A birthday isn't complete without wishes.here is mine for a scintillating year ahead,happy birthday meena parrot.
Page 35
Gidan su badee a cike yake kamar ana wani biki koda na leka yayan gidan ne suduka da jikokai se murna suke lubna na tsakiyar cousins dinta harda masu aure wayanda suka girmeta se sauran sa'annin da yayansu wani sanyi takeji a ranta,
Abduljabbar kam idonsa nakan juwairiyya diyar yaya asama'u itama da naga alamar taga saurayi me kyau daji da gayu daganandai naga yaimata signal sun fita wajen gidan,
Badeee kuwa bacci take irin Wanda harta manta rabonta da shi akan gadon ummansu su Fareeda ko se gadin ta suke lokaci zuwa lokaci umma ke leqowa kutasheta taci abinci farida tace umma kibarta harta tashi daga ganin baccin yaimata dadi,yanzuma zuwa tai taga anyi azahar bata tashiba tasameta azaune tana murmushi su asama'u na mata tsiyar wai tazo sha nono gun umma shine ta bige da Bacci, miqewa kawai tayi tsaye tace muyi sallah mana yunwa nakeji,
Muryar umma sukajiyo tana cewa yawwa dama kenazo natayar wannan bacci haka kuma bakici abinci ba sunhana natashe ki,
Ai umma yanzu natashi sallah zamuyi muci abinci,
Bayan sungama cin abinci suka hallara a palon alhaji yakara bawa badee hakuri sosae daga nan tabasu lbrn rayuwar da sukayi,
Se palon yakoma kamar gidan mutuwa sbd kowa kuka yake se alhaji kadai dayake kallonsu yana murmushi ganin yadda suka rungume juna suna kuka,
To kuyi shiru haka tausayin ya isa tunda gasunan da rai da lpy,
Abduljabbar yace Dan Tsoho don Allah naga amaryar ka kuma ta kwanta min arai ko zaka bani?,
Juwairiya datasan ita yake nufi dagudu ta fita daga palon suka bita da kallo suna dariya,
Abdulrahim ya harareshi yace waikai meyasa bakada kunya ne shikenan daga ganin yarinya,
Badee tace baruwanka kabar min y'ay'ana aini abin farin cikina ne wannan hadin zan hada kuma zeyi kyau,
Yaya mukhtar yai murmushi yace kai abdulrahim dawonan kusa daani inma kanada wacce kakeso ka fadamin ko yar sarkin garin nan ce se inda karfina yakare,
Yana Sosa keya yace dama kanwar mijin lubna ce,
Dukansu suka maida dubansu ga lubna data zaro ido tana dafe kirji,
Yaya asama'u tace yaushe kuka aurar min da y'a ban saniba?,
Lubna tace bafa gaskiya ya fadaba,
Badee tace amma dai kinsan nasan soyayya kuke keda Mus'ab ko?,
Dagudu tafita tana cewa kai mama nidai bance haka ba,
Farida tace to ni wa kuka barmin duk kun kwashe y'ay'an,
Kamar hadin baki abdulkadir da Abdul'aziz suka karasa kusa da ita suna cewa gani mama,
Dariya tayi tace kinga nasamu twins dina ko?,
Alhaji yace to Ku tashi kubani wuri inhuta,
Lubna tana daki zaune itada juwairiyya,laila diyar farida,da jalila kusan dukansu sa'anni ne se rahama dake gefe tana fama da tsohon ciki haihuwa tabiyu kenan zatayi wayar lubna tayi kara tana dubawa taga Mus'ab ne dasauri ta daga,
Baban baby ya akayi?,
Tambaya ta ma kike yau tunda kin hadu da en uwanki shikenan kin manta da miji kuma,
Ni na isa in manta da Rabin raina?kana raina kawai dai tundazu muna tare ne kasan dole hankalina yadauku kayi hakuri kaji habibi,
Rahama tadan tabo lubna,to rasa kunya seki bawa kanki excuse ko kifita can waje in kinga dama ma daga soyayyar seki soye,
Miqewa kawai tayi tana cewa sory sister's,
Daganan kuma suka sha soyayya,
Atakaice dai ranar cikin nishadi suka wuni,
Bayan kwanaki su Abdul suka fara fita aiki yayinda abdulkadir yake final year dinsa shi kuma Abdul'aziz yafara zuwa har sun fara karatu sedai fatan Allah yabasu sa'a,
Badee taji damuwarta ta ragu sosae sedai bayan lafawar komai hankalinta yakoma gun mijinta sotake kawai ta ganshi ko hankalinta ze kwanta tanaji a jikinta kamar yana cikin wani hali,
Wannan karon kuka nake kamar anmin mutuwa Dan ganin majid a tsakar gida kwance duk yafita hayyacinsa sakamakon safara'u data janyoshi tsakar gida zatayi mai wanka yanda ta saba Sega waya ankirata a gaggauce tafita tabarshinan tana cewa jirani zandawo kuma rufe gd zan Dan inno batann,
Anan tabarshi tun ba rana har tazo ta cimmasa nan gashi ko motsi be iyayi se magana yake jini na fita a bakinsa,
Nalura duk lkcn dayake son yin magana sejini yaringa fita abakinsa hakan nanufin anrufe masa bakin ne,
Saurarar sa nayi naji meyake cewa se jinayi yana cewa badi'a,
Akace ko karema yanada rana balle mutum kuma komai Nada lkc yadda komai yake da farko haka yake da karshe yau ina badeen dayake hanawa abinci?yau ina badeen dayake tauyewa haqqi?ina badeen dayabari da Sha'awa bayan yariga yasaba mata da yanayinsa idan bame hakuri bace da tsoron Allah dayanzu ta afkawa halaka,
Wannan tunanin yake yana kuka sosae yana haka Sega safara'u ta dawo haka tawankesa awulakance tajashi tamaidashi daki Sega ta da tarin takardu,
Kai inkana son samun salama ka saka hannu kan wannan takardun karka damu darashin aikin hannunka indai signing zaka mun hannun zeyi aiki,
Kallon papern yayi taga ta gidansace dake sama road gidan daya Dade da ginawa abdulrahim lumshe idonsa kawai yayi baze taba signing wannan ba yafi bukatar mutuwarsa akan hakan,
Kanta ta dafe kusan sati daya kenan yaki signing dinsu dole takoma gun malam,
Ga mahaifiyarta ba lafiya batamasan metakeyi ba batasan wake kantaba
Mayafinta taja tabar gidan gaba daya,
Duk yadda tayi damajid abin yacitura gashi yanzu taji Sha'awa ta addabeta mijinta baze iyayin komai ba,wani alhaji takira kafin ta tattara majid takai shi dakin megadi daga shi se tabarma,
Akace kowa yabar gida gida yabarshi to hakane a gurin sa yabar dangi da iyayensa suma sunbarshi babu menemansa balle yasan halin dayake ciki.
Asia m inuwa sefa kunyi hakuri da lazy writer momma na CE ta shagwaba ni kuma kar kibari tajiki kina cemin lazy Dan bataso atakuramin 😉
Meena parrot nayi late ko?sory baby.
[8/12, 11:56 AM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 36
Kuka yakeso yayi irin dakarfinnan kozeji sanyi amma gani yake idan yayi jininsa ze qare,ahankali hawaye ke sauka daga idonshi addua yake azuci Allah yakawomai dauki,(ina sharar kwalla nima nace ameen😭),
Zuwa yanzu kam badee takasa jurewa bacci ma gagarar ta yake idan tatuna da majid tadora duka laifin akanta meye nata nabaro gdnma tabaroshi da matarda batada imani kokadan a zuciyarta itakam komawa gidanta zatayi koba komai idan tana ganinsa hankalita ze kwanta dama ba korarta yaiba,
Miqewa tai tadauro alwala tayi nafila raka'a biyu da addu'o'i kamar yadda ta saba inta kasa bacci,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,lubna tafada tana zabura dasauri badee tazo kusa da ita,ke menene?,
Mama mafarkin baba nai wai ya rasu,sosae gaban badee yake dokawa tadaure tace kwanta kicigaba da baccin ki,
Mama muje mudubashi,kikwanta nace bakisan dare bane idan gari ya waye zamuje,
Dakyar ta samu lubna tai bacci washe gari tunda sassafe lubna ruwa kawai tadafa wai asha tea fita zasuyi,
Ke ina zaku tunda sassafe dazakibamu tea kawai kintaba ganin munsha tea?inji abdulrahim,
Ai hardaku zamu baba zamuje dubowa,
Babu inda zamu harku ma yana gama fadar haka yashiga daki inda mama Da hajiya,
Eh shi zamuje dubawa tunda shima mutun ne dazakazo ka tsaya min akai kana tambaya ta sekace ubana idan kai bazaka ba bazance dole sekaje ba amma nida lubna zamuje Dan naga alamar kanwar ka tafika hankali sbd tasan darajar ubanta,
Guri yasamu yazauna ganin yadda tadau zafi, mama bawai bansan darajar sa bane abinda yaimana ne bangama hucewa ba kuma banaso muje Wannan matar tasa ta cutar damu don Allah kiyi hakuri,
Shikenan mu mun tafi tafada tana miqewa tsaye, zanbiku nima inji hajiya,
A a yizamanki keda kefama da ciwon kafa kizauna aiba jimawa zamuyiba,
Su abdulrahim suka hau mashin lubna kuma suka tsaya jiran adaidaita bayan sun samu sunatafe wayarta tafara ringing baban baby tagani,bayan sun gaisa yace kina inane naji kamar iska da karar ababen hawa,
Eh muna kan hanya nida mama zamuje can gidanmu dubo baba,bani address din gidan mana nakwana biyu ban ganki ba ga baby tana kuka wai se mama take kiramin,kwatancen gidan taimasa kafin suyi sallama,
Wai nikam wannan bawa akwai kazanta kuji yadda wari ya baibaye gate din nan daka doso kamar ka amaye hanjinka,tab..bari na wankeshi tun ba ayi zaton gawa na ajiye ba.injiw safara'u data dawo daga gantalinta,
Anan tajanyo shi kan tarbarma ta jona tiyo tafara shekamai ruwan,
Su badee kam suna zuwa ba wata wata suka shigo gidan dukansu mutuwar tsaye sukayi suna kallon safara'u dake ta sheqawa bawan Allah ruwa hankali kwance,
Lubna data gano baban sune awulakance haka tai kukan kura ta shaqo wuyan safara'u takaita kasa dakyar abdulrahim ya bambare ta zuwa lokacin har tasoma fitar mata da jini ita kanta lubna tsabar bala'i da safara'u ta shuka a gidan hankalinta ya bar jikinta seda Abdul'aziz yafita gate da ita sekuka take,
Badee kam kan mijin tai tadagoshi batadamu da kazantar dake jikinsa ba,
Majid don Allah katashi ka yimin magana me matar nan tai maka?duk acikin kuka take maganar,
Abdul kukaimin shi cikin gida,abdulrahim yadorashi akafada yawuce dashi toilet din tsakar gida yakai shi kafin yashiga dakin safara'u yadauko sabulu da soso yakawo wa badee,
Ka dauko min kayanshi kaduba adakinta da sauri yakoma dakin yadauko kayan gasunan ajere amma ambarshi cikin muguwar jallabiya,
Sunanta yake kira ahankali jini nafita bakinsa dasauri tarufe mai baki kayi shiru kar jininka yakare,
Sosae ta wankesa ta saka masa kayan abdulrahim yadauko yadawo dashi harabar gidan karkashin bishiya kan tabarma,
Mus'ab yakaraso dasauri Yana tambaya meyasa meta,dasauri taja hannun su ta nuna musu wannan katon dutsen,yaya kudaga shi akwai wani Abu agurin,
Da addua abakinsu suka karasa wurin layune sunfi dozen awurin,Mus'ab yace siyo kalanzir da ashana mukona,
Haka kuwa sukayi suka kona duka,Abdul'aziz yace muje ciki mana,
Abduljabbar kitchen yashiga yasamo wuka yadawo yahau bishiya yakaryo itace masu kauri yadawo inda yabar ta abdulqadir ya tsareta se muzurai take,
Yace ke inkina bukatar kanki da lafiya to ki dauke masa wannan wahalar kuma duk inda kikasan kinsaka wani mugun Abu ciki da wajen gidannan kifada mu toneshi ko wallahi mujibgeki mun jibgi banza,
Shiru tayi tana kallonsa,
Au ba zakiyi magana ba?
Abdul kuzo mufara aiki inaga seta soma jin maza zata fada,
Dasauri tana kuka tace wallahi zanfada,
Badee kam tanacan rungume da mijinta tana kallon ikon Allah se en kananun hawaye da take,
Rana dubu ta barawo rana daya tak tame kaya.
[8/13, 5:35 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Na sadaukar da wannan shafin ga en gidan Sophie G fatan alkhairi agareku.ILYSM❤
Page 37
Nidai ban binne komai a gidannan ba wallahi ciwo ne Allah ya Daura masa banida sa hannu aci....
Kyakkyawan mari abdulrahim yadauketa dashi yakara mata wani dabayan hannu,
Abduljabbar bani itacen nan inaga sena saka jikin ta yaitsami,batayi auneba taji sun soma rangada mata itacen,
Abdulrahim banda duka inji badee,
Mama idan kinajin tausayinta ne seki tashi kikoma cikin gida koki fita waje babu Wanda ze hanamu jibgarta indai bata fada mana gaskiya ba,
Shiru tayi Dan bata taba ganin zuciyarsa irinta yauba,
Azuciyar safara'u kuwa cewa take sedai Ku kasheni bazan fadaba,
Shiru tayi tana kallon su babu alamar zatayi magana,
Aiko suka shiga dukanta kamar ankama barawon daya addabi unguwa,
Zaki fadane kose mun kakkaryaki?
Ganin dagaske suke yasata cewa zan fada wallahi zanfada,akasan zuciyarta tunanin sharadin da bokansu yabasu take tace shikenan tawa takare,
Nan tashiga nuna musu harseda suka tsorata babu inda bata binne mugun Abu a gidanba layu sunfi akirga har wani Abu dabasusan meye ba hardasu rayyyayyen maciji dakunama akwanrya aka Daura wa laya aka binne lkcn da suka hako su daga ramen bayan dakin badee seda suka tsorata Dan macijin sakunamar ba cewa sukayi b'it,hmm
Aiko majid jiyaye kamar andaukemai katon dutse aka jinsa yake wani sabo hannayensa dakomai Na jikinsa suka shiga kakkarwa nan take ya sume agurin dasauri majid yaje mota zedauki waya yakira malam se ganin badee yayi tana bawa baby abinci yana zuwa ta kwadamai harara,
Kabar yarinya ita kadai amota koda nazo tana kuka idan aka sacemin itafa?,
Sory baby bari mugama da wannan matsalar tukunna,
Malam yazo yaduba shi yabashi addua da magani da yardar Allah zedawo daidai,
Ruga gida kadaukomin key din part dina tafada tana kallon Abdul'aziz dasauri yaje yakawo ta bude dakin zanin gadon kadai tayaye aka kwantar da majid,
Safara'u kuwa dakinta suka turata suka kulle bayan sun karbe wayanta ,
Hajiya tazuba ido har tagaji basu dawoba danhaka tamiqe tarufe gidan tana fitowa ta hadu da yayan anty asama'u maza su uku abubakar,Ibrahim da muhsin sunzo gaisheda badee,
Ai batanan sunje can gidan haryanzu basu dawoba yanzuma bayansu zanbi,
To hajiya muje mu sauke ki daganan ma semu gaishe ta mubata sako kuma,
Hajiya tunda taga majid take ihun kuka tanawa tsinewa safara'u dakyar aka samu tai shiru nan en samarin sukayi waje suna bawa su abubakar labarin dukan dasuka yiwa safara'u da abinda suka gani danma har sun kona da sun nuna musu,
Badee kindawo dakinki kikula da mijinki nikuma zankoma da lubna Dan ban iya zama nikadai har mijinki yaji sauki ko,
Kunya sosae takama badee tace uhm kawai tana kaida kai,
Lubna kamar tayi kuka tabi hajiya itafa bata taba bacci ba ajikin mamanta ba Dan haka take bakin cikin bin hajiya tunda suka isa kokallon Mus'ab da baby batyiba tashige gidan tana kumbura fuska bece komaiba yawuce gida saukinsa daya baby bacci take,
Yo lubna Dan anrabaki da uwarki sekizo kinamin kumbure kumbure?to idan kinyi aure senagani koda uwarta ki zaki tafi zoki dora mana tuwo,
lubna kuka taringayi da dare tana kiran mama seda abdulrahim ya rarrasheta kafin tayi shiru tayi bacci,
Majid be farka ba se washe gari tunda ya hada ido da badee yafashe da kuka,
Badee'a don Allah kiyafemin nasan na yimiki babban laifi amma don Allah ki gafartamin gashinan tun ba aje ko ina ba nagane kuskurena,
Yi tayi kamar bata jishi ba ta kauda kanta tana goge kwalla wani sabon sonsa take jin yana tsarata kamar taje ta rungumeshi,
Dakyar ya rarrafa ya rungumeta yana bata hakuri dakyar tajuyo,
Yawuce majid bakada lpy ka kwanta ko zaka iya tashi kayi wanka kayi sallah,
Eh yace yanajinjina hakuri da juriya irin na badee ita takama masa yayi wanka tana kakkauda kai,
Badee'a ina y'ay'ana?
Wani kallo tai masa cike da mamaki,
Cikeda gayya tace dama kanada yaya ne?,
Sosae gabansa yafadi azuciyarsa yace kodai bata hakura bane?.
Wayyo Allah na gaji😩
[8/14, 11:51 AM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 38
Badee'a don Allah kiyi hakuri wallahi nima ba asonraina nake muku haka ba duk yadda naso in kyautata muku se insamu kaina dakasa yin haka,daganan kuma seya sakuka yana kara bata hakuri,
Itafa yasoma bata kunya danhaka ta janye idonta daga nasa tace,
Meye haka kakeyi kamar wani yaro?Dan Allah nidai kabari,ta miqe tana cewa ni Allah ma yasa yarannan suyi hankalin kawomin kayana da abinci nasomajin yunwa,
Jikinsa ba karfi amma haka yamiqe dasauri bari nasiyo miki masa IET,
A'a bari muka zuwa 10 inbasuzoba zanje dakaina nasiyo kaikam yaushe zaka iya fita aiseka fadi ahanya,
Rufe bakinta keda wuya sukajiyo sallamar yaran a palon badee suka tsaya Sega su sunfi to dasauri lubna taje gun mamanta,
Mama ina kwana?kina lafiya? Babu abinda ke damunki dai ko?,
Badee kam kallonta kawai take yadda idonta suka kumbura daga ganin ta kuka tayi,
Majid idonsa suka cika da kwalla,Allah sarki dayanzu yayansa sunyo kansa amma ji karamar ma kota kansa batayi ba lafiyar mamanta kawai take tambaya,
Bazaku gaisheda babanku bane?,
Kusa dashi suka karasa sunayimasa yajiki,
Ya amsa yana zubar dahawaye durqusawa yai ze nemi ga farar su dasauri suka rigashi,
Baba plssss rungumesu yai yana kuka suma sunayi,
Ihu lubna tasa tafadi kasa tana birgima cikeda tsoro suka juyo suna kallonta kafin badee tace ke meye haka sekace wata ta goye?,
Mama bakiga sunrufeshi ba Niko ganin sa ma banyi ba,
Mtsww to shine zaki samana ihu haka?inji abduljabbar,
Dakansa yakarasa kusa da ita yadago ta Ku kyale min lubna ta ai gaskiya tafada yakarashe maganar yana murmushi,
Dukansu sukayi murmushi daganan suka zauna cin abinci,
Shiru babu motsin safara'u badee tace su bude ta ko lafiya shirun yayi yawa kuma abata abinci itama ai mutun ce kamar su,
Safara'u kam nacan reshe yajuye da mujiya se muzurai take tunda ta tashi daga bacci takasa koda motsa Dan yatsanta ne kuka kawai take tana Dana sanin biyewa mahaifiyarta datayi yanzu gashi bataga lpyrta kuma bataga dukiyarda tazo ci Dan sun karbe komai har kudin dake account dinta sun tursasata tatura su account din majid domin dama ba nata bane,
Sosae badee'a ta tausaya mata majid yace sukira bakanike ya duba lafiyar motocinsa zasu maida safara'u kware inda mahaifiyarta,
Haka kuwa akayi dukda badee bataso tafiyarba amma babu yadda zatayi haka suka hada kayan safara suka miqata kware babanta yai kuka kamar ransa ze fita dakyar suka rarrasheshi dganan majid yabawa safara'u takardar ta saki biyu babanta yace kayimin daidai Dan haka ke Hajiya tunda kindan samu sauki seki cigaba da girban abinda kika shuka gashinan tun ba aje ko ina ba kinfara gani dama Na fadamiki inasane daduk abinda kuke kuma Allah baze kyalekuba koda dabba kika cutar balle Dan Adam rai yakai hamsin Wanda kika saka cikin mawuyacin hali saboda biyan bukatarku ta banza,hmm
Daganan suka dawo sokoto gidansu badee suka fara zuwa majid yanemi ga farar su suka yafe mai suka karayimai nasiha sosae yai godia,
Umma tace badee'a zo inason magana dake,
Ke kina ganin babu matsala ko?banason abinda zekara cutar min dake,
Umma babu wata matsala kibari idan hankali ya kwanta zanbaki labari yadda zakifi gamsuwa,
To shikenan Allah yayi muku albarka,
Ameen,
Part din safara'u majid yasa aka kwashe mata kayanta kaf aka tura mata kware,
Part dinsa suka koma yasa aka gyara gidan yai kyau,yaje dasu Abdul kasuwa suka ga shagunan kasancewar baya nan yasa shagon duk arufe yaran sa sungaji sun rufe sun gudu da Dan cinikin dasu kayi,
Office ma yaje yai reporting abinda yafaru kuma yana bukatar Hutu yakara warwarewa,
Wai!duniya sabuwa Dan har hajiya aka dauko ta dawo gidan danta da zama lubna ko da dakinta kullum zatayi bacci setayi kuka wai an rabata da mamanta,
En uwan badee da yayansu wuni guda suka yiwa badee agidanta abinci har seda suka gaji daganinsa lubna Dan ba'asaba ba taci abinci har babu iyaka ranar seda taikiba ta musamman,
Badee tafito daga wanka sotake ta kwanta tahuta tasha yawo har tagaji,
Tana tsaye gaban mirror taji an rungumeta,majid mai zan shafa fa,
Bana bukatar jikin ki da mai,yahade bakinsu,dasauri tazare bakinta tace,
Lahhh meye haka sekace yaro?
Nafi Abdulrahim jin luv da kuruciya daganan sukayi gado,
Ai a 200 nabaro dakin ina dafe kirji wannan luv haka sekace meela da adeel😉
[8/15, 12:58 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 39
Bayan awa uku nadan leqa don in gani ko akwai wani rahoto dazan dauko,lahaula wata sabuwar soyayyar dagani yasa nayiwa kaina kiyamullaili nabar gidan gaba daya sedai zuwa gobe daidai komai ya lafa😉
Washe gari seda nai wanka nai sallahn asuba ko kwalliya ban tsaya yiba nakama hanyar domin da kafa zani babu kudin adaidaita kuma nakafe kai dafata sena dauko muku rahotonnan saboda nacika alkawarin Dana dauka,
Bansamu isaba se karfe takwas harda rabi,
Majid kasa ke ni mana intashi kofa sallah bamuyi ba kalli yadda rana tafito,
Dasauri yamiqe zaune yana murtsike ido,
Subhuhanallahi Ashe munmakara haka ya'akayi,
Ka tambayeni ya akayi bayan Kaine ka hanamu bacci,
Munacin lokaci tashi muyi wanka,
Kadaiyi ninayi dakina,tattara kayanta tayi tabar masa dakin sefaman murmushi yake seyaimin kamar wani ango,
Zaune tasami lubna fuska shabe shabe da hawaye,
Ke meye haka kika zauna kina kuka?,
Bake bace kinsan bamu kwana tareba kuma baki fito ba seyanzu kuma ni inaso inganki,se wani sabon kuka,
Waike yaushe kika lalace da wannan shagwabar?inace aure zakiyi?shikenan kuma sekice danmun saba kwana tare yanzu bazaki kwana ba seda ni?kinada aiki ja agaban ki maza tashi kiyi shara da moping,
Tashi tayi tana turo baki tafice daga dakin ta share ko ina har tazo dakin badee ta sameta zaune kan sallaya,
Zama tayi tana jiranta harta shafa adduarta,
Mama wai sallar me kikayi yanzu?
Kingama shara da moping din?,a'a nadaiyi shara nan dakin zanshare senayi moping,
Shine kika zauna tambayar abinda be shafeki ba?to ki tabbatar kafin nagama hada breakfast kin kammala shara Da moping,
Hmm,kawai tace tacigaba da aikinta,
Tana zaune adakin badee tana game awaya Sega kiran Mus'ab,
Ummm uhm uhm nikam na shiga uku kabar sona tafada tana kukan shagwaba,
Kekam yaushe kika sangarce haka komai shagwaba?,bakaibane kusan awa ukufa yanzu baka kiraniba,hmm yi hakuri nidai yanzu baba na nan zanzo ingaisheshi ne,
Eh yananan befara fitaba tukun,OK to gani nan zuwa,
Majid anzama baba yazauna shida Mus'ab se labari suke ya yaba da hankalinsa sosae kuma yaimasa godiya akan taimakon daya yiwa su badee,
Babu komai baba ai yiwa Kaine dama nazo ne neman izinin zuwa gurin lubna kafin naturo magabata na ayi magana tunda naga insha Allah komai ya daidaita,
Babu komai Mus'ab insha Allah zaka iya cigaba Dazuwa,
Sosae yayi godiya kafin yaimasa sallama yafito a harabr gidan suka sha hirar soyayyar su kafin yawuce,
Bayan sati biyu Mus'ab yaje gidan yayan mamansa dakuma kanin babansa Wanda yaje babu Wanda be zubda kwalla ba acikin su sbd watsi dasu kayi da zumunci suka ringa Neman gafarar sa yafada musu cewar dama za aje nema masa aure ne ranar asabar me zuwa iyayenta suka bashi yaturo,
Ranar Saturday akayi magana kuma an bawa Mus'ab lubna,majid sukaje gurin iyayen juwairiyya nemawa Abduljabbar aurenta sekuma safnar abdulrahim wacce bansan lokacin da suka dinke ba seganin majid nayi da sauran mutane sunje gidan dayamma alhmdllh komai yatafi yadda akeso sedai majid yace se ayi hakuri da auren se bayan sundawo aikin hajji shida iyalansa,
Ai lubna dataji labari dagudu taje ta rungume babanta tana murna wani sanyi majid yake ji azuciyarsa yace wai dama Ashe haka yaya suke jiyake kamar ya hadiye su,
Baby kinji baba wai sekunje hajji kindawo nifa nagaji na matsu wallahi senan da wata uku fa,
Kadaina kirana dasunan yata kuma bangane ka gaji ba ka matsu dame?,
Naganki matsayin matata mana bakisan yadda nakeji bane idan nace inason ki sosae senaji kalaman sunyi kadan,
Uhm kayi hakuri kaji Dan samari kamar gobe ne insha Allah,
To Allah yakaimu lokacin da rai da lafiya,anjima zan kawo miki baba Dan safna zataje gidan kawu kwana biyu kafin ta dawo,
Aikam dai wallahi nayi kewarta ina zuba ido,
To shikenan en mata na se anjima.
Soyayya ruwance inkasha sekaba masoyi nima nasha naba nawa masoyin😉
Kamar yadda meenar parrot kebawa masoyinta abdul😜
[8/16, 11:57 AM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Ameera IbrahimY'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Ameera Ibrahim wannan shafin nakine dalilin kyautar dakika min jiya har mafarkinnayi nasiya miki mota😎 Allah yabar soda kauna ameen.
Page 40
Alhamdulillah su lubna andawo daga makka se shirin biki ake domin saura sati biyu adaura aure majid bakin nan yaki ruhuwa ze aurar da yayansa su uku sejinknsa yake daban kamar ba shiba,
Hello ramla banason wulakanci tun dazu nake kiranki kinki dauka,
Dalla kirabu dani da abinda yake damuna dama yau nake da niyyar zuwa hargida infada miki salim ya takura seda aka matso da date din bikinmu kusa bayan tafiyarku jibi za afara bikin ga ankonki nan nasiyo miki shi zanzo nakawo miki bansan kozaki samu zuwaba tunda kema ankusa bikinki,kawai seta fashe da kuka,
Ke kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa bari gani nan zuwa gidannaku kuma biki aidole dani za'ayi koda kuwa ankaini yaune akafara bikin washe gari senazo bare ma akwai sati daya a tsakani,
Ajiyar zuciya ramla tasauke,to shikenan amaryar Mus'ab sekinzo,
Yawwa matar salim,
Ranar Saturday saura sati daya bikin su lubna kuma aranar aka miqawa salim matar sa ramla sedai fatan asha amarci lafiya,
Majid dakansa yatura abduljabbar kware yakai wa goggonsu invitation arabawa dangi Dan hajiya tayi rantsuwa lubna bazata kuma fitaba se an fara biki,
Takowane bangare se shirye shirye ake safna ma se gyara ake sha juwairiyya yaya asama'u tace ta tattaro tadawo inda lubna susha gyaran tare dakyar ta samu tazo wai ita kunyar badee takeji koda tazoma tana dakin lubna babu abinda ke fitar da ita idan badee tazo kawo wani Dan abin gyara da gudu take shigewa toilet sbd kunya yauma suna zaune da sassafe badee ta shigo da Dan hadinta a kofuna da sauri riyya ta miqe zata gudu,
Inkika sake kika shiga bayinnan wallahi sena ranqwasheki uban wa kike kunya anan?tsaf zan zaneki danni ba wuce duka kuka yi agurina ba maza zoki karba ki shnye ina gani Dan nafara zargin zubarwa kike,
Lubna tace nikam mama bani idan wannan me dadin ne kuma wannan Dan karamin kofin baze isheni ba,
Sannu kekuma rasa kunya,tunzuro baki tayi,
Ahankali juwairiyya tazo takarba tazauna tana sha a hankali harta shanye,
Badee na fita juwairiyya tacewa lubna waike baki gaji da waynann abubuwan bane da ake dirka mana nifa nafara jin yanayi kumama nikam banaso suyi yawa naje ya hallakani a banza,
Wane irin hallakawa sekace baya sonki Nikam wannan kazar ne bazan tabaci ba bakiga ba akawomana ba?ninace karsu wahalar dakansu wallahi gara wannn kodan dadin sa zaksha,
Juwairiyya tayi dariya kawai Dan ita mamakin lubna take yadda bata iya boye abinda keranta,
Biki kam anshashi har angode Allah ranar Saturday da safe aka Daura aure da dare misalin karfe Tara aka miqa kowacce dakinta bayan sun sha nasiha lubna kam ita aka kai karshe Dan maqalewa tai jikin badee tana kuka itafa seyanzu da za akaita tagane tafa bar gidan kenan danhaka taringa kuka seda majid yazo ya rarrasheta tana rungume jikinsa yakaita mota,
Hmm lubna amarya.
Abdulrahim kam da abduljabbar basu yi wata wataba suka angwance daganan suka kwashi baccin su me dadi,
Bangaren Mus'ab da lubna kuwa rarrashinta kadai seda suka kai karfe dayan dare kafin suyi alwala suyi sallah dacin kaza seda yadaukesu awa daya,
Wayyo yaya bacci nakeji,tab..yace wannan karatun dolene yau kibari idan kingama dauka sekiyi baccin kinji daganan al'amura suka chanja (dama ni bana tsayawa daukar irin wannan rahoton saboda dalilai danhaka nafito najamusu kofar sedai fatan Allah yabada zuri'a Dayyaba ameen),
Washe gari misalin 10:12 am tafarka dasauri ta tashi zata miqe,
Wayyo Allah na tace takomawa zaune,shikenan yakassarani mama kizo kigani ban iya tafiya tasa kuka,
Gogan cikin bacci yajyo kukan lubna dasauri yatashi,
My lady ya akayi?sannu kinji,bari na hada miki ruwa namiki wanka,
Banda kuka da shagwaba tana kara narkewa babu abinda take,
Bayan sunyi sallah yace,my lady Kindaina jin zafin?,
Juya fuskarta tai gefe tana jin kunya tace um um,zo induba kose anyi Dinki ne?,
Nikam ka kyaleni jikina duk ciwo yake kuma bacci nakeji,
To ki kwanta bari naje nasiyo miki magani kinji,
Abdulrahim kam yarasa inda ze tsoma kansa Dan dadi ko motsi safna tayi seyace sannu,
Wani Abu dayake ban dariya shine koda naje abduljabbar da juwairiyya kunyar juna suke ji sunkasa hada ido,
Yaya asama'u ita tai abincin aka kai musu suka ci,
Lubna na zaune a Palo Sega kiran safna awayarta,
Matar yaya,inji lubna
Matar yaya Mara imani,
Yayanki daine bashida imani muryata seda tadaina fita,
Dan bakiga abinda yayanki yaimin bane ke ko tafiya ban iyayi fa,
To uban waye yake iya tafiyan dalla daga chan ni se anjima maganama wuya take min,
Sosae safna tai dariya kafin suyi sallama.
Dana sani na tsaya najiyo ihun Lubna koda shine nayo recording amma nextym video zanyi Basenasha wahalar typing ba 😉
[8/16, 8:35 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 41
Bayan wata daya da en kwanaki lubna ta soma laulayi duk abinda taci seta Harar yauma zaune suke itada Mus'ab da yamma ya karbo mata tuwo gun momynsu,
My lady pls tashi kidanci koda loma goma ne kinji,
Nikam kabarni idan naci amai zanyi,ba zakiyi Amai ba kina ci zanmiki alluran daze hanaki Amai,
Dakyar yasamu tadanci yaimata allura yace tadan kwanta kafin yaje masallaci yadawo tasamai kuka dakyar ya rarrasheta tabarshi yafita gashi ta hana ya fadawa kowa tunjiya ta rikice,
Sallar magrib kadai tayi agurin tafara Amai tanayi tana kuka ahaka tayi kokari ta gyara gurin,
Sallahr isha'i ma azaune tayi saboda jiri take ji tana gamawa sewani aman gabadaya ta gama galabaita kuka kawai take ahaka Mus'ab ya zo yasameta abokinsa yakira yataimake sa yakawomai ruwa da magani baze iya fitaba zesaka mata drip din agida,
Mus'ab gara ka kawota asibiti kawai tunda batada lpy sosae bekamata ka ajiye ta gidaba Dan kana takamar kai likita ne tana bukatar kulawa sosae amma fa shawara ce,
To shikenan Ibrahim gamunan zuwa Dan wallahi ko magana bata iyayi nagode,
Shege Mus'ab sharp shooter haka fa ka yiwa jamila kaikam bakasan dadin amarciba,
Kujimin Dan iska dallah nidai gani nan zuwa banza kawai,
Suna zuwa akayi admitting dinta akaimata komai daya kamata tasamu bacci,
Se washe gari yakira gidansu yafada hankalin badee sosae yatashi tafada wa majid tare sukazo lubna na bacci majid be jima ba yawuce kafin yamma asibiti en uwa duk sunzo dubiya zuwa lokacin ta farka amma takicin komai ita tsoro takeji,
Safna,juwairiyya, Rahama da babynta,laila da ramla duk suna dakin badee taje gida tayo wanka,
Safna tace,waikukam bakuda uzuri harkun abinnan?, tayani fada inji juwairiyya duk kwazaban yayanki dai ba asamu rabo ba,
Ita dai kallonsu kawai take batajin zata biye musu amma Wallahi tanajin sauki duk seta fige su Dan seta rama,
Se dariya suke suna kiranta me hazaqa aiko taji bazata iya hakuri ba majid na zuwa tasoma narkewa a jikinsa tanace wa,
Wayyo My man yunwa nakeji,ko inbaki abincine zaki gwada ci ne?,nikam ba zanyi Amai ba?,insha Allahu bazakiyiba, miqewa yai yadebo tuwo kadan a plate ya leqa toilet ya wanke hannunsa yadawo yazauna yanajanyota jikinsa,
Su safna anzata abin Na kallo ne kawai sesukaga yafara bata tuwo abaki tanaci tana kukan shagwaba ahankali suka silale waje suna fita se dariya juwairiyya tace kai amma wallahi lubna er iskace kukaga yadda tabamu kunya fa,
Safna tace aitayi maganin tsiyar damuke mata,
Seda tai sati daya a asibiti tadanji sauki ta matsa aka sallameta,
Wanka tai taci abinci ta kwanta Dan dare yayi Mus'ab ma wanka yayi suka ya kwanta yana janyota jikinsa,
Cikin dare yaji kamar lema akasan su dasauri yatashi yakunna wuta,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, jini duk agadon lubna se baccin ta take Tashin ta yashiga yi tashinta yai daidai da murdawan maranta dasauri taduba jikinta ihu ta kwalla shikenan se suma jinin kuma kamar ankunna famfo sekara zuba yake kwasar ta kawai yayi sukayi asibiti,
Zama nai akasa na ringa ihu INA gun jin kuka nashiga uku har na hangomu ranar suna munacin rengem😭🙆🏻,
Kafinma su isa cikin yafita dafe kansa yayi kamar zeyi kuka se Ibrahim ne yai kokarin tsayar mata da bleeding din tasamu bacci se kusan la'asar ta farka sekuma ciwon Mara haka taringa wahala kuka kawai take tana juyi tasha injection kamar me amma bawani chanji,
La'ilaha illallahu yarnan haka kike wahala?wannan cikin ya gwada miki boni sannu kinji inji hajiya se kuka tana kamawa lubna,
Har kusan magrib Abu yakici yakicinyewa,
Ji tayi tagaji da gadon ma kasa takeso ta kwanta batasan lokacin da ta fizge cannula din hannunta ba ta fado kasa ta kwanta tana kiran mama,
Mama Dan Allah kitaimakeni marata jinake kamar zata fita baba kutaimakeni wallahi mutuwa zanyi,
Mus'ab ji yayi kuka yazo masa amma yadannne kmata yai yamaidata gadon yasa auduga yana danne gurin data cire cannula din sbd jini dake fita,
Sannu lubna kidaina wannan ihun kina addua kinji?,
Wayyo Mus'ab kaceci rayuwata incikinnan ne ke min haka Dan Allah kuciremin shi inba hakaba shine ajalina,
Bashi bane yi hakuri kinji bari Ibrahim yakawo allura insha Allah daga anmiki ita zakiji sauki,
Mus'ab nagaji da alluran nan kuciremin cikinnan don Allah,
Majid ne yashigo yariko hannun ta lubna kiyi shiru kiyi addua ba ihuba kinji kuma kidaina zancen aciremiki ciki kinji?,
Baba harda kai baka sona?yaushe kabar sona?don Allah kutausaya min bakusan me nakeji ba wallahi jinake kamar zan mutu,
Abdulrahim dake gefe yaji hawaye Na kokarin zubo masa da sauri yajuya yai waje yana kuka kamar yaro baze juri ganin er uwarsa hakaba yana jin sonta fiye da tunanin me karatu,
Mama kema kinbar sona?to kice sucire mun cikinnan nasan ke kinaso na,
Na lura lubna bata hayyacinta danhaka dasauri nabar dakin inata kuka kuma nace sena fadawa mamana😫😩.
[8/17, 6:18 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 42
Shiru ta lafe jikin Mus'ab ahankali bacci ya kwashe ta tana sauke ajiyar zuciya,
Washe gari garau ta tatashi sedai Dan abinda baza arasaba kafin yamma ta wartsake se shagwaba take zubawa,
Kwana daya ta kara aka sallameta badee ta wuce da ita gida seda tadan kwana biyu gidan badee tace mijinta yazo yadauketa takoma gidanta suna zuwa Momy tace takoma part dinta seta kara samun sauki wannan wahala haka aidole tahuta sosae,
Sega lubna tana kasa dakai yanzu kunyar Momy akeji,
Subhuhanallahi yaya meya sami safnar?,ohh harkun dawo gida?OK to insha Allah inanan zuwa yau idan Abu Zara yadawo,ahh haba aisena zo karma kace a'a akwai ma zancen danake so muyi da safnar,to shikenan Allah ya inganta mana,
Tab...su safna angama yimin tsiya Ashe ta kwasa,hmm
Aikin ta tacigaba dayi tana goye da baby,
Baban baby kagama cin abincin nan dasauri muje dubo safna wai batajin dadi,
Meyake damunta?kwazabar Ku kedamunta mana ciki ne da ita amma ba serious ne ba ciwon kawai kasala ne,
Safna dama haka en gdnku suke?kema bakida dangana daga zuwa har kinyi wannan,
Er iska baznji haushi ba ai nasan ramawa kike,
Dariya sukayi daganan suka shiga hira har dare lubna ta koma gida,
After two month lubna ta sake kwasar wani sedai wannan daga bayyanarsa ya fita tasha wahala kamar wancen Dan haka tana Dawowa gida bayan kwana biyu tana zaune gefen gado Majid na shirin fita office tace,
Dan Allah nikam yau idan zaka dawo kadawomin da maganin planning mana,
Maganin planning? Waye zesha?yakamata taje asibiti kafin tafara sha,yafada yana yagyara belt dinsa,
Nice zansha fa kaima kasan yakamata na huta koda shekara dayane?,
Waike meyasa kike Abu kamar bakida hankali?kawai Dan kinsamu miscarriage sau biyu sekice zakiyi planning? To wallahi ban yadda ba kuma idan kikayi aboye bazan taba yafemiki ba,
Ai dole kace haka tunda bakaine kasha wahalar Dana shaba,
Koma dai menene inkinaso musami matsala dake to ki gwada yin abinda kikace wallahi me rabani dake se Allah shashancin banza,
Sosae ranta yabaci Dan haka tace, ni wallahi senayi inba haka ba sedai in bar maka gidanka bazan zauna inna dauki ciki yana wahalar dani kuma inma yafita sena wahala ba kuma ace bazan dauki mataki ba ai hutawa nace zanyi ba cewa nai bazan kara dauka ba,
Wannan maganar da jahili yaita bazanyi mamaki ba amma kisani kekam kinban mamaki kuma Dan Allah karki fasa,
To shikenan zakaga jahilci kuwa,
Fuuuu ta fice kayan ta ta hada tabar gidan yadda zuciyarta tazo wuya,
Yana kallonta ta hau adaidaita ransa abace yanufi wurin aiki,
Lubna meye haka daga INa haka kika kwaso kaya?,
Mama Mus'ab ne,meyai miki?,wai Dan nace zanyi planning shine yarufeni da fada kuma yana fadamin bakaken maganganu,
Lubna shine kikayo yaji?,Tass..ta sauke mata mari kafin tacire sleepers din kafarta tashiga dukanta,
Ashe bakida hankali,dakika zo nan uban me zanmiki,maza dauki mayafinki kibarmin gida babu ubanda ze rakaki ni haka kikaga nayi wace kalar wahalar ce ban shaba da bazaki kwaikwaiyo da halinaba kiyi hakuri billahillazi idan kika kuma yin yaji kikazomin nan sena kusa illataki balle wannan banzan dalilin naki dabe taka kara ya karya ba,
Lubna da tuni tasoma nose bleeding tabi hanya babu mayafi se dankwali kawai akanta,
Mus'ab jiyai baze iya hakura ba bari yabi bayanta yana kokarin shiga yaci karo da ita zata fito badee na bayanta da mayafinta ahannu tana kiranta amma ko juyowa bataiba,
Riqeta yai sosae amma dakarfi ta kwace dganan tashiga buga kanta duk inda tasamu dakyar ya riqeta ya lalubo numbern malam ya kirashi yazo addua yaimata se bacci,
Mus'ab tashi kaje gurin aikinka kaji bayan azahar daidai tafarka sekazo ka kwashe ta Dan bazata kwanarmin agida ba,
Godiya yai yafita daga gidan yana cewa dole Na kiyaye bacin ran lubna wannan bala'i haka dabadan nazo ba haka zata fita ana kallemin jikinta,
Koda yadawo daukarta har suka isa gidan ko kallon sa bataiba bata fasa bashi abinci ba haka tashiga kitchen tadafa abinci me rai da lafiya,
Da dare taje gun momy,lubna lafiya jiya bakizo kin karbi baby ba kuma da safe bakizo ba mun gaisa nace ko lpy larai ta dubomin tace bakwanan,
Eh Wallahi bacci ya kwasheni jiya se 11 nafarka shiyasa banzo ba kuma d sassafe naje gida banjima da dawowa ba,
To lafiya daiko,lpy lau fa kawai dai naje ne,
To shikenan babyn nacan tana bacci tagama rigimar Neman ki,
Ai dole tawuni ta kwana bataga uwarta ba bari nadauki abita mutafi nayi missin shagwabarta,
Momy tai dariya kawai tana jin dadin yadda lubna ke kula da baby.
[8/18, 8:59 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 43
Wanka tayi tayiwa baby duk yana zaune amma ko kallonsa batayi ba secin magani take,
Kwanciyarta tayi bayan ta musu addua tashafe jikinsu da ita ganin haka yasashi cire jallabiyar jikinsa ya hau gadon ahankali yadauke baby yakaita gefe yamaye grubinta jikin lubna jin tadan matsa baya yasa yagano idonta biyu danhaka yafara laluben kalmomin da ze rarrasheta,
My lady don Allah kiyi hakuri dukda nasan inada gaskiya akan abinda kike shirin yi kiyi hakuri mu cigaba da rokon Allah insha Allah daga kinkara daukar wani cikin zamu dauki matakin da idan Allah yataimaka baze fita ba amma don Allah ki fahimceni inason naga Dana ko yata daga gareki kitaimaka muyiwa babynmu kani ko kanwa kinji,
Allah nagode maka daka azurtani damiji me sanyin hali nice nai masa laifi amma shine yake bani hakuri Allah ka bamu zaman lafiya dahakuri Allah ka kauda shedan a tsakaninmu,
A hankali tafara kuka tana kara shiga jikinsa,don Allah kayi hakuri kayafe min daga muryata danai akanka dakuma fita danayi bada izininka ba,
Ohhh nahakura maman baby kinsan banason kuka musamman naki muyi bacci kinji,daganan nikam nadawo gidan babana na rungume nawa sweetheart din (pillow😩) dakyar nai bacci,
Washe gari yanata sauri ze fita yayi letti sun fito kenan tayo masa rakiya Sega wata mata da zumbulelen hijab tsayawa sukayi suna kallonta harta karaso kusada su,
Durqusawa tai gabansu tafara rero kuka,Mus'ab don girman Allah kayi hakuri abinda nai maka kagafarta min don Allah Badon halinaba wallahi rudin shedanne da zuga daga wurin Momy gashi ta rabani da mijina da yata mafi soyuwa agareni wallahi ba laifina bane,
To da farko dai na yafemiki domin Allah ma munai masa laifi kuma ya gafarta mana amma kisani tunda nake ba aimin abinda ya batamin rai ya tabo zuciyata irin wannan ba,Dan haka gaskiya tsakani da Allah bazan iya kara zaman aure dakeba ina rokar miki Allah daya baki wani mijin Wanda yafini ga yarinya ta nan Allah da ikonsa ya rayamin ita cikin koshin lafiya,
Allah ya isa taringa jerawa Momy aranta kafin daga baya ta share hawaynta,ta miqa hannu ta karbi baby sosae takejin sonta na ratsata hakika tayi wauta da rashin hankali data yarda ta wofintar da rayuwar er ta tun tana cikin tsumman goyo,
Don Allah ka yimin alfarma daya inaso adan ringa kaimin yarinyar nan koda na awa dayane domin na ringa ganin ta,
Dama Waze raba da da mahaifi?zata ringa zuwa ganin ki bakida wannan matsalar,godiya tai musu kafin tashiga bangaren Momy itama taneme gafararta akan rashin kunyar da taimata,
Anan kuwa tagafar tamata takama gabanta,
Kishiyar Momy wacce itace silar faruwar duk wani mummunan abu agidan tazo tana Neman gafara ganin yadda Allah yai da ita yasa suka gafarta mata bakinta kadai ke aiki banda shi babu wani Abu mnajikinta dayakeda amfani,
Da room freshener na ahannu nashiga dakin da safara'u take amma se kamshinsa ya hade da mummunan warin dake tashi adakin akwance nasameta kan tabarma,
Yo waike kukan ubanme kikewa mutane duk kinbi kin suna daki da azababben wari wannan warin Allah ya agajeni karya kasheni sbd masifa munyi yawon asibiti har mun gaji amma babu wani ci gaba duk Dan abinda natara ya kare gurin neman magani wallahi bar ganin ki kwance zan wanwanka miki mari bakar munafuka,
Mahaifiyarta ke wannan masifan ta miqe a dudduqe takarasa dakinta Dan tuni tamaida safara'u dakin ajiye shirgi acewaeta bazata juri wannan warinba,
Baban safara'u ne yabiyo se shiga gidan a hankali yajiyo muryarta tanakiransa saboda tausayinta dayake ji yasashi shiga dakin yana toshe hanci,
Baba don Allah kakiramin su badee'a in roke su gafara ko zan samu sassauci,
Hawayensa ya share yace Allah yasa zasu yafe miki nima tabarma nazo dauka domin su majid din sunshgo gari yace badee tana tafe itada lubna sunzo ganin gida,
Aidasauri tace kataimakeni ka kiramin su inrokesu ko Allah zesa su yafemin domin na cutar dasu,
Majid kam warinta yagama isarsa kuma bayajin ze iya yafe mata danhaka yajuyard fuskarsa gefe,
Cikin muryar kuka da tsantsan tsoro badee tace nayafemiki safara'u Allah yayaemiki wannan lalurar majid don Allah kayafe mata bakaga halin da take cikina,
Tunawa yai duk laifin dayaiwa badee batareda ta tsaya wani tuna niba tayafemasa kuma yaiwa Allah laifuka da dama yana Neman gafarar sa meze hana yafewa wannan matar kila sanadiyar haka shima Allah yayafe masa,
Babu komai mun yafe miki Allah ubangiji yatakaita wahala,
Yana gama fadar haka yai waje,anan badee tai musu Dan ihsani kuma ta roki inna da ataimakawa safara'u da wanka lubna kam jikinta duk amace yake kalli wannan matar katuwa ji yadda takoma batada maraba da kwarangol,
Allah ka gafarta mana zunubanmu wayanda muka aikata da gangan da wayanda bamusan mun aikata ba
[8/19, 1:38 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 44
Hello yaya abdulrahim ina wuni,
Lafiya lau sisi yajikin ki?,
Naji sauki sosae gashi ma ina shirin zuwa muku wuni yau,
Kin cika yawo kuma gashi lafiyar ma bata isheki ba to yau bama nan,
Kuna ina yaya,tafada muryarta kamar zatayi kuka,
Muna asibiti safna ta sauka dama shinakira nafada miki,
Wani ihu datayi seda tasauke wayar daga kunnensa,
Tsaya mana hajiya,
Yaya me muka samu?,
Baby boy,
Aiko ganinan zuwa dama a shirye nake,
Bata jira ya amsaba ta katse wayar,
My man tashi muje asibiti safna ta sauka munsamu baby boy,
Alhmdllh, amma kidaina wannan tsalle tsallen karki mana wata barnar,
Murmushi kawai tayi tace bari naje Na fadawa Momy kilama zata bimu takaiga jika,
Dariya kawai yayi yabi bayanta,
Bayan ansallamesu abdulrahim yayo gidansa da ita badee takirashi awaya,
Nace kamayarda safna gida acan zatafi samun kulawa lubna tace kayi can gidanka da ita,
Yanzu mama seta koma gida?harfa se bayan kwana arba'in,
To rashin kunya zaka yimin?,kokuma shawarar ka nanema?,
A'a yace murya a sanyaye,to kamaida ita gida zatafi samun kulawa,
Badan ransa yasoba yai yadda badee tace,
Yanzu cikin lubna yana wata hudu kenan,
Yau ake suna kasancewar gidan za ayi suna yasa en uwa zuwa suka tare part din lubna tunda sassafe zasuyi aiki,
Ta fito zata fada musu ga abinda za ayi Mus'ab yajnyeta daki sunyi jira har sun gaji Dan haka suka fara gyara kayan miya,
Ke Zainab tunda ke gidan yayanki ne danje ki kwankwasa musu rana keyi fa ga mutane sun fara zuwa amma ba agama abinci ba,
Zainab diyar kawunsa ce zuwa tai ta kwankwasa kofar lubna na zaune gefen gado da hand dryer hannunta tana busarda gashinta Mus'ab kuwa yana tsaye yana Daura agogo tsintsiyar hannun sa tace waye? Zainab ce wai anty juwairiyya tace kifito rana nayi basusan meza afara ba,
Zainab ki shigo bana jinki,itakam tsaye tai jikin kofar taki shiga Mus'ab yagama shirin sa yai mata sallama ze fita taimasa Allah yakiyaye ,
Kishiga mana Zainab kika tsaya anan,shiga tai duk kunya ta isheta tace,
Yaya lubna aiki fa mukeda kikazo kika zaunan nan tundazu,
Laifin yayanki ne meyasa baki masa fada ba seni zakizo kinawa Turin baki nidalla mikomin doguwar rigata cikin wardrobe dinnan tafarko daga sama zaki ganta nasa mutafi karku cini gaya babu miya,
Dariya Zainab tayi tace to kiyi sauri,
Atakaice dai sunan yayi dadi yaro yaci suna abubakar sadeeq Allah yaraya mana,
Ramla ma ta haihu tasamu baby girl sunanta Aisha juwairiyyan abduljabbar ma ba abarta abayaba seda ta suntulu yarta mace kamar lubna tayi kaki,nan abduljabbar yaiwa badee'a takwara suna kiranta mami,
Lubna kadai ta rage ta sauke nata Dan har ta koma gida saboda kumburi babu abinda take iyayi se salla shima dakyar tana numfarfashi har ta gama badee bata bari tai komai kullum tana kwance,
Lubna tana zaune wayar badee na gefenta taga yaya asama'u Na kiranta miqewa tai dakyar tayi hanyar palon majid da wayar a hannunta,
Majid na zaune kan doguwar kujera badee tayi pillow da kafafuwansa da alama ma bacci take dasauri lubna ta juya zata fita majid yace,
Daughter zo mana ko jikin ne?,
A'a baba wayar mamace ake kira shine nakawo mata ta ajiye wayar kan center table tafita da murmushi a fuskar ta,
Se sukan la'asar badee ta farka da sauri ta miqe saune,
Haba majid meyasa kabarni inata bacci haka?gashi nace yau dambu zamuci komai ban shirya ba,
Hmm gadai wayar ki lubna ta kawo yaya asama'u nakira,
Zaro.ido tai tace lubna taganmu a haka?,eh mana amma wayar kawai ta ajiye ta fita,
Aiduk laifinka ne seda nace zanje daki nakwanta kace nai kwanciyata anan yanzu gashi kaja ta ganmu duk kunya ta kama ni,
Dariya kawai yayi yace ji yadda kikayi da fuska kamar wata yarinya nidai kije ki matsa mata kafafuwanta naga sun kumbura,
Wallahi haka suke kullum ko jiya seda najira tai bacci nima nayi segumi take duk sanyin dakin tausayinta nakeji bata taba jin dadin cikiba,
Nima ina tausaya mata ganin kotafiya dakyar take yi amma ai takusa sauke wa Allah dai yasauketa lpy,
Ameen bari inje indubata,
Washe gari tunda ta tashi sallar asuba take jin abubuwa amma dai ta daure har gari yayi haske,
Dafa gadon tayi zata miqe ta kasa jin yadda bayanta ya riqe tace washhh,dasauri badee ta taso,lubna ko abinne?,
A'a bayana ne kawai naji yariqe,😳kuma kikace a'a?, ina wayar ki nakira Abdulqadir yakaimu asibiti,shiru tayi zufa naqaryo mata,pillow badee ta daga tadauko wayar dasauri takira abdulqadir jikinsa har rawa yake daga masallaci yadawo gida dasauri,
Lubna kiyi kokari ki tashi muje mota mana,
Mama wallahi kodaga nafara bazan iya yiba,to bari nakira abdulqadir Yakama min ke,kusan karo sukayi tace zoka kamamin wai bazata iya tafiyaba,
Yana zuwa ya sureta se mota se cije baki take tana runtse ido sosae,
Dasauri aka karasa da ita labour room Sega Mus'ab kamar ze tashi sama yashige dakin,
Har karfe goma na safe babu wani labari,ta wahala iya wahala saboda girman babyn se kusan karfe goma sha biyu ta haifi namiji ni narasa dawa yaron ke kama gashinan babba kamar insace ingudu.
Rawa naringa yi ina murnar zamusha biki sedai wani Abu Dana tuna yasa jikina yai sanyi😔
[8/19, 8:38 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017.
Second to d last page
Page 45
Baka tafi kabarni ba gashinan ankawo wata tsohuwa secin zalina take,inji lubna dake waya da Mus'ab,
Metai miki?,yatambayeta da muryar murmushi,
Muna fa zuwa ko zama banyi ba mama tasa tamin wanka daruwa me azabar zafi,
To kiyi hakuri taimakonki take ina baby,
Yanacan hannun mama tana shirya shi shima anmai wanka shima naji se tsala ihu yake,
To kije ki rarrashe shi mana,ta zaro ido tace rufani ka sayani kar kasa mama ta fige ni dama tana cewa banida kunya,
Dan kinrarrashi danki shine bakida kunya?,eh mana kaibakada labari ne dama ba Dan fari bane bari inci abinci zan baka labari yunwa nakeji,
To bye luv u,luv u too my man,
Dakin badee suke zazzaune duka matan sa'anninta Sega badee tashigo da baby karbi lubna bashi nono yaronma yanada dangana tunda yazo duniya benemi abinci ba se bacci yake,
Karbar sa tayi tana kallon su safna kasa kasa itafa akwai matsala yaza'ayima shekara da shekaru tana boyon Abu yau kawai bainan nasi ace taciro shi kowa yagani hijab ta janyo tasa ta tura babyn ciki,
Ke meye haka?inji badee,
Mama nikam wallahi banaso suganmin jikina,
Yo naji wani shashncin banza jama'a Ku tayani gani ko a tarihi bantaba jin wannan labarin ba,
Aiko mesu safna zasuyi ba dariyaba,
Ke zaki ciro mamman kibashi yadaina mana kuka kokuwa senazo naciro dakaina?,
Toni ban iyaba,dada kika kunshe cikin hijab mezakiyi?,tana masifa tanuna mata aiko yana kamawa ta fizge tana ihu,
Wallahi lubna watan cin ubanki ne yakusa kamawa Dan marinki zanyi zaki kamane yadai tsallar masa a fuska kose yayi kuraje?,
Wallahi mama zafi bakiji ba daya kama,ai kowa da haka ya saba ki kama dalla malama yaro yunwa yakeji shayarwa yazama wani jidali kuma,
Sudai su riyya se dariya suke,lubna kuwa harda Dan kwallanta ita anganemata jiki kuma gashi tanajin zafi,
Nikam murna kawai nake yaune suna danhaka nace sena yanki en biki Kure adaka zanyi nadauko kayan sallana a kasan akwati domin yaune suna,
Inacikin shiri cikin Dan ubansun lace dina sega momma na (Zainab inuwa #antysis) tashigo cikin shirin ta nace mama wannan wankanfa inazuwa?,
Tare zamuje Dan bazan yadda kije kina tsokanar meela ba kuma gakida Dan iskan kwadayi,duk inda raina yake seda yabaci dn bazan manta ba bikin jawaheer ma haka taimin seda nasha ranqwashe ko babbar tusa hanani tayi,
Haka nagama shiri ina ta turin baki harna shiga mota muka tafi ban daina fushi ba Dan nasan ba zanci rengem ba yau,
Tun gate na hango meela dasauri na dauke kaina araina nace mummuna kawai kamar ba er gidanmu ba,
Mamaki ne ya cika ni lokacin Dana hango ayarin en gidan Sophie G kowa tadau wanka sunkame akan kujerun roba se hankadar mutane suke,
Can Na hango su anty billyn Abdul,cute Zara,maman Nana,anty badee social,baby nurse daga gefe se yagar naman rago suke aiko idona nakansu se hadiyar yawu nake,kyakkyawan rankwashi naji senaci uban makiyanki bikin nan bazamu jima ba Dan bazaki sani kunya abinda kikeyi ko sultan bayayi kwadayi kamar mayya,
Nidai se zare ido nake nasan banida gaskiya meela tabiyo gefen mu tace andai ji kunya kwadayayya kawai,nace wallahi zamu hadu yanzu Dan kinga mamane kinsan bazata bari muyi fada anan ba,
Biki yai biki se shagali ake mama takasa ta tsare haka naita kumburi ga ankawomana abinci ta nama anhanani ci dole na dangana atakaice dai banji dadin bikinba,
Gaisawa kawai nayi da en gidan ZBI mama tasani agaba mukayi gida bayan anbiyomu dakayan bikin anan nema naji sunan yaro Muhammad,
Har mukaje gida bakina kamar zetabo bango,haba sweetheart zokiji banason wannan fushin yi hakuri banaso kina fada da meela yayarki ce kingani kuma kwadayi bakyau kinji kidaina,
To mama insha Allah nabari daga yau,yawwa er albarka Allah yanunamin aurenki,ai a 360 nabar palon ina rufe fuska naji kunya amma akasan zuciyata se ameen nake cewa😉,
Allah ya raya mana muhammadu ameen.
[8/19, 8:38 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017.
LAST PAGE
Inaso Ku saurareni dakyau kunga yadda rayuwa ta zame mana inaso Ku dauki rayuwar duniya abakin aure Ku masu mata kuriqe matayenku da kyau kuriqesu irin riqon dazakuyiwa kanku yayayenku Ku kasance masu kula da rayuwarsu da tarbiyarsu lubna kekadaice mace kiriqe mijinki dakyau kikula da tarbiyar yayanki kiyi yadda kikaga inayi sirrin mijinki shine babban abinda zaki boye lubna kinji labarina kuma kingani da idonki don Allah Ku taimaka Ku kasance masu riqe amana kuma kusani kune ABIN ALFAHARI NA,
Nan sukayi murna kowa zuciyarsu fess majid dake jikin kofa yashigo yana cewa,
Madalla da samun mata irinki madalla da samun uwar yaya irinki badee'a hakika nima Y'AY'ANA ABIN ALFAHARI NA ne,
Murmushi sukayi sukace madallah da samun iyaye kamarku muma muna alfahari daku,
Allah yai muku Albarka yasa mugama daduniya lafiya,ameen muka amsa harnima.
ALHAMDULILLAHI
Anan na tattaro alqalamina na ajiye shi sekuma wani lokacin idan Allah yakaimu da rai da lafiya acikin sabon littafina me suna DUNIYA DA ZAMANI.
Kudan bani lokacinku anan don Allah,
Idan kunlura acikin wannan littafin nawa ina girmama Kalmar HAKURI wasu dayawa suna cewa babu mace irin badee a duniya Toni anan banace muyi hakuri irin nata bane a'a inaso ne mu kwatantayin hakuri koda Rabin nata domin akowane kunci to akwai walwala,akowace wahala akwai sauki,akowane kuka to kucigaba da kallon fuskar me kukan zakuga murmushi ashimfide domin akowane duhu haske nanan zuwa,
Kufahimci cewa akwai dangana dakauda ido awurin badee da yayanta domin da babu haka atattare da su da sundaukowa uwarsu rigima yanada kyau mukula da yayanmu,
Akwai sanin darajar yaya da iyaye dakuma en uwa semuriqesu dakyau,
Idan mukayi hakuri zakuga Allah ya kwato muku hakkinku tun anan duniya kamar yanda yafaru da safara'u semu kiyye mukasance masu fahimta da hakuri.
Masoyana kusani nima inasonku kuma nima INA ALFAHARI daku nagode dakuka bada precious time Dinku kuka karanta littafina kuma INA fatan Allah yasa kun karu da abinda ke cikinsa,
Mata masu aure da yaya Allah yabaku hakuri da zaman lafiya Allah ya albarkaci yayanda kuka Haifa dawa yanda zaku Haifa yabaku ikon tarbiyarsu,
Yan mata irinmu Allah yabamu mazaje nagari da zuriya Dayyaba,
Wayanda suka rigamu gidan gaskiya Allah yajikansu mukuma Allah ya kyautata namu karshen Allah yagafarta mana,
Na sadaukar da wannan shafin ga dukkan marubuta Allah yabiyaku da mafificin alkhairi ameen.
#AnaTAre😍