibiti, zazzab'ine ya rufeta."
"Ayya, Allah sarki yarinyar kirki, Allah ya bata lafiya."
"Ameen Mama."
"Ai Umar Faruk kayi dacen mata wallahi, Allah dai ya baku zaman lafiya."
"Ameen Mama." ya fad'a a d'arare.
Yana fita daga nan ma d'akin mahaifiyarshi ya nufa, bayan sun gaisa ne tace "Umar Faruk ina ne matarka ta fita tunda safe haka? kuma kana kallonta ta fita da wannan kayan, kuma naga duka yaushe ne tazo da har zata fara fita."
"Kuyi hak'uri Mama, duk ni naja muku, amma insha Allah zan d'auki mataki akan hakan."
"To shikenan, amma dai banda duka ko wannan muguntar taka ka kama bakin mutum ka murd'e ko mintsini, ka mata cikin ruwan sanyi harta fahimta."
Cikin dariya yace "to Mama."
Daga nan kuma yayi d'akin Baba kuma ya sameshi yana karin kummalo, kuma Abbakar da Aliyu ma duk sunje gaisheshi, a tare ya musu nasihar daya saba na suji tsoron Allah su kyautata ibadarsu, sannan su guji d'aukar hakk'in wanda Allah ya had'asu zama dashi kona minti d'aya ne, daga nan kuma ya sallamesu suka tafi Umar faruk yayi tunanin sai Baba ya masa magana amma yaji shiru, yana fitowa yaga motarta a k'ofar gida, fita yayi suka gaisa da driver wanda Mamie ta fad'a masa unguwar shi kuma yayi tambaya, makullin ya amsa driver kuma ya koma dan ya hau taxi, shima d'aki ya dawo ya aje mata makullin sannan ya zuba abinci ya ci, Ruk'ayya ya tura ta gyara d'akin ta kuma d'auko kwanuka da kazar da bata ci ba.
_Kuna wulak'anta min kaza faπ_
Tunda ya nufi wajen aiki yake tunanin yanda mutane zasu kalleshi, kuma kam hakane ya faru dan yana shiga suka dinga zuwa suna masa wai barka, da qyar ya zauna mazauninshi Ishaq ya zuro kai yace "mutumina ina amaryar, ba dai ka hana ta fito ba?
Wata harara ya wurga masa yayi banza dashi, dan tunaninshi na gareta yana so yaji ya take a yanzun, gashi kuma baya da lambar wayarta, dubara ce ta fad'o masa daya tuna manager, kai tsaye bureaunshi ya nufa, yana bashi izinin shiga ya shiga ya samu wuri ya zauna, kai fa fara sosawa ya kasa magana.
Ganin haka yasa manager cewa "angon Hajiarmu, ya kuma kayi shiru? ina Hajiar tamu take? ko dai har yanzu baku gama cin amarcin bane?"
Wani tarr yayi da ido yace "kai manager, amarci fa? da Hajiar taku ? kamar dai ka mantata, nifa kaga ba wannan ne ya kawoni ba, lambarta ma nazo ka bani ina so zan kira."
"Me!? lambarta fa? kwananka nawa a matsayin mijinta? amma kace baka da lambar wayarta? anya Umar faruk."
Shiru yayi kawai yana jira ya bashi, ba yanda ya iya shima dole ya bashi lambar sannan ya fito yana doka mata kira, tunda taga lambar ta shigo wayarta taji gabanta ya fad'i ba gaira ba dalili, gashi kuma lambar sassauk'a hakan yasa ta birgeta, saida ta tsinke ya sake kira sannan ta d'auka, shiru dukansu sukayi kafin shi yace,
"Hello."
Lumshe ido tayi saboda yanda muryarshi ta daki kunnuwanta cikin nutsuwa, "hello." tace a matuk'ar sanyaye.
Shima dafe qirji yayi saboda wani irin bugawa da yaji yayi, da qyar yace "kina ina?"
"Mai gida kenan, ina asibiti har yanzu, sΓ©rum aka saka min."
Cike da nuna kulawa yace "subhanallah, amma kuma shine baki kira ba?"
"Dame zan kira? bana da lambarka ai, kuma kaima nasan yanzu ka samu tawa."
"Amma ai na samu, ki fad'a min inda kike yanzu zanzo."
"Ina Clinic d'an magori." tana fad'a ta kashe wayar, shi kuma yabi wayar da kallo.
Fita yayi ya hau mashin d'inshi ya koma gida sannan ya d'auki motarta ya tafi da ita dan ba zai dawo ba sai tare da ita πkasan kuma ba zata hau *Utu utu* ba.
_Kuna ganin zata yarda ta taho tare dashi a motarta, ko kuma shi zai dawo a qafane ya kai mata motar kenan?_π
_Luv u sis Alawiyya_π
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
```My Meelat, wannan page taki ce ke kad'ai, i love you.```
2⃣4⃣
Saida ya kirata ta kwatanta mishi wajen da take, yana kaiwa kofar d'akin docteur d'in ta fito danta basu wuri, gaisawa sukayi kafin ta fice tana yaba mijin na Khairat, koba komai a yanda ta ganshi tasan zaiyi wuya Khairat ta rainashi, kallon juna sukayi lokaci d'aya kuma suka d'auke idonsu, zaune yayi bakin gadon ita kuma ta nad'e qafafunta, kallon ruwan yayi yaga harma sun kusa qarewa, shiru sukayi babu mai magana har wayarshi tayi qara, yana ganin Zuby ce sai yaji wani haushi ya kamashi, tunawa da yayi abinda ya faru, amma kuma sai yaji tausayinta a wani b'angaren ganin yanayin daya barota, muryar Khairat ce ta katse masa shiru da "ka d'auka mana, ko sai tayi hushi, zaifi maka ka lallab'ata dan ita kad'ai gareka."
D'auka yayi baice mata komai ba, a daqile yake amsa gaisuwarta, da qyar yace mata "ya kike, da fatan kinji sauk'i?"
Zuby dake gaban Mama tana kallonta tace "da sauk'i dai, amma fa har yanzu ina jin ciwo."
"Ayya, sannu kinji, zai bari insha Allah, yanzu ki kashe waya zan kiraki ina wani wuri ne."
"Ina kenan yah Umar?"
Saida ya kalli Khairat ta gefen ido sannan ya rage sautin murya yace "ina asibiti."
"Subhanallah, wake asibiti yah Umar?"
Wannan karan kallon idon Khairat yayi wacce take latsa wayarta sai dai zuciyarta bugawa take da k'arfi, haushi take ji yana taso mata tana ji kamar ta bugeshi tare da wayar, sannan yace "auntynki ce ba lafiya, amma yanzu zamu koma gida serum d'in ta kusa qarewa."
Zaro ido tayi ta kalli Mama sai kuma tace "tana kusanka ne?"
"Eh, wani abu ne?"
"A'a, ka gaisheta."
"Zata ji."
"Yah Umar. " ta kira sunanshi.
"Na'am." ya amsa yana kallon Khairat.
"Sumbata nake so kamin wacce baka min ba jiya ka tafiyarka, kuma na d'auka zaka kirani amma baka kira ba."
Umar Faruk kam mamaki ne yasa yace "sumbata kuma?"
Da sauri Khairat ta d'ago ta kalleshi, sai kuma ta mayar da kanta k'asa.
"Eh, ko ban cancanci sumbar bane duk da jiya ne darenmu na farko?"
Qasa yayi da murya yace "kinga zan kiraki anjima."
"Wallahi ban yarda ni saika min." ta fad'a cikin shagwab'a harda kukanta.
A hankali ya tashi ya fita bakin k'ofar d'akin ya danna mata sumbar sannan ya kashe wayar, sai dai kuma Khairat tajishi hakan ya qara harzuk'ata.
Tana aje wayar tace "shikenan Mama, na shiga uku, wallahi harta fara laulayi."
_Keπππ laulayin lafiya._
"Meya faru, meya ce miki?" cewar Mama kamar zata had'eta.
"Waifa suna asibiti bata lafiya, kinsan dai ba haka kawai za tayi rashin lafiya ba, gashi abinda muke gudu ya faru, kuma ni na riga na bashi kaina tun ban tare ba."
πππππ _FAN'S JIHADI sukace ke kika jiyo_
Ajiyar zuciya Mama ta sauke tace "to kin gani, wallahi ba zan iya wannan kayan takaicin ba, dan haka shiryawa za kiyi kawai ki tare gidansa kema, in yaso duk abinda suke ayi a gabanki, dan zai iya mantawa dake anan d'in, yana can ya samu mai kud'i kenan ya fita harkarki, dan haka ki koma can ki zauna duk abinda suka ci kema kici wanda sukasha kema kisha, kinji ko?"
"Amma fa Mama ba...."
"Amma me? dan ubanki ana nuna miki annabi kina rintse ido, duk abinda nake yi ba saboda ke bane nake yinshi, dan haka ki fara shiri wallahi kin kusa komawa gidanki."
Tashi tayi ta barta ita kuma ta koma ta kwanta dan har yanzu ba dad'in jikinta take ji ba, dan ba qaramar wahala tasha ba abinka ga sabbin shiga.
******************
Ran Khairat a matuk'ar b'ace ba tare data kalleshi ba tace "ka kira min *Sadiya* tazo ta cire min na koma gida."
"Ki bari ta qarasa mana." ya fad'a yana kallon ruwan.
Bata san me yake damunta ba amma bata kosan had'a ido dashi, a zafafe tasa d'aya hannun ta janye sirinjin daga hannunta hakan kuma yasa jini ya fito tunda bata cire yanda akeyi ba, kallonta kawai yake ita kuma ta d'auki mayafinta ta laga a kafad'a tasa takalmi tayi hanyar fita, da kallo ya bita yana k'ok'arin kiran sunanta.
"Khai...k.k..." tuni ta fita dan haka ya biyota da sauri, har zai tari gabanta saiya tuna lokacin data maresa,π( ba kyau), cak ya tsaya sai kuma ya fara binta a baya har suka fita, Sadiya ce taga fitarsu a ranta tace "Allah ya had'aka sai hak'uri."
Tana fita farfajiyar ta tsaya saboda ganin motarta, juyowa tayi ta kalleshi lokacin daya tsaya gabanta, hannu ta tara masa tace " bani makullin motata."
D'ago hannu yayi zai mik'a mata sai dai kuma baya so ya bata, da k'arfi ta fizgi makullin tana fad'in "ka bani nan, ko taka ce?"
Tana karb'a ta dalla masa harara tace "inma kanayi ne dan naji haushi to ba zanji ba, da kai da matarka baku isheni kallo ba, kana k'ok'arin kaci mutuncina a gaban k'aramar yarinya saboda kaga damata, to kaje ka had'iyeta mana iyakar sumba , ba shikenan ba saiku huta."
Motar ta nufa ta bud'e ta shiga ta tako da k'arfinta tayi kwana domin ta hau kan titi, saida ta tsaya inda yake ta zuge galss tace "ka tari taxi ta mayar da kai inda ka fito."
Rik'e kugu yayi da hannu d'aya d'ayan kuma ya rik'e wuya, yana so ya fahimci wani abu amma ya kasa, to duk miye na wannan harzuk'ar? qarasawa yayi gaban titi ya tari taxi yace ya mayar dashi ma'aikata, abin mamaki shine baijin komai dan gane da abinda ta masa, ranshi bai b'ace ba kuma baijin haushinta, to me yasa?πka tambayi Hasfat A A, haka ya koma jiki ba k'wari wata zuciyar na raya mishi ya dinga taka tsantsan ya daina waya da Zuby a gabanta, wata zuciyar tace masa to akan me? ai matarka ce, haka dai har yamma tayi ya tashi ya nufi gida yana tunanin yau kuma wacce zai isko.
***************
Da qyar takai kanta shagon wani *Saminou* saboda jiri dan dama ba'a tashi lokaci d'aya idan aka gama sΓ©rum, kuma gashi ba wani abu bane a cikinta, tana zuwa ta paka motar anan, fad'a mishi da tayi bata jin dad'i yasa ya shiga motar ya tukata ya kaita gida, tare suka fita ya bata makullin motar a shiga gida shi kuma ya hau acaba ya mayar dashi, ganin layin da take yasa suka fara tunanin ko shaye shaye take, Ruk'ayya ce ta taso da Umar Faruk ya bata makullin d'akin ta bud'e mata sannan ta shiga, da k'arfi ta fad'a saman gado ta fashe da kuka tana fad'in "wayyo Mamie, zuciyata zafi take, ji nake kamar zata fasa qirjina ta fito, dan Allah Papa kazo ka d'aukeni mu kuma gida."
Ruk'ayya da taji haka yasa ta shigo a hankali ta fara cewa "aunty Khairat, lafiyarki k'alau? me yake damunki? ko baki da lafiya ne?"
Da qyar tayi zaune tana kallonta hawaye na ci gaba da zuba mata tace "ki bud'a fridge akwai madara a ciki ki d'auko min nasha."
Da sauri ta juya ta d'auko ta kawo mata saida ta bud'e murfin sannan ta bata ta kifa kai, saida ta shanye duka sannan ta jefar da kwalin , Ruk'ayya kuma d'aukar kwalin tayi ta rik'e ta sake tsayawa gabanta tana kallonta tace "aunty kina buk'atar wani abun?"
Saida ta goge hawayen dake fuskarta cikin shagwab'a tace "kin iya dafa indomie?"
_Ko dai kin manta ba Umariri bane?_
"Eh, aunty Khairat na iya." ta fad'a cikin ladabi.
Nuna mata tayi da hannu tace "ki bud'a coffre d'in nan akwai indomie, ki d'auki guda biyu ki dafa min, idan akwai k'wai ki had'a min dashi guda uku."
"Ai kuwa aunty babu k'wai, sai dai in za'a siyo ne?"
"Yanzu babu kwai a gidan nan? to jeki dafa hakanan kawai."
Tana fad'a ta kwanta saboda jiri, d'aukar indomin tayi ta fita nan ta fara dafa mata, cikin k'ank'anin lokaci ta gama ta kawo mata kuma taji dad'inta sosai, hakan yasa ta kalli Ruk'ayya tace "ke ba kamar yayanki ba, kina da kirki."
"Shima yana da kirki aunty Khairat, kawai dai baki fahimceshi bane."
"Ke mugu ne fa, k'etar tsiyace dashi."
Yar qaramar dariya Ruk'ayya tayi tace "ba zance miki a'a ba, yaya kam akwai zafi kuma akwai salon k'eta, amma kuma in dai har zaka dinga jin maganarsa sannan baka rainashi ba, to gaskiya zaku zauna lafiya dashi."
Cike da basarwa tace "ok, kije, idan na fita zan siyo k'wan saiku aje."
Tashi tayi tana fad'in "to aunty Khairat, an gode."
****************
Yana shigowa gidan tanti Ma'u ya samu tare da Mama suna hira, har qasa ya tsugunna ya gaishesu sai dai bai bari sun had'a ido da tantin ba, dan yasan tasan me yayi kuma tana kallonshi da abun, Mama ce tace masa "akan maganar tarewar Zubeida ne, ta yarda ta dawo gidan mijinta ta zauna itama tayi karatunta."
Kallon Mama yayi ya kuma kalli tantin, tanti Ma'u ce ta katseshi da "ko dai baka shirya tariyarta bane, kafi son ka dinga zuwan can gida kana....."
"Na amince tanti, yaushe ne?" ya katseta dan yaga zata tona mishi asiri, ita kuma dama ba ruwa bane a idonta, dan haka ba komai bane a wajenta danta fad'a kowa yaji.
"Nan da kwana uku ne." ta fad'a a kausashe.
Tashi yayi ya nufi kewayen nasu yana mamakin canzawarsu, tunda ya tunkari d'akin yaji kid' na tashi, can cikin mak'oshi yayi sallama dan haka ma bata ji ba, shiga kawai yayi tare da tsayawa k'ofar d'akin yana kallonta tana tiqar rawarta, kayan jikinta su suka d'aga masa hankali tare da tayar masa da wata kafirar sha'awa da bai tab'a jin irinta ba a rayuwarsa, iya cinyoyinta wandon yake sai rigar da ba za'a kirata da bras ba haka kuma bata fi bras girma ba, rintse idonshi yayi sosai ya cije labb'enshi , bud'e ido yayi ya sake saukesu a kanta, da k'arfi ta juyo hakan yasa gashinta dake sake saida ya tashi sama shima ya juya sosai, duk da ganinshi da tayi ba tayi wani yunk'urin kare jikinta ba sai dai dakatar da rawar da tayi, gumin data had'a yasa ta fara takowa itama da nufin fita, tsaye tayi saboda ya tare hanyar fitar kuma har yanzu idonshi na kanta ya kasa d'aukewa , hannayenta ta d'aga tana tattare gashinta tana kallonshi tace,
"Ka bani hanya zan wuce."
Ganin ya kasa gusawa kuma har yanzu kallonta yake yasa ta matso daf dashi ta d'aga kanta tana kallonshi saboda ya fita tsawo sosai, wani mayan kallo ta masa tana murmushi tace "yadai, kana jin wani abu ne?"
Da sauri ya dawo hayyacinshi hakan yasa girgiza kai, wani murmushin ta sake yi tace "hakan yafi maka."
Saida tayi kamar zata fad'a jikinshi kafin ta samu ta wuce saboda ya kasa matsawa a hanyar, takalmi tasa ta shiga douche tayi wanka duk da ta d'auki lokaci hakan yasa ma Umar Faruk tafiya masallaci saboda idan ya tsaya jiranta zai b'ata lokaci, harya dawo bata shirya ba sai d'aurin qirji daya sameta dashi tana shirin saka kaya, bai sake kallonta ba harya saka doguwar rigarshi zai shiga wanka tace "kayi hak'uri fa, d'azu na baroka acan wajen." ta fad'a tana dariya.
Kallonta yayi kawai yace "hmmmm, ya jikin naki?"
Saida ta nufo wajenshi ta bud'e fridge ta d'auki ruwa sannan ta fara bud'ewa tana fad'in "da sauki, amma dai ba zaka sake bari na kwana a cikin sauron nan ba ko? dan nan gaba nasan mutuwa zanyi."
Sallamar tanti Ma'u ce ta katsesu ta shigo ganin amarya, Umar Faruk ne ya leko yana fad'in "tanti shigo mana."
Khairat kuma wajen kayanta ta nufa ta fara neman wanda zata saka har tanti Ma'u ta shigo, Umar Faruk ne ya bata wajen zama amma Khairat ko kallo, cikin taushin murya yace "Khairat, wannan itace magajiyar Mama kuma mahaifiyar Zubeida."
"Oho , ina wuni Mama, ya Zubeida? fatan tana lafiya?"
"Um , lafiya lau."
Tana fad'a ta tashi tace "Umar ni zan wuce, zaka zo ganin matar taka?"
Saida ya kalli Khairat yace "eh tanti zanzo."
Tanti Ma'u kam mutanen nan ne da bakinsu baya da linzamin, kawai sai cewa tayi "da alama karuwancin harya fara tasiri a kanka, tunda gashi har saika kalleta kafin ka yanke hukunci."
Labule ta bud'a zata fita Khairat ta rufe wajen kayanta ta matso tana fad'in "yadai tsohuwa, me kika ce? sai naji kamar kince karuwanci ko?"
"Eh, haka nace, ko k'arya nayi ba karuwar bace ke? me ake kiran mace irinki inba karuwa ba? ke kar kice zaki min fitsara dan wallahi ba mutunci ne dani ba, ba zan duba cewa ke sarakuwata bace ko kuma kishiyar 'yata, tsaf zan kwab'e kayana na dakeki son raina."
Dariya kawai Khairat tayi, kasancewar ba mai son hayaniya bace hakan yasa kawai tace "bansan me kika sani akaina ba da har kike kirana da karuwa, amma ga dukkan alama 'yarki kike tayawa kishi tunma bata shigo gidan ba, to ba komai kije, amma ki sani ni Khairat da karuwa ce, wallahi da Umar Faruk bai kusanci 'yarki ba a daren jiya, ki dinga sanin me kike fad'a dan baki san me za'a fad'a miki ba idon kin b'arota da zafi, Umar Faruk kuma gashi nan ki d'auka ki kaiwa 'yarki, amma nasan saiya dawo gareni, koba haka ba...... *Faruk*?"
Ta fad'a tana fad'awa jikinshi tare da shafo fuskarshi, tsikar jikinta ne ta tashi haka shima, a take yaji zufa na tsattsafo masa, ba abinda ya masa dad'i kamar kiransa da tayi da *Faruk* dan babu wanda ya tab'a kiranshi da haka sai yau, bai iya cewa komai ba saboda mamaki, tanti Ma'u kuma cewa tayi "ke dai wallahi anyi tsinanniya marar kunya, yanzu a gabana kike rik'eshi haka kamar wata uwarki ce ta haifeshi."
"To wace kunya kuma? mijina ne fa, nan da qananin lokaci ma cikinshi zaki gani jikina." duk tayi maganar ne tana sake cukwikuye Umar Faruk.
"Mtsssss, Allah ya wadaranki 'yar iska kawai, wato kinzo kin samu wuri harda mik'e qafa, kamar ba kece yar d'an siyasan nan ba da ba'a fadanshi da alkhairi , ke da gani nasan baki samu tarbiyya ba daga wajenki uwarki, kuma nasan hakan ba zai rasa nasaba da tasu rashin tarbiyyar suma iyayen naki."
D'agawa tayi daga jikin Umar Faruk tace "ke tsohuwa, kifa kama girmanki, ba mutunci ne dani ba wallahi saina zubar miki da...."
Yayi saurin saka hannunshi ya rufe mata baki yana kallon tanti yana fad'in "dan Allah tanti kiyi hak'uri ki tafi, nace zanzo."
"A'a, saketa ka barta ta fad'i abinda take son fad'a danta nuna min ita yar zamani ce, da wallahi nima saina nuna miki ni tsohuwar zamani ce, wai har wani cika baki kike zaki raba Umar Faruk da Zubeida ko? to bismillah, idan kika fasa raba tsakanin nasu ke ba *'yar halak* bace, baki haihu cikin uwarki da ubanki ba, shed'aniya kawai marar kunya."
Jin abun na tanti wuce ya gona da iri yasa ya dafa kafadunta ya fitar da ita daga d'akin, Khairat kuma kanta ne taji yana sarawa da k'arfi sosai ga qirjinta da take jin yana d'an zafi ga kuma dukan da yake mata, hannu biyu tasa ta dafe kanta sosai ta rintse ido dan kamar saukar guduma take ji a cikin qoqon kanta, da qyar Umar Faruk ya fita da tanti daga gidan ya had'ata da Aliyou dake kofar gida yace ya rakata ta shiga taxi, wannan masifa data dinga yi yasa mahaifiyar Umar Faruk itama kanta ya fara sarawa saboda hawan jini ne da ita, ko kad'an bata qaunar hayaniya koya take.
Mikewa tayi da qyar badan tana ganin gabanta ba ta fara bud'a duk wani abinda take ganin za'a aje abu ciki mai mahimmanci kota samu taga maganinta, tana cikin dubawa Umar Faruk ya dawo d'akin, binta yake da kallo saboda ganin tana abu kamar makauniya dan ba daidai ba ma take tafiya, ganinshi a bayanta yasa ta dago hannunta dafe da kai tana ganin dishi dishi ta fara masa magana cikin yanayin matukar shan wahala,
"Dan....Allah ka tai ....maka min, a cikin kayan nan ka ....duba min...ma...ga...maga."
Bata qarasa ba tayi luuu ta fad'i kasa, da gudu Umar Faruk yayo kanta ya zube qasa ya fara kiran sunanta, shiru bata amsa ba, cike da damuwa yace "na shiga uku, tanti ta kwanto min bala'i, yanzu gashi bansan meye matsalar ba, ya zanyi da ita?"
Tashi yayi da sauri ya d'auki ruwan data aje akan fridge yazo ya zuba a hannu ya fara shafa mata a fuska, da qyar ta farfad'o sai dai da wani sabon ciwon kan, da kuka ta farka tare da saka hannaye biyu akai tana fad'in,
"Kaina zai fashe, ka taimaka dan Allah ka d'aure min, zai fashe, kaina zai tarwatse, ciwo yake min sosai, dan Allah ka d'aure minshi *Faruk*."
"Kanki ne ke ciwo?" ya tambaya cike da tausayi.
Itama cikin kuka tace "qirjina ma fashewa zaiyi, amma nafi jin ciwon kan nan, dan Allah ka taimaka min ka samo abu ka d'aure minshi."
Rufe ido yayi lokaci d'aya kuma ya bud'e ya saukesu a kanta, tsaye yayi tare da sungumarta ya rumguma a jikinshi, yanda ta kwantar da kanta a qirjinshiya yasa hankalinshi ya sake tsananta tashi, domin kuwa tsaf yake jiyo yanda jijiyoyin kanta ke harbawa, a hankali yake takawa da ita harya direta akan gado, ya qura mata ido yana ganin jijiyoyinta duk sun fito, alamu ne qarara suka bayyana masa irin wahalar da take ciki, haka kawai sai yaji inama ciwon ya koma kansa, koba komai zai fita juriya da hak'uri, gyara zamanshi yayi a kan gadon yasa hannayenshi biyu ya fara shafa kanta daga farkon inda take aza goshinta wajen sallah, har zuwa inda gashinta ya tsaya kusa da kunne, ya jima yana shafa mata kamar yana wasa jin haka kuma yasa Khairat shako wuyar rigarshi cikin azaba da rad'ad'i ta bud'e ido danta masa magana amma sai taga dishi dishin ma har yafi d'azu, dan haka ta d'ago kanta ta kai bakinta har saman hanshinshi sannan tace "ka d'aure min kaina nace, ko so kake na mutu? mugu kawai azzalumi."
Shidai baice qala ba harta saki wuyan rigarshi, yana cikin shafa mata ya matse daidai inda gashinta ya tsaya sosai da yatsa biyu, wata siririyar qara tare da zabura ta cakumi rigarshi ta shige qirjinshi tana rik'e hannunshi daya matse mata kai da k'arfi sosai, k'ok'arin k'wace hannunshi take dan ba qaramin matsa ya mata ba, shi kuma ya rik'e sosai hakan yasa ta kasa k'watar kanta, turmutsutsu kawai take a jikinshi tana zubar da hawaye, gashi tana rok'on ya saketa amma bata jin muryarta na fita, da qyar yayi dauriya ya k'arasa addu'o'in da yake karanta mata saboda yanda take had'a jikinshi da nata tana murzawa, ba tare daya d'auke yatsunshi ba yaja yatsun nashi da k'arfi har saida ya diresu akan inda take aza goshinta wajen sallah sannan ya saketa, tana jin wani sauk'i ya zirnyarceta ta fad'a saman pillow tana sauke numfashi amma idonta rufe, sai lokacin taji kan yana mata sauk'i sosai sai kuma taji qirjinta kamar zai tsage, hannaye ta d'ora akai tana murzawa, ganin haka yasa ya d'auke hannayenta yace "bara na taimaka miki, shima zai bari da yardar Allah."
Kallonta yake yana tunanin yanda zaiyi wannan taimakon, kiran sallah isha'i ne ya riske kunnuwanshi, a hankali ya fara k'ok'arin sauka daga kan gado amma sai yaga ta dunk'ule waje d'aya tana dafe qirjinta sosai, wani sauk'ak'ak'en numfashiya sauke sannan ya dawo ya zauna, gyara mata kwanciyarta yayi ta mik'e sosai kamar wata gawa sannan ya d'auke hannayenta daga qirjinta, "um um, Umar faruk, karka fara." cewar wani b'angare na zuciyarshi.
"Ba komai, matarka ce ai, ka d'auka yanzu ma wani *Jihadi* ne za kayi, domin tana cikin halin rayuwa ne da mutuwa."
"Hummmmmmm." cewar Umar Faruk.
A hankali ya kai hannu ya sab'ule d'aurin qirjin dake jikinta, wata 'yar k'aramar numfashi yaja tare da saka tafikan hannayenshi ya rufe fuskarshi, ba k'aramin rikita mashi lissafi sukayi ba, kasancewar Allah ya horesu gasu kuma b'ul b'ul dasu kamar na mai k'aramin ciki, jawur suke har sunfi fatarta haske uwa uba kuma kanπ, kamar wani abu ya cijesu saboda yanda suke jawur dasu kamar an sulb'esu, gasu giri giri suke babu alamar kunya a idonsuππ, bud'e idonshi yayi ya sauke a fuskarta sai dai idonta a rufe suke, da alama bata ma cikin hayyacinta, "k'uk'ut." ya had'iye yawu kafin ya kai hannunshi da tuni suka fara karkarwa ga gumi dake tsattsafo masa, dan tuni ya shiga masifa network kuma ya kawo service, awazarta duka biyu ya soka hannayenshi a qarqashi ya tallabosu, wata irin bank'arewa tayi ta tusa masa qirkinta a nashi qirjin saboda masifar zafin da taji, kwantar da ita yayi saita kuma tasowa tana kara 'kwak'umeshi, sake mayar da ita yayi yana fad'in "ki tsaya mana, bana son mugunta fa."
_To wai fan's, me Umar Faruk ke nufi da baya son mugunta, mema aka masa na muguntar?_
Nan ma dai addu'a ya mata ya tofa mata sannan ya rabu da ita yana ji yana gani jam'i ya wuceshi, sauka yayi daga gadon ya bud'a wajen kayanta ya d'auko wata rigar bacci da wandonta silip ya aje mata yana fad'in "ki tashi ki saka."
Sai dai bansan Khairat azabar ciwon kai yasa ji da ganinta sun d'auke ba na wucen gadi , ko alamar taji ma ba tayi ba hakan yasa ya d'auki kayan ya warware rigar yana kallo........
_Me kuka ce?π zai saka ne ko kuma dai yaya zaiyi?_π
πluv u my Meelat.π
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
*Sadaukarwa ga*
_Fateema_ momyn Dady
_Maman tasleem_
_Bismmilahir-rahman-rahim_
_Allahumma antas- salam, wa minkas-salam, tabarakta ya zuljalali wal-ikram._
*Astagfirullah wa atubu ilaikh.*
2⃣5⃣
Kamar zai fita daga d'akin kuma saiya kashe wutar d'akin ya dawo da rigar a hannunshi, duk da ba'a gani amma haka ya lalabata ya qarasa zame towel d'in, wandon ya d'auka ya fara saka mata sannan ya zura mata rigar, saida ya tabbatar komai yayi daidai sannan ya kunna hasken d'akin, daga inda yake ya kalleta ganin kayan sun mata d'as gwanin kyau, fita yayi daga d'akin danya tafi masallaci sai dai kuma yasan alwalarshi ta karye dole saiya d'anyi wankaπ ko sama sama neπ, haka kam akayi saida yayi wanka ya fito ya bud'a kayanshi zai ciro wasu kayan ya saka kawai yaga maganin da kakarta ta bashi, a hankali ya fara tuna maganganun iyayenta dama kakarta d'in, hakan yasa ya ya fad'a a fili "kenan wannan ne abinda ke damunta? to me yake janyo mata shi?"
Maganar kaka ya sake tarowa baya kawai sai yace "uhum, kenan b'acin rai da damuwa ne kamar yanda mahaifinta ya fad'a? ikon Allah."
Maida kallonshi yayi gareta tana bacci hankali nutse, shiryawa yayi ya aje magungunan kusa da ita ya fita ya nufi masallaci, shi kad'ai yayi sallah shi sannan ya hau mashin d'inshi ya d'an fita, baifi awa d'aya ba kuma ya dawo, har yanzu bacci take dan haka ya fito da clΓ© USB daya siyo ya mak'ala a tv ya jona ya fara sauraren k'ira'o'in, wannan karatun ne ya tasheta yana ganin haka ya taso zunbur yayi kanta, tana dafe da kanta ta fara k'ok'arin bud'e idonta, a kanshi ta saukesu tana kallonshi, saida ta saisaita kanta sannan ta kalli d'akin da kyau ta kuma kalli jikinta, da sauri ta dafe qirjinta ta kalleshi a tsorace.
"Ba wannan kayan bane jikina, waya canza min kayana?" ta tambaya tana kallonshi.
"Dank'ari." cewar Umar Faruk.
Da sauri ta sauka daga kan gadon tana fad'in "waya canza min kayan jikina, ka fad'a min gaskiya Faruk, kaine? yanzu kenan ka kalleni saboda kaga bana cikin hayyacina? kamin adalci kenan? saboda kawai kana mijina."
"Kinga dan Allah, bafa abinda kike tunani bane, ba..ni ba...bane ba sauya miki kaya."
Kafeshi tayi da ido tace "kalleni."
Kallonta kam yayi sai dai gaba d'aya gabansu dukan uku uku yake, a hankali tace "ka rantse ba kai bane, ni kuma saina yarda."
Shiru ya d'anyi kafin yace "kiyi hak'uri, ni na canza miki, amma...."
"Amma me? baka kalleni ba za kace?"
Kuka ta saka da k'arfin gaske harda bubbuga qafafu tana fad'in "shikenan ya gama dani wallahi, ace kamar wannan yaron ne zai saka min kaya a jikina, shikenan ta qare miki Khairat, baki da bakin magana kuma tunda haka ta faru, nan gaba kuma kusantarki zaiyi daga nan kuma saiki d'auki cikinshi sannan ki haifeshi , bayan nan kuma saiya...."
Da sauri Umar Faruk ya janyo k'ugunta ya had'e da nashi ya d'ora yatsarshi akan labb'ata suna kallon juna, wani yanayi yake ji dashi kad'ai yasan me yake ji, dakewa yayi ya kama gashinta ya fara wasa dashi kamar gaske harda murmushi kafin yace mata "kiyi shiru, bana so mutanen dake waje su d'auka wani abu ne nake miki, dan haka kuskure ne, ki cire wannan tunanin a qwaqwalwarki dan haka ba zata faru ba, ni Umar Faruk ba zan iya had'a jikina da naki ba."
"Saboda me? ni karuwa ce? kaima haka kake gani? amma me yasa ka aureni to?"
Ganin hawaye sun cika idonta sai kuma ta bashi tausayi sosai, a hankali ba tare daya raba jikinshi ba yace "ni ba haka nake nufi ba, kawai dai ba zan iya had'a jikina da naki bane, saboda ina da matuk'ar kishi."
Qasa tayi da idonta tace "kenan yanzu da ice ka had'a jikinka? ko kuma kana nufin daga wannan had'awar da kayi yanzu ne ba zaka sake had'awa ba?"
Sakinta yayi yace "daga wannan ba zan sake ba."
Har zai wuce tace "baka ji mena fad'awa mahaifiyar matarka ba kenan? idan naso Faruk zaka zama nawa, idan nayi niyya zaka zama kamar raqumi da akala sai yanda nayi da kai, ka daina cika baki."
"Hummm, ba wani cika baki, ina da yarda da kaina ne shi yasa."
"Ka tabbata?"
"Qwarai ma kuwa."
"Ok, zamu gani, ni kuma zan ruguje wannan yarda da kai d'in."
"Kinga maganinki nan ki d'auka kisha yafi miki mahimmanci."
Juyawa tayi inda ya nuna mata ta kalla, maido kallonta tayi gareshi tace "ina ka samu magani na?"
"Matata ce ta bani."
Wani irin murd'awar kayan ciki taji lokaci d'aya kuma zuciyarta ta turnuk'o, a dake tace "wace matar taka? ba dai wannan d'iyar masifafiyar matar ba?"
Dariya ce ta kama Umar Faruk, karo na farko da Khairat taga dariyarshi, kafeshi tayi da ido harya tsagaita yace "wannan ta dabance , duk cikin matan nawa babu mai qaunata kamar ita, shi yasa nima na mata waje na musamman a zuciyata."
Duk da Khairat ta fahimci Umar faruk zaiyi dad'in zama kuma kamar yanda Ruk'ayya tace ta fad'a ne, amma kuma wani bala'i da taji ne a zuciyarta yasa ta rasa meke damunta, haka kawai taji bata so yana danganta kanshi da kowace mace a duniya, ba tare daya ankara ba Khairat ta kai masa duka a qirji harda fad'in "aisai kaje gaka gata ku cinye junanku."
Juyawa tayi zata haye gado tana fad'in "aikin banza kawai, ni gidanmu ma zan koma."
Da k'arfi taji ya janyota har saida ta fad'a qirjinshi, kafe juna sukayi da ido na d'an lokaci kafin yayi k'arfin halin cewa "meye wannan nake gani a idonki?"
Tsaki tayi mai k'arfi ta janye kanta daga jikinshi, fizgota yayi niyyar yin sai kuma,
"Assalama alaikum." sallamar Ruk'ayya ta katsesu.
"Shigo Ruk'ayya." cewar Umaririπ.
Shigowa tayi tana aje kwanukan Khairat tace "kina zuwa a lokacin da bai dace ba fa."
Ruk'ayya dai sakin ido tayi tana kallonta, har zata fita kuma tace "kina ji? ki dafa min."
A hankali Ruk'ayya ta tako ta zo ta d'auki indomien inda ta d'auka d'azu sannan ta fita tana guna guni, kwance tayi akan gado ta d'auki wayarta ta fara kiran lambar Mamie, muryarshi taji yace "ki daure ki dinga suturta jikinta koda gaban mace ne 'yar uwarki."
Hannu d'aya ta rumgume a qirji ta mike qafafunta tana girgizawa tana murmushi tace "to meye a ciki, naga jikina ne ba bana ka ba, kuma kace baka qaunarshi ba zaka tab'a had'ashi da jikinka ba, to miye na damuwa?"
Muryar Mamie ta daki kunnuwanta dan haka tace "Mamie ya kike, shine kun manta dani ko kirana ba kuyi ba?"
Shiru tayi kafin tace "ba wani nan, kudai kuna can kuna soyayyarku da Papa, tunda yanzu babu kowa a gabanku, dama nice kuma kun kawar dani."
Turo baki tayi cikin shagwab'a tace "wallahi Mamie nayi kewar Papa, nan fa gaba d'aya ba dad'i, yau fa har zazzab'i ya kamani, amma dai da sauki."
Nan suka dinga hira har Ruk'ayya ta shigo ta kawo mata sannan ta kashe wayar, sauka tayi daga kan gadon ta zauna kujerar da Umar Faruk ke cin abinci harda turashi take da k'ugu tana fad'in "duk kabi ka matse waje kai kad'ai."
Plate d'in imdomin ta ta aza ta fara ci itama, satar kallon hannunta yake wanda suka sha jan lalle, tana ci tana kallonshi ta wutsiyar ido tana kuma tunanin abubuwan da matar nan ta fad'a mata, alwashi taci saita saka matar nan tayi nadamar abinda ta mata, to amma tayaya? dole saita samu kusanci da Umar Faruk, to shima tayaya? abu mai sauk'i, namiji neshi ke kuma macce, kawai ki samu kusanci dashi, a hankali ta juya ta kalleshi, caraf idonsu suka had'u, kallon baka da hankali ta masa yayin da shi kuma ya bita da harara, tunawa da plan d'inta yasa ta turo baki gaba cikin sigar shagwab'a ta d'an mangareshi da kanta, hannu tasa ta debo lomar indomie ta nufi bakinshi da ita, ganin yana mata kallon rashin fahimta yasa ta sake langab'e kai tace "bud'a bakinka mana."
Kai ya gurgiza mata alamar a'a, a bakinta ta saka lomar ba tare data kallesa ba tace "hum, kama daina kallona haka."
Wata sallamar ce ta katsesu daga k'ofar kewayen nasu, Umar faruk ne ya fita jim kad'an ya dawo, tsaye yayi a kanta yace "ki canza kaya Baba nasan ganinmu."
"Meya faru?" ta tambaya.
"Ki tashi, duk litinin ana zama wajenshi da wannan lokacin."
"Me ake tattaunawa?"
"Oh, Khairat, kiyi abinda nace mana."
"To bari na gama cin abinci na."
Ba yanda ya iya saida ta gama sannan ta wanke hannu ta d'auki doguwar riga tasa ta d'auki kallabi ta yafa, yana kallonta yace "hijab zaki saka."
"A'a, nifa bana iya zama dashi, kuma ba kace wajen Baba ne zamu ba."
Hijab d'inta da take sallah ya d'auka ya matso kusanta ya gyarashi , bai b'ata lokaci ba wajen saka mata, k'ok'arin 'kwacewa tayi ya mata wani jan kallo dole ta tsaya, gaba ya sata suka fita daga d'akin bayan ya rufe, suna daf da shiga d'akin Baba inda gaba d'aya mutanen gidan suke, hannunta Umar Faruk ya kama ya gyarawa yatsunsu waje d'aya tare da murzawa har suka shiga yayin da yayi sallama, amma suna shiga ya saki hannunta suka samu wuri suka zauna, tunda ya rik'e hannunta taji wani *baqon yanayi* a tare da ita da bata tab'a jin irinshi ba, kamar yanda shima abubuwan da yaji sunfi k'arfin wasa, dan saida ya tuna da maganar Ishaq cewar *wataqila yanzu ne ya fara soyayar gaskiya.*
Kallon kowa take yayin da su kuma suke sauraran nasihar da Baba ke musu akan rik'o da zumunci, sun jima sosai kafin Baba yaba Zeinab damar rufe musu taron da addu'a, sosai yarinyar ta shiga ran Khairat saboda ganinta bata fi yar shekara bakwai ba, amma sink'i sink'i addu'o'i na fitowa daga bakinta, haka suka tashi suka fito, kowa makwancinshi ya nufa sai Umar Faruk daya kalli Khairat yace "muje kiga Mama."
Binshi kawai tayi suka nufi d'akin Mama, da sallama ya shiga ita kuma tun k'ofar d'akin take kalle kalle har suka shiga, zaune yayi kusa da Mama dake kwance amma ganinsu tare yasa ta tashi zaune tana fad'in "ah, ashe tare kuke da 'yata."
Sai lokacin ta d'anyi zaune akan kujera tana kallon d'akin da kyau, k'aramar panka take kallo a ganinta ba zata musu komai ba, muryar Umar Faruk ce ta katse yana fad'in "ya jikin Mama?"
Kallon Mama tayi tace "dama baku da lafiya ne?"
"A'a 'yata, ai nama ji sauk'i."
Umar Faruk ta kalla dan haka yace "hawan jininsu ne ya tashi, amma sunsha maganinsu."
"Wane irin magani, kuma baku kaita asibiti ba?"
"Eh, akwai maganin da aka rubuta musu, to shine suke anfani dashi." cewar Ruk'ayya dake gyara shinfid'a.
"Amma ai hakan bai dace ba, me zai hana ku dinga kaita asibiti duk lokacin da bata jin dad'i? amma zama da ciwo ana shan magani barkatai."
Tsam ta mik'e daga kujerar ta durk'usa kusan Mama ta tallabota ta zauna daidai, kallon Ruk'ayya tayi tace "ki bani hijab d'insu."
Ba tace komai ba sai hijab d'in data mik'o mata, saka mata tayi sannan tayi tsaye tana ciccib'ar Mama tana fad'in "muje asibiti Mama, lafiyarki tafi komai mahimmanci, kuma suma kansu yayanki nasan sun san da haka, amma babu mai fasahar kaiki asibiti, sai sun rasaki kuma za kiga sunfi kowa damuwa da kuka."
Kallonta kawai Umar Faruk da Ruk'ayya da sauran yaran suke, tsaye yayi yana fad'in "ba wai bamu damu bane, muma muna...."
"Dan Allah kayi shiru, ni ba tambayarka nayi ba."
Mama ce tace "'yata dama kin barshi wallahi, naji sauk'i ai da dama jikin ba kamar d'azu ba."
"A'a Mama muje kawai, sai dai kuma ko kina so ki nuna min ni ba 'yarki bace."
Suna fitowa farfajiyar gidan ta kalli Umar Faruk tace "ka rik'e Mama, zan d'auko makullin mota."
Tana fitowa kuma da makullin da post d'inta ta kuwa haka ta rik'e Mama har suka fita inda Baba ya fito da su tafi tare amma Khairat tace kawai yayi zamanshi, tare da Umar Faruk suka tafi suna gaba ita dashi tana tuk'i, Mama na baya in banda addu'a da qaunar Khairat babu abinda take ji, bata san kuma me yasa ba amma taji daga haka son sarakuwar tata ya kamata, suna zuwa asibitin da taje da safe docteur Sadiya ta tafi sai wani docteur d'in, cikin qwarewa ya duba Mama kuma ya fad'a musu jininta ya hau, allura aka mata na saukar da hawan jinin sannan aka rubuta wasu magunguna masu matuk'ar tsadar gaske, ita ta biya kud'in sannan suka kamo hanyar gida, saida ta tsaya babban pharmacie ta siyo duka magungunan sannan suka tafi gida dare yayi sosai lokacin.
Har d'aki suka kai Mama ta kwanta Khairat taja zanin rufa ta rufeta, gefen fuskar Mama ta shafa tace "kiyi bacci Mama, dan Allah banda damuwa da tunani, ki more baccinki babu mai takuraki."
Mik'ewa tayi tana fad'in "saida safe Mama."
Hannunta taji ta rik'e hakan yasa ta koma ta durk'usa tana kallonta, cike da jin dad'i da tsantsar qauna Mama tace "na gode yata, ubangiji ya saka miki da mafificin alkairinsa, Allah ya kareki daga sharrin masharranta, Allah ya baki abinda kike so, Allah ya saka miki da gidan aljanna, Allah ya albarkaci rayuwarki da zuri'arki baki d'aya, Allah ya sakawa iyayenki da alkairi, Allah ya kareki daga bakin duniya, Allah....."
Rufe bakinta Khairat tayi ta fashe da kuka ta fad'a jikin Mama ta rumgume, saida tayi mai isarta ba wanda ya bata hak'uri kafin ta d'ago ta share hawayenta ta rik'e hannun Mama sosai tace "Mama, kin kusa kasheni da farin ciki saboda wannan addu'ar taki, tunda nake a rayuwata ban tab'a jin addu'a irin wannan ba, ko mahaifiyar data haifeni bata tab'a kwatanta yimin irin wannan addu'ar ba, Mama nice da godiya bake ba, ina da yak'inin wannan addu'ar taki ba zata fad'i k'asa banza ba, a yanzun nan sai nake ji kamar ni 'yar aljanna ce kuma zan gama da duniya lafiya, Mama Allah ya bar mana ke, kuma nayi alk'awarin zama a gidan nan har qarshen rayuwata in dai har zan dinga samun irin wannan addu'a a wajenki."
Tana fad'a ta bar d'akin tana kuka, Umar Faruk ma bayanta yabi bayan sunyi sallama da Mama, yana shiga ya sameta kamar ba ita bace mai kukan nan harta murje idonta tayi kwance, sai dai abinda Umar Faruk bai sani ba ta rufe ido ne amma addu'a Mama ce ke yawo a qwaqwalwarta, kashe wutar d'akin yayi bayan yayi shirin kwanciya sannan ya kwanta a saman kujera, zunbur ta tashi zaune tana lalubar wayarta ta kunna haske, a daqile tace "malam nifa bana bacci a cikin duhu, ka kunna fitilar mana in dai ba wani abu bane a ranka."
Wayarshi ce a hannunshi yana duba kiran da Zuby tayi bai d'aga ba, ba tare daya kalleta ba yace "ni kuma gashi bana bacci a cikin haske, ya kenan za ayi?"
_To fan's ne zasu bamu shawara, ya kuka ce akashe ko a barta kunne?_
_Idan an kashe akwai d'an dannau mai taushe mutun cikin dareππ, idan an bari kuma shed'anun aljanu na anfani da hasken su cutar da bil'adama._
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
*_Masoyanaπ, kune abin alfahari na, ina matuk'ar ji daku fiye da tunaninku, fatana Rabbi ya bar qauna tare da soyayya, nasan ba zamu iya had'uwa daku ba dukanku, amma ina fatan Allah ya sadamu da alkairinsa sannan ya taramu a aljannatul-firdausi._*ππ
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣6⃣
Wajen makunnin ta nufa tana shirin kunnawa yayi saurin tare gabanta, d'auke idonshi yayi daga nata saboda masha Allah akwai girma kamar idon Barbie ga kuma kyau da yalwataccen gashi, "dan Allah ka matsa min na kunna, bana iya bacci a cikin duhu, tsoro nake ji."
Da kanshi ya nuna mata gado yace "kije kiyi addu'a saiki kwanta, babu abinda zai sameki da yardar Allah."
"Ba zaka gane ba, dan Allah..." bata qarasa ba saboda hannunta data kai ta kunna wutar shi kuma ya rik'e.
Janye hannunta tayi tana sauke ajiyar zuciya tace "shikenan, kar Allah yasa ka kunna, amma wallahi naji hannun mutum a jikina ana lalubata, to zaka sha mamaki dan saina fasa maka kai wallahi."
Dariya ce ta subece masa komawa yayi kawai ya kwanta, harta kwanta itama amma data rufe ido saita ga su Musa a idonta, sosai ta rintse ido amma duk da haka bata daina gani ba, bud'e idon tayi taga duhu sosai, zaune tayi ta kalli wajen da Umar Faruk yake tace "malam nasan ba kayi bacci ba, dan Allah ka taimaka ka kunna ko hasken fitalar wayarka ne."
"Wayarki fa?" ya fad'a cikin taushin murya.
"Haka kawai zan kunna harsken wayata har safe, ai tunda ka hana a kunna wallahi na wayarka zaka kunna."
"To zan gani, wayata ce kota wani."
"Kaji kamar mai wata wayar million d'aya, wallahi saika kunnata ko kuma."
Ta fad'a tana saukowa daga kan gadon, jin tahowarta yasa ya tashi zaune yana fad'in "ko kuma me?"
"Gani nan ai a aikace zan nuna maka."
Da hasken wayarta taga wayar tashi akan qaramin teburin dake tsakanin gadon da kujerar da yake, tunkararta tayi gadan gadan tare da kai hannu zata d'auka, da sauri ya d'auki wayar tare da ajeta bayanshi ya rumgume hannaye yace "ki d'auka idan ke jan wuyace."
"Dan Allah ka bani, wallahi bana iya bacci a duhu, kuma gashi dare keyi har yanzu banyi bacci ba, zanfa maka kuka wallahi ko kuma na fad'awa Mama."
"Wace Mamar?" ya tambaya.
"Mamank...." kuma kawai sai tace "Mamana."
Kallonta yayi dan ya mata tambayar ne dan yaji me zata ce, a hankali ya zura hannu ya d'auko wayar ya mik'o mata kamar sakarai, hararanshi tayi tace "ka kunna mana, meye saika wani bani a hannuna."
Baiyi magana ba kuma bai bar mik'a mata ba, cike da haushi tasa hannu ta karb'a ta kunna fitilar, murmushi tayi ta kalleshi tace "kaga tasirina ya fara aiki a kanka, tun ma ba'a je ko ina ba kenan."
Zaune yayi yana fad'in "ke bani wayata, tasirin me? kin d'auka dabararki ce tasa na baki?"
Juyowa tayi tana kallon qwayar idonshi ta soka wayar a cikin rigarta tsakiyar mamanta sannan ta rik'e k'ugu tace "kazo ka d'auka idan ka isa."
Murgud'a baki tayi ta koma gado ta haye tare da fitowa da wayar ta aje gefenta, baki sake ta barshi yana kallonta har bacci ya d'auketa, saida ya tabbatar tayi nisa sannan ya taso zauna bakin gadon yana kallon fuskarta, baisan menene asalin abinda yake ji ba, sai dai yana ji kamar a yanzu haka baya so ta masa nisa, to amma me yasa? *my aunt Aishan Umma* ce zata baka amsa a gaba, wata irin nutsuwa ce yake ji tana sauko masa, ga kuma taimakon da tawa mahaifiyarshi wanda yafi komai faranta masa rai, ya jima a wajen sosai yana tunani akanta kafin ya tashi ya koma wajenshi, ko bacci bai d'aukeshi ba yaji Khairat ta farka a tsorace.
Da sauri ya dawo kanta yana kallonta, numfashi kawai take saukewa kamar wacce tayi tseren gudu, a hankali ya furta "Khairat, lafiya? meya faru dake?"
Kallonshi tayi a firgice sai kuma ta rufe bakinta da hannu tana fashewa da kuka, wata nauyayyen ajiyar zuciya ya sauke ya kau da kansa danya lura tana da saurin kuka akan komai, sake cewa yayi "Khairat, meya faru?"
Share hawayenta tayi tana kallonshi tace "ba komai, kaje ka kwanta kawai."
"Ya zaki ce ba komai? bayan ga komai nan ya faru."
"To me kake so nace? na fad'a maka bana son duhu, sune ke sake zuwa min duk da qoqarina nasan ganin na manta komai, fyad'e ba abu bane mai sauk'i, amma duk da haka ina so na manta dan nayi rayuwata ba tare da damuwa ba, naso na zama marar tsoro da fargaba, amma su sun saka na zama mai tsoro, sunsa min fargaban da bana iya sakewa a kowane lokaci, kullum ji nake kamar zasu qara dawowa gareni ne."
Hawaye ta goge tace "ka kwanta kawai." tana fad'a ta koma ta kwanta ta bashi baya.
"Tashi zaune." yanda ya fad'a yasa ta tashi ba tare da gardama ba.
"Kiyi addu'a kafin ki kwanta."
Kallonshi tayi kuma lokaci d'aya ta dauke idonta, a hankali yace "baki iya bane?"
Nanma shiru tayi kawai sai yace "to ki d'aga hannayenki, saiki dinga fad'ar duk abinda na fad'a, kinji?"
Yanda yace tayi, *ayatul kursiyu* ya fara karantawa sannan *ammana rasul*, kafin suka karanta *falaq* da *nas* sannan ya karanta mata *Allahuma aslaftu nafsi ilaikh, wa fawadhatu amri ilaikh, wa wajahtu wajhi ilaikh, wa aljahtu zahri ilaikh, ragabatan wa rahabatan ilaikh, lamalja'a wala manja minka illa ilaikh, amantu bi kitabikal-lazi anzalta wabi nabiyikal-lazi arsalta.*
"Ki shafe jikinki." ya fad'a.
Shafawa tayi sannan ta koma ta kwanta, a hankali ya tashi yana sake nanata kalmar fyad'e a bakinshi, karo na farko daya ji haushin masu laifi kuma yaji inama shiya d'auki mataki akansu , wutar d'akin ya kunna tare da komawa shima ya kwanta, ganin haske yasa ta kashe na wayarsa sannan ta sake rufe ido sai bacci.
******************
Koda tanti ta koma gida tasa Zuby ta kira mata sauran 'yan uwanta a waya kasancewar duka matane 'ya'yanta guda hud'u, nan fa ta fad'a musu matar Umar Faruk taci mutuncinta tare da fad'a musu qudirin Khairat, nan fa suka fara zaginta suna aibatata tare da cin alwashin fitar da ita daga gidan, sannan suka qara kitsama Zuby wani sabon shiri a kanta tare da alk'awarta mata sabon had'in magani na musamman domin yaqar Khairat.
Sai dai tanti ita burinta ya wuce nasu dan haka safiya ma take jira kawai tayi, danta lura yarinyar dole sai an had'a da malamai.
******************
Tunda Khairat take a gaba d'aya tsawon rayuwarta, bata tab'a bacci mai dad'in na yau ba, bata tab'a jin natsuwa da farin ciki ba a cikin bacci kamar yau, gashi kuma ubangijinta ya nuna mata wani abu da ko kad'an bai firgitata ba saboda nutsuwar data farka da ita, a baccinta Allah ya haska mata tanti Ma'u tana matuk'ar biyarta da sharri , sai dai ta rasa waye kuma me yasa ya fad'a mata cewar ta rik'e addu'a tafi komai mahimmanci, koda Umar Faruk ya tasheta tayi sallah zaune tayi ta murje idonta kafin yace mata "ki fad'i abinda zan fad'a."
Kai ta jinjina alamar tana sauraro, *Alhamdulillahi lazi ahyana, ba'ada ma'ama tana wa'ilaihir-nushur.*
Nanma fad'a tayi kafin ta shafa ta sauka daga kan gadon shi kuma ya nufi masallaci, har tayi alwala tazo ta kabbara sallah tana tunanin akan me matar nan zata nemeta da sharri, shin akan yarta ne ko kuma akan abinda ya faru tsakaninsu? da qyar ta saita nutsuwarta ta samu tayi sallah tana gamawa kuma ko hijab bata cire ba ta zauna bakin gado, a hankali take tunano addu'a da Umar Faruk ya fad'a mata jiya, tana haka kuma ya shigo d'akin.
Kayanshi ya bud'a ya d'auko duk litattafan daya fad'a jiya sannan ya zauna akan kujera, kallonta yayi yace "dawo nan ki zauna."
Ba musu tayi yanda yace, littafi mai tsarki ya bata sannan yace ta bud'e, a farko ta bud'e sannan ya fara biya mata daga qananan surori har guda goma, kallonshi tayi jin daga nan yake tsayawa yasa tace "to wai meka d'aukeni, iya haka zaka tsaya min? kaga ni qara min kawai ai zan iya."
"Da farko dai ina so ki d'aukeni a matsayin malaminki, dan ta hakane za kiga haske da albarka a karatun, sannan ki girmamani domin samun sauk'i, sai kuma jin maganata a duk lokacin dana miki, kin fahimta?"
"In dai sai nayi haka zan samu albarka a karatuna, to na shirya zama dalib'a 'yar shekara biyar a gaban malaminta."
"Da kyau." ya fad'a kafin yace "idan kina so na qara miki, ki fad'a min wanda na fad'a miki sannan."
Gyara zama tayi kamar zata kwanta jikinshi sannan ta d'ora yatsarta a littafin ta fara biya masa, duk da a cikin salon koyo take karatun, amma abin abin birgewa da sha'awa, bakinta yake kallo wanda take motsashi a hankali tana biya karatun domin gudun kar tayi sauri tayi b'ata kuma, sosai Umar Faruk ya girgiza domin kaf a cikin waje d'aya kawai ya mata gyara, shima kuma ta fad'a ne ba daidai ba, murmushi yayi har hak'oransa suka fito fili yace "kinyi qoqari sosai, kuma ina fatan zaki kasance haka, har ranar da zaki hardace al'Qur-ani a kanki."
Wata irin lallausan dariya tayi data tafi da imanin Umar Faruk dan bai tab'a ganin irinta ba a fuskarta, cike da jin dad'i tace "nima zan hardace a kaina, na zama kamar k'anwar nan taka?"
"Zama ki fita in har kika saka kanki."
"To shikenan qara d'ora min wani." ta fad'a cike da zumud'i.
Nan ya sake dora mata har suka kai suratul *Qari'a* sannan yace ta rufe littafin tare da cewa "ki tabbatar kin kawosu gobe, idan ba haka ba kuma."
"Idan ba haka ba me?" ta tambaya tana kallonshi.
"Zaki sha bulala ne, saboda ke dalib'a ce."
Wata dariya ta kece da ita mai qarfi kafin tace "ai bama zaka fara ba kaima, dan kasan zamu iya dakuwa da kai."
Kunnanta ya kama ba zato ba tammani ya murd'e fuska a had'e yace "ni kike fad'awa haka? anya kina neman albarka kuwa?"
Hannayenshi ta kama duka biyu tana rokon ya saketa tana fad'in "dan Allah kayi hak'uri wallahi ba zan sake ba malam, dan Allah kasa min albarka ko nayi saurin fahimta."
Sakinta yayi yana tunanin ya samu hanyar da zaibi da ita cikin sauk'i dan haka yace "idan akayiwa malam laifi har qasa ake duk'awa a bashi hak'uri, dan haka ki fara in dai har da gaske dalib'a ce mai neman albarka."
Ita kuma yanzun nan taji a ranta bata da wani buri daya wuce na karatu, musamman da taji wai yau itace take karatun littafi mai tsarki haka, shaukin abin ya shigeta sosai dan haka bako tunani ta zube qasa ta kamo hannunshi ta rik'e tana murzawa ba tare dama tasan me take yi ba tace "naji to kayi hak'uri dan Allah, ba zan sake ba, nidai ina sonna samu albarkar karatuna."
Shima biye mata yayi ya dinga murza tattausan hannunta yace "ba albarkata kad'ai kike buqata ba, akwai ta iyayenki, dama mutanen da kike zaune dasu."
Cikin mamaki tace "wai har suma?"
"Eh, basu cancanci saka miki albarka bane?"
Cikin turo baki tace "toya zanyi?"
Mik'ewa tayi yace "yanzu zaki fara ai."
Ta qasan ido ta harareshi kafin tace "toya zanyi yanzun?"
Wani shu'umin murmushi yayi ya tashi tsaye yace "biyoni muje."
Saida suka fita sun nufi d'akin Mama Maimuna yace "za muje ne mu gaida iyayenmu, sai kice kina neman albarkarsu."
Kallonshi tayi kamar zata fashe da kuka tace "zafa ka rusa min jiji da kaina, gaskiya ba zan iya ba."
"Shikenan, koma ki zauna, amma ki sani za kiyita karatu bakya fahimta, saboda ba albarkar manya a ciki."
Bubbuga k'afafu tayi cikin shagwab'a ta kutsa kai d'akin Mama Maimuna, ganinta kawai tayi ta fad'o mata dan haka ta tsorata, da sallama ya shiga sosai ya gaisheta duk idonshi na kan Khairat da har yanzu ta b'ata rai, da ido ya mata alama kafin ta fahimta ta kalli Mama Maimuna tace "ina...kwana, an tashi lafiya, ina neman albarka dan Allah ki saka min."
Mama Maimuna mamaki ne ya hanata magana, saida Khairat ta sake cewa "ba zaki samin bane kome?"
Kai ta girgiza da sauri tace "a'a 'yata, kin tashi lafiya? Allah ya miki albarka."
"To na gode, sai an jima." tana fad'a ta tashi ta fita shi kuma ya mata sallama ya fita.
Kewayensu ta nufa shi kuma ya janyo hijab d'inta ya nuna mata kewayen Mama Sa'a, ciki suka shiga amma Mama Sa'a harda rumgume Khairat tanata wasar baki tana gaisheta, haushi ne yasa Khairat yin shiru ta kasa gaisheta, danta lura irin mutanen nan ne masu shishigi, Umar Faruk kad'ai ya gaisheta kuma yanawa Khairat alama da ido akan tarbiyar gaisheta amma tak'i, fitowa sukayi suka shiga d'akin Mamanshi, suna shiga da sauri ta qarasa ta durk'usa gaban Mama tana rik'o hannunta da fad'in "Mama ya jikinki?"
Cikin sakin fuska tace "da sauk'i 'yata, kin tashi lafiya."
"Ina kwana aunty Khairat." murayr duka yaran dake d'akin ta daki kunnuwanta.
D'an murmushin gefen labb'a kawai ta musu kafin suka juya kan Umar Faruk suka ce "ina kwana yah Umar."
"Lafiya lau, kun tashi lafiya?"
"Lafiya lau." suka amsa.
"Mama kinsha maganinki?" cewar Khairat.
"A'a 'yata, yanzu dai zanci abinci sai nasha."
Juyawa tayi ta kalli Ruk'ayya dake shirin fita tace "har yanzu baku gama bane?"
"Eh aunty Khairat, yanzu ma zan d'ora."
"Me? yanzu fa? kuma Mama ta zauna tana jiranki? me yasa ne wai kuke haka? kamar dai baku damu da ita ba."
Mtsssss, taja tsaki tare da tashi rai bace ta fita daga d'akin har tana karo da Abbakar da Saratu da zasu shigo suma, wayarta ta d'auko ta dawo d'akin tana ci gaba da kira amma ba'a d'auka, saida ta aika kira na hud'u sannan mutumin ya d'auka jiki na rawa, tana jin ya d'auka tace "ka kyauta, amma yanzu bata kai nake ba, ka gaggauta had'a min duk wani abinda kake dashi yanzu, amma karka saka arom (d'and'ano) a ciki na mai tension ne, da zaran ga kama ka kirani."
"To Hajia." ya fad'a ta kashe wayar.
Umar Faruk ta kalla wanda suma dukansu kallonta suke tace "dan Allah ka d'auki makullin motata kaje *riva side* ka karb'owa Mama abinci."
Fita tayi shi kuma yabi bayanta, makullin ta d'auka ta bashi ta bud'a post d'inta ta d'auki kud'i ta bashi, kai ya girgiza mata yace "ki barshi zan biya."
"Kai kayi magana a maka oder koni? kaine ka sani koni nayi niyya? dan haka karb'i kawai."
Karb'a yayi ya cire doguwar rigarshi ya sake kayan sannan ya fita, yana fita ita kuma ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin riga da siket na shadda, kwalliya tayi sosai kafin ta d'ora gyale a kafad'a ta d'auki jaka da takalmi, wayarta ta d'auka da nufin kiranshi sai gashi ya shigo, hannu kawai ta tara masa ya bata makullin sannan ta fita.
Bayanta yabi amma sai yaga ta shiga d'akin Mama, Mama ce kad'ai a d'akin dan haka ta sake zubewa qasa tace "ga abinci nan kici Mama, sannan ki saka min albarka zan fita wajen aiki."
"Allah yayi albarka yata ,daga yanzu har zuwa fitar numfashina na qarshe sanya albarkata ba zai tab'a nesanta dake ba."
"Na gode Mama." ta fad'a tana yunk'urin tashi.
Hannunta Mama ta rik'e tace " 'yata."
Komawa tayi yanda take tace "na'am Mama, akwai abinda kike sone?"
"A'a 'yata, ina so na fad'a miki wani abu."
"Ina jinki Mama."
" 'Yata, wannan kayan na jikinki, bai kamata ki fita dasu ba a matsayinki na matar aure, ki sani Allah ya umarcemu damu dinga rufe jikinmu a duk lokacin da zamu fita daga cikin gidajenmu, kuma hakan nada alfanu sosai, hakan da zaki fita baiyi ba sannan shi kanshi mijinki zaiji ba dad'i, yata, ina so ki zama salihar mace kuma yar aljanna, amma fa ki sani ba'a zama salihar mace a haka, dan Allah yata ki kare mutuncinki ko dan gudun sake faruwar abinda ya faru dake a baya, ki kame kanki ba kowa jaki da alade bane ya kamata ace sunga surar jikinki, idan zai yiwu ki gwada saka hijab ki gani, na tabbata zai miki kyau, dan sutura ce mai rufa asirin mace tare da qara mata kwarjina da haiba."
Murmushi Khairat tayi ta sake makale hannun Mama tace "na gode Mama, kullum mahaifiyata na fad'a min na dinga rufe jikina, yau kema gashi kin fad'a min, hakan na nuna irin soyayyar da kike min."
Tsaye ta mik'e tace "ina zuwa Mama."
Nan ta bar jakarta ta fita ta koma d'akinsu, cikin hijabban da Mama tasa aka d'inka mata ta d'auko kalar aikin shaddarta ruwan qasa, tana saka hijab d'in ta kalli kanta a madubi, wani murmushi ta saki ganin yanda ya d'auki jikinta ga hannayenta da suka fito ya tsaya iya gwiwarta, fita tayi daga d'akin ta koma na Mama, su Mama Sa'a mamaki ne ya kamasu ganin tana safa da marwa a d'akin, tana shiga Umar Faruk da Mama suka sakar mata ido, tsaye tayi gaban Mama tace "Mama haka yayi, nayi kyau?"
"Yata fad'ar kyan da ki kayi ma bata bakine , Allah ya kareki."
"Ameen Mama, na gode saina dawo."
Tana fad'a ta d'auki jakarta ta bar d'akin ko kallon Umar Faruk, tana fita ta d'auki hanya amma saboda rashin sabo yasa taji kamar an d'aureta , kasa jurewa tayi hakan yasa ta cire ta ajeshi saman kujera harta isa ma'aikatar, d'aukar hijab d'in tayi ta saka ta d'auki jakarta sannan ta fito, da gudu massinger yazo ya tareta yana gaisheta, hannu kawai ta d'aga masa tayi gaba, tunda ta shiga idon kowa ke kanta suna gaisheta da mamaki, kowa da abinda yake sak'awa a ransa, Khairat a wajen aiki tunda safe haka gashi ko Umar Faruk d'in bai zo ba, sannan da sabuwar shiga, harta tunkari office d'inta, dago ido Habiba tayi amma saita saukesu ba tare data mik'e tsaye ba kamar yanda ta saba, saida Khairat ta tsaya gaban tebur d'in tana kallonta, k'amshin turaren da taji ya tabbatar mata Khairat ce, a zabure ta tashi tsaye tana fad'in,
"Kiyi hak'uri Hajia, wallahi ban...ban ganeki bane."
"Wato *arniya kafira* yau ta shigo da hijabi, shi yasa har zaki kasa ganeni? dama wad'ancen shashanshun sun bini da ido, shine kema zaki min fitsara."
Wucewa tayi mazauninta tana shiga ta zauna kuma ta cire hijab d'in ta rataye, a gaba d'aya ma'aikatar kuma maganganu aka d'auka, wasu na ganin Umar Faruk yayi namijin qoqari da har ya iya canza Khairat a qanqanin lokaci haka, wasu kuma na mamakin ta yanda ya iya juyata harta zama haka.
_FAN'S ya kuka ce? nifa sai nake ganin kamar qoqarin na Mama ne ba Umar Faruk ba._
Abun mamaki jakarta naga ta d'auka kawai ta fito da littafin da Umar Faruk ya bata, budawa tayi ta fara karatunta a hankali daki daki , dan bata so gobe ya tambayeta ta kasa fad'a mashi, kodan gudun bulala.π€ͺ
_Shin kuna ganin zai iya dukanta idan ta kasa kawo karatun daya koya mata?_
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣7⃣
Tunda ta fita ya bita da ido, Mama ce tayi murmushi tace "tana da taushin zuciya, cikin sauk'i zata dinga fahimtarka in dai kana binta a hankali."
Shiru yayi shi dai abinda kawai yake ji a zuciyarshi yake so ya gano ko menene, "ka tashi kaje ka shirya karka makara kuma." muryar Mama ta katseshi.
Tashi yayi cikin sanyin jiki ya fara shiri harya gama, tsaye yayi bakin madubi yana b'alla mab'allan rigarshi tare da wani hamshak'in murmushi a fuskarshi, yana gamawa ya makala agogo sannan ya d'auki jakarshi ya rataya zai fice, rigar baccin data cire da asuba ya gani akan gado ya d'auka, rufe fuskarshi yayi da riga yana shak'ar wani tattausan k'amshi da ba zaka tab'a jinshi ba in har ba shak'a kayi ba a kusa, aje rigar yayi amma har yanzu ya kasa daina wannan tsadaddan murmushin, ko kari baiyi ba kawai ya fita saboda ji da yake yana so ya kusanta da ita, wayarshi ya d'auka akan tebur har zaisa aljihun riga kuma saiya k'ura mata ido, tunawa yayi da wajen da wayar ta shiga jiya, wani murmushi ne ya sake sub'uce masa hakan yasa ya mannawa wayar sumba tare da mannata a qirji, haka ya d'auki hanya cike da sabon yanayi a tare dashi da sabon farin ciki, yana shiga yau ma dai haka gaisheshi wasu keyi cike da girmamawa wasu kuma tsabar izgilanci ne kawai, zaune yayi ya fara abinda ya kawo, alk'alami ya d'auka da farar takarda ya fara zana wani sabon sanfirin takalmin, ji yake yana so yaje wajenta amma kuma yana jin fargaba, jin ya kasa samun sukuni yasa kawai ya tashi ya nufi wajenta zuciyarshi na d'ard'ar na abinda zata masa ko zai tarar.
Koda Habiba ta ganshi ta tashi ta bud'e masa k'ofar tare da gaisheshi, shiga yayi cikin sakin fuska amma saiya tsaya cak yana kallon Khairat, chocolat a hannu tana sha sai kuma littafinta data duqufa da karatu, d'ago kai tayi tana ganinshi ta saki murmushi tare da fad'in "yawwa, qaraso mana."
K'arasawa yayi zauna kujera yana kallonta, tasowa tayi daga kujerarta ta zauna kujerar kusa dashi ta aje littafin tace "bara na karanta maka kaji, saika sake d'ora min wani."
"Anan d'in?"
"Eh miye to, ba bureau na bane?"
Basarwa yayi kamar ba ganinta ne ya kawoshi ba ya mike tsaye yace "ba zan iya ba, kuma shine kika cire hijab d'in ko? ai za muje gida saina fad'awa Mama ta janye sawar albarkarta."
Juyawa da yayi zai fita yasa tayi saurin tashi da nufin ta riko hannunshi, sam bata kula da inda ta rik'e ba sai zuba take tana fad'in "dan Allah malam kayi hak'uri karka fad'a mata, wallahi na daina daga yau, kuma rashin saboda ya janyo haka, kaima kasan ai ba zan yaudari Mama ba, dan Allah karka fad'a mata."
Da k'arfi ya fizgota ta fad'a jikinshi yana mata wani kafirin kallo mai kashe jiki yace "to cire hannunki."
Ido ta bud'o tace "a ina?"
Raba jikinsu yayi ita kuma ta kai kallonta ga hannun nata, d'aya hannun tasa ta rufe baki ganin ceinture (belt) d'inshi ne ta cakumo, hannu biyu tasa ta rufe fuskarta saboda kunya, shi kanshi dariya ce ta kubce masa hakan yasa ya juya ya fita, zaune tayi tana mamakin abinda tayi kuma ba tare da tasan tayi ba, shi kuma yana mamakin wasu b'oyayyin halayen Khairat da sai yanzu ne suke fitowa, dan kunyar data nuna taji ma ya masa dad'i sosai, misalin *10:00* Khairat tasa aka tattara kowa dake ma'aikatar suka shiga meeting, saida ta saka hijab d'inta sannan ta fita, anan ta fad'a musu zangon shekara yazo qarshe, dan haka ana buk'atar kowa ya fito da nasa sabon sanfirin domin aga bajintar kowa, sallamarsu tayi sai kuma manager da accountant da suka tsaya suka yi wani lissafi sannan suka tashi suma, tana fitowa jakarta kawai ta d'auko ta kama hanya zata fita, dan dama aikinta ba jimawa take ba.
Tunda ta fito kowa ke kallonta kamar wacce tayi wani mugun abu, ranta ne ya bace harta tsaya ta fara kallon kowa zata fara zazzaga masifa, sai kuma taga kowa yasha jinin jikinshi saboda ganin zata koma musu Khairat d'in ta asali, lokacin ne ta fahimci dalilin kallon nata, hakan yasa ta saki murmushi a fuskarta sannan ta fara takawa cikin rangwad'a ta tsaya bayan teburin Umar Faruk, duk da yaji alamar akwai mutum a bayanshi, duk da turarenta ya bayyana mishi ita amma baisa ya juyo ya kalleta, cike da tsantsar shagwab'a da bubbuga qafafu Khairat tace "shine ma zaka wani kyaleni ko ka juyo ka kalleni, ni wallahi zanyi hushi da kai."
Mamaki ne yasa ya juyo dan ganin dawa take, qara waro ido yayi tare da dage giranshi sama, kasa magana yayi saboda kowa na wajen kallonsu suke, sake shagwab'ewa tayi ta fara kukan sakuwa tace "uhum uhum uhum, wallahi Allah saina fad'awa Mama mana."
Kunyar data fara basa ne yasa ya mik'e tsaye yana kallonta cikin mamaki yace "ya dai, me yake damunki ne?"
"Gida zan tafi wajen Mamie, shine nazo kamin sumbatata ta ban kwana."
"Sumba kuma?" ya fad'a da k'arfi har mutanen suka sake sakar musu ido.
Lab'e baki ta sake yi tana "uhum uhum uhum uhum uhum uhum uhum."
Zaiyi magana kuma saiya d'an kalli mutanen da wutsiyar ido, ganin yanda hankalin kowa ke kansu yasa ya zura hannu ya janyota yana fad'in "oh mon bΓ©bΓ©, meya faru ne waya tab'a min ke?" ya fad'a yana shafar fuskarta.
Kamar zata janye hannunta kuma saita goge ido kamar mai hawayen gaske tana magana cikin shagwab'a tace "toni sumbata nake jira."
Wasu yawu ya had'iye danshi dai ba zai iya ba kome za tayi, kallonshi tayi ta fahimceshi dan haka ta nuna mutanen tana fad'in "wai kunyarsu kake jine? su d'in fa duka yaranka ne, tunda shugabarsu ma a qarqashinka take."
Saida ta d'an d'aga qafafunta ta kai bakinta daidai kunnenshi saboda ya fita tsayi sannan tace "ko ba wannan ne burinka ba? ace Umar Faruk mijin Hajia Khairat."
Sai kuma ta sake tsayawa yanda take tana murmushi tana kallon fuskarshi, ganin zai b'ata mata lokaci yasa ta kalli idonshi tace "wato zaka iya yiwa waccen figaggiyar matar taka sumba a waya, amma ni gani gaka ma ba zaka iya ba ko? to bara ka gani."
Sake d'aga qafafunta tayi ta daidaita tsawonsu tare da d'ora bakinta akan nashi bakin, ji kake muahhhhhπ ta sumbaceshi, daga cikin wasu mutanen dake wajen ne sai kuwa suka saka tapi tare da shewa, yayin da Khairat kunyar abinda tayi ta lullub'eta, ficewa tayi ba tare da sun had'a ido ba ta bar wajen, ta jima zaune kafin ta tayar da mota ta tafi, tun tana tunanin dalilin da yasa tayi haka, har dai ta fara sakin murmushi da ba tasan dalilin yinshi ba, wannan ce sumbatarta ta farko, dan ko Raj dake ba musulmi ba bata tab'a yarda ya sumbaceta a baki ba, haka ma su Musa da suka keta mata haddi babu wanda ya damu da bakinta, da wani irin sabon farin ciki daya lullub'e zuciyarta ta isa *marina market score*, siyayya tayi mai yawan gaske kayan abinci da kuma kayan mak'ulashe saboda kanta, a bayan mota aka saka mata daga nan kuma gida ta nufa wajen Mamie.
***************
Tunda ta d'ora labb'anta akan nashi ya sandare tare da lumshe ido, ba komai ya tafi dashi ba kamar taushin labb'anta, ga kuma wani sabon k'amshin turare daya baibaye hancinshi, harta fita bai iya zaunawa ba har saida Ishaq ya janyo rigarshi yana dariya yace "sabon shiga kenan, kai yanzu bizou (kiss) ne ya sukurkutar da kai haka? tofa wannan inaga har yanzu ba wani labari tsakaninku ko? dan inaga ranar da kaje bakin boda, tofa sai dai mutanadi makarar da zamu saka gawarka."
Duk da ya zauna amma hankalinshi baya jikinshi, sake tab'ashi Ishaq yayi yace "kai, ko dai ka zaucene, sumbata ce fa."
A hankali ba tare daya kalleshi ba yace "ya danganta dawa ya sumbaceka, wannan ta dabance Ishaq, ba zaka gane ba."
"Wow." ya fad'a tare da dogara hannayenshi akan teburin dake gabanshi ya tusa hannayenshi a cikin sumar kanshi, bakinshi har kunne yayin da hakoranshi suka kasa b'oyuwa, wani irin sanyi ne yake ji yana shigarshi a hankali, zuciyarshi kuma na qara narkuwa akan wani abu da take so sosai, sai dai bai yarda son Khairat bane take.
_Zama kayi magana Umariri_π
****************
Da sauri mai gadi ya bud'e mata k'ofar ta shiga, tun kafin ta fito kuma yaja ya tsaya gabanta yana fara gaisheta tun kafin ta fito, qafafu ta zuro kafin ta qarasa fitowa, "barka da zuwa Hajia, sannunki da zuwa uwargijiyata, 'yar Alhaji da Hajia, 'ya d'aya tilo kuma farin ciki da sanyin idaniyar gidan mai gidanmu, takawarki lafiya yar albarka jikar arzik'i, sannu da zuwa."
Hannu ta d'aga masa tana kallonshi tace "baka tab'a min irin wannan kirarin ba, halan da wani abu a qasa?"
Kai ya d'an sosa amma baice komai ba, "humm, nasan dama da wani abu, dan banza bata kai zomo kasuwa, ka jira na shiga ciki na fito."
Tana fad'a ta wuce shi kuma ya sake rakata da wasu kirarin, saida yaga ta shige yaja baki yayi shiru yana mamaki Hajia Khairat da hijabi, lallai mijin nan mai sa'a ne, kuma da alama zai juyata yanda yake so.
Mammie ce zaune a falo ita kad'ai tana kallo, da gudu ta qarasa ta rumgumeta tana fad'in "Mammie na."
Rumgumeta tayi itama tana fad'in "lah, Khairat d'ina, ashe kece?"
D'ago kanta tayi tana gyara zama tace "nice Mammie, kema baki ganeni ba saboda nasa hijab?"
"Ah haba, ni na isa na kasa gane 'yar gudaliyata, kawai dai gani nayi kin qara min kyau da haske."
Kumatunta ta kama taja suna dariya tace "kin ganki tsohuwar nan, wato harda haske na qara, bayan duhun da nayi saboda bala'in zafi da cizon sauro."
Dariya Mammie tayi cike da zolaya tace "ba wani nan, kinje kin manta dani kina kwasar amarcinki, yanzu zaki ce wai zafi da sauro , kedai sai dai in kin samo min wani d'an gudaliya ne kawai."
Fashewa tayi da kukan shagwab'a tana fad'in "lah Mammie, d'an gudaliya fa, tun yanzu? wallahi ba dani ba, Mammie yana da mata fa."
"Eh na sani ai, amma ina ruwanki da matarshi? ke daban ita daban."
"Humm, Mammie baki sani ba fa, wallahi ni ba sona yake ba ita kawai yake so."
Hannu tasa ta rufe mata baki tace "bana so, karna sake jin haka daga bakinki, shiya tab'a fad'a miki baya sonki?"
"To Mammie saima ya fad'a, jiya ma fa cemin yayi ba zai tab'a had...."
Mammie ta rufe mata baki, kai ta girgiza tace "Khairat, kefa yanzu ba yarinya bace, kamata yayi ace kina rik'e sirrinki, musamman irin wannan sirrin mai tsada, ki sani duk abinda ya faru tsakaninki da mijinki to bai hallata ki fad'eshi koda ga mahaifiyarki bace bare kuma waninta, dan haka bana so na sake ji kinji yar albarka."
Hannayenta ta matse sosai tace "naji Mammie ba zai sake ba, kinga yanzu nima na fara sauyawa, ina so na zama 'yar aljanna."
Muryar Mamie ce ta katsesu da cewa "nayi hushi dake, tun d'azu nake jiyo muryarki amma kin kasa zuwa inda nake."
Yanda take maganar da shagwab'a ne yasa Khairat yin dariya tace "kiyi hak'uri Mamie, ina nan tare da wannan tsohuwar k'awar tawa."
Hannaye Mamie ta bud'e alamar Khairat ta taho, abinda Khairat d'in ba tayi tunani bane hakan yasa da mamaki ta tashi ta tafi, tana zuwa Mamie ta rumgumeta sosai a jikinta tana fad'in "nayi kewarki sosai 'yata."
"Nima haka Mamie, ina Papa?" ta fad'a tare da tashi daga jikinta.
Hannunta ta kamo tace "Papanki ya tashi *Germany* amma yace ba zai jima ba."
"Ta'bb, yanzu shine har Papa yayi tafiya ban sani ba? lallai gidan nan kun daina sona."
Mamie data qura mata idone tace "Khairat, wannan sabuwar shigar fa?"
Saida ta cire hijab d'in tace "wallahi Mamie mahaifiyar Faruk ce tace na dinga rufe jikina, matar tana da kirki gaskiya ga yiwa mutum addu'a a kullum."
Duk da Mamie ta gano kuskurenta anan take amma bata nuna ba, murmushi tayi tace "Alhamdulillah, ashe 'yata ta kusa zama salihar mace itama."
"Eh Mamie, kuma ma yanzu har karatu na fara, Faruk ke koyar dani, wallahi Mammie baki ji dad'in dake akwai ba idan kana karatu."
"Alhamdulillah, ashe yaron ya kusa canza min yarinta ta yanda ba zan ganeta ba nan gaba? to Allah ya mishi albarka, ke kuma Allah ya baki sa'a ya taimakeki a karatunki."
"Ameen Mamiena." ta fad'a tana sake rumgumeta.
Mamie ce tace "to amma daga ina haka? kina ganin ba kiyi saurin fara fita ba kuwa?"
"Mamie daga wajen aiki nake fa, kuma shima na baroshi acan."
"Amma kin fad'a masa?" cewar Mammie.
"Eh, nace masa zanzo gida."
"To ya mutanen gidan, ba wata matsala dai ko? inji Mamie.
"Eh to, bana shiga sabgar kowa, amma akwai kishiyar mamanshi tana da zakewa, amma ba komai zan gyara mata zama."
"A'a."
"A'a."
Mammie da Mamie suka had'a baki a tare ,Mamie ce ta d'ora da "haba yarinyar kirki, 'yar aljanna, aiba girmanki bane wannan, ki rabu da ita kawai, kinji?"
"Shikenan." tayi maganar tana gyara zama.
Su kuma kallon juna sukayi saboda mamakin canzawar Khairat, magana d'aya tak Khairat tace to ko shikenan, tab', dole ma mu nemi yaron nan mu qara gode masa, saboda wannan namijin k'ok'ari da yayi, a kwana uku rak ya gyara musu 'yarsu cewar Mamie.
Saude da Biba da kuma Baraka masu aikinsu ne suka fito suka gaisheta, ba yabo ba fallasa ta amsa suka koma ciki ana mamakin Hajia Khairat.
Mamie ce ta kira Papa ta bashi Khairat d'in suka gaisa, anan kuma yake fad'a mata lallai lallai ta shirya tare da mijinta zasu zo Germany suma nan da kwana biyar tare dasu Mammie da Mamie, dad'i taji sosai saboda zata keta hazo, anan ta wuni gida sam tama manta da wani gidan aurenta, ji take kamar ta tsaya a inda take ba tare data koma waccen kurkukun ba.
******************
Yamma sosai Mammie ta iza qeyarta zuwa gidanta, haka ta tafi ba dan rai naso ba, tana zuwa ana kiran sallah dan haka koda ta shiga gidan wasu na alwala wasu sun tafi masallaci, sai dai ganin moton Umar Faruk ya tabbatar mata ya dawo, tana shiga ta tub'e ta shiga wanka sai dai bata jima ba ta fito saboda yanzu tana son yin sallah akan lokaci, cikin gaggawa ta shirya amma saboda qananan kaya ne saita dora doguwar riga a sama sannan ta saka hijab, harta kammala sallah bai shigo ba har qaramar kwalliya tayi sannan ta d'auki hula (hana sallah) ta zatsa akai, wata k'atuwar chocolat ta d'auka ta d'auka ta fara sha ga kuma k'atuwar loli pop d'inta a hannu, abin sauraronta ta dasa a kunne ta fara biyar waqar Zaho mai taken *Allo* tare da rausaya.
Da sallama tare da d'aga labulen ya shigo, baiyi mamaki ba saima birgeshi da tayi , bak'in dogon wando da farar riga mai hannuwa sai bak'ar hula itama, kamar ita ta rera waqar ga kuma yanda take tafiyar da kowace gab'a ta jikinta cikin qwarewa, shiga yayi ya zauna dan sunyi ido takwas takwas dashi amma bata nuna ta damu ba, a cikin takon rawa ta bud'a jakarta ta d'auki makulli ta mik"o masa ya karb'a yana kallonta da mamaki, ta jima kafin tace "akwai kaya a mota a deb'osu."
Duk tana maganar ne tana girgiza rawarta, hararanta yayi da fad'in "waye zai d'auko?"
Nunashi tayi da hannu tana ci gaba da abinda take , cilla mkullin yayi a saman gado harya kusan bugeta, cire abin sauraron tayi tana kallonshi tace "ni kake so na kwaso to?"
"Eh, saboda ke kika siyo."
D'aga kafad'u tayi alamar ba matsala, fita tayi daga d'akin ta zura takalmi harta kai k'ofar fita daga kewayen yayi saurin fitowa yace "ke."
Duk da taji amma bata saurareshi ba, wucewa tayi ta kuma yi sa'ar ganin Aliyu da Usman sun shigo, da sauri ta mik'a musu makullin tana fad'in "yawwa karb'i nan, akwai kaya a cikin mota ku fito dasu saiku shiga dasu madafar gidan nan."
Suna karb'a suka fita ita kuma kawai tasa kai ta shiga d'akin Mama dan ganin jikinta, duk da saurin da yake ya rik'ota tuni ta shige, dafe kai yayi yace "duk kaine ka jawo Umar Faruk, da kayi abinda tace daba haka ba."
Mama na zaune duka yaranta suka ga ta shigo, gaisheta sukayi qasa qasa kamar yanda ba wanda ta amsa ma, zaune tayi kad'an tace "Mama ya jikinki?"
"Da sauk'i sosai 'yata, ya kike?"
"To yayi kyau, kinsha magani?"
"Eh nasha." Mama ta fad'a tunda taga ba kowace magana take amsawa ba.
Tashi kawai tayi ta kalli Ruk'ayya dake koyar da k'annanta karatu tace "akwai kaya za'a shigo dasu."
"Mama saida safe, Allah qara lafiya."
"Ameen 'yata saida safe."
Tan a fitowa suka ci karo da Umar Faruk dake sauraronsu, wucewa kawai tayi a lokacin kuma su Aliyu suka fara shigowa da kayan, saida suka gama duka sannan Aliyu yayi sallama ya bawa Umar Faruk makullin, mutanen gidan ne suka fito suna tambayar ina za'a da kayan, Zeinab aka aika ta tambayo tana fitowa ta fad'a musu wai nasu ne, kowa dai yayi farin ciki amma banda Baba.
Umar Faruk yasa aka kira masa, bayan ya fito yace dashi da ita su sameshi d'akinshi, ba b'ata lokaci suka hallara bayan yasa tasa dogon hijab, zaune suke gaban Baba ya fara da " 'yata, munga abin arzik'i da kika mana kuma mun gode, amma sai nake ganin da kinbar bawa kanki wahala haka, tunda cikin ikon Allah muna ci muna sha kuma muna rayuwa cikin rufin asiri, dan haka ba buk'atar ki dinga bawa kanki wahala."
Kallon Baba tayi ido tsaye tace "Baba, karka wahalar da kanka, in har nima d'aya ce daga cikin 'ya'yanka, to inada damar da zan taimaka maka, bawai inayi bane saboda wani abu, haka kawai nake ganin ya dace na taimakawa duk wanda yake tare dani, a shekarunka mune ya kamata ace muna ciyar da kai da d'aukar duk wata d'awainiyarka, dan haka kamin addu'a kawai bawai magana akan na daina ba, dan hakan a cikin jinina yake zaiyi yuwa na daina."
Tunda ta fara magana Umar Faruk ya saki baki yana kallonta, mamaki yake irin yanda take girmama iyayenshi kamar dai ta sansu, yana mamaki shin dama haka hallayarta take ko kuwa dai wani abu take nufi, muryar Baba ce ta katseshi da yace "to yata Allah ya miki albarka, amma duk da haka dai ki bari, tunda kinga dama bani bane nake ciyar da gidan nan a yanzu, Umar Faruk ne da yayanshi Abbakar."
"Baba, ai nima 'yarka ce yanzu, koba komai ka haifeni, bugu da qari kuma kuma ni matar Faruk ce, ina da damar da zai iya taimakawa mijina."
Tana fad'a tabar d'akin ba tare data bi ta kansu ba, shima dai bayanta yabi dan kawai ji yake kamar tana masa nisa ne a kowane tako, suna shiga ta cire hijab d'in ta d'auko littafinta ta zauna kusa da Faruk,
"Dan Allah ka biya min wani." ta fad'a a tausashe.
"Khairat." Umar Faruk ya kira sunanta yana kallon idonta yayin da zuciyarsa ke azalzalarsa Alan sonta.
Shiru tayi tana kallonshi itama amma kawai saiya basar daga abinda yaso fad'a mata, dan a ganinshi ba abu bane mai yiwuwa, sam ba zai lamunci hakan ba.
Kawai karatun sukayi tare da fara karanta husnul muslim saboda ta iya addu'o'i shima sosai ta maida hankalinta akai har suka gama, sallah isha'i ce ta fitar dashi
bayan ya dawo kuma Ruk'ayya ta kawo abinci, sam Khairat bata ci ba sai karatunta daya d'auke mata hankali.
*Me kuka ce fan's, ya fad'i abinda ke ransa ko yayi shiru.*???
πππππππ
_Na gode 'yan uwa, naji dad'in addu'arku tare da fatan alkairi, ku sani Sameera na yinku sosai, kuma sister's d'ina ma sunce suna godiya._
_Ban d'auka zaku samu Jihadi ba a yau, amma farin cikin da nake ciki yasa na qoqarta na qarasa muku typing d'in nan, wannan page baki d'aya na bawa k'annaina ita, *Ameera* da *Haleema*, wallahi ina sonku 'yan uwana abin alfaharina._
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
2⃣8⃣
Shima wani littafi ya bud'a ya fara karantawa, ya jima sosai kafin ya aje ya tashi yayi wanka ya fito ya fara shiryawa, ganin zai saka kaya yasa Khairat sauka daga kan gadon zata fita, tana saukowa tari gabanta yana mata wani irin kallo yana warware rigar dake hannunshi zai saka, giftashi tayi zata wuce ya sake tareta, numfashi ta sauke ta kalleshi fuska ba annuri tace "meye matsalar?"
Saida yaja wani dogon numfashin kafin yace "d'azu kin sumbaceni, me yasa?"
"Me yasa baka tambaya ba tun acan sai yanzu?"
"Nan ne ya kamata muyi maganar."
"To idan ka gama saka kayan na dawo sai muyi magana."
Zata fice ya janyo hannunta, wani kallo da sukawa junansu lokaci d'aya kuma Khairat ta d'auke idonta, cikin kissa da mazantaka Umar Faruk ya rumgumo kugunta ya had'a da nashi yasa hannunshi d'aya ya cire hular dake kanta ya fara wasa da gashinta, kafeta yayi da ido akan yasa ta kasa kallonshi, qirjinshi kawai take kallo gabanta na faduwa sai dai kuma shima tana jin yanda zuciyarshi ke bugawa saboda hannunta na kan saitin zuciyarshi, a hankali ya sunkuyo da kanshi ya kalli fuskarta, ganin tayi quri da ido tana kallon qirjinshi yasa ya hura mata iska a ido, da sauri ta lumshesu kai tsaye kuma ta bud'e ta kalleshi, saida ta had'e yawu masu daci sannan tace "me ka keyi haka, ka manta meka fad'a jiya?"
Wani shu'umin murmushi yayi yace "ke kika tab'oni ai, akan me kika sumbaceni? dan haka ramawa zanyi."
A k'arfi ta kwaci kanta tayi baya ta nunashi da hannu tana fad'in "karma ka fara wallahi, karka dauka nayi ne dan jin dad'i, kawai ni nayi ne saboda mutanen dake wurin, idan kuma kace zaka tab'ani harka sumbaceni, wallahi...."
"Ba sai kin qarasa ba." ya katseta da sauri.
D'orawa yayi da "meye na rantsuwa, karki wahalar da kanki, kece zaki kwana a ciki danni ina da mata, yanzu haka ma wajenta zanje."
Wani dammm, taji gabanta yayi amma saita dake tace "to ina ruwana da matarka ni, kuma wallahi kaje ka kai mata kwana na, to ban yafe ba."
Busehewa yayi da dariya yace "zaki yafe, tunda ke kika ja komai."
Duk da ganin ya zame towel d'in jikinshi sai qaramin wandon dake jikinshi baisa ta daina fad'ar abinda take fad'a ba ta rufe ido sai masifa take "wallahi ba zan yafe ba ko mutuwa za kayi, haka kawai ka mayar dani wata ballagaza kana cin amanata, toni ba sakarya bace wallahi, kuma kaje daga kai har matarka zaku shigo hannuna, aikin banza kawai kace waini na janyo komai, ba wani nan dama kana so kawai baka samu damar tafiya bane inda za'a baka."
Yana cikin d'aure belt d'inshi ya kalleta yace "kema ai nasan kinji wani abu a lokacin, watak'ila har yanzu kina jin shauk'i tunda mutum ce ke, sai dai ko in kina da k'arancin isassar lafiya."
"Kuutt, ni d'in ce ma banda lafiya? wallahi lafiyata k'alau ni, sai dai in kaine baka da lafiyar."
"Ni ai dama bance miki bana da ba, ke dai nake tunanin ba kyada ita."
"Wallahi ina so da." ta fad'a tana juya baki.
"Kin tabbatar?"
"Eh." nan ma tayi maganar tana zabga masa harara.
Matsowa yayi kusanta yace "kenan kema kinji wani abu d'azu."
"A'a, a'a wallahi ni babu abinda naji."
Saida ya b'alla botir d'in rigarshi yace "to in kina so na yarda babu abinda ki kaji, ki bani dama na bincika da kaina saina gane, amma in ba haka ba to qarya kika fad'a kina b'oye wani abu a ranki."
Babbar yatsarta tasa a bakinta tana kallonshi tana tunani, fito da yatsar tayi tace "ka rantse babu cuta a ciki."
"Cutar me kuma? gani gaki fa, kuma a gabanki za ayi gwajin."
"Na amince to." ta fad'a da gyara tsayuwarta.
Matsowa ya sakeyi kusanta yana fad'in "ok, bani minti d'aya tak ya isa na gano gaskiyar komai."
Kafin tayi magana taji bakin Umar Faruk a nata bakin, "ahhhh." kuma sai tayi shiru tare da lumshe ido.
Shi kanshi ji yake kamar bashi ba dan bai shirya yin hakan ba, zuciyarshi kawai yaji tana izashi akan yin komai, bayanta yake shafa a hankali yana latsawa har lokacin daya zura tafikan hannayenshi ta cikin rigarta, bras dake jikinta ya balle ba tare daya cireta ba yakai hannayenshi a mamanta, jin yanda yake shafasu ne yasa Khairat qamqame Umar Faruk sosai tare da turo masa gabanta, shi kanshi sake fita hayyacinshi yayi yanda yaji gaban tsam tsam dashi kamar an hura mata iska, wani numfarfashi yake saukewa yana ji yana so yakai wata gab'a da baisan ko zai iya jarumtar hakan ba.
_Wannan abu yafi qarfina_π♀π♀π♀
Yanda ta qamqameshi tare da cabko harshenshi ta fara tsutsa yasa gaba d'aya ya rasa wanene shi me kuma yake yi, biye mata yayi suka fad'a kan gado, harya fara shirin rabata da rigarta sai kuma ya tuna minti d'aya ne gareshi, a zabure ya tashi tsaye yana gyara jikinsa da saisaita nutsuwarsa, Khairat ma a firgice ta tashi zaune tana ganin an fara cire mab'allan rigarta tayi saurin rufe qirjinta tare da duk'e kanta qasa, kasa had'a ido sukayi harya d'aga qafafunshi ya bar gidan.
Yana fita ta shafi gashin kanta tace "oh Allah na."
Kasa motsawa tayi daga wajen tana tunani har bacci ya fara fizgarta, daga nan kuma ta kwanta sai bacci.
***************
Yana fita daga nan siyayya yayi ta yan kayan motsa baki ya wuce gidansu Zuby, dan tun ranar daya rabata da budurcinta bai sake komawa ba, bai samu tanti a gidan ba sai Zuby kad'ai, yayi mamakin rashin tanti a gida a wannan lokacin amma ya zaiyi, da gudu Zuby ta qaraso ta rumgumeshi, shima rumgumeta yayi dan dama a tafashe yake, amma abin mamaki shine, abinda yaso yaji bashi yaji ba, ga dukkan alama ba tayi wanka ba kodan bata san da zuwanshi bane oho, a hankali ya raba jikinta da nashi yana murmushin yak'e, "sannu da zuwa yah Umar, shine ko ka sanar dani kana zuwa?"
"Ina so na miki bazata ne." ya fad'a suna nufa d'akin da aka ware mata.
Tsaye yayi yana kallon d'akin ganinshi a yamutse, da hannu ya nuna mata yace "meye haka Zubeid? na d'auka nan shine muhallinki."
"Eh yah Umar, ai an fara tattare min kayana ne gobe za'a kaisu can gida ayi gyara d'akin, jibi kuma saina tare." ta k'arashe maganar da jin kunya.
Ya karb'i uzurinta hakan yasa ya bata ledar hannunshi yana fad'in "ya jikinki."
"Kai yah Umar, yayi sauk'i fa." ta fad'a cikin rufe fuska.
Hannunta ya kamo ya sake rumgumeta a jikinshi cikin sanyayen muryar da baima san yana da ita ba yace "kinyi kewata kuwa?"
Cike da jin kunya tace "eh mana yah Umar."
"Kenan....zaki sake...bani wani abu ne?"
Cikin tsoro ta bud'e baki tace "yah Umar, ba yanzu ba gaskiya, ka bari saina dawo gidanka."
Cikin shagwab'ar da tunda yake a rayuwa bai tab'a irinta ba yace "kenan tsoro kike ji? zafi ke akwai ne har yanzu?"
"Eh to yah Umar, akwai zafi kuma akwai wahala, amma dai ba sosai ba."
Sakinta yayi yace "shikenan to na hak'ura harki shigo hannuna."
Kafin tayi wata magana yace "ni zan koma gida, ki gaida tanti idan ta dawo."
"Yah ko zama ba kayi ba fa?"
"Karki damu, ki gaisheta kawai."
Sallama sukayi ya fita, fitarshi kuma tanti ta tsinkayeshi sai dai shi bai ganta ba, tun daga soron gidan ta fara kiran "Zuby, Zuby, ke kina ina fito fad'a min waccen mara mutuncin me yazo ya miki, injin dai baki yarda dashi ba? dan na lura yaron nan so yake saina mashi rashin mutunci."
Zuby dake tsaye tana kallonta tare da sauraronta ne tace "kai Mama, bafa abinda ya kawoshi kenan ba, kawai yazo ganina ne."
"Aina d'auka iskancin ne ya kawoshi."
Dorawa tayi da "kinga abinda nake fad'a miki ko, tunda ki kayi aure nake fad'a miki ki saba da yawon wanka amma ba kyaji, yanzu gashi ya miki zuwan bazata, ke ko kunya baki ji ba?"
Ganin zata maida bala'in a kanta yasa ta shigewarta d'akin ta d'auki ledar tsirenta ta fara ci, shigowa tayi tana ganinta ta fizge ledar tana fad'in "shegiya matsiyaciya , wato ke kad'ai zaki ci saboda baki da mutunci."
Fita tayi da ledar Zuby kuma ta bita tana fad'in "wai Mama me yake damunki ne, to kema ke kad'ai zaki ci, dan Allah ki bani kayana."
_Ganin uwa da d'iya zasu botsare akan ledar tsire yasa na fito,danni ba wajen kuka na bane, da kaza ceπ da sunga sabon tashin hankali *amma fa shima ina sonshi, musamman na madugu mai nama*._πmaman Dady.
*************
Ishaq ya samu a kofar gida dan haka ya tsaya suka gaisa, "kaga mijin mace biyu, matashin yaro mai sa'a a duniya, wanda ya fara da zankad'a zankad"an mata a lokaci guda, kai Umar Faruk ina fatan Allah ya bani irin taka."
"Idan ka gama shiriritar ni zan shiga ciki dan bana da lokacinka."
"Humm, ba wata shiririta, kai dai kawai kace za kaje ne tana jiranka, aini na gama sanin komai wallahi."
Kashe motan yayi yace "me kenan?"
"Kuma, ka manta dazu a ma'aikata kun nuna mana sanfiri a fili mun gani."
Duka ya kai masa ya goce yana fad'in "kaifa d'an iska ne wallahi, to an fad'a maka sone ya kawo hakan? kawai tayi ne saboda ire irenku 'yan gulma."
"Kaiba wani nan wallahi, kawai kuna cikin shauk'i ne."
"To naji, saime kuma?"
Dariya yayi yace "halan daga wajen Zuby kake?"
"Eh, daga can nake, da wata matsala ne?"
Rik'e kan mashin d'inshi yayi yace "kaii , amma fa Umar Faruk kana more rayuwa wallahi, ace ko ina jin dad'i ne ya baibayeka, ka fita daga gida kabar santaleliyar lace kaje wajen wata santaleliyar, gashi kuma zaka sake shiga ciki waje wata zankad'aziyar."
"Allah ya shiryaka Ishaq, wallahi kayi sauri kayi aure, inba haka ba zaka mutu."
"Miye zai kasheni to?"
"Ba zaka sani ba inba matakin ka kai ba."
Tayar da mashin d'in yayi zai wuce cikin gida Ishaq yace "za kasha mamaki idan na fad'a maka wacce nake so."
Hararanshi yayi yace "ya wuce kace Ruk'ayya kake so, banza kawai dake tsoron fad'an abinda ke ransa."
Da k'arfi ya rik'e moton yana fad'in "waye ke tsoro d'in? naga ai bani kad'ai bane ya kasa fad'a, kaima ka kasa fad'a."
Sake kashe moton yayi yace "wa wai? ni kake nufi? ai kasan ni tuni na wuce wajen wallahi."
"Qarya kake, domin soyayyarka ta gaskiya yanzu ne ta fara."
"Me yasa kake sha'awar mayar dani baya, kasan sau nawa ina fad'awa Zuby kalmar so? yafi sau dubu."
Sosai Ishaq ya kalleshi tare da nuna ba wasa a abinda zai fad'a yace "saboda ba ainihin sonta kake ba, Khairat itace wacce zuciyarka ta kamu da sonta, watak'ila ka fahimci hakan, ko kuma ka sani kana take sanin ne, amma ka sani tun fil'azal dama Zuby ba sonta kake ba, kawai sone na 'yan uwantaka da kuma shak'uwa."
"Kasan me kake fad'a? kaifa kasan Zuby da Khairat, kuma kasan matsayin kowace a zuciyata, to me yasa kake so ka nuna bana qaunar Zuby?"
Rumgume hannayenshi yace "sanin haka ma yasa nace maka Khairat itace masoyiyar zuciyarka, amma ba Zuby ba, kayi tunani hakan haka da kanka zaka fahimci gaskiyar da kake b'oyewa, kayi tunani da kyau zuciyarka zata bayyana maka alamomin a fili wanda take fad'awa a duk lokacin da tayi tozali da Khairat."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "haka dai kace, ni saida safe."
Dariya yayi shi kuma yace "hakane ma."
***************
Saida ya shiga yaga Baba ya mishi sallama haka ma d'akin Mama sannan ya wuce d'akin, ganinta kwance tana bacci yasa ya cire kayan jikinshi ya watsa ruwa ya sauya kayan bacci sannan ya zauna makwacinshi, remonte ya dauka ya kunna qira'a ya fara biya.
Sautin k'ira'ar daya kunnane yasa ta farka, saida ta murje ido sannan ta zuro da qafafunta ta sauko daga kan gadon duk yana kallonta, tana kallonshi taji haushi ya lullubeta wato ya dawo daga wajen matarshi, hararanshi tayi ta bud'a ma'ajiyar kayanta ta d'auko qaramin wando iya cinya da rigarshi hannayen sun d'an sauko zuwa damtse, yana kallo ta cire rigarta sai bras d'in daya b'alle mata ko gyarawa ba tayi ba, juyowa tayi sai kuwa sukayi ido takwas takwas, hararanshi tayi ta juya ta zage bras d'in ta d'auki rigar baccin ta saka, juyawa tayi ta sake kallonshi tace "zan saka wando fa."
"Miye nawa a ciki to?" ya fad'a yana d'auke kai daga barin kallonta.
"Ka rufe idonka to." ta fad'a a kaurare.
"Nak'i d'in, idan zaki saka ki saka, kuma ma ai naga ke ba lafiya ne dake ba." ya fad'a kamar bashi ke maganar ba.
Da hannu a nunashi tace "kai, karka qara cemin bana da lafiya, Allah ranka zai b'ace."
"An fad'a d'in, inga b'acin ran dan Allah."
"To ka sake cemin banda lafiya ka gani."
"To kina da lafiyar ne? aini ba zan tabbatar ba har sai jarabaki na gani."
"Hahahahaha, kaji yaro, waini zai mayar shashasha mahaukaciya, to an fad'a maka ni d'in yar shekara goma ce da zaka mayar dani abar wasarka, to bari kaji, inma wani abu kake nema a wajena ka sani ba zaka samu ba, ka jira amaryarka tazo sai kuje ku cinye kanku, tunda naga ita d'in marar aji ce da har zata bada kanta tun bata tare ba."
Maida kanshi yayi Γ§a tv yace "kedai kiyi fatan kar Umar Faruk ya buk'aceki, dan hakan na faruwa to ki sani kin zama sorry."
"Dan Allah Faruk ka buk'aceni, ni kuma a lokacin zan nuna maka nawa d'anyan kan."
"To waima me kake tunanin zaka min? tausheni ta k'arfi kamin fyad'e."
Saida ya kalleta yace "kina ganin ba zan iya bane?"
Cike da raini tace "hmm, jarumtarka bata kai can ba."
Tana fad'a ta juya ta fara zuge dogon wandonta, bata kai ga cirewa ba taji an hankad'ata saman gadon ta fad'a, kafin taga wanda yayi aika aikar kuma aka tausheta , duk da dai ta gane Umar Faruk ne amma bata fahimci yanayinshi ba, had'e hannayenta yayi da katifar ya taushe tare da sakar mata gaba d'aya nauyinshi, taushe mata qafafu yayi da nashi qafafu sannan ya had'a goshinsu wuri d'aya yana kallon qwayar idonta, yunk'urawa tayi da nufin ta tashi amma taji ko matsawa ta kasa yi dan ba qaramar matsa ya mata ba, bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba suka fara gangarowa ta kunnuwanta, da qyar take fitar da numfashi sama sama ga zuciyarta dake barazanar fitowa waje, tausar daya mata yasa yake iya jiyo bugawar da zuciyarta keyi, cikin muryar kuka tace,
"Dan Allah Faruk ka d'agani, wallahi ni ba dakai nake ba, ina jin tsoron abinda za'a aikata, zaka iya jimin ciwo kamar yanda suma suka min."
Wani mugun tausayinta ne ya rufeshi dan take qwaqwalwarshi ta hasko mashi photonta kwance a gadon asibiti bata san inda kanta yake ba, basarwa yayi ya mata kallon ki shiga hankalinki sannan yace "wannan sanfiri ne na nuna miki, idan kika qara qalubalantar mazantaka ta, to zan wuce inda bakya zato kuma nayi kaca kaca dake."
Da sauri tace "wallahi ba zan qara ba, wanda nayi ma na tuba."
D'agata yayi ya koma mazauninshi yana fad'in "sai tsoron tsiya amma kuma ba hus, hada wani wai zaka jimin ciwo, ko ciwon me zanji ma wacce ke a bud...."
Sai kuma yayi shiru dan yasan ba lallai maganar ta mata dad'in ji ba, ba abinda bata jiba hakan yasa ta share qwallanta tace "eh naji, nasan idan ka kusanceni ba zan galabaita ba, amma kuma nasan dole zansan ka shigeni, saboda na yarda da kaina, kuma nasan cika bakin ba zai rasa nasaba da waccen figaggiyar matar taka ba, ita dake budurwa ai banga kayi sammakon zuwa kai mata d'auki ba."
Saida ta sauke numfashi sannan tace "wallahi ka sake cin zarafin matsayina saina had'aka da mahaifinka ya shiga tsakaninmu."
Bata damu dashi ba ta zage wandon ta saka na bacci sannan ta kwanta, tunowa da addu'a yasa ta tashi ta kalleshi tace "ka taimaka ka koya min addu'ar kwanciya bacci."
A wulak'ance ya kalleta tare da harara, itama hararar ta banka masa had'e da juya baki , tasowa yayi yazo kan gadon ita kuma tana ganinshi ta wuntsila ta sauka, ta kan gadon ya taka ya ritsata saboda bata da hanyar bi, hannu ya kai zai shak'o bakinta ita kuma tasa hannu ta rufe bakin tana fad'in "na tuba, wallahi mantawa nayi ba zan sake ba."
Kunnenta ya kama sosai ya murd'e yana fad'in "zaki koma kenan in dai har kina mantawa."
"A'a wallahi, a'a ba zan sake ba, na shiga uku kunnena , dan Allah kayi hak'uri kunnena zai cire, dan Allah Faruk kunnena."
Duk tana maganar ne tana tsalle tsalle da yarfa hannaye ya saketa , "sai kinyi alk'awarin ba zaki sa...."
"Nayi nayi, wallahi nayi, ba zan sake ba." ta fad'a tun bai qarasa ba.
Sakinta yayi ya sake kafeta da ido yace "me sunana?"
"Faruk, fa...Umar Faruk....Umar Faruk sunaka."
Da k'arfi ya bugi bangon dake bayanta yace "sunana kenan na yanka, amma ba sunan daya kamata ki kirani dashi ba kenan, ina so naji sabon sunana."
Kallon gefenshi tayi tana sharb'ar majinaπirinta ansha kukan nan ta fara girgiza kai tana fad'in "dan Allah ka bari zanyi tunani akai."
"Me? sunan ne sai kinyi tunani? zan zubar miki da hak'ora ma."
Ya fad'a kamar zai kai mata mazga, dafe kai tayi ta durk'ushe, "tashi tashi." ya fad'a yana mata alama da hannu.
Tsaye ta mik'e duk tayi kalar tausayi sannan yace "ina jinki."
"Malam." ta fad'a kamar zata fashe da wani kukan.
"Um um, bashi nake so ba."
Gashinta dake kwance kan wuyanta ta kama tana wasa dashi tana ta rarraba ido, can ta tuna ta kalleshi cikin lab'e baki tace "baby."
Wata shegiyar dariya Umar faruk ya kece da ita kafin yace "baby? ki aje wannan sunan har ranar da kika shirya d'aukata a matsayin mijinki, amma ba yanzu ba."
Hannunta ya janyo ya zaunar da ita a inda ta tashi yaja zanin rufa ya rufa mata sannan yace ta d'aga hannayenta suyi addu'a, haka sukayi har suka gama sannan ta shafa ta kwanta, kallonshi tayi tana mamakin izzarshi da kwarjini, ko ba tayi niyyar abu ba inda ya canza yanayinshi to dole take yi, tunawa tayi da sak'on Papa hakan yasa tace,
"Ka shirya inji Papa, nan da kwana biyar za muje Germany."
Kallonta yayi yace "Germany kuma? wajen me? kuma dole sai dani?"
"Haka dai yace, wai tarone mai mahimmanci."
"Kiyi hak'uri, gaskiya bana jin zanje."
"Me yasa?" ta fad'a tana tashi zaune.
"Jibi Zubeida zata tare, kinga kuwa za'a shiga hakk'inta."
Rudududu, 'yan cikinta suka ya mutsa , da k'arfi tace "tariya kuma?"
"Eh, da matsala ne?"
A hassale ta sauko daga kan gadon ta fara nunashi da yatsa tana fad'in ".....
_Me kuke tunanin za tace_?
_Shin ya kamata ya bisu su tafi?_
*Kuyi hak'uri da wannan masoyana.*
0 comments:
Post a Comment