Bayan tafiyarsu Mamie take fad'awa Papa batun b'atan sarqarta da kuma kama matar, cikin b'acin rai Papa yace "yanzu yarinyar nan har takai matsayin da zata iya sakawa a d'aure mutum kuma ma mace, to ba zan d'auki wannan iskancin ba, jiya ba yau bace dan haka gobe nan zansa a fitar da ita."
Yana komawa d'akinshi yasa aka kulle duk wani asusun baki da Khairat ke dashi, bawai dan wani abu ba sai dan ta d'and'ana rayuwar rashi hakan zaisa ta qara hankali, haka ma ya kira manager da accountant ya gargad'esu, duk da ayukan da suka masa yawa yayi qoqari ya d'orawa kansa wani nauyin, ta yanda babu sisin kwabon da zata fita daga ma'aikatar ba tare da saninshi ba, da haka kuma yake burin ganin gobe.
***************
Zuby na k'ofar d'akin Mama su Khairat suka shigo, baki bud'e take kallonsu harta shiga d'akinta, rufe baki tayi tace "jaraba ba zata rabu dashi ba cikin sauk'i."
Khairat na shiga d'aki ta d'auki maganinta tasha na ciwon kai sannan ta kwanta, ganin tak'i kulashi yasa ya fita daga gidan, bai dawo ba saida yayi sallah isha'i, a lokacin suka shigo tare da Ruk'ayya da Mama, sallama sukayi ta amsa tare da cewa "shigo." saboda taga babu wanda ya shigo.
Shiga sukayi da wata sabuwar sallama, zaune sukayi akan kujera Umar Faruk kuma akan gado, Mama ce tace "Khairat, nazo na sake baki hak'uri ne akan abinda ya faru, kiyi hak'uri kinji, insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba."
Zaune tayi bakin gadon ta kalli Mama tace "Mama ba komai, komai ya wuce ai tunda gani na dawo."
Wani kallo da tabi Ruk'ayya dashi yasa cikin Ruk'ayya murd'awa, a hankali ta sauka daga kan kujerar ta durk'usa ta rik'e rigar Khairat tace "dan Allah aunty Khairat kiyi hak'uri ki yafe min, wallahi ba nayi haka ba danna tozartaki ba, raina ne naji baimin dad'i ba da naga yah Umar na kuka, amma wallahi ina sonki aunty Khairat kuma ina son zamanki da yah Umar, dan Allah kiyi hak'uri." ta qarashe da fashewa da kuka.
Allah sarki Khairat da taushin zuciya, hannun Ruk'ayya ta kama ta zaunar da ita kusa da ita tace "shikenan Ruk'ayya, komai ya wuce, ban fahimceki bane da farko saboda bana da d'an uwa ko 'yar uwa, amma yanzu da kika fad'a min na fahimta, ba komai wallahi."
Ruk'ayya ce tasa hannu ta share mata hawayen da suka zubo mata tana fad'in "dan Allah aunty ki daina kuka, wallahi ni daga yau ma na koma qanwarki, bani ba yah Umar zan d'aukeshi a matsayin mijin yayata ne kawai, kin amince?"
Ta fad'a tana nunata da hannu, murmushi tayi da yasa hawaye suka qara zubowa tace "Ruk'ayya waye zaik'i d'an uwa, da ina ni kad'ai yanzu kuma na samu qanwa."
Tashi Mama tayi ta fita tana goge qwalla dan wani irin tausayin yarinyar taji sosai har zuciyarta, Umar Faruk kusan qwallan yayi yayin da qaunarta ke qara ratsashi, fita yayi ya barsu Ruk'ayya kuma ta gyara mata kayan da suka zube a lokacin da take shirin tafiya gida, sunayi kuma suna hira har Khairat ta fad'a mata zata fara zuwa wajen koyan girki, da farin ciki Ruk'ayya tace "gaskiya kam aunty Khairat ya kamata, kuma kinga nima munyi magana da Mama akan zan shiga, amma tace na bari har aurena ya taso saina fara zuwa."
"Ah haba, indai kina so kawai kishirya gobe muje muji yanda abubuwan suke."
Shiru tayi ba tayi magana ba, tana mamakin hali irin na Khairat, katseta tayi da cewa "ki shirya kinji, zan miki magana."
"To." ta fad'a cikin sanyin jiki, ta jima sosai suna hira har saida taji sallamar Umar Faruk sannan ta mata saida safe, yana shigowa kayanshi ya cire ya shiga wanka, koda ya fito yana shiryawa Khairat itama ta shiga wankan, cikin doguwar rigar bacci ta shirya mai kyau fara tas sannan ta kwanta, kallon qeyarta Umar Faruk yayi danta juya masa bayane , cikin taushin murya yace "Khairat, kiyi hak'uri abis....."
"Ya isa haka, nace komai ya wuce." ta katseshi, murmushi yayi ya d'ora kanshi a tsakiyar wuyanta yace "indai hakane me yasa zaki bawa mijinki baya, kin manta hakan babu kyau?"
Juyowa tayi ta sauke idonta a kanshi tace "to na juyo, hakan yayi?"
Murmushi ya sake yi yakai bakinshi a hankali zai sumbaceta, da sauri tasa hannunta tsakiyar bakinsu, b'ata rai yayi yana kallonta, ba alamar wasa tace "kayi hak'uri Faruk, bana so ka sake neman wani abu a gareni, dan ba zan iya baka ka, ina ji har yanzu kamar ban cika cikakakkiyar mace ba, domin kuwa ana kallona a matsayin wacce ka taimaka."
Janye hannunta yayi yana kallon qwayar idonta yakai bakinshi a hankali harya had'e bakinsu, saida ya gaji da tsutsa ya saki ya kalleta da idonshi harsun canza kala yace "ki bani dama ta qarshe na nuna miki kece wacce zuciyata take so, dama d'aya tak nake so ki sake bani Khairat, ni kuma zan nuna miki matsayinki a wajena ya wuce yanda kike tunani."
Kallonshi kawai take da ido ta kasa magana, ganin haka yasa ya sake lulawa da ita wata duniyar, saida ya jima yana lashe ko ina kafin ya fara shirin gangarawa , kallon fuskarta yayi cikin siririn haske daya bayyana a d'akin, yana ganin yanda ta rintse ido sosai hawaye na zubowa ta kama damtsenshi sosai ta rik'e, yana danna kai ciki ta saki wata tausassan qara, harshenshi yasa ya dinga lashe hawayen fuskarta yana ci gaba da daidaitawa kansa zama, numfashinshi na fizgarshi yana neman shid'ewa sai hawaye dake zubo mishi yana qara matseta a jikinshi sosai yana sauke numfashi da qyar, tausayinta ne ya sake kamashi ganin kullum sai taji wannan azabar, kuma har yanzu ya kasa gane dalilin haka, kuma har yau yana mamakin yanda bata bud'ewa.
Bakinshi yakai a kunnanta yana fad'in "Allah ya miki albarka alkairina, Allah ya biyaki da gidan aljanna, Allah ya tashemu a aljannatul firdaussi, ina sonki Khairat, ina qaunarki Khairat, wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba, Khairat ki tausaya min karki kasheni dan Allah, wallahi ina so na zauna dake har qarshen rayuwata, Khairat ki fad'a min abinda kike so a duniyar nan, ni kuma nayi alk'awarin yi mikishi ko menene a duniyar nan, Allah ya saka miki da alkairi baby."
πππ *Ba magana*
******************
Shiryawa Khairat tayi tace ma Umar Faruk "nida Ruk'ayya zamu je wani wuri, ina neman izininka."
"Wani wuri bashi da suna?" ya fad'a yana tsefe sumar kanshi.
Matsowa tayi kusa dashi tace "da zaka taimaka saika ajemu , tunda motata na gida."
Juyowa yayi yana kallonta yace "muje
to." juyawa tayi zata wuce ya janyo hannunta ta fad'a jikinshi, rumgumeta yayi tare da sumbatar kanta, wani numfashi yake saukewa ido lumshe yana tuno....jiya (kun gane ai), d'agota yayi daga jikinshi ya kalli fuskarta yana dafe kumatunta yace " ina qaunarki *bugun zuciyata*."
Kallonshi kawai tayi ta janye jikinta daga nashi ta fita, bayanta yabi ita kuma tama Ruk'ayya magana suka tafi tare, akan hanya ya nuna mata aikin daya fara na d'aya compagnie sai dai baiyi komai ba, kallonshi tayi tace "meya janyo haka to?"
Kallonta yayi ya d'an cije gefen lips d'inshi yace "kwana biyu kin daina bani kulawa, wannan ne yasa Umar Faruk rasa duk wani kuzarinshi." ya qarashe tare da kanne mata ido.
Harara ta cilla mishi tana kallon computer bata sake mishi magana ba, suna daf da isa wajen kiran Papa ya shigo wayarta, d'auka tayi Papa yace "ki sameni a gendarmerie yanzun nan."
D'if ya kashe wayar, kallon Umar Faruk tayi za tayi magana wayarshi tayi qara shima, daga yanda yace "ok Alhaji insha Allah." yasa ta gane Papa ne.
Ajiyar zuciya ta sauke ta aje computer ta rumgume hannayenta tana kallon titi, tana tunanin me zai faru, shima baice da ita komai ba suka d'auki hanya......
_Bara muji meya faru bayan fitarsu_
*************
Abdul waid ne yayi irin durk'ushin nan nakan tafikan qafafu da kulki a hannunshi yana zarewa Mama ido, a nutse yace "Mama, Mama, Mama, sau uku ko? ina ganin girmanki shi yasa ban dakeki ba tunda kika zo nan, amma yanzu kin kaini bango mafita d'aya itace nasa a lallasa minke, in kuma baki son a dargajeki to ki fad'a mana yanda akayi kika samu sarqar tunda kince bake kika d'auko ba."
Cikin rawar jiki da tsoro dan ganin ba sauk'i a al'amarin yasa tace "a'a yi hak'uri zan fad'a, wallahi zan fad'a maka gaskiya."
"Ina jinki Mama."
Cikin kuka tace " 'yata ce, sunanta Zubeida, wallahi ita ta d'auko bani ba."
Zunbur ya mik'e tsaye yace "bani adresse d'inta?"
Had'e hannaye tayi tace "dan Allah kamin rai yaro karka tona mata asiri, wallahi tana da aure kuma tana da kishiya, idan maganar nan ta fita wallahi aurenta zai iya mutuwa, nima kuma zan iya mutuwa."
A tsawace yace "tasan da auren nata kuma tayi sata, mu aurenta bai damemu ba, aikinmu kawai mukeyi, ki bani kwatancen gidanta." ya fad'a da sake d'aga murya.
Cikin kuka ta fad'a musu takwacen gidan malam, fitarsu Khairat ba wuya motar jami'ai tazo gidan, guba biyu daga ciki ne suka kutsa kai cikin gidan, a lokacin Zuby na zaune tana gurgurar tsamiya, saida gabanta ya fad'i data gansu, idon jami'in akan Mama Sa'a yace "sannu ko, dan Allah Zubeida muke tambaya a gidan nan?"
Ba Zuby ba har Mama Sa'a saida kayan cikinta suka murd'a, a duburbuce take kallonshi tana kallon Zuby da ido ya raina fata , cikin d'aga murya yace "Hajia dake muke magana kinyi shiru."
"Gata nan, wallahi gata nan, bani bace." cewar Mama Sa'a cikin harshen zarma, dan dama shi tafi iyawa.
Ganin sun tunkari inda Zuby take yasa Mama Sa'a tashi da dugu ta shige d'akinta, tun basu qarasa wajenta ba ta fashe da kuka tana kiran sunan Mama ta fito ta taimaketa, Saratu Mama da Mama Maimuna ne duk suka fito, Mama kad'ai tayi k'arfin halin tambayar "bayin Allah lafiya, me tayi?"
Shirun da sukawa Mama yasa dole taja baki tayi shiru, tsawa d'aya suka mata ta tashi ta d'auki hijabi tasa suka wuce, cikin qanqanin lokaci sai gata a prison (cell) tare da Mama, hannu ta d'ora a kai tana fad'in...
"Na shiga uku Mama kin cuceni, yanzu da wane ido kike so na kalli yah Umar, haka kawai kinja mana abin kunya, akan me zaki fad'i sunana kamar ba 'yar da kika haifa ba?"
Tsaye Mama ta mik'e tace "wallahi ubanki zaki ci idan baki min shiru ba, mahaukaciya kawai, dan ubanki ke ba banza ki kayi dani ba anan d'in kina can kina iskanci, shine ni kuma saina rufa miki asiri, to mu shirya d'aukar hukuncin da za'a mana, danna gama lura yarinyar nan 'yar akuya ce, ba zata tab'a sawa a fitar damu ba."
Kuka ta sake fashewa dashi tana fad'in "haka kawai na jawa kaina, yanzu ya zanyi da cikin dake jikina? kina nufin zanyi rainon cikine a magarqama kome? wallahi ni dai ban yafe ba."
Kwaf, Mama takai mata bugu a baki tana fad'in "ubanwa kike cewa baki yafe ba, ni Zubeida, ni?"
Murgud'a baki tayi ta kawar da kanta, suna haka Khairat suka qaraso, nan ta samu Papa ya hakimce yana jiran zuwanta, masu tsaron lafiyarsa ne suka sara mata alamar gaisuwa kafin ta zauna, bayan sun zauna Abdul waid yace "Khairat dama yanzu nake tunanin kiranki , saboda an samu wanda ta d'auki sarqar."
Kallon Umar Faruk tayi ta maida kallonta ga Abdul waid tace "an sameta, wacece, tana ina?"
Papa ne ya katsesu da "bana kiraki bane danna saurari haka, ina baki umarni da ki janye qarar nan sannan kisa a rufe qarar, wannan ba girmanki bane."
Kallon Papa tayi tace "amma P..."
"Amma me, kiyi yanda nace kawai."
Furzar da iskan bakinta tayi ta kalli Abdul waid da ido kawai ta masa alama, kai ya d'an jinjina yace "an gama."
Da mamaki Umar Faruk ya kalleta, shi girma da ikonta ne kawai ke qara bashi mamaki, wata takarda ya bata tasa hannu sannan ya kalli wani jami'i yace "ka fito dasu."
Da mamaki duka suke kallonsu kowa da abinda yake ayyanawa a ranshi, har suka tsaya gabansu cike da kunya dan sun kasa d'aga kai su kallesu, da qyar Umar Faruk yace "Zubeida, dama da ha...."
Papa ne yace "tunda kun sansu , kuyi hak'uri ku koma gida, bai kamata kuyi magana anan ba."
Kai kawai Khairat ke girgizawa yayin da Ruk'ayya ta rik'e baki, tsaye ta mik'e ta nunasu da hannu tace "na tabbata izuwa yanzu kun gama fahimtar abin kunyar da ku kayi, kunci albarkacin mahaifina wallahi, badan haka ba da sai kun gane shayi zalla ruwane, amma duk da haka nasan kun gane wacece ni, kuma in halinku ne nasan zaku koma, a wannan lokacin kuma zan muku d'aurin da goro ma saiya fiku kyan gani, daga qarshe kuma dole za'a shiga tsakanina daku, danna tabbatar ba alkairi kuke nema dani ba, kamar yanda jikina ke bani ba kun d'auki sarqar bane dan kawai ku siyar, ina fatan zaku gyara halinku in kuma hakan yaci tura to da fatan zaku kiyaye qara yiwa Khairat sata a karo na biyu."
Da harara ta bisu tare da tsaki ta fice daga wajen, Abdul waid ne ya bawa Umar Faruk sarqar yasa aljihu, bin bayanta sukayi shi da Ruk'ayya, Papa ma tashi yayi ya wuce da qyar suka rarrafa suka fita daga wajen, tun a bakin titi Zuby ta fad'awa Mama abinda ya faru bayan tafiyar Khairat gida, a wahalce Mama tace "muje gidana."
Taxi suka hau ta ajesu gidan Mama, suna shiga sukayi zaune kamar kayan wanki suna jajantawa kansu, Mama ce tace "ashe haka yarinyar nan take?"
"Humm, ai bata da mutunci ko kad'an."
Kafin Mama tayi magana Zuby tace "bama wannan ba, nifa akwai wasu maganganu da yarinyar ta fad'a min a ranar sun d'aure min kai sosai, amma nasan ke zaki sansu."
"Wace magana?" cewar Mama tana neman cire riga dan tayi wanka.
Maganganun da Khairat ta fad'a mata ta maimaita mata, cak Mama ta tsaya da cire rigar da take, da sauri ta juyo ta kalli Zuby ta kafeta da ido, ta kasa d'auke idonta kuma ta kasa magana, saida Zuby ta d'aga murya tace "Mama."
Zabura tayi ta sake kafeta da ido, "lafiya Mama?"
A hankali ta girgiza kai tace "ba komai, bara na fito daga wanka saiki tafi gidanki."
Harta d'ibi ruwa ta shiga bayi jikinta ba qwari, saida ta fara kwararawa kanta ruwa ta dawo hayyacinta, *wacece Khairat, ya akayi tasan sirrin dako 'yan uwanta basu sani ba, taya tasan wannan sirrin? shine dai kad'ai nasan abinda na aikata wanda nake tsoron duniya ta sani, inba shi ba me Khairat take nufi???* wannan sune tambayoyin da takewa kanta harta fito daga wanka, Zuby ma tattarawa tayi ta kama hanyar gida, da sand'a ta shiga gidan dan ba zata iya had'a ido da kowa ba, d'akin Mama ta nufa kai tsaye ta samu ta kwanta.
Khairat kuma daga nan gida suka dawo saboda takaici da zulumin abun, Ruk'ayya da Umar Faruk kuma babu wanda ya fad'i maganar a gida, d'aki take kwance tana karatu dan yanzu shi kad'ai ne ke cireta damuwa.
Ana sallah magrib kuma Mama tasa Zuby ta shirya tace ta koma d'akinta, ba gardama ta shiga ta hakimce tana sabgar gabanta, Umar Faruk na shigowa bayan sallah isha'i yaga d'akin bud'e da alama qarara tana ciki, wata shegiyar qwafa yayi ya cire belt d'inshi ya tunkari d'akin........
_Wallahi nima gidana zanje, wannan hushi haka Umar Faruk_π
*Kuyi hak'uri da rashin cika alk'awari da nayi jiya, hakan ya faru ne saboda daukewar da wata tayi ina cikin typing.*
23/08/2019 Γ 12:51 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
*Allah Ka qara mana tsoronka*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
5⃣1⃣
Daf da zai shiga d'akin Mama ta kira sunanshi, juyowa yayi yaga Mama tsaye a k'ofar d'aki, b'oye belt d'in yayi ya nufi wajen Mama, sunkuyawa yayi har qasa yana fad'in "gani Mama."
Saida ta shiga d'aki yabi bayanta daga tsaye tace masa "na mayar maka da matarka, dan Allah bana son jin wata hayaniya, kayi hak'uri da duk abinda ya faru, kaji?"
Jim ya d'anyi kafin yace "shikenan Mama."
Tsaye ya mik'e zai fita ta sake cewa "azumi ke tahowa,amma banga kana shirin tarbansa ba kamar yanda kake kowace shekara."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "ina tune Mama, insha Allah za'a fara gudunar da komai kamar yanda ake kullum."
"To shikenan, Allah yayi albarka."
"Ameen, saida safenku." ya fito daga d'akin.
Saida ya harari d'akin ya wuce d'akin Khairat, tunda ba za'a barshi ya mata shegen duka ba, gwara ko hukunci ya mata wanda zata san ta b'ata masa rai, tsakiyar gado take ta mike qafafu ta jingina bayanta ta rufe da zanin rufa tana karatu ya shigo, bayan amsa sallamarshi ta bishi da "sannu da zuwa."
"Sannu." kawai ya fad'a ya fara cire kayan jikinshi, douche ya shiga yayi wanka sannan ya fito, wando iya gwiwa yasa ya feshe jikinshi da turare ya haura kan gadon, computernshi dake gefe ya d'auka ya fara aikinsa, ganin shiru babu mai magana yasa Khairat cewa "baka jin yunwa ne?"
"Ya zanyi idan ma ina ji, wa nake da da zai bani abinci naci?" shine abinda ya fad'a ba tare daya kalleta ba.
Jaye zanin rufan tayi ta fita daga d'akin, tununya ta d'ora a gas sannan ta shigo ta d'auki indomie ta dora mishi, ba jimawa ta gama dafawa ta juye a plate ta kawo masa, saida ta janyo tebur d'in har gabanshi ta aje masa, ruwa ta d'auko da lemu mai sanyi ta aje masa, kallonshi tayi ganin ko kallonta bayayi tace "bismillah yallab'ai."
Abinda bata sani ba, kaf kai da kawowarta a idonshi tayashi, ya kuma kalleta ne da idon rahama da qauna, aje computer yayi ya sauko da qafafunshi, cokalin ya d'auka yana kallonta yace "kefa?"
Kai kawai ta girgiza alamar a'a, fuska a d'aure ya janyo hannunta ya zaunar da ita akan cinyarshi, kafeta yayi da ido yace "me yasa ba zaki ci ba?"
"Naci abinci tare da Ruk'ayya." ta fad'a tana kawar da kai.
Hannu yasa ya juyo da hab'arta yana kallon fuskarta yace "Khairat, bansan da wane baki zan baki hak'uri ba, amma ina baki hak'uri daga gaba d'aya zuciyata."
Kallonshi tayi cike da yanga tace "manta kawai ya wuce, hakan da sukayi aiya nuna nice a samansu."
D'an lumshe ido yayi kafin ya bud'e ya fara cin indomien ba tare daya d'agata daga cinyarshi ba, yana ci tana shafar qasumbarshi kamar daga sama sukaji qarar Zuby.......
Tsakin da Umar Faruk yayi yasa Khairat kallonshi tace "yadai, kasan meya faru ne? kaje ka duba."
"Meye fa idan ba iskanci ba." ya fada yana ci gaba da cin abincinshi, itama sherewa tayi saida yaji hayaniyar mutane sannan ya d'auki singlet yasa ya fito, ganin mutane a k'ofar d'akin nata yasa ya qarasa cike da takon izza, Mama na ganinshi tace "ka d'auko makullin mota ka kaita asibiti, ina jin fa tayi b'arine."
Ba zaice yaji dad'i ba amma dai yasan baiji zafin barewar cikinta, dan a halin yanzu baya ma buqatar had'a zuri'a da Zuby, juyawa yayi a kasalance ya koma d'akin Khairat ya sanyo doguwar riga ya d'auko makulli ya fito, Khairat ma dai lek'owa tayi taga tanata birgima tana dafe ciki, sosai taji tausayinta lokacin da Mama Sa'a da Mama suka kamata zasu fita taga jini ya b'ata mata jiki, cike da rashin jin dad'i ta girgiza kai ta koma d'akinta, tana komawa d'aki ta kwanta ruf da ciki ta janyo computer Umar Faruk tana kallon aikin daya fara, kamar da wasa saita fara dora mishi tata fasahar zanen, bata daina ba har saida ta gama, kallon sabon sanfurin zanen takalman tayi tayi dariya, dan a ganinta babu abinda zaiyi dashi, bacci ne ya fara fizgarta har tana gwara kai ga computer, sulalewa tayi ta aza kanta daf da computer yayin da hannunta ke saman ceybor d'in, cikin kuskure saiko Khairat ta aika da sakon a shafin yanar gizo na compagnien da yake ma aikin.
*************
Koda suka je ma wankin ciki aka ma Zuby dan ciki kam ya b'are, duk wasu kudade da aka caza saida ya biya sannan yace zai koma gida, tunda dai ance saida safe a sallmeta, Mama bata hanashi ba tunda babu abinda ya rage Zuby kuma bacci take, amma koda aka kira Mama aka fad'a mata ta garzayo tazo, abin mamaki ko kallon Mama ba tayi ba wai ita tana hushi saboda bata je ta ganota ba, haka ma Umar Faruk bata kulashi ba kamar yanda shima bai kulata ba, Mama Sa'a kad'ai ta tambaya yanda ake ciki, ana fad'a mata tace su tafi gida ita zata zauna wajenta, hakan kuma ba qaramin dad'i ya musu ba, dan haka Umar Faruk ya dawo dasu.
*****************
A hankali ya shiga d'akin da sallama d'auke a bakinshi, da murmushi ya qarasa wajenta ya zura hannu zai gyara mata kwanciya, cak ya tsaya yana kallon computer dake gabanta da tsananin mamaki, d'aukar computer yayi danya tabbatar da abinda idonshi ke gane mishi, ai kuwa dai gaskiya idonshi ya nuna mishi, sanfurin daya aika an karba kuma ana tayashi murna, tare da turo mishi adadin wasu manyan kud'ad'e a account d'in daya bud'e bada dad'ewa ba, da sauri ya janyo sak'on daya tura ya gani, nan yaga sanfurin da aka tura, shi dai yasan bashi bane kallon Khairat yayi dake bacci abinta, dariya yayi ya aje computer kamar daga sama Khairat taji an d'auketa sama, cikin dubara ya azata bayanta yana juyi da ita tsakiyar d'akin,
"Wai miye haka Faruk?"
Fad'a mata yayi abinda ake ciki, itama murna ta tayashi kafin yasa tayi alwala suka dinga jera nafilfili har zuwa sallah asuba, yau kam sunyi karatu kuma yayi mamakin yanda bakinta ya fad'a sosai akan karatun, qara mata yayi sannan suka shirya dan tafiya wajen aiki, amma shi dole zai fara biyawa asibiti, suna hanya ya kalleta yace "saina biya asibiti fa."
"Ba komai." ta fad'a tana kallon gefen hanya.
Ba b'ata lokaci suka isa asibitin, a tare suka shiga ciki kafad'unsu na gugar juna, da sallama Umar Faruk suka shiga sab'anin Khairat data d'auke kai, tsaye tayi kofar d'akin ko kallonsu ba tayi ba, Umar Faruk d'in ne kad'ai ya zauna bakin gadon suna gaisawa, gaba d'aya sama sama suke gaisuwar dan kowa da abinda ke ranshi, Zabba'u ce tazo shigowa d'akin, ganin Khairat a k'ofar yasa ta shirya ta taqarqare ta bankad'e Khairat har saida ta fad'a bayan Umar Faruk dake kusanta, yar qaramar qara tayi tare da maqale wuyanshi sosai, jin a jikinshi ta fad'a yasa ta canza rik'on da tayi masa dΓ salon shafa, kanta ta zuro ta wuyanshi tana kallon Mama da Zuby da suke fuskantarta, kashe musu ido d'aya tayi kafin ta d'ago tana kallon Zabba'u wacce ke tsaye Umar Faruk ma kallonta yake, murmushi ta mata tace "sannu."
Kamar jira take sai kuwa ta shak'i wuyan hijabin Khairat ba tare data shirya ba, kamar Umar Faruk ta shaka sai kuwa yayi zunbur ya mike tare da qwaqwale hannunta ya nunata da yatsa yace "karki sake dora hannunki akan matata, marar kunya kawai, meta miki to? bayan turowan da ki kayi mata bai isheki ba saikin ci mutuncinta a gabana, to ki kiyaye ni wallahi."
Juyawa yayi ya kalli Zuby dake zaune tana kurb'an pure water yace "nasan ai kinsan laifinki, kiyi qoqari kada ki bari wani ya sake jaza miki sabon laifin."
"Kai Umar Faruk, kana cikin hankalinka kuwa, dama abinda kazo fad'a mata kenan, kuma dan wulak'anci shine saida wannan zaka zo ganinta? kawai dan kana so kaci zarafinmu." cewar Mama.
A kaurare yace "hmm , Tanti, naci zarafinku fa ki kace? ai kune kuka gama cin zarafina."
"Mu kuma, wai yaushe ka zama marar kunya fitsararre ne? nidai ba haka na sanka ba."
Saida ya rik'e hannun Khairat cikin nashi yana murmushi yace "tun ranar dana samu soyayyar gaskiya, ranar na fara banbance tsakanin qarya da gaskiya, kuma ranar na fara sanin asalin masoyiyata, ranar dana samu wacce ta dace da rayuwata, matsayina, mafarkina, da kuma burina."
Hannunta Umar Faruk yaja zasu wuce ta juya ta kalli Mama ta sake kashe mata ido, wayarta ce ta sub'uce daga hannunta ta fad'i qasa hakan yasa Umar Faruk sakinta ta sunkuya ta d'auka, da murmushin mugunta ta sunkuya ta d'auki wayar tana d'agowa ta d'ora wayar a kunne kamar da gaske tana fad'in " Hello, Bala , ka sameni office za muyi magana da kai, eh akan maganar nan ba, ok saika zo."
D'auke wayar tayi tare da juyawa ta kalli Mama data sake baki da kunne tana saurarenta, wata kafirar dariya tayi ta juyo tare da gimtse bakinta dan kar Umar Faruk ya gani, bakin k'ofar kuma suka had'e da wata matashiyar likita mai sunan *Jamila* , da farin ciki suka mik'awa juna hannu ita da Khairat suka rumgume juna, sosai suka gaisa ana gaisuwar yaushe gamo saboda an jima ba'a had'u ba, saida sukayi musayan lamba sannan suka fita, dariya na takura mata saboda yanayin da taga Mama, suna cikin tafiya Umar Faruk yace "waye Bala kuma?"
Gimtsewa tayi tace "ba komai." ta fad'a.
"Ban yarda ba." ya fad'a yana kallonta.
A tak'aice tace "wannan Alhajin da muka had'u dashi ranar."
"Waye shi?" ya sake tambaya.
Cikin qosawa tace "ba komai fa, idan da wani abu ma ai lokaci zaiyi da zaka ji."
Wayarta ta fiddo ta fara aikawa Jamila sak'o kamar haka " k'awata naso na miki magana tun acan, amma muna buqatar sirri."
Maido mata tayi da fad'in "k'awata baki da dama, ina fatan dai ta samu?"
"Sosai kuwa, wata alfarma nake nema a wajenki idan zan samu?"
"Fad'i kawai, kinsan umarninki abin bine."
"Na gode, aiki nake so kimin akan yarinyar nan dake qarqashin kulawarki."
"Ina jinki."
"Ina so ne ki rik'esu har nan da kwana biyu."
"Me yasa, meye tsakaninki da ita?"
Maida mata tayi da "ita d'in kishiyata ce, kuma tana min kallon raini, ni kuma bana so, ina so tasan wacece ni."
"Shegiya qawata, ashe zaki iya zama da kishiya? aina d'auka baki da ra'ayin auren mai mata, amma karki damu ba zai gagara ba insha Allah."
"Na gode qawata, zaki ji nauyi a lalitarki."
"Da kyau qawata, shi yasa nake sonki wallahi."
Suna gama message Khairat ta fara qoqarin tura mata da kud'i, ganin an nuna mata ba zata iya cire kud'i ba yasa tace "ban gane ba, wannan wane salon iskancin ne kuma?"
Kallonta Umar Faruk yayi yace "meya faru?"
"Kud'i zanyi transfert yanzu ana nuna min ba zan iya fitar dako sisi ba."
"Wataqila kin cinye wajen siyan sweet da kayan jiki." cewarshi ba tare daya kalleta ba.
"Haba dai, kasan nawa ke cikin asusu nan kuwa?"
Wayarshi ya fito da ita ya kalleta tare da bata wayar yace "ki turawa duk wanda kike so kuma ko nawa ki kayi niyyar turawa."
"A'a ka barshi kawai, zanje bankin naji meye matsalar."
Murmushin gefen labb'a yayi yana kallonta yace "wane banki kike ajiya?"
"Bank centrale." ta bashi amsa.
Nanma wani murmushin yayi ya fara danna wayarsa , 'yan daqiqu ya fara magana " mutumina ya kake?"
Jim yayi yana sauraro kafin yace "lafiya lau wallahi, dan Allah kana aikine yau?"
Nanma shiru kafin yace "zan turo maka da lambar wani asusu ina so nasan nawa ne a ciki, dan ana so a cire kud'i bayayi, ina so nasan meye matsalar."
Jim ya d'auke wayar daga kunnanshi ya bata wayar yace tasa lambar asusun, tura mishi yayi bayan wasu mintina ya sake kira, nan ya fad'a masa mai girma Mani Bukar ne yasa aka rufe asusun, take ya fad'awa Khairat yanda ake ciki, waya ta ciro tana dannawa Umar Faruk yace "me za kiyi?"
"Papa zan kira." ta fad'a a tak'aice.
Fizge wayar yayi yace "ba yanzu ba, tunda ki kaga sunyi haka to da dalili, ki sarara musu dan Allah."
Dole ta hak'ura badan taso ba, da haka suka isa ma'aikatar, kowa mazauninshi ya nufa amma Khairat ta kasa samun sukuni saboda abinda Papa yayi, bata tab'uka komai ba har lokacin tashinsu yayi, tare da Umar Faruk suka koma gida, alwala yayi ya wuce masallaci, saida yayi sallah isha'i ya dawo kai tsaye wanka ya shiga, tunda Khairat taga haka tayi niyyar babu inda zaije, dan haka yana gama shiryawa ya rumgumeta yace "zanje asibiti na dawo."
"Saika dawo." ta fad'a a qasan maqoshi.
Zai tafi ta rik'e hannunshi......
_Anya kuwa zai tafi?_
23/08/2019 Γ 12:51 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
5⃣2⃣
Ta had'e bakinsu waje d'aya, salonta ta fara masa wanda yasa ya manta komai dake gabansa ya biye mata, take ta lula dashi wata duniya har suka fad'a kan gado, nan dai naji ya fara karanto wannan addu'ar mai kayar min da gaba, da gudu na fito daga d'akin na barosuπ♀π♀π♀.
***************
Tun bayan fitarsu Khairat Mama tasa gyalenta ta goge gumi, a ranta kuma tace "nifa nayi mamaki, tabbas yarinyar nan tasan Alhaji Bala, to amma meye tsakaninsu da ita da har take kiranshi da Bala haka ba girmamawa? kodai itama karuwarsa ce, wata zuciyar ta fad'a mata."
Zuby ce ta katse mata tunani da "ni dan Allah suzo su sallamemu naje gida, wanka ma nake so nayi."
Kallonta tayi amma ba tace komai ba, Zabba'u ce tace "kiyi hak'uri mana zasu sallameki ai."
Sai lokacin Mama tace "nima dai na matsu, dan yanzun haka akwai abinda ya taso min mai mahimmanci."
Zuby ce tace "Mama badai wajen malam zaki koma ba?"
A fusace tace "eh wajenshi zan koma saime? ba dole naje ba, ke baki ga abinda ya faru bane kuma yake shirin faruwa."
"Kamar me kenan?" cewar Zuby.
"Mtsssss." tsaki kawai tayi ta shareta Zabba'u ce tace "to ai qwara aje wajen malam, dan ina tsoron kar karuwar can tasa miki hannu a cikin zubewar cikin nan."
Kallonta Zuby tayi tace "kuma fa hakane, gaskiya kam."
"Ah to fad'a mata." cewar Mama.
Jamila ce ta shigo ta fad'a musu tana buqatar sake murmurewa , dan haka sai nan da kwana biyu zasu sallameta , da farko fad'a Mama tayi saboda ba zata iya zama waje d'aya ba haka, amma da Zabba'u tace "ku kwantar da hankalinku mana, wannan ma ai hanyar samun kud'i ce a hannun yah Umar."
"Shegiya, kuma fa hakane wallahi." cewar Mama tana dariya.
_Allah ya shiryeku_
Zuba ido suke da dare suka Umar Faruk amma shiru, sai Saratu da Abbakar Baba dasu Mama ma duka sunzo amma banda shi, tun lokacin Zuby ta fara damuwa tare da kuka tana fad'in Khairat ce ta hanashi zuwa, haka dai su Uwani da suka zo suma aka rarrasheta.
_Tukunna ma Zuby, ke kika tsokano min qawata._
****************
Da safe ma saida Khairat tayi abinda yasa suka makara, hakan yasa dole suka wuce wurin aiki ba tare daya biya asibiti ba, a ma'aikatar ma bata barshi ba, basu fi minti talatin da zuwa ba tasa Habeeba ta kira matashi, yana shigowa ta taso tasa makulli a k'ofar ta zaunar dashi akan kujera, qafafunshi ta zauna ta b'alle masa botir d'in riga, yanda ta rikirkitashi yasa ya cire mata tata rigar itama, duk da a tsorace take dan bata manta wahalar da tasha ba, amma haka ta daure suka dinga....duk da komai bai faru ba amma anji jiki sosai kuma ankai maqura.
A daddafe suka kai yamma suka koma gida, kamar kullum alwala yayi ya tafi masallaci sai bayan sallah isha'i ya dawo, wanka yayi cike da kasala ya fara shiri, tun bai qarasa ba Khairat ta sauko daga kan gado ta nufi hanyar fita, yana kallonta ta madubi yana b'alla mab'allan rigarshi, saida ta saci kallonshi ta gefen ido taga yana kallonta ta madubi sannan ta dafe kai da fad'in "ahhhhh, washhh kaina."
Da sauri ya juyo yayi kanta ya rik'ota yana fad'in "baby lafiya, meya faru ne?"
Cikin lumshe ido da kasallaliyar murya hannunta dafe da kai tace "kaina ne kemin ciwo, harna fara ganin jiri."
"Ayya, sannu, zoki kwanta to." ya fad'a yana nufa da ita kan gado, a yamutse tace "karka damu kanka, zai bari yanzu."
"Ke lafiya kike? bana da hankali ne zan barki a wannan halin, kinsan yanda nake jinki kuwa?"
Kafin tayi magana ya nufi da ita kan gado ya kwantar da ita yace "bara na samo miki magani."
Shiru tayi harya bud'a drower ya fito da maganin ya d'auko ruwa ya d'agata yasa mata maganin a baki tare da kai mata ruwa, bata bari ya wuce ba ta maidoshi a jikin Umar Faruk kamar wacce ke aman gaske, rik'e rigarshi tayi ta sake yunquro wani aman kamar gaske, ganin babu abinda ya fito daga bakinta yasa ta koma ta kwanta, kallonta yake harya cire rigar yasa ya goge mata bakinta a tunaninshi amai tayi, fitar da rigar yayi ya dawo da abin gogewa ya goge na kan gado, gefenta ya zauna ya d'ora kanta akan cinyarshi yana shafarta yace "tun yaushe kike jin haka amma baki fad'a min ba?"
Da qyar kamar marar lafiya tace "ban jima da jin haka ba."
Lek'o fuskarta yayi yace " to me yake damunki, kodai akwai ajiyata ne anan?" ya qarashe da dafa cikinta.
Shiru tayi ta rufe ido ta nuna bacci harya d'auketa, jin shiru yasa ya sake kallon fuskarta, ganin tana bacci yasa yace "to, ke kuma naki mai bacci ne."
Tana jin haka ta bud'a ido tayi murmushi tana d'aga ido tana kallonshi dan tasan ba ganinta zaiyi ba, murmushin gefen labb'a tayi a ranta tace "kad'an kika gani Zuby kike ko uwar wa, zaku san dani kuke magana."
Daga haka kuma har baccin gaske ya d'auketa, saida yaga ta jima tana baccin sannan ya gyara mata kwanciya, lokacin dare yayi sosai dan haka ya kabbara sallah...
***************
Ganin shiru yau ma yasa Mama fita tace za taje ta dawo, haka ta bar Zuby ita da Zulfa'u a asibiti, daga nan kuma wajen malam ta nufa.
A gaban malam take ta fad'a mishi abinda ya faru tun washe garin ranar data bar wajenshi har izuwa yau, kwantar mata da hankali yayi kafin ya d'ora da "ke dai kinsan komai game da gidan nan, matsalar da aka samu a game da aikinmu shine wannan tsaron dake cikin gidan, abu d'aya da zakiyi yanzu shine, da zaran yarinyar ta fita daga gidan ki gaggauta kirana ki fad'a min, ta haka zamu samu sauk'in yin nasara a kanta."
"To amma malam aiba gidanmu guda ba, taya zansan ta fita?"
" xYarki ba gidan take ba? ki fad'a mata ita saita fad'a miki idan ta fita."
"To shikenan malam, za ayi komai." da haka ta baro wajen malam ta dawo asibiti, koda ta tambaya yazo akace a'a, masifa ta fara asibitin tana fad'in ya rainata ma.
************
Shi kuma yana gida ko fitar baiyi bama shima mutan gida sai kula da Khairat ake , dan gaba d'aya ya fad'a musu bata da lafiya, kowa na tunanin itama ciki ne a kwasa,shi yasa kowa ke bada gudumuwarshi , sai bayan sallah azahar ta nuna ta warware babu abinda ke damunta, amma duk da haka Umar Faruk bai barta har saida akayi sallah magrib, a lokacin ne Khairat ta buk'aci Zuby ta dawo gida, sai dai tana jin kunyar tama Jamila magana ba tare data tura mata kud'in nan ba, dan haka ta kalli Umar Faruk tace,
"Baby."
"Na'am baby, me d'an baba yake so?"
Murmushi tayi tace "ba komai, maganar kud'in nan ne da zan tura, ina buqatarsu ne kuma bansan me nawa Papa ba ya rufe min asusu na."
Wayarshi ya mik'a mata yace "gashi kisa lambar saiki aika."
Karb'a tayi kuwa ta tura iya wanda tayi niyyar tura mata, ganin hankalinshi baya kanta yasa ta duba lambobin daya kira ko suka kirashi, cikin sauk'i ta samu lambar Zuby a wayar, saida ta d'auka a wayarta sannan ta bashi wayar, fita yayi dan sallah isha'i dan rabon daya dawo irin wannan lokacin harya manta, saida tayi sallah tana zauna ta dannawa Jamila kira tace a sallami Zuby, saboda taji nauyi a lalita yasa yace "an gama hajiyata."
Suna gama waya ta kira lambar Zuby, Zuby na zauna taga baquwar lamba, d'auka tayi ba tayi magana ba, "Hello."
Yanda muryar ta daki kunnanta yasa har saida gabanta ya fad'i, kafin tace wani abu Khairat tace "Zubeida, kiyi hak'uri da rashin ganin mijina a asibiti, kar kiga laifinshi indai kina da wayo, mahaifiyarki ce ta fara tsokanoni, a qarshe kuma sai kika nuna min kina so mu fara siyasa a cikin zaman namu , da wannan nake so na nuna miki cewar, ni jinin siyasa ce kuma na gajeta ne ba kamar ke ba da tsinta kawai ki kayi a hanya, bara na nuna miki kad'an daga cikin ikona, yanzun nan za'a sallameki daga asibiti, dan nasan kuna tunanin an ajeku ne kawai, to nice nan nasa aka rik'eku, zai iya yiwuwa ba ara miki mijina yazo ya d'aukoki, bye bye."
Tana kashe wayar ta tuntsire da dariya tana fad'in "waya fad'a miki barno gabas take, turnuqu fad'an iblisai, yaro bai gani ba balle ya raba, da uwarki ma a shirye nake nayi kishi bare kuma ke."
π€Έ♂π€Έ♂π€Έ♂π€Έ♂π€Έ♂π€Έ♂
Cike da jin haushi Zuby ta buga wayar a qasa ta fashe, a tsorace Mama ta kalleta tace "ke lafiya, meye haka dan ubanki?"
Kallon Mama tayi zatayi magana sai kuma ta fashe da kuka, da qyar ta tsagaita da kukan ta fad'awa Mama abinda tace mata, dafa kafad'arta tayi tace "kwantar da hankalinki, zamu je gidan ai wallahi sai Umar Faruk d'in ya raina kansa."
Tana cikin daddab'ata wani namiji ya shigo shiya sallamesu, tattara kaya sukayi suka fito daga cikin asibitin......
**************
Lambar Jamila ta kira amma kafin ta d'auka saita katse kiran, hakan yasa Jamila maido kiran kuma ta dauka, cewa tayi tayi hak'uri ba ita taje kira ba, *anya ba wani abu a game da kiran nan* suna kashe kiran tun kafin ya shigo Khairat ta kirashi a waya, yana d'auka tayi fuska tace "dama qawar nan tawace ta kirani waina fad'a maka kaje ka d'auko marar lafiyarka, an sallamesu kuma sun kasa samunka a waya."
"Amma ai wayata a kunne take." ya fad'a da d'an mamaki.
"To nidai haka ta fad'a min, kaje kawai saika dawo."
"Ok to, ki kula min da kanki da babyna."
"Ina babyn yake?" cewar Khairat.
Dariya yayi yace "bari na dawo zan nuna mikishi."
"Allah ya tsare, saika dawo."
"Ameen." ya amsa ya shiga mota dan dama da makullinshi a aljihu, ita kuma goge kiran da tawa Zuby tayi da wanda tama Jamila, amma bata goge wanda Jamilar ta mata ba da wanda tama Umar Faruk.
************
A k'ofar asibitin ya samesu suna jiran taxi, tsayawa yayi gabansu harya fito, "sannunku." kawai ya fad'a, kayansu ya d'auka yasa ciki sannan ya shiga ya zauna yana jiran shigowarsu, saida suka gama wainashi sannan suka shiga motar, Zuby ce gaba Mama baya sunyi nisa babu mai magana, shirun ne yayi yawa yasa Mama cewa,
"Umar Faruk, ina kallonka mai hankali, amma gashi kana nuna min ba haka ba, me yasa kake haka?"
"Me nayi tanti?" ya tambaya cike da gadara.
"Yanzu yaushe rabon da kazo asibitin nan? saika nuna mana kai ka auri karuwa, gaba d'aya tabi ta shanyeka ta hanaka komai, inba ka sakar mata fuska ba har tana da ikon da zata kira Zuby tana fad'a mata magana, har za tace wai zata ara mata kai kazo ka d'auketa, shi yasa kazo kenan?"
D'an juyowa yayi ya kalli Mama yace "Khairat d'in ce ta kira Zubeida?"
"Eh mana, ko qarya zan mata?"
"A'a, ni bance ba, amma da mamaki."
"To shikenan, kaimu gidan saika tambayeta a gabanmu kaji."
"To." ya fad'a a tak'aice.
Suna zuwa gida ya shigo da kayansu, nan aka fara musu sannu da zuwa har Mama Sa'a da Mama sukace "shirin tafiya muke yanzu kam, amma gashi an muku sallamar dare."
"Ki tambayi karuwar surukarki, ita tasan yanda akayi tasa aka rik'emu sai yanzu kuma tasa aka sallamemu."
Kallonta Umar Faruk yayi yace "tanti ba karuwa ba dai, Khairat sunanta, idan kuma sunan na miki wuyane zaki iya kiranta da alkairi."
ππππ
"Ubanka." ta fad'a cikin hushi harda mishi da hannu.
Gimtse fuska yayi Mama kuma tace "ka fito da munafukar mana ta fad'a a gabanku kuji."
Juyawa yayi ya nufi d'akin ya sameta zaune tana karatun littafi mai tsarki, daga qofar ya tsaya yace "kizo dan Allah."
Da kai ta masa alamar to, hijabi tasa sannan ta biyo bayanshi, ganin kowa cirko cirko yasa ta tsaya kusanshi tana kallon Zuby tana fad'in "yar uwa, yanzu kuka shigo, ya jikin naki?"
Kallonta Zuby kawai take Mama ce kad'ai ta samu damar yin tsaki, Umar Faruk ne ya kalleta yace "alkairina, akan me kika kira Zuby kika fad'a mata magana har kina cewa zaki ara mata ni."
Da sauri ta bud'e baki tana kallon kowa dake wajen da tsantsar mamaki, cike da rainin hankali tace "baby, nice na kira Zuby, akan me kuwa zan kirata, ina na samu lambarta ma?"
Maida kallonta tayi ga Zuby tace "ni d'in na kiraki, tunda muke na tab'a kiranki ne? wallahi kuji tsoron Allah ku tuna zaku mutu fa."
Mama da Zuby kasa magana sukayi sai Umar Faruk ne yace "kin gani tanti, na fad'a muku dama da mamaki, babu ruwanta da sabgar kowa."
Zuby ce dake dafe da cikinta tace "kece za kiji tsoron Allah munafuka kawai, kina nufin zaki qaryata mahaifiyata ne? ai wayarta nanan a duba kiran za'a gani. "
Ta qarasa da kallon Umar Faruk, kallon daya ma Khairat ne yasa ta nuna mishi d'aki tace "tana d'aki, ka d'auko da kanka ka duba."
D'akin ya nufa Khairat kuma ta kalli Mama tace "da kike cewa mahaifiyarki zata min qarya, ita littafi mai tsarki ce da ba za tayi qarya ba, ta aikata laifin daya fi na qarya ma bare kuma wannan."
Kallon Mama Zuby tayi ta kalli Khairat tace "me tayi? ki daina kwalo kwalo ki fito ki fad'a mana in kina da gaskiya."
Matsawa kusan Zuby tayi tace "Ina ruwanki to da zaki ce ta fad'a, karna sake jin bakinki."
Fitowar Umar Faruk yasa sukayi shiru suna kallonshi, saida ya gama duba kiran sannan ya bawa Zuby wayar yace "duba ki gani, kiran da qawarta ta mata ne ta fad'a mata naje na d'aukoku, sai kuma kirana da tayi ta fad'a min, amma duk da haka kike neman d'ora mata laifi."
Saida Khairat ta maqale hannunshi ta d'ora kanta akan kafad'arshi tana kallon Zuby tace "Allah yasa zata gane idan ba asarar kud'inku ku keyi ba kuna zuba mata ecole d'in."
Mama Ruk'ayya Mama Sa'a Umar Faruk harma da Mama Maimuna dariya suka saka, aida bak'in ciki ya taso mata sai kuwa ta buga wayar qasa itama, a take wayar ta fashe ita kuma ta dora "sai dai dukanmu muyi asara, shegiya kawai."
Juyawa tayi zata nufi d'akinta Khairat tace "wallahi ina rabaki da yawan kiran wani shege, zafa ki iya jin kunya a qarshen al'amarin, kuma waya da kika fasa mijinki ne zai biyani."
Maida kallonta tayi ga Mama tace "ki fad'a mata komai ko zata daina kirana shegiya, inba haka ba wallahi da kaina zan fad'a mata komai."
Itama d'akinta ta shige ta barsu nan, Umar Faruk kuma daukar wayar yayi yaga ta fashe sosai, yanzu dole saiya siyi sabuwaππ, haka dai Mama ta fita ba nasara Zuby kuma wanka ta samu tayi ta kwanta, d'akin Zuby ya kwana bayan ya gargadeta sosai tare da ja mata kunne, nan ta fad'a mishi itama wayarta ta fashe, cewa yayi "ke kika fasa wayarki saboda b'acin rai, kuma kika fasa ta mutane, dan haka karki d'auka zan siyo miki tsadaddar waya ce, wacce kika fasa ita zan siyo miki."
"Kenan itama zaka siyo mata wacce na fasa ne?" ta fad'a tana kallonshi.
"Sosai kuwa, wannan ai shine adalcin da kike cewa bana yi."
A haka sukayi bacci suna nesa da juna, da safe kuma ba wayoyinsu kad'ai ya siyo ba harda kayan d'inkinsu na sallah, dana gaba d'aya sauran mutanen da yasan yana musu....
_Indai Zuby ce nasan yanzu ma za tace wani abun ne_
23/08/2019 Γ 12:51 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
5⃣3⃣
Da safe Umar Faruk ya bawa kowa kud'in d'inki tare da damar tafiya kai d'inki, Khairat kuma yace ta zauna ta huta tunda bata da lafiya karta wahalar masa da babynsa, saida ya fita tace "na shiga uku nikam na jawa kaina."
Zuby ta zuba ido tana so taga Khairat ta fita kai d'inki danta kira ta fad'a, ganin shiru bata da niyyar fita yasa itama ta fita kai nata, kuma harta dawo bata ga alamar Khairat ta fita ba, dole ta hak'ura ta cire rai amma dai tasan dole zata fita koba yau ba tunda uwar yawo ce.
Saida Umar Faruk ya dawo yace Khairat ta shirya ya kaita, cewa tayi ya bari har ranar data karb'i girki saisu tafi, bai mata musu ba ya barta dan tayi tunanin abinda shi baiyi tunaninshi ba.
*Bayan kwana uku* ranar litinin kuma a ranar aka tashi da azumi, a ranar Khairat tasha wahala sosai dan saida ta tafi aiki ta dawo misalin 12:00, wanka kawai tayi da sallah ta fara aiki saboda abinda take sonyi yana dayawa, duk da ta fara da wuri kuma Ruk'ayya dasu Fateema Zeinab duk sun kama mata saida ta gaji sosai, an soya an dafa an motsa haka tayi shirye shirye sosai domin taya mijinta tarban wannan watan, koda suka gama wanka kad'ai ta fito aka sha ruwa, Umar Faruk kuma dama duka mazan sai an gama sallah isha'i suke shigowa dan daga gidan ake fitar musu da wasu daga cikin kayan shan ruwan.
Tunda ya shiga d'akin yaga abubuwan ci da sha zube kala kala ya saki baki, saida ta zaunar dashi ta fara taimaka masa sannan yace "babyna wai duk ke ki kayi wannan abun, yaushe kika zama babban qwararriyar Mai girki ne?"
"Idan ka gama ci zaka san ranar."
Hannunta ya kamo ya zaunar da ita akan cinyarshi yana kallon fuskarta yace "kenan kin wahalar min da babyna ko? gaskiya ni bana son haka, daga yau ba zaki sake aikin nan ba, kibar komai su Ruk'ayya zasu yi."
A raunane ta kalleshi tace "baby nifa bana da komai, ka daina tunanin inada ciki fa, bana da komai."
Ta qarashe da shagwab'ewa, sumbatar kumatunta yayi yace "idan ke baki tabbatar ba ni na tabbatar."
"Tayaya?" ta fad'a tana kallonshi.
"Zan nuna miki anjima." ya fad'a yana kallon tarin kwanukan dake gabanshi.
Azumi ake yayin da abubuwa sukayi dama, sai dai kullum da dramar da za ayi tsakanin Zuby da Khairat, wani lokacin dramarsu tana bawa mutanen gidan dariya, danko Baba ya gani yakan dara saboda yanda Khairat ta bala'in raina qurar Zuby, a hankalce da dubara da salo take fad'a mata magana, a qarshe sai dai ta shiga d'aki tana kuka, kullum cikin waya suke da Mama tana fad'a mata abinda ke faruwa gidan, Mama kuma tana cewa tayi hak'uri watan azumi take jira ya qare suci gaba daga inda suka tsaya, ta mata alk'awarin dole wata rana gidan zai zama mallakinta, a haka kad'ai take jin sanyi a ranta, duk da qoqarin da Umar Faruk keyi akanta bata ganinshi, Allah ya sani ya saba da irin rainon Khairat hakan yasa idan yazo d'akinta yake sa ran samun irinsu, amma sam baya samun damar hakan kuma idan ya buqaci ta bashi jikinta kawai shiya juyata bata yarda, dan haka ya gama lura ita d'in mace ce da bata damu da wasanni ba, ita dai kawai kaje mata lokaci d'aya, abin haushi kuma da an fara haqar rijiyar sai tace ta gaji ko gaba d'aya ba'a haqa ba, zuwa yanzu kam badan haqqinta ne ba daya daina kusantarta , tunda dama ba wani abu yake jiba (π a dauri kashi ko a b'ata igiya), ita kanta idan ta zauna tana jinjinawa qoqarinshi, matsalar d'aya shine tana ganin kamar yafi nunawa Khairat soyayya, alhalin Khairat ko bai tab'a jikinta ba ita zata kai ga jikinshi, hakan yasa take ganin kamar yafi sonta ne.
*Kwana sha biyar* da fara azumi Papa yayi aike gidan, mota guda aka aiko ta dinga sauke kayan abinci babu abinda babu, bugu da qari harda shaddodi da atamfofi, saida aka gama shigowa dasu kuma driver ya ciro enveloppe ya bawa Mama yace abawa malam inji mai girma baban Khairat, godiya dai kan anshata kuma shima yaji tukuici sosai, Khairat ma na d'aki bata san me ake ba, tana can tunanin bayin Allah da take taimakawa ya dameta, bata san a wane hali suke ba yanzun, gashi yanzu mahaifin nata na mata wuyar samu ko a waya saboda waya da harkoki suka masa, sai lokacin Fateema ta shigo ta kirata, fita tayi taga kayan ta tayasu murna.
*A gurguje fan's*
Haka suke tafiyar wa rayuwar, idan yana d'akin Khairat yana farin ciki, idan yana d'akin Zuby qorafi da fad'a suke takura masa, haka kuma har yanzu zaman na Khairat da Zuby ba dad'i, yayin da Khairat keta qunsawa Zuby baqin ciki kala kala, kullum da sabon tuggun da take zuwa mata dashi, kuma har yanzu sun kasa samun nasara a kanta saboda sau d'aya ta fita taje gida wajensu Papa tare da Umar Faruk, har yanzu bata sake fita ba har Umar Faruk d'in kanshi yana fad'in taje takai d'inkinta amma tak'i takai, kuma tak'i tafiya ne saboda tana da d'inkin da zata iya sakawa ranar sallah, gashi kuma Zuby har yanzu ta kasa sakewa da Umar Faruk kamar ba mijinta ba, (mutan da).
Alhamdulillah rayuwa sauyawa take, Umar Faruk alert kawai yake ji hankali kwance, ga kuma albashin aikinshi shima yana samu, da wannan yanzun haka ya fara qoqarin kafa kanshi ta hanyar kama wani babban shago yana zuba takalma da jakunkuna wanda ake bugawa a wannan compagnie dana Khairat, duk da dai burinshi shine shima ya samu nashi ma'aikatar da zai fara buga nashi takalmin, komai na tafiya daidai saboda yana samun albashi mai tsoka sosai, da wannan arzik'in Umar Faruk ya fara bunqasa.
*RANAR JAJIBIR*
Saniya Umar Faruk ya yanka ya rabawa masara qarfi, bayan ya wadatan gidan da kajiπda zabi, bayan sallah la'asar ya shiga d'akin Khairat ya samu tana kuka abinda ya jima bai gani ba a tare da ita, bayan rarrashinta da yayi ya tambayi me yake faruwa, cikin muryar kuka ta fara magana "Faruk bansan ya zanyi ba, bansan me nawa Papa ba ya hanani samun kud'i tako ina, Faruk ina jin kunyar su Mama saboda na kasa musu komai a bikin sallah, akwai mutane da dama wanda nice ke taimaka musu a wannan lokacin, nasan wasu zasu je gida nemana su samu bana nan, wasu kuma kirana a waya amma kunya ta kasa na d'auka dan babu abinda zan iya yi musu, dan Allah kaje ka bawa Papa hak'uri ka fad'a mishi ya taimakawa duk mutanen da yasan ina taimakawa, wallahi bana jin dad'i."
Rumgumeta yayi jikinshi yace "yanzu akan haka kike zubar min da hawayenki? nifa na tabbatar babu abinda kika yiwa Papa, wataqila wani horo ne yake so ya miki, amma karki damu zan bashi hak'uri insha Allah, yanzu ki fad'a min nawa zai isheki biyan duk buqatun nan da kika zayyana?"
Girgiza kai tayi tace "a'a Faruk, ka barshi kawai, ba zan yarda ka tauyeni ba akan me zan yarda ka tauye wata, da ni kad'ai gareka zan iya fad'a maka haka tun tuni, kuma kud'i ne masu yawan gaske dani kaina bansan nawa nake kashewa ba a kowane wata, ka barshi kawai."
"Kenan har yanzu bamu zaman d'ayan da komai nawa naki ne, kuma komai naki nawa ne?"
"Ba haka nake nufi ba, amma dai..."
"Amma me? dan haka dole ki fad'a min."
"Wallahi ni ban sani ba, kawai ka barshi kamar yanda na fad'a maka, zanfi jin dad'i idan ka gano min laifin da nawa Papa."
Tabbatarwa da yayi ba zata fad'a ba yasa ya tashi ya bud'a wradrob d'inshi ya d'auko daurin kud'i yazo ya mik'a mata, kallonshi tayi ta fara girgiza kai hakan yasa ya d'aure fuska yace "ranki fa zai b'ace."
Turo baki tayi gaba ba tare data karb'a ba, d'aga hannu yayi kamar zai mazgeta yana fad'in "zan gabjeki wallahi."
Da sauri taja baya tana fizgo kud'in daga hannunshi, "nifa wallahi bana ssss.." bata qarasa ba Yusuf ya shigo d'akin da sallama cikin murya irinta yara, amsawa sukayi Umar Faruk ya d'aukeshi yana fad'in "babban mutum ya dai, ya azumin?"
Baiko kulashi ba sai Khairat da yake kallo yana fad'in "aunty Mama na ciyanki."
Cikin dariya ta aje kud'in hannunta akan gado ta tara hannu ta amsheshi duk da ba qarami bane tana fad'in "Mama ke kirana?"
"Eh." ya fad'a, hanyar fita ta nufa tana fad'in "to muje."
Umar Faruk ma bayansu yabi shima, suna fita suka samu Papa ne yanzu ma yayi aike, naman jajibir ne mai tarin waya da kuma kud'in cefane na sallah, yaron da aka aikone ya kalli Khairat ya bata enveloppe biyu yace "Alhaji ne yace abaki keda yar uwarki."
Bata tankasa ba harya fita su Umar Faruk yabi bayanshi dan bashi tukuici, kallon enveloppe d'in tayi taga d'aya sunanta ne a baya da signature d'in mahaifinta, d'aya kuma sunan Zuby ne nanma da sa hannun Papa, tasan akwai dalilin da yasa ya saka suna, ba kuma zai wuce adadin kud'in ne ya banbanta ba shi yasa ya raba musu, da Yusuf a jikinta ta qarasa inda su Zuby ke aiki ita dasu Saratu ta mik'a mata ba tare data mata magana ba, a wulaqance ta kalleta tace,
"Miye wannan d'in?"
Itama a daqile tace "ki karb'a mana saiki duba ki gani."
Saida taja tsaki ta karb'a tana kallon sunan da aka rubuta, kallonta tayi tace "wai miye wannan iskancin?"
A hassale Khairat tace "ba iskanci bane, mahaifina ne yace a baki, kuma na tabbata yayi hakane saboda yana kallonki a matsayin 'yarsa kamar ni."
Wani tsaki tayi kafin tayi dariya irinta daba tace "kiji wani rainin hankali, to an fad'a miki bana da hankali ne ko kuma sakara ce ni? to bari kiji wallahi asirinku ba zaiyi tasiri a kaina ba, kuma koba komai Allah ya kiyayeni naci kud"'in haram kud'in da bansan ta wace hanya aka samesu ba."
Muryar Umar Faruk ce ta katsesu yana fad'in "waike me yasa baki da hankali ne, le kullum inba tsokano abinda za ayi tashin hankali ki kayi ba hankalinki baya kwantawa, gidan nan sai kace ni kad'ai ne mai mata kullum a masifa nake kuma duk saboda ke, ko kad'an ke baki d'auki iyaye a wata tsiya ba shi yasa baka jin kunyar aibata na kowa, to wallahi na gaji da wannan iskancin naki, nakai maqura ta qarshe dan haka ba zan sake yarda ba, ya zama karo na qarshe da zan sake jin kina mata rashin kunya, ke inma banda raina mutane da ki kayi ba itace gaba dake ba a komai, amma kuma tana hak'uri dake bata miki cin kashin dake kike mata, to wallahi kashedi ne na qarshe wannan, in baki ji bari ba zaki ji a jikinki ma ba hoho ba, yar rainin hankali kawai."
Yana fad'a ya juya ya fita daga gidan, Khairat ma da yau takai maqura matsowa tayi kusan Zuby tace "ina da yaqini akan mahaifina cewa baya tab'a anfani da dukiyar daba tasa ba, sanin kowa ne da arziqinshi ya shiga siyasa, bawai yayi kud'i bane bayan ya fara siyasa, kin jima kina cin zarafina amma ina d'aga miki qafa, ki sani yau kin kaini qarshen da ba zan iya hak'ura ba, ya zama dole na nuna miki kuskurenki Zubeida, dole ki gane baki da wayo a duniyar nan, wallahi saina nuna miki banbancin dake tsakanina dake, Zubeida inhar bansa kinji kunyar mutanen gari ba ki canza min suna, Zubeida inhar gobe bansan kin kasa kallon kowa na gidan nan ba kice ni ba yar Na'ima bace, Zubeida inhar bansa kika kika tuhumi mahaifiyarki ba kice da zina Mani Bukar ya haifeni, wallahi gobe i warhaka ba zaki gane halin da kike ciki ba wannan alk'awarina ne."
Aje Yusuf tayi tasa hannu ta share hawayen da suka taho mata masu zafi tana kallon Zubyn, da k'arfi ta fizge enveloppe d'in dake hannnunta ta nunata da ita tace "saina sa kin fahimci haramcinki tafi haramcin da kike tunanin kud'in nan na d'auke dashi insha Allah, wallahi zaki gani za kuma ki gane kurenki, daga gobe zaki fara tunani kafin ki zagi asalin mutum ko ki masa rashin kunya, banza kawai da baki san inda duniya tasa gaba ba."
Tana fad'a ta juya ta shiga d'aki, aje enveloppe d'in hannunta tayi ta d'auki wayarta ta dannawa Bala kira, yana d'auka cike da girmamawa yace "ranki shi dad'e, barka da warhaka."
A tak'aice tace "barka Bala."
"Hajia ya hidima damu , ya k'ishin ruwa?"
"Alhaji Bala magana nake so muyi da kai."
"To to Hajia, ai lokacina gaba d'ayansa naki ne, ina jinki."
Ajiyar zuciya ta sauke tace "kullum kana fad'a min girma da matsayin da nake dashi a wajenka, wani aiki ne nake so kamin a matsayin alfarma idan zaka iya."
"Hajia, aiba alfarma tsakaninmu, ki bada umarni kawai aikina cikawa ne."
"Na gode, Bala kasan me nake so dakai?"
"A'a Hajiata sai kin fad'a."
Juyawa tayi ta kalli kanta a madubi tace masa " lokaci yayi da ya kamata ka waiwayi ajiyarka da kayi shekarun baya, ina so ka amshi 'yarka dake hannun Asma'u."
Jim yayi kafin yace "Hajia hakan nada alaqa da alfarman da zan miki ne?"
"Hakan da za kayi taimakone bawai alfarma ba, Bala yarka na takura min sosai ta hanyar aibata min mahaifina kullum, ba wai burina na muzguna mata ba, danni ina da tabbacin nafi soyuwar a zuciyar mijinmu , idan so samu nane ina so mu zauna lafiya da ita, amma ita kullum cin zarafin iyayena ne burinta, kuma abinda za kayi bawai zaisa tabar gidan nan bane, kawai ina so ne ka fito a matsayin mahaifinta na gaskiya."
Shiru ya sake yi sannan yace "Hajia wannan ba matsala bane, a gaskiya bata kyauta ba kuma banji dad'i ba, kuma na tabbata hakan na faruwa ne ta sanadiyar mahaifiyarta, dan Asma'u ba mutumci ne da ita ba, amma karki damu Hajia zanyi abinda ki kace bawai a matsayin taimako ba, a'a sai dan na taimaki kaina da kuma ita yarinyar, lokaci ne yayi da zan tono shukar dana binne tsawan lokaci, kuma lokaci ne yayi da zan sadata da yan uwanta su san juna, kawai ki fad'i lokacin da kike so Hajiata."
Da wani mugun murmushi a fuskarta tace "gobe nake so."
"An gama Hajia, Allah ya kaimu goben."
"Ameen, zan fad'a maka lokaci da kuma kwatancin gidan."
Tana fad'a ta kashe wayar, dan ita dama bata bari ku dindige take kashe waya , yana daga cikin ikonta da take nunawa, wasu matasa ta kira su uku tace su sameta gida, suna zuwa ta basu wannan kudaden wanda Umar Faruk ya bata dana wajen Papa harda na Zubyn duk ta lissafa musu inda zasu kai, gida na farko data fad'a musu shine gidan Alhaji Bala, sannan sauran gidajen mutane, dama kuma yaran sune ke taimaka mata kowace shekara, suna girmamata ta yanda kiran Allah dana iyayensu ne kad'aizai hanasu amsa kiranta.
Tunda Umar Faruk ya fita bai dawo ba kasancewar daren sallah ne kowa baiyi bacci ba, mutanen gidan nata hayaniya Khairat kuma na d'aki tana tunanin hanyar da zata tara yan uwan Zuby da mahaifiyarsu a gobe, yayin da Zuby ma ke nata d'akin tana tunanin abinda Khairat ta fad'a, ganin ta kasa fahimtar komai yasa ta kira Mama ta fad'a mata, Mama ma hankalinta ya tashi sosai dan tana tunanin abinda zatayi, da tsoro da fargaba bacci ya d'auketa.
Khairat ma haka saida tayi bacci Umar Faruk ya shigo gidan, bai kuma tasheta ba sai sumbatarta da yayi ya kwanta gefenta badan yana jin bacci ba.....
*Gobe sallah, kuma gobe tonon...*π
23/08/2019 Γ 12:51 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
*Ina alfahari daku*ππ
5⃣4⃣
Kiran sallah asuba ne yasa Khairat bud'a ido, dan yanzu tana jin kiran sallah take tashin kanta, sauke idonta tayi akan Umar Faruk dake zaune yana kallonta shima, zaune ta tashi tana murza ido tana masa murmushi, cikin muryar bacci tace " kai kuma haka ake saika kasa tashina?"
A shagwab'e yace "kema kuma haka ake sai kiyi bacci ba tare da kin jira mijinki ba?"
Dariya tayi wacce bata da sauti tace "ka gafarci wannan sakaryar matar taka, har yanzu quruciya na damunta ne."
Dariya yayi yace "nadai fahimci yanzu babyna yasa kin rage bani kulawa, amma ba komai girmanshi ne ai."
Kamar zata fashe da kuka tace "baby, na fad'a maka fa banda komai, me yasa kake son tsokanata ne? ina so ko zan fara haifa maka yara sai mun qarasa cinye amarcinmu."
Yanda take maganar yasa ya janyota jikinshi ya rumgume yana fad'in "ina laifi wanda muka ci ma, ai kawai ki fara antayo minsu a shirye nake."
D'agowa tayi ta kalleshi tace "ko 'yan uku uku ne ka shirya?"
"Ai ko 'yan shida shida ne zan karb'a."
Dariya tayi ta fara qoqarin sauka daga kan gadon, da sauri ya rik'ota yana fad'in "bara na cajeki na gani, dan naga baki yarda kina da ciki ba."
Saida ta sauka da qafafunta qasa ta juyo saboda ya rik'e qugunta ita kuma ta zagaya hannayenshi a wuyanshi suna kallon juna, kallon qirjinta yake da yaga ya mishi wani b'ulb'ul ya cika sai walqiya yake kamar ta shafeshi da man gyad'a, bakinshi yasa ya janye rigarta ya cabko kan nononta ya fara tsutsa har yana lumshe ido, itama rufe idon tayi tana qara danna kanshi tana shafar kanshi, jin yana tutsa hannayenshi cikin rigar yasa ta janye tana fad'in "baby."
Kallonta yayi yace "ki tsaya mana na nuna miki kina d'auke da cikina."
"Um um." ta fad'a tana maqale kafad'a.
Hararanta yayi yace "kinsan zan gano gaskiya kenan."
"Indai ba coge kake son min ba kamar yanda ka fara min wayo a farkon zamanmu ta hanyar samun kusanci da jikina, to ka fad'a min baki da baki kawai."
Hannu ya mik'a mata yace "naji to zo kiji."
Matsowa tayi tace "ina jinka to."
Cikin wani irin kallo ya fara da "da farko dai na lura da sabon canji daga jikinki, saboda wannan kayan sun qara fitowa suna cika min ido sosai yayin da kullum suke min qwalele, sun cika fiye da baya kuma sai sheqi suke." duk yayi maganar ne yana shafarsu.
"Na biyu kuma yawan bacci da kike yanzu, ke baki fahimci hakan ba amma ni uban yaro tuni na fahimta, na uku kuma baki son cin abinci yanzu."
Dangware masa kai tayi tace "hamagon uba kawai."
Cikin dariya ya sake kamo hannunta yace "ya kuma had'u da hamagiyar uwa ba."
Tashi sukayi dukansu suka fita, alwala sukayi shiya wuce masallaci ita kuma ta dawo d'aki.....
**************
Gaba d'aya akayi girki a gidan, hakan yaba kowa damar samun shirin tafiya Eid da wuri, kowa fitowa yayi cikin shirinshi mai ban sha'awa, Umar Faruk kam cikin dogon d'inki yake na shadda kalar ruwan zuma, hula takalma agogo duk wanda suka dace da kayanshi, Zuby ma na cikin shaddar daya siya mata da d'inki kalar data dace da ita, Khairat ma fitowa tayi cikin shaddarta baqa wulik wacce aka d'inke ko ina da kwalliya, idonka kad'ai zasu nuna maka d'inkin yaji kud'i ba kad'an ba, hijabin dake jikinta baqi da takalma baqaqe kalar kwalliyar kayanta ne, tunda ta fito sanyayyen qamshin turarenta ya bige Umar Faruk da sauran mutanen wajen ma, Zuby kuma d'inki da shaddar take kallo tana tunanin ita Umar Faruk ya raina ya siyawa wannan shaddar da bata banzan kud'in d'inkin da basu kai na Khairat ba.
A motarshi su Ruk'ayya da sauran yara da kula matanshiπ suka tafi, banda tsaki da hararan mutane ba abinda Zuby keyi, Khairat kuma da angonta da sauran yara kowa zikiri ne a bakinshi kamar yanda sunna tazo dashi, a haka suka isa babban masallaci sukayi sallah, ana idawa kuma bayan taya juna murna suka d'auko hanyar dawowa gida, koda suka zo kowa ya samu waje ya zauna aka zubo abinci a manyan plate, gaba d'aya mutanen gidan ne aka taru maza daban mata daban aka ci abinci amma a waje d'aya.
Khairat kuma da tsarin ya birgeta kallonsu take cike da birgewa, Umar Faruk ma da kallonshi ke kanta suna had'a ido ya da hannun ya tambayeta lafiya, murmushi tayi ba tare da b'oyewa ba tace " ina kallonku ne, ganin kun taru gaba d'ayanku kuna farin ciki, sai naji inama ina da yan uwa nima, da yau zan tarasu gaba d'aya mu mori farin cikin wannan ranar, amma ni kad'ai, sai kuma ku dana samu a matsayin sabbin ahlina."
Mama ce ta dafa kafad'arta tace " 'yata, ki d'auka mu naki ne, dukanmu nan mun zama d'aya kinji ko."
Dariya tayi ta shafi kumatun Mama tace "na sani Mamana, nima ina kallonku kamar ahalina."
Suna haka dai aka gama cin abinci, a qa'ida mazan ma basa fita sai bayan sallah azahar, hakan yasa Umar Faruk da uwar gidansa Khairat suka shige d'aki suna lobayyarsu, saida akayi sallah azahar suka fita Khairat ta kira wayar Bala, yana d'auka tace " kana da lambar mahaifiyarta ne?"
"A'a Hajia, amma dai ina da wanda nake da tabbacin yana da lambarta."
"Ok to ka samu lambarta, idan ka kira ka fad'a mata zaka karb'i 'yarka ne." tana fad'a ta kashe wayar.
Baisha wahalar samun lambar Ma'u ba dan haka ya danna mata kira, cike da shaqiyanci yace "nasan ba zaki manta da muryar nan ba, dan haka ba buqatar fad'a miki waye ni."
A gigice Ma'u ta mik'e tsaye tace "Bala, kaine ka kirani, lafiya, me yasa ka kirani?"
"Kwantar da hankalinki ba abun damuwa bane, kawai dai ajiyar dana baki ce nake so ki maido min da ita saboda nine ubanta."
"Kai Bala ka kiyaye ni wallahi, kasan me kake fad'a kuwa? to kaji da kyau, wannan 'yar da kake magana akanta, itace 'yar daka kasa d'aukar nauyinta kuma ka manta da ita har wannan lokacin, shine yanzu dan rainin wayo zaka wani ce wai 'yarka kake so, to ka fita idona wallahi, dan dama a qufule nake da kai dan ba yanda zanyi ne na qyaleka , ka rasa wacce zaka fad'awa wannan sirrin sai kishiyar yata, wallahi ka cuceni ka cuci 'yarka mugu kawai."
"Bana kira bane danki fad'a min wannan banzar maganar, na kira ne danna fad'a miki zanje har gidan auren nata danna fad'a mata nine ubanta, kuma karki sake kirana da macuci, dan in kin kirani da wannan sunan bansan wane sunan za'a kiraki dashi ba, kuma ai kema mai laifince tunda kika aurar da 'yata ina raye, kuma da sunan wani uban bani ba."
Yana fad'a ya kashe wayar tunda umarnin da aka bashi kenan, Khairat ya kira ya fad'a mata yanda sukayi tace mishi kawai yazo gidan yanzu, kwatanta mishi tayi kafin tayi kwance akan gado tana jiran zuwan Mama.
Ai kuwa baifi minti talatin ba saiga Bala ya paka yar motarshi data sha jiki, su Sa'ad na qofar gida yasa suka masa sallama da Baba, fitowa Baba yayi suka gaisa kafin Bala ya d'ora da " malam nasan baka sanni ba, to nidai sunana Alhaji Bala, kuma nazo ne ina son ganin sarakuwarka Zubeida."
"To, Zubeida kuma, meye had'inka da ita?"
"Eh to malam babbar magana ce ta kowani, kuma zanso kamin izinin shiga ciki danna ganta."
"Amma daka fad'a min abinda ke tsakaninku ai zaifi, tunda kaga matar aurene a gidan."
"To nidai mahaifin Zubeida, kuma mahaifiyarta tasan da zuwana."
π±π±π±π±π±π±
_Kuyi hak'uri da wannan._
23/08/2019 Γ 12:51 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
5⃣5⃣
Kallon mahaukaci malam ya masa yace "uhum, malam ina jin dai kayi b'atan kaine ko? amma inba haka ba ya za kace haka."
Cewar Bala "malam, maganar nanfa tafi k'arfin tunaninka , ba kuma zaka tab'a fahimtar komai ba inba dama ka bani na shiga ciki ba."
Tsayar taxi a qofar gidan yasa suka kalli Ma'u dake fitowa a hargitse, duk da kayan sallah ne a jikinta shaddar da Umar Faruk ya bata amma yanda ta fito yasa ba zaka gane kan shirin nata ba, a harzuqe ta qaraso wajensu tana kallonsu, a d'arare tace "Bala, kenan saida kazo nan, wai me yasa kake haka, wannan wane irin tonon asiri ne dan Allah?"
"Kinga mushiga ciki ki fad'awa 'yata koni waye, inba haka ba wallahi anan zan tara miki Jama'a."
Bud'e baki tayi zatayi magana kuma sai tayi shiru, juyawa tayi ta kalli mutanen dake kai da kawowa sannan ta kalli malam daya kafesu da ido, saita nutsuwarta tayi tace "naji mu shiga ciki, amma dan Allah kamin alk'awarin ba zaka fad'a mata komai ba, zamu shiga ne kawai ka ganta."
Wata shed'aniyar dariya yayi yace " idan ganinta nake so nayi ai abune mai sauk'i, kinga fa lokacina kike b'ata min."
Malam ne ya kalleta yace "Asma'u, kiyi hak'uri da duk abinda zai faru ki d'auka yau itace ranar da dubunki ta cika, kaga malam mu shiga ciki dan ba zan yarda ku tara min jama'a ba anan."
Ganin sun shiga yasa dole tabi bayansu itama, abin haushin kuma kowa na tsakar gidan harda Zuby da kuma Khairat da bata jima da fitowa ba, gaisawa yake da mutanen yayin da malam ya janyo mishi kujera ya zauna, Bala kam ko kallon Khairat baiyi ba sai Zuby da yake kallo, a hankali yace " xyata, zo mana."
Wani kallo ta masa ta tab'e baki ta kawar da kai, murmushi yayi ya kalli Ma'u yace "ki fad'a mata nine babanta tazo wajena mana."
Mamaki ne ya fito kan fuskar kowa harda ita kanta Zubyn, Khairat kuma da farin ciki ta kalleshi tace "lah, ashe babanmu ne."
Da sauri ta taso daga inda take zaune tazo gabanshi ta mishi irin neman albarkar indiawa tana fad'in "Baba ka sama min albarka."
Jin abun yayi banbaraqwai,amma dan karya kwafsa yasa ya d'an shafi kanta yace "Allah miki albarka."
Tashi tayi zata koma wajenta ta zauna Umar Faruk da Abbakar sukayi sallama tare da Ishaq, gaishe da Bala sukayi harda Umar Faruk dake mamakin ganinshi, danya tuna shine suka had'u a shago ranar, Bala ne ya kalli Umar Faruk yace "wannan ne surukin nawa ko? masha Allah Allah yayi albarka."
Da mamaki Umar Faruk ya kalleshi yace " suruki kuma,amma bakai muka had'u da kai a....."
Khairat ce tayi saurin cewa "baby surukinka ne baka gane ba, baban Zuby ne fa?"
Maida kallonsu sukayi gareta har saida Bala ya fahimci hakan sannan yayi gyaran murya yace "bai sani bane ai shi yasa, amma yanzu kowa zaisan komai."
"Kai, wai baka da hankali ne, tashi ka fita daga gidan nan?" cewar Mama.
Zuby ce ta mik'e tsaye tace "a'a Mama barshi, nasan turoshi akayi, kuma ba kowa bace sai wannan shegiyar matar marar mutunci."
"Ke." Bala ne ya daka mata tsawa tare da tashi tsaye shima, a hassale yake kallonta idonshi har sunyi ja, ganin abin fa ba qarami bane yasa Mama tattara yaran dake wajen tace suje d'aki, Bala ne ya kalli Ma'u cikin b'acin rai yace "Asma'u, kina jin irin furucin dake fita daga bakin wannan yarinyar amma baki tab'a taka mata birki ba, yanzu wannan maganar ta dace aji ta fito daga bakinta? to kinga ni ba b'ata lokaci nazo yi ba, ki fad'a mata ko wanene ni a wajenta kawai."
Hannu biyu Ma'u tasa ta dafe ciki saboda murd'awar da yake mata, kowa kuma qura mata ido yayi yana kallo, Mama ce cike da nutsuwa tace " yar uwata, kinsan mutumin nan ne, meya kawoshi me kuma yake fad'a ne haka?"
Wasu yawu ta had'e masu nauyi da d'aci tana kallon Mama, Umar Faruk ne ya kalli Khairat yace "meye haka, waya gayyatoshi gidan nan?"
Da mamaki tace "ni kuma taya za ayi na sani, gashi a gabanka mana ka tambayeshi."
Tsaki yayi sannan ya kalli Bala yace "dan Allah malam inba wani abu mai mahammanci bane ya kawoka zaka iya tafiya."
Saida Bala ya kalli Ma'u ya kalli Zuby da Umar Faruk yace "wannan yar tawa nazo karb'a, karb'a kuma ba ina nufin zan rabaka da matarka bane, ina so ne ka ara min ita muje tare taga yan uwanta kawai."
Salati kowa ya fara dake wajen ana kallon kallo, Khairat ma bud'e baki tayi cike da irin tana mamakin nan, Zuby da gabanta ke dukan uku uku ne ta qurawa Mama ido ta kasa d'aukewa, da qyar ta d'aga qafafunta ta matso kusan Mama tana ci gaba da kallonta.
Cikin wani irin gunjin murya tace "Mama, kina jin abinda mutumin nan ke fad'a, shin da gaske ne?"
Kasa jurewa Mama tayi sai hawaye da suka taho mata, sake maimaitawa tayi tace "Mama tambayarki nake, da gaske ne abinda yake fad'a cewar ni 'yarsa ce?"
Da k'arfi ta fashe da kuka ta durk'ushe gaban Zuby tayi zaune tana rera kuka, hakan kuma ya bawa kowa tabbacin abinda Bala yake fad'a gaskiya ne, duk'awa Zuby tayi ta dafa Mama tace "Mama ki fad'a min gaskiya dan Allah, zuciyata bugawa take karta fashe."
Kai Mama ta girgiza mata cikin matsanancin kuka tace "kiyi hak'uri Zuby, wallahi ban tab'a tunanin wannan ranar zata zo ba shi yasa ban shirya mata ba, kiyi hak'uri dan Allah ki yafe min, haqiqa wannan shine mahaifinki, kuma hakan ya faru ne lokacin da nake kallon mahaifinsu Uwani ba'a bakin komai ba, amma wallahi nayi nadama Zuby na tuba."
Hawaye ne ke fitowa daga idonta amma ta kasa ko qyabta ido, lokacin da kanta yayi wata sarawa ne yasa ta kwamtsa qara mai k'arfin gaske ta qarasa zubewa wajen somammiya, ganin haka yasa hankalin kowa ya sake tashi, da gudu Khairat ta qarasa wajenta dan gaba d'aya ta manta da abinda ke tsakaninta da Zuby, zubewa tayi ta fara girgiza Zuby cike da tsoro da tunanin halin da take ciki take fad'in,
"Zubeida, Zubeida ki tashi dan Allah, ki tashi Zubeida karki mutu, dan Allah ki tashi Zubeida karki dora min laifin mutuwarki , wallahi ba nayi haka bane danna saki wani hali, kawai nayi tunanin zan kub'uta ne daga yawan aibata iyayena da kike, dan Allah Zubeida ki bud'a idonki wal....."
Bata qarasa ba Umar Faruk ya suri Zuby ya rumgume ya fita da ita yasa mota, kai tsaye asibiti ya nufa da ita inda ta kwanta kwanan baya, Khairat bata tashi daga wajen ba hankalin kowa baya jikinshi Ma'u ta d'auko tab'arya, a lokacin da Mama Maimuna ta kula lokacin tana daf da kaiwa ga Khairat, ai kuwa saita sauke wa Khairat ita akai, qarar da tayi tare da zubewa wajen yasa kowa ya kallesu, da sauri kowa yayi kansu dan kai mata d'auki, ganin ko motsi ba tayi itama yasa matan suka kamata suka sa a motar Bala aka nufi asibiti da ita, Mama ce ta fad'a mishi asibitin da zai kaisu, acan suka samu Umar Faruk da aka shiga da Zuby urgency, ganin halin da suka shigo da Khairat sai hankalinshi ya kuma tashi, ana shiga da ita itama ya fad'i zaune a qasa ba tare daya ma san ya zauna ba, cire hular kanshi yayi ya dafe kai hawaye na zuraro mishi, a hankali yake furta "inna lillahi wa inna ilaihi raju'un."
Haka yake maimatawa tsawon lokaci har aka d'auki minti talatin, babu wanda ya zauna sai Umar Faruk da baya hayyacinshi, tunaninshi matanshi da baisan halin da suke ciki, kuma babu wanda ke cikin nutsuwarshi daya damu ya rarrasheshi ma, ana haka kuma wata likita ta fito daga d'akin da Zuby take, zunbur ya mik'e yana fad'in "ya ake ciki dan Allah, tana raye?"
Kallon mutanen da suka kewayeta tayi kafin ta kalli Umar Faruk daya kawota tace "tana nan lafiya, jininta ya hau sosai, kuma ba'a son haka na faruwa dan zai iya janyo mata matsala, musamman qaramin cikin dake jikinta, dan Allah a dinga kiyayewa."
Da sauri yasa hannu ya rufe ido yana sauke numfashi, a hankali ya furta "alhamdulillah."
Jin qarar bud'a d'akin da Khairat ce ciki yasa suka sake d'unguma suna tambayar Jamila data fito daga ciki, qura mata ido kawai sukayi babu mai magana saboda murmushin dake kan fuskarta, kallon Umar Faruk tayi tace "yallab'ai zan maka albishir amma saika ban goron tukuici na."
Da mamaki yake kallonta cikin dakusashiyar muryarshi yace "matata kwance a asibiti kuma kina maganar na baki goron albishir?"
"Eh mana, saboda na gano maka tana d'auke da d'an qaramin cikinka."
Wani irin bayyanannen farin ciki ne ya bayyana a fuskarshi tare da cakumo hannun Jamila ya rik'e jim yana fad'in "ki fad'i abinda kike so zan bakishi , tabbas kin kawo min albishir mai dad'i, kuma dole na muku babbar kyauta, dan wannan daidai yake da albishir d'in haihuwar yan biyu."
Kowa na wajen dariya yake da farin ciki fal a fuska, saida ya basu tukuici duka likitocin kafin suka d'aukosu suka tafi gida, suna shiga Mama ta taso ta tarbi Zuby, hannu ta d'aga mata tace "dan Allah ki tafi bana son ganinki yanzu.", zatayi magana Mama ta dafata tace "ki barta kawai, yanzu ranta a b'ace yake, muje d'akina.", wucewa sukayi itama ta shiga nata d'akin, sai lokacin Umar Faruk ya kirasu Mamie ya fad'a musu halin da ake ciki, amma babban abin birgewa shine yanda mahaifiyar Khairat ta nuna kamar ba komai a zahiri, koda dai bata ji dad'i ba amma dai bata nuna mishi ba, fad'a mishi tayi zasu zo anjima su ganta, saida akayi sallah magrib Baba ya buqaci ganin kowa a d'akinshi, a lokacin Zuby na kwance a d'aki ta dunqule tana hawaye Umar Faruk ya shigo, saida ya tayar da ita zaune ya rumguma a jikinshi yace,
"Meye kuma na kuka yanzu, shin baki san abinda kike dauke dashi bane? yanzu fa damuwa da tunani ba naki bane, ina so ki d'auki hakan a matsayin qaddarar rayuwarki, tunda dai ya tabbata wannan ne mahaifinki to kiyi hak'uri ki d'aukeshi a matsayin mahaifinki, damuwarki kawai nake buqatar ki kawar da ita ki tayani rainon d'an gatan nan, kinji ko."
Ya qarashe yana kallon fuskarta, wasu hawaye ne suka sake gangaro mata kanta qasa ta kasa kallonshi, share mata yayi yace "haba dai, ba nace bana so ba, kina so nima na shiga damuwa ne, ko kuma kina so ki b'ata min rai ne?"
Kai ta girgiza cike da nadama da qunci tace "yah Umar taya zan daina damuwa, ai dole na damu kuma nayi kuka, wanda nake tunanin shine mahaifina yau ance bashi bane, wanda nake kallon yan uwana nasu uwa d'aya uba d'aya yau an raba alaqar zama uba d'aya dasu, yah Umar yau naji kunyar kaina dana mutane, abin baqin ciki bata hanyar aure aka sameni ba, da aure akayi zina aka samu cikina, yah Umar me mahaifiyata ta zama haka, me yasa zata lalata min rayuwa, me yasa zata cutar dani haka? yanzu shikenan ta rabani da kai."
"Ke ke." yayi saurin katseta, d'orawa yayi da "waya fad'a miki zamu rabu, ina tare dake har abada Zubeida, wannan abun ba zai zama silar dagulewar alaqarmu ba, ke baki ga yanzu ma muka sake gyara sabon zama ba, domin kuwa akwai ajiyata anan." ya qarasa da zolaya.
Murmushi tayi tace "ka tabbata ba zaka rabu dani ba?"
Kai ya girgiza mata yace "hanyar da aka sameki Zubeida ba zai shafi aurena dake ba, kuma koda baki mazaunin matata haka ta faru ai akwai aure tsakaninmu kuma zan iya aurenki, bare kuma kina matsayin matata, dan haka dan Allah kar kisa damuwar da har zata haifar miki da wata matsalar, ba zanso hakan ba kuma zan iya yin hushi dake idan kika ja mana matsala."
Murmushi ta sake yi tace "shikenan yah Umar, na daina insha Allah ba zan sake ba."
"Yawwa yarinyar kirki, tashi muje to Baba nasan ganinmu."
Hijabi tasa suka fito, a qofar d'akin yace "kije zan kira 'yar uwarki."
Da kai ta masa alamar to ta wuce d'akin Baba, da sallama ya shiga d'akin Khairat dake kwance akan qafar Mammie da basu jima da zuwa ba tare da Mamie, kallonta yake harya zauna yana kallon bandejin dake kanta, gaishe dasu Mammie yayi ya d'ora da "ya mai jikin?"
"Ah jiki da sauk'i." cewar Mamie.
"Allah ya qara sauk'i, ya kiyaye gaba."
Da "ameen." suka amsa.
Kallonta yayi yace "Khairat, Baba kesan ganinmu a d'akinshi yanzu, zaki iya tafiya?"
Ta d'an dafe kai ta tashi zaune tana kallonshi, saida ta daidaita zamanta tace "zan iya mana, muje kawai."
Tsaye ya mik'e tare da mik'o mata hijabinta tasa, hannunta ya kama suka fara takawa a hankali, suna daf da fita daga d'akin ta kalleshi tace " kuyi hak'uri Faruk dan Allah karku d'ora min laifi, nima ba'a son raina bane."
Murmushi ya mata yace "karki damu, muje."
Yana rik'e da ita har sukayi sallama d'akin suka shiga, kusa dashi ya zaunar da ita kafin suka maida hankalinsu ga Baba, kallonshi Baba yayi yace "amma ba naga mahaifiyarta sunzo ba?"
"Eh Baba suna ciki."
"To ka musu magana mana." cewar malam.
Tashi yayi ya koma d'akin ya kirasu suma dan ayi gabansu, zaune sukayi suma ana kallon kallo, Baba ne yace "to alhamdulillah kowa ya hallara, kuma ba komai yasa na taramu ba sai dan kawo qarshen matsalar data kunno mana kai, da farko ina so nasan musabbabin matsalar danta hakane zamu yaki matsalar dan gudun sake faruwar haka anan gaba."
Khairat ya kalla yace "Khairat, kinyi wata magana a lokacin da Zuby ta some wacce nake tunanin kinsan komai, shin zaki iya fad'a mana meya faru?"
Kallon Zuby tayi ta kalli Mama ta kuma kalli Umar Faruk kafin ta kalli malam ta fara magana cikin taushin murya da rawar murya tace "sanin kanku ne inhar cacar baki zai had'ani da Zubeida, to sai tasa iyayena musamman mahaifina, jiya ma hakane ya faru lokacin da Papa ya aiko mana da kud'i nida ita, bayan bata karba ba saida ta fad'a min baqar magana da banji dad'inta ba, kuma Ruk'ayya da aunty Saratu shaida ne dan suna wajen, shi yasa ni kuma naci alwashin kawo qarshen matsalar ta hanyar bayyana mata mahaifinta na gaskiya, dama kuma nasan Bala tunda jimawa, kuma shine ya fad'a min ita 'yarsa ce da suka haifa bata hanyar aure ba, shi yasa nace yazo ya karb'eta koba komai zata san mahaifinta na gaskiya."
Ajiyar zuciya malam ya sauke yace "to Zubeida kinji dalilin da yasa tayi haka, kuma inhar za abi ta gaskiya to kece kika tunzurata har tayi haka, a zahirin gaskiya ba zamu ce tayi kuskure ba, koba kamai ta taimakeki wajen sanin mahaifinki na gaskiya wanda mahaifiyarki ke b'oye miki, laifinta kawai data tona abinda bai kamata ace ta tona ba, da tayi hak'uri wataqila lokaci ne zai bayyana hakan, dan haka ina rokonku da ku gafarci junanku ku kuma yafewa juna, rashin had'a kanku da ku kaki yine ya janyo hakan, yana da kyau kusan shifa aure ibada ne, kuma qarin aure ma Allah ne ya hallata mana shi, fad'a da kuke da junanku sam bai dace ba, idan kuka had'a kanku kuka zauna lafiya, shi kanshi mijinku zaifi samun nutsuwa da kwanciyar hankali, haka kuma Allah zai qara yalwata mishi arziqinshi, dan haka ina sake baku hak'uri tare da shawartarku daku yafewa junanku dan Allah dan soyayyarku da Allah."
Kallon da yake musu yasa Khairat sauke ajiyar zuciya ta kalli Zuby tace "kiyi hak'uri Zubeida, ki yafe min? nima kuma na yafe miki abisa komai."
A cije Zuby tace "na yafe miki, nima ki yafe min."
"Ba komai 'yar uwa." cewar Khairat.
"To masha Allah, sai kuma ke Zubeida, ina so kisan abinda ya faru qaddara ce kuma jarabawa, kiyi iya qoqarinki wajen cinye wannan jarabawar, hakan zai qara hauda imaninki a wani mizani da zai qara miki qarfin imani, kuma karki saki ki kalli mahaifiyarki da wani ido dama idon rahama ba, haka shima mahaifin naki ki girmamashi dan saikin kyautata musu ne duniya da lahirarki zasuyi kyau, kiyi koyi da sahhabai da tabi'ai wajen hak'uri nuna soyayya da kuma cinye jarabawa ko wace iri ce, ki zama jarumar gaske wajen shanye abinda ke zuciyarki, kuma karki tab'a kallon Khairat da abun, hakan zaisa shaid'an ya sake galaba a kanki, kuma ki sani iyaye nada girma da darajar da babu mai ita a duniya idan kika cire Allah da manzonsa Annabi Muhammad (S.A.W)."
Sosai malam ya mata nasiha daga bisani kuma sauran iyayen suma suka tofa albarkacin bakinsu, a haka suka tashi daga zaman cike da fatan alkairi, amma fa duk abinda aka tattauna ta bayan kunnan Mama yabi ya wuce, dan tayi niyyar saita d'auki fansa akan Khairat dama shi kanshi Bala...
*Wasa farin girki*
_Ku biyoni dan jin me kuma zaici gaba da faruwa yanzun._
_Wannan sadaukarwa ne ga *Ummu Fawzan,* sama da tsawon lokaci har yau tana tambayata lafiyar mahaifiyata, wanda zaiso mahaifiyarka babban masoyine wallahi, ina sonki sister_
29/08/2019 Γ 14:33 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
*MUJI TSORON ALLAH AKAN DUK ABINDA ZAMUYI*
_Bismmilahir-rahman-rahim_
5⃣6⃣
Kwance take akan qafafunshi suna hira yana shafar kanta, bacci ne ya fara d'ibarta yanata surutu amma yaji shiru, leqa fuskarta yayi yace "wai bacci ki kayi?"
D'an bud'a ido tayi ta kalleshi lokaci d'aya kuma ta maidasu ta rufe, dariya yayi yace "lallai aiki fa ya samu."
"To shikenan tunda dai bacci kike, kinga gobe kenan ba zuwa gida gaskiya, dan ba zan kaiki ba kije kina musu bacci ba a gida."
Tunda yaji shiru ya tabbatar bacci take bilhaqqi, dan da idonta biyu da zata tashi ta fara mishi rigima, gyara mata kwanciyar yayi yana kallon fuskarta yana yawo da yatsunshi a tsakanin fuskarta da qirjinta, saida yaji bacci na shirin d'aukarshi shima sannan ya tofa musu addu'a ya kwanta yana qara matseta jikinshi kamar za'a rabashi da ita.
*************
Da safe kuma fitowa sukayi cikin shiri ita da Zuby saboda zai kaisu gidajensu ne duka su wuni, tare suka fita bayan sunyi sallama da mutanen gidan, gidan baya Zuby ta bud'a ta shiga Khairat kuma gaba, saida ya fara aje Zuby a gida ya shiga tare da Khairat dansu gaisa, duk sallamar da sukayi Mama bata amsa ba, gaisheta sukayi shima shiru ko kallo, tausayinta ne ya kama Khairat dan haka ta d'an matsa da nufin ta mata magana, da hannu ta nunata tace "karki kuskura wallahi, kinga raunin kanki yanzu zan miki wanda ya fishi, wallahi na tsaneki bani bake har abada, kuma zaki gani a cikin qwaryar cin tuwanki , bake kad'ai ba harda shi banzan Balan daya taimaka miki, wallahi saikun gane kurenku, saina nuna muku nayi nisan da bana jin kira, kuma kamar yanda banji tsoron bakin iyayena ba wallahi ba zanji tsoron bakin wasu ba, dan saina nuna muku bakin mahaifiyata na yawo dani har yanzu, zan ajiye sauran imanin daya rage mini domin na tarwatsa ratuwarki, kuma abin kunya ba gareni farau ba bare ya qare kaina, dan haka ba zan sake jin kunyar wani ko wata ba akan abinda nayi, tunda wasu sunyi fiye da abinda na aikata, kuma ki zuba ido kiga abinda zai faru, ba dai kin tona min asiri ba, to kema zan tona miki naki asirin, wallahi sai kinji abinda nida 'yata mukaji, ku b'ace min daga gida, har kai bana son sake ganinka."
Da qyar Khairat ta iya tashi ta kama hanya, Umar Faruk na bayanta shima yana tunanin abinda Mama ta fad'a, tunda suka shiga mota babu mai magana harya ajeta gida suka shiga, ba wani kuzari haka suka gaisa sannan ya barta, yana fita Khairat ba tayi nauyin baki ba wajen fad'awa su Mamie abinda Ma'u tace, Mammie ce tace ta Allah ba tata ba kuma babu abinda zata gani sai alkairi, haka dai tayi wurin ranar ba walwala ba kuzari, sai bayan sallah isha'i yazo ya d'auketa daga nan suka wuce suka d'auko Zuby, wacce itama tayi wunin ba dad'i ba walwala, gidan suka wuce suka zuwa kowace tayi d'akinta Umar Faruk kuma yabi bayan Zuby dan itace dashi, saida ya tabbatar da Zuby taci ta qoshi kafin ya nufi d'akin Khairat, duk da ba komai take son ci ba da qyar tasha yaghourt ta kwanta itama.
*DAGA WANNAN RANA* komai ya sauya sosai da sosai, Zuby ta zab'i zaman d'aki indai tana gida, shi yasa take jin dad'in tafiya school dan tafi sakewa acan, gida kuma ta daina kula kowa sai kula da Umar Faruk ke bata, ko akasi yasa sun had'u da Khairat a tsakiyar gida bata kulata, hakan kuma yana wa Khairat dad'i dan kowa harkar gabansa yake yanzu, cikin Zuby cikin ne mai dad'in raino , danko ciwon kai ba tayi sai cin abinci kamar tashin hankali, komai so take taci komai sha'awa yake bata.
Sab'anin na Khairat dake wahalar da ita, sam bata son cin abinci sai Umar Faruk da Mama sun matsa mata take ci, shima kuma tana cinshi zata amayar, ga yawan zazzab'i, wani lokacin kuma matsanancin ciwon ciki da kasala, idan ta fara haka zata dinga rusar kuka tana matsar ciki, hakan yasa kowa yafi tausayinta fiye da Zuby dake garas da ita, Khairat uwar kwalliya amma yanzu wanka ma sai Umar Faruk ya taimaka mata take yi , harta manta rabon data d'iga kwalli a fuskarta, daga kwanci sai kwanci bata iya zaune na tsawon lokaci, hakan kuma ya shafi har zuwa wajen aikinta, danta daina zuwa yanzu saboda larura, gashi kuma yanzu Papa ya bud'e mata tattalin arziqinta tunda ya gane duk abinda take akanshi ne take, sai dai babu wani anfani da hakan yayi saboda bata cikin qoshin lafiya bare ta mori kud'in, kuma yanzu Umar Faruk ne ke musu duk abinda suke so, saboda bud'i kullum Allah yake masa.
Mama kuma ba zama, kullum a tafiye take tana shiga lungu da saqo na gari dan ganin ta tarwasta Khairat kamar yanda take, kamar yanda ta fad'a ta murje idonta ta nuna kamar ba komai daya faru ta qara shiga duniya, tayi sabbabin qawaye yan duniya wanda suka qara kaita suna shirin barota, a cikinsu ne wata ta kaita wajen wani babban malamin tsibbu suka kai kukansu akan Khairat da Bala, a take ya fad'a musu zai nakasasu suje gida kawai su kwanta aiki ya qare, cike da kwankwanto Mama taje gida tana tunanin aikin malam d'in.
*************
Yau ma kamar kullum Khairat ce a d'akin Mama kwance akan gado da d'an dabino a bakinta tana tsutsa, Mama ce tayi sallama ta shigo ta zauna qasa tana fad'in "to taso ga abincinki kici."
Juya baya tayi tace "wallahi Mama bana son ci, dana ci amai zanyi."
Kallonta Mama tayi tace "Khairat, kin rainani ko? idan da mijinkine ya miki magana d'aya da kin taso."
Juyowa tayi tana kallon Mama ta tashi zaune, gyara siket d'inta tayi daya tattare sannan ta sauko qasa, janyo kwanan tayi tasa hannu ta fara laquta, tun kafin takai baki take jin amai na taso mata amma saboda Mama sai tayi k'arfin halin kai lomar, bata kai ga had'eta ba amai ya taho mata da gudu ta tashi tayi qofar d'akin ta tsugunna ta fara qheqashi, saida tayi kamar zata amaye kayan cikinta sannan ta kurkure baki ta dawo d'akin, a galabaice ta kwanta qasa tana rufe ido, Mama dake jin kamar ta zubar mata da qwalla ne ta d'auki wayarta ta kira Umar Faruk, yana d'auka tace "dan Allah kazo gida, abin yarinyar nan ya fara bani tsoro wallahi, tun jiya har yau babu wani abinda ya shiga bakinta ya zauna bata amayeshi ba."
Cike da tausayi yace "shikenan Mama ganin nan zuwa, tana kusanku ne?"
"Eh gata." ta fad'a tana bawa Khairat wayar, tana d'orawa a kunne yace "baby, kina so kisa gwarzon mijinki kuka?"
Murya qasa qasa tace "a'a bana so."
"To indai hakane ki fad'a min abinda kike so na taho miki dashi yanzu?"
Shiru tayi tana tunanin abinda zata fad'a, duk iya tunaninta bata tuna wani abinda take sha'awar ci ba, a hankali tace "baby ba komai, ni kawai kai nake so kazo nayi kwance saman jikinka."
Dariya ce ta kubce mishi yace "shi kad'ai kike so?"
"Eh." ta fada tana turo baki gaba, cewa yayi "to ki d'auka an gama saboda kai da kaya ai duk mallakar wuyane."
Cikin shagwab'a tace "uhm uhum, wayo ko? to na yarda kai da komai naka duk mallakina ne."
"Dama haka nake nufi nima, gani nan zuwa."
"Sai kazo." tana fad'a ta kashe wayar, bawa Mama tayi tanata juyi a tsakiyar d'akin, Yusuf ne ya shigo ya nufi wajenta ya zauna yana cin gyad'a, juyowa tayita kalleshi tace "d'an tanti me ake ci ne haka?"
"Guciya." a cewar yaron.
Ruf da ciki tayi ta tokare hannayenta ta amshi ledar gyad'ar ta cika hannu ta fara b'arewa tana ci, ganin tana ci yasa yaron ya sake mik'a mata ledar gaba d'aya ya tashi ya fita, jim kad'an sai gashi ya shigo da wata a hannu, suna haka kuma Umar Faruk ya shigo, kusanta ya zauna yana aje ledar hannunshi yana fad'in "Ina kuma aka samu gyad'a?"
Yusuf kawai ta kalla ba tayi magana ba, Mama kuma tuni ta tashi ta fita dan tasan sai sun saiyar da halinsu a gabanta ma, ganin Mama ta fita ta matsa ta d'ora kanta akan cinyarshi tana kallon fuskarshi, shafa fuskar yayi yace "tashi kiga abinda na kawo miki, kuma nasan zaki soshi sosai."
Janyo ledar yayi ya fara fito da abin ciki ita kuma ta tashi zaunen, kifi ne soyayye ga bala'in zafi π zaiyi dad'in ci, da sauri ta rufe hancinta tana fad'in "meye wannan kuma? ka rasa me zaka siyo min sai kifi."
Kallonta kawai yake ya kasa magana, cike da b'ata rai tace "dan Allah baby ka fitar dashi wallahi amai zai sani."
Shi kuma mamaki ma ya hanashi motsi gani yake kawai dagangan takeyi, bud'a baki tayi tace "bab......" da gudu ta qarasa fita daga d'akin sai kuwa amai, ganin haka yasa ya tashi yabi bayanta, kallonta yake tana yunqurin aman sosai daga ruwa sai gyad'ar da taci, d'akin ya koma ya d'auko kifin ya nufi d'akin Zuby dashi dan yasan ita tsaf zata handameshi, wucewa yayi yaji su Mama Sa'a na magana akan wahalar da Khairat kesha, da sallama ya shiga ya samu tana bacci, daddabata yayi ta tashi zaune da d'aurin qirji saboda zafin dake akwai, aje ledar yayi qasa yana fad'in "ga kifi nan."
A yamutse ta kalleshi tace "wallahi yah Umar bana son turaren nan naka, tayar min da zuciya yake sosai da zaka daina anfani dashi da naji dad'i."
Murmushi yayi yace "to nama fita daga d'akin gaba d'aya, kici dai kinji ko."
Binshi tayi da kallo harya fita, qasa ta zauna ta samu kifin nan taci abinta sosai ta qoshi, saida ta gala ta fito ta wanke hannaye ta koma d'aki....
Kwance ya samu Khairat a tsananin galabaice abin tausayi, duk ta rame ta fita hayyacinta sai ido masha Allah, a lokacin Mama na d'akin ta kalleshi tace "Umar Faruk, ko dai zaka kaita gidansu ne ta wuni, wataqila idan taje ta d'an saki jikinta har taci wani abu, amma inba haka ba da matsala gaskiya, kuma idan zaku tafi ka biya asibiti adubata dan Allah."
"To Mama."
Kallon Khairat yayi yace "tashi mu tafi ko."
Lokacin kuma wani bacci ne yazo mata, da qyar tayi tsaye tasa hijab dan yanzu zamanta d'akin Mama yafi yawa, slipas d'inta tasa tace "muje."
"Haka zaki tafi?" cewar Umar Faruk, kallonshi tayi kafin tayi magana Mama tace "to danAllah wanda yake takanshi me kake tsammani dama."
Haka suka wuce suka kama hanyar asibiti, kuma wannan fitar ita ta zama silar qara lalacewar komai, zaune suke gaban Sadiya bayan ta gama fad'a mata abinda ke damunta, had'e hannayenta tayi tace "cikin naki yakai wata nawa?"
Kallon Umar Faruk tayi shima ita yake kallo kafin tace "uhum, wallahi ban sani ba."
Dariya suka saka mata ita da Umar Faruk kafin tace "yanzu ciki a jikinki kice baki san watanshi nawa ba? kai Khairat Allah ya shiryeki wallahi."
Umar Faruk ta kalla tace "yallabai, dole zamu mata Γ©co (scanning) muga lafiyar cikin nata, dan ciwon cikin shi yafi zama matsala, zai iya yiwuwa cikin ne ya shiga cikin mara ko ya fita daga mahaifa, amma yanzu idan muka mata eco sai muga lafiyarshi."
"Ba damuwa madam."
Tsaye tayi tace ma Khairat ta taso, shamakin dake tsakanin gadon mai jiya suka shiga ta kwantar da ita, da mamaki take kallon Khairat dan a iya ganinta bata ga ciki a jikinta ba, photon ne ya fito suka fito daga wajen, zaune sukayi ana kallon juna sannan ta sauke numfashi tace ,
"Khairat kin tabbatar kina da ciki?"
Da mamaki Khairat tace "alamu na nuna min haka, kuma a asibitin nan ne aka fara fad'a mana haka."
"To a gaskiya ni dai banga wani ciki ba a jikinki Khairat."
"Me?" cewar Umar Faruk, d'orawa yayi da "me kike nufi da da bata da ciki? dubi fa yanda ta koma saboda laulayi, kuma a hakan ne bata da ciki."
Khairat ma kallonta tayi tace "Sadiya, kin tabbatar da abinda kike fad'a kuwa, ko dai cikin yabi wata hanyar ne daban kamar yanda kika fad'a d'azu, amma inba haka ba ina shan wahala fa sosai."
"Wallahi na tabbatar da haka, idan kuma baku yarda ba kuje wani wurin a duba muku."
Kallonta Umar Faruk yayi ya kama hannun Khairat suka fita, kai tsaye wata asibitin suka nufa, nanma dai abinda aka fad'a musu kenan, saida sukaje asibiti har hud'u duk sakamako d'aya ne, tashin hankalin da Khairat ta shiga yafi wanda Umar Faruk ke ciki, kuka ta dinga yi a cikin motar har suka isa gida, tare suka shiga kuma da kanshi ya fad'a musu halin da ake ciki, Mamie da Mammie dake shirye shiryen komawa india ma duk hakalinsu ne ya tashi suma, nan ya barta ya tafi da niyyar dawowa da dare ya d'auketa.
**************
Tun tafiyar Umar Faruk Khairat ta rikice musu cikin gidan, wani zazzafan zazzab'i ne ya rufeta mai tsananin zafin gaske, har saida Mammie ta dinga sakawa hijabinta ruwa suna rufeta dashi, ba kuma zazzab'i kawai ba ciwon qafafu da hannaye kamar ba'a jikinta, zafi take ji mai rad'ad'in gaske wanda bata tab'a jinshi ba bare ta kwantata, hawaye kad'ai ke iya fita daga idonta ta kuma nemi addu'a a bakinta ta rasa sai a zuciyarta kad'ai take iya istigfari da tasbihi, Mamie ganin abin bana qarau bane yasa suka kira Umar Faruk yazo, har d'akinta da take kwance ya shiga, kallonta yake sosai har yana karkace kai, so yake ya fahimci abinda idonshi ke hango mishi a tare da ita d'in, wani murmushin takaici yayi ya cije gefen labb'anshi ya kalli Mamie yace "zamu tafi gida, komai zaiyi daidai."
Da kanshi ya d'auketa ya kaita mota sannan suka wuce gida, da kanshi ya shiga da ita cikin gida kai tsaye d'akin Mama ya wuce da ita, duk uwayen gidan binshi sukayi suna tambayar lafiya, yana cikin fad'a musu Khairat ta bud'a ido, fashewa tayi da qara mai k'arfin gaske tana fad'in ya mayar da ita gida wajen Mamie, rik'eta ya fara yi yana so tayi shiru amma ina shure shure kawai take, zaune yayi kusanta cikin daka tsawa yace "kalleni nan."
Bud'a ido tayi ta sauke a kanshi take ta kuma d'auke idonta, hakan ya tabbatar mishi da abinda yake zargi wato sharrin shed'anu ne, janyota yayi jikinshi ya rumgume yasa bakinshi a kunnenta yana mata karatu, fizge fizge ta fara sosai tana gunjin kuka tana so ta k'waci kanta, wani shegen rik'o yayi mata yasa ta kasa kubcewa, har saida ta fara rera kukan a hankali tana sauke ajiyar zuciya sannan ya kwantar da ita, a haka kuma bacci ya d'auketa, tashi Umar Faruk yayi ya fita yana ci gaba da fad'awa su Mamie abinda ya faru, a haka ya fita sallah magrib yana mamakin sabon al'amarin daya b'ullo musu.
**************
Tana farkawa ta sauko daga kan gadon ta fito duk a yamutse da ita, Mama na k'ofar d'akin akan sallaya taga fitarta, bata mata magana ba saboda ganin yanayinta, Zuby ce ta fito daga d'aki suka kalli juna, wata shegiyar qwafa Khairat tayi ta wuce d'akinta, Zuby ma tab'e baki tayi ta wuce sabgar data fito da ita.
Tana shiga d'akin taji ya mata zafi sam ba zata iya zama ciki ba, a turmuje ta ciro akwatinta ta fara had'a kaya, Umar Faruk na shigowa na nufi d'akin Mama, da hannu ta masa alama tana d'akinta, wucewa yayi kai tsaye yana shiga ya tsaya yana kallonta, qarasowa yayi ya zauna gefen gadon yana fad'in "yadai, tafiya zamuyi ne?"
Ko kulashi ba tayi ba sai ci gaba da had'a kayan da tayi, tsaye yayi bayanta dan yaso ya fahimci halin da take ciki, cikin wata irin murya da baya yinta inba marar lafiya ya samu ba da zai taimakawa ba yace "ke."
Cak ta tsaya amma bata juyo ba, sake maimaitawa yayi cikin amon murya yace "dake nake, kalloni nan."
A hankali ta juyo ta sauke idonta a kan nashi, amma saboda bala'i da kwarjini da tsoro kawai saita zube qasa ta fashe da kuka cikin muryar da daga ji ba tata bace ta fara cewa ita kawai ya kaita gida bata san zama anan, banza yayi da ita ya d'auki cup ya zuba ruwa ciki ya fara yan karance karancenshi duk yana kallonta, koda ya gama tofawa a cikin ruwan ya taso yayo kanta, tana ganin haka ta zabura ta tashi tsaye tana ja da baya tana fad'in "a'a, a'a, karka matso kusa dani, kar kayi fa, wallahi zaka cutar da ita a banza, zafa ka iya kashe abinda ke cikinta, a'a zaka jamata fa."
*Allah my sister na,π na tuna lokacin da kika sha wannan wahalar, a lokacin da naje gidanki da niyyar jinyarki, amma a qarshe sai tare muka dawo gida,π kai anga rayuwa fa, wallahi wannan ciwon na Khairat da nasa bawai qirqira bane, sak irin ciwon da sisterna tayi ne, Allah ka qara karemu daga sharri masharranta*π
Saboda an saba gwagwarmaya irin haka yasa bai kula da abinda suke fad'a ba, hannu yasa ya d'ibi ruwan ya watsa mata ruwan, wata qara ta kwamtsa tana numfashi sama kamar zata d'auke rai, cikin gunjin kuka take fad'in "ka daina, ka daina haka."
Fuskar nan a daure ya aje cup d'in ya zauna kan gadon yana fuskantarta yace "fad'a min, meya kawoku jikinta, meta muku da kuke neman cutar da ita, akan wani dalili kuka shiga jikinta? kuma idan kuka min qarya wallahi jikinku zai fad'a muku."
Cikin wata irin tsawa yace "maza zauna nan."
Zaune tayi inda ya nuna mata tana susar jiki saboda rad'ad'in ruwan daya zuba mata a jiki, cikin muryar daba tata ba ta fara magana....
_Ikon Allah, lallai ta bakin Mamien mu tace namijin duniya, yau kam na tabbatar, to amma kuna ganin zasu fad'i gaskiya ne?_
*WASA FARIN GIRKI.*
29/08/2019 Γ 14:33 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
ππππππππππ
*TASKU*
ππππππππππ
_*My BK,* ina tayaki murnar fara wannan novel naki mai cike da abin al'ajabi, Allah ya baki ikon kammalashi cikin qoshin lafiya da hazaqa, fatan alkairi masoyiyar *Meerah.*_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Ohhh my sweet and lovely *Heenat*, kin tuna min da wannan had'uwar nima, ba zan tab'a manta ranar nan ba, soyayya hadin Allah ce kuma shi yake sakata a zuqatan bayinshi a sanda yaso, *My HEENAT* kin tambayi me nake so ko? to abinda *Meera* take so shine ganin kyakyawan murmushinki a koda yaushe, soyayya kuma *Meera* ta samu daga Heenat, dan haka kisha zamanki ki huta, Allahn daya had'a shine zai raba da izininshi._ π❤π
_Bismmilahir-rahman-rahim_
5⃣7⃣
"Umar Faruk, mun maka farin sani shi yasa muka shirya da kyau kafin shiga jikin matarka."
Suna fad'a da iya k'arfi aka fizgi Khairat aka bugata ga bango, take ta fad'i gurin kamar babu rai, da sauri Umar Faruk yayi kanta ya rik'eta, "Khairat, Khairat."
D'aukarta yayi ya aje kan gadon ya d'auko cup d'in ruwa ya shafa mata, numfashi ta sauke da nauyi amma bata bud'a ido ba, ajiyar zuciya ya sauke saboda ganin tana sauke numfashi a hankali, a zuciyarshi kuma yana tunanin hanyar da zaibi wajen magance matsalar, danya lura suna son cutar da Khairat ne kawai da abinda ke cikinta, duk da ance babu shi amma bai yarda ba, yana shafar kanta yana kallon fuskarta data fita tayi fiyau da ita duk ta rame ta fice, qwaqwasa qofa yaji yasa ya tashi ya fita, Mama ce tsaye tace "Umar Faruk har yanzu jikin nata?"
Saida ya juya ya kalleta daga qofar d'akin yace "har yanzu Mama,amma ta samu bacci yanzu."
"To kazo mahaifinka nasan ganinka."
"To Mama." ya fad'a yana saka takalmanshi.
D'akin malam suka shiga da sallama suka zauna a tare, Baba ne yace "Umar Faruk mahaifiyarka ta fad'a min abinda ya faru yau d'in nan, nayi mamaki sosai tare da jimami, amma abinda nake so ka sani shine, babu abinda ya samu cikinta, kuma yana nan cikin qoshin lafiya kuma da yardar Allah za'a haifeshi/ta, dan haka ba sai na fad'a maka abinda za kayi ba, nasan kasan abinda ya dace da ita, amma idan kaga akwai cutarwa ga lafiyarta ko abinda ke cikinta saika sassauta kabi a hankali, kaji ko?"
"Naji Baba, kuma nima abinda na fahimta kenan, kamar suna sob cutar da ita ne saboda yanda suka bar jikinta a yanzun, amma dai insha Allah basu fi k'arfin addu'a ba."
"Allah ya kyauta." cewar Mama da Baba.
Kallon Mama yayi kallo na tsanake yace "komai muqaddari ne daga Allah, ciwon Khairat kuma yana da sila kamar yanda ko mutuwa akance ga sila wani lokacin, zuciyar Khairat fara ce Mama bata qullatar kowa, amma tanti ta kasa fahimtar hakan har tana so taga ta cutar da ita, bai zama lallai na iya yin shiru ba Mama, amma dai zan qoqarta naga mun rabu da lafiya da shed'anun aljanu da kuma shad'anun mutanen, amma wallahi sukayi taurin kai, to Mama sai dai kiyi hak'uri, dan gaskiya zansa su koma kan wanda ya turosu, ba wai zargin tanti nake ba a'a tabbas ne nake da itace." duk da dai ranshi a b'ace yake, amma baya jin zai iya cutar da yayar mahaifiyarshi, kawai ya fad'i haka dan ya bada tsoro.
Baba ne yace "Umar Faruk, ina kasan haka, me yasa kace itace?"
Baba ya kalla yace "da bakinta kuma a gabana ta furta kalamai marasa dad'i akan Khairat, ban damu bane saboda nasan gidan nan na cikin kariyar ubangiji, kuma Khairat d'in yanzu bata da bace, kullumtana cikin karatu ne da kuma ibada, saboda ta gyara halayenta marasa kyau domin son rabauta, kuma tun ranar da tanti tayi wannan maganar ban tab'a kwanciya bacci ba ba tare dana tofa mata addu'ar bacci ba da kaina, koda kuwa ba'a d'akinta ba nake, hakan daya faru ya sake tabbatar min lallai sihiri gaskiya ne kuma zai iya shafar kowa idan Allah yaso hakan."
Ajiyar zuciya Mama ta sauke wacce ke sairaranshi gabanta na fad'uwa, shirun da iyayen sukayi yasa ya tashi yana fad'in "saida safenku iyayena."
D'akin Zuby ya fara shiga ya sameta kwance tun d'aurin qirjin daya sameta dashi da rana, tuhumammen kallon da yake mata yasa ta tashi zaune tana kallonshi itama, ita ba tace komai ba shima kuma baiyi magana har tsawon minti biyu, da qyar ya iya cewa "kin samu labarin abinda ke damun 'yar uwarki?"
Cike da rashin kulawa tace " a'a, meya sameta?"
Gyara tsayuwa yayi yace "da kyau tunda baki sani ba, na d'auka kina da labari ne danna miki hannunki mai sanda, amma duk da haka ina fad'a miki da kuji tsoron Allah Zubeida, kusan zaku koma gareshi kuma wallahi zai mumu hisabi, baya kuma yafe haqqin wani akan wani bare ka samu alfarma, lahirar nan da kika gani mai kad'aita Allah ne kad'ai ke shigarta ba wanda yake neman biyan buqata ga waninsa ba, kuma nine Umar Faruk kin samu, bai kamata a cutar da wani ba saboda kawai ana so a rabamu ko *d'aukar fansa* a kanshi."
Matsawa yayi kusanta ya sunkuya yasa hannu ya shafi cikinta yana kallon idonta yace "ina fatan yana lafiya, kinci abinci?"
Kai kawai ta d'aga masa, d'agawa yayi ya shafi kumatunta ya manna mata sumba a d'aya kumatun yace "ki kula da kanki, saida safe."
Fita yayi kai tsaye ya nufi d'akin Khairat, yana so ko da Zuby nada laifi ya lallab'ata saboda cikin dake jikinta, kuma koba komai addini ya nuna ka rabu da mace da kyautatawa, tunda baya da hujja akan lallai da hannunta ba zai matsa mata ba, kayanshi ya cire yayi wanka yazo ya shirya duk Khairat na bacci, saida ya zauna ya d'auki littafi mai tsarki zai fara karatu kawai ta farka tana dafe qeyarta data bugu sosai, fashewa tayi da kuka tana shirin sauka daga kan gadon, tasowa yayi ya hau gadon yana so ya lallab'ata, kuka take sosai tana fad'in ya kaita gida ita ba zata zauna nan ba.
Yayi rarrashin duniya amma tak'i shiru kuma gashi dare yayi, duk iyayen gidan babu wanda ya ritsa saboda rigamar da Khairat keyi, saida suka ga abin bana qarewa bane suka samu suka kwanta, amma babu inda suka kai aka kira sallah asuba, rana ta farko a tarihin rayuwar Umar Faruk da yayi sallah a gida, hakan yasa yaji abin ba kan gado saboda rashin sabo, yana gamawa yace mata ta tashi tayi sallah idan ta gama ta shirya ya kaita gidan, tashi tayi ta shiga douche ta kama ruwa ta d'auro alwala, fitowa tayi daf da zata shiga d'aki taji anyi sama da ita an buga qasa, qara ta saki wanda tasa Umar Faruk fitowa da gudu gudu, taimaka mata yayi suka shiga ciki, ganin yanda take dafe bayanta yasa yace "baki ji ciwo ba ko?"
A marairaice ta kalleshi tace "akwai zafi mana, bafa santsi ne ya kayar dani ba, amma dai ina mamaki."
"Karki damu kinji, je kiyi sallah ki shirya muje."
Hijabi tasa a matuqar galabaice saboda babu komai a cikinta, da qyar ta gama sallah ta tashi zata shiga wanka, ganin yanda take yasa Umar Faruk zaunar da ita ya d'auko fresh milk ya bata, ji tayi har yawunta na tsinkewa tana so tasha, da azama ta daga ta fara sha ba qaqqautawa, saida ta gama ta tashi Umar Faruk yace "muje na miki wankan."
Tare suka shiga ya fara mata wankan, suna cikin yi sai kuwa amai, saida ta amaye fresh milk d'in kad'ai aman ya sarara mata, haka suka fito kafin ya shiryata ya sake d'auko wata madarar da ayaba da kankana ya bata, da qyar taci ayaba guda biyu bata sake cin wani abu ba bayan ita.
Fitowa sukayi ya shiga da ita d'akin Mama, da sallama ta shiga ta zauna tana d'ora kanta a qafar Mama tace "ina kwana Mama."
"Lafiya lau Khairat, antashi lafiya?"
"Lafiya lau Mama."
"Ya jikin naki da dama?"
Saida ta tashi zaune tace "da dama Mama."
Ruk'ayya ce ta sallamo ta aje kwano gaban Mama tana fad'in "auntyna kin tashi lafiya?"
"Lafiya lau Ruk'ayya." ta fad'a tana bud'a kwanon, ganin d'umamen tuwo sai qamshin man shanu ke tashi ya birgeta sosai, kallon Mama tayi tace "Mama ina so naci amma."
"Indai kina so kici yata kici kawai, idan kina sawa ranki komai ki kaci zakiyi amai to da kinci kuwa sai kinyi."
Kallon Umar Faruk tayi tace "baby bara na d'anci kad'an saimu tafi."
Shi kam farin cikine ya kamashi tare da mamakin wacce ke kuka sai an kaita gida, hannu tasa tana d'an qwalbatar tuwon tana kaiwa baki, ji take kamar taci ta qoshi amma yanzu haka zuciyarta ce ke tashi, cire hannu tayi suna kallonta harta wanke ta dawo d'akin ta kalli Ruk'ayya tace "ki bani dabino dan Allah."
Ledar dabino Ruk'ayya ta bud'e ta ciko hannu ta bata, karb'a tayi tana fad'in "ke qaro min malama."
Da dariya Ruk'ayya ta qaro mata sannan sukawa Mama sallama suka tafi, tafiya suke a hanya tanata gwaigwayar dabinonta harta fara d'an b'ata rai saboda aman dake taso mata, hannunshi ta rik'e da yake tuqi ta kalleshi, alama kawai ta mishi ya tsaya, kai ya girgiza mata shima ba tare daya tsaya ba, tafiya suke ba mai magana har wayarshi tayi qara.
D'agawa yayi suka gama hirarsu duk tana jinshi, saida ya gama ta kalleshi tace "akan me kake magana?"
Ajiyar zuciya yayi ya kalleta yace "har yanzu muna kan magana ne bamu tsayar ba, dan haka ban fad'awa kowa ba."
Kallon titi yayi yace "ina sone na tashi nawa compagnie nima."
Murmushi tayi tace "naji dad'i kuma na maka murna, Allah ya sanya alkairi."
"Ameen, yanzu ciniki ya fad'a, biya kawai zanyi kafin muje mataki na gaba."
Da wannan tattaunawar suka isa gida, har ciki ya shiga suka gaisa sannan ya musu sallama ya tafi, kwance tayi akan kujera Mamie tayi saurin cewa "kije d'aki mana ki kwanta za kifi sakewa."
Zaune ta tashi tana yamutsar fuska, Mammie ce tace "me kike so a dafa miki kafin ki tashi?"
A yamutse tace "dambu zanci."
"An gama shalelen Papa." cewar Mamie.
Tashi tayi zata nufi d'akin Mamie kawai qafafunta suka kasa d'aukarta, zubewa tayi qasa kamar wasu kayan wanki, Mamie ce ta tashi ta kamata tana salati, zaunar da ita tayi tana kallonta da mamaki, matsa qafafunta tayi tace "Mamie, kamar ba qafafuna ba, wallahi ciwo suke min sosai."
Kallon juna sukayi da Mammie, kafin kace kwabo kuma sai ciwon ciki mai tsananin gaske, Papa suka kira yazo gida yaga halin da take ciki, tausayi ta bashi sosai harya kira likita yace yazo ya sameshi gida, koda likita ma yazo shi cewa yayi baiga wani abu dake damunta ba, amma su kaita asibiti a duba lafiyar d'an cikin nata, Mamie ce tace ya tafi kawai sunji, yana tafiya ta kira Umar Faruk yazo, ruwa suka bashi a cup a mata addu'a, zai bata tasha tace ai ina bai isa ba, saida su Mamie suka kama mish suka d'ura mata ruwan tasha sannan taji sassaucin ciwon kamar an cire mata qaya, daga nan kuma bacci ya d'auketa.
****************
Tunda Zuby taji fitarsu ta kira Mama duk da yanzu ba wani sosai suke waya ba, kira ta dinga yi amma ba'a d'agawa harta gaji ta daina, amma maganganun Umar Faruk na mata yawo har yanzu a qwaqwalwa, tana haka Ruk'ayya ta kawo mata nata abincin, gyara zama tayi ta handami abinta ta qoshi sannan ta d'auki kayan karatunta ta fara tilawa dan suna daf da fara jarabawa kwanaki suka rage musu.
******************
Koda yaje daukarta ma ya sameta kwance ranga ranga, Mammie na gefenta tana share qwalla, zaune yayi yana tambayar "Hajia lafiya kike kuka, meya faru ne?"
Cikin kuka Mammie tace "wannan wane irin laulayi ne yarinyar nan take, tunda ka kawota gidan nan har yanzu wallahi ko ruwa tak'i sha idan ba ruwan addu'a daka bata ba, taya mutum zai rayu to a haka bare d'an cikinshi, gaskiya nidai abin ya fara bani tsoro."
"Hajia dan Allah kuyi hak'uri ku daina kukan nan, insha Allah babu abinda zai faru sai alkairi, ku tayi mata addu'a kawai ita take buqata daga gareku."
Ganin tana bacci yasa yace "ni zan tafi Hajia, tunda ta samu bacci ba sai an tasheta ba."
"To shikenan, saida safe."
A haka ya tafi gida rai ba dad'i ya fad'awa su Mama abinda ake ciki, d'akin Zuby dole ya kwanta amma baiyi bacci ba, yana cikin tsayuwar dare Papa ya kira wayarshi......
ππππ
Yana d'auka Papa yace "Umar Faruk jikin yarinyar nan fa yayi tsanani, koda wani abinda da kuke bata ne?"
"Subhanallah, Papa ku d'ora mata wayar a kunne."
D'ora mata yayi shi kuma cikin taushin murya yace " Khairat, me yake damunki?"
Cikin matsannancin kuka tace "Faruk mutuwa zanyi, mutuwa zanyi Faruk, ciwo nake ji tako ina a jikina, ba zan iya cewa ga abinda yake damuna ba, amma dai bana jin dad'i ko kad'an, Faruk ka taimaka min dan Allah bana son cikin nan wallahi, dan Allah ka taimaka ka cire minshi kafin na mutu."
Saida taji numfashinshi cikin kunnenta, a hankali ya lumshe idonshi daga inda yake tsaye, wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mishi, tsantsar tausayinta ne ya lullub'eshi, saida ya saita nutsuwarshi yace "haba baby, ya kike fad'an haka? komai yayi farko yana da qarshe, kowace uwa da kika gani a duniya da kalar nata wahalar da tasha kafin ta haifi abinda ke cikinta, kema kamar hakane Khairat, ki sani wannan d'anki ne ko 'yarki kike d'auke dashi, ki daina cewa ba kya sonshi hakan zai iya tasiri akan abinda ke cikinki koda yazo duniya ne, yanzu kinsan me nake so dake?"
"Ina jinki Faruk." ta fad'a cikin kuka da sake kama cikinta sosai tana matsewa.
"Ina so ki sake neman gafarar iyayenki, wala'Allah ki samu sassauci, wataqila mahaifiyarki tasha fiye da wahalar da yanzu kike sha, sannan karki bari anbaton ubangiji ya fita daga bakinki inba bacci kike ba, kinji ko baby?"
Sassauta kukanta kawai tayi ba tare da tace komai ba, d'orawa yayi da "kinsan me?"
"A'a." ta fad'a cikin muryar kuka.
Saida ya kalli Zuby dake bacci hankali kwance yace "duk abinda kika haifa na bakishi kyauta, kisa a ranki d'anki ne ba nawa ba, kece zaki zab'ar mishi sunan da kike so, ni nawa kawai hidima ne gareshi da kuma ke."
Duk da bala'in ciwon da take ji bai hanata jin dad'i ba har cikin zuciyarta, su Papa dake tsaye mamaki ne ya mamayesu ganin murmushin da tayi, cikin ikon Allah sauqi saiya samu hakan yasa da Umar Faruk yaji bacci na shirin d'aukarta sai yace ta rufe ido zai mata addu'a, tun tana jin sautin muryarshi yana mata addu'a har bacci ya d'auketa ba tare daya daina ba, ganin bacci ya d'auketa yasa Papa d'auke wayar a kunnenta ya mayar a nashi, Papa ne yace
"Ikon Allah Umar Faruk, kaga yarinyar nan tayi bacci, meka mata ne haka?"
Murmushi yayi yace "ba komai Papa, sai dai Papa dan Allah kar kuyi sake da addu'a musamman idan tana irin haka, sannan na fad'a mata ta sake jaddada neman afuwarku, hakan nada anfani musamman ma Mama, dan zai iya yiwuwa tasha wahala fiye da wacce take sha yanzu."
Papa kam kallon Mamie yayi yace "bansan komai ba game da wannan lokacin Umar Faruk, dan haka ba zan iya cewa komai ba, kuma insha Allah zamuta yi mata addu'a."
"Shikenan Papa saida safenku."
"Allah sadamu da alkairinsa."
*Asuba ta gari*
Ko abinci bai tsaya ci ba suka fita tare da Zuby ya ajeta makaranta, daga nan kuma wucewa yayi wajen da zasu had'u da mutanen da zabawa kudin tsohon store d'in daya siya danya tayar dashi, suna gamawa ya wuce gidansu Khairat, zazzab'in data tashi dashi shi kanshi saida ya bashi tsoro saboda zafin jikinta, amma saboda dauriya data ganshi haka ta tashi zaune tana gaisheshi, ya jima gidan yana hira da ita harya tashi tafiya, koda ya mata maganar yaushe zaizo ya d'auketa su koma gida, take yanayinta ya canza dan haka kawai ya rabu da ita......
Daga nan kuma yaje wata harkar, koda lokacin tashinsu Zuby yayi ya wuce ya d'aukota, suna isa gida koda suka shiga suka samu tanti zaune da alama zuwan Zuby take jira, kallonta Umar Faruk keyi saboda ganin wata sabuwar shiga ga tantin , duk da dama ba ma'abociyar saka hijabi bace, amma kuma siket d'in daya gani a jikinta da kwalliya a fuskarta ne yafi d'aga mishi hankali, kamar yanda ya samu suma mutanen gidan mamakin da sukeyi kenan, d'aki Zuby ta bud'a tanti tabi bayanta suka shiga ko magana, shi kuma juyawa ma yayi ya bar gidan saboda b'acin rai.....
0 comments:
Post a Comment