Da gudu tayi waje tana rabza kuka ganin halinda ɗan nata ke ciki tana ƙoƙarin ficewa daga parlon domin ta samu ta kira mai gadi ya taimaka mata,a nan sukayi karo da Papi wanda ke ƙoƙarin shiguwa.
Ganinta a rikice ne ga kukan da take ya sashi saurin sakin jakarsa tare da jawota jikinsa,kuka ta fashe dashi tare da faɗin.
"wacce uwace ni?ina ƙoƙarin kashe ɗana da kaina wlh.."kukan da yaci ƙarfinta ne yasa bata samu damar ƙarasa abinda tayi niya ba.
Bayanta ya shiga bubbugawa tare da jijjigata,shi kansa tun safe ba dai² yake jinsa ba fargaba tsoro bugun zuciya faɗuwan gaba shine abinda yake damun ransa dalilin hakan ya tattaro kayansa zuwa gida,cikin dauriya yace.
"lafiyanki ɗaya wannan kukan duk na mene?".
Cikin firgici ta shiga bashi labari ai bata ƙarasa ba yasa hannu ya tureta da gudu yay flat ɗin faisal,yana shiga ya ganshi yashe a ƙasa bai tsaya jiran komai ba ya sunƙuci ɗan nasa yay waje.
Hijab Ammi ta ɗauka tare da rufa masu baya cikin sauri ta shiga motar da wani irin speed Papi yaja motar daman tuni mai gadi ya buɗe get cikin sauri ya halba hancin motar kan titi.
Lokacin kaɗan suka isa Amino kano teaching hospital,suna zuwa ma'aikantan asibiti sukayo kansa a haka aka ɗurashi zuwa bed ɗin marasa lpa akai cikin emagency room dashi.
A nan ƙofar emagency ɗin suka shiga zirga-zirga sosai zallar tashin hankali ya bayyana kan fuskar Papi tym to tym yakan girgiza kansa tare da fesar da numfashi.
Sun ɗauki wajan 1hour kafin likitocin su fitu da sauri Papi yay wajan babban likitan tare da faɗin.
"Dr meke faruwa da lafiyan ɗana?"
Gomi Dr ta ya share kana ya kalli Papi yace.
"follow me" yana hakan ya juya zuwa cikin office ɗinsa,jiki babu ƙwari suka rufa masa baya,glass ɗin idanunsa ya zare kafin yaja numfashi yace.
"tunda na ganka nasan ciwon Faisal yayi tsauri kusan kullum yana zuwa amsar magani"cikin rashi n fahimta Papi yace.
"kullum fa Dr ka sani a fargaba pls meke faruwa?".
Tausayin Ahalinne ya kama Dr numfashi ya ƙara kafin ya maida glass ɗinsa yace.
"ciwon zuciya ya kama Faisal kuma ciwo mai tsanani irin na lokaci guda ɗinnan,yanzu mun ɗurashi bisa magana kamar su,H2Blockers,
Lisinopril
Perindopril
Quinapril
Trandolapril
Angiotensin,ya buƙaci kada na sanar dakai sabida yana saran samun lafiya nan kusa,amma abin mamaki kullum Faisal cikin ƙunci da damuwa haɗi da tunani nayi nayi ya faɗamin damuwarsa yaƙi,yanzu haka zuciyar sace ta buga bashi da wani sauran lokacin sai wanda ya ubangiji ya tsara masa but i'm sorry to say zai wahala ya tashi zuciyansa yaje matakin ƙarshe ta tashi daga aiki".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"shine kawai abinda Papi ya shiga faɗa gaba ɗaya jikinsa rawa yake kansa ya ɗura kan table ɗin dake kusa dashi idanunsa na fitar da wasu ƙwalla na tausayin kansa da kuma ɗan nasa.
Ammi kam tsoran da yay mata yawa ne yasa yawa ne yasa ta kasa cewa komai kukanma ya tsaya gaba ɗaya sai kanta data ɗaga sama tana tunani.
Miƙewa Papi yay kai tsaye special room ɗin da aka kwantar da Faisal ya nufa yanz ya gansa kwance flat gaba ɗaya jikinsa na'oruri ne sai ƙara suke hannunsa ɗaure da drip,zama yay gefen bed ɗin tare da riƙe hannunsa cikin muryar kuka Papi yace.
"Son kada kayimin haka dan Allah ka tashi ka faɗamin damuwarka wlh wlh na ɗauki alƙawarin cika maka ita da dukkan aƙarfina lafiyata aljihuna dan Allah ka tashi na tsani ƙwanciyar nan"ya faɗa lokacin da kuka ya ƙwace masa,ƙansa yaji an dafa hakan yasa Papi saurin ɗaguwa cikin farin cikin ganin Faisal na mutsa hannunsa,hannun ya kama ganin rubutu a tafin hannunsa ya sashi riƙe hannu abinda yaga an rubuta ya sashi saurin runtsa idanun ko shine ya nuna masa ba dai ba,a fili Papi ya ƙara duba rubutun.
"I want see her,my eyes want to see my Lili,i knew she's alive itane damuwata pls".
Cikin damuwa da kuma aro jarumta Papi yace.
"tabbas tunda zuciyanka yaƙi baka Lubna ta rasu babu shakka akwai wani ɓoyayyen sirri akan hakan,zanje insha Allah zanyi ƙoƙarin naga na haɗaka da muradin ranka"yana faɗin hakan ya fice daga cikin room ɗin.
Najma
Baƙaramin wahala tasha wajan Faisal ba domin ba tayi tsammanin hakan ba,ta ɗauka abin zai ƙayatar za taji daɗi fiye da yadda ake fasallata mata daɗinsa,ta ɗauka zai mantar da ita duniyar da take cikin ta hanyar dulmiyar da ita a cikin salon nasan ƙwarewar,ta ɗauka zai jiyar da ita daɗi da kuma farin cikin da'a taɓa yiwa wata ƴar mace ba,amma saiya shayar da ita gubarsa da kuma ɗacinsa haɗi da azabartar da ita ya dasa mata tsoran abun.
Da rarrafe ta shiga toilet ruwan zafi da haɗa tare da zare rigar jikinta cikin ruwan ta shiga azabar data jine yasa ta fawa ihu tare da ƙanƙame jikinta waje guda,sosai take kuka cike da muradin rama abinda yay mata danta ɗauki alƙwarin nemo maganin dake saka feelings in five minutes,wanka tayi tare dayin wankan tsarki tare da ɗaura towel a jikinta tana tafe tana kwala ƙafa,ta kusa zama kan bed ta hangi wani dairy ɗauka tayi tare buɗe shafin farko da manyan baƙi taga an rubuta MY BEBY BOO kafin a rubuta wasu zafafen kalaman soyayya a haka ta shiga duba sauran shafukan har tazu last page inda aka rubuta "WHEN ALL IS GONE" tashin hankali wanda ba'a saka masa rana jikin Najma ne ya shiga ɓari tare da karkarwa yayinda wata zufa ta shiga ƙeto mata dai² lokacin da tabbas baya nan da Faisal ya rubuta ya gama tabbatar mata Dad da Mamy haɗi da Fahad sun jima da rasuwa kuka ne ya ƙwace mata ta rerawa saida tayi mai isarta kafin ta duba bayanin ƙarshe.
_ko kowa zai yarda kin mutu babu ni domin zuciyata a kullum da tunaninki take bugawa,ina nan ina zaman jiranki daga nan har ƙarshen rayuwata,kece farin cikina muradin raina da sonki nake ƙwana nake tashi i luv u i luv the rest of my life i luv soo much i'm always be ur side my Bby boo mu'ahh💋_
Wani ƙyaƙƙyawan murmushine ya suɓucewa Najma cikin farin ciki tace "Mutuwarki ya zama abu na farko daya sanyaya miƙe daya daɗe yana damuna shekara da shekari kin ƙwace komai nawa ƙyau ilimi farin jini gata muradin raina hankali nutsuwa komai dai kin ƙwace why Lubna i lost everthing because of u pulish gril i hate u tsana mai yawa,koda baki mutu ba na ɗauki al'ƙawarin ra baki da ranki kamar yadda kika rabani da dukkan wani farin cikina zuwa now he is mine for rever and ever".
*** ***
Abuja.
Idan tace abun duniya bai isheta ba tayi ƙarya gaba ɗaya cikin firgici take kullum a tsorace take,ita kanta bata san meke damunta amma ƙasan ranta tana ji akwai wani baban kuskure data tafka kullum ciki tunani da zullumi take yayinda a koda yaushe ƙyaƙƙyawar fuskarsa keyi mata gizu a cikin dara-daran manyan idanunta waye shi?a ina yake wannan shine tambayar dake damunta wacce a kullum take son furtawa wa wani ko zata samu sauƙi a ranta amma babu dama,babu wanda zata gayawa taji daɗi,Yusrah da take matsayin ƙanwar wanda zata aura ko kuma Momma dake matsayin uwa a wajansa ko kuma shi ɗin kansa zata tambaya tace zuciyarta wani take muradi bashi ba? Lumshe idanunta tayi hakan ya bawa hawayen cikin idanunta damar sakkowa daga cikin idanunta zuwa kan fuskarta,lumshe ido ta ƙara cike da muradin son ƙara ganin fuskarta duk da har yau ba full face ɗinsa take gani ba amma ganin fuskar tasa ya fiye mata komai a yanzu domin sosai takesa zuciyarta nutsuwa da kuma dai² tuwar bugun zuciyarta,ɗan cije lips tayi ganin ba taga abinda take muradin gani ba hakan yasa ta fashe da wani irin kuka haɗi da cusa kanta cikin fillow ta shiga rera kukanta,sai yaushe ne zata daina jin abinda ta keji a cikin zuciyarta,yaushe ne zata daina kukan rashin Ahalinta?mai yasa ƙaddara take juya rayuwarta kamarta samu ƙwallo a cikin fili.
Bata ji a wannan karan zata iya rauninta domin damuwar sosai take son fallasa abinda yake cikin zuciyarta cikin sauri ta miƙe tare da sakin siririyar ajjiyar zuciya,Tunawa da yayarta ta ya zama wani garkuwa a gareta ya kuma zama wani farin cikin daya samu gurbin raƙe mata damuwar ranta.
Ƙatun hijab ɗinta ta ɗauka tare da kallon madubi ya mutsa fuska tayi ganin yadda fuskarta ta faɗa sai idanunta daya ƙara girma ga ƙyan fuskarta ya ƙara fituwa babu abinda ke birgeta a fuskarta sama da cute peach lips ɗinta daya ƙara ɗan tudu da kuma sharning sosai take samun kulawa wajan Momma da kuma gogan nata Sufyan.
Ficewa tayi daga ɗakin ta nufi parlo a nan ta tarar da Momma sai Sufyan da shiguwarsa kenan sosai yay kyau cikin shigar blue ɗin t.shirt sai long dark black jeans dake jikinsa yana zauna yana danna waya,ƙamshin turarenta ya kawowa hancinsa ziyara lumshe idanunsa yay tare da buɗesu ya mannasu akanta sosai tayi masa kyau yana jin ina babu Momma awajan da babu abinda zai hana ya shaƙi daddaɗan ƙamshin turarenta.
Jikin Momma taje ta lafe tana ji tamkar a jikin Mamynta take bakinta na rawa tace.
"Momma ina neman izinin zuwa kano wajan sister na tuna da ita ina buƙatar ganinta".
Kanta Momma ta shafa tare da faɗin "Lubna kin faɗa a ƙorarran lokaci gashi jibi jirginmu zai tashi suwa bikin ƴar uwar mijikin a can za'a haɗa ai naki keda Sufyan"
Turo baki LILI tayi tare da ƙara shigewa jikin Momma ta shiga sauke numfashi ita sam ta manta matsayin uwar miji take,cike da zallar shagwaɓa tace.
"pls Momma i want see her ita ɗaya nake da"murmushi Momma tayi tare da zare jikinta daga na Lili tace.
"babu damuwa kuyi magana da Sufyan gobe da safe saiya kaiki"gdy tayi mata.
Miƙewa yay ya dawo inda take zaune kallonta yay sosai kafin ya maida idanunsa kan lips ɗinta ganin ya fara fita on his mood domin sosai ƙamshin turarenta yaƙe ƙara masa wutar sha'awarsa harya matsu sati ya zagayo domin ta zama mallakinsa.
Miƙewa yay tare da kallonta yace "7 zamu bar gida so don't keep me waiting"yan faɗin hakan ya shige cikin flat ɗinsa jin wani hurt feelings ɗinta na tasu masa.
_The secret issues_
*💖JUYAYI💖*
*22-23*
*_Wattpad_*
https://my.w.tt/jN2GLY5RKcb or Nimcyluv
*_Telegram_*
https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ
_Just follow me,follow my pen,be with me,luv my story🥳rubutu yanzu muka fara karantu yanzu kuka fara fas masoya i solute you maƙiyama i solute you🤾🏻♀️_
بسم الله الرحمان الرحيم اللهم صل وسلم على سيدنا محمد رسول الله عليه و سلم.
......Lumshe lulu eyes ɗinta tayi tana jin wani irin ya nayi na ratsa sassan jikinta,peach lips ɗinta ta shiga taunewa tana me fitar da wani zazzafan numfashi,a hankali ƙyaƙyawawan sexy eyes ɗinsa suka shiga bayyana cikin idanunta ƙara curewa tayi waje guda tare da saki wani ƙawataccen murmushi mai cike da nuna “SO” da kuma “ƘAUNA” daga zuciya zuwa zuciyar da aka amince da ita,babu abinda yake faranta irin taga ƙyaƙƙyawar fuskarsa nayi mata gizo wanda har yau bata gama ganin his full face ba kuma tana ganin rabi sometimes afi ɓoye mata fitinannun idanunsa wanda tafi muradin,tunaninsa ya zama patner ɗinta bawai yanzu aka fara hakan ya samu a saline wajan 7year back da suka shuɗe.
Cike da tunaninsa da kuma kewar wani haɗaɗɗan bacci yay gaba da ita a nan kan sofa,sanyin asuba tana A.c sune suka data da ita daga dugun baccin data tafi,a sanyaye ta miƙe tare da shigewa bedroom ɗinsu tana shiga ta huce toilet ta haɗa ruwa mai zafi a hiter cikin sauri tayi wanka tare dayin brush ta ɗaura alwala,jallabiya ta mata ta zura a jikinta tare da saka hijab ta shimfiɗa prayer mata ta data sallah raka biyi (Raka'atul fijir)lazimi ta tsaya yi kafin ayi Assalatu ta miƙe tare da gabatar da sallah ta daɗe tana yin addu'a tare da neman zaɓin uban giji a kan auren,duk da haryau bata baƙin ciki da auren kamar yadda bata ɗauki Sufyan matsayin abokin rayuwa ba,amma ta ganin ƙimarsa cikin sanyi jiki ta ɗaga hannunta sama idanunta na fidda ƙwalla ta fara addu'a.
_Ya Allah kaine ka halicceni kuma kaine ka ɗuramin duk wata ƙaddara dake zuwarmin badan baka sona ba sai dan gwada ƙarfin Imani na,tabbas na amince wlh na yarda ƙaddara mai kyau da mara amma zuciyata bata ƙwari mai rauni banjin zata iya ɗaukan lukutar ƙaddarar,inajin zuciyata nayimin zafi da raɗaɗi ubangiji ka kawomin ɗauki Allah ka haskamin zuciyata domin fahimtar abinda ta keso,Ya Allahu ya Samadu Ya Malikil mulkuzul jalalu wal'ikram ka bayyanin sayin idaniyata kuma ka nunamin cikakkiyar fuskarsa ko Allah zan ganshi a gasken gaske kuma a zahiri,shiɗin garkuwa ne tabbas bangone na rayuwata Ya rabb kasa ya zama muradin rai da ruhi haɗi da gaggar jikina,Allah kayi iyayena sakayya tun a nan gidan duniya Allah ka kawo makamin da zai taremin ƙatun yaƙin dake gaba na Ameen ya rabbil alamin_
Lumshe idanu tayi tare da fitar da wasu siraran hawaye,sosai take jin matsanancin kewa haɗi wutar son ruhin cikin idanunta shiɗin farin cikin tane, murmushi tayi tare da faɗin "Allah sarki Faisal luƙutar ƙaddara mai zafi ta rabani dakai ubangiji yasa Sufyan ya zama mai hqr da sanyi hali irin naka,Allah ka raba Sufyan da zafin rai da miskilanci haɗi da kafiya irin na Boobyn"
Ganin lokacin naja yasa ta miƙe cikin ƙaramin lokacin ta gama shirinta cikin wata lafiyayyiyar duguwar riga ta atamfa ɗinkin Ashap gashin kanta ta gyara tare da tufkewa bata wani saka ɗan kwali ba ta ɗauki milk ɗin beby hijab ta saka wata ya dace da milk and cofie ɗin atamfar data saka,babu wani tarin make up a fuskarta sai bby peach lipstic data saka a lips ɗinta,sabuwar wayarta ta ɗauka tare da saka cikin hand bag ɗin hannunta kana ta kalli Yusrah dake bacci har yau bata tashi ba kasan cewar ba sallah take ba.
Zaune tasa mesu a parlo ya gama shirinsa cikin shaddarsa mai kyau yana danna wayarsa,wajan Momma ta ƙarasa tare da shigewa jikinta,murmushi Momma tayi tare da faɗin "Amaryar Sufyan an fitu maza ku tafi tym is not our side kusan gobe zamu ɗaga yana da kyau kuyi sauri"jinjina kai Lili tare da sakinta "oyya muje ko"ya faɗa tare da ficewa daga parlour'n.
Lokacin data isa harya shiga mota yay mata key ita kawai yake jira,side ɗin mai zaman banza ta zauna tare jingina jikinta ta jikin kujera,cije lips yay tare da ɗauke kansa taga kallonta, key ya ƙara yiwa motar tare da cillata kan titi ya farara sharara gudu daman sam bai iya dreving a cikin nutsuwa ba,few hours suka ƙarasu garin kano ta dabu tubbin giwa ko dame kazu anfika.
*** ***
Duk yadda Fahad yasu zillewa Afnerh abun yaci tura kullum cikin kuka take masa akan yay hqr ya nuna mata so amma taƙi yarda duk yadda ya keson fahimtar da ita illar hakan idanunta ta rufe yanzu da safe saida yay mata tsawa tare da alƙawarin zaizo kiranda Maman take masa sannan ta hqr ta barshi ya tafi hospital ɗin daya samu aiki domin duba marasa lpa.
Shiguwarsa kenan ya watsa ruwa tare dayin sallar la'ar ya kwanta saman duguwar sofa bacci fal idanunsa gashi sam baison tunani da zarar ya rufe idanunsa firgitattiyar surar jikinta take masa yawo cikin idanunsa duk yadda yasu yaga fuskar mamalkin tsarkakkiyar surar abin yaci tura,shi kaɗai yasan wahalar da zuciyarsa kesha idan surarta ta gama haukata tunanin wani lokacin a kan Fauwaz yake hucewa yayta surfa masa ƙatuwar masifa a haka harya gaji ya daina,kuma abin mamakin yana gama masifar zai dawo jikin Fauwas ɗin ya shigesa yayta sauke ajjiyar zuciya a haka bacci yake ɗaukesa wani lokacin.
Ƙara lumshe tsumammun idanunsa yay tare dajan sajen daya ƙawata zagayayyiyar fuskarsa mai cike da kwarjini da kuma haiba haɗi da hasken addinin daya gama rasa zuciyarsa da gaggar jikinsa,baiji shiguwarta ba sai hannunta da yaji ya sauka a kan fuskarsa,ko mutsi baiyi domin ta fara bashi haushi sam baisan raini kuma ya fahimci tana dash,turo baki Afnerh tayi tare da faɗin "Allah ka tashi bafa bacci kake ba"still shuru ya ƙarayi kafin ya ankara ta fasa masa wani ihu aka,cikin firgici ya miƙe tare da jawota ya ƙanƙameta danshi tsakani da Allah ya ɗauka wani abunne ya bata tsoro koya cijeta.
Lafewa tayi jikinsa ta shiga rera kuka ganin babu komai iskancinta ne yasa hannu ya janyeta jikinsa tare tsuke fuska ya miƙe tsaye,da sauri ta riƙe hannunsa tare da faɗin"ka Manta kiran Mama?"hannunsa ya zare tare dayi mata kallon sama da ƙasa da ƙyar ya wara laɓɓansa ta hanyar cewa.
"Ban hanaki koda wasa ki ƙara taɓa jikina ba?keko kunyata baƙya ji"tayaya zan soki ina son mace mai kunya da kamala da kuma riƙo da addinin Annabi muhammadu S.W.A,kije darajarki ta ƴar mace idan kina son naga ƙimarki kira kuma zanine ai dan haka ɓace daga ɗakin nan kafin na ƙwarfeki"
Yana faɗin hakan ya shige cikin toilet few minutes yay taken shower ya fitu ɗaure da towel a waist ɗinsa jikinsa na ɗigar da ruwa,sosai yay mamakin ganinta a tsaye taurin kai yay mata yawa,tsaki yaja tare da shigewa cikin bedroom ɗinsa,cikin saurin ya shirya tare da saka dark blue ɗin yadi mai ƙyan gaske da manyan zane sosai yadin ya amshi farar fatar jikinsa har singlet ɗin jikinsa ana iya gani,sumar kansa ya gyara tare da ɗaukan mayataccen turarensa na Ohud mood mai daɗin ƙamshi farin glass ɗinsa ya ɗauka tare da mannashi a fararen manyan idanunsa wayarsa kawai ya ɗauka ya fitu,a nan parlour ya tarar da Fauwaz yana shan coffe,zuba masa ido yay na wani lokaci kafin yaɗan ya mutsa fuska sosai maƙoshinsa keyi masa zafi sbd da maganar da Afnerh ta sashi ɗazu.
"oya Man tashi" sarai ya gane nufinsa amma ya share yace "inafa nikam na gaji"haɗe rai Fahad yay tare da matsawa bakin ƙofa yace"banzon tantirance"dry Fauwaz yay tare da ajjiye glass cup ɗin hannunsa ya miƙe suka jera suna tafe yana jansa da shira kasan cewar shiɗin ba gwanin shira bane sai yaja bakinsa yay shuru saidai kawai ya jinjina kai,a haka suka isa bakin get ɗin gidan cike da mutuntawa Getman ɗin ya buɗe masu ƙofa.
A compound na gidan suka tsaya Fauwaz ya ɗauki wayarsa ya kira Fannerh lokacin ana tsaka dayi mata gyaran jiki taji wayarta na ƙara Afnerh ce ta ɗauka tare dasa a speaker"gamu a compound hope dai Mama na nan dan yace bazai daɗe ba baijin daɗi" dry Afnerh tayi farin ciki fal zuciyarta danta tabbatar yau Mama zata amsar mata soyayyarshi kamar yadda tayi mata alƙwarin.
"ok come in side mana"shine abinda Fannerh tace tare da kashe wayar dan ita ɗagawar Fahad ɗin mugun fusata ta keyi fushinta ya kusa kufcewa a kansa,da gudu Afnerh ya miƙe taje ta faɗawa Mama ita kuma ta shige bedroom ɗinsu tare da sauya kayan jikinta aka fesa uban turare.
Da sallama suka shiga parlour Fauwaz na gaba Fahad na bayansa fuskar nan tasa a haɗe babu yabu babu fallasa,gaba ɗaya suka durƙusa tare da gaida Mama kafinsu miƙe tare da zama kan sofa,"Fahad kaji saƙona wa..."maganarce ta maƙale mata bakinta na rawa ta shiga kallon Fahad tare da nunasa da hannu tace"Fahad kaine..kaine yau a gidana kuma a gabana?"ɗago kai yay cikin sauri zabura yay ya miƙe da sauri ya ƙarasa gabanta tare da faɗawa jikinta a hankali yace "Mamana" sai kuma ya fashe da kuka tare da ƙanƙameta ya shiga rera kukansa a hankali wanda ita kaɗai take iya jin kukansa,lallai ran maza ya ɓaci ba ƙaramin abu zaisa kaga Fahad na zubar da hawaye ba,ita kanta sau ɗaya ta taɓa ganin kukansa lokacin dazai tafi U.S karatu sosai yay kuka kamar ransa zai fita sbd bai son zuwa,bayansa ta shiga bubbugawa tare da shafa sumar kansa "kuka kuma kamar ga ƙwarzon yarona ba ya isa haka nan"ƙara shigewa jikinta yay yana jin kamar ajikin Mamynsa yake,ya jima maƙale da ita kafin ya zame jikinsa ya zubawa Mama idanunsa tare da shagwaɓe mata idan da sabo ta saba da shagwaɓar Fahad.
"Mamana ina Uncle ɗina?"hararar wasa masa tare da faɗin"wanne irin uncle ɗinka kaifa nake shirin tambaya coz wajan watansa guda da rabi da tafiya wajan Daddyka why kuma nida nake nan zaka tambaye ni shi"kallon rashin fahimta yay mata tare da faɗin"u mean Uncle na wajan Daddyna how can that happen? Daddy is no more baya raye wajanwa zashi to"kallon maras hankali tayi masa tare da cewa"wannan wacce lukutar magana ce,waye baya rayen? Idanunsa ne suka sauya kala bakinsa na rawa yace "Mamana niɗin marayane mara gata i lost everthing luv,happiness,care,everthing Daddy,Mamy,Lili babu ko ɗaya cikinsu duk an kashesu"cikin firgici da fitar hayyaci ta ɗaga hannunta tare da sharara masa wasu firgitattun mari,tsabar girman mari saida yay maya lokacin hawayen idanunsa suka sami damar zubuwa daga cikin idanunsa,durƙushewa yay gaban Mama tare da kifa kasan in btw her laps ya shiga zauke numfashi mai zafin gaske jikinsa duka rawa yake.
*** ***
_Maiduguri road_
Horn suka danna da gudu mai gadi ya leƙo ganin sabuwar mota bata gidan ba ya sashi leƙowa tare da faɗin.
"yallaɓai wajanwa kake nema?" kallon Lili Sufyan yay kanta ta leƙo dashi waje tace"Anty Najma fa?"jim ya ɗanyi kafin yace"ayya ai ƙaramin mai gida Faisal ne babu lpa suna Emergency na Aminu kano".
Faɗuwar gabanta ce ta ƙaru lokaci gudu tsoro ya kamata tare da tunanin abinda ya sami farin cikin nata“Astagafirullah”shine abinda tayi saurin faɗa sanin cewa yanzu ya haramta gareta tunda yana auren ƴar uwarta,hawaya ne ya ɓalle mata ta shiga zubar dashi,Sufyan ne ya leƙa yace"mungode Baba"yana faɗin haka yaywa motar key tare dayin ribers ya jata da gudu tare da harbata kan titi.
Lokaci kaɗan suka isa asibitin har lokacin kuka take wanda ita kanta bata san na mene ba,wayarsa ya ɗauka tare da latsata yana sauraran kukanta,ganin bashi da niyar fituwa yasa tayi saurin buɗe ƙofar kafin ta buɗe ya danna mata pin,kallonsa tayi da alamun tambaya"ki tsaya ki gama kukan ko?"share hawayen tayi cikin rawar muryar tace"pls get in"jinjina kansa yay kafin ya buɗe ya fitu itama ta fita, a tare suka jera suka nufi cikin Emergency ɗin.
Ɓangaren Faisal kam tunda ya fita bai ƙara shiguwa ba sai cikin dare,yana shiga Faisal na buɗe idanunsa tare da zubasu a kan mahaifin nata,haka ya tabbatarwa da Papi tambayarsa yake game da Lili,zana yay tare da shafa kansa yace.
"Kayi ta wakkali Faisal cikar imanin mutum shine yadda da ƙaddara,ka yarda Lubna bata raye kuma kowa na haka ne kaci gaba dayi mata addu'a itane abinda take buƙata indai ka yarda kana sonta Rabbi yasfika Allah ya baka lpa ka rungomi matarka ka ɗauki hakan matsayin ƙaddararka"murmushi kawai Faisal yay domin yasan babu wanda zai yarda dashi a kan Lilinsa bata mutu ba,bai taɓa son Najma ba haka kuma bai taɓa tsanarta ba hasalima tausayinta ya keji ganin bata da kowa amma ta zaɓi baƙanta rayuwarsa da kuma duniyarsa,ta zabi ha ɗashi da mahaifiyarsa har tayi mummunan Lafazi a kansa meye laifinsa kodan ya nuna ƙauna da soyayya wa ƙanwata kodan zuciyarsa taƙi yarda ta amsheta matsayin mata,yayi hakanne sbd bai son ya tafi yabarta da marayun yara dan yana tabbacin bazai taɓa tashi ba.
Washe gari da safe Najma ta karasu asibitin tana tafe tana buɗa ƙafa dan sosai tasha wahala wajan Faisal ita yanzu haka maza tsoransu take,wajansa ta ƙarasu tare dajan kujera ta zauna lokacin ya samu bacci zuba masa ido tayi ganin ya ƙara mahaukacin kyau tare dayin wani fari fiye da jiya fuskarsa ta faɗaɗa ta yalwataccen murmushi,wata wutar sonsa ce ta ƙara tasu mata tana jin a duniya tafi kowa dacen mijin ɓangare guda kuma tana jin tsanar Lili fiyeda da,domin ita ta haddasa komai a kanta yaƙi amsarta a matsayin mata a kanta ta shiga damuwa.
Ta daɗe a zaune har bacci ya ɗauketa a jikinsa,wata ƙarar na'oura ce ta farkar da ita daga bacci cikin tashin hankali ta miƙe ganin gudan jini na fita ta hancinsa da bakinsa hannunsa dafe da ƙirjinsa,jikinsa gaba ɗaya rawa yake,da gudu ta tayi waje domin kiran Dr tana ƙoƙarin fita suna ƙoƙarin shiguwa Ammi ce sai Papi sai kuma wani ƙyaƙƙyawam namiji a bayan kafin wata mai hijab ta biyo bayansa,cikin farin ciki Papi yac"indai Lubna ce damuwark daga yanzun ta kau,domin ga muradin ranka a gabanka"
A hankali ya ware idanunsa tare da zare oxcygen dake bakinsa muryarsa na creating yace "Bby..boo"da gudu ta ƙarasu tare da faɗawa jikinsa ta saki wani mahaukacin kuka mai tsuma zuciya,kanta ya shiga shafawa tare da ɗura bakinsa saitin kunnan ta yace "i luv u more most"ya manna mata lafiyayyen kiss a wuyanta.
Kallamar shadar da taji yana faɗa ne yasa tayi saurin ɗago kanta wani ƙawataccen murmushi ya sakar mata fuskarsa ta cika da fara'a kafin yaja idanunsa ya rufe tare da sakin hannunta,gaba ɗaya na'ourorin da suke cikin room ɗin suka shiga ƙara a lokaci ɗaya,kaita shiga girgizawa tare ƙanƙameshi tan faɗin "no pls no Faisal why zakai bacci a lokacin da nake muradin ganinka da son jin muryarka dan Allah ka tashi"
Likitoci ne suka shigu da gudu tare dayin kansa suna zuwa suka shiga dubashi tare da girgiza kai wani Dr yace "saidai kuyi hqr Ubangijin daya samar dashi ya amshi abinsa kum... Ihun da Lili tayi shine ya dakatar dashi daga faɗin abinda yay niya kanta tayo ta shiga dukansa tare da faɗin"wlh ƙarya kake bai mutu kuma bazai taɓa mutuwa" cikin saurin Sufyan yazu ya ƙwace daga jikin likitan tare da mannata a jikinsa ya shiga jijjigata"dan Allah Sufyan kace bai mutu ubangiji kasa mafarki nake ba gsky ba"tana faɗin hakan tayi kan Faisal lokacin har an lullubesa da farin yadi,kafin ta ƙarasa taji saukar wani ƙarfe a tsakiyar kanta ƙara ta saki tare da juyawa da hannu ta shiga nuna Najma wacce take tsaye hannunta ɗauketa da wani ƙarfe cikin kuka Najma tace"wlh kema saikin bishi shegiya mayya aida lafiya muke zaune dashi Wlh nice aljalinki kamar yadda kika sani kuka nayi alƙawarin ganin bayanki"ƙara ɗaga ƙarfenta tayi zata ƙwaɗa mata a kai Sufyan yay saurin riƙewa tare da sauke mata wasu lafiyayyen mari,zafi da raɗaɗin ƙarfin dukan da taji ya sata yin baya lokacin jini ya gama wanke mata fuska nanta sulale ta faɗa jikin gawar Faisal babu numfashi..
_Wlh wlh wlh Allah kenan indai yau mutum sama da ashirin ba suyimin comments ba,kuma dukkan wanda yasan yana karantawa baiyi comments babu shakka zai koma na kuɗi duk nayi alƙwarin free ne amma naga baku da halin kai ina ƙoƙarin na ɗauke kai ni ban fiya kace nace balabu ɗaya nake faɗa,wlh duk wanda yake karantawa yau bai comment ba ya tabbatar kuɗinsa zai kuka domin ko biyar na rabaka da ita nadai rabaka da itan🤷🏻♀️shawara yana wajanku_.
F@y@l
_The secret issues_
*💖JUYAYI💖*
*24-25*
*_Wattpad_*
https://my.w.tt/jN2GLY5RKcb or Nimcyluv
*_Telegram_*
https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ
يايهاالذين ءامنوا اذكروا الله ذكرا كثيرا، وسبحوه بكرة وآصيلا.
......Cikin tashin hankali Sufyan yay kanta tare da ɓanɓareta daga jikin gawar Faisal,ɗaukanta yay tare da fitar da ita daga cikin room ɗin gaba ɗaya.
Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana tabbas ko wanne bawan Allah saiya ɗanɗani cin mutuwa da raɗaɗinta haka da zafinta,kuma dukkan mai rai mamacine,Allah baya barin wani dan wani yaji daɗi a ko'in kake Ubangiji na iya ɗaukan ranka a duk lokacin daya gadama,Allah daya halicce mutum shike da ikon karɓan ransa saida wani yay sanadi.
Papi duk dauriyarsa saida ya zubar da hawaye,a hakan ba ƙaramin ta waƙƙali yay ba domin Faisal yay mutuwa mai kyau mutuwar dako wanne bawa zaiso yay irinta,Ammi kuka tayi harda suma yayinda tsanar Lili ta dira acikin zuciyarta lkc guda tsanarta mai girma ta shiga ko wacce ƙofa ta jikinta,ta tabbatar da baƙin cikin Lilin ya mutu aida bai mutu ba saida tazu,da ƙyar aka samu kan Ammi,Najma kusan haukacewa tayi saida aka yi mata allurar bacci ta wajan 24hours,haka aka ɗauki gawar Faisal aka saka a ambulance suka nufi gida da ita,lokacin mutane sun cika cikin gaggawa aka shiga da Faisal tare dayi masa wankan gawa aka shirya yashi cikin lafiyayyen kayansa kaya na har abada kayan da ya zamewa ko dolen sashi a ranar da zaiyi kwanan ƙarshe a nan gidan duniya,ana gama shiryasa akai waje da gawarsa cikin makara.
Sufyan na fita da Lili babu inda ya tsaya da ita sai wani specail room,aka shiga dubata tare ɗinke inda Najma taji mata ciwo,ganin ciwonta na Asma na shirin tashi yasa sukayi mata allura tare da ɗaura mata drip,ganinta samu baccine yasa Sufyan fita tare dayin harabar asibitin ya shiga motar ya nufi gidan da suka baru dan yana da tabbacin nanne gidan da akai rasuwar,tunda yake bai taɓa ganin mutuwa ido biyu wacce ta tsora tasa tare da ƙara masa ƙarfi imani ba irin mutuwar Faisal,sosai yake gudu harya isa unguwar Maiduguri road yana zuwa ana gama sallatarsa mutum biyu ne suka shiga motarsa cikin saurin suka rufawa motar gawar lokaci kaɗan suka isa maƙabartar,lkcn angama haƙa kabarinsa babba da uwar ɗaki,bisimillah akai tare da sakashi a ciki idan nan bai cika ba sai ɗebu ƙasa tare da dannawa cikin kabarin,daga ƙarshe aka ɓallo ƙatun reshan bishiya aka ciccika a cikin kamarin ana gamawa aka shiga zuba ƙasa saida aka gama sannan aka shiga yi masa addu'a tare da kafa allo aka rubuta.
_Rest in peace_
_Faisal khalil cibaɗo_
_wed/jan/13_
Ana gamawa kuwa ya shiga mota aka barshi shi ɗaya daga shi sai halinsa,mutuwar Faisal ba ƙaramin girgiza Papi taima amma yay ta wakkali tare da rungumar ƙaddararsa,kuwa ya ganshi sai yaga ramar da yay ya faɗa lkc guda idanunsa yay zuru-zuru,ta'aziya Sufyan yay masa tare da bashi ƙaramin card ɗinsa mai ɗauke da adress haɗi da number waya sannan yay masu sallama a kan zaije ya ɗauki Lili su tafi Abuja kar dare yayi.
Sufyan na shiga mota yay asibiti da gudu bai daɗe ba ya isa cikin asibitin,yana shiga daret babu inda ya nufa sai room ɗin da take ƙwance zuciyar cike da tsanar yayarta ta,ƙwance take flat tana sauke numfashi a hankali kana kallan fuskarta kasan bata cikin nutsuwarta musamman idan ka lura da yadda ta haɗe fuskar hawaye yay mata fata-fata a saman innocent face ɗinta,zama yay tare da kama hannunta ya ɗan murza ka ɗan tare da ranƙwafawa ya sakar mata sumba a gefen lips ɗinta cikin sanyin muryar yace.
"Lovely bbyn am sorry bansan zaki tarar da ƙatuwar tashin hankalin nan ba daman kawo ki ba pls for give me ban ƙarawa..numfashi yaja tare da shafa gefen fuskarta yana mai jin wani iri a jiki tabbas da ace matarsa a yanzu babu abinda zai hanashi jin ɗumin jikinta,lumshe ido yay yana maijin wani abu a zuciyarsa mai kama da fargaba,ƙara kallonta yay yace"Lovely bby ina kishinki sosai da wannan mamacin amma bana fushi dashi domin shiɗin abin tausayi ne amma banjin zan iya hqr dake komai wahala komai daɗi dama yau igiyar aure ta shiga tsakanina dake da yau saikin tabbatar da zallar ƙaunar da nake maki ruhi da kuma gangar jikina,amma babu damuwa kamar yadda na jure sati huɗu haka zan jure sati ɗayan ban dama bikin waccan sakalya mai zaisa subar gari".
Haka dai yayta surutu shi ɗaya kafin ya miƙe ya zare drip ɗin hannun ya saɓata a shoulder ɗinsa yay waje,yana zuwa ya buɗe side ɗin mai zaman banza tare da ƙwantar da kujerar ya ƙwantar da ita akai ya sakar mata wani lafiyayyar murmushi"yi baccinki bbyn zuciyanki na buƙatar hutu akwai lokacin da shayar dake zallar soyayyar zan maki madarar soyayyar da babu wani namiji dazai iya baki ita"gefen wuyanta ya shafa tare da rufe ƙofar ya koma side ɗin drever yaywa motar key tare dayin ribers ya figeta da wani irin speed yay waje yabar cikin asibiti yana fita ya harba motar kan titi sai Abuja.
Basu isa Abuja ba sai dab da magrif ganin sun ƙarasu area ɗinsu ya shiga dreving a hankali harya kawo babban get ɗin gidan wani ƙyaƙƙyawan horn yay da sauri Getman yazu ya wangale masa get ɗin,hancin motar ya cilla cikin harabar gidan yana gama parking a parking space ya fitu daga cikin motar tare da ɗaukanta ya nufi cikin gida da sauri jin yadda jikinta ta ɗauki zafi.
Da mamaki Momma ta tsaya tana kallonsa bakinta ɗauke da tambaya amma ta share,bedroom ya nufa tare da ƙwantar da ita har ya saka hannu zai cire hijab ɗin jikinta sai kuma ya fasa yaja mata duvet tare da ƙara gudun A.c'n yay waje.
A nan parlon ya tarar da Momma ita da Yusrah sai haɗa kayan tafiya suke,daman Alhaji baya gari sai ana ƙwana ɗaya ɗaurin aure zai dawo,zama yay kusan Momma tare da ɗura kansa a kafaɗarta ba tare data kallesa ba tace
"Meya faru?" kallonta yay da idanunsa da suka sauya kala sam baison tafiyar nan gani yake kamar akwai abinda zai faru,nan ya shiga labarta mata abinda ya faru,shuru tayi na wani lokaci sai kuma tace.
"Allah sarki wannan bawan Allah tabbas naji wannan mutuwar Allah ya jiƙansa,daman aƙwai ƴan uwa masu irin wannan halin jin ƴar nan inda ta tunda murnar ganin ƴar uwarta amma ji abinda ta aikata mata dole a kira Dr yadu bata before mu huce gobe"
Jinjina kai kawai Sufyan yayi kafin ya miƙe tare da shigewa bedroom ɗinsa,a daren aka kira Dr yadu bata inda ya tabbatar masu babu matsala amma sai zuciya gobe zata farka sbd tsoro da firgicin data shiga,sallama yay masu sannan ya huce abinsa.
Yana fita Sufyan ya kalli Momma yace"amma mai yasa dole sai munyi tafiyar nan ina ganin a hqr kawai ayi auren a nan a bani matana"
Harara ta watsa masa kafin tace"idan bakka so babu dole kana iya zama"tana faɗin hakan ta huce flat ɗinta,ya daɗe yana kallon Lili kafin ya sakar mata sumba tare da tsotsar laɓɓanta ya fice da sauri,flat ɗinsa ya huce shima yana shiga ya faɗa saman bed ɗinsa tare da lumshe ido hannu yasa ya shiga danna mararsa tare da shafawa jin yadda ta kumbura tare dayi masa zafi ya daɗe yana juyi kafin ciwon ya lafa masa ya shiga sauke numfashi a haka bacci ya ɗaukesa.
*** ***
A can Kano kuma bayan tafiyar Sufyan manyan mutane ne suka shiga zuwa wajan Papi ta'aziyya kowa da ƙyaƙƙyawar addu'a a bakinsa,babu abinda za'ace sai halinsa na gari ya bishi domin duk wanda yasan Faisal ansan mutumin ƙwarai ne hankali nutsuwa biyayya uwa uba riƙo da addininsa.
Haka akai ta karɓar gaisuwa har dare yay Papi ya koma cikin gida,yana zuwa yay flat ɗin Ammi amma taƙi buɗewa yay yin duniya taƙi buɗe,rabuwa yay da ita sbd yasan condition ɗin da take ciki a yanzu babbar rigarsa ya cire tare da ƙwanciya akan duguwar sofa cikinsa ya shafa jin yana masa zafi da murɗawa sai lokacin rabosa da abinci tun jiya da safe shima tea kawai ya iya sha,tunanin Lili ne ya faɗu masa a zahirin gsky yana tausayinta domin baisan halin da zata shiga ba,batun Najma kam bai fiya damunsa sbd ba ƙaramin haushi ta bashi ba duk da yana jin tausayinta a cikin ransa domin baisan a wanne hali zata farka ba,a haka bacci ya ɗaukesa.
Washe gari tun shida na safe Anty Kausar ta sauka sbd tun jiya jirginta ya tasu wajan baƙwai kuma Anty billy ta shigo tun daga waje ta fasa wani kuka mai rikitarwa suka ƙanƙame juna ita ƴar uwarta Anty kausar sosai suke kuka kamar ransu zai fita,da ƙyar Papi ya rarrashesu domin har sukai shuru kallonsu yay yace.
"ya kamata kuje wajan matarsa can asibitin"Anty Kausar ce ta turo baki tare da faɗin.
"Allah Papi ban zuwa sam ba taimin ba,ba zance ita ta kashemin ɗan uwa ba,amma tunda ya aureta Faisal baya da sukuni bashi da fara'a kullum cikin ƙunci da baƙin ciki yake,ko vedio call muke haka zai sakarmin kuka yin duniya amma bazai faɗan damuwar ba,Papi idan ba ita ba wake da alhaƙin saka Faisal damuwa"
Ta ƙarasa faɗa tana faɗawa jikin Papi tare da sakin kuka dan gani dake tafi kowa jin mutuwar Faisal ɗin.
Papi ya gama sanin ƴar tasa daka fiya dan haka yace Anty Billy ta shirya ta tafi babu musu ta ɗauki key tare da basket ɗin abinci tayi waje.
Rumgome ƴar tasa yay tare da tapping ɗin bayanta ya shiga rarrashinta tare da nusar da ita yadda da ƙaddara da kuma hqr a kan hali da bawa ya tsinci kansa kuma mutuwa nakan kuwa yanzu Faisal addu'arsu kawai yake buƙata a haka ya samu ta shiga sauke ajjiyar zuciya.
Anty few minutes da ƙarasa asibitin babu inda ta tsaya sai ɗakin da aka ƙwantar da Najma tana zuwa ta kanta ƙwance sai numfashi take saukewa hannunta ɗaure da drip,juyawa tayi tare da zama kan sofa ta gumi tayi domin sosai take tausayin matar yayan nata duniyar tunani ta lula a haka bacci ya ɗauketa sbd kukan data ƙwana ta nayi jiya.
*** ***
Tun asuba da suka farka basu koma ba sbd bakwai na safe jirginsu,Momma da kanta ta shirya Lili take ƙwance kamar gawa ta saka mata wata a baya mai blue black ta gyara mata gashin kanta tare da naɗa mata vail ɗin a bayar a kanta ta fesheta da turare,tana gamawa ta fice daman ardy ta gama shiryawa sun zuba kayansu a mota Sufyan kawai suke jira.
Cike da ta ƙama yake tafiya harya ƙarasu inda Momma da Yusrah suke zaune gaisheda Momma yay Yusrah ta gaidashi,kallonsa Momma tayi tare da faɗin.
"daman kai muke jira kaje ka ɗakko Lili kasa memu a mota kada ka tsaya sakalci".
Kai kawai ya jinjina mata tare da nufar cikin bedroom ɗin yana shiga ya lumshe manyan idanunsa tare da buɗe hancinsa ya shiga shaƙar daddaɗan ƙamshin dake fita a cikin ɗakin,can tsakiyar bed idanu ya zuba mata ya daɗe yana kallonta harya ƙarasa wajanta sunkuyawa yay ya ɗauketa tare da matse a jikinsa ya shiga fitar da numfashi ji yake inama zai iya mai data jikinsa babu shakka da yay hakan sosai wutar sha'awarta ke barazana da numfashi da kuma ganggar jikinsa a dukkan lokacin daya haɗu da ita musamman sukai haɗu jiki da ƙyar yake iya jan numfashinsa tare da dai² ta nutsuwarsa,ƙara matseta yay tare da sunkuyawa tare da cafke lips ɗinta na ƙasa ya shiga tsosa,kasancewar bacci take bata san abinda yake aikatawa ba,ƙara shigewa jikinsa tayi ta shiga mamul² da lips ɗinsa sai haka yay kamar tana sucking lipa ɗinsa take,saurin cire bakinsa yay lokacin idanunsa ya kama sauya kala sosai yake fitar da numfashi mai zafi saida ya dai² nutsuwar dankar Momma ta gane kana ya saka kai ya fice daga cikin gidan.
Tun daga nesa ta zuba masa idanu domin ganu abinda take tunani haɗe fuska tayi lokacin da tunaninta ya gama bata abinda zuciyarta ke rayawa,yana ƙarasuwa ta zabga masa harara tare da faɗin"sakalan banza Yusrah koma gaba ya miƙomin ita nan"haka akai badan ransa yasu ba ya ƙwantar da ita cinyar Momma sannan Yusrah ta shiga gaba shi kuma ya shiga mazaunin drever,key yaywa motar sannan ya cilla hancin motar waje,da sauri drever'nsu ya nemi napep yabi bayansu sb shine zai dawo da motar.
Sun isa fitin tashi da jirgi take garin abuja lokacin har sun makara suna zuwa ana kiransu basu ɓata lokaci ba suka shiga cikin jirgin Momma da Yusrah suna ƙujerar tsakiya yayinda Faisal ke rumgome da Lili a ƙujerar baya,ya matseta a jikinsa tare da zare vail ɗin kanta ya tura hannunsa cikin sumar kanta yayinda ya sauke laɓɓansa a dugun wuyanta, a haka jirginsu ya lula sama.
*** ***
_Folato_
Ganin yadda ya birkici mata ne yasa ta tsaya da kukanta ta shiga shafa sumar kansa tare da karanta masa addu'ar samun sauƙi a cikin zuciya sun daɗe a haka kafin ta samu jarumtar yi masa mgn"Yarona kana son gayamin ɗan uwana kuma yayana baya yare,kana son gayamin nima na tabbata marainiya mara gata kamarka"ƙara shigewa jikinta yay yana lumshe idanunsa sosai maganganun ƙanwar Daddynsa keyi masa barazana a zuciyarsa sosai ya kejin zafi da raɗaɗin maganganunta amma ƙaddara ta riga fata dashi da ita babu yadda zasuyi da hukuncin ubangiji haka ya tsara masu dole su amshi jarrabawarsu hannu bibbiyu,ɗago kai yay a lokacin idan ka ganshi baza kace idanunsa sun zubar da hawaye ba sosai ya dai²ta nutsuwarsa ɗan ƙwaɓe fuska yay tare da faɗin.
"Mamana amma wannan yarinyar fa?"
Murmushi tayi tare da shafar sumar kansa tape.
"laa yarona ya manta twins sister ɗinsa" ware manyan idanunsa yay tare da faɗin"what twins don't tell me suka dawo haka?"
Dry tayi masa tace.
"Yarona shekara nawa rabonka dasu tun muna nigeria bama kasan mundawo nan ba sai ƙaddara data kuma haɗamu"
"kuma danta rainani shine za tace tana sona kamar wani sa'anta"
Shuru kawai Mama tayi masa danza tafi kuwa farin ciki idan hakan ya faru,hannunsa da taji saman fuskarta shine ya dawo da ita daga tunaninta"Lili fa bata mutu ba Mama zuciyata ta kasa yarda sister bata raye inajin zafi da raɗaɗin rashin da ace tana kusa dani da zuciyata ta samu sauƙi daga ciwon da take min,Mamana bana iya bacci ban iya cin abinci ko hospital naje ban iya aiki banjin daɗin duniyar sam ina zan ganta wanne hali take ciki shine ban sani ba"
Sassautar muryarta tayi tare da faɗin"idan bata raye tana ina,yana da ƙyau ka ɗauki ƙaddararka a matsayinka ma musulmi ka yarda Lubna bata yare"
Runtsa idanunsa yay idan akwai abinda ya tsana bai huci a kira masa Lili da sunan matacciya ba tana raye tabbas tana numfashi a doran ƙasa kamar yadda shima yake numfashi.
Haka ya ƙare yinin ranar wajan ƙanwar Mahaifin tasa wacce a yanzu yake mata kallan Mamynsa,tasha taɓararsa duk mutsi kaɗan zaice"Mamana"yana faɗin hakan zaija idanun ya rufe ruf,sai dare ya miƙe tare dayi mata sallama kamar baiso tafiya haka Fauwaz yaja hannunsa suka nufi flat ɗinsu.
Jikin shirinsa na fita hospitan ya fitu wata gezner nace mai kalan skyblue tare da black coppet shoe mai ƙyau ko hula bai saka ba,sai sumar kansa da tayi luff tasha gyara sai sheƙi take idanunsa manne jikin farin glass,tun daga nesa zaka san yana tafe sbd wani daddaɗan turare daya saka mai sanya nutsuwa.
A hankali yake takawa hannayensa ya zurasu jikin aljihun rigarsa compund ɗin gidan yabi ganin cars sun ƙara taɓe baki yay tare da sanya kansa cikin babban parlon gida bugawar da zuciyarsa tayi ne yasa shi runtsa idanunsa tare da saka hannu ya dafe saitin zuciyarsa a hankali ya ware jajayen laɓɓansa yace “MY SUNSHINE” mutsin daya jine ya sashi ware manyan idanunsa tare da saukesu a kan wani matashin sauri wanda kallo ɗaya yay masa ya fahimci yaro ne dan zai girme masa da wajan shekara uku zuwa huɗu,kallon 3min yay masa ya ɗauke kai,shikam matashin saurayin sosai ya shagala da kallon Fahad duk ƙyansa amma saida ya raina kansa da yaga Fahad baiwar ƙyau da kuma tsarin halittar da ubangiji ya bashi yake kallo ga wani ƙwarijini haɗi da haiba daya gani ƙwance saman fuskarsa uwa uba kuma annuri addinin musulunci daya gani a kan fuskar tasa.
Afnerh dake tsaye tace"laa bro Fahad wannsan Sufyan kenan sunzu bikin Fannerh wanda za'a haɗa da nasa matarsama na ciki babu lpa"
Tsaki yaja cikin wata murya mai sanyi da daɗi yace"talkative" yana faɗin hakan yaja tsaki tare da juyawa ya shiga mota ya jata d wani irin mauƙacin gudu yabar gidan gaba ɗaya.
_wanda yay dai² ya sani gashi nan dai Readmore 4 ne,ƙyautatawar daza kuyimin shine comments da share_
F@y@l
_The secret issues_
*💖JYY💖*
*26-27*
*_Wattpad_*
https://my.w.tt/jN2GLY5RKcb or Nimcyluv
*_Telegram_*
https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ
*SELF DU'A🌚👇🏻*
```Ya Allah ka yarda dani,kasoni kasa mala'ikunka su soni,kasanya mutanen kirki su soni,Allah ka rufamin asiri,kabani sa'ar rayuwa da mutuwa,ka samu rayuwata albarka..Allah ka kareni daga sharrin mutum..Aljan..da dabba,Allah na roƙeƙa ka karenu daga sharrin mai sharri da zargin mai zargi da munafunci mai munafurci da hassadar mai hassada,Allah kasa na gama da duniya lafiya Ubangiji ka sanyamin Albarka..```
Not edited🥱
......Baki Sufyan ya saki tare da jinjina girman jin kai irinna Fahad ɗin,ata rihin rayuwarsa zai iya cewa bai taɓa ganin mutum mai ɗagawa da jijjida kai ba sai yanzu da Ubangiji ya haɗashi da Fahad haka kawai yaji bai masa ba,lkc guda yaji wani matsanancin kishinsa ya dirar maza a zuciya,basarwa yay tare da kallon Afnnerh yace "Muje ki tayani ɗakko kayan matana"washe baki tayi tare da kama hannunsa suka isa gaban wata ƙatuwar mota,bayan motar ya buɗe ya shiga sakko da kayan jiki saida ya gama ya rufe ya ɗibi manyan aƙwatinan ita kuma ta ɗauki ƙanana,yana gaba ta binsa a baya a haka suka ƙarasa cikin parlon,Momma da Mama ne zaune sai kuma Yusrah wacce take kusa da Fannerh,da sallama ya isa yana zuwa ya ajjiye aƙwatinan tare da zama a kan sofa mai ɗaukan mutum guda,Mamace ta amshe da faɗin "Sufyannu manyan yau dake bikin kane ai naganka a gidana ko,gaba ɗaya mantawa kake da gidan ƙanin wan mahaifin naka sbd kirki da yay maka yawa,na tabbatar a hanya ka haɗu da twins ba lallai kasan ka haɗa dangi dasu ba"ƴar dariya yay tare da cewa"yanzu Mama bagani ba and how many time I'm telling you ki daina kirana da wani Sufyanu haba haka nan kamar wani tsohu just say Sufyan shine abun wahala haba Mamana"dry gaba ɗaya sukai.
Miƙewa yay tare da zubawa ƙofar bedroom da aka saka Lovely bbynsa a ciki kana ya girgiza kai yay flat ɗin da aka masa.
yadda yake dreving cikin fusata tare dajan motar da gudu shi zai tabbatar maka baya cikin nutsuwarsa,why zuciyarsa zatai masa hk,mai yasa a kullum baya jikin nutsuwarsa da tunaninsa?.
Ina zan ganki when zuciyana zai daina beating a kanki?.
Idan akai da duba da shekarun baya da suka huce ba abin mamaki bane domin ta riga ta zama jinin jikinsa kamar yadda yake da tabbacin itama ya zama jinin jikinta.
Motar ya ficika da ƙarfi lkcn da ƙyar yake buɗe idanunsa wanda suka gama yi masa nauyi.
Wani ƙawataccen murmushi yay wanda ya ƙawata ƙyaƙƙyawar fuskarsa wacce take zagaye da yalwataccen saje baƙi siɗik zai ƙyalli yake.
Tura hannunsa yay cikin tulin sumar ƙansa wacce take ƙwance luff saman kansa.
A ƙaro na farko bayan rasuwar iyayensa yaji wata nutsuwa da kuma farin ciki sun saukar masa,bayace ga dalili ba domin shi kansa baisan dalilin hakan ba abu ɗaya ya sani he is in happiness.
Lafiyayyun jayayen laɓɓansa ya wara cikin lion voice yace “MY SUNSHINE BBY”.
Ƙira'ar sheik Sudais ya saka cikin suratul yaasin,ya shiga bin karatul cikin daddaɗar muryarsa ya nayi yana lumshe idanunsa a haka ya ƙarasu babban asibitin prvt hoptl dake unguwar Folato a garin paskitan.
Parking yay a harabar asibitin tare da kashe ƙira'ar dake tashi fituwa yay daka ciki ganin yadda aka zuba masa idanune yasa shi tsuƙe fuska tare da sadda kansa ƙasa yana tafiya cikin nutsuwa.
Wata nurse dake gefensa ita da wata mata tace.
"wow Rabbi yaban irin wannan mijin a matsayin maɗin rayuwata komai nasa ya haɗu kalli yake tafiya kamar wani ɗawisu".
Taɓe baki yay tare da taune lips ɗinsa a ransa yana mamakin mata masu irin wannan halin.
Ganin bashi da wani tym ne yasa shi hucewa duba marasa lpa.
Sosai ya duba marasa lafiyansa yana shirin fita wani Dr ya shigo da sauri tare da faɗin.
"Dr Fahad pls wata zaka duba babu lpa"
Numfashi yaja tare da faɗin"babu tym"
Cikin sauri Dr ya ƙara faɗin"wlh she is critical condition Asmer ya takura mata"
Jin cutar da yaji Dr ɗin ya faɗa ne yasa shi saurin kallonsa.
Runtsa idanunsa ya runtse da ƙarfi cutar daya tsana ko sunnanta baison jin cutar data takura masa little sis ɗinsa yana jin tausayin duk mai irin cutar.
"where is she?"...yana faɗa tare dayin gaba,cikin rawar murya Dr ɗin yace.
"tana Emergency"
Yadda zuciyarsa ke bugune yasa shi tsayawa daga ƙoƙarin shiga room ɗin.
Dafe zuciyansa yay tare da faɗin"ya rabb"
Yana faɗin hakan ya tura kansa cikin room ɗin,tun daga nesa ya kejin ɗaukewar numfashinta zai ƙoƙarin shaƙa mata inhela suke a baki.
"oya waje"shine abinda ya samu damar faɗe cikin sauri suka fice,a nutse ya shiga mata taimaƙon gaggawa cikin iƙon Allah numfashinta ya fara dai²ta Oxygen ya saka mata tare da ɗaura mata drip ya zuba injection a ciki.
Ganin komai yay nrml ya fice daga ɗakin lkc ya duba yaga 2 saura daɗan sauri ya shiga cikin toilet ya ɗaura alwala.
Yana fituwa ya ɗauki key ɗin motarsa yay waje.
Motar yaywa key tare da janta da gudu ya nufi masallacin juma'a.
*SUFYAN POV*
Yana shiga bedroom ɗinsa deret toilet ya nufa yana zuwa yay taken shower cikin sauri ya ɗaura alwala,bai jima ba yazu ya shirya cikin jallabiya ganin da sauran lokaci na zuwa masallaci,faɗawa kan bed yay tare dajan numfashi,rashin kulawar da Fahad yay masa sosai ya tsaya masa a rai,haka kawai ya kejin abin na damunsa"harni zai kalla ya watsar who is he"ya faɗa a zafafe tare da fiddo manyan idanunsa,ƙyaƙƙyawar fuskarsa wace take masa kama data Lovely bbynsa itace ta tsaya masa a rai,sosai fuskarsu ke yanayi data juna musamman eyes ball ɗinsu da yanayin yadda suke lumshe ƙawawan idanunsu,tsaki yay tare da faɗin "whatever dai she's beautiful more than him" ya ƙara jan tsakai na rashin dalili a haka bacci yay gaba dashi ba tare daya sani ba.
Waje ne mai ƙƴan gaske musamman idan kayi duba da hasken glove ɗin dake bada difference colour masu ƙawatarwa,jama'ane gota ina duk inda ka juya su zaka gani sanye da fararen kaya tare da furanni a hannunsu,cikin farin ciki ya ƙarasa inda take zaune sanye da kaya na alfarma tayi kyau tare da haske kamar daran goma sha huɗu,yana zuwa ya saka hannunsa tare da miƙar da ita tsaye, murmushi ya saki tare da ƙoƙarin haɗata jikinsa fincigarta akai tare da ɗaukanta aka dannata cikin mota,ihu ya saki gannin yadda aka sace masa mata akan idanunsa a rana mafi muhimmanci a cikin ranakun rayuwarsa,kuka ya saki tare dayin jifa da dukkan abinda ya gani.
Some hours ago wata ƙyaƙƙyawar mota tayi parking wani matashin magidan cine ya fitu kana ya buɗe ɗaya side ɗin wata matashiyar budurwa ta fitu cikin shiga mai kyau,da gudu ya miƙe daga durƙushen da yake,hannu yasa zai kamata tayi saurin daka masa wata mahaukaciyar tsawa,sbd yadda idanunsa suka rufe da ganin matarsa yasa sam baiji tsawar da tayi masa ta shigesa ba,saima ƙara tunkararta da yay,ƙaton cikin daya gani a jikinta ne ya sashi sakin wata mahaukaciyar ƙara.
A firgice ya farka daga nannauyen baccin daya ɗaukesa gaba ɗaya jikinsa rawa ya firgita sosai da mafarkin da yay,wace wannan?waye ya ɗauketa?cikin waye?wannan shine tambayoyin dake ransa,sanin bashi dame bashi amsane ya miƙe jiki a sanyaye tare dayin toilet ruwa ya wasa tare da saka toilet a jikinsa,cikin sauri ya shirya tare da ɗaukan paryer mat da key ɗin motarsa da take ajjiye a gidan,yana fita ya yaga babu kuwa a parlo sai Mama,murmushi yay mata kana yace"Mama zanje masallaci amma zanga jikin matana"ɗan murmushi tai masa kafin tace"zamani kenan idan kuma aka fasa ita fa?..har kake wani Matana"saurin kallonta yayinda zuciyarsa ya bada sauti da ƙarfi kamar zai kuka yace"ayya Mama babu kyau irin wasanan fa,ita ɗin matana ce"yana faɗin hakan ya nufi ɗakinsu Afnerh ƙwance ya sameta sai sauke numfashi wahala ta faɗa sosai sai fari data ƙara,brest ɗinsa sun ƙarayin sama sam ba zakace tana halin ciwo ba,tsora mata idanunsa harya ƙarasu inda take ƙwance,gefen fuskarta ya shafa haɗi da riƙe hannunta yaɗan murza ya daɗe yana kallonta kafin ya shafi sumar kanta yay waje,yana fita ya nufi compound na gidan tare da shigewa mota ya nufi masallaci.
Misalin 4 Sufyan ya dawo daga masallaci saida ya tsaya yay la'asar,a hankali yay parking tare da fituwa ya nufi cikin gidan kai tsaya,a gajiye yay sallama gaba ɗaya suka haɗa baki wajan amsa masa,babu wanda ya kula sai wajan daining area daya nufa yana zuwa yaja kujera plate yaja tare da buɗe wamer ya zuba dambun shinkafa wanda yaji zugale da kifi sai ƙamshi yake zabgawa,cikin sauri ya ɗauki spoon ya shiga cin dambun saida ya gama sannan ya miƙe tare da dawowa parlon dryar Yusrah ce ta ƙwance kafin tayi magana Mama tace"ashe yunwa ta rufe maka idanu ka kusa taƙen ƙafa" dry suka ƙara saki mai kula kuwa ba yaje ya zauna kusa da Afnerh wacce tayi shuru tare dayin ta gumi"wannan tagumin fa?kamar ance maki saurayinki ya fasa aurenki"turo baki tayi kana tace"haba bro wlh ina sonsa kar kayimin baki"kaiya dunguri mata yace"eyee waye haka yay dace yay wuff dake"murmushi tayi sai kuma ta ƙwaɓe fuska tace"i luv him wlh ina sonsa bansan yaya zanyi ba"harara ya cilla mata yace"kaji shirme da wane yace baki sonsa?"hawayen da take ɓuyewa ne ya samu damar sakko mata tace"baya sona bro Fahad ne wanda kuka gaisa ɗazu" zuba mata idanu yay ashe kam zaki mutu wannan mai ɗan banzan mai jida kan,a fili kuma yace"Allah ya kyauta"hannunsa ta riƙe tana goge hawayen idanunta tace"pls bro do something wlh ba kaji zuciyata ba" Allah ya ƙyauta bai shirya ɗaukan wulaƙanci ba ya faɗa a ransa,miƙewa yay tare da shige bedroom ɗinsa ganin magrib ya kawo kai.
*FAHAD POV*
Tunda ya fita daga asibitin yaje majid bai dawo gida ba sai bayan isha'i,yana shiga Fauwaz ya bishi da idanu yana jin tausayin abokin nasa yasan rabonsa da abinci tun safe indai ba cewa akai ya zauna yaci abinci ba bazai taɓa zama yaci ba,bai taɓa ganin mutun irinsa ba wanda bai damu da lafiyarsa ba,abune mai wahala kaji cikin Fahad ga ɗan banzan miskilanci saiku shafe zama tare ba zaice ƙala,idan aka damesa ma tashi yake yabar wajan,"lafiya dai ka kai wannan daren?"lumshe idanunsa yay tare da buɗewasu a kan Fauwaz kai kawai ya jinjina masa ya shige cikin bedroom,girgiza kai Fauwaz yay tare da faɗin"Allah ya ƙyauta" wayar Fannerh ya kira sbd yazu basa ganin juna wai ana mata gyaran jiki shikam wannan gyaran jikin ya cucesa tunda ya hanashi ganin wafy ɗinsa,sun daɗe suna shira kafin ya kashe wayar,da mamaki yake bin Fahad ganin har yay wanka ya sauya kaya yana latse² a p.c ɗinsa,"yause ka dawo?"banza yay masa yaci gaba da aikinsa shi kaɗai yasan mai yake a gobe ya ɗauki niyar zuwa garin yola tunaninsa acan ya manta takaddun da Dad ya basa,haushine ya kama Fauwaz yace"mutum shikenan fuska babu walwala babu farinci koda yaushe kana cikin ƙunci kamar kaika ɗurawa kanka damuwa wannan fa ba dai² bane bana jin daɗin yadda nake ganinka kullum,na ɗauka ganin Mama zai rage maka damuwa ashe ba haka bane"still bai ɗago ba kuma bai tanka saba,saida ya gama aikinsa sanna ya ajjiye komai ya ɗauki wayarsa yay waje,yana shirin ficewa sai kuma ya tsaya yace"tayaya farinci zai dauma a raina bayan babu silar farin cikin nawa"yana faɗin hakan ya fice daga cikin gidan deret get ɗin gidansu Mama ya nufa daga shi sai wando 3gauter sai black ɗin riga mai ƙaramin hannu hakan ya sanadiyar fituwar murɗaɗdiyar damtsen hannunsa tare da bayyanar faffaɗan ƙirjinsa har tsinin nipples ɗinsa ana gani sbd yadda rigan ya kamasa,hannunsa sake cikin aljihun wandonsa a haka yake typing cikin takunsa wansa yake nuna shiɗin lafiyayyen namijine mai taƙama da ƙyan halittar da bayyawar surar da ubangiji ya bashi haɗi da ƙwarjini,a haka ya isa ƙofar da zata kaisa babban parlo lumshe idanunsa yay haɗi da taune lips ɗinsa kansa ne ya sara sosai jiyaye kamar ya juya sai kuma ya tuna yau gaba ɗaya baiga Mamansa ba,a hankali ya murɗa handle ƙofar tare da turawa ya danna kansa ciki bakinsa ɗauke da sallama.
Gaba ɗaya suka juyo suna kallonsa har Sufyan dake zaune saman sofa yana waya,tsaki yaja mai tsauti a ransa yana faɗin "Mayu"yana faɗin hakan yay wajan Mama yana zuwa ya zauna kusanta tare da shigewa jikinta cikin sassayan muryarsa mai daɗi yace"Mamana nayi missed naki"kansa ta shafa tace"na ɗauka nayi laifine ai,yanzu nake shirin kiranka"lumshe gajiyayyun idanunsa yay tare da ƙara lafewa a jikinta,cikinsa ta shafa taji wayan ya lafe kamar zai haɗe da bayansa tayi sauri faɗin"Yarona mai yasa bakkason cin abinci?"Fannerh ta kalla tace"maza ɗauki plate ki cikomin shi da abinci tare da ruwa da kuma juice"Afnerh ce tayi saurin miƙewa bata daɗe ba ta dawo hannunta ɗauke da plate ta cikoshi da dambun cuscus yaji kayan lambu da bushasshan kifi sai ƙamshi yake.
spoon ta ɗauka zata kai bakinsa yay saurin riƙewa murmushi tayi ta ajjiye spoon tare dayin bisimillah tasa hannunsa a haka ya fara cin abinci wanda duk rabi sakalcine.
Baki Sufyan ya saki ganin sangarta ido biyi ko Yusrah ba zatai wannan taɓarar ba,amma ƙato dashi wajan shekara sama da talatin ya zauna yana wannan shagwaɓar ransa ne ya ƙara ɓaci ya shiga ja tsaki,ƴan matan kam gaba ɗaya idanu suka zuba masa musamman Afnerh da Yusrah wanda komai nasa yake tafiya da tunaninsu haɗi da zuciyoyinsu.
Sarai Fahad ya lura da yadda Sufyan yake ja masa tsaki amma shiko a jikinsa,da ƙyar Mama ta samu yaci rabin plate ɗin tare da shan gorar ruwa lemon kam cewa yay a'a,ƙara rungometa yay ya sakar mata sumba a kumatu yay saurin miƙewa jin kansa na sara masa ga yadda gudun zuciyarsa daya ƙaru,yana gab da ficewa daga cikin ɗakin yaji an saki wata mahaukaciyar ƙara daga cikin wani ɗaki,kamar an haɗa baki shida Sufyan suka zura da gudu cikin ɗakin har suna gware.
Sorry for the short typing am not ok.
0 comments:
Post a Comment