***************
Har *12:40* Khairat bata dawo ba, ganin haka yasa Zuby girki d'an sassauk'an abinci ta zuba a plate ta rufe da d'aya tare da cokali ta tunkari d'akin Khairat.
πππhumm, zaki jawa kanki.
"Assalama alaikum." tayi sallama cikin taushin murya.
"Wa'alaiki salam, shigo." ya fad'a.
Bud'a labulen tayi ta zura qafafunta ta shiga, ganin Zuby yasa ya tashi zaune dan baiyi tsammanin ita bace saboda murayar daya ji, "Zubeida, kece dama?"
Saida ta tsaya gabanshi tace "eh, kona koma ne baka buk'atar ganina?"
"Ah haba, ni na isa."
Ganin tayi zaune a bakin gadon kusa da qafafunshi tana wani yamutsa fuska yasa ya d'an qara gyara nutsuwarsa yace "ina jinki, magana zamuyi ne?"
"Abinci na kawo maka, dan nasan kana jin yunwa, tunda naga ita har yanzu bata dawo daga walagigin ba." ta fad'a tana bud'a plate d'in.
"Me kike nufi da abinda kika fad'a?" ya tambaya.
Cikin had'e fuska tace "ka fini sani mana."
Qara gyara zama yayi yace "Zubeida, ku matana ne, kuma nine mai alhakin kare mutuncin kowace daga cikinku, ya kamata kisan me zaki dinga fad'a akan Khairat, duk cin zarafin da zaki mata kamar ni kikawa , haka itama idan ta miki ni tawa, tunda kika zo gidan nan kike kiranta da sunan da bai dace ba, na miki shiru ne kawai amma naga baki gani ba, to daga yanzu bana so na sake jin kin kirata da sunan karuwa, dan ita ba karuwa bace kamar yanda kike fad'a, dan haka ki kiyaye, idan kuma abincin kika zo bani zaki iya ajewa ki tafi na gode."
Cike da makirci ta fashe da kuka tana fad'in "ni dama sani baka sona yanzu, wallahi banyi tunanin haka daga gareka ba yah Umar, gaba d'aya ka canza saboda waccen matar, shine ba komai ba anfanin zamana a gidan nan in dai har baka sona."
Tsaye ta mike ta fara tafiya taji ya rik'e hannunta, saukowa yayi daga kan gadon ya rumgumota jikinshi yana shafa kanta, cikin rarrashi ya fara fad'in, kiyi hak'uri, baki fahimceni bane Zubeida, ina so ki gane cewa, ke da Khairat ba zan bari wani ya cutar da d'aya ba, ko itace take fad'a miki haka abinda zanyi kenan, ke da ita duka Allah zai tsayar dani ranar gobe kuma ya tambayeni yanda na shugabanceku, Zubeida na zama mutum azzulumi da baya iya adalci tsakanin matanshi, da farko naci amanar Khairat ta hanyar kusantarki a kwananta, dan Allah ki taimaka karna sake aikata wani laifi, banyi adalci ba idan nayi shiru ina ji kina kiranta da karuwa, amma kiyi hak'uri kinji."
D'ago da kanta yayi yana kallon fuskarta yace "kiyi shiru to, yanzu kije d'akinki ki zauna zanci abincin, bana son mai d'akin ta sameki anan, dan nasan yanzu tana kan hanyarrrr."
Bai k'arasa ba kuma Khairat ta bud'a labulen d'akin ta shigo, daram dam, shine tsinkewar da gaban Khairat yayi ganin Zuby a qirjin Umar Faruk, bugun zuciyarta ne ya qaru ta yanda ba zata iya saisaita kanta ba, sauke idonta tayi akan Zuby ta fara takowa cikin d'akin, itama Zuby d'in ita take kallo harta aje plate d'in hannunta akan center tebur d'in d'akin, ganin yanda suke kallon juna yasa Umar Faruk cewa "Zuby ki wuce d'akinki."
Saida ta gama hararan Khairat sama da qasa sannan taja dogon tsaki ta nufi hanyar fita, aikam dama zuciyar Khairat a wuya take hakan yasa ta finciko rigar Zuby ta shake sosai ta zubar da kayan hannunta harda wayarta ta mata wani jan kallo tace "dawa kike, ni Khairat ki kewa tsaki, ni kike wa tsaki? dake nake magana."
Ta qarashe maganar da d'aga murya, matsowa Umar Faruk yayi da nufin magana Khairat ta daga masa hannu tace "dakata min dallah, bari na gama da ita sannan, kana kallo qaramar yarinya zata nemi taci mutunci na, akan miye zata min tsaki?bayan nice ke daidai nayi mata tunda ni na sameta a d'akina, koda yake ba laifinta bane laifinka ne, da baka kirata ba aiba zata zo, shine har zata dinga min kallon raini da iskanci, wallahi sai naji wanda ya d'aure miki gindi a gidan nan."
Ta qarasa tana jinjigar Zuby dake hannunta, Zuby kam tuni idonta suka fara kawo qwalla, cikin gunguni ta rik'e hannun Khairat tace "dallah sakeni malama."
Wani murmushin rainin hankali Khairat ta mata ta sake shak'ar rigarta ta jinjina tace "ki k'wace mana idan kina ganin k'arfinki yakai, tabbas gata da shagwab'a ne suka raini ne, amma ki sani ina da k'warin k'ashi da tsabagen tsagwaron k'arfi, ta yanda idan na rik'i kamarki wallahi ba zaki iya k'watar kanki ba, amma idan kinyi musu toki gwada ki gani."
Qara qoqarin qwaqwale hannun Khairat tayi amma tajita jim a hannunta, sake maqale murya tayi tace "dallah nace ki sakeni ko."
"Hum, bari kiji na fad'a miki, dama nasan dole za kiyi rawar kai dan tunda naga mahifiyarki na tabbatar da haka, tun ranar da kika shigo gidan nan kike min kallon bi aho amma na miki shiru, to ki sani qyaleki nake ba dan komai ba sai dan canjin da aka samu, idan kuma kika kuskura kika tayar da qwanqwanman Khairat harna dawo asalin Khairat d'ita, tofa akwai matsala dan ba lallai gidan nan su iya dani ba, kashedi na qarshe, karki bari na sake ganin qafarki cikin d'akina dan ban yarda dake ba, kamar yanda ban yarda da mahaifiyarki ba."
Da kai ta mata alamar ta wuce kawai, ficewa tayi da sauri saboda hawayen dake son taho mata, kai tsaye d'akinta ta wuce ta fad'a saman gado ta fashe da kuka, duk da zuciyarta naso ta qaryata abinda take ji, amma dai tabbas ta tsorata da Khairat yau d'in nan, dan tasan gaminta da ita ba zai mata kyau ba, saida taci kukanta ta koshi sannan ta kira Mama ta fad'a mata abinda yake faruwa, fad'a sosai Mama ta mata tare da zaginta gaba da baya kafin ta sake jaddada mata tayi aiki da magungunan nan.
Bud'ar bakinta cewa tayi "ai Mama maganin ne nasa a abinci nakai masa, shine fa tsinannar ta shigo."
"Toki kwantar da hankalinki, nasan ai zaici abinci, da yaci kuma magana ta qare."
"To Mama, sai an jima."
***************
Tana fita Khairat ta wurga masa harara tana hango Zuby a qirjinshi, ta gabanshi taso wucewa amma saiya tareta, kallonshi tayi tace "matsa min a hanya."
"Ba zan iya ba, saboda kina hushi dani."
"Ka matsa min nace ko, inba so kake na huce a kanka ba."
"In dai zaki huce na amince ki huce a kaina."
K'arfinta tasa ta tureshi gefe hakan yasa yayi baya da k'arfi, amma jarumta tasa bai fad'i qasa ba, tsaye yayi sosai a gabanta a hankali ya rik'o hannunta tare da zube gwiwoyinshi a qasa ya marairaice kafin ya fara magana,
"Kiyi hak'uri, nasan ke mai hak'uri ce, ki yafe min domin nasan kin yafe min laifin da yafi wannan ma, kimin uzuri danna fahimci ke mai ilimi ce, my *Khairiri* ki yafewa wannan hamagon mijin naki mana, ke alkairi ce a gareshi kamar yanda fassarar sunanki yake, duk da dai bana da laifi, amma ina neman gafararki matata, idan baki yafe min ba zan shiga tashin hankalin da nake da yak'inin ban tab'a shiga irinsa ba, domin kuwa Khairat ta zama wani b'angare na sassan jikin Umar Faruk, a yanzun yafiyarki ce zata zata tabbatar da ci gaba da farin cikin mijinki ko akasin haka, domin kuwa ba Umar Faruk in dai har ba Khairat, hushinki na second d'aya, tamkar hushin duka mutanen duniya ne a wajen Umar Faruk, ki tausaya kuma agazawa wannan bawan Allah wanda rayuwarsa ta kasance kece mahad'inta, kuma nasan ko Khairat ce ta b'atawa Umar Faruk rai, zata sunkuya har qasa sannan ta nemi afuwarsa, a lokacin kuma Umar Faruk zai rumgumo Khairat jikinsa sannan yace na yafe miki my Khairat."
_Kaji mai wayo, wato ya fad'a mata abinda ya kamata tayi cikin dubara._
Inhar Khairat tace kalaman nan basu shiga sassa da b'argo da jijiyarta suka ratsa zuciyarta ba, to qarya ta fad'a hakan yasa ta sunkuya itama ta rumgumeshi tace "na yafe to, amma me yasa zata shigo min har d'aki kuma ta raina min wayo?"
K'eya ya d'an sosa yace "kiyi hak'uri, abinci kawai ta kawo min."
Sai lokacin ta juya ta kalli plate d'in dake aje, takawa tayi ta d'auki plate d'in ta dauka ta bud'a, tsaki tayi tare da fad'in "aikin banza kawai, inba munafirci ba meye na kawo maka abinci? bayan ba ranar girkinta bace, to ba zaka ci ba danni ban yarda da ita ba."
Tana fad'a ta fita da plate d'in ta aje akan gajerar katangarsu sannan ta dawo ta fara cire kayanta, bayanta ya tsaya ya fara cire mata bras yana fad'in "naji dad'i da kika yafe min, nan gaba zan kiyaye b'acin ranki."
Tana d'aure kitsonta tace "kayi nasara akan Khairat, dama wannan kalaman kad'ai Khairat take buk'ata kuma gashi ta samu maiyi mata."
Da haka ta shiga wanka shi kuma ya nufi masallaci, yana dawowa kuma ya samu tana sallah, kayan data barbaza ya fara tattarewa, wanda ta cire kuma ya ninkesu ya mayar drower, tana gamawa ta taso ta sumbaci goshinshi tare da qarasa addu'arta ta fad'a a fili cewa "Allah ya dawwamar maka da farin ciki a rayuwarka."
"Ameen." ya fad'a yana kallonta yace "addu'a kika min?"
"Eh mana, addu'a nawa mijina." ta fad'a tana cire hijabinta.
Yana kallo ta fara shafe shafe da murje murje, humra kusan kala bakwai yaga ta shafa kafin ta d'auki qaramar riga iya cinya ta saka sai pants, wasu turaren yaga ta dauka tana fesawa har kala hud'u suma kamar dai abun hauka, *pure love*, *Mid night*, *Blue dive* da kuma *love flowers*, amma fa cikin k'ank'anin lokaci d'akin ya gauraye da k'amshi mai dad'in shak'a, a hankali ta juyo tana kallonshi cikin takon d'aukar hankalitana jijjiga qirjinta ta tsaya gabanshi.
Rumgumarshi tayi cikin kunne tace "me kake ji?"
Dogon numfashi yaja ya gagara maidowa saboda ji yake kamar zai mutu, wani irin rikitatacen k'amshi ne mai tafiya da hankali, nanfa suka lula wata duniyar wacce Khairat ce kad'ai ta samu nutsuwa amma banda Umariri π, dan wata sabuwar sha'awa ce ta taso masa wacce inba fa can yakai ba ba zai samu nutsuwa ba, a haka tafi masallaci sallah asar , yana dawowa kuma ya sameta tasa kayan marmari gaba tana shan kayanta a maimakon abincin rana, zaune yayi kusanta ya d'auki ayaba yana fad'in "me zaki dafa min?"
"Yaushe? wai da gaske kake? shi yasa kenan naga tukunyar gas."
"Eh mana." ya fad'a tare da kai ayabar bakinta.
Bud'a bakinta tayi sosai ta tsotso tana kashe masa ido, shi kanshi abinda tayi wata ma'anar ya bayar ta daban, a take yaji wani abu yana masa yawo dan haka ya rintse idonshi, cire ayabar tayi daga bakinta ba tare data d'iba ba tace "me kake so na dafa maka?"
"Komai ma." ya fad'a numfashinshi na fizgarshi.
Aje tuffan dake hannunta tayi ta mik'e tsaye tace "zaka sha mamaki yau, dan zaka ci abincin shalelen Papa."
Canja kayan jikinta tayi ta saka riga da wando kafin tace masa "to ta ina zan fara?"
Murmushi yayi a zuciyarshi kuma yace "zan kuwa sha mamaki."
Kallonta yayi yace "ki fara tanadar kayan aikin, daga baya sai kiyi tunanin abinyi."
"To ina suke kayan?"
Dariya yayi dan da alama shima yau zai d'ana girki, fita yayi ya kira Ruk'ayya dake fama da nasu aikin, tana zuwa tace "yah Umar gani."
Cewa yayi "kije ki d'auko mata duk wani abu da kika san za'a buk'ata wajen sarrafa doya da k'wai da miyar...."
Sai kuma ya kalli Khairat yayi shiru, itace tace " umm , jus kawai nake buk'ata na mayonnaise da albasa."
"Me zai hana ki had'a da sardines?" cewar Umar Faruk.
"Um um, bana cin kifi da daddare."
Kallon Ruk'ayya yayi yace "jeki kawo, ai akwai komai ko?"
"Akwai yah, doya ma akwai sauran wacce ka siyo."
Tana fad'a ta fito tana dariya dariya murmushi murmushi, qanqanin lokaci ta had'a mata komai a kewayenta ta tafi ta kama nata aikin, tare da Umar Faruk suka fito tana kallon kayan, rik'e k'ugu tayi ta yamutse fuska, satar kallonta yayi ya bushe da dariya ya koma ciki, "humm, dariya ko? zaka sha mamaki."
Tana fad'a ta dawo d'akin wata santaleliyar wuk'a ta d'auka ta fita, d'aya daga cikin kujerun wajen ta zauna ta janyo doya ta gatsa mata wuk'ar, aikuwa sai doya ta rik'e wuk'ar Khairat ta jinjina wuk'a tak'i fitowa, haushi ne ya kamata ta taso cikin shagwab'a ta samu Umar Faruk dake shirin fita.
"Eh, lallai ma malam Umariri, wato ka had'ani da aiki, shine kake qoqarin fecewa daga gidan, to muje idan ka datsa min doyar ka fita."
Bata bari yace qala ba taja hannunshi sai waje, zaunar dashi tayi akan kujerar ita kuma tayi tsaye tace "to fara, dama aikin doya na maza ne irinku masu k'arfi."
Shi dai in banda dariya ba abinda yake, yana tab'a wuk'ar kuma sai yaji ta biyo hannunshi, kai kawai ya girgiza ya fara sara mata ita harya gama sannan ya yunk'ura da nufin tashi, maidashi tayi zaune tana fad'in "kasan me? bara na d'auko wata wuk'ar sai naga yanda zaka fereta , dan ba zan iya ba."
Tana fad'a ta koma d'akin ta d'auko wata wuk'ar, zaune tayi ta d'auki doyar tace "to fara ina kallo."
"Yanzu ina namiji meye had'ina da wannan aikin? bafa wuyane dashi ba."
"Ehe , kaji ka da wata magana, to miye a ciki? naga koda ma na iya ai zaka iya kama min aiki, koka manta ka fara bani tarihin rayuwar *Annabi muhammad (S.A.W)*, kuma kai ka fad'a min yana taya matanshi aikin gida, kaga kayi koyi dashi kenan."
Yamutse fuska yayi yace "Allah ko?"
"Eh mana, d'affak'a sunna." ta qarashe da d'aga mishi gira sama.
Ferewa ya fara yi itama tana ganin yanda yake tana yi, surutu kawai take zubawa yayin da shi kuma a d'arare yake, ya matsu koya tashi dan gidansu ana ganinshi anan duk iliminsu zai tashi a banza, za ace ya zama mijin tace kawai, duk a ciki qwaya biyu kad'ai ta fere shima saida Umar ya d'auka a nuna mata yana fad'in "dubi bata feru da kyau ba."
Suna gamawa ta mik'e tsaye da wuk'a a hannu tana gilmawa da ita ta gabanshi tana fad'in "gashi yanzu harka samu lada, to me zanyi a gaba?"
Qarewa yayi a kujerar yana kallonta da tsoro cikin zolaya yace "wuk'a fa kike nuna ni da ita, zaki yankeni fa."
"To nidai fad'a min me zanyi?"
"Ki kunna wuta saiki d'ora tukunya , saiki wanke doyar ki zuba a ciki bayan kinsa ruwa saiki zuba gishiri."
"Yeeeee, ashe mijina kuku ne." ta fad'a da rumgumeshi.
Yanda ya fad'a tayi amma shiya kunna wutar dan kasawa tayi, suna azawa ta kuma cewa "to saime yanzu?"
"Ki yanka albasa ki b'are tafarnuwa, kinga ni tafiyata zanyi."
Albasa ta d'auka da nufin yankawa amma da qyar ta samu ta fitar da hancin, hannunta ya kasa tsayawa sai rawa yake, shi dai yana kallonta har yaga wuk'ar ta kubce ta daki hannunta, saida ya rigata rintse ido danji yayi kamar wuk'ar ta sauka a qahon zuciyarshi ne, ji yayi ba zai iya jura ba, hakan yasa Umar Faruk cewa "kawo na yanka miki, d'auki tafarnuwa ki b'are."
Dad'i taji sosai nanta fara b'ara tafarnuwa amma fa shima ansha wahala, saboda akaihun dake hannunta duk sun rarraba tafarnuwa gashi ita kanta zafi take ji a akaihun nata, da qyar ta b'ara 'yar kad'an tace ta isa, "to ya zanyi yanzu?" ta tambayi Umar Faruk.
"Ki d'auko turmi ki jajjaga."
"Tu me?"π³
"Ba zan iya daka ba hannuna yayi ruwa." tana fad'a ta shiga d'aki jim kad'an sai gata da blender a hannu cikin kwalinta, bud'ewa tayi ta had'a sannan ta zuba kayan miyar gaba d'aya ta dawo d'aki ta jona a waya ta markad'asu, Umar Faruk kam cewa yayi "dama saboda irinku akayita."
Gama markad'an yayi daidai da dahuwar doyan, nanfa ta d'auko passoire (abin tace macca) da roba ta aje zata sauye doyar, wani k'yale tasa ta kama tasa zata sauke amma tace tsoro take ji karta zubar, karb'a Umar Faruk yayi ya juye mata zai jiyo ya kalleta yaji saukar sumba a kumatu tana fad'in "na gode Faruk."
Aifa buga k'wai a kazo, humm reader's kuzo kusha kallo wajen fasa k'wai.....
_Wai nikam wa yayi girkin nan ne, *Umar Faruk* ne, ko *Khairat*???_
*Ina buk'atar addu'arku masoya.*
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_πππJe vous aime tellement.πππ_
_Bismmilahir-rahman-rahim_
3⃣7⃣
Tana bugawa da k'arfinta k'wain ya baje gaba d'aya, kallon Umar Faruk tayi da yake mata dariya yana rufe baki, fashewa tayi da kukan shagwab'a harda turmusa qafafu a qasa, tasowa yayi ya tsugunna kusanta ya dago fuskarta ya fara share mata hawayen yana fad'in "haba babyna, kiyi hak'uri ki daina kukan, kawo na fasa miki."
Karb'a yayi ya fasa k'wain kafin ta zuba kayan had'i yace ta soya, a tak'aice dai haka tayi suyar rabin mai ya zube qasa rabi ya fallatsar mata a jiki rabin kuma ya qone bayan ta kammala, sauce d'in ta had'a shima da taimakon Umar Faruk har suka gama, idan ka ganta saika tausaya mata kuma ta baka dariya, saboda yanda ta had'a zufa ta ko ina biyar jikinta take, amma saboda turarukan dake jikinta yasa zufar ke fitar da k'amshi, sauke kaskon yayi daidai da fara kiran sallah, da gaggawa Umar Faruk ya shiga yayi wanka saboda duk jikinshi ya d'auki odeur d'in abinci kafin ya fito da gaggawa ya nufi masallaci.
***************
Abincin da Zuby ta kawo masa kuma Ruk'ayya ce ta had'a da kayan wanke wanke zata kai wajen da zata wanke, cikin tsautsayi kwanukan suka zube qasa abincin ya b'are, Mama dake zaune saida tayi ta mata fad'a saboda ganin abinci lafiyayye ya zube, hak'uri taba Mama tare da gyara wurin kafin ta fara wanke wanken.
*****************
Kasancewar Khairat yanzu ba abinda take bawa mahimmaci kamar sallah yasa ko wanka bata tsaya yi ba tayi alwala tayi sallah, tana gamawa ta fito ta zuba abinci a wasu shegun kwanukan masu kamar yan shafesu da gold ta zuba, akan tebur ta kai ta aje sannan ta d'auko carap (jug) wanda sukayi daidai da kwanukan ta aje sannan ta d'auko lemu a cikin fridge *chivita* ta juye a ciki, tana jin kiran sallah kuma ta mayar da isha'i sannan ta shiga wanka.
Tana shiga Umar Faruk ya shigo gidan, zaune yake yana jiranta ta fito suci abincin yaji ko zai ciyuπ amma shiru, yunce ke ciciyarshi saboda tun break d'in safe baici komai ba sai kayan marmari, hakan yasa ya janyo plate ya d'auki cokali ya bud'a kwanukan, lumshe ido yayi danko ba dad'i dai akwai k'amshi, jin k'arar ruwa yasa ya kalli douche d'in yace "aifa, mod'a kenan sarkin wanka, an samu randa sai nink'aya ake."
Saida yasa hannu ya d'auki yankan doya d'aya ya dangwala sauce d'in yakai baki ππ, "tohhh, ashe dai na iya girki."
Ya fad'a yana qara dangwalar wata sauce d'in, d'iba yayi ya zuba a plate ya fara ci ba k'akk'autawa, duk a zuwan shiya iya girkiπ _karka raina mana hammata mana_, harya kusa gamawa ta fito, kallon kallo suke tana kallon plate d'in,
"malam Umariri kenan, bako bismillah?"
Lumshe ido yayi yace "um um, idan na gama kinci."
Qara d'aure towel d'in dake qirjinta tayi ta zauna kusanshi ta d'ora hab'arta akan kafad'arshi ta rik'e damtseshi sosai tana fad'in "fad'a min na iya girki ko?"
Hararanta yayi yace "kaji malama, ki kayi girki a ina? na iya dai."
Cakulkuli ta masa tana fad'in "wallahi sai kace na iya girki sannan zan rabu da kai, kaji mutum duk qoqarin nan da nayi."
Cikin dariya ya tuntsire baya ya kwanta saman kujeran yana kare kanshi yana fad'in "kin iya, kin iya Hajia rumdub'e."
Tsalle tayi ta tashi daga wajen tace "wayyo Allah Mamie na."
Ta fad'a tana d'aukar wayarta, kira ta aikawa Mamie kuma cikin sa'a ta d'auka, Mamie na d'auka cike da zumud'i Khairat tace "Mamie albishirinki?"
"Goro fari tas shalelen Papa, badai kin samar min d'an jika ba?"
Da k'arfi ta fad'a kan gado tayi ruf da ciki tace "kash Mamie, wane irin jika kuma yanzu? da wuri haka? nifa dan nace miki ne yau da kaina nayi girki, kuma yayi dad'i."
Jim Mamie ta d'anyi dan sai yau kuma yanzu ta fahimci wani babban kuskure data tafka, amma saita basar tace "ayya, gaskiya na miki murna, to ki dage kinji ko, kuma da mijinki zai amince da saiki dinga zuwa ina koya miki? dan wannan aikina ne a matsayina na uwa."
"Humm, sai yanzu kika fahimci hakan? to naji zan masa magana, idan ya amince zaki ganni, idan bai amince ba bazan zo ba, ki gaida Mammie."
Tana fad'a ta kashe wayar ba tare data juyo b'angaren da Umar Faruk yake ba, dan itama sai yanzu taji kunyar kanta ace bata iya girki ba, abu d'aya taji ya shiga ranta shine ta koyi girki kota halin yaya, daga haka kuma tana tunanin nan bacci ya d'auketa saboda wahala da gajiyar da tayi.
Saida ya gama ya wanke hannayenshi yazo kan gadon, saida ya tsaya bayanta ya lek'a kanshi ta fuskarta cikin kunne yace "gaskiya kin iya girki, ban tab'a cin abinci mai dad'in wannan ba."
Jin shiru yasa ya sake cewa "ya ku kayi da Mama? naji kince zaki nemi izini na."
Nanma shiru ba amsa, gyara kwanciyarshi yayi ya mirgino da ita gabanshi, kasak'e yayi yana kallon kyakyawar fuskarta da tayi fiyau da ita saboda ba'a shafa komai ba, towel d'inta ne ya d'an sassauto daga qirjinta, a hankali ya shafi fuskarta har zuwa qirjin nata kafin yasa bakinshi ya fara tsotsa.
A cikin bacci taji manya manyan sak'onni na isketa, babu yanda ta iya data kama mishi suka shiga wata duniyar, sunyi nisa sosai kamar kullum ya fara k'ok'arin wuce gona da iri, dakatar dashi tayi amma sam baya jinta dan haka ya matseta sosai ya rad'a mata "me yasa Khairat, dan Allah ki barni, yau kad'ai ya rage min a cikin sati d'aya da zan miki."
Shiru tayi saboda wata guduma data daki zuciyarta da k'arfin gaske, jerowa kanta tambayoyi ta fara yi _"yanzu shikenan daga yau ni da Umar Faruk, yanzu duk abinda yake min shi zaije yayiwa yarinyar can, yanzu duk soyayyar da yake cewa yana min da kuma nuna min da yake, daga gobe zai fara nunawa wata irinta koma fiye da ita, tunda ita ya santa 'ya mace, kenan sanfiri ne suka nuna min d'azu shi yasa na sameta a d'akina, wayyo Allah na, gashi bana da wannan abun bare na bashi kaina ko nima yayi alfahari dani, to miye abunyi yan....."_
Bata fad'a ba taji Umar Faruk na fad'in *"Allahumma janibna shaid'an, wa jannibi shaid'an ma razak'tana."*
Lumshe idonta tayi hawaye suka zubo mata, ji tayi ta rasa duk wani kuzari da k'arfinta, jira kawai take yayi abinda zaiyi da ita, idan kuma ya gama ya koreta gidansu dan tasan qarshen alak'arsu ce tazo, to in kinsan haka me zai hana ki hana mishi kanki? ko dai kina son farin cikinshi ne? in kuwa hakane kema kina sonshi kenan kuma so na gaskiya.
ππππππππππππππ
Bayan doguwar wahala da jarumta da *Jihadi* da kuma gumurzu da Umar Faruk yasha kafin ya samu hanyar wucewa, a qarshe dai ya samu ya wuce bayan 'yan dubaru tare da taimakon zuma da vaseline kuma yayi nasara.πππ
_Hmmmmmmmm_
*KHAIRAT* dai naga kuka take, amma Umariri bansan ainihin meye yake ba dan ban fahimceshi ba sosai, kwance yake yana kallon rufin d'akin yayin da kukan Khairat ke hanashi tantance yanayin da yake ciki, jin ta qara sautin kukan ne yasa ya juyo da ita ya d'ora kanta akan qirjinshi yana shafar gashinta, ba zai iya magana ba a halin da yake ciki shi yasa yayi shiru yake daddab'ata kwai.
Jin tak'i yin shiru sai rera kukan take kamar wata sabuwar amarya yasa ya fizgo nutsuwarshi ya mayar a jikinshi ya saisaita kanshi cikin murya qasan mak'oshi yace "Khairat, kinsan yanda nake jin kukan nan naki kuwa? tamkar zubar tafasasshen ruwa ne a jikina, a halin da ake ciki yanzu Khairat, kukanki shi yafi komai d'aga min hankali, dan Allah kiyi shiru ki daina kuka, nasan na rabaki da abinda yafi komai, kuma ba zan iya maido miki shi ba, amma in har hankalinki zai kwanta ne kawai idan na maido miki shi, to ki shirya yanzu, saina rama miki abinda na miki."
Duk da barkwanci ya mata a qarshe, amma abinda ya fad'a shine mai mahimmanci a wajenta, yunk'urawa tayi ta tashi tayi saurin qamqame hannunshi ta rintse ido tace "washhh."
Janyota yayi ta koma jikinshi yana fad'in "kiyi a hankali mana, kinfa aikatu sosai."
Nanma dai bata kulashi ba sai cewa da tayi "meka karb'a daga gareni?" cikin muryar kuka harta shak'e.
Saida ya lumshe ido yana shafa bayanta yace "abinda yafi daraja a wajen 'ya mace mana."
Cikin shakk'ak'ar muryarta tace "ban gane ba, me kake nufi?"
"Ina nufin budurcinki."
Ji tayi kawai yana mata izgili ne dan haka ta tashi zaune da qyar ta fashe da sabon kuka, shi kuma kamar tana tsikara masa wani abu haka yake jin kukanta, janye hannayenta yayi yasa nashi hannayen yana goge mata hawayen, d'ago da kanta yayi yana kallon idonta duk sun kumbura sunyi ja, kai ya girgiza mata cikin rarrashi ya fara da,
"Khairat, nasan me kukanki yake nufi, amma kafin nace komai ina so ki sani kuma kisa a ranki cewa, babu wani d'a namiji a duniyar nan daya tab'a sanin Khairat a matsayin 'ya mace sai mutum d'aya, mijinki na sunna, wato *Umar Faruk* ni kenan, ina so ki manta baya ki fuskanci gaba, nima kuma abinda zanyi kenan a yanzun, ki d'auka a ranki babu wani abu daya tab'a shiga tsakaninki da wani sai yau kuma dani, ina fatan kin fahimceni? kuma zaki bani goyon baya tare da mallaka min kanki ni kad'ai naci gaba da saninki har qarshen rayuwata kamar yanda ni na fara, shin kin amince zaki bani kanki ki zama tawa har abada?"
Fashewa tayi da wani kukan ta rufe bakinta tana girgiza masa kai, da qyar ta fara magana cikin kuka tace "kayi hak'uri Umar Faruk ka yafe min, na kasa kawo maka abinda yafi komai mahimmanci, abinda kowane namiji yake burin samunshi a tare da iyalinshi, amma ni na kasa, na kasa Umar Faruk, ban cancanci yafiya ko soyayyarka ba, amma ka sani nima nayi iya k'ok'ari na Faruk dan ganin na kare makashi ,amma kuma sunfi k'arfi na."
"Khairat, karki damu kanki da wannan, ni ba shine a gabana ba, nifa ke nake so kuma so na gaskiya nake miki, Khairat zan iya zama dake a kowane irin yanayi a kowane hali, ni zan jure rayuwa dake ba zan tab'a barinki ba Khairat duk tsanani duk wuya."
Kai take girgiza masa tana fad'in "ba gaskiya bane Umar Faruk, kawai dai ka b'oyene dan karna fahimta, amma dole zaka ji ba dad'i tunda zuciya ne da kai, kuma zuciya bata da k'ashi, Umar Faruk ba zan iya cutar da kai ba, dan Allah kace na tafi gidanmu, dan nasan koba yau ba zaka goranta min haka ma 'yan uwanka, ni kuma ba zanso ranar da za'a wulak'antani ba akan abinda bani nayiwa kaina ba."
"Babu wanda zai wulak'antaki Khairat, ina tare dake, wallahi wallahi Khairat ni _Umar Faruk, nayi alk'awarin ba zan tab'a bari wani ko wata ya sake cin zarafinki ba, ke matata ce kuma uwar 'ya'yana, zan iya b'atawa da kowa a kanki Khairat inhar kika cire iyayena, Khairat ki yarda dani kema ki bani kanki danni na mallaka miki kaina, kiyi yanda kike so dani Khairat, wallahi sai yanda ki kaso za kiyi dani bana da bakin magana."_
A take maganar Mamie ta fad'o mata a rai cewar tana so a daren farkonta ta samu kyauta zuviyar mijinta dashi kanshi, share hawayenta tayi danta hango tsantsar gaskiya a tare dashi, hannunshi ta kama tana d'an murmushi tace "Faruk ka yafe min, nayi maka laifi a baya , amma yanzu zan gyara kuskure na."
Fuskarta ya shafa yace "wane irin laifi kuma? a iya sanina nidai babu."
"Akwai Faruk."
"To ina jinki."
Qasa tayi da kanta cike da kunya tace "ranar dana fad'a maka kalmar so, wallahi a ranar ba daga zuciyata ta fito ba, amma yanzu na fahimci kaine wanda ya dace naso kuma kafi cancanta dani, Umar Faruk ka yafe min dan Allah, wallahi yanzu ina sonka so na gaskiya nima."
Murmushi yayi tare da janyota jikinshi, "washhhh." ta fad'a saboda zafin da taji daga qasanta.
Da sauri ya kalleta yace " ayya sannu, bara na d'ora miki ruwan zafi kinji."
Yana fad'a ya sauka daga kan gado ya d'auko doguwar riga yana zura, wani kallo ta dinga masa hakan yasa yace "kodai na dawo ne?"
"Ayi me?" ta fad'a tana kallonshi.
" *Jihadi* mana."
Da sauri ta juya baya tana fad'in "a'a ba dani ba, kaje kai kad'ai."
Fita yayi ya d'ora mata ruwan, kafin suyi zafi kuma ya shiga wanka, sai lokacin ne ya fara jin wata irin matsannanciyar qaunar Khairat na sake ratsa kowace gab'a ta jikinshi, sonta kuma ya gauraya da numfashinshi ta yanda baya jin zai iya rayuwa babu ita, rufe ido yayi yana tunano abinda ya faru awa biyu data wuce, tabbas Khairat ta cancanci ya mallaka mata komai daya mallaka a fad'in duniya, ta cancanci ya sota fiye da yanda yake son kansa, tabbas Khairat ta bashi farin cikin da tunda yake a rayuwa bai tab'a shiga kwatankwacinshi ba, hak'ik'a in dai har haka Khairat take to zai dage da addu'a Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakaninta da Zuby, dan Khairat da Zuby tamkar moto ne da jirgin sama, murmushi ne mai tsadar gaske a fuskarshi harya fito ya juye mata ruwan.
Tuna irin wahalar da yasha yayi kafin ya samu k'ofar shiga, hakan ma yasa yayi wani tunani, anya kuwa an yiwa Khairat fyad'e, anya maza hud'u sun santa a matsayin 'ya mace, taya wacce maza hud'u suka yiwa fyad'e da k'arfi kuma take tsuke haka, me yasa, me yasa to???
D'aga kafad'a yayi yace " Umar Faruk dai a budurwa ya samu Khairat, dan haka daga yau babu wanda zai sake aibata min matata."
"Gaskiya ne an mata fyad'e." cewar wani b'angare na zuciyarshi.
Da sauri ya tusa hannunshi cikin kanshi saboda bala'in kishin da yaji ya taso mishi, kenan in dai har wasu sun rigashi saninta, kenan duk abinda yaji suma sunji, watak'ila ma fiye da wanda yaji tunda su sune farko, rintse ido yayi sosai zuciyarshi na tafarfasa kamar zata fito ga wani irin haushin su Musa ya kamashi.
Haka kuma ya fito sam ba walwala a tare dashi, duk da ya taimaka mata ta samu ta gasa jikinta tare da tsarkake kanta, amma ta lura da sabon canji daga gareshi, daurewa kawai tayi dan tasan dole zata fuskanci wannan matsin dama, doguwar rigar bacci tasa ta kwanta zuciyarta na rawa tana ji kamar ta sake fashewa da wani kukan, juya mishi baya tayi dan tasan ko ba tayi ba shi zaiyi, bacci harya fara d'ibarta saboda wahalar da tasha kawai taji Umar Faruk ya mirgino da ita ya d'orata akan qirjinshi yana shafata tare da daddab'ata, wani farin ciki ya lullubeta hakan yasa ta qamqameshi ta fara sauke numfashi sai bacci.
Ci gaba yayi da shafarta yana sumbatarta yana sake matsata a jikinshi shima har baccin ya d'aukeshi......
_Me kuka ce masoya?_
πππ
06/08/2019 Γ 00:06 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
πππππππ
_My *Heenat*, my *Meelat*, my *BK*, haqiqa kun taka rawar gani a cikin rayuwar Sameera ta yanda harta kawo yanzu data zama wata tsiya, ku na dabanne a gareni kuma na musamman, ina alfahari daku mutanena._
ππππππ
_Bismmilahir-rahman-rahim_
3⃣8⃣
Ganin yanda take baccin tana sauke numfashi yasa kawai ya gyara mata kwanciyarta ya tashi ya tafi masallaci, bai jima yau dan ana sallamewa ta dawo gida, yanda ya barta haka ya sameta saida ya sake kura mata ido ya kalleta yana ji komai nata na birgeshi kuma yana da kyau kafin ya tangale kanshi da hannu ya sumbaci bakinta, a hankali Khairat ta fara bud'a ido harta sauke akan Umar Faruk, murmushi ya sakar mata tare da fad'in "barka da asuba *madame Faruk*."
Itama murmushin ta sakar masa ta shafi fuskarshi tace "barka da asuba malam Faruk."
Saida ya d'ora bakinshi a kumatunta yace "ya jikinki?"
Zanin rufar dake jikinta taja ta rufe fuska tana murmushi, kallonta yake yace "wai kunya, to bara ki gani."
Yana fad'a ya zame zanin rufar yayi sama da ita bai tsaya ko ina ba saida ya direta douche, bud'a ido tayi ta kalleshi yace mata "akwai ruwan d'umi a butar nan, nasan zasu miki anfani."
Cikin shagwab'a tace "uhum uhum, nifa zafi nake ji."
Sumbatar bakinta yayi yace "hak'uri za kiyi, dole kiyi anfani dasu, inba haka ba kuma."
"Inba haka me?"
"Kedai ki gama kawai ki fito." yana fad'a ya fita ya barta.
Kafin ta dawo harya canza zanin gadon tare dana rufa, cire rigarshi yayi ya kwanta dan wani sanyin baccin ne yake jin yana ratsashi, shigowarta ce yasa ya bud'a ido, yana kallonta harta canza kaya ta fara sallah, tana gamawa kuma ta d'auko kayan karatu tazo ta hau gadon itama, a pillow d'aya kansu yake ta bud'a littafin amma fa yau an samu matsala, saboda rashin bitar karatun da ba tayi ba yasa sam ta kasa kawoshi yau, kallon da Umar Faruk ya mata yasa ta lab'e baki, fuskar nan a had'e yace "kika min kukan nan karyaki zanyi, mena miki to, tun ban dakekin ba?"
Zaune ta tashi tace "yanzu saika dakeni?"
"Me zai hana? ai karma kiyi tunanin zan d'aga miki qafa, dan yanzu muna matsayin malami da d'aliba ne."
Za tayi magana yace "sauka qasa."
Baki ta bud'e tana kallonshi, "dake fa nake magana."
Bata daina kallonshi ba harta sauka tayi tsaye tana kallonshi, qare had'e rai yayi yace "aro min cazar wayarki."
Juyawa tayi ta d'auko cazar ta kawo mishi, "gwiwanki qasa." ya fad'a.
Da mamaki take kallonshi sai kuma ta tuna ranar data sakashi zube gwiwoyinshi qasa a office d'inta, a hankali ta sulale qasa tana ci gaba da kallonshi, sai lokacin ya kalleta ya tashi zaune, kallonta yake sosai yace "meya hana ki kawo karatunki yau?"
Had'e baki tayi tana rarraba ido ta kasa magana, muryarshi taji yace "wasa kika tsaya ko?"
Baki bud'e take kallonshi hakan yasa yace "rufe bakin, sannan ki bani hannunki."
Mik'a masa hannu tayi tunaninta zai taimaka mata ne ta tashi zaune, harara ya wurga mata yace "tafin hannunki."
Da sauri ta juya tafin hannun tana kallonshi kamar sakarya, ganin ya d'aga cazar wayarta zai tsula mata a hannu yasa tayi saurin janye hannun tayi baya da k'arfi, da azama shima ya rik'o hannunta ta dawo gabanshi, tana ganin haka tasa kuka tana fad'in "wayyo Mamie na dan Allah ki taimakeni, kayi hak'uri malam wallahi gobe zan kawoshi, dan Allah karka dakeni, banda lafiya fa."
"Meya sameki?" ya fad'a fuska a had'e.
Cikin turo baki tace "to ba kaine ba jiya da daddare ka...."
Hannu yasa ta rufe mata baki ya zaro mata ido yace "idan har akace muna cikin ajin karatu, to zaifi miki kyau ki manta da abinda ke tsakanina dake, na fad'a miki haka tun farkon fara karatunmu, ki d'auka abinda ya faru jiya da mijinki ne, yanzu kuma kina ajine gaban malaminki."
"Kin fahimta?" ya fad'a da sake zaro mata ido.
"Eh, eh na fahimta."
"Bani hannunki." yayi maganar yana sakin hannunta yana gyara cazar hannunshi.
Yawu ta had'iye sosai ta fure ido ta bashi hannun, "ahhhhhh."
Ta fashe da qara saboda cazar data ratsa hannunta, sake rintse idonta tayi sosai hawaye na zubowa taji yace "bani hannun."
Gani nayi shima ya rufe ido tare da kau da kanshi sannan ya sake tsala mata a hannu, da sauri ta janye hannun tana matsashi da d'aya hannun tana kuka, jin shiru yasa ta ta bud'e ido a hankali hawaye suka sake zubowa, yana ganin ta bud'e ido ya basar ya daidaita kansa kamar baiji komai ba, alhalin ita taji zafin ne a hannu shi kuma zafin yana ratsa zuciyarshi ne, da hannu ya nuna mata gefenshi ta zauna sannan ya sake maimaita mata karutun jiya tare da qara mata kad'an.
Suna gamawa ta haye gadon taja zanin rufa ta kalleshi a lokacin daya tashi yana zura rigarsa tace "in dai sunana Khairat, wallahi daga yau ba zaka sake dukana ba akan rashin kawo karatu."
Dariya yayi lokacin daya saka rigar ya matso kusanta tare da manna mata sumba a goshi yace "haka ake son d'alibi ya zama, fatan alkairi madame Faruk."
Tana kallonshi ya fita daga d'akin tasan wajensu Mama zaije ya gaishesu da kuma Zuby, tashi tayi itama ta canza kayan jikinta tasa hijab sannan tabi bayanshi, d'akin Mama ta fara shiga ita shi kuma d'akin Mama Sa'a, a haka suka dinga sab'ani shi zai shiga can ita ta fito, saida ta gama ta fito zata koma d'aki ta ganshi ya nufi d'akin Zuby, da sauri ta qarasa d'aki ta haye gado tayi shiru, duk qoqarinta saida taji hawaye na neman zubo mata, basarwa tayi kawai ta d'auki wayarta da abin sauraro ta danna wani indian film tana kallo.
Yau ma haka ya fito daga d'akin Zuby duk da qoqarin da yayi ya rumgumeta amma ita sai tayi ta tureshi tana bata so, yana zuwa ya sake cire rigarshi ya kwanta kusan Khairat dan bacci yake so yayi sosai tunda yau lahadi ba aiki, ganin abinda take kallo yasa yace "kina jin me suke fad'a kenan? tunda naga kema 'yar garinsu ce."
Murmushi kawai ta saki ba tace komai ba, zare d'aya abin sauraron yayi yasa a kunnenshi yaji indianci ne, kallonta yayi yace "ki dinga fassara min to."
"To." ta fad'a tare da jinjina kai, suna rumgume da juna suna kallo tana fassara masa wani, wani kuma tayi shiru har bacci ya d'aukesu.
Tun Zuby na had'a abin kari take leken kofar tana ganin takalman Umar Faruk amma shiru ba motsinsu, harta gama taci tayi wanka ta shirya, mutanen gidan suka fara kujuba kujubarsu amma su shiru kake ji, zuciyarta ce ta fara tafasa ji take kamar ta dinga aika ashar ta yanda kowa na gidan hankalinshi zai tashi.
Ruk'ayya ma haka tazo ta tattara kwanukan wajen tayi wanke wanke tayi shara amma koda wasa ko lek'awa ba tayi ba bare taga meke faruwa, *10:25* Umar Faruk ya farka, saida ya fito daga wanka harya shirya kafin ya dawo wajen Khairat ya kalli fuskarta ya shafa, sumbatarta yayi a kumatu sannan ya daddab'ata.
Itama wanka ta shiga ta fito tana cikin shiri kuma Umar Faruk ya shigo da leda a hannunshi, plate ya d'auka ya juye musu abincin a lokacin ta gama shiryawa sannan suka ci, suna idawa ya kalleta yace "zan fita gari, ki kula min da kanki kinji, ina sonki *alkairina*."
Rumgumeshi tayi tace "nima ina sonka jarumina."
"Yaushe na cancanci wannan sunan?" ya fad'a da zolaya.
Cikin kunya tace " *daren jiya*."
Sake qamqameta yayi sosai yace "ashe jarumtata har takai haka? ai kuwa zan qara himma."
"Lahhh, idan ka qara himma zan iya mutuwa fa, wallahi ba qaramar wahala nayi ba jiyan nan."
D'ago fuskarta yayi yace "ki fad'a min sirrin abinda naji jiya, danni na kasa yarda cewa wasu sun fara..." sai kuma yayi shiru.
"Sun fara kafin kai?" ta qarasa masa.
Kai ya d'aga mata alamar Eh, cike da tabbatarwa tace "tabbas wasu sun rugaka, amma ni bansan komai ba."
Shafar jikinta ya fara tare da mata wani salo yana sumbatar wuyanta dan yaji zafin maganarta, kawai baya so ta fahimta ne, cikin rad'a yace "amma fa ni ban tabbatar ba, kawai dai nasan nasha wahala kafin na samu hanyar wucewa izuwa duniyar Khairat mai wuyar mantawa."
Idonta ne suka kawo qwalla ta kalleshi a marairaice duk tayi kalar tausayi tace "dan Allah ka fad'a min gaskiya Umar Faruk, shin nima zaka iya kallona da darajar da zaka iya kallon wacce ka samu a matsayin budurwa? Umar Faruk zan shiga tashin hankali da damuwa idan ka juya min baya, ba zan iya jura rasaka ba domin kuwa haka na taso tun farko, ina samun duk abinda nake so, bana so na rasaka Umar Faruk zan iya mutuwa, wallahi mutuwa zanyi idan ka wulak'antani ko ka rabu dani, Umar Faruk mutuwa zanyi ba zan iya rayuwa ba."
Ta qarashe da sulalewa qasa tana fashewa da matsanancin kuka, ita kanta bata san lokacin da take fad'an maganganun ba ta daisan kawai daga zuciyarta suke, shi kanshi ji yayi kamar zaiyi kuka amma dakkakiyar zuciyarshi ba zata bari ba , sunkuyawa yayi ya d'agota ya fara share mata hawayen kafin yace "Khairat, ki kwantar da hankalinki dan Allah ki sawa zuciyarki nutsuwa da salama, in dai har kin yarda da cewar kina samun duk abinda kike so, to ki yarda kin samu Umar Faruk, Khairat ki d'auka Umar Faruk ya zama naki, kuma ba zan tab'a juya miki baya ba saboda kin zama rayuwata nima."
Cikin kuka ta kalleshi tace "ka tabbatar?"
"Na tabbata Khairat, babu abinda zaisa na gujeki, muna tare har qarshen ratuwarmu."
Dariya tayi tare da kamo kanshi tasa bakinta a nashi, saida taji ya fara birkicewa kafin ta barshi, cikin muryar galabaita yace "ni na wuce."
Hannunshi data rik'e yasa ya juyo yana kallonta da idonshi da har sun canza, "ya dai?" ya tambaya.
Langab'e kai tayi tace "ina so ne na maka kallon qarshe, dan daga yau zamu nesanta na d'an wani lokaci."
Shi kam harga Allah harya manta da yau ne, marairaicewa yayi ba tare daya nuna mata rashin jin dad'in hakan ba a fili yace "da nasan haka zan samu Khairat, da banyi qasa a gwiwa ba wajen wuce wannan wurin."
Cikin dariyar mugunta tace "nima da nasan haka zan sameka da jarumta, da ban yarda na baka ba ko jiya."
"Ashe dai na bada tsoro." ya fad'a yana shirin ficewa daga d'akin.
"Kawai ma, ba wani tsoro, kara nake maka dan kar kaji ba dad'i idan nace maka *ragon namiji*, amma ba komai da naji."
Juyowa yayi yana mata wani mugun kallo, k'ofar d'akin ya tsaya ya mik'o mata hannunshi yana murmushin mugunta yace "zo baby."
Ita kam da bata fahimci komai ba takawa tayi a hankali ba kamar yanda take tafiyarta ba tana d'an cije lips saboda ciwon da take ji a qafarta da qasanta, saida ta kusa kaiwa gareshi ya kauce da sauri ya shigo d'akin ya sake mik'a mata hannu yana fad'in " so nake naga kin taho kamar yanda kika saba da k'arfi."
Kai kawai ta girgiza masa ta sake tahowa a hankali, bata tantance ba taji ya fizgo hannunta ta fad'a qirjinshi, wata qara ta saki da k'arfi dan ji tayi kamar qafarta ta cire hakama k'ugunta, rufe mata baki yayi yace "me kika ji?"
D'agawa tayi daga jikinshi ta koma kan kujera ta zaune tana hararanshi, dariya kawai yake mata harya zo kusanta ya danna mata sumba a goshi ya tallabo fuskarta yace "ina sonki Khairat, ki kular min da kanki, saina dawo."
Janyo fuskarshi tayi ta sumbaci bakinshi itama tace "ina sonka baby, ka kula min da kanka, kuma karka bari wata ta qwace mana kai."
Dariya yayi yaja dogon hancinta yace "kishi ko? toni me zanyi da wata bayan Allah ya bani ku."
Bye bye ya mata ya fita, gyara zama tayi ta rumgume hannayenta ta shiga duniyar tunani, da farko kishi ne ke ciciyarta na abinda ya fad'a, amma sai tayiwa kanta karatun tanutsu ta shiga tunanin sabbin hanyoyin da zata samu zuciyar Umar Faruk, dan yanzu itama sonshi take so na gaskiya, sai inda k'arfinta ya qare a kanshi.
****************
Mamie ce zaune tayi tagumi Mammie ta sameta a wurin, harta zauna bata sani ba saida ta d'aga murya wajen magana, "ke, waime kike tunani?"
"Na'am Mama, ba komai."
"Ya za kice ba komai bayan ga komai na gani, fad'a min meke faruwa?"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Mama, sai jiya na tuna da wani *kuskure* da nayi mai girma a rayuwa wanda ba lallai yanzu ya gyaru ba."
"Wane irin kuskure ne wannan da ba zai gyaru ba?"
"Mama, jiya Khairat ta kirani take fad'a min da kanta tayi girki, Mama abin takaici shine dad'i take ji saboda tayi girki d'aya tak a gidan miji, tun farko dana koya mata da duk haka bata faru ba, yanzu bansan ya za tayi ba gashi tana da kishiya, Mama nayi kuskure sosai a game da rayuwar Khairat, tabbas bamu rik'eta ba kamar yanda ubangiji yace mu kula da 'ya'yanmu ba, rashin iya girki ba qaramar matsala bace a gurin 'ya mace, shi yasa nake tunanin abinyi."
Saida Mammie ta jinjina al'amarin kafin tace "akwai mafita har yanzu, duk da tayi aure ba zai hana ki jata a jikinki ba sannan ki koya mata girki."
"Nima haka nace mata jiya Mama, amma kinsan halin Khairat."
"Karki damu, ni zan mata magana saita fara zuwa nan kina koya mata in mijinta ya amince."
"Yawwa Mama na gode."
"Karki damu."
***************
*16:30* Khairat na zaune tana waya da Papa, tambayarta Papa yayi ita kuma ta fara kora mishi bayani kamar haka "wallahi Papa ba komai, Faruk yana sona kuma nima ina sonshi, kuma kaga zamu zo tare dashi Germany, ina farin ciki da kasancewarmu tare, kuma kunga yana koya min karatu kullum, yanzu haka na kusa zama malama."
Ko bata fad'a ba Papa yasan ta canza daga yanda ta kirashi da kunga a maimakon baya da take cewa kaga, "ai kuwa ya kyauta, da alama wannan mai sa'a ne tunda yayi sa'ar shiga zuciyar gimbiyata , dan haka ki fad'a min me kike so na masa?"
"Kawai Papa kaima ka soshi, sannan ina so ka samar mishi aikin da yafi wanda yake yi a k'arkashina, saboda matakin karatunshi ya wuce nan."
"An gama shalele , akwai manyan masana'antu a k'asashen waje da nake da hannun jari a ciki, idan kina so sai a samar masa d'aya daga ciki."
"A'a Papa, bana son aikin da zaisa ya bar garin nan, in dama ni kad'aice da saimu tafi tare, amma mu biyu ne."
"Ai yanzu anci gaba shalele, zai iya zama anan kuma yana aiki a k'ark'ashin wani ma'aikatar, computer ta isa tayi komai."
"To Papa, kayi abinda ya dace kawai." haka dai suka jima suna waya kafin sukayi sallama.
Sallama take ji daga k'ofar d'akin kamar muryar data sani, "shigo." shine abinda ta fad'a cikin d'aga murya.
Tana bud'a labulen d'akin ta shigo Khairat ta daka tsalle tare da ihu ta rumgume Hibba, murna sukayi sosai har Hibba ta dago da ita tana fad'in cikin harshen zarma "oh Khairat, kin canza."
Itama a harshen zarma ta mayar mata da "ni ai na kusa nayi hushi dake, ace sai yau zaki zo gidana."
"Kiyi hak'uri Khairat, kinsan fa karatu yayi zafi, wallahi yanzu haka daga ecole nake tare da driver."
"Kuma fa hakane yan jarabawa ne." ta fad'a a harshen frensh.
"Zauna mana."
"Ba lokaci Khairat, yanzu haka ina zuwa gida zan tarar da malamin maths yazo."
Juyawa tayi Khairat tabi bayanta suka fita suna hira tana shaida mata zata zo ta wuni idan sun gama jarabawar , sai lokacin Khairat taga ashe yamma tayi sosai ita tana d'aki zaune, Zuby suka tsinkaya wajen girki ita da Ruk'ayya da Saratu suna kama mata aiki saboda yau zata karb'e Umar Faruk, sallama Hibba ta musu suka amsa cikin sakin fuska kafin ta wuce, Khairat ce ta dawo zata wuce Zuby ta bita da harara, Khairat kuma wani burin son koyan girki ne ya shiga ranta dan haka ta fara danna kiran wayar Mama daga shigarta d'aki, Zuby ma dai ji tayi itama tana fatan samun k'ugu da gaba irin na Khairat d'in masu kyau da d'aukar hankali.
***************
"Mamie, ki fad'a min yaushe zan fara zuwa wajen koyan girkin?"
Da mamaki Mamie tace "Khairat zaki koya? idan kin fad'awa mijinki ya amince zaki iya zuwa kowane lokaci."
"Ok zan fad'a masa, zaki ganni."
"Amma ba zaki bari harmu dawo ba?"
"Eh Mamie saimun dawo." tana fad'a ta kashe wayar.
Wayar Umar Faruk ta kira, "hello baby." ya fad'a daga b'angarenshi.
"Baby ya kake? "
"In dai kina lafiya, to nima haka."
"Lafiya lau nake, dama magana zamuyi."
"Yanzu kuma?"
"Eh."
"To ina zuwa."
"A'a ba sai kazo ba, zamu iya yi a waya ma."
"To ina jinki."
"Dama Mamie ce tace me zai hana na dinga zuwa gida tana koya min girki, shine nace zan fad'a maka dan saida amincewarka zanyi komai."
"Me kuwa zai hana baby, ki shirya kawai ki fara zuwa, ai farin cikina ne kuma jin dad'ina idan kika zama chief a wajen girki."
"Na gode baby, saika dawo."
"Muahhhhhhhh."π ta qarashe da sumbatarsa, saida ya lumshe ido saboda dad'i da yanda sumbar ta ratsashi.
*************
Kusan magrib ya shigo gidan tare da Abbakar, d'akin Zuby ya nufa yana kallon d'akin Khairat, da shigarshi bai sameta ba sai dai k'amshin turaren wutane ya mishi maraba, ga kwanukan abinci da aka jera masa abin birgewa, fitowa yayi ya d'auki buta ya fara alwala, yana cikin yi ta fito daga douche tayi wanka, saida tazo kusanshi zata shiga d'akin tace "sannu da dawowa."
"Yawwa sannu, ashe ana can ana wanka." ya fad'a lokacin da yake shafar kai.
"Um, na shiga wanka."
Aje butar yayi ya kalleta yace "na wuce masallaci."
"A dawo lafiya, amma fa karka dad'e." ta fad'a a shagwab'e.
Murmushi yayi yace "ba zan jima ba."
Masallaci ya wuce itama ta shiga ciki ta fara sallah kafin ta tsalla shirin tarbar mai gidanta.....
09/08/2019 Γ 21:40 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Wow wow wow wow wow wow wow wow, my *Heenat* ina tayaki murnar kammala wannan zazzak'an novel d'in naki mai sunan *nida yah Al'ameen*, a gaskiya ya ilmantar tare da nishad'antarwa, babban abin birgewa shine darasin dake ciki tare da manya manyan kalaman da ki kayi anfani dasu, shi yasa a kullum nake cewa ke *uwargijiyata* ce, insha Allah zamu kammala *k'angin rayuwa*, ina sonki tawa.ππ_
_Bismmilahir-rahman-rahim_
3⃣9⃣
Sai bayan sallah isha'i ya dawo gidan kai tsaye d'akinta ya wuce, tana zaune da alama shi kawai take jira, tsaye tayi tana fad'in "sannu da zuwa yah Umar."
"Yawwa sannu, ya gidan?" ya fad'a yana zaunawa da alamar gajiya a tare dashi.
Mab'allan rigarshi ya fara cirewa yana kallonta yayin da take zuba mishi jus d'in data had'a dominshi, saida ya cire rigar ya aje gefe sannan yasa hannu ya karb'i cup d'in da take mik'a masa, "na gode, Allah ya miki albarka." ya fad'a yana murmushi.
"Ameen yah Umar, nima na gode."
Yana shan sanyayyen jus d'in ta kuma zuba mishi abinci har kala uku, dad'i ne ya rufeshi sosai nan fa ya bud'e ciki ya kwashi abincinshi yasha ya k'oshi kafin yayi hamdala tare da sake saka mata albarka, kallonta yayi yace "dan Allah taimaka ki had'a min ruwa zanyi wanka."
"To yaya." ta fad'a tare da tashi.
Tana kai masa ruwan shi kuma ya fita yaje yayi wanka, koda ya dawo ya samu harta gyara wurin kamar ba aci abinci ba, yana so ya shirya kuma gaba d'aya kayanshi ne d'akin Khairat, kallonta yayi yace "k'anwata."
"Na'am yah Umar."
"Wallahi kaya nake son sakewa kuma gashi duk suna can d'akin."
Cikin murmushi tace "lah yah Umar, kaje ka d'auko mana."
Kanta ya dafa yace "Allah ya miki albarka."
"Ameen."
Fita yayi ya nufi d'akin Khairat, da sallama ya shiga ya sameta kwance akan gado da kayan bacci da littafi tana karatu, tana ganinshi ta mike tsaye akan gadon ta bud'e hannayenta, da azama shima ya qarasa wajenta shima ya rumgumota ya sauko da ita yana juyawa da ita tare da aika mata sumba, saida suka jima kafin ya sauketa suna kallon juna tace "nayi kewarka na wuni d'aya kawai."
"Nima haka, ya kike?"
Cikin turo baki gaba tace "lafiya k'alau, ya kake?"
"Tunda kina cikin k'oshin lafiya to nima haka."
Sakinta yayi ya nufi wajen kayanshi ya fara dubawa, bin bayanshi tayi ta mak'ale mishi a wuya yana ci gaba da da duba kayan yana d'auka, har saida ya gama tana bayanshi a mak'ale kafin yace "to sauko ni zan tafi."
Saukowa tayi tana fad'in "yanzu shikenan tafiya za kayi, ni kad'ai zan kwana?"
"Idan kina so na kwana ai saina kwana." ya fad'a kamar da gaske.
Da sauri tace "a'a ba dani ba, ba zaka jamin magana ba."
Rumgumota yayi ya sumbaci labb'anta yace "ki kula da kanki kinji."
"Insha Allah, saida safe."
A hankali yake sakin hannunta yana ji kamar karsu rabu, yana fita tabi bayanshi ta rufe k'ofar d'akin, kwance tayi tasa panka gabanta saboda zufar da take ji tana fito mata, bugawar da zuciyarta take ne da kuma harbawar da jijiyar kanta keyi yasa ta d'auko maganinta tasha sannan ta koma ta kwanta amma duk da haka tunani da kewar Umar Faruk sun dameta , abun kamar wasa saita fara tunanin irin abinda ke faruwa a d'aya d'akin, a hankali saita fara kuka har saida bacci ya d'auketa.
_ALLAH ka rabamu da haukan kishi, ka sausauta mana kishinmu._
A wajen ango kuma da amarya yana shiga ya sameta ta cancara wata arniyar rigar bacci, amma tana jin shigowarshi sai taji ba zata yarda ya ganta a haka ba, da sauri ta haye gado ta rufe da zanin rufa, shi kuma ya riga daya ganta sai dai ba sosai ba, aje kayan hannunshi yayi yana dariya ya mik'a mata hannu yace "zo mana."
Qara rufe fuskarta tayi tace "um um yah Umar."
"Taso mana, nifa mijinki ne, ina so na ganki da kyau."
Yanda yayi maganar yasa ta fara janye zanin daga jikinta, da qyar ta taso ta rarrafo ta sauko ta tsaya gabanshi amma tana kare jikinta, ganin yanda yake k'are mata kallo yasa ta rufe fuska ta juya zata koma kan gado ya rik'e hannunta, kwantar da ita yayi a jikinshi yana shafar duk wata gab'a ta jikinta, jin yana d'an wuce gona da iri yasa ta fara nok'ewa tana d'an tureshi daga jikinta, cikin muryar....yace "haba Zubeida, me yasa?"
Kwantar da ita yayi akan gadon ya fara sarrafata cikin k'warewar daya samu a kwanakin da yayi a d'aya d'akin, saida ya kai mak'ura yayi kwance yayin da ya rad'awa Zuby a kunne tare da kai hannunta a....... yana so ta bashi a gajin farko kafin suje mataki na gaba, sam Zuby tak'i tare da dauke hannunta da sauri saboda ita abarma tsoratata tayi ba kad'an ba, yayi juyin duniya ta masa dan zaiji dad'i sosai saboda ya d'an saba da hakan amma tak'i, (wacce ta kasa tab'awa da hannu zata iya sakawa cikin...πmy Heenat da aunty Aisha da auntyna Meerah suna nan), haka ya tashi ya fara hak'ar rijiyar amma baije ko ina ba Zuby ta fara masa kuka tana fad'in ta gaji ya daina zai kasheta, shi kam mamakinta yake ganin darensu na farko itace taja hankalinshi, (ranar ma ai sakata a kayi bayin kanta bane), haka ya tsaya babu abinda k'arda bare ya samu nutsuwa.
Duk da sunyi wanka bai hana ya matsata a jikinshi ba yana sumbatarta dan yana so ya manta da abinda zuciyarshi keta raya mishi, ma'ana yana so ya manta da Khairat a qwaqwalwarshi musamman da yake d'akin daba nata ba, Zuby kam ganin kamar zai sake takurata ne yasa ta tureshi daga gareta da k'arfinta jiki na rawa ta juya masa baya, dan harga Allah taji ya gundireta a yau d'in nan kuma tana ganin da alama zaiyi jaraba, basar da ita kawai yayi har bacci marar dad'i ya d'aukesu.
**************
Kamar yanda ya zama jiki kowa na gidan yayi sallah asuba kafin suka karya, Khairat ce yau tazo d'akin Zuby domin yin kari, ba yabo ba fallasa suka gama ta koma d'akinta, a lokacin da Umar Faruk zai fita saida ya shiga d'akin Khairat, duk da abinda ya dinga mata bata ji komai ba da qyar ta lallab'ashi ya fita, a motarshi yau ya fita Khairat ma a tata motar ta fita izuwa gida.
Ta samu Mammie da Mamie zasu tafi gidansu Muzaffar ganin mahaifinsu ba lafiya, a motarta ta kaisu gidan kuma suka shiga tare, zaune suke a falon Baban suna masa sannu da jiki, likita ne suka shigo tare da Muzaffar, ko kallonshi ba tayi ba yayin da shi kuma ya kasa d'auke idonshi daga kanta yana kallon yanda tayi wani b'ulb'ul da ita ta qara yin fresh da ita ta qara kyau, mamaki d'aya yake shine hijabin dake jikinta wanda kuma ya kare masa ganin muhimman abubuwan da suke birgeshi a kanta tun kafin aurenta, ganin likitan ya fara duba Baban yasa suka mishi sallama suka tafi yana binta da kallo yana d'an cije lips tare da had'e yawu.
*A d'an gurguje fan's.*
Kwana biyu kad'ai yayi a d'akin Zuby amma kewar Khairat ta dameshi, yafi jin dad'in zamanshi acan danko ba komai tasan yanda take tana samar masa da nutsuwa, a yanzu kam bai damu ba tabbas kunya tana da kyau ga 'ya mace, yana tunanin meye banbanci tsakanin Khairat da Zuby, koda kuwa Zuby kunya tafi Khairat kuma za'a kira Khairat da marar kunya to shidai yana son wannan rashin kunyar dan yana da tabbacin shine kad'ai keda Khairat a yanzun.
Khairat ma tana kewarsa kuma tana kishinsa, amma ganin lokacin tafiyarsu yayi yasa ta gama musu shiri tsaf gari kawai take jira ya waye.
Zuby kuma a nata b'angaren takura da jaraba ne kawai sukawa Umar Faruk yawa, a kwana biyun nan ya gama gubdurarta dan kullum cikin sumbata da shafe shafe yake, a cewarta komai saiya tab'a jikin mutum ita kam ba zata iya ba.
Duk ya gama sallama da 'yan uwa da iyaye wayewar gari yake jira yana ganin damace da zata sake mannashi da Khairat d'inshi.
***************
Yau ta kama yammacin ranar *talata*, kuma *awa* d'aya ce ta rage jirginsu ya tashi, Umar Faruk ne tsaye kofar d'akin Zuby bayan sunyi bankwana , a tsakar gidan ma duk mutanen gidan sun taru sai yara dake ecole, haka ma Ishaq yazo danshi zai saukesu aireport da motar Umar Faruk, Khairat ce ta fito cikin riga da siket na kanti masu masifar kyau sai d'an kwalin data yane kanta dashi, babbar jakarta ce a hannu da waya sai qaramin farin glass d'in dake hannunta, tsaye tayi gabanshi tana kallonshi da murmushi a fuskarta, hannunta tasa a hankali ta kamo nasa hannun ta rik'e sosai tace "mu tafi."
Ajiyar zuciya ya sauke ba tare daya kalli mutanen dake wajen ba dan soyayya ta rufe masa ido, sake qamqame hannunta yayi shima kafin ya janyota suka tsaya gaban iyayensu yace "iyayena mu zamu tafi, kuyi mana fatan alkairi."
Baba ne ya fara da "to Umar faruk, Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya, sannan ya dawo daku lafiya, sannan a kula sosai kaji, banda wasa da sallah da kuma karatu duk da dai ba jimawa zakuyi ba."
"Insha Allah Baba."
Khairat ce ta d'ora da "ai dama littatafaina zan tafi dan muci gaba da karatu."
Kallon Mama tayi tace "Mama zamu tafi, saimun dawo."
Addu'a suka musu Khairat kuma ta rumgume duka iyayen mata tare da Ruk'ayya, tana kawowa wajen Saratu ta tsaya tana kallonta, janyo Saratu tayi jikinta ta rumgume kafin ta saketa tana kallonta tace "ku kula da Yusuf."
Cikin murmushi da jin dad'i Saratu tace "insha Allah 'yer uwa, Allah ya tsare."
Hannun Umar Faruk ta sake kamawa suka juya zasu fita sukayi tozali da tanti Ma'u ta shigo cikin gidan.....
Kai tsaye wajen Zuby ta nufa dan tafi kusa da 'kofar shigowa, cikin rad'a tace "ke me yake faruwa a gidan?"
Itama cikin rad'a tace "Mama bana fad'a miki zasuyi tafiya ba? to ai yau ne."
Harara ta banka mata kafin tayi wajen da suke tsaye, Baba ta fara kallo tace "malam, da hankalinka da iliminka, amma shine ka amincewa Umar Faruk da sutafi da wannan karuwar yarinyar qasar waje."
Yanda maganar bata ma kowa dad'i ba haka ma Umar Faruk, sunkuyar da kai yayi yace "dan Allah tanti ki daina kiranta karuwa, hakan ba kyau."
"Kai tafi can dallah, ba dakai nake ba da mahaifinka nake, zan dawo kanka daga baya."
Maida kallonta tayi ga mahaifiyar Umar Faruk tace "ke dama bana take, dan kowa ya debo shararshi kanki yake dorawa, amma ki sani za kiyi nadama inhar kika bari d'anki ya tafi tare da wannan yarinyar, danna tabbata wani mugun abu suke nufinshi dashi."
Kallonta takai ga Umar Faruk tace "kai kuma, me kake nufi, kana so kace 'yata zatayi zaman gadi ne a gidan har lokacin da kuka gamo gantalinku kuka dawo sannan ka sameta? to bari kaji sam ba zai yiwu ba wallahi, kamar yanda wannan abar take matarka haka itama Zuby matarka ce, dan haka babu inda zaku je ba tare da ita ba, in kuma kace tafiya zakuyi to akwai sharad'i."
"Sharad'i na farko shine, kodai ku tafi da ita, ko kuma dai kaika fasa tafiyar ka barta ita kad'ai ta tafi dan dama ita ta saba bi garinta , k'in d'aya daga cikin biyun nan, to ka sani kana tafiya nima zan tafi da Zubeida daga gidan nan, kuma yanzu basai an jima ba."
Shafa wuyanshi yayi yana tunanin abinyi Baba ne yace "haba Asma'u, bai kamata irin wannan magaganun na fitowa daga bakinki ba, kefa babba ce zaki iya jawa kanki raini a wajen 'ya'yan cikinki, da amincewata ne Umar Faruk zaiyi tafiyar nan, kuma ina da tabbacin babu abinda zai faru, tunda Umar Faruk namiji ne ita kuma mace, dan haka ki dubi girman Allah ki barsu su tafi."
Cikin d'aga murya irin na marasa nutsuwa tace "iyee , yau ake shirin yinta fa a gidan nan, lallai abin duniya ya rufe muku ido, inba haka ba kai yanzu har wani alfahari kake saboda d'anka zaiyi tafiya da wannan, ko kunya baka ji ba dan Allah malam?"
Mama ce tayi k'arfin halin cewa "babu wani son abin duniya kamar yanda ba kwad'ayi bane, mu mutane masu girmama mutane da suka karramasu, alk'awari ma abune mai girma shi yasa muka amince su tafi tare, badan komai ba sai dan ya cika alk'awarin daya dauka, dan haka Umar Faruk zai tafi domin shima yanzu d'aya ne daga cikin dangin Khairat, danko yanzu bama cire rai kan cewar Khairat na d'auke da cikin Umar Faruk, kinga kuwa sun riga da sun zama d'aya, zaifi kyau ki barsu sutafi ba tare da rai ya b'ace ba, Zubeida kuma naga ai koba auren Umar Faruk a kanta ainan gidansu ne, dan gidan nan ba bakonta ba zata iya zama koba Umar Faruk, kuma da kike cewa zaki taf da ita saida izinin Umar Faruk Zubeida zata bar gidan nan."
Umar Faruk najin haka yaja hannun Khairat zasu wuce tanti ta sake shiga gabansu tana fad'in "wallahi idan kaga ka fita daga gidan toka tabbata ka bani takardar Zubeida."
Zuby na jin haka ta matso kusan mahaifiyarta ta dafa kafad'arta tace "Mama, ki daina dan Allah, karki rabani da mijina."
"Ke rufe min baki, duk danwa nake abun? badan ke ba."
Sake maida kallonta tayi garesu tace "kaga kaifa nake jira."
"Tanti...." hannu Khairat ta d'aga masa.
Kallon agogon hannunta tayi ganin lokaci yasa ta mak'ala glass d'inta a fuska wanda ya qara mata kyau, kallon idon Umar Faruk tayi tana murmushi tace "kayi hak'uri Faruk, ka zauna da iyalinka tare da matarka, ina cikin farin ciki kasancewarmu tare, bana so raina b'ace bare na b'ata ran wani, ni zan tafi."
Tana fad'a ta d'an d'aga qafafunta ta shafi fuskarshi tare da manna masa sumbata mai kyau a baki harda tsotsawa tayi kafin ta sakeshi a hankali suna kallon juna, kallon tanti Ma'u tayi fuska a had'e tace "ki tabbatar kun raba tsakanina da Umar Faruk kafin na dawo, idan kuma bakuyi ba, to ki sani al'amarin ba sauk'i dan dawowar ba zata muku dad'i ba."
Tana fad'a ta fara raba hannunta dana Umar Faruk wanda ya rik'e hannunta gam amma ya kasa magana saboda mutanen dake wajen, a lokacin data qarasa zare hannunta daga nashi saida ya rufe ido saboda bugawar da zuciyarshi tayi , ganin tana tafiya da gaske yasa murya qasa qasa yace "Khairat."
Duk da ba kowa yaji kiran daya mata ba amma saida ta juyo dan itama zuciyarta bugawar take, bye bye kawai ta masa ta wuce tare da Ishaq ya tafi kaita aireport dansu Mamie suna jiransu.
Yana ganin b'acewarta ya juya da sauri ya nufi d'akin Mama, da shigarshi ya fad'a kan gado ya fashe da kuka danshi ji yake kamar ta rabu dashi kenan.
Itama a mota cire glass tayi ta fara kuka Ishaq sai baice komai ba har suka isa, saida ta gyara fuskarta kafin ta bud'a murfin zata fita kuma ta tsaya, kallonshi tayi tace "Ishaq ko?"
"Eh Hajia."
"Dan Allah ka fahimtar da Umar Faruk banyi haka dan b'ata masa rai ba, na fahimci hakan ne kawai maslaha, inba haka nayi ba lallai ya hakura da tafiya dani ba saboda yamin alk'awari, bana so na zama silar samun matsala tsakaninsu, ka kula min dashi, karka bari ya shiga damuwa dan inada tabbacin son da yake min na hak'ik'a ne."
Tana fad'a ta bar motar bata jira me zaice ba, ta samu su Mammie na tsumayinta kuma suna daf da tashi, ai kuwa babu b'ata lokaci suka tashi duk da tambayar da suke mata ina Umar Faruk amma babu amsa, taga kawai take kallo hawaye nabin fuskarta danta riga data tsara yanda tafiyarsu zata kasance tare da bada armashi, a haka dai har suka sauka manyan jami'ai ne suka d'aukosu a filin jirgin kamar yanda shugaban qasar ya tsara kuma ake zuwa tarbar kowane babban bak'on.
Babban hotel ne aka kamawa manyan bak'in kowa da nashi d'aki mai kyau da 'kawa , kai tsaye Khairat d'akinta ta wuce zata shiga wanka saida taji inama suna tare da tare zasuyi wankan, haka ta fito ta shirya sannan suka fita wajen cin abinci tare da manyan mutane....
_Kar kuce bakuji dad'i ba da basu tafi tare ba, hakan ma nada nashi fa'idar._
πππ
09/08/2019 Γ 21:40 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
πππππππ
*my BK*
πππππππ
_Bismmilahir-rahman-rahim_
4⃣0⃣
Kallonta ake sosai saboda ganin shirin da tayi, doguwar riga ce ja mai kyan gaske da hannaye iya gwiwa, amma saita b'ata tsarin ta hanyar d'ora qaramin hijab wanda ya rufe mata wuya, kujera kawai taja ta zauna ba tare data kula dasu ba, abinci suke ci har lokacin da idonta ya sauka akan teburin da Muzaffar ke zaune wanda ya kasa komai sai kallonta, wata tattausa harara ta jefa masa kafin ta d'auke kanta, a haka suka gama kowa ya tashi dan komawa masaukinshi, Khairat na daf da shiga d'akinta taji an rik'e hannunta.
Da mamaki ta juyo tana ganin Muzaffar ta qara had'e rai tace "malam miye haka? sakeni dallah, ko ka manta ni matar aure ce?"
Wani murmushi ya mata yace "matar aure, to saime, ina mijin naki yake? ko dai shima ya kasa zama dake ne ya korok....."
Shak'ar wuyar rigarshi da tayi yasa yayi shiru, kamar zata sumbaci fuskarshi ta matso sannan tace "karka sake ka fad'i maganar banza a kaina ko mijina, danshi ba jahili bane irinka."
Sakinshi tayi ta bud'a d'akin da makullin da aka basu ta shiga ta kuma maida k'ofar ta rufe, yana kallonta ya jima kafin ya koma nashi d'akin yana mamakin yanda Khairat ta sake mulmujewa bayan yasan wanda ta aura ba mai kud'i bane, ga kyau data qara sai yaji sabon kishi da qaunarta sun mamayeshi, tana shiga ta cire doguwar rigar ta d'auki wata qaramar riga shara shara ta saka wacce ta tsaya iya k'ugunta, daga ita sai pant ta kwanta akan gadon ta d'auki waya ta dannawa Umar Faruk kira.
*************
Mama na ganin ya shiga d'akin itama tabi bayanshi, cikin tashin hankali da mamaki Mama ta qarasa kusa dashi ta dafa kafad'arshi, shiru bai d'ago ba amma saiya tsayar da rera kukan da yake, d'an daddab'a kafad'arshi tayi tare da cewa "Umar Faruk."
Tashi yayi zaune yayi qasa da kanshi yana goge fuskarshi kafin yace cikin muryar kuka "na'am."
Hab'arshi ta kamo ta mayar da kallonshi kan fuskarta tace "hawaye a idon namiji, meya faru Umar Faruk, meya saka zubar da hawaye haka, saboda ta tafi ne?"
Wasu hawayen ne yaji sun sake malalo mishi a fuska, hakalin Mama ne ya rubanya tashi da sauri tasa hannu ta share mishi tana fad'in "Subhanallah, dan Allah ka daina, kana tayar min da hankali mana, ka fad'a min meye damuwar."
Sake goge hawayen yayi ya saisaita nutsuwarsa sannan yace "Mama ban tab'a sanin a baya baso nake ba sai yanzu, ban tab'a sanin cewa Zuby ina mata son yan uwantaka bane saida Khairat ta shigo rayuwata,Mama ji nake kamar ta tafi da rayuwata ne, bansan me yasa naji na kasa tausar zuciyata ba, amma tunani nake kamar ta tafi kenan ba zata dawo gareni ba, wallahi Mama bana jin dad'i gaba d'aya, Mama ki taimaka min dan haka, ki taimaka min Mama."
Ya qarashe da fad'awa kan cinyar Mama da bai tab'a yin hakan ba tunda ya mallaki hankalin kanshi, cike da tausayinshi da qauna ta fara shafashi tana fad'in "kayi hak'uri babban mutum, bana son kukan nan kaji, insha Allah Khairat zata dawo, nasan ba zata wuce kwanan ukun da kuka d'iba ba dan na yarda da ita, maganar Zuby kuma Umar Faruk ni dama nasan babu soyayyarta a cikin zuciyarka, saboda ban tab'a jin kalmar so daga bakinka ba izuwa Zubeida, ba kai kace kana sonta ba mune muka hadaku, kuma cikin sa'a kuka mana biyayya baku bijire ba, ba zanyi mamaki ba dan yanzu ka samu masoyiyar zuciyarka, kamar yanda nake da yakinin ba zaka tab'a fifita Khairat akan Zubeida ba, saboda na yarda da kai kuma na yarda da tarbiyar da muka baka, bugu da qari kuma kana da zuciyar da zaka iya boye abinda kake so kuma kana da zuciyar da zaka iya son mak'iyinka ma, dan haka abu d'aya nake so da kai yanzu shine, ka cire wannan damuwar ka kuma kwantar da hankalinka ta yanda hakan ba zai shafi Zubeida ba, kaji ko?"
D'agowa yayi ya sake goge fuskarshi yace "to Mama, insha Allah zanyi yanda ki kace."
"Yawwa Umar Faruk, yanzu ka tashi kayi alwala, nasan yanzu an kira sallah saika tafi masallaci."
"To." kawai ya fad'a ya fita yayi alwala sannan ya bar gidan, lokacin tanti tabar gidan kowa ma ya kama gabanshi Zuby ma na d'aki tana kuka, ko kallon d'akinta baiyi ba dan maganar gaskiya ji yake baya son ganinta, yana fita yaji wayarshi na kururuwa, ganin bak'uwar number yasa ya saki murmushin gefen labb'a tare da d'agawa ya d'ora a kunne.
Cikin sanyayyen murya tace "baby, ya kake?"
Lumshe ido yayi yana jin wani irin dad'i da sanyi yana ratsashi, a hankali ya furta "banda lafiya, saboda kin tafi kin barni."
Rufe ido tayi kafin tace "kayi hak'uri, hakan ne kawai maslaha, amma ai zan dawo da wuri."
Takawa ya fara yi a hankali yana fad'in "baby kin tafi kin barni da sonki, Khairat, sai yau ne na qara tabbatar da irin son da nake miki, yaune na samu tabbacin gazawar da zanyi idan na rasaki, Khairat dan Allah karki rabu dani ki zauna tare dani hakan ne kad'ai zai sani farin ciki, sannan kiyi sauri ki dawo gareni dan a gaskiya ba zan iya farin ciki ba alhalin kina nesa dani."
Hawaye ne suka fara bin fuskarta sai taji kamar ta samu kanta a gabanshi, cikin kuka tace "karka damu Faruk, ba zan iya rabuwa da kai ba nima, ina sonka kuma babu abinda zai rabu insha Allah, yanzu ka rufe idonka."
Cikin murmushi kamar yana gabanta ya rufe ido, a hankali ta furta "je t'aime (i love you), prend bien soin de toi (ka kula da kanka)."
Kasa bud'a ido yayi saboda farin ciki, jin ana gaf da tayar da sallah yasa yace "baby, zan shiga masallaci."
"Kayi mana addu'a baby."
"Wace iri?"
"Um, ka mana addu'a Allah ya barmu tare, Allah kuma ya tsone idon mak'iyanmu, bizou." tana fad'a ta kashe kiran.
Masallaci ya shiga sukayi sallah magrib bai fita ba har akayi isha'i sannan suka fita tare da Ishaq yaje gidansu, number da Khairat ta kira ya fara kira amma bata shiga, Ishaq ne ke kallonshi ganin ya aje wayar gefe cikin fushi yasa Ishaq gyara zama yace "kasan wani ma? Hajia Khairat fa ta bani sak'o wajenka."
Da sauri ya kalleshi yace "me tace dan Allah?"
"Um, tace nace kayi hak'uri, tasan za kaji ba dad'i rashin tafiyarku tare, amma dai ita maslaha ce tayi a ganinta, kuma bata son shiga tsakaninka da danginka, sannan wai..." sai yayi shiru yana kallonshi.
"Sannan me?" ya tambaya cike da zumud'in son jin abinda zai fad'a.
Hararanshi yayi kafin yace "waina kula mata da kai, kamar wani qaramin yaro, ko kuma ni d'in yaronka ne."
Fashewa yayi da dariya ya d'auki pillow ya rumgume amma ya kasa magana, duka Ishaq yakai masa yana fad'in "mijin Hajia, kaifa yanzu nan bala'in sonta kake ko?"
"Kana mamakin hakan ne? ai yanzu bana jin zan iya numfashi idan babu wannan Hajiar taku, bansan ya akayi sonta yamin mugun kamu ba haka, amma dai ina qaunarta fiye da yanda nake qaunar kaina."
"Amma dai sai nake ganin zaifi kyau ka dinga sassautawa tare da b'oyewa, tunda kaga ba ita kad'ai gareka ba akwai wata, zaka iya shiga hakk'in d'ayar, hakan kuma kasan zai iya halakar da kai."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "hakane abokina, yanzu haka ji nake inama ace ina da hali, da zanbi Khairat ne har inda take, haka kuma yanzu haka ji nake bana son ganin Zubeida da mahaifiyarta, saboda da bata fad'awa tanti ba da bata zo gidan ba, amma dai duk da abinda nake ji a kanta zanyi qoqari naga na b'oye hakan, ba kuma zan tab'a tauyeta ba insha Allah, dan bana so na tashi a ranar gobe da shanyayyen barin jiki, a matsayin wanda bai adalci a tsakanin matanshi."
Sun jima suna hira kafin ya tashi ya shiga gidan kai tsaye kuma d'akin Zuby ya shiga, zaune ya sameta akan kujera ta zuba tagumi idonta jawur alamar tasha kuka, cikin sanyin jiki ya zauna kusa da ita yana kallonta yace "Zubeida."
Kallonshi tayi tace "na'am."
"Meya faru, kuka kike?"
Kai kawai ta girgiza masa, kasantuwar baya son doguwar magana yasa ya janyota jikinshi ya kwantar da ita yana daddab'ata, duk da tana jikinshi amma hankalinshi baya wajen gaba d'aya, tunanin 'yar qaramar rayuwar da sukayi da Khairat da irin farin cikin daya samu a tare da ita, jin yanda yake ta shafarta yasa ta d'aga daga jikinshi tana fad'in "bara na zuba maka abinci."
Bata jira maganarsa ba ta fara zubawa, shima kuma baisan ta fad'a ba, harta gama zubawa ta juyo ta kalleshi da nufin magana amma saita tsaya tana kallonshi, da mamaki ta fara kallonshi ganin yayi kamar gunki murmushi kad'ai ke bayyana a fuskarshi, ga dukkan alama yayi nisa a tunani, a hankali ta d'an kai hannunta a hannunshi ta bubbuga, da sauri ya zabura yana kallonta, "kaci abinci." kawai ta fad'a.
"A'a, bana....." ganin ba zai kyauta ba yasa kuma yace "to."
Gyara zamanshi yayi ya fara cin abincin badan yana jin dad'in abincin ba, da qyar ya d'an tuttura badan yaci mai yawa ba ya barshi, tashi yayi ya shiga wanka koda ya dawo ta gyara wajen, kayan bacci yasa ya fita wajen Baba sukayi saida safe hakama Mama da sauran iyayensu, saida ya tsaya kofar d'akin Khairat yana ji kamar ya shiga amma ganin ba zai kyauta ba yasa ya koma d'akin, koda yaje ya samu harta kwanta ta duk'unk'une kamar mai bacci.
Jiki a sanyaye ya kwanta gefenta zuciyarshi na hasko mishi daren farkonshi da Khairat, a hankali ya gyara kwanciyarshi yana sakin murmushi, rumgume hannayenshi yayi ya rufe ido kamar mai bacci, amma abinda yake tunani yana gaf da zautar da tunaninshi, jin shiru bai tab'ata ba yasa ya bud'a ido ta juyo ta kalleshi, da matuk'ar mamaki ta kalleshi ganin ya juya mata baya shima kamar yanda tayi, duk da hakan bai mata dad'i ba amma ba zata iya masa magana ba ita, dan haka ta shereshi itama kawai tayi baccinta, shi kuma saida ya raba dare biyu kafin bacci ya d'aukeshi wanda rabinsa duk mafarkin Khairat ne a ciki.
**************
Tana zaune akan gado ta shiga Internet tana duba yanda ake girki Mamie ta shigo, zaune tayi gefenta tana kallonta tace "hutawa ake?"
"Eh Mamie, ina duba yanda ake girki ne."
"Toh , to ina ganin ko zamu fara ne tun daga nan, tunda naga kina son koyon girkin da wuri."
Da sauri ta aje wayarta ta rik'e hannun Mamie tace "eh Mamie, dan Allah mu fara."
Dariya tayi ta shafi kumatunta tace "karki damu zamu fara, tunda zamane kawai zamuyi kafin isowar sauran bakin, amma kafin nan ki fad'a min, me yasa baku taho tare da Umar Faruk ba? bayan nasan an shirya tafiyar dashi."
"Mamie, an samu matsala ne, wannan masifaffar matar ce ta hana mu taho tare."
"Wace mata ce wannan?"
Cikin yamutsa fuska tace "wannan mahaifiyar matar tashi mana."
"To shikenan, bara na samo abin rubutu saimu fara kafin mu koma gida muyi a aikace."
Fita Mamie tayi bayan wani lokaci ta dawo da littafin rubutu da alk'alami, zaune Mamie tayi tace "to ga wannan, zan dinga fad'a miki sai kina rubutawa."
Kamar wasan yara kuwa sai suka fara, sun jima Mamie na fad'a mata tare da fayyace mata komai kwatta kwatta kafin suka tashi yin sallah.
*A gurguje fan's*
A kwana *uku*
_Need your prayers_
09/08/2019 Γ 21:40 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
4⃣1⃣
A kwana ukun nan Khairat da Mamie ba suda abinda suke daya wuce koya mata girki, indai har suna zaune basu tafi abinda ya kawosu ba to aikinsu kenan, idan kuma ba tare da Mamie ba to Khairat na d'aki tana kallon yanda ake wasu kalolin girkin a Internet, gaba d'aya basu cika waya da Umar Faruk ba ,domin kuwa sam baya son shiga hakk'in Zuby, idan yana wajen aiki kad'ai suke samun yin waya a nutse sai kuma tsakanin sallah magrib da isha'i, da anyi sallah isha'i kuma gida yake shiga kuma baya fita a wannan lokacin, hakan yaba Khairat damar koyan abubuwa da dama a wajen Mamie a wannan 'yan kwanakin, kamar yanda a wannan kwanakin ne ta qara tabbatar da irin son da take ma Umar Faruk, tunaninshi na hanata sakewa sosai kamar yanda maganganunshi ke hanata walawa, hakan yasa ta matsu ta koma dan tana kewarshi sosai kuma tana so ta faranta masa fiye da baya.
A ranar da duka bak'i suka hallara anyi abinda ya tarasu bayan gabatar da kai da kowa yayi, sai lokacin Khairat taji haushin rashin tafiyarsu tare da Umar Faruk a lokacin data gabatar da kanta a matsayin mai aure, amma mijinta bai samu halartar taron ba, sab'anin kowa daya gabatar da iyalenshi gaba d'aya, haka ma Muzaffar ya gabatar da kanshi a matsayin shi kad'ai (single) π, a haka dai aka gabatar da taron cikin farin ciki tare da qarawa juna ilimi, inda shuwagabannin suka keb'e domin tattaunawa, yaran mata ma haka maza ma haka, su Khairat ma sun tattauna ta yanda zasu bawa iyayensu gudummuwa domin ci gaban siyasarsu, anan aka watse tare da tunanin safiya ta waye kowa ya hau jirginshi su koma gida.
****************
Sam rayuwar babu dad'i tunda Khairat ta tafi, duk ya zama wani silent dashi kamar ba mai kazar kazar d'in nan ba, yana matuk'ar buk'atar wasu abubuwa amma ya kasa samu a wajen Zuby, yana buk'atar jin sumba daga wajen Khairat da wasanni da kuma yawon surutunta da wayan tab'a jikinshi, a yanzu hakan ne kawai ke d'awainiya dashi, dan lokuta da dama sai yaji kamar tana masa magana ko kuma ta sumbaceshi, turarenta kuma yanzu haka su yake fesawa a jikinshi, kamar yanda kullum saiya shiga d'akin da sunan zai d'auko wani abu, haka zai kwanta akan gadon ya d'auki kayanta yana shak'ar k'amshinsu hakan ne kad'ai ke masa dad'i.
Yayi iya qoqarinshi wajen ganin ya manta da hakan ya kuma mayar da hankalinshi akan Zuby, amma abin yaci tura kuma Zuby ta bada gudumuwa wajen hakan, wani lokacin haka zai daure ya fara sumabatarta saita dinga janyewa tana nuna bata so, baisan me yasa take haka ba amma dai shima ya gaji, dan gaba d'aya tunaninshi dama na wani wajen, duk da baya tauyeta ta ko wane b'angare, amma fa tunani da murmushi ne sukafi yawa a cikin al'amuranshi yanzun, dan ko abinci bai cika ci ya k'oshi ba."
A yanzun Zuby ta fahimci hankalinshi na kan Khairat, hakan kuma ba qaramin b'ata mata yayi ba, ta fad'awa Mama amma tace ta rabu dashi karta yarda ta nuna masa tana damuwa da halin da yake ciki, da kanshi zai dawo ya nemeta tunda itace a gabanshi yanzun, wannan shawara da Mama ta bata bata anfaneta da komai ba sai k'unci, shareshin da tayi yasa shima zuciya ta d'ebeshi ya shareta, idan ya shigo kwanciyarshi kawai yake yayi karatu daga nan bacci ya daukeshi, sam ya daina nemanta tsakaninshi da ita kawai gaisuwa, sai maganar ci abinci ko sannu da zuwa, duk da hakan na damunta amma bata nuna masa, kuma gashi an horeta akan karta kulashi ita shine zai kulata, shi kuma yana ganin ai shine namiji kuma yayi iya qoqarinsa amma bata bashi had'in kai, hasali ma nuna ya gundureta take shi kuma baya jin dad'in hakan.
Ana cikin hakane kuma ta koma Γ©cole, shike ajeta kafin ya wuce wajen aiki, kasancewar ranar juma'a ce hakan yasa ya biyo ya daukota, kuma tun safe ta fajimci yana cikin farin ciki, kuma tasan yana farin ciki ne saboda yau kwana uku, a lissafinta yau Khairat zata dawo, to amma ba komai tazo duk da haka ai kwananta bai qare ba, a fa tunaninta.
Har yamma Umar Faruk na gwada kiran wayar Khairat amma bata shiga, hankalinshi ne ya fara tashi amma daya tuna dama ita ke kiransa bashi ba saiya kwantar da hankalinsa.
***************
Tashin dare jirginsu zaiyi, tare take da Mammie da Mamie da Papa zasu shiga acessaire (lift), mutane suka samu sun shiga, ganin sai sun jira yasa Khairat kama hannu Mammie cike da karsashi tace "kawai muje a matakalar haba, kinga saimu motsa jiki."
"Ke ke, rabu dani dan Allah, ba zan iya ba, jiri nake gani idan na hau." haka Mammie ke fad'a tana bin bayan Khairat data ja hannunta.
Haka suka fara takawa a hankali, ganin yanda Mammie ke rik'e da wajen take takawa a hankali yasa Khairat sakin hannunta ta fara takawa da sauri tana sauka tana fad'in "saimun shekara bamu kai qasa ba in muka bi ta taki."
Tana kusa da sauka taji qarar Mammie, da sauri ta juyo ganin Mammieta fad'i qasa yasa ta jefar da jakar hannunta ta ruga a guje ta qarasa, "Mammie, lafiya, meya faru ne Papa?"
Suna cikin jajen abinda ya faru saiga ambulance har ankira musu saboda anan ba wasa da lafiya, babban asibiti mai kyau aka kaisu, bayan duba Mammie aka basu izinin zasu iya tafiya, amma tana buk'atar hutu sannan ba'a so ta taka qafarta, kuma gashi bayanta ma ya bugu shima an d'orata akan magani, wayar Umar faruk ta fara kira danta fad'a masa halin da ake ciki, bugu d'aya biyu ana uku aka d'auka.
"Hello baby." cewar Khairat cikin taushin murya.
A gadarance Zuby tace "baby dai, waye babyn to, ke yanzu wannan ya miki kama da qaramin yaro? to yana hutawa kuma yace baya buk'atar takurawa bare a tasheshi daga bacci, dan haka ya bani ikon na d'aga wayar duk wani qare da jaki daya bugu masa."
Tana fad'a ta kashe wayar ta aje tana dariyar mugunta, da sallama ya shigo d'akin yayi wanka tare da d'auro alwala, bai kula da komai ya fara shirinshi tana zaune tana kallonshi, har saida ya gama shirinsa cikin wani farin yadi shara shara mai kyau wanda ya amshi jikinshi, machette ya d'auka tare da hula da agogo ya nufi inda Zuby take ya bata, karb'a tayi tana kallonshi shima ita yake kallo.
"Me zan maka dasu?" ta fad'a cikin rashin fahimta.
"Ke yanzu har saina fad'a miki me za kiyi? saka min za kiyi to, tunda naga ke baki tab'a tunanin tayani shiri ba bare nasa ran wata rana zaki min shirin da kanki ma."
Aje kayan tayi a saman gado tace "oho, kana fad'a min yanda waccen karuwar take maka ne? to ba zan iya ba, saika jira idan tazo saita maka har wanka ma idan kana so."
Wata irin tafarfasa yaji zuciyarshi nayi, a qufule yace "Zubeida na fad'a miki karna sake jin kin kirata da karuwa ko, kuma idan ma karuwar ce ai tawace, dan haka karna sake ji, idan ba zaki iya abinda na saki ba ki bari amma ba sai kin fad'a min magana ba."
Tsaki yayi ya d'auki kayanshi ya fara mak'alawa ita kuma ta d'ora da "ba zan daina kiranta karuwa ba tunda ai karuwar ce, dama kasan ina da haushinka wallahi shiru kawai na maka, bansan dame waccen karuwar ta fini ba da har kafi sonta a kaina ba."
Rintse ido yayi yace "karki sake fad'a mata karuwa."
"Saina fad'a d'in, me zaka min?"
Wata zuciyar ce ta d'ebeshi ya kifeta da wani marin da saida ta fad'a kan gado, duk da ta fashe da qara amma sam bata ji ba saboda jinta ya d'auke, da hannu ya nunata yace "wannan ba d'abi'arki bace, ki sake hali inhar kina so mu zauna lafiya dake, ke kinfi kowa sani na bana d'aukar raini, amma na lura dake tun ranar da kika ganni ba kaya a gabanki, kika rainani ko kuma nace aka saki kika rainani, to wallahi ba zan d'auka ba, ke kinsan waye Umar Faruk."
Ko sallaya bai d'auka ba ya fita ya bar gidan, kuka ta dinga rerawa har Ruk'ayya dai taji abin yayi yawa ta shigo ta sameta, daga tsaye ta dafa kafad'arta tace "Zuby, yaya ne ko?"
Shiru tayi dan haka tace "dan Allah kiyi hak'uri ki daina kuka, idan Mama taji ba za taji dad'i ba kema kin sani, kuma ya kamata ki dinga bin yah Umar a hankali, tunda ke kinsan halinshi da zuciya da hushi ga kuma saurin hannu, dan Allah ki daina kukan nan kiyi shiru ki rabu dashi."
Ko motsawa ba tayi ba bare ta amsa mata, dan haka ta fita daga d'akin tana mamakin Zuby, dan bata santa da haka ba kuma duk da bata shiga harkarsu, amma dai ta d'an fahimci akwai matsala a tare da ita, dan ko zaune suke tsakar gida yah Umar ya shigo, sai dai ya wuce d'aki shi kad'ai ita kuma sai dai tace sannu da zuwa daga nan inda take zaune, ba zata tashi ba inba wani babba yace ta tashi ba, haka ko d'akin ta shiga idan suna tare, sai dai ta sameta ita akan gado shi akan kujera, koshi a kujera ita akan gado sam ba zaka gansu kusa da juna ba, sab'anin Khairat da zata samesu daf da juna wani lokaci ma ko qafafunshi akan jikin Khairat d'in ko ita nata qafafun, da wannan tunanin dai ta shiga harkar gabanta.
***************
Yana fita ya fad'a mota dan yanzu ya barwa Aliyu motonshi, kasa tayar da motar yayi saboda zafin da zuciyarshi take, ji yake kamar ya d'auki mataki marar dad'i akan Zuby, danshi baya son matsala ko kad'an, ganin yake akan me Zuby da quruciyarta zata lalata kanta ta zama kamar wata tsohuwa, yana nan inda yake wayarshi ta sake ruri, yana dubawa yaga farin cikinshi ce, itama kuma ta maido kiran ne dan bata yarda da abinda Zuby ta fad'a ba, yana ganin lambar ya d'auka jiki sanyaye ya d'ora a kunne.
Shiru tayi saboda tana so ta tabbatar dawa ya d'auki wayar yanzu, jin shiru yasa yace "Hello."
Jin amon muryarshi ba karsashi ba kamar yanda ya saba ba yasa tace "baby, meya faru, waya tab'a min kai ne?"
D'auke wayar yayi daga kunne ya kalla sannan ya sake mayar da ita yana fad'in "me kika gani?"
"Baka cikin farin ciki, ni kuma ba haka nake so ba, fad'a min waya tab'a min kayana, yanzu shima ranshi ya b'ace."
Wata tambaya ce zuciyarshi ta wurgo mishi _"anya kuwa Zuby itama tana sonka?"_
Basarwa yayi yace "tabbas, bana cikin farin ciki, amma ki barshi kawai."
"Haba dai, bana da hankali ne da zan barka a wannan halin, kaga ina zuwa, yanzu kayi connectΓ© kaga abin mamaki."
"A'a Khairat, ba yanzu ba, masallaci zanje yanzu."
Cikin d'aga murya da raha tace "a'a ban yarda ba, kawai kayi abinda nace, ba zan tab'a barinka kaje masallaci cikin b'acin rai ba."
"To naji." ya fad'a ba annashuwa a tare dashi."
Yana d'orawa Khairat ta kirashi appel vidΓ©o, d'auka yayi amma a take ya lumshe idonshi, ganin haka yasa Khairat bushewa da dariya tace "bud'e ido malam Umar Faruk."
Bud'e ido yayi ya sauke akan qirjinta daya fito yayi fam, saboda wata qaramar bras ce tasa wacce ta matse qirjinta ya fito sama, sai kuma qaramin wando iya cinyarta shima, ga gashinta data baza a bayanta ba zaka tab'a rabata da larabawa ba ko india, d'an yatsanta tasa tana yawo dashi akan fuskarta harta saukar dashi akan bakinta sannan tasa yatsu biyar ta sumbata tare da kashe mishi ido ta kuma watsa mishi sumbatar.
Wani irin narkewa yayi a kujerar motar yana d'an cije lips yana marairaicewa kamar zai fashe da kuka, ganin ta fara kamashi yasa ta tashi tsaye ta aje wayar yanda suke kallon juna da kyau ta fara taka rawa irinta india cikin qwarewa da iyawa tana rera wak'ar *humsafar*.
_Mere tu sare savere._
_Baho me tere tehre._
_Mere tu sare shave._
_Mere sat nahi hai_
Da irin haka ta dinga karairaya jikinta tana rawa (in baku manta ba gogagiyar 'yar rawa ce ko a india), saida ta gama ta koma ta kwanta Umar Faruk kuma wata azababbiyar sha'awarta ce ta taso mishi, da qyar ya fizgi muryarshi yace "baby....yaushe...zaki dawo..gareni?"
Kafin ta bashi amsa wayarshi ta d'auke babu caji, dole ya hak'ura ya lik'a wayar a cajin dake motar a haka ya tayar da mota ya matsa k'ofar gidansu Ishaq ya fito suka wuce , duk da ya shiga farin ciki, amma kuma ta barshi da ciwo.
Haka yaje masallaci ya dawo ba qwarin jiki, saida Ishaq ya shiga gida ya fito suka sake wucewa wajen aiki tare, babu abinda yayi sai ganin Khairat a wannan yanayin, shi dai kawai ya sani koma karuwanci ne Khairat ke masa, to tabbas yana son wannan karuwancin, a haka suka tashi yana tunanin idan ya koma zai sameta tazo, amma kash yaje ba Khairat, hakan yasa tunda yayi sallah magrib ya fara kiran wayarta amma shiru.
Khairat kam na d'akin Mammie suna hira har saida tayi bacci, sannan kowa ya koma d'akinshi, tana zuwa kuma bacci itama ya d'auketa....
**************
Saida safe yana wajen aiki ta kirashi take fad'a masa abinda ya faru, cikin rashin jin dad'i yace "ayya, dan Allah ki gaishe min da amaryar, kice ina mata sannu."
"Zan fad'a mata insha Allah."
"Yanzu kenan yaushe zaki dawo?"
"Ai tare zamu taho idan taji sauk'i."
"To, ya zanyi? sai hak'uri, Allah dai ya bata lafiya."
"Ameen."
*************
Mamie kuma naci gaba da koya mata girki da kalan jus da wasu abubuwan tab'awa, a haka suka qara kwana biyu kuma a ranar suka sake shirin tafiya, Khairat ce ta fita tace zatayi siyayya kafin su wuce...
_Me kuka ce fan's?_
πππ
14/08/2019 Γ 15:32 - Meerahgee❤: ππππππππππ
*JIHADI*
_Umar faruk_
ππππππππππ
_NA_
_SAMIRA HAROUNA_
_DEDICATED TO_
*MA FAMILLE*
πΈπ¦ *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_π€π€
_Bismmilahir-rahman-rahim_
4⃣2⃣
Tunda ya shigo haka ya gama duk abinda ya saba amma babu wanda ya kula wani tsakaninshi da Zuby, ganin babu ko plate akan tebur yasa shima ya shareta bai mata maganar abinci ba, akan kujerar ya kwanta yana latsa wayarshi, a hankali yake duba photunan da suka d'auka da Khairat musamman wanda take sanye da hularsa, haka ake kwance abinshi har gari ya waye.
Washe gari ma tare suke shiri da ita amma babu mai kallon wani, har saida suka gama ta d'auki jakarta zata fita a daqile yace " haka zaki fita baki karya ba?"
Saida ta harareshi tace "kana da matsala da cin abinci nane? "
"A'a, kije."
Yana fad'a yayi wuf ya fita daga d'akin ya barta tana rufewa, kosu Mama bata kalla ba ta wuce, su kuma da kallo suka bita yayin da sukansu suke tunanin, yaushe Zuby ta zama haka marar kunya, suda suke zaton wuta a maqera sai kuma su ganta a masaqa, k'ofar gidan ta sameshi ya paka motar da alama ita yake jira, d'auke kai tayi ta kama hanya ta nufi bakin titi, kallon kan bala'i ya bita dashiπ da tsananin mamaki, yana kallo harta kai bakin titi tana jiran taxi, kai ya girgiza ya taka motar da k'arfi, yana kaiwa kusanta ya kawar da kanshi kamar baisan da wata halitta ba a wurin ya wuce, ganin ya wuce yasa ta bishi da kallo baki bud'e, dan tunaninta zai biyota ne kuma ya bata hak'uri, a ranta tace "anya Mama ta bani shawara mai kyau, karfa na tsaya jan aji da hauka Umar Faruk ya sub'uce min."
Da qyar ta samu taxi hakan yasa taje a makare, ta kuma yi niyyar idan aka tashi kai tsaye gida zata je ta fad'awa Mama, dan ba zata iya da wannan shawarar ba, gashi duk da ta saka mishi magani a abincin amma bata ga wani canji ba, kuma itama tayi wanka da wanda aka bata amma shiru, na wajen Khairat ne kawai ya rage tayi aiki dashi, kuma duk kusantar da yake mata bai nuna yana wani jin dad'in da zai iya kasheshi, a tak'aice dai bata ga wani anfanin abubuwan da take yi ba.
************
*13:20* ta shiga gida, zaune ta samu Mama akan tabarma tana cin wake da shinkafa, jefar da jakarta tayi har tana neman buge Mama sannan ta zauna tana cire hijab da d'an kwali, Mama kallonta take harta d'auki ruwa tasha kafin ta aje tace "Mama, akwai matsala fa?"
Cikin harara Mama tace "to ke kuma dan ubanki, baki gajiya da matsala ne, me kuma ya faru yanzun?"
Cikin turo baki tace "Mama, sam shawarar da kika bani ba tayi ba, haka ma wannan magungunan naki babu abinda suka qara mana, yanzu haka maganar da nake miki yah Umar jiya marina yayi, kuma har yanzu bama magana ko kulani baiyi ba."
"Mtsssss." shine dogon tsakin da Mama tayi.
"To shine me, dama wannan ce matsalar, waike yaushe zakiyi hankali? kina mace amma sam ba kyada aji da kama kai, to yanzu me kike so na miki da kika zo nan so kike nace kije ki masa magana ko? to kiji yarinya, kamar yanda nace karki yarda ki kulashi, ki barshi zaiyi ya gaji ya dawo gareki , kuma karki qara cewa magungunan dana baki basuyi ba, sai dai in kece ki kayi ba daidai ba."
"Mama, wallahi duka nayi yanda ya dace, kawai dai ba sa'a ne wallahi, nifa gaba d'aya na rasa me yake damun yah Umar, wallahi ni harma na fara tsanarshi, kwata kwata bana son zaman gidanshi ma duk na fara takura."
"Ke! fita idona wallahi, ke kinsan me kike fad'a kuwa? to kima cire wannan tunanin a ranki, dan aurenki dashi mutu ka raba ne takalmin kaza, wallahi kina gidanshi har sai yayi kud'i kuma mun moreshi."
Da mamaki tace "kud'i kuma Mama, an fad'a miki zaiyi kud'i ne?"
"Ke kuma a tunaninki nan zai zauna baiyi kud'i ba?
"Aina jima da sanin zaiyi kud'i, shi yasa ma na shiga na fita na had'aku aure."
"Tohh, lallai, nidai yanzu kawai kisan ya za kiyi dani wallahi, danni rainin hankalinshi ya fara isata."
Cikin sassauta murya Mama tace "yana kusantarki kuma?"
Cikin jin kunya tace "Mama fa tun ranar da waccen karuwar ta tafi bai qara neman wani abu wajena ba."
"Bai nema ba kodai baki bashi ba?" ta fad'a cikin d'aga murya.
Sosai kai tayi tace "eh to, amma aike kika ce na dinga jan aji, kuma ni wallahi bana ma son yana kusantata, saboda...."
"Saboda me?"
Cikin yamutsa fuska tace "kefa Mama baki sanshi ba, wallahi jaraba ce dashi, baya da aiki sai lagudar mutum, gashi inya fara baya dainawa sai yaga ya maka liqis, gashi da tsinannan k'arfi, ga...."
*Wal'iyazu billah, towana miji asiri irin haka, abin yayi muni yan uwa, kuma ace uwar ta kasa kwab'arta , nidai ba zan iya fad'a ba gaskiya* π
"To kinsan me za ayi? yanzu zan sake komawa wajen malam na fad'a mishi komai, ina tabbatar miki wannan karan, ba sauk'i a al'amarin dan aiki zansa yayi sosai."
Shiru tayi hakan yasa Mama cewa "waini ke kad'ai ke zuwa ecole d'in?"
"A'a Mama, shi yake kaini, yaune na tafiyata saboda bama magana."
"Da motar tashi yake kaiki ko motar waccen karuwar?"
"Haba Mama, nice zan shiga motarta, da tashi muke zuwa."
"Hum, aini fa wannan tsinnaniyar motar ma saina sa an faffasata kafin ta dawo."
"Mama rufa min asiri, jiya fa saboda nace mata karuwa ne ya mareni , idan kin fasa mata mota kuma sai dai ya sakeni, dan wallahi na fahimci yafi sonta a kaina."
"Ai kuwa za kiga me zanyi, kuma wallahi saina raba tsakaninsu, ni na fad'a miki wannan maganar."
Kiran Umar Faruk ne ya shigo wayarta, dan yaje gida abazata bai sameta gidan ba, hakan yasan ya kira dan yaji ina taje....
_Kafin muji me za tace mishi, zamu waiwaya baya muji tarihin mahaifiyarsu Zuby ._
*WAIWAYE ADON TAFIYA*
*Fatima* shine sunan mahaifiyarsu wato kakarsu Umar Faruk, mahaifinsu kuma *Mamman*, sun haifi yara biyar hud'u mata *Khadija, Asma'u, Maryama, Zeinabu* sai kuma autansu namiji mai sunan *muhammad Sani*, yaran sun samu tarbiya da kuma ilimi na boko da addini, kasancewar mahaifinsu yasan anfanin ilimi, kuma cikin ikon Allah sun sameshi yanda ya kamata, sai dai matan basa wani zuzzurfan karatu ake aurar dasu.
Suka yaran suna aiki da tarbiyar da iyayensu suka basu amma banda Asma'u, tun tana yarinya iyayensu suka fahimci bata da kirki kamar sauran yaransu, sam bata da ragowa ga yan uwanta gata da masifar fad'an tsiya, ga kuma son kud'i da tijara akansu, saboda son kudinta yasa ta kasa fitar da mijin aure har saida ta samu zabinta , a lokacin kuma har qanwarta Zeinabu ta isa aure, dan haka aka had'asu tare aka aurar dasu.
*Hamza* shine wanda wannan hau ta fad'a ma, a waccen zamanin yana d'aya daga cikin masu kud'in da ake ji dasu, amma aurenshi da Asma'u saiya zama silar tarwatsewar komai, ta samu ragama da akalarshi tana juyawa yanda ranta yake so, bata d'aga masa qafa ba wajen rabashi da yan uwanshi dama mahaifiyarshi d'aya da yake da ita a duniya, hatta fita sai taga dama take bari ya fita, hakan yayi sanadiyar raba alak'arshi da abokan harkokinshi mak'ota da abokan arzik'i, sannu sannu kuma sai arzik'inshi ya fara durk'ushewa sakamakon yawan bani bani da take masa kuma bata bari ya fita ya nema, a hankali sai abubuwa suka fara canza musu har takai ya fara siyar da k'adarorinshi daya mallaka.
A lokacin kuma ciwo yaci qarfin mahaifiyarshi, amma babu kud'in da zai iya siya mata koda magani bare ya kaita asibiti, da qyar Asma'u ta bashi izinin zuwa yaga mahaifiyarshi bayan dogon rarrashin daya mata, yana zuwa kuma ya makara dan sai gawarta ya samu, ya girgiza sosai da mutuwar mahaifiyarshi, amma rashin imani na Asma'u bata barshi ya qarasa jimamin rashin mahaifiyarshi ba ta fara azabtar dashi ta wata sabuwar hanyar, a lokacin ta fito da wani sabon salo ta hanyar d'ora mishi duk aikin gida, saboda kawai yanzu ba yada komai, kuma duk abin nan da ake akan idon 'ya'yansu mata guda uku da Allah ya basu, ko sau d'aya bata tab'a tunanin yayanta mata bane kuma zasu iya koyi da ita, haka take azabtar dashi yaran kuma na gani kuma dukansu basu damu ba, dan dama tana d'orasu ne akan turbarta.
Kasancewar suna nesa da gida yasa iyayenta da 'yan uwanta basu riga sun fahimci halin da take ciki ba, a ranar da suka samu labari mahaufiyarsu tayi tattaki izuwa gidan, anan kuma idanta ya gane mata tabbas, danta samu Hamza ya tak'ark'are yana sharar gida, ran Fateema ya b'aci sosai kuma taji kunyar abinda ta gani, amma abin takaici shine, koda ta fara mata magana akan abinda take saita mik'e ta fara zuba rashin mutunci da fad'a, cike da quna Fateema tace,
"Yanzu Asma'u ni kike fad'awa wannan maganar, ni kike kallo kike fad'a min wai na takura miki?
Cike da rashin kunya tace "eh mana, na fad'a miki, gidana fa kika zo, kuma naga mijina ne ba mijinki ba, to miye a ciki? nifa ba zan iya wannan banzar rayuwar ba irin taku, kana zaune gidan miji bakin ciki da takaicin namiji ya kasheka , ai muna gani tun muna qanana irin rayuwar da kike a gidan mahaifinmu, hawan jinin da kike fama dashi ma ai duk shine sila, shine kike so nima na zauna ya qaqaba min, wannan da kike gani namiji shima, kuma dana bashi dama babu abinda zai hana yamin tsiyarsu irinta maza."
Cikin sanyin murya tace "naji, tunda haka kika zab'arwa kanki, ga hanyar nan, kuma duniya ta isheki riga da zanin d'aurawa."
Qarasa mata tayi da "harda d'an kwali ma."
"Haka kika ce? shikenan kije , amma ki sani akwai ranar qin dillanci, akwai ranar da za kiyi nadama, bansan ko zamu riski lokacin ba, amma dai nasan tabbas zata zo, kuma ki sani daga yau ba zan qara shiga sabgarki ba."
"To saime, nace saime dan baki shiga sabgar tawa ba? hakan ma yafi min dad'i, yanzu ne kuma zan sake watayawa yanda nake so, dan haka tafi nono fari, danni ko baki kika min ba kamani zaiyi ba." duk tayi maganar ne tana murgud'a baki.
"Haka kike gani, ai kuwa da zan miki wallahi ba zaki kai ko ina ba, amma ina jin tsoron karki qara lalacewa."
"Kiyi mana, wallahi babu abinda zai sameni, ina yin duk abinda nake so kamar yanda nake samun duk abinda nake so, dan haka babu abinda bakinki zaimin ."
"Haka ki kace?"
"Eh, haka nace."
"Shikenan kije , kije kya gani."
"Wallahi sai dai naga alkairi."
Juyawa tayi ta bar gidan rai b'ace tare da tunanin yaushe Asma'u ta zama haka, da wannan tunanin takai gida kuma ta kwanta bacci ba tare data fad'awa mahaifinsu ba, dan tasan inta fad'a masa toshi zai tsine mata ne ba tare da b'ata lokaci ba.
Babu wanda yasan me zai faru a gaba, badan haka ba da Fateema ta janye mugun bakin data ma Asma'u tun kafin ta kwanta bacci, domin kuwa wannan baccin data kwanta bacci ne na qarshe, baccin da babu tashi sai lokacin da aka busa qaho na biyu.
Haka lokaci yaja sosai babu abinda ya sauya a game da al'amarin Hamza, har suka aurar da *Salamatu* wacce suke kira da Uwani, da kuma Zulfa'u ya rage Zabba'u, lokacin kuma aka samu cikin Zuby amma sam Asma'u bata bari Hamza ya sani ba, domin kuwa cikin ba nashi bane na abokinshi ne, kuma hakan ta faru ne lokacin da abokin yazo gidan domin sanin meke faruwa ya daina fita, daga ranar suka qulla wannan alaqar kuma tana jin dad'in haka saboda yana sakar mata kud'i masu yawa, sai dai ta manta da ciki d'an dumane dole wata rana zai fito kuma ta haifeshi.
A ranar da Hamza yaga cikin kuwa, ya sameta ne d'akinta kwance da kayan bacci, anan yaga cikin dake jikinta d'an wata shida zuwa bakwai wanda take b'oyewa kullum,
"Me zan gani haka Asma'u?" ya fad'a yana sake kallon cikin gidan nata.
Cikin baccin daya fara d'aukarta taji muryarshi, a zabure ta tashi zaune tana d'aukar hijabin da take ajewa saboda gudun irin haka, cike da dakiya tace "mefa kake gani, miye haka zaka shigo min d'aki a wannan daren?"
"Asma'u, ciki fa nake gani a jikinki, ko kuma kina so kice min wannan ba cikin mutum bane?
"Ciki kuma, a ina?"
Da hannu ya nunata amma ya kasa fad'ar komai saboda yanda zuciyarshi ke bugawa, ya jima yana nuna hannun amma baice qala ba, daga haka kuma ya fad'i qasa wanwar , fashewa tayi da qara hakan yasa Zabba'u fitowa daga d'akinsu, nan dai aka samu aka kaishi asibiti amma ina lokaci yayi Hamza, shima nan aka tabbatar musu da zuciyarshi ce ta buga, Asma'u bata ji mutuwarshi ba saboda lasisi ne ya bata ci gaba da harkarta, bayan wattani kuma ta haifi Zuby kuma samu kulawar mahaifinta wanda mutane sukewa kallon aminin mahaifinta, sai dai tunda akayi arba'in d'in Zuby shima Alhaji *Bala* ya fita sabgarta, da farko tayi yunkurin tona musu asiri, amma sai Bala ya nuna mata ya fita zama d'an iska, domin kuwa cewa yayi taje ta fad'a, shi namiji ne bai gudun abinda mutane zasu ce, bayan tunani da tayi saita fahimci ita zata jefa kanta rijiya, dan haka taja bakinta tayi shiru.
Sai dai rayuwar ta sauya musu sosai, dan abinda zasu ci wani lokacin wuya yake musu, wani lokacin ma saita d'an kula maza kafin ta samu abinda zata ciyar da Zuby da kanta, rufi asiri d'aya shine su Zulfa'u suna taimaka musu wani lokacin, a haka rayuwa ta tafi har girma ya risketa tare da yarta Zubeida.
Ranar wata *litinin* Zuby ta taso daga Γ©cole, a qasa take tafiya ga rana ga yunwa, Umar Faruk ne ya b'illo akan hanyar da take, nan dai suka gaisa kuma ya d'auketa ya rage mata hanya, suna zuwa gida kamar yanda ya zama saban Mama zama k'ofar gida a bakin bishiya, yauma nan take zaune daga ita sai kallabin dake kanta, saida ya sauka daga kan mashin d'in ya gaisheta sosai kafin ya tashi ya tafi, Zuby kuma tuni dama tayi cikin gida bata ko kulata ba, bin kowannensu tayi da kallo tana girgiza kai, har zuciyarta taji sun birgeta kuma sun dace da juna, hakan yasa tayi tunanin had'a aurensu, sai dai kuma Umar Faruk talaka ne haka ma mahaifinshi, amma ba zata aiwatar da komai ba har saita nemi shawarar malam sannan.
Ba tayi qasa a gwiwa ba wajen zuwa wajen malam tare da fad'a mishi abinda ya kaita, bud'ar bakin malam cewa yayi "tabbas, wannan yaron zaiyi arzik'i, kuma arzik'in zaizo ta sanadiyar matarshi ne ta farko."
"Ban gane matarshi ta farko ba, kana nufin ba yata kad'ai zai aura ba, kuma wacce zai aura farko itace silar arzik'inshi, to wacece ita.?"
Rarraba ido yayi, dan na farko ma yayi qarfin hali ne ya fad'a da d'an abinda shed'anu suka nuna mishi, duk da yasan ba lallai gaskiya bane, amma saboda ita d'in abokiyar harka ce ba zaiso mutuncinshi ya zube ba, dan haka yace "haba Ma'u, ai 'yar taki nake nufi."
A wulak'ance tace "ka tabbata?"
"K'warai ma kuwa, ai kisan yanda za ayi ki hadasu, dan arzik'inshi na tattare da ita, yarinyar akwai qashin arzik'i."
"Gado tayi gaba da baya." ta fad'a tana yamutsa fuska.
A lokacin da taje ma iyayen Umar Faruk da maganar basu ce komai ba sai fatan alkairi, haka ma Umar Faruk da aka fad'a mishi, bud'ar bakinshi cewa yayi "Allah ya sanya alkairi."
"Ameen, Allah ya maka albarka." cewar Mama
"Ameen."
Daga wannan rana ne sai Asma'u take turo Zuby gidan tazo har takanyi sati biyu wani lokacin, shakuwa ta shiga tsakaninsu duk da dai Umar Faruk baya jin komai a zuciyarshi a game da ita, amma a lokacin da girma ya qara zuwa masa ya sake mallakar hankalin kanshi, a lokacin yana da shekara *30* sai buk'atar aure ta kamashi, amma sam Zuby tak'i amincewa tace saita samu certificat d'inta na (BEPC) sannan suyi aure, dole ya hak'ura tunda baida wacce yake so kuma baya da ra'ayin yin mata biyu a cikin qananin lokaci da kuma qarancin shekarunshi.
*Wannan* ne dalilin da yasa tanti ta tsani Khairat ba tare da wani dalili ba, ta yarda d'ari bisa d'ari akan abinda malam ya fad'a ,musamman da tasan Khairat 'yar babban mutum ce, tasan ba makawa sai yayi kud'i ta silarta, hakan yasa ma tayi gaggawar shigo da Zuby gidan.
*WANNAN KENAN*
πππππ
*_CIGABAN LABARI_*
Tana d'auka yace " ina kika je?"
Cikin gunaguni da harare tace "ina gida wajen Mama."
"Da izinin wa kika je?"
"Toh , wajen mahaifiyar tawa ma da zanzo saina fad'a maka? to da izinina nazo."
Da qyar ya taushi zuciyarshi yace "naji, na miki uzuria karo na farko, amma ki sani kika sake maimaita irin haka, wallahi ranki idan yayi dubu zai b'ace, sannan, ki gaggauta dawowa gida nan da minti talatin ina jiranki."
Yana fad'a ya kashe wayar ita kuma ta kalli Mama tace "kiji rainin wayo."
Shiru Mama ta mata ganin haka yasa ta tashi ta kimtsa nata yanata sukayi sallama ta kama hanya, dan nisan dake tsakani ma zai iya d'aukarta minti talatin d'in, da qyar ta samu taxi ta hau, koda taje bata samu Umar a gidan ba, hakan kuma ya mata dad'i sosai.
*************
B'angaren Khairat kuma tana babban shagon siyayya , kud'i kawai take kashewa yayin da take tuna iya mutanen dake cikin qwaqwalwarta take siya musu kaya, ta jima sosai kafin ta fita ta d'auki hanyar komawa masaukinsu, tana zuwa su Mammie ita suke jira , dan haka basu b'ata lokaci ba wajen isa filin jirgi kuma suka tashi da izinin Allah suka sauka lafiya.
_Me kuma zai faru yanzu? my Hajja fa ta dawo._
*Kamar yanda na fad'a, babu abinda zai tsayar dani rubutu idan harna fara rubutawa,amma fa akwai yiwuwar na dakatar da rubuta _Jihadi_ na d'an wani lokaci, danna lura kamar kun fara gajiya da comment, comment bawai yana nufin a turo makaπ tsalle koπ€Έ♂talar qafafu ba, ko striker dake cinye data, tabbas muna jin dad'in addu'a, amma mutum yayi sharhi akai shine zai baka tabbacin an karanta abinda ka rubuta d'in, so idan kun gyara zanci gaba, idan ba haka baπbana da matsala, zan sawake ma kaina ta hanyar ajiyeshi gefe ko kuma na dinga turawa masu so na fita daga duk grp d'in da basa comment.*
_Ina muku barka da sallah, Allah ya nuna mana ta bad'i, Allah ya karb'i ibadunmu , Allah ya gafarta mana zunabanmu, Allah yasa muna cikin bayin da aka 'yanta._π *Ameen ya Hayyu ya Qayyum.*
0 comments:
Post a Comment