Numfashinsa yaja da ƙarfi yana shaƙar iskar da take kaɗawa awajan, me sanyi da fitar da ƙamshin ruwa,sabida ruwan saman da aka gama sheƙa musu yanzun.
Furzar da iskar bakinsa ya yi ahankali, anutse yace.
Momy ina zuwa bari na kira su Annah naji Wanda ya rasun, zan maido maki kira yanzun in Sha Allah."
Ya faɗa yana katse kiran, bai jira ta yi magana ba.
Murja tabi wayar da kallo kamar me nazarin wani abun cikin wayar.
Idanunta ta ɗago ta kalli Sa'adah wadda bugun zuciyarta tuni ya canza, idan ka tsayar da hankalinka wajan kallonta zaka gane Tsaf bata cikin nutsuwarta, a firgice take, sabida yadda take rarraba idanu, wanda suka tara ruwan ƙwalla.
Cike da mamaki tace.
"Baby! Kina nufi ba'ayi rasuwar ba? Ko kuma basu faɗa masa bane? Naji yace maminki tace jiya kunyi fira? Kinga hakan yana nufin ayau bakuyi magana ba?"
Sa'adah da ta sake shiga ruɗani saboda rashin madafa, ga tsoron abinda Yusuf zai kira yace, tasan kawai zai ce ƙarya take.
Zuciyarta ta bata ƙwarin guiwa ta tsaya kai da fata akan anyi mutuwar, gwara daga baya tace amafarki ta gani ashe ba zahiri bane.
Bakinta na rawa tace .
"Wlh ina shigowa ɗazu da rana lokacin da na kawo muku abinci, aka kirani anan falon, yayana Mubarak ni dai nasan ba mafarki nake ba, Ammy ce ta rasu, basan me yasa Annah basu faɗa masa ba, ko basaso ace ko wata biyu banyi ba, nazo gida tafiya me nisa."
Ta ƙarashe maganan cikin kuka kalar tausayi, tana jimamin abinda zai biyo baya, daga Yusuf na cewar ba'ayi rasuwar ba.
Amman ita ta yi alkawarin zata kafe akan anyi koda za'ace aljanun ne gareta akan a ƙureta ta yi ƙarya, tana tsoron abinda zai biyo baya idan Murja ta gane ƙaryar take, dole zata zargi tajita tana waya ne.
Murja ta janyota jikinta ganin yadda take kuka, tace.
"Ok ya isa basu faɗa masa bane, daman nayi mamaki ɗazu yadda kike kukan nan, idan ba rasuwar ba me aka maki, ya isa yi shiru Baby Allah ya mata rahama, idan yazo zamuje baki ɗaya muyi gaisuwa daga nan zumunci ya ƙara ƙarfi, tunda basu Sanni ba."
Ikram tace.
"Inama zan iya atafi da ni Niger, kiyi haƙuri dukkan mai rai mamacine, ALLAH yasa mu cika da imani."
Sa'adah tai shiru Murja na share mata hawayen fuskarta, tana sauke ajiyar zuciya, tana shirya yadda zatayi aljanun ƙarya, matuƙar Yusuf ya kira yace, ƙarya take ba'ayi rasuwaba.
Jikinta ta janye daga Murja tana ƙura wa wayar hannun Murja ido.
Murja tace.
"Ki saka min lambar na kira nayi gaisuwa Baby."
A hankali tace.
"Toh Momy na baro wayan can part ɗinmu, idan na koma sai na taho da ita."
Yusuf kuwa yana katse kiran na Murja, Abbi ya fara kira mahaifin Sa'adah.
Kiran bai jima da shigaba, ya ɗaga tare da sallama, kyakkawan dattijo buzu me kamala.
Yusuf ya masa yace.
"Abbi daman naji kamar ana cewa anyi rasuwa, kuma bamu saniba nida Sa'adah, shine nace bari na kira naji, ko dan bata jimaba da zuwa ba'a son a ɗora mana nauyin zuwa, shiyasa baku faɗa min ɗazu dana kira ba?"
Abbi ya gyara zamansa cikin dattakunsa yace.
"Yusuf! Rasuwa kuma nan cikin familles namu? Gaskiya ba'ayi ba, koda Autah Sa'adah ta yi maka ƙarya tana son zuwa gida ne?"
Yusuf ya sauke numfashi, yace.
"A'a Abbi ba ita bace batama san najiba."
Abbi ya yi murmushi yace.
"Kai dai ka rufawa matarka asiri, dan Allah Yusuf ayita haƙuri da Autah, yanayin shagwaɓarta ta taso ita ce ƙarama yayunta suna sonta sosai sai abinda take so takeyi, amman duk da haka bamu saka mata ido ta gurɓata tarbiyyarta ba."
Yusuf yace.
"Abbi ai ko maƙiyin Sa'adah zai yabi kyawawan halayenta, sai anjima Abbi."
Albarka Mas'ud ya saka masa yana murmushi yasan Sa'adah ce kawai ta kirasa, dole zai kirata ya mata faɗa karta ɗagawa mijinta hankali da batun zuwa gidan yanzu wata ɗaya da kwanaki kawai da aure.
Yusuf yana katse kiran, ya sake kiran Annah bayan sun gaisa ya mata tamabyan akan rasuwa itama tace.
Babu nasu da ya rasu.
Yusuf bayan ya gama wayan, ya dafe goshi yana faɗin.
"Toh me yasa Baby ta yi irin wannan ƙarya? Lallai akwai babban dalili na sakata yin ƙaryar rasuwa."
Lambar Momyn ya kira, bugu ɗaya Murja ta ɗaga tana faɗin.
"Yusuf ya akayi anyi rasuwar ne ko ba'ayi ba? Dan kaina ya kunce."
Yusuf ya furzar da iskar bakinsa anutse cikin kamewa ya furta.
"Anyi rasuwar Momy, wai basason faɗa dan kar Sa'adah ta taho duka auren wata biyu ma bai rufe ba, yanzun ma Abbi yace bazata zo ba gaisuwa a waya ya wadatar."
Murja ta kalli Sa'adah da take rarraba idanu tana shirin tayar da aljannun ƙarya, tace.
"Allahu Akbar shi kenan amman naso aje a musu gaisuwa, ba komi se ayi gaisuwar ta waya."
Anutse Yusuf yace.
"Momy bani Sa'adatun idan tana kusanki."
Murja ta kalli Sa'adah da idanunta suka cicciko da ruwan hawaye, tace.
"Amshi wayar yana magana, dan Allah Baby ki rage kukan haka kar kanki ya yi ciwo mana, tashi ki shiga ciki kuyi magana kukan naki baya min daɗi."
Sa'adah kamar jira take ta miƙa ta nufi Bedroom din Murja.
Ikram ta miƙe tana faɗin.
"Kai matar yaya akwai shagwaɓa dayawa duk ta birkice lokaci ɗaya.
Momy Bara na leƙosa yana waya me mahimmanci ne shine na barsa ya gama."
Murja tace.
"Ok sai kin dawo."
Ikram ta manna mata kiss a kumatu ta fice.
Sa'adah tana shiga bedroom ta rufo ƙofar tana zama akan 2 seater da take cikin Bedroom din, ta sakar masa kuka me cike da shagwaɓa ba tare da ta iya amsa tamabayarta da yake ba.
Numfashinsa yaja sosai yana jin daɗin iskar wajan, Amman kuma kukan nata ya fara dagula masa lissafi.
Anutse ya furta.
"Babe! Kukan fah? Ko ɗagamin hankali uhm?"
Gaza magana tai tana cigaba da kukanta tana dunƙule jikinta waje ɗaya.
Numfashinsa ya kuma ja tare da furzar da iskar bakinsa, ya furta.
"Ƙaryar mutuwa Babe? Me yasa? Kina son zuwa gidane uhmm?"
Cikin shasheƙar kuka tace.
"I'm sorry Babe kaji? Ngd da rufamin asiri da kayi i love You My Babe."
Ɗan ƙaramin murmushi ya yi yace.
"Love You too Amman dole idan nazo zaki faɗa min me yasa kikayi ma Momy ƙaryar mutuwa, nasan akwai dalili, saboda yadda tace kin ɗaga mata hankali da kuka."
Sa'adah tace.
"Eh Mon trésor zan faɗama se ka zo ɗin."
Anutse yace.
"Ok toh maza sharemin hawayen bana son ganin baby face ɗin matata da hawaye, faɗa min kinci abinci?"
Ashagwaɓe tana turo baki tace.
"Eh kaɗan sabida rashinka. Amman jibin da wuri zaka iso koh?"
Murmushi ya yi yace.
"Eh me zaki bani me daɗi?"
"Komi ma Baby zan baka."
"Ok ya yi kyau Mah love Ƴar buzuwata me ƙarya."
Ɗan kukan shagwaɓa haɗe da sangarta ta sakar masa tace.
"Ka daina faɗa Mon trésor kaji?"
Dariya ya yi yace.
"Zan faɗawa Momy gaskiya fa sai kiji da ita kuma."
Kuka me ɗan sauti ta sake saki tace.
"Don Allah Babe kayi haƙuri haba! Mon trésor kai zakaso Momy ta tsaneni ne?"
"Oh! Wai kukan dai kuma? Toh ya isa, wasa nake maki, kinaso wahalar min da kakin wajan ciwon kai, ina wayanki?
Ashagwaɓe tace.
"Tana can gidanmu yanzu na shigo nan ɗin, ina girki ban kammala ba."
"Bakya ji ko Babe?"
"Allah zan iyane shiyasa fa nayi Babe."
Murmushi ya yi yace.
"Momy tace min me aiki tazo?"
"Eh."
"Good bari na katse lokacin sallah ya yi ki shirya bayan Isha'i zamuyi video call."
"Shagwaɓe tace.
"Toh kayi min kwalliya, dan Allah Babe inda kake ba ƴan mata koh?"
Dariya taso suɓuce masa, sai yakai idanunsa wajan wasu ƴan mata guda uku daga gefensa na hagum wanda ɗayar baki ɗaya hankalinta na kansa.
Miƙewa yay tsam, ya fara tafiya anutse, yace.
"Babu Babe, bye zan kiraki anjima."
Kamar zatayi kuka tace.
"Ɗan Fulanina kiss me Ni dai."
Idanunsa ya ɗan lumshe yace.
"Oh! My God! Muahhhh I love you shi kenan koh?"
Kamar tana gabansa ta ɗaga kanta tana faɗin.
"Yeah Babe love you too ka kulamin da kanka sosai da sosai."
Ajiyar zuciya ya sauke mata ta wayar yana murmushi ya katse kiran, ya nufi hanyar da zata kaisa masaukinsa.
Sa'adah ta rungume wayar tana murmushi ta lumshe idanunta, tace.
"Ina son Babe Yusuf, Allah sarki mutumin kirki yana son matarsa ta yi farin ciki sosai."
Ta faɗa tana kallo wayar sai taji tana son shiga cikin wayan ko ta samu wani abun.
Kallon ƙofar ɗakin ta yi arufe ruf yanda ta rufe.
Da sauri ta shiga cikin Whatsapp, akwai saƙonnin da bata budaba dayawa, sunan Farko da yaja hankalinta ta buɗe da yake saƙonta ne na ƙarshe ba'a maido mata ba, kuma an duba kodan data arufe ba mamaki an maido in.
Kobata faɗa ba itace Lubnah sabida hoton Momyn ne asaman dp, kuma sunan an saka L+M.
Tana shiga bata tsaya duba komi ba tayi cochén su ta danna zuwa aikawa kanta.
Lambarta ta shiga dubawa cikin sa'a ta samu an saka Baby Sa'ah.
Turawa tai jikinta na rawa, suna zuwa tai saurin gogewa ta fita daga WhatsApp ɗin ta miƙe ta isa wajan Camera ta ɗaukota dan yanzu bata buƙatar sheda camara ta abinda ta tura ta isa.
A rigarta ta saka Camera, tai saurin fitowa falon.
Murja bata nan.
Sa'adah ta zauna tana kiranta.
"Momy ! Kina ina?"
Daga kitchen Murja Tace.
"Ga ni a kitchen Ina nunawa Lawisa abubuwa Baby."
Sa'adah ta miƙe ta nufi kitchen ɗin.
Tana zuwa tace.
"Momy kije ki zauna bari na ƙara nuna mata komi. Ga wayan."
Murja ta amshi wayan tace.
"A'a kije ki huta wannan kuka da kika sha ya isheki."
Sa'adah tace.
"Lah! Ban sauke miya ba, bari naje na duba kinji ana kiran Maghrib Momy idan nayi sallar Isha'i zan taho mana da abincinmu me daɗi nayi mana."
Ta faɗa tana ficewa da ƴar sassarfa.
Murja ta bita da wani irin kallo tana faɗin.
"Ok Baby se kin taho ɗin."
Lawisa tace.
"Aunty kalla kamar ba ɗazu ba ta gama kuka."
Murja ta yi murmushi batace komai ba, ta juya tabar kitchen ɗin...
Kai tsaye Bedroom ɗinta ta nufa.
Ikram kuwa Adam yajata suka fita ana sallar Maghrib gidan wani abokin aikinsa wanda yake nan da iyalinsa, shi kaɗai yake zuwa Maiduguri duk ƙasashen wata yake zuwa nan Gombe.
Toh shine tun yamma ya matsa suzo gidan nasa tun yamma Adam yace se bayan Maghrib, shine suna sallar Maghrib suka ɗau wanka suka tafi bayan sunyi wa Murja sallama.
Sa'adah tana zuwa ɓangarensu, jikinta har rawa yake ta yi alwala ta yi Sallah, tsabar tana son ganin abubuwan da suke cikin wayar bata tsaya yin azkhar sosai ba kamar yadda ta saba, ta cire rigar sallar ta saka Jean iya cinya da ƙaramar riga cibinta ma bata rufe mata ba, sabida wani irin zafi da takeji, duk da ta kunna A/C ta fito falon tana rawar jikin ganin tsiyar da Murja take ƙullawa.
Camera ta ture wajan zama ta faɗi bata tsaya bin ta kanta ba, sabida ta ɗan shige ƙasan kujera kaɗan, ta ɗauki wayanta, kira 12 ta gani na ƴan gidansu, na Annah da Abbi, da Nusaiba, sai Salha. yayarta.
Dariya tai tana faɗin.
"Kunga kuyi haƙuri, ita kuma Ammy Allah ƙara mata tsawon rai da kuma lfy, na kasheta lokacinta bai ba."
Ta faɗa tana kunna data.
Saƙonni suka fara shigowa.
Na wajan Murja ne na ƙarshe.
Jikinta har tsuma yake ta buɗe.
Wani hoto na Lubnah, ta furgita tana tsirara tai saurin gogewa tana sakin kuka.
Se me na Momy ta gani shima tsirara tana dafe da tsohon nonuwanta, ta zuro harshe waje, ta kashe ido ɗaya."
Idanunta ta runtse tana sake fashewa da kuka tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!"
Goge hoton ta yi da sauri, tana danna wani voice.
Jikinta tsuma ya fara jin yadda Murja take wasu irin surutai kamar namiji na saduwa da ita, tana kiran Lubnah ta mata kaza ta mata kaza.
Sosai ta shiga tashin hankali, shima ta gogeshi sabida zuciyar Yusuf zata iya bugawa idan yaji wannan masifa da uwarsa take aikatawa.
Wani hoton ta gani wanda Lubnah ta aiko tana kan Murja kamar mace da namiji bakinsu a buɗe wayam alamar ihu suke, lubnah ce me ɗaukan hoton ga hannunta nan.
Sa'adah tace.
"Na shiga uku! Na lalace Qalu innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Allahumma ajirni fi musibatihi wakhlifni khairan minha, wayyo ALLAH Yusuf na tausaya maka, na tausayawa kaina da zan haɗa jini da wannan annobar mata."
Wani video ta gani ta danna wanda duk yafi ɗaga mata hankali, Lubnah da Murja abinda suke ba banbanci da mace da namiji, kanta ta kauda tana fashewa da kuka, ta gaza magana.
Voice ɗin Murja na ƙarshe ta danna taji bayani yana fitowa.
"Lubnah! Sbd kin rainani shine kika kashe min waya muna magana? Toh wlh bari kiji in dai akan Baby Sa'ah ne, ki shirya kwasar baƙin ciki idan bazaki iya haƙuri ba, ke wlh nida inada hanyar ɗauketa na gudu da ita, zanyi hakan.
Amman ina YUSUF ina son farin cikinsa, dan haka ki kama kanki wajanta daban naki daba, duk kishinka na sani bai wuce ina mata abinda nake miki ba, toh sau daya ne na sameta shima yau ne idan na banka mata maganin zanyi na kirki, Ni dai kinsan ban iya rufa-rufa ba, kece munafuka, dan haka ke kika jiyo bye idan kin huce mayi waya i love You."
Sa'adah tana gama jin voice ɗin ta sake kecewa da kuka tace.
"Ya ALLAH ka karni daga sharrin baiwar ka, ka tsareni ka shiga tsakanina da ita, shin me takeji me take nema ajikin mace ƴar uwarta? Wannan wace irin masifa ce?"
Cikin kuka ta danna lambar Salha zatayi kiranta taji kamar daga sama an warce wayan, an katse kiran bai kai ga shiga ba, ana faɗin.
"Shi kenan ɓoye-ɓoye ya ƙare yanzu za'ayi wasan idonki na gani Na rantse da Allah tunda kika ga asirina baki isa ba, zan iyama kasheki kowa ya huta, sai dai bazan hakan ba, kinsan irin kalar sharrin da ƴan lesbian suka iya kuwa?uhmmm! .
Bari kiji tunda lokacin da naga kukan nan da kalamanki sun sakamin ayar tambaya, sai ga ƙarya ta biyo baya mijinki ya ɗaure miki gindi duk ƙyar nake ganinku.
Wato kinji ina waya da Lubnah kishiyarki koh?"
Murmushi ta yi tace.
"Ai nasan kinason Yusuf dayawa koh? Kuma kina son zama da shi? Hummm kinyi kuskure babba shiga wayana satan sirrina, wato kina son ki kaashemin ƴaƴana Ikram da YUSUF da baƙin cikina, ki rabani da ƴan uwana wanda daƙyar na samu muka shirya koh? Toh baki isaba"
Baby Ni kikaci amana? Kinsan abinda kikayi? Kinsan ma wacece ni? Zaɓi uku zan baki ayau akan dai ki tonamin asiri, har ki saka bayanai ɗiyata mutuwa da tsohon ciki, Yusuf ki kashemin shi, ko ki saka ya tsaneni, duk zanyi maganinki."
Ta faɗa tana zama kusan Sa'adah ta rungumeta, tana shafa cinyarta tace.
"Baby kenan, wato kin ɗaukeni daƙiƙiyar uwa koh? Ai babba babba ne Sa'adah. Kinci sa'ar sonki ya gama min illah, da son rayuwar ƴaƴana ta ɗore, Amman fa sai kinbi sharaɗina naki auren zai tsira."
Ta faɗa tana kamo fuskarta ba ɓata lokaci ta manna bakinta akan bakin Sa'adah, tana tsotsa tare da cusa hannunta cikin figigiyar rigarta.
Sa'adah wacce take cikin fitsari jagba wanda ta sakeshi a zaune jikinta na wani irin bala'in kyarrrma idanunta baki ɗaya warwaje suke numfashinta na ƙoƙarin barin gangar jikinta, wato nason ɗauke wa baki ɗaya, jin abinda uwar mijinta take shirin yi mata, wani irin matsiyacin amai ne ya kuɓuce wa Sa'adah, cikin bakin Murja, wanda dai-dai lokacin numfashin Sa'adah wanda take ƙoƙarin riƙewa da ƙarfin tsiya, dan tsiratar da rayuwata, amman ina numfashin ya yi nasara ɗauke wa baki ɗaya ta suma....
Umma Zainabu A'isha masoyiya ALLAH ya jiƙanku ya muku rahama Ameen.🙏🏽😭_*SHEƊANIYAR*_
```{Suruka}```
_*Free Nobel🫱🏼🫲🏽*_
19/3/2023
_*SADAUKARWA Aunty Hajarah Hajeer Lawal,😘 And lovely Halimat Musa Waziri,Son So domin ALLAH😘*_
😍TUKUICI gareki Hajiya Fadilah Salisu Hamza❤️
بسم الله الرحمن الرحيم
*Chapter 29&30*
Kwance take na'urori jone ajikinta, a hankali hannunta me ɗaure da drip ya fara motsi.
Abubuwan da suka faru da ita suka fara dawo mata, tana shirin fasa ihu
Sama-sama tajin sautin muryoyi na tashi, idan ba ƙarya kunnenta yake mata ba, muryan Yusuf takeji yana magana, cikin nutsuwarsa sai dai yanayin yadda muryansa ke fitar da amon sauti akwai alamun yanayin damu acikinta.
"Momy inaga dole fa za'a fitar da ita waje, tunda ALLAH ya horemin, wlh inajin nauyin iyayanta tun suna kawaici har su gaza su amsheta, gwara kawai na fita da ita tunda nan ɗin taƙi farfaɗo wa, kwana tara fa! Ga mahaifiyarta na cikin damuwa sosai ita da yayarta sai nake ganin kamar Aunty Salha tanajin haushin mu, duk tabi ta ɗaure fuska bata ma son shiga sabgarmu tunda tazo sai ya zama dole.
Momy! Me yasa kikace karna fitar da ita ƙasar waje?"
Sa'adah sosai ta shiga tashin hankali, jin kwananta tara akwance batasan wanda yake kanta ba! Shin me Murja ta mata bayan sumanta? Ya akayi aka kawota asibiti? Da yaushe Yusuf ya dawo? Yaushe iyayanta suka san batada lafiya har suka zo?
Murja ta matso ƙwalla tana faice majina, cikin muryan tashin hankali tace.
"Kawai bana son nisa da ita ne muci gaba da addu'a in Sha Allah zata samu lafiya, yayarta da kake magana kuma me haɗin mu da ita? Me aka mata, naji Ikram na faɗin sai faɗa take da yarensu bamu saniba bare mu fuskanci me take nufi damu, yarinya dai bazamu bayar ba."
Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yana sake kwantar da murya, yace.
"Please Momy komai ayi na girma ki amince min a fita da ita koda India ne."
Murja gudun zargi tace.
"Ok shi kenan amman dani za'aje..?"
Dai-dai lokacin Sa'adah ta buɗe idanuwanta wanda suka mata nauyi, ga wani irin bala'in zafi da suke mata, jikinta ko ina ciwo yake mata.
Idanunta akan Yusuf suka sauka yana kallon mahaifiyarsa ya furta.
"Momy! Da kinyi haƙuri muntafi dai da mahaifiyarta zaifi koh?"
Gudun ɗasawa ɗanta zarginta tace.
"Ok shi kenan ba damuwa ALLAH ya maka Albarka inason duk abinda kakeso."
Cikin farin ciki Yusuf ya rungumeta yana godiya.
Sa'adah gabanta ya faɗa lokacin da ta kalli Murja, abubuwan suka sake faɗo mata, atake jikinta ya fara ɓari tana wani irin numfashi, na'urorin jikinta suka fara ƙara, ta buɗe baki da ƙarfi tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yusuf kaini wajan Annah, kaini Niger don ALLAH don Annabi."
Ta faɗa da mahaukacin kuka.
Da mugun mamaki Yusuf juyi jikinsa na rawa ya rungumeta gam yana riƙeta sabida fizge-fizgen da take.
"Sa'adah tsaya buɗe idanunki Kinga nine Yusuf ga Momy su Annah suna nan buɗe idanunki Please Babe."
Kai take girgizawa tana kuka sosai.
Murja tace.
"Alhamdulillah! Yusuf jeka kira doctor dasu Annah."
Sa'adah riƙe shi tai gam tana girgiza kanta tace.
"Karka barni Yusuf karka fita don Allah karka fita na haƙura da ganin Annah."
Ta faɗa tana sake sumewa.
Cikin tashin hankali Yusuf ya danna na'ura kiran Dr yana girgizata da kiran sunanta.
Kusan tare Annah da likitocin suka shigo.
Salha kuka take sosai tana son yin magana Amman bata riƙe hujja ba.
Annah ta ƙura wa ƴarta idanu, tana ƙara daure zuciyarta.
Murja sai kuka take tana salati.
Babban likitin ya kalli Yusuf yace.
"Don ka fitar da matan muyi aikinmu anutse, ga shi nan zuciyar yarinyar nan saura kadan ta buga."
Yusuf ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba, yama gaza magana.
Waje ya fita dasu Murja ya basu haƙuri ya dawo shima haƙuri suka basa ya fita dole.
Yana fati Mahmood da matansa suka iso.
Yusuf ya rungume yayansa yana sauke wani irin ajiyar zuciya.
Mahmood ya buga bayansa yace.
"Kayi haƙuri Yusuf matarka zata tashi in sha Allah, muna addu'a."
Kai ya jinjina yana sauke numfashi.
Ikram da aka zo da ita cikin girmamawa ta gaishe da Annah da Salha, tana tambayarsu me jiki."
Annah tace.
"Alhamdulillah! Ikram baka zama agida kana yawo haka ka tsufa? ALLAH ya raba lfy."
Ikram batace komai ba saboda kunya.
Hannun Yusuf ta kama tana kallon Murja tace.
"Wlh Momy har yanzu Ban fita daga Shock din abinda ya samu Aunt Sa'adah ba."
Murja hawayen munafurci da suka ƙi tsayawa tace.
"Toh keda bakya nan bare nida abun ya faru gaba, naje naga yarinya ta buga ihu ta yanke jiki ta zube ba rai, kuma ba abinda aka mata ya zan manta wannan musiba. Ya ALLAH kaba Sa'adatu lafiya."
Ta karashe maganan cikin kuka.
Yusuf ya zaunar da Ikram kusan Murja shima ya zauna ya kamo hannun Murja yace.
"Momy kiyi haƙuri bawa baya wuce ƙaddarasa, nafiki damuwa haƙuri kawai nake, mu mata addu'a."
Kai ta jinjina tana kallon ɓangaren su Annah.
Ido suka haɗa da Salha, sai taga Salha ta mata wani irin kallo tana haɗe fuska tam, ta kauda kanta tana ma Annah magana ƙasa².
Fadilah da Halima suka gaisa da mahaifiyar Sa'adah kamar kullun idan sunzo cikin girmamawa.
Kusan 45 mnts likitocin sukayi akan Sa'adah suka fito.
Babban likitin suka keɓe da Yusuf, can office ya masa bayani ta farfaɗo amman a kiyaye ganin abinda yake firgitata, idan akwai wanda ya mata wani abun cikinsu wanda idan ta gabansa take shiga tashin hankali ya dakata da zuwa asibitin har ta warke.
Yusuf sosai ya sake shiga damuwa, shi baisan abinda akayi ba, iya abinda mahaifiyarsa ta faɗa masa wanda ta
0 comments:
Post a Comment