Harabar gidan Major ta cika da motoci, sai hayaniya ake ji ƙasa ƙasa tun daga harabar gidan.
Falo ya cika ya batse da mutane.
A tsawon Kwanakin da Rumaisa ta yi a gidan Major, taga gata da karamci, kullum Afra tana tare da ita, ga Salman da take jin shima kamar nata ne, ga kuma Little da aka ce 'yar ta ce ta mutu ta bari, gashi suka yi wani irin sabo da Na'ima, duk da zasu yi sa'anni da Naima, amma Rumaisa tana girmamata kasancewar ita ta riƙe Abra. Bulama yana nan garin Kano, kullum cikin sintiri yake gidan Major, dan ganin Rumaisa da 'yarsa da kuma jikarsa, amma sam Rumaisa tayi mursisi ta dinga surfawa Bulama rashin mutunci, dan babu babban abinda ya ƙara mata tsanarsa irin jin shine dalilin da ya sanya ta rasa 'yar ta a karo na biyu, bayan sace su da aka yi da fari.
Rumaisa ta fito falon, jin yadda gida ya cika da mutane, sai dai babu zato babu tsammani idanunta suka sauka a kan Abra da ke kusa da Salman, ga kuma Afra a gefe guda. A gigice ta nufi wurin da Abra take tana sambatu.
" 'ya'ya na, duk nawa me sun dawo basu mutu ba 'ya'yana ne, Abdallah zo ka gani" Rumaisa tayi maganar tana nuna Abra da Afra.
Ƙurii Abra ta yiwa matar da ido, ko ba a gaya mata ba, tabbas wannan matar suna da alaƙa.
Zuwa tayi ta rungumesu gaba ɗaya, ta dinga gunjin kuka, har mayafin abayarta ya cire, dogon gashinta bar tsakiyar bayanta ya sauka, tayi larabci, tayi Hausa tayi turanci.
"Abra she's your Mum" Abbi ya faɗa yana kallon Abra.
Wani irin zillo Abra tayi, itama ta rungume matar, tana jin wani abu ya ratsata ba tare da ta gane takamaimai menene ba.
Bulama ne yayi sallama ya shigo, yana sunkuyar da kai tamkar munafuki, yana sunkuyar da kai, Yaya Musa me ya ce "Laa Inna, baki gane wannan ba?".
Inna ta ce "Ina zan manta shi, baƙin tsinanne, aka kashe mini miji a Asibitinsa, shi kume meye ya kawo shi nan, baƙin Azzalimi, muna ji muna gani yaƙi zuwa kan bawan Allah nan har ya mutu" Waro idanu Afra ta yi ta ce "Kenan kai kayi sanadiyyar mutuwar Mutumin da ya riƙe ni kamar uban da ya haife ni?"
Adnan ya ce "Ba mutuwar mariƙinsa kawai ba, har da kisan 'yar sa a Asibitinsa wadda ta kasance matata Abra, sai dai gata nan a gabana, na kasa gane mafarki ne ko zahiri".
Bulama ya samu wuri ya zauna, ya sunkuyar da kai yana zubar da hawaye, ya ce "Haƙiƙa wannan ishara ce Allah ya nuna mini, mutane sun rasa rayukansu a saboda sakacina, da sa neman kuɗi a gabana fiye da lafiyar mutane mugun halina ya zame mini DARE DA DUHU, babu lallai 'ya'yana su ƙaunace ni, sakamakon kowacce na bar mata wani tabo mai tsayawa a zuciya, dan Allah ku yafe mini, dama hausawa na cewa, idan kana mugunta ba ka yiwa kanka ba, baka iya ba, na watsar da dangina, na zalunci matar da ta mini halacci, an salwantar da rayuwar 'ya'yana, wadda na riƙa da soyayya ta ci Amanata, gaba ɗaya rayuwata ta zama DARE DA DUHU, da bana tunanin garin zai wayewa wannan duhun dare nawa, ku yafe mini dan Allah".
Rumaisa ta ce "Wallahi ba zan baka yarana ba, kuma ka tattara duk wata dukiya tawa ka bani abata, wadda ka cinye kuma, zamu haɗu a kotu, sai ka biyani"
"Rumaisa duk hukuncin da kika ɗauka a kaina daidai ne, amma ni ya aka yi naga Abra, bayan an sanar da ni ta rasu?".
Abba ya ce gyara zamansa sannan ya ce "Eh wannan bayanin duk shi ne ya tara mu a nan, Adnan ya auri Abra ne bayan ya gano 'yar ka ce, dan ya ɗau fansar abin da kayi masa, na sakaci mahaifiyarsa ta rasa ranta.
Tsawon zaman da Abra tayi da Adnan...
Adnan ya katse shi ta hanyar cewa "Dan Allah Abba kayi mini rai"
A fusace Abba ya ce "Zan tsinka maka mari, ka mini shiru mutumin kawai".
Abba ya ɗora da "Ya auri Abra, duk muna sa ran ya samu yarinyar kirki, suna zaune lafiya, ashe ba baka bane ba, sai ranar da Abra ta kusa rasa ranta, ya gigice ya dinga faɗar irin zaman da yai da ita, ya dinga azabtar da ita, bayan mun dawo daga wurin likita, ya bamu shawarar idan ta warke daga C.S ɗin da aka yi mata, a kaita India, saboda suna da ƙwararrun likitoci da Asibitocin da suka ƙware, a wurin bada kulawa ga masu ciwon, kuma tun da bata kai last stage ba, zata iya warkewa.
Daga nan na fara processing yadda Abra zata tafi India, katsam Adnan da bakinsa ya dinga faɗar yadda ya rayu da Abra, bayan an mata C.S jikinta ya rikice, duk mun ɗauka ta rasu, a lokacin da shi mijint, da Salman da ita Maman Salman duk sun suma, Nurses sun basu ɗaki, likitoci suka zo suka dudduba Abra, ba su ce mana komai ba, suka dinga mata ƙoƙari, suna dannna ƙirjinta suna mata allurai, har Major yana cewa kar su wahalar da gawar Abra, suka ce masa bata mutu ba, suganta ne yayi ƙasa fiye da kima, jinint ma ya sauka. Cikin ikon Allah ta cigaba da numfashi, amma bata hayyacinta, a ranar na buƙaci Major, da kar mu kuskura wani ya san Abra bata mutu ba, saboda za'a kaita India ne babu tabbacin ta dawo da rai, dan haka kar musa musu rai, na ɓoye masa ainihin dalilina na rashin san kowa ya san Abra bata mutu ba.
Muka tafi da Abra Abuja, na barota ita da Major, kwanan su ɗaya a General Hospital Abuja, suka tafi indiya, likitan da ya dubata ya mata cs, suka haɗamu da da likitocin Asibitin da za'a kai Abra. Cikin ikon Allah ana kaita suka karɓeta, muka biya komai aka fara bata kulawa ta musamman.
Lokacin da Maman Salman ta farfaɗo mun sanar da ita, an kaita gidana an mata sutura a binneta, duk da tayi mita a kan danme za a rufe Abra ko sallama ba suyi ba. Haka Adnan muka tabattar masa da an kai gawar Abra Kano, an binneta. Major ya baro Abra a can india, amma duk sati biyu ko ni ko shi, muna zuwa mu dubata, a nan Nigeria kuma, mun saka anata saukar Alqur'ani, har umara muka biya akaje aka yiwa Abra ɗawafi, Allah ya bata lafiya, idan kuma ba zata rayu ba, Allah ya sa ta cika da imani.
A cikin ƙudirar ubangiji sati uku, Abra ta fara samun Lafiya, na samu Abra na sata a gaba, ta gaya mini komai a kan zamanta da Adnan, dan da farko so tayi ta rufawa Adnan Asiri. Na roƙeta a kan kar ta gaywa Major, halin da ta zauna da Adnan.
Cikin ikon Allah watanni biyar kan na shida, aka tabattar mana da Abra ta warke ras ba wata damuwa da take damunta Yanzu.
Alhamdilillah, a jiya ni da Major muka ɗauko Abra daga airport, ta kwana a gidan wani abokinsa, da safe muka wuce da ita Asibitin da mijinta yake, muka taho nan, haƙiƙa mun ɓata muku na ɓoye muku gaskiyar cewa Abra na raye, amma dan Allah kuyi mana afuwa. Zan yi amfani da wannan dama, wajen karɓar takardar sakin Abra daga hannunka Adnan, ka rubuta saki ka bani na Abra, zan mayar da ita Makaranta".
"Haba Abba, Wallahi nayi nadama ka duba halin da nake ciki, na san tabbas a kowane lokaci zan iya rasa raina, dan Allah ku bari mu ƙarasa rayuwarmu tare, ko dan saboda yarinyar mu*.
Rumaisa kuwa cewa ta ke "Dan Allah ita dai in ya saki Abran, a haɗa mata kan yaranta ta tafi da su".
Adnan a ransa ya ce "Ji wannan matar da son kai, Wallahi ba in da matata zata da Aurena".
Bulama ya ce "Dan Allah Afra, da kuma Abra dan Allah ku yafe mini, ku kalleni a matsayin uba ko sau ɗaya a rayuwata, yanzu bani da wani abu da yayi mini saura idan baku ba, hatta 'yan uwana basa ta tawa, saboda Saudat ta rabani da su".
Gaba daya duk ɗokin da Afra take a kan son ganin mahaifinta, taji baƙi cikin kasancewar wannan azzalumin shine mahaifinsu, ba zata manta yadda aka bata labarin yadda ya wulaƙanta Baba har ya mutu ba, gaba ɗaya bai bata tausayi ba, mussaman da aka bada labarin cin amanar da ya yiwa mahaifiyarsu.
Kowa da abin da ya dame shi a falon nan, kowa neman mafitar kansa kawai yake yi, gaba ɗaya kan Abra ya fara ɗaukar zafi, dan haka ta miƙe ta nufi ɗakinta, wanda Afra ce a ciki Yanzu.
Kan gadon taje ta haye tana kuka, yau ranar farinciki ce a gareta, ko ta baƙi ciki? Ya aka yi suka fito daga tsatson azzalumi irin wannan mutumin?
Duk yanayi na rashin lafiya da Adnan yake ciki, haka ya tashi yabi bayan Abra.
Yana zuwa ya fara ƙoƙarin abin da zuciyarsa ke muradi, wato ya rungumi Abra a jikinsa. Duka ta fara kai masa ta ko ina tana kuka "Adnan ka cikani na tsaneka, Azzalimi sai ka sakeni ka daina wani pretending ma".
"Abra nayi kewarki, harshe ba zai iya bayyana abin da ke cikin zuciya ba, dan Allah ki yafe mini, mu koma mu zauna na miki tanadin soyayya irin wadda baki taɓa tunanin akwai taba".
"To hell with your fucking useless love Adnan, duk wata soyayya idan har daga gareka take iska ce da shirme, kuma aikin banza, maƙaryaci, mayaudari, kuma maha'inci, ka aureni ka cutar da ni cutarwa mai muni, na tsane ka ko ƙaunar ganinka bana yi".
Cikin hawaye Adnan ya ce "Abra, nine fa Adnan, baban yarinyarki amma kike gaya mini haka?".
"Kaje kai da 'yar na bar maka, bana son duk wani abu da ya shafeka, dan haka ka tafi da 'yar ka na baka, kar ka sake zuwa in da nake"
"Abra dan girman Allah.
"Dan Allah Adnan ka rabu dani, ka bar mini wurin nan, tun kan in maka illa, Wallahi na tsnake, baka da bakin da zaka iya bani haƙurin da zai wanke zaluncin da ka yi mini, rashin lafiyata ƙuruciyata da maraicina a wannan lokacin bai sa ka tausaya mini na tsira daga rashin imaninka ba, na dinga binka a kan gwiwowina ina kuka, amma sau ɗaya baka kalleni da idon rahama ba, kome nayi maka kai ka koya mini, dan haka ka rabu da ni" ta ƙarasa Maganar tare da ficewa daga ɗakin ta bar Adnan saroro yana kallonta, bai taɓa zaton Abra ta iya wannan rashin mutunci ba.
Falo fa ya rikice, dan Bulama har da hawaye, amma Afra taƙi ko kallonsa, dan ko fuskarsa bata son gani, ga rigima ta kacame tsakaninsa da Rumaisa na sai ya dawo mata da duk dukiyarta, kuma ta saka rigima a kan da yaranta zata tafi.
Salima dai ta zama 'yar kallo, komai ya kwaɓe ba mai jin kan wani.
Abbi kuwa ya ce "Ko nan da airport babu mai zuwar masa da yaransa, ba za su bawa Rumaisa yaran nan ba" aikuwa ta sa musu kuka ta ce bata yarda ba.
Abbi ya ce "Ba muna son mu rabaki da yaranki bane ba, amma kinga Abra tana da Aure, Afra kuma very soon za'a ɗaura mata aure, kinga ba zasu bar aurensu su biki ba, sai dai ki dawo ki zauna da mijinki, wato babansu a Nigeria, yadda zaki dinga ganinsu.
Aikuwa Rumaisa tai tsalle ta ce ko ana ha maza ha mata, ba zata zauna da Bulama ba, itama wataran kasheta zai yi, ko ya dawo ya kashe mata 'ya'ya, dan haka kotu zata kai shi, a raba aurensu a bata yaranta, dan kar a kuma kashe mata su.
Gaba ɗaya fa gida ya sake rikicewa, ana wannan turka turka, Adnan ya kuma dawowa falo, ya zube a gaban Abbi ya haɗa hannayensa ya ce "Dan Allah Abbi, na tuba nayi nadama, na san nayi wauta, amma dan Allah ayi haƙuri, ina cike da baƙincikin rashin mahaifiyata, da kusan aka kashe mini ita a kan idona, saboda sakaci da son zuciya na wannan mutumin"
"Ka gayar kalamanka, kar ka sake ka kausasa harshe a kan mahaifina, duk lalacewar iyaye iyaye ne, balle babu lalacewa a iyaye, ƙaddara bata wuce kan kowa ba" Abra tayi maganar cikin rauni, tana kallon Bulama amma ta kasa jin ɗigon soyayyar Bulama a ranta, tabbas ya cutar da Adnan, mussaman yadda ya bada labarin a yadda mahaifiyar tasa ta rasa ranta.
Abba ya girgiza kai ya ce "Adnan ka bani kunya, yarda da irin soyayyar da Abra take maka, ya sa na haƙura na aura maka ita, ba dan ina so ba, dan a son samuna tayi karatu, amma ganin tana sonka ya sanya na aura maka ita, amma kaci amana Adnan, ina son Abra a zuciyata fiye da yadda nake jin Salman ɗan da na haifa, dan haka nima ba zan takurata ba, ka rubuta takardarta ka bani kan ka bar garin Kano".
"Mama dan Allah ki saka baki, Mami kema kiyi magana su bani matata dan girman Allah".
Mami ta haɗe rai ta ce "A'a ka bar mini 'ya ta ta huta, gara ta dawo gabana ban gaji da ganinta ba, balle ka kashe ta a banza da baƙinciki a kan laifina da baita ta aikata ba" Wata irin Soyayar Hajiya Na'ima ta kuma mamaye zuciyar Abra, duk da irin wahalar da ta sha a hannunta, amma tana son baiwar Allah nan, saboda ta bawa ratuwarta gudunmuwa sosai.
Hajiya Mama tace "Allah ya sa ya zame maka darasi, har kullum da laifukan da kake yiwa Allah, da su yake maka hukunci, da baka rayu yadda kake so ba, amma ka ɗau fansa a kan wadda ita kanta bata san waye mahaifin nata ba, kuma tai shiru ta rufa maka asiri, duk da tana ƙishirwar son sanin mahaifinta, amma hakan bai sanya ta tona maka asiri ba, lallai Abra ta cancanci yabo, ta soka tsakani da Allah amma ka rusa damarka".
Abba ya ce "Ku kuka tsaya biye ta tasa, Salmanj kawo takarda ya saketa ta huta" aikuwa Salman ya zaro jotter da biro ya miƙo, tabbas da Adnan na kusa da Salman ba abin da zai hana ya fasawa Salman baki.
Abba ya wurgo masa takardar ya ce "Saketa maza, daga nan ta wuce Dubai wurin mamanta, ta huta itama"
"Dan Allah Abba kayi haƙuri, ba zan iya ba"
Wayar Bulama tayi ringing babu adadi, ya ɗauko wayar a hasale ya ɗaga wayar.
"Gwamnati ta rufe maka Asibitinka, kuma an turo maka sammaci daga kotu, an kai ƙararka da Asibitinka"
[11/28, 8:05 PM] Abk: Muryar wani mutum ta doki dodon kunnansa a kausashe da faɗin haka. Rarraba ido ya fara yi cikin rawar murya ya ce. "Ban gane ba, wa..wake magana?"
"Ba ka da buƙatar sanin hakan, kai dai kawai ka amsa kiran kotu, an je gidanka har sau uku ba ka nan, shi ya sa muka nemi lambar wayarka don mu sanar maka, takardar sammacin tana hannun mai gadinka."
Daga haka aka katse kiran. Gumi ne ya shiga tsatstsafowa a jikinsa duk da ac dake parlour'n, gabaɗaya mutanen gurin kallon shi suke cikin neman ƙarin bayani. Taɓe baki Ummi ta yi cikin harshen turanci ta ce. "In dai bala'i ne yanzu ka fara ganin shi a cikin rayuwarka Yusuf, tunda ka fifita kuɗi fiye da komai a duniya, ciki har da tsoron Allan ka. Ka zaɓi rayuwar cin zali da rashin tausayi ga wanda ba shi da shi, a garin hakan har mutumin da ya riƙe maka ƴarka ya mutu, wallahi ka yi asarar rayuwarka." Ta yi maganar cikin tsantsar ɓacin rai da tsanar shi. Girgiza kai Abba ya yi cikin Dattaku ya ce. "Yanzu me ya faru? Me aka ce maka a wayar?" Cikin raunin murya ya ce. "Daga court aka kira ni, an kama asibitina tare da turo mini takardar sammaci."
"Subhanallahi, Ubangiji ya kawo maka mafita."
Abbi ya faɗa cikin tausayawa
Hawaye Bulama ya fara tare da faɗin. "Ko me ya faru da ni, ni na janyo wa kaina, na biye wa son zuciyata na yi ta aikata kuskure, duk da na san hakan ba daidai ba ne, Ubangiji kuma ya yi ta ba ni nasara, fiye da shekara ashirin ban taɓa fuskantar wani ƙalubale akan abin da nake aikatawa ba sai yanzu komai ya rincaɓe mini." Ya nisa sannan ya cigaba da magana. "Na rasa matata mai ƙaunata da ta ba ni dukkan yardarta, sannan na rasa soyayyar Ƴaƴana waɗanda duk duniya babu abin da na ji ina so sama da su a yanzu. Tabbas bahaushe ya yi gaskiya da ya ce. "Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya tak ta mai kaya."
Wani mugun kallo Adnan ya wurga masa cikin tsana, ko kaɗan bai ji tausayin shi ba, sai ma takaicin shi da ya ƙara cika zuciyarsa, saboda shi ne Ummul aba'isin duk abubuwan da suka faru. Kasa magana kowa ya yi, Abra Sarkin kuka sai hawaye take yi, zuciyarta ta karye, wani irin tausayin mahaifinta ya cika mata zuciya. Miƙewa Bulama ya yi ya kalli Ummi da su Afra ya ce. "Zan tafi cikin baƙin cikin tsana na da nake gani kwance akan fuskokinku, amma don Allah ina roƙon ku alfarma guda ɗaya, ku yafe mini, ku kuma kasance masu yi mini addu'a, domin na san da ƙyar mu ƙara haɗuwa, saboda abubuwan da na aikata na cancanci zaman gidan kaso na har abada, kotu za ta iya yanke mini hukuncin ɗaurin rai da rai." Kawar da kai Ummi ta yi cikin ƙoƙarin danne tausayin shi da ya taso mata, duk da cikin harshen Hausa ya yi maganar amma yanayin da yake ya karyar mata da zuciya. Tashi Abra da ta fi su raguwar zuciya ta yi ta rungume shi tare da fashewa da kuka. Duk lalacewar Uba, Uba ne, kuma hannunka ba ya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar. A hankali Afra ta tashi ta ƙarasa ta janye Abra, cikin ɗacin zuciya ta ce. "Wannan mutumin ba abun tausayi ba ne, kar ki bari wannan kalaman yaudarar tasa da marairaicewar da ya yi su yi tasiri a zuciyarki, domin shi bai san hakan ba ga al'umma, wallahi ba zan taɓa yafe masa mutuwar da Babana mai ƙaunata ya yi ba saboda shi, taho mu bar kusa da shi kar baƙin....."
Da sauri Abra ta toshe mata baki da hannunta tare da girgiza mata kai ta ce. "Ki daina faɗar haka ƴar'uwata, duk lalacewar shi mahaifinmu ne, shi ya yi sanadin kawo mu duniya, ko da kowa ya ƙi shi bai kamata mu ƙi shi ba, kar ki manta da Uba ake ado, a lokacin da ba mu san shi ba muke cikin ƙishirwar ganin shi addu'a muke ko yaya yake Allah ya nuna mana shi, yau ga shi Ubangiji ya amsa addu'armu, bai kamata kuma mu butulce masa ba. Wannan halayyar tasa ƙaddararsa ce a haka da mu baki ɗaya, Ubangiji ya riga ya rubuta duk abin da ya faru sai ya faru, babu yadda za mu yi." Ta ƙarashe maganar cikin kuka mai taɓa zuciya. Rungume ta Afra ta yi cikin hawaye, kalaman ƴar'uwar tata sun tsinka mata zuciya. Babu wanda tausayin su Abra bai ratsa wa zuciya ba a gurin, musamman Ummi da take ganin kamar ita ce ba ta zaɓa musu Uba na gari ba. Kan Bulama a ƙasa cikin tsananin jin kunya da nadama ya fice daga parlour'n cikin harɗewar ƙafa tamkar mai koyon tafiya, Abra da Afra suka raka shi da ido cikin wani irin yanayi. Tasowa Ummi ta yi ta rungume ƴaƴanta suka cigaba da kukan a tare.
Bayan sun nutse sun yi shiru Baffa da tun ɗazu bai ce komai ba sai nazartar kowa da yake ya gyara zama ya ce. "Alhamdulillah komai ya yi farko zai yi ƙarshe, kuma komai na rayuwa nan mai wucewa ne. Tashin hankali da rashin nutsuwar zuci da Yusuf Bulama ya tsinci kansa a ciki ya ishe mu ishara da sauran masu irin halayyar shi. Allah ya sa mu dace, ya sa mu fi ƙarfin zuƙatanmu." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Abba da bai manta da batun sakin Abra ba ya dubi Adnan ya ce. "Yanzu kai kaɗai muke jira, ka ba mu takardar sakin Abra." Kuka Adnan ya fashe da shi zai yi magana Abba ya ɗaga masa hannu tare da faɗin. "Idan har ba ka yi abin da na umarce ka ba a yanzu to ka sani babu ni babu ka..."
"Ashsha! Me ya yi zafi haka Alhaji? Duk abin bai kai haka ba, abi komai a sannu. Saki ai ba shi ne mafita ba, Ubangiji ma da ya halatta a yi shi ba ya son a yi shi, yanzu a bar wannan maganar don Allah, na roƙi wannan alfarmar, a taimaka a yi mini ita."
Baffa ya katse Abba da faɗin haka.
"Amma Baffa da ka bari ya sake tan, tunda yarinyar ita ma ba ta son shi a yanzu."
"Idan ba ta so babu mai yi mata dolen sai ta koma, amma abun da nake so a ba ta lokaci ta huta ta yi tunani, idan har lokacin da aka ba tan ta ce ba ta son shi ni da kaina zan karɓar mata takardar saki a hannun Adnan. Don mu sulhu muke so ba ɓatawa ba."
Cikin gamsuwa Abbi ya ce. "Haka ne, na gamsu da bayaninka sosai Baffa, a ba ta lokacin, ko dan darajar yarinyar dake tsakaninsu." Ajiyar zuciya mai ƙarfi Adnan ya sauke ya cillar da jorter da pen ɗin hannunsa ya rarrafa gaban Baffa ya dinga kwarara masa godiya.
Murmushi Baffa ya yi ya shafa kan Adnan ya ce. "Ba komai yaron kirki, kai dai ka dage da addu'a da kyautata mata, hakan zai taimaka gurin kankare mikin da ka yi mata a cikin zuciyarta." Gyaɗa masa kai ya yi idonsa a kan Abra, wadda ke wurga masa muguwar harara.
"Yanzu tsawon wanne lokaci za a ba ta kafin a ƙara jin ta bakinta?"
Abba ya tambaya.
"A ba ta wata guda."
"Shikenan Allah ya kai mu lafiya, amma kafin lokacin ina son a yi bikin Salman da Afra."
Dam zuciyar Abra ta buga, Faris ɗinta ne zai auri ƴar'uwarta? 'Ya Allah.' ta faɗa a cikin zuciyarta tare da yin ƙasa da kanta cikin wani irin yanayi na karayar zuci. Salman dake lura da ita ya sauke numfashi, so yake su haɗa ido amma ta ƙi ɗago kanta.
"Please ku bar maganar auren nan? Ku ba ni na tafi da ƴaƴana can ƙasata." Ummi ta faɗa cikin hawaye.
"Babu mai hana ki Ƴaƴanki duk duniyar nan, amma tunda suna son junansu ita da Salman ki bari a ɗaura auren sai ku tafi dukanku har shi, mun san kin yi haƙuri na zaman da kika yi a nan tsawon lokaci, ga ƴan'uwanki suna ta son ki koma don su gan ki dake Ƴaƴanki, amma ki ƙara wani haƙurin, ana ɗaura auren da sati biyu insha Allahu za ku tafi."
Tana ganin mutuncin Baffa sosai kuma ba za ta iya jayayya da shi ba, kallon Uba take masa tunda ya haife ta, hakan ya sa ta ce masa ta amince. Tashi suka yi suka bar iya su Abbi a parlour'n suka ƙara tattaunawa, sun tsayar da lokacin bikin sati uku masu zuwa. Su Abra sun fito suna yi wa Abba da su tafi sallama Adnan ya kafe ta da ido