K'ok'arin saita kansa yayi had'i da rik'o hannunta suka zauna saman kujera... Lokaci guda yake mata nasiha gameda duniya da kuma tawakkali da duk wani hukuncin da Mahaliccin ka ya k'addara zai sameka... Saida yayi mata nasiha sosai ya kwantar mata da hankali kana yaci gaba da fad'in "Salma ina so ki nustu kuma kimin alk'awari bazaki d'aga hankalin ki ba...."
A hankali ta jinjina masa kai kana tace "Insha Allah bazan d'aga ba Soja...."
Jinjina kai Naseer yayi kana yace "Jamila ce take asibiti bata da lafiya tana nan asibitin koyarwa, tun daren jiya suke asibiti saidai basu sanar damu ba gudun kada hankali ya tashi... Amma da sauk'i don yanzu Fawaz ya min waya yana can...."
Duk juriyarta ganin batayi kuka ba saida taji hawaye na ciko idanunta, duk yanda taji mai jinya yanzu tsoro take ji, musamman wani nata tunda ta rasa mahaifanta... A hankali ta soma jinjina kai ba tareda ta d'ago idanun ba take fad'in "Soja ka kaini pls, ka kaini naga Addah don Allah...." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya...
Rungumota Naseer yayi cikin jikinsa yana lallashi kana yace "Zan kaiki Salma amma sai kin kwantar da hankalin ki, idan kikaje wajenta haka zaki kuma d'aga mata hankali ne, kuma mai ciwo irin nata basa son tashin hankali kinji koh..."
Kallonsa Salma tayi hawaye na bin k'uncinta kana tace "Soja wani ciwo ne ke damun Addah? "
Saida ya d'an yi jim, kafin ya shafi goshinsa ya d'ago had'i da rik'o hannayenta kana yace " She's surfing from Cardiovascular disease,.."
Girgiza kai Salma take tana dubansa kana tace "Soja wllhi ban gane ba, hasalima ban tab'a jin irin sunan ciwon da ka ambata ba... Me hakan yake nufi...."
Naseer ya kuma rik'ota tausayin ta na ratsa zuciyarsa kana yace "Ciwon zuciya...."
Bursting Salma tayi cikin kuka tana fad'in "A'a ba Addah Jamila ta ba k'ila dai bakaji da kyau ba... Don Allah kace min ba ita bace...." Gaba d'aya she's going out of control...
Sosai Naseer ya rungumeta yana kwantar mata da hankali ta hanyar lallashi had'i da nuna mata illan tada hankalin ga lafiyar 'yar uwarta... Saida ya tabbata ta sami nutsuwa kafin suka mik'e suka nufi asibitin...
***
Suna isa suka tarar su Momy ma isowarsu kenan, Momy da Aunty Saudat Lubna kuma ta tafi exams...
Cikin sauri Momy ta k'arasa ta rungume Salma wacce tun daga hangosu kuka ke k'ok'arin kufce mata, kai tsaye Amenity ward suka nufa gaba d'aya... Sister Nafisa ce ta hangesu idanunta gaba d'aya itama sun kod'e sabida kuka, tana rungume da Falaq a hannunta, cikin sauri ta k'arasa tana directing nasu d'akin da Jamila take....
Fawaz dake can gefen d'akin yana hangosu ya fice cikin sauri daga ward d'in hawaye shar-shar a idanunsa. ...
Aunty Saudat tabi d'an nata da kallo cikeda tausayin sa, itama sai taji hawaye na neman ciko idanunta, zuciyarta na neman karyewa....
***
Ilham suka hanga zaune gefen Jamilar hannayen su rik'e cikin na juna, ga na'uran taimaka ma numfashi manne a hancin Jamilar, idanunta a lumshe alamun batama san mai ke wakana ba...
Shareefah da Mamy harma da Affan suna rakub'e gefe abin tausayi.... Sosai hankulansu ya tashi musamman Shareefah wacce suka sha fira da Jamilar a daren jiya, ikon Allah kenan, cikin k'ank'anin lokaci sai ya maidaka ba komai ba, amma d'an Adam baya hankalta....
K'arasawa Salma tayi jikin gadon Jamilar, had'i da kamo hannayen Jamila da Ilham, Ilham tanajin hannu saman nata tasan cewa 'yar uwarsu Salma ce ta iso...
Murya na rawa Ilham take fad'in "Addah Salma, kice min Addah Jamila zata tashi, don Allah kice min bazata tafi ta barmu kaman yanda Baffah da Innoh suka tafi suka barmu ba..." Salma dake k'ok'arin rik'e kukanta sam bataso ta ta kuma tada wa k'anwarta hankali, dole tayi k'ok'arin saita kanta kafin ta rungume Ilham murya na rawa take fad'in "Ilham ki kwantar da hankalin ki Addah zata sami lafiya kinji koh... Mu ci gaba da mata addu'a.. Zata warke da yardar Allah..." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya had'i da lumshe idanu tuni hawaye sun gangaro saman kumatun ta...
Gaba d'aya mutanen dake cikin d'akin tausayi da tsoron duniya ya cika zukatansu... Mamy kam hawaye ne taji suna zarya a fuskarta, don ba kowa ya fad'o zuciyarta ba illa Azeema... Cikin sauri Mamy ta fice daga d'akin don sosai taji kuka na zuwa mata...
Alh Ali Safwan ne da wasu likitoci guda biyu suka shigo bayan sun gama tattaunawa... Nan likitocin suka buk'aci a d'an basu waje su duba maras lafiyar...
Salma da Ilham a tare suka fice suna rungume da juna abin tausayi...
Affan da Naseer ma suka fice a tare don sai lokacin suka sami zarafin magana ma juna.
Shareefah ce keta faman kwantar wasu Salma da hankali yayinda Momy ke tareda Mamy itama baki take kan faman bata...
Aunty Saudat kuwa can bayan ward d'in yanda ta hangi Fawaz saman wasu kujeru ta nufa don basa baki, gaba d'aya Fawaz ya fice a hayyacin sa...
Baisan sanda ya rungume mahaifiyarsa yana kuka sosai ba...
"Mum I love her.. I still do love her.... Mum don Allah kice Jamila zata tashi...." Kasa ci gaba da magana yayi sabida kukan da yaci k'arfin sa...
Sosai Aunty Saudat ta rungumesa tana shafan sumarsa take fad'in "Fawaz addu'a zaka mata ba kuka ba... Jamila tanada rai ka daina kuka tamkar wacce ta Mace babu dawowa... Kayita karanto mata addu'o'i kaji koh...."
Bai iya amsata ba sai jinjina mata kai da ya shiga yi tamkar k'aramin yaro....
Su Sadiya dasu Zainab k'awayen Nafisa dake kewaye da ita gaba d'aya tausayin Nafisa ya cika masu zukata, musamman idan suka kalli yanda take rungume da Falaq, duk tsiyan da suke mata sarkin tausayi sarkin imani yau sai jikkunansu yayi sanyi gaba d'aya, sai faman bata baki suke suna fad'in k'awarta Jamila zata sami lafiya da izinin Allah... Tabbas ba daidaiton shekaru bane k'awance idan hankali da tunani yazo dai-dai ne ake abota, don kuwa Jamila ta grime ma Nafisa, Nafisa saidai tayi sa'a da k'anwarta Salma, domin kuwa d'aliba ce a kwalegin d'alibai dake cikin asibitin na horas da malam jinya....
***
Suna zazzaune a reception suna jiran fitowar likitocin kowa da irin addu'ar dake bakinsa nan suka hangi Dr guda ya fito ya nufosu...
A tare suka mik'e gaba d'aya suka nufi likitan...
Dr ya shiga kwantar masu da hankali yana fad'in ta farfad'o kafin ya buk'aci Salma da Ilham su shiga su gana da 'yar uwarsu kaman yanda ta buk'ata... Aiko kaman jira suke cikin sauri suka nufi d'akin, Salma na rik'eda Ilham....
Jamila tana hangosu ta saki murmushi, fuskarta tayi fayau sosai alamun mai jinya, hasken fatarta da dogon hancinta ya kuma fitowa, kyaunta ya kuma bayyana sosai yau d'in dama duk tafi su kyau.
Murmushi suke suna goge hawayen idanunsa sanda suka isa gareta, bud'e masu hannaye Jamila tayi cikin murya irinta marassa lafiya tace "Kuzo nan..."
Babu musu suka isa suka rungume Addarsu Jamila...
Ilham fad'i take "Addah nasan zaki tashi.... Nasan bazaki tafi ki barmu ba...."
Murmushi Jamila tayi tana shafan fuskar Ilham kana tace "Ina sonki, ina sonku gaba d'aya.... Allah yayi maku albarka, ko yau na bar Duniyar Mu nasan 'yan uwana suna hannaye masu kyau...." Ta maida dubanta ga Salma kafin taci gaba da fad'in "Salma nasan nayi abubuwa da dama marassa kyau a baya, amma tuni na fahimci kure na kuma na gyara, keda Ilham da kuma Falaq ina k'aunarku, kuma ina fata na had'u daku a rayuwar da zamuyi gaba... Salma ki rik'e 'yan uwanki ki kuma rik'e hud'ubar dasu Baffah suka mana.... Kar kuyi watsi da wasilcin Baffah da Innoh domin kuwa iyaye jigo ne na rayuwar d'an Adam.... Sannan nima irin wasiyar da zan maku kenan, ko kusa kada ku bari k'yale-k'yale na duniya ya rud'eku har ya kaiku ga sab'a wa mahaliccin ku...." Tari ya hanata ci gaba da magana.....
Daga Ilham har Salma kuka suke babu ko k'kk'autawa... Ilahm kam ta kasa fad'in komai sai kuka...
Salma cikin shesshek'a take fad'in "Addah don Allah ki daina mana irin maganganun da Innoh ta mana, Addah nasan zaki sami lafiya, zakiji sauk'i cikin yardar Allah.. Don Allah ki daina karyar mana da zukata don Allah....." Kuka yaci k'arfinta itama...
Rungume juna sukayi gaba d'aya su duka ukun suna kuka sosai mai ban tausayi... A haka likita ya shigo ya samesu kafin ya buk'aci su Momy su fitar dasu...
Kallon likitan kawai Jamila take tana murmushi sanda d'akin ya rage saura ita da likitan kana tace "Dr babu abinda zaka iya min a yau, ina ganin abinda kai baka gani.... Don Allah ka k'yaleni nayi sallama da 'yan uwana...."
Jikin Dr yayi sanyi sosai don shi kansa yasan Jamila tana jin jiki yamaji mamaki da har take iya magana, idan kuwa da gaske ban kwanan take lallai Allah ya bata daman da bama kowa yake badawa ba....
Muryarta ne ya katse ma Dr tunanin sa..
"Dr ka taimaka ka kira min Dr Fawaz Santana da kuma Sister Nafisa Arabi.."
A hankali Dr ya jinjina kai kafin yayi yanda tace...
Nafisa ce ta soma shigowa tana rungume da Falaq, hango Jamila da tayi kwance saman gadon marassa lafiya sai ya kuma karyar mata da zuciya...
Tunda Jamila ta hangi Falaq take murmushi har suka k'araso gareta, da k'yar Nafisa ta zauna gefen Jamila ba tareda ta bari sun had'a idanu ba sabida hawaye ne tab cikin idanun nata...
Hannu Jamila ta mik'a ta d'an kamo hannun Falaq da tunda suka shigo take faman mata murmushi tana tsalle alamun taga mahaifiyarta...
Jamila ta shafi fuskar Falaq fusaknta cikeda da murmushi kana tace "Allah maki albarka masoyiya ta.... Naso na rayu dake A DUNIYAR MU na baki duk wani kulawa da kika rasa daga wajen mahaifin ki amma Allah bai k'addara hakan ba.... Ki sani Allah baya barin wani don wani, Al'amarin sa _Kun fa yakun_ ne, ina sonki Falaq ina k'aunarki da duka zuciyata, ina rok'on mahalicci na ya rayaki cikin aminci da tsoronsa... Allah yayi maki albarka...." Tana kaiwa aya taji Nafisa ta fashe da wani irin kuka, kukan da take kan faman dannewa... A dai-dai lokacin kuma Fawaz ya turo k'ofar d'akin ya shigo, Idanunsa shima a jik'e suke sharkaf.... Tamkar wanda ruwa ya shanye haka yake takawa har ya isa jikin gadon da Jamila take....
Cikin muryar kuka yake fad'in "Why? Why Jamila, meyasa kika saka ma ranki damuwa bayan baki d'auke da wata cutar HIV, meyasa kika saka ma kanki ciwon zuciya, meyasa ki kasa sanar da kowa halin da kike ciki... Meyasa kika zab'i mutuwarki sama da rayuwarki... Jamila why...?"
Murmushi take tana duban Fawaz kafin tace "Fawaz ka sani ko d'aya ban zab'a ma kaina mutuwa ba, ka sani idan numfashin bawa ya k'are second guda mala'ikan d'aukan rai baya k'ara masa.... Fawaz wannan shine K'ADDARA TA (littafin Hauwa Usman Hauwata) A DUNIYAR MU, Fawaz ina sonka sannan naso na rayu dakai A DUNIYAR MU amma Allah bai k'addara hakan ba... Ina fata in the next life mu kasance tare, rayuwar da babu k'arshe, rayuwar da take permanent ba temporary ba..... Fawaz don Allah ka rik'e amanar da zan bar maka...." Ta maido da dubanta ga Nafisa da Falaq yayinda kukan Nafisa da Fawaz ya k'aru sosai har baka jiyo sautin kukan sai zuban hawaye...
Jamila taci gaba da fad'in "Fawaz ka rik'e min Falaq amana, ka nisanta ta daga wannan wajen mai tarin munanan histories.... Kaida Nafisa nasan zaku iya zaku iya rik'e min amanar d'iyata kuyi nesa da ita daga nan.... Fawaz Nafisa don Allah kuyimin alk'awarin kasancewa k'ark'ashin inuwa guda, kuyi min alk'awarin rik'e min tilon d'iyata amana...."
Fawaz ne ya katse ta cikin kuka.. Fad'i yake.. "Jay pls stop... Stop saying all those things, Jamila zamu kasance tare A DUNIYAR MU... Zan tambaya mana malamai muddin babu aya ko hadisi ko maganganun magabata da zai haramta aurenmu Jamila zan aureki, wllhi zan aureki...... Zamu kasance tare A DUNIYAR MU Jamila don Allah don't leave me... I love you... So much..." Kuka yaci k'arfin Fawaz..
izuwa lokacin Jamilar ma kukan take, su duka uku kukan suke wanda tuni Falaq ma ta soma kukan kaman tasan abinda ke faruwa....
Cikin kuka Jamila take fad'in "Zan mutu da soyayyarka Fawaz, ka sani ko bayan raina Jamila tana k'aunarka, kuma zaka taddata a rayuwa na gaba cikin yardar Allah.... Nafisa na gode nasan nayi katsalanda ma rayuwarki da yawa, but pls do this for me, for my only daughter pls Nafisa....." Ta kasa ci gaba da magana sai tari da take babu ko k'akk'autawa.... Nafisa da Fawaz kuwa sai kuka..
Tuni jini ya soma kwararowa daga bakin Jamila, a d'ari Fawaz ya fice tamkar zaucecce yana kiran sauran likitocin wanda yasa hankulan mutanen dake wajen kuma tashi.... Kan kace me Nafisa ma ta soma nata iya k'ok'arin
Saidai kafin likitocin su iso tarin ya lafa mata sai salati da take karantowa a hankali, shigowan likitocin tareda Fawaz a dai-dai lokacin ta rufe bakinta da kalimatusshahada....
Durk'usawa Fawaz yayi a wajen saman gwiwoyinsa yana hango idanunta yanda suka kafe suna kallon sama... Ya nemi kukan da yakeyi ya rasa....
Dai-dai lokacin wani nurse da police officer suka shigo da Alh Kabeer saman keken guragu da shike yana cikin asibitin ba'a sallame sa ba, tunda yaji an kawo Jamila babu lafiya yake rok'on a kawosa wajenta ya nemi gafarar ta...
Juyowan da Fawaz zaiyi suka had'a idanu da mahaifinsa... Wani irin tsalle yayi ya shak'e mahaifin nasa yana fad'in "This is all your Fault, I swear I'll kill you, wllhi kaima sai na kashe ka yau...."
Police d'in ne keta k'ok'arin k'watan Alh Kabeer daga hannun Fawaz don tuni ya soma zaro idanu waje.... Saida Naseer ya shigo ya janye Fawaz kafin aka samu Fawaz ya saki wuyan mahaifinsa..
Sosai Fawaz yake kuka yana duban Naseer yake fad'in "Uncle this man's nothing but a disaster, he's nothing but a curse.... Uncle please......" Kasa ci gaba da magana yayi sai durk'ushewa a wajen da yayi yana kuka mai tsuma zuciya...
Su Salma da Momy ta d'an fice dasu daga ward d'in suna hango Nafisa ta fito cikin kuka suka mik'e tsaye cikin tsananin tashin hankali.....
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*66*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Kallo Dr Fago yabisa dashi bayan ya sanya kayan ya fito parlor.... Dr yayi murmushi yana mai duban Fawaz d'in kana yace " Ka mance hula...?"
Fawaz ya d'an kallesa cikeda k'osawa don harga Allah sam baison yin musu wa Dr Fago, dukda abokin sa ne amma ya girme masa, d'an yamutsa fuska yayi kana yace "Dr please... Wllhi nauyi yake min..."
Jinjina kai Dr yayi kana yace "Na sani amma don Allah ka saka na yau...."
Fawaz ya d'an dubesa kafin ya koma cikin d'akin, closet d'in nasa ya nufa yanda huluna ke jere tamkar mai sakawa, layin Zanna daban na damanga daban...
Bak'ar damanga ya d'auka ya saka saman kwalliyan shaddar nasa ruwan toka, abinka da farin fata sai shigar ta amshe sa sosai, dukda rama da yayi amma kam yayi kyau...
Dr Fago na ganinsa ya saki murmushi kafin ya mik'e yana fad'in su tafi...
Ta window su Aunty Saudat suka hangi su Fawaz, dad'i ya cika zukatansu, Dr Fago ya cika abokin amana....
Dr Fago ke driving Fawaz na gefe har suka iso unguwar Jahun yanda gidan su Nafisa yake...
Kallon Dr Fawaz yake sanda ya ida parking d'in kafin yace "Dr wai dan Allah ina ne muka zo....?"
Dr Fago ya murmusa kana yace "Wajenta muka zo...."
Gaban Fawaz ya buga, lokaci guda yake duban Dr Fago.... Kai amma Dr ya shammace sa, da yasan wannan ne plan d'insa sam da bai biyesa ba... K'ila baisan yanda yake ganin girmansa bane da baiyi katsalanda irin haka ma rayuwar sa ba...
Ko takan Fawaz bai bi ba ya hangi wasu yara zasu shige gidan da alama nik'a zasu kai cikin gidan, kiran yaran yayi da niyyan aikensu saiga wani dattijo ya fito daga cikin gidan hannunsa rik'e da cazbaha da alama shine mahaifin Nafisa...
K'arasawa Dr Fago yayi yana mai rusunawa yake gaidashi, lokaci guda Fawaz ya fahimci Dattijon shine mahaifin Yarinyar... K'arasawa shima yayi had'i da d'an duk'awa ya gaida mutumin wanda yaji Dr Fago na kiransa da Baba...
Faran-faran mutumin ya amsa masu yana mai fad'in "Faruqu kun sami isowa kenan...."
Jinjina kai Dr Fago yayi still suna duk'e a k'asa kana Baba yace "Toh madalla sannunku da zuwa...." Ya dubi yaro guda dake k'ok'arin shiga gidan yace "Kai yaka d'an saurayi maza shiga kace Habibu ya fito da tabarma ko.. "
Yaron ya jinjina kai yana fad'in "Baba mai mashin yau bazaka bani carbin malam d'in bane..."
Murmushi Baba yayi kana yace "Ba'a gama ba, anjima sai kuzo ku karb'a koh...."
Yaron ya shige yana d'an tsalle had'i da murna...
Baba yace "Hankali dai kar ka zubda marked'en naka...."
Duk wani k'unci da Fawaz ke ciki sai yaji zuciyarsa ta masa sanyi, wannan Dattijo ya burgesa, gashi dai environment d'in da suke rayuwa babu wadata amma kuma suna living lives d'insu cikin jin dad'i da kwanciyar hankali, abinda ya rasa A DUNIYAR SA, ya kuma yarda arziki ba shine jin dad'i A DUNIYAR MU ba, kwanciyar hankali shine gaba da komai.... Allah sarki Fawaz ire-iren tunanin da yaketa yi kenan a zuciyarsa....
Bayan an kawo masu abin zama k'ofar gida sun zauna ne Faruq Fago yayi introducing Fawaz d'in wa Baba donma already Baba yasan da zuwan su.... Mamaki ne kurum ya cika Fawaz yanda yaji Dr Fago nata kwararo bayanai akan sa...
Baba ya d'anyi gyaran murya kana yace "Faruqu kai ka zamto kamar wa a wajen Nafisatu, kai kayi duk wasu d'awainiya na karatun ta, mai babban suna (Da shike sunan mahaifin Baba Dr Faruq Fago kedashi wato Umar, don haka bai kiransa Umar kai tasye ko ya kirasa Faruqu ko ya kirasa mai Babban suna) na tabbata bazaka tab'a zab'awa Nafisatu abinda zai cutar da ita ba koda baka kasance miji a gareta ba, babu maganar bincike muddin kai ka kawo wa Nafisatu miji, don ka wuce gaban bincike a wajen mu Faruqu.... Amma kasan shi sha'ani na aure abune mai but'atar nutsuwa da kuma fahimtar juna.... Idan Nafisatu ta amince babu matsala daga wajena saidai nayi masu fatan alkhairi, burin ko wani mahaifi ne d'iyarsa ta sami miji na gari..."
Jinjina kai Dr Fago yake yayinda jikin Fawaz yayi sanyi sosai, don Baba saida ya masu nasiha mai shiga jiki sosai, gaba d'aya Fawaz sai yaji sha'awan inama shikeda mahaifi irin haka.. Allah sarki abinda ya rasa A DUNIYAR SA...
Koda suka zo tafiya Dr Fago ne ya buk'aci zasu shiga su gaida Mama don shi dama d'an gida ne, sabida Fawaz d'in ya nemi izini wajen Baba...
Sallama sukayi tun daga zauren cikin gidan.... Gaba d'aya bataji sallaman ba don earpiece ne manne a kunnenta sai faman tankad'e garin tuwo take.... Tana sanye da riga bulawus had'i da zanin atampa....
Mama ce ta fito tana amsa sallamar lokaci guda take faman fad'awa Nafeesan....
Ai bata ankare ba sai ganin mutane tayi suna shigowa, da gaske Dr Santana take gani cikin gidansu.... Zunbur ta mik'e tana cire earpiece d'in tana binsu da Kallon mamaki, ko a hanya bata tab'a kiliya da Dr Santana cikin irin shigar da ta gansa yau ba.... Banda shirirta na Nafisa sai ta soma tuno k'awayenta su Sadiya masu son Dr Santana yau kam da zasu gansa cikin wannan shiga da sun kuma mutuwa akansa.... Lokaci guda Jamila ta fad'o ranta da wasiyar data bar masu.... Gabanta yayi wani irin yankewa ya fad'i... Muryar Mama kurum taji tana fad'in "Lafiyarki kikayi tsaye wa mutane haka kina dubansu... Zaki wuce ko kuwa...."
Sum-sum Nafisa ta shige d'aki ba tareda ta sami zarafin masu magana ba.... Fawaz yabita da kallo don zai iya cewa bak isa ya tantance kamanninta ba sai yau, bak'a ce amma ba can ba, bata da tsayi sannan bata a layin gajeru... Tanada d'an jiki kad'an da ya tafi da dai-dai tsawonta.... Sam Nafisa ba irin matan da yake so bane.... Shi gaba d'aya ma soyayyar Jamila bazai bari ya dubi wata mace yaga wai har ta masa ba... Tabbas auren Nafisa da zaiyi saidai yayisa domin Jamila da kuma Falaq yarinyar da ya d'au alwashin zai zameta garkuwa A DUNIYAR SU.....
Koda ya koma gida Naseer ya soma tuntub'a da batun, Naseer kuma ya sami Abbu da maganar don sune magabantan sa sune masu nema masa aure... Su kansu sun sha mamakin yanda lokaci guda Fawaz ya kawo maganar aure, shiko a b'angaren Fawaz d'in ba komai yasa ya d'ago maganar auren gadan-gadan ba sai don ya cika ma Jamila burinta ya d'auke Falaq daga Nigeria suyi nesa da k'asar.... Ya d'au alwashin rik'e Falaq har k'arshen rayuwar sa like his own....
Tuni an soma maganar aure gadan-gadan abu kaman wasa....
Wata guda da wasu satuttuka aka saka auren Fawaz da Nafeesa, tuni Affan ma ya kawo nasa k'ok'on baran saidai a had'a aurensa dana Fawaz d'in... Da farko kowa ce masa yayi a bari ayi aikin idon Ilham tunda nan da wata watan likitoci suka ce za'ayi surgery d'in, idan yaso bayan ta warke ayi biki.... Sam Affan yak'i aminta da hakan, kawai shi a had'a aurensa da Fawaz... Naseer kam yaji dad'in hakan don bikin nasu ne ta ko ina....
Satin auren Salma ta tattara ta koma gidan Momy, wani kulawa na musamman Momy ke bata tunda ta lura da kasalan da take yawan yi ga tsiri ba komai take ci ba.... Yau da dare suna zaune a parlor gaba d'aya hardasu Mama Kaltum
Lubna ta kyafta idanu wa Mama Kaltum kana ta bud'e murya tace "Anty Saly waini ba kince wa Yaya a kawo mana Shawarman Spice Cafe bane...."
Harara Salma ta galla mata kana tace "Ban sanin ba ina ruwanki, inace don nace kimin chicken bread ne kike min wulak'anci... Wllhi Food network babu ruwana dake... Kuma ki daina min magana...."
Gaba d'aya dariya sukayi kafin Momy ta janyo Salma jikinta tace "K'yalesu Chicken bread ko na ina kike so za'a sayo maki a daren nan kinji koh... Bari Sojan ya shigo..."
"Momy amma ai nawa take so... Wllhi tak'i cin wanda muka sayo mata jiya a sky crown...."
Salma dai ta cika tayi fam bata ko amsata ba....
Sallaman Naseer ya katse masu hiran tasu....
"Yauwa alhamdulillah gwara da Allah ya kawo ka.... Mama K da Food network sun saka min d'iya a gaba... Sunk'i su mata abinda take so...."
Kallon Lubna Naseer yayi kafin yace "Food network zaki tashi a fav sis idan dai zakina tab'a Reina...."
"Yaya wllhi Anty Saly tsiri ne da ita... Kaga hidiman biki fah ake wai sai na mata Chicken bread kuma wai nawa kawai take so....."
"Eh ki mata pls kinsan lallab'ata ake bata da lafiya...."
Lubna ta saci kallon Salma kafin tayi k'asa da murya sanda Naseer ke magana dasu Aunty Saudat da shigowarta parlorn kenan.. A hankali tace da Salma "kuma sai na saka cinnamon ciki...."
Salma ta kuma galla mata harara kana tace "Na k'oshi bana so ki bar abinki...."
D'an kallon Lubna Naseer yayi kana yace "Anty Foodnetwork zamufa yi fad'a.... Bata son warin cinnamon kar ki saka...."
Gaba d'aya mutanen parlorn dariya sukayi yayinda Mama Kaltum tace "Nidia mun gaji da wannan tsiri an tak'urawa d'iyata Lubna, gwara kuyi ku koma gidanku a bar min d'iyata ta huta..."
Murmusawa kawai Naseer keyi yana d'an sadda kai k'asa yayinda Momy taci gaba da kare Salmar ta.... Kana ganinsu kasan rayuwa ta soma dai-daita masu...
***
Su Momy sun so a dawo da Ilham nan gida wajensu tinda can gidan Daddy za'a maidata idan an d'aura auren.... Saidai daga Daddy har Mamy sunk'i aminta da hakan, a cewar su Ilham d'iyarsu ce koda ta auri Affan...
Ana gobe d'aurin aure Salma ta jima sosai gidan Daddy yanda suka kulle kansu a d'aki itada k'anwarta suka ci kukan su mai ban tausayi, had'i da tuno kalolin iftila'i da suka arangama dasu A DUNIYAR SU, daga bisani addu'o'i sukayi ma 'yan uwansu da suka rigayesu gidan gaskiya... Basu fito daga d'akin ba har saida Shareefah ta shiga ta samesu
***
Ranar asabar shad'aya ga watan Satumba aka d'aura auren Fawaz da Nafisa da kuma Affan da Ilham a babban masalllacin k'ifar Fada dake garin Bauchi... Auren da ya sami halarta mutane da dama... Alh Kabeer na tsare a police station ya sami labarin, kukan na dama da takaici ya dinga yi wanda babu adadi, Fawaz tilon d'ansa yayi aure ba tareda saninsa ba... Allah sarki Duniya kenan mai makaranti aji daban-daban....
Tafe yake saman kwalta sai watsa gudu yake don ya sami auren k'anin nasa kuma amini da kuma 'yar uwa k'anwa a gareshi, gaba d'aya ya makara hakan yasa yaketa falfala gudu saman kwalta... Kaman daga sama yaji ya d'aga wata mata ta fettu gefen kwalta... Cikin sauri Dr Fago ya fito ya nufi matar da ya kad'e.... Jini tuni ya rufe fuskarta saidai ga dukkan alamu matar kaman mahaukaciya ce, sabida yanayin da ya ganta ciki...
Cikin sauri Dr Fago ya ciccib'eta ya shigar da ita motar sa ba tareda k'yank'yanin halin da matar ke ciki ba, burinsa kurum ya ceto rayuwarta... D'aurin auren da bai tafi ba dole ya d'auki hanyar asibiti....
****
Da tsananin mamaki Dr Fago ke dubanta sanda yaji tana magana babu alamun tab'in hankali ciki...
"Kar ka damu kuma kada kaji tsoro ba gamo kayi ba ni 'yar Adam ce just like you.... Likita dan Allah ka taimaka ka kiramin 'yan uwanan kafin na bar DUNIYAR MU...." Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya wanda yafi kama data mai jin jiki....
Dr Fago dai dubanta yake yanda take magana cikeda tsoro ga askin gashi gashi gaba d'aya kamar wata wacce tayi shekaru cikin junyar hauka...
Da k'yar ya iya bud'e baki yace "Baiwar Allah bakisanar dani sunan naki ba balle na 'yan uwan naki..."
Murmusawa ta d'anyi kana tace "AZEEMA...Sunana Azeema, idan kanajin Ali Safwan family toh su zaka kiramin..."
Gaban Dr Fago ya kuma fad'uwa domin kuwa tabbas sunan data kira tare za'a d'aura auren d'an gidan da Fawaz.... A hankali ya jinjina kai kafin ya fice daga d'akin jikinsa babu laka...
***
Jikin Magajiya yayi sanyi sosai da jin labarin Innah, bata tab'a jin tanada ranar barin bayan gari ba sai yanzu.... Lallai ta yarda DUNIYA abar tsoro ce gaba d'aya sai ta koma wata sukuku da ita, al'amarin duniya ya bata tsoro sosai da kuma Al'ajabi.... Babban abinda yafi d'aga mata hankali shine duk jinyar da Innah ke ciki wai bata saduda ba ta sami hali zata d'auki fansar ta... Lallai ta yarda Innah tayi nisa wajen taurewan zuciya....
Jigum tayi tana duban Innah da jikinta ke rawa tamkar mazari... Domin kuwa a 'yan kwanakin ko tsayuwar wasu mintuna jikin Innah baiyi vibrating kawai take tamkar wacce aka saka mata baturi.....
Suna a haka suka ji gidan gefe dasu sai watsewa ake a guje ana fad'in ga 'yan hisba ga 'yan hisba....
Shazali ya shigo a d'ari yana fad'in "Uwar daba ki tashi mu ware mu bar wannan rub'ebb'iyar a nan...."
Kallonsa kurum uwar daba tayi kana tace "Ni sunana Atika daga yau kar ka kuma ce min Uwar daba, kaima ka nustu ka daina daudanci ka tsaya a halittar ka ta namiji da Allah yayika... Kuma babu k'anda zan gudu naje gwara na tsaya a nan a kamani a min duk hukuncin da ya dace dani, domin daga rana mai kaman ta yau na daina wannan mummunar sana'a ehe...."
Baki sake Shazali ke dubanta kafin ya shiga tafe hannaye da cinyoyi yana fad'in "Toh kuwa kinga tafiyata bazan tsaya kimin salalan tsiya ba.... Duniya yanzu na soma cinta fad'i gareta....."
Shazali bai kai aya ba yaji an rapko sa an damk'e aiko nan ya saki ihu yana fad'in Su rufa masa asiri ya mutu a d'aki maza su kaisa....
Kame sosai sukayi a gidan karuwan sannan Innah na d'aya daga cikin wad'an da aka kame.....
****
Gaba d'aya layi sukayi gaban gadon da Azeema ke kwance bisa kowa hawaye na kwararo masa......
Mamy ta kuma rungumo hannayen Azeema tana fad'in "Azeema ki daina karyar mana da gwiwa zaki tashi cikin yardar Allah kinji koh....."
Murmushi Azeema tayi tana duban Mamy kafin tace "Mamy alhamdulillah ko yanzu mahaliccina ya d'auki rayuwata burina ya cika na dawo ga dangi na, na dawo cikin 'yan uwana... Kuma na tabbata Saude bazatayi k'arshe mai kyau ba domin a ranar da nake tunanin an karya asirin da tayi ma Daddy a ranar ta zube a k'asa ta rasa k'afafunta, bata kuma bi takaina ba sai jiya data sakani a mota tace a tafi dani Enugu.... A nan na samu nayi 'yan dabaruna namu na mata har na shek'awa driver d'in hodar da ya kamata ya Shek'a min, na samu na gudo kafin wannan likitan ya kad'eni saman kwalta...."
Ta juyo ga dubanta ga Daddy murmushi saman fuskar ta kana taci gaba da fad'in "Daddy dan Allah ka yafe wa Mamy, wllhi Mamy tayi nadama irin wanda ku bakuyi tsammani ba a gidan Laure, Daddy Laure itace ummul haba'isin d'aid'aicewan zuri'ar ka A DUNIYAR MU... Hassada da k'yashi ya sanyata aiwatar da duk manana abubuwan da ta d'aura Mamy kai.... Daddy Mamy tana k'aunar ka da duka zuciyarta, wllhi ni shaida ce.... Alhamdulillah burina ya cika da na ganku gaba d'aya... Ina k'aunarku..."
Daddy ya murmusa hawaye na zubo masa kafin yace "Allah maki albarka Azeema, tabbas ke d'in Garkuwa ce mana A DUNIYAR MU ba tareda sanin mu ba.... Allah ya maki albarka ya baki lafiya...."
Murmusawa tayi itama, a hankali ta furta "Ameen Daddy..." Lokaci guda ta dawo da dubanta ga Shareefah wacce murmishi da hawaye suka wanke mata fuska...
Mik'a ma Shareefah hannu tayi, Shareefah tayi saurin k'arasawa ta damk'e hannun Azeemar su duka suna murmushi... "Nayi kewarki 'yar uwata.... Sannan na gode ma Allah da ya fahimtar damu muka daina sab'on da muke a baya... Soyayyar gaskiya na tsakani da Allah nake maki a yanzy Azeema, ba soyayyan sab'awa mahalicci ba... Ina rok'on Allah duk masu irin wancan d'abi'an su daina musamman 'yan mata a gida guda da suke had'e d'aki guda ko kuma a makarantin kwana... (K'alubale A DUNIYAR MU... ALLAH Ya fahimtar damu baki d'aya ya ganar da masu wannan mummunar sab'o... Ameen,)
Azeema ta maida kallonta ga Affan wanda shima kwanciyar hankali ta nuna a fuskar sa... Murmushi ta sakar masa shima ya maida mata martani...
Affan ya d'an dubi su Mamy kafin yace don Allah su d'an basu waje yana sonyi magana da Azeema just the two of them...
A tare suka jinjina kai kafin suka fice suka basu waje
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*65*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*Allah sarki, A DUNIYAR MU mai masoya A DUNIYAR MU mai ban tausayi A DUNIYAR MU mai tarin kayan Al'ajabi ban mamaki da kuma nishad'i... Ashe haka A DUNIYAR MU ya sanya idaniya zubda k'walla ya kuma matsowa zukata Allah kusa... Alhamdulillah da wannan baiwa.... Comments d'inku sun sanya jikina yin sanyi sosai da kuma tsoron DUNIYA.... Allah kasa mu gama da DUNIYAR MU lafiya Ameen....♥!*
*Meena Slimzy this one's for you... Kyaun alk'awari cikawa Sameena na k'aunarki fisabilillah😍🤝🏼*
Girgiza kai Salma take tana duban Nafisa wacce Momy ta rik'eta sosai tana tambayarta meke faruwa...
Nafisa kasa furta komai tayi sai hawaye dake kwaranya a idanunta ga kuma Falaq na faman kuka sosai itama.... Momy ta amshi Falaq hannun Nafisa ta zaro d'ankwalinta cikin hijab d'inta tana k'ok'arin goya Falaq d'in.... Bata kuma bin takan Nafisa ba ta nufi ward d'in
Salma dai bata san yaya akayi ta tako gaban Sister Nafisa ba sai ganinta tayi tsaye gabanta.... Ji tayi fatun bakinta sun mata nauyi ta kasa rabasu balle tayi tunanin bud'esu ballanta har kalamai su iya fitowa daga bakin nata....
Kuka Nafisa take babu ko k'akk'autawa.... Dai-dai nan Naseer ya k'araso yanda suke shima tashin hankali ne sosai ya nuna a fuskar sa.. Ilham kuwa sai lalume take tana k'ok'arin k'arasowa yanda suke...
Nafisa tana hango Naseer ta wuce cikin sauri sabon kuka na taso mata...
Cikin sauri Salma ta k'arasa ta kamo hannun 'yar uwarta Ilham suka nufi ward d'in ko kula Naseer bata sami zsrafin yi ba..
Kasa taresu yayi balle yayi yank'urin hanasu shiga ward d'in, toma ta yaya zai soma hanasu shiga bayan mai auka ya riga da ya auku....
Shar-shar Alh Kabeer ke kuka yana fad'in "Kitty why did you choose to leave me.. Meyasa kika tafi kika barni, kin manta na ce maki dake zan rayu A DUNIYAR MU... Kitty I loved you.... Soyyayar da ban tab'a yiwa wata d'iya mace ba... Meyasa kika barni.... I was only lying da nace maki na saka maki cutar k'anjamau, I had no option dole na maki k'aryar don ki yarda ki bini..... I just can't believe you're gone..... Kitty I'm sorry..... I truly I'm.... Please forgive me for all the pains I caused you... Ki yafe ni Kitty...."
Fawaz da kansa ke kife ji yayi kukan nasa gaba d'aya ma ya tsaya, mamakin mahaifinsa ya cika zuciyarsa... Da k'yar ya d'ago yana watsa wa Alh Kabeer mugun kallo kafin yace "You really have no shame Dad... How dare you say those things.... Wllhi kaji kunya, you're the worst thing that ever happened in my life.... Kayi yunk'urin matsowa kusan gawan Jamila wllhi zaka bak'unci lahira kaima... Jamila a tsarkake ta tafi, ya rage naka idan kanada ranar shiriya a gidan yari...."
Dai-dai nan su Salma da Ilham suka k'araso cikin d'akin.... Salma idanunta kan Addar su Jamila wacce tuni an rufe fuskarta da farin mayafi.... A hankali take janyo hannun Ilham har suka k'arasa jikin gadon.... Hannun Salma na rawa take k'ok'arin yaye mayafin daga fuskar Jamila.... Lokaci guda wani irin kuka ya kufce mata sanda taga 'yar uwar tasu kwance tamkar mai bacci...
"Hey wake up.... Wake up.... Kin manta kince wa Innoh zaki kula damu A DUNIYAR MU, then why did you leave us...Addah don Allah ki tashi.... Kar ki tafi please....." Kuka ya hanata ci gaba da magana...
Ilham dake tsaye gefe hawaye sai zubowa daga idanunta suke, shikenan kowa tafiya yake ya barsu a wannan duniyar, shikenan haka tasu k'addaran take... Hannu tasa tana shafa gawan Jamila lokaci guda take fad'in "We loved you amma Allah yafimu sonki, Allah ya sadaki da Innoh da Baffah, watarana duk babu mu A DUNIYAR MU, zamu tafi yanda kuka tafi, ina rok'on Allah ya sadaki da rahamar sa Addah Jamila ya kuma yafe maki kurakurenki,..." Ta k'arashe tana mai kwantar da kai saman gawar Jamilar...
Jikin Salma sai yayi sanyi gaba d'aya, sai take ji tamkar Ilham ta koma itace babba da ita, lokaci guda ta soma jero innalillahi wa Inna'ilaihirraji'un, don abinda ta mance bata fad'i ba kenan.... Shi wannan kalma yana sanya dangana a cikin zuciya.... Gaba d'aya kwanciya sukayi saman gawan Jamila suna kuka maras sauti wanda duk wani mahaluk'i dake a cikin d'akin saida suka basa tausayi... Harta Fawaz sai yaji ya koma tamkar shine macen sabida Salma da Ilham har sun fisa dauriya.... Naseer kansa ya sha manikin yanda sukayi tawakkali dukda yasan can cikin zuciyarsu akwai tashin hankali sosai, amma kam sunyi dangana kuma sunyi namijin k'ok'arin a matsayin su na d'iyoyi mata masu kuma k'aranci shekaru wanda zakayi tunanin jarabawa da suke fuskanta yafi k'arfin su iya d'auka a 'yan shekarun su... Saidai fah fad'in Allah ne... _Laa yukallifullahu nafsan illa wus'aha_ Allah baya d'aura ma rai face abinda zata iya... Allah ka bamu ikon cin jarabawar da zaka jarabce mu dashi A DUNIYAR MU.. Ameen.
Gaba d'aya gidan Daddy Ali Safwan suka nufa aka mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya, Allahu Akbar, rayuwa kenan A DUNIYAR MU dole a barki watarana duk son da ake maki _Kullu man alaiha faan_
Lubna daga makaranta ta wuco gidan rasuwan gaba d'aya itama jikinta ya kuma yin sanyi, mutuwar Jamila ya girgiza zukatan mutane, Nafisa da mahaifiyarta da k'annenta 'yan mata guda uku kullum a gidan rasuwar suma suke yini har akayi kwana uku...
Gaba d'aya idan kaga Fawaz bazaka shaida shi ba, yayi bak'i ya rame kaman ba d'an matashin balaraben nan ba.... Duk ya canza ya sauya ya koma wani abu daban, bai tab'a tsammanin zai had'u da iftila'i irin wanda ya had'u dasu ba A DUNIYAR SA lallai Allah buwayi ne gagara misali, zai jarabceka ta yanda bakayi tsammani ba...
Bayan kwana bakwai Daddy ya umarci Salma da ta koma d'akinta, su Mamy ma sun goyi bayan hakan, Salma kam sam yanzu bataso tayi nesa da Ilham da kuma Falaq, amma bazata iya sab'a umarnin su Daddy ba don basu da iyayen da suka fisu.... Saida Ilham d'in tayita kwantar wa Salma da hankali tana nuna mata she'll be fine kafin Salma ta d'anji relief amma kam tasan zatayi kewar 'yar uwar tata...
Haka rayuwa taci gaba da tafiya masu Falaq na wajen Mamy itace mai kula da ita da shike Ilham ma gidan Mamyn take... Abbu da Mama Kaltum sun cika alk'awari sun dawo Nigeria wanda hakan ba k'aramin faranta ran su Aunty Saudat harma dasu Lubna yayi ba.... An shiga kotu gameda case d'in su Alh Kabeer da Maina da kuma jagoran tafiyar nasu wato Innah, tuni Alk'ali ya Jefa Maina gidan Yari sabida kamasa dumu-dumu da laifin kisan Malam Ladan mahaifin Deeni da yayi, Alh Kabeer kuwa yana nan a tsare Alk'ali bai ida Shari'ar su ba shida Innah a cewar sa har sai ranar da aka capko Innah amma za'a ci gaba da tsare Alh Kabeer hannun jami'an tsaro....
Yau ta kama wata d'aya cif da rasuwar Jamila, Affan da Ilham ne zaune ta gefen dining area yana janta da fira kaman yanda ya sabar wa kansa a 'yan kwanakin, nan ya sako mata zancen asibitin ta..
Ilham d'an murmusawa tayi kana tace "Ya Affan kenan.... Na gode da k'ok'arinka amma nikam idan don ta nice idanuwa a rufe sun faye min.....mai zan gani A DUNIYAR MU... Duniyar da babu komai cikinta sai tashin hankali, Duniyar da babu komai cikinta sai sab'on mahalicci, Duniyar da babu komai cikinta sai yaudara k'arya, cin amana, ha'inci da kuma zalunci..... Ya Affan rungumar k'addarata A DUNIYAR MU ya faye min komai... Kayi hak'uri bawai na k'i aminta da gudumawarka ma rayuwata bane, a'a ko d'aya, zamana a haka ya faye min don bansan meyasa Allah ya barni haka babu idanu A DUNIYAR MU ba...."
Jikin Affan ya kuma yin sanyi sosai... Kafeta da idanu yayi yanajin hawaye suna k'ok'arin ciko idanunsa, gaba d'aya zuciyarsa ta karaya da hidimar Duniya.... A hankali ya soma fad'in "Ilham idan har A DUNIYAR MU kika sami cuta ta makanta ki sani ba haka Allah ya halittoki ba, ciwo ne wanda idan har akwai possibility na warkewar ki neman magani shi yafi alkhairi, don Allah shi ya halicci cuta ya kuma halitta magani don mu kasance masu godiya a gareshi.... " D'an fasali ya d'anja yayinda jikin Ilham yayi sanyi da jin kalaman Affan wanda suke masu tsananin taushi da ratsa zuciya...
Affan yaci gaba da fad'in "Amma ki sani Ilham, koda zaki tabbata babu idanu wllhi tallhi Affan bazai daina sonki ba... Ina sonki Ilham ina sonki a duk yanayin da zaki tsinci kanki ciki, zan aureki a haka kuma na sadaukar da rayuwata wajen kula dake da abinda zaki haifa mana in future... I love you Ilham with all my heart..." Yana gama fad'in haka hawayen dake mak'ale idanunta suka zubo...
Mamy da Shareefah dake tsaye gefe suna dubansu suma hawaye ne sukaji na zubo masu.... A hankali Mamy ta k'araso kafin ta dafi kafad'un Affan da Ilham tace "You two deserve each other... You both match each another.... I'm proud of you, ina alfahari daku , ina sonku 'ya'ya na ina son ku kasance tare...."
Murmushi Affan yake yana dubanta kafin ya mik'e ya rungumeta yana fad'in "I love you Mamy.... I love you so much.... Na yarda you're a changed person now..... I hope Azeema will soon come back to us, dawowar Azeema garemu shine cikoton farincikin mu A DUNIYAR MU....."
Mamy ta murmusa tana mai shafan kansa hawaye na k'ok'arin ciko idanunta take fad'in "Azeema zata dawo da yardar Allah Affan.... Allah ya maku albarka gaba d'aya...."
Shareefah dake tsaye gefe cikin sauri ta k'araso ta rungume Mamy da Affan, soyayyan juna na ratsa zukatansu...
***
Saida Salma dasu Mamy suka sa baki kafin Ilham ta yarda taga likitan idanu a Asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa University.... Likita ya dubata yanda ya gano cewa tun tana yarinya 'yar shekara uku cutan k'yanda wanda a turance ake kira measles shine ya tab'a idanun nata.... Magunguna ya d'aurata akai na tsawon watanni uku kafin a yi aikin....
Affan baya sama baya k'asa duk wani d'awainiyar maganin Ilham shike kula da ita, saiko idan ya tafi can base d'insu ya bar wa Mamy amanarta, gaba d'aya he's dying for Ilham, gani yake idan bai mallaketa ba za'a sami error...
A 'yan kwanakin maganan aure ya kankama tsaknin Momy da Abbu wanda harta su Naseer abin ya shammace su, Mama Kaltum ita ta tsara kayanta ko sani su Mamy basuyi ba da wannan shiri da take sai k'ok'on barar ta data kai masu.... Shikam Abbu dama ya kyasa hakan cikin zuciyarsa saidai ma yace matar tasa ta kai mak'ura wajen iya karantar zuciyarsa don tamkar ta karanci zuciyar tasa ne...
Abu kaman wasa batun aure ya kankama, abinka da manya ba wani d'aukan lokaci akayi ba, cikin 'yan satuttuka aka d'aura auren Momy da kuma angonta Abbu, zaman gidan sai ya kuma masu dad'i, babu kaman Lubna da Aunty Saudat,...
A b'angaren Fawaz kuwa shirye-shiryen tafiya k'arin karatu k'asar England yake, nisantar wannan waje shi yafiye masa alkhairi....
Yana zaune d'akinsa yana tattara wasu 'yan stuffs d'insa cikin jaka yaji wayarsa na ruri.... Sunan Dr Fago ne ya bayyana masa b'aro-b'aro... Saida yaji k'irjinsa ya d'an buga kafin ya d'aga wayar.... Bayan sun gaisa ne Dr Fago ya sanar dashi gashi a k'ofar gidansu....
Gaban Fawaz ya kuma fad'i don bai tsammaci zuwan Dr Fagon ba... Saida ya shafi naman goshinsa kafin yace gashi nan fitowa...
Yana tafe yana mamakin mai ya kawo Dr Fago don dai shikam basuyi magana da kowa cikin colleagues d'insa dangane da tafiyar sa ba, hasalima shi yaso sai ya tafi kafin su sani...
Dr Fago yana hangosa ya bud'e motar sa ya fito, Fawaz dake k'ok'arin k'ak'aro murmushin k'arfin hali yace "A'a Doc pls ka shigo da motarka ciki..."
Girgiza kai Dr Fago yayi yana mai mik'a masa hannu sukayi masabaha kana yace "Kar ka damu Dr nan ma yayi.... "
Fawaz ya d'an jinjina kai kana yace "Mu k'arasa ciki...."
Kallo Dr Fago yabisa dashi yanda duk ya rame ya d'aid'aice kafin ya gyad'a kai yayima motarsa lock kana yabi bayan Fawaz d'in....
***
Shazali ya toshe hanci yana watsa wa Innah mugun kallo wacce gaba d'aya bata a hayyacin ta sabida tsananin jinya da take ciki a 'yan kwanakin, tab'e baki ya kuma yi yana yamutsa fuska kana ya shiga tafe hannaye yana k'ok'arin shure Innah da k'afafu yake fad'in "Gaskiya Uwar daba da sakel, nifa na gaji na gaji ehe... Bautar karuwa bautar da babu lada sai zunubi.... Wllhi Uwar daba kizo asan yanda za'ayi da wannan matar don ta k'ara kwanaki a gidan nan, tofah gidanga bazai shigu ba yasin muma kore mana samari zatayi ehe...." Ya k'arashe yana mai tafe hannaye yana taunar cingam...
Innah dake numfashi da k'yar yunk'urin mik'ewa tayi tana son janyo kofin kokon da tun safe yake wajen k'udaje sun gama had'ansu akai tana k'ok'arin kaiwa bakinta Shazali ya hankad'e kofin ta fad'i k'asa... Allah sarki d'an sauran kokon da Innah tasa rai shima ya kware a k'asa...
Wasu irin hawaye masu zafi suka ciko idanun Innah.. Wai yau itace Duniya ta maidata haka, babu kalan mulki da batyi ba gidan Sa'oud Santana, babu kalan arzikin da bata gani ba amma wai yau itace sutura tafi k'arfinta balle abinda zatakai bakin salati..... Tana cikin zuban hawaye don batama da k'arfin yin kuka taji muryar Uwar daba wato magajiya akanta tana fad'in "Chuss a gaskiya ni na gaji da zamanki a nan wllhi nima na gaji don Shazali tayi gaskiya kinga yoyon gudawan nan da kike ba k'aramin illa yayiwa gidan nan ba, don yanzu na lura ba zallan abincin gidan nan ake k'yama ba harta 'yan mata na, na gidan nan k'yamarsu ake... Gaskiya na maki iya taimako bazan bari garin taimakon ki na jefa kaina a tara ba.... Yanzu ki soma tunanin yanda za'a watsar dake kafin na umarci su Shazali su aiwatar da hakan..." Ta k'arashe tana mai toshe hanci....
Innah ta d'ago hannu da k'yar tana share hawaye kana ta dubi Magajiya tace "Uwar Daba wllhi banida makoma banida wajen zuwa...."
Kafin takai aya uwar daba ta tsareta da fad'in "Toh ni uwar mai kikayi A DUNIYAR MU har kika d'aid'aice haka. Duk tsofin karuwan da suke zuwa su zauna damu a nan har suyi jinya tasu ta d'aukesu ban tab'a cin karo da mai case irin naki ba,.... Anya da mutane 'yan Adam kikayi naki barikin a lokacin ki kuwa, gashi ke da gani zaiyi wuya a samu iyayenki raye balle nace aje a samesu a rok'esu gafara ko kya samu sassauci....."
Innah tayi murmushin k'arfin hali kana tace "Uwar Daba kenan.... Ni da kika ganni nadama bata tab'a shigata ba kuma bazata tab'a shigata ba... Idan kuka watsar dani a bola na gwammaci na k'are rayuwata a bola akan na koma wajen wad'anda na masu laifi na rok'esu gafara... Kuma ko yau na samu hali zan fice na je na cika burina A DUNIYAR MU....."
Daga Shazali har uwar daba baki hangame suke kallon Innah da k'arfin hali irin nata...
Kad'e buje Uwar daba tayi had'i da zama gefen Innah tana fad'in "Toh fah ga wata karatu A DUNIYAR MU barin zauna na saurara, gaya min, ki sanar dani labarinki koda warin tsutsar dake fita jikin ki zaiyi ajalina....."
Murmusawa Innah tayi had'i da muskutawa sabon d'oyi ya kuma tashi kafin ta soma baiwa Uwar daba labarin ko ita wacece...
Shazali kuwa tab'e baki yayi ya fice yana yauk'i yana fad'in ba dashiba ashwaki da tutuwar masara.....
****
Girgiza kai Fawaz yayi a karo na biyu kafin yace "Dr bazan iya ba, wllhi bazan iya ba, bazan iya auren ko wacce mace ba, Jamila was the love of my life, alk'awari nayi ma kaina zan tafi zanyi nesa da wannan duniyar kuma bazan tab'a aure ba... In fact bana ma son zancen wani aure Dr, pls understand me...."
Girgiza kai Dr Fago yayi kana yace "Fawaz idan baka auri Nafisa don kowa ba zaka aureta don Jamila, Fawaz don Allah kayi hak'uri ka karb'i k'addarar ka, kada kayi fushi da lamarin ubangiji, don Allah ka auri Nafisa...."
Shiru Fawaz yayi yana duban Dr Fago yana tuna kalaman Jamila na k'arshe kafin ta bar duniya, zuciyarsa ta kuma masa nauyi, wanne zaiyi wanne zai bari.... Baya jin zai iya zaman aure da wata mace har ya bata hakkokin ta koda yayi auren... Shin wai ya zaiyi ne......
Ganin yayi shiru yasa Dr Fago kuma gyara zamansa kana yaci gaba da fad'in "Fawaz kar ka damu dani don tuni na rabu da Nafisa wllhi. Kai ka fi cancanta ka mallaki Nafisa kaman yanda Jamila ta bar maku wasilci...."
Fawaz zaiyi magana Dr Fago yayi saurin katse sa kafin ya isa closet d'insa ya shiga zab'o masa kayan sakawa...
Kallon mamaki kurum Fawaz ke binsa dashi yanda ya d'auko wata shadda ruwan toka tasha aiki mai kyaun gaske...
"Oya karb'i ka saka....." Dr Fago ya fad'i sanda ya mik'awa Fawaz d'in kayan wanda yayi sororo yana duban Dr Fagon...
"Dr why do I have to wear this.....?" Ya tambaya yana mai girgiza kai..
"Fita zamuyi, no more questions... Karb'a ka saka...."
"But....."
"Shiiii" Dr Fago ya katse sa kafin ya d'auki wayarsa saman Sofa yana mai fad'in "Ka shirya ka sameni a parlor... Bai jira cewar Fawaz d'in ba yayi ficewarsa parlor....
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU*🌖🌖
*67*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
D'an shafa kansa yayi a karo na biyu yana mai jin nauyin kalaman dake fitowa daga bakinsa....
"Azeema nasan kina sona kina k'aunata tuntuni.... Nima ina sonki ina k'aunarki saidai bana tunanin irin k'aunar da kike min nake maki... Azeema to be honest with you tamkar Shareefah na d'auke ki... Ji nake muddin na aureki toh zan iya auren Shareefah... I'm sorry.. Dan Allah kiyi hak'uri kada ki dubi maganganu na da wata fuska.... Har kullum zanci gaba da baki matsayi irin wanda nake bawa Shateefah.... Kiyi hak'uri nasan kalamaina dole su kasance masu zafi a gareki... But Azeema bazan iya had'a soyayyan Ilham da wata mace ba... I'm not that strong, na tabbata I might end up hurting you koda na maki alk'awarin zan aureki.... Ina son matata Ilham, ina sonta da duka zuciyata soyayyan da na tabbata na had'ata da wata mace zan iya kai kaina ga halak'a ne... I'm sorry please Azeema... Ina fatan kema zaki sami farin cikin ki A DUNIYAR MU kaman yanda na sami Ilham...."
Bata bari ya ida maganan ba ta shiga murmusawa mai d'an sauti kana tace "Com'on Baby bro... Relax, duk a cikin soyayyar Ilham ce ka daburce haka? Haba Soja mazan fama ashe mace babu wanda ta bari har soji.... Kai gaskiya nifah ban yarda da Ilham d'in nan ba mai tabawa k'anin mu ya sususce haka akanta...."
D'an gimtsewa yayi kana yace "Waye baby bro, waye k'anin naku....? Kindai san Soja baison raini koh....?"
D'an murmusawa Azeema take kana tace "Affan wllhi kaida Ilham kun dace sosai da juna, kuma ina tayaku murna, ina rok'on Allah ya baku zaman lafiya mai d'orewa da kuma zuri'a d'ayyiba ciki har a samo min takwara.... Kar ka damu da Azeema, wllhi tunda muka zauna tareda Mamy gidan Arniya Laure nake jin Mamy tamkar wacce ta tsuguna ta haife ni, Affan a halin yanzu ji nake tamkar nono guda muka sha nida kai da kuma Shareefah, ina jinku tamkar wanda muka fito ciki guda, bana fata batun aure ya kuma shiga tsakani na da kai... I'm your sister, big sis ma ya kamata ka soma kirana...."
Harara ya galla mata lokaci guda kuma sukayi dariya su duka biyu.... Dai-dai nan Dr Fago da wani likita suka shigo su Daddy na biye bayan su...
Dr Fago sai tsokanarta yake yanda tayita sunbatun zata mutu... Gaba d'aya sai murmusawa suke..
Mamy ta bud'e murya tace "Yaushene za'a sallamo min d'iyata ta dawo gida don na k'agu naga 'ya'yana duka a gabana.... "
Sharrefah tayi karaf tace "Nidai Affan ya kamata ka had'a mana dinner d'in bikin ka da kuma Sword Crossing tunda hankali ya kuma kwanciya dama sabida b'atan Zeema Mamy da Daddy suka ce babu wani activities...."
Azeema ta d'an mik'a hannu tana mintsilin Shareefah take fad'in "Wato da a naki tunanin ina can mayanka kike so ayita hidiman biki ko ajikin ki koh..."
"A'a ni dama jikina ya bani zaki dawo baza'a yanka ki ba.... Kai amma zanso ganin idanun Lauren nan sanda ta maku aski...." Ta k'arashe tana dariya...
Mamy ta kai mata duka tana fad'in "Ja'ira ai da kece Laure ta kame ki da bansan kalan gudawan da zakita sakewa ba don tsoro... Zeema ta jaruma ce....."
Gaba d'aya suka murmusa sanda d'aya Likitan ya gama d'aura mata wani drip d'in... A tare suka fice harda Dr Fago da Daddy suna tattauna case d'in Azeemar..
Affan ya d'an dubesu yana kuma duba agogon hannunsa kana yace "Nifa zan tafi... Kunsan an bar amarya ita kad'ai...." Bai kai aya ba Shareefah dake faman dariya take fad'in "Ohni Affan wai ko d'an kunyar nan babu.... Toh idan bakaji kunyar mu ba kaji kunyar Mamy tunda ita ma Mamyn Ilham ce kaga ta zama in-law d'inka..."
Mamy tayi k'wafa kafin tace "K'yaleni da ja'iri... Kuma Ilham ba yanzu zata tare ba kaji da kyau sai an mata aiki ta warke ras.. Kai saima kun zauna a gida naga kamun ludayinka don bazan baka d'iyata ka tafi da ita bariki ba ehe..."
Affan ya marairaice fuska had'i da zaro idanu waje kana yace "Ai Mamy na wasa kike koh, ko su Sharee Addar kwabo su mana dariya...."
Daga Shareefah har Azeema dariyar draman Mamy da Affan suke, dai-dai lokacin Santana's suka yi sallama suka shigo gaida Azeema..
Abbu, Mama Kay Momy Lami, Aunty Saudat, Salma da kuma Lubna, Fawaz kam ya tsaya daga waje yanda suka had'u dasu Dr Fago..
Gaisawa aka dinga yi ana barka wa juna, nan Abbu yake fad'in ai Fawaz ne ya sanar dasu dashike Dr Fago mutumin da ya kad'e Azeemar abokin Fawaz d'in ne... Gaba d'aya akata barka da murna ma juna.. Azeema ta rok'i Salma gafarar abubuwan da suka masu a baya...
Girgiza kai Salma take kana tace "Haba Azeema ki daina tuna baya, komai ya wuce ya zama tarihi.. Allah shine abin godiya..." Azeema ta jijjina kai tana mai fad'in "Wannan haka yake... Allah yafe mu gaba d'aya don nima ban mance sanda kika saka mana barkwano cikin pants d'inmu ba...." Gaba d'aya akayi dariya .... Wato dai Azeema bata bar halinta na barkwanci ba... Daga nan ta'aziyar Jamila tayiwa kowa kafin daga bisani Abbu yayi addu'o'i sanda su Daddy da Fawaz suka sami shigowa...
Affan ne ya tsare su Aunty Saudat su Momy da tambayar yaya aka bar masa amaryar sa ita kad'ai, gaskiya dole ya tafi ya kula da kayansa yanzu....
Su Momy kam dariyar Affan suka dinga yi yayinda Mamy ta d'an dungure sa tana fad'in "Toh rasas kunya... Kaidai baka surkunta da kowa...."
Affan ya d'an shafi kansa yana murmusawa yake fad'in "Mamy dan Allah ki barni na tafi... Baby fah ita kad'ai suka bari..."
"Ka min shiru.... Tam! " Mamy ta fad'i tana galla masa harara
Saurin kame bakinsa yayi yana fad'in "Namayi shirun, ba dolena ba kar a hanani d'aukar matata..."
Fawaz dai kallon yanda Affan keta rawan k'afa yake yana murmushi, ganin shi a nasa b'angaren sam baya d'aukin auren...
Fitowarsu daga haraban asibitin suka hangi wata mata ana turota cikin akori kura wata mata na turota sai rawa jikinta yake.... Ta kasa takawa sabida wani irin ruwa dake bin k'afafunta, babu motan da ya iya kwasanta sabida d'oyi da takeyi...
Yanda suka fito gaba d'ayansu cak suka tsaya suna duban wad'annan bayin Allah cikeda mamaki had'i da tausayi...
Gaba d'ayansu babu wanda ya d'ago fuskar matar balle ya shaida kamannin ta.....
Sanda sukayi dab da yanda suke tsaitsaye cirko-cirko ne suka hangi fuskar matar tamkar sun waye ta....
Lubna dake gefe tafiya ta soma yi ta nufi a kori kuran hawaye na gangaro mata, tabbas idan kamannin kowa zai b'ace mata duk tsanani kamannin Innar ta bazai b'ace mata ba...
Gaba d'aya kallo suka bi Lubna dashi cikeda mamaki.....
Aiko Lubna tana k'arasawa gaban akorikuran ta fashe da wani irin kuka had'i da durk'ushewa a wajen....
Innah ta shiga bin Lubna da idanu yanda take kwance cikin akorikuran cikeda tsananin jinya.....
Uwar daba baki sake take kallon ikon Allah....
Muryar Lubna na rawa take fad'in "Innah... Innah kece haka, kece kika koma haka..... Innah don Allah kece wannan.....?" Kuka yaci k'arfin Lubna dake durk'ushe a wajen...
Cikin sauri Naseer ya k'araso ya d'aga k'anwarsa yana mai duban yanda Innah ta koma cikeda Al'ajabi.... Fawaz dake gefe hawaye ne yaji sun ciko idanunsa.... Innah itace mutun ta biyu wacce ta zamto silan k'uncin sa A DUNIYAR SA bayan Mahaifinsa.... A hankali yake takawa har ya iso yanda Naseer da Lubna ke tsaye... Kukan da yaketa mak'ewa yaji yazo masa sosai... Jinginuwa shima yayi jikin Naseer d'in yana kuka sosai...
Naseer kam gaba d'aya sai jikinsa ya kuma masa wani irin mugun sanyi... Musamman da Lubna da Fawaz suka kwanta jikinsa suna kuka ga kuma Innah gabansa ta koma wata halitta daban....
#SameenaAleeyou
#ADM
#1love
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*68*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Lokaci guda idanun Naseer sukayi jazir haka ma fatan jikinsa, jijiyoyin goshinsa sunyi rud'u-rud'u lokaci guda kamanninsa ya sauya.... Ganin Innah da yayi sai ya tuno masa da iyayen sa... Innah tayi zalunci mafi muni A DUNIYAR SU, ta kashe masa iyayen sa sannan bata bashi daman sanin ko shid'in wanene ba duk tsawon rayuwarsa.... Ji yake bazai tab'a yafe mata abinda ta masa ba.... A hankali yake takawa har ya isa gaban akorikuran da Innah ke zube ciki....
Cikin wani irin murya mai tsananin rawa ya soma fad'in "Why...? Meyasa kika kashe su.... Meyasa kika azabtar da Aunty Saudat.... Meyasa baki d'auki fansarki akaina ni d'aya ba.... Innah why.....?"
Innah da gaba d'aya idanunta sun k'ek'ashe duban Naseer take dukda jin jiki da takeyi bai hanata fad'in "Sabida na tsani duk wani jinin Hidaya.... Naseer nasan izuwa wannan lokaci kasan me uwarka ta min..." Tayi saurin yank'urawa had'i da d'aga rigarta tana mai nuna masa tabon da mahaifiyarsa ta mata da iron.....
Girgiza kai yake yana duban Innah cikeda mamaki kana yace "Shin wannan har ya kai ki aikata muggan laifukan da kika aikata A DUNIYAR MU.... Shin burin d'aukan fansarki har ya kai ki hallak'a rayuwka.... Innah wacce irin 'yar Adam ce ke.... Wani irin zuciya ne dashe cikin k'irjinki..."
Bai kai aya ba Innah ta katse sa da fad'in "Tabbas zuciyata ba irin ta kowa bace.... Da ace mahaifiyarka Hidaya bata kaucewa mahaifiyata ta fad'i k'asan bene ba da mahaifiyata bata mutu ba..... Dole ce ta sakani yin duk wasu abubuwan da na yisu A DUNIYAR MU.... Na tsani jan fata ko wani iri ne.... Auren Sa'oud da nayi ba don komai bane sai don na cika burina na d'auki fansata akan duk wani jinin Hidaya da zan sami dama.... Kuma ko yau ba bar duniyar mu nasan na k'untatawa zuri'ar Hidaya, koda duka burina bai cika ba na tabbata kashi sittin cikin d'ari ya cika wanda shine mai rinjaye....."
Ba Naseer kawai ba, basu Lubna da Fawaz kawai ba.... Duk wani mahaluk'i dake wannan wajen saida mamakin Innah da tsoron Duniya ya kuma shigarsu..... Atika Uwar daba kame hab'a tayi tana kallon ikon Allah... Bud'e murya tayi kana tace "Lallai na yarda zuciyarki ba irinta kowa bane... Nima a nan zan barki na nisanta kaina dake kafin bala'inki ya auka min... Allah ya gani tsarkakken tuba nayi...."
Ta maido da dubanta gasu Naseer kana tace "Toh bayin Allah nayi nawa... Kunsan ance naka naka ne hannunka bai rub'ewa ka yanke ka yar.... Ga 'yar uwarku ku d'ora da jinyarta daga yanda na tsaya.. Nikam nayi gaba kuma...." Ko jiran cewarsu batayi ba ta soma tafiya baka jiyo sautin komai sai k'aran slippers d'in Atika Uwar daba har ta bar wajen....
Suna nan tsaye cirko-cirko mamaki da Al'ajabi bai bar jikkunansu ba saiko ga 'yansanda sunzo tattaran Innah don dama wanted ake nemanta....
Innah ihu take tana kururuwa tana fad'in bazata tafi gidan yari ba.. Inaaa ko kulata basuyi ba suka tattara ta... Lubna kuwa kuka take kaman ranta zai fita... Haka Naseer ya dinga lallashin Lubnar abin tausayi....
Washe gari aka shiga Kotun su Innah yanda Alk'ali ya yanke masu life Imprisonment daga ita har Alh Kabeer.... Innah sai kururwa take tana ihun bazata gidan yari ba, ga jinya dake cinta abin tausayi...
Ga mamakin d'inbin jama'an dake wajen Naseer rok'on Alk'ali yayi kan ayi sassauci wa Innah sabida hali na jinya da take ciki...
Alk'ali fir yak'i aminta a cewarsa Innah babbar criminal ce wacce barin irinsu cikin Al'umma ba k'aramin had'ari bane saidai za'a kula da lafiyarta a asibitin su na gidan kurkuku....
Allahu Akbar wannan kenan.... Duniya tafi gabaruwa iya jima.... Ka gama shuka duk tsiyanka ranar girbewa na nan tafe.... Allah ka bamu ikon shuka khairan... Ameen....
Abin sosai yayi affecting Lubna sabida duk yanda taje tazo Innah mahaifiyarta ce... Allah sarki idan kaga Lubna dole ta baka tausayi....
Aunty Saudat ce a gefenta tana ci gaba da lallashinta had'i da bata baki... Gaba d'aya ta tak'ure waje guda abin tausayi.... Naseer ne yayi sallama ya shigo....
Aunty Saudat ce kawai ta iya amsa masa sallaman nasa kafin ta mik'e ta nufo k'ofa...
Kan Lubnar na kife ba tareda ta d'ago ba.... Kallon juna Aunty Saudat da Naseer sukayi.... Kafin ta d'an girgiza masa kai alamun har yanzu Lubna bata dawo dai-dai ba....
Daga d'an gefenta kad'an ya zauna had'i da kamo yatsun hannayen ta.... Saidai kafin ya sami zarafin magana Lubna ta kuma bursting cikin tsananin kuka....
Naseer ya kwanto da kanta jikinsa yana mai lallashin ta cikin murya mai taushi da kwantar da hankali...
"Ya Naseer shin ni Allah baya sona ne ya fito dani cikin mutanen banza mugaye irinsu Innah da Yaya..... Ya Naseer wllhi ji nake dama banzo duniyar nan ba da babu komai cikinta sai tarin k'unci....." Hannu Naseer yasa ya d'an toshe bakin Lubna... Cikin muryar da tafi kama da d'an fad'a yake fad'in
"Kar na kuma jin irin wad'annan kalaman daga bakin ki Lubna.... Wannan shine k'addarar mu A DUNIYAR MU.... Allah baya hukunta ka da laifin wani..... Lubna kina kewaye da mutanen da suke k'aunarki... Abbu Mama Kay Momy Aunty Saudat ga kuma Fawaz.... And above you've your Ya Naseer.... Gaba d'ayanmu muna k'aunarki ki kwantar da hankalin ki kinji....."
Kallon Naseer take tana jin k'aunar d'an uwan nata har cikin ranta.... Lokaci guda tausayin sa tausayin su gaba d'aya ya cika zuciyarta... Saurin rungumarsa tayi wasu hawayen na zubo mata.... Cikin muryar kuka take fad'in "Ina sonka Ya Naseer....."
D'an shafa kanta shima yayi kana yace "Nima ina sonki k'anwata... So much...." Salma dake d'an tsaye jikin k'ofa tausayin su ya cika zuciyarta a hankali tasa bayan hannu tana d'an share hawayen da suka zubo mata....
***
*A gidan Daddy*
Yasu-yasu suka d'an had'a 'yar Dinner a harabar gidan, daga mutanen Mamy saiko mutanen Shareefah sai abokan Affan..... Yanda akayi decorating gidan sosai yayi kyau ba wani kashe kudi akayi ba amma yayi kyau don dama ba wani gayyatan mutane akayi sosai ba, don lokaci guda Shareefah tazo da idea d'in...
Ango ya cake cikin occasional uniform d'insa ba k'aramin kyau yayi ba abin sai wanda ya gani.....
Shareefah bata sama bata k'asa har saida taga rigar da Ilham zata saka ta zama ready, doguwar riga ce kalan uniform d'in Affan wato navy blue.... Sake baki Shareefah tayi tana kallon Ilham sanda makeup artist d'in ta ida fesa wa amaryar kwalliya mai d'aukan hankali, ga rigar nata ya zauna sosai a jikinta, Masha Allah... Abinda Shareefah ta iya fad'i kenan kafin ta soma sakawa Ilham jewelries..... Ilham dai don babu yanda ta iya da Aunty Shareefah ne amma itakam sam ba son dinner d'in take ba...
Daddy na zaune a parlorn sa Mamy ta k'araso cikin nata shirin tasha gayu da kyau itama... Sihirtaccen kyaunta na asalin Katsinawa ya fito sosai....
Tuni Daddy ya janye idanuwansa daga TV ya maido da dubansa ga Mamy....
Murmushi suka sakar ma juna kafin Daddy yace "Masha Allah uwar amarya uwar ango karfa kifi amarya yin kyau....."
Mamy ta wani murmusa had'i da fari da idanu wanda tuntuni d'abi'arta ce kafin tace "Kai Daddy wato dai bazaka girma ma zolaya ba....."
Daddy ya kuma murmusawa kafin yace "Randa na kawo maki taki k'anwar zolayar zai tashi akanki ya koma kanta....."
Ai bai kai aya ba Mamy tayi kicin-kicin da fuska... Lokaci guda kuma ta saki murmushi kana tace "Yanzu ba da bane.... Na yarda da kaina ko mata nawa mijina zai k'aro min..... Ashe dama tuncan rashin yarda da hukuncin ubangiji ne da kuma rashin yarda da kai yake janyo mana tsoron da zai jefamu ga halak'a , tsoron dai zai jefa mutum zuwaga shirka ga mahaliccin sa.... Daddy wllhi I'm ever ready ka kawo min abokiyar zama muddin bazatazo da k'ulli cikin zuciyarta ba... Niko saidai na mana fatan Allah ya bamu zama lafiya ya kuma rabamu da sharrin mugayen k'awaye irinsu Laure...."
Alh Ali Safwan bakin Mamy kawai yake gani yanda take furta kalaman cikin tsanaki.... Soyayyarta na kuma dabaibaye masa zuciya da ruhi... A hankali ya mik'e daga saman kujeran da yake ya tako har gaban kujeran da Mamy ke zaune.... Hannu Daddy yasa ya d'an kamo kafad'unta ya mik'ar da ita tsaye......
Kallon juna suke cikin idanu.... Saida suka d'an d'au lokaci a haka kafin Daddy ya d'an murmusa yace "Asma'u kenan.... Asma'un Aliyu, kina nan da kyaun ki saidai Laure ta rage da ta aske sumar nan kinsanni da son mace mai suma...." Ya k'arashe cikin sigan wasa...
Murmusawa Mamy tayi tana kuma fari da idanu kana tace "Sumar ma soon zai fito insha Allah... Barinje na fitar da d'iyata don ina tsamman Affan da abokan sa ne suka iso...."
Daddy jinjina kai yayi had'i da matso da bakinsa saitin kunnen Mamy kafin ya rad'a mata "Kema yau amaryar ce ki gama da hidiman yaranki kizo ki tarbi naki angon....."
Murmushi Mamy tayi had'i da d'an rufe fuska alamun jin kunya.... Sim-sim ta wuce Daddy still murmushi kwance saman fuskarta har ta fice daga parlorn....
***
Affan da abokan sa suna isowa suka zauna a wajen da aka tanadar domin su.... Sai rarraba idanu yake yana lek'en ta yanda Ilham zata soma fitowa.....
Aiko nan ya hangeta cikin shiga ta alfarma Mamy ta rik'ota suna takowa.... Affan gaba d'aya sai ya kasa d'aga idanu daga duban Ilham.... She's just gorgeous.... Tuni MC ya soma announcing fitowar amarya..... Nan Shareefah da friends d'inta suka mik'e suka nufesu suna taka rawa....
Daga can tsakiyar fili suka tsaya yanda MC ya buk'aci ango ya tashi ya k'araso da amaryar sa.... Aiko Affan kaman jira yake tuni ya mik'e ya nufi yanda suke tsaitsaye Su Shareefah iyayen son biki sai tik'an rawa ake.....
Babu ko kunya ya shiga rungumo matarsa yana manneta jikinsa.... Shiyayi mata d'an jagora har suka isa mazaunin su....
Salon nasu amarya makauniya sosai ya birge jama'an dake wajen.... MC sai kod'asu yake, sanda aka kirasu fili domin yin rawa Affan ne ya rik'o kayansa suka fito filin don nuna irin tasu farin cikin.... Gaba d'aya yak'i sakinta, cikin kunnenta yake rad'a mata "Baby you look spectacular.... I love you...." Sai sunbatu yake mata itako murmusawa kawai take idan taji abin nasa zai wuce gona da iri ta d'an taka masa birki....
Azeema ma dukda bata gama warwarewa ba saida ta fito filin event d'in.... Rayuwa ta daidaita saiko godiyar Allah.... Dr Siraj likitan Shareefah dashi akayi komai a wajen... Shiko Dr Fago bai sami zuwa ba don yana can ta fannin abokin sa Fawaz tinda bai sami d'aurin aure ba ya kamata ya d'an lek'sa dukda ba wani event za'ayi ba....
***
Sashen Fawaz dake a cikin gidan aka gyara aka saka amarya, dama already Fawaz d'in yace ba sai anyi wahalan kayan d'aki ba shi zaiyi komai kuma ma ba zama a k'asan zasuyi ba.....
A 'yan kwanakin tuni ya soma processing duk wani abu na tafiyar Nafeesa da za'a buk'ata.... Sosai Abbu da Naseer suka masa nasiha mai ratsa jiki musamman gameda aure, sabuwar rayuwar da ya tsinci kansa ciki....
Zaune Salma tayi a d'aki tana tunanin k'anda zasu rabu da Falaq, ta yaya Fawaz zaice zai d'auke Falaq, itakam gaskiya bata shirya rabuwa da d'iyarta ba... Tunanin kalan rayuwar da suka fuskanta ya shiga zarya a zuciyarta.... Tana nan zaune tana matsan k'walla taji ya turo k'ofa sallama bisa bakinsa....
Kasa d'agowa tayi ta kallesa sai goge hawayen data ci gaba da yi.....
Naseer ya d'an tako ya k'araso cikin d'akin fuskarsa babu walwala... Daga can gefe ya tsaya yana b'alle cufflinks d'insa..... Kota kanta baibi ba ya ida abinda yake ya nufi bathroom... Tasan za'a rina hakan tunda tasan sam baiso yake ganinta cikin tashin hankali.... Juyawa tayi had'i da gyara kwanciyarta sanda taji fitowarsa....
Saida ya ida duk wani Al'adan sa da yake kafin barci kana ya k'araso saman gadon... Tana jinsa ta runtse idanunta tamkar mai barci...
Murya ya bud'e ya kirawo sunanta wanda ya sanyata bud'e idanunta ba tareda ta dubesa ba ko ta amsa sa....
Naseer yaci gaba da fad'in "Ki tashi nace muyi magana...."
A hankali ta tashi baki a ture tana kuma goge ragowar hawayenta.....
Kafeta da idanu yayi kafin yace "Reina kuka.... Na d'auka mun wuce maganar kuka irin haka kuma a gidan nan.... Reina ko kinsan yawan shiga damuwarki could affect our baby.... Meyasa bakijin magana ta huh....?" Ya k'arashe da d'an tsattsauran murya....
Tuni ta dad'a jin kukan na zuwa mata, wato ta d'ansa dake jikinta yake ba itace damuwarsa ba... Cikin kuka take fad'in "Ni gaskiya bana so Fawaz ya d'auke Falaq ita kad'ai muke gani mu tuna Addah... Gaskiya ni bazan amince da wannan hukunci ba ya mana tsauri daga ni har Ilham...." Ta k'arashe sabon kuka na zuwa cikin muryarta....
Jikin Naseer ya d'anyi sanyi... Matsowa yayi kusanta ya janyota cikin jikinsa yana lallashi...
"Akan haka ne kike min asaran hawayen ki kike d'agawa kanki hankali... Idan dai akan wannan ne Fawaz sai ya d'auki matarsa su tafi su bar mana Falaq domin kece kikafi cancanta ki rik'eta ko a shari'ance ne.... Ki daina min asaran hawayenki kina tadawa kanki da Babyn mu hankula kinji koh...."
D'an turo baki tayi had'i da k'wace kanta daga rik'on da ya mata kana tace "Ai ba damuwa dani kayi ba.... Na lura yanzu duk abinda nayi ba damuwarka lafiyata ba damuwarka Baby ne....."
Murmushi Naseer yake yana kallon yanda uwa ke kishi da d'anta kafin ya kuma yunk'urin rik'ota.... Murya can k'asan mak'oshi yake fad'in "Wayace maki ban damu dake ba Reina, You're the first best gift I had received....." Yakai hannunsa saman d'an shafeffen cikinta yana shafawa a hankali kafin yace "And this is the second.... Kece kyauta ta farko da Allah ya albarkaceni dashi kafin abinda ke cikin ki.... So kada ma kike kawo wannan tunanin cikin zuciyarki kinji.... You're my Queen.... Abinda ke cikin ki could be my Prince or Princess... but you'll always remain _Mi Reina..._ My Queen...."
Kallonsa take yanda yake fad'in maganar direct from his heart... Ita kanta tasan she's blessed... Naseer daban ne.... He's every girl's dream.... A hankali ta rungume sa had'i da lumshe idanu kafin ta furta "I love you Roy...." Shima ido a lumshe yake furta "And I love you more Reina...." Daga nan wasan nasu ya soma sauyawa yanda suka shiga nunawa juna tsan-tsan soyayya....
***
Fawaz ya d'an girgiza kai yana duban Naseer kana yace "Uncle pls.... Kar ku min haka.... Dan Allah kada ku rabani da Falaq, pls ku barni na cikita ma Jamila wannan buri nata... Pls Uncle...." Ya k'arashe muryarsa na tsananin rawa
Kasa furta komai Naseer yayi sai kallon tausayi da yabi Fawaz d'in dashi.... Rashin sanin mai zaice wa Fawaz d'in ya sanyasa mik'ewa ya fice kana ya nufi sashen su Abbu domin maganar ta manya ce sai abinda suka yanke....
Koda aka samu Daddy da batun ma duk sun goyi bayan Fawaz d'in ya tafi da Falaq kaman yanda mahaifiyarta ta bar wasiya saidai sun yanke shawarin sai an kuma tuntub'ar Salma da kuma Ilham...
Safiyar ranar lahadi gaba d'aya suka hallara a parlorn Abbu hardasu Daddy da shike Abbu shine gaba.... Tattauna lamarin suke yanda suke son jin ta bakin kowa....
Fawaz ne ya d'anyi gyaran murya had'i da gyara zama kana ya soma fad'in "Abbu.... Daddy babu damuwa, I understand the situation, nasan d'auke Falaq lokaci guda dole ya tashi hankulan 'yan uwan mahaifiyarta... Babu damuwa zan tafi da matata a halin yanzu idan yaso daga baya ko bayan abin ya bar jikkunan su zan dawo na d'auki Falaq d'in.... Allah sa hakan yayi maku...."
Gaba d'aya murmusawa iyayen suke domin kuwa sosai shawarin Fawaz yayi masu...
Albarka iayayen suka sanyawa Fawaz yayinda Naseer ya d'aga masa babban d'an yatsa kana ya d'an dafa kafad'arsa yace "I'm proud of you Fawaz.... Duk yanda Kake kana tareda addu'o'in mu....."
Murmusawa kawai Fawaz yayi kafin suka bi bayan iyayen nasu....
Cak suka tsaya suna duban ikon Allah yanda suke hangosu daga waiting....Ilham da Salma a tare suka mik'awa Nafisa Falaq lokaci guda Salma take fad'in "Nafisa Falaq da Fawaz amana ne a hannunki... Dan Allah ki rik'e amanarsu ki kula dasu ki zamto jigo na dawowar farin cikin su A DUNIYAR MU... Munai maku fatan alkhairi. Allah ya baku nasara a duk yanda kuka nufa.... Kuna tare da addu'o'in mu....."
Nafeesa dake hawaye rungume Falaq tayi lokaci guda take hawaye tana fad'in "Insha Allah zan rik'esu amana tsawon rayuwata A DUNIYAR MU..... ALLAH Ya saka maku da mafificin alkhairi...." Tana kaiwa aya suka rungume juna gaba d'aya....
Su Momy su Mamy aka saka k'asan mayafi ana sharan k'walla....
Daddy yauma idanunsa akanta domin harta ita kanta yau kam ta lura da kallon da yake sata daga gareta... Gaba d'aya sai kunya ya lullub'eta....
Dad'i da farin ciki ya lullub'e Fawaz da illahirin jama'an dake wajen.... D'ago kai yayi yana duban Naseer hawaye da murmushi saman fuskar sa... Lokaci guda ya rungumo uncle d'in nasa Naseer...
Lumshe ido Naseer yayi yana shak'an iska na sauyin rayuwa A DUNIYAR SU had'i da godiya wa Rabbil Izza
***
Ranar Monday akayi aiki ma Ilham a idanunta yayinda Fawaz yaci gaba da shirin tattara iyalansa zuwa k'asar England birnin Liverpool....
Komai na Ilham tareda Affan akayi for second bai bar gefenta ba.... Ilham taga soyayyan dangi kama daga gidan Daddy zuwa gidan Abbu....
Alhamdulillah aikin was successful sai godiyar Allah...
A halin yanzu burinta bai wuce taga Falaq ba kafin su bar k'asan saidai bata tunanin hakan zai yuwu domin kuwa kwanaki k'alilan ya rage su Fawaz su d'aga zuwa k'asar England, ita kuwa likita yace kafin a bud'e bandage d'in da aka lullub'e mata idanunta dashi sai nan da sati guda sabida dokan aikin idon kenan...
Ana gobe zasu wuce Abuja suka zo sallama da Ilham domin jirginsu ta Abuja zai tashi...
Allah sarki daga yanda take masu sallama zaka fahimci rauni cikin muryarta, Affan na gefenta hannayensu sakale cikin na juna yana kuma k'arfafa mata gwiwa....
Tsakanin Mamy da Affan an rasa waye yafi kula da Ilham, gaba d'aya harma kaman gasa suke... Ilham ta yarda Affan masoyinta ne na asali, wanda zai k'aumaceta a duk halin data tsinci kanta ciki....
****
Ranar da za'a bud'e idanun Ilham gaba d'aya hallara sukayi a asibitin.... K'irjinta sai bugu yake sanda Dr ke tambayarta ko ta shirya a bud'e idanun.... Affan na rik'e da hannayenta duka biyu yake fad'in "Baby kar kiji tsoro I'm here kinji, I'm with you...." Bata iya ce masa komai ba sai jinjina kai da takeyi...
A hankali take fad'in "Addah Salma fah ina take....?"
Salma dake gefe hawaye na k'ok'arin cikowa idanunta k'arasowa jikin gadon tayi tana fad'in "I'm here too Ilham... Dukanmu muna nan tareda ke kinji... You'll be fine..."
Jinjina kai kurum take still hannayenta suna rik'e cikin na Affan...
A hankali Dr ya soma warware bandage d'in da basmala saman bakinsa....
Saida ya d'auki wasu mintoci yana warwarewa kafin ya umarceta da ta bud'e idanunta a hankali....
K'irjinta bai daina bugawa ba tana ganin abin kaman a mafarki wai yau itace zata kuma gani A DUNIYAR SU... A hankali ta soma yunk'urin bud'e idanun nata tana mai ambaton sunan Allah...
Duru-duru ta soma gani kaman inuwan mutane...
Hannayenta dake rik'e cikin na Affan ta soma kallo... A hankali take bin hannun nasa da kallo har ta d'ago zuwaga fuskar sa.. Lokaci guda hawaye suka cika idanun nata sanda tayi arba da kyakkyawan fuskar Affan shima hawaye da murmushin farin ciki sun wake masa fuska....
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*69*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*A duk yanda kuke kun canci yabo da jinjina...♥*
*Sholingaye (ZBI)*
*Haly mom Farhan(ZBI)*
*Mrs Alkhaleey(ZBI)*
*Cutielurv(ZBI)*
*Mom Ummqais(SAN)*
*Anmunah masoyiya(SAN)*
*Aysha Umm Khadija(Aysha Sada Machika Novels)*
Kasa furta komai sukayi su duka biyun sai kafe juna da idanu da sukayi hawaye na ci gaba da gangarowa daga idanun su.... Ilham was very shocked sanda tayi arba da kalan mijin nata, ko a mafarkinta bata tab'a kawowa zata sami kalan wannan mijin ba a yanda take makahuwa sai gashi mijin nata har ya zarce yanda take hasaso shi sa... Bashi a layin farare sannan shi ba bak'i bane, yanada kwantattun gashi irinta filanin usul, dogon hanci gareshi wanda yayi dai-dai da doguwar fuskar tasa.... A tak'aice dai yafi kama da mutanen k'asar Sudan ta arewa....
Murmushi mai bayyana hak'wara Affan yake hawaye suna masu ci gaba da gangaro masa,... Kallonsa kurum take don harga Allah bazata ce ga irin soyayyar da Affan ke mata ba... Lokaci guda ya rungumeta ganin tayi bursting cikin kuka...
Fad'i yake "Baby finally.... Allah ya bud'e maki idanunki A DUNIYAR MU... Baby kina gani na... Can you see me... Baby kina sona a haka a yanda nake... Baby talk to me mana, ki daina kuka yau ranar farin ciki ne..."
Gaba d'aya mutanen dake wajen tausayin Ilham da Affan ya cika zukatansu, lokaci guda soyayyar su yana kuma birgesu.....
Mamy ce ta k'arasa tana k'ok'arin d'ago Ilham d'in take fad'in "Ilham ki daina kukan nan haka kinji koh, Dr yace kar a dami idanun da yawan kuka..."
Jinjina mata kai kurum Ilham take ba tareda ta d'ago ba tana nan mak'ale jikin mijinta... A dai-dai lokacin kuma Salma ta k'araso hawaye sun wanke mata fuska.... Cikin wani irin rawar murya take fad'in "Ilham Sistu.... Tell me you can see me"
A hankali Ilham take d'ago idanunta wanda har yanzu tana jinsu da d'an nauyi ta shiga duban 'yar uwarta Salma still hawaye na gangaro masu su duka biyun.... A hankali Ilham ke mik'ewa har ta tashi tsaye saman k'afafun ta....
Kallon juna suke sosai ita da Salma hawaye da murmushi sun cika fuskokin su..... Lokaci guda suka rungume juna sai kuka ko ya kece masu sosai....
Ilham fad'i take "Addah Salma ina kallonki.... Ina ganinki a yanzu, kamannin da nake ganinki dashi a idanun zuci shi ya bayyana gabana a halin yanzu.... Addah Salma na gode ma Allah da ya bud'e min idanu na... Na gode maku gaba d'aya Allah ya biyaku da mafificin alkhairi.... Naso ace su Innoh Baffah da kuma Addah Jamila suna raye na kallesu amma haka Allah ya hukunta, kuma na gode masa da wannan ni'ima da yayi min wanda bama kowa yakeyi ba...."
Jikkunan su suka yi sanyi sosai, tsan-tsan tausayin Ilham ke ratsa zukatansu....
Daga nan ne Affan ya rik'o Ilham ya shiga nuna mata sauran family d'in... Duk wanda aka zo kansa kapsewa Affan yake sai yace mata oya guess wanene wannan? Ilham kuwa da zaran taji murya sai ta d'ago ko wanene... Affan yace tana masa ojoro su daina magana ta canka da kanta... Haka abin ya koma tamkar game kowa ya cika da nishad'i... Bayan su Daddy sun watse ne ya rage daga ita sai Affan d'inta saiko su Salma da Naseer...
Salma ke parking kayayyakin Ilham d'in sabida likita ya riga ya sallame su yayinda Ilham d'in ke d'an tayata lokaci guda Ilham ke jimamin rashin ganin Falaq da batayi ba gashi tuni sun d'age zuwa k'asar England.... Salma sai faman lallashinta take tana bata baki... Dai-dai lokacin Naseer da Affan sukayi sallama suka shigo hannun Affan rik'e da 'yar k'aramar gidan medicated glass wanda likita ya baiwa Ilham d'in...
Affan fah babu sauk'i yana shigowa ya shigayiwa Salma mitan ta bar Ilham na aiki.... Daga Salma har Ilham d'in dariyar draman Affan suke lokaci guda Naseer ya tsoma baki da fad'in "Nima d'in ai Matata batada lafiya wannan aikin ba nata bane...."
"Eh amma ai kune manya...." Affan ya fad'i murmushi saman fuskar sa....
Girgiza kai kurum Naseer keyi suna masu aika ma juna kallon soyayya shida Salmar sa...
Glasses d'in Affan ya shiga k'ok'arin mak'alawa Ilham itako sai shagwab'a take zuba masa tana fad'in "Ya Affan nifa banson glasses d'in.... Kuma wai sai barci na cire gaskiya zai tak'urani..."
Affan ya ida mak'ala mata yana hango 'yan manyan idanunta ta cikin glasses d'in ga d'an peach lips ta turo shi gaba so cute... Gaba d'aya sai ta dad'a masa kyau har baisan sanda ya kusan kai mata sunba a wajen ba... Zaro idanu tayi tana turesa take fad'in "Ya Affan me kake yi it's embarrassing...." Ta k'arashe tana satan kallon su Salma da gaba d'aya hankulansu bai wajen yanaga tattare sauran stuffs d'in Ilham d'in suma soyewansu suke yayinda suke parking kayan..... Salma na zipping jaka yayinda Naseer ke saka medications cikin wata 'yar leda...
Affan ya d'an matsota cikin jikinsa kana yace "Soyayya fah nake nunawa matata banga abin jin kunya ba.... Baby bana kunyar duniya ta shaida cewa ni masoyinki ne...." Ya k'arashe idanunsa tarr cikin nata...
Murmushi kawai tayi tana dubansa don da ta saka glasses d'in sai tafi gani clearly.....
"Ya Affan nafi ganinka da kyau da na saka glasses d'in.." Ta fad'i murya fal yarinta...
Murmusawa yayi kana yace "See na fad'a maki ai... Kuma ya maki kyau sosai, I love my Baby...." Ya k'arashe yana murmushi mai bayyana hak'wara....
"Lovebirds kufa muke jira oya ku taso mu wuce kasan anjima munada meeting kuma ya kamata ka halarta...." Cewar Naseer dake k'ok'arin mik'awa Affan jakan kayan Ilham....
"Kai gaskiya Captain nifa amin uziri I've patient...." Affan ya fad'i yana k'ok'arin kamo Ilham da hannu guda....
Murmushi Naseer yayi yana mai girgiza kai alamun you're not serious kana yace "Ilham zaki bamu aron wannan Romeo d'in naki na wasu 'yan awanni idan yaso sai na bar maki Addar taki ta maki yinin ai ya maki koh...."
Ilham da kunya ta gama lullub'eta d'an sunkuyar dakai tayi kana tace "Kai Ya Naseer..."
Gaba d'aya murmusawa sukayi Salma na fad'in "Wllhi hakan ma yafi...."
Affan ya d'an dubeta yana murmushi kana yace "Kun dai k'ulla keda mijinki amma ai Baby ni kad'ai ke iya kula da ita...."
Daga Naseer har Salma dariyar Affan suke... Lokaci guda suke jiyo knocking daga k'ofa...
Naseer ne ya k'arasa yana amsa knocking d'in yake k'ok'arin bud'ewa....
Gaba d'aya da mugun mamaki suke dubansu...
Fawaz murmushi ya sakarwa Naseer d'in had'i da gaidashi...
"Dr kar dai kunyi missing flight....?" Naseer ya fad'i yana duban Fawaz d'in
Girgiza kai Fawaz yayi kana ya d'an matsa gefe ya baiwa Nafeesa dake rungume da Falaq Hanya suka shigo cikin d'akin sallama saman bakin Nafeesa....
Wani irin murmushi ne had'i da sabon hawaye ya shiga gangarowa a fuskar Ilham, tabbas ta cire rai da ganin Falaq sai gata a gabanta a zahiri.... Tuni ta cire glasses d'inta ta shiga mutstsuka idanun tana mai murmushi wanda ke bayyana hak'wara... Fuskar Nafisa d'auke da murmushi ta mik'awa Ilham d'in Falaq....
Lokaci guda Ilham ta lumshe idanu sanda ta rungume Falaq cikin jikinta... A hankali take furta "Habibty kece wannan.... Ashe zan ganki A DUNIYAR MU...." Ta d'ago Falaq d'in dake faman mata dariya had'i da 'yan tsalle lokaci guda take duban sauran mutanen dake d'akin tana mai fad'in "Kun gani itama taji dad'in gani na.... Ta gane yau idanuna sun bud'e na ganta....." Ta maida dubanta ga Fawaz kana tace "Fawaz na gode.... Thank you so much..."
Murmushi ya sakar mata kana yace "Na tabbata yanzu zamu bar k'asar in peace tunda kinga Falaq d'inki...."
Jinjina kai Ilham take still tana kuma jujjuya Falaq tana kallonta take fad'in "Baby Falaq Hayaty yau Momy Ilham ta Kalle ki... Hey do not forget how much we love you okay...." Falaq kuwa sai dariya take mata kaman tasan mai take fad'i, sauran jama'an d'akin ma sai murmusawa suke cikeda farin ciki....
Daga bisani ne aka sami zarafin gaisawa da juna kafin Fawaz ya sanar dasu sun d'an tura tafiyar nasu zuwa satin da za'a shiga... Abin sai ya kuma yima Salma da Ilham dad'i at least zasu d'an kuma samun time da Falaq....
Gaba d'aya gidan Daddy suka wuce harda Nafeesan Fawaz, nan fah suka had'e dasu Shareefah da Azeema aka saka chaptan labarai, Azeema na basu labarin gidan Laure suna k'yak'yata dariya lokaci guda suke mamakin bak'in zuciya irin na Laure.... Nan Azeema ta fahimci Nafeesar Dr Fagonta ne nan kuma wani tad'in ya kuma kecewa, dama Azeema yaya balle ta sami abin yi... Salma dai d'akin Mamy ta shige ta d'ale gado don yin barci don gaba d'aya surutunsu ya cika mata kunne... Aiko sai zolayarta suke Maman 'yan tara....
A ranar ne kuma iyayen Dr Siraj suka kawo tambayar Shareefah, abin kaman had'in baki washe gari Dr Fago ya kawo nasa tambayar shima, Masha Allah dama haka ne lokaci guda sai Allah ya wanke maka k'uncinka A DUNIYAR KA, bayan wuya sai dad'i....
Wannan karan gaba d'aya Mamy ta tattari su Shareefah harma da Affan da Ilham suka tafi Katsina yanda ta nemi gafaran danginta bisa neglecting d'insu da tayi... 'yan uwan gaba d'aya sunji dad'in ganin su Mamy da iyalenta har sukayi alk'awarin yanzu kam za'ake zumunci idan da laifin Mamy suma da nasu, sun d'au alk'awarin zuwa bikin Shsreefah da Azeema muddin Allah ya basu daman hakan, daga Katsina suka wuce Daura wajen dangin mahaifin Azeema yanda suma sosai sukaji dad'in ganin su Azeemar... Mamy ta basu nasu goron gaisuwar Azeemar had'i da sanar dasu an saka biki... Sosai suka nuna tasu farin cikin suma had'i da alk'awarin halarta koda ba dukansu ba.... Tafiya tayi dad'i domin kuwa sun nufo Bauchi da tarin tsaraba musamman Affan da amaryarsa Ilham....
***
*United Kingdom (Liverpool)*
Fawaz da family d'insa sun sauk'a abirnin Liverpool lafia sai godiyan Allah.... Dukda ba wani sakewa ma'auratan sukayi ba har yanzu amma kowa na k'ok'arin yaga ya kyautatawa d'an uwansa musamman Nafeesa wacce tuni Sister ta Anty Haly ta sanar da ita karatun rik'e miji kafin su bar gida Nigeria... Sam Nafeesa batayi wasa da hud'ubar Anty Haly ba musamman data lura da yanayin mijin nata... Gayu da jan hankali sosai take kula da wannan fannin... Uwa uba soyayya da kulawa da take baiwa Falaq sai ya kuma siye zuciyar Fawaz....
Yau a gajjiye ya dawo gidan after a long day, sabida yau ya k'ok'arta ya samawa Nafeesa gurbin karatu a University d'in nasu yanda zata karanci degree a fannin Nursing....
Bayan Nafeesa yake hangowa tana tsaye jikin gadon Falaq wanda yake kaman lilo irin dai ta yaran turawa, ta d'an rakub'e jikin gadon tana jijjiga gadon alamun tanaso Falaq d'in tayi barci... Da alama su duka biyun barci ya dace su don Nafisan ma gadon ya d'anyi supporting d'inta wanda hakan ya hanata fad'uwa.....
Cak Fawaz ya tsaya yana k'are ma bayanta kallo, sanye take cikin red top wanda yake bayan a tsattsage irin rigar nan dai da ake kira crazy, wando ne jikinta wanda ya kamata sosai ya kuma fitar da asalin kyaun surarta.... Ga sumarta irinta asalin mutanen Africa bak'i mai cika ta tupkesa tsakiyan kai da jan ribbon, ta masa kyau har ta gaji, duk jajayen fatan da ya fita yayita arba dasu sai yaga babu wacce ta kamo k'afar matarsa cikinsu.... A hankali yake takawa har ya iso yanda suke.... Fuskar Nafisa Fawaz ya k'urama idanu yana kallon sihirtaccen kyau na asalin bak'in mutum, a hankali yake furta "Black's beautiful...." D'an bakinta da yasha jan baki yafi komai stone masa idanu a fuskar nata.... Baisan sanda ya soma k'ok'arin kwanto da fuskar sa saitin bakin nata ba har saida ya soma jiyo tururin numfashin ta... Dai-dai lokacin barci yaci k'arfin Nafisa da batasan wainar da angon nata ke tuyawa ba.... K'iris ya rage ta fad'i k'asa Fawaz yayi saurin tallafota ta fad'o jikinsa dai-dai kuma lokacin Falaq ta farka ta soma kuka... Daga Fawaz d'in har Nafisa basu ankare da kukan Falaq d'in ba sunyi nisa cikin kallon juna, kallonta yake daga fuskarta har zuwa k'irjinta wanda wasu igiyoyi guda biyu suka zuge gaban rigar, ga wani ni'imtaccen k'amshi dake tashi jikinta, gaba d'aya ta tafi da Fawaz uwa wata duniyar har saida Nafisa tayi yunk'urin k'watan kanta sannan ya cikata... Lokaci guda ta isa ga Falaq ta sureta tana faman lallashi... Shid'inma k'arasowa yayi yana tayata lallashin Falaq d'in, sai sannan Nafisa ta samu zarafin masa sannu da dawowa, tana fad'in bataji dawowar sa ba....
Ga mamakinta yau murmushi mai ji da class taga yana mata harda d'an amsa mata hiran nata kafin ya shige bedroom ya tsalo wanka ya shirya cikin summer wears d'insa da shike ba lokacin sanyi bane...
A parlor Nafisa ta shirya masa abinci kaman yanda ta saba ta suri Falaq tana mai ci gaba da mata wasa had'i da canza salo na tafiya wanda kana gani kasan da gayya take,... Ai Fawaz kam da k'yar ya had'iyi loman abincin da yakai bakinsa... Nafisa ta sace hankalinsa gaba d'aya, ji yake da ace yana ganinsu itada Falaq a gefensa da sai abinci yafi wuce masa.... Yana ida cin abincin ya d'aga wayarsa ya tura mata sak'o su fito parlor suyi kallo sannan yanada wani surprise da zai bata...
Nafisa ta dinga juya wayan tana mamakin yau Fawaz ne ya gayyace zuwa parlor kallo, mutumin da sam baiso zama waje guda ya had'asu sai lalura, sannan ko meye surprise d'in sai Allah, uwa uba data tuna irin rik'on da yayi mata d'azun da kallon da yake binta dashi.... Ita kad'ai dad'i ya mamaye mata zuciya tasan tarkonta ya kama Fawaz, gaskiya bazatayi wasa da shawarin Anty Haly ba..... Sauri sauri ta kuma shiryawa had'i da yin duk wasu abubuwan da Anty Haly ta sanar da ita tayi kafin taje gaban miji sannan ta d'auki Falaq da tuni ta koma barcinta ta nufi parlorn da ita... Gogan kuwa idanunsa k'yam akanta...
Kai tsaye k'arasawa tayi ta ajiye Falaq saman gadonta kafin ta k'araso cikin parlorn, gefensa ya mata nuni dashi saman carpet kana yace tazo ta zauna... Babu musu ta k'araso ta zauna a yanda ya nuna mata...
Mutuwan Jamila ya kuma maida Fawaz wani miskili, wanda hakan sai ya koma masa tamkar ji da kai,...
Nafisa dai sai satan kallonsa take tana jira taga surprise d'in da ya sanar da ita zai mata... Saida ya d'ibi wasu mintoci ba tareda ya dubeta ba kafin daga bisani ya mik'a hannu ya janyo jakan laptop d'insa, wasu takardu ya ciro had'i da mik'a mata...
Nafisa ta d'an dubesa kafin tasa hannu biyu ta amsa...
A hankali ta furta "Na menene Dr....?"
Idanunsa naga TV yace "Ki bud'e ki gani....."
A hankali ta soma bud'e envelope d'in... Takardu ta gani kashi-kashi yanda ta shiga warwaresu d'aya bayan d'aya...
Lokaci guda taji murmushi saman fuskarta, tabbas takardun makaranta ne Fawaz ya sama mata gurbin karatu... Bata san sanda farin ciki ya mamayeta ba wanda sabida tsaban murna batasan sanda tayi tsalle ta rungumo masa ba tana mai fad'in "Na gode.. Na gode Abban Falaq...."
Sabon sunan data kirasa dashi sosai ya masa dad'i... Itako Nafisa d'an kunyarsa taji ta yunk'ura da niyyan barin jikinsa saidai tuni ya manneta mat a jikinsa ya hanata barin jikin nasa...
Bakinsa dake saitin kunnenta yayi maganar tamkar mai rad'a
"What did you call me... Did you say Abban Falaq... Sunan ya min dad'i pls kullum ki dinga kirana haka kinji..."
Nafisa kam saida ta had'iyi wata miyau kafin ta jinjina masa kai a hankali ba tareda ta iya furta koda kalma ba don gaba d'aya yau kam Likitan nata ya koma mata wani abu daban... Cikin kunnenta yake ci gaba da rad'a mata "Abban Falaq da Ummin Falaq ko basu maki dad'i ba sunayen....?"
Nanma bata iya amsa sa ba sai jinjina kai.... Sak'onni masu wuyan fasaltuwa Fawaz ke aika mata.... Masha Allah tundaga wannan rana Fawaz da Nafisa sun zamto cikakkun ma'aurata cikeda soyayyan juna da kuma fahimtar juna had'i da soyayyar d'iyarsu Falaq, duniyar su ta masu dad'i sai godiyan Allah....
****
Cikin Salma ya fito sosai don ta shiga wata na shida, ga bikin Daddy da Aunty Saudat da ya kunno kai wanda gaba d'aya abin shammatansu yayi, abin farinciki da k'ullin zumumci ya kuma had'e family guda biyun... Kowa wannan abu ya masa dad'i babu kaman Abbu da Naseer... Fawaz ma koda aka masu waya aka sanar dasu ba k'aramin farin ciki sukayi ba, saidai bazasu samu daman zuwa don already Nafisa ta soma karatu shima kuma yana tsaka da nasa karatun, saidai yace wa Uncle Naseer d'insa duk abinda ake ciki ya keeping d'insa posted...
Mamy ce tayita ingizawa ayi bikin Daddy a 'yan kwanakin don a samu ayi na 'ya'yansa Azeema da Shareefah daga baya... Gaba d'aya Mamy itace uwar biki ita ke shirya komai sai ka rantse ba kishiya za'a mata ba... Dole akwai kishi amma haka dole ta danne don itama nata farin cikin kenan... Musamman yau data kama ranar d'aurin aure da kanta ta ida shirya Daddy cikin shiga ta alfarma... Tana murmusawa take fesa masa turare kana tace "Aliyu kayi kyau... Ina maka fatan alkhairi, Allah ya baka ikon rik'emu bisa gaskiya da amana... Ina k'aunarka...." Tsananin rawa da muryarta keyi ya katse mata maganan nata...
Daddy da gaba d'aya yaji jikinsa yayi sanyi soyayyar Mamy na ratsa b'argo da tsokarsa, a hankali ya kamo hannayenta wanda suka sha ado da k'unshi.... Gaba d'aya sai ta tuna masa da k'uruciya da yaji ta ambace sa da sunansa na asali don rabonta da hakan tun suna university tun kafin suyi aure, tabbas ya yarda dole ko wata mace tana kishin mijinta saidai ta danne wanda dannewan shine mafi alkhairi..... Gaba d'aya sai yaji kaman bai kyautawa Mamy ba... A hankali ya soma fad'in "Asma'u idan baki son auren nan sai a fasa kinji...."
D'an turo baki tayi tanai masa kallon wasa kafin ta murmusa tana mai kuma gyara masa zaman babbar rigar nasa kana tace "Idan ka fasa kuma ni aka zalunta ai don tuni nasa rai zanyi k'anwa, kaid'in zaka zamto d'an gatanmu cikin yardar Allah... Farin cikin ka shine nawa, Allah dai kawai ya tayaka da adalci....." Bata ida magana ba taji Daddy ya kai mata sumba... Saida suka sha soyayyan su kafin Mamy ta k'yale ango ya fice d'aurin aure....
Masha Allah, sai son barka komai ya tafi yanda ya kamata, amarya Saudat ta tare a gidanta suna zaune lafiya da mijinta da kuma abokiyar zamanta tareda 'ya'yan mijinta, babu kaman Affan gaba d'aya ya zama d'an gidan Aunty Saudat dama Ilham kam 'yar gidan Mamy ce sai aka raba abin gashi tun lokacin bikin Daddy take fama da yawan zazzab'i yau fari gobe tsumma... Gaba d'aya sai ta tunowa Affan sanda ya abducting d'inta ya gana mata azaba... A 'yan kwanakin sai ya zama kaman lusari, jin laifin yake har cikin b'argo da tsokarsa... A hankali ya rik'ota daga bathroom bayan ya gama wanke mata aman da tayi gaba d'aya duk ta jigata, kwantar da ita yayi saman gado yanai mata sannu kafin ya k'arasa gefen bedside ya ajiye mata glasses d'inta bisa gaba d'aya Affan ya rasa meke masa dad'i ji yake gwara ya sanar da Ilham cewa shine wancan guy d'in koda zata tsanesa at least yadai sanar da ita gaskiya.... Itako Ilham gabinsa haka duk sai ya d'aga mata hankali, gani take ciwonta ne ya sanyasa shiga tashin hankali gashi tak'i yarda suje asibiti ta kuma k'i bari ya sanar wasu Mamy cewa batada lafiya...
D'an daurewa tayi ta yunk'uro ta mik'e ganin baiyi barcin ba kuma bai kwanta ba... A hankali ta matso dab dashi had'i da kwantowa saman bayansa... Murya can k'asa take fad'in "Love don Allah kayi hak'uri idan akan ciwo na ne na amince zanje asibiti zanga Dr kaji, wllhi banson ganinka cikin damuwa haka.... " Ta k'arashe murya na rawa...
Juyowa Affan yayi had'i da rungumeta lokaci guda yaji hawaye na neman ciko idanunsa sanda ya tuna wai da hannayensa yayita azabtar da Ilham d'insa wanda ya tabbata da ace wani ne da sai yanda k'arfinsa ya k'are...
Murya na rawa Affan yake fad'in "Baby I'm sorry... It was me... I was the...." Kasa ci gaba da maganar yayi sabida hawaye da yaji suna zubo masa lokaci guda...
Ilham ta rasa gane meke faruwa, k'ura masa idanu tayi don saima ta nemi ciwon da takeji ta rasa, ga bugu da k'irjinta keyi...
A hankali Affan ya sauk'o daga saman gadon ya durk'usa saman gwiwoyinsa yana mai fusakantar Ilham d'in still hawaye na gangaro masa kafin ya soma fad'in "Ilham.... I'm sorry, I truly am..... Ilham banida zab'i ya zama dole na sanar dake gaskiya koda zaki hukuntani..."
Kasa fahimtar sa tayi sai hawaye dataji itama suna neman wanke mata fuska, murya na rawa take fad'in "Love don Allah ka Sanar Dani wai meke faruwa ne.....? " Ta k'arashe cikin tsananin rawar murya....
Hannayenta ya kamo still yana durk'ushe a k'asa kafin ya soma fad'in "Baby promise me bazaki barni ba, ki min alk'awari duk hukuncin da zaki min bazai min tsauri babe... Baby don Allah ki...."
Gaba d'aya tsoro ya cikata, jada baya ta soma tana k'ok'arin k'wace hannunta.... Cikin kuka take fad'in "Wai meke faruwa ne, meyene ya faru.... Dan Allah ka sanar dani..."
Affan da gaba d'aya tashin hankali ya nuna a fuskar sa saurin mik'ewa tsaye shima yayi had'i da rik'ota cikin jikinsa... Murya na tsananin rawa ya soma fad'in "Baby bansan yaya zaki d'auki maganar bane bansan wani hukunci zaki yanke min ba, Baby ki yanke min ko wani iri amma banda rabuwa dani kinji....."
Zabura ta kuma yi tana yunk'urin k'watan kanta take fad'in "Ya Affan ka sakeni dan Allah, ka k'yaleni naje na kirawo su Mamy ko su zaka sanar dasu...
Affan da siriryar hawaye ke gangaro masa, idanunsa naga k'asa a hankali yake fad'in "I was the guy.... I was the that kidnapped you... Ilham nine mutumin da ya sace ki ya kuma azabtar dake...."
Ai bai kai aya ba taji jiri na neman kada ita ga bugu da k'irjinta yayi tamkar an sauk'e mata guduma....
*SameenaAleeyouNovels📚*
🌖🌖 *A DUNIYAR MU* 🌖🌖
*70*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
*_FINALE_*
*Gaisuwa tareda fatan alkhairi ga duk wanda ke biye da wannan labari daga fari har k'arshe... Na gode matuk'a da k'aunarku gareni... Inama zan iya zayyano sunayenku da na jeroku daki-daki amma ku sani a duk yanda kuke Sameena na k'aunarku kuma tanai maku fatan Alheri, Rabbi ya bamu dacewa A DUNIYAR MU baki d'aya... Ameen...*
Girgiza kai kurum take tanajada baya cikin rashin yarda da abinda kunnuwarta ke jiyo mata, wai Ya Affan shine mutumin da ya saceta, shine mutumin da ya azabtar da ita wanda har ya kusan mata fyad'e... Innalillahi wa Inna'ilaihi raji'un.... Kalman dataji zuciyarta na nanata mata kenan.... Bata ankara ba sai jin hannayen Affan tayi cikin jikinta yana k'ok'arin rik'ota...
Wani zaburerren k'ara ta saki tana mai k'ok'arin k'wace jikinta don gaba d'aya sai ta shiga tuno wancan lokacin da yanda hannuwan mutumin ke yawo jikinta.... Cikin tsananin kuka take fad'in "Let go.... Let me go.... Ka sakeni nace!!!!" Ta k'arashe tana mai bud'e muryarta sosai cikin fad'a wanda sam ba d'abi'arta bane, zan iya cewa tsawon rayuwarta bata tab'a irin wannan fad'an ba....
Affan girgiza mata kai yake hawaye na gangaro masa yake ci gaba da fad'in "Baby please do forgive me... Dan Allah ki yafe min kinji Ilham.... Wllhi I also hate myself for that.... Ilham please...." Bai kai aya ba ta shiga dukan k'irjinsa tana fad'in ya saketa ta tsane sa bata k'aunar kuma ganin sa.....
Cikin tsananin kuka take ci gaba da fad'in "So it was you..... Kaine Wancan bak'in azzalumin mutumin wanda babu d'igon imani a tattare dashi... You know the worse part of it..... You played innocent.... Kowa ya zaci kai mutumin kirkir ne my saviour not knowing kaine mugun.... Why meyasa... Me nayi maka, meyasa ka zagayo ka aureni daga baya..? Meyasa kakeda fuska biyu... Wllhi na tsaneka kuma bazan tab'a yafe maka ba... Kuma bazan ci gaba da zama da azzalumi irinka ba..." Ta k'arashe cikin tsananin kuka tana mai ci gaba da k'watan kanta daga rungumar da yayi mata...
Shid'inma cikin hawaye yake fad'in "Ilham the abu da zanyi kenan A DUNIYAR MU rabuwa dake... Never bazan tab'a iya rabuwa dake ba alhali muna raye... You're the love of my life.... Kiyimin ko wani hukunci amma banda rabuwa dake....."
Da k'arfin gaske ta finciki jikinta saidai ta kasa k'watan kanta daga rik'on da Affan yayi mata, sosai take kuka tana dukan k'irjinsa da duka hannayenta biyu....
Shiko sai dad'a jawo hannayen nata yake yana fad'in "Hit me... Go ahead and hit me.... Ki bugeni iyaka yanda kike so amma kar kice zaki rabu dani....."
Tsananin kukan da take ya hana ta saurari abinda yake fad'i.... Gaba d'aya k'arfinta ta saka ta ture Affan wanda gaba d'aya ya zama weak lokaci guda....
Cikin sauri ya nufota ganin ta nufi k'ofa... Aiko a d'ari ta juyo tana watsa masa mugun kallo take fad'in "Don't you dare... Wllhi kada ka kuskura kazo yanda nake.... "
Yana ganin taci gaba da tafiya ya kuma rik'ota yana fad'in "Baby don Allah ki tsaya ki tsaya ki saurareni I'll explain everyth...."
Fincikan da tayi wannan karan saiko ta zube a k'asa, cikinta ya bugu da gefen gado..... K'ara ta d'an saki tana tattamke idanu had'i da kame cikinta take fad'in "Cikina.... Cikina....."
A d'ari ya durk'usa cikin tsananin tsoro yana dubanta..... Aiko kafin ya sami zarafin magana yaga jini na bin k'afafunta..... Gabansa ya kuma yankewa jin irin nishin wahala da Ilham keyi....
Murya na rawa Affan yake fad'in "Innalillahi wa Inna'ilaihirraji'un...." Lokaci guda ya mik'e a rikice ya nufi sashen su Mamy.....
Mamy ce kawai da Aunty Saudat a parlorn Mamyn suna hiran su gwanin ban sha'awa yayinda Azeema da Shareefah ke can b'angaren Aunty Saudat suna kallon Reality Show d'insu don sun san yanda su Mamy suka baje kolin labarai bazasu barsu suyi kallonsu in peace ba shiyasa ma suka tattara zuwa parlorn Aunty Saudat...
A yanda su Mamy suka gansa gaba d'aya sai suka dasa aya wa hiran nasu suka mik'e tsaye cirko-cirko suna tambayarsa lafiya.... Don rabonsu da ganin irin wannan yanayi a tattare dashi tun kafin abubuwa su lafa A DUNIYAR SU....
"Mamy... Aunty ku taimake ni please I don't wanna lose her.... Dan Allah ku taimake ni....."
Daga Mamy har Aunty Saudat sosai jikkunan su ke rawa.... Mamy kam a d'ari ta fice bakinta na furta "Affan ina Ilham... Mai ya sameta....?" Bata sami zarafin sauraren amsar nasa ba don tuni ta fice....
Aunty Saudat kuwa k'arasawa ga Affan tayi tana k'ok'arin calming d'insa had'i da tambayarsa meke faruwa... Hannun Aunty Saudat kurum Affan ya kamo suka fice suka nufi sashen su Affan d'in....
Momy salati ta dingayi tana k'ok'arin kamo Ilham ga jini dake bin k'afafunta tamkar an yanka k'aramar dabba....
Aunty Saudat ma a kid'ime tayi kansu don da ganin wannan jini basai ance maka miscarriage ta samu ba.....
Ganin Affan ya nufosu tamkar wani sakare ya kuma k'ular da Mamy don gaba d'aya bata yarda dashi ba... Tsawa Mamy ta darara masa tana fad'in ya fito da mota su tafi asibiti.....
A kid'ime ya fice yayi yanda Mamy tace.....
Suna zuwa asibiti kuwa aka wuce da ita emergency gaba d'aya ta jigata don sosai jini ya zuba a jikinta.....
Sanda Daddy ya dawo gida ya tarar gaba d'aya su Mamy basa nan saiko su Shareefah da Azeema, nan suma suke fad'in basu san yanda su Mamyn sukaje ba don gaba d'aya ko k'arar fitar mota basuji....
Gaba d'aya daga su har Daddy cirko-cirko sukayi kafin Daddy ya kuma duban Shareefah yace "Sake dialing layin Mamyn naku...."
Jinjina masa kai Shareefah tayi tana mai ci gaba da dialing yayinda Daddy yaci gaba da trying layin Aunty Saudat da kuma Affan.... Aunty Saudat kam ma nan gida ta bar wayan nata.... Na Affan kuma ba'a d'agawa....
Da k'yar Daddy ya samu Affan daga jin yanayin yanda Affan d'in ke magana yasan babu lafiya.... Nan yake sanar dashi Ilham ce babu lafiya lokaci guda ya sanar da Daddy asibitin da suke.... Aiko Daddy baiyi wata-wata ba ya fice daga gidan aka bar Azeema da Shareefah cikeda jimami kowacce tana addu'an Allah ya kawo masu da sauk'i don har tsoron suji wani a asibiti suke.....
***
Gaba d'aya babu wanda yasan da cikin sai yanzu da ya zube kosu iyayen abinda ke cikin basu sani ba balle kakannin....
Wani sabon tashin hankali maras musaltuwa ne ya kuma ziyartan Affan... Ashe dama Baby ciki ne da ita... wayyo inama ya sani wllhi da bai soma sanar da ita wancan maganar ba... Gaba d'aya sai yaji laifin duka nasa ne.... Ya rasa d'ansa ya rasa gudan jinin sa because of his stupidity, kame kansa yayi a reception d'in lokaci guda ya kuma mik'ewa tasye ganin Daddy sun fito Dr na biye dashi yanai masa bayani....
Wani kallo kawai da Daddy ke watsa masa ya kuma sa jikin Affan mutuwa... Gaba d'aya sai yaji ya tsani kansa.....
Jiki a mace Affan ya nufi d'akin da aka kwantar da Ilham Mamy da Aunty Saudat suna gefenta suna mata sannu....
Aiko Affan na shigowa Ilham ta kuma fashewa da sabon kuka tana fad'in ya fice bata son ganin sa....
Banda turiri babu abinda Mamy keyi ita tasan za'a rina, shi ya saka Ilham yin b'ari.... Tayi k'wafa sabida tsananin b'acin rai batama san mai zata soma fad'i ba.... Kallon data watsa masa ya sanyasa ficewa jiki a mace ga hawaye na gangaro masa.. Allah sarki he lost his child..... Ganin haka yasa Aunty Saudat mik'ewa ta d'an saci jiki tabi bayan d'an gidanta.....
***
Aunty I swear to you.... I..... I didn't know she was pregnant.... Wllhi ban sani ba... This is also hard for me... Aunty d'ana fah na rasa... Meyasa Mamy da Daddy suka kasa fahimta ta....?" Ya k'arashe cikin tsananin rawar murya....
Hannunsa Aunty Saudat ta kamo suka zauna saman kujerun dake reception d'in kafin ta soma fad'in "Affan I know this is not easy for you either.... But what you did was wrong... Very wrong..."
Cikin rawar murya yayi saurin katseta da fad'in "Yeah... I know.... Na sani I was stupid, heartless and idiot... But Aunty wllhi wllhi tun a wancan lokacin na tsani kaina for what I did... And I don't even know if I can forgive myself.... Aunty ina son Ilham da duka zuciyata, I just can't imagine life without her..."
Cikeda tausayi Aunty Saudat ke dubansa... A hankali ta d'an fuzar da iska kafin ta shiga kwantar masa da hankali da kalamai masu taushi
"Ka kwantar da hankalinka Affan everything will be alright kaji koh... And sanar da Ilham da kayi you were right about that.. And I'm pretty sure da ace kasan tanada juna biyu da bazaka soma tunanin sanar da ita ba... Amma sanar da itan da kayi zai kuma tabbatar mata cewa you really do love her.... Ka kwantar da hankalin ka kaji Ilham zata sami lafia insha Allah... Sannan Mamy da Daddy nasan zasu sauk'o da fushin nasu kaji koh...."
D'an jinjina kai yayi yana mai jin dad'in shwawarwarin Aunty Saudat....
****
Tunda suka dawo gida bata koma sashen Affan ba tana nan sashen Mamy... Mamy na faman riritata, Ko gaisar da Mamy ya shigo yi Mamyn ma a ciki take amsawa balle Ilham wacce gaba d'aya tamkar batasan na existing ba... Sosai abin ya dami Affan...
Yau Salma tazo mata yini yanda tayita d'an mata fad'a gameda abinda takewa Affan tana nuna rashin jin dad'inta....
Ilham ta katseta da fad'in "Tabb lallai sannu Addah Salma cewa na kike na koma sashen Ya Affan bayan na fad'a maki shine mutumin da ya sace ni, shine dai wancan mugun mutumin.... Haba Addah Salma that monster almost raped me fah...." Tsananin rawar da muryarta keyi ya hanata k'arashe maganar nata....
Hannayenta Salma ta kamo kafin ta soma fad'in "Sistu I know exactly how you feel.... But at least Affan ya canci yafiyarki kuma da baiyi nadama tun wancan lokacin ba da ya aiwatar da mugun nufinsa akanki amma baiyi ba... Sannan sanar dake da yayi yanzu don yana k'aunarki ne shiyasa ya sanar dake gaskiyan lamari... Sistu pls ki yafe wa mijinki bakida wanda yafi shi....."
Ilham kallon Salma kurum take hawaye na kuma kwararo mata kana ta d'an saka bayan hannunta tana sharewa kafin tace "Addah Salma a lokacin da idanuna suka bud'e banida burin da ya wuce na soma saka Ya Affan a idanu na.... Wllhi ji nake zamata a makanta yafiye min A DUNIYAR MU sabida ganinsa da nayi na kuma tsunduma kogin soyayyarsa. I don't know, I'm so sad and confused..." Da sauri Salma ta rungumota ganin kukan nata na k'aruwa... Cikin kukan taci gaba da fad'in "Addah I lost my child... Na rasa baby na....." Salma sai faman shafa bayanta take tana mai ci gaba da lallashinta....
A b'angaren su Naseer kuwa a parlorn Affan d'in suke zaune yanda Affan ke gayawa Naseer d'in kukan sa shima Naseer d'in k'ok'arin lallashin Affan d'in yake kan faman yi....
"You know.... I feel responsible for everything... I... I just don't know... Naseer na kashe gudan jini na da kaina...."
Saurin dakatar dashi Naseer yayi kafin yaci gaba da fad'in "Affan you better take things easy... Kar kayi maganar da zai sa ka kauce hanya, abunda ya faru haka Allah ya k'addara and you can't do anything about it... Mu gode wa Allah da ya kawo mana da sauk'i... Ka san abinda nake so da kai ka tashi muje ka sami matarka kuyi magana ni zanyi wa Mamy magana ta k'yaleka ku gana da matarka kaji.. I'm quite sure Salma has already spoken with Ilham... Maza tashi muje Soldier... Ka daina bada Sojoji dan Allah, Mace duk ta susuta ka lokaci guda...
Murmushi Affan yake yana duban Naseer d'in kafin yace "Nifa Captain idan Ilham tace na ajiye kakina toh zan ajiye babu musu...."
Sosai Naseer ke dariya kafin ya rik'o Affan d'in suka fice....
A parlor suka tararda Mamy tana amsa kira a wayarta... Nan suka sami waje suka zuna Affan kuwa sai faman shan jinin jikinsa yake ganin irin kallon da Mamy ke watso masa ...
Gaisawa Mamy sukayi da Naseer cikin sakin fuska yayinda Affan ko kallon arziki bai samu daga gareta ba....
Naseer ya d'an kuma gyaran murya had'i da d'an turowa gaba daga cikin kujeran kafin ya soma fad'in "Mamy dama alfarma muka zo rok'a..."
Tuni Mamy ta katse Naseer da fad'in "Idan dai akan Affan ne ka cire kanka cikin maganar nan Naseer don na gama magana Ilham babu yanda zatabi Affan yaje can yayi tafiyar sa shi kad'ai amma banda d'iyata ehe...." Ta k'arashe tana huci..
Affan ya kuma marairaicewa had'i da zamowa daga saman kujera yana mai fad'in "Mamy kiyimin rai ki k'yaleni na tafi da matata wllhi zan kula da ita yanda baki tsammani...."
"Rufe min baki...." Mamy ta katsesa kafin taci gaba da fad'in "Ku tashi ku fice min ku bani waje...."
"Mamy a taimaka a bar Affan su d'anyi magana da Ilham pls Mamy a taimaka, a d'an duba lamarin....."
K'wafa Mamy tayi had'i da jinjina kai tana mai duban Affan d'in take fad'in "Kaci albarkacin Naseer kuma ka tak'urata nida kaine...."
Affan dai k'unshe murmushinsa yayi yana mai jinjina kai yake fad'in "Thank you Mamy insha Allah bazan sata kuka ba we would fix this......"
Mamy dai tab'e baki kawai tayi kafin Affan ya nufi upstairs Naseer kuwa sai binsa da kallo yake yana murmusawa, draman Affan da Mamy na birgesa....
Daga k'ofa Affan ya d'an rakub'e yana masu knocking....
Salma ce ta basa izinin shigowa tana mai gyara mayafinta...
Haka ya shigo yana faman satan kallon Ilham sanda suke gaisawa da Salma ... Nan Affan ke sanar da Salma Naseer's waiting for her downstairs....
Sallama Salma tai masu kafin ta mik'e da k'yar sabida zungureren cikinta sannan a nufo k'asa...
Shigowar Aunty Saudat ya hana su Salma tafiya suka d'an kuma zaman gaisawa....
***
Rungumota Affan ya kuma yi yana shak'an k'amshinta da yayi missing.... Idanu a lumshe murya can k'asan mak'oshi yake fad'in "Baby why didn't you tell me about the pregnancy... Ilham mai yasa baki sanar dani kina d'auke da Baby na ba....." Yanda yayi maganar murya har na rawa
Baki a ture tana goge idanunta take fad'in "I didn't know either... Nima ban sani ba...." Kuka ya kufce mata
Saurin matseta jikinsa ya kuma yi yana fad'in "It's okay Baby, ki daina kuka kinji Allah zai kawo mana masu zama kinji koh...."
Bata iya amsa sa ba sai lamo da tayi cikin k'irjinsa ita kanta tasan tayi kewar mijin nata
Shiko tuni ya dad'a sakin jiki yana mai ci gaba da wanke kansa "I'm sorry baby.... Ki yafe min kinji Love....."
Ilham dai hawaye ne ke zubo mata baki a ture sai narka masa shagwab'a take shiko na biyeta. .
"Baby kin yafe min zamu tafi Cyprus tare koh....."
Kafad'a ta mak'e masa alamun o'o...
Ya kuma marairaice murya yana mai ci gaba da fad'in "Haba Baby kinsan dai bazan iya rayuwa A DUNIYAR MU ba without you by my side..." Gaba d'aya sai rikita ta da kalolin soyayyar sa yake wanda tuni ya mantar da ita wani fad'an da suke...
Mamy dai dataji shiru sawun Affan tabi, yanayin data gansu ya hanata kutsa kai cikin d'akin... Dad'i ya mamaye zuciyar Mamy ta dinga hamdala a hankali tabbas itama fatan ta kenan yaran nata su d'inke.....
***
A 'yan satuttukan Affan da Ilham suka soma shirin tafiya k'asar Cyprus yayinda bikin Shareefah da Azeema ya rage sati guda jal..... Su Affan basu sami bikin ba saidai sun masu fatan alkhairi, Salma ko cikinta na wata na takwas akayita hidiman bikin don haka itama ba duka activities d'in ta sami halarta ba....
Alhamdulillah Matan Doctors ko wacce ankaita gidanta hankalin Mamy ya kuma kwanciya... Allah ya cika mata burinta A DUNIYAR TA, saidai son barka....
***
Zaune suke bakin Auditorium fitowarsu kenan daga lectures don an dawo daga hutun zangon karatu na biyu an soma fresh semester kenan, ko waccensu logbook d'ina ne a hannunta alamu zasu tafi IT kenan.....
Lubna ta kuma duban Nazeera kana tace "Yanzu dan Allah da gaske anyi withdrawing Faty... Allah sarki wllhi banji dad'i saida tazo har aji hud'u sauranta aji biyar jal ace an koreka makaranta gaskiya da ciwo...."
D'an tab'e baki Nazeera tayi kana tace "This is what she chooses.... Dama ance duk wanda yak'i sharan masallaci zaiyi na kasuwa wanda baiji bari ba yaji hoho... Wllhi Lubna kinada sanyin zuciya.. After all what she's done to you amma still tausayinta kike.... Mai za'ayi da muguwar k'awa irin Faty Shazumami...."
D'an murmusawa Lubna tayi kana tace "I don't hold grudges on to people... Duniyar duka nawa take, yau kaine cikinta gobe bakai bane, da d'an adam yasan aikin dake gabansa bazai b'ata lokaci wajen rik'e wani a zuciyarsa ba.... Allah dai kawai yasa mu dace..."
Murmusawa Nazeera tayi kana tace "Hakane kam maganarki gaskiya ne... Ameen ya Rabb...."
"Kinga tashi mu isa Bus stop don bana tunanin Malam Tanimu zaizo....." Lubna ta fad'i tana d'aukan handbag d'inta...
Nazeera ta mik'e tana fad'in "Allah sarki where is that your driver... Baby driver inji Faty, gaskiya shikam yasan aikinsa don naga har jiranki yake ki fito daga lectures ku tafi...."
Lubna tayi murmushin k'arfin hali domin kuwa an fama mata mikin dake cikin zuciyarta...
A hankali ta furta "Deeen..." Saida ta sauk'e nannauyan ajiyan zuciya kana tace "I don't know his where about Nazee..... Deen ba driver bane kawai a wajena.... He's the love of my life... Gashi ya tafi ya barni, but tuni nasa ma raina dangana kalan tawa k'addarar kenan A DUNIYAR MU...."
Jikin Nazeera sai yayi sanyi gaba d'aya sai taji dama bata tambayeta ba.... A hankali ta d'an dafa Lubna kafin ta soma fad'in "Lubna kiyi hak'uri kinji... Tabbas Shak'uwa da dad'i rabo da wahala, if you two were meant for each other ina mai tabbatar maki Deen zai dawo gareki kinji... Allah zab'ar da abinda yafi alkhairi..."
A hankali Lubna ta amsa da ameen... D'ago kan da zatayi taji k'irjinta ya wani irin bugawa... Wa take gani a gabanta... Tabbas shine dukda d'an rama da yayi bazatace bata ganeshi ba.... Shid'inma idanunsa k'yam akanta ya nufosu...
Nazeera ta d'ago kai tana duban ikon Allah... Wad'annan masoya biyu saida suka iso tsakiyan fili kafin kowannen su yaja yayi birki .... Tuni hawaye sun soma gangarowa idanun Lubna...
Cikin sanyin murya ya furta "I'm sorry...."
Saurin dakatar dashi tayi ta hanyar d'aga hannu kafin taci gaba da fad'in "Mai ka dawo Yi? Ka dawo ne ka kuma breaking heart d'ina into thousand pieces ... Deen why? Why please...?" Kuka yaci k'arfinta
Tuni idanunsa sun ciko k'wallan soyayya shima... A hankali yake fad'in "Lubna I'm sorry.. Please do forgive me.... After I left, I realized that I can't go on without you... I realized that my happiness is here with you... You're my happiness, my dream of Love... Dan Allah ki yafe min and give us chance to reconcile..... I.... I promise I won't leave you again kinji happiness..." Ya k'arashe muryar sa na tsananin rawa...
Tuni Nazeera ta k'araso ta rik'e Lubna dake kuka sosai tana lallashi...
"Deen ka tafi.. Ka tafi please before I hate you.... Banason duk wani abinda zai kuma breaking d'ina... I've had enough already... Please leave..."
Yayinda hankulan cincirindon mutanen dake wajen gaba d'aya ya yo kansu Deen ya kai gwiwoyinsa k'asa ya durk'usa saman su... Hawaye na gangaro masa yake fad'in "I can't go on like this... Dan Allah ki fad'a min abinda zanyi ki yafeni kuma ki yarda dani... Remember they say.. If they love you they will come back..."
Lubna hawaye take amma murmushi take lokaci guda kunyar jama'an dake wajen ya cikata... A hankali take furta "Hey... Get up please it's embarrassing.. Dan Allah ka tashi..."
Girgiza mata kai yayi kana yace "Sai kin amsa min tambayata.. Lubna Sa'oud will you be mine forever....?"
A hankali take jinjina masa kai alamun eh ga hawaye na bin k'uncinta annuri ya cika fuskarta take fad'in "Yes... Yes I'm your forever....."
Haba nan fah waje ya kacame da ihu da tafi, yanda kasan a wasan kwaikwayo haka Deen da Lubna suka birge dandatson d'aliban.. Nazeera ko babu wanda yakaita murna..
Dawowar Deen dasu Mama Tani ba k'aramin dad'i ya haifarwa Family d'inba.. Tuni an soma maganar auren Lubna da Deen gadan-gadan... Washe garin bikinsu Lubna Salma ta santalo d'iyarta k'atuwa mai kamanninta sak saidai hasken fatan Naseer ta d'auko da yanayin gashin sa... Masha Allah sai son barka.. Ranan suna yarinya taci sunan Maman Naseer wato Hidaya suna kiranta Heeda... Soyayya da gata wannan yarinya da mahaifiyarta sun gansu daga 'yan uwa da abokan arziki.. Babu kaman Naseer wanda farin cikin da ya shiga maras misaltuwa ne.. Salmar sa ta haifo masa mai kamannin ta kuma mai sunan mahaifiyar sa dole ya gode wa Allah ya kuma gode masa da wannan baiwa da yayi masa...
Ranar da Hidaya ta cika sati biyu cur a duniya aka kirawo Naseer daga prison yanda aka sanar dashi jikin Innah yayi tsanani.... Tuni Naseer yasa an d'auketa an mayar da ita TH yanda k'wararrun likitoci suke..
Allah sarki idan kaga Innah dole tsoron duniya da imani su kuma shigan ka...
Naseer ya kuma duban Likitan kana yace "Are you seriously serious..... Haba Dr ya zakace mutuwa zatayi.. Kaine da rayuwa a hannun ka ko me..? If you're that incompetent to the point that you can not do anything sai ka sanar damu mu canza mata asibiti bawai ka yanke tsammani wa mutum ba..." Cikin tsananin b'acin rai yayi maganar..
D'an murmusawa Dr yayi kafin yace "Calm down Captain... This is my job.. Ni na sani kaman yanda kasan bakin bindiga haka nasan bakin allura... Captain ina mai tabbatar maka matan nan ko taci gaba da rayuwa wahala kawai zata ci gaba da yi.. A tak'aice barin fayyace maka komai... Na farko ita lesbian ce na biyu Smoker.. Cigarette smoking can cause the following
Alzheimer
Dimentia
Lupus
Cohn's disease
Psoriasis
Bladder cancer
Cervical cancer
Colorectal cancer
Rheumatoid arthritis
Stroke
TB
Liver cancer
Lung cancer
Diabetes type 2
Heart disease
Vision loss... Kaji duka wad'annan cututtuka dana lissafo maka Innah tanada su except stroke.. shima d'in sabida cutan Parkinson da take fama dashi shiyasa Stroke bazai sami gurbi jikinta ba..."
Ya ilahi kawai Naseer ke furtawa.. Shi tunda yake bai tab'a jin sunayen wasu cututtukan ba wai duka suna nan jikin Innah... innalillahi wa Inna ilaihiraji'un.. Wllhi d'an Adam shi ba komai bane idan yana tunanin shi komai ne, in seconds sai Allah ya maidaka abin tausayi and there's absolutely nothing you can do about it.. Allah ka bamu k'arshe mai kyau..
Naseer na hawaye yake duban Dr kana yace "Can I please see her...?"
Dr ya jinjina masa kai kana yace "Zaka iya ganinta amma sai ka saka mask sabida isolated area take..."
Naseer ya jinjina kai yana kuma tsoron duniya.. Jikinsa bai gama yin sanyi ba saida yayi arba da Innah tamkar ba mutum ba sabida tsananin rama da muni da tayi... Da alama magana take son masa amma ta kasa.. K'ok'arin d'ago hannunta take shima ta kasa.. Allah sarki Duniya budurwar wawa... Shigan Naseer wajen Innah da kad'an tace ga garinku Allah yayi mata cikawa.. Haka hawaye suka rink'a zarya a idanun Naseer.. Da shike shid'in yanada zuciya mai kyau sam avubuwan da Innah tai masa bai hanasa rok'a mata yafiyar Allah ba da kuma fatan dacewa...
Mutuwar Innah ya kuma haifar masu da tsoron Allah a zukatansu.. Sosai abin yayi affecting Lubna, haka Deenin ta yayita lallashinta yana riritata, for second bai bar side d'inta ba.. Lubna ta amince ta yarda ita d'in tayi dacen gwarzon miji mai k'aunarta...
A haka rayuwa taci gaba da tafiya masu bayan hankula sun kuma kwanciya.. Ko wacce tana gidan mijinta sai son barka..
***
_*16 years later*_
Tafe yake cikin dandatson Sojin sama, duk yanda ya gifta k'ame masa kawai ake ana sara masa.. Kamannin sa bai wani canza ba sai girma da k'warjini da ya k'ara... Kallo guda zakayi ma Uniform d'in dake sanye jikinsa kasan cewa ya sami d'inbin nasarori cikin shekarun....
CHIEF OF AIR STAFF kenan wato AIR VICE MARSHAL NASEER SA'OUD SANTANA... Gefe dashi kuma amininsa ne kuma abokin aikin sa wato AIR COMMANDER AFFAN ALI SAFWAN.. Gaba d'ayansu sun sami d'inbin nasarori wanda kana ganinsu basai an sanar dakai ba.. Yanayin murnan da ake masu zai tabbatar maka bukin basu muk'aman ake....
Da k'yar Naseer ya samu ya saci jikinsa ya fice daga wajen ya shiga dialing Sarauniyar sa... Bugu biyu ta d'aga tamkar wacce take jira..
Da sallama ta d'aga wayan yanda Naseer ya amsa mata murya cikeda jin dad'i.. Lokaci guda take masa shagwab'an yak'i dawowa daga Abuja ga Heeda da Miemie kullum maganarsu a koma school suma su koma Abuja suga Daddy..
Tuni ya soma riritata yana fad'in "Reina nayi missing d'inku gaba d'aya keda Princesses d'ina.. Sannan nafi missing Unborn ya kamata na dawo muyi masabaha sosai..."
Murmusawa tayi had'i da d'an sadda kai k'asa tamkar yana ganinta don tuni ta d'ago nufinsa..
Naseer ya katse mata shirun da fad'in "Ki shirya tarban Chief of Air Staff nan da sati guda insha Allah.."
Ware idanu tayi tana murna kana tace "Are you serious Roy.. OmG I really can't wait... Na zaci bukin k'arin girman na 'yan Abuja ne kawai banda mu..."
Naseer ya murmusa kana yace "Ai muk'amin naki ne gaba d'aya sai yanda kikayi dashi..."
Dad'i ya kuma mamayeta lokaci guda ta dinga jero masa addu'o'in cin nasara a rayuwa, kafin daga bisani sukayi sallama..
***
*Liverpool _United Kingdom_*
Wani irin tsawa ya darara mata wanda saida ya sanyata zabura... Cikin sauri ya k'araso d'akin yana mai ci gaba da tururi yake fad'in "How many times do I have to warn you bana so kina d'aukan ko wanne book d'ina... Falaq since when kika soma rashin jin magana...?"
Nafeesa dake tsaye bakin k'ofa rik'e da wani yaron da bazai haura shekaru hud'u ba ta d'an taresa da fad'in "Honey please...."
"No you stay out of this.. I need to teach my daughter a lesson, sabida tasan she's not British she's Nigerian, bazan bari d'abi'un turawan yamma yayi tasiri a rayuwar yarana ba don ina zama a k'asar su....."
Tuni idanunta sunyi rau-rau.. A hankali take fad'in "I'm sorry Dad... I just want to become a successful doctor like you... Kayi hak'uri pls Dad.. I won't do it again..."
Gaba d'aya sai jikinsa yayi sanyi don da ace da ne da tuni Falaq tayi zuciya da kowa a gidan, don gaba d'aya d'abi'un turawa gareta.. amma da mamakin su yau sai sukaji akasin haka...
A hankali Fawaz ya k'arasa shigowa cikin d'akin kafin ya kamo face d'inta yana kallon hawayen dake kwararowa a idanunta... Cikin sanyin murya yake fad'in "Sweetheart bawai bana sonki bane nake maki fad'a. .No I just want you to be good gir.. Kinga high institution zaki shiga kuma wad'annan d'abi'u na turawa sam ba naki bane kinji sweetheart..."
Hannu tasa tana goge hawayenta kafin tace "Dad who's Jamila... who was she to you.....?"
Daga Fawaz har Nafeesa sai k'irajensu suka buga...
Bakinsa na rawa yake fad'in "Jamila's your sister mana.. Meyasa ki. ...." D'ago masa diary d'insa da tayi ya sanyasa had'iye maganar sa..
Falaq na hawaye taci gaba da fad'in "Na karanta komai... nasan komai yanzu kaida Mom baku bane kuka haifeni... but I'm so grateful... Na tabbata ban tab'a kukan maraici ba saima b'ata maku da nayita yi... I'm sorry Dad.. Mom dan Allah ku yafe min.. Haihuwata ce kawai bakuyi ba amma iyakacin gata da soyayya na iyaye kun nuna min..... And har abada zaku kasance iyaye na...."
Murmushi Fawaz keyi yana hawaye kafin ya rik'o hannunta yace "Thank you sweetheart.. thank you for accepting us bayan gaskiya ya bayyana maki.. Ko aure kikayi zaki kasance matarsa ce but you'll remain my daughter... I love you so much both you and your siblings.. you're my priorities..."
Murmushi Falaq take kana tace "Banda Mom...?" Fawaz ya d'an juya sukayi ido hud'u da Nafeesa ya sakar mata murmushi kana yace "She's my life...." Gaba d'aya sai sukayi murmushi lokaci guda Nafeesa ta k'araso suka rungume juna gaba d'aya... Dai-dai lokacin Jamila ma ta shigo dawowarta kenan daga school uniform sanye jikinta.. Tuni ta isa ta fad'a kansu tana fad'in Family hug...
A 'yan satuttukan Fawaz ya shirya masu komawa Nigeria gaba d'aya wanda hakan ba k'aramin faranta ran families d'in yayi ba....
Masha Allah zuri'a tayi albarka.. Musamman Daddy ya had'a liyafan murnan dawowar Fawaz da family d'insa Nigeria ba tareda sanin Aunty Saudat ba...
Yana zaune a parlor da d'an autan sa d'an gidan Aunty Saudat wanda yake tamkar jika wa Daddy... Nan su Mamy da Aunty Saudat suka sanar da Daddy ai tuni zabirar sa ya fallasa suka k'arashe suna nuni da Safwan autan Daddy dake faman buga game a parlorn Daddy, gaba d'aya parlorn Daddy ya koma wajen buga game sabida autan sa.. Nan sukayita dariya ganin Safwan kam ko ajikinsa sai buga game d'insa yake.. Mamy tace "Ai dai idan Safwan na gidan nan toh Daddy baka iya mana wani Surprise ba...." Aunty Saudat tace "Ah toh nima dai haka nace sai ya tafi boding tukuna...."
Daddy na murmushi yake shafan kan Safwan kana yace "Babu yanda Baba na zai tafi.. muna nan tare mutu ka raba A DUNIYAR MU... Shigowan Affan da ayarinsa yasa Safwan mik'ewa aguje yayi wajen 'yan uwansa.. Kan kace me su Azeema da Shareefah da nasu ayarin suma sun iso .... Gaba d'aya suka tattara suka nufi gidan Abbu don acan za'a gudanar da shagalin...
Har aka iso gidan Abbu Mamy bata daina tuno yanayin dataga Laure ciki ba.. Babu sitira jikinta ga hauka gashi ta koma gurguwa... Allah sarki rayuwa kenan abin tsoro shuka khairan A DUNIYAR MU domin samun sakamako mai kyau...
Masha Allah.. Alhamdulillah Zuri ' tayi albarka... Lubna da mijinta Deeni duk yanda suka zauna toh fah draman su dole ya baka dariya... Allah ya albarkace su da yara biyu mace d'aya namiji d'aya.. Affan da matarsa Ilham suma yaransu Uku biyu mata guda namiji, Azeema da mijinta Dr Fago suma yaransu hud'u uku maza biyu mata, Itako Shareefah da mijinta Dr Siraj d'ansu d'aya ne namiji.. Saiko Naseer da matarsa Salma yaransu biyu duka mata sai unborn d'insu da muke fatan a kuma samun Air staff a zuri'a...
Naseer sai faman bin mutanen dake wajen da kallo yake d'aya bayan d'aya... Babu kalan da babu cikin zuri'ar kama daga turawa larabawa zuwa bak'ak'en fata.. Alhamdulillah ya furta a hankali don yasan tabbas babu wani sauran nuna banbancin launin fata da zai kuma gifta tsakanin su A DUNIYAR SU tunda cikin ikon Allah sun had'a gaba d'aya.. Alhamdulillah... Allah abin godiya...
Nima kuma a nan na ijiye alk'alamina had'i da furta ALHAMDULILLAH!
A nan na kawo k'arshen wannan labari nawa mai taken A DUNIYAR MU.. Ina rok'on Rabbi fad'akarwan dake cikinsa ya amfane mu dashi baki d'aya, kurakuren dake ciki Allah ya yafe mana baki d'aya... Amee!
*Sadaukarwa ga duk wanda ya tab'a fuskantar wariyar launin fata kona k'abilanci A DUNIYAR MU*
*Ke d'in ta dabance a duk sanda na d'aga alk'alamina da sunan rubutu kece mutum ta farko dake zuwa zuciyata... Allah ya bar k'auna ya barmu tare my Sisi... Rally Garba kin wuce aminiya a gareni ke d'in 'yar uwa ce har kullum zan kasance inai maki fatan alheri A DUNIYAR MU.. Rabbi ya sadaki da alkhairan sa.. Ameen!*
*Bazan mance dake ba a duk yanda kike.. Special Adviser Aysha B Abdullahi (Shaby) K'aunar mu daga Allah ne Allah ya bar zumunci Uwar Shema tawa!*
*Jinjina gareku*
Aysha Sada Machika
Aunty Aysha (Mrs Splendid)
Shawty
Haleema Mai Keke
Meela Adeel
Hauwa Usman (Jidda)
Allah shi bar zumumci
*Kud'in na daban ne Sameena Aleeyou Novels..... Ina alfahari daku ina kuma jidaku Rabbi ya barmu tare har a Aljanna*
*Zaurukan Alkhairi ana tare🤝🏼*
*Aysha Sada Machika Novels*
*Zauren Biebee Isa*
*Fadeela Talba Novels*
*ROF 2*
*Maman Hneep novels*
*Dama sauran da ban ambata ba ana tare gaba d'aya. . Na gode k'warai masoyana a duk yanda kuke A DUNIYAR MU ana musulmin tare... Sameena Aleeyou ke maku fata na alkhairi..🤝🏼*
#SameenaAleeyou
#ADM
#1love
#Anatare