Babson! Hanny tace "friends Babson ne, wallahi shine" Babson na jin haka yayi gefe ze wuce Hanny ta jawo Hanun shi kafun yayi magana Hanny ta d'aukeshi da mari tau.......tau har guda biyu ta rufeshi da duka tana cewa " macuci,mayaudari mugu wallahi se Allah ya sakamun Hassy me kuke jira?" Su Hassy suka zo suka rufe Babson da duka kota ina nan da nan mutane suka taru kowa na fad'in albarkacin bakinshi wani tsoho yace "y'an mata meyayi muku haka kuke masa wanan duka?" Hassy tace "Baba wanan mayaudarine ka barmu da shi kawai" ta juya ta d'auke Babson da mari haka suke dukanshi su kai masa jina jina da k'yar wani mutun ya k'wace shi ya fada Motan shi aguje ya tafi a 360 su Hassy suka dunga jifan motan Hanny tana kuka tana cewa"Babson insha Allah se anyima d'iyar ka abun da kaimun banza mayaudari kawai ".
Meena CE ta rik'e Hanny tana bata hak'uri suka hau sahu suka tafi .
Suna zuwa gida Hanny ta fad'a d'aki tana kuka tana surutai ita kadai " Babson ka cuceni ka ra bani da budurcina Allah ya saka mun .
Biki saura Sati d'aya su hassy se shirye shirye akeyi basu nan basu can Hanny tece "Hassy muje gida kinga Deen se kirana ya ke yana jirana agida kinsan yau ya dawo, so sati d'aya kenan bamu hadu ba?" Hassy tace " muje don kar yayi ta jiranki" tana zuwa gida ta tarar da Deen a zaune a saman motanshi ta zagaya ta baya tace"Amincin Allah ya tabata agareka ya masoyina "Deen ya sauko yace " tare da ke amarya ta " hmmm tun ma ban zamaba "Deen yace" saura kwana 7 kinzam tawa na zama naki habibty".
Deen yace "Habibty kinsan wani Abu?wallahi wani Abu ne ya b'atamun rai yau wata yarinyan mak'otan mune tai ciki ,kinsan meye?" Hanny tace "seka fad'a" yace"da k'anwa tace wallahi Allah kadai yasan me zan yi mata hmmmmmm "........ Nan fa cikin Hanny yabada kuluuuuuuuuuuuuuuuu.........nan tsoro yak'ara kamata Ahaka dai ta daure ta na masa dariyan da be kai cikiba har suka gama firansu ya wuce.
Tana shiga tace " Hassy na Shiga uku wallahi Deen ya tsana yarinyan data zubar da budurcinta a titi ya zanyi Hassy?ko dai nafasa aure nan ne?" Hassy tace "a a Hanny ba zeyiwu Allah ya rufa miki asiri ke kice zaki tonawa kankiba ,muje Akwai wata hajiya Landi me kayan mata za muje ta hadaki insha Allah Deen baze ganeba".
Niko nace (wane ke Hassy ai abunda ya tafi baze dawoba)😂
Hajiya Landi ta had'a mata kaya tare da bata shawar wari suka biya kud'i suka wuce Hanny tana ta shan magani duk don ta matse kar Deen ya gane.
Biki yayi biki yau ake kamun Hanny beelaza faces 👸🏻aka kira ta canza ma Hanny kamani ta dawo kamar sabuwar balarabiya ni kai na ban gane Hanny ba sei da naji tace " Minash karfa idonki ya fad'o "da sauri na kawar da kaina don kunya🙈.
Hall ya cika kota ina mutane ne nan na hango su Hassy sunci anko dasu Meena ni kaina saida naje su hassy anyi rawa an cashe 💃💃💃💃se da nace Meena karfa ki b'ale naga se juyi kikeyi.
K'arshen tuka tika tik! Hanny ce keta kuka za'a kaita Ummah ce ta dafa mata kai tace" Hannatu Allah ya bada sa'an shiga ki ta hak'uri domin hak'uri shine jigon zaman aure da rayuwa ma baki d'aya "ta rungume Hanny ta je ta sakata amota akatafi .
Wow haka naji mutane nata yaba kyan gidan Hanny dake hotoro kowa ya watse anbar Hanny se kuka ta keyi tana fargaban idan Deen yasan cewa ita ba virgin bace ya zeyi tayi nisa atunani seji tai an daga mata mayafi da sauri tad'ago don taga waye se taga Deen yana mata murmushi nan itama ta mayar mai da murmushin da bekai zuciya ba saboda tsoro da fargaba.
Kamo hanunta yayi yana yaba zanen lalen da akai mata yace" Habibty godiya ya tabata ga Allah subhanahu wata'allah da ya malakamun ke amtsayin matata "Hanny tai murmushi Deen ya d'aga mata mayafi yana yaba k'an datayi ya jawota jikinshi nan yashiga kissen dinta kota ina yana shafata yana wani irin nishi Hanny ko se kuka ta keyi tana fargaban abundan ze faru da k'ar ta k'waci kanta tace " Deen bamuyi sallah ba? please. tashi kai sallah? "Yace " kefa?" Hanny ta sunkuyar da kai tace"ina Hutu sallah se nan da kwana uku "nan fa Deen yaji duk jikinshi yayi sanyi ammah haka ya daure yayi sallah yazo ya kwanta ya jawo Hanny jikinshi yana shak'an dadad'an k'amshin jikinta ahaka bacci yayi gaba da su.(asuba ta gari Ango da amarya)
Yau kwanan Hanny uku Deen se rawan jiki yake yau Hanny zata gama nanko be San Hanny k'arya taimashi don tsoron abunda ze faru idan ya. gane cewa ita ba virgin bace ba.
Wurin k'arfe 8na dare Deen ya shigo yana mai farincikin yau ze zama cikaken Ango nan ya zauna ya cika cikinshi da abincin da Hanny ta mai, ya gama suka gabatar da nafila raka'a biyu tun a kan darduma Deen ya fara ma Hanny wasani yana shafata yanabin ko ina na jikinta da kiss Hanny gabanta se faduwa ya keyi tana hawaye Amman INA shi ogan ma be San tana yiba ya dauketa cak ya koma kan gado da ita seda yayi nasaran raba hanny da kayan jikinta...........da sauri najawo musu k'ofa na koma fallo nan Nima bacci ya daukeni.
Kaman a mafarkina naji ana cewa"kin cuceni! Kin cuceni..............
[10:56PM, 8/13/2017] +234 806 677 6651: *A SANADIN 🙆 TSARABA🙆*
*Written by*
🖊🖊 *Minash*💝💝
*DEDICTED 2 ALL MY FANS nagode da adua'arku gareni Allah ya bar k'ak'auna*
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*we don't just entertain and educated we touch the heart❤of the readers*
P.M.L
🔚
PAGE 40-50
"Kin cuceni Habibty, meyasa zaki mun haka?Ku mata duka haka kuke ne? Atuna nina na samu kamilar mace me tarbiya ammah se inga akasin haka"
Hanny tace "wallahi Deen ba laifina bane" Deen yace ki mun shiru baki da abun da zaki fad'a mun cuta dai kin riga kin cuceni kuma wallahi zakisan Ni kika ha inta"yafita ya bar Hanny tana kuka da dana sani tana cewa"oh Ni Hannatu *A SANADIN TSARABA*na jawa kaina Allah ya isa tsakanina da kai Babson Allah ya bimun hak'ina"nan Hanny taci kukanta har asuba sanan tayi wanka tana idar da sallah ta shiga kitchen ta had'a ma angonta break fast 8dai dai ta gama kamshi duk ya cika gidan .ta koma d'aki tayi wanka ta tsara kwaliya da wani Riga da wando. iya cinyarta rigar ta kai wandon kuma dogone har k'afanta ta zo fallo tana jiran angonta ya fito ammah har 10 bai fitoba nan baci ya kwasheta don jiya bata samu barci da ya waba.
10:30 Deen ya fito k'amshi duk ya cika mai hanci yana juyowa yaga Hanny se bacci take a nutse, ya dad'e yana kalanta saboda shi kanshi tayi masa kyau ammah haka ya share ya wuce ta.
Ahaka kullum Hanny take, ammah Deen ko kulata bayayi ya daina cin abincinta yadaina kwana tare da ita gaisuwanta kawai yake amsawa, shima se ya gadama ya fad'a mata kuma nanda lokaci kad'an ze auro zankad'ediyar budurwa Hanny banda kuka da danasani kullum bata da abunyi se shi.ahak har sukai wata d'aya ahaka.
Hanny ta rame tayi bak'i saboda damuwan abun da angonta yake mata gashi takasa fad'awa kowa don gudun tonuwan asirinta.
Yaune su Hassy zasu kawowa Hanny ziyara don dama sunce setayi wata d'aya zasu je don taci amarcinta da kyau.
11:00 yayima su Meena agidan Hanny suna shiga suka tarar da Hanny zaune tana Kalo fuskanta fayau ba kwaliya se fowder data saka jalabiyace ajikinta tasa shine saboda bataso su Hassy su gane ramar datayi .
Hassy tace"wow Hanny ba dai har kin kamuba?don naga kinyi baki" meena tace dama ko kinsan wasu bak'i sukeyi, wasu kuma haske"teema tace "wasu kuma kiga sunyi k'iba" Hanny se dariyar yak'e take musu tace "Ku wallahi Baku da kiriki daga zuwa se sa ido".
Hassy tace" ba dai Deen na nanba?kika samu muketa surutu"Hassy narufe baki Sega Deen ya shigo ya shigo da dariyarsa saboda yaga takalma daga waje yace "a a yau manyan bak'ine agidan namu " yana fad'a yana murmushi Hanny kam se yak'en dole takeyi don kar su Hassy su gane irin zaman da suke yi.
Ya zo kusa da Hanny ya zauna ya rungumota jikinshi kad'an yana cewa "habibty yau ba ma d'an tarban da akemun Dan anga su Hassy an manta dani" ita ko Hanny murmushi tayi tace"a a kunyan su Teema nakeji "a a wallahi mu ba ruwanmu kijidai da gulmarki " inji Meena.
Hanny ce tafara tari ahnkali tana rufe hanci saboda k'amshin turaren Deen dataji yana son sata amai.
cikin alamar rudewa Deen yake mata sanu yana dad'a jawota cikinshi aguje Hanny tayi band'aki tana amai kaman hanjin cikinta zefita nanfa Deen ya rud'e dasu Meena suna ta mata sanu "
Deen ya rad'a mata akune yace" ko aman jini zakiyi ba zan fasa auro zankad'ediyar budurwa ba"se ji sukai luuuuuuuuu Hanny ta yanke jiki Zata fad'i cikin sauri Deen ya tarota ta fad'a jikinshi yace" Hassy kawo ruwa please da Sauri " Hassy saboda rud'ewa takasa kawo ruwan Deen jin Hassy shiru yasa yayi waje da Hanny yasata cikin mota ya fita a 360 sukai asibiti mafi kusa .
Ya na isa aka amshe Hanny akafara bata taimakon gagawa cikin minti 10 ta farfad'o akasamata ruwa tare da d'iban urine dinta akatafi lab da shi .
Doctor na fitowa yacewa Deen"ka biyoni office"da Sauri Deen ya bishi domin ya rude don har yanzu San Hanny nan aranshi duda rashin kawo budurcinta da bata yiba daurewa kawai ya keyi yana shareta saboda ya bak'anta mata kaman yanda ta bak'antamai .likita yace"Kaine mijinta?"Deen yace"eh nine Doctor" yace "meyasa kake barin matanka cikin damuwa? Gashi saboda yawan tunanin da takeyi yana nema ya haifar mata da ciwon zuciya",likita yayi ta masa fad'a da nasiha nan Deen yace" insha Allah likita za'a kiyaye " nos ce ta shigo tare da result d'in test din da tayi taba likita ya bud'e ya d'ago yana murmushi ya mik'ama Deen hanu yace "congratulation madan tana dauke da ciki na kwana 31 " cikin murna Deen ya mik'e yana cewa"nagode likita zan iya ganinta ?" Likita yace "eh nasan yanzu ta farka " da Sauri deen ya fita yayi gurin Hanny.
Yana zuwa ya rungumeta yana cewa" Habibty nagode miki kin sa marmun farin ciki me yauwa na yafemiki saboda wanan d'an nawa dake cikinki yau zan jewa ummah ta da albishir me dad'i ta dad'e tana aduan Allah ya nuns mata ranar daza taga nayi aure tasamu jikokinta yaugashi Allah ya amsa aduanta I LOVE YOU so much Habibty "ya k'ara matseta ajikinshi seji yayi Hanny tace" I love you 2 my husband" ashe tun shigowan shi Hanny tafarka tayi lamo ajikinshi se ji sukai ana tafi suna juyowa su kaga su Hassy dagudu sukaje suka rungume Hanny suna cewa"congratulations friend muntayaki murna "meena tace " muma Allah ya bamu mazaje na gari"Deen yace "Ameen"
Kwanan Hanny biyu aka sala meta sedai d'an laulayi da ba'a rasaba wani sabon tatali Deen yake bata bayabari tayi komai wai kar ta wahalar mai da baby
Ahaka cikin Hanny yayi ta girma tanasamu kulawa daga kowane bangare don kullum in low d'inta seta kawo mata kayan mak'ulashe duk abun da ta keso shi akemata .ahaka har cikinta yashiga wata na Tara.
Yau Hanny ta tashi da ciwon baya ahaka ta dunga daurewa don kada Deen ya fahimta .qarfe 4:00 Hanny taji ciwo yana k'aruwa ta kira Deen a waya cikin minti goma ya iso koda yazo lokacin Hanny tafara galabaita ya dauketa sukai hospital ana zuwa aka shiga da ita labour room cikin minti 20 senaji kukan baby (nace Allah me iko su Hanny ansauka) se ji nayi doctor yana cewa"madam push push akwai saura " nan danan se ga wata baby aka shirya baby's aka shirya Hanny aka kaita d'akin Hutu .murna agurin Deen ba'a magana kafun kace mene asibiti yacika dam da yan uwa .
Hassy ce tace "a a wallahi Hanny kinyi k'ok'ari kinga girman yaran kuwa ?" Hanny tace kema saura kwana nawane ? In cedai nanda sati hudu zamu kaiki? kinga daga anshiga magana ta k'are"
Kwanan Hanny biyu ta dawo gida y'an barka suka cigaba da zuwa har ranar suna idan yara sukaci sunan Abban Hanny da Abban Deen wato Ibrahim da Muhammad zaa dunga kiransu da Hanif da Arif.
Bayan shekara biyu naji Hanny tanacewa"Abban Hanif muje gida hakanan wlh nagaji ga Babynka se damuna yake da motsi"yace "toh muje ammah kitafi ahankali kar ki takurama yarana don nasan wananma biyune " suna fitowa suka shiga mota Hanny ce tace "Abban hanif gawani almajiri can tunda zamu shiga naganshi please bari inbashi sadaka" yace"Hanif kira wancan bawan Allah "yanazuwa Hanny taciro 5k ta bashi yanata godiya har ta rufe mota setaji yanacewa "Hanny Hanny"da sauri Hanny suka juya danganin wanene suna fitowa taji yace" Babson ne Hanny kiyafemun Hanny Na tabatar alhakin kune ya kamani garin yaudaran June na yaudari wata yarinya Ashe tana da k'anjamau yanzu haka ita ta rasu nikuma dangina sun cireni acikinsu kitaimakeni ki yafemun "yana fad'i yana kuka.
Hanny tace" dama nafad'a maka se Allah ya sakamun gashiko sakayata tabaya na tun anan duniya Ammah duk dahaka nayafe maka Allah ya yafe mana baki d'aya "Hanny se kuka tashige mota suna tafiya Deen yace "Habibty kukan me kikeyi?" Hanny tace "INA tuna cewane *A SANADIN TSARABA* ne Da kwad'ayi yasa har Babson ya munhaka😭😭😭😭"yace" ya isa haka komai ya wuce my dear Allah ya kiyaye gaba"tace"Ameen tana dariya" ko kefa Habibty shiyasa nake sonki 😂😂😂😂nima shiyasa nake sonka "inji Hanny seji sukayi su Arif sunce mumy dady muma muna sanku 😂😂💝
*Tamat bi hamdulillah anan na kawo k'ashen litafina,kuskuren da nayi Allah ya yafemun sak'on dana issar Allah ya anfanar damu Ameen👏🏻*
TAKU *💝 MINASH💝*