Bayan Kwana biyu....
Lokacin lunch time dinsu ne yai, Khalid ya zaro wayarsa dake cikin dan safe din desk dinsa, murmushi yai akan sunan Zainab wanda a jikin alan wayar aka rubuta Babylove, wani sansanyan murmushi ya sake bayan wayar ta fara ringing, ganin harta katse bata dauka ba yasa ya ajiye wayar.
Sako ne ya shigo wayarsa, dauka yai ganin Nazifi ne yasa ya bude.
鈥淜halid in da hali zaka iya zuwa plx?鈥�
Hankalinsa ne ya tashi dan ya tabbatar abin ya shafi Zainab, fitowa yai ya hau adaidaita sai dai gani yake kamar bata gudu saboda hankalinsa dake tashe.
Yana isa Station din nasu ya kira Nazifi, da sauri Nazifi ya fito ya sameshi, Khalid cikin tashin hankalin daya kasa boyuwa yace 鈥淣azifi ya akai?鈥�
Nazifi yace 鈥渋n ba damuwa ko zaka shiga ciki?鈥�
Me ya faru da ita?
Nazifi ya kalleshi yace 鈥渋ta da directors da producers ne, ta sasu a meeting room tun safe ta koma office dinta ta zauna鈥�
What?
Nazifi yadan girgiza kai kadan yace bansan me ya faru ba.
Cikin hanzari Khalid ya shiga ciki, office dinta ya wuce direct tana zaune tana ta aikinta sanye take da glass saboda yawan kallan screen yasa take sawa.
Secretary dinta na kokarin sanar da zuwansa Nazifi ya girgiza mata kai, Khalid na shiga ta kalleshi tace 鈥渨aye?鈥�
Yace oganta.
Oganta? Sai kuma tai dariya tace 鈥渙hhh na gane.鈥�
Zainab ta dago zatai magana jin shiru bayan kuma an shigo.
Ganin Khalid yasa cikin mamaki ta zare glass dinta, murmushi ya sakar mata sannan ya nufi inda take.
Mikewa tai tace 鈥淪weet me kake a.....鈥�
Rungumetan dayai ne ya sata yin shiru a hankali ta dago tana kallansa, fuskarta yadan taba yace 鈥測a isa haka nan, okay?鈥�
Tace 鈥渕e?鈥�
鈥淣a sani haryanzu kina jin haushinsu saboda abinda ya faru da ne, kin nuna musu matsayinki ya isa haka nan鈥�
Kallansa tai tace 鈥淎llah saboda kai ne ban koresh ba duk ba abinda suka sani sai zaman kashe wando da gulma鈥�
Yace 鈥渋 know amma in kin duba manya ne su sannan sunada iyalai, zaki iya korarsu amma a hankali sannan ki sanarda kowa 2years before saboda ya shirya.鈥�
Fuska tadan hade tana kallansa tace 鈥渄an Allah ka dawo nan da aiki, canfa wahala kawai kake sha.鈥�
Harararta yai yace 鈥渕e suke a meeting room din?鈥�
Tadan kauda kai tace 鈥減unishment na basu na aiki, dan nasan ko zasu kwana acan bazasu iya samo mafitarba.鈥�
Ohhhhh ya fada yana hada goshinsu.
Murmushi tai tace 鈥渘aji zan ce su barshi.鈥�
Ummmm thanks.
Saketa yai yace 鈥渮an koma.鈥�
Dan rikeshi tai tana dai jujuya kai, murmushi yai sannan ya sumbaceta ya juya ya fita.
Nazifi ta kira ta bashi izinin su barshi sannan tacemai ya shirya tana so ya rakata yin signing din contract da zasuyi da masu company na detergent.
Nan ya juya cikin jin dadi.
Tare suka fito driver dinta na gun aiki ne ya shiga motar Nazifi ya zauna a gaba ita kuma ta zauna a baya tana tambayarsa abu yana bata amsa har suka isa.
C.E.O din na jin isowarta ya kalli magidancin dake durkushe gabanshi yace 鈥渢ashi ka fita dan Allah, bana san in samu matsala ta harkar business dina.鈥�
Kabir ne ya kalleshi yace 鈥渒a taimaka ka fadawa abokinka ya dauken aiki a gidan Tv dinsa, inada experience sosai akan harkar.鈥�
Zainab ganin haryanzu ba鈥檃 basu izini ba yasa ta watsama secretary dinsa kallo, nan ta juya ta kara shiga, daidai nan Kabir ya mike saboda jin yacemai ya tashi ya fita kafin yasa a koreshi.
Haka ya fito jiki a sanyaye, idanu suka hada, kallansa ta sakeyi sosai, tadan shafi saman kanta tana kara kallansa.
Da kyar yace 鈥淶ainab?鈥�
Wani kallo tamai sannan ta mike ba tare da ta kulashi ba ta nufi hanyar ciki.
Bakinsa na rawa yace 鈥淶ainab?鈥�
Kofar ta bude, CEO din ya taso da sauri yace 鈥淗ajiya barka da zuwa.鈥�
Kallansu yai da sauri, Zainab ta kalleshi tana murmushi tace 鈥淵allabai barka.鈥�
Kabir na tsaye kamar hoto aka rufe kofar, kasa ko daga kafarsa yai sai da secretary din yace 鈥渋n baka fita ba zan kira security.
Kabir haka yaja kafarsa dakyar yabar gun.
*******
Karfe Biyar da rabi Khalid ya dawo, tsayawa yai ya siyo 鈥榶an abubuwan bukata sannan ya karaso gida, ya san bata nan hakan yasa ya wuce kitchen ya ajiyesu, murmushi yai ganin kitchen din a gyare, yana fitowa ya wuce toilet yai wanka tare da alwala, yana fitowa tana turo kofar dakin.
Salama tai kamar mai shirin yin kuka, amsawa yai yana goge jikinsa da karamin towel yace 鈥淎n dawo?鈥�
Kusa dashi tazo tace 鈥淎llah kaina ciwo.鈥� Tai maganar tana zama akan gado.
Kallanta yai sannan yace 鈥渒insha Magani?鈥�
Kai ta girgiza mai alamar a鈥檃 tana neman kwantar da kanta akan pillow, da sauri yasa hannu ya tare kan nata.
Kallansa tai tadan lumshe ido, maida ta yai ta zauna daidai yace 鈥渕agrib ta kusa karki kwanta.鈥�
Hannu tasa ta riko hannunshi tasa a kanta tace 鈥渒ama min kaina.鈥�
Stress ne ya miki yawa, kiyi kokarin rage aiki kina barin na kasa dake suna yin nasu aikin, amma komai kice sai kinyi da kanki ko sai kin duba da kanki abin zai miki yawa.
鈥淜a dawo gurina ka tayani in ka damu dani.鈥�
Murmushi yai ya dau mai yana shafawa baice komai ba.
Kan kafadarsa ta kwantar da kanta tace 鈥渘ima zanyi magana.鈥�
Uhm ina ji.
Tace 鈥淪weet please daga yanzu duk abinda nai karka dinga dauremin fuska kaki kalona ko kuma kaki kulani, please ka dinga fadamin.鈥�
Dan juyowa yai hakan yasa fuskarsu tai daf da juna, dan kansa ya kwantar kadan saman kanta.
Tace 鈥渘ima zaka iya daukan magana ta selfishness amma banasan zamanmu ya cigaba in nama abu ka dinga dauremin fuska ba tare da na sani ba, Allah baka san yanda nakeji bane.鈥�
Kusa da kunnenta ya kai bakinsa yace 鈥渁 ina kika samo point din?鈥�
Dan dago da kanta tai saboda abinda ya dan ratsata, bugemai fuska tai hakan yasa yai dan kara kadan, da sauri ta mike tace 鈥渘a bige ka sosai?鈥�
Hancinsa ya rike yace 鈥渄a saninki ko?鈥�
Ni da kaina ke ciwo ina zan bugashi da sanina?
Da zafi? Ta tambaya tana dan neman zare hannunsa.
Ina budewa jini zaki gani.
Ido ta zaro tace 鈥渟osai ne?鈥�
Hannunsa ya sake yana murmushi, harararsa tai sannan ta mike.
Hannunsa ya sakalo ta kugunta yasa kansa akan kasan bayanta cikin sanyin murya yace 鈥渄azu dan ban zo ba me kike shirin yi musu?鈥�
Shiru tadanyi, yace 鈥渦mm?鈥�
Tace 鈥渟ai sanda da tashi in basuyi abinda nake so ba, duk da manyane ai basusan aikinsu ba, tunda abinda nace suyi akan aikinsu ne kaga ba wai ramuwa nai ta hanyar da basuda mafita ba.鈥�
Dan dagawa yai ya juyota saitinshi yace 鈥測a isa haka nan kinji?鈥�
Kallansa tai saboda yanda yai maganar ta sigar lalashi, tace 鈥渦hm na kyalesu amma in suka cigaba da yin abinda bai daceba zanyi replacing dinsu.鈥�
Kai ya daga mata, tace 鈥渕aganar dazu baka ban amsa ba.鈥�
Tai maganar cikin dan salo.
Saketa yai ya mike ya dau farar vest dinsa yasa yace 鈥渟hikenan.鈥�
Tace 鈥渋n ka sake min fa?鈥�
Yace 鈥渋n na sake zan ma kaina hukunci.鈥�
Murmushi tai tace 鈥渒a bari ni nai hukunci.鈥�
No ni zanyi da kaina.
Fadamin wani iri zakai?
Ummm ya ce tare da zura riga yace 鈥渒amar na hana kaina shan ruwa na awa uku?
Baki ta bude tace 鈥渟hine hukuncin?鈥�
Turare ya fesa sannan yace 鈥渄a alama kanki ya daina ciwo.鈥�
Tace 鈥淎llah yanayi kawai dai ba kamar da bane.鈥�
鈥淭o kiyi alwala muyi sallah sai kisha magani.鈥�
Kallansa tai sannan ta wuce toilet, shiru tai tana kara dubawa haryanzu fa ba abinda yazo, kwana 10 kenan, meke faruwa? Dan jiya ta duba taga stress ma nasa period yai late amma ai nata ya wuce 7 days.
Alwala tai ta fito sukai sallah, shiru tai akan sallaya taba tunani, ganin haka yace 鈥渁kwai paracetamol a gidan?鈥�
Kallansa tai tare da girgizamai kai alamar a鈥檃.
Mikewa yai yace 鈥渂ari na siyo.鈥�
Shiru tai dan ba paracetamol take bukata ba test take san yi, ba kuma tasan ta fadamai karyasa rai akan abinda ba haka ba, ta ina ma zata samu ciki? Bayan shekararta 4 da Adam ko bari bata taba yi ba? Gwara da farko tasan tai planning amma daga baya tana so amma ba alamarshi.
Yana fita ta dau waya tana duba abinda ke sa period yaki zuwa har tsawon 10days, sai dai duk inda ta duba zancen test ne gaba in har negative ne to sai ta duba ragowar matsalolin.
Mikewa tai ta fito falo tadan zauna a kasa, ta jawo laptop dinta tana duba wasu report da za鈥檃i program dinsu gobe.
Kofar da Khalid ya bude ne yasa ta kalleshi, mika mata ledar yai ta amsa ta mike tai kitchen, hadiyan maganin tai sannan ta dauko abincinsu ta fito.
Kallanta yai harta kawo ta ajiye yace 鈥渒e da bakida lafiya?鈥�
Murmushi kawai tai batace komai ba, zubawa yai da kansa, yace 鈥測aushe zaki dan share dakincan? Naga an kusa hutu su Nabila na zuwa.鈥�
Kallansa tai tace 鈥渟ai yanzu za鈥檃 budeshi?鈥�
Dan kansa ya shafa yana dariya yace 鈥渁i saboda ke na rufeshi, haka kawai nasan in dashi shareni zakiyi ki koma daki daya kina aikinki.鈥�
Ahhhh d鈥檃n Umman nan
Murmushi yai sannan yace 鈥渢aho muci abinci.鈥�
Harzatace bari na gama sai kuma ta fasa, mikewa tai ta matso ta zauna sukaci tare, yana shan ruwa tace 鈥淪weet ko mu koma can gidan in sunzo hutu? Nan kamar zai dan matsemana, dan Asiya ma zatazo, nasan su Amir ma nasan zuwa.鈥�
Kallanta yai yace 鈥渉ardasu Amir?鈥�
Tace 鈥渂asu sukace ba nice dai naga hakan, tunda ga Nabila da Asiya nasan zasu kula dasu.鈥�
Shiru yai yana dan nazari, tadan sa hannu kan cinyarsa tace 鈥渟ati biyu ne in suka tafi sai mu dawo.鈥�
Kallanta yai yace 鈥淣usaiba fa?鈥�
Shiru tadanyi tare da kallansa tana neman abin cewa.
Yace 鈥渘aga tare suke zuwa.鈥�
Cikin saurin magana dan karya gane tace 鈥渋ta a dole sanka takeyi fushi take dani nasan ba zuwa zatai ba.鈥�
Kallanta yai kawai ya sa dariya yace 鈥渟annu wannan maganar fa?鈥�
Tace 鈥渨ace?鈥�
Murmushi yai yace 鈥測arintace ke damunta in ta dawo ki hadani da ita a waya.鈥�
Da sauri tace 鈥渕e zakace mata?鈥�
Dan gefen kunnensa ya sosa yace 鈥測ayanta zai mata fada?鈥�
Aww ta fada tana dan jin kunyar kanta.
Har suka kwanta tana tunanin wannan lamari ko wani abun ne ya sameta? Bada menopause din data karanta yana hana period ba shine da ita ba? Ai bata girma ba batakai 50 ba, sai kuma tai ajiyar zuciya cikin damuwa, karfe biyar da rabi ta farka.
Tana tashi ta wuce kitchen miyarta ta duba ganin akwai ragowa yasa ta daura ruwa akan tukunya sannan ta fara wanke wanke, tana gamawa ta sa mai ta hau dan fere dankali.
Khalid dake kwance tun fitarta ya farka, mikewa yai ya gyara dakin tas sannan ya shiga toilet yai wanka tare da alwala, yana fitowa ta shigo dakin itama ta shiga wanka.
Cikin sauri tai wankan ta fito sannan ta sa kaya, falo ta fito inda ya dan gyara throw pillows din.
Tsintsiya ta dauko yana kallanta ta fara shara, cikin sauri ta gama, break dinsa ta kawo mai ta dau flask din tea dinta ta hada, tana fitowa daga kitchen ta kalli agoggo gani bakwai saura minti biyar yasa tai hanyar daki.
Khalid ne yace 鈥淏aby.鈥�
Naam ta fada tare da kallansa.
Alama ya mata da hannu, hakan yasa ta nufoshi alama ya mata data zauna kusa dashi zama tai tana kallansa.
Fork dinsa yasa a gabanta yace 鈥渃i鈥�
Cikin shakka tace 鈥済ishiri yayi yawa?鈥�
Ci ya maimaita yana kallanta.
Tace 鈥渟orry ina sauri ne bansani ba.鈥�
Kallanta yai ya kalli abincin, hakan yasa ta debo tai spoon daya, kallansa tai da sauri tace 鈥渂a abinda yai ko bakina ne?鈥�
Yace 鈥渘o ci, karki kara fita bakici abinci ba, wannan shan shayin ya isa haka nan.鈥�
Wuyanta ta dan shafa sannan tadanci.
Yauma tare suka fito sai dai yau bai bita ba a titi ya sauka haka ta tafi zuciyarta duk ba dadi.
*******
Yau su Nabila aka dawo hutu zuciyar nan fal take da zumudin zata gun Aunty, dan sam wannan term din haka tayishi ba dadi saboda Nusaiba haryanzu a kule take da ita, da batada kawaye amma wannan term din sai datai friends dayawa.
Abin nasu ma sai ya koma gasa, in Nusaiba taga Nabila da kawaye biyu itama sai ta nemo nata kawayen biyu, haka sukai ta wannan shirmen har sukai hutu.
********
Zainab kam yau tun safe takejinta ba daidai ba, ga abubuwa sunsha kanta ta kasa ma samun nutsuwan zuwa gun likita, ga tsoron yin test takeyi saboda tasan ba ciki bane.
Dayake yau asabar tana kwance har karfe 11, Khalid ne ya shigo cikin dakin, ya zauna kusa da ita yace 鈥渓afiya kuwa?鈥�
Kallansa tai tace 鈥渂akomai gaba daya karfine bandashi tun jiya.鈥�
Mikar da ita zaune yai yace 鈥渕uje asibiti?鈥�
Kai tadan girgiza tace 鈥渒o mu bari sai gobe?鈥�
A鈥檃 muje yau.
Shiru tai tana kallansa, kallanta yai shima yace 鈥渕e kike tsoro?鈥�
Shiru tai tana kallansa yanzun ma.
Are you that scared? Kar suce miki ciki ne?鈥�
Kallansa tai da sauri tace 鈥測a akai ka san abinda ke raina?鈥�
Dan yake yai yace 鈥渢un yaushe ya kamata period dinki yazo baizo ba? Kusan 3-4weeks kenan taya bazan gane ba?鈥�
Kanta ta sunkuyar, yace 鈥渂akyasan haihuwa?鈥�
Kallansa tai da sauri, yace 鈥渒ina dana sanin bakiyi planning ba abi yazo da haka?鈥�
Hannunta ta fixge daga hannunsa tana kallanshi, yace 鈥渂a haka bane?鈥�
Ranta a bace tace 鈥渨ani zance kale yi haka?鈥�
Yace 鈥渒e kike sani yin wadannan tunanukan, nasan shekarun da kukai da Adam na yadda bakyasan wani abu ya kawo miki cikas a aikinki, shiyasa ban ce miki komai ba haryanzu.鈥�
Ido ta zubamai jitai hawaye ya gangaro mata, a kufule taja bargo ta koma ta kwanta.
Baby? Ya fada yana neman juyo da ita, ganin taki juyowa yasa ya dan rukufo kanta yace 鈥渕eye hakan?鈥�
Kallansa tai tace 鈥渢aya zaka fadan kalaman nan?鈥�
Yace 鈥渢unanin dayazomin kenan nake fada miki.鈥�
Tace 鈥渒a san sau nawa nake fatan samun ciki? Kasan yanzu tsoron kar inje acemin ba shi bane shine ya hanani zuwa? Ka san yanda nake ji.......鈥�
Muryarta ce ta sarke, dagota yai ya rungumeta yace 鈥渁m sorry baby.鈥�
Zare jikinta tai tana kallansa, yace 鈥測a isa haka nan鈥�
Tace 鈥渞an laraba dady yace zasuzo, in mun fita zuwa asibitin sai na kira Nusaiban.鈥�
Kai ya daga alamar to, tace 鈥渮amu koma can din?鈥�
Muje mu dawo tukun.
Kai ta daga alamar to tace 鈥渁mma Allah naji haushi.鈥�
Yace 鈥渘a sani, sry鈥�
Tana shiga toilet zuciyarta ta fara tashi saboda kamshin sabulun, jin amai ne yasa Khalid shiga toilet din da sauri, amai take sosai ga ba abincin a cikinta aman sai wahala yake bata.
Bayanta ya shiga dan bugawa har ta gama.
Kallansa tai idanunta sunyi jaa, ruwa ya mika mata ta kuskure baki, dagota yai suka fito yace muje asibitin in kin dawo kyayi wankan.
Kai ta daga mai alamar to sannan suka fito.
A hanya ta kira Nusaiba, har sai data kusa katsewa ta daga murya a dakile tace 鈥淎unty.鈥�
Khalid ya ce 鈥淵aran makaranta an dawo?鈥�
Da sauri ta mike tsaye tace 鈥淯ncle?鈥�
Yace 鈥測an makaranta an dawo lafiya?鈥�
Tace 鈥渓afiya kalau.鈥�
Yace 鈥測aushe zakizo yayarki tana san ganinku.鈥�
Shiru tadanyi hakan yasa yace 鈥測anzun ma fushi tai nina lalabata taya kina kanwarta bazaki nemeta ba?鈥�
Shiru tasake yi dan batasan me xatace ba, yace 鈥渋n kinzo lalai sai kin ba yayarki hakuri dan ranta ya baci 鈥�
Cikin sakalci tace 鈥渘ima ai Aunty bata neman ba.鈥�
Inji wa yace miki? Bayan tunda kuma dawo take zumudin xakuxo?鈥�
Tace 鈥渄a gaske?鈥�
Yace 鈥渒i shirya inkunxo kya bata hakuri kinsanta in tai fishi.鈥�
Nusaiba tace 鈥渢o Uncle zan bata xan hada kayana yau.鈥�
Haka suka kara magana kadan kafin suyi sallama.
Zainab dake kwance a jikin kujera ya kalla, yace 鈥渟annu.鈥�
Murmushi tai tace 鈥淭hanks da alama Nusaiba xatazo.
Kallanta yai yadanyi murmushi.
**********
Kallan Dr din ta sakeyi bayan anyi test tace 鈥渕e kikace?鈥�
Tace 鈥淏akiyi test a gida bane?鈥�
Shiru tadanyi kafin tace 鈥淏anyi ba.鈥�
Murmushi tai tace 鈥渁bu harya kau 2mnt ya akai bakiyi ba?鈥�
Shiru Zainab tai, ta bata shawarwari kafin ta fito.
Khalid na ganin ta fito ya taho da sauri yace 鈥測a akai?鈥�
Kallanta yai yaga yanda duk tai wani iri, hanyar waje tai ya bita har suka isa gaban mota.
Budewa tai ta shiga, shiga yai shima yace 鈥淏aby?鈥�
Hannunsa ta kamo takai saman cikinta tace 鈥淪weet tace baby ce a ciki.鈥�
Kallanta yai da sauri, idanunta ne suka ciciko tace 鈥淚 never never.......鈥�
Rungumeta yai hawaye ne suka zubo tace 鈥� a duk sanda nai tunanin baby sai naga kamar na shiga hakkin wanda nake aure saboda bana haihuwa, ban taba yadda da gaske nima Allah zai dubeni ba.鈥�
Tai maganar cikin rauni, shikanshi idanunsa sai da suka dan canza saboda abu biyu na jin dadi da tausayin ta.
Haka suka taho gida hannunta rike cikin nasa.
*******
*******
Ayusher 馃弻馃徎鈥嶁檧
[1/23, 2:26 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
Good luck and tons of best wishes. God bless you in whatever you do. This is my heartiest wish for all of you馃挅
{70}
Tun a hanya yasai katin waya suna isa gida ya baje a falo ya kira Abba ya sanar musu, dadi kuwa agun Abba da Umma abin ba'a cewa komai, sai da sukai sallama ya kira wayar Dady yana sanar dashi.
Zainab dake kwance kan gado ta saki baki tana kallan ikon Allah, daga cikin wayar tanaji yanda Dady ke nuna matukar farin cikinshi, sai hamdallah yake yana godewa Allah.
Yana kashewa zai kira Salmanu tace "me kakeyi?"
Ya kalleta, cikin mamaki tace "baka kunyar fada?"
Yace "kunyar me?"
Kai ta dan girgiza tace "maza sai a barku"
Kallanta yai yace "dame za'a barmu?"
Ta gyara kwanciyarta tace "bandaice ba kar ace nace."
Dan dariya yai yace "ai kin gama fada."
Idanu ta rufe saboda yanda zuciyarta ke tashi, mikewa tai a hankali yace "ina zaki?"
Komawa tai ta zauna akan kujerar ta kalleshi tace "zamuje can din?"
Shiru yai yana kallanta, hannu tasa akan kafadarsa hakan yasa ya sake kallanta.
Please ta fada cikin sanyi.
Uhmmm ya ce tare da daga kai alamar eh.
Cikin tsananin jin dadi tace "Thanks" tadan kwantar da kanta akan saman kansa.
Murmushi yai yadan shafi fuskarta yace "Dady jin kina da ciki yace gobe su Nabila zasuzo, kenan sai dai mu koma yau."
Gobe? Ta tambaya cikin jin dadi.
Kai ya daga mata, tace "to ko mu hada kaya inyaso zuwa dare sai mu koma?"
Kai ya daga mata alamar eh fuskarsa ta kasa daina murmushi.
*******
Zuwa dare suka koma can Zainab dai har dare ta kasa cin komai kamar wanda aka zigo abin dan gaba daya ta rasa mema ke birgeta, ga uban yunwa wanda ya sa gaba daya karfinta ya tafi.
Bayan sunyi isha'i ne ta zauna akan gado tana ta daura pillow a cinyarta ta daura laptop dinta akai tana duba abu sai dai dishi dishi take ganin rubutun saboda yunwar dake damunta.
Khalid daya fita siyo abubuwan bukata ne ya dawo wajen karfe 9, kitchen yakai sannan ya shigo dakin, kallanta yai yace "tashi muje ki duba wani abu kici."
Kallansa tai tace "Allah bansan cin komai jikina ma duk ba karfi."
Fuska ya dan daure yace "haka kikeso ki wahalar da Babyn tun yanzu?"
Baby? Ta tambaya tana kallansa, tace "wannan kuma fa?" Ta nuna kanta da yatsa.
Dariya yai yana dan sosa cikin kanshi yace "maman baby?"
Tace "maman baby?"
Yace "eh ai yanzu kuma kin girma da sunan."
Fuska ta daure sosai tace "na zama babba ko tsohuwa kake cewa?"
Yace "Hajiya dama ai ke babba ce."
Kai ta kauda tare da dan juya kai saboda yanda yunwa ke galabar da ita.
Ya dan zauna kusa da ita yace "Da kin haihu da wuri na tabbatar da baby na primary hala."
Primary? Yanzu dai cemin kake na zama tsohuwa kenan?
Dariyarsa ya guntse yace "karki damu nima na zama tsohu tunda na baki wata bakwai."
Haushi ne ya kamata tace "ba sai ka tuna min mata sunfi maza saurin girma ba." Tai maganar a kule tare da kauda kai.
Dariya ya danyi sannan ya mike ya sa hannu ya dagota, yace "muje."
Kallansa tai fuskarta haryanzu a daure suka je kitchen, yace "duba abu kici."
Bude fruit din daya siyo tai sannan ta kalleshi ayaba ta dauka sai dai tana barewa taji amai ya taho mata, da sauri ta ajiye tai toilet, a wahale ta gama gaba daya jikinta rawa yake saboda yunwa.
Dagowa tai dakyar ya kalleta sannan ya dan kamota yace "sannu."
Kan gado ta kwanta tana maida numfashi sama sama.
Jiki a sanyaye yace "ko zakisha tea?"
Murmushi tai tare da dan daga kai, abinda ke yawo akanta kuwa ya zatai ga jibi akwai aiki.
Tea ya hado mata ya kalleta yace "tashi kidan sha."
Mikewa tai dan ita kanta yunwar takeji, ta dan kurbi kadan, sai dai duk yanda take san tea yau kam sam ta kasa sha, dakyar tai kurba uku ta girgiza kai jin gaba daya yana neman dawowa, kwanciya tai hakan yasa ya kalleta, tare da gyara mata bargon.
*******
Su Nabila da Nusaiba karfe 2 na rana suka sauka, a lokacin Zainab ta samu tai wanka tana kwance akan gado, Khalid ya kira Umma ya fada mata Zainab ta kasa cin komai, nan Umma tace "kai matsalar ba abinda ka iya, tunda gobe Asiya zata zo zan hado mata su garin kunu ta taho dashi, ita in tana nan ta dinga yi mata."
To shikenan.
Abba ta kalla tana dariya tace "Khalid na ji da matar nan"
Abba ya kalleta yace "da bai ji da ita da ke zaki fara mita."
Dariya tai tace "ni me nacici in inada cikima?"
Kallanta yai yace "hajiyar farau farau."
Dariya tasa sosai tace "na dauka ka manta."
Maganar radio dinsa ya kara yana cewa "ina zan manta bayan an kusa maida mana gida gidan farau farau.
Dariya sukai a tare.
Asiya dake hada kaya a daki ne ta fito jin Umma na kiranta.
Umma ta kalleta tace "dan zo ki dubomin garin kunu naga yawanshi.
Asiya ta dauko mata ta duba sannan tace "dauko garin tuwo nagani."
Nan ta kona ta dauko, Umma nata harhada su guri daya.......
********
Suna saukowa daga cikin mota Nabila ta shiga da gudu tai ciki, Zainab dake kwance kan kujera tana jin shigowar mota ta dan mike zaune, Nabila ce ta bude kofa ta shigo da sauri ta rungumeta.
Zainab tana dariya tace "zaki karyani."
Nabila ta dan saketa tana dariya tace "Aunty farinciki zai kasheni, Aunty zata haihu."
Tureta Zainab tai tace "wa kike jira ya shigo miki da kayan?"
Au tace sannan ta mike, fita tai taga Nusaiba a tsaya a kusa da akwatunansu tana zabga mata harara.
"Maida wukar Malama na dawo"
Nusaiba tace "karma ki dawo kema kinsan bazan dauki ko tsinkenki ba."
Zuwa tai ta ja nata akwatin da jakar hannunta tace "na sani."
Ciki sukai Mamman na musu dariya, suna shiga falo Nusaiba ta tsaya a jikin kofa tana kallan Zainab.
Zainab ta guntse fuska tana daga zaune tadan jingina saboda batada karfi ko kadan.
Nusaiba ta kalla ta mata alama da hannu akan tazo, a hankali ta tako zuwa inda take ta zauna tana kallanta cikin jin kunya.
Zainab ta jawota ta rungumeta, wanda hakan yasa Nusaiba sa kuka tana cewa "Aunty kiyi hakuri."
Zainab tai murmushi ta dagota tace "ya isa haka nan"
Nabila ta sa dariya tacs "ansha sakalci Auta."
Auta? Nusaiba ta kalleta ranga a bace.
Nabila ta mata gwalo, a kufule Nusaiba takalli Zainab cikin alamar kuka tace "Aunty kinganta ko?"
Murmushi Zainab tai da kyar tace "Nabila ki shiga hankalinki dani wlh."
Nusaiba ta mata gwalo itama.
Khalid ne wanda ya fita sallah ya shigo, Bala na sake gaisheshi.
Ganin Maman a harabar gidan yasa ya karasa da sauri ya mika mai hannu.
Maman ya mikamai shima suka gaisa, cikin jin dadi suka dan hira yana tambayarshi jikin Dady, yace da sauki abin ne dai ba dadi amma Alhamdulila.
Sun dan taba hira kafin Khalid ya shiga ciki.
Ganin ba kowa a falo yasa ya kalli Zainab dake kwance.
Kallansa tai tana murmushi tace "suna sallah."
Kai ya daga alamar to sannan ya zauna kusa da ita yace "yanzu fa? Kin dan sha yoghurt din?"
Nasha dan na kusa shanye robar ma.
Cikin jin dadi yace "good, yanzu kina san cin wani abin?"
Tace "in Nabila ta idar zata dafamin taliya."
Kallanta yai yace "sorry mijinki bai iya komai ba."
Zatai magana wayarta tai kara.
Dauka tai ganin number Basma, mamaki bayyane a fuskarta dan duk da suna da number juna ba waya suke ba.
Kallansa tai kafin ta dauki wayar hakan yasa ya kalli alan wayar.
MATAR GIDA abinda ya gani a jikin wayar kenan, wanda bai san sanda ya kalleta ba.
Dauka tai tare da sawa a kunnenta a hankali tace "Uhm."
Basma tace "Zainab ya jiki?"
Da sauki
Su Nabila sun iso?
Eh
Shiru suka danyi kafin tace "Naji shirmen da Nusaiba tai na mata fada kiyi hakuri, yarintace ke damunta.
Na sani.
Shiru suka sakeyi, tace "Jikin naki sosai ne?"
No
Jin dai wayar taki yiwuwa tace "shikenan Allah ya kara sauki, a gaida mai gidan."
Okay kawai tace ta kashe wayar.
Basma tai murmushi tare da kallan Dady, tace "at least ta daga."
Yace "kin taba kiranta ne?"
Kai ta girgiza alamar "a'a."
Yace "bani ruwa nasha."
Mikewa tai.
*****
Acan gidan Khalid kuwa.
Khalid ne ya kalleta, tasan magana zai mata hakan yasa ta koma ta kwanta akan kujera, yace "meye matar gida?"
Tace "matar gidan dady."
Dan dariya yai yana girgiza kai yace "matar dady dai matsayin uwa take a gunki, balle kun hada jini da 'yarta."
Uwa? Ta maimaita aranta batace komai ba.
Yace "ki canza mata suna ko maman Nusaiba kika sa yafi matar gida, yanzu in Nusaiban ta gani zataji dadi?"
Shiru tai tana kallanshi yace "bazai yiwu ba?"
Kwanciya ta sakeyi tace "bance ba."
Murmushi yai yace "thanks."
Yasa hannunsa akan saman kanta.
fitowarsu Nabila daga daki ne yasa ya kallesu yai saurin sauke hannunsa, fuskarsa dauke da murmushi yadan matsa daga kusa da ita.
Gaisheshi sukai ya amsa Nusaiba sai kasa take dakai.
Nabila yunwa nakeji ta kalli Khalid ce tace "Sweet kaima yunwa kakeji, me zakaci?"
Kallanta yai yace "daga isowarsu kar a sasu aiki dayawa suyi taliyar kawai gaba daya."
tadanyi yaji? Ta tambaya tana kallansa.
Murmushi yai yana kallanta sannan ya daga kai.
Mikewa sukai suka shiga kitchen.
Nabila ce ta kalli Nusaiba tace "Nusaiba mareni in mafarki nakeyi."
Nusaiba tace "mafarki?"
Nabila tace "da gaske Aunty ce a zaune a falan can?"
Nusaiba tasa dariya tace "na dauka ni kadaice nai mamakin abinda na gani."
Oh ni Aunty ce take magana ba yanda ta saba ba? Sannan abinci ma sai ta tambayeshi?
Dariya sukai Nabila tace "Sweet kaima yunwa kake ji me zaka ci?"
Dariya sukai a tare kafin su sa abincin.
Suna gamawa Nabila ta fito tace "Aunty an gama."
Zainab tace "okay bari nazo."
Mamaki ya kara kama ta dan tasan da dane hankalinta a kwance zatace Nabila zubomin.
Mikewa tai ta shiga kitchen ta dau na flask din ta hada ta dau tire din tai daki.
Nusaiba da Nabila suka saki baki suna kallan ikon Allah.
Ajiyewa tai ya mike da sauri yace "ke da baki da lafiya me kikeyi hakan?"
Dan jikinshi tasa kanta tace "kanshin abincin ke damuna tun ana dafawa."
Yace "ki dan daure in kikaci kadan kila kamshin zai tafi."
Dakyar ta iya cin loma hudu duk yanda taso ci kasa wa tai.
Ya kalleta yace "kin sanar dasu gobe bazaki samu zuwa ba?"
Kai ta girgiza tace "zanje"
Wani kallo ya mata yace "a hakan?"
Tace "eh ai zama zanyi ba yawo ba."
Ban yaddaba ba inda zaki cikin yanayin nan.
Hankalinta a tashe ta kalleshi tace "wani yanayi?"
Kallanta yai yanda take toshe hanci ya kalli abincin, ido ta zaro da sauri ta sauke hannunta tana neman sake ci, sai dai kamshin sam ya hanata.
Mikewa tai idanunta sun yi rau rau tace "Allah zan iya."
Kallanta yai yace "wai ina zaki a haka?"
Shiru tai jin kamshin na hawa kanta yasa ta bar dakin da sauri.
********
Tun a falo tai bacci tana kwance suna Nabila na kallo har bacci yai gaba da ita.
Ganin goma tayi bata shigo ba yasa ya fito falo ganinta a kwance tana bacci yasa ya kalli su Nabila yace "yaushe tai bacci?"
Nusaiba tace "tun 9"
Karasowa yai, tabata yadanyi sau dai bacci take sosai ga baccin dama a wahale tayishi saboda yunwa.
Kallansu hai sannan ya daure kawai ya dauketa yai ciki da ita, Nabila da Nusaiba suka saki baki har ya rufo kofar.
Kwantar da ita yai ya zuba mata ido yana kallan yanda fuskarta tai fayau duk ta fada kwana biyu kacal? Haka abin yake?
******
Alarm dinta ne yai kara 5:30am sam ta manta bata canza ba, mikewa tai ta zauna tare da haska fitilar wayarta.
Khalid tadan haska wanda ke bacci ta dan haska dakin kafin ta fara kokarin saukowa daga kan gadan.
Jitai an rike hannunta.
Kallan Khalid tai yace "bafa zaki aiki a haka ba."
Tace "Sweet Allah in naje zanfi warewa ma."
A'a in naga kin ware sosai gobe kyaje.
Inada meeting 11 bazanyi zirga zirgaba sannan daga naji abin yamin yawa zan dawo gida.
Kallanta yai sannan ya saki hannunta tare da gyara kwanciyarsa.
Komawa tai ta kwanta tana kallan saitinsa tace "kaji?"
Yace "me kikeso nace kuma?"
Tace "naji zan dawo bayan azahar, kaji?"
Kallanta yai kamar zai hanata sai kuma yai tunanin kila ta fi warewa in ta fita dan rungumeta yace "Thanks."
Kwanciyarta tadan gyara kadan tai tace "Sweet na fara tsoron harkar nan, ban dauka abin haka yake ba."
Yace "insha Allahu komai zaiyi sauki."
Murmushi tai kafi ta mike.
Wanka tai dakyar ta fito sannan ya shiga.
Duk abinda takeyi idanunsa na kanta, haka ta shirya tace "break fa?"
Yace "tea da bread kawai zansha." Tasan saboda ya rage mata aiki ne, sannan yana san ganin ko tana da karfin yin aikin.
Dan ya yarda ta warke din yasa ta daure ta ware sosai tai kitchen ta hado mai, amsa yai yana sha yana kallanta.
Sai daya gama yace "kefa?"
Gudun magana yasa tadan sa bread a bakinta, yace "haka zakici?"
Tace "kaima kasha da ruwa ai farkon auranmu."
Murmhshi yai haka tadan ci kadan tai sa'a bataji ya dawo mata sannan lafiya kalau tadanci.
Sai data gama sannan suka fito tare.
Duk yanda baisan shiga motar yaukam bai isa ba saboda yanayin jikinta.
Sauketa yai ya kalleta yace "zanzo na maidake lokacin lunch."
Kai ta daga sannan ta fito, harta shiga yana kallanta kafin ya juya.
********
Zuwan Asiya ba karamin taimaka wa yai ba dan ta iya abubuwan gargajiya wanda hakan yasa Zainab ta samu kwanciyar hankali take cin abinci.
Shakuwa sosai ce ta shiga tsakanin yan matan uku, duk da su biyun sun fiya magana ba kamar Asiya ba wacce magana bata dameta ba sai dai tunda ta hadu dasu ta kasa daina dariya, sosai fadansu ke birgeta ga suyi ta sata cikin fadan kowa nasan ta tare mai.
Khalid na zaune yna waya da Salmanu yace "ba dai cemin zakai ba saboda ni ka kira wayar nan ba?"
Salmanu yai dariya yace "nifa bansan fassara dan kawai nace ya kanwarmu?"
Yace "kadai san bazaka aikeni na kai mata wayar ba ko?"
Dariya Salmanu yai yace "wannan yaya akwai tsauri an hanata waya ance sai ta gama secondary yanzu ka kai mata wayar ma kace bazakai ba?"
Dariya Khalid yai yace "in dai taimaka ma."
Zainab dake kwance yana murmushi, falo ya fito yace "Asiya."
Asiya dake kitchen ta fito da sauri waya ya mika mata ya koma ciki.
Mamaki ne ya kamata ta sa a kunnenta.
Salmanu yace "kanwarmu ashe kin gudu ba sallama."
Nabila ce ta kara kunnenta a jikin wayar Nusaiba ma ta matso hakan yasa Asiya kunya ta shige daki da gudu.
*****
Sosai wannan hutun ya musu dadi Khalid da Zainab sunji dadin zuwansu dan gidan yayi albarka anji dadin zumuncin nan dan ma Zainab nata fama ga Khalid ya sa mata doka 2 take dawowa dole, sai dai hakan ba karamin taimaka mata yake ba saboda tana samu ta huta sosai.
Haka har lafiyarta ta karu, hutu kuma ya kare, dan ma jarabawa zasuyi in suka koma shine karshen term dinsu.
Ganin wahalar da takesha yasa Khalid ya biyama Asiya kudin Waec da Neco a private anan skul din dake kasan layinsu ta dawo nan, kafin ta fita takeyin komai wanda hakan ya sa hankalin Dady kwanciya yai tama Khalid godiya.
********
Mahaifin Xoxo da Allah yamai Rasuwa Allah ya jikansa da Rahama, ragowar musulmai da suka rasu Allah ya jikansu馃憦馃徎
*****
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
[1/23, 2:26 PM] Zuraiyah Zuzu 馃専: 馃崁A GIDANA馃崁
.........................
*H虧a虧s虧k虧e虧 W虧r虧i虧t虧e虧r虧s虧 A虧s虧s虧o虧c虧i虧a虧t虧i虧o虧n虧*
*Wattpad :-AyusherMohd*
聽聽 Wattpad link馃憠馃徎聽 https://my.w.tt/FKRWfhajS1
*艐膮 A虉踏蕪蕣謫搔蓻蕗 蕧蕣搔蓶馃弻馃徎鈥嶁檧*
#OneLove鉂�
{71}
Rayuwa ta ratsa yau da dadi gobe babu a haka cikin Zainab yakai wata takwas wanda daga lokacin dole ta hakura da fita aiki sai dai tai a gida ta tura, da kanta ta sanar da Khalid akan yama Salmanu magana ta samar mai aiki a gun aikinta, shikam cikin murna ya amince da hakan.
Dady kam zumudin jika ya sa kusan kullum sai ya kira, daga kano kuwa Aunty duk bayan sati daya zuwa biyu sai tazo ganinta.
Saboda kammala makarantar dasu Nabila sukai Dady ya turota amma ita kadai saboda yana ganin ba dadi a dinga sa Khalid barin gidanshi saboda su, inyaso in Nabila ta dawo sai itama taje, dayake Asiya ta koma tunda jikin Zainab yai sauki sannan kuma ta kammala jarabawarta.
Nabila sosai take kula da Zainab, a koda yaushe mamakin halayen yayarta takeyi gaba daya yanzu ta canza tun balle akan mijinta a koda yaushe cikin maganarshi take abin na ba Nabila dariya, in ta shiga daki ta kira Nusaiba tana mata gulma, bata damu da saurayi ba sai dai ganin yanda Auntynta ke canza yasa ta fara tunani kula samarin dake santa.
*******
Adam ne ya kalli Raziya dake neman komawa ciki yace "tafiya zakiyi?"
Tace "me zan ma to?"
Murmushi yadanyi yace "magana zamuyi."
Kallansa tai tace "bana san jin shirmenka."
Dan dariya yai yace "Maganar ki ce da abokina Kamal na miki maganarshi kwanaki."
Wani banzan kallo tamai tace "nacema neman kai nake da kaina?"
Bakicemin ba amma haka zaki cigaba da zama?
Kai haka zaka cigaba da zama?
Dariya yai yace "haka nace miki?"
Dan kai ta karkartara tace "kaje kai naka auran ka bar damuwa da auran wadanda bakada alaka dasu."
Ta nufi kofa jitai yace "Raziyya."
Yanda ya kirata ne yasa jikinta yai sanyi, juyowa tai ta kalleshi yace "laifin danama Fiddausi za'a ban dama na wankeshi?"
Kallansa tai yace "me kike tunani game dani?"
Kai? Ta tambaya tana kallansa.
Yace "eh ki amince dani."
Idanu ta zaro tana kallansa, tace "ni?"
Kai ya daga, da sauri ta shige cikin gida tana maimaita maganar sa.
Sau biyu yana dawowa kafin ta amince dashi dan Baba ya amince.
Sai da akasa rana sannan ya ma Khalid magana ya fadawa Zainab ta sanarwa Dady, Khalid yaji dadi sosai jin zai auri Raziya.
Adam kam rayuwa ta canza shi duk da ba babban aiki bane amma a kalla yana iya kula dasu, har dan mashin dinsa ya siya.
Goggo kam taso dawowa birni amma Adam ya hanata yace ta zauna acan ta cigaba da sana'ar man gyada sai dai yana bata kudi iya kokarinsa, haka nan ta hakura wani sa'in in taji yara sun dawo daga gidan kallo sai taji kamar tai ihu ta shiga cikinsu suje tare.
Amma tsoron zagin da za'a mata a kauye yasa dole ta hakura, sai kokarin bada labarin fina finan data kalla a gidan Zainab.
Abin mamaki ma da sam bata manta su ba, dayawa suna kanta in ta fara labari kai kace ita ta tsara ma masu shiryawan.
*********
Sai cika take tana batsewa a cikin daki, Ayaan dake kwance a kan gado ta kalla yanata baccinsa, agoggo ta kalla sannan ta mike ta fito daga dakin.
Nusaiba dake zaune wace tazo da suna tana zaune a kasan carpet tana ya kallan hotunan suna tana ta murmushi ita kadai, ganin yanda Mumynta suka tsaya tare da Zainab aka musu hoto duk da Zainab ta dan kaude kai saboda bata san yi amma itakam dadin hoton.
Zama tai kusa da ita tana kallo itama.
Kallan Nusaiba tai tace "Nusaiba zama haka ba dadi ko?"
Tace "ba dai kamar da Nabila ba amma ai ina dan shiga makota."
Shiru Zainab tai kafin tace "in an barmiki Ayaan zaki iya zama dashi?"
Zaki wani gun ne?
Aiki na, sam aiki a gidan nan hankalina bai kwanciya.
Dariya Nusaiba tai tace "Ya Khalid zai barki?"
Shiru tadanyi sannan ta mike tai kitchen, tsumi tasha sannan ta dan dama na sha da madara.
Daki ta shiga ta bude wardrobe ta dauko riga wata yar karama ta saka, ta dameta sosai tasa skirts three quarter.
Tayi kyau sosai, turaren farar humra ta dauko ta shafa a jikinta, murmushi tai saboda tare da fatan yin sa'a a abinda take shirin nema.
Karfe biyar da rabi ya dawo, yar karamar mota toyota daya siya ya shigo da ita sannan ya shiga ciki.
Nusaiba na kitchen tana abincin dare hakan yasa ba kowa a falan, sai kuka Ayaan dayaji.
Da sauri yai daki, tana zaune tana bashi mama.
Maida kofar yai ya rufe yana murmushi, kallansa tai tace "sannu da zuwa."
Hanayensa ya harde yace "na dauka kina aiki bakiji kukanshi ba." Ya karasa kusa da ita tare da kallan Ayaan.
Murmushi yai sannan ya karbeshi, mikewa tai ta karbeshi, kallanta yai cikin rada tace "bari in kaima Nusaiba shi."
Kaya ya fara cirewa ita kuma ta fito dashi.
Nusaiba ta goyama a baya sannan ta koma daki, zanin data daura saman skirt dinta ta zare.
Kallanta yai yana zaune akan gado da vest da karamin wando yana san shiga wanka, karasowa tai kusa dashi yace "Are you trying to seduce me?"
"eh" tace tare da zama kusa dashi, murmushi yai yace "ahhhh." Ya fada yana kara kallan ta daga sama har kasa.
"Meye na fada tunda ka sani?"
Ohhh sry na janye.
Yai maganar yana jawota jikinsa, dan hannunta ta kwace alamar dan karamun fushi.
Jawota yai yana dariya yace "a ina kika iya fushi haka?"
A gunka?
Dariya yai yace "ni?"
Tace "eh malamin hade rai." Tunawa tai da abinda tazo yi hakan yasa ta dan kwanta a jikinshi.
Dagowa tai ta sa hannu saman fuskarsa tana dan taba labansa a hankali.
Jawota yai sosai ta fado kanshi baya yai wanda hakan yasa ta fada samansa a hankali ta sa bakinta cikin nashi...........
Kwanciya tai akan kirjinsa tace "Sweet me kake gani in na koma aiki nextweek?"
Murmushi yai dan yana ganinta jikinsa ya bashi abinda take so.
Yace "yanzu ke zaki iya fita aiki ki bar Ayaan?"
Tace "ba dadewa zan dingayi ba, in naje 10am zan dawo 2pm."
Zaki iya?
Ta kalleshi da sauri tace "eh."
Fuska ya daure tare dacewa "ni me kika fi so ne a rayuwarki?"
Kallansa tai tace "so kake nace kai?"
Laifine in naso hakan?
Murmushi tai tana cewa "in kuma nace aikina fa?"
Wani kallo ya mata dariyarta ta guntse tace "ni Sweet kishi kake da aikina?"
Mikewa ya shiga neman yi ta danne shi tana dariya tace "wasa nake, kaima kasan nafisanku kai da Ayaan ai wancan na saba ne ga hankalina ya kasa kwanciya gani nake kamar zasu lalata min komai in bana kusa."
Kai ya daga alamar gamsuwa yace "hakan yayi"
Tace "zaka dawo can muyi aikin tare?"
Murmushi yai yace " Maman Baby magrib zatai"
Dagashi tai yana shirin mikewa tace "Sweet ka kaini toilet please."
Kallanta yai yana dariya yace "in kira Ayaan ya kaiki babanshi bashida karfi."
Haushi ne ya kamata taja pillow din dake gefenta ta cilomai, cafewa yai sannan ya cila mata, makuwa yai akan fuskarta hakan yasa tai kara tare da rike gefen idanta.
Idona.
Hankalin Khalid ne ya tashi ya matsa kusa da ita yace "idanki?"
Mikewa zaune tai tana shishitun jin zafi, muga?
Ya fada yana neman zare hannunta.
Dariya ta kwashe mai dashi tare da zare hannunta.
Wow yaushe kika fara fooling dina?
Dan harshenta ta fito dashi kadan tace "yanzu? Dazu? I can't tell."
Mikewa yai kawai yana murmushi ya shiga toilet.
*******
Ayaan ne yake ta kuka da daddare mikewa tai tana jijigashi, in ta kalli Khalid na bacci sai taji kamar ta tasheshi, wai komai na yaro ita zatai? Falo ta fito tana jijigashi
(Nace Hajiya Baby maman Baby haka abin yake馃ゴ)
Haka taita jijigashi harya koma bacci komawa daki tai, dan ido ya bude kadan yace "Ayaan ne?"
Eh tace sannan ta kwantar dashi, kwanciya tai bacci ya dauketa.
Tana sallar asuba ta shiga kitchen, dankali ta fere tana yi tana hamma, tana soyawa tana kare wanke ragowar kwanukan da tai amfani dasu.
Falo ta fito ta ajiye tana tunanin yanda zatai in Nusaiba ta tafi tunda skul ake nemar musu da zaran sun samu zasu bar nan.
Tana shiga dakin taga Ayaan a hannun Khalid da alama ya tashi.
Zama tai kusa dashi tana sake yin hamma kallanta yai yace "jiya bakiyi bacci sosai bane?"
Tace "Ayaan ne yai ta farkawa, kai kuma kana kwance kanata bacci."
"Sorry nadaiji shi kamar cikin bacci."
"Ahhh maza kuna samun sauki mu haihu sannan kula da yaro duk mune."
Haccin Ayaan yadan taba yace "ai shiyasa aka kiraku Uwa aka kiraku mata."
Mikewa yai yana shiryawa, yana gamawa ya fito falo ta biyoshi dauke da Ayaan a kafadarta tace "In na dawo daga gun aiki Aunty zata dan zo."
Kice baki za'ai akwai abinda kike bukata?
Tace "in akwai zan aiki Nusaiba kasan layi."
Wallet dinsa ya zaro ya ciro 1000 ya ajiye kusa da ita.
Kallan kudin tai kamar tace ya barshi sai dai tasan ransa ne zai baci amma itakam gaba daya ta rasa me zatai gata da kudi ga yanzu kudinta sai karuwa suke amma sam bata isa yin wani abu na gida ba, sai dai kamar kayanta na sawa tana siyo lokaci lokaci duk shima yana siyo mata, hakan yasa tai shawara da Khalid ta fara kai sadaka masallatai da gidan marayu.
**********
Rayuwa ta ratsa, yau da gobe sai Allah, yanzu shekarar Zainab da Khalid biyar da aure, a wannan lokacin abubuwa da yawa sun canza.
Ciki harda auran Asiya da Salmanu da akai shekaru uku da suka wuce, auren Adam da Raziya suma a shekara ukun da ta wuce da yanzu Raziya harda tsohon cikinta.
Adam kam Alhamdulila an dage ko dayake dole ma ya dage dan Raziya bata mai da sauki sam, daga taga yana neman biya abokai zaman majalisa zata tsawatar mai hakan yasa tun yana yi lokaci lokaci yanzu ya daina.
Kallan Adam tai yauma bayan ya dawo daga gun aiki tana mai kallon tuhuma, dariya yai yace "Allah ba inda na tsaya."
Hannunsa ta rike tace "ba cewa nai ka tsaya ba."
Zama yai a dan falan nasu ya dan daga labulen dakin ganin dan karamin dakin dake waje kusa da kitchen a bude, kallansa tai tace "Goggo!"
Tadan kwala mata kira.
Goggo ce ta fito daga dakin, kallansa tai tace "Adam an dawo?"
Ciki mamaki ya kalli Raziyya.
Murmushi tamai tace "kaga na kusa haihuwa ba babba a gidan shiyasa na kirata a waya"
Goggo ya kalla wace duk girma ya kara hawanta, yace "Allah yasa ba sa tv a gaba zakiyi kina kallo har ta haihu a bandaki ba?"
Dariya Goggo tai zatai magana Raziyya tace "ai tana ma daki nan ba koda yaushe zata dinga shigowa ba."
Yawon bakinta Goggo ta hadiya tace "Uhmm"
Raziya ta sake kallo wannan kam sai na lalabata in ba so nake na koma kauye ba.
*******
Karfe biyar saura ta mike ta wuce kitchen tasa abinci, dawowa tai toilet din falo tai wanka sannan ta shiga dakinsu Ayaan da Ayra ta daga Ayaan dake baci ta shiga dashi toilet ta mai wanka sannan ta fito ta tashi Ayra.
Tana fitowa ta wuce dakinsu, Khalid ke shafa musu mai yana sama Ayaan kaya lokacin.
Ayra ta ajiye ta fito kitchen.
Ayra yar shekara biyu ce ta kalli dake shafa mata mai tana zilewa.
Khalid yana dariya yace "Ayra tsaya lokaci na tafiya."
Ayaan ta kalleshi cikin yanayin shagwaba tace "School nake so nima."
Ayaan ne ya mata gwalo yace "ke yarinyace gidan Aunty zaki sai kin kara girma."
Haushi ya kamata, Zainab ce ta dawo dakin ta kalli Ayaan tace "a wuce a ci abinci"
Ayra tasa kuka tace "nima Mumy school nake so."
Naji aje aci abinci.
Fita tai a bakin madubi tana shafa mai tace "Na tambayi school din Ayra jiya sunce zata fara next term."
Necktie dinsa yake sawa yace "shikenan Allah ya kaimu."
Tace "in kawo abincin nan?"
Yace "a'a gama mu fita."
Kallansa tai sannan tadan sumbaci kumcinsa tace "yaushe raban da mu gana?"
Yace "bansan haka abin yake in da yara ba, gaki kullum kin gaji baccin wuri rannan da na tasheku tsakar dare haka kika wuni kina hamma."
Ajiyar zuciya tai tace "mu dinga sasu bacci da wuri?"
Murmushi yai yace "Kin kawo shawara."
Dariya tai ta gama sa kaya suka fito falo.
Khalid ne ya fara cin abincinsa itakam dan dankalin kadan taci tasha tea.
Mikewa tai ta koma daki ta sharo, tana fitowa falo suna gama cin abincin.
Ummy na a wuce asa takalmi.
Ayra tace to.
Fitowa sukai suka Ayra ta shiga motar Zainab shikuma Ayaan ya shiga motar Khalid suka fito daga gidan.
Gidan Asiya tai parking, tana kwankwasawa Asiya ta fito sanye da hijab, Ayra ta tafi da gudu ta rungumeta.
Zainab tace "Asiya sai na dawo."
To Aunty.
Ayra ta kallantace "baki tambayeni kawarki ba?"
Ayra tana dariya cikin maganar suka shiga ciki.
Zainab na isa office dinta Ramlatu ta shigo dauke da uban takardu, ajiyewa tai a gabanta tace "Hajiya ga su na duduba."
Kallansu tai tace "good yanzu, ina Nazifi yake da Salmanu? Su duba gun exams din yanda baza'a samu matsala ba"
Tace "okay na sanarma securities din suma.
Kai ta jinjina tace "well done."
Sakone y shigo wayara.
Zainab dan Allah ki dubi girman Allah d'ana zaizo yin jarabawa karki duba abinda na miki ki koreshi, dan Allah, wallahi rayuwa ta juya mana dakyar na samu ya gama karatu.
Kabir
Kallan Ramlatu tai bayan ta kira number tace "ki samar dashi nafi karfin na hukunta wani saboda laifin mahaifinsa."
Ramlatu ta amsa jin muryar Kabir ta sanar dashi, ya shiga godiya.
Ajiye wayar tai sannan ta juya.
Zainab ta kalleta dan sosai Ramlatu ta shiga hankalinta taba aikinta mahimmaci da rayuwarta.
*******
Khalid na isa makarantar ya riko hannun Ayaan yaji ance "Khalid?"
Juyowa yai Afreey ce ta karaso tace "ikon Allah ashe kai din ne."
Afreey ce ta dan karaso tana kallan Ayaan wanda ke tsananin kama da Khalid.
Murmushi tama yaran, Khalid ya kalleta yace "Safiya."
Tace "ban taba tunanin zan ganka ba."
Murmushi yai yace "Ayaan a wuce ciki, ya fada yana duba agoggon hannunsa, ganin bakwai da ashirin yasa yace "Wani kika kawo?"
Tace "eh yarinyata."
Masha Allah, Allah ya rayata.
Ya fada tare da bude mota.
Kallansa tai tace "aiki?"
Eh.
Murmushi tai tace "Allah ya taimaka yace Ameen."
Mota ya shiga ta kalli motarshi sannan ta shiga katuwar motarta ta bar gun.
Yana fitowa lokacin lunch ya kira Dady ganin missed call.
Basma ce ta dauka bayan sun gaisa tace "Khalid jikin nashi me yadan tashi dama shine zan fadama."
Inalilahi sosai ne?
Tace "a'a kawai dai in da hali dan Allah da weekend kuzo kila inyaga su Ayaan yadan ware."
Ok insha Allah
******
Alhamdulila
Godiya mai tarin yawa gareku masoyana da masoyan wannan littafi, hakkika ima godiya kwarai ga dumbin kaunar da kuka nuna mai.
Nagode kwarai da gaske馃
Godiya ta musamman gareku masoyana na wattpad masu bin wannan novel馃
Yan
The Queen Bee
Haske Writer's
Zauren Biebie
Ayusher Fan Club
A Gidana Novel
A Gidana Fans
Masarautar BillynAbdul
Kundin Haske
Zauren Khadeeja Candy
Huguma Conversation Centre
Unity Girls (Sauyi 馃グ)
Nagode kwarai ga duk wanda yabi novel din nan da wanda na sani da wanda ban sani.
I wish i can write those names whom always make a long comment on each page馃na sani kun sani ina godiya kwarai da gaske馃
Kuskuren da ke ciki Allah ya yafe mana wanda muka fada dai dai Allah ya bamu ladansa
Much Love 馃挄
*****
Ayusher馃弻馃徎鈥嶁檧
*******
*****