'YAR KWALLIYA Page 6-10
.
Can saiga Binta ga gare sarkin kwadayi da umman ta suna ta howa Yauwa Allah na gode maka ga binta cewar Abu Dan rainin wayo da sassafen nan a aiko gidan mutane ace suzo ko uwar me za a mana cewar Binta Abu tace Kema dai kya fada gamunan ana surfo mana zancan banza Eh waye yake zancan banza ke kuma Binta ba a koya miki gaisu waba bakya ganin manyane a gurin nan cewar liman dake zaune a gefen me gari Binta da umma suka samu guri suka zauna Abu tace Wanda yatsargu dahi nake Babba bangan shiba saidai naga me gari tinda ba a barni naci abinci ba nazo nan to kowa yayi hakuri da abinda zeji koya gani cewar binta Liman yace kaji yara da rashin kunya Barsu dani liman cewar megari Umma ta gaida me gari binta kuwa aikin gun guni kawai takeyi Sauran mutanen gurin hanci a to she sun kasa cewa komai daga liman sai megarine kawai suke magana Binta kinji wai dan mun daki wa yancan 'yaran hine aka kawo mu nan gasu 'ya'yan kuli da mai cewar Abu Binta tace Kan uba Yasin bazan zauna ba akan su aka hanani cin abinci tafiya zanyi Yasin karki yarda binta kanki tafi kizo ki daki rabon ki zan taya ki cewar Abu Sukayi kansu zasu daka liman da megari mutuwar zaune sukayi wato kanhin jikin Abu dana binta da itama tafara hawa layi sukaji sukayi lup kamar basa gurin Megari yace Karku sake Ku tabasu kuna jiko wai warin me nake ji haka ina kuke kusa baki mana meye aikin ku liman Caraf Abu tayi da cewa nice nan kanhin tirarena babu inda baya zuwa megari ka gode Allah tinda kaji kanhin tirarena Megari yace Tirare kuma tab Wannan uban warin shine tirare
.
liman ba lbr yakasa cewa komai sai kallo da ido sauran ma sunyi shiru Megari cikin bacin rai yace waime nake gani haka kun dena magana ne kuma banson sha shanci kunwani zuba min ido me kuke nufi Me gari sai hakuri binta Abu kuzauna cewar inna da umma Binta hannu a dun kule tana shirin kai naushi take cewa Inna kubar mu dasu yanzu mu koya musu hankali Nura cikin muryar tsawa yake cewa kuzauna karku bari na kara magana Ganin fuskarshi ba alamar wasa yasa suka zauna Megari yace gaskiya yaran nan abin naku azimun ne kuma da laifinku wajan bata yaran nan kuduba fa Ku gani baruwansu da babba koyaro duk wanda ya musu yi mishi zasuyi Me gari ayi hakuri zamu gyara insha Allah cewar umma Me gari yace To shi kenan gaskiya kudau mataki inba haka ba ni da kaina zandau mataki Wani yaro ya fito daga gidan me gari hannun shi rikeda samira Tinkafin ya karaso Binta sarkin kwadayi tafara hadiyar yawu wayanda suke kusa da ita saida sukaji karar Yaron ya gaidasu ya ajiye kwanon a gaban liman Binta idonta na kan kwanon ko kiftawa bata yi ta janyo kwanon kusada ita Kanshin abinci yadawo da liman daga dogon suman da yayi Liman yace Ke me kike nufi yajanyo kwanon gaban shi Binta ko magana ta kasa hankalinta nakan kwanon Liman Allah ya yanka maka binta taga abinci ranta ya biya dan haka ka bata taci cewar Abu Liman yace In naki fa dawani bakinki dayake zuba wari anya kina wanke shi kuwa Abu tace Yasin wanke baki kahe hakori yake hiyasa bana yi liman kaida kanka kace hi bakin me azumi kanhin Almuski yakeyi hiyasa nima na dena wanke baki saboda Almiskin yazauna a bakina nafita daban daku nawa basai ina azumiba ta fada tana Dariya Liman baki yasaki yana kallon Abu Megari yace ke Abu anya kina da kai kuwa Abu tamika mishi kanta tace shafa kaji Inna ta rufe bakinta tana kallon Abu Megari ina fada maka saika dauki babban mataki akan Abu da binta cewar liman Bakomai kubani lokaci zansan abinyi kuna iya tafiya amma kubar binta da Abu liman ze musu fada cewar megari Waaaanii gaskiya babu abinda zan iya fadawa wayan nan yaran banshirya takun saka da suba sunyi nisa basa jinkira cewar liman Yi shiru liman nagama magana cewar megari Inna,umma da Nura suka tafi Binta batama San tafiyar suba itadai burinta taji abinda ke cikin kwanon a cikinta Liman kabata abincin nan taci yasin tanada cutar duka idan aka hanata abinda takeso hine suke tahi cewar Abu Liman Ya kalli binta dake zaune hannu a dunkule ido akan kwano tana sude baki Liman yace Me gari Abuya tabbata duka zatayi kalli kaga
.
Liman karka zama soko mana kayi musu fada sutashi su tafi ita kuma binta ka bata taci cewar megari Kwanon ya miki mata ta ansa tabude tana ci kamar kura yaga nama Binta ta gama ci tasa kafa ta ture kwanon ta kalli 'yar me gari tace jeki kawo min ruwa Niii kalle ni sama da kasa nayi kama da 'yar aikin gidan Ku cewar yar me gari Zancen banza meye dan kin debo min ruwa yan matan garin nan kaf yan aikina ne saboda na fisu haduwa cewar Abu Ya isa kunutsu kuyiwa kanku fada kungirma aure zakuyi gidan wani zaku kuyiwa Allah kudena abinda kukeyi Dariya suka yi suka tafa kinji wai aure cewar Abu Binta tace kaika sanshi nidai tinda ba a bani ruwaba bangode ba taso mu tafi To tace suka tashi zasu tafi Binta tarike ciki tace washiii cikina ya motsa Binta tayi nishi saiga tusa ya biyo baya Megari yatoshe hanci yace liman Sa a kamo min yarin yarnan Binta da Abu najin haka suka sa gudu
****
*WACECE BINTA DA ABU*
ABU 'yace ga munzali malam munzali fatauci ne sana arsa shikadai yake tafiya inya tafi saiya jima kafin ya dawo sai matarsa Suwaiba yaranta na kiranta da Inna yaransu 4 Ramatu itace ta farko tana aure a garin da suke me suna *DARAUDAU* sai zulai itama tayi aure sai Nura da Zainabu Abu itace auta
ABU yarin yace mara tsoro duk girman mutum inya mata saita mai farace tas amma qazanta ya maida ta baka dan qazanta kokitso intayi saiya dankare layin ya bace kafin inna tai mata ta karfi ta tsefe Binta 'yace ga murtala Malam murtala mahaucine Allah ya masa rasuwa tin Binta tana karama a hannun ma hai fiyarta ta tashi sunan ta Baraka binta kadai ta haifa BINTA yarin yace mara nutsuwa ga kwadayin tsiya idan taga abinci jikinta har rawa yakeyi itama bata barin ta kwana dan haka tasu tazo 1da Abu gasuda taurinkai
*****
Binta da Abu na cikin gudu wata yarinya kanta dauke da buhu ta tsaya a gaban su ta shaki wuyan Abu Ke meye haka a ina nasanki cewar Abu Tace idan maye ya manta uwar diya bazata mantaba nice wadda kika daka kika cimin gyada kika kuma zubarda sauran Abu tace Kinsan abin da yawa yanzu me kike nufi da kika shaki wuyana Dukanki zanyi na kwashi saura nakai gidanku cewar yarin yar Banga Alamaba ance da kuturu a gama lpy ni Abu banga wanda ya isa yamin abinda kika fada ba ba a hai fehiba Binta tace ke ware inba haka ba hmm jiki zeyi tsami Ke waya sa dake ni din nan da kike jida gani ban tinkare kuba saida na samo makarin ki ke binta dan nakula kema matsalace ta daban cewar yarin yar Makarina kuma ni binta banganshiba anan gurin yau banga abinda zesa na bar kiba batareda na sosakida bulala ba Ko to shikenan nida ke za a ga me gaskiya yarin yar ta Bude buhun taciro goriba,kurna,magarya da gyada Tinda ta Ciro Binta ta hadiyi yawu kamar yanda ta saba tabi hannun yarin yar da kallo Abu tace Ke karki sake ta rudeki da abin hannunta Binta nizan siya miki fiye dahi Ko jinta binta bata yiba Tamika hannu alamar ta bata harya rinyar ta miko mata saita janye Binta tace meye haka kuma bana son irin Wannan Kina zaton kai tsaye zan baki batareda na kafa miki doka ba Meye dokar cewar Binta Yarin yar tace zakiyi Alkawarin cewa bazaki sa hannu a fadana da Abu ba inkikasa hannu zan kwace abina Binta ta kalli Abu ta kuma kalli ledar hannu yarinyar da irin abinda ke ciki Nan tashiga raba idanu
.
Jikin Binta sai rawa yake Na amince bani Yarin yar tace in na baki ki tafi ko juyowa karkiyi Binta tace to bani dai Tana ba binta tawuce ta tafi Yarinyar tace yanzu daga ni seke Abu tace hakane kuma zam miki dukan tsiya kamar mu2 muka miki Yarin yar ta kama Abu da duka Abu na ramawa Abu ta Bude baki ta sakar mata cizo a hannu Waiyoo kika cizeni Yasin bazan yarda ba koni koke a gurin nan cewar yarin yar Saukar duka yarin yar taji bazata koda ta juyo Binta ta gani zatai magana binta ta dauketa da mari binta da Abu sukayi mata taron dangi saiga yarin yar a kasa wanwar tana kuka Abu ta bude buhu ta leka taga garin tuwo tayi dariya Binta ta daga ta juyewa yarin yar a jiki Inkinje gida saikiyiwa tsohuwa bayani yanda Akai da garin tuwo cewar Abu Suka tsalla keta suka wuce Binta tace Abu kina jin abinda liman yayi mana dan yaga me gari waimun girma aure zamuyi Rabu dashi nasan abinda za muyi mihi damu yake magana ba a taba mubama munyi fada bare ka ta bamu zomuje cewar Abu Ina zamu cewar binta Zaki gani cewar Abu Koda suka tafi basu tsaya ko ina ba sai gidan liman Abu tace Sallama Alaikum goggo me tuwo Goggo me tuwo ta amsa da Wa'alaikumus salam Abu Binta yaukune agin namu Eh wlh cewar Binta Goggo me tuwo tace Gashi kuma ban gama tuwonba yanzuma na dora Bakomai mu abindaya kawo muma daban ne bansan ta yanda zanfara fada mikiba goggo cewar Abu Kar kuji komai kufada min idan baku fada minba wazaku fadawa bayan nasan Ku tin kuna yara nan kuke zuwa cintuwo cewar goggo Binta tace Hakane munsan da wannan goggo hine dalilin da yasa mukejin nauyin abinda zamu fada miki Binta Abu kufada min bakomai komai girmanshi zansan abinyi Abu tafashe da kukan karya taceTo hikenan goggo kiyi hakuri da abinda zakiji sai Abu takara sautin kun da takeyi Binta ma kukan karya takeyi tace yi hakuri Abu bakomai sakai yar daze mata kenan Nanfa hankalin goggo ya tashi tace kunga kufada min duk kunbi kun daga min hankali Abu tace goggo dagir manki da komai liman ze miki kishiya Gogo ta mike tsaye tarike kirji tana huci
.
Ni liman zewa haka zezo ya sameni bemin kishayaba tin ina yarinyata saiyanzu dana tsufa Goggo abinda ze kara daga miki hankali hine irin kalaman da yake mata idan yaje zance cewar binta tafada tana kuka Dan rahin mutunci hine ta aiko mu da kala man soyayya muzo mu fada mihi Takuma ce karya manta yau yazo zance ita kadai tasan abinda ta tana dar mihi cewar Abu Kafar goggo ya haurawa taji juwa na ibanta tajin gina da bango ta ciji lebe a nan gidan ze kwana daiko badamuwa ina jiranka cewar goggo Binta takara sautin kuka tace babban abin hine mahaifin yarin yar yace liman yaturo anbahi ita Suna fada goggo ta zube kasa ba nunfashi Munhiga 3 Abu munyi kisa cewar binta Abu tace ke bata mutuba tsabar kihine kawo ruwa kigani Binta takawo ruwa Abuta watsa mata taja dogon nunfashi tabude ido tana Cewa ina yake kumiko min shi Abu tace goggo aibaya nan bari zahigo saiku yita takare Goggo tace bakomai zaka dawo kasa meni liman nida kaine yau agidan Goggo mu zamu tafi Nagode muku binta da Abu Allah ya muku Albarka Goggo me tuwo macace me kishi akan kishi zata iya yin komai sanin hakane yasa Abu da binta sukazo gurinta sunsan ita zata hukun ta musu liman yanda suke so Ameeen goggo aiyiwa kaine suka ce suka nufi hanyar fita harsun sa kafa zasu fita Abu ta gano liman yana ta howa da alama gidan zezo da sauri ta riko binta suka boye cikin wani duhuwa dake zauren gidan liman Liman yayi sallama ya fada gida kai tsaye ya nufi bandaki Goggo na jinshi binta da Abu Suka dauke sawun takalmi suka matso tayanda zasuji kuma suga Abinda ke faruwa Liman yafito yashiga daki yasa sababbin kaya yafesa tirare Nanfa kishi ya turnike goggo me tuwo tashiga waigen Abinda zata samu tarike ta hukun tashi dashi Me gari ya fito yana gyara hula yace in na kike na fito zan tafi Goggo tafito tana huci tace nasani kagai sheta wato danka raina min hankali nika ajiyeni a gida kaikuma ka fita kana neman aureko har ance katuro Yace ni liman a ina kikaji zan cen nan wlh bana ne man aure a ko ina ni liman ke kadai kin ishe ni Tace karyar banza ba abinda zaka fada min na yarda bayan nasan komai yanzu kayan nan dakasa kafesa tirare ina zaka Abuda binta na labe suna ji kuma suna ganinsu suna dariya Yace daliban malam rabi'u ne zasuyi sauka yau shine aka gai yace ni na shirya yanzu zan tafi Bata gamsu da abinda yace ba yasa tafara buga kafa tana tsaki
.
Tace malam malam ni goggo ni zakai wa kishiya Tana juyawa taga murhuna cida wuta ta Ciro icen dayafi ci tasa mai ababban Riga wuta yafara ci liman na ihon temako yana kokarin cire baban riga dakyai ya samu ya cire abin beyiwa gogoba ta dauko tukunyarda ta gama hada kayan hadin miya ta kwaramai a fara ren kayan shi Binta da Abu dariya harda faduwa Ta rarimo bokiti tana jifan shi dashi ganin abin nata bana Kare bane yasa liman ya mike ya zuba da gudu Binta da Abu suka Tsaya a gaban shi Abu tace liman mun girma aure zamuyi ko toga auren mun gwada maka tafada tana dariya Binta tace waiyoo cikina liman mezan gani haka yazaka gudu kaida yadace kai mata fada kamar yanda kayi mana dazu Amma dai yaran nan kwai shedanu kune kuka hadani da matata bakomai dani kuke magana Abu tace gogo me tuwo gashinan Liman yasa gudu binta da Abu na dariya Raina fesa cewar binta Duk wanda yace ze higa harkarmu to yadebowa kanhi kwarkwasa cewar Abu Sukayi dariya suka tafa Suka nufi gidan su Abu Liman be tsaya ko inaba sai fada gurin me gari wayanda suke tareda megari ganin liman yashigo da gudu suma suka mike zasu gudu Megari yace kudawo Ku zauna liman mezan gani haka da girmanka da komai Allah yabaka yawan rai ai duk abinda ya sameni kaine sila saida nace ba fadan da zanwa Binta da Abu kace kaisam saina musu gashi abin daya jamin dagir mana da komai na yanko ta cikin unguwa da gudu kowa na kallona Yanzu binta da Abune sukai maka haka a garin nan cewar me gari Liman yace hmmm ni nasan su sarai shiyasa tin farko naki kadage kace sainayi yanzu gurin saukarma ba halin zuwa ta kona babban rigar sukuma wayan nan kaga dai yanda tai musu harda manja a jiki kamar za a Kada miya gashi badamar na koma gida yanda ranta yake a bace Kai kutashi kuje Ku ne mo min su A'a kudawo Ku zauna Allah ya baka yawan rai nayafe Abarsu kawai nidai goggo me tuwo itace kadai damuwata ita taimin hakafa
.
Nan yakwashe duk abinda ya faru yafada wa megari Shine zakace a barsu gwara mu koya musu hankali cewar megari Eh Bakomai a barsu cewar liman To shi kenan zansa a kiramin gogo me tuwo zan mata bayani karka samu damuwa To shikenan godiya nake Allah ya baka yawan rai Kai tsaye suka shiga gidan ba sallama Yaushe zaku girma abin naku kara lala cewa yakeyi ko Abu da Binta cewar Inna Saida suka samu guri suka zauna sannan sukace salama Alaikum Inna tace Allah nagode maka binta da Abu Nura yatafi maka rantar boko Yinme inna cewar Binta Inna tace Yaje saku a maka rantar boko daga nan yamai daku isilamiya dan harda rashin ilimi a abinda kukeyi Abu tace Boko tab ba inda zani Inna bokoko awuta kike nunfin zamu toko su yan bokokon Awuta tsoron bokon sukeyi ba inda zani saidai ko binta gata nan Waaaaniii tab namutu Allah yasani awuta ba bokon da zani cewar Binta
.
Wlh baku isaba haka kuke so mu zauna daku a jahirce cewar Inna Yasin bazani ba wuta tsilim cikin sauki bokoko Awuta bada niba cewar Abu Binta ta tashi daga inda take ta koma kusa da Inna Tace Inna kisa baki akahe maganar nan dan baze taba yiyuba Yasin haka kawai ze Kaimu lahira da kanhi Kanshi kanshi inna taji yana tashi A jikin Binta Tato she hanci tace Binta warin me nake ji haka kardai kema kinhau layin rashin yinwanka Dariya Abu tayi tace Inna nice nan nadorata alayi tam bayeta kiji ita kanta tafijin dadin jikinta yanzu fiye da da Rufemin baki sakarai qazama nayi dake *'YAR KWALLIYA* Binta kiyiwa Allah karki bari Abu ta koya miki rashin Wanka da Wannan maya taccen KWALLIYAR nata Inna saidai kar a kuma dankuwa karatu yamin qanhi yabi jiki bakiga irin kallon da megari yake minba nikadai nagane meyake nufi cewar Binta Abu tace Nagani rabu dahi binta ze fado hannu banda hima ya tema kawa kanhi besa bakiba aida tuni munkoya mihi hankali kamar yanda muka koyawa liman Oohni Inna ina zansa kaina nan nasamu lbr anga liman yana zuba gudu a gari har ana zaton ya Hauka ce ashe ba Hauka cewa yayiba gamo yayi da 'ya'yan Aljanu binta da Abu babban gamo yai cewar Inna Abu kwaso kayan KWALLIYAR muyi muje gidan Amaryar da aka kawo nan bayan layin ku cewar Binta Abu tace Hakane fa banjeba kuwa Tashiga ta dauko ta ajiya a gaban binta Inna tace shiyasa tin farko banso qawan cen kuba wlh nasani sarai cewa abinda kuke da NA yanzu saiya fishi kuma gashi na gani Suka kafe inna da idanu Inna tace bance komai ba ni badaku nakeba Allah yabaku hakuri Suka juya suka cigaba da KWALLIYA Salama Alaikum inna nadawo Wa'alaikumus salam gonda da Allah ya kawo ka Yi shiru Inna nasamu lbr komai inaji nasan sune zasu aika tawa liman haka komai yazo karshe na sasu amaka rantar boko hakama isilamiya ga kayan maka rantar nasu Alhamdulillah shikenan kurinkus kandan bera boko Saikun je kokuna so ko ba kwaso cewar Inna Abu tace Boko Boko dai hikenan naji duk abinda ake fada akan boko ance yan wutane hine mu za a kaimu saboda ba a sonmu Ba a San naku gobe zaku fara zuwa daga nan idan kuntaso saiku wuce isilamiyar malam rabi'u Binta ta tashi ta daka tsalle tace rabi'u Yasin ba inda zani Wannan bakin mugun baki da Wannan kan nahi dayake kyalli kamar an cirohi A tandun mai Malamin naku kinga binta nasan irin takun sakar da kukeyi da malam rabi'u idan kika bari yakawo min karar ki kikuka da kanki irin dokan dazan miki baze faduba harda ke Abu cewar Nura Abu tace hikenan dai zamu leka wutar bakomai amma idan mukaji da zafi bazamu sake koma waba Tsaki Nura yayi yatafi ya basu guri Sukaci uwar KWALLIYA suka fice basu cewa Inna komai ba
.
WASHE GARI Abu tana tashi tasa kayan maka ranta ta janyo kayan KWALLIYA zata yi Nura yace karki sake kiyi KWALLIYA makaranta zaki ba dandaliba Abu tace Tab yaya Nura gaskiya bazan iya fita banyi KWALLIYA ba ga kanhin tirare i nayi Amma ba KWALLIYA a fuska ta Nura yace Eh ba a KWALLIYA idan za aje makaranta Abu dole kidena wasu abubuwan yanzu tinda kinfara zuwa makaranta Binta ta shigo ba sallama agaban kayan KWALLIYA ta zauna zatayi KWALLIYA Nura yace ke Binta ba sallama Bakomai kiwani zo gaban kayan KWALLIYA Binta tace yaya Nura tinda nafito banyi magana da kowaba Gahi yanzu kasa nayi magana Almiskin bakina yafita Hanci yatoshe yace naji Almiskin kice kema kinbi layin qazantar Abu ko makaranta zaku zakuje kuga yanda Ake safta Binta tace *'YAR KWALLIYA* mezan gani haka meyasa bakiyi KWALLIYA ba Abu tace Binta kibarni kibarni kwai ni Abu *'YAR KWALLIYA* ni za a hana yin KWALLIYA badole kiga haka ba Binta tace shine kike daga hanka linki ina Inna Abu tace tana ciki Binta tace yaya I na bayanka gwanda daka hanata bani kayan KWALLIYAR NA shiga dasu au baza kibaniba bari na dauka da kaina Binta na shiga ta juye kayan KWALLIYAR a Jakarta tafito Binta tace bata cikifa Abu tace hakane yanzu ta fita zomuci Abinci bayan sun gama cin Abinci Nura ya kaisu maka ranta Duk wanda yaga fuskar Abu ba KWALLIYA sai yayi mamaki dan bata taba fita ba KWALLIYA ba Suka shiga Aji Binta tace Abu Albishirin ki Abu rai a hade tace goro Binta ta bude Jakarta tace kalli Abu cikin mamaki tafasa kara ta rungume binta ta tsalle a aji Hankalin daliban ya koma Kansu Abu tace muna fukai me kuke kallo da sannu duk zanyi maga ninku
.
Daliban Suka dena kallon su Suka baje kayan KWALLIYA sunayi malami ya shigo aji akatashi ana gaisuwa banda Abu da Binta KWALLIYA kawai suke yi Malamin ya karaso gurin su yace Ku meye haka kwalliya a cikin aji me kukeyi a nan aji bantaba ganin kuba Abu tana shafa Jan baki tace baza kasan muba hime maka rantar be sanar dakai komu suwaye bako hege wato ya cinye kudin ko to hikenan Yace bagane me kuke nufiba fa Binta tace kaga waimu sa babbin dali baine kuma nanne ajin mu kana jiko jeka to Yace kee Nifa malamin kune kibani girma bakowana magana zaki dinga fada minba Abu tace inji kaba girma idan karike girmanka mutayaka rikewa idankuma kaki rikewa mubi takai mu wuce Malamin yayi murmushin keta yace kugoge fuskarku sannan kubani kayan KWALLIYAN Abu tace tab ba abinda zamu baka kuma ni Abu bazan goge KWALLIYA ta ba Binta tace nimadai bazan gege ba malam kabar daliban naka a tsaye fa Yace kuzauna yayi murmushin yaje gaban Allo yafara koyar dasu kamar yanda ya saba Abu tace gaskiya nagaji baza a yi wani abin bane bayan Wannan kazo ka I hemu da surutu Binta tace a he kekina jin hi tinda yafara har I yanzu banji komai ba ni yunwa ma nakeji Yace Anya karatu kuka zoyi kuwa Abu tace waya sani Abu a duhu Nifa karatun higa wutan nan beda meniba dahi da bahi duk1ne bokoko Awuta Binta tace gaya mihi kadai koyarda su dan naga kamar suna gane wa Yace anya Ku muta Nene kuwa ke dawani fuskarki kamar aljana waya gaya miki karatun shiga wuta nake koyawa Binta tace baka jiba bokoko a wuta hine zakace bakaratun higa wuta bane Yace kutashi Ku fita daga ajin nan kufita kuyi shir menku a waje Abu tace seme danka koremu kahiga wutar kaika dai kacike gurin karkabari asa wani Yace keni zaki fadawa haka Tamurguda baki Yadauko bulala ya zuba mata Tasaki kara
.
Binta tace meyasa ka daketa kai ko a qauyen mu mune muke yiwa maza duka hmmm Yace me kike nufi nima dukana zakuyi kenan Abu tace meze hana tinda ka dakeni saina rama Yace waya gaya miki idan malami yadaki daliba tana ramawa Binta taja hannun abu Tace Abu rabu dahi zomu fita ze fito ya same mu damu yake maga mekoya karatun higawuta dole mukoya mihi hankali Suka fita Abu kinga ya aika a siyomai abinci Abu tace waye ya aika asiyo mihi abinci mekoya karatun higa wuta Binta tace Eh hine zomuje Yaron ya siyo abincin zekai wa malam binta da Abu suka tsare shi Abu tace Kai bamu abinci kaje kadebo min ruwa zansha kagani ba quwace Yace malam ya aikeni bari nakai mishi nadawo saina debo miki Binta tace harna hadiyi yawu banga abin dake cikiba amma nasan zeyi dadi tafada tana dariya