Yadda yayi din sai ya bata tausayi,don haka ta ajjiye wayar tana cewa
"Wai tausa da dadi ne?" Dariya ta taso masa amma a yanayin da yake ciki batayi wani tasiri ba,ya maye gurbin ta da murmushi don ta bashi dariyar sosai can qasan ransa
"Sosaima" ya furta a hankali yana lumshe idanunsa sanda tattausan tafin hannunta ya sauka a tsakiyar bayansa.
Tun tana dari dari har ta sake,ta dage ita bilhaqqi da gaske tausa take masa,yayin da idanunsa suka kasance a rufe,yana jin yadda hannuwanta ke kai komo a bayansa,shi kadai yasan abinda yake ji cikin ruhi da gangar jikinsa.
Kasa daurewa yayi,cikin wani irin zafin nama yayi mata wani irin juyi ya maidata gurbin daya tashi shi kuma ya maye nata gurbin ta hanyar mamayeta gaba daya,hadi da yi mata rumfa da mayalwacin qirjinsa.
Tsoro ya gani a rubuce cikin idanunta,ta soma rarrabasu tana kallon gajiyayyar fuskarsa dake cike da shauqi da mayen so da qaunarta,da kuma burin kasancewa da ita.
A tausashe ya rungumota cikin jikinsa,fatarsu ta hade guri guda,dumin jikin junansu ya gauraye waje daya,ya sanya kansa cikin wuyanta ta soma gaya mata wasu kalamai da suka saukar mata da nutsuwa,suka kuma sakata narkewa a wajen ba tare data sake qwaqwqwaran motsi ba.
Cikin salo da kuma qwarewa ya fara aike mata da wasu saqonni da dukkan jikin da jini ke gudana a cikinsa zaiyi wuya ya tsallake musu,saqonnin da suka dinga bin dukka wata jijiya dake aike da tunani da kuma tantance abu suna tsinketa,suka dinga dilmiyar da ita zuwa wani bigire na daban,bigiren da dukka wani tsoro nata ya gushe yayi nasa waje.
Saida komai ya kankama sannan ta fara gani kuskuren data tafka,tuni aikin gama ya gama,ya sake tabbatar wa zuciyarsa da gangar jikinsa cewa ita din mallakinsa ce halak malak.
Kamar wancan karon,wannan karon ma yanayi ya shiga sosai,ya riqeta sosai cikin jikinsa yana sauraren siririn kukan da take fitarwa,wanda kusan fiye da rabinsa shagwaba tafi yawa a ciki,yasan yau dinma dole zata jigata ta kuma ji jiki,don shi kansa yasan halinsa ta wannan fannin,amma kuma bazai kai karonsu na farko ba,baiji komai ba ya biye mata ya dinga lallashin abarsa,yana kuma dauke kowanne hawaye nata da harshensa.
Jinta yake takai masa ko ina,koma meye zai iya yi mata,haka ya lalace wajen rarrashinta.
Har sukayi sallar asuba suka idar taqi duban fuskarsa,ta gaidashi kanta a qasa,ya saki murmushi,ya matso kusa da ita ya zauna sosai har gwiwoyinsu suna haduwa,yasa hannu a hankali ya janye hijabinta baya,kyakkyawar fuskarta ta bayyana,ya sanya hannu ya kamo tafin hannunta ya saka cikin nasa yana ci gaba da kallonta
"Fushi ake dani baby?" Ya tambayeta yana narkewa kamar shima zai sakar mata kukan,kamar jira takeyi ita saita rigashi,ta sakar masa nata kukan qasa qasa
"Ba kaine ba......shine ka yimin wayo,saboda kaga ka girmeni" tayi maganar tana mele baki,kaman zaiyi dariya amma sai ya danne
"Am sorry,nima fa ba'a son raina ba,bansan nayi ba sai daga baya"
"Kuma fa gidan nan kasan akwai baqi,yanzu idan mom ahmad ta gane me zance mata?" Dariya sosai ta sake kamashi kamar yayi me,amma ya tabbatar idan yayita yanzu zai jama kansa jagwal
"Waye yace miki ana ganewa?, ba'a fa ganewa kayi,kuma ma....." Sai yayi qas sosai da muryarsa,ya sake matsowa da fuskar sa dab da ita kamar zai shige cikin hijabin
".....kowa yanayi,itama nasan sunyi jiya......." Bata barshi ya qarasa ba ta cure waje daya cikin hijabinta
"....don Allah uncle" a wannan lokacin kasa boye dariyarsa yayi,ya dora fuskarsa saman qafafunta yayi dariyarsa sosai yana jin nishadi yana wanzuwa a rayuwarsa.
**********Sati guda daya rak amma dai dai yake da wasu shekaru a wajensa,sati guda daya daya canza rayuwarsa da tunaninsa,tayi wani mugun tsayawa cikin rayuwarsa,ta kuma barma zuciyarsa wani babban tambari da yakejin har duniya ta nade bazai taba goguwa ba.
Jinta yake sosai a ransa,wani irin ji da yake ratsa zuciya matuqar ratsawa,tattali qauna da soyayya yake nuna mata irin wadda idanuwa basu saba gani ba,wasu abubuwan shi da kansa baisan yana yinsu ba,ta mantar dashi dukka wata damuwa tasa da matsalar da yakejin yana ciki.
Duk da bata gama sakewa dashi gaba daya ba,amma zai iya cewa ya samu fiye da rabin abinda yakeso,ya sani cewa da zarar ta sake sanin darajarsa ta kuma sake hankali da wayo,zai shiga sahun mazan da sukayi sa'ar matana aure a duniya,wani irin qauna da kimar hajiyarsa ke sake kwaranya a zuciyarsa,uwa uwa ce......uwa daban take,ashe irin wannan take ta kwadayin samar masa shi yasa ta dage cikin qanqanin lokaci sai data shigo da widad din cikin rayuwarsa?.
Ta fannin widad din ta sake zama wata tabararriya ta gaske,shagwabarta take zubawa yadda taga dama,biye mata yakeyi,ta koma tamkar su mimi,ko tari tayi sai ya tambayi ba'asi,duk wani koke koke da take masa a duk sanda ya samu yadda yakeso sam basa damunsa,yasa hannu ya karbe ya kuma shnaye dukka rigimarta,hasalima shagwabarta na daya daga cikin abubuwan dake saurin kunnoshi da rura wutar soyayyarta a zuciyarsa,wannan ya sake haifar da shaquwa tsakaninsu shi da ita,duk da har a lokacin yana tantamar tasan kalmar so?,abu na qarshe da yakeson ya gina gini mai ingancin da bazai rushe ba cikin zuciya dama rayuwarta gaba daya.
A qarshen watan ya gama yanke shawarar meye mafi girman tukuci da zai bawa rayuwarta?,yana tsaka da wannan tunanin saiga kyautar kujerar hajji har guda biyu daga wajen tsohon governor ya bashi kyauta,yayi masifar jin dadin aiki da abbas din,kuma har yau yana yaba masa,wannan yasa time to time yake tabo abbas din,inda tason ran Excellency dinne da tuni abbas din ya koma aiki qarqashinsa,saidai shi bashi da wannan interest din,dole ya haqura ya qyaleshi,amma lokaci lokaci yana taboshi akan wasu harkokin tsaro da suka shafeshi,kamar yanzun da zaiyi tafiyar,yaji ba wanda ya dace ya tafi dashi da yafi abbas din.
A lokacin babu wanda yaga ya dace da wannan tafiyar sai widad din,don haka ya karba daya yasa sunanta a daya ba tare da tasan ma da kujerar ba,aka soma processing na tafiyar,wadda zasu yita ne in group cikin tawagar his Excellency din.
Cikin sati na gaba suka shirya zuwa bauchi,tun bayan zuwan da sukayi suraj da matarsa sukazo musu basu sake zuwa bauchi ba sai a yanzu.
*********Karon farko data zauna ta hadawa abbas din kayan tafiya bauchin,a lokacin ya fita office,baisan ma ta hada din ba,sai daya dawo daga aiki,ya buda akwatin,ya jima tsugunne yana kallon luggage din, murmushi yana kubce masa,yadda ta shirya masa komai kamar shi da kansa ya shirya kayan nasa,ya girgiza kai ya miqe yana jin qaunarta tana sake ninkuwa cikin ransa,tasan buqatarsa,tasan choices dinsa tun yanzu.
Kai tsayr toilet ya shiga ya gama wanka ya fito,yana tsaye gaban mirror yana tsane ruwan wankan dake jikinsa,wanda ke fidda qamshin daddadan turaren wankan daya cakuda dana shower gel dinsa,fuskarsa yake kalla,cikin kwanakin har wani canzawa yaga yayi,kuzarinsa ya qaru,kamar yadda yaga yadan sake cikowa,fatarsa kuma ta qara haske kamar mai amfani da wani mai na daban.
Ana taba qofar ya maida idanunsa ga bakin qofar,ya kasa ya tsare yana jiran shigowarta.
Da sallama ta shigo cikin siririyar muryartan nan,sanye take da wata fara sol don smoked gown,kanta babu dankwali sai farin ribbon data matse sassalkan gashinta,fuskarta fes yau babu digon komai saina man lebe da ya sanya siraran lips dinta suketa qyalli,ba shiri ya saki comb din ya waiwayo harde da hannayensa a qirji yana qare mata kallo.
Shigar yau ta fidda asalin tushenta wato larabawa,kamar diyoyin larabawan da suka samu kyakkyawan kulawa,rigar ta karbeta,haka gyaran data yiwa gashinta wanda gaba daya wani abune da bilkisa ta koya mata kafin su tafi
"Bakison kiga uncle din yafi ji dake akan kowa?,to haka zaki dinga yi,ma sha Allah,inda nice da wannan jikin naki da wannan gashin.....ai da tuni na kori hafsat" ta fada tana qyalqyala dariya,don dama sam babu jituwa tsakaninta da hafsat din,duk da amintakar dake tsakanin mazajensu, bilkisa bata daukar raini ko wulaqanci,hakanan dama tun usul ita bata jituwa da marowacin mutum,wadan nan siffofi kuwa dasu hafsat tafi shuhura,wannan dalilin yasa matan abokansa da suke manyan mutane masu manyan muqamai iri daban daban a gwamnati suka janye jiki daga matarsa da gidansa,don babu wadda kejin dadin mu'amala da ita,idan sunzo gidan sai dole,kamar haihuwa da sauransu.
Dukka hannayensa ya bude mata,yana mata alamar ta taho,saita tsaya daga bakin qofar ta noqe kafada tana tura baki gaba,tana tuna azabar da tasha daren jiya a hannunsa
"C'mon mana baby doll,nayi alqawari fa bazan sake ba har sai kin yarda"
"Promise?" Kai ya jinjina yana murmushi sannan yace
"Amma kada ki manta,kema kinyi alqawarin zaki barni nayi komai banda wannan abun dai....." Yadda yayi maganar a narke shi kansa zaka dauka yarone dan shekara tara ko goma,abun ya bata kunya sosai,ta sanya zara zaran fararen yatsunta ta lullube fuskarta tana dariya,sannan ta fara takowa a hankali zuwa gabansa,yayin da shi kuma ya kafeta da ido yana jiran ta qaraso,bugun zuciyarsa na daduwa,yanajin kamar tana ja masa aji ne,kamar bata sauri.
Taku biyu ya qara ya cimmata a hanya,ya durqusa gabanta ya lullubeta cikin ingarman qirjinsa dake cike da muscles da gargasa suka yiwa tufa,haka qirar jikinsa yake tun asali,wannan ya qara masa interest na shiga aikin police.
Cikin abinda baifi second goma da shiga jikinsa ba dukka jikin nasa ya dauki rawa,ya cusa kansa a wuyanta yana shaqar qamshinta da har yanzu bai sake jin wani qamshi da yake burgeshi kamarsa ba,yadda bugun zuciyarsa ya qaru haka speed na fitar numfashinsa,banda girman alqawarin daya dauka babu abinda zai hanashi karyashi.
Tayi lamo a jikinsa ita kanta,tana jin yadda numfashinsa ke kewaye fatarta yana ratsata har cikin qashi,ko qwaqwaran motsi batayi ba,wani yanayi yana sauka a jikinta,har ya haqura don kansa,ya daga kansa a hankali zuwa ga fuskarta yana riqe da fuskartata a tsakanin hannuwansa
"Ki rage tsoro don Allah baby.....i love you" murmushi ta saka a kunyace tana son sake boye kanta,sai ya miqe yana cewa
"Nooo.....wannan kwalliyar na siyeta har fuskar,zan biya.....don Allah a barni na kalla" cak ya dagata ya azata saman madubin,ya jawo dressing chair ya zauna akai ya buda lotion dinsa ya fara shafawa,yana shafawar yana duban fuskarta hadi da tsokanarta ta hanyar tuna mata da abinda ya faru daren jiya.
Kukan shagwaba ta sakar masa tana bubbuga qafafunta
"Nidai Allah uncle......Allah.....Allah" dariya ta dinga cinsa,irin abinda bata taba gani ya sake haka yana dariya ba
"Shikenan.....wasa nake miki,na daina,amma bakiji bane?,nima fa na kira hajiya har bansan adadi ba,na dauka mutuwa zanyi,yarinyar nan haka kike da......" Ba tare data shirya ba ta saka hannunta ta rufe masa baki idanunta dukka a waje,tana jin kamar qasa ta tsage ta shige,sai kawai ta nemi silmiyowa daga saman madubin,cikin zafin nama ya tareta da cinyoyinta,sai gata zaune sosai a samansu
"Yarinya kin kawo kanki" ya fada a tausashe murmushi na kubce masa.
°°°°°°°°°Karfe goma na safe suka fito shi da ita,kallo daya zakayi musu kaji sunyi mugun burgeka,kamar hadin baki,shi da itan duka shigar sky blue sukayi,shi shadda ainihin gezner ya saka,ita kuma wani lace ne cotton mara nauyi.
Yau din bai nema wani dan rakiya ba,shi da kansa yayi driving nasu daga kadunan zuwa bauchi,duk da jirgi ma yaso subi,amma sai yaji yana da muradin awannin da zasuyi a tare cikin motar waje guda kafin su isa kadunan,don yasan dole kuma ya bawa hafsan lokaci kodon fita hakki,amma for now ya fara tunanin yadda zai dinga raba musu kwana duk lokacin da suka je bauchi,musamman idan zaiyi kwanakin da yafi biyu.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 85
Yau din tunda suka tashi daga kaduna basu tsaya ba,don bata jima ba bacci ya dauketa,don dama yawanci saboda ita yakan tsaya din,ya samar mata wani abun da zataci,to har suka je inda yakan tsaya din suyi sallah da sauransu tana baccinta,don haka ya wuce abinsa kai tsaye,lokaci lokaci yana waiwayawa ya kalleta,yana monitoring baccin nata.
Bata farka ba sai da suka shiga unguwarsu,tadan kalleshi,suka hada ido,yasan me takeson cewa,gidan hajiya takeson zuwa,to amma bayajin zai iya barinta,tunda duka duka kwana hudu zasuyi su juya,suya saki murmushi kawai ya shafi gefan fuskarta
"Ba kwana gidan hajiya wannan karon,i need you by my side" shuru tayi kawai,ta langabar da kanta gefe guda ba tare data ce komai ba,duk da ba haka taso ba cikin ranta.
Yana gama parking kusa da motar hafsat din data dauki qura mimi na shigowa ita dame daukota daga makaranta,ganin motar babanta ya sanyata tahowa da gudunta tana kiran sunansa,ya dagata ya rungumeta yayi kissing dinta,saita zame daga jikinsa ta koma wajen widad.
Ta yima widad din nauyi,amma saita riqe hannunta tana tsokanarta hadi dayi mata waqar 'yar makaranta,tana ta dariya,dadi ya cika yarinyar,ko banza tana samun nishadi kulawa da kuma canjin rayuwa a duk sanda baban nata da antyn nata sukazo.
Kamar sama sama take jiyo muryar mimi din tana kiran sunan baban nata,sai taja tsaki ta share,a ranta tana jin haushin yadda yarinyar keda qulafucin ubanta,tana tsoron gaba kadan ma zaiyi wahala idan batafi sonta akan uban ba,saita ci gaba da lissafin kudinta,amma kuma jin shiru bata ji motsin mimin ba,saita ajjiye wayarta da take lissafin a ciki ta miqe tana gyara daurin zaninta,ta sako kai zuwa harabar gidan.
Dai dai sanda sale ke cire kayansu a booth din motar,abbas din yana gaya masa kada yayi nisa zai kaishi kasuwa.
Cikin wani mugun mutuwar jiki ta sauke hannuwanta data tokare bakin qofa dasu
"Kanbun bal bala'in bala'i!" Bakinta ya furta duk da batasan yaushe hakan ta faru ba,daga inda take tsaye tana iya hangen widad wadda ke riqe da hannun mimi,fuskarta kwance da murmushin daya qarawa fuskar tata kyau da kuma kwarjini
"Wanne irin girma ne haka cikin wata guda kacal?" Ta tambayi kanta da kanta,har yanzu idanunta na saman fuskar widad din,ko sau daya ma bata waiwayi inda abbas din yake ba.
Takawa ta soma yi zuwa inda suke tsaye a hankali tanason sake gasgata abinda idanunta ke nuna mata,saidai duk taku daya idan tayi bugun zuciyarta sai ya qaru,kyau da yadda girma ya fara nunawa a jikin widad din suka soma bata mamaki.
Qaramar jakarta abbas ya dora mata saman mota bayan ya kulle motar
"Keda mimin banga marabarku ba" yayi maganar yana kafeta da idanu hannayensa duka biyun cikin aljihun rigarsa.
Dariya ya bata,tadan juya ido cikin irin nuna mamakin nan,saidai hakan batasan mugun kyan da ya qara mata ba
"Uncle kace na girma fa?" Har tsakiyar zuciyarsa ta aike da saqo,bayason yayi saurin bada kai tun yanzun,tunda dai nan ba kaduna bace
"Yes.....amma ga jakarki nan,ki dauka sai mu gani" ya fada tsadajjen murmushin nan nasa yana fita daga fuskarsa.
"Uncle itama wannan din da nauyi don Allah....." Widad ta fada cikin shagwabar data saba yi masa
"Ya salam" ya fada yana miqa hannu hadi da dauke jakar,yayin da hafsat taji tana shirin faduwa,sai takai hannu tana neman abinda zata riqe gudun faduwa,hannunta ya sauka kan kyakkyawar luggage din widad guda daya da tayi saura sale bai dauke ba.
Hannunta ta janye,mamaki yana sake kasheta,gata kusa da wajen amma cikinsu ba wanda yama lura da wanzuwarta a wajen,wani tunani yazo mata,tayi qoqarin saita kanta ta hanyar yin gyaran murya kadan,abinda yasa duk suka waiwayo
"Sannu da zuwa,saukar yaushe?" Tayi maganar tana tsare gida hadi dayin kicin kicin da fuska,sannan ta miqa hannu tana son karbar jakar widad dake hannunsa a zuwan tasa ce
"Yanzu ne,ko kayanma ba'a gama daukewa ba"
"Fitar wuri kukayi kenan" ta sake fada tanason calling attention dinsa,sai ya dan gyada kai,abun nata nayau yana dan bashi mamaki
"Ina wuni" widad ta fada ba tare data dubi sashenta ba,haka kawai takejin wani abu mara dadi yana dan taba zuciyarta,taji kuma.ba zata iya gaidata yadda ta saba ba,sai hafsat din ta waiwaya tana kallonta,sai a lokacin ta sake ganinta sosai
"Oh..... amarya lafiya lau" can qasan ranta tana dan mamakin yanayin data gaisheta dashi,ba haka ta saba gaisheta ba dashi,ta saba ta gaisheta tana fara'a bayan ta rusuna mata,sa'an nan idan tayi kamar bata ji ba sai ta sake maimaitawa
"Ba jakata bace ta qanwarki ce" ya fada yana kulle motar sanda yaga tana nufar sashensa da jakar
"Oh, okay" ta fada tana dawowa baya inda widad ke tsaye da mimi,kai tsaye ta miqa mata jakar,don dama abinda takeso kenan ta karba kayarta.
Ba tare da nufin komai ba ta kalli abbas din a shagwabe
"Allah uncle da nauyi,kuma kace zaka kaimin fa"
"Bance na fasa ba ai" ya fada yana miqawa hafsat hannunsa,kamar sakarya ta sakar masa jakar,xallar mamaki yana cikata,ta bishi d kallo sanda yake cewa
"Muje na ajjiye miki"
Su ukun suka juya zuwa sassanta,mijinta..... diyarta ta bisu da kallo,me yake shirin faruwa ne wai?,ko kuma tace meye ne ya farun?.
Kamar wadda aka tsikara saita kasa tsaiwa,ta daga qafarta da hanzari tabi bayansu,ta cimmasu ya karba keys din ya saka yana bude mata qofar sassan nata,sai ya waiwayo yana duban hafsat din da tayi tsaye a bayansu,ta kasa ta tsare tana dubansu,ya dauke kai ya qarasa buda qofar ya matsa mata gefe ta sanya kai ta shige ita da mimi da suketa surutunsu ko a jikinsu.
Cikin falon ya ajjiye mata jakar,sannan ya juya ya fice daga falon yana tsokanar mimi,a sannan hafsat din tana qifar parlor din bata shigo ba,saidai tana jin zuciyarta na mata wani iri,ta kasa tuna komai bare tayi tunanin me ya kamata tayi,jikinta yayi mugun sanyi,zuciyarta kuma tana bata akwai wani abu.
Kallonta ya sakeyi sanda ya fito,tana tsaye qyam kamar wadda aka bawa gadin qofar falon,yadan kalleta sai kuma ya wuce,ta taka ta bishi a baya,zuciyarta kamar sata fito daga qirjinta,tanason masa qorafi to amma kuma tace masa meye?,haka taci gaba da binsa a baya har zuwa sashen nasa.
Sanda ya bude waiwayowa yayi yana kallonta,qura fal sashen,wannan abu yana masa ciwo,baisan sai yaushe zai fara dawowa yana samun sassan nasa a tsaftace ba,suna hada ido ta kauda kai,tasan qorafi yakeson yi,amma ba zata bashi dama ba,zata gyara tunda ga widad tazo,wasu ayyukan zasu ragan mata ai,sai ta karba jakarsa ta wuce bedroom dinsa da ita.
*_BAYAN AWA BIYU_*
Yana zaune saman kujera take gyaran falon,tana aikin tana gyara daurin zaninta dake kwancewa,fuskarta sam babu walwala,tunani ne cunkushe fal a ranta.
Nawwara na zaune saman doguwar kujerar da yake kai,yanata bare mata chocolate tana sha tana masa surutu,lokaci bayan lokaci yakan daga kai ya dubeta,tun daga tsefaffen gashinta da yayi cibiri cibiri har zuwa qafafunta dake cike da kaushi,babu digo lalle ko kadan bare su samu arziqin suturta kaushin qafartata,brassiere dinta ta saki sosai,don kana iya hangota ta gadon bayanta.
Ya lumshe idon takaici yana cikashi,duk wani abu da diya mace zaga gyara a jikinta ya bada sha'awa hafsat din ta kauda shi da kanta da mugun qazanta da rashin sanin ciwon kanta,tattausan qshin widad ya tuna,babu sanda zata giftashi bakaji tashinsa ba daga jikinta,sabanin hafsat din da saidai yaji wani na daban bawai qamshi ba.
Ta gama gyaran tana jin tayi wani gagarumin aikin azo a gani,gaba daya qugunta har ya riqe,saita taka zuwa qofar fita,tanason kiran widad din tazo ta gyara mata kitchen hade da kayan miya zata dora girki,sannan ta kama sauran gyaran falonta zuwa sassan part din nata
"Zo mana" ya kira hafsat din yana sauke lallausar qafarsa a qasa tsigar jikinsa nadan xubawa,haka kawai yake ji gyaran data yiwa sassan nasa bai gamsar dashi ba,saboda ya riga ya saba.....muddin widad din tayi gyara to sai ka rantse da Allah wani engine akasa aka kauda qazantar waje.
Dan jim tayi don ta qagu ta kira yarinyar,tanason jin abubuwa da yawa daga bakinta ko zata samu haske kan zarginta,amma ganin ya kafeta da idanu yasa ta kasa bashi uzurin cewa tana zuwa din,ta juyo ta dawo ta samu waje ta zauna
"Meye da meye a kayan amfaninki ya qare?" Ya tambayeta yana hada hankalinsa sosai a kanta with seriousness,don shikam Allah ya sani,bayason ya zalunceta,amma muddin za'a ci gaba da tafiya a haka komai zai iya faruwa,zuciyarsa zata gaza daurewa hada waje da ita.
Sosai ta kalleshi,saita girgiza kai
"Babu komai" shuru yadanyi yana jinjina amsarta,sai ya miqe ya kama hannun nawwara
"Ban yarda ba,muje na gani", kamar zata fasa kuka haka ta miqe,shigarsa sassanta tasan ba abinda zai dadeta dashi wani bacin rai,bata da damar musu,haka ta miqe tabi bayansa.
Suna fitowa daga sashen sukaci karo da wata iska mai qamshi dake kadawa dukka ilahirin harabar gidan,yaja iskar sosai cikin hunhunsa ya fesar,a wajen mutum daya yakejin wannan qamshin,kuma ko yanzun ya tabbatar yana fitowa ne daga sassanta,kewarta yaji ta saukar masa,tamkar sun dauki wani lokaci mai tsaho ne basu tare,yayin da hafsat ta dinga shaqar qamshin itama,tana tunanin daga ina yake haka?,da bata gane ba saita watsar,ta raya a ranta qilan daga maqota ne.
Suna ratsa falon yana qare masa kallo,yadda dukka yabi ya haukace,harda kayan wanki zube saman kujera,ko meye ya kawo.kayan wanki falo oho,suna isa bedroom dinta ta qarasa tsinkewa da al'amarinta,anya hafsat bata da ciwon qazanta?,wani lafiyayyen zani da bashi bashi ne yake fitowa daga bandakinta yana baiwa dakin wani irin yanayi mara dadi,katifarta gayanta ce kawai,babu zancan bedsheet akai,dukka qofofin wardrobe din nata a bude suke hanhai,ga kaya wasu a qasa wasu a ciki.
Iska ya shaqa ya fesar yana lissafa yadda zai kutsa kai bandakin,yaja iska sosai cikin hunhunsa sannan ya saka kai tana biye dashi,ranta dukka a bace,inda ya bari widad ta gama gyarawa ai kome zai shigo yayi sai yayi.
Da daya da daya yake bude kowacce locker dake bandakin,dukka kayan da yake siya da sunanta na gyara kama daga shaving cream,shower gel, mouth fresh,relaxers,hair mist hand and foot cream dukka gasu nan jibge,wasu har ya manta daya siyesu ma saboda tsabar dadewa da sukayi,da ya saka hannu ya dauko da yawansu ma sun gaji da zama sun bushe a ciki,wasu sunyi expire,haka ya dinga tarkatosu gaba daya ya zuba a wani qaramin bucket ya fito dasu daga bandakin.
A bedroom din ya tsaya,ya sake wangale qofofin wardrobe din nata yana duba kayanta daya bayan daya,yanaso yaga ta inda ya gaza,yanason yaga ko daga shine,saidai dukka sutturunta suna nan danqare,ya buda bangaren kayan baccinta dake jibge masu uban yawa,kasancewarsa ma'abocin son nighties baya rabo da siyansu komai tsadarsu,su dinma suna nan kar kar dasu,wasu ma a cikin ledarsu bata bude ba,sai ya juyo yana dubanta,idanunsa fal bacin rai da kuma soma gajiya da halayenta
"Ta ina ne na gaza hafsat?,me kikeso nayi miki ne?,wanne hakki naki ne ban sauke ba?" Yaune kadai ta danji nauyi,amma girman kai da qi fadi yasa taqi hari hakan ya fito,sai ta bata ranta kadan tana cewa
"Nifa bance ka gaza ba,sannan kuma nima ya kamata ana dubawa anamin uzuri,aidai kasan ba haka ka auroni ba,kuma ba haka nakeyi ba tun farko ba,yanxun yarane da hidimar gida ta yimin yawa" ransa ya baci sosai,a qalla tunda taga laifinta quru quru ko accepting ai ya kamata tayi ko?.
"Ina yaran suke?,ni ban gansu ba,yara qwaya biyu kacal?" Ido ta fidda
"Aikai raina hidimarsu kekeyi?"
"Eh na raina,tunda koni ija iya hidimarsu,meye bana iya musu?" Baki ta tabe tana riqe qugunta,shikam ya fiya jidali da daga hankali,batasan meye damuwarsa ba da rayuwarta,yanzun nan ta gama gyaran sashensa ko hutawa batayi daga wahalar aikin ba ya tasota a gaba yana son tozartata.
Wani bacin rai dake taso masa ya hadiye,cikin danne fushinsa yace
"Am tired.....na gaji da wannan halayen naki hafsat,anzo gabar da dole ki gyara,bazan ci gaba da lamuntar haka ba" maganarsa ta farki zuciyarta ta kawo mata fassararta,zuciyarta na sake qarfafa mata gwiwa ba shakka akwai wata a qasa,bai taba gaya mata wannan kalmar ba sai yanzu,anya yarinyar can kuwa bata fara zamewa rayuwarta barazana ba
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 86
"Ka gaji?,ka gaji dani kenan kake nufi?,saika dauki mataki ai k......." Kafin ta qarasa ta daka mata tsawa,dukkan yadda yakeson ya taushi kansa haqurinsa ya gaza
"Kada ki gayamin maganar banza da wofi,kin dauka ina tsoronki ne da bazan iya daukan mataki a kanki ba?,to ki shiga hankalinki wallahi,saboda idan nace hukuntaki zanyi abun bazai miki da kyau ba" yana kaiwa nan yayi gaba abinda har yana yin ball da botikin daya ciko da tarkacen kaya masu tsada daya wulaqantar.
Da kallo ta bishi zuciyarta na suya,mamaki kuma ya cikata,wai yau ita abbas yakewa haka?,sai zuciyarta ta karye qafafunta sukayi sanyi,hawaye ya fara sauka daga idonta,ta koma ta zauna gefan gadonta tana share hawaye.
Zuciyarsa na zafafe sosai sanda ya baro mata sashen,ya isa sashensa kai tsaye ya wuce bedroom dinsa,wannan karon bazai qyaleta ba,ko yaya zaiyi magana da wani magabacinta ko za'a samu sassaucin wani abu,yana tsoron faruwar abubuwa da yawa a nan gaba daga gareshi,baisan me zamansu zai zama ba a gaba,ga yara mata da yake dasu da yasan dolen dole wataran gidan wani zasu je,uwa uba kuma yanayi na lafiya,ta yaya muhalli babu cikakkiyar tsafta za'a samu ingantacciyar lafiya?.
Saman sofa bed dinsa ya zauna yayi waya ta a qalla mintuna goma,koda ya gama wayar riqeta yayi a hannunsa yana jin banbarakwai babu dadi,yau ya aikata abinda bai taba aikatawa ba wato kai qarar hafsat din, tsahon zamansu tare na wasu shekaru.
Ta bangaren widad tuni ta gama tsaftace sassanta, hankalinta bai kwanta ba saida ko ina ya dauki qamshi,ta fiddawa mimi uniform dinta ta sake mata wanka,akwai ragowar kayanta a sassan tun wancan zuwan da tayi,ta saka mata su,saita tsaya tana kallonta.
Yarinyar kyakkyawace,kawai rashin tsafta da gyara ne yake dakushe duk wani kyau nata
"Anty ki kaini wajen daddy yaga kwalliyata,dama inata cewa mommy tayimin tana cewa bata da lokacin wannan" murmushi ta sake
"Wanka zanyi nima,ki bari idan nayi saina kaiki" marairaicewa tayi
"Don Allah anty,nidai yanzu" ba yadda zatayi,dole haka ta dora qaramin mayafinta ta kama hannun mimin suka fice tana cewa
"Duk chocolate din da daddyn ya baki kin yarda zamu raba?" Tana dariya ta gyada mata kai.
Babu shi a parlor din sanda suka shiga,saita cewa mimi
"Bari na duba shi a daki" ta gyada kai yarinyar ta zauna saman kujera cikin zaquwa.
A nutse ta tura qofar dakin,daidai lokacin da yake zaune cikin sofa bed din,ya kwantar da bayansa sosai a jikin sofa din,idanunsa da suka rusuna ya daga yana kallon fuskarta sanda ta tsaya daga bakin qofar tana riqe da handle din tana kallonsa kamar yadda shima.ya zuba mata ido,duk sai taga kamar ya sauya daga zuwansu bauchin.
Hannunsa ya daga yayi mata nuni da tazo,ta saki qofar ta soma takawa a hankali kamar mai tausayin qasa,ya zuba mata ido yana jin nutsuwa tun gabanin ta iso gareshi.
Hannunsa ya bata sanda ta iso kusa dashi,ta saka nata hannun a ciki,sai ya fincikota cikin jikinsa a tausashe,ya mata kyakkyawan masauki a qirjinsa,yasa labbansa masu taushi yayi kissing goshinta,sai ta dan saki ajiyar zuciya
"Mimi na rako zata nuna maka kwalliyarta" ta fada a shagwabe kamar yadda ta saba yi masa magana,birkitota kadan yayi yana kallon fuskarta
"Ina taki kwalliyar.....ita tafi muhimmanci" kunya ta kamata ta sauke fuskarta a qirjinsa tana shaqar daddadan qamshinsa
"Banfa yi wanka ba,aiki na gama yi,gurin duk yayi qura" girarsa ya dage sama duka biyun
"Iyyee,abun 'yar haka ne?,shine kika share iya wajenki banda nawa ko?" Kai ta girgiza da sauri tana 'yar dariya
"Ba haka bane uncle,nasan mummy hafsat ta gyara maka fa" kai kawai ya jinjina
"Yanzu yaushe ne za'a yimin kwalliyar,ta musamman nakeso,i will pay" dariya ta saki,tanajin dadin yadda yake yaba komai nata
"Za'a yi maka uncle" ta furta tana rufe fuskarta da hannunta
"That's my baby doll" shima ya amsa mata yana jan dogon hancinta
"Muje naga mimi' ya sake fada yana dagata a jikinsa,gaba daya sai ya rasa kaso hamsin na bacin ransa, shigowarta kawai ya tafi da komai,ta miqe ya sanya hannunsa cikin nata ya riqe gam suka fara takowa xuwa falon.
Babu irin abinda bata saqa a ranta ba sanda take tsaka da kukan,sai datayi me isarta sannan ta dauraye fuskarta,bata da wata mafita,komai ya tsaya mata cak,batasan me ya kamata tayi ba,saita dauki wayarta ta soma lalubar number anty ummee ko xata samu wasu shawarwari.
Abun takaicin tana kira taji suna sanar mata kudinta ya qare,dama already taci bashin mtn na kusan dubu uku,duk kuwa da cewa duk wata sai abbas din ya saka mata kudin credit ta account dinta bama credit din ba,taja tsaki ta sauka ta koma bank dinta ta sakawa layin bashin da suke binta,bonus din da suka bata tayi amfani dashi ta kira anty ummee din.
Shuru tayi har ta gama bayaninta sannan ta dora
"Ina tsoron kada yarinyar nan ta fara shiga rayuwarsa anty ummee,ni zuwan nan da sukayi ma sai naga kamar ta fara budewa ta zama mace,harda kai mata kayanta sashenta fa,duk da na sanshi bashi da girman kan wannan wa iyalinsa,amma yarinyar ai bata cancanci wannan kulawar ba" baki anty ummee ta tabe,tana jin kamar ta jawo hafsat din tayita jibga
"Nidai da farko saidai nayi miki addu'ar Allah ya yaye miki wannan baqar qazantar,bansan irin ribar da kike samu da ita ba" maganar ta bata ran hafsat,don duk yadda kake da ita kace mata qazama ce to sai an ganku a rana
"Meye haka anty ummee?,nifa ba akan wannan na nemi shawararki ba,tunda dai ni ina iya bakin qoqarina,abubuwane sukeyimin yawa,kuma nayi nayi ya daukon mai aiki yaqi,to bazan kashe kaina ba" kai anty ummeen ta jinjina,gwara ta bita a yadda suka soma,kada ta yiwa kanta rasa rasa
"Ke gaskiya ce baki so,na daina kuma gaya miki,amma indai kansa kike san shawowa dole kidan gyara inda idanunsa zasu ganki tsaf,tunda da tsafta aka jarabceshi ke kuma ea qazanta.....muddin kinason ganin dai dai dole ki sauko daga ra'ayinsa kibi nasa ko yaya ne,koni da kikaga ina yadda nakeso,wasu abubuwan ra'ayinsa nake bi kafin na murda idan naga ya biyu yadda nakeso na koma kan nawa ra'ayin" sun dan dauki lokaci suna fafatawa ma kafin hafsat ta fahimci abinda anty ummee take nufi,dole ta yarda tadanyi gyara a ranar ko zata cimma manufofinta ta ruwan sanyi.
Suna gama wayar ta miqe tana tunanin ta inda zata fara,sai ta yanke ta shiga da kanta ta kira widad din,can qasan ranta tana mamakin yadda ko motsinta bata sake ji ba bare ta shigo taga abinda ya kamata tayi mata.
Tun bata qarasa ba taga sassan nata a kulle,ta juya cike da mamakin ina taje?,ko gidan hajiyan da aka rufe babinsa ta koma?,harta dawo da baya.....amma tana kallon sashen abbas din akalar tunaninta ya canza,saita nufi can,duk da zuciyarta na gaya mata bata ciki,to amma mafi rinjaye na tunaninta yana rinjayarta ga zuwa sashen nasa.
Tana buda qofar falon abbas dake riqe da hannun widad yana bude ta bedroom din,idanunsa na kallon gefansa yana magana da widad din,cak hafsat din ta tsaya kamar an dasata,qirjinta yana harbawa,ta zuba masa ido tana son ganin waye yake biye dashi.
Wani mugun ashar ne taji ya taso mata,saidai abinda yazo ya tsaya mata a wuya ya hana kowanne kalma fita daga bakinta,widad fa take gani,widad yau a dakin mijinta?,riqe da hannunsa?,baqar zuciya da kuma fushin dake cin zuciyarta ya sanyata cikin zafin nama ta harbo zuwa cikin falon.
Takunta yaja hankalinsa sanda yake tsokanar mimi tayi kyau,ya tashi daga durquson da yayi,ya zuba mata idanu,don kallo daya yayi mata zuciyarsa ta bashi akwai wani abu na daban.
Kafin ta qaraso idanunsu suka sarqe cikin na juna,wani irin baiwar idanu gareshi masu tsananin kwarjini,abinda yayi mata tasiri kenan,kallonsa ya ratsa zuciyarta ya karya duk wani zafi data debo da kima qissime qissime da zuciyarta keyi mata na irin abinda zata aiwatar,saurin data kwaso ya canza zuwa nawa.
Kallon kallo suka ci gaba da yiwa juna,sai taji zuciyarta kamar zata fashe idan bata ce komai ba,a sannan ta tuna ita din me laifi ce,ta kuma tuna gargadin da anty ummee tayi mata
"Kissa saida kwantar da kai"maganar data gaya mata ta qarshe kenan
"Nace me za'a dafa maka?" Ta maye gurbin dukka wani bala'i daje qasan zuciyarta da wannan tambayar,tambayar da yaji sam bata dace da yanayin da ya ganta a ciki ba,to amma koda ta tambaya dinne da gaske,yanajin ya zuwa yanzu ya kamata ya nuna mata fushinsa,saiya dauke idonsa daga kanta ya maida kan 'yarsa
"Bana buqatar komai" ya amsa mata a dake yana duqawa yana gyarawa mimi kwalar rigarta.
Wasu irin hawaye ne masu dumi suka cika mata idanu,ta zubawa widad ido,wadda sam idanunta baya wajen,ta tattareshi akan tv,haka kawai takejin wani irin itama cikin ranta, yanayin gidan a yau ya sake mata rashin dadi,ta tabbatar a lokaci irin wannan a kaduna ita dashi din suna kitchen tare suna girki,ko suna backyard dinsu suna wankin undies,ko suna karatu ko kallo.
Qwafa taja can qasan ranta tana danne hawayen,batason ta zubdashi a gaban widad din,ta juya tana barin falon,kamar zatayi bindiga ta fashe haka takejin kanta,nadama da dana sanin ma tambayarsa me za'a girka din ya cika Zuciyarta,gashi ya yarfata a gaban qaramar yarinyar da a haife ta haifeta.
Hanyar data fita yabi da kallo,yaja dan qaramin tsaki sannan ya koma ya zauna kusa da mimi
"Hadamin coffee ko black tea" ya bata umarni yanason danne shima nasa fushin,tadan kalleshi da wani irin yanayi,cikin zuciyarta takejin akwai wani abu dake damunsa,don ba haka yake ba,kamar zatayi magana saita fasa,ta miqe tana nufar qofa.
Tana sanya qafarta a falonta taji an biyo bayanta,ta tsorata sosai,taja da baya tana dubanta,sai data gane hafsat dince saita saki ajiyar zuciya tana lumshe idanunta hadi da budesu tana kallonta.
Wani irin kallo take bin widad dashi,tana jin kamar ta fincikota ta rufeta da duka,yarinya qarama amma tana neman dagula mata lissafi,tanaji a jiki da zuciyarta abbas ya sake canzawa ne sosai ta sanadin aurenta,a baya idan ya fiya cika masa ciki tattarawa yake ya koma inda ya fito,sanda suna gari guda kuma saidai ya tsiri zaman gidan hajiya,ko kadan bata damuwa,saboda tasam ba wani wajen yaje ba,kuma shi din ba mai kula kulen mata bane,asalima sam basa cikin tsarinsa,don haka ba kasafai ta fiya damuwa,idan ya qare fushinsa zai dawo yaci gaba daci abincinsa ko yaya ta dafa kuwa,idan yaji bai masa bama zai shiga kitchen ya dafa da kansa
(Hmmmm,duk a lokacin bata taba kawowa miskilanci bane irin na mijinta,ta aza hakan akan babu yadda zaiyi da itane,kamar dole yayi duka abinda yakeyi din).
"Uban me kika shiga yi dakin abban mimi" kamar daga sama furucin yazowa widad,mamaki ya kamata,for now dai ta fahimci matsayinta daya da hafsat din,ta kuma fahimci me kalmar aure take nufi,indai haka ne bataga muhallin wannan tambayar ba,duka wannan ba damuwarta bane,abinda yafi bata mata rai kalmar UBAN WA data fada,wanda dai dai yake da zagi a wajenta
"Dake nake!" Ta sake fada cikin tsawa kamar zata kai mata duka,amma ga mamakinta sai taga widad din ta tsireta da manyan idanunta
"Ai ba haramun bane tunda kema naga kina shiga" ta fada a sakalce abunta tana dubanta.
Zallar mamaki ya saukowa hafsat din,tayi sakato tana kallonta
"Ni kike gayawa wannan maganar?" Ta fadi tana jin wani zafi har cikin ranta
"Me nace mommy?" Ta tambayeta kanta tsaye,a karo.na biyu ta sake shiga mamaki,anya kuwa?,anya abinda take tunani bai faru ba?,yaushe yarinyar tabfara fahimtar abubuwa haka?.,da tayi wani qaramin tunani sai tabar wancan maganar tace
"Ki wuce kije kiyi aikinki,suna can suna jiranki"
"Tom,bari na dafawa uncle tea" tea?,har tea yake sakata dafa masa saboda zallar jawo mata raini?,wanne girki ta iya da zai buqaci tea daga wajenta
"Ni kike.maidawa magana widad?" Juyowa tayi tana kallon hafsat din,ita gana daya sai taji ta sire mata daga zuciyarta,tunda ta fahimci akwai qaryayyaki da yawa data taba gaya mata,a dabi'arta kaifi daya ce,ko meye za'a yi mata bata qarya haka ta taso tun quruciyar ta,dalilin da ya sanya ta sake shan wahala kenan sosai a wajen 'yan uwanta da cousins dinta
"Me nayi mommy?,aikinsa shine gaba da kowanne aiki fa,ba kyau miji ya saka kaqi" zuwa lokacin gaba daya hafsat din ta gama sarewa,lallai qaryarta ta fara qarewa,tund har yarinyar ta fara sanin ma'anar kalmar miji,ta kuma fara tantance bin umarnin wata a gaba da nata umarnin,basu taba musayar magana da ita ba koda da sau daya,amma yau da ita suke musu?,tana ce mata ga yadda za'a yi itama kuma tana fadin nata,ah wannan babbar musifa da babbar guguwar canji ce ta tunkarota,wadda take buqatar zama na musamamn da shawarwari don sanin meyenmatakin dauka na gaba,daga wannan sai bata sake cewa komai ba,ta juya tana barin wajen tana jin kamar duniyarta tazo qarshe gaba daya.
Tsakin da batasan yazo bakinta ba shi ta fitar,tadan harari hanyar data wuce din
"Kawai kawai ni...."sai kuma tayi shuru tana quna quni,ita tunda taga yadda taketa wani tsare mata uncle dinta da kallo taji tana jin haushinta,bata taba ma kula da haka take zuba masa ido ba sai yau din,haka ta shiga kitchen din,ta fara duba kayan hada tea din da tasan yana matuqar so ta fara hada masa,lokaci lokaci tana dan jan tsaki.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 87
Wayar anty ummee ta sake kira cikin mugun rudani da tashin hankali tafara gaya mata yadda ake ciki,ita kanta abun ya bata mamaki sosai
"Wannan maganar bata waya bace,ki daure ki cinye komai kiyi masa duk abinda yakeso,zuwa jibi in sha Allah zamu dawo daga bikin 'yar yayar babansu khadija(mijinta),gaata in sha Allah da wurwuri zaki ganni,idan ban samu fita bama zan miki magana saiki shigo mu hadu.
Wannan maganar ta tayar da hankalin hafsat din sosai,ganin jibi take tayi mata mugu mugun nisa
"Don Allah ki katse bikin nan anty ummee,kizo mu samu mafita,ina cikin mugu yanayi,ji nake zuciyata ba zata iya dauka ba,kamar zata fashe nakejinta"
"Indai bakiyi juriyar dana gaya miki ba kikace zakibi son zuciyarki to komai zai lalace miki ne" abinda tace da ita kenan.
Tayita kwatanta yadda zata fuskanceshi da fuskar komai ba komai ba amma ta kasa,kwata kwata zuciyarta bata da irin wannan juriyar da jarumtar irin ta anty ummee din,ta gama cusguna ma rayuwarta kuma tayi masa abinda yakeso?,babu abinda idanunta ke hango mata sai sanda suke fitowa daga dakin,yau hannun abbas dinta ne cikin na wata macen?,turakarsa da duk duniya ita kadai tasan kalarta yau sai ga wata mitsitsiyar yarinya ta fito daga ciki?,wa yasan ma me suka aikata suka ajiye mata yarinya a falo?.
Duk yadda ta juya ta kasa aiwatar da komai,kawai saita kulle kanta a dakin ita kadai,saqa da warwara ba irin wadda batayi ba akan yadda zata bullowa al'amarin,kota kan yaranta ba ma bata bi,suma yaran dawowar widad yasa basu sake nemanta ba,suna can wajenta,wadda bayan ta gama hada masa tea din ta koma yin wanka ta wuce dasu,ta sake yiwa nawwaran ma wanka,don ita kanta ba cikakkiyar tsafta a jikinta.
Zamansa a sassan nasa sai zuciyarsa ta kasa jurewa rashin ganin gilmawarta,ta saba masa da qamshinta,girkinta da a yanzu duk duniya babu girkin da yakejin taste dinsa idan ka dauke na hajiyarsa bayan nata,ya dinga qoqarin danne xuciyarsa,don a qa'ida awannin na hafsat ne,bayason kuma ya fara sabawa jiki da zuciyarsa da aikata wani abu da zai jagoranceshi ga zamowa kasashen namiji mara adalci,dole yayi wanka ya shirya ya biya ta sashenta don a qalla cikin su biyun ya kamata wata a ciki tasan inda zashi kada a nemeshi,hafsat ya dace ya soma fadawa,amma yaci alwashin bazai shiga sashenta ba,zai mata horon da zata sake shiga hankalinta.
Tana tsakiyar su mimi din suna assignment,ta dora abinci a kitchen,gown ce a jikinta na chiffon material butter color da zanen green flowers qananu
"Zan fita amma bazan dade ba zan dawo" ya furta jikinsa na amsawa,don daga inda yake tsayen yana iya jiyo qamshinta mai dadi,ga kuma qamshin da sashen kansa yakeyi wanda ya cukude da qamshin girkinta.
Marairaice fuska tayi tana kallonsa da farare sol din idanuwanta
"Uncle.....don Allah kada ka dade" murmushi ya subuce masa, ya jinjina kai yana kallo labbanta
"In sha Allah" kusan a tare sukayi masa a dawo lafiya,har ya isa bakin qofa yaji bazai iya wucewa ba,ta gama kashe masa jiki,yana qishirwar lausasan labban nan nata,sai yadan waiwayo ya mata sign din tazo.
Miqewa tayi tana sakin murmushi,tana kaiwa bakin qofar ya jawota cikin labule yadda yaran ba zasu iya hangosu ba,baiyi wata wata ba ya mannata da qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya,ya dago fuskarta yana dubanta,idanunsu suka sarqe waje daya,sai suka hau yiwa juna kallon kallo,cikin zafin nama ya hade bakinsu waje daya.
Da qyar yayi controlling din kansa,ya zareta daga jikinsa yana sake kissing goshinta
"Allah yayi miki albarka,take care" ya fada yana ficewa a hankali,sai ta kasa motsawa ta bishi da kallo,yayin da wani lafiyayyen murmushi ya dinga fita daga fuskarsa,yana ji a jikinsa kallonsa take,wannan dalilin ya hanashi waiwayo,don ya bata damar kallon nasa sosai yadda ranta yakeso,ya hangi wasu abubuwa sosai daga zuciyarta,wanda ba lallai ita din ta fahimci shigarsa rayuwarta ba.
Sai data daidaita kanta sannan ta koma cikin yaran tana tana labbanta da yatsunta, batasan me yasa duk sanda yayi mata irin wannan abun take tsintar kanta a wani yanayi ba
"Kema kin zama yar iska ko?" Ta tambayi kanta da kanta,sai ta bushe da dariya ita kadai,har yaran suna kallonta dukansu,mimi ta tambaya
"Mene ne anty" dan zubawa yarinyar ido tayi har yanxu murmushin dake saman fuskar ta bai bace ba,sai ta kama kumatunta
"Babu komai mimi,kawai inason daddy uncle...." Ta furta maganar ba tare data shirya ba.
Farinciki ya kama yarinyar,ta washe bakinta tana dariya
"Shima yace yana sonki" ido ta fidda
"Yaushe?"
" rannan dinnan" murmushi ta kuma saki,tana juya maganar yarinyar a ranta,saita miqa mata pencil din sukaci gaba da rubutun,zuciyarta wasai cike da tunaninsa,abinda bata taba tsintar kanta a ciki ba akan wani halitta.
Dole saboda yunwar cikinta ta fito ta shiga kitchen,ta fara tunanin me ma zata dafa musu?taja tsaki yafi a qirga,ta rasa dame zata fara,saita matsa ta window gaban window din kitchen din nata ta zugeshi saboda iska ta shigo.
Tana gama budewar iska me dadi mai hade da wani hadadden qamshin abinci ya cika mata ciki,ta hadiyi yawu da kyau tana tunanin ta inda qamshi kala kala yau yake cika mata gida,tabi wajen da kallo tana qaramin nazari,sai ganinta ya tuqe a sassan widad.
Gabanta yadan fadi,kada ya zamana yarinyar ke girkin dake bada irin wannan aroma din,kai ta kada,ko jikinta kunne ne ba zata yadda da haka ba,yarinyar da aka kawo ko ruwan zafi bata iya dafawa ba,yaushe akayi dare har garin zai waye ta iya girki haka?.
Tun tana aikin tana basarwa har ta gaza,sai ta ajjiye abinda takeyi ta juyo ta baro sassan nata ta doshi sashen widad din,tana kusantar part din iska da kums hancinta suna tabbatar mata daga can ne qamshin abincin ke fitowa,sai tayi tsaye daga bakin qofa yatsanta a baki,ya akayi haka ta faru?,bata da abinda zatayi,dole haka ta juya ta koma gwiwa a sanyaye,amma kuma ta cika da mamaki tare dason gano yadda akayi haka ta faru.
Tana girkin amma gaba daya tunani ya cika mata kanta,ranta a jagule yake,bata qaunar ganin wani ci gaba sauyi ko walwalar rayuwa daga yarinyar gaba daya.
Sallama taji da muryar mimi,a mamakance ta waiwayo tana kallon yarinyar
"Mommy kizo inji daddy"
"Ke.....waye ya koya miki sallama?" Daria ta saki cikin jin dadi
"Anty amarya ce,tace duk inda za'a shiga sai anyi sallama,ba kyau shiga guri idan ba'a yi sallama ba" haushi takaici da kuma baqinciki suka cikata,wanne irin sanabe ne haka za'a fito mata dashi akan diyarta,sai taha qwafa
"Shi kuma me zanyi masa,har ya gama fushin nasa ne?" Ta fada tana kallon yarinyar kamar itace zata bata amsa,ita dai batace komai ba,sai taja tsaki ta kashe gas din ta fito zuwa dakin baqi da tace yana can.
Tunda tayi sallama taga kawunta gabanta yayi mummunar faduwa,saboda tasan cewa lallai ruwa baya tsami banza,ta saci kallon abbas dake zaune daura da kawun nata suna taba hira,wadda duka akan abinda ya shafi security na qasa ne,baiko dubi sashenta ba,haka ta daga kai ta isa ga kawun nata ta zube tana gaidashi kanta a qasa.
Shuru tayi ta nutsu sosai kamar da gaske tana sauraron kawun nata sanda yake mata fadan tsafta,iya abinda yafi abbas din yakai qorafinta akai kenan,amma ji take gaba daya ya gama tozartata ya wulaqantata,hausawa sukance wai wanzami bayason jarfa.
"Nifa kawu kawai baya ganin qoqarina ne,amma ai inayin duk abinda naga zan iya bakin gwargwado"
"Oh.....qarya yake miki kenan?,nace qarya yake miki,to ko ni da nake namiji ai gashi ina gani" ya fada yana nuna dakin baqin da ya hada qura sosai,sai kawai ta saki kukan takaici,kawun ya qara da cewa
"Duk qoqarin da abbas yakeyi babu wanda bai san dashi ba,don bai taba kawo qararki ba tsahon zamanku tare sai yau,kuma bazai taba tiwuwa ace shekarun duka da kuka kwashe ke dashi baki taba yi masa laifi ba,saidai kece d baki gani"
"Nima kawu ai yana yimin"
"Rufen baki,me ya hanaki ki fada" ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,yayi mata fada sosai ya kuma tursasata ta bashi haquri.
Kamar wadda aka cusawa tsumma a baki kanta a qasa haka ta furta kayi haquri,gaba daya ma abun sai ya jishi banbarakwai,don zaiyi mugun mugun wahala kaji kalmar ban haquri daga bakinta,daga qarshe dukansu kawun ya hadasu yayi musu nasiha sannan ya wuce gida,abbas ya fita ya rakashi har bakin mota sannan yayi masa alkhairi,duk da cewa da qyar ya karba.
Daya dawo tana ta kumbure kumburenta sai ya watsar yayi kaman bai gani ba,ya tattara ya fita sallah,bai kuma dawo ba sai bayan isha'i,don ya tsaya ya saurari karatun da ake a masallacin duk bayan sallan isha'i zuwa qarfe tara na dare.
Silk sleeping dress ce a jikinta baby pink mai gajeran hannun net,duka tsahonta iya qaurinta yake,ta lullube kanta da wata qaramar hular net mahadin kayan,ta cusa duka gashinta aciki,idan kayi mata kallon farko saika dauka batasan ko zo na kasheka da hausa ba,dakin babu wadatar haske sosai,sai na screen din wayarta dake hannunta.
Gaba daya bata jin dadin chart din da takeyi,zuciyarta duka babu dadi,wani irin kewarsa ce take taba zuciyarta a hankali,tun dazu daya shigo yace zai fita bata kuma ganinsa ba,kuma dazun taji shigowar motarsa,taji mimi tana masa oyoyo,amma bai shigo ya sake ganinta ba?,wani abune da bata saba dashi ba,duka sai taji qirjinta da zuciyarta sun quntata,wayar ma ta fita a kanta,ta maidata gefa ta ajjiye tana zamewa ta kwanta,idanunta suna hada ruwan hawaye.
A gajiye yake jinsa,don haka ya nufi sashen widad yayi mata sai da safe,ya murda qofar ya jita a kulle
"Sarkin tsoro" ya fadi yana sakin murmushi,ya saka nasa key din ya bude ya shiga.
Falon nata neat kamar ba'a zauna ba,qamshinsan nan yana nan,amma akwai qarancin haske,da alama ta gama shirin kwanciya.
Lumshe idonta tayi sanda taji sallamarsa,sai taji wani abu da ya tokare mata a qirji yana sauka,ta bude idonta tana amsa masa sallamar,dai dai sanda ya shigo dakin,ya saka hannu ya kunna fitilar haske ya gauraye ko ina.
A kanta idanunsa suka fara sauka,suna hada ido sai taji zuciyarta ta karye,ta sake narkewa tana jin idanunta suna tsatstsafo da hawaye
"Bakiyi bacci ba?" Ya tambayeta yana takowa inda take,maimakon ta amsa masa saita cusa kanta cikin pillow tana sakin kuka,yaji a jikinsa kukan take,saboda haka ya tako da sauri ya iso inda take
"Wuud(qauna/soyayya,sunan da ya kuma fara kiranta dashi kenan)" sake cusa kanta a pillow din tayi,sai ya haura gadon gaba daya,ya birkitota jikinsa yana leqen fuskarta
"Me ya faru?,kuka?" Gaba daya ta saki kukanta,ta kuma qanqameshi tana saka kanta a qirjinsa,cikin narkakkiyar muryar kukan tace
"Ba kaine ba?"
"Nine?,nayi me?" Ya fada tana fidda idanunsa
"Tunda ka fita baka sake shigowa ba kayi tafiyarka,kuma daka dawo ka shiga wajen mommyn mimi ni kuma sai yanzu ka shigo,bayan ma a can zaka kwana"
"Kishi?!" Ya fada a zuciyarsa yana zaro idanunsa waje,wani lafiyayyen murmushi kwance saman fuskarsa,maganarta dai dai take da albishir a gareshi na rainon da yakewa zuciyarta ya fara kaiwa ga gaci,albishir ne a gareshi na zai fara tarbar sabuwar rayuwar daya raina,sabuwar zuciya da jaririyar soyayyar data fara ginuwa.
Rungumeta yayi gaba daya a jikinsa,cikin taushi da laushin harshe ya fara gaya mata wasu kalamai da suka sata jin kunya,tun tana ya bari yana qi har kunya ta sakata ta shige jikinsa gaba daya,sai daya tabbatar ta nutsu sannan ya sakata ta kwanta,ya rufeta da duvet da kyau,ya saita mata sanyin ac dana fanka guri daya,ya kuma rufe mata dukka windows dinta dama sashen gaba daya.
Tana jinsa yana fita kamar tace masa ya dawo,to amma ta samu dakiyar zuciya tunda ya gaya mata goben a nan zai kwana,ta rufe idonta tana sake bawa kanta qwarin gwiwa,duk da zuciyar dai babu dadi.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 88
*W A S H E G A R I*
Ture plate din da ya gama cin chips din yayi gefe guda bawai don ya qoshi ba,a'ah sai don babu wanu taste a tattare da dankalin,salam dashi,yakai dubansa ga yaransa daketa cin abinsu hankali kwance,saboda rashin sabo da kuma rashin sanin dadin bakinsu.
Kallonta yayi itama tana ta cin abinta kamar yaran,tun kayan daren jiya ne a jikinta,duk da tayi wanka a hakan,ya danyi gyaran murya
"Yau din ba sai kinyi shirin komai ba,zan kwana wajen qanwarki,jibi sai na dawo wajenki,idan mun koma jibin shikenan,idan bamu koma ba sai a dora da haka" maganar taxo mata a mugun ba zata,ta daga kanta da sauri tanason ganin da gaske abbas ne ke mata zancan rabon kwana tsakaninta da widad din,tsabar mamaki da tsorata sai kuwa ta qware,dankalin ya shaqe mata wuya,tahau tari babu qaqqautawa,take idanunta duka suka firfito,ya tsiyaya ruwa da sauri ya miqa mata yana mata sannu.
Ko data gama shan ruwan numfashinta ya dai daita sai taji kamar ta kurma ihu,abbas din yayi wani mugun baqi a idonta,duk qoqari da jarumtar da tayi a jiya bai gani ba?,shine da safiyar Allah zai zo da wani zancan na daban,banda rainin wayo da rainin hankali,su gama satittikansu a can,sannan a nan ma a cinye mata weekend dinta?.
Bala'i ke cinta sosai tana kuma son ta saukeshi akan abbas din,amma kuma batason tayi wani abu da anty ummee zata ce ta bata plan din gaba daya,duk da haka ta kasa haqura,ta kafeshi da ido sosai tana kallonsa
"Abban mimi.....ni kake cewa zaka yiwa rabon kwana da widad diyar cikina?" Cikin second uku kacal ya gama qare mata kallo,a nutse ya jingina jikinsa da kujerar da yake kai sannan ya gyada mata kai yana lumshe ido hadi da budesu,sai ta janye nata idanun,ranta yana qoqoluwar baci,daya daga cikin yanayin da zaka gane hankalinsa a kwance yake,kuma ransa bai baci ba kenan idan yayi maganarsa,kuma sign dake nuna tabbatacciyar magana ce da babu canzawa,sai kawai ta miqe da sauri ta nufi daki,batason hawayen da suka taso mata su zubo a gabansa yaga rauninta.
Tana kuka tana kiran anty ummee,wadda tuni ta saba da ganin kiranta,kiranta babu alkhairi kamar yadda kiran nata ba samuwa bace damuwa ce,haka siddan idan bata da matsala ba zata taba nemanta ba,tana dagawar kuwa taji sautin kukanta
"Anty ummee ni yau abbas ke gayawa wai kwanan widad ne?"
"Abbas din?" Anty ummeen ta fada abun yana girgiza ta itama
"Eh,shifa" shuru tayi mamaki na ratsata,wanne irin kafaffen namiji ne abbas din,duk hanyar da aka bullo masa sai ta warware?,tsahon minti biyar suna kan wayar hafsat na mata kuka,taja dogon numfashi tana cewa
"Kinga,kiyi shuru da bakinki,inaso kiyi kamar baki damu ba,kada ma ki bari ya gane kinyi kuka,amma yau bai isa ya kwana a dakin yarinyar nan a gaban idonki ba,ke har su koma wallahi,ki kwantar da hankalinki,indai kinbi abinda zan gaya miki yanzu" sosai taji qunci da takurar da zuciyarta ta shiga yana warwarewa,ta goge hawayenta fes tana sakin dariya
"Bansan wacce irin godiya zan miki ba 'yaruwa,bansan dame zan saka miki ba"
"Ni dubu hamsin ma nake nema,inda zaki bani ita da komai lafiya lau"
"Ki bari zamuyi maganar kawai anty ummee" ta katse zancan
"Shegiya uwar son abun duniya,duk bala'in son abun duniyar taki wallahi Allah sai naci dake,duk wayon amarya sai an sha manta" anty ummeen ta fada a zuciyarta
"To shikenan,sai na jiki" daga haka sukayi sallama,saita miqe ta shiga bandaki ta gyara fuskarta,ta dawo tahau gyaran dakin nata,cikin ranta tsanar widad na sake shigarta,gyaran dakin da a baya saita manta ma ya akeyinsa,don ita ke komai,koda brassiere dinta ta yasar duka zata kwashe ta kuma wanke,amma gashi cikin qanqanin lokaci komai yana shirin canzawa?,ba zatayi sake ba kuwa,ba zata bari haka taci gaba da faruwa ba cikin gidanta,zata bi kowacce hanya don ganin komai ya dawo bisa kan tsari yadda ta shirya.
************washegari wajen sha biyu na rana saiga nujood ita da sauran qannenta,dadi ne sosai ya kama widad,ta rungumeta kana taja baya tana cewa
"Hajjaa fa?" A shagwabe,nujood daketa baza hanci ta dubi widad din batace komai ba,har sai da widad din tadan daki kafadarta
"Kina jina ina tambayarki don wulaqanci"
"Aina kasa magana ne,wani shegen qamshi kikeyi widad,ke bakiga ma yadda kika canza ba gaba daya,kinga wani shegen kyau da fatarki tayi?,wai dama haka auren yake amma naji abba na maganar saina gama secondry na shiga university ki higher institute?" Harara widad ta watsa mata,tana ji a ranta nujood din bata da hankali
"Ke kike ganin haka dalla malama" dariya suka saki a tare,sannan suka zauna saman kujerun falon,suka hau surutu har wani bayajin muryar wani.
Nan suka wuni a tare,saidai rabi da rabin hankalinta yana kan abbas din,yace mata zaije yakai hajiya dubiya,idan sun wuce ziyarce ziyarce zataji shuru,idan kuma sun gama da wuri he promised her zai dawo gida da wuri.
Zuwa azahar ta gama yanke abinda zata dafa masa,taja nujood kitchen din,nujood nata tsokanarta
"Uhmmm,kaga matan aure,Allah har mamakin girkinki nake widad,yaushe kika qware haka?" Murmushi tayi
"Online classes ne dani sun kusa guda goma,kuma kowanne da irin abinda suke koyawa,dukkansu kuma expert ne,idan suna miki classes kamar a gabanki akeyi"
"To ya girkin mutuniyarki?,har yanzu yana nan jiya iyau,hala kina dan sanmata idan kika dafa?" Nujood ta fada tana dariya,saboda tuna girkin da aka tarbesu dashi ranar da suka kawo widad din.
Shuru widad din ta danyi tana nazari,sai kuma ta tuna,da sauri ta daki bayan nujood tana dariya kafin ta tsagaita
"Oho,da yake ni bacin girkinta nakeyi ba"
"Ah dole uncle abbas yaji dake wallahi,irin wannan delicious haka,lallai kwanan nan mommyn mimi za'a shiga uku" ta fada tana feshewa da dariya,tana kunna gas ta kalleta
"Kaman yaya?,saboda girkina yafi nata sai uncle yafi ji dani?" Harara nujood ta balla mata
"To zauna nan,ke bakisan maza mayun abinci bane?,ki dinga kula daga yau,yadda yakecin abincinki da yadda yakecin nata" nan kuma sai hira ta balle.
Nujood tadan girmi widad da kadan,ta kuma fita wayo da shiga cikin jama'a,don takanje gidajen qannen hajjaanta hutu,kuma dukansu yaran mata ne,wasunsu suna da abokan zama,tana ganin yadda suke abubuwa,uwa uba qawayenta na makaranta suma kusan suna da yayye aurarru,kuma suma suna zuwa gidajensu,to idan aka hadu hirarsu bata wuce ta aure da gidan miji,musamman yanzun da suka shiga ss,kowacce tana ganin kamar ta zama senior.
Shuru widad tayi tana biye da hirarrakin nujood,mamaki ya dinga kamata, zuciyarta ta dinga kawo.mata abubuwa da yawa game da hafsat,kenan matsayinsu daya da ita duk da qarancin shekarunta?,duk da ta girmeta amma matsayinsu daya kenan?,duk da bata tambayi nujood komai ba,amma ta tsinci abubuwa da yawa cikin hirar da sukayi.
Nujood ce ta kama mata aikin,ta shurya lafiyayyar wainar shinkafa da miyar agushi data zuba naman rago wadatacce,don da safiyar abbas din ya aiki yaron office dinsu yayo cefane na duka kayan buqata na gidan,ita dama yawanci idan yasa akayi irin wannan siyayyar kadan yake diba mata,tunda basa wuce kwanaki hudu a bauchin suke komawa,saidai idan wani abunne ya taso.
Ta taba ganin ya aika an siyo masa wainar,saita gwada yi masa sau daya,duk da bata tashi ba amma tayi dadi ba laifi,ya kuma ci sosai,data tambaya muneera sai taji ashe tana cikin favorite foods dinsa,yanzun kuma ikon Allah sai bata bata kunya ba,ta tashi tayi kyau sosai,tayi saqa saqa a ciki,ta kuma yi laushi,anty madeena ce ta bata wannan recipe din ta gwada,ta kuma sake tambaya a classes din da takeyi.
Bayan ta gama suka gyare gidan fes tare, nujood ta soma hada kan yaran
"Yamma tayi yanzun zakuga bala ya iso daukarmu" fuska widad din tadan bata
"Haba mana nujood,ku bari zuwa magriba" baki ta kama
"Waaa....niiii?, rufan asiri bazan iya.kallon love din da za'a balle yau ba, bakiji wai irin qamshin daya cika gidan na ba?,har waje wallahi,ina ganin kishiyarki yau saita hadiya yawu ya kusa sau saba'in" ta sheqe da dariya,hakanan maganar nujood ta bawa widad dariya
"Ki daina sharri wallahi,ba lallai ma ta jiyo qamshin ba kike abunki" ido nujood ta zaro
"Lallai yarinyar nan bakisan kishiya da kishi ba" harara widad ta watsa mata
"To yaya babba" sai suka saka dariya.
Kayan makeup ta hadawa nujood da sauran qannenta,sannan ta bata turare tace ta kaiwa hajjaa,ta rakasu farfajiyar gidan,saida drivern ya iso suka shiga mota sannan ta juya zata koma ciki.
Kacibus sukayi da hafsat din,ido ta zubawa widad,itama saita zuba mata nata idon,dauke kai widad din.tayi ta wuce abinta,abun da ya qara daurewa hafsat din kai,tabi da kallo mamaki yana cikata,sai kuma ta ja qwafa cikin ranta tana sakin murmushin mugunta
"Yaro man kaza,yaro baisan wuta ba sai ya taka" ta fada a fili,nishadi yana cika Zuciyarta.
Ganin duhun magriba ya kawo jiki sai ta lafe a falon tanata duba agogo,sanda taji shigowar motarsa saita narke cikin kujerar tana tsumayin shigowarss,ba jimawa kuwa yayi knocking,ta taso a hankali tana tura baki gaba ta bude masa.
Ko gama buduwa qofar batayi ba ya shigo ciki,cike da zaquwa ya sanya hannu ya dagata cak ya rungumeta cikin jikinsa yana sansanar kowanne sashe na jikinta,idanunsa a lumshe kunnuwansa na karbar daqon shagwabarta,ya tattara dukka qarfin halinsa ya taka zuwa ciki da ita,suka zube saman kujera,muryarsa na rawa yace
"Me ya faru baby doll?,kukan na meye?"
"Uncleeee......" Ta kirashi a narke
"Ba kai bane,baka dawo da wuri ba,tun da rana nake jiranka" muryarta har tsakiyar kwanyarsa,tattausan murmushi ya subuce masa,ya cusa kansa cikin gashin kanta bayan ya zame dankwalin
"Uhnnn......inda na dawo me zaki bani?" Ba zato yaji bakinta a kunnensa,da zazzaqar muryar ta din nan ta rada masa wani abu da ya sakashi qanqameta cikin jikinsa
"Wayyo Alla na" ya fada cikin taushi,saita qyalqyale masa da dariya cikin matsananciyar kunya tana boye fuskarta,hannuwansa duka biyu ya saka ya daga fuskartata yana kallonta cikin tsakiyar idanunta da nashi idanun da suka canza launi
"Gani na dawo,ko yanzun baby banyi late ba,don Allah kada ki fasa" ido ta lumshe sosai tana sake sakin murmushi,cikin hirarsu da nujood ta tsinci wannan,ashe haka uncle din nata keso yaji ta furta hakan?
"Naje nayi sallah na dawo?" Ya tambayeta a narke shima,kamar qaramin yaro,saita gyada masa kai,ya miqe cikin qarfin hali yana dubanta
"Bari nayi alwala.na fito"
"Na rakaka uncle?" Ido ya zaro
"Bakyason alwalar tawa ta tsaya kenan?" Saita saki qaramar dariya tana kwantar da kanta a hannun kujera.
Kafin ya dawo ta gama sallarta itama,haka kawai yau ta tsinciki kanta cikin zumudin kasancewa tare dashi,wani irin sabo kullum zuciyarta ke sake yi dashi,saita miqe ta hada masa ruwan wanka,ba'a dade da.idar da sallar isha'i ba ya sake shigowa.
Zaman cin abincin yayi bayan ya gama wankan,ya shaqi daddadan qamshin da miyar ke bayarwa,take tsohuwar yunwarsa ta tash,sanda yakai abincin bakinsa kansa qarasa kuncewa yayi,kamar kullum qarawa hannunta zaqi akeyi
"Ki zabi dukka tukuicin da kikeso na baki na dafa min abinda nafiso da kikayi" murmushi ta saki
"Kace Allah yayimin albarka,haka ummu ke yimin idan nayi mata wani abun kirki" kai ya jinjina yana sake samun gamsuwa da yarinyar a ruhi da gangar jikinsa gaba daya,tun daga tarayyarsu zuwa yau ya tabbatar ta samu cikakkiyar tarbiyyar da irinta tayi qaranci ga yaran yanzu,shikam zai iya cewa ya tsincik diamond ne a cikin tarin duwatsu marasa daraja can can.
Cikin lallausar muryarsa data karye ya fara mata addu'a,addu'ar data dinga amsawa tana murmushi,saboda da gaske tayi mata dadi sosai.
Karar sautin wayarsa ya katse musu daddadan yanayin da suke ciki na wata irin hira me tafi da hankali da tunani,daya duba sai yaga hafsat ce,ya danyi mamaki kadan,duk da dazun daya shiga ya sameta tana sallah,sai kuma bai qara komawa ba,ya bari sai yazo rufe gidan,ransa bai kawo komai ba ya jawo wayar ya daga.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 89
Sallama yayi sannan yayi shuru na wasu seconds
"Okay' taji yace,ya sauke wayar yana sakin ajiyar zuciya sannan ya kalli widad
"Baby.....ina zuwa" kawai sai taji ranta yayi mata babu dadi,a sanyaye ta gyada kai,ya sunkuya a hankali yayi kissing goshinta sannan ya fice.
Tashi tayi ta tattara kayan abincin da ya gama ci,ta gyara wajen sannan ta dawo saman kujera ta kwanta tana maida idanunta ga tv,saidai kuma fiye da rabin hankalinta yana kan abbas,ko yaya taji motsi sai ta daga kai taga ko shine.
Tun tana kallon agogo da marmari har ta sare,tun tana danne zuciyarta har ta kasa ta fara sharar hawaye ganin sha daya ga sha biyu itama ta gota an tafi qarfe daya na dare,saita fashe da kuka tana curewa cikin kujera,tsoro haushi da takaici hadi da baqinciki suka mamayeta,me yasa uncle zaiyi mata haka?,daga cewa gashinan yanzu yanzu?.
Hada kai da gwiwa tayi tsakanin cinyoyinta ta saki kuka sosai,zuciyarta na wani irin tafasa,ya tafi wajen mummyn mimi ya barta ita kadai?,bayan shi yayi mata alqawarin a nan zai kwana yau.
Tun tana kukan da qarfinta har ta soma jin babu dadi,zuwa uku na dare kukan ya isheta ita kanta,a hankali kuma wani wahalallen bacci mai hade da bacin rai ya dauketa nan cikin kujerun falo.
Cikin mamaki yake saka kanshi cikin falon,wayam babu kowa,sai tarkacen kwanukan da suka gama cin abinci da sauran datti wanda dama falon baya rabo dashi,haka ya dinga tsallake shirgi har yakai qofar dakinta.
Yana murda handle tana sakin wani irin nishi,abinda ya sanyashi buda qofar da dan hanzari ya saka kai ciki.
Male male ya sameta,kwance qasan tiles tana juyi daga wannan bangon zuwa wancan,tana ganinsa ta dago masa hannu,idanunta jagab da hawaye.
"Subhanallah" ya fada yana qarasowa da sauri inda take kwancen,ya saka hannu yana dagota,gaba daya jikinta sharkaf yake da gumi,ya dorata saman cinyarsa yana tambayarta
"What's going on?,me yake damunki?"
"Cikina abban mimi......cikina zai fashe.....wayyo Allah" ta sake fada da qarfi tana wani irin murdewa.
"Relax,ya isa" ya fada yana riqe hannunta dake saman cikin nata
"Mutuwa zanyi,mutuwa zanyi,ciwo yakeyimin" ta sake fada tana riqeshi da kyau
"Ba abinda zai sameki,ki nutsu,bari na fiddo mota sai mu wuce asibiti" gan ta riqe hannunsa cikin nata
"Don Allah kada ka tashi,wallahi kana fita zan iya mutuwa"
"Just a minute......yanzu zan dawo,saina kira widad ta kwana da yaran kafin mu dawo" kai ta jijjiga masa tana fashewa da kuka
"Don Allah nidai kada ka tafi,ka mayar dani kan gado,sanyin wajen nan kamar zai fasamin qashi" duk yadda zai motsa ta hanashi,ko waya da yakeson kira taqi bari,haka ya miqe ya dauketa ya azata saman gadon,tana ajjiyeta ta kanainaiyeshi da hannuwanta tana ci gaba da matagugun ciwo.
Da qyar ta bari ya saka hannu ya kade shimfidar gadon saboda datti datti da yake ji akai,ya jawo mata pillow dinta da pillow case din ta gaji da haduwa da dattin dauda,sai tasa hannu ta kare
"Ka barni a jikinka please,ina samun relief" ta fada tana hawaye,hakanan ya zauna jingine da makarin gadon yana fatan ta samu sauqi,duka hankalinsa akan agogo yana mamakin yadda lokaci yaja haka,widad na ransa,ya dauki wayarsa ya fara kiran layinta.
Har wayar ta qaraci ringing dinta ba'a dauka ba,ya sake kira nan ma ba'a daga ba,ya danji relief,saboda ranshi ya bashi cewa bacci ne ya dauketa.
Jin shuru abun ya lafa sai yadan motsa da nufin sa mata pillow yaje ya duba yaran ya wuce sassansu,ji yayi tayi caraf ta riqeshi,cikin kuka kuka tace
"Yanzu ba zaka iya zama dani ba daddyn mimi?" Tayi maganar tana sake riqeshi d kyau
"Ya isa shikenan,yara zan duba,kuma.nabar qanwarki batasan me ake ciki ba" banza tayi taci gaba da sharba kukanta kamar ma bataji abinda yace ba.
Duka duka baccin minti arba'in yayi aka qwala kiran sallar asuba,ya zame jikinta ya kwantar da hafsat dake baccinta sosai,har ya buda toilet dinta yaji bazai iya shiga ba,ya koma ya buda dakin yaran.
Sai daya duba lafiyarsu sannan ya shiga nasu bandakin dake da sauqin qazanta yayi alwalar ya wuce masallaci idanunsa akan sassan widad.
Tun kiran sallar farko ta tashi,ta farka tana sauke ajiyar zuciya na kukan data sha,ta kalli agogo saiga wasu hawayen,ranta ya motsu qwarai,kawai sai ta miqe ta wuce dakinta tana jin bacin rai yana cikata.
Alwala ta daura,ta dawo cikin dakin ta jawo akwatinta guda daya ta fara sauke kayanta kaf tana lodawa a ciki,tana yi tana sharar qwalla,itakam yau ta gama kwanan bauchi.
Akwati biyu ta shirya cike da kaya,ta jawosu falo sannan ta koma dakin tayi sallah,sai ta shiga wanka kawai,bayan ta fito ta shirya cikin atamfa dinkin riga da skert,ta zabi hijabin daya dace da atamfar jikinta ta dawo falon riqe dashi tayi zaune kusa da akwatunta tana share qwalla lokaci bayan lokaci,jiran shigowarsa kawai takeyi.
A gurguje ya kammala azkar dinsa ya baro masallacin,gaba daya hankalinsa yana kan widad din,key dinsa yayi amfani dashi ya bude qofar falon,ya tura a hankali yana mamakin ganin qwan wutar falon a kunne
"Subhanallah" ya fadi sanda yayi tuntube da akwatin widad,sai yaja baya yana kallon akwatunan guda biyu dake maqare da kaya,sannan ya maida dubansa ga widad din.
Fuskarta a dinke tsaf,sai qananun qwalla da take sharewa,ta dauke kanta daga gareshi gaba daya,sam taqi yarda su hada ido,ya fahimci laifi ya tafka a jiyan,kuma da alama laifin babba ne a wajenta,ya zube hannayensa a aljihun rigar jikinsa yana qare mata kallo gami da sakin murmushi,wata qauna da soyayyarta mai kaifi tana hudashi,sai ya fara takawa a hankali zuwa gabanta.
Yana isa ya tsugunna saman qafafunsa yana qoqarin leqa fuskarta,amma kuma ta hana hakan faruwa,mamakin hawayen dake kwance saman fuskarta ya kamashi
"Is that serious?,kuka take da gaske?" Ya tambayi kansa
"Assalamualaikum" ya fada a tausashe,amma maimakon ta amsa saima hade rai data sakeyi tana share qwallar dake kwarara
"Ya salam,baby kuka kuma?" Shuru nan ma tayi masa
"kinga,ya isa,yi shuru ki gayamin menene?" Sai ya miqa hannunsa a nutse ya kamo hannuwanta,saita zame hannuwan nata ta fashe da kukan da take dannewa
"Ba kai bane, kayimin alqawari,shine kuma ka tafi can ka kwana"
"Ya salam......kishi?" Ya tambayi kansa cikin mamaki hadi da tsareta da idanu,saidai kuma wani abu mai sanyi na kwarara cikin zuciyarsa
"He won.......ta fara sonshi" ya bawa kansa amsa yana jin duniyarsa na cika da farinciki,ya gyara tsugunnon da yayi a gabanta zuwa zama sosai yana sake kama lallausan hannunta
"it was not intentionally.......naje na sameta bata da lafiya ne,i called you ki duba wayarki" sam ji tayi bata nutsu ba,gaba daya garin ya gama fice mata aka,sai ta sake zame hannuwanta
"Ni tafiya zanyi" ido ya fidda cikin fargaba,ya kuma tambayeta cikin hanzari
"Ina?"
"Kaduna,bazan sake kwana a nan ba" ta fadi tana sake sakin kuka.
Ajiyar zuciya ya sauke yana kama kunnuwansa da kyau
"Am sorry please forgive me"
"Allah ni tafiya zanyi,bazan sake kwana a nan ba".
Duk yadda zaiyi yahi mata akan tayi haquri su qarasa weeknd dinsu amma ta tubure tace sam,itafa a yanzun saiya shirya sun wuce,daga bisani yace mata ta bari zuwa yammaci nan ma ta tubure masa,sam taqi zama suyi magana da nutsuwa da fahimta dashi,gaba daya ta birkice masa,saiya sauke ajiyar zuciya yana kallonta yadda take kuka riris,zuciyarsa na wani irin suya,kukanta a yanzun shine abu.mafi girma da zuciyarsa bata qaunar ji,ba kuma zata iya jurewa ba,sai ya sanya hannu ya jawota cikin jikinsa yayi mata kyakkyawar runguma yana shafa bayanta a hankali cikin sigar lallashi.
Da qyar yadan shawo kanta ta tsaida kukan,dole ya soma hada kayansa sannan ya wuce toilet ya fara shiri.
Ta bangaren hafsat kuwa yau ranta fes ta tashi,anty ummee ce mutum ta farko data soma kira ta zayyana mata komai,sunci dariya abinsu kamar ba gobe
"Na gaya miki indai zaki iya jura wannan yarinyar juyata ba wani babban aiki bane,nawa take gaba dayanta?,da kanta zata ja qafafunta ta koma gidan ubanta".
Sun jima suna hira da ita sannan sukayi sallama,tanaso tadan sake gyarawa kodon abbas din amma kuma tana tunanin idan tayi hakan kamar zaiyi saurin dago plan dinta,don haka ta narke taci gaba da kwanciyar ta.
Tsaf ya gama shiryawa yau din cikin qananun kaya,trouser da shirt na kamfanin Armani masu asalin tsada da aji,ya waiwaya a hankali cikin kamewa da nutsuwa ya dubi widad da har yanzun ranta yake a hade,suna hada ido ta sake dauke kai,dariya ta taso masa,ya saki qaramin murmushi yana girgiza kai
"Am done qanwata" kalmar qanwar tawa daya fada ta sakata waiwayowa tana kallon idanunsa,dama abinda yake da muradi kenan,abinda kuma yayi kewa kenan,ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na zubawa,yayi missing nata har baisan adadi ba
"Zan iya zuwa nayi sallama dasu mimi?" Ya fada da wata kasalalliyar murya,saita gyada kanta a hankali,har ya taka zuwa gaba ta bude baki a hankali
"Kada kuma ka sake zama irin ta jiya" cak ya tsaya yana dariya qasa qasa,wow......at her age amma ta iya kishi haka?,what if idan ta sake girma da wayo?,haka yayi gaba yana murmushi shi daya bayan ya amsa mata da
"Yes ma'am I will be back quickly" cikin ransa yana raya girman mulki irin na diya mace,banda haka widad din da ya haifeta amma kai tsaye take bashi command,kamar ba shine ke bawa manyan zaratan police order ba kuma subi cikin hanzari da gaggawa
"Mace ta wuce haka" wata zuciyar ta raya masa,ya jinjina kai yana sake sallamawa lamarin mata.
Da murmushin da ya jima bai gani ba saman kuncinta ta tarbeshi
"Ina kwana?" Ta gaidashi tana kallonsa da kyau,yayi mata kyau over,sai taji wani kishinsa yana ratsata,abbas din ba daga nan ba,mutum ne mai wani irin class da iya ado da gayu,ko yaya ne sai ya dauki hankalinki idan yayi kwalliya,sassanyan qamshinsa ya cika dakin gaba daya
"Lafiya alhmdlh,ya jikin naki?" Sai ta sake sakin murmushi tana cewa
"Da sauqi,naji dadin jikin"
"Ma sha Allah,Allah ya qara lafiya"
"Ameen" ta bashi amsa tana ci gaba da qare masa kallo
"Su nawwara fa?"
"Basu tashi ba......kayi kyau daddynsu" da dan mamaki ya kalleta,don kalma ce baquwa a kunnensa da bakinta,har widad da tazo daga baya bayanta ta fita iya fadinta,har baisan adadin sau nawa ita din ta fada ba
"Thank you,na gode"
"Amma wannan kwalliyar da safen nan fa?" Gyara tsaiwarsa yayi,don gaba daya bayajin dadin wanzuwarsa cikin dakin,iskar da take kaikawo a dakin bata masa ba at all
"Inajin zamu wuce Kaduna ne" cikin mamaki ta qanqance ido
"Kaduna kuma fa kake cewa,yanzu yanzu?" Yasan dole sai taja magana,bai kuma san sanda zasu gama ba,don haka ya taimaki kansa ya matsa window din dakin ya yaye labulen ya kuma bude glasses din Windows din ya bawa iska damar shigowa,kafi ya gama aikin ya amsa mata ta sake sakin qorafi,har qasan zuciyarta bata gamsu da wannan tafiyar ba ta gaggawa irin haka
"Amma dai gaskiya daddynsu wannan tafiyar......kalli fa qarfe nawa gaba daya?"
"Uzuri ne na gaggawa ya taso,so dole a tafin yanzu" shuru ta danyi har zuwa sanda ya ajjiye mata dukka kudaden da ya saba aje mata idan zai tafin,sukayi sallama tana daga kwance bata motsa ba,ya saba da wannan idan da sabo,don haka ba wani damuwa ya wuce dakin yaran,sunta bacci ya tofa musu addu'a ya fito,ga mamakinsa sai ya sameta zaune hannun kujera a falo,ta dubeshi sannan tace
"Muje na rakaka mota" baice komai ba ya juya yayi gaba tabi bayansa.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 90
Tun kafin su qarasa gaban motar tasa idanuwanta akan widad,a lokacin bata kula dasu ba,sai da suka kusa da ita,iska ta fara debo mata qamshinsa,saita lumshe idanunta tana sauraren bugun zuciyarta tare da dakon isowarss,qamshin nasa na daya daga cikin ababen da ko a bacci zata iya tantancesu.
Data waiwaya sai ta gansu su biyu,haka kawai taji ba dadi,saita dauke kanta ta dauki wayarta kafin su qaraso ta fara dannawa,hakan ya bawa Hafsat daman qare mata kallo da kyau,wani bahagon kishi na dukanta
"Kada fa dan hakkin data raina yazo ya tsone mata ido" ta fadawa kanta da kanta sanda take qarewa gefan fuskar widad din dake kwance da wani gashi mai santsi
"Anya kuwa batayi kuskure ba data gaza rabasu tun a farkon tafiya?" Ta sake tambayar kanta,da qyar ta hadiye wani abu mai tauri,taja ta tsaya kafin su qarasa tana yin magana da abbas din
"Kasan dai akwai ragowar kwanaki na akanka" dubanta ya danyi, mamaki ma take bashi idan tana zancan kwana,kamar ta wani bashi muhimmanci,ya furzar da iska daga bakinsa
"Na gaya miki amma uzuri ne ya taso ko?" Kai kawai ta gyada tana maida dubanta ga widad daya hakimce a gaban mota,zuwa yanzun ta zura earpiece a kunnenta ma.
Mintunan agogon wayarta take ta kalla tana lissafa mintunan da sukayi a tsaye shida ita,tanata qoqarin danne abinda yake taso mata harta gaza,ta daga fararen idanunta masu girma,ta sake sauke glass din motar,a shagwabe ta kira sunanshi
"Uncle......don Allah ka taho mu tafi......naaaa gajji"
"Kambu" Wasu tagawayen duka qirjin hafsat yayi,sautin muryar widad din sai ya zame mata kamar saukar ruwan dalma a kunnenta,yayin da ta fusgi hankalin abbas sosai,har dai daya sauke wata qaramar ajiyar zuciya da hafsat din ta jiyota har tsakiyar kanta,wannan ya sabbaba mata maida dubanta kansa cikin sauri ba tare data shirya ba.
Wani irin kallo da ita daya ta sanshi cikin idanunsa ta hanga kwance cikin idanuwan nasa yana yiwa widad din shi,wani malolon abu ya tokareta,dukka juriyar da takeson gwadawa ta gushe
"To uwarmu,saiki saurara mana,ko sallamarma bazamuyi ba?" Ta fada da madaukakin sauti tana duban widad din da wani irin kallo,kallo daya widad din tayi mata ta dage glass din motar,gab da zata kammala rufewar ta daga yatsunta tayi masa sign na i love you,hafsat din bata gane me ake nufi da hakan ba,taga dai ya saki siririn murmushi,sannan ya maida dubansa ga hafsat din da takejin kamar ta taka zuwa gaban motar ta fusgo yarinyar.
Cikin nutsuwa ya miqa mata tattausan hannunsa alamun musabaha,wannan kusan dabi'arsu ce shida widad,sai tabi hannun da kallo
"Amma dai kasan ni ba namiji bace ai" murmushin da bai shirya ba ya qwace masa,ya manta ba widad bace,sai ya matsa gabanta kadan yayi kissing goshinta yaja baya yana mata sallama,yayin da widad daga cikin motar tana hangesu,saita tura baki gaba tana jin haushin abinda yayi mata.
Har abbas din ya shiga motar ya tayar hafsat tana tsaye tana kallonsu,sai da suka fice daga gidan sannan ta koma sassanta da sauri kamar zata tashi sama,yau tabbas dole ta hadu da anty ummee,koda ba anty ummeen ba dole ta nema abokin shawara,tana jin alamu da qamshin lalacewar komai anan kusa idan bata sake daura damara ba,ta gaji da wanna pretending din,gwara ta fito sak a mutum ko zatafi qwatar 'yancinta tare da nunawa yarinyar ita ba kanwar lasa bace,ba kuma sa'ar yinta bace ita.
Juyawa yayi yadan kalleta kadan jin tayi shuru,tunda ya shigo motar batace komai ba,sai yaga titi kawai take kalla,ya motsa kadan ya saka tafin hannunsa cikin nata ya riqe da kyau cikin taushi
"Ba dai shikenan ba,kin hanani zama ko?" Daman jira takeyi,saita turo baki
"Bayan harda kiss dina ka yiwa mummyn mimi" sosai dariya ta kamashi,ya dan daki sitiyarin motar yana dan dubanta
"Wato kiss din ma naki ne.....wai.....yaushe kika koyi qorafi haka ne babyn uncle?" Fuska ta hade bata ce komai ba,ya sake sakin murmushi
"Yaushe kika koyi kishi ne baby?,Ita kiss dinki nayi mata,ke kuma uncle din kika dauke gaba daya,ba shikenan an raba ba?" Murmushi tadan saki ta jijjiga kai
"Good,yanzu bani labari,me dame za'a yimin idan mun koms,kinsan nayi missing dinki.....nayi missing abun nan....." Ya fada ba tare daya qarasa ba,saita juya tana kallonsa,girarsa daya ya dage mata tare da kashe mata ido,abun ya bata kunya sosai,sai ta rufe fuskarta da hannuwanta tana dariya,shima ya tayata dariyar idanunsa na kallon titi.
Ko wanka bata tsaya yi ba,saboda tana ganin kamar zai bata mata lokaci ne kawai,ta canza kaya ta canzawa nawwara pampers,ta kada kan yaran ta zubasu a motarta suka wuce gidansu.
Kallonta kawai mamanta takeyi sanda take gaya mata duk irin abubuwan da suke faruwa
"Amma su uwa sun ha'inceni,keda duk da wadan nan matsalolin cikin gidanki amma kike zaune haka kina amfani da gurguwar shawarar ummee?,don ta kai mata ke lallai ne takai mikin?,bari na kira hajiya shuwa naji wanne malamin zata hadaki dashi" ta cire wayarta dake kusa da ita a chargy ta soma neman number din.
Kamar hafsat tace abarsa,duk ds yadda matsalar take damunta,amma dai sai ta kanne tana sauraren mamar tata sanda suke gaisawa da hajiya shuwa din.
Tana zaune tana sauraren umman nata tana yiwa hajiya shuwa bayani,bayan ta gama suka shiga tattanawa,kusan minti talatin sannan sukayi sallama,ta dubi hafsat
"Baki da wata matsala,itama kanta fadan zaman da kikeyi takeyi,tace yanzu ai ba'a zama,kada kiga wai yarinya qarama,idan batayi ba magabatanta zasuyi mata,bare sadakar yalla?,ai sai addu'a kawai,shu'umai ne" kai ta jinjina tana jin abun yana damunta har cikin zuciyarta
"Yanzu kudi kawai zaki fito dasu,sai mu saka rana mu sameta,tunda baya gari ma komai zaizo da sauqi"
"Kudi kaman nawa?" Ta tambaya tana duban umman nata
"Daga dai dubu dari zuwa sama"
"Za'a kaiwa malamin?" Hafsat ta tambaya tana dan riqe da habarta
"Eh,har miliyoyi ma ai kashewa akeyi,ita ranar biyan buqata rai ai ba'a bakin komai yake ba" janye hannunta tayi tana gyara zamanta,itakam bata jin ko naira dubu goma zata iya fitarwa,kudin da take fadi tashin tarawa rana daya ta wafci wani abun a ciki ta fara kaiwa wani suna raba dai dai,koma ya fita ci
"Shikenan umma,ki bari idan na shirya sai ayi mata magana sai muje" wani kallo uwar ta watsa mata,dama tuni labarin yadda ta baci da son abun duniya yake zuwa mata
"Kudin ne ba zaki iya fitarwa ba kenan?,ko a jikinsa ba zaki tarasu ba hafsatu?,gwara ki zauna da damuwarki kenan?" Kai ta girgiza
"Ni ba haka bane umma,kawai dai matsalar batayi girman da zan kashe wadan nan kudaden ba,mu bari kawai anty ummee din tazo nasan tabbas akwai mafita daga wajenta,basai an kashe komai ba" haushi takaici da baqinciki suka cika umman,saita dauke kanta gefe tana cewa
"To ai shikenan,sai kici gaba da zama har sai sanda matsalar ta girmama ta zama babbar".
***********Tunda suka koma ta tattara ta watsar da batun mommy hafsat din ta shiga sabgoginta,sosai ta maida hankalinta ga karatunta koyon girke girke online da kuma practical classes da akeyi cikin garin kadunan.
Cikin lokaci qalilan ta zama expert,hannunta ya sake fadawa,ta kuma qware da kalolin abinci masu dama.
Zamu iya cewa batason so ba,amma tana jin wani abu mai qarfi akan uncle din nata,wanda inda da cikakken wayo kai tsaye zata fahimci soyayyarsa ce ta fara kafa kanta a zuciyarta,sam bata iya wuni guda cikin nutsuwarta muddin baga ganshi ba,kowanne lokaci burinta shine tayi abinda zaice
"That's my baby.....ma sha Allah baby wannan yayi......baby doll inason abu kaza,babyn uncle wannan yayi dadi ko yayi kyau" wannan ya sanya ta sake zagewa da dukan iyawarta ta haddace abinda tasan yafiso yafi muradi,gefe guda anty deena da anty madeena harda hajja sun zage sosai suna wayar mata da kai dai dai gwargwado.
Ta gefan abbas kuwa abun har baya faduwa,wani irin wawan kamu soyayyar widad tayi masa,ta yadda shi kansa yake mamakin kansa,zuciyarsa ta koma sabuwa,tamkar bai taba qaunar wata halitta ba cikin rayuwarsa,yarinyar ta tafi da dukka zuciyarsa,ta kuma shiga rayuwarsa fiye da kima,har bayason wani abu da zai kawo su nisanci juna,duk da yana fama da shagwabrta sakalci da kuma wauta amma hakan sai ya zame masa kamar wani abun debe kewa,ya kuma zame mata ado,kasancewar bai saba ganin wannan ba.
A koda yaushe hafsatun na masa magana ne a tsaitsaye,tana kuma nuna masa ita din me wayo ce,bata da lokacin shagwaba ko karya murya,kamar yadda take ganin bai kamata ace mutum yana da wani choice a rayuwarsa ba na tsafta abinci turare sutura da sauransu ba,banbancin ra'ayi me girma da kuma tarin yawa ne a tsakaninsu.
Sabanin widad,da komai nata nashi ne,komai zatayi tana duba zai burge uncle?, uncle zaiji dadi?,hatta da shopping tana yinsa ne base on his choice,komai ta dauka saita tambaya cikin shagwabar nan tata
"Uncle yayi?" Wani lokaci yace baiyi ba,wani lokaci kuma ya barta da zabinta,ya zuwa yanzu bayajin akwai wani abu da zai iya shiga tsakaninsa da widad din,ta shiga rayuwarsa fiye da kima,ta samu gurbi a zuciyarsa sama da yadda kowa yake hange.
Tun daga wancan ranar ta rage binsa weeknd bauchi kwata kwata,koda ta bishi ma raba kwanan take tsakanin gidan hajiyan da kuma gidansu,dukkansu shi da hajiyan da suka fuskanci hakan yafi samar mata da nutsuwa sai suka rabu da ita.
Hafsat na gama kwananta baya iya jurewa,haka zai je gidan hajiyan da kansa yayita raragefen daukarta saboda kunyar hajiyan,abinka da uwa,takan bishi da murmushi ne kawai sannan ta sanya widad din shiryawa ta kuma bishi,a yanzun duk duniya tafi kowa samun farincikin canjin da abbas din ya samu,idan ka kalleshi da kyau zaka fahimci hakan,don har wata murjewa yayi,yayi 'yar qiba,ba shakka ko ta iya fannin abinci kawai dole rayuwarsa ta sauya,saboda shi din mutum ne da baya wasa da cikinsa,sai Allah yasa widad din bata da wani fatinciki itin ta ganta cikin kitchen tana sarrafa wani sabon abu da basu saba ci ko basu taba ci ba,koda yaushe hajiyan godewa Allah takeyi da sauyin da abbas din ya samu,nutsuwa sosai tazo masa,duka matsalolin hafsat ma sai suka rahe damunsa,tunda ko ba komai akeai gefen da yake samun nutsuwa gamsuwa da kwanciyar hankali,inda widad din yakeso takai wanda bata qarasa kaiwa ba yanata qoqarin horar da abarsa cikin soyyaya qauna kulawa da kuma nutsuwa.
Gefe daya hafsat din itama bata sake tayar da zancan ba,saboda anty ummee ta kwabeta kan ta barta haka,kada a fahimci takunta,saidai akwai sabbin hanyoyin da zasu sake dubawa.
_wannan kenan_
*Masu karatu muje zuwa,akwai sinqi sinqin CAKWAKIYA a gaba*
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 91
Sassanyan qamshi parlor din yake fitarwa baya ga wani kwantaccen yanayi da duk wanda ya shigo ciki sai ya burgeshi,awa guda kenan da gama dukka aikinta,ta kuma shirya kanta cikin wata gown ta yadin chiffon mai qaramin hannu,plain ne black babu digo ko adon komai a jiki,ta matse gashinta da jiyan abbas ya kaita da yammaci aka gyara mata shi,yana daya daga cikin abinda yakeso,shi yasa shima yake bashi kulawa har fiye da yadda ita ke kula da sumartata,duk sanda take kwance a jikinsa zaka samu hannunsa saman kanta yana yamutsa sumartata mai tsaho da santsi,abinda yake yawan haifar mata da kasala,saita lafe a jikinsa.
Hankalinta ya dauku ga wayarta sosai,tana karanta wani hausa novel mai suna HANGEN DALA,labarin ya tafi sosai da hankalinta,ya kuma fara ankarar da ita matsayin hafsat a wajenta.
Ya dauki mintuna kusan uku tsaye a bakin qofar yana qare mata kallo ba tare data sani ba,hancinsa kuma yana shaqar daddadar iskar da parlor din yake fitarwa.
Tayi masa wani mugu mugun kyau,cikin kwanakin gaba daya wani kyau take qarawa,ga wani irin fari data sakeyi kamar ka sanya hannu jini ya fito,ta kuma qara qibar data sakata murjewa,alamun hankali da girma sun fara nunawa a jikinta,qibar tayi mata wani irin kyau dake dimauta masa tunani,shi kansa wani lokaci yakan tuhumi kansa
"Abbas anya baka zauce akan yarinyar nan ba?" Bai sani ba ko zaucewar yayi,amma shi kansa yasan yana mata wani irin so da bazai misaltu ba,baya gajiya da kallonta,baya gajiya da ganin shirmenta,baya gajiya da sauraren hirarta,ko ba komai zai samu nishadi irin wanda duk duniya idan ba wajenta ba babu wajen wanda yake samunsa.
Yaga alamun hankalinta yayi nisa sosai,don haka ya sanya qafarsa cikin tattausar muryarsa yayi mata sallama,suna hada ido ta miqe da sauri bayan ta watsar da wayar gefe,ta kuma tako da sassarfa yadda ta saba yi masa ta dane shi,ya sanya dukka hannayensa ya tarbeta,ya kuma dauke abarsa cak ya aza a jikinsa yana aika mata kisses ta ko ina,laushin fatarta da qamshinta kamar zai zautashi.
Kamar ko yaushe ta sunne kanta tana jin kunyarsa,ya saki qawataccen murmushi yana shiga cikin falon sosai da ita hadi da cewa
"Gayamin.....me zanyi na qarasa cire kunyar nan baby......tana qwarata wani lokacin fa" ya fada murya qasa qasa kamar su da wani ne a falon,saita sakar masa murmushi tana shigewa jikinsa.
A hakan yana dauke da ita suka shige bedroom dinsa tana masa sannu da zuwa
"Yau anyi zafi,wanka zan fara yi baby,ba wani abinci yau" dariya ta sakar masa,sannan ta wantsalo daga hannuwansa zuwa qasa,ya tareta da sauri yana cewa
"Yi a hankali,wai bakiga kin fara zama 'yar lukuta ba?,inajin na kusa fara kasa daukarki" baya taja tana bata fuska
"Ka kusa daina daukata kuma uncle?" Ta fadi tana bubbuga qafa a shagwabe,yasan yanzun zai ballowa kansa ruwa,sai yayi saurin yin kwana
"Wasa nake miki fa babyn uncle.....amma fa wait.... seriously kin fara zama 'yar lukuta,ban yarda ba akwai abinda yake faruwa,me kike ci bakya sanmin?" Siririyar dariya ta saki
"Uncle ka fini ci fa,saidai wanda nake ci da daddare kana bacci" kai ya gyada yana dariya
"Harda rabona kike ci ai,kuma ban bayar ba,saina fanshe abuna,zo nan" ya fada yana takawa gabanta idanunsa a narke a kanta,ta saki dariya taa fadawa toilet da gudu.
Tsayawa yayi ya bita da kallo har ta shige,qugunta ya bude sosai,qirjinta ya fara cika irin yadda yakeso,abinda yake sake dimautar dashi a kanta koda yaushe,saidai har yau 'yar shagwabar tasa kukan amarci takeyi bata daina ba,hakan baya damunsa,hakan ma burgeshi yakeyi,ya zauna ya lallashi kayarsa.
Gaban mudubi ya taka ya zuge jakar daya shigo da ita yana duba takaddun daya shigo dasu,ya sake sakin murmushi yana tunanin irin yadda zataji idan ya gaya mata komai na tafiyar ta saudiyya ya kammala,yana tsaka da dubawar kuwa ta fito tana goge ruwan hannunta da qaramin towel
"Uncle ka shiga na hada" ajjiye su yayi,ya matsa zuwa gabanta,a tausashe ya kamo qugunta ya hade da nashi yana duban qwayar idanunta,itama shi take kallo,tana samun kanta cikin wani irin yanayi a duk sanda irin hakan zata faru,tana ji da ganin wani abu na musamamn cikin idanuwansa
"Amma dai na gaya miki,indai kina yin wankanki bakya jirana,zaki dinga wanka biyu ko?" Fuska ta narke masa sannan ta turo masa dan qaramin bakinta
"Uncle saina zauna ka dawo kaga qazantata?" Bin siraram lips dinta daketa qyallin lip gloss yayi da kallo tsigar jikinsa na zubawa,sannan ya dauke ya maidasu cikin manya kuma fararen idanuwanta,har cikin zuciya da ruhinsa yana yaba mata,yadda bata qaunar ya ganta ba wanka,naturally haka take,sometimes kafin ya dawo daga salla tayi wankanta
"Okay,tunda haka ne zaki biya ladan qin jin maganar uncle" bai barta ta samu damar cewa komai ba ya hade bakinsu waje daya ya shiga aika mata da wani zazzafan kiss da ya sanya taji kwanyarta tana yamutsawa,cikin lokaci kadan ya sauke mata wani saqo mai nauyi daya sanya jikinta saki gaba daya,yayin da ilahirin nashi jikin ya dauki rawa gaba daya,kusan ta saba da wannan yanayin nasa,tun tana tsoro harta saba gani,ta saba ganin wannan romance din mai zafi daga wajensa,fice mata a hayyacinsa yakeyi cikin lokaci qalilan,wannan yake rudata itakuma tayita masa kula,kukan da baya samun damar lallashinta sai bayan komai.ya kammala.
Yau dinma daga bata ladar rashin jin magana ya zarme,shi kamsa baisan me yakeyi ba,illa dai zuciyarsa da qwaqwalwarsa yaji sun kasa jurewa,bai kuma barta ba sai daya isa ga muradinsa duniyarsa qarshen farincikinsa.
Tana a jikinsa tana masa 'yan koke koken data saba,hannunsa cikin sumarta yana yamutsata,idanunsa a rufe,lips dinsa kawai ke motsawa suna fidda sautin wasu kalmomi masu zaqi da kwantar da rai,yayin da zuciyarsa tayi nisa wajen son gano iya matakin matsayin da widad ta tsaya a ransa,ko yaushe yana jin kamar a ranar ya fara saninta,tana da wata irin baiwa da bai taba tsammanin za'a sameta jikin kowacce diya mace ba,a duk sanda ya kasance da ita burinsa na sake kasancewa da ita baya raguwa saidai ya qara hauhawa
"Uncle wayo" ta fada a shagwabe da siririyar muryarta, murmushi ya kubce masa,hakan take yawan gaya masa duk sanda irin hakan ta faru
"Kiyi haquri dani babyn uncle,na jarabtu dake har bansan iyaka ba,am sorry....but I have something special for you,muje muyi wanka ki gani".
Tare sukayi wankan duk da tana dan zuzzulle masa,suka shirya ta gabatar masa da abinci yaci cikin nutsuwa da kwanciyar rai,best taste for ever a wajensa.
Bayan ya kammala ya jingina bayansa da kujera qafafunsa a miqe harde wajen guda,yatsun hannunsa ma a hade yana dubanta,kamar cin abincinta yadan ragu,tun ranar nan ya gani,amma kuma bai sakashi damuwa sosai ba,ganin bata canza ba,saima murjewa da jikinta yakeyi,hannu ya miqa mata alamun ta taho,saita maqale kafada
"Uncle wayo" ta fada tana dariya,bai shirya ba dole shima dariya ta kubce masa,a baya yakan jima baiyi dariya irin haka ba,amma a yanzu.widad ta maidata abu mai sauqi a wajensa idan yana tare da ita,dukka tsare gida shan kunun nan da kamewa sun koma office da sauran guraren aiki
"Kizl ki karba albishir din naki,ba wayo bane yanzu" matsawa jikin nasa tayi,ya kuwa riqeta gam yana fidda takaddun ya fara mata bayani.
Ruqunqumeshi tayi da kyau cikin farincikin da batasan yawansa ba tana sake tambayarsa
"Uncle da gaske?"
"Na taba yi miki qarya?" Kai ta girgiza
"Baka taba uncle" ta fada hawayen farinciki yana sauko mata,saiya bata fuska kadan
"Kuka?,noo baby,don't cry mana" ya fada yana janta jikinsa hadi da dan bubbuga bayanta alamun lallashi.
Irin godiyar data dinga masa sai daya ji qwalla ta sauko masa,godiya ce da bai taba jin irinta daga bakin hafsat ba,duk kuwa da ya kaita gurin da yanzun widad din zata je a qalla sau uku kenan,sai ya saka hannuwansa yana sake lullubeta cikin jikinsa da kyau,yana sake jinta tana shiga rayuwarsa da gasken gaske.
A ranar ta dinga kira waya tana shaidawa kowa,ummunta mommynta da abbanta sune farko,sannan uncle muhsin anty madeena anty deena dasu hajja,kowa yaji dadi ya kuma yi farinciki da wannan labari,ya kuma tayata murna qwarai, uncle muhsin ya kirashi yayi masa godiya,kai kawai ya girgiza
"Bakasan wacece widad a wajena bane muhsin,she meant alort to me,bansan ya zan fasalta maka ba" yayi furucin tun daga qasan zuciyarsa.
Murmushin jin dadi uncle muhsin ya saki,amma a fili sai yace
"Easy sir.....surukinka nake fa kaketa fallasamin sirrin zuciyarka" sai suka sanya dariya a tare.
Cikin satin yace ta shirya zasu wuce bauchi,batajin son zuwa bauchin sam,amma tana son ganin hajiya dasu mimi,don ta kwana biyu bata je ba,bata nuna masa komai ba,cikin karsashi ta shirya musu dukka jakankunansu,ta kuma siyawa su mimi da hajia tsaraba,bayan tace ya turo rose ko samuel su kaita kasuwa,sai gashi ya kashe aikinsa da kansa yazo ya kaita ta siya duk abinda takeso,don yanzun ba kasafai yake bari wani ya kaita wani waje ba,idanma ta kama to saidai ya turo mace.
**********Tunda sale ya bude gate din gidan ta gane motarsa ce,amma data fahimci bashi kadai yazo ba saita ci gaba da zamanta saman plastic chair din da take zaune a kai,ta jibge kayan da take siyarwa tana faman lissafi,gefenta su mimi ke wasa kamar ko yaushe futu futu abinsu,kai bakace akwai interlock cikin gidan ba.
Widad dake bacci abinta cikin motar ko shigowarsu cikin gidan bata san dashi ba,ya waiwaya yana mamakin nauyin baccin da takeyi a 'yan kwanakin nan,fuskarta tayi wani mugun fresh hasken fatarta ya kashe masa idanu,ya daga hannu da nufin tashinta,saidai mimi da nawwara sun rage masa aiki,don tuni suka fara kiran sunanshi suna rige rigen isowa,muryarsu ta sakata bude idanunta a hankali,ta saki murmushi tana kallon yaran har suka iso garesu.
Ita dashi aketa rige rigen tarbarsu,tayi nasarar riqe mimi shi kuma ya dauki nawwara,daga inda hafsat din take kamar zuciyarta zata fado,ta janye idanunta tana jin kamar zuciyarta xata fashe,ta gaji da jiran da anty ummee tace tayi,sai take gani kawai ta soma gajiya da lamuranta,tunda ta nemi aron dubu dari biyu bata bata ba.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 92
Kasa ci gaba tayi da lissafa kudin,idan tayi gaba sai ta dawo baya,dole ta zube kudin tana jin kamar ana sukar zuciyarta da mashi,ta miqe tana gyara daurin zaninta da dan qaramin cikinta wanda ya fara fitowa kadan,duk da duka duka bai wuce wata uku ba,amma saboda tana da tumbi har ya fara bayyana kansa.
Tana doso su tana qare musu kallo,dukkansu daga shi har ita sun canza,kamar wadanda ke rayuwa a wajen nigeria ba
"Hafsatu kina me?,kina me kika zauna kina gadin gida?,kina meye kika zauna?" Zuciyarta ta fara raya mata,take taji ranta yayi mugun baci,kamar ma kada ta isa inda suke,tunda tun tsaiwarsu babu wanda ya fahimci wanzuwarta a wajen.
"Sannu da zuwa" ta fada ciki ciki,qamshin turaren widad wadda ta tsaya daura da ita na cika mata hanci yana kuma qara iza wutar kishinta a zuciyarta.
Waiwayawa yayi ya dubeta,har ya daga hannu zaiyi welcoming nata kamar yadda suka saba da widad,sai kuma ya tuna yanzun zata ce yara,ko ta canzawa abun akala,yayi qoqarin sakin qaramin murmushi yana kallon yadda ta canza,cikin tun baiyi nisa ba ya fara birkitata
"Sannu mom mimi,ya gida ya jikin?" Ya tambayeta,duk da kullum sai ya kira yaji jikin nata
"Alhmdlh" ta furta tana qoqarin saisaita kanta,saboda wani mugun muzanta da taji tayi tsaiwar da tayi kusa da widad din,ta glass din motar da suke tsayen take satar kallon mugun tazarar banbancin dake tsakaninsu da ita,saita zama kamar wata mai aikin gidan,don haka ta janye jikinta a dabarance zuwa gefe sanda widad din ke gaidata,gaisuwar data qona mata rai,don duka hankalinta nakan mimi tana janta da wass,ta amsa mata ciki ciki.
Motar ya rufe yana ci gaba da riqon nawwara a hannunsa,ya juya zuwa sassansa yana yiwa naawara waqar da ya saba yi mata hafsat din tabi bayansa da sauri
"Uncle" widad tayi kiransa da narkakkiyar muryarta,ba abbas da aka kira sunan shi ba,hatta da hafsat sai da ta tsaya cak,yaji kiran har jikinsa duk kuwa da ya saba,amma yau sai yaji kamar muryarta ta qara zaqi
"Kayana please uncle,nagaji part dina zan shiga na huta"
"Hutu" hafsat ta fada a ranta
"Bai kamata acena qyale ta har tana samun damar hutawa cikin gidan nan ba"hafsat din ta fada a ranta,batasan ya akayi ta barta harta ajjiye dukka wani aiki da take mata ba
"Munyi haka ne dake?" Ya fada yana narke mata shima da salon da ita ta koya masa,sai hafsat din ta daga kai da sauri ta kalleshi cike da mamaki,abbas din ke abu kamar wani qaramin yaro?.
Baisan me akeyi ba,don idanunsa na ga widad
"Alqawari ne zan cika Allah uncle" ta fada tana maqale kafada
"Alright" ya amsa mata yana miqawa hafsat nawwara da nufin ta riqeta
"Ajjiyeta mana" ta fadi cikin zafin zuciya, ganin yadda ita yakewa maganar,amma duka hankalinsa na kan widad din,baice komai ba ya juya da nawwara a kafadarsa ya daukar mata luggage din yana biye da ita a baya har zuwa sassanta.
Da idanu ta rakasu,wai me yake faruwa ne?, yaranta ma farinciki suke da zuwan yarinyar ne?,ga wani abu me girma data lura yana gilmawa cikin idanuwansu shi da ita.
Ko kafin ya dawo tuni ta tsufa cikin falonsa,tunani yayi mata katutu,koda ya shigo falon ta daga kai ta dubeshi sai taji gaba daya ta raina kanta,ga laulayi daya sanyata ta kwantsame ta fita hayyacinta,gefe guda rashin gyaran da bata daukeshi a bakin komai ba shima ya taka rawa wajen lalacewar tata.
Kusan yinin ranar cikin qunci ta yishi,tana aikace aikacen da ba kasafai ta fiya yinsu ba sai abbas din yazo tana fama da qunci,itakam widad koda ta isa sashenta zagewa tayi ta gyarash fes,yaran na biye da ita har ta gama,ta kama yaran bisa radin kanta tayi musu wanka,tana jin dadin yadda yaran ke qaunarta,a nan falonta ta barsu bayan ta dora aninci mai sauqi,ta shiga itama ta sake wanka.
A gaban madubi ta tsaya daure da towel tana kallon kanta,ko ina na jikinta ya fara cika,abinda yaketa bata mamaki kenan,hasken data qara ya ninka nata nada,tasan bata canza mai ko sabulun wanka ba bare tace ko sune suka saka,don kanta ta gaji da kallon kan nata,bata kuma gano dalilin wannan canjin ba saita tabe baki kawai taja manta ta fara shafawa.
Hafsat din na gyaran sashen shi kuma yana gyaran closet dinsa,duk da yasan zaiyi wahala gobe widad din bata gyara ta ba,amma kuma yana tausayinta,yana ganin kamar aikin yana mata yawa,don sanitation irin wanda yakeso take a sassan nasa bayan hafsat ta gama jiqa jiqarta.
Baisan ma ta gama ta fice ba sai daya gama wanka yana neman wasu qananun kaya nashi,ya tuna suna cikin akwatin widad din,dole ya dora jallabiyya saman towel din dake daure a qugunsa ya wuce sassan nata don ya ciro kayan.
A falo ya tambayi su mimi antynsu,sukace tana ciki,ya wucesu bayan ya sake canza musu channel zuwa mbc 3.
Sanda ya buda qofar dakin nata ta zame towel dinta tana saka brassiere,tsaf ya qare mata kallo ta cikin mudubin yana jin numfashinsa yana sauyawa,don komai ya fito masa muraran,komai na widad din sake daukan hankalinsa yakeyi kowacce rana,sai yaji ya kwadaitu da son jin duminta cikin jikinsa,don haka ya taka a hankali har ya isa gareta,yayi caraf ya riqe towel din sannan ya fincikota a tausashe zuwa jikinsa.
Tare suka sauke ajiyar zuciya shi da ita,ya zaci zata nema qwacewa ko zame jikinta,sai yaji tayi luf cikin qirjinsa,qamshin sabulun wankansa yana mata dadi sosai har zuciyarta,wannan ya bashi damar aiwatar da abinda zuciyarsa ke kwadaita masa hankali kwance,har sai da taji yana niyyar zarmewa sannan ta zare jikinta tana tuna masa su mimi dake parlor.
Da jirkitattun idanunsa da suka sauya launi yake dubanta tare da tayata daura towel dinta da ya zame,daurin gaba yayi mata,ya cukuikuye towel din a tsakiyar qirjinta yana duban wajen,sai tasa hannunta guda daya ta rufe,daya hannun kuma ta jawo hijab dinta dake gefe ta soma yunqurin sakawa,ya saki siririyar dariya yana cewa
"Please mana,minti kadan fa zan dan kalla saiki rufe". Ya soma kicin kicin qwacewa ita kuma tana nade kanta a ciki tana dariya,da wannan har ta sake komawa jikinsa.
Ganin aikin take kamar zai kasheta,ga laulayi gaba daya jikinta babu cikakken qwari,don haka ta tsame hannunta daga yankan salad da takeyi ta nufo sassan widad din.
Tun a hanya take kwatanta da yadda zata fuskanceta do kada ma taga sassauci a fuskarta ta nema kawo mata wargi.
Bin ko ina na falon ta dinga yi da kallo,ko ina fes kamar yadda abbas yakeso,ya koya mata kenan,tsinanniyar tsaftar nan tasa,taja mugun tsaki tana tambayar su mimi widad din
"Tana daki,yanzu abba ya shiga kiranta" wata mummunar faduwa gabanta yayi,abbas kuma?,me yakeyi a dakin?,bayan yau din kwananta ne?,ta gama masa wahala daga kaucewarta har ya baro sassan?,cikin mamaki zafin zuciya da kuma kishi ta doshi dakin,batayi wata wata ba ta murza handle din ta tura da qarfi ta shiga,shigar da batayi mata dadi ba sam,shigar da sai da taji kamar kanta zai tarwatse,abbas dinta widad din kwance a jikinsa suna qyalqyala dariya,duk sun yiwa shimfidar gadonta squeezing.
Tare suka daga kai suka dubeta,saita kasa jurar ganinsu ta soma girgiza kai,ga widad kuwa mo gezau batayi ba,tadai ci gaba da janye hijab dinta daga hannunsa tana cewa
"Laaa,mummyn mimi wallahi bamuji sallamarki ba,uncle ne,yana nan yana......." Ido ta runtse da sauri taja baya,ta kuma buga qofar da kyau,gudu gudu sauri sauri ta fice daga sassan kuka yana kubce mata.
"Yana nan yana me uncle din?" Abbas ya fadi yana jefa mata hararar tsokana,can qasan ransa a bace na yadda ta kutso mata har bedroom dinta ba tare da sallama ko neman izini ba, dariya ta qyalqyale dashi,duk.da qasan ranta taji haushi,ta riga ta saba da dabi'ar yin sallama kafin ta shiga waje,amma ita hafsat din qatuwa da ita batasan tayi ba?
"Ba komai" ta amsa masa tana dariya,saiya tsaya kawai yana kallonta yanajin wani farinciki yana wanzuwa cikin rayuwarsa,tsahon seconds sannan ya miqe yayi kissing goshinta,ya qarasa akwatin ya dauki kayansa yana tsokanarta ya fito.
Yana dosar dakinsa ya jiyo sautin kukanta,ya girgiza kai kawai yanajin takaicin hafsat din,yana saka kansa cikin dakin ta daga kai tana dubansa,idanunta sharkaf da hawaye,tasan halinsa sarai,miskili ne na qin qarawa yaso,ganin yayi.kamar.bai ganta ba ya nufi dressing mirror dinsa saita buda baki a zafafe
"Na gode,na gode sosai da cin fuskar daka yimin,yau kacal amma harka fara satar kwana na kana kai mata?" Kamar bazai.amsata ba har ya gama fesa turarensa bayan ya fidda jallabiyyar jikinsa,sai a sannan taga towel kawai yake daure dashi, zuciyarta ta sake fusata qwarai,ya juyo ya dubeta
"Ina kwanan yake?,ina cewa rana ce yanzu?,da kika shiga kuma wani abun kikaga munayi?" Tambayoyin nasa sai taji gaba daya na rainin wayo ne
"Kayi laifi amma kana yin kamar bakayi komai.ba abban mimi?" Ta fadi tana nuna qirjinta da yatsanta,zare towel din ya qarasa yi yana sanya kayansa,sai da ya gama tsaf har sannan tana zaune tana dubansa,ya dawo gabanta ya tsugunna yana kallon qwayar idonta,ya sauke idanunsa zuwa ga hannuwanta da farcenta ya dan soma taruwa,ga 'yan qananun datti nan sun fara shiga qasan farcen,sun nuna kansu ne saboda yadda hannun da farcen suka kode dalilin rashin digon lalle ko kadan a jikinsu,abinda yafi tsana kenan ya gani,shi yasa sanda yake bauchi da kansa yake daukarta ya kaita gidan qunshu ya ajiyeta ya kuma bar mata kudi masu dan yawa akan ayi mata,amma da wahala idan ya kaita sau goma ayi sau uku saita kawo uzuri tace layi yayi yawa bata samu ba,wani lokaci ma kafin yazo daukarta ta hayo motar haya ta dawo gida,yasan kuma tabbas kudinta kawai take karbewa daga wajen mai qunshin,a yanzun yanason kama hannun nata amma yanajin wani iri,tun daga ranar da widad ta fuskanci me son lalle ne bata sake zama hannunta haka ba,hasalima bata rabo da sargen da take sawa yatsunta idan bata samu lallen ba,abinka da farar fata,mugun kyau yakeyi mata,wani zubin har tukuici sai ya ajjiye mata.
Duk da haka ya kama yatsun hannun nata yadan ja kadan yadda zata fahimci zancan yace
"Dani dake waye yafi wani laifi?,Allah da kansa fa cikin qur'ani yake cewa 'yaku wadanda kukayi imani,kada ku shiga gidajen da ba naku ba har sai kun nemi izini kunyi sallama akan ahalin gidan,wannan shine mafi alkhairi a gareku,idan ma baku samu kowa ba a cikinsu gidajen kada ku shiga har sai an muku izini,idan kuma akace ku koma ku koma' kinga anan kin sabawa koyarwar qur'ani da sunnah" tunda ya fara maganar ta zuba masa ido tana hawaye,yau gidanta ake cewa ba zata shiga duk inda taso ba saita nema izini saboda ya ajjiye wata
"Yanzu abbas gidana kake kafamin wadan nan sharuddan a kansa?"
"Ya salam"ya fada yana lumshe ido takaici yana kamashi,wacce irin qwaqwalwa take da ita,yana gaya mata Allah da annabi tana gaya masa molanka da son zuciyarta, kafin ya buda idanun ta dora
"A jikinka fa na sameta,ranar kwana na,kaci amanata kanason juya laifin kaina,wallahi sai yanzu na gane dalilin da ya sanya yarinyar nan ta fara rainani,kana raba mana kwana,kana duk abinda kakeyi dani da ita,tana shirme kana biye mata shi yasa take kallon kowa a banza.....". Tsam ys miqe
"Excuse me"ya fada a taqaice yana rabata ya wuce,don bazai iya ci gaba da daukar rainin hankalinta ba,kamar yadda ya fuskanci gaba daya ba zata taba gane abinda yake nufi ba.
Gaba daya ranar ta bata ta da kuka da takaici,taji a ranta ta riga ta gama yin sake,saidai har yanzu akwai sauran dama da zata nunawa yarinyar ita ba kanwar lasa bace.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 93
Widad kuwa sabgarta take a sassanta,don ko leqowa batayi ba bare ma su hadu,su mimi suna wajenta,sukaci lafiyayyen abincinta suka qoshi,daga qarshe ma bacci a nan ya dauki mimi,nawwara kawai ya dauka sanda yazo yi mata saida safe,tace yabar mata mimi din ta kwana a nan.
Uwar bata wani damu ba,a lokacin kawai kallon raguwar hidimarsu bisa wuyanta takeyi,bayan ta kwantar da nawwara ta cimmasa a bedroom,ya gama shirinsa cikin kayan bacci,sassanyan qamshinsa ya cika dakin,yana zaune yana amsa waya hankalinsa kwance,saita bude closet dinsa ta duba doguwar riga cikin kayan baccin da yakan ajjiye a dakin,ta tube rigar lace din jikinta ta aza kayanta tayi fuska,babu batun sake wanka,tunda dai an tsira da wankan safe,ta dawo ta zauna,lokaci lokaci tana kallonsa har ya gama wayar ya aje yana dubanta
"Ya akayi?" Ya fada yana kallonta, don yasan halinta,ungulu ce bata jewar banza,zaman da tayi lallai akwai magana a bakinta
"jari nake buqata ka bani,jari na yayi qasa" yana daga kwancen yake kallonta,ya rasa me takeyi da kudi,ashana baya barin mace ta siya masa,ko yaushe cikin tura mata kudi yakeyi,suttura har wardrobe dinta baya rufuwa saboda yawansu kuma gashi ba sanyawa akeyi ba,hakanan ba bayar dasu akeyi ba,bata taba cikakken sati ba tare data nema kudi a hannunsa ba,sai ya lumshe idonsa sannan yace
"Kamar nawa?"
"Fice hundred thousand only"
"Only?" Ya maimaita zancanta na qarshe,ba tare da ya jira amsarta ba yace
"Allah ya hore" wani kallo tayi masa sheqe qe,amfanin da zatayi da kudin ta gama kasafta zasu fita ne a jikinsa,don ba zata iya fiddasu daga cikin kudinta ba,amma zaizo mata da wannan zancan
"Allah ya hore,saidai idan ba zaka bayar bane?" Miqewa yayi ya zauna sosai yana kallonta cikin idanu
"Kullum me yasa babban burinki da jin dadinki ki kawo sabani a tsakaninmu?,me yasa zaman lafiya baya miki dadi?" Maganganunsa sai taji kamar gugar zana yake mata,take ta cika tayi fam ta fara zubda maganganu
"A hakanne banason zaman lafiya?,duk da tarin haqurin da nakeyi kai baka gani ba?,ina cewa makaranta ka maida waccan yarinyar kana kashe mata kudi,ko ka dauka bansan private ka kaita mai tsada ba?,itama taci kudinka ballantana ni,ita din da duka duka kwananta nawa a rayuwarka,duk kawaicina baka ganshi ba kenan tunda ni dama a wajenka babu abinda na iya na alkhairi"
Ido ya maida ya rufe kamar me shirin bacci,saidai ba baccin zaiyi ba,yana sauraren bugun zuciyarsa ne da duk bugawa take bugawar da zallar qaunar yarinyar tare da ambato sunanta,she means alort to him,batasan wace widad cikin rayuwarsa ba,yana dai qoqarin dannewa ne kawai,bai baiwa soyayayyarta kaso daya cikin goma damar fitowa ba saboda kada ya bada kafar barna ko baraka a tsakaninsu,a wannan yanayin yasan duk bayanin da zaiwa hafsat din a banza,ba zata fahimceshi ba sam,idan idanunta suja rufe kan abu kamar cin qwan makauniya,burinta kawai ayi mata abinda ranta yakeso,yana jinta tana ci gaba da zayyano dalilai marasa tushe bare makama,da ya gaji da jinta sai ya miqe tsam kawai ya dauki pillow ya yada a qasa ya kwana abinsa,abun da ya sake tunzurata kenan,ta miqe ta cire rigar baccin jikinta ta maida rigar lace dinta data cire,ta buda qofar tayi ficewarta,yadan bude idanunsa a hankali yabi bayanta da kallo harta fice,sai ya gyara kwanciyarsa yana rufe idanunsa,sam baiji wata damuwa ba don ta fita din,tun yana tunane tunane har bacci yayi gaba dashi.
A ranar kwanan kuka tayi ta godewa Allah,gaba daya tsanar widad ta gama cika mata zuciya,abubuwa da yawa basa faruwa saita sanadin zuwanta,gaba daya ta hargitsa mata gida ina dalili?,cikin ranta da zuciyarta takejin matakin data dauka shine dai dai, hukuncin data yanke kuma yayi dai dai,domin a yanzun babu wani abu da zai saurin sadata zuwa ga cimma burinta idan ba ta wannan hanyar ta biyo ba.
Washegari widad din ta shirya ita dasu mimi,tun da safe tayi musu wanka,ta cire kaya cikin wadanda abbas a taho musu dashi ya manta su cikin kayanta tayi musu kwalliya da kyau suka wuce gidan hajiya.
Taji dadin ganinsu matuqa,ta rasa inda zata sanyasu,a nan akayi mata jan lalle har bayan hannunta,hatta hajiya sai data yaba, idanunta na buye da Widad din tana ji a ranta anya ba juna biyu widad din ke dashi ba?, quruciya ta hanata ganewa,shi kuma uban gayyar hankalinsa baikai ba?,amma da yake hajiyan bata cika sanya baki a lamuran surukanta ba duk da tana jin widad sosai cikin ranta,kamar diyar data haifa a cikinta,duk da haka sai tayi shuru,cikin ranta ta bisu da addu'a.
Da yamma tace masa zata koma taje tayi girki,suna shirin tafiya sai gashi,tayi mamaki don bata tsammaci zaizo ya dauketa ba,haka kawai yaji duka gidan babu dadi bayan fitarsu,amma hakanan dai ya daure suka wuni da giwar tasa a haka😂,duk da babu abinda ya tsinta a zaman,don gaba daya babu fara'ar arziqi a tattare da ita bare hirar arziqi,to dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka?.
Tunda ya shigo shima yake binta da kallo,lallen ya sake fito da ita sosai,ya kasa daurewa har sai daya bita kitchen yasha dumin jikinta sannan ya samu nutsuwa,suka tattare sukabar gidan hajiyan suka wuce gida.
Tare yau sukayi girki kamar yadda suka saba a Kaduna,gaba daya yau sai takejin kasala,har yana tsokanarta
"Kindaiyi qiba baby kawai" saita hau bubbuga qafa
"Niba wata qiba,Allah banaso" dariya mai taushi ya saki,ya dauketa cak ya dorata saman kantar kitchen din
"Ni kuwa bakiga yadda kikayimin kyau ba,komai ya fito yadda nakeso.....fiye ma da yadda nakeso,sannan kin qara dad......." Hannu tasa ta toshe masa baki,don tasan qaarshen zancan,kalmar tana matuqar bata kunya,amma taga shi kansa tsaye yake fadarta.
A daren ya same tantancewa,ya kuma sake nutsuwa da gamsuwa da cewa Allah ne kawai ya dubi zuciyarsa ya bashi widad din a lokacin da bai shirya ba,zuciyarsa kuma bata taba kawo masa ya aikata hakan ba.
*W A S H E G A R I*
Tunda sukayi sallar asuba tace masa tana son zuwa saloon,daga can zata wuce gidan uncle muhsin,kallonta yayi
"Baby.....salon yawo ko?,kinsan banason kina yawan fita,jiya me yasa baki gayamin an hada duka ba?" Kai ta langabe gefe,kwata kwata batason zaman gidan,sannan haka kawai takejin haushin hafsat duk sanda ta kalleta,shi yasa batason ma hada waje da ita,bare yau tasan can zai kwana,may be tana kallonsa zaua tafi can ya barta ita kadai a sassanta,sai mimi dake tayata kwana,ta narke fuska
"Don Allah uncle,na dade fa banje ba" ido yadan zuba mata,sai kuma yadan saki murmushi
"Shikenan" qanqameshi tayi tana fadin
"Thank you uncle" ido ya lumshe yana murmushi,jikinsa na amsawa saboda yadda ta manna masa jikinta sosai,hannunsa yasa ya dagota yana duban qwayar idonta,kamar me rada yace mata
"In dan qara?" zamewa tayi tana dariya hadi da boye fuskarta cikin hijabinta,duk sanda ya buqaci kadaicewa da ita a fargaba yake sakata,har yanzun bata saba da abun nan ba
"Ni uncle....banason nayi ciki,mutuwa zanyi idan nayi ciki fa" ta fada a shagwabe,tattausan hannunta ya kamo ya riqe,duk da qarancin shekarunta amma yasan tana da matuqar juriya dashi,shi kansa baisan me yasa baya gajiya da ita ba
"Bana gaya miki ba wannan abun ne yake sawa a samu ciki ba?,sai kinsha ruwa kin qoshi sosai idan aka gama shine ake samun ciki" kai ta gyada a hankali alamun gamsuwa,ya bita da kallo can qasan ransa yana danne dariyar daketa cinsa,yana mamakin yadda ta yadda da wannan dabarar daya shirya mata,quruciyarta tana bala'in tafiya dashi,wani abune da yake kallonsa na musamman tattare da ita,don tana debe masa damuwa sosai,tana barinsa a nishadi duk sanda ta tafka wani babbar wautar da quruciyar.
Tada da himma sosai,duk da tana danjin kasala da nauyin jiki amma sai data gama gyara gidan tsaf,ta shirya breakfast sannan sukayi wanka,tare suke wanka daman,indai ba wani babban uzurin fita bane ya taso masa,wannan yasa suka gama da wuri ya rigata fita parlor ya fara yin break din,ita kuma tana ciki tana qarasa shiryawa.
Cikin baqa wul din abaya mai wani irin aiki da stones masu sheqi ta shirya,wani irin kyau tayi mai daukar hankali saboda yadda abayar tabi lafiyayyar farar fatarta ta kwanta da kyau,ita kanta sai data kalli kanta har sau babu adadi,ta juya gaba da baya sannan ta rola mayafin sama kanta,ta dauki wata 'yar mitsitsiyar hand bag mai hade da takalmi ta jefa wayarta a ciki sannan ta fito.
Mug din da yayi niyyar kaiwa bakinsa ya sauke,ya bita da kallo tamkar yau idanuwansa suka saba ganinta
"Ma sha Allah!" Ya furta yana kallonta,yana ji kamar ya buda zuciyarsa ya sanyata ya huta da radadin sonta da yake ji.
Sama sama tayi break din,yanata tsokanarta da zumudin zuwa gidan uncle ya hanata cin abinci,suka fito tare
"Bari na sallami antynki" ya fada yana buda mata motar ta shiga,sannan ya wuce sasssn hafsat din,tadan bishi da kallo saita dauke kanta zuwa gaban motar,ta jawo wani littafi ta soma buda shafukansa don ta ragewa kanta damuwar da take ta ji,da kuma wata irin faduwar gaba data tashi da ita tun dazun da safe.
Suna zaune da yaran suna breakfast suma,wanda ba komai bane sai ruwan tea da tsurar bread,ya dauki yaran ya musu wasa yayi kissing dinsu sannan ya ajjiyesu,ta gaidashi fuska a cunkushe ya amsa mata,har batason kallonsa musamman idan ta tuna daga inda ya fito,wajen waye ya kwana,ya ajjiye mata kudi yadda ya saba,zai fita mimi tace ya tsayata zata gurin anty weedad
"Antynku fita zatayi" jin haka yasa hafsat din tasha jinin jikinta kan tare zasu fita,don haka ta miqe sa nufin masa rakiya,abun yadan bashi mamaki don ba sabonta bane,amma.bai hanata ba,suka jero tare suka fito.
Cikin jikinta taji kamar yana tahowa,ta daga kai sai ta hangosu a jere da juna,tashin farko taji wani abu ya tsaya mata a wuya ganin yadda suka jera din,ta maida dubanta kan fuskar hafsat din,wani haushinta ya cikata,saita dauke kanta ta mayar kan littafin tayi kamar bata gansu ba.
Har suka iso wajen idanun hafsat din na kan widad,wani irin zafi me tsanani takeji a ranta game da yarinyar,kyan da tayi ya tsaya mata a rai,ta fito sakkk balarabiya,to amma tana samun sassauci ta wani fannin idan ta tuna gab take da yin maganin matsalarta,kowanne lokaci ne daga yanzu,don haka tayi masa a dawo lafiya tan juya zuwa ciki ranta yana mata suya da yadda yarinyar ta nuna halin ko in kula da ita,gaisuwar ma da take mata yau bata sameta ba,lallai ta yarda raini ne yake ci gaba da tsirowa a tsakaninsu,sai kuma ta saki wani irin murmushi tana jan qwafa
"Zakisan ni ban sa'ar yinki bace yarinya" ta furta tana shigewa sassanta.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 94
Tunda ta isa gidan uncle muhsin sai ta sake sosai abinta cikinsu nujood,bayan sun gama hira da hajjaa a kebance,ta tabbatar babu sauran abinda yake damunta,saidai lokaci lokaci gabanta yana yawaita faduwa,saita tsaya da abinda takeyi idan ya lafa kuma taci gaba da sabgarta.
Da yamma ya kira ta yaji kota wuce saloon din,tace eh gata ita da nujood sun fito zata rakata,abun mamakin saita taddashi acan,zaune cikin mota yana jiran isowarsu.
"Gaskiya gaskiya nima cewa abban zanyi ko ya samo min police na aura,ko ya samomin cikin abokansa,irin wannan kulawa widad ba kowacce mace ke samun irinta ba,just saloon ma sai an miki rakiya ko anzo an jiraki harki gama a maidaki gida don kada ki shiga motar haya?" Idanun widad din akan abbas din sanda nujood ke maganar,duk da basu qarasa ba suna kusa da qarasawar amma idanun kowa yana kan dan uwansa,saita saki murmushi kawai ba tare data amsawa nujood ba, saidai can qasan ranta ita kadai tasan ya takeji akan uncle din nata,har wani lokacin takan zauna tace wai shin wa tafi ji dashi,wa tafi so tsakanin shi ummu ko mommynta?(quruci dangin hauka,kowanne so akwai kalarshi,na iyaye daban na miji daban).
Fitowa yayi ya taka mata har zuwa bakin qofar wajen,sannan ya gaya mata abinda ya saba fadi
"Ki fada mata tayi miki mai kyau,irin wanda ba'a taba yiwa kowacce mace ba" dariya ta kamata itama kamar kullum,shidai yanason gayun nan,yana son kwalliya,duk sonta da kwalliya ta samu wanda ya fita,tana murmushi ta shige,yayin da nujood ta rigata yin gaba tana jin kunya,saboda tamkar mahaifi take kallonsa.
Sanda aka gama sai suka sauke nujood a gida,bayan ya bata kyautar dubu biyar,ta shiga ta yiwa hajjaa sallama,wadda ta hada mata kayan miya,kamansu kuka daddawa kubewa mai kyau da sauransu, saboda itama tasan abas din dason wannan cimar na gargajiya,tayi musu sallama ta fito.
Suna tafe a hanya suna hira,duk da uncle din nata shine jigon hirar,kadan kadan take saka baki,saboda yadda faduwar gabanta take qara yawa fiye da dazu,a wani shopping mall ya tsaya yana dubanta
"Zaki rakani?" Ya fada a tausashe,ta sake masa murmushi tana ajjiye jakarta ta fito tabi bayansa.
Tana biye dashi ne kawai,shi ya dinga daukan kalar kayan da yakeso,wanda duka qananun kaya,irinsu mini skert leggings shirt shirt na masu daukan hankali da kuma lalatattun sleeping wears,kusan wannan din al'adarsa ce,yanason wannan shigar a wajen matarsa,a lokacin da hafsa kadai yake da ita,duk sanda yayi siyayya irin wannan asarar kudinsa kawai yakeyi,don ba sakawa takeyi ba,a yanzun kuwa kusan tare suke zabar kayan da zata saka masa duk rana shi da widad din,musamman idan suna Kaduna,sai wanda ya zaba zata saka masa,bata wani damuwa saboda kayan sunfi mata dadin sakawa a yanzun,idan tana cikin gida zaiyi wuya ka ganta da atamfa bare lace ko shadda,kayanta kenan,wani mugun kyau kuma sukeyi mata,bama kamar idan ta raba gashinta biyu,kota musu manyan kalba,yakan lalace wajen kallonta ne,itakam da batajin nauyin jikinta tayita tsalle tsallenta abinta.
Chocolate ya hada dasu masu dan yawa saboda su mimi ya biya kudin suka fito,ya miqa mata ledojin yana cewa sanda yake shirin kunna motar
"Ta kayan taki ce,ta chocolate kuma ta sha zumamu mimi ce" qaramar dariya tadanyi, tanason zaqi kam yarinyar,sai ta buda ledar kayan nata tana diban wasu tana zubawa a ledar su mimi,yadan kalleta yana yin reverse
"Me kikeyi haka?"
"Mommyn mimi na sakawa wasu kayan,baka siya da ita ba,naga kudin da yawa" kai ya girgiza suna haurawa kwalta
"Kinason kiyimin asarar kudina na kawai....." Sai kuma yayi shuru ba tare daya qarasa ba,sannan ya sake cewa
"Duka naki ne,jibi nakeson ki zaba me kyau a ciki.....wadda tafi kowacce kyau ki sakamin,ita kuma duk sanda muka fita ko tace tanaso saina siya mata nata daban" bata kawo komai cikin kanta ba ta gyara ledar ta mayar dasu yadda suke.
Ana kiran magariba suka isa gida,wasu masallatan ma har sun tayar,ya kashe motar ya rakota,gudun kada sallar ta qwace masa saiya tsaya daga qofar falonta ta bude ta shiga shi kuma ya koma da dan sauri don ya riski sallar.
Duhu falon saboda ta kashe dukka qwayaye kafin ta fita,tana tsoma qafarta gabanta yayi mummunar faduwar da har sai data dora hannunta a qirjinta,wani irin mahaukacin tsoro ya saukar mata,saita saka hannu tayi hanzarin kunna wutar sassan nata.
Duk da haske ya wadaci wajen amma abinda ya gushe na tsoron daya saukar mata din bashi da yawa,ta fara takawa a hankali kamar mai sanda ta nufi dakinta,duk inda ta tsoma qafarta ta dauke sai taji kamar ana biye da ita,wannan ya sakata qara hanzari,ta fada dakinta ta tura qofar tayi zaune bakin gado tana wuwwurga idonta cikin dakin,cikin sa'a bakinta ya kama kalmar
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil,ni'imal maula wa ni'iman nasir" sannu a hankali saita fara jin tsoron yana raguwa,ta rufe idonta tayita maimaitawa kafin ta bude idon a hankali,sai taji tadan samu nutsuwa,ta ajjiye ledar da mugun takatsantsan saboda qarar ledar tana jinta har cikin kanta,ta cire mayafinta ta shige bandaki tana fatan mimi ta shigo mata ko ta rage zaman shurun.
Alwalar data yo ta qara mata nutsuwa,ta dawo ta tayar da sallah,sanda ta idar sai tayi zaune saman abun sallar,gidan shuru ba motsin kowa,sai qarar babban generator dake aiki a farfajiyar gidan,yana daya daga cikin abinda yasa ta tsani bauchin,wannan zaman,inda a kaduna suke da yanzun tana jikin uncle dinta,suna karatu k suna wani abun tare,komai ma tare sukeyi ita dashi,ba wani abu da suke rabawa,kama daga wanka bacci cin abinci,sallar ma wataran jam'i sukeyi ita dashi,ya tsefe mata kai ya yanke mata farce,wani zubin ma har ya gwada mata kalba,amma a bauchi fa,duka time dinsa yana rabasu ne a tsakaninsu.
Tana nan zaune har akayi kiran isha'i ta tashi ta gabatar,ta sake komawa ta zauna,tun yamma rabonta da abinci,amma kuma bata jin yunwa,batasan me yake damunta ba,wani lokacin ta tashi da mahaukaciyar yunwa,wani lokacin kuma ta tashi bata sha'awar cin komai,duk da haka dole ta tashi ta shiga kitchen bayan ta leqa window ko zataga wulgawar mimi amma ba ita ba alamarta,ta tsaya ta dafa indomie guda daya ta soya qwai biyu,tana yi tana takatsantsan,duk duk wani motsi da zatayi da kwanukan firgita takeyi,tana gamawa ta dawo daki ta zauna ta tasa abincin a gaba.
Tana fara ci taji bataso,saita ture plate din,zuciyarta na mata wani qunci,kawai sai ta fashe da kuka sosai tana curewa waje daya,gidan gaba daya ya fice mata akai.
Yana zaune da wayarsa a hannu yana amsa saqonni,su mimi na gefe suna wasansu,yayin da hafsat din ke hada masa abincin dare
"Yau ba zuwa wajen anty mimi?" Ya tambayi yarinyar yana aje wayarsa bayan hafsat din tace ta gama zubawar
"A wajen mahaifiyarta zata kwana" hafsat dake shirin zama tayi caraf da maganar,duba daya yayi mata ya kauda kansa gun yaran yana gayyatarsu suzo suci abinci,kusan al'adarsa ce wannan,tunda mamarsu bata iya cin abinci dashi ba,tare dasu yake cin abinsa,tun bai saba ba har ya zame masa jiki.
Tana daga zaune a gefensu,bata ce komai ba,suna cin abincin suna hirar su da yaransa yana dariya abinsa,abinda yake sake qule hafsat kenan,sai abu mai ciwo ya faru,tana ganin abun yakai munzalin bacin rai,amma sai yasa yaransa a gaba suyita sabgarsu,taja qwafa can qasa tana jijjiga kai,idan komai bai faru ba ashe bata cika hafsatu ba.
Suna gama cin abincin ta kada kan yaran zuwa dakinsu,basa jin bacci a sannan amma haka ta tilasta musu kwanciya,ya fahimci me take nufi,bayason suje wajen widad din,sai shima ya watsar da ita,ya wuce toilet yayi wanka hade da brush,ya shirya cikin wasu silk pyjama sky blue,ya dauki wayarsa ya wuce sassan widad din don ya mata sallama,ta bishi da harara ba tare da yasan me takeyi ba,cikin ranta fana fadin
"Na kusa maganin matsalata naga qarshen wannan rawar kan".
Tun kafin ya qarasa yaji ya qagu ya isa din,ya buda qofar da sallama a bakinsa,yadda yaga falon komai a kashe yasan tayi shirin kwanciya ne,don haka ya zarce bedroom dinta kai tsaye.
Buda qofar da taji anyi har tsakiyar kanta,ta zabura ta daga kanta da sauri hantar cikinta na kadawa,wani mugun tsoro yana mamayarta,suna hada ido ta miqe da sassarfa ta isa gareshi hadi da fadawa jikinsa ta rushe da kuka
"Ya salam......ya Allah" ya furta a tausashe hannunsa a bayanta yana dan bubbugawa
"Menene baby?,mene?" Ya tambayeta yana sunkuya dai dai fuskarta,hucin bakinsa dake bada qamshin blueberry mouth spray yana sauka saman fuskartata,saita cusa kanta wuyansa tana sake sakin wasu hawayen.
"Tom,abun ya motsa kenan" ya fadi can qasan zuciyarsa yana dan sakin murmushi,ya riqeta sosai suka koma gaban gadon suka zube a qasa,ya sanyata a jikinsa yana sake lallashinta.
Sun jima a haka sannan ya samu ta tsagaita kukan,ya zaunar da ita sosai saman qafafunsa yana kallon fuskarta da tayi jajur saboda kuka
"Me ya faru?" Sai tayi masa narai narai da ido xata sake sake masa kuka,yayi saurin cewa
"Noo....ya isa, kinci abinci?" Sai sannan ta maida dubanta ga abincin data zuba din,shima ya tayata kalla,yasa hannu ya jawo plate din ya motsa abincin yana kallon qwayar idanunta
"Zakici wannan din ko na canza miki wani?" Kai ta girgiza alamun zata cin,ya sake daukan cokalin ya fara diba a hankali tana zaune saman qafafunsa yana bata hadi da sako mata irin hirar da yasan zata sanyata ta sake.
Babu laifi tadan sake din,don kafin ya gama bata tana murmushi,duk da qasan ranta wani irin tsoro ne keta mata tasiri,bayan ta gama ya tabbatar ta kammala komai na kwanciya,yayi tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa yana kallonta
"Shikenan?,saida safe?" Kanta ta kawar gefe,tana jin ranta ya motsu,yanzun tafiya zaiyi wajen mummyn mimi,saita gyada masa kai a sanyaye,sannan tace
"Mimi ba zatazo tayani kwanan ba?" Dan jim yayi kafin ya amsa
"Sun wuce dakinsu kafin na fito,don't worry ki kwamta ki rufe idonki,yanzun nan zakiga safiya tayi, okay?" Saita gyada masa aki a hankali,tausayinta sosai yaji,yasan ko yaya batason rabuwa dashi,bare yanzun data saba da zama jikinsa kamar wata 'yar mage,ya sunkuya a tausashe yayi kissing dinta,ya juya zai kashe mata hasken dakin tace
"Ka bari zan kashe" don batason duhun da zata zauna a ciki kafin bacci ya dauketa
"Okay" ya furta can qasan maqoshi,ya juya a hankali ya fice a dakin yana waigenta.
Idonta ta mayar ta lumshe tana jin ficewarsa,wani abu na tsaya mata a wuya,ta gwammace taci gaba da barin idon a rufe maimakon ta bude ta kalli hanyar da yabi ya fice din.
Cikin mintunan da basufi qwaya biyu ba taji yanayin dakin ya fara sauyawa,kamar komai na dakin motsi yakeyi,ciki harda kujerar data kwanta a kan,zuciyarta tayi mugun bugawa, madaukakin tsoro ya mamayeta,kafin takai ga bude idanunta taji dukka wata gaba ta jikinta tayi nauyi,kamar wadda DANNAU ya danneta,ta kasa motsa koda dan yatsanta bare tayi yunqurin tashi daga inda take kwance..........
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 95
Tayita qoqarin motsa wata gaba ta jikinta amma ta kasa,wata mummunar shaqa taji an yiwa wuyanta,abinda ya sabbaba mata numfashinta ya soma wahalar fita kenan,cikin gigita firgici da kuma tsoro ta soma bude idanunta a hankali tanason ganin waye a dakin?,waye yayi mata wannan aikin.
Wayam......babu kowa a dakin,daga ita sai kayan gado labulaye zuwa frames a dakin.
Idanunta ta wulga gefe,sai ya sauka ga bangon dakin da take fuskanta,wani irin motsi taga yana yi,yana kuma darewa a hankali,wani dogon hannu yana ratsowa har zuwa inda take kwancen,ta motsa bakinta da nufin addu'a amma komai ya gaza fita,idanun nata yana kan hannun da yaci gaba da ratsa bangon dakin yana qara shigowa hadi da ci gaba da shaqe mata wuya.
Ci gaba tayi da kokawa da numfashinta tare da qoqarin ganin ta kira sunan Allah,tsahon wasu mintuna kafin ta samu ta fusgo addu'a da qarfi daga bakinta
"Ya Allah..... innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fada da qarfi,kalmar da tayi sanadiyyar yankewar komai,jikinta ya sake, bangon dakin ya koma dai dai,motsin da dakin yakeyi ya tsaya cak,ta miqe da mugun hanzari,ta nufi qofar dakin da gudu tana sake kiran sunan Allah da mabanbantan sunaye.
Kai tsaye ta fada dakin abbas din ta maida qofar ta rufe sannan ta zube a wajen tana tokare bayanta da qofar kamar me shirin hanawa wani shigowa dakin,ya sulale ta zube a wajen tana riqe da wuyanta,saita fara karanta ayatul kursiyyu da qarfi,ko ina na jikinta yana wani irin rawa kamar me shirin ficewa daga hayyacinta.
Ta jima a wannan yanayin tana karanta ayatul kursiyyu da dukkan addu'ar tsari da tazo bakinta,har sai da dukka yawun bakinta ya dauke,Allah ya saukar mata da wata nutsuwa,saidai har yanzu jikinta rawa yakeyi,tsoron dake tattare da ita ya ragu sosai,saidai a firgice take qwarai da gaske.
Kusan awa guda kenan kafin ta samu kuka yazo mata,ta tattare guri daya cikin wani irin yanayi na tashin hankali,tana jinta ne tamakar a tsakiyar wani daji da babu gida gaba babu gida baya,ita daya qwal a sashen,ta ina zata iya fita tabar sassan?,ta baro wayarta a dakin da batajin zata iya taka koda qofar dakin ne bare tayi kiran abbas,cikin wannan yanayin taci gaba da zama a bakin qofar dakin,rabi kuka rabi addu'a,a haka ta qare darenta tsaf a zaune dungurgur har aka kirayi sallar asuba.
A jikinsa ya dinga jin tunaninsa ya karkata a kanta,don haka ana idar da sallar asuba ya baro masallaci ya wuce sassanta.
Kamar numfashinta zai tsaya haka taji sanda taji motsi yana buda sassan nata da key dinsa,ta qanqame jikinta guri daya tana sakin kuka sosai tana kiran sunan Allah,har ya buda ya shigo falon ya kuma duba dakinta bai ganta ba tana zaune a wajen ta kasa motsawa,mamaki ya cikashi ganin har bandaki ya duba,babu ma alamun ta shiga,don a bushe bandakin yake,sai tunaninsa ya bashi ya duba dakinsa,don haka ya fito ya nufi qofar dakin.
Daya murda handle din yaji alamun a kulle take sai hankalinsa yadan kwanta,cikin ransa yana murmushin ya akayi ta canza daki ta koma nasa dakin?,sai ya gyara tsaiwarsa yana rayawa a ransa lallai yau zaiyi mata tsiya.
Knocking yayi,widad dake zaune jikin qofar ta runtse idanunta tana jin kamar numfashinta zai dauke,ya sake qwanqwasawa murya can qasa ya kirayi sunanta,abinda ya bata qwarin gwiwar miqewa da hanzari ta bude qofar,batayi wata wata ba ta fada jikinsa,ya tareta da sauri cikin mamaki da tashin hankalin jin irin kukan data fashe dashi.
A rude yake ta jero mata tambayar me ya sameta?,me ya faru?,menene?,amma ta gaza amsa masa tambaya ko guda daya,sai sake riqeshi da tayi da kyau kamar mai tsoron kada ya subuce mata,a haka tana jikinsa ya jata zasu koma dakin amma ta turje taqi,dole sai parlor suka dawo saman kujerar tana kwance a jikinsa tana gurzar kuka.
Kusan minti talatin suna a haka sanann ya soma lallabarta,yace tayi sallah?,tace a'ah
"Kije kiyi sallah sai kizo ki gayamin abinda ya faru" ko motsawa daga jikinsa qi tayi,sai a sannan ya sake experiencing tsoron dake tattare da ita,mamakin abinda ya haifar da irin wannan tsoron daga wajenta ya saukar mishi,duk da ya sani ita din matsoraciya ce,to amma tsoron nata baikai haka ba,hasalima ta fara sabawa da gidan,ta rage tsoron sosai.
Sai shine da kansa ya rakata bandakin ya kuma tsaya tayi alwalar ta kuma yi sallar,ta hanashi motsawa ko ina,tana kwance a jikinsa wani irin zazzabi ya fara saukarwa jikinta,dole yaja duvet ya lullubesu ita dashi, hankalinsa gaba daya ya tashi,gashi tambayar duniya ta gaza ce masa komai,sai dan uban kukan da take masa..
Wani irin tsoro ke dawainiya da ita shi yasa ta kasa gaya masa,tana ji kamar idan ta fada masa abun zai sake dawo mata,don haka ta kasa cewa komai sai kukan,hankalinsa dukka a tashe yake,yayi lallashin duniya tayi shuru tunsa taqi fadin abinda ya faru amma ta kasa yin shurun,sai hawaye da taketa fitarwa,a haka har rana ta fara fitowa tana kwance a jikinsa saman gadon,a haka yayi azkar dinsa yana duban fuskarta wadda a sannan bacci ya fara fusgarta,wani irin zazzabi yana sake lullubeta.
A hankali bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,sai a sannan ya samu ya zare jikinsa ya tula mata pillows yadda zata tsammaci shine,ya miqe ya soma bincike gidan wai ko wani abun ta gani,tun daga dakinsa zuwa nata dakin,bandakunansu qasan gado kitchen ventilation dinta dako ina amma baiga komai ba,dole ya haqura ya wuce kitchen ya hada ruwan zafi yasha zuciyarsa cike da wasu wasi da tunane tunane.
Sanda ta farka zazzabin ya riga yayi qarfi a jikinta,dole ya zare mata rigar jikinta ya jiqa towel ya soma rage mata qarfin zazzabin,ba yadda bai lallabata tayi wanka ya kaita taga likita ba amma taqi,yace zai kira Dr gida nan ma tace bataso,sai kukan da taketa masa,wanda ya qarasa rudashi gaba daya.
Ta bangaren hafsa hankali kwance take hidimarta,ta gama shirya breakfast suka ci abinsu da yara,tana ta kai kawo tsakanin falonta zuwa farfajiyar gidan hankalinta na sassan widad din,har sha daya na rana bataji motsinsu ba,don ta tabbatar yana sassan widad din,tunda ga motarsa ba fita yayi ba,saita koma ciki ta dauki wayarta tayi kiransa.
A lokacin ya sanya widad din a gaba yana bata tea,da qyar take karba sai sharar hawaye take,sai da yayi da gasken ma ya samu take amsa din
"Naji shuru daga sallah baka dawo ba,ga kuma break dinka" ido ya lumshe yana jin zuciyarsa babu nutsuwa gaba daya,a yanzun ma shi baijin wata yunwa,bare ma yasan ba wani break din arziqi ta tanada ba,idan tayi wutar duniya......ta qure adaka ta soya chips da fried egg
"Ina cikin gidan,widad ce bata jin dadi" baki ta tabe,ranta fes ba tare da taji wani abu ya dameta ba
"Inason fita ne,umma bata jin dadi xanje na duba jikinta"
"Ki gaisheta" kawai ya fada a taqaice ya katse wayar,yasan dama kiran bawai don baici abincin bane main purpose ba,ya ajjiye wayar gefansa ya sake maida hankalinsa ga widad din.
Ido ya zuba mata,gaba daya dare daya duka ta fada ta birkice masa,ya lumshe ido yana jin wani abu yana taba ransa
"Me ya faru baby..... please tell me ko raina zai nutsu" kamar ko yaushe sai hawaye suka fara taruwa,ya tareta da sauri
"Ya isa, shikenan" ya miqa mug din bakinta yana cewa
"Qarasa shanye wannan" cikin ransa yana tunanin yadda zai lallabata taga likita,bazai iya zama yana ganin uban zazzabin nan a jikinta ba.
Wayarsa ta sake qara,sai yaga hafsat ce,ya sake daga wayar ya sakata a handsfree
"Na tura mimi ka bata kudin mai zan saka mai a motata" takaici ya cikashi,ya lumshe idanunsa yana qoqarin hadiye bacin ransa
"Kada tazo,ba kudi a jikina,kije zan tura miki ta account idan kinje gidan man kya basu ATM dinki su cira"
"Tom" ta fada hankalinta kwance yana ajjiye wayar,ko kunya sam.bataji ba,ita dashi duka sun dani full tank yakewa motar tata,bama motarta kadai ba,hatta motar da zaya bari a gida idan zai koma kaduna.baya barinta haka,yaja qaramin tsaki qasan ransa yana fadin
"Astagfirullah" sau tari idan hafsat din tayi masa abu,sai yaga istigfari kawai ya dace yayi,wala'alla yayi wani laifi ma Allah ne daya kasa gane me ya aikata din.
Wunin ranar gaba daya tana maqale a jikinsa,duk inda zai motsa zata bishi,kwata kwata tsoron gidan ya kamata matuqa da gaske,tana jin kamar ta bude ido ta ganta a kaduna,ga zazzabin da ya hanata sukuni wunun ranar,taqi yarda kuma taga likita sam,sai gige mata jiki daya dinga yi da ruwa mai sanyi,ya bata paracetamol tasha sannan aka samu sassaucin sa,sai daga baya ya sake dawowa.
zuwa dare ta dinga masa kuka saboda yadda wata muguwar tsanar gidan ta shigeta,ta dinga kuka sai sun koma kaduna,ba shiri cikin daren ya soma hada musu kayansu,bai kwanta ba sai daya gama shirin tafiyar tasu.
Da safen ta tashi da 'yar walwalarta saboda jin zasu tafi,kafin ya gama nasa shirin ita tuni ta gama,sanda ya kammala shiryawar kuwa zaije ya sallami su hafsat farfajiyar gidan ta fito ta zauna tana jiransa,sam bata doshi wajen hafsat din ba,haushinta takeji musamman duk sanda zasu kebe da uncle din nata,ko zata ganta kusa dashi,idan wani abu ya kawo ga ta tabashi kuwa saidai tabar wajen tana goge qwalla,ita kanta batasan manufar hakan ba,batasan kuma abinda yake kawo mata jin hakan a zuciyarta ba (kishi😄, Allah sarki,quruci dangin hauka,ta fara kishin uncle din nata ba tare data sani ba).
Tana tsaye daga bakin window din falonta tana hangensu sanda ya gama sallamarta ya fice,bayan ta gama mita da qorafin akwai sauran kwana daya daya rage ai bai cika shi ba,bai biyewa qorafin ta ba,don koma yaya yayi dai sai ta yishi,ya zama kamar cikin jininta abun yake.
Murmushi ta sauke sanda suka fice din,cikin wata walwala da jin dadi ta fada saman kujera tana tunano abubuwa masu yawa a zuciyarta,lallai a baya ita taso har aka kai wannan matsayin ma da ake kai yanzu kamar yadda ummanta ta gaya mata,ashe wannan hanyar itace hanya mafi sauqi da sauri ta maganin matsalar ta ta tsaya tana biyewa hasashe da hanyoyin anty ummee masu tsauri?.
Assalamualaikum
Yanzu an wuce lokacin da za'a dinga novel na qaryar soyayya tsura kawai a ciki da uban tarin dukiya daga qasa zuwa qasa,dole mu fuskanci reality na abubuwan da suke faruwa yanzu suke damunmu,akwai darasi sosai da nakeso mu cimma cikin labarin nan,kuyi haquri muje harmu cimma gaci
Sannan tun asali duk wanda ya sanni labaraina ba gajeru bane,daga bayan nan ne nake gajeru,to wanann salon labarin yazo a haka ne,sanann raguwar tsahon pages din yasa numbers din sukayi yawa,amma in sha Allah i will try my best naga pages din sun dan qara tsaho ta yadda numbers din zasu ragu, thanks for choosing me.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*
Page 96
Wata wawiyar ajiyar zuciya ta saki tana samun nutsuwar ruhi da gangar jiki sanda taga sun dauki hanyar kaduna,duk da jikinta babu wani qwari sosai saboda zazzabin daya gallabeta,amma at least ta samu wani sassaucin.
Dan waiwayo yayi kadan ya dubeta,sannan ya cire hannunsa guda daya daga kan motar ya kama dogon hancinta yadan ja
"Hankalinki ya kwanta ko?" Saita sakar masa murmushi, murmushin da yayi masifar kewarsa,yaketa kuma struggling na ganin tayi shin amma bai sameshi ba sai yau.
Tun basuyi nisa ba ta soma bacci,wani irin nannauyan bacci da shi kansa abbas din ya dinga kallonta,ko sau daya baiyi.marmarin tashinta ba,baccin ma datayin dadi yayi masa,aqalla yasan zata rama bashin baccin da batyi ba kwana biyu,sai ya kunna radio station yana sauraren labarai,da sauran programs da suka jibanci harkokin tsaro,da ya gaji ya maida karatun qur'ani,wanda ya qarawa baccinta dadi sosai,baccin da bata farka ba sai da suka isa kaduna.
Tun daga wannan ranar bata sake binsa bauchi ba,don ko cewa yayi zasu weekend yanzu zata rage walwala,gaba daya garin ya fita a ranta,shima bai takurawa, don asalinsa ba mutum bane mai takura da tsanani akan abu bane,sai ya barta yaje yayi kwana biyu ya dawo,har kusan watanni uku.
Cikin hakan bikin diyar yaaya bara'atu ya taso,ya gaya mata,duk da bataso amma ta gaza nuna masa,yana da tsananin kirki da karamci,yana mata kyautatawar da duk duniya baya ga ummu bata ganta a wajen kowa ba,wannan ya sanya duk wani abu da tasan bayaso ko zaiji babu dadi take nisantarsa(bawai don tasan muhimmancin hakan ba,kawai saboda yadda kyautatawarsa taje da nauyi a idanunta).
Kaya ta fitar ta bayar akayi mata dinkuna masu kyau, zuciyarta duka babu dadi,cike da tsanar bauchin amma haka ta dinga shirya,duk da tana boyewar amma ya karanci akwai abinda ke faruwa,don kuzarinta ya ragu,a sanyaye take komai.
Ana gobe zasu tafi da daddare,yana zaune kan sofa bed yana shan black tea din data hada masa ita kuma tana rufe wata qaramar jakarta data zuba qananun abubuwan amfaninsa da tasan zai buqata,duk inda ta gifta idanunsa yana biye da ita,baya gajiya da kallonta,barin yau din da tayi kwalliya ciki wani mini skert da wata riga da sukayi matuqar karbarta,zuwa lokacin komai nata ya cika yayi yadda akeso ya zamana a jikin diya mace,ta zama wata 'yar duma duma da ita,haske da laushin fatarta ya qaru,hakanan tsahon gashinta cikarsa dama baqinta,lips dinta ya qara zama pink sosai haka idanunta sun sake fitowa,ta fannin mu'amalarsu ya sake zama wani mayenta,shi kansa baisan yadda akayi ya sake horancewa ba,baiqi duka dare ya dinga kasancewa da ita ba,baya gajiya da ita,wata baiwa ke gareta ta musamman mai dimauta tunanin mutum,saidai widad din tashi har yanzu raguwa ce,batayi qwarewar da yakeso tayi ba,kullum hakan ta kasance sai yayi zaman lallashi,shagwabarta da sangarta take zube masa,shima sai ya biye mata.
Ajjiye mug din hannunsa yayi yana fakon isowarta,aikuwa tana zuwa giftashi ya sanya hannu ya fincikota jikinsa,yayi mata kyakkyawan masauki saman cinyarsa dake bayyane a waje cike da gargasa,hannuwansa ya saka ya zagaye qugunta dasu ya sake matso da ita sosai,ya saka fuskarsa a tsakiyar dukiyar fulaninta yana shaqar qamshin dake fita a wajen.
Hannu ta saka ta riqe kansa,tana jin tsigar jikinta tana tashi saboda yadda labbansa suka sauka a wajen,ta saki dariya tana janye jikinta baya,ya daga idanunsa da suka fara sauya launi yana murmushin shima ya kalleta
"Kamar baki shiryawa zuwa bauchin nan ba" kanta ta langabar gefe,a zahiri batason zuwan,amma bai kyautu ta nuna masa ba,saita girgiza kai
"Aah,kawai kasala nakeji kwana biyun"
"Nayi noticing canji da yawa,kin koyi bacci,sannan ga overdose kyau baby da kike qarawa,overdose dad......" Hade bakinsu tayi waje daya yau da kanta,don batason ya qarasa fadin kalmar,bala'in sakata jin kunya takeyi,hakan da tayin saita tafi dashi wata duniyar ta daban,tasa ya dimauce ya mance dukka maganar da zai fada din,sanda zata qwace kanta kuma yace baisan zance ba,sai da ya cimma gaci sannan ya samu nutsuwa.
Washegari da wuri suka isa,don sha biyun rana ma a can tayi musu,sassanta ta wuce kai tsaye,gidan duk bai mata dadi ba saboda su mimi basa nan,hajiya tasa anzo an daukesu,an musu kitso da qunshi kamar yaran kowa,an kuma dauki kayansu sai bayan biki zasu dawo.
Wannan karon hafsat din bata hana ba,bata ma isa ta hana din ba don tasan abbas din ko zai jure komai banda wannan,kuma kai tsaye shi yayi kiranta yace ta bada yaran,ta hada musu tarkacen kayansu,gasu dai a ido masu kyau da tsada ne,amma dauda da rashin kula duk sunci mutuncinsu.
Tsaye hajiya tayi kawai cikin takaici tana qarewa kayan kallo,banda ma gidan yana samun feshin maganin qwari da kuma gyaran da uban kewa dakin nasu duk sanda ya samu chance....ta tabbatar ba za'a rasa wani qwaron a ciki ba,hajiyan nada masifar tsafta,sai tattara kayan tasa akayi aka bayar,banda ma masu tsada ne da kuma sauran qwarinsu qazanta ce ta cinyesu,a wajen hajiyan bola ce tafi kamata dasu.
Har ta fitar da kudi ta bayar za'a sake musu sabuwar siyayya mimi tace akwai wasu kayansu a wajen anty widad.
Hajiyan da kanta ta kira widad din tace mimi tace suna da kaya a wajenta,ta fiddo musu dasu umar zaizo ya karba,tana shiga sassanta kayan ta fara hadawa,a killace a tsaftace a kuma goge,umar din ya karba ya tafi dasu.
Tunda ta sauka gidan ranta yayita baci,gaba daya kamar an tattaro dukka bacin rai an aza mata,haka ta dinga dannewa,ta hau gyaran sashen nata,sai data tabbatar komai yayi neat din ta sake wanka ta canza kaya,ta dauki wayarta ta kira abbas don tanason zuwa saloon da qunshi,na qafafunta duka sun fita,kuma batason shiga mutane haka,abinka da farar fata, babban adon hannayensa da kyan ganinsu ayi musu qunshi.
Lokacin yana tsaye a qofar toilet yana amsa wayar Jasmin yana jiran hafsat dake ciki ta gama wanke masa zai shiga saboda dan uban qurar daya hada,bata damu ta shiga ta gyara ba,sai ya bawa Jasmin excuse ya katse kiran nata ya daga na widad din.
Cikin shagwabar nan tata dake sake narkar dashi tace
"Uncle"
"Babyn uncle" ya amsa mata tattausan murmushi yana subuce masa,sunan da hafsat taji ya kira saita miqe tsaye dafe da cikinta ta kasa kunne tana sauraren hirar
"Zanje saloon da qunshi,kaina da hannuwana duka ba dadi"
"Ba laifi,amma baby......ina kishi fa gaskiya,ki zaba duk inda kikeso zan sa a kira miki su har gida special services mana" kafada ta noqe,ita zaman gidan ne bataso har ga Allah
"Don Allah uncle,yaushe rabon da nazo bauchi" ta fada da wata irin narkakkiyar shagwaba da har data sakashi lumshe ido ba tare daya shirya ba
"Shikenan,ki shirya zan fita headquarter yanzu,sai mu biya"
"Thank youuuuuuu" ta fada tana dariya
"You are welcome" ya amsa yana sauke wayar sannan ya sake kiran Jasmin yace mata zai shigo nan da minti talatin.
Sauri sauri tayi ta gama wankewa ta fice ta bashi waje,ya shiga ya hada ruwan wankansa da kansa,abinda bai sani ba kenan muddin suna tare da widad.
Sassanta ta nufa tana sakin ashar cikin zuciyarta,ita ta dauka ma wannan karon shi kadai yazo,ashe sai data sake biyoshi,akwai sauran rina a kaba kenan?,saita jinjina kai,ta buda wardrobe dinta ta fiddo kayan sawa,sannan ta buda bandakinta ta shiga ta fara kwaskwarima.
Cikin wata doguwar rigar atamfa da tayi mugun budewa daga qasa ta shirya,brown ce mai adon blue black,tayi amfani da blue black hand bag veil da kuma takalmi,kalar ta haska farar fatarta da kyau, daurin da tayi wanda ta kawoshi gaban goshi ta fidda gashinta ta qasan daurin ya qara mata wani irin kwarjini,ko yaya ta motsa jikinta qamshi yake fitarwa.
Saboda saurin da take ta fita a gidan ta rigashi isa parking lot,tayi tsaye jikin motar tana jiran fitowarsa,wayarta sabuwa da ummu ta aiko mata da ita a hannunta suna hira da bilkisa ta watsapp,tana ta kwasan dariya,don bikisa din ba daga baya ba,ko yaushe qoqarinta taga ta dora widad din kan hanya,ta kuma ganar da ita wace hafsat.
Cikin wasu lafiyayyun indian blazers ya shirya blue black din shima,tamkar yasan color din da zata saka kenam,tun daga nesa kwalliyarta ta tsone masa ido,ya zuba mata dukka idanun nasa yana takowa a hankali,ko qifta idanunsa a kanta qyashin yi yakeyi.
Cikin jikinta taji yana wajen,saita daga kanta ta sauke a kansa,kamar shi,itama kwalliyar sa tatafi da ita ainun,yayi wani mugun kyau,ya koma yaro sosai da bai wuce sha tara zuwa ashirin ba,murmushi ya subuce mata,bakinta ya dinga motsawa tana jiran ya qaraso ta tsokaneshi,saidai dab da zai qaraso din hafsat ta bayyana,ta kwaso sauri cikin baqar abaya data saka ta yafa baqin mayafi wanda ya kasa zama a kafadarta saboda sauri dason ta cimmasu kafin sukai ga fita.
Ganinta sukayi kawai tana kiciniyar bude gaban motar tana cewa
"Banajin dadi abban mimi,ka miqa ni asibiti don Allah" tayi maganar tana shigewa gaban motar.
Da kallo dukkansu suka bita,widad ce ta fara dauke kanta kamar bata ga abinda tayi ba,sai ta matsa ta dauke handbag dinta dake saman motar ta juya zuwa cikin gida
"Ina zuwa kuma?" Dan dakatawa tayi da tafiyar
"Na fasa zuwa ne" iska ya furzar
"Aah,kizo Muje na fara sauketa saina qarasa dake" kai ta girgiza
"Um um.....naje ko gobe ko jibi" ta fada tana qoqarin boye damuwa sa fushinta,kawai ba zata iya hada mota da hafsat din ba,kallo daya tayi mata tasan neman rigima ya fiddota,dazun da umar yazo karbar kayansu mimi taji yana wayar jiya yakai hafsat din asibitin awo
"No....,wuce muje" ya fada yana takowa inda take tsaye,yana karbe jakarta daga hannunta
"Uncle....."
"Wai ba magana ake dake ba!.....yara suyita musu da na gaba dasu,kaga abban mimi just leave her mu tafi kawai" hafsat ta fada cikin tsawa,bayan baqincikin yadda taga yana lallabarta hadi da riqe mata jaka ya saukar mata ya tsaya mata a qirji.
A sukwane widad din ta waiwayo tana jin wutar dai dai take da ita a yau tana tashi cikin kanta,fes ta kalleta ido cikin ido,cikin lallausar muryarta a nutse ta amsata
"Sorry mommy....bafa dake nake ba......da uncle dina......au mijina na,da mijina nake magana"
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 97
"Sorry mommy.....bafa dake nake ba,da uncle dina,oh mijina,da mijina nake magana" widad din ta fada kanta tsaye,idanunta cikin na hafsat.
Wani abu mai nauyi hafsat din taji kamar an aza mata,kanta ya buga har tana jin wasu sautuka cikin kunnuwanta,ita widad din yau take kalla kai tsaye.....kuma kai tsaye,ido cikin ido take gayawa haka?,a gabanta take kiran abbas da mijinta?.
Kafin ta yanke abun yi har widad din ta soma qoqarin zame jakarta daga hannun abbas din,saidai yaqi cika mata,ganin yaqi cika matan saita juya ta fara takawa tana nufar sassanta,tana jin zuciyarta na mata qunci,batasan me yasa mommyn mimin keson shiga harkarta ba,bayan ita ko ganinta batason yi,batason su hada inuwa guda da ita, infact haushinta ma takeji,musamman lokuttan da zata gansu tare da uncle dinta.
Sanda hafsat din ta yunqura da nufin fita a motar tabi bayan widad din abbas yayi gaba,sai tayi mutuwar zaune tana binsa da kallo tare da son ganin inda zaiyi,zuciyarta na wani irin bugawa,tana fatar ba bayan widad din xaibi ba,yadda ta zata hakance ta faru,sassan widad din ya shige.
Tana shiga ta zare dankwalinta ta aje saman kujera,itama ta haye kujerar wayarta na hannunta tana ci gaba da chat dinta,duk da ranta a bace yake sosai amma batason tabar idanunta da suka tara hawaye su zubda qwalla.
Daga bakin qofa ya tsaya hannuwansa cikin aljihun wandonsa,ya zuba mata ido yana kallonta,qamshinsa ya sanyata gane ya shigo,ta daga kai sau daya ta kalleshi ta maida kanta ga chat dinta,qaramin murmushi yaso subuce masa,yana saurin karantarta fiye da kowacce mace a duniya,ya gane fushi takeyi amma batason nunawa,amma kuma shi bashi yayi laifin ba amma abun yana son qarewa a kansa,sai ya tako ya iso gabanta,ya zame a hankali ya duqa saman qafafunsa,ya riqe hannayenta da take chat din dasu yana duban qwayar idanunta
"Tashi mu tafi weedad......" Ya kira ainihin sunanta a tausashe,kawai tana daga kai suka hada ido dai kuka ya kufce mata,ya matse hannayenta gam cikin nasa yana jin wani abu na masa suka cikin zuciyarsa,bayason kuka sam,kukan ma kuma nata,bai hanata ba sai datayi kusa minti goma tana yi,sannan ta zare hannunta daga nashi ta dauki dankwalinta ta nufi bedroom dinta.
Binta yayi da kallo,bai taba zaton zata bisun ba,amma ga mamakinsa sai gata ta fito,ta wanke fuskarta fes ta sake shafa powder da lip gloss,ta zizarawa fararen idanuwanta kwalli
"Muje" ta fada fuskarta babu walwala,yi yayi kamar baiji ba amma idanunsa suna kanta,har zuwa sanda ta tako tazo dab dashi xata wuce sai ya matse mata hanya,ya kuma sanyata cikin jikinsa
"Bakya kyau da fushi baby doll,smile please" ya rada mata a kunne,a hankali murmushi ya kubce mata tana dan boye fuskarta.
Tuni ta gama cika ta batse,duk inda bacin rai yakai ranta yakai qololuwar zuwa wajen,sau biyu tana aika mimi tayi kiran daddynsu sai tace qofar na a rufe ne,gashi tashi yanzu wuya yake mata,har sai data yunqura zata fita taje da kanta ayi wadda za'a yi,sai gasu sun fito.
Sanda ta kalli fuskokinsu ji tayi qafafun ta sun riqe,haka abbas din zaiyi mata?,fuskar widad din kamar ma komai bai faru ba,ta shaqa iya shaqa,sai taji kamar numfashinta xai dauke,dole ta kauda kai daga kallonsu,wata zuciyar na bata shawarar ta fice a motar kawai tace ta fasa zuwa,amma sai wani sashen na zuciyarta ke gaya mata,idan tayi hakan ai kamar taci galaba a kanta kenan.
Fuska fs muryarta duka wasai tana tsokanar mimi daketa shirya beads masu dauke da alphabet nawwara na watsa mata,ta buda gidan bayan ta shige,taja yarinyar jikinta ta kama hannunta tana tayata saka beads din tare da warning nawwara cikin wasa kan kada ta sake ta taba musu.
Tsantsar baqinciki da bacin rai ya hana hafsat din magana har suka isa asibitin aka sauketa,taso bar musu yaran duka amma nawwara taqi sai mimi ce tabi widad din.
Abinda bata sani ba kwata kwata yara basa damun widad,hasalima ita din mayyar yara ce,ko hana mimi zuwa tayata kwana da takeyi hakan baya mata dadi kwata kwata,ita kadai tasan yadda taji,baya ga dan uban tsoron dake bibiyarta harda kewar yaran.
Kamar ko yaushe zama yayi a waje ya jirasu har aka gama,wannan karonma mimi ta samu albarkacin widad din,an wanke mata kan tsaf,yarinyar sai murna take tana shafa sumartata tana kallon widad
"Anty ashe da dadi" sarai widad ta fahimci me take nufi,tana nufin kanta yayi mata sawai,kuma ta tabbatar iska mai dadi yanzu tana shiga kan.
Tunda suka iso gidan,tun basu shiga ba gaba daya aka saukar mata da bacin rai da baqinciki,taji kamar ta cewa abbas don Allah kada ya shiga ya koma da ita,haka ta dinga qoqarin dannewa har ya saka kan motarsa cikin gidan.
Tana tsaye daga bakin window tana hangen komai dake faruwa cikin gidan,don haka tana hangen sanda ya ajjiyeta ya koma,ta jijjiga kai tana sakin labulen falon.
Da daren ranar ta dinga tsoron kada abinda ya faru xuwanta na qarshe bauchi ya sake maimaita kansa,idan ta runtse ido saita bude,ba motsin komai ko alamu na faruwar wani abu,daga baya tayi dukka addu'o'inta don haka ta samu relief sosai,saidai gidan gaba daya taji ta tsaneshi,tsananin tsana ta gasken gaske,a lokacin taji bata da wata buqata data wuce tabar gidan,bata da wata buqata data wuce ta ganta ba cikin gidan ba,haka ta dinga yawo tsakanin falonta zuwa bedroom,sai tayi kamar zata fita saita koma bakin qofa ta zauna ta fashe da kuka,kusan awa uku tana a wannan halin kafin daga bisani bacci yayi awon gaba da ita a nan bakin qofar a yashe a qasa.
*W A S H E G A R I*
Yadda parlor din yake fitar da sassanyan qamshi mai dadi,hakanan jikinta yake fidda nashi salon qamshin daban,girkinta ne ko ba girkinta ba,wannan duka bai dameta ba,kusan qamshi da tsafta sun zame mata gaado idan ana gadonsu,tun daga hannun ummu kawo yanzu.
Ita daya ce a parlor din,kwance cikin doguwar kujera mai cin mutum biyu,wani doguwar rigar material onion color ne a jikinta mai gajeran hannu,kanta babu dankwali sai sassalkar sumarta mai tsaho baqi da santsi data dameta cikin robber band,sai qyalli take saboda gyaran kan da taje shekaran jiya, hannunta wayarta ce,sunata hira da balkisa,bata jin dadin zaman ita daya,yau gaba daga ko dauriyarsa mimi ba,abinda bata sani ba hafsat dince ta hanata shigowa kwata kwata,ita kuwa koda wasa batayi gefan hafsat din ba,indai ba dalili bane ya hadasu a farfajiyar gidan,suna iya gama kwanakinsu duka basu hadu ba,hatta da gaisuwa da take zuwa mata a yanzun ta ajjiyeta gefe,idan sun hadu su gaisa,idan basu hadu ba fine,ta bawa bilkisa labari, bilkisan tana ta tsokanarta
"Sanda nace ki daina gani kikayi kamar sabo nayi ko?,yanzu fa?" Dariya kawai tayi,its har ga Allah zafin hafsat takeji,batason ma su faye haduwa,data gayawa balkisa dalili sai da tayi dariya sosai
"Anya widad,anya kuwa?,wannan zazzafar soyayya mai cike da kishin tsiya da akewa uncle?"
"Kishi kuma anty?"
"Qwarai da gaske" ta jima a ranar tana son gane banbanci tsakanin kishi da kuma abinda takeji akan hafsat din.
Sake gyara kwanciyarta tayi tana jin yadda gaba daya cikinta yake a cushe,duka cikin kwanakin nan bata jin dadin cikinta da jikinta sam,sai tajishi kamar a kushe,mararta babu dadi,amma saita danganta hakan da rashin zuwan period dinta da take saka ran ko yaushe zata iya ganinsa,tun tana lissafi da xuba ido harma ta share taci gaba da harkokinta hadi da cewa cikin ranta
"Wai meye ma don baizo ba zan damu?,nima na huta da takurarsa" har zata gayama abbas saita fasa,tana tsoron kada yace suje asibiti,daga nan ace sai anyi allura.
Tsayawa tayi da replying massage din da takeyi sanda sassanyan sound din data sama wayarta na musamman saboda shi ya shigo
"Baby uncle" shine sunan da tayi saving dashi, qaramin murmushi ya kubce mata saman fuskarta,bata gajiya da ganinsa,duk sanda zata bar kwana sassansa hafsat ta karba tana jin raunin zuciya sosai,tana jin kamar ta riqeshi ya barta tayita kwana,amma bata iya hakan.
Karbar jakarsa data gani daxun hafsat tayi ta kuma bishi sassansa ya fado mata a rai,saita tura baki sannan ta daga wayar a shagwabe tayi masa sallama.
Hannu yasa ya buda qaramar qofar dake jikin sashensa,wadda take bullo dashi zuwa parking lot na gidan,shi daya yake amfani da ita time to time,ya soma takawa a hankali yana fita daga sassan,sanye cikin wani yadin kaftan na maza,qafarsa sanye da lafiyayyen baqin half cover na maza qirar kamfanin aldo mai asalin kyau da tsada,kansa babu hula sai gyaran da yasha,komai nashi fes yana zuba qamshin nan nasa mai aji da daukan hankali.
Ya tabbata don hafsat bata nan ne,don bayan ta ajjiye masa abinci ta fita sashenta,kafin ta dawo ya shirya ya fito ko abincin bai tsaya ci ba,don gida zashi,akwai dan zama da zasuyi meeting shi da yayansa da yayyensa mata.
Idonsa ya lumshe,wani abu na tsarga masa sanda tayi masa sallama da shagwababbiyar muryarta,kwanaki biyun da zai cikashe a yau ba tare da ita ba sun masa mugun nisa,jinsu yake kamar shekaru biyu
"Kina ina baby?"
"Ina parlor"
"Okay,ki sameni ta qofar bayan part dina,fita zanyi"
"Okay sir" yadda ta fada cikin shagwaba da kuma salo na girmamawa dole yabar murmushi saman labbansa,ya zare wayar ya jingina da motarsa da ya saka sale ya wanketa kusan tun safe,idanunsa akan hanya yana jiran fitowarta.
Dakinta ta shiga tayi fitsarin daya cika mata mara,tana ta mamakin yawan fitsarin da takeyi yanzu akai akai,har ta gota madubinta ta dawo da baya,ta dauki turarenta ta sake fesawa sannan ta dawo parlor din ta zura slipper dinta ta fito ba tare data nema dankwali ba.
Tar harabar gidan take da wadataccen haske,wannan ne ya bashi damar hangota tun daga nesa,ya zuba mata idanu kamar ko yaushe yana kallonta,wani abu mai sanyi yana ratsa zuciyarsa,canji yake gani daga widad din da gasken gaske,murjewa takeyi tana sake ninka kyau da farinta
"Fatabarakallahu ahsanul khaliqin" ya samu kansa da furtawa yana shafa qirjinsa da hannunsa saitin zuciyarsa.
Dab dashi ta tsaya,ta langabe kai tana kallonsa, murmushi ya saki yana gyara tsaiwarsa,irin wannan kallon nata,duk sanda ya gani yasan zaisha rigima ne
"You look so good baby.....You look so cute,bansan yadda zan fasalta miki ba" dan murguda masa qaramin bakinta kadan tayi
"Duk ban yadda da wannan dadin bakin ba, kwalliyar ka kaima yau tayi yawa,ina zakaje?" Mamaki da dariya suka tuqeshi,yau itama zata rama kenan?,gefe daya kuma tana nufin kada ya fita yaje wajen wata?.
"Wajen hajajju zani ranki ya dade,na rantse babu inda zani daga nan" yadda ya rantse mata din yana daga hannuwansa sama alamun surrender ya bata dariya,ta tuntsire da dariya shima yana tayata,kafin daga bisani ya gyara tsaiwarsa yana dubanta
"Me zaki kaima yaa baraka na gudunmawa?" Fararen idanunta dake dimautar dashi ta juya sannan tace
"Na baka zabi,ko zabamin kome kaga ya dace,sai nakai din" folding hannayensa yayi yana kallonta, sosai ta bugeshi kimarta tana sake cika masa zuciya,sai ya tuna yadda sukayi da hafsat dazun da safe,kai tsaye ta nuna kudi zai bata,ya bata din kuma ta karba abinta,yasan halinta farin sani,bashi da tabbacin kuma zata kai abinda yakai kimar abinda ya batan,kansa ya jinjina ya buda baki zaiyi magana,saidai kafin yace komai hafsat ta bayyana a wajen from no where,daga shi har widad babu wanda yaga tahowarta bare isowarta wajen,tana isowa kuma babu inda ta nufa sai kan widad gadan gadan,batayi wata wata ba tasa hannu takai mata shaqa tana fadin
"Yau sai kinci ku******mar ubanki,zaki gane ke qaramar 'yar iska ce" cikin sauri da kuma tsananin tsoro widad din ta kauce,saita sake kai mata cafka,dai dai sanda abbas yayo kanta yana daka mata tsawa
"Ke hafsa,meye haka?,kina da hankali kuwa?,me kike yi haka" ko sau daya bata nuna ma ta jishi ba bare ta dakatar da abinda take shirin aiwatarwa,burinta kawai ta cimma widad din ta ida nufinta,cikin wani irin zafin nama ya isa garesu ya kuma shiga tsakiya yana duban hafsat din cikin wani irin mummunar bacin rai da zaka jima baka ganshi kan fuskarsa ba.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 98
"Matsa daga gurin nan hafsa tun raina bai baci ba" ya sake fada cikin kausashiyar murya,shammatarsa tayi sai kawai ga hannunta jikin widad,ta shaqeta sosai tana dura mata ashar,kai zaka dauka mahaukaciya ce sabon kamu.
Cikin qasa da second biyu,cikin wani irin bacin rai fushi da kuma qarfin hali itama widad ta shaqetan
"Ya salam" abbas din ya fada da qarfi yana kama hannun hafsat ya fincike daga jikin widad,sannan ya janye widad din gefe yana riqe da hannunsa tsam cikin nata
"Wuce cikin gida tun kafin raina ya gama baci!" Ya fada a tsawace
"Bazan wuce ba,ba inda zani, wallahi wallahi yau saina koyawa yarinyar nan hankali don ku****mar ubanta,ni za'a dinga rainawa hankali ana cin amanata?"
"Ba ubana kike zagi ba,naki kika zaga wallahi" widad ta fada cikin bacin rai,tana jin kamar abbas ya saketa ta sake komawa kan hafsat din.
Sake yunqurawa tayi a zafafe jin raddin da ta mayar mata
"Ni kike gayawa haka?,ka barni nayi mata dan banzan dukan da ba zata sake magana ba" kafin ta qaraso ya buda qofar bayan sashensa ya sanya widad wadda itama takeson qwacewa ya maida qofar ya rufe sannan ya juyo yana kallon hafsat da idanunsa da suka canza launi saboda bacin rai,ranshi a mugun bace yace
"Ki shiga hankalinki, banason rashin mutunci da hauka"
"Nice mara mutunci?,nice kuma mahaukaciya?,ai dole ka fadi haka,kun hada kai kuna cin mutuncina,kuna cin amanata,Allah ya isa wallahi ban yafe ba,Allah ya isa na" ta fada da qarfi,saidai......tun kafin ta kammala rufe bakinta ya kwasheta da wani kyakkyawan mari a kuncinta.
Cak wuta ta dauke mata,yayi mata mugun ba zatan da bata taba tunanin zai iya aiwatar wa ba,itace yau abbas ya daga hannu ya mara saboda widad?
"Stupid!" Ya fada yana huci,wani irin fincikar jikinta tayi tana dosar qofar
"Wallahi yau sai na daketa naga abinda zakayi" dab da zata qarasa ya isa gabanta yana nuna mata hanya,amma burinta ta qarasa ta bude qofar ta fiddo widad
"Ka matsa ka bani waje azzalumi kawai"
"Kibar wajen nan hafsa na gaya miki"
"Saina shiga,saina shiga azzalumi" wani lafiyayyen marin ya sake sauke mata hagu da dama,gaba daya sai wuta ta dauke mata,taci burki tana kallonsa kamar wata zararriya riqe da kumatunta
"Don kina iskanci da rashin mutuncinki kina ganin kamar bazan iya daukan mataki a kanki ba kin yaudari kanki,sassauci na da dauke kan da nake miki inason na zama mafi alkhairi ne ga iyalinsa,amma ke gaba daya tosashiyar kwanyarki ta kasa gano miki hakan,to wallahi wallahi kinyi na farko kinyi na qarshe,bazanci gaba da dauka ba,ki bacemin daga wajen nan tun ban bi ta kanki ba!!!" Ya fada da wata irin rugugin tsawa,ba hafsat dake tsaye a wajen ba,hatta da widad dake daga cikin falon saida cikinta ya juya, tsoron sosai ya kamata,ta koma ta zauna saman daya daga cikin kujerun dake dab da qofar,karin farko da taji sautin fushi da bacin rai daga gareshi kenan.
"Ko meye zaka ce, kuma ko me zakayi bazan fasa fadin cutata da kakeyi da cin zarafina ba,yarinya qarama ta mallakeka sai yadda tayi dakai,sai abinda tace,kanata zalunta ta,bazna yafe ba wallahi,sai Allah ya sakamun,kai da ita dukanku bazan yafe muku ba" cikin fushi ya sake daga hannu sai kuma idanunsa suka sauka kan cikinta,ya janye hannun yana qoqarin hadiye fushinsa,bai taba dora hannu a kanta ba sai yau,sai ya kama hannunta ya saita mata hanya yana gaya mata cikin tsawa ta bace masa a wajen.
Jinta take kamar ba'a tsaye take saman qafafunta ba kamar akan iska take haka ta juya ta fara barin wajen, hannunta har yanzu akan kuncinta,idanunta na malalar hawaye masu zafi da quna,yau ita abbas ya mara?,wannan shine mummunan abun tarihi na farko daya faru a iya zamansu da ba zata mance dashi ba.
Ido ya zuba mata cikin fushi har ta bace a wajen,sannan ya juya ya bude qofar,wanda tuni widad dake zaune saman kujera ta miqe tana dakon isowarsa,saidai zuwa yayi ya wuceta abinsa yana wani irin huci,kaman zai zauna akan kujera amma sai ya kasa,ya dinga kai komo widad din tana kallonsa tana kuka qasa qasa
"Shut up" ya fada mata da wata irin tsawa data sakata qanqame jiki waje daya hadi da runtse idanunta,bayason jin kukanta ne kwata kwata,tana qara hasala masa zuciyarsa ne ba tare data sani ba,a cikin yanayin da yake kuma a yanzun bazai iya lallashinta ba,sai kuma ya koma ya zauna bayan ya sakar mata tsawar,jikinsa yana mutuwa,qaramin sautin kukanta yana sake ratsa falon.
Kusan minti talatin suna a haka,ta kasa shuru shi kuma ya kasa lallashinta,sai da suka doshi minti arba'in sannan ya miqe ya fice,ba jimawa ya dawo dauke da hijab dinta da wayarta ya miqa mata,sannan ya isa gaban freezer dinsa ya ciro ruwan gora mai sanyi ya bude ya miqa mata,tasa hannu ta karba tana satar kallonsa,idanunsa ba'a kanta yake ba,wani gurin daban yake kalla,sai takai ruwan bakinta ta fara sha,ya fara sauka cikin cikinta yana ratsa qirjinta dake suya,yana kuma rage mata radadin da takeji.
Kusan rabi tasha sannan ta miqa masa,sai ya sake saka hannu ya karba ba tare daya kalleta ba,bakinsa yakai ya shanye sauran yana yin gaba,ya cillar da robar yana cewa
"Wuce muje" bayansa tabi ba tare da tasan ina suka nufa ba,motar sa ya bude tun kafin su qarasa da remote control,ya isa seat din gefan driver ya bude mata ta shiga ya mayar ya rufe,sannan ya zagaya shima nasa bangaren ya shiga ya tayar da motar suka bar gidan.
Lamo tayi cikin motar,ta kwantar da kanta a makarin kujerar tana 'yar sheshsheqar kuka,idonsa ya dinga runtsewa,sautin kukanta yana qonashi da yawa,basarwa ya dinga yi yana zaton zai iya daurewa amma sai ya kasa,tausayinta ya lullubeshi,yadan daki kan motar,sai ya gangara gefan hanya yayi parking ya juyo sosai ya zuba mata ido yana hadiye bacin ransa da qyar
"Why widad.....why.......me yasa kika biye mata?" Idanunta dake jiqe da hawaye ta daga ta kalleshi
"Amma uncle.....itace ta fara fa" kai ya jijjiga
"Na sani,amma kina zaton zan tsaya ne a wajen ina kallo ta cutarmin dake?" Kai ta kada a hankali alamun a'ah
"So kike ki koyi irin abinda takeyi?,kinaso na daina samun walwala gaba daya?" Kai ta girgiza nan ma sabuwar qwalla na sauko mata
"Kayi haquri uncle......am sorry" a hankali ya lalubo hannunta da hannunsa guda daya ya hadesu waje daya yana hadiye wani bacin rai daya tsaya masa
"Am sorry too baby,na miki tsawa,it was not intentionally.......hankalina ne a tashe,raina a bace,banason kema ki koma wani abu daban"
"Bazan sake ba uncle" ta kuma fada hawaye na sake balle mata
"Kina qonani baby doll,kina qona zuciyata,ki daina wannan kukan" ya fadi yana kamo fuskarta cikin hannunsa,tare da zaro handkerchief dinsa ya soma goge mata fuskar cikin wani irin salo na tausasawa da nuna zallar qauna,hausawa sukance gaida mai gaidaka ko bazai amsa ba,ko meye zai mata idan tana cikin bacin rai bai fadi ba,widad ce kadai ke fahimtar ransa a bace yake ko yana fushi,saita tabbatar tayi abinda zai samu sassauci kota saukeshi daga fushinsa,duk da kusan ba itace sila ba.
Saida suka shiga unguwar ta fahimci gidan hajiya ya kawota,bashi da wani solution illa hakan,saboda yasan kwana zatayi kuka ita kadai,babu lallai ta saki jikinta,a nan ne kawai zata sake tayi baccinta.
Mamaki ya kama hajiya lokacin data gansu tare,baice ma hajiyan komai ba ya barta a nan ya koma setting room din qofar gidansu suka shiga meeting din da suka shirya yi din.
Itama batace komai da hajiyan ba,saidai hajiya ta fuskanci sanyi jiki kadan tattare da ita,tanata kallon widad din,canzawar da tayi tayi yawa,ta kasa cinyewa wannan karon bayan sun gama meeting din ya shigo gidan,widad din ta tafi kawo masa abincin da bai samu ci ba tace dashi
"Anya abbas ba juna biyu yarinyar nan take dashi ba?" Ido yadan lumshe yana sakin qaramin murmushi,hasaso 'yar rigimar tashi da ciki kawai yakeyi,inda hakan zata kasance da yafi kowa farinciki,amma fa yasan daru ne za'a shashi
"Banjin haka hajiya"
"Bata amai bata yawu,ba zazzabin dare?" Dan jim yayi sannan ya girgiza kansa
"Babu hajiya"
"To ma sha Allah,Allah ya kawo nagari masu albarka"
"Ameen ameen" ya fada cikin dan jin nauyi.
Muneera ya nema yace ta gyara daki daya widad din zata kwanta a ciki,ba jimawa muneera ta gyara din,don dama ba dakin da hajiyan ke barinsa da dauda.
Yana zaune ta wuce dakin,hajiya tace taje ta kwanta,taga kamar tana alamun bacci a idanunta,ta yima hajiya sai da safe,ta juyo zata masa sallama suka hada ido,sai ta basar tace
"Sai da safe"
"Allah ya bamu alkhairi" ya amsa ta yana binta da kallo,inda suna kaduna waye zai shiga tsakaninsu a irin wannan lokacin,kaf rayuwarsa yana qaunar dare yayi,saboda lokacine da zai rabi jikinta sosai ya kuma kwana yana jin duminta hadi da shaqar tattausan qamshinta.
"Ba yanzu zaka wuce bane" hajiya ta tambayeshi ganin goma da rabi na neman gotawa,agogo ya kalla sannan yadan dubi hajiyan
"Wannan program din nake jira su gama saina wuce" ya bata amsa yana maida dubansa ga tv din,saidai a zahiri gidan ne baya qaunar komawa,idan ya tuna abinda hafsat din tayi sai yaji ransa ya baci,yana so ya sake hucewa ne kafin yakai ga shiga gidan,bayason komawa da zafinsa shaidan ya ingizashi ya yanke mummunan hukunci.
"To bari na shiga na kwanta nidai" sukayi sallama da hajiyan,amma yace idan ya gama zai wuce zai mata magana.
Ido yabi hajiyan dashi har ta shige daki,sai yayi zumbur ya miqe yana zuba hannuwansa a aljihun rigarsa ya wuce dakin widad.
Tunda ta shiga dakin tana kwance ne kawai amma bacci bai zowa idanunta ba har sannan,har yanzu zuciyarta a bace take kan abinda hafsat din tayi mata,tunda take ba'a taba yi mata makamancin abinda hafsat din tayi mata ba,gaba daya kimarta babu ita a idanunta,duk wani sauran mutunci nata da take gani a yanzu babu shi,to me tayi mata da har take yunqurin dukanta?, tabbas inda ta dora hannunta a kanta babu abinda zai hanata ramawa kowa kuwa gemunta na jan qasa ne saboda girma da shekaru,tunda ai bataga abinda tayi mata ba.
Sallamarsa tasa ta daga idanunta zuwa fuskarsa,ta zuba masa ido na wasu sakanni,haka kawai taji tausayinsa ya kamata,tausayin da batasan na meye ba,ya tako a hankali zuwa gaban gadon,sai ya matsa jikin switch na fankan yana rage gudun fankan dakin,sannan ya dqwo gefan gadon ya zauna yana cewa
"Wannan iskan ai tayi yawa"
"Zafi nakeji" ta fada muryarta qasa qasa,ya waiwayo yana dubanta cikin mamaki,don garin a sake yake da iska, baice komai ba yakai hannunsa jikinta ya taba,da gaske gumi takeyi,sai yasa hannu ya dagota gaba daya yana zare mata rigar jikinta,ya barta daga ita sai farar vest me siririn hannu, idanunsa suka sauka a qirjinta da suka cika suke a tsaye kyam,sai tayi hanzarin jan bargo zuwa qirjin nata ta koma da sauri ta kwanta tana boye fuskarta.
*H A F S A T*
Kuka ta zauna tana yi sosai kamar zata fidda zuciyarta,ba zafin marin ne yafi damunta ba,wadda aka mareta ta sanadinta ne damuwarta,hannun abbas yau da yakai fuskarta ya daketa saboda widad din?,takai ta kawo,ta kasa zama tana jin kamar abinda yake cikinta zai fito a yau.
Tana tsaka da wannan taji tashin motarsa,da sauri ta daga labulenta tana leqensa har ya fice, zuciyarta ta dinga qissima mata abubuwa da yawa,shi da waye?, abinda yafi tsaya mata a rai kenan,sai kawai kuka ya qwace mata,ta dauki wayarta da hanzari ta danna wa mamanta kira,tana jin baqinciki kamar zai kasheta,ba zata iya hadiyar wannan bacin ran ita kadai ba.
Ashar mamanta ta dinga zundumawa
"Saboda baisan darajarki da mutuncinki ba?,cikin daren nan,da tsohon ciki a jikinki zai kamaki ya daka?"
"Ni umma anya wannan hanyar tana aiki kuwa?"
"Bana shakka akai,saidai kice wani abu da ya kawo tasgaro ya faru,amma koma meye ki daga waya ki gayawa uwarshi abinda yayi miki,yadda yasa kika tasheni a bacci itama ki tasheta" akan wannan suka rabu,ba tare da wani dogon tunani ba kuwa ta laluba number hajiya ta kirata.
Dai dai lokacin da dattijuwar ke saman abun sallah tana shafa'i da wuturi taji qarar waya
"Subhanallah" ta furta bayan ta gane number wadda ke kira,tabbas matsala ce ta faru ta tabbatar,don ba zata iya tuna sanda taga kiran hafsat din a wayarta haka siddan ba tare da komai na matsala ya faru ba.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 99
"Hajiya ina wuni"
"Lafiya alhmdlh,ya nauyin jiki?"
"Lafiya lau" ta fada a gaggauce,sannan ta zauna ta fara rattabo mata abinda ya faru.
Fiye da rabin maganar ta canzata, hajiyan tayi shuru tana saurarenta har ta gama fada sannan ta rushe da kuka
"Ya isa,kiyi shuru haka ki daina kukan ko don abinda yake jikinki,zan laluba gaskiyar maganar,indai na sameshi da laifi saina bata masa,ki kwanta kiyi bacci zan nemeki in sha Allah" a haka suka rabu da hajiyan,can qasan ranta tana jin haushi haushi,wai zata bincika taji,itama ta fara canza hali kenan.
Ajiyar zuciya hajiyan ta saki
"La haula wala quwwata illa billa" ta fada a fili,qaddarar abbas kenan shi kuma,kalar tasa jarrabawar rayuwar kenan,yunqurawa tayi ta miqe tana fatan ta sameshi a falo,duk da sha daya na dare ma ta gota,amma yace zai mata magana idan zai wuce.
Murmushi ya bita dashi sanda ta koma ta kwanta tana boye fuskarta,sai yaja mata bargon sosai,ya sunkuya yayi kissing dinta lightly,sannan ya motsa bakinsa zuw kunnenta cikin rada yace
"Kiyi bacci mai dadi babyn uncle" a dole murmushi ya subuce mata,hakan yayi masa dadi,sai ya rage mata hasken dakin sosai,ya sake lullubeta ya fice yaja mata qofar.
Dai dai lokacin hajiya ta fito a dakinta,sai sukayi kacibus,kunya ta dan kamashi,sai hajiyan ta kauda kanta
"Yanzu nake shirin shigowa muyi sallama" ya fada yana shafa kansa
"Gwara da baka wuce din ba ai,zo ka zauna muyi magana" tuni jikinsa ya bashi tayi halin,ya dawo gaban hajiyan ya zauna
"Matso" tace dashi,sai ya dawo saitin qafarta
"Wanne abu ne ya shiga kanka da zaka saka hannu ka mammari matarka da tsohon ciki?" Kansa ya saddar qasa na wasu sakanni,sannan ya dago
"Hajiya na fara gajiya da hafsat,na gaji da halayenta,inajin taqi kadan ya rage mu rabu"
"Aah,kada ka sake fadin haka,yanzun me ya hadaku?" Bai boye mata komai ba ya gaya mata,tayi shuru abun na tsumata,ko yaushe abun na hafsat gaba yake ba baya ba?
"Iya qoqarina hajiya inayi,ina dannewa,ban taba kai qararta ba,amma kome nayi ita bata gani,da qyar wani lokacin nake iya tanqwara zuciyata akanta,tana kaini bango,bani da guarantee din abinda zai iya faruwa gaba"
"Haquri zaka ci gaba dayi,ko don albarkacin zuri'a data ratsa tsakaninku"
Duk da ita kanta hajiyan abubuwan sunata kwance mata,to amma ita din uwa ce,duk yadda uwa take da juriya aka santa,ba yadda zataso abbas din yayi wani abu na rashin dadi ko kyautatawa,har abada da naka yayi cuta gwara shi a cuceshi,baki ta dinga baki da nasiha cikin hikima ta dattawan mutane masu hankali da sanin ya kamata,taga bacin rai da damuwa masu yawa a idanunsa
"Ku shirya gobe ku koma inda kuka fito kawai abbas,banason wannan tashin hankalin,mun yafe bikin" statement din hajiya na qarshe kenan,don shine kawai mafita.
Kamar dama ta shiga xuciyarsa,don darajarta ce kawai take sanyashi yawancin lokutta yake zama a garin har yayi kwanaki idan yazo.
Sha biyu da minti goma ya isa gida,tana falo zaune don ta kasa runtsawa,ta kuma ji shigowarsa,sai taci gaba da zama tana tsammatar shigowarsa ganinsu mimi,amma har aka qara mintuna talatin shuru babu shi babu bayaninsa.
Shikam sashensa ya shige,ya fidda kayan jikinsa yayi wanka,sannan ya shirya kayansa waje daya kafin nan ya kwanta.
Har qarfe daya na dare tana zaune shuru,ranta yana sake baci,zuciya na mata saqa iri daban daban,yana nufin har kwanan nata ma ya saraya kenan?,idan bai shigo yanzu ba ta tabbata da safe zai shigo,zata ga da wanne ido zai kalleta.
Daga sallar asuba ya zarce da wanka,kafin qarfe shida ya gama shirinsa tsaf,ya fidda luggage dinsa ya saka a mota.
Sale ya barwa envelope yace ya bawa matar gidan,kudaden hidimar gida ne a ciki,ya zare dukkan wasu kudade daya saba bar mata wanda suke kyautatawa ce kawai bawai na haqqin dake wuyansa na shari'a ba.
*********Da farko ta watsar dashi kamar yadda ya watsar da ita,don ba qaramin shaqar takaici tayi ba sanda ta karba saqon ta hannun sale,ya rasa wa zai bawa aiken kudin amfanin gidanta sai salen?,bata sake shiga rudu ba sai dataga kowanne kudi ya fadi na meye,babu ko qarin sile akan abinda ya saba bata,gashi buqatar kudin take da gaske saboda fara adashin asara data yi,ko cikin satin ummanta tace lallai lallai ta tanadi kudi,saboda ba zasu taba bari sakaci ya shigo cikin aikin da aka fara ba,wannan ya sanya ta sake qullatar widad din qwarai,a duniya idan aka bata bindiga akace ta kashe mutum daya widad din zata fara harbewa.
Yadda ya dauke mata wuta abin ya fara damunta,gashi tana fuskantar EDD dinta yana sake matsowa,wata zuciyar tana ta kirashi wata tana ta shareshi,a haka kwanakin suka fara tafiya, dole daga bisani ta karya billent ta kirashi,ta kuma maida komai ba komai ba,don lallai tana buqatar kudi.
*B a y a n wa t a u k u*
Bayan watanni uku hafsat din ta sauka,ta sake samun baby girl,zagayowar kwanaki hudu abbas ya dauki excuse don zuwa ganin baby,dole widad ta soma shirin binsa itama,don rabonta da bauchi tun wancan lokacin da suka samu sabani da hafsat,duk sanda zaije weekend tabar binsa,saidai yaje yayi kwanaki biyu ya dawo Kaduna,hakan yafi mata kwanciyar hankali,har ya zamana koda wasa batason taji ya ambaci xuwa bauchi da ita,yanzu zataji hankalinta ya tashi.
Ta shirya tsaf tayi sabbin dinkunanta,gyaran gashi zuwa lalle suka wuce bauchi,ranar ta shiga sassan hafsat din,wanda rabonta dashi har ta manta.
Ba wani mutane bane sosai, kasancewar ita din dama bata mutane bace,mai zuwa mata sha'ani sai wanda ya dubi Allah,anty ummee ce sai wasu baqi mata biyu sai 'yar yayarta data dauko saboda aikace aikacen gidan,sai hajiya habiba.
Ciki ciki hafsat din ta amsa mata barkan data mata,itama sai bata saka kanta can ba,ta zauna daga hannun kujera,anty ummee ta miqa mata baby da aka gama yiwa wanka tana qarewa widad din kallo tsafff tana kaduwa da yadda taga ta sauya,ta karbeta tana jin sha'awar yarinyar har cikin zuciyarta,kasancewarta mai son yara sosai.
"Uhmmm.....ko a bar miki ita ne?,naga kin kasa daina kallonta" hajiya habiba ta fada tana wani munafukin murmushi tana kallon widad,sai ta saki murmushi kafin tace komai hafsat ta rigata,taja wani mugun tsaki tana gyara zamanta
"Ki daina irin wannan wasan hajiya habiba......haihuwa wasa ce da zaka dauki yaro danka ka baiwa yaro,wanda ko ciwon kansa bai sani ba?,tab..... garinsu da nisa ai,idan fitsari banza ne kaza tayi mana" tsaf ya fahimci abinda hafsat din take nufi,don haka ta miqe tsam ta miqawa anty ummee babyn tana cewa
"Allah ya rayata" ta fice a nutse a falon ta wuce sassanta,don saukarsu kenan ta fara shigowa nan din.
Tare hajiya habiba da anty ummee suka dauke kai daga kallon widad bayan ta bace musu,suka maida kan hafsat data fara qananun motoci tana sakin tsaki kamar ta tsinke harshenta
"Banso kika sanya baki ba,kallon me juna biyu nakewa yarinyar,naso na bugar mana cikinta muji akwai ko babu" hajiya habiba ta fada tana duban hafsat
"Ai banza ce,nima kallon da nakeyi yarinyar kenan tunda ta shigo,kamar me yaron ciki,canzawar tayi yawa,ni tsorata ma nayi dana ganta wallahi,ta zama wata babbar mace?" Anty ummee ta fadi tana kama bakinta.
"Allah ya kiyaye Allah ya sawwaqe,ni kuwa ina me zan zauna na barta tayi ciki?,haba don Allah,bazai yiwu ba" hafsat ta fada tana girgiza kai,cikin zuciyarta tana jin wani irin zafi kamar ma ance cikinne,tana qiyasta yadda zata cakuda 'ya'yanta da 'ya'yan wata matar?,ba zaiyuwu ba,ba zata iya ba,barin widad din ta samu ciki harta haihu shine babban kuskuren da zata tafka
"Idan ba mataki kika dauka ba sanda zai narka mata cikin sani kikayi?,kina nan kina bacci saidai ki tashi ki ganshi" hajiya habiba ta fada tana miqewa tsaye gami da daukar jakarta
"Bafa wannan maganar hajiya,matakin nasa aka dauka,shi yasa nake cika miki baki"
"To yanzu naji magana.....hmmm aikin hadu da alaqaqai ciwon zamani mai wuyar magani"
"Ko tunata banason yi wallahi hajiya,ban taba kawowa yarinyar nan zata shiga rayuwata tayimin karen tsaye har haka ba" hafsat din ta fada yana sauke idanunta a sassan widad din tana jin ranta yana mata ciwo.
Duk da jego take amma hakan bai sanyata ta barwa widad din kwananta ba,haka take diban jiki tabar masu tayata zama ta wuce sassansa ta kwana,ko daya widad din bata bari taga damuwarta ba,saita shiga sabgar gabanta kawai.
Da kansa yace me take buqata na taron suna,tace zata kirasa idan ya fita,saita dauki waya sukayi magana da anty madina
"Kiyi komai naki ta yadda ba ruwanki da abincin taronta,wanda ya shigo miki ki bashi,wanda ma baizo na ya hutasheki" da suka gama wayan saita kira hajjaa ita kuma ta gaya mata yadda suke komai na taron suna,ta yiwa abbas din waya ta gaya masa,ya ajjiye mata komai,da taimakon hajja takai aikin abincinta,masa da sinasir sai soyayyiyar shinkafa (fried rice).
Ana gobe suna ta yiwa uncle muhsin waya ya bar nujood tazo suka kwana tare,washegari aka tashi da suna.
Kwalliya ta dinga yi sosai,tana canza shiga cikin kayan da abbas din ya dinka musu,duk da na hafsat din ya dara nata,da kadan da kadan saiga mutane sun cika sashen nata, don duk wanda ya shigo din ga abinci nan zaici ya qoshi,sashen mai jego kuwa babu bayani,don kudinta ta adana,ta sada mutane da wata irin jallop din shinkafa data hadu da taqadiriyar dahuwa mara tsaro,dukka lemon roban da yasa aka jibge ta debesu,ta musanya da zobo dan dauri.
Daga qarshe dai sassan widad sai ya zamana kaman a nan akayi haihuwar,duk wanda ya shigo din kuwa saiya qoshi da abinci me kyau,hafsat na daga sassanta amma labarin abinda ke faruwa a sassan widad din tuni yaje mata,ta cika tayi fam,musamman matan abokan abbas din da suka yada zango a can bayan sun mata barka,don ba wadda ta zauna a cikinsu,saboda ba wani kyakkyawan mu'amala bace tsakaninsu,tsananin kirkin abbas din ne ma ya sanya suka kasa qin zuwa,dama kuma idan ka gansu a gidan to saifa irin hakan ta kama.
Kasa zaune bare tsaye hafsat din tayi,da yammar ta canza kaya na biyu shima bisa takurawar anty ummee
"Kiyita zama,suttura iya sutura an miki amma kin jibgesu,ga kishiyarki can kowa fadin shigar ta yakeyi,keda ake taron don ke amma kamar saboda ita akeyi" sannan ne ta sake saka wata atamfar.
Sanda ta fito falon tayi baqi ta hangi fitowar widad din ta window din falon nata da aka dauke curtains dinsa,ta yima matan abokan nasa rakiya,tana sanye da shadda 'yar mali,baqa ce da aka yiwa adon mustard yellow,zo kaga baqar shadda jikin farar mace,an tsara mata wani mugun dinkin bubu,ido kawai ta runtse hafsat din tana dauke kanta daga wajen tana jin Zuciyarta kamar zata fashe.
Kwana biyu da suna suka koma inda suka fito,tabar hafsat din da tarin ciwo a zuciyar ta,da kuma K'ULLACI hadi da ALWASHI iri daban daban akan widad din.
Duka duka sati uku da komawarsu bauchi tafiyarsu ta taso,zasu tashi ta kano,don haka suka shirya zuwa bauchin yayi sallama da hajiyansa,ya kuma sallami gida sannan su wuce kanon.
Kamar ko yaushe,cikin tsoro da wani mugun bacin rai da qunci ta sauka a sassan nata,yau din tana jin tsanar gidan sosai fiye da ko yaushe,cikin qafafunta takejin kamar ba lallausan carfet take takawa ba,kamar qayoyi ne zube a sassan nata gaba daya,haka ta dinga qoqarin dannewa ta fara gyaran sassan nata tayi ta kammala ta samu waje ta kwanta,wata muguwar kasala da nauyin jiki suna mamayeta,wanda a kwanakin nan sai sake gaba abun yake,har abbas din yace muddin sukaje hajjin suka dawo babu wani sauyi to ko bataso dole taje taga likita.
Kamar wancan karon,wannan karon ma har bacci yadan fara fusgarta taji kamar an soma shaqeta,ta farka da sauri tana ambaton sunan Allah,sai numfashin ta ya ware ya koma dai dai,ta miqe a hankali tana sauke ajiyar zuciya,tana jin kamar ta fice a gidan kota yaya,sai ta zura slipper dinta kawai ta bude qofarta ta fito.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*
Page 100
A hankali take taka harabar gidan,tana jin kamar magnet ke janta zuwa waje,har ta kusa da gate din ta taka wani dan qaramin dutse mai tsini,zafin da ya soketa ya sanyata furta
"Subhanallah" ta tsugunna tana dub qafar,Allah ya taimaketa bata huje ba,banda zafi da radadin da takeji kawai,koda ta dago sai ta tsaya tana duban qofar fita daga gidan dake kulle,tare da tunanin meye ya fito da ita a wannan daren?,saita girgiza kai ta juya tana komawa ciki.
A hankali yake takowa zuwa dakin solar na gidan,don ya duba yana tunanin kamar sale bai kulle ba,cike da mamaki yake kallonta sanda take takawa zata koma sashenta,to daga ina take?,da alama ma bata ganshi ba,sai ya canza akala ya dosheta.
A tausashe ya kamo lallausan tafin hannunta ta baya,tadan firgita kadan sannan ta waiwayo suka hada ido,ta saki waya ajiyar zuciya mai nauyi
"Ina kikaje haka"
"Babu ko ina,kawai na gaji ne" qarara ya karanto zallar gajiya da qin da takewa garin na bauchi a idanunta,sai ya jinjina kai
"Muje kidan motsa,dama kin fara qiba ba dole ki dinga gajiya haka kawai ba".ya fada cikin salon tsokana yana lakuce mata kumatu,sai ta shagwabe masa tana tabe baki kamar mai.shirin sakin kuka,sakato.yayi yana kallonta tana sake tsumashi,don dama duka.yau din baiga wannan narkakkiyar shagwabarta ta ba,sai tsomoshi da shigar data dinga yi a sunan data dinga yi,duk sanda zai.shigo kuma sai yayi tozali da ita,ya dinga jin kamar ya dauketa subar gidan ya samu ya rage zafi,amma sanda yaga yawan jama'ar dake sashenta dole ya haqura ya hadiye,hafsat kuma ko a yanzun a dakinsa ya barta,ko kwana daya bata yarda ta bariwa widad din ba.
Sassanyar iskar daren dake kada jikkunansu ta dinga haifar musu da wani yanayi cikin zukatansu,kada ma abbas din yaji labari,ya sake matsowa ya.kama hannunta suna ci gaba da strolling
"Jibi zamu wuce,gobe ki kammala komai naki" da mamaki take dubansa har batasan murmushi ya subuce mata ba,bata dauka zasu koma da wuri haka ba,saboda taji yana cewa babu cinkoson aiki sosai,ya waiwaya a hankali ya sauke mata narkakkun idanunsa
"Oh......murna ma kikeyi?" Nata fararen idon ta juya,lallausan murmushin dake qara fidda quruciyarta ta saki tana maida dubanta gefe
"Dole ne ai......zan sake da uncle dina" murmushi mai dan sauti ya saki yana kallonta cikin mamaki,sannan cikin tsokana yace da ita
"La la la.....eh lallai zan gayawa uncle muhsin,yarinyarsa tasan dadin mijinta" ya fadi qasa qasa dab da fuskarta,sai ta saki dariya tana zame hannunta daga nasa cikin jin kunya
"Don Allah uncle karka fada" ya bita da sauri yana son cimmata yana sake tsokanarta kan sai fa ya gaya masa.
Kamar yadda yace din kwana daya suka qara suka tattara suka koma kaduna abinsu,hafsat din tana ta cika tana batsewa,don ko fitowa batayi ba,daga daki sukayi sallamarsu suka gama.
Ajiyar zuciya mai nauyi widad ta sauke sanda motarsu ta fita daga qasar bauchi tahau ta kaduna,har sai da abbas din ya juyo ya kalleta.
*********Cikin wata muguwar zabura ta farka tare da miqewa zaune saman gadonta tana rarraba idanu,gumi sharkaf ya jiqa mata ilahirin rigar atamfar da take jikinta yana zartarwa cikin jikinta,kadan ya rage ta danne baby yusra dake bacci a gefanta,ji tayi kamar alqiyamarta zata tsaya,wannan wanne irin mafarki ne mai muni mara dadin gani?,me mafarkinta yake nuna mata kenan,widad dauke da baby tana miqo mata ita?,me hakan yake nufi?.
Wayarta ta jawo tana dubawa kamar me neman wani abu,a sannan tayi ido hudu da number abbas,waddda itace kira na qarshe a jerin lambobin da aka kirata ko tayi kiran,awanni hudu da suka wuce,yake gaya mata jibi zasu iso bauchin,duk da sai da suka kusan dan samun sabani saboda a maganarsa ta fahimci da widad din xasuzo,abinda duk duniya ta tsana kenan a yanzu,take kuma neman hanyar da zata kawo qarshen faruwarsa.
"Anya ba ciki ne da yarinyar ba?" Wata zuciyar ta gaya mata,saita hau girgiza kai da sauri kamar hauka sabon kamu,kai kace ita da wani suke magana a dakin
"Inaaa,inaaa,bazaiyiwu ba" ta fada a fili,ba zata taba barin haka ta faru ba muddin tana raye,cikin abbas ace ya tabbata a jikin wata?,da kuwa lallai ta rako maya duniya,ta kuma cika hasararriya,iya qiyasta hakan kawai da tayi sai taji kamar zuciyarta zata tsinke tabar qirjinta,haka fa na nufin ya hada shimfida da ita?,ya santa a matsayin diya mace
"Aah..... a'ah" ta sake fada tana girgiza kai da sauri.
Ji tayi kamar ta kirashi tace su taho gobe,lallai kuma yazo da widad din, saboda tanason ganewa idanunta,shin da gaske ne abinda zuciyarta ke raya mata?,ko hasashe ne hadi da shirmen mafarki?.
Wanann daren sai ya zame mata baqin dare,don tunda ta farka ta gagara komawa,saidai ta zauna idan ta gaji takai ta kawo har asuba ta risketa a haka.
********Sau biyu yana duba agogonsa sannan ya maida dubansa ga qofar fitowa daga sassanta,kusan minti goma tace tana zuwa,amma har yanzu bata fito ba,bata saba hakan ba,ba halinta bane,duk sanda zasuyi tafiya ko zasuje waje bata fiya bata masa lokaci ba,idan yace qarfe kaza kome takeyi ta kammalashi kafin wannan lokacin.
Fitowa yayi daga motar hannunsa sanye a aljihun wandon yadin cashmere mai asalin kyau da tsada,wanda ya karbeshi qwarai,ya tunkari sassan nata yana fatan samunta lafiya.
Saman kujera ya sameta zaune,tayi likimo a ciki kamar bamai shirin tafiya daga kaduna har bauchi ba,sai daya isa kanta sanann ta daga idonta ta kalleshi,saita miqe cikinmu mutuwar jiki tana sauko da qafafunta qasa hadi da gyara rufin veil dinta tana cewa
"Sorry uncle,yanzu nakeson fitowa"
"Me ya sameki?" Ya tambayeta kansa tsaye yana tsare sosai da idanu,qas tayi da kanta,batason gaya masa amai tayi kuma jiri take ji,batason hankalinsa ya tashi
"Me yake faruwa dake ne?,ki gayamin gaskiya,karki yadda kicemin ba komai,jiya da daddare na ganki,tashinki nawa kina shiga toilet,na tambayeki kuma kikacemin lafiya qalau" yadda yayi tambayar cikun seriousness sai ya koma mata ASP abbas sosai,miskilin nan mai tsare gida da baiwa masu laifi tsananin tsoro,dole ta buda baki a hankali tace
"Amai nayi,sai jiri,sai kuma fitsari da nakeji,idan naje yi kuma sai naga dan kadan,marata tayi kamar an saka dutse" shuru yayi yana kallon fuskarta,wani abu ya darsu a ransa,amma sai wata zuciyar ta kawar,don ba haka ya saba gani ba,ya miqa hannnunsa a hankali ya taba wuyanta ya janye hannun jin babu zazzabi
"Subhanallah,amma shine kike ta cewa ba komai baby?" Kai ta langabe batace komai ba,sai qishirwa dake damunta,kamar ya gane me take nufi,ya isa fridge ya ciro mata ruwa mai madaidaicin sanyi ya bude ya miqa mata,tana tsaka da sha ya nema gefanta ya zauna yana murza agogon hannunsa
"Banajin tafiyar nan zata yiwu......"
"......don Allah uncle" tayi saurin katsar numfashinsa,tunda taji zasuje ayi mata vaccination na tafiyarsu wadda duka duka saura kwanaki biyar ta matsu suje din,ido ya lumshe yana dariya
"Bance wai an fasa ba,nima inason zuwa naga hajiyata,bazata yiwu ya mota ba,bari na duba mana rocket ko zamu samu koda evening flight ne" ido ta rufe tana dariya,kunya kuma tana kamata na yadda tayi saurin yanke masa hanzari
"Kayi haquri uncle"daga kansa yayi daga danna wayar ya kalleta yana murmushi,bai taba zaton bada haquri abu bane mai sauqi wajen diya mace ga mijinta ba sai daya zauna da widad,kalmar haquri kalma ce mai matuqar tsada da wahalar furtawa a wajen hafsat,tsahon shekaru bakwai,adadin lokuttan da ta taba buda baki ta bashi haquri tsaf zai iya qidayesu da yatsun hannunsa.
Kafin su fita daga gidan zuwa airport ta qarfafa jikinta,duk don wai ya sake yadda ba wani ciwo take ba,ya kuma janye maganarsa na suna sauka yau din gobe zai kaita a dubata.
Sau uku tana kiransa wayarsa a kashe,ta qagu su iso tayi ido hudu da widad din kamar yadda ummanta tace ta fara tsaiwa ta tabbatar da gaske da cikin?,ta duba idan taga wani canji tattare da ita,idan akwai alamunsa to zasu bincika su dauki matakin da duk hafsat din taso.
Tana parlor tana shayar da baby yusra,su nawwara sunata sabgarsu cikin falon,sassan dai kamar ko yaushe sauqi sai wajen Allah,duk da ta dauko diyar anty ummee ta tayata zama har zuwa sanda zatayi arba'in,to amma itama yarinyar aikij ya mata yawa,abinda taga zata iya shi takeyi.
Ko kusa ko alama bataji alamun shigowarsu ba,don mota ya dauko daga airport,ba kamar yadda ya saba ba,idan flight zai biyo yana kiran umar yazo ya dauka motarsa dake nan ya daukoshi ya kawoshi gida.
Yusra ta cire daga shayarwar da takeyi,idanunta a kansa sanda yaran suketa rige rigen isa wajenshi.
Mummunan kishi ya kama zuciyarta,duk sanda zaizo mata weekend sai taga ya canza,sai taga ya qara fresh ya qara murmurewa fatarsa tayi wani lumaui,komai nasa fes kamar wanda akewa wankan inji.
Qarasowa yayi ya duqa yana shirin karbar yusra,dai dai sanda take masa sannu da zuwa,ya amsa yana dan dauke numfashinsa hadi da daukan yarinyar yana kallonta,tausayinta yana cika zuciyarsa,ba alamun qamshi jikinta bare na mahaifiyarta,yadan ja kumatunta yana mata wasa duk da ba gane komai takeyi ba,yayin da hankalin hafsat ke kansa,tanason jin tare suka zo?.
Amsarta ta fito kuwa sanda mimi ke tambayarsa ina anty widad?,yauma batazo ba?.
Murmushi ya sake,qauna ce sosai da shaquwa me yawa tsakaninsu da widad din,tamkar ma itace ga haifeta ba hafsat din ba
"Tazo,muje ku gaisa" sai ya sanyasu a gaba suka fice,suka bar hafsat da lissafin yadda zata shiga ta ganta din,don yarinyar ya canza hali,wani irin canji da tafi zaton akwai masu zugata na gasken gaske daga gefe,tasan tsaf daga halinta ba zasu hadu ba sai ranar da zata koma Kaduna.
Ya sameta harta cire kayan jikinta,ta saka wata black rmless gown A shape,tabi lafiyayyar farar fatarta ta.kwanta,ya bita da kallo tsigar jikinsa na zubawa,yana jin wani abu mara dadi na masa yawo a rai,yasan yau da gobe duka zaiyi missing dinta,saidai yasan zasu hade a kano,kuma tabbas zaya fanshe kafin su tashi.
Bakinta har kunne ta karba yusra tana mata wasa,ita da mimi da nawwara duka sun zagaye yarinyar,tana mata waqa suna mata amshi,sai ya koma gefe ya harde hannayensa yana kallonsu murmushi yana qwace masa,yana hasashen yaranta kamar haka.
Daga kai tayi suka hada ido,sai ya kashe mata ido daya yana mata murmushi,ta maida masa martani,Allah ya zuba mata son yara,baisan wanne irin son yara gareta ba,abinda ko uwarsu data haifesu bata damu da yi musu ba amma ita saita bata lokaci tana wasa dasu hadi da kula dasu.
Anan yabar mata duka yaran ya wuce sashensa, pampers din yusran da widad din taga ya cika da kashi ta cire mata cikin jin tausayin yarinyar
"Tun dazu da take kuka na cewabmommy kashi tayi sai tace ba yanzu zata cire mata ba" duban mimi widad tayi cikin mamaki,itadai ta sani,yayyenta da matan gidansu duk sanda yaro yayi bayan gida cire masa shi sukeyi,takanji sunce yana cin jikin yaro sai wajen yayi ja ya zama ciwo.
Wanka tayi mata da ruwa mai dumi sosai,ta shafeta da farar powder ta goyata ta fara gyaran sashennata,tana aikin yarannna biye da ita,yau daya nishadinsu ya canza,sashen ba aiki sosai don ba datti bane sai qura,nan da nan ta gama ta cikashi da wannan qamshin da ya zamewa gurin jiki.
Ko kafin ta gama ma yarinyar tayi barci,saita kwantar da ita tayo wankan itama ta sauya kaya ta zura hijab ta tayar da sallah.
Tana idarwa hafsat tana sallama,ta shigo idanunta akan widad din kamar zata cinyeta,bata lura ba don zuciyar a wanke take,ta gaidata ba yabo ba fallasa,ta amsa tana sake qare mata kallo.
Tabbas tayi qiba,ta kuma yi fari sosai fiye da farinta nada,amma kuma sanda ta miqe zata dauko mata yusra dake bacci bataga tudun komai a tare da ita ba,wannan shi ya saka mata shakka a ranta,ta debi yaran suka baro sashen tana lalubar number ummanta.
Bayani tayi mata na canjin data gani din daga wajenta,sannan ta dora mata da
"ta danyi watanni umma da wannan canjin,idan ciki ne ya kamata zuwa yanzu ya fito,amma banga alamar komai tare da ita ba" shuru ta danyi tana nazari,ta sauke ajiyar zuciya sannan tace
"Ba'a nan take ba hafsatu wai an dannewa bodari kai,zanyi magana dashi,kome meye yake akwai su basa rasa ganinsa".
Yana zaune daga bakin gadonsa,hannunsa dauke da tab,yana bibiyar statement na wasu masu laifi dake tsare a hannunsu,hafsat na daga gefe tana lallaba yusra tayi bacci fuskarta aa hade ranta a bace,tunda abbas din ya gaya mata kafin ta iso gadon tayi wanka take kumbure kumbure harta gama ta maida kayan jikinta ta dawo gadon,yayi haka na bawai don yana da bauqatarta ba,kawai ya fuskanci idan ba wanna titsiyen ya fara yi mata ba haka zata ci gaba da tafiya,sau daya ya kalleta bai sake dubanta ba,baisan me yasa har abada take sha'awa shigo masa bedroom da kayan data wuni dasu cikin gida ba,baisan sau nawa zai kwatanta mata bayason hakan ba,a yanzun da yake ganin sauyi daga wajen widad,sai abun ya daina bata ransa,tunda at least yana samun sassauci idan ita din taqiyi masa yadda yakeso,sai mamaki kawai da take bashi,sau tari tafi ganewa ta kwana da tufafinta,atamfa ko shaddar da tasha kwaramniyar yini guda da ita.
Dakin shuru kamar ba kowa har ya gama aikinsa,koda ba aikin yake ba haka zaman yake dama,ita bata iya hira da miji ba,shi kuma dama tun asali miskili ne,yayin da take kallon miskilancinsa a matsayin zallar wulaqanci ne kawai (bata iya tsaiwa ta karanci ya yake).
Tab din ya ajjiye a bedside drawer yana jan duvet dinsa zuwa qugunsa yana kallonta
"Kiyi qoqari gobe da sassafe ki rubuta duk abinda kuke da buqata na kamar wata biyu haka,idan Allah ya kaimu ranar alhamis zamu wuce hajji ni da widad".
Kamar wadda wuta taja ta kalleshi da sauri
"Kai da wa?" Ta sake tambayarsa ba tare data bi takan sauran bayanansa na baya ba,sunan daya fada sai taji kunnenta kamar baiji mata dai dai ba
"Widad" ya sake fada yana kallonta hankalinsa kwance idonsa yana dan lumshewa saboda baccin daya fara ji.
Cikin zafin nama ta miqe ta zauna sosai, kaman zata bige yarinyar saboda yadda ta tashin da sauri
"Kasan me kake cewa abbas?,da widad zaka tafi hajji?" Dubanta yayi
"Me na fada da yake alamta ba cikin hayyacina nake ba?" Yadda yayi maganar cikin bagararwa kamar ba wani mummunan abu ya aikata mata ba,ta tsareshi da ido,wani yayyafin zafi yana sauka daga zuciyarta yana ratsa kowanne sashe na jikinta,tafasa sosai zuciyarta ta dinga yi,ta rasa wacce kalma ce ta dace dashi,saita kuka kawai.ya balle mata,ta miqe tana sauka daga kan gadon cikin hargagi masifa da daga murya ta fara sake masa maganganu marasa dadi,ya rufe ido yana jinta har zuwa sanda tace
"Kuma duk munafukan da suke sake shirya wannan abun Allah ya tsine musu albarka idan basu fasa ba,ni dasu shege ka fasa"
Wata gigiyacciyar tsawa ya daka mata,yana dubanta da idanunsa da suka fito waje
"Shirmenki ya isheni haka,fita ki bani waje shashasha mara hankali,a gabana zaki tsaya kina furta tsinuwa munafukai da sauran shirmenki!,zaki fita ko sai na baki mamaki?" Hannu tasa tana son dauke yusra daga kan gadon,tsananin bacin rai yasa ya janye yarinyar gefe,saita koma ta tsaya tana cewa
"Mamaki kuma na nawa?,aika gama bani mamaki,wallahi tallahi inda nasan haka kake da bazan taba aurenka ba,amma kaje na barka da Allah" ta juya da gudu tana kuka da qaqqarfan sauti ta fice a dakin.
Hannunsa gaba daya qaiqayi yake,tabbas inda wani ne a waje yayi masa hakan yau sai ya gane shayi ruwa ne,bayason shaidan ya dinga tunzarashi ta sanadinta ya zama madoki,sai ya dinga ambatar Hasbunallahu wani'imal wakil.
*********Karfe goma na safiya ta gama shiryawa,tun jiya cikin zumudi ta kwana,tayi zaune a parlor tana jiransa.
Da sallama ya shigo falon,muryarsa tayi laushi sosai saboda baccin da bai samu ba isashe daren jiya,ya zama wani so cool yayi kyau cikin shigar qananun kayan da ba kasafai ya fiya sanyasu ba,yau din yayi amfani da sun glasses wanda zai hanaka gane ainihin qwayar idanunsa,sai ya qara masa wani mugu mugun kyau,har widad ta kasa dauke dubanta daga kansa.
Duk da yadda ya sakaye qwayar idanunsa amma hakan bai hanata ganin canzawar mood dinsa ba
"Oga zumudi..... let's go,banaso rana tayi mana sosai,inason na dawo gida na huta"ya fada yana duba agogon hannunsa.
Tare suka jero zuwa harabar gidan yana riqe ds hand bag dinta tana gyara rolling na mayafinta tana masa shagwabar don Allah idan anzo yin allurar ya tsaya a wajen.
Murmushi ya sake,ko yaushe tabararta na nasarar korar bacin rai ko damuwarsa,wannan ya sanya koda daga office wani abu ya bata ransa,tattara komai yake ya dawo gida,yana da yaqinin zai samu magani sa sassauci,koda batasan me yake damunsa din ba,koda batayi komai da nufin korar bacin ransa ba.
Da kansa ya bude mata seat din motar ta shiga,ya tsugunna ya tattare mata rigarta data fito sannan ya miqa mata hand bag dinta.
Hadawa tayi da hannunsa ta riqe tana kallon qwayar idanunsa
"Me?" Ya tambayeta ganin yadda ta bata fuska
"Smile mana uncle,kayi kyau yau,amma kaqi kayimin dariya.....haba mana uncle" ya qarasa fada a shagwabe.
Don dole bai shirya ba siririn murmushi ya kubce masa,ya duqa a tausashe yayi kissing goshinta sannan ya zagaya ya tayar da motar.
Suman zaune hafsat dake kallonsu ta dakin solar dinsu dake daura da wajen tayi,taji jiri kamar yana dibanta,har sai data samu waje ta zauna ta wucin gadi,kafin kuma kuma ya qwace mata,ta jima zaune a wajen tana kukan,har sai dataji shigowar sale sannan ta miqe tana barin wajen don kada ya sameta a haka raini ya shiga tsakani,saidai tana jin zuciyarta ta tsike gaba daya,zuwa yanzun komai ta fanjama fanjam,don haka wayarta kawai ta dauka ta fara neman number ummanta ba tare data damu da kukan da yusra ke tsalawa ba, wadda ta tashi daga bacci tun dazun taji ba'a Kula da ita ba.
Idanunta fal tsoro,ta waiwaya tana dubansa sanda zata shiga dakin da ake bada rigakafin tana kallonsa
"Please uncle,don Allah ka rakani"
"Muje" ya fada yana maida wayarsa aljihun wandonsa suka shiga dakin a tare.
Yadda taga suna gaisawa da likitar ya tabbatar mata akwai sabo tsakaninsu,tadan kalleshi,abbas din badai miskilanci ba,ya sansu amma ya maze mata,suka hada ido ta masa sing na zan rama,ya dage mata girarsa daya kawai.
Fitsarinta suka fara buqata,tayi ta kawo mata aka bada gwaji.
Gyara zaman glass din fuskarta likitar tayi sannan ta dago kai tana duban abbas din
"Sir,bakasan madam nada juna biyu bane?" Sosai ya kalli likitan,sai ya zare gilashin idanunsa
"Juna biyu?,Kina nufin,she's pregnant?"
"Yes sir.....alamu ma sun nuna kamar yafi wata biyu"
"Ya salam ya Allah"ya fada zuciyarsa na wani irin bugawa da matsanancin farinciki,kamar wanda aka yiwa albishir da samun haihuwa karon farko bayan wasu shekaru daya diba yana neman haihuwar ba tare daya samu ba,ya bude idanun nasa fuskarsa na fidda wani irin murmushi yana sauke dubansa ga widad.
*H A F S A T*
Kamar zata zauce sanda taketa kiran ummanta ba tare data daga ba,muryar umman kawai takeson ji ta isar mata da saqon abubuwan da takeso a gabatar mata akan widad din,tana jin idan bata d'ai d'aita rayuwar yarinyar,ta gigita mata rayuwa ba tabbas mata ta rako duniya,indai bata dauki mataki mafi muni a kanta ba bata cika hafsatu ba,yarinyar tayi mata abubuwa masu.muni dake da yawan gaske,ba zata yaba qyaleta ba itama,ta rabata da abu mafi soyuwa a wajenta,halittar da duk duniya ba wadda take qauna sama da ita ABBAS dinta.
Sai data yi mata kira biyar a jere,ana shidan ta dauka,kafin hafsat din tace komai ta rigata
"Yauwa,nima ke naketa nema ai,ina hanyar dawowa daga gun aiki ne......,akwai gagarumar matsala hafsatu,akwai matsala" kalmomin umman nata da kuma tashin hankalin dake cikin nata kwanyar suka hadu suka kusa fasa mata kwanya,saita sulale ta zauna sosai a wajen tana jiran jin gagarumar matsalar dake tunkarosu din.
*A L H A M D U L I L L A H*
*_Masu karatu..... bakuji komai ba,baku karanta komai ba,kawai abinda zance daku shine......kuyi jumirin bibiyata,muje zuwa bayan hutun azumi,in sha Allah ina tafe da kashi na biyu na labarin A RUBUCE TAKE k'addarata,nima ba haka naso ba,amma yanayin yadda labarin ya dauko tunda farko,bazai taba qayatarwa ya bada ma'ana ba sai an cimma gacinsa,zanyi qoqari da ikon Alalh bayan sallar pages din sunfi wadan nan da muka gama tsaho in sha Alllah,fata na Allah ya bamu aron rai da lpy_*
ina muku fatan ALKHAIRI AREWABOOKS FOLLOWERS dina,wadanda baku gajiya da bibiyata, alkhairin Allah ya kaimuku a duk inda kuke,ayi ibada da bukukuwan sallah lafiya,na barku lafiya