Achan Madina kuwa Danmallam dai da Sarood balarabiya suna ta gwangwajen amarcin su sosai fa ya Saki jiki yana Morewa Saboda ai ya Dade Rabonsa da mace tun Kan Amina wannan kuma ai ya Daukesa a matsayin Rabo ne shiyasa daya samu wannan Damar yake ta amfana da ita Domin Daman Daurewa kawai yake yi Yana fama da azumin Litini da alhamis saboda kariya da Tsare kansan.
Ita kanta Sarood din sai alokacin tasan ta yi aure sai kuma ayanzu tasan tana kishin Mijinta ada kamar bata Damu da kishin Sakina ba ammh yanzu da tasan waye Umar sai taji har Sakina ma tana matsanancin kishi da ita ballatana Amina datafi Tsayamata arai ganin itace yarinya sannan kuma Amarya.
Sosai take ta shagwabanta shi kuma yana lallabata Dalilin haka ne ma yasa har yau bai kira Amina ba Saboda ai sun yi mgana da Hajiya washegarin Ranar data koma Gumel a wayar Nazir Saboda ya cika alkwari yaje ya kwana Daya Ranar Litini da Safe ya hau Jirgi ya koma hankalinsa ya kwanta daya ga Hajiya lafiyanta kalau Cikin koshin Lafiya.
Da farko kafin Bullowan Cikin jikin Amina har ya fara Cuku cukun nema mata Takardan Zama madina sannan har sun yi shawara da Aliyu kan zai shigar da Takardan kan zai karbi Gidan malamai na makaranta Saboda gidansa yayi musu kadan sai ya saka Amina ana Cikin makaranta,Sai kuma ga wannan al"amarin da hajiya tace ya Dakatar da komai Shiyasa ya dan Samu Sauki ya fara shirin Tahowa saboda Sakina sannan uwa uba Amina yana son yazo ya ganta Tunda ya tafi bai fi sau hudu sukayi mgana ta waya ba sannan Sakina duk sanda sukayi mgana ta Dinga mai kuka keman tana fadin yazo ya tafi da ita Tsausayinta yake ji ganin halin Datake Ciki yasa yayi mata alkawarin zai zo nan da wata Biyu zai zo sai su koma Tare Umra yake so yayi shiyasa ya Dakata da Tafiyar Sannan Sarood ma tayi Damara sai taje kuma in yace bazai je da ita yayi rashin adalci ko Iyayanta sai sun ga rashin adalcinsa...!
Tunda suka yi mgana da Hajiya tace kada ya sanar ma kowa ko Aliyu bai Fadama komai ba yadai Fadamai laluran nan tasa Allah ya basa waraka da Taimakon shawarwarin mallam Daganan kuma sun ma Dade basu yi mgana ba daya kirasa sai ya Fara mai Tsiyan ya barsa ne yaci amarcinsa da yar Balarabiyarsa Danmallam Tsaki kawai yake yi da Dariya domin ba karya yana fa shan amarci.
Sai da Amina tayi kwana Goma A Abuja sannan ya nemi wayarta da lambar da Jafar ya Dade da Turomai sai kuma ya kara jin wayar a kashe bai ji Dadi ba in yace Amina bata aransa yayi karya abubuwa ne suka sha mai kai sannan da Tazaran Dake Tsakaninsa da ita da rashin shakuwa da kuma Basu wani saba da juna ba.
Aisha ya kira kawai saboda ko ya Kira Hajiya bata kusa da Amina.
Daman duka kannensa suna kiransa awaya suna gaisheshi lokaci bayan Lokaci Haka suke basu yar da tarbiyan gidan mallam ba ko da yayyinsu basa kusa dashi suna Kiransu a waya suna Zumunci dasu Lokacin Ba'rin Sakina sun ta Kiransa suna mai Jaje.
Lokacin da yake tambayan Aisha mganar yaji wayar Amina akashe ya Aisha tace bata sani ba ammh Zata tambayi Aminar taji tunda ita tama manta da mganar wayar sannan batama Taba ganin Aminar da wayar ba.
Yace to ta fadama Amina yana son mgana da ita ta kuna wayarta Ya Aisha ta amsa da insha Allahu zata Fada mata ya tambayeta ya jikin Aminar..?
Ta sanar dashi lafiyanta kalau sai godiya Zazzabin Dare dai take fama dashi sai amai sannan bata iya cin kowani abinci sai Tea sai Kuma wainar Fulawa,Komai Taci baya Zama sai ta Amayar dashi sai yaji Tausayinta gata yarinya ga shi ya Dora mata nauyi sun yi mgana da ya Aisha sosai ya sanar da ita suje asibiti tace eh Usman ne yace ta bari ya Dawo yaje Kaduna wani aiki Da haka suka rabu..
Suna gama wayar Aisha ta nufi Dakin Yakaka tana shiga ta iske Amina Zaune saman Cafet tayi Daidai tana cin wainar Fulamai mai manja da Saude mai aikinta tayi mata Tun Safe bata ci komai ba Tea din ma yau taki sha ita sai Wainar Fulawa Shine Yakaka tace Saude tayi mata Wainar Fulawan har Sauden tana Dakin ne suna ta Hira Yakaka na basu labarin Cikin kakan su Usman har ta Haihu kanwa ne abincinta sai da bakinta ya Lashe saboda Cin kanwa tana Fadama Amina ta godema Allah tayi ma Ciki mai kyau tunda batayi mugun laulayi ba sannan ta iya shan Tea da Cin wainar Fulawar tayi kyan ma Laulayi.
Amina sai cin abunta take yi tana Dangwala yaji tana Sanye Cikin Bakar Doguwar riga cikin kayan ya Aisha ne da ta bata take sakawa tunda kayanta sun Daina Shigarta Cikin fa Kiba kawai da Budewa yake saka Amina ta bari ne Usman ya dawo su je asibiti da kasuwa ta siyo ma Aminar Dogayen Riguna tunda duk ta bata na wajen nata sannan sun ma Aminar karanci.
Shiga Dakin tayi da Sallama Suka amsa mata,Saude tama mgana tace taje Kitchen ta Dora Girkin Rana Ta amsa da Toh ta fice sai da ta fita sannan ya Aisha ta kalli yakaka tana Fadin"Yakaka sannu da Hira..!
Tana Dariya tace"Yauwa Sannu Aisha..Hala har kin kwanta Hirarmu ta, tada ke..?
Aisha tace"A"a Wlh ina ta gyare gyare ne ma Yakaka ban ji ma Hirarku ba..!
Yakaka tace"Au ho..Ai ina nan ina ma Takwarata Tsiya ina fadin ta godema Allah tayi Ciki mai kyau ba laulayi sannan ta na cin abincin Zamaninmu ni lokacin da nayi Cikin Gaddafi har na Haihu kanwa ce abincina..!
Ya Aisha ta jinjina kai tana fadin"Kanwa..?
Taba..Yakaka kin sha wahala..!
Ta yi Dariya kafin tace"Ai Darajan Uwa ta Daban ce Aisha..Allah dai ya bama kowa nashi kema ina miki addu"an Allah ya baki naki Aisha ita Aminatu ai tana mai kyau ma Kinga banda aman da take yi to sai Zazzabin Daren dana ce miki tana Faama dashi..!
Ya Aisha tace"Eh zamu je asibiti taga Likita ma yakaka in Usman ya Dawo..!
Ta jinjina kai kafin tace"Hakan yana Dakyau..Allah ya Dawo dashi lafiya..!
Suka amsa da Ameen harda Amina Data gama ci ta Kora da ruwa ta koma Tana Sauke Numfashi.
Ya Aisha ta kalleta tana Fadin"Amina ina wayar da Hajiya ta baki da Zata tafi..?
Amina ta Dafe Cikinta daya Fara Fitowa ta yamutsa Fuska kafin tace"To ina na sani..?
Tunda ta bani chan Dakin na wurgar da ita..!
Ya Aisha ta hararrta tana Fadin"To daman don ki ijiye Aka baki wayar..?
Kefa kina da sarkaci bayan ma jidalinki wani Lokaci..!
Amina ta kalleta kafin ta Tura baki ya Aisha tace"Tashi muje ki Daukomin ita na saka miki chaji tunda Daman Hajiya tace Sabuwa ce..Mijin ki ya Kirani yace yana son mgana Dake in fada miki ki kunna wayar hannunki..!
Amina ta kalleta Shekeke kafin tace"Mijina kuma..?
Ya Aisha tace"Eh ko ba mijin naki bane..?
Amina ta Hura Hanci kafin tace"Ina Laifin kice yaya danmallan..?
Ya Aisha tace"Ni yayana ne ke kuma Mijin ki ne..karyan iskanci kike yi bakin ki ya Bude yanzu ko..?
Amina ta Yi fari da ido kafin ta bata rai Lokaci Daya tana Fadin"To ni yaushe rabon daya nemeni?
Ko tawayar Hajiya yaushe da Rabon Daya Kira yace abani..!
Tafada tana bata rai saboda Tsakani ga Allah tana jin takaicin hakan wato bai Damu da ita ba..?
Ya Aisha ta rike baki Tana Fadin"Au Daman kina jiran sai ya nemeki ne..?
tab kina da aiki kada ki manta wata matar garesa achan sannan anan ma yana da Sakina mu masu mu kadai muna Kula da Mazajenmu ballatana ke mai Kishiyoyi har biyu.?
To ki rage wannan Sakarcin naki ko ba Haka ba Yakaka..?
Yakaka ta gyara Zama Tana Fadin"Au to gayamata dai ai ni nan Tunda naji yarinyar nan da Zama da kishiyoyi har Biyu nace Zama bai ganni ba..Tana Haihuwa Gyaran yan maiduguri zan
Mata wanda ba su biyu ko su Uku ne itace ta Hudu sai ta fita Zakka..Ai mu masu sunan mu ba Borori bane..Muna da Tasiri sannan wlh badai mutum ba Sai ta Allah..
Amina na Dariya Ita da ya Aisha wacce tace"To ai Kirarin ta kenan Yakaka Aminene badai ta Mutum ba sai ta Allah..!
Yakaka tace"Ai Gaskiya ne..Ke kwantar da Hankalin ki yar nan har nan Zai zo yana mana yar murna sai mun Wahalar dashi ammh dai kafin nan tashi maza ki Dauko wayar ajonata in ta Cika sai ki kirasa ai mune akasansa ba komai in min nemesa muma watarana Zai nememu ko don Darajan wannan abun da ke Tare Dake in ya manta Dake don Kaniyarsa ai bazai manta da wannan aikin Daya kunsamiki ba..!
Amina sai ta kasa mgana kunya ya kamata ya Aisha kuma ta Fice sum sum tana Dariya Dole Amina ta mike tabi bayanta suka shiga Dakin atare ta Dauko wayar nan Gefen katifa inda ta Watsar da ita Aisha ta karba ta Bude ta a kwali ta jona mata achaji Tana ta mata Fada fadi take"Wlh ijiye wannan Jidalin naki Zaki yi agefe wajen bautar aure ba wannan ake Bukata ba..ki iya Kissa da Kisisinan rike miji..Ni ban ma jin balarabiyar nan Sakinar ce mai ido a Tsakar ka..Kema ki Samu ki Zama mace awajensa..!
Amina dai batace komai ba aranta Tace ai so ma suke ya Sakeni baki sani ba.
Afili kuma batayi mgana ba Saboda abun ya fado mata arai duk da Tana kokarin Cire abun aranta ammh kuma har Abada bazai taba Fita ba..
Har ya Aisha ta gama fadanta ta fita batace komai gefen katifa ta koma ta Zauna tayi tagumi in ta Tuna kalaman mamanmu na kashe mata uwa sai taji ta tsaneta kamar tayi tsuntsuwa ta ganta agabanta ta Chaka mata wuka har sai ta Daina Numfashi.
Sannan ga kewar yaya aranta ga kuma Rashin samun wanda Zata Fadamawa baalle ta samu sauki ta kwanta akan jikinsa tayi kukan abunda ke ranta.
Haka ta Dinga kuka ita kadai ta Share Hawayenta ta sulale nan saman katifar ta kwanta ta na maida Numfashi har barci ya kwasheta bata Sani ba sai Wajen Biyu na rana ta Farka shima Ya Aisha ce ta tada ita tayi sallah Sai da tayi wanka tayi salla Ta maida Doguwar rigar jikinta ta koma Dakin yakaka ta Haye gadon ta kwanta tana jin yakaka Dake zaune a saman Cafet tana goga goranta tana Korafin ta rage yawan barci mai Ciki da zirga Zirga aka santa tana jinta ta kara Dunkule kanta Cikin Filo aranta tana fadin Yakaka ba kisan irin barcin dana ke ji bane ita dai sama sama ta dinga jin yakaka dagachan kuma barci ya sake Daukanta la"sar nayi yakaka tatasheta tace ta tashi tayi salla ta Daina kuma barcin la"asar.
Fadi take"Ke bake kadai ba..Ki rika barci har yamma tayi in kina son Lafiyanki da abunda ke Cikin ki sai kin kiyaye wasu abubuwan ku yaran yanzu komai Cikin gata kuke yi mu alokacin da in kina da Ciki ko barcin sai kin Ragesa har na Dare bama na yammah ba..!
Amina dai batace komai ba ta Fada Tiolet ta Dauro alwala tazo tayi sallar tayi addu"a domin ta daina Sakaci da addu",an kamar baya da kuruciya yake Dauke mata hankali.
Tana Idarwa ta Dauko Sauran wainar Fulawanta ta Sake ci tana ci tana jan yaji Yakaka na kallinta tana Girgiza kai fadi take"Ki Sautata ma kanki Cin yaji nan wajen haihuwa nake jiyemiki basir ya taso miki..!
Amina tace"Au daman yana Tasowa ne..!?
Yakaka tace"Zaki sani ne in kika shiga Dakim Haihuwa..!
Amina Dariya kawai tayi sai ga Ya Aisha ta shigo tana Fadin"Amina wayar ta Cika na kunna miki..Rike ta Hannunki na Fadama ya Danmallam Zai kiraki yace..!
Ta Fada tana mika mata wayar ta karba tana Tura baki ya Aisha ta Dunguremata kai Tana Fadin"Kinsan Allah ki fita Daga idonaa Amina na Rufe..!
Zamu zo mu Tsara abubuwan da Zaki rika koya fanni girki da gayu dasauran abubuwa sannan har karatu Zamu rika yi,ga yakaka nan na san ban da matsala zata koya miki Dubarun Zaman duniya..!
Yakaka tace"Ai ita Duniya basai an koya maka Dubarunta ba..Ita ke koya maka yin Hankali da ita..barni da ita ai muna Tare har Madina in tayi ba Daidai ba tasha rankwashi..!
Amina tace"Tab wazai bisa madinan..?
Ya Aisha tace"Yakaka kina jinta ko..!?
Tace"Yi tafiyarki barni da yar nema..!
Bata lambar mijin nata ta Kirasa da kanta..!
Ya Aisha tace"Munyi mgana yanzu yace zai kirata..!
Yakaka ta amsa da Toh fita Aisha tayi ta barta da yakaka sai Fada take mata ta shiga bata labarin irin yadda tayi gwagwamarya agidan kakan su Usman Cikin mata Biyu har sai mijinsu ya rasu ana ta Kishi da ita Amina dai tayi bakam tana jinta kafin tace"Yakaka in ka hadu da masu asiri fa suna zuwa gidan Boka..?
Yakaka tace"To Sai me..,?
Ai akwai su duniya ta lalace sai ka koma gefe ka rike Allah ka sa aranka Bawa bai isa yayi maka abunda Allah bai maka ba..yar nan rike gaskiya ki rike Allah ko min Dadewa gaskiyanki Zata bayyana sannan Allah baya barin Azzalumi da sannnu hakki zai bayyana .!
Kai ta jinjina domin ta gamsu da mganar Yakaka suna Cikin hirar ne Taji karar wayar dake gefenta da Farko ta Firgita sai da Yakaka tace mata wayar tace sannan hankalinta ya kwanta Mikewa yakaka tayi da Go ranta ta fice tana Fadin"Mgana mai Dadi kuma ban da Tura masa wannan bakin..Ki ce sabuwar amaryansa tana gaishesa .!
Ta fice ta bar Amina da waya a Hannunta sai da ta Katse sai kuma ya Sake kira tabi jerin lambobin da kallo bata Nigeria bane,Daukan wayar tayi Domin sak irin ta yaya ce tasan yanayinta tana Daga Kiran taji Sanyayyar Muryansa yana mata sallama sai taji kamar an kwara mata Ruwan sanyi ko"ina na jikinta yayi Sanyi har Bakinta ma yayi nauyi ta kasa amsa mai sai da ya maimaita sannan ta iya amsa murya shake Cikin Haibansa yace"Amina ya jikin ki..?
Tura baki tayi kamar yana ganinta kafin tace"Ni ai lafiyata kalau..!
Gemunsa ya sosa kujeran Office dinsa tana Dan juyawa dashi,yace"To ko ya nauyin jiki zan ce..?
Amina sai taji kunya ta kasa mgana cikin wani yanayi yace"Nayi ta Kiranki ban samu ba tunda Hajiya tace min ta baki wayar..!
Uhm kawai tace ya Cigaba da Fadin"Amina kinga lamarin Ubangiji ko..?
Wannan rabon Dake Tsakanin mu shine silar Faruwar duk abunda ya Faru..!
Amina tayi shuru batayi mgana ba shims shurun yayi kafin yace"Ba inda ke miki ciwo ko..?
Amima sai taji wani Rauni ya shigeta kafin tace"Eh..!
Cikin Rudewa yace"Eh kuma..?
To ina ke miki ciwo..?
Amina kai Tsaye tace"Menene mgani in an yi ma mutun sihiri sannan ta wata hanya Zai gane an yi masa..?
Umar yaji mamakin mganarta Cikin mamakin yace"Amina waye akayi ma Sihiri..?
Cikin wani yanayi Amina tace"Ni ce..!
Baki ya Bude kamar tana ganinsa Cikin mamaki yace"Ke kuma..?
Ta ce"Eh..!
Sai kuma kawai ta Fashemai da kuka Har da Sheshsheka Saboda Dacin abun na taso mata lokaci Daya Rauninta na bayanna.
Danmallan jikinsa yayi sanyi Cikin wani yanayi yake fadin"Kinga Amina..bar kuka nan yimin bayani yadda zan gane..!
Ina ko jinsa batayi sai faman kuka take yi Dagacin kukan datake yi Daga karkashin Zuciyarta ne kansa ya Dafe Cikin wani yanayi duk da yasan yarinyar akwai kukan banza har da na siyarwa sai dai jin kalamanta da wannan kukan datake yi tabbatar wani ya faru wanda kedamunta acikinta kuma ta kasa fadamawa kowa..!
Cikin sigar lallashi yake fadin"kiyi hakuri ki daina kuka sanar dani abunda ke faruwa..!
Sai taji muryansa kamar wani waraka ne ga matsalanta yasa tace mai cikin kuka"ban taba Fada ma kowa ba sai kai..Wlh duk abunda Zan fada maka ba karya bane ya Dannallam..!
Da Sauri yace"Eh naji bazan Fada ma kowa ba taimakeni kibar wannan kukan saboda yanayin Dakike Ciki..!
Amina ta share Hawaye tana jan majina tace"Yaya..Yaya. !
Ta fada sai kuma ta kara sakamai kuka Umar ya shiga wani yanayin Tashin hankali da jin kukanta Cikin mamaki yace"Yaya. ?
Amina tace"Eh yaya ba mutuwa tayi ba Kasheta MAMANMU tayi..!
Ta fada tana matse bakinta kada kukanta ya kara fitowa yana Zaune ne sai da ya mike Cikin wani yanayi a Muryansa yace"Yaya ba mutuwa tayi ba kuma..?
Mamanmu ta kasheta..?
Amina ta amsa mai da Eh Cikin kuka Umar ya katseta Cikin Muryansa da kaifi yace"Ki bar wannan kukan yimin bayani sosai yadda Zan gane..!
Amina sai kawai taji ta yarda Data Fadama Danmallam abunda taji ko zai Daina Damunta aranta ko Zata Samu Saukin abunda take ji..
Cikin kuka ta fara Fadamai komai Tun farkon wayar da taji Anty Amarya nayi a ranar da Hajiya tace zata tare da kuma Ranar da Ta kama mamanmu tana mgana da duka mganganunta,Sai dai ta Boye sunan Hajiya Uwa tunda bata san meye Tsakaninsu ba..
Amina ta sharbe hawaye tana Fadin"Da kunbina naji suna waya ya Danmallan..Da kunnina naji mamanmu na Fadin malaminta ta saka ya kashe mana uwa Saboda ta Samu Aba yadda take so Sannan da kunnena naji tana Fadamin Ba ni taso na ZAMA haka ba ya Jafar taso ya lalace da kunnina naji Tana Fadin Bazan haihu Dakai ba Sai Sakina sannan sukace har Abada sai dai aurena Dakai ya kare a gantali..Zuciyata tana min Zafi tun Ranar da naji haka..nayi kukan rashin Uwa Ya Danmallam bansan Dadinta ba Duka Mamanmu ta nesanta dashi ya Zanyi..? Abun na Damuna Zuciyata zafi take min kamar Zan mutu. !
Ta karishe fada Cikin kuka Danmallam Zufa kawai yake yi kansa na juyawa Mamaki da Dimuwa da al"ajabi sun kamasa ya kame awaje daya salati kawai yake maimaitawa acikin Ransa kafin ya samu yar natsuwa Cikin Wani irin Sauti yace"AMINA..!Kin tabbatar da mganar da kika Fadamin..?
Amina ta kara fashewa da kuka Tana Fadin"Wlh in nayi maka karya Allah ya..!
Da Sauri ya Katseta da Fadin"Amina ba kyau irin wannan rantsuwan ba kyau..!
Sai yaji yama kasa mgana Saboda mamakin abunda yaji,Amina kuka ta Cigaba da yi kamar ranta zai Fita yana jinta ya kasa mgana sai chan yace"Kin Sanar da Hajiya ne..?
Saboda yana tunanin kodai Hajiya ta sani ne Data Dauki wannan matakin sai Amina tace bata Fadama kowa ba...kansa ya Daure Tunaninsa ba Lokaci Daya bane yana Bukatar natsuwa Cikin lallashi yace"Ki daina kuka..Sannan ki cire damuwa aranki..Zan yi Bincike a barayina in dai mganar ki gaskiya ne akwai yuyuwar kowa yaji labarin nan,Alkawari Zaki min zaki Daina Tunani da Damuwa bakin gayamin ba .?
Da yardan Allah komai zai zama Daidai kada ki damu..!
Amina ta koma sheshshekan kuka tana Fadin"Haka mamanmu ZAta kashe mana uwa a banza kenan ya Danmallam..?
Kai ya girgiza kafin yace"Ai hakkin Rai ma bazai barta ba Amina..In ma da Gaske ne Allah bazai barta ba sai ya Wulakantata aduniya..Sannan ai Allah ya nuna musu basu isa ba..Suna nasu ne Allah shi kuma yayi nashi..Amina Kina da juna Biyu wannan kadai ya isa kisan Allah ne Kadai mai yi alokacin da yaso a kuma Sanda yaso..!
Amina taji jikinta yayi sanyi ammh bata bar kuka ba shi kuma ya tattaro Jarumtarsa yana ta bata baki da lallashinta Shima kenan datake da shekaru ya shiga wannan Halin balle ita mai karancin shekaru kamar Amina..?
Dakyar ya samu Amina ta bar kuka shi Tunaninsa ma kada Damuwar ta Haifar da Matsala ga abunda ke Cikinta sai da ya tabbatar da ya lallasheta tare da alkawarin komai zai zama Daidai ya karishe da Fadin"Zan zo Gida watan gobe..In nazo sai mu Sake zama muyi mganar musan yadda zamu bullo ma lamarin ni dai ki daina Damuwa Sannan kada ki Fadamawa kowa..!
Amina ta gyada kai kafin tace"Zaka zo nan ne..?
Wajena..?
Yace"Eh zan zo na ganki naga yadda Kika koma in kuma ga yadda Cikina ya zauna ajikinki !
Sai kunya ta kama Amina ta kasa mgana shi ma bai wani Damu ba,baya Cikin natsuwarsa Daganan ya mata sallama ya katse kiran.
Zagayen office dinsa ya farayi kansa ya Dafe ya shiga Tunanin mganganun Amina bai san mamanmu a boye ba sai dan Zahirinta Daya sani kadan ana Fadin Kirkinta,ko abakin yaya yasha jin haka Sannan shi bai da wani Sakewa da ita iyakarsa su gaisa sannan ita kanta Anty Amarya gaisuwa ce Tsakaninsu har gwara itama sukan yi Doguwar mgana Sanadin Sakina Sai dai kuma ya fara jiyo kamshin gaskiya kan mganar Amina Duba da Yaya ance Lafiyalau ta kwanta sai gawa duk da ita Mutuwa ko da Ciwo ko ba Ciwo sai an tafi..!
Ammh Amina yarinya ce ba yadda Zata Zauna ta Tsara mgana haka in ba ji tayi ba Sannan ya tuna yadda Sakina tada hankalinta kan Auran sa da Amina da kuma Matsalan data Faru tsakaninsa da Sarood Aliyu ya fara Hangomai Lamarin a matsayin Shihiri ammh bai yarda ba sai da Mallam ya sanar dashi Cikin Hikima har ga Allah bai zargi Sakina ba ammh kuma yanzu Dayaji wannan mganar sai ya shiga kokonta ya tuna Bakin kishi Sakina da Burinta ita ta Samu Ciki ta Haihu har wani Lokacin ya Dinga mata Fadan ta roki mafi alheri..
Bawai ya yarda da mganar Amina Duka bane sai dai kuma ya shiga Rudi da kokwanto agidansu ake wannan Tsantsan jahilcin da mugunta har da kashe rai..!
Indai ko gaskiya ne Anty Amarya da mamanmu Allah bazai barsu ba sannan sai ya nuna musu basu isa su raba auran da Allah ya kulla da kansa ba.
Cikin tashin Hankali ya kira jafar a waya yana Tambayansa Amina na karya?.. tunda sun fisa sanin yarintar ta shi ba mazauni banw baisan komai kan Rayuwarsu ba.
Ya jafar ya fara fada yana Fadin"Hala iskancinta ta maka..? Ai Amina sai Allah..Wlh ya Danmallan ka daina Sake mata ne. !
Cikin haushinsa yace"Tambayata zaka bani amsa ko zaka Tsaya kana gayamin abunda zan yi da matata ne..?
Saj jafar ya rike baki yana yar Dariya kafin yace"Amina bata da Halin karya..Bata da kumbiya kumbiya ita Free take abunta bata da Tsoro sannan tana da kafiya da Taurin kai yadda kasan zuciyan kafuran farko bantaba ganin wanda duka baya Sata tayi Laushi ba sai Amina..Ko zaka kasheta sai tayi mgana sannan abunda yake gaskiya take fada
Bansanta da karya ba gaskiya..Sai dai Rashin kunya da tsiwa da Tonen fada da Yawon tsiya..!
Danmallam ya jinjina kai alamun gamsuwa kafin ya Datse kiransa ya jafar afili yace"Ko son Amina ya Danmallam ya fara ne..?
Dariya yayi kafin yace"Tab..bai Fada hannu na gari ba..Amina ai jidali ce..!
Danmallam kuwa suna gama mgana ya saki Huci Amina tana da gaskiya wani abu na Faruwa sannan ya Fara ZArgin Hajiya tasan wani abu shiyasa ta hana Amina ta zauna a gumel sannan kuma ta hana kowa yasan da Cikin jikinta tabbas ya hasaso wani abu..
Sai dai koma menene ya kamata yaje Negaria yaga Amina su yi mgana sosai sannan yaga ta ina zai Bullo ma al"amarin da ke faruwa agidansu karkashin Tarbiyan mallam..?
Lalle ana Zaton wuta a makera sai aka sameta a masaka..Zuciyarsa ne taji ta Bude da duka mganar Amina da Tsausayinta da bai taba jiba ba..Dole ya tafi gida cikin watanan mai Shiga abubuwa Dadama suna Bukatar yaje ya gabatar dasu tukunnah..!
*Janafty*
*TFZB2018*
*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Tun daga ranar Danmallam bai taba kwana batare daya Kira Amina ya lallasheta ba ganin da gaske fa abun na cinta aranta Fatansa Allah yasa kada Damuwar ta haifarma da abunda ke cikin wata matsala sannan bayaso ta fadama kowa abunda ta Fadamai mganar tana Bukatar Bincike da Lura sannan ba kowa bane zai iya Daukan mgar har ya Fahimceta sannan yayi tunanin mafita Shiyasa yake kokarin kiran Aminar yana amfani da Hikimarsa wajen kara Lallashinta da bata Baki.
Wani Lokacin yafi Kiranta in yaje Wajen aiki ko in ya bar gida Zashi masallacin Madina ammh in yana Gida baya Kiranta Daga ita har Sakinar saboda Gudun matsala Ga Sarood kamar ta goyasa haka take ji Dashi bazai so yayi abunda zai ci mata Fuska ba shiyasa yake kiyaye wasu abubuwan sannan nauyi ne akansa ya kwatanta adalci Tsakanin mtansa.
Abunda Amina ta Fadamai na nan aransa kamar ya Tuntubi Hajiya da mganar sai kuma ya fasa yana Tunanin ta ina Zai fara duk da fa yana da Zargin Hajiya tasan wani abu Shiyasa ta Boye Amina da Cikin Dake jikinta,Mallam ma kamar Zai mai mgana sai kuma yaga ai bai da wata Sheda itama Aminar ji tayi bata Nadi murya ba Tunkarar wani da wannan mganar ma a yanzu bai taso ba,Sannan abu ne na Kashe rai duk da daman kowa yasan Mutuwa ta Allah ce sai dai mutum ya Zama Sanadinta.
Bangaran Sakina kuma ai ya Dade da Fahimtar mganar Amina Hakane kodaga yadda bata taba mai mganar Amina ba Ranar Dayake so ji ta Bakinta suna waya sai Rigima take mai kan yaushe zai zo ya Dauketa..?
Ita ta gaji da Zama agarin nan baya nan sannan ta yi bari tana son maida Cikinta,Mirmishi kawai yayi kenan mganar Amina ta fito su Burinsu kawai Sakina ta Samu Ciki ta Haihu..?
Saboda ya jarabata yasa yace mata Bata taba Tambaynsa ina Amina ba..?
Sai Sakina tayi Tsaki kafin tace"To ni ina Ruwana..Tunda ta bar min gidan mijina ban damu ba..Ba"an ce hajiya takai ta wani waje ba..?
Yana jinta ammh Daganan bai kara mata mganar Amina ba Itama Sakinan bata Damu ba,ita kamar ma Dadi Take ji tunda ta bar mata gidanta ai taje koma ina ne bata Damu ba Allah ya raka taki gona..!
Allah duk ya shafe musu Tunanin Mezai sa rana Tsaka a Dauke Amina Daga Gumel..?
Duk basu yi wannan Tunanin ba Idonsu ya Rufe da nasu Cikar Burin dukkansu.
******
Usman mijin Aisha ya Dawo washegari suka kai Amina asibiti shi da Aisha speacialist Hop suka kaita Inda Aisha ke zuwa in Bukatar Hakan tataso,anyi mata Scan cikin Amina Har ya shiga wata na Biyar sannan jininta yana sama kadan Saboda Tana saka Damuwa sannan kuma Sugar masu Ciki na son kamata ammh ita da Abunda ke Cikinta suna Cikin koshin Lafiyan an bata mganin karin jini su Vitamin c da sauransu sai kuma na cin abinci tunda Aisha Tayi Korafin batacin abinci Likitan yace Normal ne indai tana cin abunda Cikin yake so ba wata Damuwa...!
Ya sanar dasu zata fara zuwa awo Duk bayan Sati Hudu sannan in yayi shiga wata shidda za"a sake mata wani Scan din
Basu Dade a asibitin ba suka Dawo Gida suka ijiye Amina suka kara Fita kasuwa suka shiga Aisha ta Zabo ma Amina Dogayen Riguna guda Biyar da Wanduna plazo sai ruguna masu yalwar wadanda zasu mata Saboda ta kara kiba kaya wanda tazo dasu sun mata kadan sannan nata bazasu wadaceta ba.
Data kawo ma Amina taji Dadi sosai kamar ta goya ya Aisha tana Daga rigunan adakin Yakaka take fadin"Yakaka kalli Rigar nan bata miki kyau ba .?
Tana zaune saman Cafet tana Gogan goranta tace"Sosai ma ai sai ma kin sakata Ajikin ki takwarata ai mu duk kayan da muka saka sai ya karbemu..!
Ya Aisha na Dariya ta Fice tana Fadin"Ki fito kiyi ma Darling godiya yana Falo..!
Amina in Aisha ta Kira mijinta Da Darling mamaki take bata,agida shuru shuru kamar bazata aikata ba kamar ma batasan komai ba.
Kwashe kayan tayi ta maida a leda ta Saka Hijabinta ta fita falo ta Durkusa tama Usman godiya ya amsa mata yana Fadin"Bakomai Matar yayanmu..Kin dai ji abunda Likita yace ko..?
Ta gyada mai kai kanta na kasa tana jin kunya ya cigaba da Fadin"To sai ki yaye in kina Bukatar wani abu ga Sweety nan ga kuma Yakaka Dukkansu They are Their for u..!
Kanta na kasa ta amsamai Lokaci Daya damai godiya kafin tatashi ta koma Dakin yakaka tana Santin kayanta ta gwada wannan ta gwada wannan tana nuna ma yakaka ita kuma tana yabonta Amina ta gwada wata Riga Mai yalwa ta juya ta Sake juyawa kafin tace"Sai yanzu najini Daidai...Ammh wacce ya Aisha ta bani jan nan tamin kadan fa yakaka..!
Yakaka tace"To Daman ai irin wannan ne Daidai dake..Daga gani ba wani Girman Ciki Zaki yi duk a kiba Zai tsaya .!
Amina ta bata rai kafin tace"Wai sai nama kara Kiba yanxu..?
Yakaka na cin soyayyan gyadan da su Aisha suka siyomata a kasuwa tace"Af ai sai kin ninka kibanki na yanzu..
Ai sai Amina ta Zauna akasa ta Fashe da kuka Yakaka ta saki baki tana kallonta Kafin ta tabe baki tana Fadin"Yarinyar nan kin samu waje..Ki bari Balaraban Madina yazo sai ki mai wannan shagwabar..!
Amina Ta tura baki Batayi mgana ba Yakaka tayi Dariya kafin tace"Tsoro kike ji kada su kwace shi..?
Amina tace"Tab..Allah ya Tsareni ni bana tsoron su har ita gajeran ma..!
Yakaka tayi Dariya kafin tace"yauwa haka nake son naji Tsoro ai ba namu bane..kada ki Damu kina Haihuwa Zaki Dawo silandiyan dinki..!
Amina ta washe baki Tana Fadin"Da Gaske kike yakaka..?
Yakaka tace"sosai ma ai mu ko da kiban mu muka je mune agaba bazamu taba komawa baya ba. !
Amina ta amsa da wlh kuwa Daganan ta warware suka Cigaba hirarsu Daman kukan Aminar na Tabara ne da jidalinta.
Hajiya suna waya da Amina ta wayar Amina Tunda Aisha ta Tura mata lambar Aminar koda yaushe sukayi mgana sai Amina tace ina su hanne abasu su gaisa sai Hajiya tace ba yanzu ba ko Aba bata yarda ta Kira ba sai Mallam kawai ta Turo mata Lambarsa ta Kirasa suka gaaisa ya Dinga mata nasiha da Saka albarka yaji Dadin jin tana Lafiya kalau..
Amina tana jin kewar su Hanne sosai Kamar yadda suma suke kewarta Tunda suka ga sun fara Jarabawar Fita Amina bata Dawo ba suka Sare Hanne tace da sun san ba tare da Amina zasu zana Jarabawar Fita da Mallam ya bar su sun gama SS3 Kamar kowa sai dai ina bakin alkalami ai ya Riga ya bushe.
Duk damuwarsu basu kai Sa"adatu ba wanda hakan da mallam yayi yanuna cewa bazasu Dade agida ba suma zai aurar dasu Shine tashin hankalinta su kuma su Hanne Amina ce Damuwarsu Saboda rayuwar ba Dadi ba ta abaya ashe ba Rashi sukayi ba Tunda Amina na kusa dasu yanzu kuma da basu da tabbas din ina take sai Damuwar tafi ta baya,Sun gaji da Tambayar Hajiya sun kare har Mallam sun tambaya yace su tambayi Hajiya Hamida data tambayi Aba shima yace Hajiya bata Fadamai ba.
Ganin Hamida ta Damu ne yasa Mamanmu ta Kikkira su Jaleela ta tambayesu ko wajen su Hajiya ta kawo Amina ammh har Jordan ta Kira amsar Daya ne A"a sai ta fara Dawowa Hankalinta ta fara Tunanin ina Hajiya takai Amina..?
Har su Zulaihat ta Kira suma suka ce mata bata wajensu kuma kowacce ta Kira sai ta nemi karin bayanin ina Aminar ba"a ganta bane..?
Sai Mamanmu tace wayasani Hajiya dai tace Zata kaita Gidanjenku gashi Wajen Wata Daya da wani abu ba Labari sannan Hajiyar taki Fadan inda take in sukaji basa Damuwa cewa suke ai Hajiya bazata kai Amina inda Za"a Cutar da ita kada ma mamanmu ta Damu Hajiya Zata Dawo da Amina kamar yadda ta tafi da ita.
Mamanmu ta fara Tunanin kodai da wani abu ne..?
Sai kuma ta Tuna ance Dubaran Zaman aure za"a koyamata tuna haka yasa ta watsar da mganar Amina aranta tana ma Hajiya Dariya Tana Wahalar da kanta ne saboda auran Amina da Danmallan ai haka zai kare agantale.
Da sukayi waya da Anty Amarya ma sai da ta mata batun Anty Amarya ta Saki Tsaki Tana Fadin"Nace miki ki daina mana wannan mganar mun gama da wannan shafin..Ba inda Zata kaita Daya wuce maiduguri garinsu tana da inda yafi chan ne..?
Mamanmu tayi Dariya kafin tace"Ai Tunanina bai kawo nan ba..To Allah ya raka Taki gona ya mganar Sakinan..?
Madina ina son kema naga Burinki ya Cika kamar yadda nawa Burin ya Cika .!
Anty Amarya tace"kada ki Damu Saura kadan..Cikin watan nan Danmallan zai zo ya tafi da Sakina kinga in ya tafi da ita shikenan sai naji da Hajiya uwani kuma..!
Mamanmu tace"Ai Hajiya Uwani matsiyaciyace..!
Anty Amarya tace"Babba ma kuwa sai kin ga yadda take shigema Hajiya..Kamar ta Allah..!
Abunda basu sani ba ai Daman in Dubunka Zata cika rasa Dubara kake yi Hajiya gefe ta koma tayi bakam tana karban kowa yadda yazo mata Sannan tana Daina yarda da kowa ta gama Sarewa da lamarin duniya sannan Haj.uwani bata san wani abu ba ita adole tana shigema hajiya tasan wasu sirrukan ai ta Dade da Cin Taliyar karshe tunda Hajiya ta ganota ta DAina bata labarin abunda ya Shafeta da ya"yanta..
Har Falonta tazo tana bin bakin jin ina Amina take taki Fadamata Saboda Sai Daga baya tasan ma Aminar bata bata nan shima abakin Haj Nasara taji Data Tambayi mallam yace hakane ita mamakinta Daya meyasa Hajiya ta Kauda Amina Daga gabanta..?
Ko madinar Aka Turata sai dai tana Tunanin ba Haka bane Tunda taji ana mganar Dawowar Danmallan din Cikin wannan watan..
Sai Hajiya ta bangarar da Tunanin Haj.Uwani da cewa Amina ba Nisa tayi ba Jarabawa take yi a inda take in ta gama Zata Dawo to ganin suma su Hanne sun fara sai ta yarda da mganar Hajiya aranta tace ita wannan auran ai su Amarya da Balaraba sun gama gantallar dashi.
Dayake itama ba Aminar ne agabanta ba Sai ta Watsar da mganar ta Ita yanzu babu abunda ke gabanta sai Shirye shiryen dawowar Nazeem gabadaya Cikin Sati mai Shiga yace mata Zai dawo gabadaya in ya Dawo kuma aikin da zata karisa ai kadan ne har ta Fara hango kanta ta Cika Burinta mganar Anty Amarya kuma bata gabanta tasan ko giyan wake tasha bazata fasa mganar nan har wani yaji ba..Kuma tasan Mama ta sha gaban Bokansu har Mganin Data Karbo ma Sakina sai da mama ta labartamata Dariya kawai tayi in su suna zaune ita ai ta Dade da kwana atsaye kan Cikar Burinta ko kofa bata taba badawa ba ballatana a samu matsala..!
Ashe ashe bata sani ba shi Allah ba"a masa Dubara sannan a lokacin Daka ke Tunanin ka Rufe kofar gefenka ta kofar da bakayi Tunani ba sai Allah ya Wangale taa asirinka ya gama Tonuwa a idon Jama"a.
*******
Kamar yadda Aisha tayi ma Hajiya alkwarin ta kuma ta gayama Amina bata sauya Shawara ba Haka take tasa keyar Amina Kitchen in suna Girki da Saude ta rika gani tana koya mata Saukakkun girke girke,Tun Amina na Tura baki tana kunkunin tana barcinta ya Aisha na takura mata har tazo ta saki ta Fara maida hankali To Saboda ko ta koma Daki Yakaka ke Fatattako ta dole ta Dage tana maida Hankali ballema ya Aisha data koyi Fada tunda tayi aure.
Haka Zata Zaunar da Amina tana koyamata yar shagwaban nan da yadda zata rika ma ya Danmallam mgana da karaiyaya Amina sai ta Dinga Dariya aranta tana Fadin a ina ya Aisha ta san wasu abubuwan agidan kamar in ka samata Hannu abaki bazata Cija ba Kamar ya Aishan tasan abunda take Tunani ta Dunkure mata kai tana fadin"Ban son iskanci ana koya miki yadda zaki zama Tauraruwa wajen ya Danmallan kina Iskanci ko..?
Nasan kina mamakin ina duk nasan wadanan abubuwan ko..?
To ai gidan aure makaranta ne Amina sannan tunda ya siyamin babbar waya nake dan shige shige ina koyan wasu abubuwa sannan Addini ma ai ya koyamana yadda zamu yi mu"amala da kowa har da gidan auranmu..!
Amina ta jinjina kai Domin tana ganin yadda ya Aisha ke yi in ya Usman yana gari kwalliya da salon mgana da kwarkwasa duk tana gani kuma tana Dauka Domin a Zahirin gaskiya itama tana so ta zama mace sannan tunda ga inda kaddara ta kaita ai sai ta Dage Uwa uba kuma taci Uban Sakina ta nuna mata nasu ba irin nata bane Sannan bazatace ta fara son ya Danmallam ba ammh sun fara Shakuwa da juna tunda koyaushe suna Tare a waya kullum Cikin Tambayar baki da wani Damuwa ko.?
Yau da gobe bata bar komai ba sannan ita ai Zuciya tana son mai kyautata mata Amina tana da Budaddiyar zuciya ne shiyasa nan da nan mutum ke Shiga ranta abunda bata sani ba shi ya Danmallam ai jinin jikinta ne shi da take Dauke da Kwansa acikin jikinta,Sannan kuma ba kamar Soyayyarsu da Aminu bane,da ba Sakewa Cikin Tsoro da Fargaba tayi ta wannan kuwa a sake take sannan in suna waya sai tarika jin wannan fa ai mijinta ne wani abu ke shiga ranta batare data sani ba.
Sannan abunda ya Faru Tsakaninsu ya Haifar da wani bond mai karfi wanda Bawa bai isa ya hasaso farkonsa ba ballatana karshensa ba abu Daya ta saani tana jinsa aranta sannan tana Kishi da Sakina daman chan tana jin haushinta balle yanzu da suka Hada miji ko sunanta taji sai ranta ya baci bata ma Damu da balarabiyar nan yadda ta Damu da Sakina ba.
Ko kwana Daya yayi bai kirata ba ta Dinga fushi kenan tana Tura baki in ya Kira taki Dauka Sai Yakaka ta mata Fada da cewa"Tsiya na Dake Sarkaci Takwara..Haka ake karban miji a Hannun kishiya..?
Amina na hura Hanci tace"To bashi bane Jiya fa bai kirani ba..!
Yakaka ta aika mata da Dakuwa tana Fadin"Kin ga naki nan..?
Don bai Kiraki ba sai me..?
Ai kinsan yana da uzuri ko..?
Kada ki Dauka sai ki barma ita balarabiyar ki koma baya ke ko yan Dubaran nan na yaran Zamani da suka iya su Tadama Mazajensu hankalinsu in suna nesa saboda su zo wajensu da wuri baki iya ba,Sai Sakarci da Kunkuni kadai kika iya..!
In yakaka ta fara fadanta bar mata Dakin Amina ke yi abunta ranar kuwa sai taja mai aji Zata Daga kiransa in kuma ta Dauka yana mgana ta basar dashi yasan Laifinsa sai yayi mirmishi yace"Amina kiyi hakuri..!
Sai ya fara fadamata Uzirinsa sannan Zata Hakuri koda yaushe Cikin Tambayanta lafiyanta yake yi tana Bashi amsa ba wata matsala bawani Hira suke ba na ma"aurata ba sai dai suna Hirar abunda ya shafi mganar da Amina ta Fadamai koda yaushe sai tace mai yaushe zai taho Ranar dai yace mata"Cikin karshen watanan..Sannan yana so yazo da Sarood su yi Sati Biyu sai su koma Tare da Sakina..!
Ai Har suka gama wayar Amina bata kara Dariya ba wani Tukikin Takaici take ji wato zai zo da wannan balarabiyar sannan ya koma da Sakina ita ko Oho..?
Sai kuka da Ya Aisha tazo ta ganta Tana kuka Har Hankalinta ya tashi ta Zata ko jikin ta ne take jin wani abu..?
Sai Amina na kukan ba Hawaye tsabar Takaici tace"ba ba..ya Danmallan bane yace wai zai zo da balarabiyar matarsa ba..Sannan in sun tashi tafiya su koma da wannan gajerar matar tasa..!
Galala Aisha ta Saki baki tana kallon mgana kafin ta Tsintsire da Dariya Amina ganin haka yasa ta kara bare Baki ya Aisha ta buge bakin tana Fadin"Kefa ko ya'ya Dubu Zaki haifa na tabbata wannan iskancin naki bazai barki ba..Miye na bare min baki kmar na yankaki Salon yakaka Dake Daki Taji tace nayi miki wani abu..!
Amina ta hura Hanci kafin tace"To bake bace ina gayamiki mgana kina min Dariya ba .!
Ya Aisha ta matso ta kama Hannunta tana Fadin"to na bari kanwata gayamin yaki keso ayi..?
Amina tace"To ni kada ya tafi da Sakinar nan gaskiya..ni fa kadai zai bari anan kuma sai ya Dade kafin ya Dawo. !
Ya Aisha tace"Yanzu waya isa ya hansa tafiya da matarsa Amina..? Ai bamu isa ba matarsace kuma kinga Daman achan take sannan duk keki keda matsala ina nan ina Koya miki irin kissar da zai saka Miji yazo gareka bai sani ba kin ki Dauka nace miki watarana ki sakamai kuka kice cikin ana Miki motsi ke zaki mutu ki Tadamai hankali yayi lallashi ki kinyi Shuru Da gudu zai taho ma Lokacin Tafiyarsa bai yi ba ammh sai ki kalleni kina Dariya..,!
Amina tace"To ai kunya nake ji..Kuma kuma..!
Ya Aisha tace"Kuma me..?
Amina tace"to ai naga shi babba ne. !
Dariya ya Aisha tayi kafin tace"to ai ke kin ji Dadi ma baki san sirrin auran irin su ya Danmallan ba..?
Gaki da kuruciyarki Amina da Shagwaba da Yarintarki zaki sacemai Zuciya shi kuma ya lalace akanki Wlh irin ku an fi sonku kiyi ta Jidalinki yana lallabaki shiyasa na Fada miki shima wannan Jidalin naki aikwai Inda ZAI miki amfani balle nasan shima ya Danmallam din ai yana son soyayya..!
Amina tayi Dariya "To kuwa matarsa bata iya ba..bandai sani ba ko wannan Sarood din..!
Ya Aisha tace"Ke ya akayi kikasan bata iya ba..?
Amina tace'Tab ai na Zauna da su..!
Aisha tace"ai bata iya komai ba sai Fadin rai ita kuma wannan Sarood din naga kamar ta Biye mata sun maida ta wata wawiya ma..!
Amina tace"ai kamar ma wawiyar ce..!
Dunkure mata kai ya Aisha tayi tana Dariya tana Fadin"Tunda ke kin iya sai ki Dage ki rikitamana yayanmu.!
Amina taji kunya ta kasa mgana.
Tundaga ranar ta Bude kunne tana kwasan Abubuwa awajen ya Aisha Da gaske take yi duk sai ta nuna ma su Sakina basu iya komai ba Aminene ai Ta musu Zarra.
Bangaran karatu kam sai da ya Aisha tasha mamakin Amina ba inda baza"a bude mata a Qur"ani ta karanta ba Hadisi kuwa tunda ga na farko har na bakwai suna kanta sannan ta haddace Arba"una Hadith sira ma haka Tajwid wasu Littafan Ya Aisha mamakin Amina ya isheta sai da ta Furta mata tace"Yanzu daman Amina kin iya wannan duk abubuwan kike iskanci a makarantar islamiya da Haddda..?
Amina Dariya kawai tayi tana Fadin"ai ya Aisha ba kowani Hali muke sani na mutanen da muke Tare dasu ba..Muna sanin wanda suka bayyana mana ne..!
Ya Aisha ta jinjina kai tace ba Shakka ko bangaran Boko sai da ta Kusa raina kanta sun yi kunsan mintinaa Talatin suna hira da Usman Cikin Harshen Turanci Amina bata kage ba sannan ba Turancin yan koyo ba Turancin ya Zauna abakinta sosai har Usman sai da yayi mamaki yace mata"Amina fa tana da kwakwalwa..In ta samu cigaba da makaranta sosai zata Zama wani abu watarana. !
Ya Aisha ta jinjina kai tana Fadin"Agida ko sai kace bata gane komai..Bama Damuwa tayi da karatun bafa..!
Dariya yayi yace"ai irin su sun fi raina ma mutane hankali da basa ganewa nan kuwa sun fi kowa Dauke komai Lokaci Daya..Muma lokacin muna Secodary sch muna da wani Dan ajin mu haka mai suna yahaya kamar wawa fa ana karatu yana wasa wlh a Exam shine Overoll..!
Ya Aisha tace"irin Aminace..A aji Dakikiya a Result sai kaga ta Doke kowa ko su hanne Dake maida hankali Tana gabansu..!
Usman yace"Da yawam irin masu baiwar nan basa samun masu Courage dinsu ne in ana kushe su ana cewa basa yi sai su boye baiwarsu sun fi bayyanasa wajen wanda ya yarda suna da ita kanta baiwar..!
Ya Aisha ta jinjina kai domin tagamsu da hakan yanzu sannan baba mallam koda yaushe Cikin Fada yake Uwata yar baiwace nan gaba sai mun baku mamaki aiko gashi ta bata yau wlh Bata Taba jin Amina tayi Turanci ba Duk azatonta batajin komai sai Tsinta tsinta.
Daman haka Lamarin Allah yake Tsammanin Abunda baka Tsammani ba..!
*******
Bayan kwana Shida..!
Nazeem ya Diro gumel Ranar wata Laraba da yammah tun Safe Haj.Uwani ta kasa zama ayi chan ayi nan tasa su Baba lami sun shiryamai kayattacen abincin daya fi so Priderice da soyayyan kaza an yi pepe dinta da kunin aya,Tasa su Akilu sun Share masa Dakinsa an gyara an goge an Baza Turaran wuta Duk ta kasa Zaune sai da ya Shigo gidan Abunda yafara bata mata rai duk yadda Taci Burin Dawowarsa sai da ya Fara Shiga Shashen Hajiya suka gaisa ya Dade ma suna Hira sannan ya kariso wajenta ammh Dayake yar Duniya ce sai bata nuna mai ba ta karbesa Cikin maraba da lalenta kamar ko yaushe.
Ya Duka yana gaisheta ta amsa Cikin Sakewa tana Fadin"An gama karatu gabadaya Nazeem an dawo gida..?
Daman ance kowa ya bar gida..Gida ya barsa..!
Yana Dariya kansa a kasa yace"Hakane Mommy..Mun dawo sai Fatan mu samu aiki atayamu da addu"a..!
Tana Dariya cin nasara tace"ai kama samu aiki ka gama Nazeem..kai fai tashi ka karisa Dakinka kayi wanka ga abincinka nan tafe. !
Ya mike yana mata godiya har ya fara Tafiya tana Binsa da kallon alfahari ganin ya kara girma sam bai yi kama da ita ba yafi kama da Mallam ne kuma suna bala"in kama da Danmallan.
Juyowa yayi yana Fadin"Mommy ina Umai..?
Ya jikinta..?haj.uwani tace"Taji Sauki har ta koma ma islamiya da Hadda.
Kai ya jinjina ya fice yana fadin Allah ya bata lafiya..
Yana fita itama ta fita Kitchen din Tsakar gida tace su kaimai abincinsa da komai da komai tana Tsaye sai da Taga an Dauka an kai ta koma Shashenta ta Kira Batula ta Fadamata Dawowar Nazeem.
Batula tace"Dakyau..To gobe zan yi Sammakon zuwa Minna in samu mama na mata bayani yadda ake Ciki Zaki ji..!
Haj Uwani tace"Nagode batula..Kada kiyi sanya..Kinsan wani Lokacin jinkiri ma yana batamana aiki. !
Da sauri Batula tace"Haba a baya ma ban yi sanya ba..Ballatana da yanzu da muke gabda Cikar Burinmu..?
Kedai sai kin jini..
Daga haka suka sauke wayar Haj.Uwani Bakinta har kunne sauran matan ma su Anty Amarya sai Da Daddare suka san Nazeem ya Dawo da suka gansa Falon Mallan har suka gaisa
Mallam yaji Dadin Dawowarsa Saboda Nazeem akwai natsuwa ga Hnkali yana ta mai fatan alheri da fatan samun aiki mai kyau.
Ranar Hajiya Uwani bata Samu kebewa da Danta ba washegari ma Tare da yan"uwansa Nasir da Jafar suka shigo mata ranta ya sosu sai bata nuna ba ta barsa sai da ya kwana Biyu da ya shigo gaisheta da Safe tana Dakinta taji suna gaisawa da Umaima da Jikin nata yayi sauki yanzu har tana Fitowa falo ta Zauna.
Daman jiransa take yi yana shigowa bayan sun gaisa ta sako mai mganar Dake ranta Cikin Dakiyarta tace"Tunda ka Dawo gida..sai ka fara bin Baban ku sa"idu gidan gona kana Duba wasu abubuwan tunda kaima Harkan kasuwancin nan ka karanta..Wani abun gwara ku masu Dukiyar kuna kusa zaku fi ku kula dasahi Dakyau akan bare..!
Ya Dade yana mamakin kalamanta kafin yace"Mommy ai baba Sa"idu kuwa ba bare bane kema kinsani..Kada ma ki Fada baba yajiki bazaki ji Dadi ba sannan shekaru aruru yana kula da kasuwancin Baba ko Da rana Daya bamu taba jin kansu ba..Sannan infact ma ni bana Sha"awar aiki a karkashin Mahaifina gwara na samu aiki na tara gumina..Na ma yi interview da wani kamfanin Sarrafa fata dake Lagos sun ce xasu neme ni Albashi 100k sukace zasu rika Biyana Duk wata..!
Kafin ya gama mgana ya sha Harara nan ta Rufesa da Fada tana Fadin"Inda Uzairu ya fika kenan shi Burinsa ya gama karatu yazo ya taimaka ma mahaifinku kai kuma Shashaha kana wani mganar kamfani Dubu Darin banza..?
Kasan iya adadin Dukiyar mallam ne..?
To ahir dinka..ba inda zaka yi aiki sai karkashin mallam kuna chan sake da Baki wasu dagachan nesa suna amfana da abunda yake watarana mallakin ku ne.
Gargadi na shine in mallam yamaka mgana ka amsa mai wlh ka kunyatani sai na sabamaka..!
Har ya fice yana mamakin me yasamu mommy ne take irin wannan mganganu ?
Washegari Batula ta kirata tace Mama tace yau da Daddare ta tunkari mallam da mganar bazai mata gaddama ba.
Cikin jin Dadi da Nasarar ta Ta tunkari mallam adaran Daman ita keda Turaka yana cin abinci ta lamkwashe kafa agabansa tana Fadin"Mallan nace tunda Nazeem ya gama karatun nan ya Dawo gida kafin aiki ya samu kasan kasar tamu yadda takkoma sai Kana da wani asama..Sai naga Tunda shima bangaran Kasuwanci ya karanta mai zai hana ya fara Bin Sa"idu gidan gona yana ganin waau abubuwan yana taimakai ko wajen Rubuce rubuce ne tunda naga Jafar ke taimakamai shima kuma kaga ga aikinsa..!
Har ta Sare da ba nasara taji mallam yace"Hakane..Zan m Sa"aidun mgana sai ya fara Binsa yana da kyau hakan Zai taimakamai..!
Haj.Uwani taji kamar ta goya Mallam Dole ta karama Mama kudi haka ta shiga yi ma mallam godiya sai da ya ji mamakinta.
Abunda bata sani ba wani abun yana Tarda Sa"a ne mallam yayi la"akari da nazeem ya Dawo gida Zaman banza zai yi kafin ya samu aiki daman kuma yana da wannan Tunanin shiyasa bai mata gaddama ba.
Da Safe da Aba yazo su gaisa ya Sanar dashi yaji Dadi Sosai,suna ma Cikin Tattaunar ne sai ga Nazeem ya shigo gaida mallam nan ya sanar dashi bai iya cewa komai bs tunda Haj.Uwani tace in yayi gaddama sai ta sabamai.
Shi dai zai bi umarninta dana mallam ne ammh yana samun aiki bazai Zauna ba.
Aranar suka fara tafiya gidan gona shi kanshi a wuni Daya kawai da yayi aikin Lissafi kadai ya yi sai da ya Jinjina Dukiyar baba mallam Aba na Fadamai a duk sati ana Fita da kwai Fin na miliyan Daya sai da ya Rike baki ya dai san gidan gonar babbane ammuh bai Taba maidakai akai ba.
Da Daddare suka Dawo Haj.Uwani daya Shigo Falonta Tana jansa da Hira anan nema ya gayamata tana jin Uban kudi ta zare ido tana Fadin"kaji ko..?
To ban da na gonakinsa kila in kaji abunda yake samu a shekara sai kanka ya Kasa Dauka..!
Sai jin Dadi take yi tana Mirmishi shi dai wannan baya gabansa dukiyar Mallam bazata Burgesa ba Tunda ba nasa bace.
Kwana Hudu da Fara zuwan Nazeem gidan gona da Sakar masa ragamar Wasu abubuwan da Aba yayi Mamammu taji labari shima suna Tare ne taji yana waya da Nazeem da ya gama ta tambayeshi yake fadamata Tare suke kasuwancim mallam yanzu yana taimakamai sosai da Umarnin mallam din.
Mamanmu jiki na rawa ta koma Daki ta kwalama Anty Amarya Kira ta Sanar da ita abunda Aba ya Fadamata.
Anty Amarya ta lailayo ashar ta maka kafin tace"Ammh Uwani dai an yi bakar Tsinanniya..Allah dai ya Tsine mata albarka..
Mamanmu ta amsa da Ameen madina da gaske take yi fa..!
Anty Amarya tace"Ai na rigata..Nasha gabanta wlh..!
*Janafty*
*TFZB2019*
*Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yada'ashi..Pay N500 via Jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Mamanmu tace"To yanzu menene mafita..?
So nake ki nuna ma Hajiya Uwani ita din banza da wofi..bata isa ba kuma bata kai ba wlh..
Anty Amarya tayi kwafa kafin tace"Ki kyaleni da ita Dayyaba..Ni yanzu abu Daya ke gabana Umar yazo ya tafi da Sakina Madina,kuma Hakan na gabda Faruwa saboda Cikin sati nan mai shiga yana tafe sakinar ma ke fadamin jirgin yawo zai fara yo gaba da kayansu..Kinga suna komawa shikenan hankalina ya kwanta Sai na Fuskanceta na nuna mata bata isa ba Daga ita har Sa"idun sai sun Dawo karkashin cewata ai Fara Bin sa gidan gona ba shi ne Mallam ya sakar mai komai ba Tukunnah dai Dayyaba akwai sauran rina akaba..!
Mamanmu gabadaya yanayinta ya Sauya jin kalaman madina har suka gama wayar sama sama take amsata tana faman mata gatsine,Har dai ita mamanmu tagaji ta katse kiran lokaci daya tana bin wayar da Harara tana fadin"Haka kurum na kiraki da kudina da wayata ki Zauna kina neman gayamin mgana ina Dalili..!
Dukiyar ai bataki bace Ko shi mallam din Daya tara bai Damu da ita ba sai ku kuna ta neman halaka kanku Saboda ita har kina Fadin har sa"idun sai ya Dawo karkashin cewarki..?
Haka kurum ba kara sai ki maidamin Miji kamar kwallo ki dinga garasa yadda kika ga Dama to wlh madina Baki isa ba kan Sa"idu zan iya yin komai Ciki har da Raba Hanya Dake sai kowa yayi ta kansa kan mene ina Dalili wannan Bakinciki ina jin Dadi na Samu yadda nake so aikuwa Allah ne ya Hada mallam da Sa"idu ban ga mai rabasu ba haka kurum Madina ke wata mganar banza..!
Surutun ma tana yi ne bata san tanayi ba Aba ne ya fito zai shiga bayi yaji tashin mganarta har ya shiga ya fita tana mganganunta shiyasa ya Leka Dakin nata yana Fadin"Balaraba ke da waye kike ta fada haka..?
Tun dazu nake jin tashin mganarki nama Zata ko da hamida kike ne sai na Leka Dakinsu naga sun kwanta ita da Jawaad.
Sai alokacin mamanmu ta Dawo Cikin Hayyacinta ta fara inda inda tana Fadin"Ni da masu yarenan ne yan iskan sai su kira ka suna maka gwaranci ko kai basa kiranka..?.
Ya saki labulen yana Fadin"To da kin ji sune ai sai ki kashe wayar ki ni ai bani da Lokacin Sauraran irin su. !
Da haka ya koma Dakinsa Mamanmu ta Sauke ajiyar zuciya ta biyosa tana Fadin"Shikenan kuwa haka zan dinga yi musu sai mu rabu lafiya. !
Aranta sai taji salama da Aba bai Tsinkayi wasu daga cikin magnganunta ba.
Ai data shiga goma ba uku ba.
Acikin Satin kamar yadda Danmallam ya Tsara jirgi ya fara yo gaba da kayansu saboda yayi ma iyayansa da matansa siyayya musamman ma Amina Komai ya gani sai yace zai ma masu Ciki kyau harda kayan jarirai masu kyau duk ya siya ammh bai bari Sarood ta gani ba sannan yazo da Ruwan Zam zam mai yawa saboda mallam yamai mgana yana so da Dabinio sai sauran abunda ba"a rasa ba kuma bai sanar da kowa shi da Sarood zai taho ba sai dai agansu kawai.
Kwana Biyu Tsakani kayan suka iso Jafar da Nasir suka je Filin jirgin Kano suka karbo kayan Direct Gidan mallan akayo da kayan Dakin Hajiya Daman kowa yasan in irin wannan ya faru kayan da komai Shashen Hajiya ake ijiyesu kafin ya Danmallam din ya sauka.
Sakina ana chan ana shiri miji zai Dawo tayi gyaran kai tayi kunshi Sannan tayi gyaran jiki da na chan Shawaran Aliya ne ita ta Hadata da mai kayan matan ta siya awajenta.
Miji kawai take jira ta riga ta gama Shiryawanta.
Ko Amina in sukayi mgana in ta tambayeshi yaushe zai dawo sai yace ya kusa bai saka mata rana ba,yaki gayamata ranar da zai dawo so yake ya bata mamaki sai dai ta ga ya Kirata da Layinsa na Nageria.
Haka kuwa akayi Ranar laraba suka sauka da karfe sha biyun Dare,kwana Biyar da sau kan kayansu suka iso a kano jirgi ya saukesu saboda Dare ne yasa bai kira kowa ba suka samu Tashar Mota shi da Sarood sai jakar kayansu suka nufo gumel sai wajen Biyu da wani abu na Dare suka iso gidansa ya wuce kai Tsaye sai dai Sakina taga Bakin Dare sai murnanta ta koma Ciki ganin Sarood sai da ta nuna afuskantar duk yadda taso ta boye hakan Sarood ko Cikin Murna taje ta Rumgume Sakina Tana Murnan ganinta....
Sakina tayi yake kawai tana Tunanin yadda Umar ya maidata banza ai bai gayamata kafarsa kafar matarsa ba Tana jin dadi ta gagari Amina Zama agumel shine zai jajibomata wannan Sakaryan.
Dakin da aka bama Amina ta Zauna Sarood ta shiga sai dai yanayin Dakin da sauran kayan Amina Data gani yasa tasan an zauna adakin Saboda Gajiyan Hanya da kuma Dare yasa sai da Safe ta ma Sakina Zencen tunda suna Dawowa Umar Dakinsa ya nufa yayi wanka ya kwanta Sai barci sai da Safen suna kari Sarood ke tambayan sakina kayan waye tagani adakin ta..?
Sakina Cikin kissa ta ke sanar da ita kayan Amaryan sa ne Amina nan ta Zauna Sarood ta kallesa sai dai batace komai ba ammh ranta ya baci meyasa Sai Dakinta baga Dakinsa ba..?
Sannan wato ita aka raina meyasa bai ce ta Zauna Dakin Sakina ba..?
Kwafa tayi har suka gama karyawa batace komai ba Sakina sai jin Dadi take yi ranta Fes domin da asuba sai da ta ribaci Umar yayi wani abu da ita kuma taga Chanji Sosai yadda ya rikice mata sannan karin jin Dadinta yadda ta zuga Sarood Cikin Ruwan Sanyi batare data gane ba Tunda ita Sakaryace shi kuma Danmallan kunu yasha baisan wata mgana yasan Nufin Sakina tunda ba yau ta saba raina ma Sarood din hankali ba.
Ganin yadda ya Hade rai ne yasa Sarood din bata yi mganar ba Sai dai Daga yanayin ta sha ka matuka da Kishi Sosai.
Suna gama karyawan suka shirya suka suka nufo Gidan Mallam Jafar ya Kira yazo da mota ya Daukesu daman Tun shekaranjiya an san sun iso
Gida ya Rude da Murnan dawowarsa Gabadayansu har da Matan nasa duka Shashen Hajiya suka fara Sauka Har Sakinar domin ba hanyar da zata fara wucewa Shashen Anty Amarya ganin yadda ya Tsare gida..
Gabadaya matan mallam har da Anty Amarya nan shashen Hajiyar sukazo musu maraba su Hajiya Uwani kada aji labari sai barin jiki take yi Danmallan kallon Anty Amarya kawai yake yi yana Tuna labarin da Amina ta sanar dashi bai san Dalili ba sai yaji bai yarda da ita ba Tun balle ma ganin yadda take ta Kiftama Sakina Ido tana so su kebe suyi mgana ganin wannan balarabiyar da bata san da Zencen zuwa da ita ba, yana ganin su yayi kamar bai gani ba.
Nan ya barsu ya tafi falon mallam shi da Nazeem suka hadu da Aba suka gaisa basu Dade ba suka tafi gidan gona ya Dade shashen mallam suna kara Tataunawa .
Fitarsa ne ya bama Sakina Daman sulalewa ta koma Shashen Anty Amarya suka kebe Anty Amarya Cikin Bacin rai tace"Sai naga kuma wannan Sakaryan. ?
Sakina ta tabe baki kafin tace"Nima yadda kika ganta haka na ganta..Ashe da ita zai taho..!
Anty Amarya tace"To me kika fahimta da Zamansu tana nan a Hotonka ko kin Fahimci sauyi. !?
Sakina tace"Anya..?nidai ban Fahimci komai ba..!
Anty Amarya tace"To ki saka musu ido duk nasan aikin mallam na Dadewa yana Tasiri..!
Da toh sakina ta amsa mata suka Ciga da Kulle kullen su tana bata Labarin Tambayar da Sarood tayi na wacce ta Zauna Adakinta da abunda Sakinar tace mata Anty Amarya na Dariya tace"Gwara da kika fadamata haka..Sakaryan sai ta bisa da tsiya..Ai Amina ba zaman gidanki ba ma Mijin da garin gumel gabadaya ne ya gagareta. waya gayamata Barno gabas take..!
Sakina Tayi dariya kafin tace"Wlh kamar fa anyi ruwa an Dauke ko mganar fa bayayi..!.
Anty Amarya tace"Ai bazai yi ba..Wayama sani ko auran ya Dade da Mutuwa fasawa ne ba"ayi ba kada aji kunya su Hajiya an yi Zani an yi Riga. !
Sakina tace"Zai iya yuyu wlh Anty..!
Allah ma yasa hakan ne..!.
Ta amsa mata da Ameen suna Dariya Ranar dai suna gidan har Dare wannan karon Sarood Shashen Hajiya ta Zauna tare da su Hanne tunda suna gida basu da Jarabawa wannan karon Sakina taji Haushin zuwa da ita da akayi yasa bata jata ajiki kamar baya ba
Sai Dare suka koma gida,Washegari shi kadai yazo su suna gida Shashen Hajiya ya yada Zango aka Bude kaya ya bama Hajiya Tsarabanta na Turaren da Hijabin larabawa na mata sai Dogayen riguna guda Biyu masu kyau da Tsada da takalmi haka ma Anty Amarya da Haj.Nasara da Haj.Uwa dogayen riguna da Turare,Wannan karon har Hanne da Hamida yama Tsaraba domin bazai manta da kaunar da Amina ke musu ba, waya goma sai ta ambace su shiyasa daya siyo mata suma ya siyo musu Ya kuma nuna mata tsaraban Amina da Siyayyan kayan Jariran Da yayi,Hajiya Taji dadi sosai ta dinga yabawa sai dai Bata ga Tsaraban Mamanmu ba Tunda Har Aba ya yoma Tsaraba Sai alokacin ya tuna ma da ita Har ga Allah bai yi niyyar bata bane kawai Saboda tundaga Labarin da Amina ta basa yaji matar bata kwanta masa ba sai bai nuna ma Hajiya ba yace ya manta ne sai Hajiya tace bari ta bata Cikin nata.
Sai ta hada mata da Ruwan Zam zam da Dabino.
Hajiya ta aika ma su Haj.Nasara da Tsaraban Danmallan suna ta godiya haka su Hanne suka yi ta Tsallen murna,Ganin har dasu a Tsaraban Hamida da Hannen ma suka kai ma Mamanmu nata ta karba tana ta godiya da Santi tana auna kanta in tayi ma Aba kwaliya da ita..
Mallam dai Turarensa ne na Arab sai Zam zam da Dabino.
Tsaraban sakina gida yakai mata nata Sai jin Dadi take yi ganin har da takalma ga kayan masu kyau da Tsada
Na Amina kuma wajen Hajiya ya barsu su hanne kuwa tunda suka ga basu ga Amina ba kwana uku da Dawowar ya Danmallam ba labarin Dawowar Amina sai suka cire rai da Mganar Hajiya da kullum take sanar dasu Amina zata dawo nan kusa sai suka Sare..
Gashi har sun yi nisa a jarabarwarsu suna gabda gamawa gabadaya sai basa jin Dadin zama,ba Amina suma sun yi ahuru kamar basu agidan da ko da Amina ke nan wlh sai su shiga gidan mallam sau goma gidan Aba ma haka Rashin jinsu kawai yasa Dole ma asan dasu ammh yanzu sai a kwana awuni ba ba"aji ko motsinsu ba.
Islamiya da Boko ma an gaji da Cigiyar Amina Daga baya ma su Hanne cewa kawai sukayi an cireta Daga mkaranta bata agarin harta mariya abokiyar fadanta da malaman makarantarsu Mallam Datti da kansa ya Kira mallam ya tambayesa Amina Mallam yace mai Amina bata gari ne shiyasa..!
Kwana hudu da dawowarsa Ranar yazo Gidan da Safe Ya shiga shashen Hajiya suka gaisa da sauran matan Sannan ya koma wajen mallam to basu Dade da Mallam ba aka kirasa agidan mai anguwa Idi ya tafi kaisa Aba kuma baya nan sai ya tafi Dakin Nazeem ya dan kwanta ya Huta Sarood Tun abunda Sakina ta Fadamata take shamai kamshi sai bai Biye mata ba Sakina kuma kamar rana Daya zai mata Ciki takuranta ne ya Ishesa,yake barin mata gidan ita da Sarood din su ci kansu.
Amina kuma tun washegarin ranar daya sauka daya Kirata bayan ya saka Layinsa na nan ya fadamata ya Dawo suka gaisa har take fadamai sun je asibiti ta fara awo sannan an mata Scan,basu wani jima suna mgana ba yace zai sake kiranta,kuma bai Samu Lokaci ba,Basu zauna sun yi mgana da Hajiya bane yana so yaje ya ganta kafin ya koma tunda ba wani Dadewa zai yi ba Sati Biyu ne zasu yi,zasu koma.
Yana kwance har ya fara barci yaji sallama kamar daga sama yana Bude idanuwansa ya ci karo da Hanne da Hamida suna rabe raben shigowa Hanne na Tura hamida itama tana Turata mikewa Zaune yayi Daga kan gadon yana fadin"Ku shigo mana..!
Jin haka yasa suka shigo Dakin kansu na kasa kamar wasu marayu duk suna Sanye da manya Hijabi har kasa mamakin ganinsu yayi gabansa suka Duka kamar masu neman gafara gaishesa sukayi ya amsa yana Dan Nazarinsa dazu a falon Hajiya yaga Hanne sun gaisa hamidan ne dai bai gani ba. !
Hamida kuma hanne ce taje ta jawota kan suzo su tambayi Ya Danmallam Tunda Hajiya taki fadamusu inda Amina take kila shi zai fadamusu shine suka zo a bakin Hajiya sukaji yana Dakin ya Nazeem Shine suka zo sun kuma kasa mgana saboda ba Sakewa Tsakaninsu sannan yana musu kwarjini.
Shine yaga suna Sunkuye sunkuye kai da taba juna yayi mirmishi kafin yace"Lafiya..?
Baku je makaranta bane yau..?
Hanne tace"ai jarabawa muke yi yau bamu dashi sai monday..!
Ya gyada kai sai yanzu ya tuna da Tsarin Tun farko,tunda Hajiya ta sanar dashi yadai manta ne,Cikin Sanyinsa yace"Kuyi mgana ina Fatan dai lafiya ko..?
Hamida ta sanda kanta kasa tana Fadin"Dama..Dama..Muna so mu tambayeka ne ya Danmaallan..!
Zama ya gyara yana Fadin"Allah yasa na sani..!
Hanne ta zungura ita kuma sai ta kara kasa da Murya tana Fadin"Dama kan mganar Amina ne yaya..
Kai Tsaye yace"Amina..?
Me ya faru da Aminar.?
Hanne tace"Bakomai tunda Hajiya ta tafi da ita har yanzu bata Dawo ba..Muna ta tambayanta ina take taki gayamana gashi har mun fara jarabawa ba Amina muna kewarta ne Hajiya sai tayi ta ce mana zata Dawo Zata Dawo ammh shuru..Shine mukace bari muzo mu tambayeka muji ko kasan inda take..?
Wlh kuma bamajin Dadin Zama ba Amina..!
Hanne ta karbe da cewa"Kawayen mu sai tambayan mu ita suke yi..Kowa sai yace ina Amina.?
Mu kan mu muna son sanin inda take..!
Sai da suka gama Mgana yana kallonsu kafin ya saki Mirmishi ya tuna sanda ya kira Amina yace ya Dawo abunda ta fara tambayansa yaga Hamida da Hanne..?
Don Allah ya gaishesu yace tana missing dinsu.ai shi shaida ne Saboda Rabin wayarsu mganar Hanne da Hamida ne ya Dade yana jinjina wannan kaunar Dake Tsakaninsu Amina tana matukar ji da Hanne da Hamida in tana Hiransu haka Zakaji Farinciki da Murna acikin muryanta Shi bai wani zauna dasu ba ammh yasan dai tare suke su uku ammh baisan Rayuwarsu ba gaskiya.
Gyaran Murya yayi kafin yace"Kada ku Damu Amina na Cikin koshin Lafiya..Itama tace na gaisheku sosai tana kewarku..!
Suka kallesa kafin su koma su kalli juna sai Hawaye duk ya Cicciko Idanuwansu Hanne tace"Muma muna kewarta don Allah tana ina..?
Kuma yaushe zata Dawo..?
Kai Tsaye yace"kuyi hakuri bazan iya Fada muku inda take ba..Ammh tana Cikin Koshin lafiya..Sannan zata Dawi kowani Lokaci itama bata manta daku ba koda yaushe Cikin Zencen ku take yi..!
Kawai sai suka fara mai sharan kwallah ya kallesu baki bude bai yi mamaki ba in ya Tuna yadda suka rika uban kuka Ranar da zai tafi da Amina gidansa.
Gyara zama yayi kallesu yana Fadin"ku share hawayenku..Ku Zauna Dakyau yau labarin Amina zaku bani Tundaga Farko har karshe..!
Yau ina so naji nima..!
Hama kurum yake son jin Labarin Amina,batare da yasan Dalili ba.
Jin haka yasa suka gyara zama suka Fara bashi Labarin Amina da yarintarsu Hanne tayi in ta gaji Hamida ta karbe in suka fadamai wani abu baya sanin ma yana Dariya jin jina Jidalin Amina kawai yake yi aransa ashe haka tayi nisa bai sani ba ?
Kirarinta ke basa Dariya in ya Tuna wai Aminene ikon Allah badai ta Mutum ba sai ta Allah lalle yarinyar nan sai Allah taci kuma kirarinta..
Hanne ta Karbe da Fadin"Wlh ya Danmallam Amina tana da kirki sai wanda ya Zauna da ita ya sani...Tana da son yan"uwanta sai dai akwai abu Daya Amina tana da riko in ta Tsaneka sai Alllah sannan tana da Fada da Tsiwa kuma bata Laushi ko bata da gaskiya sannan ga son jin gulma,Amina fada ko ba nata bane siyanta take yi a makarantar boko da Islamiya ba malami ko Dalibin da baisan Jidalin Amina ba,ba wanda ta Kyale tana da Fara"a sai dai bata Daukan Reni bata kuma son arainata kan Hamida da hanne Amina Zata iya yin komai tasha Fada saboda mu kuma duk wani abu da ake yi Amina ce gand leader din mu.
Ya Danmallam ga ni Amina wata Hudu ta bani Hamida kuma wata uku ta bata ammh nuna wa take kamar ta Girmemu Amina bata san Faduwa ba bata nuna gazawarta Wlh ko su ya Abida ban shaku dasu yadda na shaku da Amina ba tunda muka taso bamu taba Rabuwa ko na kwana Daya ba,Shiyasa Rashinta ya ke sakamu cikin Wani hali komai baya mana Dadi..!
Hamida ta karbe da Mirmishi tace"kuma ba"a zaman minti goma da ita ba"ayi fada da ita ba..tafi Fada dani Fiye da Hanne saboda ni bana gani na kyale Hanne kuma bata da yawan mgana,Mu yi fada mu Shirya hakanan muke zaune duk duniya ba wanda yakaimu sanin Amina sannan mun san Halinta sai muka ci Mganin zama da ita, jidalin Amina ni da Hanne kadai muke iya Daukan ta, ko Ciwo tayi kowa sai yaji wani iri saboda Amina mai Fara"a ce sannan tana da Dadin zama ga wanda ya santa sai dai kawai Fada da Zafin rai sannan bata Daukan Reni Haka Aminene take bata da tsoro bata Shakka Kirarinta badai ta mutum ba sai Allah..!
Ko abunda ya faru na Aminu Tsausayi ne wlh ba Halin Amina bane nan ta shiga bashi labarin soyayyar ta da Aminu tundaga farko Har karshe da abun da ya Faru Hamida ta kareshe da Rantsuwan wlh tallahi ya Danmallam Tsautsayi ne ammh wannan ba Halin Amina bane barta da Jidalanta ammh Namiji baya gabanta soyayyarta da Aminu kaddara ne ta Ubangiji..!
Da Dukkan Hankalinsa yake sauraranasu duka labaransu suna shiga kansa wasu labaran na Amina abun Dariya ne wasu kuma ya Dauki wasu abubuwa da mganar Data Fadamai akwai kamshin gaskiya ko wani yaro akawai irin yarintarsa ammh na Amina yayi yawa wannan Rashin Tsoro da rashin jinta yayi yawa ba nata bane ita kadai da gaske an kara mata ne duk da abun ya Tarda Halinta ne ya gasgasta mganar ta Dalilai da dama sannan ga abunda ya Lura dashi a wajenta lokacin da ya kusanceta din nan ya Fahimci akwai matsala sannan ga mgangan su Hamida sosai yaji tsausayin Amina da wani Kaunarta na shiga ransa bai sani ba..
Mganar Aminu kuma mallam yadan Fadamai kadan Daga Cikin abun da ya faru Lokacin bai wani mai da kai ba kan mganar tunda alokacin yana ganin Aaminar kamar ta riga ta gagarane aransa kuma sai yaji ya baci da jin Labarin yadda su Jafar suka Dinga Dukan mai mata gaskiya ransa ya baci da Yana Kasar sai ya hanasu ai wannan abun yayi yawa kamar sun sanu jaka su bazasu Fahimci wani abu kan Amina ba..?
Yayi mamakin da ko mallam bai Taba kaawo wani abu acikin Ransa ba sai dai kila wani abu Allah bai Cika bayyanasa da wuri ba sai Tafiya tayi tafiya mganar Aminu kuma bai Damu ba yasan ba son shi Amima ke yi ba yarinta ne da kuma kaddaran auransa da Amina shi kamar ma taimakonsa yayi sannan da kuma karfin rabon dake Tsakaninsa da ita
Mirmishi yayi har Hakoransa suka bayyana kafin yace"Wato Aminene dai ikon Allah ce badai ta mutum ba sai ta Allah..!
Hamida da Hanne sukayi Dariya suka Dukar dakai shima Dariya yayi yana tuna wai tace ma malamar corper dinsu tana warin maza kawai sai yaji wani abu mai gardi da Zumudi kan Amina na kara mamaye ransa
To ai a jidalin nata zata zama uwa..!
Lalle akwai kallo sannan Jidalin akwaishi kam
Nan ya samu ya lallaba su hanne yace zai hadasu suyi mgana da Amina ammh bai sanar dasu inda take ba sun ji Dadi da sanyi tunda Amina dai tana Lafiya sannan tunda yace zai hadasu susan bazai musu karya ba sannan yace kada su fadama ko Hajiya mganar da sukayi.
Adaran yayi ma Hajiya mganar zuwa Abuja Hajiya tace ko da yaushe ya shirya yaje mana ya ganta..
Kansa na kasa yace zai sanar da Mallam jibi sai ya tafi gobe zai je Dutse shi da su Sarood su gaida Aliya matar Aliyu tana asibiti Ciki na bata Wahala...
Hajiya ta jajanta kai Tsaye tace ma Danmallam ya Dauki Aliyu ya rakasa Abujan mana.
Cikin mamaki yace"Hajiya kin manta kin ce ko shi kada yasan komai..?
Hajiya tace"Ka sanar dashi nasan shima bazai sanar da kowa ba..Bai kyautu kaje kai kadai bane..!
Ko Jiya sai da nayi ma Sa"idu Tsiya kawaicinsa yayi yawa bai Taba Tambayana ina Amina ba ko ina na kaita ba.?
Anya akwai Uba irin Sa'idu kuwa..?
Cemin yake yarda da nayi Dake Hajiya yarda kika rikeni Tsakani ga Allah na Tabbata duk inda Zaki kai Amina Za"a kula da ita kuma bazaki kaita inda Za"a Cutar da ita ba .!
Danmallam mirmishi kawai yayi bai ce komai ba Tsakanin Baba Sa"idu da Hajiya ko mallam baisan Tsakaninsu ba ballatana shi da ba mazauni ba sun Dade suna Hira da Hajiya kafin ya mata sallama Shashen falon ya koma sukayi mganar Tafiyarsu Dutse gobe da zuwansu Abuja shi da Aliyu mallam yace yana da kyau hakan Aliyu ai Aminini sosai sannan ya bada Sakon gaisuwarsa ga Mamarsa Amina.
Daya fito daga wajen Mallam shi da Nazeem suka yi hira sai after 10 ya koma gida Sarood ta kwanta Sakina dai na Zaman jiransa ya riga yaci abinci shashen mallam shiyasa bai ci wanda suka shiryamai ba yasan Daman abunda take mawa shi har mamaki take basa zafin nema na kawo samu ne..!
Tunda ya Dawo bata barsa ya Huta ba koda yaushe abu Daya ce mata akayi haka ake samun Ciki..?
Koda yake duba da Cikar Burinsu ai yasa tama Fita daga hankalinta Kada ya Danne mata Hakkinta yasa ya Biye mata kuma duk Shawaran Anty Amarya ne Ta Dake ta maida Cikinta Datayi barinsa.
Washegari karfe tara na Safe suka Dauki Hanyar Dutse shi ke Driving din Sakina na gidan gaba Sarood na baya sun isa da wuri Ajiyan aka Sallami Aliyan tana gidan chan suka wuce Direct bayan sun ci abinci sun huta sai mazan suka shiga Cikin gari suka bar matan agida
Sakina da Aliya suna mgana da Hausa suna Yamutsan fuska suna zunden Sarood, ita kuma tana kallon su tana washe baki batajin me suke Fadi Daga baya ma tashi sukayi suka shige Ciki suka barta ita kadai afalo kamar mayya su kuma sai bayan La"asar suka Dawo abokansu suka ziyarta da sukayi makaranta tare da aiki ya kawosu Dutse da zasu dawo suna Hanya Danmallan yace gobe da Safe ya zo zai rakasa Abuja Aliyu bai kawo komai ba Tunaninsa wani abun zai kai Umar din Abuja.
Yasa bai matsamai da Tambaya ba ya amsa masa da toh Allah ya kaimu.
Bayan La"asar suka Dauki Hanya bayan su Aliyu sun rakosu da Fatan isa Lafiya da suka Dawo gidan mallam suka Sauka sai aranar suka shiga gidan Baba Sa"idu suka gaisa da mamanmu shima adaran ya shiga shida Aba suka gaisa da ita sai kallonta yake yi yana Nazarinta haka kurum daman shi tun Farko kirkirta bai mai ba sai kuma ta kara Dora kanta azargi da Aba ya shiga Shashensa ta fara tambayansa Amina harda sharan kwallarta na karya wai Hajiya taki sanar ma kowa inda takai Amina..
Mirmishin yayi kafin yace mata shima bata Fadamai ba sai ta fara sallallanmi tana Fadin Allah yasa to dai lafiya.
Har ya mata sallama ya fita yana Auna mganganunta Biri dai yaso yayi kama da mutum a kaunar datake ma Amina in har na gaskiya ne Amina Bazata kai wannan wattanin bata nan ba bata wani damu ba gaskiya bai yarda da ita ba daman mutum ya cika Kirki wani Lokacin mugu ne.
Sai dare ya kwashi matansa suka koma gida adaran ya Fada musu gobe zai je Abuja wani aiki zai kaisa ba su Damu ba ita kanta Sakina bata kawo komai aranta ba ta Dauka dai aikin zai kaisa kamar yadda yace.
Washegari kuwa agidan mallam suka Hadu da Aliyu bayan ya gaida su Hajiya suka Dauki Hanya,Hajiya ta bata Goriba da su Rama da zogale da kulu su gauta da yalo da Daffafiyar gurjiya akaima Amina sun yi mgana da Aisha ta fada mata abincin zamani Amina bataci sai na gargajiya.
Danmallan ya taho da Tsaraban Amina tare da Ruwan zam zam din daya riga ya karanta mata duka ayoyin dake karya sihiri aciki sannan da Sauran addu"o"in Tsari Domin ya yardan ma kansa Amina ba ita kadai bace.
A motar Aliyu sukayi tafiyar dayake sun tafi da wuri sha Biyu suka shigo Abuja Usman mijin Aisha Danmallam ya Kira yayi musu kwatance cikin Lokaci sai gasu a anguwan maitama Dayake gidajen akawai lamba sai gasu agidan Usman ya Fito ya tarbesu daman yana gida ya samu dan break yana Hutawa kuma shima sai da Safen nan Ya Dannallam ya kirasa ya fadamai suna tafe kuma yace kada ya Fada su Aisha..!
Sai da suka iso gidan ne Aliyu yaga Usman sanna ya kalli Umar yana Fadin"Daman gidan Aisha zamu zo..?
Ko wannan ba mijinta bane..?
Lokacin Usman din yayi gaba suna Binsa abaya zuwa Cikin gidan.
Danmallam yace"Eh ammh ba wajenta nazo ba..!
Aliyu Cikin mamaki yace"To wajen wa kazo..?
Ai naga har sako Hajiya ta baka ka kawo mata. !
Kamar bazai yi mgana ba sai kuma yace"Zaka ganta ita wacce nazo Dominta..!
daidai suna shiga kayattacen Falon na gidan Aisha.
*Janafty*