Fateema da Zeinab ne suka amsa da "munyi aunty."
Kumatunsu ta shafa tace "da kyau 'yan mata, zan wuce, idan na fito zan baku tsarabarku."
Wucewa tayi Ruk'ayya tabi bayanta da kayanta, tana shiga d'akin taga yasha gyara, kallon Ruk'ayya tayi tace "kece ko?"
Cikin dariya tace "eh aunty, ai naga bakya son k'azanta, shi yasa nake shigowa ina gyarawa duk da ba kya nan."
"Kin kyauta." ta fad'a tana shirin fitowa yin alwala.
"Amma fa aunty naga sai farin ciki kike, kodai da wani abu ne?" cewar Ruk'ayya.
Cak Khairat ta tsaya amma bata juyo ba, ajiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske, ita kanta haka take ji tana farin ciki, kuma baya rasa nasaba da kusanto da kanta da tayi wajen Umar Faruk, ba tare data juyo ba kuma ta wuce ta fad'a 'yar qaramar toilet d'insu, koda ta fito bata samu Ruk'ayya ba, a haka ta kabbara sallah kuma harta kammala Umar Faruk basu shigo ba.
Jakar data zuba tsarabara ciki ta janyo ta fito da ita tsakar gidan, fitowarta yayi daidai da fitowar Zuby daga d'aki itama, kallon juna sukayi Zuby kuma ta bita da harara, Khairat kuma binta tayi da kallon zan kamaki a hannuna, wajensu Mama ta nufa inda suke zaune akan tabarma, zaune tayi itama tana cire hijab d'in jikinta danya d'an takurata sannan ta bud'e jakar, kayan kanti ne masu kyau da qualitie wanda ta siyowa Zeinab, Fateema, Yusuf, Ubaidullah, Bilal, Abdul rahaman, bawa kowa tayi sai lokacin ta fahimci ba kowa ya samu ba, dan dama ba wani sanin yaran tayi ba tayi anfani da ganinsu ne yau da gobe, kallon sauran tayi tace "ayya, kuyi hak'uri kunji, insha Allah kuma zan siyo muku naku."
Mama Sa'a kuma cewa tayi "haba, aiba komai ba, wannan ma an gode wallahi, Allah yashi albarka."
Mama kuma dad'i taji sosai saboda ganin anyi daidai, dan Bilal d'ane ga Mama Maimuna kuma ya samu, Abdul rahaman d' ga Mama Sa'a kuma shima ya samu, Zeinab kuma 'yarta ce itama kuma ta samu, sai Fateema da Yusuf yayan Abbakar, suna cikin godiya kuma saiga takalma ta fiddo ta bawa Mama Sa'a Mama Maimuna da kuma Mama, suna da kyau kuma basu da tudu ko kad'an, nanma godiyar suka fara sai kuma ga wasu kayan masu kyau tabawa Ruk'ayya har kala uku, wata agogo ta fito da ita mai shegen kyau qirar rolex ta bawa Mama Sa'a da tafi kusa da ita tace "wannan na Baba ne."
Kafin tayi magana Khairat ta fito da wata agogon qirar gucci ta fata tabawa Saratu tace "na mijinki ne wannan."
Sannan ta bita da wasu had'add'un turare kala uku tace naki ne wannan."
"Kai, amma na gode sosai yer uwa, irin wannan tsaraba haka."
Sallamar Aliyu da Usman ce ta katsesu, 'karasowa sukayi Usman na fad'in "matar yaya, yaushe garin?"
A harshen zarma ta amsa mishi da "ana sallah na shigo."
"Sannu da zuwa, ya hanya?" cewarsu gaba d'aya.
"Lafiya lau." ta fad'a tana mika musu wasu kwalaye wanda ko a cikin bacci aka basu zasu san na miye, Aliyu ne ya waro ido yace " Iphone7, ta mece aunty?"
"Naku ne." ta fad'a ba tare data kallesu ba.
Su kuma mamaki ne ya hanasu karb'a, saida ta juyo tace "baku sone?"
Da sauri Aliyu ya karb'a yana fad'in "ah haba aunty, mu mun isa? mun gode Allah saka da alkairi."
Karb'a yayi duka ya mik'awa Usman d'aya, amma sai Usman yace "na gode, amma gaskiya ni bana so, wannan ma ta isheni."
Ba tare da damuwa ba Khairat ta kalli Aliyu tace "ok , ka bawa maiso ko cikin abokanka."
Mamaki ne ya cika kowa dake wajen, Usman d'in ne yace "kud'i fa kika saka kika siyo saboda ni, me yasa ba zaki aje ba koki siyar?"
Wani d'an murmushi tayi mai sauti tace "ba wakai ba na siyo, na siyo ne wa mutanen da nake rayuwa dasu, tunda baka so ai ba za'a rasa maiso ba."
Gyara zama tayi tana kallonshi tace "da farko na shigo gidan nan ne a matsayin bana son d'an uwanku , duk da haka kuma zan iya sadaukar da komai nawa dominku, yanzu kuma da nake son Faruk, ina ji zan iya taimaka muku da k'arfina ma ba iya dukiyata ba kad'ai, ko zaku kasheni ba zan daina muku alkairi ba domin kuwa a jinina yake, haka ma kome za'a fad'a ba zan daina taimakawa mutane ba."
Tana fad'a ta tashi zata wuce d'aki Mama Sa'a tace "dan Allah yata kiyi hak'uri, karki bi ta abinda ya fad'a."
Juyowa tayi za tayi magana idonta ya sauka akan Zuby dake k'ofar d'akinta zaune, shiru tayi ta wuce d'aki tana ji kamar bata kyauta ba da bata bawa Zuby komai ba, domin kuwa kishiya aina mak'iya bace, coiffeuse d'inta ta kalla, da sauri ta qwala kiran sunan Ruk'ayya, tana shigowa ta d'auki wasu turaruka wanda suke birgeta har guda biyu ta bata tace "ki kaiwa Zubeida."
Da mamaki Ruk'ayya tace "amma aunty sai naga kamar naki, me yasa zaki batasu?"
Cikin d'an murmushi tace "Ruk'ayya, wannan ba komai bane danna bawa Zubeida wannan, itafa kishiyata ce bawai mak'iyata ba, zan iya bata fiye da wannan ma musamman idan ta buqata ko kuma naga buqatar hakan ta kamata."
"To aunty." ta fad'a tare da fita daga d'akin.
Tana bud'a labulen suka ci karo da Umar Faruk wanda labarin zuwanta ya sameshi tun a tsakar gidan, rab'awa tayi ta wuceshi shi kuma ya shiga ciki, Khairat na ganinshi ta daka tsalle tare da qara ta nad'e a jikinshi,shima rumgumeta yayi sosai a jikinshi yana juyi da ita a tsakiyar d'akin yana dariya, cikin murna take fad'in "nayi kewarka sosai baby, nayi kewarka, nayi farin cikin ganinka sosai."
Sauketa yayi da nufin ya mata magana amma saita had'e bakinsu waje d'aya, shima bai tsaya b'ata lokaci ba wajen biye mata suka lula wata duniyar, sunyi nisa sosai a duniyarsu suka ji wata hayaniya a tsakar gidan, dakatawa sukayi Umar Faruk kam fad'awa yayi akan gado yana sauke numfashi, ita kuma gyara rigarta tayi ta lek'o daga d'akin, jin hayaniyar ba qarama bace yasa ta qarasa fitowa, tsakar gidan ta fito tana kallon Zuby dake masifa wai Khairat ta bata turare bayan ta mata sihiri a ciki, su Mama ne ke bata hak'uri da ban baki, amma ganin haka sai yasa ta buga kwalaben a qasa suka watse a banza, ganin hakane yasa Khairat nufa wajen Mama ta kama hannunta har saida ta shigar da ita d'aki sannan ta zaunar da ita tace "ki zauna ki huta Mama, dan Allah kada ki kulata, nima kuma ba zan kula ba."
Bata jira me Mama za tace ba ta fita daga d'akin, tana fitowa ma kai tsaye d'akinta ta nufa tana fad'in "dan Allah duk mai aikinyi yaje yayi."
D'aki ta nufa Zuby kuma tace "hum, wato an mayar dani mahaukaciya, to bari kiji wallahi sihiri da qulubotanki ba zai tab'a kamani ba, kuma ni dake mu zuba mu gani shege ka fasa."
Juyowa Khairat tayi ta kalleta tace "ke, ni bana da lokacinki, yanzun lokacin mijina ne, idan kuma kin shirya masifa dani to ki bari har gobe, kinsan me yasa nace har gobe? domin kuwa gobe ranar aikina ne, kuma ko wannan uwar taki bata isa ta b'ata min abinda nayi niyyar shiryawa ba, dan haka ki aje masifarki har goben."
Wucewa tayi ba tare data kula kowa ba, suna ganin shigarta kusan kowa ma ya watse, Mama ta kaiwa Baba agohonshi kuma yayi godiya sosai, haka ma Abbakar shima yayi godiya, a kwance ta sameshi dan haka ta kwanta kanshi ta fara sumbatarshi.
Saida suka kusa shiga duniyar da ba zan iya binsu ba sannan suka tsaya, Khairat ce tace "baby."
"Um." ya fad'a cikin maqoshi.
"Har yanzu ba kace komai ba."
Saida ya janyota jikinshi ya d'ora hannunshi akan mazaunanta yana shafawa yace "me zance? bayan kin hanani fad'ar komai."
"Duk da haka kace wani abu."
Saida ya sake mannata a jiki yace "to da fatan kinzo lafiya? ya hanya yasu Mama?"
Saida ta sumbaci kumatunshi tace "lafiya lau, yana sameka?"
A sanyaye yace "lafiya lau."
Kallonshi tayi hakan yasa numfashinsu ke gyauraya tace "Faruk ina qaunarka, ina sonka fiye da raina, sonka yamin mugun kamun da ba zan iya kub'uta ba, kuma na fahimci hakan ne a tazarar da muka samu na kwana biyar, dan Allah baby ka zauna dani har qarshen rayuwarmu."
"Baby, ba zan iya rabuwa dake ba nima, ina sonki kuma ina qaunarki, rabuwa dake kamar rabuwa da numfashina ne, dan haka babu maganar rabuwa."
Shigewa tayi jikinshi suka sake dunk'ulewa suna sauke numfashi, tunawa da Zuby yasa Umar Faruk tashi zaune yana d'aukar rigarshi yana sakawa, fahimta da Khairat tayi yasa ba tace komai ba harya gama saka kayanshi, saukowa tayi itama tana fad'in "yanzu sai yaushe zaka zama nawa? wallahi ina buqatarka kusa dani"
Kumatunta ya shafa yace "nima haka baby , amma ai gobe ne."
Turo baki tayi gaba kafin tace "to yanzu me kake so na dafa maka gobe?"
Cike da zolaya yace "wai harkin gogene?"
"Sosai ,kana tamtama?"
"A'a, ina dai mamaki ne."
"To fad'i me kake sha'awar ci gobe?"
"Tuwan shinkafa."
"Ai kuwa zaka ci insha Allah."
Sumbatar kumatunta yayi yace "gobe zai sauke miki gajiyar tafiya, ki kula min da kanki."
"Um, kodai ka saukar min da wata gajiyar ba, saida safe." ta fad'a tana d'aga masa hannu.
Yana fita itama ta fito ta shiga wanka kafin ta fito tayi shirin kwanciya, da tunanin gobe bacci ya d'auketa saida asuba.
**************
Koda Umar Faruk ya shigo da nufin tashin Khairat tayi sallah ya samu har tayi alwala zata kabbara raka'atanil fijir, murmushi ta sakar masa tace "baby, ina kwana, ka tashi lafiya?"
Wani sanyi yaji yana ratsashi na musamman kafin ya shafi kumatunta yace "lafiya lau, fatan kin tashi lafiya."
"Tunda dai kana cikin k'oshin lafiya, to nima haka."
"To, ni zan wuce masallaci."
"Saika dawo baby."
Juyawa yayi zai fita yana bud'a labulen tace "baby."
Juyowa yayi ya kalleta, cikin wani kallon dake kashe jiki tace masa " *ana uhibbuka khasiran*."
Murmushi ne ya bayyana a fuskarshi wanda ya bayyana haqoranshi a fili, kallonta kawai yake yayin da qwaqwalwarshi ke zuwa mishi da tunani kala kala a game da ita, ya jima a haka kafin yace " *ihubbuki*
Sumbatar hannunta tayi ta jefa mishi kafin ya fita, haka ya tafi masallaci yana jin wani irin nishad'i da farin ciki na lullub'eshi , yana zuwa masallaci kuma saiya samu Malam baya jin dad'i dan haka yace ya jagoranci sallar saboda Abbakar bai riga yazo ba, haka yaja sallah cikin farin ciki da nutsuwa, kuma ya sake gazgatawa sallah cikin tsantsar nutsuwa wani lokacin yakan danganta da irin yanayin da kake ciki.
Khairat na gama sallah bata kwanta ba, saida ta zagaya ta gaishe da iyayen gidan kafin ta shigo d'aki ta cire hijab ta fara.......
_Meta fara to?_
*Dad'in comment d'inku ya sani sake muku posting duk da na fita unguwa, samun posting sau biyu ya danganta da yawan comment d'inku, dan gaskiya yau na samu comment sosai, kuma kuyi hak'uri da rashin maidawa saboda ina muku typing d'in ne.*
_Luv u guy's_π
17/08/2019 Γ 20:13 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
4⃣4⃣
Zanin gado ta fara canzawa abinda kuma bata tab'a yiba kenan tunda take a rayuwarta, tana gamawa ta d'anyi goge goge duk da ba datti ke akwai ba, tana gamawa tayi shara sama sama itama dai da wuya tayi ta dan bata tab'a yiba, turaren tsintsiya da kuma na wuta ta jona a kuran tayi, sannan ta had'a da airfreshner ta feshe d'akin dashi, zaman kujerar d'akin ta canza tare da qaramin teburin dake d'akin, hakan yasa kujerun dake waje suka samu matsugunni a d'akin, a gajiye ta shiga wanka ta fito, tsaye take tana tsane ruwan jikinta tare da gashin kanta data wanke.
******************
Koda ya dawo daga masallaci yace wa Zuby "zanje muyi karatu, kinsan tayi tafiya, ya kamata muci gaba."
A lokacin da take saka wasu littafin a jakar makarantarta ne ta kalleshi wulak'ance tace "wacece?"
A dake yace "Khairat mana."
Tashi tayi ta fara cire hijabin jikinta tana fad'in "oho, karatu dai, wane irin karatu kenan?."
Shiru yayi kawai bai tankata ba harta fara sarrafa abin karyawa, zaune yake yana tilawar karatu amma hankalinshi na kan Khairat, a haka harya yayi shirin tafiya wajen aiki, Zuby ma ta shirya tsaf zaune tayi ta fara karyawa, kallonta yayi yace "ki jira 'yar uwarki mana."
Wani irin yamutsa fuska tayi kamar taga kashi tace "ban dafa da ita ba, kuma gashi ban dafa da kai ba bare ka bata naka, in kuma zaka tuk'eni ne na amayar da wanda naci saina gani, tunda dama kafi sonta a kaina."
"Zubeida wai me yasa kike hakane, me yasa kika sauya gaba d'aya, wannan wane irin kishine kike nunawa haka? me zai hana kiyi koyi da 'yar uwarki, itafa ya kamata ta nuna kishi a matsayinta na wacce kika sameta a gidan, amma ba tayi ba saboda tasan bata da wani dalili nayin kishi a game dake, me zai hana kema kiyi wannan tunanin."
A hassale ta mik'e tsaye tace " eh mana, ai bata da dalilin yin kishi dani ne shi yasa, kasan me yasa? saboda tun fil'azal tare muke da kai, kuma a tare ta samemu ana shirin aurenmu, kenan sai tayi kishi dani saboda kawai ita jahila ce bata san ciwon kanta ba? to wallahi kaji ba zaka tab'a samun kwanciyar hankali ba tunda ka nuna kafi sonta a kaina, bakai ba kwanciyar hankali tunda nasan wacece ka had'ani da ita, karuwa, karuwa, babu yanda zanyi naci gaba da zama karuwa a gidan nan da karuwa, kamar yanda na haramta maka kaina dan ba zan yarda ka had'ani da jaraba ba wallahi ina zaman zamana."
Zaune ta koma tana cin abincin tana gunguni, nunata yayi da yatsa yace "sai dai ki rasa kwanciyar hankali amma bani ba, na fad'a muku tun farko, wallahi babu wacce ta isa ta tayar min da hankali, kuma na kasa maganinta, bansan ko kinsan auren zobe ba? to idan kin sani ko shine aka min daku wallahi zan tsigeku daga gareni, dan ba'a haifi matar da zata rainani ba, ke kinyi, amma ki sani ina raga miki ne saboda darajar iyayenmu, wallahi wallahi Zubeida kika kaini bango, tofa ki sani abinda ba kiyi tsammaninshi bane zai faru."
D'aukar jakarshi yayi ya wuce yana fad'in "haka kawai ki mayar dani mahaukaci, aure da tarewa cikin qanqanin lokaci, amma kina neman kisani yin abinda za'a dinga yi dani a gari, iskanci kawai."
Kai tsaye d'akin Khairat ya shiga, yana zuwa ya sameta tana goge ruwan jikinta, aje jakarshi yayi akan kujera yana kallon gyaran d'akin da tayi, yana qarasawa ya rumgumota ta baya, juyowa tayi tare da rumgumeshi tana fad'in "sannu da zuwa baby."
Kallonta yayi yace "ke ki kayi aikin nan?"
Cike da murmushi tace "ni nayi, kana mamaki ko? nima nayi mamaki da nayi aikin nan, yau kuma na sake tabbatarwa so zai iya sa komai, dan a yanzu ina jin zan iya zama da kai a kowane irin yanayi."
Rumgumeta yayi cike da qaunarta da kuma tausayinta da yaji ya lullub'eshi a take har idonshi sun kawo ruwa yace "zaki iya zama dani a kowane hali Khairat? "
"Zan iya Faruk, wallahi har zuciyata nake fad'a maka haka, a yanzun zan iya zama da kai koda a cikin rijiya ne, Faruk ina sonka so mai tsanani, son da ba zan iya fassara makashi ba, kuma a game da hidimar gidanka, to a shirye Hajia Khairat take wajen shanye kowace irin wahala, badan komai ba sai dan farin cikin mijina abin alfaharina kuma uban 'ya'yana."
Kafin yayi magana kuma ta daga qafafunta ta kaima tsayinshi, a hankali ta d'ora bakinta tana sumbatar wuyanshi tare da d'an tsotsawa, rufe ido yayi yana murmushi harya fara qyqyata dariya, rumgumeta yayi sosai ya rad'a mata a kunne "ina sonki Khairat, kina sani farin ciki sosai, ina fatan Allah ya barmu tare har abada, Khairat zan iya rayuwa dake ko babu 'ya'ya."
Kallonshi tayi da sauri tace "da gaske? kaga ni kuma ina so na haihu, na samu yar mace domin na d'orata akan tarbiyar da kuka d'orani kai da Mama."
Murmushi yayi yace "ashe kina son yara, in kuwa hakane yau d'in nan saina baki ajiyarsu."
Waro ido tayi tace "harsu nawa to?"
D'aure fuska yayi yace "da uku uku mana, dan kiyi saurin gamawa."
Fashewa tayi da dariya tace.....
_Kuna ganin zai iya?_π
_Sorry fan's, wlh wani aiki ya taso min bazata, shi yasa kuka jini shiru, kuyi hak'uri da wannan._
17/08/2019 Γ 20:13 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
4⃣5⃣
"Zaka iya kuwa?"
Wani kallo ya mata yace "kina qalubalantar mazantakata kenan? to bara kiga sanfiri."
Yana fad'a ya sungumeta ya dire kan gado, da zafi sosai yake aika mata da wasu gunduma gunduman sak'onni, yana daf da shiga wata sabuwar duniyar Khairat ta dakatar dashi, da qyar ta samu suka daidaita nutsuwarsu kafin ta kalleshi tana dariya tace "nifa duk da haka ban yarda zaka iya ba."
Lumshe idonshi kawai yayi yana shak'ar k'amshin daya gauraya d'akin, yunwar data ji ce tasa ta sauka daga kan gadon ta bud'a drower ta d'auki riga iya gwiwa ta zura ta fesa turaruka sannan ta bud'a wajen ajiyarta, gΓ’teau (cake) ta d'auko da chacolat ta aje akan tebur sannan ta d'auko jus mai sanyi tare da kayan marmari duk ta tule gabanta sannan tazo wajen Umar Faruk da har yanzu yake kwance ido rufe, hannayenshi ta kamo ta tayar dashi zaune sannan ta d'auki rigarshi ta saka mishi ta sauko dashi daga kan gadon duk yana kallonta, a ranshi kuma addu'a kawai yake mata akan Allah ya sata farin ciki kamar yanda take sakashi, kumatunshi ta dafa tace "to naji, yanzu ka samu dai ka fita ko nima nayi abinda ke gabana."
Saida ya sauke ajiyar zuciya yace "to, nine fa mijin Hajia Khairat, ko kuma nace madame Khairat, idan naso ma zan iya zamana tare dake."
Shafa cikinshi tayi tace "da fatan dai ka cika minshi sosai, dan naga bai taso ba."
Dariya yayi yace "kina so kiga ya taso ne kamar mai cikin wata hud'u ko biyar? aike ya kamata naga haka gareki, a lokacin da kika fara kula min da 'yan ukuna."
Turo baki tayi gaba tace "nidai ba wasu 'yan ukun da zan haifo maka, ina son d'aya d'aya dai, yanzu dai zo kaci ko kayan marmari ne saika wuce."
Baya so ya nuna baici komai ba daga wajen Zuby hakan yasa yace "a'a, nifa bana buk'atar cin komai saboda na k'oshi."
Wata yar ledata d'auko mai kyau ta bud'a ta d'auki wannan qaton cake d'in ta saka mishi a ciki tare da chocolat, sannan ta rufe ta bashi jakar tace "wannan kyautace daga gareni, bana so ka manta dani duk inda za kaje, ina so kayi anfani dasu." tana fad'a ta sumbaceshi.
Rumgumeta yayi yace "ki kula min da kanki sosai."
"Zanyi, kaima ka kula min da kanka, kuma banda kallon 'yan mata."
Dariya yayi yana sakinta yace "ni kuma me zan kalla a jikin wasu, bayan inada ku."
Murmushi tayi tana kallonshi harya d'aga mata hannu zai fita tace "kayi sauri ka dawo fa karka jima, kasan yau zan maka girki da kaina."
Cikin dariya yace "oho, kina so na dawo da wuri kenan saboda na tayaki aikin ko?"
Itama cikin dariyar tace "a'a a'a, aini zanyi da kaina, kai kawai zaka ci ne kuma kasha sannan kayi kwance kayi bacci."
D'an hararan wasa ya mata yace "bacci kuma, kema kinsan ai ina bala'in kewarki, tun ranar da kika d'and'ana min zumarki wacce ta haukatar dani kuma har yanzu ta kasa sakina, dan haka yau ki shirya sam ba zan d'aga miki qafa ba."
Dariya kawai take ba tace komai ba harya fita shima yana dariya, saida yaga Zuby zata fito da niyyar shan iska a tsakar gidan sannan ya tuna ma da wata hallita Zuby da kuma b'acin ran daya fito dashi daga d'akinta, yanda ta d'auke kai daga barin kallonshi yasa shima ya wuce bai kulata ba, haka ya wuce wajen abokanshi zuciyarshi fal da farin ciki.
************
Zaune tayi tasha kayan marmarin nan sosai, da haka ta koshi kafin ta d'auki littafi ta fara tilawar karatunta, ta jima sosai a wurin har lokacin sallah azahar, saida tayi sallah sannan ta kira Ruk'ayya ta d'ebo mata shinkafa, jik'ata tayi sannan Ruk'ayya tasa aka qarasa had'o mata kayan miya, lemon kankana ta fara had'awa tasa a fridge kafin ta shiga aikinta gadan gadan, duk da Ruk'ayya taso taimaka mata amma tace a'a ita za tayi da kanta, tana cikin yi Umar Faruk ya kirata, tana d'auka yace,
"Baby, ya kike?"
"Lafiya lau baby, ya aiki?"
"Alhamdulillah, ya zaman gida?"
"Ina jin dad'i, saboda ina rayuwa a gidanka."
'Waike, kullum maganganunki masu dad'i ne?"
"Aiki nane saka nishad'i, kuma aikin office d'ina ne samar maka da farin ciki mai d'orewa indai ina da rai da kuma lafiya."
"To na gode, kuma ina fata nima Allah ya bani ikon sakaki farin ciki na har abada, yanzu kinsan me nake so?"
"Ka fad'a kawai, ni kuma aikina ne cikawa."
Saida yayi murmushi kamar yana gabanta yace "fura nake so ki dama min, kisa Ruk'ayya ta kawo miki, amma nafi son ki dama da hannunki, akwai abokanaina da zamu zo tare dasu, ko zan iya samu?"
"Ka d'auka an gama ranka shi dad'e, zaka samu yanda kake so insha Allah."
"Kina ganin zaki iya damun fura?"
"Ban tab'a ba, amma yau zan fara saboda kai."
"To shikenan, Allah ya miki albarka."
"Ameen baby, na gode."
Da haka suka kashe wayar, aiki yayi aiki Khairat nata bada himma, da kanta ta tuk'a tuwon kuma tayi miyar agushi da nama mai had'e da kifi k'anana, saida ta kammala dasu a lokacin gida duk ya dau k'amshi tako ina kafin ta d'auki fura da nufin damawa, duk iya qoqarinta kasa damawa tayi saboda ta riga data gaji ga kuma wahala da rashin iyawa, wata dabara ce ta fad'o mata, a blender tasa ta markad'ata haka ma da ayaba tasa ta markada ta juye a cikin furar , zuma tasa a ciki da kuma dagen kwakwa (yaghourt mai kwakwa), fridge tasa sannan ta feshe d'aki da turare haka ma gado saida ta d'auki turarenta ta fesa mishi.
*Wannan wani had'in damun fura ne, ku jaraba ku gani*
Wani bala'en'en had'in kayan marmari ne da Mamie ta koya mata tayi tasa a fridge, da zaran yayi sanyi za tasha *emergency* kenan mai qara martaba da kima da qauna da soyayya da kuma nishad'i, hmmmm, yau fa Umar Faruk zaka gane kurenka, tana gamawa ta fad'a wanka.
Shiryawa tayi cikin riga da siket na shadda daka gani kasan taji kud'i, uwa uba kuma d'inkin, sarkar zinariya ta d'ora akai sannan ta cab'a kwalliya ta fitar hankali, sakin gashinta tayi ta shafeshi da mayuka da turaren kai tare da kashe d'aurin d'an kwali, dogayen takalmi ta saka saida ta tabbatar ta gama da komai sannan ta zauna jiran Umar Faruk, kamar ya san ta gama da komai kuwa sai gashi ya shigo,
"Assalama alai." bai qarasa ba saboda rumgumewar da Khairat ta masa.....
Yanda ta fad'a kan qirjinshi da k'arfi yasashi cewa "Khairat, zaki kayar dani fa wata rana."
Kallonshi tayi tace "sannu da zuwa."
Kasa amsawa yayi yana kallon kwanukan abincin data shirya akan table, ga k'amshin dake tashi daga d'akin gwanin dad'i, kallonta yayi yace "kinsha aiki ko?"
Kai ta girgiza masa alamar eh, kumatunta ya shafa yace "ayyah, sannu, bara na dawo daga masallaci na miki tausa."
Dariya tayi ta kamo hannunshi ta fara cire mishi kayan jikinshi, da haka kuma ta shigar dashi douche ta sakar masa ruwa ta fara wankeshi soso da sabulu, cikin towel ta sakashi ta fito dashi, bakin gado ta zaunar dashi ta shafeshi da mai, ta d'auko kayan da zata saka mishi aka fara kiran sallah, cikin gaggawa ta saka mishi ta fesheshi da turare sannan ta mishi bye bye ya tafi masallaci.
Zuby da taga fitarshi da qyar takai kanta d'aki tana tunani kala kala, wato itace ya raina shi yasa ma ko wanka bayayi a wannan lokacin in yana d'akinta, qwafa tayi tace "zaizo ya sameni, wallahi saiya gane bashi da wayo, kuma ina nan akan bakana, sai dai ka gaji ka bani hak'uri akan marin daka min amma badai ni ba."
_HAMAGIYA_π
Kamar yanda saba saida yayi sallah isha'i kafin ya shigo tare da Ishaq da abokinshi Abdul da kuma Noura, saida ya fara shiga wajen Baba sannan wajensu Mama, daga nan kuma d'akin Zuby ya nufa, yana shiga ya sameta zaune tana latsa wayarta, "assalama alaiki."
Shiru bata amsa ba kuma bata kalleshi ba, zaune yayi kusa da ita yace "ya gida?"
Ko kallonshi ba tayi ba tace "ba gashi nan ba kana cikinshi, koda wani abu ne kuma?"
Kallonta yayi yana jin kamar ya maketa da duka, amma saiya daure yace "Zubeida, yanzu kina ganin haka shine daidai, kina ganin ya kamata ace ana samun wannan matsalar a tsakaninmu, me yasa kike haka, idan wani abu na miki ki fad'a min? ni ba fad'uwa bane a gareni danna baki hak'uri."
A kauce ta kalleshi tace "au, wai baka ma san meka min ba, ka duba fa ka gani."
Ta fad'a tana nuna mishi kumcinta inda ya mara tana fad'in "ka duba ka gani, har yanzu akwai shatin hannunka a lokacin daka mareni saboda kawai na fad'i sunan daya dace da waccen matar taka , amma shine kake nuna babu abinda ya faru ma."
Tsaye ya mik'e yana fad'in "in dan wannan ne to kiyi hak'uri, yanzu ki tashi muje kuci abinci."
"Humm, kaje kaci ni ba zanci ba, dan ba zan iya cin abincinta ba, kai dai da aka saba barbad'a maka kana ci kaje kaci."
Wata yar sisiriyar dariya yayi yace "idan mutum yana abu to baya da yarda da kanshi, haka zai dinga ma kowa kallon zargi yana ganin shima yana abinda yake yi , amma duk da haka ki tashi muje, danke baki isa ki canzamin tsari ba."
Tunda ya fara magana gabanta ke fad'uwa, tunaninta ko yaga abinda take, basarwa tayi tace "na fad'a maka ba zanci ba kaje kai kaci."
"Zaki tashi ko saina takaki a wajen nan." tsawar daya mata ce tasa ta tashi tsaye bata shirya ba.
_Ni kam nace, Khairat ma taji wannan tsawar bare ke_π
Hijabi ta dauka tana gunguni tasa ta wuce shi kuma yana binta da harara, tsaye taga su Ishaq amma bata kulasu ba ta wuce kewayen Khairat tana turo baki gaba, bayanta yabi shima saida suka shiga ta tsaya shi kuma ya shiga da sallama, tashi tayi daga zaunen da take tana fad'in "sannu da zuwa."
Yana mata murmushi yace "sannu uwar gidana, ana hutawa."
Wani dad'i ne taji ya kasheta wanda yasa ta fara shafar qirjinshi tana murmushi, d'orawa yayi da "bak'inki sun iso."
Sakinshi tayi tace "to bara na fitar musu da kujerun nan, koya ka gani?"
"Ai yanda ki kayi shine daidai."
Kujera ta d'auka yace "a'a, bari wannan aikina ne." matsowa yayi kusan kunnenta yace "na sani kun kinmin ajiya anan."
Murmushi kawai tayi shi kuma ya fitar da kujerun ya aje sannan ya fita da qaramin tebur d'in shima, kwanukan abincin ta fito dasu a lokacin taga Zuby tsaye, da murmushi ta kalli Zuby tace "sannu 'yar uwa."
Saida ta harara sama da qasanta taja dogon tsaki da yasa Umar Faruk kallonta, banza sukayi da ita shi kuma ya shigo dasu Ishaq, hijabi Khairat ta d'auko abinda Umar Faruk baiyi tunani ba, sawa tayi sannan ta fito ta samesu zaune tace "sannunku da zuwa."
"Yawwa, sannu madame, ya gida?
"Lafiya lau, ya qoqari?"
"An gode Allah."
Umar faruk ne ya kalli Zuby saboda jin tak'i magana, amma abin takaici saita wurga mishi harara, d'auke kanshi yayi yana murmushin yak'e, muryar Khairat ce ta katse mishi shiru da fad'in "ya aiyuka?"
"Alhamdulillah, ya fama da ango?" cewar Abdul.
"Kallon wanda yayi maganar tayi sannan ta kalli Zuby dake hararansu tace "yar uwa kinji fa, wai fama, ba wani fama da muke dashi, shifa kamar jariri ne a hannunmu."
Tuntsirwa sukayi da dariya Ishaq ya d'ora da " ashe mutumin an shiga hannun mata."
D'an matsowa Khairat tayi zata zuba abincin sukaji muryar Zuby tace "aikin banza kawai." tana fad'a ta wuce ta koma inda ta fito.
Dakewa Umar Faruk yayi ya d'agawa Khairat hannu yace "a'a baby, barshi zan zuba, kije ki huta yau duk kibi kin gajiyar min da kanki."
D'agowa tayi tana kallonshi tana murmushi tace "da babu kaine a ciki sai nace na gaji, amma hidimarka ba zata tab'a gajiyar dani, domin kowace matsowa da zanyi wajen aikinka , to a cikin lada nake, haka ka fad'a min a cikin karatunmu, ka barni na qarasa samun ladata baby."
Sumbatar yatsunshi yayi ya jefa mata, kuma harga Allah yaji dad'in abinda ta fad'a shi yasa yayi hakan, murmushi tayi ta kanne masa ido d'aya sannan ta fara zuba abincin, jus d'in data had'a ta d'auko cikin wata juge mai kyau da cup d'inta ta zuba musu, haka ma furar data dama wacce tayi kyau ko a ido ta zuba musu kafin ta kalli Umar Faruk tace "aci lafiya."
"Mun gode, Allah ya miki albarka." cewar Umar Faruk.
Saida ta d'an sunkuya kamar zata duk'a har qasa sannan tace "ameen, na gode." sannan ta koma d'aki.
Tana shiga ta zauna kan doguwar kujera tana jin yanda suke surutu tare da yabawa girkin da suke ci, dad'i taji tare da sake qudurawa zata sake gogewa wajen girki, har saida suka gama suka tashi tafiya sannan Umar Faruk yace ta fito suyi sallama, fitowa tayi sukace "madame mun gode, Allah ya saka da alkairi, girki fa yayi ba dama, muna muku fatan alkairi Allah ya bar qauna."
"Ameen, mune da godiya ai da kuka zo inda muke."
Juyawa sukayi zasu fita Khairat ta kalli kan tebur d'in tace "wa ya bar makulli?"
Juyowa sukayi da sauri Noura ya d'auka yana fad'in "Lah, nawa ne."
Wani dundu Umar Faruk ya sakar masa a baya yana fad'in "munafiki, harda cewa kaika koshi ba zaka ci dayawa ba, shine harda mantuwa."
Fashewa sukayi da dariya suka fita, ita kuma d'aki ta koma ta cire kayan jikinta ta shiga douche ta watsa ruwa sama sama cikin sauri ta fito, rigar bacci ta fara d'aukowa ta saka sannan ta shafe jikinta da turare, yanzu ma sakin gashinta tayi ya bazu a bayanta, powder kad'ai ta shafa da lips mai k'amshi sannan ta d'auko had'in da tayi ta zauna harta shanye Umar Faruk bai shigo ba, bonbon (sweet) ta d'auka tasa a bakinta saiga Umariri an shigo...
17/08/2019 Γ 20:13 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
4⃣6⃣
Tsakiyar gado ta kwanta tana tsutsar alawar bakinta cikin wani irin salo, hannu ta mik'a masa alamar yazo, ganin haka yasa ya huri iska kafin ya juya ya fita, k'ofa ya rufe sannan ya shigo d'akin tare da rufe k'ofar, mab'allan rigarshi ya fara cirewa shima yana aika mata da wani kallon, kashe wuta yayi ya haura kan gadon ya mata runfa, bakinshi yakai ga nata ya fara tsutsa, alawar bakinta suka fara wasa da ita suna tsutsa a tare....
_Hmmmmmm, sai ana sayawa fa, inba haka ba yanzu sai kaji ana cewa kaza kaza_
Basu rintsa ba a tsawon dare, raya sunna kawai suke suna gajiyar da kawunansu, duk da Khairat takai maqura ta kuma gaji, amma haka ta daure ta kasa nuna mishi gajiyarta, tare sukayi wanka sukayi alwala suka fito, da kanshi yasa mata kayan sannan yasa nashi, sumbatar goshinta yayi yace "zan tafi masallaci, amma ba zan jima ba zan dawo."
A wahalce ta kalleshi tace "saika dawo."
"Ok." ya fad'a ya sake sumbatar goshinta ya d'ora da "Ina sonki alkairina."
****************
K1mar yanda ya fad'a bai jima ba, yana zuwa suka koma kan gado tana rik'e da littafi, harta fara bud'awa dansu d'ora karutunsu ya karb'a ya aje yana fad'in "kinga kawo, yau dai kawai mu hak'ura da karatun, so nake kiyi bacci sosai."
Janyota yayi jikinshi sosai itama kuma ta qara rumgumeshi qam a jikinta, babu jimawa bacci ya d'auketa, yana ganin tayi bacci ya zame jikinshi daga nata a hankali ya fita daga d'akin, d'akin Zuby ya shiga ya sameta zaune tana duba littafinta na Γ©cole, yanzun ma bata amsa sallamarshi ba, a tak'aice shima yace "kin tashi lafiya?"
A qwalla ta d'auki second ashirin kafin ta amsa da "lafiya."
Taushe zuciyarshi yayi da k'arfi yace "idan kin shirya kimin magana na saukeki."
Jin tayi shiru yasa ya kalleta, idonsu ne suka had'u tana wurga masa harara, ranshi ne yaji yakai qololuwa wajen b'aci, cikin zafin nama ya fizgo hannunta tare da mannata a bango ya taushe, k'ashin dake wuyan hannunta ya matse sosai yana fad'in "wa kike harara, dawa kike nace?"
Tuni idonta suka kawo ruwa, kasa magana tayi hakan yasashi sanya yatsunshi biyu ya janye rigarta ya kaisu ga cikinta ya tsamuka, wata qara ta saki tare da fashewa da kuka lokaci d'aya, "ni kike harara, zaki fad'a min ko saina cire fatarki?"
Cikin fashewa da kuka tace "dan Allah kayi hak'uri yah Umar, wallahi ba zan sake ba, akwai zafi wallahi dan Allah ka sakeni."
Sakinta yayi yana hararanta yace "na sake gani wallahi ranki zaiyi mugun b'aci , tunda na lura ba zaman lafiya kike nema dani ba, kuma na fad'a miki kimin magana kafin ki tafi."
Fita yayi ya barta a tsaye tana kuka, saida ta gaji dan kanta sannan ta d'auki wayarta ta dannawa Mama kira, saida tayi kusan kira biyar ana shida Mama ta d'auka dan tana bacci ita, cikin muryar kuka tace "Mama wallahi yah Umar baya sona yanzu, waccen karuwar duk ta d'auke mishi hankali, ni Mama kawai ki raba auren nan wallahi ba zan iya ba, ni na gaji da wannan bak'in cikin."
"Me kuma ya faru yanzu da safiyar nan?" cewar Mama cikin magagin bacci.
"Mama yanzu haka fa saida ya sani kuka, ni kawai nace miki na gani kisa ya sakeni kawai."
"Kinga, kinsan me zai faru yanzu?"
"A'a." cewar Zub.
"To an jima idan kika tashi daga Γ©cole, ki biyo ta gidana muje tare dake wajen malam saiki fad'a mishi komai da bakinki, kinji ko."
Tsagaita kukan tayi tace "amma fa Mama bana da kud'i ni, ya zanyi nazo nan."
"Karki damu kizo kedai, ni zan biya komai."
Cikin farin ciki tace "to Mama, sai nazo."
"Yawwa, ki daina kuka kinji, ki rabu dashi da 'yar iskar yarinyar, duk zanyi maganinsu wallahi, kuma wannan karan harda uwayen da yan uwanshi duk zan had'a."
"To Mama na gode, sai nazo d'in."
Da haka sukayi sallama ta fara shirin tafiya ecole cikin uniforme d'inta, tana gamawa ta fito ko abinda zata ci bata tsaya had'awa ba ta fito, Ruk'ayya ta samu tana wanke wanke tace "Ruk'ayya, kije ki fad'awa yah Umar na shirya."
"To." Ruk'ayya ta fad'a ta wuce, Mama dake d'aki zaune tana jinsu tana mamakin yanda Zuby ko sau d'aya bata tab'a taka qafarta ba ta shiga d'akin da sunan tazo gaisheta, sai dai idan taje suna hira da Ruk'ayya, bare kuma sauran iyayen, tana zaunawa tsakar gida dasu dai suyi hira amma babu wanda take shiga ta gaisheshi.
Ruk'ayya kam tsaye take a k'ofar d'akin tana sallama, jin shiru yasa ta d'an had'a da bubbuga k'ofar, a tare suka motsa saishi ya sake mayar da kanta akan pillow yace "shiiii , koma ki kwanta baby, zan duba na gani."
Sake gyara kwanciya tayi shi kuma ya bud'e k'ofar, cike da ladabi tace "ina kwana yah Umar."
"Lafiya lau Ruk'ayya, yadai?"
"Zuby ce tace na maka magana."
"Ok, kice ina zuwa."
"To." ta fada ta sunkuya ta tattare kayan da Khairat tayi aiki dasu jiya danta wanke sannan ta juya ta fita.
Tana tsaye saiga Umar Faruk ya fito da doguwar riga da makullin mota a hannu, ganin ya nufi hanyar waje yasa tabi bayanshi, saida ya shiga ya tayar da motar sannan ta shiga suka d'auki hanya, babu mai magana har sukayi nisa, Umar Faruk ne yace "ya karatun naki?"
Cikin turo baki tace "lafiya lau."
"Yayi kyau, babu wani abu da yake d'aure miki kai kuma?"
"Babu."
Bai sake mata magana ba harya sauketa, suna tsayawa tayi wuf ta fita daga motar ko kallonshi, ita ala dole ranta a b'ace yake, girgiza kai yayi kawai ya wucewarshi, restaurant d'in da Khairat ta tab'a sashi amsowa Mama abinci ya biya, oder abinci ya musu sannan ya wuce gidan yana tunano daren jiya, murmushi kawai yake saki yana jin farin ciki har zuciyarshi, tabbas da yana da arziki daya mallakawa Khairat duk abinda yake dashi kyauta, dan abinda yaji jiya yafi k'arfin tunaninshi, abune daya kusan zautar dashi ya kusa sashi haukacewa, baisan dame zai iya misalta dad'i da farin cikin daya ji ba, amma dai yasan inhar haka zasu kasance, to daf yake daya haukace ko zuciyarshi ta buga saboda farin ciki, da haka ya isa gida kai tsaye d'akinta ya wuce, cak yaja ya tsaya saboda ganin Khairat wacce koda taga ya fita itama ta tashi da gaggawa ta shiga wanka, cikin riga da wando tayi sauk'akk'an kwalliya tana suyar qwai.
Cikin k'agaggen fara'a ta rumgumeshi cikin taushin murya tace "sannu da zuwa."
"Yawwa sannu, amma me yasa zaki wahalar min da kanki, kinga abin kari fa na siyo."
Kasa magana tayi sai langab'ewa da take kamar wacce tasha wani abu, kallon fuskarta yayi yana dariyar mugunta yace "yadai baby na ganki sukuku dake haka?"
Sakinshi tayi ta koma kujerarta ta zauna tana juya qwan tana fad'in "ba komai, kawai dai bacci ne bai isheni ba."
Karb'ar cokalin hannunta yayi ya durk'usa yana fad'in "kije ki kwanta to zan qarasa."
A hankali tace "da gaske?"
"Eh, na hutar dake da abinda ke cikinki."
Tashi tayi tana hamma tana murzar ido tace "babu komai a cikina sai hanji."
Binta yayi da kallo harta shiga d'aki, akan doguwar kujera ta kwanta bacci harya sake d'aukarta sai gashi ya shigo ya gama had'a komai, had'awa yayi da wanda ya siyo sannan ya tasheta suka ci, ganin lokaci ya tafi yasa Khairat nuna mishi agogo da hannu, kallo yayi ya kalleta yace "me?"
"Lokaci ya tafi, ka tashi ka shirya karka makara fa."
Cike da zolaya yace "to saime, naga nine mijin Hajia Khairat, babu wanda zai tuhumeni, kuma ma ai ina gida tare ina kula da ita."
"Kenan yau ba zaka fita ba?" ta tambaya.
Cike da kwonkwonto yace "umm , ina tunanin kamar haka dai."
Duka ta kai masa a qirji tana fad'in "tashi ni babu ruwana, abinda ma na kusa siyar da compagnie."
Kallonta yayi yace" saboda me?"
Saida ta dauke ido daga kallonshi tace "ina so ne na zauna tare dakai nayi bautar aure."
"Ke." ya fad'a da k'arfi tare da d'orawa da "rufa min asiri, kina so ki sani a bakin duniya ne? to bana ciki nidai."
Murmushi kawai tayi tace "dan Allah ka tashi ka shirya kazo ka tafi."
"Na makara fa, kina so naje manager ya hukuntani ne?"
"Aiko yana hukunta kowa banda mijin Hajia Khairat, koya kace?"
Da murmushi yace "kuma fa hakane tawa, ban biyar." ya fad'a tare da bata hannu, hannun ta bashi itama suka bige kafin ya mik'e yana fad'in "ina da sa'a fa dana zama mijin Hajia."
Da murmushi kawai ta bishi tana sake kishingid'a akan kujerar, sauke idonta tayi akan gado tana tunano daren jiya, ajiyar zuciya ta sauke tana mai jin farin ciki da Allah ya bata miji kamar Umar Faruk, mijin da zai iya wayar gari yana d'ebe maka kewa ba tare da gajiya ba, ga salo masu rikita mutum bugu da qari baya da qyanqyami, zai iya kai bakinshi ko ina na mace, da tunanin nan Umar Faruk ya fito ya sameta, tashi tayi duk da a gajiye take haka ta tayashi shiryawa cikin bleue riga da bak'in wando, kayanta ta nufa ta bud'a sai gata da wasu kwali a hannu guda uku, ajewa tayi akan gado ta bud'a babban, wasu shegun takalmi ne suka bayyana qafa ciki masu masifar kyau, maganar tsada ma an ajeshi gefe, da kanta ta duk'a har qasa bayan ta zaunar dashi akan gado ta fara saka mishi takalmin, da mamaki yake kallonta yace "wannan fa?"
"Tsarabarka ce, ko ka d'auka zan iya bawa kowa tsaraba banda kai?"
Duk tayi maganar ne tana saka mishi takalmin, da kai kawai ya mata alamar a'a, tana gam saka mishi ta dago ta d'auki d'aya kwalin ta bud'e, wata tanfatsetsiyar agogo ce ta fito itama, nan ta makala mishi kafin ta d'auki kwalin d'aya ta bashi a hannunshi, kallo yake da matuk'ar mamaki kafin yace "Khairat, ki rik'e wannan ba zan iya karb'arta ba."
Rai bace ta kalleshi tace "me yasa kuke min haka, gani kuke ni macece bai kamata ina haka ba, ko kuma kuna tunanin wata rana zan goranta muku ne kana mijina na baka abu kak'i amsa wa kake so nama? nifa na d'auka ni dakai d'aya ne, amma shine zaka nuna min ba haka bane, haka qaninka shima na mishi kyauta amma yak'i karb'a, shikenan kaima idan bakya so kaje ka jefa a cikin shara, amma ni na riga na siyo ba kuma zan tab'a amsarta ba."
Ajiyar zuciya ya sauke ya sake kallon kwalin mai d'auke da photon tsaleliyar waya qirar *IPhone XMAX*, tsaye ya mik'e ya rumgumeta yace "shikenan to daina fushin."
Tana cikin qirjinshi tace "ka karb'a?"
Saida ya qara matseta yace "dole na ai, da kai da kaya ai duk mallakar wuya ne."
Duka ta kai masa suka fashe da dariya tana fad'in "hamago, nice ya kamata nace haka ba kai ba."
Cikin kunnenta ya rad'a mata " ai Umar Faruk mallakar Khairat ne, sai yanda taso za tayi dashi, kinga kuwa ai dani da hannayena na karb'ar kyauta daga gareki duk naki ne."
Dariya ta sake yi tace "na ganoka fa, kana nufin dani da abinda na mallaka duka naka ne, shi yasa ma ka karb'a."
Kumatunta yaja yace "mai basira kenan."
Da qyar suka rabu ya tafi wajen aiki, ita kuma ta koma ta kwanta bacci danya tabbatar mata ba zai dawo da rana ba, aikinshi yake hankali kwance cike da farin ciki da nutsuwa, bayan sallah azahar saiga wani babban kira a wayarshi, ya zai gani inba Papa ba, da girmamawa ya d'auka suka gaisa, nan Papa yace yana son ganinshi inba damuwa, nan ya aje komai dake gabanshi ya tafi kiran mai gida kuma suruki.
*Bayan yaje gidan* Papa yake sanar dashi wani compagnie a qasar *Las vegas* dake *America* suna neman zakakurin matashin mai aikin zane irinshi, dan haka in yana son aiki toya shirya zuwa qarar Las vegas domin tattaunawa dasu, kuma tattaunawar ba zata wuce gobe ba, dan haka idan ya amince compagnie ya d'auki nauyin tafiyarshi da dawowarshi, wannan shine sharad'in farko, Umar Faruk ya d'auka kawai alfarma ce Papa ya mishi kasancewarshi surukinshi, hakan yasa ya amince kuma ya kama hanyar gida cike da zumud'in fad'awa Khairat abinda ake ciki, sai dai baisan ita tayi silar samun wannan aikin nashi ba.
Su Mama ya samu a tsakar gidan dukansu suna d'an tab'a hira sama sama, saida ya zauna ya fad'a musu komai dake faruwa, mahaifiyarshi dai kam tayi farin ciki, amma banda sauran iyayen nasu da suke ganin ci gabanshi na qara kusantoshi, addu'a Mama ta mishi kafin ya tashi ya nufi d'akin Khairat yana sake kallon k'ofar Zuby dake rufe, yana tunani a ranshi har yanzu bata dawo ba kenan, qwafa yayi a cikin ranshi kafi ya shiga d'akin da sallama, littafi ne a hannunta tana karatu tana ganinshi ta taso ta tarbeshi, "albishirinki?"
"Goro." ta fad'a a harshen zarma kamar yanda shima yayi.
A harshen zarma dai fad'a mata komai, rashin mamaki da tayi yasa yayi zargin wani abu, kallonta yayi yace "alkairina, kodai aikinki ne."
Zaunar dashi tayi tana kallonshi tace "kayi hak'uri Umar Faruk, ba lallai ina so na canza qaddarar ubangiji a kanka bane, amma ina so naga kaji dad'i kaima, ba dole sai kayi aiki da compagnien ba harna tsawon lokaci, amma idan ka samu wani abu mai tsoka kaima zaka iya tsayawa da qafafunka, wannan shine burina a kanka, ina so naga ka tsaya da qafarka saboda kana basira da ilimin daka wuce ka zauna qarqashin wani, amma ka yafe min idan nayi ba daidai ba."
"Shawara mai kyau, hakan kuma zai bani damar kin rattab'a hannu akan aiki dasu na dindindin."
"Hakane." ta fad'a tana murmushi.
Rumgumeta yayi yace "na gode Khairat." a zuciyarshi kuma cewa yayi " da farko na d'auka *Jihadi* nayi na aureki , amma yanzu komai na fitowa fili cewar, kece silar arzik'ina a duniya, kuma kece farin ciki da kwanciyar hankalina."
D'orawa da "ki shirya, dan tare zamu tafi dake ki nuna min gari."
Cikin dariya ta kalleshi tace "shirme."
"Allah kuwa nake fad'a miki." ya fad'a yana dariya.
_Wannan karan naga uban daya isa ya hana tafiyar nan._
*****************
Koda Zuby taje gida basu tsaya komai ba suka wuce wajen malam, nan Zuby ta fad'a mishi abinda ke faruwa, tambayarta yayi me take so a mata? cewa tayi asa Umar Faruk ya tsaneta harya saketa ma, nan yace msu "aikinku mai sauki ne, kuma zai yiwu, amma harsai kun samo wani abu daya zama na ita Khairat d'in ne, bi ma'ana abinda take sawa a jikinta koma menene, dashi za'a had'a laqanin da zai tsaneta, zaku iya?"
Mama ce ta karb'e da "zamu iya mana malam, aiba wuyane da aikin ba."
"A shikenan, kuyi qoqari ku kawo cikin kwana biyu ko uku, dan a gaggauta yin komai."
"To malam, kar kaji komai za'a kawo."
Da haka suka baro wajen malam Zuby tayi gida Mama ma tayi hanyar gida, da tunanin yanda za ayi ta samu abun Khairat taje gida, ganin motar Umar Faruk ba qaramin tsinkewa 'yan cikinta sukayi ba, da qyar ta shiga gidan tana d'an sunnewa, ganin baya tsakar gidan yasa ta fara gaggawar bud'a d'akinta ba tare data kula da mutanen tsakar gidan ba, suma babu wanda ya mata magana dan sunga abinta iskanci ne da raini, tana shiga tayi saurin cire kayanta tayi zaune gabanta na fad'uwa tana tunanin hukuncin da zai mata.
Ana sallah la'asar ya fito, koda d'akin bud'e bai kula da tsiyarta ba yayi alwala ya wuce masallaci, bai kuma dawo ba sai bayan sallah isha'i, lokacin Khairat ta sake daddaga abinci mai rai da lafiya, saida ta zubo min a babban kula tace na kawawa _Team Khairat_ amma na taho akan hanya nayi tuntube tuwon ya zube, daga nan na zaune na qarasa cinye wanda yayi saura tare da kazar dake samaπ kunsan dai akwai aminci tsakaninmu da kaza, yau ma kamar jiya sunci sunsha kuma sunyi farin ciki tare da raya darensu, yayin da Zuby haushi kamar zai kasheta, dan da yaje mata saida safe bai mata wata maganar kirki ba, hakan kuma ya qara b'ata mata rai, amma dai kuma ba zata iya bayar da hak'uri ba a tunaninta, shi kuma a nashi b'angaren yana ganin saita bashi hak'uri ta kuma gane kurenta sannan.
_Me kuka ce mutanena?_
πππ
17/08/2019 Γ 20:13 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
4⃣7⃣
Kamar kullum gaba d'aya sun taru a d'akin Baba inda yake musu nasiha akan kyautatawa, saida aka gama kamar kullum ana shirin tashi Umar Faruk yayi gyaran murya yace "am, ina da magana, dan Allah ku zauna."
Gyara zama kowa yayi Baba yace "muna jinka Umar Faruk."
"Dama akan maganar aikin dana samu ne, acan compagnie suna buk'atar naje gobe domin tattaunawa dani, kamar yanda na fad'a muku wannan aikin Khairat ce silar samar minshi, kuma ni babu inda na tab'a zuwa na qasar waje, kasancewarta wacce tasan wajen yasa nake tunanin tafiya tare da ita, amma shawara ce bansan ku me kuka gani ba?"
Baba ne yace "Umar Faruk, kaima fa yanzu magidanci ne, ba komai bane zaka nemi shawararmu akai, indai har kana ganin hakan ba matsala kuma shine daidai, ai saimu muku fatan alkairi."
"Na gode Baba." ya fad'a kafin ya d'ora da "dama wannan ce maganar, na gode."
Tashi kowa yayi zai fita Zuby kam ta kasa tashi, ganin Umar Faruk zai fita yasa Zuby kallon Baba tace "ina da magana nima."
Juyowa Umar Faruk yayi ya kalleta, kallonshi tayi itama tace "ka dawo ka zauna."
Zaunawa yayi Mama ma zata fice Zuby tace "Mama kema ki zauna."
Saida kowa ya fita Baba ya kalli Zuby yace "ina jinki Zubeida, ina fatan dai ba wata matsala bace?"
Tana kallon Umar Faruk tace "gaskiya ni ba'a min adalci ba, na fahimci yana son yin tafiya da ita, to ba komai su tafi, amma kafin su tafi ya fad'a min Γ wane matsayi nake, dan wallahi ba zan iya zaman gadi ba a gidan nan haka kawai."
Da mamaki duka suke kallonta kafin Umar Faruk yace "Zubeida wane irin rashin adalci nake miki?"
Shiru tayi harya sake maimaitawa da "Zubeida fad'a min, mena miki na rashin adalci."
Cikin turo baki tace "ai duk mai ido yasan baka adalci a tsakaninmu, domin kuwa ko ranar aikina ne idan ka shiga d'akinta saika jima kafin ka fito, kuma inhar ka shiga d'akinta to sai dai ka fito da fara'a da murmushi a fuskarka, sab'anin d'akina idan ka shigo sai kayi duk abinda za kayi ka b'ata min ran sannan kaima ka fito cikin b'acin rai, bugu da qari ita cikin kayan abincin su Mama take diba tana aiki dasu, ni kuma ka siyo min wanda basu kai basu kawo ba, dad'in dad'awa kuma duk da nasan ita yar mai kud'i ce, amma na tabbata daga cikin suturun da take sakawa akwai wanda kai ka matasu na lefenta, yah Umar idan nace zan dinga zayyano maka rashin adalcin da kake ba zai k'idayu ba."
Murmushin takaici yayi na gefen labb'a, dan yaso a kamashi da laifi danya b'ata hak'uri, amma kash ta kasa bayar da hujjar da zai d'auki laifin a kanshi, saida ya qara gyara zamanshi yace "da kin fad'i wani abu daban ba wannan ba, amma tunda haka ki kace bara na fad'a miki abinda yayi daidai da abinda kika fad'a."
"Da farko kince idan na shiga d'akin Khairat nakan jima ban fito ba kuma ina fitowa da fara'a, ba zan iya ce miki komai ba, amma ina baki shawara ki samu wata qawarki da kika yarda da ita ki tambayeta me yake janyo hakan, na tabbata zata fad'a miki gaskiya, na biyu kuma maganar abinci, to kiji in fad'a miki, wannan kayan abincin da kika gani wallahi ko Baba baya da iko akansu kamar yanda Khairat take da iko akansu, kinsan me yasa? saboda itace ta siyesu, kuma bata tab'a kulasu ba sai ranar dake kika kawo shawarar kowace ta dinga girki da kanta, Zubeida idan akwai wanda akawa rashin adalci to Khairat ce, domin kuwa a lokacin dana siyo miki kayan abincin nan ita ban siyo mata ba, sannan na d'auki kud'i na qara muki dasu, duk da haka sisin kwabo ban bata ba dan nasan ba zata karb'a ba, tunda ta shigo gidan nan zan iya fad'a miki adadin da taci abincin gidan nan, kinga kenan ita akawa rashin adalci, na uku kuma kince sutura, to kijini da kyau Zubeida, ni banwa Khairat lefe ba kece nayiwa lefe, tunda nake da ita zani d'aya na atamfa bai shiga tsakani na da ita ba, kin ganni a matsayin mijin Khairat? wallahi har yanzu idan banda wurin kwanciya da ruwan gidan nan, banga wani abu da Khairat ke anfani dashi ba wanda zan iya cewa nawa ne, sannan atamfar da Khairat ke sawa a jikinta ma kad'ai tafi k'arfin arzik'ina, bare kuma kudin d'inkinta har azo ga shadda ko less, maganar sarka da d'an kunnai ma mu barta, har yanzu babu tsaiyar dana tsinanawa baiwar Allah nan a matsayina na mijinta, hasali ma nine ke qaruwa da ita tako ina, a yanzun burina bai wuce na samu hanyar da zan saka mata da alkairin data min ba, dan duk wanda zai bawa ahalinka abinda zasu ci ya kuma dinga kyautata musu, to tabbas shi masoyinka ne na gaskiya, musamman ita da bata damu da dukiyarta ba, ita dai burinta kawai ta kyautatawa wanda yake tare da ita, ba tayi dan gobe ta fad'a tayi maka, sannan idan tayi ba'a karb'a ba tana jin zafi, domin kuwa ita alheri a cikin jininta yake kamar yanda ma'anar sunanta yake, dan haka ina baki shawara Zubeida, ki cire komai a ranki ki rumgumi yer uwarki, wallahi babu komai a zuciyarta a game dake, ko sau d'aya bata tab'a nuna min kishinta a kanki ba, ina fatan za kiyi anfani da shawarata, kuma ki yafe min idan na fad'i abinda ya b'ata miki rai."
Mik'ewa yayi da fad'in "saida safenku." danshi baiga abinda zai sashi b'ata lokacinshi ba akan banzan shirmen Zuby.
Mama da Baba ma sun gamsu da abinda ya fad'a dan haka sukayi shiru harta tashi ta koma d'akinta, yana shiga d'aki Khairat ya sameta zauna tana tunani akan karatun da Baba ya musu, dan a cikin kyautatawar daya musu magana akai, akwai kyautatawa iyaye, ita kuma tana tunanin yanda ta zauna da nata iyayen, ji tayi tana so ta basu hak'uri akan yanda ta mu'mulancesu a baya, zaune yayi kusanta ya janyota jikinshi yana fad'in "yadai, meya faru."
"Ba komai." ta fad'a tana shafa jikinshi.
"Kin tabbata?"
"Um."
Dago kanta yayi ya kalli fuskarta, turo baki yayi gaba kamar yaro ya langab'e kai yace " ban yarda ba gaskiya, akwai wanda ya tab'a min baby, fad'a min meya faru.?
Qara langab'ewa tayi tace " ba komai fa."
"To indai hakane kiyi dariya na gani."
D'an murmushin yaqe tayi tace "nifa bacci nake ji."
Tana fad'a ta kwanta tare da jan zanin rufa, Umar Faruk a ranshi cewa yayi "baiwar Allah, ko tana tunanin abinda ya faru ne wanda ya tsayar dani? koma dai meye dole nima na saki farin ciki kamar yanda kema kike sakani farin ciki, wannan itace damar da nake da wajen saka miki da alkairi."
Hayeta yayi ya fara mata cakulkuli yana fad'in "ba zan iya komai ba sai naga dariyarki."
Ai kuwa dariya ta fara qyalqyalawa daga haka kuma suka lula duniyarsu ta maji dad'i......
**************
Tunda asuba koda Khairat tayi sallah ta fara shirya musu kayansu tare da shirya kanta , Umar Faruk kuma saida ya shiga d'akunan iyayensu suka gaisa tare da d'akin Zuby, haka yayi sallama har sau uku amma ko qala ba tace ba, sannan ya qara da "kin tashi lafiya?"
Nanma shiru ba amsa, fita kawai yayi daga d'akin, yana zuwa shima shiryawa yayi a lokacin kuma Khairat ta gama abin karyawa, suna gama break suka fito cikin shirinsu, duka iyayen nasu na zaune dan haka suka qarasa suka musu sallama, sun tashi kenan zasu wuce Zuby ta fito tana rufe d'aki itama zata wuce Γ©cole, ganin ko kallon kowa ba tayi ba ta kama hanyar fita yasa Umar Faruk binta da sauri, a soro ya sameta ya rik'e yana fad'in "ki jira mu saukeki."
Fizge hannunta tayi tace "rabu dani bana so."
Ganin Khairat ta taho kuma ko Khairat ba zaiso ta rainashi ba yasa ya wurga mata wata harara, shiru tayi tana sauke numfashi ,wucewa yayi suka bi bayanshi amma abin mamaki, da hanzari Zuby ta zagaya ta zauna a gidan gaba, kallonta yayi zaiyi magana kawai yaga Khairat ta bud'a mazauninshi ta zauna, saida ta daidaita zamanta sannan ta fizgo makullin hannunshi fuskarta a had'e itama ba alamar wasa, jin tayiwa motar key yasa ya bud'a gidan baya ya zauna ya rufe yana fad'in "Allah gani gareka, ashe dama haka mata biyu suke, da zaran sun had'u sai an caza maka qwaqwalwa."
Gyara madubi Khairat tayi ta kalleshi tace "baby ka shirya?"
Gintse dariyarshi yayi ya sunne kai qasa, Zuby kuma qoqarin bud'ewa ta farayi danta fita, Khairat na ganin haka ta fizgi motar da iya k'arfinta a zuciyarta tana fad'in "uban daya kawoki gidan gaba."
Titi suka hau Umar Faruk na kallon kowace daga baya, Khairat na tuk'i hankali kwance Zuby kuma tayi tsaki yafi dubu , amma jin sun qyaleta yasa tace "aikin banza, barewa ai ba tayi gudu ba d'anta yayi rarrafe, an gada wajen uba dole a nuna hali."
Ba tare data kalleta ba tace "na fad'a miki ki daina saka iyaye a maganar data shafemu , bai zama lallai abinda zai fito a bakina ya miki dad'i ba, amma kika b'ata min rai yanzun nan saina had'a motar nan da bango."
Sai lokacin ta kalleta duk da tana tuki tace "bana tsoron mutuwa, dan Mama tace ni yar aljanna ce, bugu da qari ina tare da babyna, zanyi farin ciki mu mutu tare, idan kin shirya biyarmu to."
"To an fad'a miki ina tsoron mutuwa ne? ai gwara na mutu ma da zama dake a matsayin kishiya wallahi, inkin fasa hadamu da bango bakya tsoron Allah daya halicceki."
"Kin shirya mutuwa kenan?" cewar Khairat.
"Shege ka fasa, d'an halak sai yanka."
Da sauri Khairat ta kalleta tace "a'a malama, ki daina sako mana wannan kalmar anan, ni dai 'yar halak ce."
"Kenan nice shegiyar?"
"To ai ba kama garesu ba, kuma ba'a rubuta a goshinki ba bare na karanta, kinga kenan ba zan iya sani ba."
"In haka kike tunani, toki d'auka ni yar babanki ce."
Umar Faruk ne yayi saurin cewa "ya isa haka to, karna sake jin bakinku, inba haka ba rai zai b'ace."
Khairat kuma gani tayi aita kaita qasa, dan haka tace "ina aiki na masu hankali, amma idan haukana ya motsa to akwai matsala, ki kiyaye bakinki kafin kiji abinda zai iya tarwatsa miki lissafi."
Tsaki Zuby tayi ta rumgume hannaye har suka isa ecole d'insu, saida ta juya ta kalli Umar Faruk sannan ta kalli Khairat tace "na gode Allah, ni ba 'yar d'an giya bace."
Tana fad'a ta fita ta bar motar, Khairat binta tayi da kallo lokaci d'aya hawaye suka soma zubo mata, fitowa Umar Faruk yayi ya bud'e inda take zaune, saida ya kama hannunta ya fito da ita sannan ta zagaya ta zauna inda Zuby ta tashi, saida suka fara tafiya jin tana shashek'ar kuka yasa ya fara tausarta da kalamai masu sanyi, ba tayi shiru ba har saida taga yayi parking a k'ofar gidansu sannan, zata fita ya rik'e hannunta suka kalli juna, d'aure fuska yayi yace,
"Ki maye fara'a a gurbin d'aure fuskar nan."
Cikin muryar kuka tace "amma fa kaji abinda yarinyar nan ta fad'a min."
"Naji, kuma kamar yanda ki kace kina da hankali, to ina so ki nuna min ke mai ilimi ce, kuma naji dad'i da kika qyaleta."
Share fuskarta tayi kafin suka fita suka nufi cikin gidan, sun samu Papa da Mamie suna hira a falo, da gudu Khairat ta fad'a jikin Papa tana dariya, saida suka gama murnar ganin juna sannan Papa yace "shalelen Papa, ashe har yanzu baki girma ba? na dauka kin girmi hakan yanzu."
Turo baki tayi gaba tace "Papa wane irin girma kuma, nifa kamar autace a gareku, babu wani gabana kuma babu bayana, to in banyi ba wa zai muku."
Mamie ce ta juyo da fuskarta ta kama kumatunta tana fad'in "banga laifinka ba, kiyi yanda kike so shalelen Papanta."
Murmushi tayi tace "Mamie ina kwana?"
"Lafiya lau Khairat, ina mai gidan naki?"
Kallon kofar da suka shigo tayi danta nuna musu Umar Faruk, ganinshi tayi durk'ushe yana gaishe da Papa, ajiyar zuciya tayi ta tashi ta kama Umar Faruk ta zaunar dashi kan kujerar da dukansu suke tana fad'in "kaifa yanzu d'an gidane, bamu da wani dangi daya fika, yanzu kaine babban d'ansu bani ba, ka d'auka na baro Mama da Babana can gidan, yanzu kuma nazo gidanku ne kaima."
Murmushi Umar Faruk yayi yana jin maganganunta na sake dawo masa a qwaqwalwa, Mamie ce ta dora da "gaskiya ne kam, ya kamata ka saki jikinka, muma iyayenka ne."
Papa ne yace "wai harka shirya kenan?"
Cike da ladabi yace "eh Alhaji."
Khairat ce ta katsesu da fad'in "Alhaji kuma, Baban nawa? ni wallahi ban yarda ba, kace Papa kaima, inba haka ba, tam."
Papa ne yace "dan Allah ki rabu dashi."
Maida kallonshi yayi ga Umar Faruk yace "to amma kuma na ganku tare, kana nufin da ita zaka je?"
Nanma cikin ladabi yace "eh, saboda bansan garin ba shi yasa nace muje tare."
"To, da yake tana da biza ba matsala, amma ai ba jimawa zakuyi ba."
Kwance Khairat tayi akan kafad'ar Papa tace "Papa ba zamu wuce kwana biyu ba."
"To Allah yasa."
Papa ne ya d'ora da "ya kamata ku wuce lokaci na tafiya."
Kukan shagwab'a Khairat tasa tana fad'in "Papa korarmu kake, shikenan idan naje ma ba zan dawo ba, zan zauna acan ni da baby."
Saida Papa ya kama kumatunta yace "da kuwa kin ganmu nida mahaifiyarki, dan kinsan ba zamu iya jurar zama nesa dake ba."
Gyara zama Khairat tayi dama a tsakiyarsu take ta kamo hannayensu ta had'e wuri d'aya tana kallonsu tace "Papa, Mamie, a cikin karatun dana koya a gidansu Faruk, na fahimci girma da matsayin iyaye, iyayena ku yafe min, domin a jiya ne na gane kuskure na, nasan ban saku farin ciki ba, kuma ban zama 'ya ta gari a gareku ba, dan haka ina neman afuwarku tare dasa albarkarku, kuma nayi alk'awari insha Allah zan zama d'iya mai tarbiya a gareku, ba zan sake muku rashin kunya ba, dan Allah ku yafe min iyayena." ta qarashe da fashewa da kuka.
Kusan a tare suka rumgumota a jikinsu, kuka suke sosai yayin da Mamie take kuka tana fad'in "Khairat mun yafe miki, kuma inda mai laifi, to mune iyayenki, munja miki abubuwa da dama a rayuwarki, muma muna neman afuwarki , dan ko kad'an bamu baki tarbiyar data dace ba."
"A'a Mamie, kunyi iya qoqarinku, nice kawai ban maida hankali ba, ku yafe min dan Allah."
Papa ne yasa hannu ya share mata hawaye yace "Khairat ba laifinki bane, komai nine silarshi, nine silar faruwar komai, inada damar da zan iya gyara halina tun lokacin da nake da quruciyata , amma na kasa gyarawa harna auri mahaifiyarki bada son ranta ba, amma kuma duk da haka ban gyara ba, ganin an haifa min 'ya mace ma baisa nayi tunanin komai ba na saduda , a haka naci gaba da shek'e ayata , harsai ranar da aka ci zarafin sannan na gane kurakuraina dana tafka wanda ba zasu tab'a gyaruwa har abada, nasan a baya wasu suna kiranki da 'yar d'an giya ko kuma shugaba marar adalci, wasu ma suna kiranki da 'yar mazinaci , amma ki sani wannan sunayen dane, yanzu na daina komai, siyaya ma ajeta zanyi da yardar Allah."
Da qyar Umar Faruk ya rarrashesu sannan akasa driver ya kaisu aireport ya dawo da motar, ba b'ata lokaci jirginsu ya tashi da ikon Allah kuma suka sauka da izinin ubangiji.....
Mota aka turo ta d'aukesu, kai tsaye babban hotel aka saukesu, wanka suka shiga koda suka fito an kawo musu abinci, suna gama ci kuma aka d'aukesu izuwa compagnie da suka zo dominshi, babban compagnie ne mai dubbanin ma'aikata, d'aki na musamman aka shiga dasu domin tattaunawar, manyan mutane ne guda biyu suke zaune suna zaman jiran zuwansu , suna ganinsu suka mik'e saboda girmamawa tare da bawa Umar Faruk hannu, suna gaisawa d'aya dattijon ya bawa Khairat hannu dansu ba wani abu bane a wajensu, saboda ne yasa Khairat mik'a mishi hannu itama da nufin su gaisa, amma jan kallon da Umar Faruk ya mata yasa yan cikinta murd'awa, tabbas Umar Faruk nada kwarjini kuma tana shakkarshi, da sauri ta janye hannunta a daidai lokacin da mutumin ke neman rik'e hannunta, kallon Umar Faruk sukayi kawai suka basar, da hannu suka nuna musu su zauna, nan suka zauna suka tattauna akan abinda ya kawosu, duk da ya fad'a musu ba zaiyi aiki dasu ba na dindindin amma sun amince, dansu burinsu kawai shima su mori basirarshi, dan qirqirarshi da aka nuna musu yayi matuk'ar birgesu , abinda yaba Umar Faruk mamaki shine, bill da suka bashi kuma sukace ya rubuta adadin kud'in da yake so su dinga biyanshi , da taimakon Khairat ya rubuta adadin da yake bukata, anan suka sallameshi bayan sun bashi sabuwar computer wacce zai dinga musu aiki da ita, sannan aka ce jibi jirginsu zai kuma tashi, kai tsaye aka sake mayar dasu masaukinsu, saida suka huta sukayi bacci sannan suka shirya suka fita ganin gari, Khairat ce ke zagayawa dashi ko ina duk da itama ba wani sanin garin tayi ba sosai, a haka suka dinga shaqatawa har dare yayi sai dai lokacin kowace sallah suka samu wuri Umar Faruk yajasu , taxi suka tare ta kaisu masaukinsu, suna zuwa wanka sukayi suka ci abinci sannan suka kwanta.
*Asuba ta gari*
Washe gari ma koda suka shirya fita sukayi cikin qananan kayan sanyi, wuraren shaqatawa suke je sukayi farin ciki abinsu tare da d'aukar photuna , saida dare yayi yauma suka kamo hanyar masaukinsu, kafin su hau titi akwai tafiya kuma gashi wajen babu mutane, Khairat ce ta qamqameshi tace "baby nifa tsoro nake ji."
"Tsoro, kina tare dani d'in?"
Sunkuyawa yayi yace "hau na goyaki to." ko qarasawa baiyi ba Khairat ta haye bayanshi, tafiya suke a hankali suna hira qasa qasa, dan Khairat gabanta kawai ke fad'uwa tana ji akwai matsala, amma dai bata san me zai faru ba, suna cikin tafiya kawai wasu samari su shida dake gefen hanyar suka fito tare da tare musu gaba, a hankali Khairat ta sauko daga bayan Umar Faruk tana kallonsu cike da tsoro, hannunta Umar Faruk ya kama da nufi su wuce danshi ko d'ar bai jiba a zuciyarshi , d'aya hannu tasa ta rik'e hannunshi tana girgiza kai, kallonta yayi yaga tsoro fal a idonta da fuskarta, fuskantarta yayi ya dafa kumatunta yana fad'in "baby, kalloni nan, kwantar da hankalinki, babu abinda zai faru ina tare dake, ki nutsu kinji, kar kiji tsoro."
Kai ta girgiza da sauri hawaye na zuba a idonta dan duk gani take zasu mata abinda su Musa suka mata ne, qara rik'e hannayenshi tayi tana fad'in "dan Allah Faruk kazo mu canza hanya, wallahi tsoro nake ji, bana son abinda ya faru dani a baya yanzu ma ya sake faruwa, zan iya kashe kaina in haka ta faru, dan Allah kazo mu canza hanya, wannan basu da imani 'yan shaye shaye ne kawai."
"A'a Khairat bab......." bai qarasa ba yaji saukar abu a kanshi, qarar da Khairat tayi yasa d'aya daga cikin matasan ya fizgota a jikinshi tare da rufe mata baki, duk da girman bugun da suka mishi akai bai fad'i ba, sai dafe kai da yayi yana lumshe ido, kallon matashin daya rik'e Khairat yayi yana murmushin takaici, kamar mai ciwon baki yace "saketa, in kana son kanka da lafiya."
Biyu daga cikin samarin sun fahimci me yace a harshen frensh dan haka suka fad'a musu me yace dansu sunfi jin english, wurga Khairat yayi ga d'aya daga cikinsu, shima rik'eta yayi har yana shafar jikinta, ganin haka yasa Umar Faruk yin kukan kura kan samarin , cikin sauk'i yayi nasarar k'wace madakin dake hannun d'aya daga ciki, nan fa ya soma dukansu kamar Allah ya aikoshi , wani ne yayi nasarar dukanshi ta baya ba tare daya lura ba, qara dafe kai yayi yana ganin dishi dishi ga jiri na d'ibarshi, tangal tangal ya ya fara yana shirin fad'uwa, da gudu Khairat ta rik'eshi ya fad'a kanta, tana daddab'ashi d'aya daga ciki ya finciko gashin kanta yana fad'in "ina kud'i suke? kud'i muke so."
Cikin kuka da d'aga murya tace "babu kud'i a jikinmu, mu bak'i ne."
Rigar sanyinta yaja da k'arfi harta fita ya rage sai qaramar rigarta ta ciki, hannunta ya kamo da k'arfi ta mik'e tsaye yayin da Umar Faruk ya qarasa fad'uwa qasa yana fad'in " idan baku da kud'i, ai kina da kadara, dan haka zamu je dake mu fanshe kud'inmu."
Kururuwa kawai take tana qara tana dukanshi, a hankali Umar Faruk ya bud'a idonshi ya kalli inda suke nufa da ita, wani d'aki dake gefen suka jefata a ciki suka rufe, baya baya take ja d'aya na biyanta yana rage kayan jikinshi, qara ta qurma da k'arfi wacce tasa Umar Faruk mik'ewa zunbur, ai kuwa tunkarar d'akin yayi cikin wani sabon k'arfi da yake ji yana zuwa mishi, qafa yasa ya dinga bugun k'ofar, ana uku kuwa ta bud'e, yanzun ma dai saida aka kai ruwa rana kafin yayi nasara a kansu, wanda ya fara fitar da kayanshi ne Umar Faruk ya shak'e mishi wuya cikin zafin rai yana fad'in "me kayi niyyar aikatawa a kanta, fyad'e, shin kasan me iyali yake nufi, kasan me ake cewa mata, kasan me mutum zaiji idan akace an yiwa matarshi fyad'e a gaban idonka, shin kasan me zai ji?"
Ya qarashe da had'a kanshi da bango, zubewa yayi kamar ba rai a jiki, tsorata da Khairat tayi yasa ta kama hannun Umar Faruk da sauri suka fito daga d'akin, Khairat har had'awa take da gudu gudu, yayin da Umar Faruk zuciyarshi ke bugawa da k'arfi yake jin inama yaci naman yaran nan d'anye , dan wani sabon tsumi suka tayar masa tare da tuna su Musa, cikin sauk'i suka samu taxi suka koma masaukinsu , suna daf da shiga Umar Faruk ya lura da rigar dake jikinta, cire rigar sanyinshi yayi ya mik'a mata ta saka sannan suka wuce d'akinsu, cike da tsoro da fargaba Khairat tasa key ta murzawa k'ofar d'akin, tana juyowa taji saukar wani azababben marin daya sa ta fad'i gefe d'aya....
_Tohhhhhh, me kuka ce yan uwa?_
20/08/2019 Γ 14:26 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
4⃣8⃣
Dafe kunci tayi lokacin data kwamtsa qara dan a bazata marin yazo mata, da'gowa tayi ta kalli Umar Faruk ba tare data tashi daga fad'uwar da tayi ba, za tayi magana kuma ya sunkuya yasa hannu ya shako wuyanta rai b'ace ya had'ata da bango yana fad'in,
"Ke mahaukaciyar inace, ke wace irin sakarya ce, au dama haka ake miki fyad'en, ba kya iya kare kanki sai dai kawai ki dinga kuka, me kike tunanin zai faru idan da sun sake maimaita abinda ya faru a baya, ni sakarai saina sake hak'urin zama dake? sam ba zai yiwu ba wallahi, da kin bari haka ta faru dana rabu dake, danni ba sakarai bane da zan zauna ina qarasa ragowar 'yan iskan gari."
Hannun daya shak'e mata wuya dashi ta kam tana so ta kwaci kanta, idonta duk sun fito ta rasa shed'a cikin wahala da fafutukar neman rayuwa tace "Fa...faru.k, ka...k..ka sakeni, zan..... zaka...kasheni.."
Sakinta yayi ya tashi ya fara cire kayan jikinshi ya shiga douche, binshi tayi da wahalallen kallo tana kallon jinin dake bin kanshi, da qyar ta rarrafa ta rakub'e qasan gado tana kuka, tana nan harya fito d'aure da towel ya shirya cikin gajeran wando ko riga bai saka ba, wani hankciep ya d'auka ya d'aure kanshi kafin ya bud'a wata drower ya d'auko paracΓ©tamol, wanda ake ajewa saboda irin haka dama yasha sannan ya zauna akan kujera, matuk'a ranshi a b'ace yake dan haka ko kallonta baiyi ba, kuka take amma babu mai rarrashi sai dai ta juya ta saci kallon Umar Faruk, amma shi ko kulata baya yi, share hawayenta tayi ta tashi ta zagaya inda yake ta tsaya, d'ago da jajayen idonshi yayi ya wurga mata harara, jiki na rawa tayi saurin zube gwiwoyinta qasa, a hankali ta qara satar kallonshi, ganin yanda ya kafeta da ido ba annuri fuskarshi yasa ta sake fashewa da kuka, wani dogon tsaki yaja ya kawar da kai gefe yace "kije ki kwanta bana son kukan nan, idan kuma ba haka ba ranki zai qara b'aci."
Cikin fashewa da sabon kuka tace "dan Allah Faruk kayi hak'uri, wallahi bana da laifi, ya kamata ka...."
Cikin d'aga murya yace "kije ki kwanta nace ko."
Tashi tayi ba yanda ta iya, ko kayan jikinta bata cire ba taja zanin rufa ta rufe tana shashek'ar kuka, kusan minti ashiri babu mai magana sai jiniyar kukanta, cikin dakkakiyar murya yace "ki rufe min bakin nan fa."
Hannu tasa ta rufe bakinta tana fitar da sautin kukan a hankali, jin tak'i yin shiru yasa ya taso yazo gabanta yace "nace kiyi shiru, amma saboda kin rainani kin k'i kiyi shiru ko? to tashi zaune."
Tashi tayi zaune taja zanin rufa ta rufe bakinta tana kallonshi tace "kayi hak'uri na daina."
Kan gadon ya hau ya jingina ya mik'e qafafunshi yaja zanin rufa ya d'auki wayarshi ya fara dannawa, kallonshi take ganin baya kulata daga haka har bacci ya d'auketa daga zaune, jin yanda take sauke numfashi yasa ya d'an juya ya kalleta, ganin tana bacci yasa ya aje wayar gefe ya gyara mata kwanciyarta, kallon fuskarta yake sosai yana jin sonta na qara huda mushi zuciya, wani b'angare kuma tunanin abinda ya faru a baya da wanda yaso faruwa yau ne yake, a ranshi yace "wallahi Khairat zan kashe duk wanda ya sake keta miki haddi, haka kema zan iya kashe kaina danna huta, ki kiyaye kuma ki kare min mutuncinki."
Haka suka tashi suka shirya dan komawa qasarsu amma babu mai magana, Khairat har gaisheshi tayi amma bai amsa ba, kuma a haka har suka hau jirgi, suna cikin jirgi Khairat ta kalleshi cikin taushin murya tace "baby, dan Allah ka daina fushi dani, bana da laifi a cikin al'amarin nan, ba zan iya shiga qasarmu ba alhalin kana fushi dani, dan Allah ka yafe min."
Kallonta yake kamar ba zaiyi magana ba ita kuma tana sunne kai, hannayenshi ya bud'e mata alamar ta taho, saida tayi murmushi kafin ta fad'a jikinshi ya rumgumeta, wasu hawaye ne suka taho mata tace "Faruk ina sonka, dan Allah karka hukuntani ta hanyar nesanta kanka dani, ba zan iya jura ba."
Saida ya sumbaci kanta yace "kiyi hak'uri baby, rai nane kawai ya b'ace, amma nima ba'a son raina nayi ba, amma ba zan sake maimaitawa ba, nima ki yafe min kinji."
D'ago ido tayi ta kalleshi tace "ba zan yafe ba, sai munje gida na rama sannan zan huce."
Kallon idonta yayi yace "kina so na mutu ko?"
"A'a." ta fad'a cikin taushin murya.
"To karki fara ramawa, dan zaki gane mijinki ragone idan ki kayi haka."
"Ba wani nan, bayan jiya ka nuna min zaka iya acting as sadaukin jarumi."
Nanma qwayar idonta ya kalla yace "zan iya komai a kanki Khairat, na fad'a miki zan iya indai akan sonki ne."
"Ina sonka." ta fad'a tana qara qwaqwumeshi.
Sun sauka lafiya kuma taxi ya kaisu gidansu Papa, bayan Umar Faruk da Papa sun tattauna sannan ya d'auki motarshi suka tafi gida, tun a k'ofar gida yara suka fito suka tarbesu, haka suka shiga cikin gidan ana musu sannu da zuwa, Ruk'ayya ce ta karb'i kayansu da makulli ta bud'e ta shigar musu da kayan, Zuby ce ta fito daga wanka zata shiga d'aki, kallon kallo sukayi da Umar Faruk dan Khairat harta shiga d'aki, "sannu da zuwa."
Ta fad'a kawai tasa kai d'aki, ganin ta shige yasa shima ya wuce d'aki, Khairat ya samu harta shiga wanka dan haka ya fito ya shiga d'aya douche d'in dan yayi wanka, doguwar riga kawai Zuby ta saka ta fito dan tayi alwala dan an fara kiran sallah, ganin yara maza sun fita k'ofar gida suna alwala iyayen kuma sunyi sun shiga d'aki, kusan dai gidan ya d'anyi shiru hakan yasa ta tuna da aikin da malam ya basu, aje butar hannunta tayi ta lallab'a a hankali ta shiga d'aki Khairat, tana shiga idonta ya sauka akan gado, jaka waya da kuma mouchoir (hankciep) ta gani akan gadon, da sauri ta d'auki mouchoir d'in dan a ganinta zaifi zama qaramin abu wanda ba za'a gane ba, sai dai kash, sark'ar da Khairat ta cire ce ta rufe da mouchoir d'in, kuma wajen d'auka da sauri yasa yan kunnai suka fad'i qasa saita had'a da sarqar ba tare data lura ba.
Da sauri ta shiga d'aki ta kira wayar Mama, a lokacin kuma Umar Faruk ya fito ya shiga d'akin Zuby baiko kulata ba yasa kaya ya fita masallaci, saida taga ya fita sannan tace wa Mama "Mama na samo abinda malam yace."
"Yawwa yar albarka, amma tayaya sun dawo ne?"
"Eh Mama." ta fad'a tana warware mouchoir d'in danta kalla, ido ta waro tace "Mama, sarqa ce fa a ciki."
"Sarqa kuma, ita kika d'auko?"
"A'a Mama, ina ga cikin mouchoir d'in take."
"To kinga ki ajesu , zanzo gidan an jima saina kaiwa malam d'in."
"To Mama." daga haka sukayi sallama, kallon sarqar take sosai qarama mai kyan gaske, wani babban dutsi ne ya qawata sarqar, ajewa tayi ta jira zuwan Mama.
Khairat na fitowa ta shirya cikin doguwar riga sannan ta rama duk wata sallar dake kanta kafin ta cire doguwar riga tasa riga da wando, jakarta ta d'auka ta fara cire kayan ciki tana mayar da komai mazauninshi, kan mouchoir ta aza hannu sai taji ba komai, kallon wajen tayi amma dai taga ba komai, wajen dressing miror ta nufa danta duba sai taji ta taka abu a qafarta, "ashhhh." ta fad'a tare da d'auke qafarta ta duba wajen.
Da mamaki tasa hannu ta d'auki 'yan kunnai dake qasa zube, duba gadon ta farayi amma sam bata gani ba, aje 'yan kunnai kawai tayi ta kwanta da littafinta a hannu tana karatu, sai dai tana tunanin yanda akayi abinda ta aje anan ta kuma rasashi.
***************
Bayan sallah la'asar Mama tazo gidan ta karb'a, a lokacin Khairat na d'akinta bata sanma da zuwanta ba, koda Mama taga sarqar tace zata kaita kasuwa ta siyar, dan ba zai yiwu a mayar da ita ba kuma da alama za tayi tsada, dan haka daga nan wajen malam ta nufa takai mishi mouchoir d'in, kasancewar magrib ta gabato yasa ta koma gida da niyyar gobe zata kai sarqar kasuwa ta siyar.
****************
Har Khairat ta fara bacci Umar Faruk ya shigo d'akinta, bai yarda ya tasheta ba dan yasan tana tare da gajiya, a hankali ya lallaba ya sumbaci goshinta sannan ya sake gyara mata rufa, dauke littafin dake qirjinta yayi ya daga hannayenshi ya tofa addu'o'i sannan ya shafa mata a jiki, ficewa yayi ya rufe mata d'akin sannan ya koma d'akin Zuby, da qyar Zuby ta amince da Umar Faruk ta bashi hakk'inshi, abin takaici kuma banbaci ne nesa tsakaninta da Khairat, ba yanda ya iya dole yana da hankalin da zai iya banbace dad'i da akasin haka, yana mamakin yanda yake samun Khairat kullum kamar budurwa kullum, dan kullum saita zubar da hawaye idan zai shigeta, amma Zuby ya kasa tantance meye ma yake ji a tare da ita, koda ya samu ya tsarkake kanshi bai kwanta ba, karatu ya dinga yi har dare ya raba kafin ya kabbara sallah, nanma saida aka kira sallah sannan ya nufi d'akin Khairat, koda ya shiga ya samu har tayi alwala, dad'i yaji sosai bayan ta gaisheshi sannan ya wuce masallaci.
Da safe kuma basu samu damar karatu ba saboda yana d'akin Zuby yana bacci, Ruk'ayya ta samu ta d'ora mata karatun, suna gamawa kuma Mamie ta kirata danta mata ya gajiya, suna cikin magana Khairat tace " Mamie, jiya fa na jefar da sarqata."
"Wace sarqar kuma?" cewar Mamie.
"Mamie sarqata ta *diamond*."
Waro ido Mamie tayi kamar tana gabanta tace "diamond d'inki, garin yaya Khairat, me yasa kike da sakaci ne haka, sarqar milyoyin kudade zaki saki har a d'auke?"
Cikin katse hanzari tace "Mamie, sarqa cefa, kuma ta b'ata, ya zanyi to? dan Allah karki damu kanki, zan siye wata insha Allah."
"Humm, haka za kice mana, dan kinsan kina tambayar mahaifinki ko million nawa ne zai baki shi yasa."
"Mamie, to idan bai bani ba wa zaiba? ni kad'ai ya haifa a duniya, nice mai gadon komai nasa, ai yafi naci tun muna kan lokacinmu."
"To naji, yanzu ki aje yan kunnan, zan kira *Alpha* da *Maiga* na fad'a musu idan sun samu koda mai kama da 'yan kunnan su kawo min, dan nasan halinki zaki iya yin banza dasu."
"To Mamie, amma nidai da baki bawa kanki wahala ba."
"Kiyi yanda nace kawai."
"To Mamie." tana fad'a ta kashe wayar, Mammie ce ta kalli Mamie ta tambayeta meya faru, nan ta fad'a mata abinda ke faruwa, a take Mamie ta kira Alpha da Maiga ta kula tura musu photon sarqar da yan kunnan lokacin da aka siyesu.
****************
Tun Mama nakan hanyar zuwa kasuwa take kiran wayar malam amma yak'i d'agawa, ta alaqanta hakan da yawan abubuwa, shi kuma ya ya kasa d'auka ne saboda sam babu nasara a aikinsu, danya riga daya gama fahimtar indai har Khairat na cikin gidan nan to babu abinda zai iya yi mata, saboda tsaron dake cikin gidan, ana yawan karanta Qur'ani musamman suratul Baqara, dan haka dole dai su sake shawara.
Mama na zuwa kasuwa ta zarce wajen wani babban mai harkar sarqoqi mai suna Alpha πππ, (wallahi dariya take bani), yana ganin sarqar yace "gaskiya Hajia kinzo da babbar harka, amma ki d'an jirani zansa a duba kota qwarai ce ko jabu."
Tana wasar baki tace "ba komai ai, nasan ma ta qwarai ce." kuma ta fad'i hakane ba tare da sanin wace irin sarqar take rik'e da ita ba.
Yana shiga daga cikin shagon ya kira Mamie ya fad'a mata irin sarqarce komai da komai, amma babu yan kunnai "bani minti biyu zan kiraka." cewar Mamie.
Tana kashewa ta kira Khairat ta fad'a mata, shiru Khairat tayi tana tunani, mamaki take sosai ta yanda akayi sarqarta ta fita daga gidan, duk da dai ba tabbaci amma tana so tasan waya samu sarqar, da sauri tace "Mamie, kice ya rik'e matar karya bari taje ko ina."
"To." Mamie ta fad'a tare da kashe wayar, ba b'ata lokaci Khairat ta dannawa *Abdul waid* kira, tare sukayi makaranta abokinta ne sosai kuma gendarme ne, yana d'auka yace,
"Marar mutunci, ashe zaki tuna dani harki kirani?"
Dariya tayi dan indai sun had'u sai haka ta faru, cewa tayi "petit frère, ya kake?"
"Ba zaki daina cemin qannanki ba ko? har yanzu kina nan da shegen san girma, ke mutum koya baki shekara arba'in kina iya kiranshi qannanki."
"Saboda nasan na girmeka ne shi yasa."
"To naji, ya akayi yanzu? kwana biyu kin b'ace."
"Wallahi da dama, amma yanzu akwai matsala."
"Meya faru?"
"Shekara d'aya data wuce akwai wani diamond dana siya, to shine jiya bayan na dawo daga las vegas na ajeshi, kawai na fito ban sameshi ba, amma abun mamaki yanzu Alpha ya kirani wai wata mace tazo da irin sarqar zata siyar."
"Subhanallah, yanzu me kike so ayi?"
"Um , ina so nasan matar kuma ya akayi sarqar taje hannunta, nasan zaiyi wuya ace ba sarqata bace, tunda ga 'yan kunnan a hanuna."
Kamar yana gabanta yace "an gama ranki shi dad'e, za ayi yanda kike so baby."
Da sauri tace "kai bana san iskanci, wannan sunan yanzu mijina kad'ai keda damar kirana dashi."
"Ke tafi can marar mutunci, ai dama jira nake na had'u dake wallahi sai anyi yak'in duniya na uku, wai yarinyar nan dan kin rainani kawai sai dai naji kinyi aure a gari, ba sanarwa ba kira ki fad'awa mutane, amma ba komai nine kika tsana ai, tunda *Ma'aruf* yace da kanki kika kira kika fad'a musu."
"Ai ban kiraka bane saboda baka damu dani ba, wata na kusan hud'u ina jinya amma baka tab'a zuwa ka dubani ba."
Shiru yayi kafin yace "kiyi hak'uri Khairat, wallahi nima labari na samu akan abinda ya faru dake, amma lokacin bana gari."
"Kaga ni ka dameni da surutu, kaje da sauri dan Allah ku qwamuso min matar nan."
Dariya yayi yace "baki da dama, kina nan yanda kike har yanzu."
"Kai wallahi ba kamar da ba, yanzu in fad'a maka inka ganni ba zaka ganeni ba, yanzu fa da hijabi nake fita."
Bushewa yayi da dariya lokacin da suka shiga mota shida jami'ai guda biyu suka nufi kasuwa yana fad'in "Allah ya shirya minke Khairat, yanzu fad'a min adresse d'in mai shagon?"
"Ba matsala zan turo maka, amma fa bana so kayi saurin fad'an sunana."
"No wahala baby, za ayi yanda kike so."
"Kai, zanci..., wallahi ka kiyaye ni fa, mijina zai shek'ek'a idan yaji"
Tana fad'a ta kashe wayar ta tura masa d'Γ adresse d'in, Mamie ta kira ta fad'a mata yanda ake ciki, tana d'an duba karatun da Ruk'ayya ta d'ora mata Umar Faruk ya shigo d'akin da sallama, tashi tayita tarbeshi suka gaisa, tambayarshi tayi da "ba zaka fita yau ba?"
Saida ya shafi qasumbarshi yace cike da kasala yace "yau kam bana jin dad'in jikina, amma kuma ina so na fita, gashi kuma na makara sosai."
Itama gemunshi ta shafa tace "bara kaga yanda za ayi."
Wayarta ta d'auka ta dannawa manager kira, cike da girmamawa ya gaisheta kafin ta d'ora da "manager ayi mana uzuri nida Faruk, kasan jiya muka shigo."
"Ah haba Hajia, ai girmanku ne, ba komai wallahi."
Kashe wayar tayi ta kalleshi tace "kaje ka sake kwantawa."
Ba gardama ya sake mikewa ya fita ya koma d'akin Zuby, yana tafiya kuma sai taji hawaye sun zubo mata, sharewa kawai tayi taci gaba da karatunta.
***************
Alpha ne ya d'anja Mama da hira yace mata "Hajia saifa kin jira an kawo min kud'i daga banki."
Baki Mama ta bud'e tace "wai dama darajarta har takai haka?"
"Hajia dama baki san darajarta ba."
"A'a ba haka nake nufi ba, kasan mu tsofaffi ba ruwanmu."
Murmushi yayi yace "Hajia diamond kike d'auke da ita fa."
"Diamond?" cewar Mama da ita k'arfinta, hakan kuma yayi daidai da isowar su Abdul Waid, cikin d'aure fuska Abdul Waid ya sauko daga mota yana zarewa Mama ido, "kece wacce zaki siyar da sarqar?"
Mama da jiki ya ya fara rawa ga fad'uwar gaba da tsinkewar yan ciki tace "a'a.....a..a.., ba...b.ni."
Kallon Alpha yayi yace "mun samu rahoton anzo siyar da sarqa nan wajen, shin zamu iya sanin gaskiya."
Sarqar ya bashi tare da fad'a mishi komai, ba sauki al'amarin suka tusa Mama cikin mota suka tafi da ita, suna zuwa suka garqameta suka rufe sannan ya kira Khairat ya fad'a mata, duk da bata san ko wacece ba cewa tayi "kawai ta fad'a muku yanda ta samu sarqar."
_Ma'u ho_π
***************
Sai kusan la'asar labari ya riski Zuby da mutanen gidan, gaba d'aya Zuby ta ishi gidan da kuka da jiniya , da qyar Umar Faruk ya lallab'ata yace zaije yaji miye matsalarππ (wlh dariya kawai ke sub'uce min), koda yaje kuwa aka fad'a mishi abinda ake ciki, amma kuma Mama tak'i fad'in yanda akayi ta samu sarqar, abu kamar wasa haka labari ta fara karad'e dangi da mutan gari.
Khairat na jin abinda ke faruwa tayi mamaki sosai, to taya sarqarta taje hannun Mama? wannan itace tambayar da take wa kanta, dan haka taci alwashin sai Mama ta wahala ta kuma gane kurenta tare da fad'in yanda akayi sarqarta taje hannunta, gidan babu wanda yayi bacci a daren saboda kukan da Zuby keyi, a haka safiya tayi Zuby ta shirya dan tafiya ganin Mama.
Saida Umar Faruk ya matsa mata ta samu taci abinci, suna shirin fita daga gidan jiri ya d'ebeta ta fad'i, a firgice Umar Faruk ya d'auketa yana kiran sunanta, d'akin Mama ya kaita ya kwanta aka shafa mata ruwa ta farka, bayan qanqanin lokaci kuma zazzab'i ya rufeta, duk da haka matsawa tayi saita tafi dan haka Umar Faruk ya d'auketa suka tafi, koda taga halin da Mama ke ciki ma sabon shafin kuka ta bud'a, da qyar Umar Faruk ya fito da ita daga wajen, suna hanya yaga tana rawar sanyi sosai dan haka ya wuce da ita asibiti.
Ana dubata aka tabbatar mishi tana d'auke da qaramin cikin da ba zai juri wahala ba, ji yayi kamar almara hakan yasa saida suka shiga mota ya rufe ido na d'an wani lokaci, yana bud'ewa ya saki murmushi yana fad'in "Alhamdulillah Allah, Allah kaine Allah, ina godiya abisa ni'imominka a gareni."
Aifa ranar Zuby na jikin Umar Faruk, duk da masifar shagwab'a da kukan da take haka ya taushe ya had'iye, a ranar ko saida safe bata bari yama duka muten gidan ba bare kuma Khairat, Khairat kam ganin shiru yasa ta maida hankali ga tilawar karatunta, amma fa da taga dare yayi sosai kuma ta tabbatar ba zai shigo ba saida ta zubar da hawaye, a haka asuba tayi saida ya samu ya dawo daga masallaci kad'ai ya wuce d'akin Khairat har safiya tayi, yana shiga ya sameta kwance akan kujera da littafin *Hisnul muslim* tana karanta addu'o'i, a wahalce ta tashi zaune tana fad'in,
"Sannu da zuwa."
"Yawwa sannu." ya fad'a yana zaunawa kusa da ita, kallonta yayi yace "kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau." ta fad'a a tak'aice, janyota yayi jikinshi yace "yadai, me yake damunki."
"Ba komai."
Tashi tayi zaune ta kalleshi tace "Faruk, da zuciya d'aya nake zaune da kowa a gidan nan, zan iya sadaukar da komai nawa dan taimakawa marar k'arfi, amma duk da son taimakona a gaskiya bana son sata, bansan tayaya sarqata ta shiga hannun mahaifiyar matarka ba, amma dai nasan ta sameta ne da taimakon wani na kusa dani, ma'ana wanda yake cikin gidan nan, ni nasa aka maka wanda ya d'auka min sarqar, amma gaskiya da farko bansan ita bace."
Katse mata magana yayi da "da kuma ki kasan itace me ki kayi?"
"Banyi komai ba."
"Ai kuwa na d'auka za kisa a fitar da ita ne ,kodan matsayinta a gareni."
"A'a Faruk, ina so nasan yanda ta samu, dan nasan b'arawona, hakan na nufin akwai mai son cutar dani, ba kuma zan lamunci hakan ba."
Gyara zama yayi yana kallonta yace "dan Allah Khairat kiyi hak'uri kisa a fitar da ita basai kowa yaji ba, na miki alk'awarin hakan ba zata sake faruwa ba insha Allah."
Tsaye ta mike ta aje littafin hannunta tana fad'in "kayi hak'uri, gaskiya ba zan iya ba, dole nasan meya faru, kuma fa maganar milyoyin kud'ad'e ake, taya kake tunanin zanyi wasa haka."
Shima tsaye yayi yace "kenan kina so kice ba zaki iya fito da ita ba?"
"Eh, haka nake nufi." ta fad'a ba tare data kalleshi ba.
"In kuwa hakane baki cika masoyiyar gaskiya ba, na dauka zaki iya yin komai saboda ni, ashe ba haka bane."
Yana fad'a ya fita ya bar d'akin, ko kallonshi ba tayi ba itama taci gaba da harkokinta, shiryawa tayi bata kula kowa ba itama ta tafi office danta samu salama, taji dad'in tafiya domin ta manta da duk wasu matsaloli, sai dai damuwar d'aya shine rashin zuwan Umar Faruk aiki, da yamma ta fito dan tafiya gida amma motarta tak'i tashi, kiran Umar Faruk tayi a bugu d'aya ya d'auka, nanta fad'a masa abinda ke faruwa, saida ya shiga gida ya d'auko makullin motarshi danya tafi d'aukarta, Zuby ce ta shagwab'e sai dai ya zauna bata so ya fita, ganin ba zata barshi ya tafi ba yasa yace sutafi tare.
Koda suka isa Khairat bata damu ba tunda yau ba itace dashi ba, gidan baya ta bud'a ta zauna lokacin har mai gyara yazo duba motarta, suna fara tafiya tace "sannunku."
Umar Faruk kad'ai yace "sannu, ya aiki? kinga yau banzo ba ko?"
"To ai naga amarci kake ci har yanzu."
Karaf Zuby tace"bai kai yaci amarcin bane kome?"
Ajiyar zuciya kawai ta sauke, tsaki tayi ita kuma tana habaice habaice har tana fad'in "wataqila itama tana kurb'awa kamar gyatuminta."
Murmushi Khairat tayi tace "zanyi farin ciki ace kurb'awa nake, koba komai shan giya sai mai kud'i, amma halin b'era, ina fatan Allah yamin tsari dashi."
Zuby zatayi magana Umar Faruk ya daka mata tsawa yace "karki sake naji bakinki, wallahi idan na sake jin makamancin haka a tsakaninku har takai ga sanya iyaye, wallahi zaku gane kuskurenku."
Qwafa yayi mai k'arfin gaske, shiru sukayi suka ci gaba da tafiya, daf da wani babban shago Khairat tace "dan Allah baby inba damuwa ka ajeni nan zan duba wani abu."
D'an qaramin tsaki yayi yana paka motar yana fad'in "bana so magrib ta sameni akan hanya."
"Ba zan jima ba baby."
Ganin Zuby na kallon shagon yasa yace "ko kema zaki shiga?"
"Eh, madara nake so." ta fad'a cikin shagwab'a.
Hannu yasa ya shafi sumar kanshi sannan ya bud'e murfin yace "fito muje."
Fita sukayi suka rufawa Khairat baya, a tare suke duba kayan yayin da Khairat keta cika kwando da kaya, suna gamawa suka zo wajen biyan kud'i, ana lissafi kayan daga baya sukaji ance,
"Hajia Khairat."
Juyowa tayi amma wanda ta gani yasa mamaki ya bayyana a fuskarta fal, da farin ciki ta nunashi tana dariya tace "Alhaji....
20/08/2019 Γ 14:26 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
4⃣9⃣
"Alhaji Bala, kaine?"
Cike da girmamawa ya matso inda take ya sunkuya yana gaisheta "Hajia ina wuni."
"Haba dan Allah ka tashi mana."
"Haba Hajia, aini ba butulu bane, wallahi uwata kad'ai nafi girmamawa a duniyar nan kafin ke, duk da dai nasan nayi laifi, amma ina neman afuwa Hajia, ke babbace kina bawa komai baya komai girmanshi, musamman ga irinmu talakawanki."
"Alhaji Bala, matsalata dakai fa kenan, wasa mutum da kurantashi, to ya kwana biyu ya iyali?"
"Lafiya qalau Hajia, ya harkoki ya kuma fama damu?"
Bata amsa ba sai nuna masa Umar Faruk da tayi tana fad'in "am Bala, ga mijina nasan baka san nayi aure ba, ga kuma yar uwata abokiyar zamana."
Hannu Umar Faruk ya mika masa amma saiya nemi zube gwiwoyinshi qasa danya gaisheshi, da sauri ya rik'eshi yana fad'in "haba haba, ya haka kuma? kaifa babbane."
"Barni Alhaji na gaisheka, aiko karen Hajia Khairat dole samu girmamawa daga gareni, bare kuma kai mijinta."
Cikin jin haushi Zuby ta juyo danta fita daga wajen, idonta ne ya sauka kan Alhaji Bala, wucewa tayi dan bata sanshi ba shi kuma ya santa farin sani, binta yayi da kallo harta b'acewa ganinshi, hannu Umar Faruk ya ya sake bashi suka gaisa sannan sukayi sallama, ledojin ya d'auka harda na Khairat ya wuce dan yau dad'i yake ji ya mata hidima, kallon Alhaji Bala tayi tace "mu zamu wuce, sai kwana biyu."
"Am Hajia." ya fad'a a hankali.
Kallonshi tayi shi kuma ya d'ora da "Hajia ki kace waccen abokiyar zamanki ce?"
"Eh." ta fad'a a tak'aice.
Shiru yayi yana girgiza kai, da mamaki tace "lafiya ko, kasanta ne?"
Shiru yayi yasa babbar rigarshi ya shafe zufa, d'an hararanshi tayi tace "He Bala, nasanka fa, ka fad'a min gaskiya, kardai itama tana cikin yan matanka."
A tsorace ya kalleta yace "A'a Hajia , wallahi na jima da daina wannan harkar, wannan d'in indai sunanta Zubeida kuma ya ga Asma'u, to tabbas *d'iyata ce*."
"Me, 'yarka fa, tayaya?"
"Kamar yanda kika sani bana iya b'oye miki komai, domin kuwa badan taimakonki ba da yanzu ina bara akan titi, wannan da kika gani 'yata ce ta cikina, kuma bata hanyar aure muka sameta ba."
Bai qara komai ba daga hakan, kuma itama bata tambayi komai ba suka rabu, a mota kallon Zuby kawai take tana mamaki, Zuby kam cikin rawar kai tace "da auranka ma saika nuna halin, wannan jaraba dame..."
Bata qarasa ba Umar Faruk ya taka burki da k'arfi yana harara, cikin zare ido yace "wallahi tallahi zan zubar miki da hoqoran gaba, kinji dai na rantse ko? tom."
Tayar da mota yayi suka d'auki hanya, duk da haka Zuby bata daddara ba suna daf da shiga gida saida ta bangaji Khairat da k'arfi ta wuce, bugu da qari ta d'ora da "yar mashayi kawai, in banda qaddara me zai had'ani had'a kafada dake."
Yanzu kam Khairat takai maqura ba zata iya jura ba, kamar mai tab'in hankali haka ta zubar da kayan hannunta ta shak'o wuyan Zuby, kafin ma Zuby ta fahimci meya faru Khairat ta dasata a qasa tabi kanta da duka , ihu ta fara tana kiran sunan Umar Faruk dake gyara parking d'in mota, sosai Khairat take bugun bakinta harya fara fitar da jini, gashi girman jiki ba d'aya ba ta kasa qwatar kanta, jin kururuwa ne yasa mutanen dake d'aki duk suka firfito, da azama kowa yayi soro ya fara qoqarin rabasu, lokacin kuma Umar Faruk ya shigo, sosai ta rik'e rigar Zuby harta keta mata rigar, janyota Umar Faruk yayi a lokacin Zuby itama ta rik'e rigarta sosai, hakan yasa zip d'in rigar cirewa har rigar ta zame daga jikinta, ganin haka yasa mazan wajen komawa mafakarsu suka bar mata, cike da takaici da b'acin rai Umar Faruk ya fizgi hannun Khairat daga wuyan rigar Zuby yana fad'in "ba zaki saketa ba?"
"Ba zan saketa ba, wallahi saina ci uwar yarinyar nan, akan me zata rainani, ni tsararta ce?" duk tayi maganar nan cikin neman d'aukewar numfashi.
Duk maganganun da mutanen wajen keyi ko jinsu basuyi, da k'arfi ya b'abb'are hannayensu ya nuna Zuby yace "wuce ciki."
Juyawa tayi tana kuka tana d'yangasa qafa tana tofar da jinin dake bakinta, Khairat ma a tsawace yace "maza wuce ciki."
A hassale ta qarasa zame rigarta ta jefar ta wuce nata kewayen, zaune tayi akan kujera saboda makullin na cikin jaka kuma ta jefar da ita, Zuby na kaiwa qofar d'aki ta durk'ushe tana dafa ciki tana qara tsananta kukanta, da sauri kuma sukayi kanta ana tambayar lafiya, Mama ce da Saratu suka kamata danta shiga ciki, sake lanqwashewa tayi tana dafe ciki, Mama Sa'a ce ta kalli Umar Faruk tace "Umar Faruk tana da ciki ne?"
Kai kawai ya d'aga mata alamar eh, Mama Maimuna ce ta qara da "Allah yasa dai ba b'ari za tayi ba."
Jin haka yasa Zuby sake fashewa da kuka tana kiran cikinta cikinta, a hanzarce yace "to Mama mu tafi asibiti mana."
"A'a bari dai mu gani." cewar Mamanshi, d'orawa tayi da "bud'e mana d'akin."
Umar Faruk d'in ne ya bud'e musu d'aki suka kwantar da ita akan gado, duk wannan murqususus da take har yanzu shiru ba alamar jini ko wani abu, da qyar suka rarrasheta tare da bata baki, sannan Mama ta dora "in ki kaji wata matsala kiyi sauri ki fad'a masa kinji."
Bata amsa ba su kuma suka kama bansu, tashin hankali Umar Faruk ya ganshi a daren nan, kuka kawai take tana fad'in cikinta, sam bata barshi yayi bacci ba, kuma duk kururuwar nan da take akan kunnan Khairat dake cika tana batsewa, duk yanda taso tayi banza dasu abin ya gagara saida ta zubar da hawayen bak'in ciki ,itama dai ba tayi wani bacci ba sai karatunta data kwana tanayi.
Tunda asuba Zuby ta fahimci illar da Khairat ta mata, kallon kanta tayi a madubi taga yanda bakinta ya kumbura, ga masifar ciwon da hannunta keyi ko motsashi bata son yi, a haka Umar Faruk ya dawo daga masallaci ya sameta ba tayi sallah ba, nuna mishi hannun tayi yana gani ya kece da dariya yace "wallahi gotaki tayi, kawo na gyara miki."
Cike da jin haushi ta bashi hannu danya gyara mata, amma yana tab'awa ta fara ihu da kururuwa tana qwaqwumeshi, taji jiki sosai yayin da Umar Faruk yaki sakin hannun har saida ya gyara mata dan gwanine a wannan fannin , hawaye majina da yawu babu wanda bata had'a ba, saida ya shafa mata magani kafin ta kwanta na d'an lokaci shi kuma ya fita gaishe da iyayensu daga nan ya wuce d'akin Khairat.
Tsaye ya sameta gaban madubi tana shiryawa, dan wajen aiki take so ta tafi da wuri dan zaman gidan Umar Faruk ya fara fitar mata akai, sam akwai abinda ba zata d'auka ba ko daga wajen Umar Faruk d'in ne bare banzar matarshi, a daqile ta amsa sallamarshi ba tare data kalleshi ba, takawa yayi har yaje inda take ya kwanta akan bayanta wanda Allah ya wadatashi da tarin nama, hannu yake kaiwa cikin rigarta yana tattausa ko ina na jikinta yana sauke numfashi, yayin da wata sabuwar kewarta ke qara mamayeshi, shiru ta masa tana ci gaba da shirinta harta juyo da nufin d'aukar d'an kwalinta ta d'aura, janye jikinta tayi daga nashi ta d'auki d'an kwalin ta d'aura ta d'auki hijab ta saka, jakarta ta d'auka tasa takalmi zata fita ta rik'e hannunta, marairaicewa yayi yace "bako gaisuwa, me yayi zafi haka, kuma ina zaki je da safiyar nan? koni gani a gida ban fara shirin fita ba saike."
"Saboda kana da qarancin abinyi ne shi yasa, ni kuma akwai abubuwa masu mahimmanci dake gabana wanda suka fi zaman haka."
Janyota yayi ta fad'a qirjinshi Kutsawa yayi cikin hijabint ya manna kanshi a tsakiyar wuyanta yana sumbata, qoqarin fito dashi ta fara yi amma ya cije, jin ya fara birkicewa har yana neman zare mata rigar yasa ta turoshi da k'arfi ya fad'a kan gado, gyara jikinta tayi zata wuce ta kalleshi tace "Khairat fa ba tayi shiryuwar da zaka raina mata hankali ba, ina da 'yancin da zan iya qwatarwa kaina 'yancina da kaina, kuma wallahi ko kaine ka d'aukar min abu zan iya nuna maka b'acin raina, kamar yanda ko kai ka b'ata min ba zan gagara nuna maka hushina ba."
Banka masa harara tayi ta wuce abinta, wani irin iska ya furzar yana jin ba dad'i, tashi yayi ya koma d'akin Zuby ya samu tana bacci , shiryawa yayi shima kawai yabi bayan Khairat ba tare damu daya tashi Zuby ba, abin mamaki da d'aure kai shine, umarni da Khairat ta bawa Habeeba kan cewar bata son ganin kowa, kuma haka akayi Umar Faruk ma yazo ganinta Habeeba tace yayi hak'uri Hajia tace tana aiki, bai wani ja da tsayi ba dan yasan jiya ta dawo Khairat d'inta, kuma zai iya jawa Habeeba matsala a nata aikin inhar ya shiga da k'arfi, haka ya koma ya zauna mazauninsa ya kasa yin komai sai tunani da rashin walwala, abinda ya qara d'aga maishi hankali shine har suka tashi kowa ya kama hanyar gida Khairat bata fito ba, wacce bata iya rabin wuni a wajen, saida yaga har Habeeba ta tafi sannan ya nufi office d'in nata.
K'ofar rufe take dan haka ya dinga bubbugawa yana kiran sunanta, saida ta gama had'a kayanta zata fita tazo ta bud'e k'ofar, yana shiga ita kuma ta fito ta kama hanya, da gudu ya biyota kamar wani matashin zaki ya tari gabanta, yanda suka had'a ido yasa ya d'auke idonshi daga kallonta, wani tartsatsi yaji da rabon daya jishi tun zamanin shed'an na d'an qauye , ma'ana tun tana Khairat d'inta ta ainihin, kasa magana yayi ya kuma kasa kallonta, rab'ashi tayi ta wuce abinta tana fita ta shiga motarta ta kama hanyar gida a lokacin ana sallah magrib.
*Muje da sauri 'yan uwa*
A kwana biyu abubuwa sun faru, daga ciki akwai jinya da Zuby tayi da kuma zuwansu Zulfa'u gidan, sunzo suka tayar da hayaniya akan cewar sai sun d'aukar mata fansa, ganin basu samu wannan damar ba yasa suka ce zasu kai qararta, duk ban maganar da Umar Faruk ya dinga yi basu ji ba, har saida ya fad'a musu itace tasa aka kama Mama, kuma in suka kai qararta tofa magana zata iya yin girman da ba za'a iya tsayar dashi ba, sai lokacin sukayi shiru da bakinsu suka bar maganar qararta, a kwanankin nan aka hana kowa ganin Mama dake d'aure wacce wahalar duniya ta isheta, kuma a kwana biyun nan Umar Faruk ya had'a Khairat da Zuby ya musu qwaqwaran kashedi, ya kuma fad'a musu zai iya rabuwa da kowace in suka sake mishi tashin hankali a gida, kuma yaja kunnan Zuby sosai aka fita harkar Khairat, ya kuma nuna musu rashin jin dad'i akan haka sosai, a lokacin ne Khairat tace,
"Ka fad'a mata ta daina aibatani, wani yana da asali na qwarai, amma wani asalinshi ko waiwayarshi ba'a so ayi, kace ta bini a sannu inhar bata so na b'allo mata ruwan da ba zata iya taresu ba, wallahi wallahi tayi wasa saina tona mata asiri kuma na tonawa mahaifiyarta, mummunan aikin da mahaifiyarta aikata shekarun baya, to ni nan Khairat zan fallasa wannan ajiyayyan sirrin marar dad'in ji, tana wasa dani sosai kuma tana yawan fad'an bak'ar magana akan mahaifina, ni ba zan raina asalinta ba duk da nasan ita wacece, amma dai taci gaba da harzuqani to zata tsinci kanta a wahalalliyar rayuwa, tana wasa da ajina, bata san matsayi da girmana ya wuce duk inda take tunani ba, idan naso yanzun nan zan iya canza miki wajen zama, ba kuma wajen zama kad'ai ba harda sunan uba ma."
Tana fad'a kuma ta koma d'akinta ta barsu cike da juyayin maganganunta...
Umar Faruk ne ya kalli Zuby yace "kin gani ko, kinga abinda halinki ya ja miki, Zuby kin kasa gane cin zarafin mutum ba dad'i bare kuma iyaye, baiwar Allah nan ko kallonki ba tayi ba tare da dalili ba, amma ke kullum burinki kici zarafinta, ire irenku ne kuke saka wanda suka tuba su koma ga ci gaba da aikata laifukansu na baya, kuma irinku kuke saka wanda ba musulmi ba shakku da tamtama akan ya shiga addinin ko karya shiga, na tabbata mahaifinta yayi tuban gaskiya, amma ke sai tozartata kike ta hanyar anfani da kurakuran mahaifinta na baya, kin manta da cewa d'an adam ajizinie, yanzu gashi bakinki yaja miki kinci dukan tsiya harta kaiki ga jinya, abinda nake so na fad'a miki yanzu shine, Khairat ta dage ba zata saka a saki Mama ba har saita san yanda akayi ta samu sarqar, bana zarginki , amma dai ina fatan Allah yasa babu hannunki a ciki, dan in haka ta faru a gaskiya zanji kunya, dan ko babu aure a tsakaninmu, mu yan uwane na jini, dan haka abinda ya shafeki ya shafeni, kuma inya tabbata akwai hannunki a ciki babu abinda zan iya yi miki, dan maganar milyoyi ake, ni kuma ba zansa kaina a matsala ba saboda haukanki, gashi yanzu kinsha shegen duka a banza a wofi saboda shegiyar masifarki, ina fatan zaki kiyaye gaba."
Cikin kukan iskanci ta fara magana "lallai ma yah Umar, yanzu duk da abinda tamin amma ba tayi laifi ba?shine zaka d'ora min laifi, shikenan na gode."
D'akinta ta koma tana tunanin mafita akan Mama, shima d'akin Khairat ya nufa dan yau yana d'akinta ne, samunta yayi ta juya baya ta yanda baya iya ganin fuskarta, da alama har tayi shirin kwanciya bacci ne danta rufe da zanin rufa, saida yayi wanka yayi shirin kwanciya kafin ya haura kan gadon, jikinshi ne ya bashi akwai matsala dan tunawa da yanda Khairat ke tarbanshi idan ya shigo d'akinta, tabbatarwa da yayi ba za'a iya rik'e kanshi ba yasa ya rumgumeta ta baya yan shinshinar k'amshinta, shiru tayi kamar mai bacci sai dai tana ji kamar hawaye zasu taho mata, juyowa yayi da ita ya fara sumbatarta, tureshi tayi daga jikinta ta tashi zaune, a raunane ya kalleta yace...
"Haba baby, laifin me nayi kike min wannan hukuncin? na dauka ban cancanci haka daga gareki ba."
Cikin d'aure fuska tace "wannan shine *kuskuren da nayi*, ba kuma zan sake maimaitashi ba."
Hannunta ya kama ya rik'e yana sumbata yace "amma ai bana da laifi ko, me yasa za'a zab'i hukuntani to?"
"Baka da laifi kake cewa? taya za kace baka da laifi, bayan kana magana na fito da surukarka daga magarqama, bayan kana jin irin iskancin da matarka take min amma ban tab'a ganin ka d'auki matakin daya dace ba, kuma a hakane kake cewa baka da laifi."
Saida ta mayar da hawayen da suka zubo mata sannan tace "naji ni mahaifina yana shan giya kuma yana neman mata, amma ai yanzu ya daina kuma ya tuba ga Allah, duk da haka ina son mahaifina kuma ba zan lamunci cin zarafinshi ba a gabana, kuma ko yanzu ta fad'i bak'ar magana a kanshi, wallahi saina karyata."
Juya mishi baya ta sakeyi ta kwanta ta rufe, lalabarta ya fara yi amma ta juyo ta nunashi da hannu tace "bana so ka takura min, raina a b'ace yake har yanzu."
Cikin rawar murya yace "K..ha..ira...t, dan Allah karki min haka a wannan lokacin, Khairat ina neman taimako da tallafinki, wallahi zan iya shiga wani hali in ki kak'i kulani, dan Allah Khairat."
Banza tayi dashi haka ya dinga lallab'a amma ta shereshi, sam kasa bacci yayi ya fara karatu amma ya cije mishi, sai daf da asuba ya kabbara sallah ana kiran sallah kuma ya nufi masallaci, itama tana gama sallah d'akin Mama taje Ruk'ayya ta d'ora mata karatunta, suna gamawa ta fito ta shiga d'akin Mama Maimuna sa Mama Sa'a ta gaishesu, zata shiga kewayenta Zuby ta fito daga d'akinta da kumburin hannu har yanzu bai gama warkewa ba, tsaki taja tace "aikin kawai, sai iyayi da kurin tsiya kamar ba *Jihadi* akayi ba aka aureki."
Cak Khairat taja ta tsaya tare da juyowa ta kalleta, yayi daidai da shigowar Umar Faruk tare dasu Abbakar Aliyu da Usman, kasa tausar zuciyarta tayi saida hawaye suka wanke mata fuska, kallon Umar Faruk tayi ta d'an matso kusa dashi tace "Faruk, kai ka fad'a mata Jihadi ne kayi ka aureni?"
Kai ya girgiza mata yace "karki saurareta Khairat, kema kinsan ba zan tab'a fad'a mata haka ba, kawai tana so ta b'ata miki rai ne."
Jin haka yasa Zuby jin dad'i tace "kai yah Umar kaji tsoron Allah, yanzu ka manta da abinda ka fad'a min jiya kafin ka shiga d'akinta? tabb'."
Ta fad'a tare da tab'e baki, matsawa yayi Faruk yayi wajenta zaiyi magana saisu Mama suka fito, Baba ne shima yace "me yake faruwa ne kuma?"
Karaf Zuby tace "jiya nefa yace min shi jihadi yayi ya auri Khairat, daga na fad'a yanzu shine kuma yake cewa qarya nake yi."
Jin abinda ta fad'a kowa ya fara tamtama akan abinda ta fad'a, Khairat da kuka ya qwace mata ne ta matso kusan Umar Faruk tace "dan Allah Faruk ka sakeni, ka sakeni na koma gidanmu, wallahi ba zan iya jurar wannan wulaqancin ba saboda ban saba ba, da nasan *jihadi* kayi ka aureni wallahi da ban shigo gidanka ba, dan Allah ka sakeni."
Rud'ewa yayi ya rik'o hannayenta yace " Khairat karki yarda da abinda ta fad'a, wallahi bana daga cikin irin wannan mazan, ban tab'a magana mai kama da wannan ba da ita, Khairat ba zan iya sakinki ba."
Fizge hannayenta tayi cikin daga murya tace "qarya kake, ba zan sake yarda dakai ba Faruk, kai mugu ne azzalumi kuma marar adalci, wallahi na tsaneka na tsani ganinka, ba zan tab'a yafe maka ba abisa cutar dani da kayi."
Juyawa tayi da k'arfi zata shiga d'aki taji muryar Usman yace "kar kiyi haka kema, inhar za abi maganar gaskiya ai Umar Faruk jihadi yayi, amma kuma na tabbata bashi ya fad'a mata haka ba, kawai tana son rabaku ne."
Murmushin takaici tayi tace "ok , amma ai idan bai fad'a mata ba ai kai ya fad'a maka, tunda gashi ka sake maimata min jihadi yayi ya aureni."
Zata wuce Umar Faruk ya rik'o hijabinta, juyowa tayi a hankali ta kalleshi saita ganshi akan gwiwoyinshi yana zubar da hawaye, kasa magana yayi saboda tafarfasar da zuciyarshi keyi, haushi ne ya kama Ruk'ayya saboda soyayyar dake tsakanin 'yan uwa, rufe ido tayi ta matso kusanshi ta raba hannunshi da hijabin Khairat ta d'agashi tana fad'in "ka barta ta tafi mana yah Umar, saime, zaka kasa rayuwa ne? ai kowa yasan jihadi kayi ka aureta , dan babu wanda zai iya auren macen da namiji hud'u suka yiwa fyad'e."
Kallonta Khairat tayi sosai hawaye na safa da marwa a fuskarta, juyawa tayi ta wuce d'akinta Umar Faruk kuma a hassale ya d'auke Ruk'ayya da mari, sannan ya juya ya kalli Usman yace "ba dan ka sulhunta tsakanina da ita ba ka fad'i abinda ka fad'a."
Zuby ya nuna da hannu yace "kin jima kina yimin abinda ki kaga dama ina qlayeki, kiji da kyau, wallahi Khairat ta bar gidan tare zaku fita, bawai saboda sonta da nake ba sai dan qazafi da qaryar da kika min."
D'akin Khairat ya nufa yaci karo da ita da akwatin kayanta ta zubo wanda ya sawwaqa, rik'e akwatin yayi yana fad'in "dan Allah Khairat karki tafi, wallahi tallahi babu wanda na tab'a fad'a ma haka, rabamu kawai suke so suyi."
Mama ce ta qarasa inda suke itama cikin taushin murya tace " 'yata, kiyi hak'uri dan Allah karki sauraresu, babu gaskiya a cikin wannan maganar na tabbata."
"Mama, bana so kiga rashin kyautatawata , dan Allah ki barni na tafi."
"A'a Khairat, haka bai dace ba, dan Allah kiyi hak'uri ki koma d'akin mijinki."
Baba ne ya matso shima yace "ki koma d'akinki kinji, zan daidaita komai."
"Kuyi hak'uri, ba zan iya zama ba gaskiya, indai har canzi gaba da zama dashi, to zan dinga jin kaina a matsayin wacce ta kasa samun mijin aure, saida Umar Faruk ya taimaka yayi *jihadi* ya aureta, kusan kowa da abinda yake kira da jihadinsa, amma aurena shine *Jihadi* _Umar Faruk_."
Fizge jakarta tayi ta wuce abinta, motarta ta shiga ta wuce gida tana kuka, daga nan Umar Faruk yace Zuby ma ta had'a ta bar mishi gida ba zai iya zama da ita ba tana mishi haka, Baba ma baiji dad'i ba shi yasa babu ma wanda bashi hak'uri, itama tana kuka ta had'a yan kayanta, zata fita Mama ta tausaya mata tace ta koma d'akinta da zama, saboda Mamanta ba tanan kuma gata da cikinshi, taji dad'in haka sosai da haka take jin basu rabu ba tunda dama ba sakinta yayi ba.
**************
A gigice su Mamie ke tambayarta amma ta kasa magana sai kuka, kiran Papa Mamie tayi yazo shima saida yayi lallab'a da dubara ta fad'a masa abinda ya faru, a take Mamie da Mammie suka fahimci kawai sharrin kishiya ne, nan suka dinga bata magana tare da sake koya mata wasu sabbin salon na shanye makircin kishiya kowace iri ce ,sannan suka ce ta koma gidanta, nanfa tace ba zata koma ba ita ba zata sake zaman gidanshi ba, zuwa yamma kanta ya fara mata azababben ciwo, gashi kuma maganinta na can gidan.
**************
Umar Faruk nayin sallah la'asar ya d'auki makullin mota ya nufi gidansu tare da Baba, Papa ne ya tarbesu a masaukin bak'inshi, bayan sun gaisa malam ya fad'a mishi abinda ya kawosu, cikin nuna dattako Papa yace "ba komai malam, dan kunyi saurin zuwa ma dani zan mayar da ita da kaina, amma ku jira ni zan taho muku da ita insha Allah."
Takalmi Papa yasa ya tunkari d'akin Khairat yana tunanin rage mata daular da take samu, dan yana ganin kamar harda sakewar da take samu yasa haka, yana shiga d'akin ya sameta kwance, a tak'aice yace "tashi ga mijinki nan yazo ki tashi ku tafi."
Tashi tayi zaune tace "a'a Papa babu inda zanje, kawai kace ya tafi ni bana son ganinshi."
Rai had'e Papa ya kalleta ya tara mata hannu yace "ban makullin motarki."
"Motata kuma?"
"Eh."
"Amma Pap...." tswar daya mata yasa tayi shiru, d'orawa yayi da "ki bani makullinki kuma ki tashi ki wuce."
Mamaki ne ya hanata magana, dan ko a mafarki haka bata tab'a faruwa ba, tashi tayi a hassale ta fita daga d'akin ta sauka qasa, fitowa Papa yayi ya musu magana sannan suka wuce tare suna godiya, Khairat kuma kamar zata qurma ihu komai ya mata zafi har suka kai gida.....
0 comments:
Post a Comment