*K* o bayan da suka fito daga wankan tsokanarta yayi tayi,burinsa bai wuce ta dad'a sakin jiki da shi sosai ,suyi rayuwa mai cike da tsafta da k'aunar juna cikin ko wane hali zasu kasance,duk yadda ta sanar da shi irin son da take masa tunma kafin wannan lokacin,amma kuma yana da burin jin labarin yadda ta rayu da soyayyarsa a lokacin da basu tab'a tozali da junan suba,cikin dabara ya shiryata sannan ya shirya kansa,kamar jaririya haka ta zame masa shi kuma duk abunda take yi ko kad'an bai ganin laifinta bare ya damu hasalima burgeshi take.
Parlour suka fito tana jikinsa a lafe kamar mage,dama KHUBRA ba baya bace gurin son jiki yanzun kuma ta samu shi yasa ta dad'a manne masa,cikin kunnenta yake rad'a mata
"Baby baki bani labarin yadda kika rayu da soyayyana ba kamar yadda kika fad'a.."
Idanunta a rufe tana kwance kan chest ensa,tana ta faman zuba murmushi,abunda ya fad'a yasa ta sake duk'unk'unewa a jikinsa tana fad'in
"Nima ai baka fad'amin labarin soyayyana ba.."
Murmushi yayi mai sauti sannan ya d'ago fuskarta
"Kina son ji ne...?"
Kai ta d'aga masa,cikin zolaya yace
"Oyyahhh! idan kina son na baki labari sai kin kalleni tukun kuma yanzun.."
Dad'a sinne kai tayi a jikinsa tana fad'in
"Tabbb! wollahi a'a ban iyawa.."
"Shi kenan to tunda bakya son labarin sai a hak'ura"
Da sauri ta katse shi tana fad'in
"A'a a'a ni ka bani a haka,so kake kasa nayi ta jin kunyarka kenanma ko...?"
"A'a ta yaya zan saki jin kunya,ni da nake sonma ki dena jin kunyana gaba d'aya.."
"Ehhh! ammafa cewa kayi saina wani kalleka sannan zaka fad'amin.."
Murmushi yayi yana k'ara rungumeta tsam a jikinsa,zuciyarsa kan tsananin farin cikin da yake ciki ji yake kamar ya ciro ya bata ita kyauta ko ya samu sassaucin tsananin soyayyan dake cin jikinsa,duk da kasancewar a yanzun gashi ga ta
"Ok..! bari na baki labarin yanzun,amma da sharad'ifa..."
Ya k'arasa yana dariya
"Tabbb! ai na fad'a maka wollahi babu wani sharad'i da zan kuma yarda da shi indai naka ne.."
Dariya yayi sosai har hak'oransa suna bayyana,sannan ya fara bata labarin irin son da yake mata tun daga ranar da suka dawo gida shi da KHALEEL zuwa lokacin farkon da KHALEEL ya nuna yana sonta,da halin daya shiga akanta bayan b'acewarta,zuwa lokacin da suka had'u da ita a k'auyen ZAKIRAI da kuma dawowarta har kawo yanzun da suke tare manne da juna.
Ajiyan zuciya ta saki tana fad'in
"Dank'ari..! Amma kumafa YAYANAH kasan wani abu,Allah gani nake nafika shan wahala akan soyayyan nan,ni abunda yayi saura da zan iya cewa bai same niba,shi ne rashin lafiya amma kam daf nake da kamuwa da ciwon zuciya musammanma lokacin da aka sa ranar aurena da YAH KHALEEL,Allah ko jina nake a lokacin kamar bana raye,gani nake kamar na koma mutum-mutumi saboda a lokacin nikam gani nake shi kenan na rasaka a rayuwata...
Sai gashi na tsinci dami a akala,abunda sam ban kawowa zuciyata zai faruba sai gashi kamar a mafarki komai ya canja cikin lokaci kad'an.."
"Hakane baby amma kumafa ba zakimin wayoba sai kin bani labarin yadda komai ya faru.."
Murmushi tayi tana fad'in
"Yanzun kuwa zan fad'a maka komai.."
Nan itama ta shiga bashi labarin tun daga mafarkinta na farko da shi wanda ya janyo mata shan ruwa a gurin LADIYO data juye mata randa guda na ruwa akan batayi aikin data sata ba ta kwanta,k'arshe kuma dad'in mafarki yasa har bata ji lokacin da take rafka mata kiraba,daga nan ta d'ora masa da farkon zuwanta garin KANO zuwa rayuwarta a gidan MA'U da yadda mafarkinsa yayi ta jawo mata karb'ar na jaki a gurin MA'U har ta kai ga ta ture MA'U'N wata rana dalilin daya janyo mata targad'e kenan.Nan ta dakata tuna irin dariyar muguntar da tayi mata a ranar,dariya tayi a lokacin mai cike da sukuni na samun y'anci,hancinta ya lakace yana fad'in
"Jodi wato kema kin iya dariyan mugunta ko...?"
Kallonsa tayi tana murmushi jin ya kirata da wani suna na daban
"Uhmm! Allah ko YAYANAH ko kai da kana gurin sai kayi mata dariya,musamman yadda take tafiya kamar wata...."
Shiru tayi tana murmushi,a zuciyarta tace
"Allah yaso ban k'arasa ba,dan ko ni nasan abunda naji da dare,garama da ban k'arasa ba.."
Muryarsa ta tsinkayo yana fad'in
"Nikam babu dariyan da zanyi,dan a lokaci'nma da ina da dama to da tabbas k'ara mata zanyi.."
"Me yasa YAYANAH..?"
Sai daya runtse idonsa coz gani yake kamar a lokacin abunda ta fad'a suke faruwa,cikin dashewar murya na mutumin dake cike da tausayi ya furta
"Saboda ta wahalarmin abunda nafi k'auna a rayuwata..."
Fuskarsa ta shafa tana murmushi
"Yanzun kuma fa...Ai gani a kusa da kai ko.."
"Haka ne mafi kusama kuwa...Tunda gaki kwance cikin jikina ba..
Ammafa duk da haka saina hukunta su saboda sun aikata laifi mafi girma a gareki..."
"Ni kam YAYANAH bana son d'aukan wani mataki da zakayi,ina tunanin idan muka barsu da Allah zai isarmana,kuma ko bayan haka ma,tun yanzun kam ai sun fara girban abunda suka shuka..."
"Haka ne jodi Allah ya mana maganin irinsu.."
"Ameen YAYANAH..."
"Emmm! ina binki bashi fa..."
Kallonsa tayi da alamun neman k'arin bayani akan fuskarta
"Ehh! mana.....ko kin manta ne? ai da sauran labarin dan baki gama ba ina kuma sauraronki..."
"Kaiii YAYANAH kana da son labari.."
"Ehh! naji amma labarin ba kowanne ba"
"To sai wane iri..?"
"Irin wannan mana da kike bani yanzun,ai shi nafi so na kuma fi buk'ata.."
Ci gaba tayi da bashi labarin yadda ta gano shi ne mutumin mafarkinta har sai data k'are,kiss ya manna mata a porehead enta cikin sanyi ya furta
"Da ace inada damar maida hannun agogo baya to da tabbas nayi hakan dan na samu daman goge duk wani tabo daya shafeki a rayuwa,sai dai kash babu halin yin haka...Amma yanzunma bata b'aciba zan kasance miki matsayin miji wanda zai baki dukkan wata kariya ta ganin babu abunda zai kuma samunki a gaba.."
Tsam suka dad'a rungume junansu cike da soyayya da kulawa..Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cike da bawa junansu kulawa ta musamman.
*TWO WEEK'S LEAP.*
Kimanin sati biyu kenan da aurensu,har yau BB ko k'ofar gida bai sake koda fita ba,hasalima wayoyinsa gaba d'aya ya kashesu dan kawai kada a takura musu,a cewarsa amarci suke saboda haka babu mai damunsa.
Yau ya yanke shawaran kunna wayoyin yana kunnawa ko kiran KHALEEL na shigowa,cike da nishad'i ya d'auka yana fad'in
"MAN..! Yane..? ya iyali...?"
"A'a ku ai kune masu iyali,tunda gashi ganin kama ya gagara bare a jika ko da a waya.."
Murmushi yayi yana fad'in
"Kai da Allah ba wannan ba,yanzun kana ina ne ina son mu had'u mu k'arasa maganar karatun JODI..."
Dariya KHALEEL yayi yana fad'in
"Ehh! lallaifa ka tabbata masoyi irin wannan canjin suna cikin lokaci kad'an haka.."
Bai tanka masaba,saima hiran daya canja zuwa maganar daya d'auko na karatunta dayake so nan bada jimawa ba ace hakan ya samu.
Sai da suka gama maganar sannan yayi masa sallama,d'agowa yayi yana kallon hanyan corridor na bed room ensu,tsaye ya ganta cikin gown data kamata red colour mai suphagetti'n hannu,gashinta ta kamashi a tsakiya da red en ribbon,idanunta ya sha kajol kwalli,da red en lipstick sai kyalli bakinta keyi..Kallonta ya tsaya yi kamar wani dolo,k'amshinta duk ya cika gurin,har tazo gabansa bai sani ba,sai data masa blowing air a fuska sannan ya sauke wani ajiyan zuciya,waist enta ya rik'e dai² tana shirin zama ya janyota kan laps nasa
"Jodi wannan kwaliyyanfa haka..?"
Hannunta d'aya ta zagaye a wuyansa d'ayan kuma tana zane akan fuskansa tana tafiya da shi daga kan goshinsa zuwa saman tip noise nasa,wani ajiyan zuciya yayi yana lumshe idanunsa kamar mai jin bacci,bud'ewa yayi ya sauke su kanta cikin shak'ak'k'iyar murya yake shirin yin magana sai dai kuma ya kasa,gyaran murya yayi yana son magana again ya kasa,yatsanta tasa a kan lips ensa tana shafawa kamar tana sa masa wani abu tana kallon cikin idonsa,sai data bari ya gama kamuwa dan idanunsa har sun soma sauya launi tayi saurin mik'ewa tayi hanyan bedroom a guje tana masa dariya.Binta yayi da sauri ko kafin ya k'araso ta turo k'ofan tana k'ok'arin rufewa,da sauri yasa jikinsa ya tareta,barin gurin tayi da gudu ta haura kan bed tana dariya,murmushi yayi ya kamota
"Wato na zama abun tsokana a gurinki ko..?"
Tana kallon eye ball nasa tana dariya,kallonta yayi yana matsawa da fuskansa,porehead nasu ya had'a sannan tip noise,har lokacin dariya take tana shirin yin magana ya hanata,dai² lokacin daya kamo lower lip nata yana kissing.
Shiru tayi tana faman mutsu-mutsu,sai da yayi nisa sosai a jahar da bai san inda yake ba,ring en wayansa dake yashe kan bed ya dawo dashi hayyacinsa,a wahale ya d'ago jajayen idanunsa yana lalubarta da niyyan ya kashe ya d'auko,sai dai kuma sunan KHALEEL daya gani yasa shi d'auka,ko kafin yayi magana KHALEEL en ya katse shi ta hanyar fad'in
"To mara zumunci gamu dai a parlour muna jiranku..."
Wani uban tsaki ya saki,a fili ya furta
"Banda d'an iska yanzun mu gama waya baka fad'aminba,sai yanzun saboda ka rainama mutane hankali.."
Ransa a d'an b'ace ya koma gefe yayi rigingine yana murza goshinsa daya d'auki d'umi,dariyan mugunta tayi ta mik'e tana gyara riganta daya janye yayi sama,sai da taje bakin k'ofar fita ta juyo ta kalleshi,kallonta yake idanunsa sun canja kamar zai mata kuka yake kallonta,gwalo ta masa sannan ta fice,K'wafa yayi sannan ya furta
"Zan kamaki ne,za kuma kiyi bayani.."
Da kyar ya saita kansa ya fice,ko daya fito parlour nan ya shiga had'e fuska saboda bai son su kawo masa wasa,KHUBRA dake rik'e da hannun ZUHRA ta d'ago cikin alamu na rashin gaskiya ta kalleshi,aiko take suka had'a ido kallon da taga yayi mata yasa ta kwashewa da dariya,kallonsu KHALEEL da ZUHRA suka tsaya yi,sai dai kuma sun bagarar da lamarin babu wanda yayi magana,nan hira ya b'alle tsakaninsu,janye ZUHRA tayi suka shige d'akinta da suka gama chukuikuye bed sheet en kai kamar wad'anda sukayi dambe samansa,kallon yanayin d'akin ZUHRA tayi sannan ta kalli KHUBRA tana fad'in
"CWEETY haka kika koma kuma...?"
Cikin alamu na rashin fahimtan inda zancenta suka dosa ta kalleta tana fad'in
"Me kuma akayi..?"
"Can nake nufi..."
Ta nuna mata saman bed enta,d'an tsaki tayi tana fad'in
"Ke yanzu nefa ya koma haka,ai na gyara da safe..."
Bata kuma magana ba,dan kam ba saita tambayaba,ta gane abunda take nufi,k'ulewa sukayi cikin d'akin tana koya mata wasu abubuwan a tunaninta KHUBRA bata san komai ba,ita ko kallonta kawai take,a zuciyarta fad'i take
"Y'ar uwata kenan ke a ganinki dan na rayu a k'auye babu abunda na sani..Amma kuwa idan har haka ne to da zamana a nan bai amfana min komai ba,ko dan banyi boko ba ai hakan ba yana nufin babu abunda na iyaba,duk wannan soyayyar ai akwaita cikin ilimin addini,kuma akwai littafin da ABBANAH yake karantamin,hasalima sai dai na koya miki wani abun..."
Tagumin da tayi ta zubawa ZUHRA ido,ita ZUHRA a tunaninta sauraronta take har ta k'are yi mata hud'ubar kwalliya dasa matsatstsun kaya wad'anda zasu jaa hankalinsa,tare suka shirya dinner su kuma su BB suna nan cikin parlour suna hiransu suma,har suka gama sannan KHUBRA ta wuce bed room inda tabar ZUHRA a gurinsu,wanka ta sake sannan ta shirya cikin short nicker iya cinyanta,da wani half vest,lafaya ta d'auko mai kauri ta nad'a sannan ta kama gashinta ta nad'e shi kamar yadda indiyawa suke yi yayi gammo,simple make-up tayi bakinta ya sha white lipgloss,sai k'yalli yake kamar an sanyashi cikin tandun mai,b'arin turare tayima jikinta sannan tayi juyi a gaban mirror,tana shirin fita ya shigo yana kiranta,tsaye yayi yana k'are mata kallo yadda ta koma masa kamar wata SONAM KAPOOR a cikin phrem rhatan dhan phayoo,hugging enta yayi ta baya suna tsaye gaban mirror en suna kallon juna ta ciki,a hankali ya juyo da ita suna fuskantar juna,hab'arta ya d'ago da hannunsa yana matso da fuskarsa dai² nata,cikin sauri ta dakatar da shi tana fad'in
"YAYANAH kasanfa ba mu kad'aine cikin gidanba..."
Idonsa ya runtse yana sakin wani gajeren tsaki,haushin su KHALEEL yake saboda zuwansu ya masa shamaki da kasancewa tare da ita,dariya take ta k'unshewa dan ta kula da yanayin da yake a ranar,kanta ta sunk'e tana yin k'asa da shi,hab'arta ya sake d'agowa yana fad'in
"Bazan hanaki dariyaba,dan dama d'azunma har tsokanata kikeba kuma a gaban idonsu ko..?"
Shiru tayi babu amsa sai idanunta da take juyawa tana kallonsa,wani killer smile ya saki yana fad'in
"Tunda babu amsa nima baran barki ki fita haka nanaba,musamman wannan lips en naki da kika laftawa mai...emmmm! wai ma da haka zaki fita ne...?"
Kallon rashin fahimta ta masa shi ko gira ya d'age mata,ita kuma ta kafe shi da ido tana jiran jin me zai fad'a,hannu yasa ya rufe mata ido a hankali ya had'e bakinsu guri guda,sai da ya tabbatar ya shanye lipgloss data sa tas,sannan yaja hannunta sukayi waje inda suka bar KHALEEL da ZUHRA na jiran fitowarsu,zaman da ZUHRA ke gyarawa ya tabbabtar da itama ba k'alau ba,d'an murmushi KHUBRA tayi tana d'auke kanta daga kansu ganin sai kame-kame ZUHRA'N keyi,haka dai suka gama dinner kafin sabon hira ya b'alle ZUHRA kam duk mamakin KHUBRA take yi,ganin yadda tayi shigan kamar indi'a a zuciyarta ko fad'i take
"Lallai CWEETY ina miki kallon babu abunda kika iya a b'angaren soyayya ashe kyace sai dai ni na koya...Dole mana BB ya haukace miki,mai mata irin wannan ai dole ko wane lokaci a samu gadon baccinsu a yamutse.."
Kallon agogo BB yake,dan tun d'azun shi yake ta kallo tun da akayi salla'n isha ganin babu maganar zasu tafi yasa ya fara magana fuska babu wani wadataccen fara'a
"Wai ku kam sai yaushe zaku tafi ne...?"
"Koranmu kuma za kayi ne..? ko kuwa dan mun zo gidan kane hakan..?"
Banza yayi masa babu amsa,dan kansa kuma KHALEEL en ya kalli ZUHRA yana fad'in
"HABEEBTEEY! Tashi mu tafi kinji tun yanzun an fara korarmu.."
Kamar mai jira ko yana rufe baki ta mik'e tana had'a kayanta,suna gamawa KHALEEL ya kalli BB
"To MAN! mu mun wuce tunda ka gaji da ganinmu.."
"Ehh! ko me zaka fad'a sai dai ka fad'a bani kuma da lokacinka yau kam.."
Murmushi KHALEEL yayi sannan ya kama hannun ZUHRA suka yi waje su kuma suna binsu a baya don rakasu.Sai da suka bar gidan sannan suka juyo da nufin komawa ciki,tafiyar da takeyi kamar bata so ne yaga ya masa tsayi janta yayi ta tsaya,kafin tayi magana ya rabata da k'asa,ko ba a fad'a mataba kam tasan nufinsa,hannayenta tasa ta zagaye wuyansa,kai tsaye bedroom ya wuce da ita yana sakin sanyayyar ajiyar zuciya dan kam tsawon kwana uku kenan ba tare da ya sake mata komai ba,yau kam ai sai yadda Allah yayi da ita dan ko ita da kanta ta tabbatar da haka,musamman yadda yake mata rawar k'afa tun safe,bare kuma yanzun da suke neman kad'aita da juna cikin d'aki d'aya shimfid'a kuma d'aya..................
*COMMENT FOR MORE PAGE'S........* 💃💃💃💃💃
*~#TEAM KHUBRA-KHALEED.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE NOVEL'S GROUP@web.facebook.com
*©®2018*
*5/ɑմցմՏԵ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~___________________________~*
_Congratulations for the compilation of your amazing,wonderful and romantic novel dear *AMINA UMAR FANA (AUFANA)* Allah yasa sak'onki ya isarma al'ummar da akayi dominsu,Allah kuma ya baki ikon fara na gaba lafiya.._
*~___________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
5⃣9⃣
*S* aman bed ya kwantar da ita sannan a hankali ya shiga warware lafayan data nad'a kamar sarii har ya kammala ware shi tas daga jikinta,arba yayi da arnan kayan dake mak'ale jikinta sam tunaninsa bai kawo masa cewa zata iya sa irin wad'annan kayanba,wani murmushi ne ya sake escaping daga bakinsa,sosai kayan dake jikinta suka amsheta musamman da suka kasance dai-dai ita,d'an nickers en nata ya kalla wanda da kad'an yafi pant da kuma mitsitsiyar rigar jikita wacce yanayin kwanciyan da tayi yasa halittun jikinta bayyana ta dai² wuyan rigan,da k'arfi ya sauke ajiyan zuciya saboda kasancewar irin rakin data yita ta zuba masa cikin satin aurensu yasa ya d'aga mata k'afa har na tsawon kwanaki uku,k'ark'arinsa da ita idan sun gama shirin kwanciya ta shige jikinsa kamar mage,shi kuma haka zai rungumeta ba tare da yayi mata komaiba,sai dai yau kam baya jin zai iya hak'uri musammanma yadda ta yita kunno shi tun safe,dole ne yau kam ya sauke mata gajiyan kwana uku.Tafiyan tsutsa ya soma mata daga cikinta har zuwa dai² chest enta da suka riga suketa tsokane masa ido,tafiyan tsuntsan da yake mata yasa ta shiga mirgina kai gefe tana dariya wanda yasa ta rufe idanunta,dariyan shima yake dan da alama kam tana enjoying abunda yake mata,ci gaba yayi ba tare daya sauraraba har hannayensa suka samu daman shigewa ta k'asan ficilar riganta wacce da kad'an tafi bra,salon da yake gabatar mata a lokacin shiya dad'a hautsinata lokaci guda service enta ya harba,romantic kisses ya shiga aika mata tun daga tafin k'afarta har ya haura zuwa saman maranta,daga nan yaci gaba da yin sama har ya iso dai² inda yayima hannayensa matsuguni yana wasa dasu,ruwan kisses en da yake sakar mata yasa itama batayi k'asa a guiwaba ta biye masa saboda kasancewar a cikin y'an kwanakin kusan za a iya cewa indai ta wannan fannin ne BB ya rigada ya gama biya mata babin,wanda itama babu b'ata lokaci ta haddace har tana neman k'ari,cike da shauk'i suke kissing juna wanda ya dad'a hautsina musu tunani kafin wani lokaci tuni har sunyi watsi da kayan dake sanye jikinsu,rumfa yayi mata suna kuma ci gaba da aikawa junansu sak'onni masu girma,wanda a k'arshen wannan dare sai da KHUBRA ta gane girman bambanci na halittarsu,dan kam BB ko kad'an bai saurara mataba sai da yaji network ensa ya kawo full,sannan ya koma gefe yana rungume da ita suna maida numfashi.
Shi da kansa yakanyi mamakin dalilin da yasa ya koyi wannan jaraban bayan da ba haka yakeba musamman satinsu na farko da aure sam bai wani iya hak'uri,ko mene ne dalilin ohhoon masa,sai da suka gama maida numfashin wahala sannan yayi sama da ita sai toilet,cikin kumfan suka dad'a shantakewa ko tunanin dare yana ci gaba dayi basuyi ba,sai da suka shafe tsawon wani lokaci a ciki sannan daga bisani kuma sukayi abunda ya kaisu suka fito yana rungume da abarsa kamar baby'n robber.Bacci mai cike da shauk'i da kuma sukuni na kasancewarsu tare yayi gaba da su.
*A MONTH LEAP.*
A wata safiya bayan sun tashi kamar yadda suka saba suna manne da juna a haka suka had'a break fast,sun ciyar da junansu inda ya kasance fiye da rabin cin abincin nasu ya zama tsokana da haka dai suka kammala,sannan suka koma saman cuistion tana saman jikinsa cike da soyayya da kuma kulawa ya kalleta yana sakin mata k'ayataccen murmushinsa da ba kowa yake wa irinsaba,cikin k'asa da murya a dai² kunnenta ya furta
"JODI yau kam ina so muje gida mu gaisa dasu MAMA fa..."
Da sauri ta d'ago tana murmushi
"Allah YAYANAH....? kamar kuwa kasan dama ina son ganinsu inata kewarsu fa.."
Murmushi ya sake yi kafin ya d'aga mata kai cikin wani irin kallo mai wuyar fassara murya can k'asan mak'oshinsa ya furta
"Mene ne abun kewarsu bayan kina tare dani...Ko kuwa kinfi sonsu fiye dani...?"
Yatsanta ta d'ora kan lips ensa tana kad'a masa kai alamar a'a
"Haba YAYANAH taya zaka ce haka,bayan kaine gaba d'aya rayuwata...Bana jin a duniya kam idan har a b'angaren soyayya ne idan aka cire son ALLAH da MANZONSA (S.A.W) daya zama wajibi akansu,sannan ABBANAH bana jin bayan wannan akwai wanda zai zo bayan nan sama da kai....Idan baka manta bama ai na fad'a maka da soyayyarka na girma tun ban gama sanin kainaba har ya zamana na fahimci hakan.Kaga ko idan haka ne wannan kalmar sai dai tayi gefe dan bata kamaci mutum irinka ba."
Fuskarsa da matsanancin farin ciki yake kallonta kafin yayi magana yana kallon cikin eye ball enta
"JODI ni kam ina son sanin ta yaya akayi kika gane ni a matsayin *MUTUMIN MAFARKINKI* dan wancan labarin kin b'oyemin baki sanar dani ba..."
Murmushin itama tayi wanda ya bayyanar da hak'oranta cikin salon tsokana ta furta
"Da wad'annan idanun naka masu kama dana kyanwa..."
Sai da yayi dariya sosai sannan ya kalleta yana fad'in
"A haka kuma kika gani kika mace a soyayyar mai idanun kyanwar ba..."
"Eh! naji dad'in abunma dai ciwo bai kusa illatani ba.."
Ta fad'a tana masa dariya,hancinta ya lakace yana ci gaba da dariya,sai daya tsagaita da dariyar sannan ya furta
"JODI kin san wani abu..?"
Kamar wanda zai fad'i wani abun kirki haka ta kalleshi tana fad'in
"A'a YAYANAH sai ka fad'a zan sani..."
"Idanki ai yana kama da nawa..."
Dariya tasa masa tana fad'in
"Haba dai ai nawa yafi naka kyau kallafa naka ta tsakiya wani haske dake ciki kamar na mage.."
"Ok! tunda baki yarda ba zamu tambaya amma da *sharad'i* idan akace irin nawa ne zaki bani wani abu..."
Ya k'arasa yana mata winking.
"Hahhhh! YAYANAH sharad'i dai sharad'i dai ko wane lokaci kacemin kana da sharad'i,ni kuma na fad'a maka na daina yarda da sharad'in nan naka...Sai dai ka fad'i wani abun amma banda sharad'i..."
Cikin shagwab'a ya furta
"Ni gaskiya a'a shi kad'ai nake so,kuma idan baki yardaba zanyi miki kuka har sai kin rarrasheni da wannan abun zan hak'ura nayi shiru..."
Yanayin da yayi magnar yasa ta kwashewa da dariya tana fad'in
"Wai kam YAYANAH baka gajiya ne...?"
"Dame zan gaji JODI.....? dake wai kike nufin zan gaji ko me..?"
"Eh mana wancan satinfa sam baka barni na hutaba wannan ma haka...wai kam idan aka ce na haihu ya za kayi lokacin...?"
Hak'oransa ne suka bayyana a fili yana mata murmushi cikin d'oki da farin ciki ya furta
"Allah ameen JODI..ni yanzunma bank'i ace mun samu k'aruwa ba..yanzun ace cikin kwanakin nan nayi ajiyar baby a nan ai sai nafi kowa farin ciki.."
Yana maganar yana shafa k'asan maranta,murmushi kad'ai tayi bata yi maganaba,hakan yasa shi fad'in
"Ko bakya farin ciki ne JODI....?"
"Me ka gani YAYANAH..."
"Naji kinyi shiru ne daga maganar ciki,kuma bayan ke kika kawo zancen.."
"Laaaa! YAYANAH me yasa bazan soba bayan ya fito ta sanadin abunda nafi k'auna,shirun da nayi wani abu nake tunani ne.."
Da sauri ya dad'a rik'eta a jikinsa yana fad'in
"Haba JODI bayan gani a gabanki wane tunani kuma za kiyi..?"
"YAYANAH kenan ina tunanin ranar da za ace an kaini asibiti zan haihu ne...har na fara jin tsoro Allah.."
_Dariya sosai maganarta ta bani nida nake gefe,cikin da ba ama tabbatar akwai ko babu ba shi ne har ake tunanin ranar haifeshi...Allah ya kyauta muku da kuke maganar cikinma._
"Laaaaa! JODI mene ne abun tsoro ai tare zamu haihu,kin san baran tab'a barinki kisha wahalaba duk rintsi muna tare a mak'ale da juna.."
Mab'allan gaban rigarsa da suka kasance a bud'e wanda hakan ya bawa lallausan bak'in gashin dake kwance saman k'irjinsa damar bayyana,tasa hannu tana wasa dashi kanta kwance gefe tana ci gaba da abunda take,kamar wata k'aramar yarinya sai ta d'an ja a hankali ta saki tana sosa masa gurin wanda ya kasance kamar tafiyan tsutsa,a hankali ta kalleshi tana fad'in
"Laaaaa! YAYANAH kacefa zamuje gida kaga kuma naga kana rufe ido Allah yasa ba bacci zaka ce za kayiba....ko kacemin na bari sai an jima..."
Ido d'aya ya bud'e while the other one yana rufe
"Sai zuwa anjima idan na gama abunda nake.."
"To ammafa naga a kwance kawai kake,mai zai hana mu tafiya yanzun...?"
Idanunsa a rufe duka ya furta
"Na ce saina gama abunda nake.."
"Ammafa YAYANAH...."
Bakinta ya rufe yana fad'in
"Bana son yawan maimaita magana mu barshi iya haka JODI,idan na tashi yanzun zan sake shiryawa.."
"Shiri kuma wane iri..? canja kayan shi ne shiri kuma YAYANAH"
"A'a ba iya changing kaya bane kad'ai.."
Da mamaki a fuskarta take k'arewa fuskarsa kallo,coz maganarsa ta d'aure mata kai ta kuma kasa fahimtar abunda take nufi
"Ni dai gaskiya YAYANAH ka tashi mu tafi kagafa idan rana yayi cewa za kayi sai wani lokacin...kuma ni Allah ina son zuwa kaji..."
"Ok! muje kimin wanka to tunda kina so mu tafi yanzun..."
Ba tare daya bud'e idanunsaba yayi maganar
"Wankafa kace YAYA bayan tare mukayi wanka'n da kai...me zaisa ka sake wani sabon wankan kuma..?"
"Kece.....! kece zaki sani sakewa.."
Fuska da alamun tsoro tace
"Nifa Allah YAYANAH banyi komaiba,ta ina na zama sanadin da zaka sake wanka kuma...?"
Hannunta da take wasa da shi har lokacin a jikinsa ya rik'e yana fad'in
"Saboda wannan abun da kike yi mana,ni kuma kinga baran ce ki bari ba..."
"Hahhhh! YAYANAH haka ka koma kuma...Tabbb barin sauka a jikinka tun kafin wata ranama kace kwanciyan da nayi yasa ka....."
Bakinta ta damk'e tana dariya jin irin rik'on da ya sake yi mata
"Babu inda zaki je har sai kin k'arasa aikin kwangilar da kika amsa..."
"Hahhhh! YAYANAH kenan ni dai nasan babu wani kwangila dana karb'a sai dai ko ban saniba yanzun za a bani..."
"Uhmm! JODI kenan kwangila ai tuni kika karb'a signing ya rage kiyi..."
"Gaskiya YAYANAH ban san yaushe ka koma haka ba..."
'Dagowa yayi yana kallonta idanunsa a kanta yake fad'in
"Ke kika mai dani haka JODI tunda kinga ni lafiyayyen namiji ne,so dole sai kinyi hak'uri dani sannan kuma sai kin koyi juriya saboda mijinki..."
"Yo to YAYANAH wane juriya kuma bayan wanda nake da ita har wani zan koya..."
Dariya yayi mata "Noo! ina sone ki k'ara akan naki da kike da shi.."
"Hahhhh! to ni dai gaskiya ka tashi mu shirya mu tafi...Kaji...?"
"Ai sai kin k'arasa aikinki sannan zan yarda mu tafi,idan kuma bara kiyiba za a fasa tafiyan..."
Ya fad'a teasingly yana kashe mata ido d'aya,fuskanta ta shagwab'e kamar za tayi kuka,da sauri ya dakatar da ita yana fad'in
"Noo! kin san tun can bana son yawan kuka,so kuma abun nan it's a matter of deal,idan kin yarda shi kenan mu gama abunda ke gabanmu kafin mu tafi idan kuma ba haka ba shi kenan an fasa tafiyanma gaba d'aya.."
Kallonsa take kamar sakarai saboda jin yadda yake ta tsara zance kai ta langab'e gefe bata iya cewa komaiba,ammafa idanun nan kamar wanda aka tsoma cikin ruwa
"Yawwa! sannan idan kika yi kuka shima an fasa tafiyan yau sai wani lokacin..."
Da sauri ta shiga maida hawayenta duk dan gudun kada a fasa tafiyan yau,bayan ta gama sawa a ranta zataje taga su MAMA...
Wani killer smile ya saki yana dad'a janta jikinsa,idanunta a rufe saboda bata son tayi kuka coz tasan halin abunta tunda yace idan tayi za a fasa tsaf zai fasa en tun ba yauba tasan halinsa a d'an zaman da tayi a gidansu.Tana jinsa yana laluben bakinta ta bud'e masa dan kam a wannan lokacin gardama ba nata bane,sannan tun farko tayiwa kanta alk'awari duk abunda zai faru bazata tab'a hana shi hak'k'in saba duk runtsi,saboda a kullum abunda take tsoro kada ta hana shi Allah yayi fushi da ita,baya ga tsinuwar mala'iku da zata yita sauka akanta.
_To k'alubalenku matan aure dama y'an mata masu niyyan yin aure,wasu suna d'aukan hakan a matsayin fansa idan miji ya musu laifi sai kuji ana cewa zamu had'u da shi a gado ne ai wallahi sai ya gane kuskurensa,shin y'ar uwa idan kika yi haka bakya tunanin faruwar wani abune kam? misali ya miki laifi yanzun shi kenan baki da wata hanya davzai gane ya miki laifi har sai kin had'a da bi ta wannan hanyar? to idan baki saniba ki bud'e kunnenki ko kad'an dan kinyi haka ba shi kika cutaba kanki kika cuta,kuma ki sani yin hakan tamkar kin d'auki wuk'ane kin dab'awa kanki,dan kuwa a lokacin da yake tsananin buk'atarki idan baki bashi kankiba to tabbas abunda ba a fata zai faru,imma dai ace daga wannan lokacin ya fara bin matan banza idan har da baya yi,imma kuma idan yana yi ya k'ara a kan na da,ya rage naki ki gyara ko karki gyara,amma kam tabbas idan kika yi haka k'arshe zaizo miki da sakamakon abunda kika jefaku ciki,sannan kuma ga tsinuwar mala'iku baya ga fushi da Allah zaiyi da ke,kafin kuma ki samu k'arin tsinuwar mutane ta soma yawo akanki,kinga saiki zab'a bashi hak'k'insa ko tsinuwar....Allah ya bamu ikon gyarawa._
Harshenta yake lalube ganin yana neman wahala ta mik'a masa nan yaci gaba da aikin dake gabansa,sai da suka gama jagwalgwala junansu sannan cike da farin ciki suka koma toilet,bayan sun gama shiryawa suka fito kai da ganinsu zaka gane wannan d'anyu ne a amarci,hannunsu sak'ale dana juna,ko a motanma yana driving hannunsa d'aya na cikin nata kamar wanda za a kwacewa ita,idan ya kalleta sai suma juna murmushi mai d'auke da sak'onni daban-daban haka har suka k'arasa mai house nasu.
Ko gama daidaita parking bai yiba ta shiga k'ok'arin fita,da sauri ya dad'a rik'o hannunta,wani kallo wa watso mata idanunsa a narke yake kallonta,kanta ta sunkuyar k'asa da sauri
"Saurin mene kike yi ne kam...Kina so mu koma ba tare da mun shigaba ko..?"
Kanta ta shiga girgizawa kamar za tayi masa kuka,dariya yayi k'asa-k'asa
"To idan kina so mu shiga ki bari mu tafi tare,bana son wannan gaggawa'n da kikeyi.."
Dakatawa tayi har ya gama abunda yakeyi sannan ya fita,shi ya bud'e mata k'ofan ta fito cikin tafiyan sa ba zai ce tayi sauriba,hannunta ya rik'e a haka suka cimma parlour'n gidan.
Sallamansu tasa MAMA da BABA ZUWAIRA fitowa daga kitchen suna fad'in
"Maraba da amarya...."
Hannunta ta fizge daga nasa tayi jikinsu da d'an gudu,rungumeta sukayi suna y'ar dariya game da tsokanarta tayi kyau kamar ba itaba.
Bayan an gama gaisawa BB,ya mik'e yana fad'in
"MAMA zanje wani guri na dawo,sai zuwa dare zamu koma in Allah ya kaimu..."
Fatan alkhairi tayi masa,k'asa-k-asa yake kallon KHUBRA data wani mak'ale jikin MAMA ita kuma sai biye mata take ita ga mai y'a,har ya kai k'ofar palour yajiyo BABA ZUWAIRA nawa KHUBRA fad'an ta tashi taje suyi sallama,fuska ta kumbura kafin ta tashi ta biyo shi,har bakin mota ta rakashi yana gaba tana binsa a baya,kamar abun arziki ya bud'e motan ya shiga,ita kuma tana tsaye dafe da k'ofar ya d'ago ya kalleta ganin fuskarta a cukune yasa ya furta
"Zo nan..."
Babu musu ta zagaya ta d'ayan side en ta zauna tana kallon waje
"Wato rakiyan ne bakya so shi ne kike wannan abun ko..?
"Nifa ba haka bane..."
"To yaya ne..?"
"Babu komaifa..."
Ta sake bashi amsa kuma har lokacin bata saki fuskar ba,juyo da ita yayi fuskarsu na kallon juna ta yanda suke iya jin numfashin junansu na sauka kan fuskokinsu
"JODI nine baza ki iya rakowa ba sai an ce ki rakani...?"
Kai ta girgiza idanunta a k'asa
"Me yasa to kika b'ata fuskanki dan ance ki rakoni...? ko dan bakya so ne shi yasa..?"
Nanma girgiza masa kai ta sakeyi
"To mene ne..?"
Shiru tayi shima shirun yayi ya jingina bayansa a jikin kujeran kallonta yaci gaba dayi,ba tare da ya mata maganaba,itama taci gaba da zama kanta a k'asa ta kasa magana.
Sun jima zaune babu wanda yayiwa wani magana,shi kuma BB zuba mata ido yayi yaga iya gudun ruwanta,gajiya yayi da shirun ya fara magana fuska babu wani wadataccen fara'a
"Wato baki san kinyi laifiba ko...?"
Idanunta ne sukayi rau-rau za tayi kuka,kansa ya d'auke daga kallon da yake mata cikin muryar kuka ta furta
"Kayi hak'uri YAYANAH dan Allah.."
Dai² lokacin hawayen suka sakko kan fuskarta,kasa jurewa yayi da sauri ya furta
"It's ok...!"
Yana janta jikinsa yana patting bayanta,ajiyan zuciya ta sauke tana dad'a kwanciya jikinsa,sai daya tabbatar ya sanyata dariya sannan ya mata sallama akan sai anjiman idan ya dawo zasu tafi,cike da farin ciki ta juya suna waving wa junansu.
Har dare tana gidan kowa sai nan-nan yake da ita musamman MAMA da FATAHIYYA,a nan su ABBA suka tarar da ita lokacin da suka dawo,sosai sunyi farin cikin ganinsu hankalinsu a kwance.
A wannan lokacin ba kowa ne zai kalli ABBA'N KHUBRA ya shaida shiba,ashe dama wahala da zaman k'auye sukasa ya fara tsofewa,cikin y'an watanni har ya soma yin shar da shi,da yake Allah yayi shi mai tsafta shi yasa cikin lokaci kad'an ya dad'a gogewa musamman kuma daya had'u dasu ABBA mutanen da suka yi gogayya da turawa,yadda suke tafiyar da harkokin kasuwancinsu yanzun idan ba wanda ya san suba ba zai tab'a tunanin ba jini d'aya bane su en,dan mutane da dama suna musu kallon y'an uwan juna.
Daf da zasu tafi KHUBRA ta matsa kusa da ABBA'NTA tana masa magana,cike da sha'awar ganin yadda y'ar tasa ta koma ya kalleta yana maida hankalinsa kanta dan ya fuskanci me zata fad'a,kamar abun arziki suka dad'a gaisawa yana tsokanarta,sai dariya take shi kuma hakan shi yasa shi yake sake jin dad'i sosai
"ABBA dama fa akwai maganar da nake ta son maka.."
Kallonta ya sake yi yana fad'in
"To y'ar albarka ina sauraronki"
Sai da tayi ajiyan zuciya sannan kuma kanta a k'asa tace
"ABBA dama ba kan komai bane sai wani al'amari da nake ganin idan hakan ya kasance kowa zaiyi farin ciki..."
Dad'a d'aure masa kai tayi saboda har lokacin bata fad'i abunda zata fad'a enba,muryarta ta katse shi daga sonyin magana
"ABBA damafa shawara ne nazo da shi,nace me zai hana ka yarda da BABA ZUWAIRA a matsayin mata,kaga itama dama bata da aure mijinta ya jima da rasuwa,kuma ABBA na baku labarin yadda ta rik'eni na tabbata bata da wata matsala...Kuma kaima yanzun ABBA baka da kowa sai ni kad'ai..."
Dakatar da ita yayi fuska a had'e yake fad'in
"Maganar dama da kika zo da ita kenan saboda futsara irintaku ta y'ay'an zamani har ni kikewa maganar nayi aure...?"
Yadda taga ya b'ata rai ya kuma zage yana ta mata fad'a yasa ta shiga bashi hak'uri,amma kam bata ji dad'iba daya k'i amincewa,haka sukayi sallama da mutanen gidan da suka rakosu har bakin mota kafin suyi musu sallama suka d'auki hanya.
Cikin motan shiru babu mai magana kanta a k'asa tana matse hawayen dake sauka kan fuskarta,maganar BB ya dakatar da kukan nata
"Me kika yiwa ABBA yayi miki fad'a....kin b'ata masa rai ko...?"
Sai da ta gama kukanta ba tare data kula shiba,shi kuma sai nasiha yake mata yana nusar sa ita hanyar da zatabi su zauna lafiya da ABBA,sai da ta bari sunje gida har sunyi wanka sun kwanta sannan ta bashi labarin abunda ya had'asu,ajiyar zuciya yayi kafin ya nuna mata illar abunda tayi,sai yanzun ta fahimci laifinta dan kam tabbas ba ita ya kamata tayi masa maganar ba.Tun daga lokacin ta k'udurce a ranta duk hanyan da zata bi sai ta bi na ganin hak'anta ya cimma ruwa kuma zata dage da addu'ah akan Allah ya tabbatar da alkhairinsa................
_Wannan kenan.._
*COMMENT FOR MORE PAGE'S..........* 💃💃💃💃💃
*~#TEAM KHUBRA-KHALEED.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE NOVEL'S GROUP@web.facebook.com
*©®2018*
*6/ɑմցմՏԵ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~___________________________~*
_cwєєt ѕíѕ *HALIMATUS-SADIYA MUHAMMAD (LEEMA)* ínα tαчαkí murnα dα fαrín cíkí nα gαmα wαnnαn nσvєl mαí cíkє dα d'umвín dαruѕѕα nα *IYA KU'DINKA* αllαh чα ѕα ѕαk'σnkí чα íѕα índα kíkє вuk'αtα αllαh чαѕα mutαnє ѕuчí αmfαní dα d'umвín вαѕírαrkí dα kíkα zuвє α cíkí dα ílímí dαkє cíkín lαвαrín..uвαngíjí чα k'αrα lαfíчα dα níѕαn kwαnα mαí αmfαní._ *#1 ♥ cwєєt lєєmαtєєч.* 😍
*~___________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
6⃣0⃣
*K* imanin kwanaki biyu kenan da zuwansu gida,yauma yana zaune cikin parlour a lokacin KHUBRA na saman jikinsa kamar kowane lokaci da idan kaje zaka tarar dasu a hakan.Cike da so da kulawa ya kalleta yana fad'in
"JODI yanzun idan aka ce kizo a kaiki makaranta shin kina so ko kuwa...?"
Kallonsa tayi tana murmushi ba tare data ce komaiba,saima hannunta datake ci gaba da wasa da shi a jikinsa,ganin bata da niyyan magana yasa ya rik'e hannunta yana kuma kallon ta,a hankali ta d'aga kanta ta kalleshi tana murmushi
"Shi ne kina ji ina miki magana bara ki amsaba...? kin san dai bana son haka ko...?"
K'ure shi tayi da ido tana nazarin fuskarsa,ganin yanda yayi yasa ta d'an gyara kwanciyanta tana fad'in
"Ni kam YAYANAH wani karatu ne zanyi yanzun...? ina ganin bani da wannan daman dan kam lokacina ya riga da ya wuce,wanda nake da shima na addini ya isarmin,amma kam nayi girma da zuwa makaranta yanzun.."
Shiru yayi yana nazarin maganarta,lallaima yarinyar nan idan ba shirme irin nata ba,har wane girma ne za ace tayi yanzun da karatun,shi kam tabbas yana da burin ganinta tayi karatu,shirun da taji yayi babu magana yasa ta sake d'agowa tana fad'in
"YAYANAH waima me ya kawo wannan maganar ne kam yanzun...?"
Idanunsu sark'e cikin na juna yake fad'in
"Wato kefa a ganinki nan kinyi girma da zuwa makaranta ko...?"
Kai ta d'aga masa alamar eh,kuma har cikin zuciyarta take nufin hakan,d'an murmushi tayi kafin ta furta
"To waima YAYANAH kawai sai na wani tafi na zauna haka nan gemai-gemai dani nace naje koyan karatu ko me..?"
Da sauri ya katseta ta hanyar fad'in
"Haba hajiya bafa wani girman da kikayi da karatu kuma da kike wannan maganar ma SHEHU JAHA ma cewa yayi acikin labarinsa *"GEMU BAYA HANA ILIMI"* sannan kinga kuma yanzun baki san wane irin y'ay'a Allah zai azurtamu da suba,shin bakya sha'awar ace kin bada naki gudunmawar ta b'angaren ginuwar iliminsu...?"
Shiru ta sake yi tana nazarin maganarsa,ita kad'ai a zuciyarta take fad'in
"Gaskiya dai kuma da haka,ko ba komai zanyi alfahari da kasancewar hakan idan har ya faru,to amma abun tambayan shin zan iya kuwa....?"
Tambayan daya tsaya mata a rai kenan,ta kasa samun wani ya bata amsa,ganin jikinta yayi sanyi da maganar kuma da yiwuwar ya canja mata ra'ayi yasa baiyi k'asa a guiwa ba ya shiga kwad'aitar da ita amfanin karatun,wanda a k'arshe ya samu nasaran amincewarta,dan BB cewa yayi bazai mata doleba idan har ta nuna bata so zai bita a sannu har saita amince,saboda a nasa tunanin cewa yayi
_"Duk abunda wani yake so wani yayi,idan har wanda ake so yayin ba shida sha'awar hakan to tabbas baza a samu nasara ba amma idan yana so nan ne zaka ga ya dage dan ganin ya aikata wannan abun kuma burinsa zaka tarar bai wuce na ganin yayi nasara ba"_
Murmushin samun nasara yayi yana shafa lallausan gashinta dake kwance yasha gyara
"Uhmmm! JODI kenan wato kenan fa wai gani kike kin girma ko...?"
"Haba mana YAYA kaimafa kasan na girma ai yanzun ai wani abun da zanyi shi da a yanzun kam ko da kud'i banyinsa,bare kuma da hankalina ai baranma soma aikatawa ba"
"Gaskiya kam amma ni banga wani girman da kika yiba har yanzun"
Mik'ewa tayi a jikinsa ta tsaya tana juya jikinta cikin salo tace
"Haba YAYANAH kallenifa kaga yanda na koma hakama ai wani cewa zaiyi na zama uwar mata.."
Dariya kalamanta suka sashi,sai dai kawai ya gintse yana kallonta yana murmushi,janyota yayi yana maidata muhallinta data tashi
"Lallai kam babynah ta girma,amma wannan girman ai daban wanda nake nufi daban"
"To wanne kake nufi kai...? ni dai nasan na girma yanzun"
"Eh haka ne nima nasan kin k'ara girma amma ni barin fad'a miki irin wanda nake nufi.."
Kallonsa taci gaba dayi tana sauraren jin me zai ce,hannunsa tajiyo k'asan cikinta yana shafa dai² mararta yake fad'in
"Da ace kin girma ina tunanin ni ne mutum na farko da zai tabbatar da haka,kuma da nan gurin ya tabbatarmin da hakan koba haka bane..?"
Sakin bakinta tayi tana kallonsa,lallaima YAYA'N nan nata ya rainata da yawa wato nufinsa har yanzun bata girmaba kenan yake nufi? Har sai ya ganta da ciki zai yarda lallai ne kuwa ta bashi mamaki kuma tabbas ta d'auki alk'awari saita nuna masa itan ta girma.
Bata sake bi takan maganarba tayi cilli da ita gefe,idanunta ta lumshe tana jin yadda yake shafa k'asan cikinta ita kam bata san wane irine YAYA'N nata ba duk wani abu da zaiyi ya jefa zuciyar mutum cikin soyayya ya iya,gani take da ada ne aka tambayeta yaya halinsa yake zata ce babu ruwansa shi en kamili ne kuma bashi da fitina,amma kam a yanzun cikin d'an tak'aitaccen lokaci ta gama fuskantarsa a nata tunanin tsaf zata zane littafi hard cover da halayensa,katse mata tunani yayi da fad'in
"JODI ki shi shiryafa cikin satin nan zaki fara zuwa makaranta"
Daga haka bai k'ara ko wasalin 'a' ba ya d'inke bakinsa ta hanyar rufe idanunsa danma kada ta dameshi da tambayoyi,hakan data ga yayi yasa ta yin murmushi cikin sanyin murya ta furta
"Allah ya kaimu,ubangiji kuma ya bamu sa'a..."
Amsawa yayi yana yadda yake tare da sakin mata kiss a porehead enta,murmushi tayi tana sake tightening hands enta dake jikinsa,kamar masu bacci haka palour'n yayi shiru baka jin maganar kowa cikinsu amma kuma a hakan hira suke da junansu,kiran daya shigo wayan KHUBRA ne yasa ta d'ago ta kalleshi,shi enma ita yake kallo mik'ewa tayi daga jikinsa inda bayan ta d'auka kiran ta shiga gaida MAMA,tambayan da MAMA tayi mata ne yasa ta kallonsa da sauri kuma ta d'auke kanta tana ci gaba da sauraron maman dake maimaita mata tambayan
"Doughter wai kam ina son tambayanki,ranan da kuka zo gida mai ya had'aki da ABBA ne kam har kika janyo ya miki fad'a...?"
Ajiyar zuciya tayi kafin cikin sanyi ta shiga bawa MAMA labari bata b'oye mata komaiba,a b'angaren MAMA kam taji dad'i sosai da yarinyar tata tayi wannan tunanin sai dai kuma dalilin da yasa ABBA ya mata fad'a shine tayi k'aranta ta fad'a masa wannan maganar kamata yayi dama a samu mutum wanda yake babba mai cikakken hankali sai ya nusar da shi cikin hikima da siyasa,kuma tabbas al'amura zasu tafi yadda ya kamata idan haka ta faru.
Nasiha tayi mata sosai akan ta kira shi ta bashi hak'uri sannan kuma kada ta sake yin maganar da kowa,haka dai har suka gama wayan ta ajiye,suka sake ci gaba da uzurin gabansu...
Kwanaki sun ci gaba da wucewa yayin da kowace rana da zata zo ta wuce take tafe da nasarori masu d'umbin yawa.A bangaren su KHUBRA da BB ma hakan ce ta kasance inda maganar makarantar ta ya kankama,makaranta mai kyau wacce kuma zata koyi karatun babu wasa ya kaita,kuma alhamdulillah! al'amura na kyau sosai,shi da kansa yake kaita school sannan idan an tashi shi yake zuwa ya d'aukota,ko da ace yana office ranar da zaran lokacin komawanta gida yayi zai tattara abunda yake yi ya tafi,sai ya maidata gida sannan zai koma office ya k'arasa aikin ranar,wata ranar kuwa idan ya dawo tofa bai komawa sai dai gobe.
Rayuwarta a makarantar wani lokacin idan ta kalli da yawan d'aliban sai taga akwai wanda ko a shekaru ya girme mata bare kuma girman jiki da wasu tsaf sai su d'auketa suyi ta gudu da ita ba tare da nuna gajiyaba,wani lokaci idan taga haka sai take tuna BB lokacin da yake mata maganar karatun,sai dai kaga tayi murmushi ita kad'ai.
Zaune take k'ark'ashin wata bishiya tana duba littafinta da suka gama lesson,tayi nisa a dubawa taji an mata sallama,d'agowa tayi dan ita a tarihin zuwanta makarantar babu da wacce suke k'awance,wata y'ar matashiyar budurwa ta gani tsaye tana mata murmushi,kyakykyawa da ita son kowa k'in wanda ya nema bai samuba,cikin dakewa ta amsa mata suka gaisa a mutunce,kallonta waccan d'ayar tayi tana fad'in
"Idan babu damuwa kuma ban takura mikiba shin zan iya zama...?"
'Dan murmushi KHUBRA tayi ganin itama da fara'a a fuskarta tayi maganar
"Babu komai bismillah! ki zauna"
"To ai kuwa na gode sosai da amsamin da kikayi.."
Matashiyar ta fad'a kafin cikin d'an yanayi na kasancewarsu sababbi a gurin ta furta
"Ni suna na AMINA UMAR FANA,nima sabuwar d'aliba ce a nan,to kuma ban san kowa ba a nan sai yau Allah yasa na ganki nayi kuma sha'awar miki magana ban sani ba ko zamu iya zama k'awaye.."
"Allah sarki ai nima da yake sabuwar zuwa ce shi yasa kika ga na zauna nan saboda babu wanda na sani,amm! ni kuma suna na KHADIJAT ABUBAKAR SA'AD amma a gida ana kirana da KHUBRA.."
Dukansu suka yi murmushi wa junansu,a hankali suka ci gaba da hira jefi-jefi kuma mafi yawanci duk akan karatunsu na ranar da suka yi ne,sosai tarayyarsu ta basu sha'awa ganin sun taimakawa juna da abunda d'aya ya gane d'aya bai ganeba,har lokacin tashinsu yayi,dai² lokacin aka zo d'aukan AMINA inda tayi ta yima KHUBRA magiyan tazo su tafi tare,hak'uri ta bata tana kuma fad'a mata itama yanzun za a zo d'aukanta,haka ta tafi wanda suna yin gaba BB yayi parking,glass en side ensa ya sauke yana kallonta,d'an murmushi tayi kafin ya fito ya bud'e mata ta shiga,sai da suka d'auki hanya ba tare da ya kalletaba yace
"Wane mota na gani ya tsaya inda kike....?"
Shiru ta masa babu amsa,shi kuma yaci gaba da fad'in
"Kina sane da cewa ke matar aure ce ko...? to ina so ki kiyaye kule-kule babu ruwanki da kowa coz bana son fitina kinji me nace...kiyi abunda ya kawoki babu ruwanki da shiga abunda ba a sakiba kinji...?"
Kanata ta d'aga alamar taji.
Kwanaki biyu tsakani take bashi labarin AMINA da suka had'u a school irin kirkinta da kuma yadda suke zaune da juna,yaji dad'in yadda ta fad'a masa abunda ya had'asu kuma shima ya tabbatar da cewa yes matarsa kam y'ar baiwa ce,yanayin yadda yake zama suna lesson kan abunda aka musu a makaranta duk bayan sallar maghreb yasan tabbas baya asara...
Tun bayan da sukayi magana da MAMA akan dalilin daya sa ya mata fad'a a wani zuwa da sukayi a can baya,MAMA bata b'oyewa ABBA'N su BB komaiba ta sanar masa cikin hikima da siyasa shi da ABBA'N KHALEEL suka sashi gaba da maganar,sosai suka kai ruwa rana da su wanda daga k'arshe kuma yaga rashin dacewar k'in amincewar da yayi tun farko,shi da kansa ya same su da maganar daga baya,cikin lokaci k'alilan aka gama magana,da taimakon MAMA da UMMI suka sata gaba itama kuma sai Allah ya taimaka basu wani sha wahala ba ta amince,an yanke d'aurin aure kad'ai za ayi sai tariya kuma babu wani taro da zasu yi bare mutane su fahimci wani abu game da sirrinsu,cikin lokaci kad'an aka d'aura auren ALHAJI ABUBAKAR SA'AD da amaryarsa HAJIYA ZUWAIRA akan sad'aki mafi inganci,anyi taro lafiya wanda y'ay'ane kad'ai suka halarta babu wata gayyata da suka yi daga iyayen sai su.
ASHNA kam lokacin bikin tana ta fama da laulayin ciki kuma sosai take shan wahala,babban dalili kenan daya sa FATAHIYYA komawa gidanta tana taimaka mata,palour suka rashe sunata hira tsakaninsu BB,KHALEEL,SADEEQ BIGGY,KHUBRA,ZUHRA dama ASHNA dake fama da kanta amma a haka ta dage itafa saita zo dan baza ayi babu itaba,FATAHIYYA kam d'akinta na gidan ta tsere dan cewa tayi bata iya zama gaban yayyen nata da ko wanne yake manne da matarsa ita a nata ganin kam wannan fitsarar da suke gwadawa bata iyawa.
Haka aka gama taro kowa ya d'auki matarsa yayi gaba,sai fatan samun zaman lafiya da sab'awar halaye.
Lokaci baya jira sai dai a jira shi kamar yadda wannan magana take haka fa abubuwa suke,bayan kimanin watanni biyar da auren ABBA'N KHUBRA,ASHNA ta haifi zankad'ed'en saurayi Yaro yaci sunan ABBA'N BIGGY wato MUHAMMAD suna kiransa da AL-MUSTAPHA,fad'in hidimar suna da suka sha a wannan family'n b'ata baki ne,yayin da a b'angaren ZUHRA da KHUBRA kuma shiru kake ji babu wacce tayi ko da b'atan wata,sam hakan bai wani dame suba dan ganin samu da rashi duka daga Allah suke lokaci kad'an yake azurta mara shi kuma hakan ma ba abun damuwa bane tunda duka yaushe akayi auren da zasu d'aga hankalinsu,a b'angaren karatunta kuwa ta dad'a maida hankali sosai k'awancen su da AMINA kuwa sai abunda yayi gaba,mutane da dama suna mamakinsu wanda bayan tsayin watannin da suka shud'e kowacce ta san y'ar uwarta nada aure,k'awance na tsakani da Allah suke duk inda kaga d'aya cikin makaranta to zaka ga d'aya,mazajensu sun san juna yanzun baya ga ziyara da sukan kaiwa junansu,sun dad'a dagewa akan harkar karatunsu abunda ya kaisu shi suke yi babu wasa,tsakaninsu da mutane gaisuwa ce suna kuma matuk'ar girmama junansu.
Yau tunda KHUBRA ta shigo skul take baza idanu taga inda aminiyar tata zata b'illo amma shiru kake ji,zaman makarantar duk ya isheta haka dai tayi manage har aka tashi,ko data koma gida bayan ta kirata a waya a kashe aka shaida mata,yinin ranar haka ta yini wani iri da ita wanda shi kansa BB sai da ya gane haka,ko da ya tambaya bata b'oye masa komaiba ta sanar masa,addu'ah ya nusar da ita tayi kan Allah yasa lafiya.
Washe gari tana shiga skul ko ta hangota har ta rigata zuwa,da saurinta ta k'arasa kusa da ita tana fad'in
"Haba CWEET SIS jiya kuma sai najiki shiru,kuma line wayanki a kashe haka naita fama da tunanin lafiya..."
"Allah sarki y'ar uwa ta gari wallahi ki bari ke dai,ai ban baki labari ba,kwana biyu ne sai a slow wollah duk dare da wani irin zazzab'i nake kwana,shi nefa ogana yace lallai sai munje asibiti to ni nake k'in zuwa sai nace masa makaranta,shi nefa jiya na tashi da shi aiko shi ne yace mu tafi asibiti dana ce makaranta baki ga yadda yamin fad'aba har yana cewa lafiya ita ke gaba da komai.."
"Kai amma naji dad'i daya miki haka banda abunki ai oga gaskiya ya fad'a..."
"Ke dai bari kawai ai kuwa munje hankalinsa ya kwanta.."
"To ya jikin hope komai normal...?"
"Uhmm! ke dai bari inafa normal.."
Da sauri KHUBRA ta kalleta tana fad'in
"Kamar yaya kenan?"
"Babu komaifa da wasa nake miki,da sauk'i sosai sai dai kun samu k'aruwa.."
Wani ihu KHUBRA tayi tana rik'eta
"Wayyoo! kice min ciwon kenan dama.....To Allah ya raba lafiya,ubangiji ya kawo mana su masu alkarka.."
Wata y'ar class ensu ce ta lek'o da yake ta iya gulma da munafurci a makarantar coz idan kana neman expert ta munafukai ka samota to ka gama,nan take fad'in
*"AUFANA* lafiya kuke ihu da wannan safiyar..?"
Wani kallon k'asan ido KHUBRA ta mata tana fad'in
"Lafiya k'alau ko kinji ance miki ba lau bane..?"
"Au too..."
Ta fad'a tana barin gurin,yadda AUFANA taga KHUBRA tayi da fuska yasa ta yin dariya tana fad'in
"Kai CWEET SIS ki d'an saki fuska mana irin wannan had'e rai haka kamar wata BOSS.."
Dariya dukansu sukayi AUFANA ta furta
"Allah sarki harna tuna da wata mak'ociyata mai suna *JIDDAH* da take bani labarin yadda mijinta yake a da kafin a musu aure,wallahi ko da take fad'amin ita da sister enta *MEINERH LITTLE* sun sha wahalarsa shi yasa suke ce masa *YAH BOSS* amma kuma kafin aurensu da bayan sunyi aure data fuskanci halinsa shi kenan wai shi raini ne baya so shi yasa ya dinga musu haka..
Kuma yanzun haka wallahi idan kika ga yadda suke zuba luv sai kinyi mamaki,ammafa suna da kirki wollah musamman suka had'u su uku da wata sister en tasu mai suna *HUBBEEY* gaskiya ranar duk da suka zo har bana son mu rabu saboda y'an chapter ne.."
"Allah sarki Allah ya bar musu zumuncinsu.."
Inji KHUBRA dake k'ok'arin bud'e littafi don tana son yin nazari kafin malamin ya shigo
"Ameen ya Allah...aiko wata rana Allah ya kawoki suna nan wallahi zaki ji dad'in kasancewa da su...yini d'aya idan kukayi da su wallahi ji za kiyi kamar kun shekara da su,Allah dai ya had'aku nasan zaki k'aru da zaman da za kiyi da su sosai.."
Murmushi kawai KHUBRA tayi lokacin da take mai da hankalinta kan littafinta,itama AUFANA nan ta d'auko nata tana fad'in
"Yawwa teacher KHUBRA yau kece malamata dan kinga jiya ban zoba saboda haka amin bayanin lesson en jiya,nasan dai kam YAYA'N ki bazai barki ba sai yayi miki karatu na musamman.."
Dariya suka sake yi duka,can kuma suka tsunduma cikin karatu...
Suna zaune suna karatunsu,wani malami ya taho zai wuce bayansa da wata d'aliba itanma dai baza ta wuce tsaransuba a shekaru kallon-kallo suka yi da ita,kafin suka ci gaba da abunda suke yi,har malamin ya gota su,sai kuma ya dawo yana tambayarsu wane class suke,fad'a masa suka yi ya juya ya kalli wannan d'alibar yana fad'in
"Yawwa to kinga ga y'an uwa nan kin samu class enku d'aya da su,ki rik'esu su zasu baki masauki tunda sun jima a nan..."
Godiya ta masa sannan ta musu sallama suka gaisa a mutunce ta nemi guri ta zauna kusa dasu tana sauraron yadda KHUBRA ke zubo bayani kamar wata lecturer.Saboda yadda take bayanin karatun ko malamin nasu yaji dole ne ya sara mata saboda wani abun ma bai bud'a musu bayaninsa kamar yadda take yiba yanzun,sai da suka gama sannan AUFANA ta kalli bak'uwar tasu tana fad'in
"Sannu dai y'ar uwa..."
A mutunce itama ta amsa mata tana murmushi,saboda itama ba dai arhar dariya ba..
AUFANA tace
"Ni suna na AMINA UMAR FANA amma zaki iya kirana da AUFANA saboda sauk'ak'awa ma'anarsa kuma AU na farkon AUFANA yana nufin AMINA UMAR,shi ne idan kika had'a shi da FANA zai baki cikakken sunan,ita kuma y'ar uwata sunanta KHADIJA ABUBAKAR SA'AD,amma ana kiranta da KHUBRA."
Murmushi ta sakeyi tana fad'in
"Na gode sosai da amsata da kukayi...ni kuma sunana *MARYAM HAROUN SULAIMAN* amma ana kirana da *JANNAT*..."
Hira suka d'an tab'a kafin suka koma class saboda ganin teacher na tahowa...
Watanni sun sake zuwa har sun shud'e inda har sukayi jarabawoyi da dama wanda yanzun gashi har sun sake samun ci gaba na changing class..
Wata rana suna zaune suna hira su uku kasancewar yanzun sun zama su uku kuma k'awancensu babu algus cikinsa,suna ta hira a wata ziyara da suka kaiwa AUFANA da cikinta ya soma tsufa...
AUFANA ce ta kalli KHUBRA da JANNAT tana fad'in
"Sisters ena niko zanso jin labarinku da dalilin daya sa bakuyi karatu da wuriba musamman yadda naga Allah ya rufa muku asiri gidajenku da family enku babu talaka cikinku.."
Kallonta sukayi duka suna murmushi saboda irin shak'uwar da sukayi da juna yasa suka san da wasu sirrika na junansu,KHUBRA ce tayi gyaran murya tana fad'in
"Ai kuwa dai kam ya kamata musan dalilin dayasa mu duka haka ta faru damu,amma kafin naku bari kuji nawa...."
Gyara zama sukayi dukansu,nan ta shiga basu labarin gwagwarmayar da tayi fama da shi a rayuwarta,sai dai kamar wancan lokacin data b'oyewa BABA ZUWAIRA farkon had'uwarsu haka suma ta b'oye musu da sa hannun MAMA a saceta,da kuma wasu abubuwa da suka faru a matsayinta na wacce bata son aga laifin iyaye da danginta..Bayan ta k'are su duka hawaye ne kwance a fuskokinsu suna jinjina labarin nata da tayiwa lak'abi da *Y'AR GARUWA..*
"Lallai kin sha wahala sister amma haka Allah ya kaddara mana rayuwarmu...Badan lokaci daya k'ure ba dana baku nawa labarin sark'ak'iyata wanda nayiwa lak'abi da *"BAMBANCIN AL'ADU"* (My upcoming novel) amma ku biyo ni nan gaba in sha Allah duk ranar da muka sake samun sukuni zan baku labarina..."
JANNAT ta fad'a,cike da alhini suka rabu ranar da tausayawa halin da KHUBRA ta shiga wanda har ya kaita ga fad'awa sana'ar *GARUWA*..............
*COMMENT FOR MORE PAGE'S.........* 💃💃💃💃💃
*~#TEAM KHUBRA-KHALEED.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE NOVEL'S GROUP@web.facebook.com
*©®2018*
*7/ɑմցմՏԵ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~___________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
6⃣1⃣
*R* ayuwa nata dad'a tsayi zaman takewa na dad'a kawo shak'uwa da sabo baya ga k'imar juna da mutuntawa babu abunda ke yawo cikin wannan zuri'a ta *MALAM ABDU MAI ALMAJIRAI* wato *KAKA* duk wanda ya rab'esu ko to tabbas rabuwarsu bata zuwa face sun cika shi da d'umbin alkhairai.
A b'angaren zaman aure zuwa mu'amala ko duka yaran nasu kawunansu a had'e yake,ko da surukin gidan wato SADEEQ BIGGY ba lallai ne mutum ya ganeshi a matsayin suruki ba sai dai d'a saboda yadda su ABBA suka d'aukeshi,hankali da nutsuwa ko a gurinsa duk wanda ya sanshi a baya idan ya kalleshi a yanzun ba zai iya shaida shi ba saboda nutsuwa da yayi,shi da kanshi wani lokacin idan ya zauna yana tuna rayuwarsa ta baya sai dai kaga yana zubda hawaye,yasan ba kowa ya sashi yin irin wannan rayuwar ba face kishiyar mahaifiya,ba dan yana da ilimin addini dana zamani ba da yanzun kam yasan rayuwarsa ta gama wulak'anta,dalili kenan da idan ya tuna sai yayi k'walla.
Yaronsu ko AL'MUSTAPHA yanzun duk wanda ya kalle shi sai yayi mamakin girmansa saboda kulawa da ya samu cikin d'an lokaci yayi k'ato da shi.
Soyayyar KHALEEL da ZUHRA a wannan lokaci kuwa kamar zasu had'iye juna musamman da idan suna hiran rayuwarsu na baya,baya ga kasancewar a bayan ba wani luv sukayi ba a matsayinsu na b'oyayyun masoya ga BB da KHUBRA,idan kaga suna exchanging words na soyayya to tabbata a waya ne ko suna chat da junansu,yanzun kuma da suka samu dama sai abun nasu ya k'etare sanin mai sani.
Sosai KHUBRA ta maida hankali gurin karatu duk da dai kunsan rayuwar makaranta yau dad'i gobe akasin haka,amma a haka aka ci gaba da jalalla rayuwar da dad'i ko babu.
Cikin shekara guda da rabi da aurensu ta dad'a girma na ban mamaki duk da a gurin shi gogan har yau idan hira ya kawo su kan maganar girma yakan fad'a mata bata girma ba,wannan maganafa ta BB tana hasala KHUBRA a duk lokacin da yayi ta,shiganta makaranta da had'uwa da sababbin k'awayen nata yasa ta k'ara wayewa da gogewa,ta wani b'angaren kam takan yiwa Allah godiya bisa ga ni'imomi da yayi mata.
Yau tun da asubah da suka idar da sallah suka sake komawa cikin duvet,bacci mai dad'in gaske yayi gaba da su mak'ale da juna,sai wajen 10am sannan suka tashi cike da nishad'in zasu kasance tare a weekend en,su da kansu sun san zasu huta daga zurga-zurgan gurin aiki da skul.Sunyi wanka tare sannan suka had'a break fast kamar ko wane weekend suna cikin parlour zaune k'asa kan rug ya mik'e k'afafunsa,ita kuma tayi pillow da laps nasa,hiransu kamar kowane lokaci zuwa can maganar girma ya sake shigowa,cikin dariya da zolaya BB ya kalleta yana fad'in
"Babu wani nan nifa har yanzun baki girma ba a gurina..."
Kallonsa tayi k'asa-k'asa tana tab'e baki ba tare da ta kula shiba,shi kuma yaci gaba da tsokanarta
"Bayan har yau komai ni nake miki ke ko gwadawa baki tab'a yi ai ko in dai haka ne babu ranar da zaki girma ko JODI na.....?"
Kallonsa kawai ta sake yi tare da yin k'wafa yadda take rains mata hankali a ranta take fad'in
"Yau kam zan baka mamaki YAYANAH....Amma barin ga iya naka gudun ruwan.."
A hankali ta mik'e tana tafiya ta nufi hanyan bed room ensu,bata yi magana ba sai da taje dai² zata shige yace
"Baby ina zaki je ne..Babu ko neman rakiya...?"
"Ina dawowa YAYANAH yanzun abu zan d'auko na dawo..."
Ta fad'a tana sake juyawa,bai bata amsa ba kawai dai ya d'aga mata kai alamar babu damuwa ita kuma ta shige.Yana nan zaune cikin parlour yaga ta d'an jima bata dawo ba,kamar zai bita kuma ya fasa tunawa da ta ce masa abu zata d'auko,ci gaba yayi da abunda yake a computer da yake akwai wasu detail's da yake son shigarwa,k'amshinta ne ya fara isowa cikin parlour'n bai d'agoba ya ci gaba da abunda yake yi har ta bayyana a cikin parlour'n,a hankali kuma ya kai kansa kanta ai ji yayi kamar numfashinsa zai d'auke saboda irin shigan da tayi kuma dama irin kayan duk ranar data sa tofa tabbas basa k'arewa ta dad'i,Nicker's ne jikinta bak'i dad'an rubutu na lemon a gefe ansa *STAR* sai d'an duwatsu dake gefen rubutun wanda aka k'awata shi da su,rigan jikinta kuma colour en lemon kasancewarta half kuma ba mai wani babban hannuba,yasa duk k'irjinta yake titi,sai bak'in takalmi na snickers data sa plat cover shoe,yadda ta tsara kayan a jikinta sun matuk'ar amsarta fiye da tunanin mai tunani,tana tsaye ta coge k'afa kamar mai shirin fita pick nick,gaba d'aya ta maida shi kamar wani idol ya daskare gurin,cikin takun ta na isa tana yi tana kad'a ilahirin jikinta har ta iso inda yake,k'afarta d'aya ta d'ora kan center table dake gabansa ya d'ora computer en cikin salonta tafurta
"JAAN....ya kaga wannan kwaliyyan yayi kyau...?"
"Sosaima kuwa yayi 100%...."
Kanta ta d'an karkatar gefe sannan ta ce
"Wait a minute....."
Komawa ta sake yi cikin y'an mintuna ta sake dawowa da wani 3quarter jeas da body hug,shima da k'yar ya iya saita kansa ya amsa mata,haka ta sashi gaba ta shiga ta canja ta dawo,shi kuma yana fad'in tayi,last rigan ta d'auko wani transparerent riga multi colour,sai data gama dariyan mugunta tukun sannan ta b'alle bra en jikinta a haka tasa rigan shi kad'ai with out tasa pant ko bra,sakin gashinta tayi ya sauka har bayanta,sannan ta janyo wani hill en takalmi tasa,red lipstick ta shafa bakin tan nan kamar me saboda kyau duk da bata wani yi applying heavy make-up ba tayi kyau sosai,kaloj ta zizirawa idanunta,juyi tayi gaban mirror en duk jikinta babu abunda mutum bai hangowa,murmushi ta sakinma kanta kafin ta tasamma hanyan fita parlour gadan-gadan.
Computer ya rufe idanunsa a kan hanya dan tuni ya bar aikin da yake yi,fitowanta yasa numfashinsa tafiya yajin aikin dole,coz baiyi tunanin ganinta a haka ba,babu abunda bai hangowa daga nan,tsayin rigan gaba d'ayansa kan cinyanta suka tsaya da k'yar ya had'iye yahun bakinsa idanunsa kam ko k'iftasu ya gagara yi,har ta iso gabansa,maimakon ta tsaya kamar sauran sai kawai jinta yayi saman cinyoyinsa hannunta d'aya ta zagaye wuyansa da shi,d'ayan kuma tana wasa da shi kan face masa kamar mai zana wani abu cikin muryan shagwab'a kamar za tayi kuka tace
"JAA....AA....N.... anya nayi kyau kuwa...?"
Bakinsa ya bud'e kalmomin na hard'ewa da kyar ya iya furta
"Fi....fi....f...i....y....e....ye... da ko wane lokaci ma.."
Y'ar dariya tayi mai sauti sannan ta shiga mutsu-mutsu kan laps nasa tana fad'in
"Yawwa YAYANAH yanzun naji batu,kaga duk kayan dana sa wannan yafi kwantamin saboda amsan daka bani ya tabbatar min da haka barin je na cire to..."
Tana shirin mik'ewa ya dawo da ita yana sakin mata wani kallo mai cike da sak'onni da dama,ko ba a fad'a mata ba ta fuskanci me yake nufi,amma ina sai ta nuna kamar bata gane ba ta marairaice masa tana fad'in
"JAAN zan je nefa na cire kayan jikina kaga kada muyi bak'i su ganni haka..."
Banda aikin had'iye yahu da kyar babu abunda yake cikin kunnenta ya furta
"Noo! JODI muje zan cire miki da kaina..."
Dariyanta ta k'unshe saboda yadda yayi maganar yana marairaice fuska kamar wani maraya sai langab'e kai yake cikin salon tsokana tace
"A'a JAAN zan iya cirewa na dawo yanzun kaga na tabbatar wannan sunfi kyau duk cikin kayan..."
Kallonta yayi da idanunsa da suka soma narkewa,ba tare da yayi magana ba yayi cupping fuskarta da hannayensa,yana kallon cikin idonta ya had'e bakinsu guri d'aya sun jima suna aikama da juna sak'onni da suka mance a inda suke,kafin yayi ciki da ita d'auke a hannunsa,tun kafin su k'arasa saman bed al'amura har sun dad'a tsanani,cike da nishad'i bayan samun nutsuwa suka sake sabon wanka,d'aure da towel iya cinyanta tana kan stool ta kalle shi tana murmushin mugunta tace
"Wai kam YAYANAH d'azunfa kace wai kai baka yarda na girma ba ko...?"
"Haba mana JODI sau nawa kike so na tabbatar miki da hakan,na fad'a miki babu abunda kika iya sai dai kullum ayi miki,duk ranar da kika yi k'ok'arin yimin abu d'aya kacal cikin abunda nake miki to ranar zan yarda kin girma kinga bama sai kin haihu ba kamar yadda mutane ke fad'a..."
Ya k'arasa yana mata winking coz yasan ba abunda zata iya yi masa,y'ar dariya tayi tana kallonsa tace
"Haka dai kace ko....?"
"Yes! ai na jima ina fad'a kuma an kasa yi ba,so kawai ki yarda babu rana kwana kusa da zaki girma sai kin....."
Bai k'arasa ba yaga ta k'araso gabansa ware towel en dake jikinta tayi had'e da wurga masa a kan fuska,a hankali ya d'auke shi yana dariya had'e da mata kallon lallai yarinya baki da wayo.Nasa ta bud'e had'e da shigewa ta rik'eshi ta baya coz bata so ya fad'i,passionately take kissing ensa kafin ta durk'usa a gabansa kan guiwoyinta ta cikin towel en,hannu tasa tana zare towel data bari jikinsa,kallonta yake yana dariya coz bai san me hakan ke nufi ba,zai yi magana ta hanashi saboda aikin data d'auko yafi k'arfin yayi magana,mamaki kam tun a nan ta gama bashi,yana nan tsaye ita kuma tana fama da service nasa,sai data gama lokacin BB babu bakin magana sai kallonta yake a duniya gani yake babu abunda za tayi ko cewa akayi za tayi zai k'aryata,yana kallo ta d'ago ta kalleshi ta saki mugun murmushi sannan ta kwanta jikinsa,a hankli taci gaba da haurawa har ta dawo dai² face nasa,wani sabon murmushi ta sake kafin ta sake had'e bakinsu tana zuba masa romantic kisses,yau kam gaba d'aya ta gama birki tashi in dai a wannan fagen ne,tsaf KHUBRA ta karb'e ragamar komai daga hannunsa,after komai ya lafa tana kwance samansa still,sai da suka gama maida numfashi suka koma toilet har lokacin kuma cike yake da mamakinta,ko da suka koma toilet again k'in bari tayi yayi wanka da kansa Lamar kowane lokaci,ko bayan da suka gama shirya juna suka dawo parlour tana kwance kan cinyansa har lokacin kuma ya kasa mata magana,ba tare da ta kalleshi ba ta furta
"YAYANAH me yake damunka ne naji kayi shiru...."
Fuskarsa dake d'auke da murmushin farin ciki ya kalleta yana shafa kanta cikin murya k'asa-k'asa ya furta
"JODI yau kam kin gama bani mamaki har kinsa nama kasa magana..."
Murmushin itama tayi tana fad'in
"Dama ance ai 'Dan hakin daka raina wata rana shi zai tsokanema ido...."
"Ai kam masu iya magana sunyi gaskiya dan nima yau gashi kin tsokanemin ido...wai dama JODI haka kike....? ni har ina rainaki kan babu abun da za ki iya."
Dariya sosai tayi masa idanunta na fidda hawaye saboda yanayin yanda yayi maganar dole ne ayi dariya,ta mirgino tana kallonsa a ruf da ciki maranta taji yayi wani irin k'ullewa da sauri ta saki wani marayan ihu tana juyawa
"Arrrrhhggg...! wayyo JAAN.."
Rik'eta yayi da sauri ita kuma ta dafe mararta da sauri hannunsa ya d'ora kan nata yana fad'in
"Me ya faru dake...?"
Mararta take nuna masa sai runtse ido take shi kuma ya shiga mata massaging gurin yana mata sannu a hankali har taji gurin ya saki,bacci ne ya soma d'aukanta saboda dad'in abunda yake mata da taji zuwa can ta farka a d'an firgice tana mik'ewa,kamata yayi da sauri ya dawo da ita jikinsa
"JAAN ka sake ni zanyi girkifa kaga na manta har na fara bacci kuma baka tasheniba..."
"A'a JODI ina sane na k'i tashinki koma kiyi baccinki zan kula da komai.."
Marairaicewa tayi tana fad'in
"Please JAAN...ka barni nayi da kaina kagafa ba wani abu ke damuna ba,behind ma kuma na samu sauk'i bafa komai kawai ciwo ne lokaci d'aya kuma ya tafi naji sauk'i sosai.."
Ganin ta dage yasa shi sakinta da sauri tayi hanyan kitchen shima ya bita a baya,tare suka fara shirya kayan da zasuyi amfani gurin girkin.Bayan kamar mintuna k'amshin girkin ya fara tasowa saboda tafasa daya fara yi,fuskarta ta fara yamutsawa kamar mai jin wani abu na daban,k'amshin ne yaci gaba da tasowa sosai ta yadda ba iya kitchen en ya tsaya ba har cikin parlour,da gudu ta fice a kichen en yanayin data fita yasa shi binta da sauri yana kiranta amma ina batama san yana yiba tun data shiga toilet en taketa faman kwara amai,jiyota yayi tana ta faman kakari a toilet da sauri ya shiga ya rik'eta yana faman jera mata sannu,sai da ta gama ya wanke mata bakinta ya sake rik'ota suka kamo hanyan dawowa parlour still k'amshin data sake shak'a yasa ta kwace jikinta da sauri ta juya tana sake yunk'urin amai sai dai wannan karon babu abunda ya fito daga cikinta face zallan kakarin da take,da k'yar ta dawo dai² d'aukanta yayi yana jera mata sannu saboda jiri dake neman kayar da ita tun a toilet,hanyan palour still ya kamo cikin wahalalliyan murya ta furta
"YAYANAH kabarni nan banson jinwancan k'amshin..."
'Dan dakatawa yayi yana kallon yadda take magana,komawa yayi ya d'orata saman bed
"JAAN sanyi nake ji please ka rufeni..."
Tsigan jikinta duk ya tashi cike da tausayawa kamar zai mata kuka yayi saurin rufeta,sannan ya fice kitchen ya shiga yayi disconnecting duk wani abu na wuta dake ciki,komawa yayi gurinta ya tarar da ta shige ciki har kanta cikin tausayi yake kallonta shi kam bai tab'a ganin tayi irin wannan rashin lafiyan ba tun da suka yi aure idan aka d'auke ranar aurensu daya sameta kwance babu lafiya,da kyar ya iya samun nutsuwan kiran KHALEEL bayan ya masa bayanin komai cikin damuwa shi kuma ya nuna masa DR en family'n ya kamata ya kira,sai lokacin tunanin haka ya dawo masa yana kashewa ko ya kirashi,cikin mintuna k'alilan ya shaida masa zai iso.
Lokacin da DR ya iso ya kira shi da kansa ya shiga dashi har inda take,babu b'ata lokaci yayi mata gwaje-gwajen da zai yi sannan ya tafi akan zai dawo nan bada jimawaba da sakamako...
After some few hour's DR ya dawo da sakamako,jikin BB har rawa yake dan yaji meke damun JODI en nasa,cike da annashuwa a fuskar DR shi kuma daya kasa hak'uri har sauri yake ya tambaya sai dai DR ya katse shi da fad'in
"Congratulations sir...."
A ransa yake fad'in
"Kaji bahago ina cikin tashin hankali kana min wani murna....toma akan wace uwar yake min murnan ne...?"
Maganar DR ta dawo dashi hayyacinsa inda yake fad'in
"Madam na d'auke da juna biyu na tsawon sati bakwai....Fatan Allah ya raba lafiya...sai dai kuma akwai abubuwa da za a kiyaye saboda ba wani k'wari yayi ba kuma idan ba a kiyaye ba to za a ita rasa abunda me cikintan,haka kuma yanayin abunda zata dinga ci dole ne ta dinga cin duk wani abu da zai gina musu jiki ita da baby'n...."
Bayani sosai yayi masa sannan y zana masa prescriptions da za a nema yanzun wanda zasu taimaka mata..Bayan nan kuma ya masa sallama godiya BB yayi masa sosai,har bakin motansa ya rakashi sai da yaga tafiyansa sannan ya dawo da d'an gudu dan ya duba JODI en nasa,musamman yau da yake jinsa cikin k'ololuwar farin ciki wanda bazai iya misalta shiba................
*COMMENT FOR MORE PAGE'S..........* 💃💃💃💃💃💃
*~#TEAM KHUBRA-KHALEED.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE NOVEL'S GROUP@web.facebook.com
*©®2018*
*8/ɑմցմՏԵ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~___________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
6⃣2⃣
*S* higa'nsa d'akin yana ta sauri dan ganin ya isketa,har lokacin tana a yadda ya barta,sai dai kam har lokacin idanunta a rufe suke ta takure guri d'aya saboda sanyin da take ji,yadda ya taddata sai ya tuno ranarta ta farko a gidan,kamar haka ya taddata ta k'udundune jikinta guri d'aya,still yayi yana k'are mata kallo,nan ya shiga tuno yadda sukayi a ranar,tunawansa babu b'ata lokaci ya raba jikinsa da kayan dake sanye a jikin nasa,a hankali ya haura saman bed en,ta cikin duvet en ya zare mata kayan jikinta had'e da rungumeta tsam cikin jikinsa,cikin kunnenta yake mata magana lokacin daya ga tana motsi yasan ta tashi ne.
"JODI ina ke miki ciwo......? me kuma kike so...?"
Yana magana yana shafa k'asan cikinta dai² maranta,sosai take enjoying abunda yake mata duk da kuwa ba wani k'arfi a jikintan,kanta ta girgiza masa alaman babu komai..
"Kin tabbata..?"
Nanma nodding kanta tayi,ajiyar zuciya yayi yana fad'in
"Oyyaahh! sanarmin mene za kici to kinji nasa a kawo miki..."
Cikin wahalalliyar murya ta furta
"Nifa na k'oshi..."
"A'aa JODI kada muyi haka dake,na tabbata yanzun babu komai cikinki duk kin haras...look maza sanarmin..."
"To ai dai na fad'a maka ban son komai,ni bacci zanyi kawai.."
"Haba mana JODI kingafa cikinki yadda ya koma da ganin alamu kinsan kema babu komai,ko kuwa kina son barin baby'nmu da yunwa ne...?"
Juyowa tayi da k'yar tana kallonsa a fili kuma ta maimaita kalmar
"Baby'nmu kuma JAAN a ina kenan....?"
'Dan murmushinsa mai tsada yayi mata yana shafa mararta har lokacin ya furta
"A nan mana JODI....don't u know u are pregnant....?"
Wani murmushi ne ya sub'uce mata duk da irin halin da take ciki hakan bai hana murnarta bayyana ba,da sauri kuma ta maida fuskarta yadda take cikin magana irinta mai jinya ta kalleshi tana fad'in
"Yama akayi ka sani bayan ni banga alaman haka ba...?"
"Hahhhh! JODI kinji haushi ne dana fara sani....?"
"Nop! YAYANAH kawai na kasa yarda ne ace ina da ciki yanzun.."
Kallonta kawai yayi yana ci gaba da murmusawa abunsa shi kam ya tabbatar kuma da sannu itama zata tabbatar
"Baby DR nefa ya sanarmin yanzun,ko baki san ya zoba ne...?"
"Yanzu kuma..? yana ina DR...?"
"Ya tafi..amma kam abunda ya fad'a kenan ga can sakamakon binciken daya kawo..."
Ya mata showing inda resul en yake kan mirror,d'an kallon takardar kawai tayi,a ranta ko fata take Allah yasa haka ne dan ita babu abunda ta sani,hatta da zuwan DR en zuwa k'arin ruwan daya mata da allurai wanda BB ya cire mata time en daya k'are saboda haka ne yasa bata san da zuwan DR ba.
Hannunta ta d'ora kan nasa suka ci gaba da aikin shafa gurin,idanunsa ya lumshe yana jin ranar yau a matsayin rana wacce tazo masa da al-khairai wanda ba zai tab'a mantawa ba,cikin kunnenta yaketa sauke mata sinka-sinka,container's,trailer's,basket kai da duk ma wani abu da idan kuka zuba bare d'aukeba dad'ad'an kalamai gameda sa mata albarka yake,ita kanta duk da halin da take ciki tana jin kalamansa har k'asan zuciyarta,jin kalamansa take kamar tafi kowace mace dace a duniyar da take rayuwa.
Cikin awanni mafiya k'aranci har ta ji jikinta ya koma mata normal zazzab'in ya sauka,amma kuma har lokacin suna mak'ale da juna,kiran sallah ne ya tashe su daga hiran da suke,bayan yayi alwala ya fita masallaci,inda ya barta za tayi sallah nan cikin d'akin,bayan ta idar da salla'n tayi addu'o'inta,mik'ewa tayi ta d'auke pray mat en had'e da hijab en jikinta,bakin mirror en ta tsaya tana ware farar takardar da BB ya mata nuni d'azun,a hankali ta fara bin rubutun tana karantawa,farin ciki kam mara misaltuwa tayi shi,kan stool en ta hau hannunta rik'e da paper tana ta faman sakin smiling,hannunta ta mayar kan mararta tana feeling babynta dake kwance gurin,idanunta ta lumshe tana jan numfashi a hankali,k'arin hannu taji kan nata da sauri ta bud'e idonta duk da tasan ko waye wanda zai yi hakan,kallonsa tayi tana sake sakin murmushi,shima murmushin yayi mata sannan ya d'auketa suka fice a d'akin,suna tafe yana mata magana coz shi kam har yanzun bai hak'ura da maganar abinciba
"JODI kink'i fad'in abunda zaki ci ko...? Kin san bana son zama da yunwa bare kuma ke...Kinga JODI maza sanarmin kinji...."
Sai da tayi dariya sannan ta furta
"Ni fa babu abunda zanci..."
"A'a bana son jin wannan maganar daga bakinki idan kika ci gaba da fad'a zanyi fushi fa.."
Ya fad'a yana b'ata fuska
"A'a! a'a!! dan Allah kada kayi kaji YAYANAH cake kad'ai zanci da fruit juice..."
Y'ar dariya yayi yana fad'in
"Haba JODI wannan ai ba abinci bane kayan kwad'ayi ne..."
"Ni Allah in ba shiba baran ci komaiba.."
Cike da shagwab'a kamar za tayi kuka.
"Ok! ok! an gama JODI..Kar kiyi kuka kinji..bari mu tafi mu siyo an fasa aiken kowa ma,kinga daga nan sai mu wuce gida ko...?"
"Ehhh! kuwa dama ina son zuwa kawai ban fad'a maka bane..."
Hancinta ya lakace yana fad'in
"Ina fatan dai Babynah ba yawo zai sa mamansa ta koya ba..."
"Haba YAYANAH kawai dan nace ina son zuwa...?"
"Ehh! mana.....ammm! JODI kin san wani abu ma kuwa..?"
Kallonsa tayi lokacin da yake sauketa cikin palour,da sauri ya koma ciki ba tare daya fad'i abunda yayi niyyaba,k'aton hijab ya d'auko mata har k'asa da plat en takalmi,da kansa yasa mata,ita kuma sai dariya take ganin yau wani sabon abu daya b'illo da shi,ita da bata fita da hijab sai in zata skul,yau kuma shi ne ya d'auko mata saboda neman magana irin tasa.
"YAYANAH hijab fa ka samin.."
Bata k'arasa ba ya katseta
"Ehh! nafi sonsa yanzun gara ki saba saboda koda cikin ya fito bana son kina fita da vail wasu suna kallemin ke,kinsan a lokacin duk abunda zaki sa zaina showing jikinki sosai.."
Y'ar dariya tayi kafin ya kama hannunta suka fice cike da nishad'i,bama kamar BB da yau jinsa yake kamar sabon ango.
Sai da suka biya wani eatery suka siya cake da juice da take so,sannan suka d'auki hanyan gidan nasu suna tafe suna hira har suka k'arasa.
HAJIYA ZUWAIRA zaune parlour dan kam yanzun ta jima da tashi daga matsayin da take da,shigowarsu KHUBRA ta haye kan jikinta tana kwanciya tana fad'in
"UMMANAH nayi missing enki wollah kwana biyu kamar na shekara ban gankiba.."
"Ke ni dad'ina dake kenan baki da aiki sai na son jiki kamar kyanwa,har yanzu baki san kin girma ba kekam.."
BB dake gefe yayi dariya yana fad'in
"A'a kam UMMA'NMU ai mun girma yanzun..."
Kallonsa tayi tana fad'in
"Inafa girma anan kana kallon babu abunda ya chanja a halin matarka na shegen son jiki..Nikam wannan ko haihuwa kikayi ina ga saikin koyawa y'ay'an son jiki dubafa ba dama taga mutum zaune yanzun ta d'afe mutum kamar ta samu katifa..."
Dariya dukansu sukayi nan ta fiddo cake enta tana ci tana korawa da juice enta har taci da d'an dama,tana gamawa lokacin HAJIYA ZUWAIRA ta mik'e tayi kitchen,tashi KHUBRA tayi ta koma kusa da BB dake saman 3seater cuistion,ta kwanta kan cinyansa tana fad'in
"YAYANAH yaushe zamu gidan CWEETY..?"
'Dan b'ata fuska yayi yana kallon cikin idonta
"Wayyooo! YAYANAH mene ya faru naga ka canja fuska lokaci d'aya...Ko baka son kaini na ganta...?"
Fuskarsa ya yamutsa kafin kamar wanda akayiwa dole yace
"No...!"
"To mene ne kasan nifa har ga Allah banso naga canji irin wannan a tare da kai,gani nake kamar na maka laifi mai girma..Please dan Allah ka fad'a min kaji.."
Ta k'are maganar tata kamar za tayi kuka
"Ehhemm! laifinma aikinyi kam.."
Cikin d'an rikicewa ta mik'e daga jikinsa tana kallonsa lokacin har idonta ya gama cika taf da hawaye coz bata san laifin me tayi ba,ita kuma a rayuwarta abunda ta tsani ji kenan yace tayi masa laifi cikin rashin saninta,ranar ji za tayi rayuwarta ta mata k'unci
"Dan Allah YAYANAH kaji ka sanar dani ko dan na gyara..Please kaji HAYATEEY...!"
Banda dariya babu abunda BB yake k'unshewa saboda yadda tayi daf hawayenta suke da zubowa,shi kuma sai wainata yake,tunawa yayi da maganar DR inda yake shaida masa ba'a son mace mai ciki ta dinga shiga damuwa ko sa abu a ranta,hakan zai janyo mata matsala..
Da sauri ya saki fuskarsa yana kamota,kwantar da kanta yayi saman sholder ensa ta dama cikin rarrashi yake fad'in
"Sorry JODI ba wani abu mai tsanani bane da zaki tada hankalinki kinji ko...Kwantar da hankalinki kinji.."
"Ni dai ka fad'amin dan Allah..."
Dai² lokacin hawayen dake idonta suka sakko,d'uminsu ya jiyo saman sholder ensa da sauri ya d'agota yana zare ido
"JODI mene haka kuma..kin sanfa bana son haka ko..shi ne amma kike yi..."
Ya fad'a yana dad'a maida fuskarsa alamun da tasan babu wasa cikin maganar da tayi,kece masa tayi da kuka cikin kukan take fad'in
"To ba kaine kace na maka laifiba kuma na tambaya kak'i fad'amin...."
Kansa ya dafe yana fad'in
"Ya salaam...!"
_Ni da nake gefe nace "Kujimin d'an malfar uba bayan shi ya janyo take kukan kuma yake d'aure fuska,kai wannan koi mai murd'ad'd'en hali..ka ce an maka laifi kuma kak'i fad'a...bahago kawai.."_ 😣
Fuskarta ya rik'e da hannayensa,bakinsa ya kai dai² inda hawayen ke bi,nan ya shiga d'auke mata su,dalili kenan daya sa kukanta tsayawa tana kallonsa,murmushi ya mata bayan ya gama d'auke mata hawayen,idonta na dama ya sumbata sannan na hagu,bakinta ya nufo da sauri ta kulle bakinta tana raba ido.Kallon yadda tayi yasa shi b'ata fuska,kamar za tayi kuka ta furta
"YAYANAH bafa gida muke ba.."
Sai lokacin ya juya ya kalli inda suke,kunya ce ta kama shi ganin ya kusa aikata ba dai²ba a gidan surukai,amma ganin babu kowa yasa shi bata fake kan bakinta,wanda bata yi tsammanin samunsa a lokacin ba.
"Ni ka fad'amin abunda kake b'oyewa.."
Ta fad'a tana turo d'an bakinta gaba,bakin ya kalla yana murmushin mugunta
"Ok! amma ki daina min wannan turo bakin kinsan duk lokacin da kikayi ina kasa controlling kaina..."
Murmushine ya sub'uce mata nan ya sata gaba yana tsokana
*"MAI KUKA TANA DARIYA....AI MATA 'DAN KWA'DON DADDAWA...!*
*MAI KUKA TANA DARIYA....AI MATA 'DAN KWA'DON DADDAWA...!!"*
Dariya ta fashe da shi sosai,shi kuma nan ya shagala da kallonta yana kuma ci gaba da tsokanarta kamar wani k'aramin yaro..
UMMA'NSU ce ta fito da plate a hannu,zama tayi tana fad'in idan kin gama shagwab'ar to ga abinci can na jiranku a teburi.
Kallon plate en data ajiye gabanta tayi nan ko ta hango d'an wake da manja,ai tuni yahunta ya fara gudu,cikin sauri ta sauka kan jikinsa,gaban plate en ta isa tana zuwa kuwa ta sure shi babu ko magana ta zauna nan k'asa ta soma cin abunta har dasu lumshe ido,kallonta kawai sukeyi shi kam BB dad'i yaji sosai daya ga tana cin abincin,ita ko UMMA ZUWAIRA sakin bakinta tayi tana kallon ikon Allah,can kuma ta saki murmushi saboda wani tunani da tayi,a fili ta furta
"To to to..! ince ko dai mun samu k'aruwane take wannan zalamar...abunda nasan ba halinta bane..?"
Daroya BB yayi yana d'aga mata kai dan shi ta kalla tayi maganar,wani murmushin ta sake yi tana fad'in
"To! ko da naji...Allah ya inganta,Allah kuma ya raba lafiya.."
Fuskarta da matsanancin farin ciki na jin zasu samu jika kwana kusa,kallonsu suka maida kanta suna ta hira tsakaninsu,amma ina sam KHUBRA bata sanma abunda suke yiba har ta kammala sannan ta shiga tsotse yatsunta d'aya bayan d'aya,kallonta sukayi suna murmushi
"Haba KHUBRA zafa ki cire hannunki kan tsotsan da kike musu.."
'Dagowa tayi ta kallesu had'e da yin murmushi,sob'on data gani cikin cup ta d'auka ta tultulawa tumbinta,kan tsaban dad'in da yayi mata har lumshe ido take,da kyar ta mik'e tayi hanyan kitchen hannunta d'auke da plate data yashe abincin ciki,ko data fito BB ta nufa tana zuwa ko tayi pillow da cinyansa,take ko bacci mai d'ankaren dad'i ya kwasheta.
Sai after asr ta farka ta ganta kwance kan pillow na cuistion en,d'an waigawa tayi tana kallon cikin parlour'n,dai² lokacin ya shigo a hankali ta sauke k'afafunta k'asa ta mik'e tana tafiya inda yake,warm hug ta bashi tana dad'a lumshe idanu
"Baccin ne bai ishekiba ne...?"
Kanta ta d'aga masa,ok muje to kiyi sallah saimu tafi gida.."
Hannunta ya kama sukayi ciki,inda ya taimaka mata tayi alwala,a gabansa tayi salla'nta tana addu'ah shima ya d'aga nasa hannun,da yake su kad'ai ne cikin d'akin bayan ta k'are ya zare mata hijab en yana fad'in
"Kawo nan muje ki huta saimu tafi anjima ko..?"
Kai ta d'aga masa tana yin gaba a parlour suka dad'a rashewa ita kuma UMMA ta lek'o jin kamar magana
"A'a ashe ka dawo..."
"Ehh amma ban jimaba ma da shigowa ba."
"Ayyahh! sannu da dawowa.."
Amsawa yayi,ita kuma ta maida kallonta kan KHUBRA tana fad'in
"KHUBRATU zaki ci wani abu ne yanzun....?"
"A'a na k'oshi sai dai ko anjima.."
"To shi kenan.."
Kitchen ta koma taci gaba da aikin gabanta,kallonsa tayi nan ta tuna da abincin da aka ce suci d'azun,ita kam tun bayan data ci nata bata saniba ko shi en yaci,saurin kallonsa tayi tana fad'in
"JAAN kaci abincin kuwa...?"
Kai ya kad'a mata alamar a'a,da fuskarsa da ya maidata kamar wani yaro,da sauri ta sauke k'afafunta k'asa har tana neman fad'owa,saurin rik'eta yayi yana fad'in
"Easy JODI.....Ina zuwa kike sauri haka,bakya tsoron ki fad'i ne kam..ko kuwa kin manta yanzun bake d'aya bace...?"
Marairaicewa tayi kamar za tayi kuka
"Abinci fa zan kawo maka..."
Bakinta ya rufe da hannunsa yana d'an murmushi
"No kada ki damu naci abinci d'azun,UMMA ta bani kina bacci..."
Sai lokacin tayi sanyayyar ajiyar zuciya,sannan ta koma ta kwanta,can ta fara magana
"JAAN inafa binka bashi.."
"Uhhummm! ina jinki na mene bashin...?"
"Maganar d'azu..."
Ta bashi amsa a tak'aice
"Ohhh! ni kingama har na manta,amma ke da yake kin damu da ji kin kasa mantawa.."
Batayi maganaba sai wasa da take da yatsun hannunsa dake cikin nata,dai² kunnenta ya kai bakinsa yana fad'in
"Kin san laifin da kika min..?"
Har cikin ranta ta girgiza masa kai
"Kina kirana da suna biyu,so na kasa bambancewa wanne nawa wanne ne kuma ba nawa ba."
Kallonsa tayi shi kuma ya mata winking
"Duka mana...ai duk naka ne.."
Cike da shagwab'a yake fad'in
"Ni dai a'a gaskiya sai dai a zab'i d'aya...Kuma bana son wannan YAYA'N da ake fad'a.."
Y'ar dariya tayi tana fad'in
"As u wish yallab'ai..."
Ido ya fiddo yana fad'in
"Kinga ni ba yanzun ma kin sake k'aramin wani...ko..?"
Tana murmushi take fad'in
"To MY JAAN an daina daga yau..."
Dariya sukayi ta sake maida kanta ta kwantar tana hamma.."
A tak'aice dai basu suka tafiba sai wajejen 9pm shima ABBA ne ya korasu.
Suna tafe a mota ta zame ta kwantar da kanta kan cinyarsa,while shi kuma yana driving,bacci ne ya d'aukenta cikin alamu na magagin bacci can hannunta ta motsa duk a cikin bacci aiko nan ya tafi wata jiha ta daban,da sauri BB ya take burki,Allah ma yaso su titin babu yawan cinkoson abun hawa,gefe ya gangara sannan ya d'an dubata,gani yayi batama san abunda yake faruwa ba,d'an murmushi yayi ya gyara mata kwanciyar,sannan ya mik'i hanyan da zata maida su gida,har bedroom ya kaita,sai bayan ya ajiyeta ta bud'e ido
"Ina zaka tafi JAAN...?"
'Dan waiwayowa yayi ya kalleta
"No JODI zanyi wankane na dawo..."
"Shi ne kuma ni bara ka yiminba...?"
"Sorry naga kina bacci ni kuma kin san bana son abunda zai tada ki a baccin.."
"To ai na tashi yanzun,kasan baran iya bacci haka nan ba.."
"To tsaya na cire miki kayan ko..?"
Kai ta d'aga masa alamar toh,a hankali ya tako ya dawo gabanta,sannan ya cire mata,towel ya d'aura mata sannan ya d'auketa sukayi toilet.
Sun d'an jima ciki kafin suka fito,yadda suka fito yasa nace 'Ikon Allah wai nasara da gwado' kunsan me na gani....?
Towel ne guda d'aya sanye jikinsu KHUBRA ta rik'esa ta gaba,k'afafunta akan nasa,hannayensa zagaye da ita ta gaba,yana tafiya dasu a haka sunata faman shek'a dariya.Shi ya fara zama saman stool en sannan ita dake kan cinyansa suna kallon mirror
"Sauka na miki shafa ko..?"
"Tabbb! wollahi baran sauka ba,salon haka kawai kasa y'an group en *SMASHER & HUBBEEY 1&2,SHDG NOVELLA,SHDG COMMENT'S ONLY,LEEMA FAN'S GROUP,SAWWAMA FA'NS GROUP,BARKIN'DO & MUHIBBAT* 😜su k'aremin kallo,Allah babu inda zani,naga dai kaika cillamin nawa cikin ruwa,sannan kuma kace na sauka Allah saika samin kayana zan sauka.."
Dariya yayi mata yana mata gwalo ta cikin madubin
"Yarinya ai sun riga da sun ganki tun a toilet lokacin ina miki wanka..."
Kukan shagwab'a tasa masa tana bugun k'irjinsa
"Allah ni babu wanda ya ganni.."
"Sorry haka ne babu wanda ya ganki yi shiru to kada kiyi kuka..."
Bakinta ta murgud'a masa ta cikin mirror,tana kallonsa ya d'an cije lower lip nasa,kansa ya d'an sauke k'asa dai² kunnenta ya furta
"Idan ba tsoroba idan mun kwanta ki sake min haka ki gani..."
Kallonsa tayi ta masa fari da ido had'e da sake murgud'a masa bakin
"Yanzuma na sake me zaka iya yi...?"
"Haahh! yarinya ai tsoro kike ji shi yasa kikayi a nan,amma ki bari mu gama kinji..."
Murmushin mugunta ya mata ta cikin madubin,da k'yar suka gama abunda suke sannan ya d'auko musu nighty ensu,wani guntun singlet yasa mata mai d'an fad'i tsayinta duka bai kai kan knee's entaba,sannan ya d'auketa zuwa saman bed,ko daya direta fita yayi ya kashe duk kayan wutan dake gidan had'e da kullewa,bayan nan ya dawo ya kashe light en d'akin,kusa da ita ya kwanta ita kuma tayi saurin matsowa jikinsa..
"Wa na kama...?"
Ya fad'a lokacin data gama shigewa jikinsa yana mata cakul-kuli,dariya ta shiga kyal-kyalawa tana fad'in
"N....ii...Ka....kama..!"
"Ohh! na zata zaki ce ba keba ai....oyaaa! muyi bacci to kinji..?"
Kanta ta kad'a tana goge hawayen daya ziraro mata gefen idonta.Fake ya sakar mata a porehead daga haka bacci mai cike da nutsuwa ya d'auketa..............
*Aradu kwana biyu kunamin abunda ranku ke so,to nima zan muku abunda nake so,BB ya auri KHUBRA wato comment's kuma kun daina ko.....? Masuyi kad'an ne,so zan rage posting kullum nd yawan typing enma haka,zan maidasa 1 READ MORE kamar na cweet hulbateey...*
*~#TEAM KHUBRA-KHALEED.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE NOVEL'S GROUP@web.facebook.com
*©®2018*
*9/ɑմցմՏԵ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~___________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
6⃣3⃣
*H* ar tayi bacci shi kam idonsa a bud'e yake ya rasa me yasa ya kasa bacci a daren,farin cikinsa sam ya kasa b'oyuwa,yanda al'amuran suka faru yake ta tunawa,bayan d'umbin farin cikin data sa shi a safiyar,ta sake bashi wani bayan d'an tak'aitaccen lokaci wanda yafi kowanne zame masa abun farin ciki,shi ne yadda a ranar ta bayyanar masa a matsayin tana d'auke da juna biyu na y'ay'ansa,shi kam a yau bai san me zai mata wanda zai biyata d'umbin farin cikin data sashi ba,a ganinsa komai yayi mata bai biyata ba kan farin cikin data haifar masa,dad'a rungumeta yayi a jikinsa yana jin kamar ya maidata jikinsa su koma abu d'aya,sai da ya bari baccinta yayi nisa sosai sannan ya mik'e cikin yanayin da ya san bazai tashe ta ba,pillow yasa mata a inda ya tashi sannan ya rufe mata jikinta,fake ya sakar mata a porehead sannan ya shige toilet yana murmushi.
Wudu'u ya d'aura sannan ya fito had'e da saka jallabiyya ya shimfid'a pray mat ya hau kai had'e da kabbara,sallah ya shiga jerowa duk sujuda sai ya jima cikinta yana musu addu'a ta neman zaman lafiya,kariya da kwanciyar hankali,tare da neman zuri'a d'ayyiba.
Kusan k'arfe 2am sannan ya idar yayi addu'o'i a sauk'ak'e saboda yadda ya fara jin bacci,a nan ya bar pray mat en ya haura kusa da ita yana dad'a mannata da jikinsa,cikin lokaci k'alilan bacci mai nauyi game da dad'i ya d'aukeshi...
Haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya a yayinda ko wace rana take zuwa musu yadda suke fata da burin takasance,cike da soyayyar junansu suke kasancewa a ko wane weekends coz sauran ranaku ba wani isashshen lokaci gare su ba,amma idan aka ce weekend ya zo to nan zaka iske su tare komai kuma nasu tare suke aiwatar da shi,yadda suke gudanar da soyayyarsu da rayuwarsu a sauk'ak'e babu wanda zai gansu yaji basu birge shiba hasalima sai kaga mutum na kwad'ayin kwaikwayonsu...
Cikinta ya dad'a girma inda yanzun yake da wata takwas da y'an kwanaki,zuwa yanzun ya zamana babu inda take zuwa tana zaune gida,shikansa BB wannan dalilin yasa shi d'aukan hutu gurin aikin nasu duk kuwa da dama company ne nasu ABBA suke aiki dukansu ciki,so wannan yasa bai wani samu matsala da hakan ba inda ya damk'a ragamar hannun KHALEEL,sai dai wani lokaci yakan lek'a ya ga yadda al'amura ke wakana.
Suna zaune cikin parlour a k'asa kan rug,daga ita sai singlet mai d'an fad'i na shan iska kasancewar yadda cikin ya maidata gaba d'aya ta k'ara bud'ewa,k'afafunta a mik'e duk sun kumbura sosai babu mai kallonta yace cikin watansa takwas saboda mugun girman da yayi,shi kuma MR KHALEED sai aikin matsa mata su yake,jingina bayanta tayi jikin cuistion hannunta dafe da plate na fruit da aka yanka tana ci da fork,wani ta soko jikin fork en tana dariya tayi saitin bakinsa da shi,sai data bari ya bud'e bakinsa saita janye hannunta ta nufi bakinta da abunta tana masa dariya,kai ya kad'a mata alamar zai rama yana maida face nasa alamun yayi fushi.
"Sorry JAAN....!"
Ta fad'a tana kallonsa,d'auke kansa yayi yana ci gaba da b'ata fuska,wani ta d'auko tana sake kawowa dai² bakinsa,kamar bazai bud'e ba kuma sai ya bud'e,sake janyewa tayi tana masa dariya.
"Kingafa kina d'aukan hak'k'ina JODI idan ba bani za kiyiba kibar abinki nima idan na tashi babu abunda zaisa na sammiki nawa.."
"Haba mana JAAN kasan fa ni taka ce,kuma dai nasan zaka sammin ko...?"
Tayi maganar cike da shagwab'a tana kashe masa ido d'aya
"Haba yarinya babu wani wayo da zakimin kijima na fad'a miki.."
"Haba mana...nicefa...."
Still fuskarsa tana yadda take,yana kuma ci gaba da matsa mata k'afafuntan,janye k'afar tayi ta matsa kusa dashi kallonta kawai ya tsaya yi ganin ta janye k'afan nata kuma ta matso kusa da shi,kan cinyansa ta hau tana zagaye wuyansa da hannunta d'aya,while d'ayan kuma still da fork a cikinsa,grapes ta chaka ta kaishi bakinta,sai data gama melting ensa sannan ta kalli cikin eyeballs ensa tana kuma nufan bakinsa da nata,tun kafin ta k'arasa ya fahimci nufinta,wani murmushi ya sake mata yana dad'a rik'eta sosai a jikinsa,nasa ya bud'e ita kuma ta shiga zuba masa ruwan narkakken grapes en,licking mouth nata ya shiga yi,daga haka wasa ya canja salo,nan suka lula cikin wata duniyar ta daban,sun manta da duniyar da suke da kuma duk wani abu dake zagaye da su,basa iya tuna kowa da komai sai junansu,burinsu a ko da yaushe su faranta ran junansu.
Bayan komai ya wuce sunyi wanka yana shiryata,wayansa tayi k'ara,saurin maida rigan yayi kan bed ya nufi inda phone en ke yashe,MAMA ya gani tana kiran da sauri ko ya d'auka yana karata a kunnensa cikin sallama,amsa masa tayi sannan ta furta
"SON kana jina ko.....?"
"Ehh! MAMA wani abu ya faru ne..?"
"A'a SON ina so ne dai duk abunda kake yanzun ka kawomin BABY gida akwai wani abu dake shirin faruwa..."
'Dan kallo inda take yayi yaga shi take kallo,d'an murmushi yayi mata yana ajiye wayan kan mirror,inda take ya nufa yana zuwa yad'auka rigan ya sa mata,sannan ya nufi cikin closet ya d'auko mata Arabian gown wanda yake da d'an sakewa bazai kuma takurata ba,da mamaki take kallonsa coz ta jima bata fita ba
"JAAN ina zamu kuma naga kana shirin samin kaya bayan kasan banson zafi...?"
"No JODI zamu gida ne,ban san mene yake shirin faruwa ba,MAMA tace muje yanzun.."
Kai kawai ta girgiza masa alamun ta gane,yana gama shiryata shima ya shirya,d'aukanta yayi ya nufi hanyan fita da ita,hannayenta zagaye da wuyansa har ya sanyata a mota,k'ofar ya bari a bud'e sannan ya koma ya kulle gidan,cikin lokaci k'ankani suka iso,shigowa yayi parlour yana d'auke da ita,nan suka tarar da gaba d'aya mutanen gidan a babban palour,sauketa yayi suna bin cikin parlour en da kallo ganin yadda suma ake binsu da kallo,hannunta ya rik'e suka k'arasa ciki suka zauna,sannan suka gaida iyayen nasu dake zaune,suka kuma gaisa da sauran y'an uwan nasu,suka kuma shiga sahun jiran jin me ke faruwa akayi irin wannan taron.
SADEEQ BIGGY aka sa ya bud'e taron da Addu'a sannan ABBA ya fara magana yana kallon KHUBRA dake zaune ta mik'e k'afafunta
"Al-hamdulillah da Allah ya nuna mana rana da kowannenmu yake cike da farin ciki da kwanciyar hankali,muna k'ara godiya ga Allah daya had'a kawunanmu muke zaune da junanmu lafiya ba tare da wata fitina ta b'illo mana ba,sai dai a yau ina son ku bani aron hankalinku domin a kwai wani al'amari daya ke faruwa wanda cikinku babu wanda ya sani sai mu da muke zaune lokacin da abun ya faru haka kuma kuma wasunku sun sani sai dai da jimawa,amma idan kun saurari bayanin da za ayi yanzun zaku ita tunawa...
Da farko dai ke KHUBRA shin zaki iya shaida wad'annan mutanen dake zaune gefe...?"
ABBA ta kalla da yake mata nuni da gefe da hannunsa,hannun tabi da kallo zuwa inda yake mata nuni nan ko idanunta sukayi arba da wasu yank'wanannun tsofi mata su biyu d'aya jikinta duk wasu irin k'uraje sun feso mata a jiki saboda uwar daud'a data lillub'esu,kallon rashin sani tayi musu sannan ta kalli ABBA da sauran mutanen cikin parlour'n ta ce
"A'a ABBA ban shaida suba."
Matan dake zune gefe sai kuka suke kamar wani nasu ya rasu suka kalleta suna sake b'arkewa da kuka mai cin zuciya kowa su yake kallo,da k'yar suka kalleta d'aya tana fad'in
"KHUBRA yanzun baki shaidamu ba? tabbas babu makawa mu mun san masu laifi ne a gareki kuma dama babu yadda za ayi ki shaida mu,idan har baki gafarta mana ba to tabbas baza mu tab'a gamuwa da rahama ba cikin rayuwar da zamuyi dama wadda mukayi a baya saboda munyi rayuwa ne cikin k'unci.."
K'uresu tayi da ido duk dan ta gane su,amma hakan ya gagara ta kasa bambance kamanninsu.
"Ni ce fa MA'U KHUBRA...Dana kawo ki aikatau,wanda tun bayan wanni biyar dana kawoki ban sake waiwayoki b..."
Ido KHUBRA ta zare tana kallonta da mamaki shimfid'e kan fuskarta na yadda ta kasa game kammaninta,ko tantama babu d'ayar kam LADIYO ce dan kamarsu d'aya su biyun fun can da.
Daga nan MA'U ta kwashe komai daya faru tun bayan data bar gidan,yadda tayi mata asiri kuma cikin hukuncin Allah kasancewar bata da hak'k'i Allah ya kareta,sannan ta d'ora da yadda asirin yayi tasiri akanta ita,maza suka dinga binta itama tana binsu kamar dai yadda igiyar ruwa ke kad'awa gefe zuwa gefe,kaf ta kwashe komai har ciwon da take d'auke da shi a halin yanzun,wanda tun bayyanar cutar a jikinta ta koma gidanta,kuma har lokacin bata bar halinta na biye-biyen maza ba,a haka ne wata rana suna tsaka da aikata masha'arsu a soron gidan nata kawai sai ga wata mak'ociyarsu nan ta shigo da niyyar tambayarta kasancewarta bak'uwa a unguwar,ganin da tayi musu mak'ale da juna yasa ta fasa k'ara dalili kenan daya sa mutanen unguwa taruwa kasancewar da yamma ne kuma ranar babu aiki,da yake an san ba aure gareta ba nan ko aka shiga jibgarsu babu ji bare gani ta k'arasa da fad'in
"Da kyar na samu na gudu,daga nan ban zame ko ina ba sai nayi tasha na tafi garin KASHIN DILA gurin YAYA,a lokacin dana je na sameta cikin mawuyacin hali wanda ko abincin da zata cima gagararta yake,babu gurin kwana babu suturar kirki har sai tayi bara take samun d'an abun da zata sawa cikinta,a k'ofar gida cikin rumfa na isketa gidan kuma a kulle,ko dana tambayeta sai take shaidamin cewa MALAM BUBA ya sake ta,kuma gidanma ya sallama shi ga mai gari tare da sauran kadarorin da iyayensa suka bar masa,yayi kuma sallama da mutanen garin da sunan bazai sake dawowaba.Sannan ta sanarmin da KHUBRA kin koma tare da wasu mutane da suka shaidawa MALAM BUBA a hannunsu kike kuma dai da alamun suna da alak'a tsakanin su da shi MALAM en Lamar yadda muka samu labari yanzun,to bayan nan kuma muka ci gaba da zama a garin wahalar da muke ciki tasa muka baro can muka dawo nan gidan dana zauna a nan kano,bayan mun dawo nan mun d'auki lokaci muna zuwa wannan unguwar muna neman gidan dana kawo ki aiki,sai dai Allah bai nufa zan gane gidanba sai yau da muka shigo muna neman taimakon abunda zamu ci saboda duk wata dukiya da nake da ita ta k'are yanzun,sai Allah yasa muka ga matar dana kawoki hannunta.Shi ne ta shaida mana kinyi aure tun shekaru biyu da aula wuce,min nemi son ganinki ne a gurinta shine race my jira zata kira mijinki ya kawo mata ke.
Kunji abunda ya faru tun daga rabuwarmu har kawo yanzun ...
Parlour'n kowa yayi shiru mamaki game da d'umbin al'ajabi na hali irin na wad'annan mutane da suke zaune duk ya d'aure musu kai,KHUBRA kam zuwa lokacin hawaye sun gama wanke mata fuska banda godiya ga Allah daya kareta ya kuma tsareta daga fad'awa tarko ba tare da an samu damar keta mata mutuncin taba take yi,mik'ewa BB yayi ya kamata suka bar gurin duk maganar da suke yi na ta yafe musu kan cutar da ita da suka yi,bai bari ta tsaya gurinba dan shima da kansa haushinsu yake ji,kuma yayi niyyar d'aukar mataki a kansu sai dai ya tuna wata magana da suka tab'ayi da yake ce mata sai ya d'auki mataki kansu,amsar data bashi a lokacin itace ta sake dawo masa,dalili kenan daya sashi janyeta a gurin coz yana son rarrashinta...
'Dakinsa na da ya shige da ita,d'akin ta kalla da hawaye har lokacin a cikin idonta,yana nan kamar yadda yake da,key ya murzawa k'ofan danma kada wani ya samu damar shigowa,janyota yayi ta shige cikin jikinsa,yana d'an jijjigata har ya samu tayi shiru sai ajiyar zuciya da take,bakin bed ya zauna ya d'orata akan cinyansa yana goge mata fuska,cikin kunnenta yake hura mata iska har sai da ta koma hayyacinta,mik'ar da ita ya sake yi tsaye tayi tunanin fita za suyi,da sauri ta rik'e shi tana sake sakin sabon kuka
"JAAN please kada ka mai dani gurinsu dan Allah baran iya zama guri d'aya da suba...kaji..?"
"Ok ok..! yi shiru babu inda zamu tunda baki so kinji ko..Zo nan na cire miki rigan kisha iska.."
Matsawa tayi jikinsa,sunkuyawa yayi a gabanta ya shiga bud'e mab'allan rigan jikinta,singlet ne a jikinta ta ciki sai nicker's,rungumeta yayi ya nufi saman bed da ita,kanta ya d'ora kan cinyansa ita kuma ta kwanta a gefenta na dama fuskarta na kallon fuskarsa,sai ajiyan zuciya take saukewa,gashinta ya shiga shafawa yana mata magan-ganu masu dad'i da kwantar da hankali,saboda kasancewarta mai d'auke da juna biyu daya tasamma tsufa ba'a son kasancewarta cikin b'acin rai,kafin wani lokaci sai gata ta ware har suna wasanni cike da nishad'i..
Can ko a parlour bayan barin su gurin MA'U da LADIYO sake b'arkewa suka yi da kuka ganin KHUBRA ta bar gurin ba tare da ta yafe musuba,kan irin cutarwar da suka mata,kuka suke suna k'arawa akan a kirata su nemi gafararta,shiru mutanen dake parlour en su kayi sai sauraren su suke sai da suka yi kukan son ransu wannan suka yi shiru, suna kuma dad's tonawa Kansu aspirin abubuwan da suka yita aikatawa Wanda aka sani dama Wanda ba a saniba,cike da tausyawa halin da suka jefa KHUBRA a ciki da mahaifiyarta data jima da rasuwa saboda girman kaidi da suka dinga shiryawa mutanen cikin parlour en ke kallonsu,da kyar UMMI ta bud'e baki tayi magana wanda yasa kowa ya maida kallonsa kanta,hatta kuwa da su masu koke-koken neman gafara,kiran KHUBRA da BB tasa ayi don kawo k'arshen komai,ko da d'an aike KHALEEL yaje ya tarar da k'ofa a kulle baiyi knocking ba ya dawo dan shima akan dole yaje saboda dai kawai bazai iya cewa UMMI a'a bane yasa yaje,sanar mata yayi da k'ofar a kulle take,sashi tayi ya koma yayi knocking ai ko kamar yadda ta umarta haka yayi,bud'ewa BB yayi sukayi ido hud'u da KHALEEL a nan ya coge ya kare k'ofar ba tare daya bawa KHALEEL damar gano cikin d'akinba ya furta
"Ya akayi ne...?"
"UMMI tana kiranku yanzun..."
Badon yaso ba ya koma ciki yana b'ata rai,shi kam babu yadda za ayima ya tasheta tana bacci,saboda haka ya fice had'e da kulle k'ofar,ganinsa shi kad'ai yasa suka kalle shi UMMI tana tambayan KHUBRA
"UMMI tayi bacci ne..."
Amsa daya bata kenan fuska a murtuke,aikuwa MA'U ta hau sheshshek'ar kuka,BB wani kallo ya jefeta dashi daya sata shiga nutsuwarta tana sunkuyar da kai k'asa,babu yadda basu yiba akan a tasota ta yafe musu,shi kuma ya kafe akan wallahi babu abunda zaisa ya tasheta,kawai suje an yafe musu saboda ubangiji yana son masu yafiya kuma itama zata yafe musu in sha Allah su tafi kawai,k'in tafiya suka yi ganin sun matsa kan sai sun nema yafiyarta su da ita kuwa yace musu idan suka takura to wallahi zai janye yafiyar da aka musu.
Babu b'ata lokaci suka fice suna kuka had'e da waiwayen gidan dan sun san shi kenan kuma suda sake ganin KHUBRA bare kuma MALAM BUBA daya koma AL-HAJI ABUBAKAR,wanda yake ji da dukiya a yanzun,ta inda cikin shekaru biyu da watanni ya bawa wasu miliyoyi baya.
*WAIWAYE....*
Tun bayan lokacin da MALAM BUBA ya kori LADIYO daga cikin gidansa,yayi sallama da mutanen garin,nan ya saida duka wata kadara daya mallaka ya tattaro kan dukiyarsa,wacce a k'arshe bayan dawowarsa ya damk'ata a hannun ALHAJI SAFWAN,inda shi kuma ya kawo shawara suka had'a kai su uku suka sake bud'e wani company da yanzun yake k'ark'ashin jagorancin KHALEED da KHALEEL.
_Wannan kenan....._
Bayan tafiyarsu aka koma maida labarin yadda al'amura suka faru a baya,kowa sai jimami yake kan yadda abubuwan suka faru.Bayan komai ya lafa su ABBA suka koma bakin aikinsu a d'ayan company ensu.
Su kuma sauran yaran aka barsu nan suna ci gaba da hiran haihuwan KHUBRA nan da wani watan suna kuma ci gaba da tsara irin shagulgulan da zasu yi idan ta haihun............
*ONE MONTH LEAP...*
KHUBRA ce kwance saman gado na majinyata masu haihuwa sai juya kai take gefe wasu nurse's na turawa daga kusa da kanta kuma BB ne yana ta faman shafa mata kai yana jera mata sannu cike da tashin hankali,har aka shiga da ita labour room en,sannan aka kulle yana waje bakin d'akin sai safa da marwa yake.
Tun yana kallon mintuna da suke shud'ewa kuma yana kallon k'ofar d'akin da aka shiga da ita,har hour guda yayi ba tare da an fito da itaba,daga hour d'aya aka tafi da rabi,sannan biyu,uku,hud'u,ganin abun bana k'are bane kuma hankalinsa na kanta gaba d'aya nutsuwa tayi masa k'aura,burinsa bai wuce sanin halin da take cikiba.
Wata nurse ce ta lek'o,jin an bud'e k'ofar yasa shi nufar gurin da sauri.
"Kaine JAAN ko waye nema ohooo...?"
Bai bata amsaba ya janyeta gefe had'e da shigewa,kallo ta bishi da shi ganin ya shige babu magana,bakin gadon ya nufa ganin cikin awanni hud'u da shigowarsu babu wani abu daya canja,duk ta gama galabaita,hannunta ya rik'o cikin nasa,idanunsa lokaci guda ganin halin da take ciki har sun gama sauyawa zuwa jaa,su kuma nurse's en sai faman damunta suke kan tayi nishi amma ina babu k'arfin yin hakan a tare da ita,gaba d'ayama sun gama bashi haushi kan tsayawa da sukayi suna b'ata lokaci tun d'azun kuma har lokacin babu sauyin da aka samu tun da suka shigo da ita,hannun long sleeve ensa ya nad'e cikin b'acin rai yace su bashi guri tunda basu san aikin suba,cikin ya shiga d'an dannawa a hankali kamar dai yadda akema masu ciki idan zasu haihu,yana kuma fad'a mata kalmomin da zasu bata k'warin guiwa,matsawa ya sake yi dai² bakinta ya sanya nashi ganin yadda take kwance tana sauke numfashi da kyar,iska ya shiga hura mata hannunsa d'aya na kan cikin yana ci gaba da daddanawa a hankali.
Cikin y'an mintuna da shigowarsa ta samu d'an k'warin jiki,nishi mai k'arfi yayi escafe a tare da ita,wanda ya bawa kan jaririnta damar fara fitowa,da sauri nurse's en suka matso,da taimakon Allah sannan da nasu taimakon suka janyo jaririn,cikin y'an mintuna ta sake sabon yunk'urin wani nak'udan take wani sabon jaririn ya sake kunno kai,a tak'aice dai sai da aka zaro jarirai uku daga jikin KHUBRA.
Ko ta kan jariran bai biba,in da matarsa take ya nufa yana jera mata sannu da Santa mata albarka,itako sai maida numfashi take da kyar Dan da ganinta ko ba a fad'a ba kasan ta sha wahala,duk jikinta yayi sweat en wahala,mouth to mouth ya shiga sake mata ko dan ta samu daidaituwar numfashi.............
*COMMENT FOR MORE PAGE'S.......* 💃💃💃💃💃
*~#TEAM KHUBRA-KHALEED.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE NOVEL'S GROUP@web.facebook.com
*©®2018*
*10/ɑմցմՏԵ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~___________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
6⃣4⃣
*SECOND TO THE LAST.*
*BIGGY* kuwa tun bayan daya samu aiki a revenue office,wato ofision tattara haraji,ya daina wani aiki da yake a baya,wanda ba k'aramin mamakinsa yaransa suka yiba na ganin chanji lokaci d'aya a tare da shi,da farko sun ci gaba da zama cikin gidan nasa sai dai kuma daga baya lokacin da zai yi aure kuma har lokacin akwai wasu halayya nasu da basu dainaba,dalili kenan daya sashi yanke shawaran rabuwa da su dan kada wata rana su janyo masa bala'in daya fi k'arfinsa.
Wata rana bayan ya zaunar dasu a parlour nan ya shiga yi musu nasiha yana janyo musu ayoyi da hadisai cikin abunda Allah ya sanar da shi na daga ilimi,jin ruwan ayoyin daya ke janyowa wanda suke tsoratarwa zuwa ga masu aikata halaye irin nasu dama wasunsu da kuma narkon azaba da aka tanada ga mai aikin yasa su kuka,basu tashi a gurinba sai da sukayi masa alk'awarin in sha Allah suma sun daina,yayi farin ciki sosai da hakan ya faru,nan yake shaida musu zaiyi aure nan bada jimawaba suka masa fatan sanyawar alkhairi,tun daga nan ya sallamesu da kud'ad'en da yasan idan har sun rabu cikin su babu wanda zuciyarsa zata kawo masa d'aukan abun wani ko kuma su koma irin waccan rayuwar.Tun da suka yi sallama da shi a lokacin ya musu fatan alkhairi shi kenan basu sake had'uwa ba,shima bayan sun bar gidan ya shiga parking kayansa,dillallai ya samu sukayi cinikin gidan da kayan gidan gaba d'aya,take ko ya sai da shi da komai daga shi sai kayan jikinsa ya fito daga gidan,ko bayan ya bar gidan ya d'an kwana biyu a hotel sannan daga baya ya samu wasu dillallan suka samo masa gida a wani unguwan daban,nan BIGGY ya koma da rayuwarsa,wanda kuma nan ne aka kai masa amaryarsa wato ASHNA wacce a yanzun take MAMA ga d'ansu MUHAMMAD AL'MUSTAPHA....
《《》》
*INA LABARIN BOKA...??*
BOKA kuwa tun bayan da LADIYO ta masa wannan gani a ranar da MALAM BUBA yayi musu mugun kamu bai sake dawowa gurinta ba dalilin da yasa kuwa hakan ta faru shi ne,a lokacin bayan ya bar gidan LADIYO daga nan wani gari ya wuce wanda a wannan garin akwai wani malami mahaddacin al-k'ur'ani,tun da Allah yasa wannan bawan Allah yayi aure da matarsa d'aya wacce take fitinanniya tun tana yarinya kamar su LADIYO,tun bayan aurensu data ga ba irin wanda za tayiwa duk abunda ranta ke so bane yasa ta shiga bin malamai y'an tsubbu da bokaye duk akan tana neman abunda zata malakke shi,sai daifa hak'anta yak'i cimma ruwa sakamakon shi wannan bawan Allah ako da yaushe zaka tarar da shi cikin alwala kuma yana tilawar al-k'ur'ani,a biye-biyenta ne suka had'u da BOKAN su LADIYO,wanda a ranar da MALAM BUBA ya gansu bayan ya bar nan bai zame ko ina ba sai gidan wannan malami daya fita sallar asubah kasancewarsa limamin garin nasu,kamar ko wane lokaci bayan an idar ya zauna tilawa nan a k'ofar gidan nasa yana cikin karatu,almajiransa da sauran datijjan garin masu sha'awar neman karatu suna zaune nan gaba gare shi a haka har gari yayi haske sosai..
Can ko a gidan MALAM lokacin matarsa na tsaka da bacci gari har yayi haske tana ta faman bacci bata saniba bare ta tashi ta gaida mahalicci,zuwan bokan shi ya tasheta wanda tana yin arba da shi tayi dariya kasancewar dama sun saba,haka suka shiga aikin gabansu kamar kowane lokaci.K'arfi,mu'ujiza da girman kalmomin da ake karantawa k'ofar gida suka fara tasiri cikin gidan malamin wanda suka yi sanadiyyar daya janyo jikin boka cikin lokaci k'ank'ani ya fara hayak'i,faruwar hakan ke da wuya matar malam ta daka tsalle had'e da ingije shi daga kanta ta fice a guje daga d'akin,a tsakar gida ta tsaya tana raba ido tunawa da irin hukuncin da za a mata a garin idan har aka san abun da ta aikata yasa ta fashewa da kuka dan kam muddin malam ya sani tofa lallai ne jefeta za ayi da ranta har sai ta daina motsi kuma mutane salihai ba za su mata jana'iza ba,wannan dalili yasa ta k'ara k'arfin kukan nata,babu b'ata lokaci ta jaa mayafinta ta fice da gudu a gidan saboda wani tunani da tayi na bar in garin tun kafin asirinta ya kaiga tonuwa,mutanen dake k'ofar gidan da suka ganta a haka suka bita da kallo ganin yadda take gudu iya k'arfinta,mamaki duk ya cika musu zuk'ata,tana cikin gudun ne kuma Allah ya kawo wani mai akori kura take ya banketa,dalili kenan da ko shurawa ba tayiba nan take rai yayi halinsa tace ga garinku nan sanadiyyar fashewa da kanta yayi wannan shi ya zama k'arshenta.
Shi ko boka a k'alla sai daya kwana biyu cikin d'aki ba asan ya mutu ba jikinsa har ya fara tsutsa,mugun warin da malam yaji shi yasa shi nufar d'akin sai dai warin ya wuce tunaninsa,da k'yar dai aka samu aka bud'e d'akin wanda aka fito da gawar boka dake kwance kan gadon matar malam,had'awa akayi da katifar gaba d'aya aka fito da ita,sai a lokacin mutane da dama suka fuskanci dalilin daya sa matar malam take gudu waccan ranar,tasan abunda ta aikata shi yasa ta nemi guduwa,to yanzun dai ga abunda Allah ya nufa dasu duka babu wanda yake raye...
_Wannan kenan,su boka an tafi ga kuma yanda Allah yayi k'arshensa ya kasance dama wasu daga magoya bayansa...Allah ya karemu daga mummunan k'arshe._
《《》》
*INA LABARIN TABAWA K'AWAR LADIYO...???*
Tun bayan da LADIYO tayita zuwa gidanta akan tana neman taimakonta lokacin da take son neman MA'U a waya,a wani yammaci bayan zuwanta gidan lokacin suna zaune tsakar gida sai ga mijin TABAWA nan ya shigo,kamar ko wane lokaci nan TABAWA ta bud'e ido da murya iya k'arfinta zata fara zuba masa rash in mutunci Lamar yadda ta saba,take bata ko k'arasa fad'in abunda tayi niyyaba ya d'auke mata fuska da mari ganin yadda taci kwalarsa sannan ya shiga kora musu daga ita har LADIYO'N,kuma ya k'ara da cewa daga ranar kada ya kuskura ya k'ara ganin k'afar LADIYO a gidansa,duk kuwa ranar daya sake ganinta to ko shi kad'ai yasan me zai musu.
Tun daga ranar LADIYO bata sake yunk'urin zuwanba,dan dama mijin na TABAWA mugun masifaffe ne,dalilin sakkowar tasama kuwa ya had'u da k'arfin asirine.
Bayan tafiyar LADIYO ya zauna ya wanke TABAWA tsaf sannan ya k'ara mata da cewa zai yi aure idan kuma har ta sake ko da kallon banza tayi wa matarsa to ta kuka da kanta.
Ko bayan da yayi aurenma,ko kad'an TABAWA bata da wani power a gidan,hasalima ko k'ofar gida ya hanata zuwa bare ta shiga mak'ota,rayuwa tayiwa TABAWA k'unci a gidan mijin nasu,wanda ta koma tamkar baiwa a gurin uban gidanta,haka ta koma duk wani aiki na cikin gidan ya dawo kanta bata da sauran katab'us....
_Hattara ga masu hali irin nasu TABAWA,LADIYO,MA'U,BOKA,MATAR MALAM da sauransu,kunga dai yadda k'arshensu ya koma mask iron wannan hali tun kafin damar Ku ta kufce ya kamata kuyiwa kanku fad'a had'e da gyara tsakaninku da mahalicci dan duk Wanda ya mutu a haka Allah kad'ai ya barwa kansa sanin iron hukuncin da zai maka,Allah ya tsare my kuma ya tsare mana imaninmu..Ameen._
《《》》
Kasa fita yayi daga labour room en yana nan rik'e da matarsa,inda yabar yaran hannun nurse's suna gyara su,cikin wahalalliyar murya na mutumin daya galabaita ta kalleshi da idanunta dake lumshewa suna bud'ewa,murmushi kawai yake zuba mata.
"JAAN MAMA fa da UMMA...?"
Ido ya fiddo waje dan sam yama manta da batun ya sanar musu,kansa ya dafe yana birkita gashinsa,alamun data gani kenan a tare da shi ta gane babu wanda ya sanarma.
"JODI...Basu saniba,ni kuma na manta ma da ya kamata ace na sanar musu.."
'Dan murmushin k'arfin hali ta masa ta sake lumshe idanunta,aljihunsa ya laluba da niyyan d'aukan waya ya kira su,sai dai wayam babu wayan,sai a lokacin ya tuna da bai d'aukoba,lower lip nasa ya cije tunawa da kayan dake shirye cikin d'an akwatin kawai ya d'auko shima kuma suna motan bayan su kuma bai d'auko wani abuba.
"Ya Allah...! Komai ma na manta daya kamata nayi..JODI wait a minute....I will be back right now.."
Yana fad'in haka ya mik'e had'e da bata fake a cheeks enta na dama,cikin sauri ya fice ya nufi mota,kayan ya d'auko ya dawo had'e da bawa nurse's en ya shaida musu zai dawo nan bada jimawa ba in sha Allah,daga haka ya fice cike da sauri yayi starting motan,direct daga nan gidan UMMA ya fara zuwa wato HAJIYA ZUWAIRA,tana ganin yana yinsa ta fahimci da akawai abunda yake faruwa,ganinsa sai murmushi yake zubawa yasa ta itama tayi murmushin tana fad'in
"Kada dai ka ce KHUBRA ta haihu...?"
Aiko dariya ya sake yana fad'in
"Haka ne UMMA'NMU...Yanzun ma na barota hospital,so saboda ba waya a jikina yasa ban samu na kira kowaba,yanzunma gida zanje na koma.."
Da murna sosai take godiya ga Allah bisa ni'imar da yayi musu,sallama yayi mata ya fice ita kuma nan ta d'auka waya tana kira ABBA ta shaida masa,a lokacin ko suna tare a office d'in ABBA SAFWAN suna tattaunawa akan wasu kaya da zasu fitar sak'on ya iske su,cike da farin ciki ta sanar masa,aiko shi kansa tasa murnar kasa b'oyuwa tayi dan yadda sak'on yazo masa a lokacin sai yaji kamar lokacin IYA ke sanar masa da k'aruwar KHUBRA da ya samu,wasu hawayen farin ciki ya goge inda yake tambayarta me aka samu.Shiru tayi tana fad'in
"Tabbb! kaga kuwa abunda ban tambayaba kenan,kuma har ya tafi dan sauri yake lokacin daya zo,ya sanarmin ita kad'ai ce sai likitocin daya bari suna gyara su..."
Murmushi yayi na farin ciki sosai ya furta
"To babu damuwa in sha Allah yanzun driver zaizo gida sai kije gurinta kafin mu k'araso.."
Daga haka suka yi sallama ya kashe,yana kuma shaidawa su ABBA dake jiran ya gama,sun ga yana goge hawaye d'azun,ko da ya basu labarin abunda ya faru,su kansu murnansu da farin cikinsu kasa b'oyuwa yayi,tattara duk abunda suke sukayi da niyyan tafiya asibiti ganin jikokin nasu da basu san me aka haifa ba har lokacin..
Cikin d'an lokaci kad'an har labari ya gama zagaye dangin na haihuwar KHUBRA a yinin ranar ta jumu'ah.
Kafin wani lokaci mai tsawo har d'akin asibitin ya gama cika da iyaye da y'ay'a na gidan,kowa ka kalla kasan yana cike da farin cikin k'aruwar da aka samu na yara har uku sukutum a ranar.Maijego kuwa duk wannan budurin da ake bata sani ba tana ta faman baccin wahala dan kam ta galabaita ba kad'an ba,yara da suka zo da farin jini kowa burinsa ya d'auke su.
Daga KHUBRA har yaranta sun sha addu'ah a bakin y'an uwa da abokan arziki,haka mai jego taci gaba da samun kulawa a nan asibitin saboda k'in sallamarta suka yi duba da irin wahalar data sha kafin haihuwar,kwananta biyu aka sallameta inda UMMI ta tafi da ita dan bata kulawa ita da jariranta uku,biyu maza d'aya mace kuma ita ce k'arama cikinsu.
Gidan UMMI ya koma gurin zuwan BB kullum yana can mak'ale da yaransa da kuma y'ar matarsa,wani lokaci har sai UMMI ta gaji da shi ta kora shi dan kam ba wata kunyar UMMI yake jiba kuma dalilin daya sa aka maido da KHUBRA gidan sun san idan a gidan MAMA take zai iya komawa gidan ya tare.Sai dai kuma nan enma bata canza zaniba,kullum nan yake yini,da k'yar UMMI take korashi idan ko ya fice tofa bashi da gurin zuwa sai dai ya wuce gurin aikin nasu data tashi kuma nan zai dawo ya sake rashewa,a haka har aka shafe tsawon kwanaki shida,wanda zuwa ranar yara sun riga da sun amsa sunansu,HASSAN ya amsa sunan ABDULLAH suna kiransa da ABDUL,sa HUSSAIN da aka rad'awa ABUBAKAR shi kuma suna kiransa da SADDIQ ensa,ita kuma macen da take k'arama ta amsa sunan KHADIJATUL-KHUBRA wato sunan mahaifiyarta,kowa tambayar BB dalilin yin hakan yake,shi ko gogan cewa kawai yake haka yaga dama coz shi ba shi da niyyan sa sunan iyayensu,salon haka kawai wata rana a gaban idonsa a kira masa sunan iyayensa a zaga,KHUBRA kuma da aka tambayi dalilin da yasa ya sanya sunanta murmushi yayi sannan ya basu amsa da cewar
"Itace wacce nafi k'auna...Shi yasa na maida sunanta akan y'armu ta fari,kuma ko bayan haka sunan matar Manzon Allah ce ta fari (S.A.W)..."
Haka aka ci gaba da shirin hidimomin da aza gudanar a gobe na suna idan Allah ya nufa....
*RANAR SUNA...*
Tun da asuba bayan an idar da sallah aka sake jadadda sunayen yara kamar yadda suke,ABDULLAH,ABUBAKAR AS-SADDIQ sai kuma NANA KHADIJATU.
FATAHIYYA zaune ta tasa yaran a gaba dan tun da aka dawo da KHUBRA gidan UMMI itama ta dawo nan ta tare cikin shekaru biyu duk wanda ya kalleta sai yayi mamakin girman data k'ara ga class na musamman ba kamar daba da ba wani wayewa gareta ba.
Anyi taro lafiya wanda ya amsa sunan taro ba wai taron da yake na muna taroba,inda a ranar BB sai daya bawa mutane mamaki kan irin bajinta da yayi na kyaututtuka daya dinga bajewa ga abar k'aunarsa,duk kuma kan irin farin cikin data sashi a zamansu,haka taron suna ya watse da kyaututtukan da aula samu daga gurin y'an uwa da abokan arziki,haka taro ya watse inda aka bar mai jego da yaran hannun UMMI suna sake karb'ar gyara da kulawa....
Agogo juyi yake inda a kowane motsawar second sai kaga ci gaba ta wani bigire na daban a rayuwa,cikin kwanaki arba'in da haihuwar KHUBRA yara sun dad'a wayo musamman mazan da dama tun a haihuwarsu sunfi LITTLE KHUBRA girma.
Tun da safe a ranar kwana na arba'in en ne,BB ya kafa ya tsare a gidan UMMI jira kawai yake UMMI ta bashi approval na tafiya da iyalinsa,tun data ganshi tasan abunda yake nufi,nan ko ta had'e girar sama dana k'asa ta kuma k'i ce masa komai,tun safe har dare yana nan,ganin babu magana makamanciyar ya d'aukesu su tafi yasa ya bawa kansa hak'uri,kallon agogo yayi yaga yadda dare yayi cikin sanyi murya yace
"UMMI zan tafi..."
Bud'ar bakin UMMI tace masa
"To ka gaida gida ko..."
Shiru yayi kansa a k'asa ya rasa me zai ce mata,ita kuma tana kallonsa duk abunda yake sai dai bata k'ara maganaba daga haka,kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa,cikin sanyin jiki ya mik'e ya mata sallama fuskarsa cike da damuwa ya tasamma hanyar fita daga parlour'n,har ya isa bakin k'ofa sai kuma ya bata tausayi tasan dai ita da kanta yayi hak'uri tunda bai tab'a tambayarta akan zai tafi da ita ko makamancin hakaba,dakatar dashi tayi tana kiransa,dawowa yayi kansa a k'asa dan ji yake kamar yayita kurma mata ihu ko Allah zaisa ta bashi matarsa,hak'uri kam yayi shi har yana neman ya gagare shi.
"Zauna nan...Ina zuwa.."
Abunda ta fad'a kenan ta mik'e ta shige ciki,y'an mintuna da basu haura talatinba ta fito rik'e da hannun KHUBRA data sha ado cikin wani rantsatstsen less mai kalar sea green sai yarfan duwatsu kalar gold,tana ta fana shek'a k'amshi,fuskarta tasha light make-up tana zuba murmushi ta cikin mayafinta daya rufe mata fuska,dan dama a ranar kam tun da yazo UMMI bata bari ya ganta ba,sai dai y'ay'ansa da yaketa faman yiwa wasa,idan ya d'auki wannan ya ajiye ya d'auka wannan,sai dai da gani kasan LITTLE KHUBRA ta musamman ce a gurinsa...
Fuskarta a lullub'e da mayafinta kalar duwatsun kayanta da plat shoe a k'afarta,a hankali har suka iso gabansa,idanunsa tun da suka fito yake kansu bakinsa yak'i rufuwa saboda tsanamin farin ciki har tsaye ya mik'e bai saniba,hannunsa UMMI ta kama ta d'ora na KHUBRA aciki ta damk'e a nata,cikin sanyi ta d'an yi musu tak'aitacciyar nasiha sannan ta k'ara da fad'in cikin zolaya tana dariya
"To SON ga matar ka nan na baka....Allah yasa ba a soma fushi daniba.."
Dariyar shima yayi sannan ya rungume UMMI yana fad'in
"Na gode sosai UMMI'NMU Allah ya biyaki da mafificin alkhairin sakamako.."
Duka suka amsa da amin,sannan ya d'auki yaransa biyu UMMI ta d'auko LITTLE har bakin mota ta rakasu,inda KHUBRA ta zauna sannan UMMI ta d'ora mata LITTLE kan cinyanta tana fad'in
"To Allah ya tsare hanya,ya kuma karemin ku daga sharrin abun cutarwa...Sannan kuma idan Allah ya kaimu cikin satin nan zansa a nemo y'ar dattijuwar da zata na taimaka miki...Kinji ko DOUGHTER..?"
Godiya suka mata sosai mayafin KHUBRA lullub'e har lokacin a saman fuskarta,tana tallafe da y'arsu dake bacci sai k'amshi na musamman yaran keta zubawa kamar iyayensu.Sai da taga tafiyarsu sannan ta koma cike da farin ciki a zuciyarta mara misaltuwa.
Suna fita a get en gidan yayi parking gefe,jin ya tsaya yasa KHUBRA murmushi dan kam tasan Ogan nata yau sai yadda Allah yayi da su,tasan babu batun hak'uri a lamarinsa yau kam.Tana cikin tunani taji ya d'age mayafin kanta,da sauri ta kulle idanunta tana murmushi,murmushin shima yayi sannan ya d'auke LITTLE daga saman cinyanta,kanta ta jinginar jikin kujeran tana sauke numfashi a hankali,kusa da y'an uwanta ya kwantar da ita a back seat,sannan ya janyo KHUBRA dake mak'ale jikin kujera kamar idol.
Idanunta dake kulle ya kalla yana sakin murmushinsa mai tsada kamar idon nata a bud'e yake,kissing pore head enta yayi sannan idanunta,a hankali ya gangaro saman lips enta,sun jima a haka inda ta samu ta k'waci kanta da k'yar tana mai da numfashin wahala,shi kansa gogan da k'yar ya samu ya daidaita gudun numfashinsa lokacin kad'an har ya tsinci kansa cikin wani duniya na daban,fizgar kan motar yayi yana ta faman murmushin da na kasa gane ma'a narsa......
《《》》
*GIDAN KHALEEL.*
Tun a wayewar garin ranar da KHUBRA take da kwanaki arba'in da haihuwa ZUHRA ta tashi da matsanancin zazzab'i mai zafin gaske,hankalin KHALEEL idan yayi dubu ya tashi saboda yadda jikinta yake ga amai da taketa fama da shi,yini guda har ta fita a hayyacinta,tausayinta duk ya cika KHALEEL,yana nan zaune rik'e da ita a jikinsa DR yazo,ko bayan da aka dubata DR ya gama y'an bicikensa nan ya tabbatarwa da KHALEEL tana da shigar ciki na kimanin wata uku da sati guda,murna gurin KHALEEL kamar zaiyi me dan dad'i.
Sai dai kuma wani abu cikin na ZUHRA da alamun mai wahalarwa ne,dalilin daya sa KHALEEL ya yanke shawarar tattara musu y'an kayan da zasu buk'ata,ya tattara ta suka nufi gidan UMMI..
Tafiyar su KHUBRA kenan babu jimawa motarsu ta kunno kai gidan,lokacin har UMMI ta gama shirin kwanciya kenan sallamarsu tasa ta fito.
Ganinsu a lokacin harda luggage's ta saki baki tana kallonsu.Bayan sun gaisa KHALEEL ya mata bayanin komai,murna gurin UMMI harda taka rawa saboda zata sake jin kukan jinjiri daga tsatsonta a karo na biyu duk da a yau ta rabu da wasu jariran sai dai fa wannan na musamman ne a gareta...
_Toh ZUHRA fatan Allah ya raba lafiya..._
《《》》
*INA LABARIN HAJIYA LAURA....??*
Nasan da yawa kuna da son jin yaya ta kasance a b'angaren HAJIYA LAURA....
Tun bayan da ta san illar abunda ta aikatawa HAJIYA MURJA da labari ya iskota da kuma rashin lafiyar ita HAJIYA MURJA'N,nanfa ta ttara inata-inata ta,duk wani abu na kud'i ta sai da shi da yake dama gidan na HAJIYA MURJA ne cikin abunda ABBA ya bari kafin ya bar k'asar,ta fice ta bar gidan da shirin tserewa k'auyensu,tana cikin tafiya da y'an kayanta cikin wata jaka,har Allah ya kawo ta tasha,cikin ikon Allah,tsautsayin ya afka mata a lokacin da take k'ok'in tsallaka titi,tana tafiya ba tare da ta kula da tahowar motarba,shi kuma mai motar shima baiga lokacin data shigo ba,take ko ya kad'eta kuma ba tare da ya tsayaba kasancewar a lokacin danja ta bawa gefensa hannu ya manni motarsa,suma HAJIYA LAURA tayi yashe a gurin wanda mutane suka samu suka maidata gefen hanya,taimakon gaggawa suka fara bata.Kafin daga bisani akayi asibiti da ita wanda likitoci suka shafe tsayin lokaci suna bata taimako.
Tsawon kwanaki biyu ta shafe a sume ba tare da tasan halin da take cikiba,sannan a kwana na uku ta farfad'o tana ta fana surutai kamar zararriya,da kyar likitoci suka samu suka shawo kan matsalar tata,sai dai fa wani abu HAJIYA LAURA duk k'ok'arin likitocin sun kasa hanyan da zasu tashi k'afarta,wanda a sakamakon had'arin HAJIYA LAURA ta rasa k'afarta d'aya da hannu.
Wannan abu ba k'aramin tada mata hankali yayi ba lokacin data koma hayyacinta,tayi kukan har hawayenta sun dena zuba,sai daifa tana nan da damuwa fal a ranta na rushewar lamarinta,haka dai take ci gaba da karb'ar kulawa daga malama'n asibitin kasancewar na gwamnati ne,batun magani kuwa sai dai idan Allah yasa sun samu kud'in dubiya daga gurin masu zuwa ziyara,idan kuma Allah yasa ta samu en sai ta samu ta fanshi magani da shi Wanda shima jimawa zai k'are....Abinci kuwa ba a maganarsa ma saboda bata da wanda zaiji k'anta ya d'auki d'awainiyar bata ko wane lokaci,bare kuma ayi maganar d'an jinya,wani lokacin sai dai ko a nan gadajen kusa da ita da suke tausaya mata su sanmata,a haka har Allah yasa ta shafe tsawon shekara guda a asibitin Wanda ba tare da an sallameta ba ta tsere.
Bakin danja ta samu nan take bara ta samu abunda za taci,tana yawo da sanda wanda ke taimaka mata tana tafiya,tayi bak'i ta rame bayaga kod'ewa da tayi wahala kullum k'aruwa take a kanta,kullum ta tuna abunda ya faru da ita sanadin rasa k'afar da tayi sai tayi kuka,ga dukiyar data tattara zata gudu tun da tayi had'arin bata sake ganin jakar tataba...
A kullum burinta a yanzun bai wuce zuwa neman gafarar HAJIYA MURJA ba sai dai tsoro ya hanata tunkarar gidan hajiyar.A haka har aka sake shafe shekara guda da fitowarta daga asibitin,kuma har wannan lokaci bata tara kud'in da a ganinta ta wannan hanyar zasu tarunba.K'ark'arinta ta samu abunda zata sai abinci ta ci.Gurin kwana ko ya zame mata abu mafi wuya ya kasance yanzun HAJIYA LAURA dake da d'akunan bacci iri daban daban yanzun sai dai bin rumfunan kasuwa........
*Alhaki kuikuyo kenan jama'a ga dai yadda k'arshen HAJIYA LAURA ya kasance,ta manta a sanadiyyarta ta jefa y'ay'a da dama cikin halin da yafi nata muni,tasa su kwana bakin kasuwa,da yawon neman abunda zasu rufawa kawunansu asiri tamkar mabarata,cikin garin da basu da kowa kuma basu da komai,ta manta da had'arin dake cikin bar in y'ay'ata mata a gaban iyayensu,wanda hakan dai² yake da siyan lasisin tarwatsa musu rayuwa..Duk ta manta da haka ta kuma toshe kunnuwanta a lokacin... Huh!!...Allah ya k'ara rufa mana asiri duniya da lahira..ameen...*
*COMMENT FOR MORE PAGE'S..........* 💃💃💃💃💃
*~#TEAM KHUBRA-KHALEED.~*
*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠
*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*
🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
SMASHER,HUBBEEY,DIDEEYLOV & GENTLE NOVEL'S GROUP@web.facebook.com
*©®2018*
*11/ɑմցմՏԵ,2018*
*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~___________________________~*
*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_
*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._
*AND*
_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._
6⃣5⃣
*LAST PAGE.*
*I* sowarsu gida cikin mintunan da basu gaza arba'inba,ya fara bud'e mata k'ofan ta fito sannan ya bud'e back seat ya d'auko LITTLE dake bacci,mik'a mata ita yayi har lokacin yana sakin murmushi mai kashe jikin mai kallonsa,akan shoulder enta ta sata sannan tayi gaba,ABDUL da AS-SADEEQ ya d'auko ya d'ora su kan shoulder's ensa sannan ya tura k'ofan da k'afarsa,sai da ya tabbatar da ya kaisu har bed room ya kwantar da su,sannan ya koma don shigo da kayansu dake cikin booth.
Zama tayi gefensu tana kallon yadda yaranta suke k'ara girma,baccinsu suke hankali kwance kasancewar yaran basu da wani rigima shi yasa lokuta da dama ko a gidan UMMI ita kad'ai take kwana yaran kuma zaka tarar suna tare da UMMI.A nan ya sameta ta k'ure yaran da kallo cike da sha'awa da soyayyarsu,shigowarsa yasa ta kai dubanta gurin daya ke ajiye luggage set en nasu,ganin ita yake kallo yasa ta sakar masa murmushinta dake k'ara haske zuciyarsa,cikin d'an k'ank'anin lokaci ya k'araso gabanta,kusa da ita ya zauna yana sakin sanyayyar ajiyar zuciya,hannunta daya sha zanen henna ya d'ago yana kallo,sosai henna en ya masa kyau,kallonta yayi da alamar tambaya a fuskarsa ita kuma sai kawai tayi y'ar dariya tana fad'in
"UMMI tasa akamin d'azun..."
'Dan tak'aitaccen murmushi yayi yana kai hannun nata saitin bakinsa,kiss ya sakar ma hannun nata wanda ya haddasawa KHUBRA mutuwar jiki lokaci guda,idanunta ta lumshe tana sakin siririyar ajiyar zuciya,hayewa yayi ya kwanta kan bed en kansa na kan laps nata,ita yake kallo har lokacin bakinsa da magan-ganu masu girma sai dai yanzun kam ba lokacin yinsu bane,shi kad'ai sai sakin smile yake,idan ya juya ya kalleta ya sake juyawa ya kalli kid's ensu wani farin ciki ne mak'are a cikin zuciyarsa wanda ba shi da limit,mayafin data k'i cirewa tun shigowarsu ya kalla yana murmushi
"Yaushe kika zama matar liman kam....?"
Tambayan ya zo mata unexpectedly,sai dai data kalle shi kasa fad'in komai tayi,niko a raina nace ko dai KHUBRA bakin ya mutu tun a labour room ne..?
Ganin bata kula shiba yasa ya mik'e da sauri kamar ana fizgarsa,mayafin ya d'auke daga jikinta sannan ya sake komawa muhallin da yayiwa kansa ya kwanta,hannunta da yayi mata nauyi ta d'ora saman curly hair nasa da yake a gyare tsaf,ba kamar na samarin wannan lokacinba da za kuga yayi cukui² abun k'yama tana birkitawa,idanunsa ya shiga lumshewa dan dad'in abunda take masa a kansa yake ji kamar tana masa susa a kan,sun d'an jima a haka kafin ya mik'e yana fad'in
"JODI muyi wanka...ina jin bacci..."
Ita dai kawai ta kad'a masa kai amma magana tunda suka kamo hanya gaba d'aya kafafen sadarwa na bakinta suka tafi yajin aiki,kallonta kawai yayi da mamakin meke damunta kuma yau ta zama wata so speechless,k'ok'arin cire mata kayan ya shiga yi da sauri ta dafe tana kad'a masa kai,still yayi yana kallonta kuma bai fasa abunda yake niyyaba,kuka ta fara wanda sheshshek'ar kukanta yasa shi kallonta da matuk'ar mamakinta,yau kuma shi ne take yiwa kuka kan zai cire mata kaya to ko mene take nufi,hannunsa ta rik'e tana kad'a masa kai alamun bata so,har lokacin bai daina mamaki ba kallonta ya sake yi yana fad'in
"Me yake damunki kuma yau...?"
Shiru tayi masa kuma bata bar kukanba har lokacin,bai fasa tambayartaba yaci gaba dan ya kasa ganema kanta a yau kam,cikin sark'ewar murya wacce take cike da tsoro ta furta
"Ka bari zan iya da kaina...."
"Bakya so ne na cire miki kayan...?"
Kai ta d'aga masa alamar ehh
"Ok!....Shi kenan.."
Rabuwa yayi da ita cike da b'acin ran abunda tayi masa,kenan duk rawar k'afar da take akan d'ebosu ya tashi a banza ko me?? shi kam sam ya kasa gane nufinta,mik'ewa yayi yabar inda take amma sai yaga ko a jikinta wait an tsikari kakkausa,ficewa yayi inda yayi mata banging k'ofan,d'an tsorata tayi wanda a sanadin haka yasa LITTLE motsawa,sai dai Allah ya taimaka bata tashi ba,wani marayan kuka ta saki,cikin kukan take fad'in
"Wayyyoo! Allah shi kenan na jawowa kaina..Da na san ban masa haka ba,yanzun yaya zanyi...?"
_Niko nace mata ke kika sani kuma..._
Kukanta taci gaba da yi tana nan zaune ta sa yaran a gaba tana kallo hawaye na ci gaba da sauka akan fuskarta,yarfe hannayenta take zuwa can taci gaba da fad'in
"Ni dai gaskiya baran iya biye maka ba,haka kawai daga haihuwan nawa naje ka sake bani wani,dubifa duka shekaruna nawa amma da yara har uku,ni wallahi baran iya sake haihuwa ba wannan ma ai sun isa...."
Kukanta ne ya tsaya cak tunawa da tayi da yadda ya fita a d'akin,yanayinsa ya bata tsoro ita da basu tab'a samun sab'ani ba da shi,shi ne yanzun zata jawo ya fara tsanarta,kalmar *TSANA* data fad'o mata yasa tayi saurin mik'ewa tana kaiwa da kawowa,a fili ta shiga magana da kanta tana fad'in
"Wayyoo Allah! ya zanyi da shi,shi kenan na jawowa kaina fushin Allah zai sauka a kaina....
Idonta ta fiddo waje tana dafe kanta da sauri ta shiga cire kayan jikinta,cikin closet enta ta bud'e side en nightys enta,wani maroon colour silky ta fiddo wanda da ganin alama ba a tab'a amfani da suba sai data gama waresu tsaf ta kuma gama k'are musu kallo 3in1 ne kayan d'aya singlet ne,sai doguwa wadda zata kai har k'asa da mad'auri a gefen k'ugunta,d'ayan kuma rigane da wando do go,duka singlet en tsayinsa bare wuce saman knees entaba ta gabansa daga sama kuma wani ado aka masa da net,sawa tayi sannan ta tsaya kallon kanta ta cikin mirror dake gabanta,kayan yayi shara² sosai ta gaba kallon yadda suka bi jikinta take ta cikin kayan ana iya ganin hatta da nipples enta,gashinta ta tattara gefe ta masa tufka d'aya sannan ta kwantar dashi ta gefen necklace enta inda ya sauka har kan chest enta,sosai hakan da tayi ya mata kyau,idanta ta kalla yadda suka yi ja saboda kukan da tayi a hankali ta nufi toilet,sai da ta wanke fuskarta ta kuma sake kama ruwa da ruwan d'umi sannan ta fito,jingina tayi jikin k'ofan kanta a sama tana tunanin mafita,kanta tayi saurin d'agowa tunawa da abunda UMMI ta bata kafin ta fito da ita,da sauri ta nufi hand bag enta daya ajiye mata jikin abunda take sak'alesu,sai data d'auko abun a leda bak'i sannan hankalinta ya kwanta,wani ajiyar zuciya ta saki sannan a fili ta furta
"Sam na manta ma da wannan abun wallahi da duk haka bai faru tsakaninmu ba..."
Tunowa tayi lokacin da ummi ke mik'o mata abun bayan ta gama bata na gyaran jikin,tambayan da tayiwa UMMI da amsar data bata ta sake tunawa
_UMMI mene wannan..?_
_Karb'i ki ajiye zai miki amfani nan gaba.._
_To amma UMMI mene amfaninsa shi...?"
_Wannan da kike gani y'ay'an angurya ne...yana da amfani sosai ga macen data haihu,yana taimaka mata musamman gurin hanawa ta sake samun ciki da wuri,kinga ba sai kinyi planning ba ko dan gudun samun matsala da mai gidan naki,idan hair bai yadda ba za kuyi ta samun sab'ani,wannan zai taimaka miki har sai kin samu kin yaye wanda kike shayarwa..._
Karb'a tayi tasa a jakanta sannan ta mata godiya..
'Dan murmushi tayi da sauri ta d'ibo a hannunta tana dubawa,maidawa tayi da sauri kuma tayi parlour,ruwa ta d'auko da cup sannan ta dawo d'akin,a nan tasha sannan ta maida ragowar muhallinsu tana murmusawa,fuskarta ta gyara tare da murza powder kad'an ta shafa lip stick enta da yake matuk'ar k'auna.
Bakin bed enta ta koma ta d'auka d'ayan rigan wadda take doguwa har k'asa,ta d'ora a saman ta jikinta sannan ta kama mad'aurin ta d'aure,addu'a ta tofe yaranta da shi sannan ta fice tana nufan bed room ensa duk da irin yadda zuciyanta keta tsinkewa.
Cike da fargabar abunda zata tarar ta tura k'ofan da sallama a bakinta cikin sanyi,can k'asan mak'oshinsa ya amsa mata ba tare da ya kalli inda takeba,hakan da yayi yasa ta sha jinin jikinta,sai dai kuma tunawa da ita ta janyo komai yasa ta aro jarumta ta lik'a ta kuma ci gaba da shiga cikin d'akin,shirin kwanciya yake hakan yasa ta isa gabansa da niyyan taimaka masa,sai dai ko data k'arasa tana k'ok'arin taimaka masan matsawa yayi a gurin,cikin sanyin jiki dan kam ya gama kashe mata gab'ob'i ta furta
"Kawo na k'arasa maka...."
A tak'aice ya bata amsa da
"Barshi ban buk'ata..."
Sosai ta tsorata da abunda ya fad'a bata kuma ce masa komaiba ta nufi bakin bed ensa tana shirin zama,muryarsa da tambayan da ya watso mata suka sa ta kasa k'arasa abunda tayi niyya
"Me za kiyi a nan...?"
'Dan juyawa tayi tana kallonsa,shi enma itan yake kallo da fuskarsa da take d'aure tam kamar an aiko masa da sak'on mutuwa
"YAYA kwanciya zanyifa..."
Ta bashi amsa kamar za tayi kuka
"Su kuma yaran nawa wa kika bawa ajiya...?"
'Dan kallonsa tayi cikin rashin damuwa ta shiga ware mad'aurin rigar had'e da zareta a jikinta tana kwanciya saman bed en nasa ta furta
"Ai sunyi bacci..."
Kansa ya kad'a yana fad'in
"Na san sunyi bacci ai...Tambayar dana miki itace...Wa kika bama ajiyarsu...?"
"Kamar yaya...? naga dai ko can gidan UMMI ma ba tarefa muke kwana dasuba..."
Fuska ya dad'a tamkewa cikin fushi ya shiga mata fad'a
"Saboda kinga ina had'a shimfid'a dake shi yasa kika raina ni ko...Wato ga sakarai shi ne zaki dube ni kina gayamin ba tare kike kwanciya da suba....
Barin fad'a miki kuma ki bud'e kunne sosai kiji ni daga yau in sake miki magana ki bani irin wannan amsan na rainin wayo.....shi kenan dan kinga na miki ciki kin haihu sai ki ce zaki min abunda kika ga dama....wallahi idan baki maida hankalinki a jikinki ba zan daka ki,ki shiga hankalinki kinji dai na fad'a miki,kuma yanzun ba sai anjima ba kizo ki ficemin a d'aki...Ko an fad'a miki ni jarababbene da zaki kwaso jiki ki biyo bayan kin nunamin iyakata.... Wannan ya zama na k'arshe kada ki kuskura ki sake barin min yara su kad'ai da sunan su kad'ai zasu kwana,duk ranar da kika sake kuskuren yin haka Allah sai nayi mugun sab'a miki..."
Yadda ya bad'e idanunsa da toka yana ta zuba fad'a yasa ta fashewa da kuka mai cin rai,cikin k'unk'unin kuka take furta
"Dama nasan haka sai ya faru wata rana,duk wanda zai maka alk'awarin soyayya ba zai tab'a iya cikawa ba,tun dana taso na rasa wanda zai soni a rayuwata,na rayu da mahaifina wanda ya zame min uwa da uba....Duk duniya shi kad'ai ya soni....meye laifina a rayuwa da kowane lokaci idan na samu nutsuwa sai wani abu ya gilma tare da disashe farin cikina...? Ban san me nayiba a rayuwa da ko wane bayan zamani saina shiga k'unci,bayan duk irin rayuwar da nayi a baya tun daga gidanmu bare sa a tausaya minba...Haka na koma tamkar mabaraciya a lokacin da nake neman rufin asiri daga mahalicci wanda ya janyo har wasu suke zagina a matsayina na *Y'AR GARUWA* wacce bata da wani sauran gata,a lokacin kowa kallon y'ar iska yakemin wadda ta gudu daga hannun iyayenta,ba dan Allah yaji k'aina ba ya had'a ni da matar da ta rik'e ni a matsayin y'a ba,da haka rayuwata zata ci gaba da tarwatsewa kenan,shin yanzun kuma mene ne laifina dan nayi wannan maganar....?"
Ta k'arashe tana sake rushewa da matsanancin kuka,wani kallo ya shiga watso mata cikin k'unar rai ya furta
"Kada ki kuskura ki zageni ko mahaifiyata,dan naga rashin mutunci kike ji dashi,idan har kika kuskure kika zageta zan nuna miki iyakarki..."
Kukanta ne ya tsaya cak jin maganar da yake,da sauri ta goge fuskarta tana fad'in
"Ni ban isa na zagetaba,hasalima idan dan kana tunanin ina magana ne akan itace sanadin daya sa nayi wannan rayuwar a baya to ka daina,na sani tun ran gini ran zane,k'addarata ce kuma dole sai haka ya faru....Saboda haka kayi hak'uri ni ban isa zagin mahaifiyar kaba bare kuma kai..Ina rok'on Allah da kada ya bani ikon aikata haka...Kayi hak'uri ka yafemin nasan na b'ata maka rai,amma dan Allah ka yafemin..."
Bai sake kulataba dan yasan idan yaci gaba da magana to tabbas daren yau bazaiwa kowannensu dad'iba,saman bed ya zauna yayi addu'o'insa sannan ya kashe light en d'akin yayi kwanciyarsa.
Nan tsaye inda ya barta take har lokacin wasu siraran hawaye masu d'umi suka sake zubo mata,cikin sanyinta ta nufi hanyan fita tana kuma mamakin abunda ya faru,Wanda ko cikin bacci aka fad'a mata haka zai faru tsakaninsu zata k'aryata,har ta fice bai ko sake kallon inda take ba.
Saman bed enta ta zauna dafa'an ta shiga rera kuka mai ban tsoro da tausayi,cike da tashin hankali take kuka tana k'arawa,dan kanta kuma ta rarrashi zuciyarta sannan ta d'auko LITTLE tasa ta a gabanta sannan mazan dake kusa da LITTLE hannunta ta d'ora samansu tana sake had'asu da jikinta,da k'yar bacci ya d'auketa sai ajiyan zuciya take saukewa da k'arfi.
B'angaren BB ma hakan ce ta kasance,lokacin data fita a d'akin yana kallonta tana goge fuskarta akai²,maganganunta ne suka shiga yi masa yawo cikin kansa,tausayi had'e da soyayyarta lokaci d'aya suka kawo masa ziyara wanda suka sa sam sai yaga baiga laifintaba cikin abunda ya faru kuma gaskiya ta fad'a ba tare suke bacciba dan UMMI ma ta fad'a masa,kukanta ne ya shiga dawo masa a cikin kunnensa,mik'ewa yayi ya shiga safa da marwa cikin d'akin har dare yayi nisa idanunsa biyu ya gagara bacci,nan zuciyoyinsa suka shiga kawo masa shawarwari daban-daban sunata fafatawa akan yaje ya rarrasheta,d'aya kuma na fad'in hakan da yayi mata shi ne zaisa ta gane kuskurenta ko nan gaba,dan taga yana tsananin sonta ne yasa zata fara masa iskanci,hakan da yayi mata ko zaisa ta gane nan gaba kuma bazata sakeba,yayin da d'ayan gefen na zuciyarsa ke sanar masa da,idan ya duba halayyarta kuma da tsayin zamansu ai bata tab'a masa laifi makamancin haka na,tabbas idan yayi mata haka bai mata adalciba,kuma ina al'k'awarin daya mata na killace soyayyarta har k'arshen numfashinsa,zuciyarsa ce tayi wani irin bugu tunawa da alk'awarin,kasancrwarsa mutum mai girmama alk'awari,nan ya shiga tunani iri-iri akan yaje ya rarrasheta ko a'a,kwanciya ya sake yi lokacin da ya amshi shawarar kangararriyar zuciyar tasa.
Sai daifa a banza yadda yaga rana haka yaga daren ranar,sam bacci ya gagari idanunsa,ba shi ya samu bacciba sai wajejen k'arfe biyu,wanda ya haddasa masa yin sallah a makare.
Ko bayan daya idar bacci ne ya sake d'aukansa dan dama ba wani bacci yayiba sosai a daren.
Da asuba ta tashi tayi sallah kuma har lokacin yaran basu farka ba,baccinsu suke hankali kwance,sanin bata da mataimaki yasa bata yi tunanin komawa ta kwanta ba,fita tayi ta fara y'an aikace aikacenta,sai data gyara ko ina na cikin gidan sannan ta shiga kitchen da tunanin abunda ya kamata ta musu na break fast,markad'ad'd'iyar gyada ta d'iba ta dama dan kam kunun gyad'a kawai taji tana sha'awar sha a safiyar kuma dama ganin tana so yasa UMMI ta had'ota da gyad'ar.
Zuciyarta duk babu dad'i haka take aikin saboda abunda ya had'asu jiya ya tsaya mata a rai,sai data gama ta shirya komai a dinning,ta dawo zata wuce bed room da niyyan dubawa ko sun tashi,dan tun d'azun data fito tana aikin tana dubawa amma tsill saita samu sunata bacci abunsu.
Doorbells taji na k'ara da sauri ta nufi gurin dan dubawa a ranta kuma tana mamakin waye da wannan safiyar..?
Bata tambayaba sai data lek'a a hankali kuma ta bud'e k'ofar ganin wata y'ar dattijuwa tsaye yasa ta saki fuskarta tana fad'in
"Sannu da zuwa..."
Amsawa matar tayi da y'an kayanta cikin wata y'ar jaka tabi bayan KHUBRA,bayan sun gaisa cikin sakin fuska,matar ta shaida mata UMMI ce ta turota yanzun driver'nta ya kawota,kuma itace wacce zata kula da yaran,murna sosai KHUBRA tayi dan dama zuciyarta duk a dame take da tunanin yadda za ta dunga ma yaran wanka ta kuma shirya su.Godiya ta mata sannan ta d'auki kayan matar mai suna SABUWA tayi ciki ita kuma tana biye da ita har bed room enta inda yaran ke kwance,nan ta zauna tana kalle-kalle na yadda tun daga get en gidan ya zama abun kallo ashe tace bata ga komaiba,wanka KHUBRA ta shiga bayan ta fito ta shirya cikin riga da sket na wani atamfa daya matuk'ar yi mata kyau,ta kafa d'aurin d'ankwalinta kamar gwagwgwaro,sannan ta fad'awa SABUWA tana zuwa ga yaran nan ko da zasu tashi bata nan,nan ta nuna mata komai a sauk'ak'e sannan ta fice.
Ficewa tayi fuskarta tasha kwalliya sai dai kallo d'aya zaka mata ka gano bata tare da nutsuwarta haka nan dai ta isa d'akin nasa,kwance ta tarar da shi har lokacin yayi hugging pillow so tight,duk sai taji wani iri da bata aikata abunda tayi ba da tuni itace haka kwance jikinsa kamar ko wane lokaci na can baya,rashin jin dad'in ne ya rinjayi zuciyarta wani missing ensa ya taso mata daga can k'asan zuciyarta,k'afafunta taja cikin sanyi ta isa kusa dashi ta zauna,hannunta ta d'ora saman kansa tana shafawa murya k'asa-k'asa saboda kuka dake neman kufce mata ta furka
"Ka gafarce ni mijina na san ni mai lefi ce a gareka,amma banyi dan na b'ata makaba,sai bayan da nayi ni kaina abun ya dameni...Dan Allah kace ka yafe min ko zan samu nutsuwa da sukuni.In Allah ya yarda haka bazai sake faruwa ba da izinin Allah..."
Kamar wacce take magana da mutumin dake ido biyu taketa surutanta,hawaye na sakkowa kan fuskarta har ta k'araci maganganunta tayi shiru,mik'ewa tayi da miyyar komawa gurin SABUWA,taji an rik'o hannunta,da sauri ta juya ta kalleshi ga mamakinta idonsa har lokacin a kulle suke,mamaki ne ya cikata da ganin hakan,k'ok'arin zame hannunta taci gaba dayi,cikin siririyar murya ya furta
"Ina zaki jene...kike k'ok'arin k'wacewa..?"
Sake kallonsa tayi taga da gaske shi yayi magnar ko kuwa.? sai dai wannan karon data kalleshi sai taga ya bud'e idanunsa kuma ita yake kallo,kanta ta sauke k'asa ba tare da tayi maganaba,abunda KHUBRA bata saniba tun daga shigowarta d'akin BB yana ganinta ta tsakanin lashes en idonsa,kawai dai yayi mata fakare ne ta yadda za tayi tsammanin bacci yake,saboda haka duk maganganunta babu wanda bai jiba kuma sosai yaji ya samu nutsuwa a lokacin.
Dawo da ita yayi ta zauna sannan ya mirgina jikinta,kansa ya d'ora kan k'irjinta hannayensa zagaye da waist enta ya shiga sauke wani wahalallen ajiyan zuciya,a b'angarenta kam ko iya haka kad'ai yabar ta tabbas ya gama mata komai dan kam ji tayi kamar an mata gafara,da sauri ta rungume kansa tana sakin ajiyan zuciya,yanayinsu kad'ai ya isa ya bayyanar da yadda sukai missing junansu,kansa ya d'ago yana kallonta da sauri ya dad'a kusanta bakinsa da nata,bai jira jin komai ba ko shawara da kowaba ya shiga aika mata da zallar k'aunarsa cake sawa ta manta ita wace,suna yi suna exchanging word's da suke nuna tsantsar yadda sukayi kewar junansu.
Cikin lokaci k'ank'ani suka manta da duk wani abu daya faru dasu,sun yi nisa cikin wata duniyar ta daban da babu wanda suke tunawa face kawunansu,sun farantawa junansu inda suka manta da duk wani abu daya had'asu a wancan daren.
Haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya a yayinda kowanne ke kaffa-kaffa da gujewa b'atawa d'an uwansa,basu da aikin daya wuce farantawa junansu da kyautatama junansu,inda yaransu kuma suka ci gaba da samun kulawa k'arkashin jagorancin BABA SABUWA da tun zuwanta gidan yaran suka koma gurinta,komai ita ke musu idan ka gansu gurin KHUBRA to abincinsu suke nema wanda wani lokacin idan suka tashi tsiya lokaci guda zasusa mata kuka,ba dama ta fara karb'an d'aya sai sauran susa mata rigima,ita kuma abunda ke d'aga mata hankali kenan sai kaga ta fashe da kuka,idan an tambayeta sai tace
_"Ita bata san ya za tayi musu ba,shi kenan babu damar su kyaleta ta huta.."_
Haka za tayi ta fama,har sai BB ya rarrasheta tukun zata hak'ura tayi shiru,wani lokacin ko shima da kansa zai sata gaba yana tsokana musamman idan ta fara kumbura fuska tana k'unk'uni shima haka zai kwanta kan cinyanta cike da shag'wab'a yana fad'in
"MOMMAH....saura PAPA shima yana buk'atar ayi feeding nasa..."
Duk lokacin daya mata haka sakin baki take tayi ta kuka tana fad'in
"Shi kenan kuma na shiga tara..tunda so kuke ku na mutu sai ku kasheni ai sai ku rabani hud'u kowa ya huta.."
Shi ko nan zai sata gaba yana dariya,idan yaga ta tsananta kukan ne zai dena ya kuma koma rarrashinta...Ranar da kyar zai samu tayi shiru har ta sakko daga Fushin da take yi............
*EIGHT YEAR'S LEAP.....*
Kwance take saman bed da waya a hannunta tana latsawa,da ganin alamu kuma chart take,sai dai na d'an sake matsawa kusa dan ganin abunda take yi,nan ko na ganota tana shawagi cikin group en nasu da ba wani yawa gare suba,dan duka bana jin zasu haura su goma..
Hira suke cike da k'aunar kasancewa tare a haka har k'anshen rayuwa.
Shigowar BB yasa ta ajiye wayan a gefenta tana murmusawa.Cike da so da k'auna BB ya kalli KHUBRA data zama babbar hajiya yana kwanciya saman jikinta,cikin wani voice dake kashe mata duka gab'ob'in jikinta ya sake kallonta,ido d'aya ya kashe mata yana fad'in
"JODI yaushe zaki sake bani new baby ne...? ina son sake ganinki da babyna kwance a nan...?"
Ido ta fiddo tana rufe bakinta da hannu ta furta
"Haba MY JAAN....Yanzun har fatan na sake haihuwa kakemin...? yara biyarfa nake da su..Inama laifin kace na barshi haka ai nayi k'ok'arima hakan..."
Y'ar dariya yayi yana fad'in
"Haba mana dan kin bani biyar shi ne kike rakin kinyi k'ok'ari...?"
"Ehh! mana kaima kuma ai kasan nayin indai k'ok'ari ne,kallafa CWEETY har yanzun a uku take,dama dama ma ASHNA da muke kai d'aya,amma itama ai ta rigani haihuwan fari,kuma kana dai ganin CWEETY ko shirin sakewa bata da.Daga maza biyu mace d'aya face ya is a haka..tabbb! ni dai kayi hak'uri hakanma Allah ya raya mana su cikin aminci..."
"To ameen...Amma dai da kin daure kin k'aramin ko dozin biyu ne..."
Yadda tayi da fuska yasa shi kwashewa da dariya,pillow ta d'auka tana dukansa shima ya d'auka yana ramawa,zuwa can kuma suka zube suna maida numfashi game da dariyar farin cikin yadda rayuwarsu ta kasance...
Tsagaitawa tayi da tata dariyar tana shafa fuskarsa,da sauri ya kalleta yana d'aga mata gida alaman tambaya,a hankali ta motsa bakinta cikin coolness
"Kawai YAYANAH idan na kalleka da yaranmu sai na tuna rayuwata ta baya ne lokacin da nake matsayin *Y'AR GARUWA...* sam ban tab'a kawowa rayuwata zata zamo yadda nake a yanzun ba...Alhamdulillah! komai yayi farko da sannu k'arshensa zaizo...yau ni ce kwance jikin mijina abun alfaharina,baya ga yarana dake kewaye da ni a kowane lokaci...Tabbas Allah shi ne abun godiya..Allah na gode maka bisa ni'imomin da kaimin..."
Siraran hawayenta dake mak'ale a idanunta suka sakko.
'Dan murmushi yayi yana dad'a mannata da jikinsa,cikin kunnenta ya shiga fad'a mata magan-ganun da zasu sata ta manta da damuwar da ke neman kunno mata kai,sai da yaga ta ware sosai sannan ya furta
"Tohh! MR'S KHALEED SAFWAN yanzun komai ya wuce ai kuma maganar kin tab'a yin wani wahala da har ya kai ki zama matsayin *Y'AR GARUWA* ina so ya wuce,coz ban son wata rana wani yaji bare har ya gorantama yaranmu.....Tun da kin jima da barin wannan layin,kuma ko a yanzun aka kalleki babu wanda zai yarda kin yi irin wannan rayuwar,saboda kina da abubuwan da zasu gogema mutum tunanin haka,kina da ilimi bayaga nasarori da kika samu a rayuwa,yanzun kina a matsayin mata ga MR KHALEED SAFWAN,after all these gashi har kin haifamin sanyin idaniyata kuma abun k'aunata,so kada ki damu ako da yaushe zamu ci gaba da kasancewa tare kamar farkon auren mu...So yanzu komai zai koma FREE.....
*LOVE FREE...!*
*KISS FREE...!!*
*LIVE FREE...!!!"*
Dariya dukansu suka yi yana dad'a rungumeta a jikinsa had'e da sakar mata fake a Cheek's enta,da gudu yaransu suka shigo maza uku mata biyu suna fad'in
*"PAPA nd MOMMA.....APPY WEEDING ANNIVASERY...."*
Da mamaki iyayen suka kallesu coz basu san inda suka jiba,LITTLE ce ta kalli iyayen nasu tana fad'in
"PAPA..... UNCLE ne ya fad'a mana jiya da muka je gidan Granny's..."
Cike da nishad'i BB ya bud'e musu hannu inda MOMMA'NSU ke kwance cikin jikinsa wanda ganinsu baisa ta tashiba,da gudu ko suka k'arasa suna dariya dukansu ya rungume yana jin sonsu har cikin b'argonsa....
"To yanzun kowa ya yazo fad'amin abunda yake da buk'ata a yau ni kuma nayi muku alk'awarin bawa kowa abunda yake so..."
Kallonsa HAJIYA KHUBRA tayi tana murmushi,shi d'inma ita yake kallo kuma yana maganar,da sauri LITTLE dake da shekara takwas a lokacin ta furta
"PAPA mu dai da kid sis a kaimu saudiyya muga d'akin Allah...irin na photon nan..."
Ido KHUBRA ta dad'a bud'ewa tana kallonsu da mamaki coz batayi tsammanin jin hakaba daga bakinsu,sai dai amsar *ALHAJI KHALEED* tasa ta binsu da kallo dan ko amsa musu yayi da fad'in
"An gama...ku shirya in sha Allah idan kuka yi hutu a skul zamuje Umra next month...."
Ihu suka d'auka duka yaran suka sake rungume iyayen nasu suna fad'in
*"WE ALL LUV AND PROUD WITH U PAPA ND MOMMAH..........!"*
~K'ARSHE.....~
*ALHAMDULILLAH...!*
*ALHAMDULILLAH...!!*
*ALHAMDULILLAH...!!!*
_A nan na kawo k'arshen wannan littafi nawa na *Y'AR GARUWA..* Ina mai mik'a d'umbin godiyata ga Allah (S.W.T) daya bani iko,dama da kuma lafiyar dana kawo k'arshen wannan labari nawa,inda nayi kuskure ubangiji ya yafemin ni daku,inda kuma nayi dai² Ubangiji ya had'amu a ladan..._