Tun daga ranar da uncle ya kamata tana matsi bata kuma bari suka hada ido ba ...tana kwance tana chat dinta ...ya shigo tare da tsaya bakin kofar ya zuba mata ido ...rigar dake jikinta cottonsilk orange ta bi mata jiki sannan iyakarta guiwa ....cinyoyinta sun fito kamar irin na turawan nan ..sae gashinta data hade shi ta daure baya ....
Bude hanci take tana shakar kamshin uncle a tunanunta daga dakinshi kamshi ke fitowa ...
Pictures dinshi ta nuno tare da rungume wayar tana fadin..." I miss you uncle ...matsalanka ka fiye gano abunda yafi karfinka ...
Wa yace yafi karfina ....?
Da sauri ta juyo tana waro ido kafin ta boye kanta cikin pillow ....
dan murmushi yayi kasa kasa yace .."ki tashi ki shirya zaki rakani unguwa "..
ba tare da ya jira amsarta ba ya wuce abunshi ....dakin hanne ya shiga yace ta shirya zasu tafi ....wata uwar harara ta watsa mashi don tun dukan da ya masu over 6month take rike dashi ....
"Bana zuwa " ...ta fada tare da gyara kwanciyarta ....
Ba tare da yace komae ba ya juya ...amma a zahirin gaskia baya kaunar mutun mai riko ..
wacce yama dukan ma ita da kanta ta nemeshi tare da ba shi hakuri duk da shi ya dace ya bata din ....
Dan karamin tsoki ya sake dae dae lokacin da Hudah ta fito daga dakinta sanye da gown red ....
a tunaninta da ita yake tayi saurin kallonshi tana fadin ..."Uncle sorry wallahi gyalen na rasa inda yake "...
Dan murmushi yayi yace "Baki man komae ba Hudah ....kinyi kyau sossae ....amma bara ki fita a haka ba ...."
komawa yayi dakin ...cikin kayanta ya dauko mata bakar hijab mai hannu tare da mika mata ta sanya tana murmushi ....
A mota ma duk sec sae sun kalli juna tare da sake murmushi ...
"Zaki zauna da Auntyn kine koko kinfi so na ajeki GRA ke kadae" ...ya fada tare da dan kallonta ...
Shiru ta masa ba tare da tace komae ba ...juyowa yayi yana kallonta yaga gaba daya hankalinta ba ga motocin dake kokarin wucesu ....hannunta ya janyo tare da kura mata ido ....
"Bakya jine ".....ya fada dae dae kunnenta ...
"Me kace Uncle ? ....ta fada tare da zame hannunta daga nashi ...
Kafarda ya janyo yana kokarin rungumeta .."may be idan kina jikina kya fi fahimtar abunda nake fada ...."
"Wallahi uncle naji ..ka sakeni please !!..
Hararanta yayi sannan yace .."bana jin kinji abunda na fada tunda baki bani amsa ba !! ...ya fada tare da kokarin hade bakinta ...
cikin sauri tace .." Uncle please ka daena ....da Aunty hanne zan zauna "...ta fada tana kallonshi da idanuwanta ta suka koma kalar kuka ...
Dariya yayi kasa kasa tare da sakinta yana kallonta ...turo baki tayi tana fadin ...
"Saukeni na tafi a napep ni dae !!
"A da kenan Hudah lokacin da nake tsoron na tabaki ba yanzu ba da kika zama tawa ...kina iya yin duk kalar abunda kika so ..am ready na bi da ke yarda kike so ...duk da dama kin shirya don har ...!!.
Hannunta ta sa abakinshi tayi rau rau da ido .."
".Uncle Dan Allah kabar fada ...wallahi lubna ta bani ....!!
wani fitinannen kallo ya watsa mata tayi saurin maida kanta kasa tare da zame hannunta daga bakinshi ...
Central market ya nufa da ita ...wani katon shago suka shiga ....Wasu kayane gefe guda ...gurin suka nufa ...
"Ki duba abun da bai maki ba ...gobe zai koma dubai din sae ya sako maki wasu ..." ..ya fada yana kokarin daga mata kayan
Wani fitinannen kallo ta sake mashi tare da juyawa ta fita daga shagon ta koma mota ta zauna ....
Kallonshi tayi cikin natsuwa lokacin da yake kokarin kunna motar tace
"Uncle idan zaka hada man lefe har sae kazo dani na gani ...? ..Uncle zan iya aurenka ko babu lefe kuma na rayu dakai kamar baiwa..Ka mani komai a rayuwata uncle bansan dame zan saka maka ba ...!!
So yake ya kashe maganar yace "Lubna ta cigaba da baki abunda take baki ke kuma ...!!
Kuka ta sake da karfi tana kokarin bude motar ta fita ...hannunta ya rike yana dariya ...ita kuma sae neman kwacewa take ...
"Sorry Hudallah na daina kinji ko !! ...ya fada dae dae kunnenta ...
Kallonshi tayi tana turo baki ...sannan tace "promise" ...a hankali ...
Lumshe idonshi yayi tare da daga mata kai ......kafin ya budesu tar ya zuba mata cikin salon soyayya ...juyar da kai tayi tana kallon waje dauke da murmushi ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_74 to 75_*
*_3 month ..._*
Shirye shiryen biki ake sossae ..hanne ta zage sae gyara Hudah dun bata mata kallon kishiya sae yar 'uwa duk da akwae dan kishin kadan a ranta ..amma ta tabbata idan har ta fiyo dashi to batawa Mahmoud adalci ba ...tun da har ya jure zama da ita tsawon shekaru ba tare da cin mutunci ba...
"Aunty Hanne Dan Allah bara naje na dawo ...Lubna tashi muje !!!!
Hanne tace ..".ina zaki Hudah ..so kike mutane su zargeni ...duka gobe fa daurin aurenki kuma zaki fita ...aa gaskia !!
Hudah ta riko da hannunta ..."Please aunty hanne...wallahi daga yau baran sake irin wannan fitar ba ...dan Allah ....kinji auntyna ...!.
" To Hudah ...ki kula amma kinji ko !!!
"Yauwa" ....ta fizgi hannun Lubna suka fice ....Motar Mahmoud din suka shiga ...
"Ina za mujene ? ...lubna ta tambayeta ...
Hararanta tayi ..Gidansu Shehu ...!
"Amma Damsel baki da imani ..bayan kinki aureshi kuma har da zuwa gidansu ki masa me ....?
Bata ce mata komar ba tayi parking kofar gidan ...tare da fito da wayarta ta kira Shehun ...ta tambayeshi "yana gida ..".ce mata yayi. " eh yanzu ya dawo shi da dad asibiti suka karbo magani ..."
Lubna ta kalli .."fito muje" ...ta fada tare da yin gaba abunta...
Ba tare da tayi sallama ba ta hankade labulen falon ....cikin saa su duka ukun na zaune sae safina dake gefe guda tana wasa ...
Zumbur Dad da shehu suka mike ....Dad yace ..."Pretty"...kafin ya rufe baki Shehu yace "Sa'adah ",....sannan suka kalli juna tare ....
Yar dariya ta sake ..kafin tace ..
"Sa'adah ..damsel Pretty.. ..amma asalin sunan Hudallah Ibrahim _!!! ...
"Hudallah .".su duka duka maimata har da hajiya data mike lokacin ..
"Kwarae amma ba farat daya karamar kwalwarku zata fahimta ba ...Soyayya ......da uba da dansa ....!!
" Damsel ..".barister shehu ya fada tare da matsowa kusa da ita ..."Ban fahimceki ba ..."
"Yanzu kam zan maka yarda zaka fahimta dakai da jakin ubanka har da ma tunkiyar uwarka ...!!
"Ke mara mutunci ....uban me kike nufi ? ..hajiya ta matso a fusace ...
Dad da yayi mutuwar tsaye yace ..".karki kuma zaginta hajiya ...dan Allah Pretty ki zauna muyi magana ...wallahi har yanzu ina mutuwar sonki .!!...ya fada cikin kyarma ....
Shehu yace ..."Dad Sa'adah tawace kabar fadin haka mana ...ka lallasheta kar tace bata sona dan Allah ...!!
"Ashe kun san Allah ....? ..Yaushe kuka sanshi ..ku fada man ...!! ...ta karashe maganar cikik tsawa ...
" A gaida jakin malamin da ya tsaya fadarwa Shehu da ubansa fadin suna Allah a baki don basu sanshi a zuciya ba ....!!
" Sa'adah "....shehu ya fada tare da yin kneel down a gabanta ..."Dan Allah karki man Haka wallahi ina mutuwar kaunarki ...na tabbata idan ban sameki mutawa zanyi ...!!
"Aiko ya kamata uwarka ta tafi neman likafani tun yanzu ....!!
Lubna tace ..."haba Hudah karki yi haka ba ...karki zama mara imani ...komae suka maki bai kamata kiyi haka ba .....!!
Cikin tsawa tace ..."Kinsan Wacece Yaya Sa'a ? ....
Ba Shehu kadae ba Hatta Lubna sae da ta tsorata ....
"Yaya Sa'a ...tana iya kwana biyu bata ci abinci ba amma bata taba barin Hudarta da yunwa ko da seconds 2 ....takan kwana tana wahala duk saboda Farincikin Hudah ....Wadannan munafukan Lubna su sukayi sanadin barata da duniya ke har da ummana .... _*A DALILIN YAYATA*_ Nayi komae lubna ba wae don kowa ba sannan nayi soyayya daku !!...
"Shehu na tabbata baka manta wacece Ya ya Sa'adatu ba ...mumina saliha daka tarwatsa mata rayuwarta ....to Hudah ce kanwarta ...!!
"Wallahi nasan ban kyauta ba amma dan Allah ki gafarceni ...ki tsaya muyi magana wallahi na tuba na gyara duka halina Hudah ...duk saboda ke ...dan Allah karki barni ...na tabbata dad zai bar manke ...,!!!
" Mtsee ....gobe kamar yanzu na zama matar barister Mahmoud mutumin da kukayi forcing yazo gidanmu ashe ma haske kuka kawo mana ...!!
bata rufe baki ba ya fadi kasa yana tari ...dad da hajiyar sukayi kanshi ...dad ke fadin ...
"Karkiyi haka Hudah ...na bar masa ke wallahi na hakura ...!!
Harara ta watsa mashi ...
Tana fadin... ..."Sweetheart ayi maza aje gwajin kanjamau don na tabbata akwaeta a jikinka ...don ina tunanin har da jakar matarka ma ta kwasa ...a lisaafina Yau 6month kenan da cutar ta shiga jikinka
na tabbata tayi kwarin da barata fita ba .....bye!!! ..ta juya ta tafi ..
Juyowa tayi da sauri tana fadin ..
"Oh na manta ...Shehu ya sayar da wannan gidan akan Naira million 19..idan ya tashi ku tambayeshi ..wawan bai sani ba nina sayi gidan sannan ya maido man da kudin a matsayin kyauta ...so nan da wata daya a tattara komatsae a fita!! ......
Ta fizgi hannun Lubna suka fita ....ita kam lubna binta take da kallon kamar tv ...gani take kamar ba Hudah da ta sani bace ..
Da daddare Uncle Mahmoud ya kaisu ita da Lubna da Farida kawarsu da tazo.. gidan liman ....
Bayan su Lubna sun fita daga motar ne ya riketa ....yana shafa kunshin da aka mata na zallah bakin lalle ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
_GWS.....SWEERY ...ALLAH YASA ZAKKAR JIKINE .....PLEASE IDAN AN TARA KANKANA CIKIN KAYAN DUBIYA KI AKE MAN KIN JI KO .....😘😘_
*_76 to 78_*
Kallonsa tayi a shagwabe tana fadin ...Uncle suna jirana please ...!!
Glass din gurinshi ya rage tare da kwalawa su lubna kira da suke gefe suna jiranta ...
Suka matso Lubna na fadin "Uncle gani " ...
Lumshe ido yayi yana murza hannjnta ..."Ku shiga ciki Lubna zamu shigo yanzu ..."
"Uncle "....ta fada kamar zatayi kuka ...
Kallon da ya bita dashi ya sata yin shiru tare da maida kanta kasa ....a hankali take mashi guguni tare da turo baki tana hararanshi ta kasa ...
Idonshi na lumshe duk yana jin abunda take fada ...bata tare da ta shirya ba ya rungumota kirjinsa tare da hade bakinsu guri guda yana tsotsa ...
kokarin kwace kanta take tana yarfe hannu ...kin sakinta yayi ya cigaba da bata dpkiss ....sae ya ji ta fara kuka ne sannan ya saketa a wahale ...
"Maimaita abunda kikace !!...ya fada kasan makoshi..
kwallan daya fito ne ta saka bayan hannu tana gogewa tare da turo baki ta masa banza ....
A hankali ya bude ido yana kallonta sannan ya saka hannu da niyar rikota ...tayi saurin ja da baya tana fadin ....
"Yi hakuri zan fada maka uncle" ...ta fada tare da goge kwalla ...
Maida kanshi yayi saman sitiyari yana jiranta ...jin taki cewa komae yasashi dagowa .yana kallonta .....tayi saurin ja da baya ..
"Cewa nayi kamar baka taba aure ba !!!....ta fada a hankali ...
"Umhuh ...ina jinki ..sae kika ce mae...kuma bayan wannan?
" Shikenan fa abunda nace ."...ta fada tare da janye hannuta cikin nashi..
Dan murmushi yayi tare da rungumota yana niyar kissing dinta ...
"Zan fada wallahi ......!!
sakinta yayi tare da zuba mata ido .....
A ha kali tace .."sae kuma nace..huh...kayi hakuri Dan Allah Uncle" ...ta fada tare da kallonshi ..
"May be dama kina bukatar na cigaba da kissing dinki shi yasa baki so ki fadi abunda na tambayeki .!!..ya dago fuskarta da hannunshi na dama ..
Da sauri tace " aa wallahi uncle ..cewa nayi ka cika jaraba ....!!..ta karashe maganar tare da sanya kanta cikin cinyoyinta ...
Murmushi yayi kasa kasa tare da bude motar ya fita ya zagaya ya bude mata ...ba tare da ta kalleshi ba ta fito tare da rugawa cikin gidan da gudu ...
Binta yayi da kallo tare da lumshe ido ya jingima da motar tsawon wani lokaci ....
_Karfe 11:30_
Dae dae lokacin aka daura auren Barister Mahmoud da Hudallah Ibrahim ...wanda liman ya daura ...tare da halattar dunbin mutane daga garuruwa da dama ....
Duk yarda barister Mahmoud yaso ayi party ...liman hanawa yayi ...yace ...
"Indae kuna son aurenku yayi albarka Mahmoud to dole ku kauracewa duk wata bidi'a ...ban hanaku idan an kai maka matarka ba ...ku shirya walima cikin gidanku domin mutane su tayaku da Addu'a ...!!
Godiya sossae Mahmoud yayi sannan ya tashi suka tafi ....
Bayan magrib ne ...motocin da zasu dauki amarya suka iso ...kanwar maman Mahmoud ne ta amso amarya an nadeta cikin Saree yellow colour tun daga kanta har kafarta .....
Rungumota tayi tare da sakata cikin Clinto yellow colour ..sannan ta rufeta ta koma cikin wata motar.. aka barta ita kadae ....
Duk da baa gaban iyayenta take ba ...amma ranar mutuwarsu ta dawo mata sabowa...ta tabbata da yaya saa na raye babu abunda zai hanata zama gefenta a yanzu ...tayi kwadayin taga farincikin da zata gani a idon yayar tata ... ....
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home pf expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_79 to 80_*
Wani sabon kuka ya zo mata ..yayin da ta sa hannu tana kokarin rufe bakinta gudun kada drivern yaji ta ....
Ji tayi an janyota tare da kwantar da ita ...kamshin da tajine ya hanata firgita don har ga Allah bata dauka akwae wani a cikin motar ba bayan driver ...
A kan kirjinsa ya kwantar da ita tare da bubbuga bayanta a hankali alamun lallashi ...ba tare da yace komae ba ....
Lafewa tayi tana kuka kasa kasa ....Hannunshi ya kai tare da lalubar bakinta ya tura yatsunshi a ciki yana wasa dasu a bakinta ....
Kukan ya tsaya cak sae dae ajiyar zuciya da take saki tare da kananan kwallah ......
Jin zaa bude motar ne ya sata tashi daga jikinshi tana gyara Saree dita ....
Bude motar akayi tare da fito ta ...sannan Aunty hanne ta matso ta kama hannunta ...Uncle Mahmoud dinne ya zagayo tare da rike gudan hannun nata ....
Pictures aka dinga dauka kala kala ....ga dandazon mutanen da sukazo taran amarya ...Ba gidan barister Mahmoud din bane aka kaita ...gidan iyayenshine ....zuwa gobe idan anyi walima su wuce gida ....
Tare suka jera su duka ukun har tsakiyar babban falon Gidan ...sannan aka zaunar da Hudah din a kasan tuntu ...Shima barister Mahmoud din zama yayi gefenta ...har lokacin fuskarta na nannade da Saree ....
Falon ya dauki haske ta ko 'ina ....yana zagaye da dangin Abba da kuma na mamanshi sae su biyu a tsakiya ...
Yayar Mamanshi ce _Aunty Husy_ ta taso tare da aje yan kunne da sakar gold wanda ya kai naira million 15 ...kusa da Mahmoud ...na sayan fuskar amarya ...
Gurin ya dauki tafi ganin Mahmoud din ya tura mata sarkar yana girgiza kai ...alamun bai sayar da fuskar Hudah haka ba ...
Wata kanwar mamanshi _Aunty Zuby_ ta taso tare da cire tata sarkar da yan kunne ta hada mashi ta tura ...still tura masu yayi yana girgiza kai ...alamun bai yarda ba ...
Gurin ya kara daukar tafi lokacin da mamanshi ta taso ta cire tata sakar da yan kunne ta daura mashi a saman tasu ...
Sannan ya saka hannu ya dafa sarkokin tare da fara bude Fuskar Hudah Ahankali ..har sae ya kusa budewa sannan ya kalli kanwar mamanshi yana fadin "Gaskia Aunty Zuby ku karo wani abu tukun ..."
Aunty Husy ta mashi dakuwa tare da watsa mashi harara ..
Sannan ya bude fuskar duka yana murmushi .....
Kanta na a kasa tana kallon carpet din gurin ....
"Masha Allah ...tubarakallah ..Alhamdulillah amarya ta hadu ta ko'ina ....fatan mu Allah ya bada Zaman lafiya!! ....Babbar yayar mamanshi ta fada tare da daukar su photo ....kamar an bude gidan photo haka flash light ke tashi gurin ....
Sae da aka gama photo sannan gurin ya sake yin shiru ...Mahmoud dinne ya saka hannunshi na dama tare da dago fuskarta ...sannan ya goga hancinsa a lips dinsa yana lumshe ido ....duk uwayen mutanen dake zagaye da falon..
"Mahmoud baka da kunya ni wallahi ban ma san haka kake ba dae yau .."..kanwar Mamanshi ta fada tare da jehoshi da pillow ....Hudah kuwa yarda kasan ta nutse gurin haka take ji ..
..
Murmushi yayi kasa kasa sannan kama hannun Hudah ..tare da rarrafawa kusa da kafar Mamanshi ...
"Hudallah ki gaishe da Mama "...ya fada dae dae saitin fuskarta ...
Dukawa tayi kusa da kafar maman ba tare da ta iya cewa komae ba ...bayanta maman ta dafa ..tana fadin ..
"Allah ya maki Albarka Hudah ....!
Kowa na falon sae da suka rarrafa ya na rike da hannunta yana fada mata sunanshi tare da matsayinshi ....ita kuma tana dukar da kanta a hankali ...suna sa mata albarka sannan suka dawo inda suke zaune ...duk abunda ake idon hudah na kasa bata dago ta kalli kowa ba .....
Bayan sun zauna ne babbar yayar mamanshi _Aunty Husy_ ta kama hannunta tare da kaita part din hajiya ta zaunar da ita saman gado ta fita ....
kamar jira Mahmoud yake ta fita ya fado dakin tare da saka key kamar munafuki _nidae feedohm nace munafuncinne man_...ya zauna kusa da ita ya janyo ta jikinshi yana fadin ...
"Hudah sun man bakinciki wae anan zaki kwana ....dan kada ace nayi rashi kunya wallahi dana saceki mun koma gida ko ? ...
Banza ta mashi tare da sakin kuka ....kanta ya dago yana lallashinta tayi shiru amma sam taki yin shiru ....sae da ya fara kokarin cire mata Saree da aka lillibuta dashi sannan tayi shiru ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of Expert & Perfect Writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_81 to 82_*
"Uncle ka fita dan Allah !!....ta fada tana kokarin tsayar da kuka ...
Cikin sauri yace .."Idan na fita zaki bar kukan Hudah ...?
Daga mashi kai tayi tare da sadda kanta kasa ....dan kiss ya mata a lips tare da jan hancinta sannan ya fita yana waigenta .....duk da yayan mamarshi tace anan zata kwana hakan bai hana Mahmoud ja mata Allah ya isa ba ...
Allah ya soshi ba wanda ya ganshi lokacin sa yake fitowa don suna can suns kokarin hada mata abincin da zata ci wanda zai kara mata lafiya ...
Su biyu suka shigo da abinci tare da zame malullubinta ...Aunty Husy ce ta bata abincin a baki ...tare da daura fuska ...don farko cewa tayi bara taci ba ...sae da ta daure mata fuska sannan ta amsa ...
Bayan ta gama cin abunci yayar mamanshi ta hada mata ruwan wanka masu uban kamshi tace ta shiga tayi ...tana fitowa ta bata less red tare da head baki tace ta sanya ...da katuwar sakar gold ...sannan ta saka mata takalma hills bakake ...ta rufa mata bakin mayafi a kai ..tare da kama hannunta ..suka shiga part din Abbah ...yana zaune sanye fa farin glass suna shigowa ya mike dauke da fara'a yana fadin ...
"Marhaban Hudallah" ....hannunta Abbah ya karba daga hannun Aunty Husy ya zaunar da ita bisa tuntu ....
Aunty Husy ta miko mashi plate dauke da saubatussamina .......kadan ya diba a hannunshi sannan ya saka mata a baki...ta daukesu photo ....Fita tayi ta ta barsu su biyu ....
Wa'azi ya mata mai ratsa jiki wanda ta tattaba ko mahaifinta na nan iya abunda zai mata kenan ...bata da abun ce masu shi da liman sae dae fatan Allah ya saka masu da alkhairi ..
12:30 ..
Masu decoration suka iso ....kujeru suka fara fitowa suna jerawa a harabar gidan ...
.sannan suka fara decorating din da yadi blue da fari ....gurin yayi masifar kyau kamar baa cikin gida ba ....
Tana zaune Aunty hanne suka shigo ita da Aunty Husy suka bata Saree blue colour ....kaf jikinta sae da aka nannade idanuwanta kawai ake iya hanguwa .....
Fita da ita akayi falo ...acan taji muryar Uncle Mahmoud yana mayarwa da abokan wasanshi magana ..."wae duk family dinsu babu mai kyaun amaryarshi ......!!
Gabanta ya fadi lokacin da taji tattausan hannunshi cikin nata ....babu kunya ya daga Sareen yana kallon fuskarta tare da fadin ....
" Gaskia na iya zabe ...Tubarakallah ...Aunty Husy da an gama walimar zan tafi da matata.. ..ku dan rufe idonku for some minutes ....!!.
Aunty Husy ta kai masa duka ..".Gidanku Mahmoud ....ka rike hannunta ku fita bawae ka ma rashi kunya ..!!..
Dariya yayi tare da kissing dinta a hannu sannan ya jata suka fita harabar gidan ...
Sun nuna mata kauna sossae ... _kamar yarda exclusive suka kaunaci feedohm_ ....sabon lefe suka hada mata wae kayan karbar amarya ....
Agaban mutane ango ya ciyar da amaryarshi har ta koshi ....sannan aka ce itama ta ciyar dashi ...kasawa tayi ..ta nuna alamun zata yi kuka ...
Auntu Husy ce tace ta sayi hannun amarya naira million daya cash ta zubesu a table din da suke zaune ...
Duk da hakan kasa bashi tayi ...hannuta ya kamo ya kai bakinshi saitin fuskarta ...
"Ba kya sona Hudah? .....ya fada a hankali ...
Dagowa tayi da sauri tana kallonshi kafin ta girgiza mashi kai a hankali ...hannuta ya kama ya debo abincin sannan ya saka a bakinshi yana lumshe ido ....gurin ya dauki tafi da ihu ...abokan wasanshi kuwa cewa suke wae amaryar bata sonshi tunda har ta kasa bashi abinci ...
A hankali ya dago da fuskarta yana kallon ..."Prove it Hudah ...ki nuna masu kina sona ...ko bakya sona .?..
Ba tare da tace komae ba ta kai hannu ta debo Muhassimba ta kai bakinta ta b'alli kadan sannan ta sa mashi sauran a baki ....
Ba karamin burge mutane sukayi ba ...Aunty hanne kam na can cikin gida bata san wainar da ke toyawa ba ...Yayar Mamanshi ta bata yan shila tace ta gasa masu da ruwa ruwa idan zasu tafita a tafi da ita..dan haka bata gani ba.. bare ta kwashi takaici .....
••°°••
Bayan Magrib ne akace a fito da amarya ....sae da sukaje falon Abbah suka masa bankwna tare da Mama sannan Uncle Mahmoud din ya jata har harabar gidan inda aka ajiye motoci ....Daga ita sae Aunty Hanne da Aunty Husy kadae suka shiga motar ...dan Aunty husy cewa tayi bara su shiga mota dashi da Amarya ba tunda baida kunya .....
Sae da aka fara tafiya sannan ya masu gyaran murya lokacin Aunty Husy tana karawa Hudah nasiha ..Hudah kuwa kuka take a hankali ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_83 to 84_*
"Aunty Husy dan Allah ki barta hakanan ...kinga zaki ja ta bata kwalliyar tun kafin na gani ...kuma duk abunda kike fada mata Allah yau zan fada mata ba tare da tayi kuka ba " ....ya fada tare da kunna fitilar motar ...
Sake da baki aunty Husy ke kallonshi "∆mma Mahmoud baka da mutunci ...ashe dan Ubanka sae da ka biyomu ....shine ka karbi driving din ko?....ya maka kyau!! ....
Dariya yayi kasa kasa tare da kallon Hudah da ta kwantar da kanta sanan cinyar Aunty Husy tayi lamo kamar maijin bacci...
Hanne ta saka hannu ta kashe filitan ...ba tare da tace komae ba ...har suka isa gidansu ...sannan aka shigar da Amarya Part dinta ...amma ba asalin wanda take ciki ba da ...aa saman bene aka kaita ...dama kuma gurin rufe yake ...
Kamar yarda addini ya tsara bayan kowa ya watse ya tarasu falonshi tare da masu nasiha mai ratsa jiki ...sannan yace kowa ta fadi bukatarta ...
Aunty Hanne tace ...Idan da hali ya taimaka masu da jari saboda ita tana so ta dinga fita kasashe tana dauko kaya ... tasan ko ance ta koma karanta bara tayi abun kirki ba ....
Yacce .."kamar nawa suke bukata ?
Hanne tace " ko nawa yake da hali ..."
Hudah kam jinsu take ..don bata da wani guri da ya wuce tayi karatu domin cika gurin Yaya Sa'arta !!
Leda da ya shigo dashi yace Hanne ta je ta dauko masu plate ..
Aa tace ...yafi kyau suje can su ci abunsu kamar yarda akewa ko wace amarya ...sannan ta mike ta daga Hudah tare da daukar basket din da ta shigo dasu suka nufi part din Hudah ....bawae bata jin kishi bane sae don ganin ko tayi kishin a banza tunda bata da abunda zata iya biya mashi bukatarshi ..
Part dinshi ya shiga ...yayi sallah tare da wanka sannan ya shiga part din hanne ya mata bankwana tare da hugging dinta yana mata godiya ...don ba karamin burgeshi tayi ba a hidimar bikin ...bai tafi ba sae da ya dan bata farinciki ta hanyar romancing dinta sannan ya fita .... _Ajiyar zuciya ta sake ta bishi da kallon ..wannan ne karo na farko da ya taba kai hannunshi a jikinta da niyar faranta mata..kwallah da suka taro idonta suka gangaro mata ...._
Hudah kam inda hanne ta barta nan ya isketa ....ko da ya shigo sae da ya kura mata ido ..duk da tana lullube da maroon din saree hakan bai hanashi ganin kyauwun da ta yi ba ....bakin gadon ya zauna tare da yaye mata fuska yana lumshe ido ...
" Tubarakallah ...Masha Allah ..Alhamdulillah ya Allah .."!!!.ya fada tare da dago fuskarta yana kallonta ...kasa tayi da idonta har sae dae ya kai bakinshi yana gogawa a dukka fuskarta ....
"Tashi kiyo Alwala" ...ya fada kasan makoshi ...har lokacin bakinshi na saman fuskarta idonshi a lumshe ...
Ganin bata da niyar tashi ya sashi daukarta cak ya dire ta cikin toilet din tare da zuba mata ruwa har ta gama alwala sannan ya janyo hannunta ya shinfida masu darduma ....ya gyara mata zaman saree din a jikinta ta yarda baka iya ganin komae a jikinta ...sannan ya jasu sallah ...bayan sun ida ..ya dafa kanta Kamar Yarda Allah ya umurce mu ...ya dinga kwararo mata aduu'a sanna ya janyo basket din da hanne ta shigo dashi ...ya fito da foodflask da waterdesndr ....tare da plate da spoon ...
Yan shila ne da sukaji kayan yaji ya juye masu .sannan ya tsiya mata lemon da aka hada da kankana,gwanda,dabino da kwakwa ya tsiya a cup ya kafa mata a baki
.
Wani bala'in kunyarshi take ji...duk da ba wannan bane first time da ya bata abinci a baki ....kin karba tayi sae da ya daure fuska sannan taci kadan tace ta koshi ....
Ledar ya janyo ya juye mata kazar dake ciki yana fadin .."Zauna kici kinji..bana so ki man irin na meenalle kice ban kawo maki kaza ba My Hudah!! ....dan hararanshi tayi sannan ta mike ...
Shima mikewa yayi ...yana kwance saree dake nannade jikinta ...rike kafadarta yayi yana juyata har ya gama fitar da gyalen ya barta daga ita sae siket da wata yar rika wanda iyakar jibi da karamin hannu ....Sae kwalliyar stone dake jikin rigar ....
Wani asirtaccen kamshi ke fitowa daga jikinta ...bai ga bukatar saka wasu kayan bacci ba ...ya dauketa cak tare da direta saman gado ...sannan ya koma ya kashe wutar dakin ...
Cikin dubara har ya rabata da kayan dake jikinshi ...anan ne ya kusa zaucewa har bai san sadda ya kunne fitila ba yana kare mata kallon ...da sauri ta rugumeshi ganin haske ya gauraye dakin tana niyar kuka ...
Da kyar ya iya kai hannu ya kashe fitilan yana mayar da numfashi ..cikin kunnenta yace ..
"Allah ya ma lubna Albarka ...yanzu zan gane idan abunda take ba dawa yayi amfani..don bana son wannan rakin ya tafi a banza" ...ya karashe maganar cikin zolaya ....wani uban duka ta kai mashi a kirji tare da ko ma wa can karshen gado ta kwanta ..
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_85 to 86_*
Mirginawa yayi ya hadeta da bangon yana fadin .."Sorry na daina kinji ko "...Sannan ya janyota jikinshi yana gentling ko'ina na jikinta
••°°••
Barister shehu kuwa bayan sun kaishi asibiti aka tabbatar masu da barin jikinshi bara ya taba amfani ba _paralysis_ ...domin faduwar da yayi ga lokacin jininshi ya hau ....Hajiya da dad kuka suka sake ...yayin da take tsinewa Hudah Albarka tare da ja mata alkaba'ai kala kala ...
lokacin ne maganganun hudah suka fara mata yawo ...cutar Kanjamau kawae take tunawa ...Dad din ta kallah taga duk yayi yaushi ga kuraje da suka fara cika mashi jiki ....
Ba tare da tayi shawara dashi ba ta je laboratory tace su mata gwajin HIV ....jininta suka diba bayan mintuna suka tambar mata positive ce tana dauke da cutar ....
Kamar mahaukacya ta koma ...ta shakari wuyan Dad tana dura mashi ashar ...da kyar ya kwaci kansa ...
Doctor yace shima a mashi gwajin ...baa dauki lokaci ba aka tabbatar mashi da shima positive ne ....
Doctor din ya basu shawara da su rufawa kansu asiri su zauna tare ba tare da wani ya sani ba ...sannan ya daura su kan magani ..
Bayan shehu ya farfado ..ya tabbatar masu da ya sayar da gidan da suke zaune ...amma ba Hudah ya sayar mawa ba ...wani makwabcin su Hudah ne amma ba mamaki ita ta turoshi .. ....
Dad din yace bai yarda ba wallahi zai shigar da ita kara ...amma sae barister Shehu yace ...babu wata kotu da zata karbi gidan daga hannun Hudah tun da "ka sayar ya rabaka da abunka" ..sannan takardun gidan ma na gurinsu ....Ba karamar nadama barister shehu yayi ba a ranar ....gashi a kwance rabin jiki a mace ...sannan har lokacin akwai soyayyar Hudah a ranshi ....wanda ya tabbata bara ta taba gushewa ba ....
••°°••
A hankali ya kai fuskarshi tare da kissing lips dinta ...sannan ya sake murmushi ...bai taba tunanin rakin huda ya kai haka ba ....Ihu ta dinga mashi kamar ita kadaece macen aure a unguwar ....
Blanket ya ja mata ya mike ya fada toilet yayo wanka tare alwala ..
har sae da ya gama sallah sannan Hudah ta bude rinannun idonta tare da dallah mashi harara ...
Murmushi ya sake mata tare da fadin ..."Ni kike harara" ...
Kafarta ta sauko zata mike tsaye ta koma da sauri...tana fadin ..."Allah ya isa wallahi .Lubna..ban yafe ba ..kema zaki samu wanda zai maki irin hakan ...Shegiya kawae !!! ..ta saka bayan hannu tare da share kwallah ..
Dariya sossae ta bashi ...bafa Lubnar ta tsareta ba tace dole sae tayi amfani da abunda ta bata ...aa itane har da boyewarta ma dan kar wani ya ganta ....amma kuma zata zagi yar baiwar Allah tana can gida tana bacci abunta...
Cikin zolaya yace .."Wae Hudah me lubna ta maki tun jiya kike mata Allah ya isa ..? ..Gaskia ina neman mata gafara kinji ...!!
Harara ta balla masa tana fadin "...Ban sani ba ...ka shafa kaji ..."..
Tasowa yayi yana dariya ..
"Abu mai sauki ..muje toilet idan na hada maki ruwan wanka sae na shafa da kyau naji ....!!
Daukarta yayi tana harbe harbe ya direta cikin ruwan zafi yana mata dariya ....sae sa ya tabbatar ruwan zafin sun ratsata sannan ya canza mata wasu ruwan zafin yace "Kiyi wankan tsarkk kinji Hudah ...bara na gyara dakin kafin ki gama ko!! "...ya barota cikin ruwan tana lumshe ido..
Kusan Minti Talatin yana jiran ta fito amma shiru ko motsinta baya ji ....toilet din ya leka tare da sakin murmushi ganinta kwance cikin ruwan zafi tana bacci hankalinta kwance .....
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_87 to 88_*
Girgiza kai yayi ..sannan ya dauko katon towel ya nadeta ciki ya kwantar da ita saman gado tare da shafa mata cream kadan ....
Cikin kayanta ya dauko wata doguwar riga mara nauyi ya saka mata...sannan ya shafa mata powder ...wasa wasa kwalliya ya mata sosaae tana baccinta don lallabata yake kamar kwae ....
Fita yayi ya leka part din hanne ga mamakin shi ya tarad da ita kitchen tana hada masu break ....sai da ya tayata suka hada komae sannan ya koma dakin Hudah ....
Lokacin ta tashi amma tana kwance idonta na kallon sama ....Tana jin shigowarshi ta maida idonta ta rufe ..
"Hudah ....baki tashi ba har yanzu ....!!ya fada tare da shafa wuyanta ...
Da sauri ya janye hannunshi ...yana kallon fuskarta ...."Subhanallah ...Hudallah...ba dae baki lafiya ba ? ...ya fada a rude ...
Dagota yayi tare da rungumeta yana mata sannu ......
Sae da taji duk ya rude sannan ta bude ido tana hararanshi ta kasan ido ...
"Bakya lafiya ne Hudah .?..sorry fada man kinji ...!! ya sake tambayarta a rude ..
Banza ta mashi na tsawon lokaci sannan tace ..."Lafiya na lau "
"Amma jikinki zafi Hudah "...ya fada tare da dago fuskarta ..
Haka jikina yake fa Uncle ...!
"Kin tabbata lafiyarki lau ? ...
daga mashi kai tayi tare da mikewa a hankali ta bar dakin ...ba tare da yace mata komae ba ya bita da kallo har ta bar dakin ....
*_4 month_*
"Uncle wallahi wannan rito ne ...kuma baran yarda ba .."..ta fada tare da rike guiwar kafarta ..
"Ga Auntynki nan ta mana shari'a ...ai ta gani tsabar rigima ne irin naki ...kuma kema kin san ni nayi winning ba ke ba....."
Kusa da hanne ta koma tare da dafa kafadarta ..".Aunty hanne dan Allah ba sae da ya'yan wasana suka shiga ba sannan ya saka nashi? ...
Cikin dariya Hanne tace .."kinga Hudah ba ruwana da rigimarki ...kufi kusa...idan kin gama kya sameni kitchen ....
Gwalo ya mata tare da mayar da kudinshi aljihu ....
"Wallahi Uncle sai ka bayar dasu ...tun da bani nace ka sa kudin ba" ...
Ta fado jikinshi tana kokarin karbar kudin ...fito dasu yayi tare da yin sama da hannunshi yana mata dariya ....
Kokowa sossae take sae ta karbi kudin ...hannuwanta duka biyun ya hade tare da matseta a kirjinshi yana mata cakul kula ...
Zuciyar ta ji tana tashi ...ta fara kokarin fita daga jikinshi saboda bata son kamshin turaren dake jikin kayanshi ....bai lura da yarda take ba ...ya rike ta gam ..
Ganin ta fara kakarin amai ne, ya sashi dagota da sauri ...kafin yayi wani kokari ta wanke mashi jikinshi tsaf da amai ...
Sam Aman bai dameshi ba ..."sorry" kawae yake fada tare da rike fuskarta da duka hannuwanshi ...
Sae da Aman ya lafa sannan ya dauketa ya shigar da ita toilet din dakinshi ya wanke mata jikinta tare da mata wanka sannan ya fito da ita ya zaunar da ita gefen gado ...ya koma yayi wanka ya canzo kaya ...
"Sorry Hudah ....." ya fada a hankali kamar zaiyi kuka ....
daga mashi kai tayi a hankali ...sam bata kaunar kamshin turarenshi amma barata iya gwada mashi ba ...rungumeta ya sakeyi sossae ...yana shafa fuskarta ...
A hankali hawaye suka fara bi mata fuska ...lokacin da yake kokarin kwantar da ita sossae a jikinshi lokacin zuciyarta ke kara tashi ....cikin dubara ta zame jikinta tana mashi murmushin yake ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_89 to 90_*
Da daddare ta kwashe duka turarukanshi ta boye ....da ya tambayeta sae cewa tayi "ta gyara dakin ne ta manta inda ta ajesu" .....
da yake ranar ba gurinta zai kwanta ba ...sae tayi baccinta lafiya .....
Ranar da ya dawo dakinta kuwa ...kwana tayi tana amai gashi ta kasa fada mashi shine silar aman nata ...tun da safe ya kaita asibiti ...
Doctor ya tabbatar mashi da matarshi tana da ciki wata 2 ...farinciki sossae ya nuna ...shi kanshi doctor din sae da ya sami kyauta ta musamman ...
Kasa Hakuri yayi ya wuce da ita gidansu ...acan yake gayawa Mamanshi wae Ya kusa zama Abbah ...dariya maman tayi cike da kunya ta barshi ....Haka Hudah kasa ko da motsi tayi saboda kunya .....
Tun da suka shiga Mota taki ko da kulashi ..ya sani sarae fushi take dashi .....Hannunta ya kamo ya rike tare da kallon Fuskarta ...ganin sam hankalinshi ba ga hanya yake ba ya sata kwace hannunta tana hararanshi ...
" Uncle ka kalli gabanka mana "..ta fada tana hararanshi ..
"Taya zan kalli gabana bayan kina fushi dani Hudah .?...to naji nayi laifi kinji ko ...kiyi hakuri, farincikin da nake cikine bara ya boyi ba ba ...!!
Turo baki tayi tana kallon taga ba tare da tace komae ba ...hannunta ya sake kamowa ya hade da sitiyarin motar yana murzawa a hankali ...
Dan satar kallonshi tayi taga yarda duk ya damu da fushin nata ....kwantar da kanta tayi saman kafadarshi tana shafa gefen fuskarshi ...
"is ok Uncle ..Hudah barata taba fushi da Uncle dinta ba ....!! ...ta fada cikin kunnenshi
"Are you sure !...ya fada a hankali tare da parking motar kasan wani icce ...
Daga mashi kai tayi tare da sake mashi murmushi ...."Me zamuyi nan Uncle?
"Na gaji ne nake so na kwanta bisa k'ashin matata na huta for some minutes ...!!
Turo baki tayi .."Lallae Uncle ni ce k'ashin ? ...wallahi zaka maimaita ...!! Ta fada tare da girgiza kai..
" Oho dae ...Lokaci da zaki bukaci na maimata ke kanki rokona kike na barki .."..ya fada tare da kwantar da kanshi saman cinyarta ...
Wani uban ihu ta sake jin kamshin turaren nashi ya cika mata hanci ..ga har zuciyarta ta fara tashi ....yayi saurin tashi zaune yana tallabo fuskarta ...
"Menene Hudah "..,.Ya fada a rude ...
"Uncle Kaza ...Ji Uncle dan Allah ka sayar man zanyi kiwo ko guda Daya ce please",..ta fada don bata so ya fahimci wani abu ... _a tunaninta duk yarda na miji ya kai ga sonka bara ya ji dadi ba kace baka son wani abu daya dangance shi_
"Ohoo Hudah Wae meke damunki ..?..duk wannan ihun na kaza ne ...?..Allah ya shiryeki !! ....ya fada tare da bude motar ya fita ...
Gurin da yaga kejin kaji ya nufa ...ya iske saura kaza daya da zakara ...kudin ya biya aka saka mashi su cikin kwali sannan ya sayar masu buhun abincisu daya ....
Harde Hannayenta tayi tana watsa washi wani wahalallen kallo ..."He's such a cring person ....!! ..ta fada a hankali tare da bude mashi motar ya shiga ...suka saki murmushi lokaci guda ...
Duk lokacin da Uncle dinta zai kwana dakinta sae ta sami kerosine ta shafa a wani hanky ta riga sinsinawa ba tare da ya lura ba ...hakan da take yi ya mata rage yawan aman da take ...
••°°••
Kamar yarda ta fadawa su barister Shehu ...wanda ya sayi gidan a hannunsu yaje yace su fitar mashi daga gida..daga farko dad din yace bai yarda ba ...sae da mutumin ya nuna mashi takardun gidan tare da shaida ...sannan ya kalli Shehun cikin bacin rai zaiyi magana...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_BONJEN muyitda bueda...Aunty sis , Jeedah Aliyu,Ummi A'isha, Asy khaleel , Pherty ,Khaleesa ,Afra ,Hajja ce , Queen Mermue ,Nafee Anker, Asmy B, Billy B ,Billy G, Candy, Classic, Aisha Muhammad ,Maman khadija ,😘😘😘_*
*END...*
Sae yayi shiru ganin ba amfanin maganar domin shehu kamar gawa yake sae tarda akayi dashi ....haka suka tattara kayansu suka bar gidan ...Allah ma ya soshi guest house dinshi yana nan ....suka koma can ...
Cikin Yan watanni kudin magani suka fara cinye duk wani abu da ya mallaka...ga shehu akwance paralysis ya gama dashi kullun abun karuwa yake ..sannan shi da Hajiyar kullun suna neman magani amma abun ba saa
••°°••
Hudah kuwa Uncle Mahmoud soyayya yake nuna mata kamar ba gobe ..sannan shi da kanshi yace ta bari ta haihu sae ya maidata makaranta ...
Suna zaune cikin garden lokacin ta daina jin warin turaren da yake sawa ....lafe take a kirjinshi yana karanta mata wani novel .. _Tears drop at the sunset_ Zakaran da ya sayar mata ya biyo kazarta tibi tibi ...suka zo suka wuce ta shinfidarsu da gudu ...
Kallonta yayi yana fadin ..."Umhum ...dama barewa zarayi gudu ne danta yayi rarrafe ..."
Sam bata fahimci inda zancenasa ya dosa ba ...ta dago tana kallon kajin tare da fadin .."Uncle sun yi girma ko?
"Dole suyi girma man ...tun da mamansu ma ta kara girma ...sae dae ya kazar ya mamanta ...!!
" Uncle ban gane ba ?...ta fada tare turo da baki ...don ta fara gane magana ya fada mata ...
Huh ...yarda kazar ke gudun zakara haka mamanta ma ke guduna...kin fahimta sossae ko ?
Dan duka ta kai nashi a kirji tare da fadin ... "Kai uncle !!
" Ba haka bane ? ...ya fada tare da kafeta da ido ...
Kara shigar da kanta tayi a kirjinsa ... "to yi Hakuri ai kaga bana lafiya ne ?
Ko ? ....Ya tambaya tare da saka hannu a yana shafa jikinta ...
Bata ce komae ba sae turashi da tayi ya kwanta ta daura kanta saman cikinshi tare da lumshe ido ...
••°°••
Tun safe ta sakashi gaba tana masa kuka ...tambayar duniya ba wadda bai mata ba amma taki bashi amsa ...
wajen sha biyu ya fito daga wanka ya iske still inda ya barta tana sharan hawaye ...
Hannu ya mika yana fadin ..".Haba Hudalliyar Yaya Sa'a zo nan ki fada man me kike so kinji ko .!!...ya mikar da ita tare da zagaye kugunta da hannunsa ...
Turo baki tayi tana fadin ...
"Uncle ina indomie din da ka dafa man ranar da ka daukoni daga gidanmu ? ..
Ido ya waro ..."duk da dai ya manta amma Bai isa yace bai tuna ba ...sae cewa yayi " Na ma isa na manta ta Hudah ..ya akai ?
" Ita nake so ka sake dafa man yanzu " ...ta fada tare da kwantar da kanta a kirjinsa ...
" Hudah!! ....ya fada da sauri .."Over 6 years fa kenan ?
" Bara ka tuna yarda ka hada ta ba ? ..ta tambaya a hankali ..
" Haba Hudah ..taya zan manta ...bani 30mints yanzu na kawo maki kinji ko ....? ..ya fada tare da shafa kanta
Peck ta mashi a kumatu cikin jin dadi....har ga Allah bawai don ta bashi wahala ba ...aa ta tashine kawae tana son cin irin indomie din ...duk da itama ta manta koda kalar taste din bare shi da ya dafa ...
Kitchen ya shiga kasancewar Hanne bata ban ...tana gurin kasuwancinta ...rasa abunda zaiyi yayi ...Hudah ta riga ta shagwabashi in banda yankan albasa da zuba maggi a abinci babu abunda ya iya ..hana rantsuwar tana bashi ya mata taste yaji idan abincin yayi dadi da kuma zubawa a coler ....
Lumshe ido yayi a hankali ya bude fridge dauke da addu'a ...ya fito da fura da youghurt da inibi da kwakwa ya zuba a blender ya dama mata ...sannan ya saka kankara kadan ...
Sae da yayi addu'a sannan ya shiga dakin ...cikin fara'a ta mika mashi hannu ..tana ganin fura ta bata fuska zatayi kuka ...
Dukawa yayi gabanta tare da dafa guiwarta .."
"sorry Hudah ...wallahi da zan iya tuno yarda na dafa maki ita babu abunda zai hanani kare rayuwata a matsayin kukunki ...Kin sani duk wani abunda zai sakaki farinciki nima shi nake so Hudah ...Kiyi Hakuri kinji ko ..ki sha furar kafin naje kitchen din na dafa har Allah yasa zanyi wadda zata maki dadi kinji ko ...!!
Hannunta ta kai ta karbi furan tare da rike hannunshi da cup din guri guda ...sannan ta saka gudan hannun tana shafa sumar kanshi ..tare da kissing din goshinshi ...
"Nagode Uncle .!!....ta fada cikin kunnen shi tare da hura mashi iska a hankali ..
" Zan sha wannan din ka ji uncle dina ...wallahi indomie din ma ta fita raina karka damu ...kayi hakuri idan na bata maka rai ...!!.
°°••°°.
Cikinta na cika wata tara ta haihu santaleliyar diyarta mai kama da Babanta ....Murna gurin family din ba'a magana ...kudi kuwa kamar suke nomansu ...
Ranar suna diya taci Sunan Sa'adatu ...ana kiranta da MUNIFFAH ( _Sabon farinciki.._ ) ...ita kanta Hudah bata san sunan Mahmoud zaya saka ba ...sae daga baya take ji gurin wanda suka shigo ....
Tana zaune tana bawa babyn mama ya shigo cikin mayan kaya yayi mata masifar kyau ....dagowa tayi ta zuba mashi ido har ya iso kusa da ita ...tare da dukawa ya sumbacin babyn sannan ya kai lips dinshi saman na Hudah yana kallon cikin idonta
Lumshe ido yayi yana fadinn .."Wannan kallon fa? ...baki san kin haihu ba ? ko so kike ki ja man aiki !!!
Dan murmushi tayi mai sauti kafin ta zame daga kan gadon ta koma kasa tare da rike kafafuwanshi ...
"Uncle ...ban da wani bakin da zan iya gode maka ..Illa iyaka na barwa Allah ya saka maka da mafificin Alkhairi ....Tabbas kai haskene daga lokacin da Allah ya hada ni da kai na tabbata na cika mai sa'a ga dukkanin rayuwata ....Uncle duk yarda kake tunani ka wuce anan arayuwata ...ka zama wani jigo babba gareni ...ka katangeman duk wani bataccen lamari a rayuwata ...Tabbas ban da kamarka Uncle ..sae dae ina tabbata maka da ana bautawa wani babu abunda zai hana Hudah dawwama tana bauta maka ...Sae dai Alhamdulillah Allah kadae muke bautamawa kuma shine zai saka maka da abunda kaman ...Na maka alkawarin Uncle zan dauwama ina faranta maka har na koma ga mahaliccina ......
Dagota yayi a hankali ya rungumesu tare da babyn a kirjinshi .......
_Rabbana aamannaa bimaa 'anzalta wat-taba'nar'rasuula faktubnaa ma'ash shaahidiin....🙏🏻_
_Bhoti munkje abta neyza pyaza wutebin photah nahi myezida boti..._