Ranar da muka koma hutu kuwa munyi farin ciki saboda a class d'aya aka had'e mu, Shamow ya kawo wata Friend d'in shi Nuratu yace "shix my frnd wai tana da sha'awar kasnacewa a cikin mu ne, shine nace zan kawo ta ku gani",
Reesha yace "tou muna da dokoki sai idan ta aminta dasu sannan zata shiga cikin mu"
Da sauri ta d'aga kanta tana kallon shi,
"K'ungiyar mu duk wanda ya shiga cikin ta zai mana alk'awarin bazai tab'a fita ba har sai lokacin da mutun zayyi aure, sannan kuma duk lokacin da muka yanke hukunci a abu babu wanda ya isa yace a'a, zamu ringa tallafawa junan mu idan wani yana buk'atar taimako, idan wani zayyi *BIRTHDAY* dole mu had'a kai mu faranta masa rai, kin yarda?",
"Ehh na yarda wallahi na amince"
"Good, miye Sunanki?",
"Sunana Nuratu Abdullahi",
"Kinyi register daga yanxu kin shiga cikin mu".
Nidai haka nan nake cikin k'ungiyar ba wai dan ina so ba sai dan bana so na b'atawa Afnan rai dan naga itace silar k'ungiyar.
Shamow yaji dad'i sosai yace "tou amma ya kama ta mu canja suna ko?"
"Ehh ya kamata gaskiya" Reeshat ta fad'a.
"Why not mu saka *AREWA STARS?* wato taurarin arewa", Reesha ya bayar da shawara.
Tafa hannu duka mukayi saboda sunan yayi dad'i sosai.
*******
Haka mukaita k'ara yawa har lokacin da muka kai mutun 15, daga nan Reesha yace a rufe shigar da mutane haka nan saboda idan mukayi yawa sosai abun bazayyi dad'i ba za'ayi ta samun sab'ani. Hakan kuwa mukayi bamu k'ara d'aukar kowa ba duk da akwai mutun uku da sukayi requesting amma akayi rejected nasu.
Wata rana English teacher'n mu ya shigo shine first period ya fara lesson mu kuwa muna baya muna meeting akan *Birthday* d'in Iby dake gabatowa, wani taku muka fara jiyowa na takalmi tun daga farkon class, a tare muka d'aga kai mukayi duba ga wata kyakkyawar budurwa sanye da sabbin uniforms d'in ta, skirt d'in ta ko guiwar ta bai rufe ba sai d'an hijabi akan wuyan ta, hannun ta na jan wani d'an trolley bag k'arami irin wanda ake saka littattafan makaranta. Duka hankalin 'yan class d'in ya koma gare ta saboda wani kallon raini da take watsa ma kowa,
Baki ta tab'e tare da zare dark glasses d'in dake idon ta tace "excuse"
Shi kanshi malamin sai da ya tsorata da ita, dan daga ganin wannan ba xatayi kunya ba, nan ta hau yi masa bayani cikin British English nata cewa Principal ya gwada nata nan class d'in yace taxo, sosai turancin yarinyar ya burge shi, take ya gwada mata baya yace ta zauna acan saboda duk gaban a cike yake, bayan kuwa mune kad'ai saboda kowa yana tsoron mu a class d'in yasa babu mai iya tinkarar wurin mu ya zauna.
*Amrah nd Rerbee'art sk novels📚*
[1:08pm, 24/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: [12:31pm, 20/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page 34-35
*We Dedicated this page to ```Pharty KK``` you always pray for me, tanks alot for the caring, Amrah loves youh much😍😍😍*
A yatsine ta ringa kallon mu tana jira mu matsa mata wuri ta zauna, kallon raini mu duka muka bita dashi kamar yanda ita ma shi take mana, har a lokacin English teacher'n mu bai daina kallon ta ba, ganin mun k'i bata wuri yasa yace "hey! Two of you let her sit down mana, shix a new commer fa you have to welcome her",
Da sauri Afnan ta kalle shi tana k'ok'arin yin magana ya d'ora yatsun shi akan lab'b'an sa da nufin baya so tayi magana, gunguni ta hau yi tare da matsawa ta shige jikin Shamow da shima ya kasa kauda kallon shi daga kan Kerry.
Bayyanannen tsaki tayi tare da harar Afnan sannan ta zauna teacher yaci gaba da lesson d'in shi daga inda ya tsaya.
Da mamaki sai ga Kerry ta fiddo iphone 6s+ tana latsa, duk kan mu mun tsorata da ganin wayar saboda zuwan wayar kenan Nigeria, ban tab'a kallon ta a zahiri ba sai yanxu.
Bayan an tashi break fast duk aka fita aka barmu zaune muna ta surutu, itama Kerry d'in bata fita ba sai latsar wayar ta take yi, yaron da muka aika ya siyo mana moi-moi ne ya shigo ya same mu "naje wai yau ba'a kawo moi-moi ba sai dai fried rice" tsawa Reesha ya daka masa tare da fad'in "ba ance daga Crispy ake kawo ta ba? na baka enough money ka hau mashin ka siyo mana mana? Ko so kake har a dawo bamu ci abinci ba?"
Da sauri yaron ya fita dan yana tsananin tsoron Reesha, dama saboda aike yasa aka d'auko masu hayar shi kullun yake zuwa makarantar baban su yana biyan shi albashi duk wata.
har a lokacin Kerry bata daina latsar waya ba, kira ta latsa bayan an d'auka ne tace "mom ba'a kawo min breakfast bafa" a shagwab'ance.
Ban san me aka fad'a ba daga d'aya b'angaren sai naji tace "ok mom am waiting" ta tsinke wayar.
Banda kallon ta babu abunda muke yi, daga ganin yarinyar big gal ce, Afnan dai kallon raini kawai take aika mata, ni kam burge ni ma tayi saboda shix very classic, ga kyau da komai ta had'a.
Kafin d'an aiken mu ya dawo aka kira Kerry a waya ta d'auka "yes" tayi shiru daga nan kafin ta kuma cewa "a kawo min mana ina class, ka tambayi Principal yasan inda ya gwada min na shiga ai, ni bazan iya fitowa ba" ta tsinke wayar taci gaba da latse latsen ta.
Da rawar jiki principal ya shigo hannyn shi rik'e da basket had'ad'd'en gaske, har k'asa ya duk'a sannan ya mik'awa Kerry shi, "keep it there" ta fad'a tare da nuna masa d'an nesa da ita.
Ajiyewa yayi sannan ya fita yana d'an waigen ta.
Da k'arfi muka d'auki shewa muna kallon shi, a kunyace ya fita ba tare daya sake waiwayowa ba.
********
Haka dai mukaci gaba da rayuwa da Kerry ba tare da mun san ko sunan ta ko tasan namu ba, ko k'ala baya had'a mu da ita, babban abunda ya bani mamaki bai wuce yanda take da sharp brain ba, so da yawa idan ana lesson hankalin ta baya ma wurin malamin amma da zarar ya tambaye ta sai ta bashi answer, su kansu malaman suna mamakin k'walwa irin tata. Wani lokacin har Iby yana cewa zayyi mata magana amma sai Afnan ta hana shi.
Gata da yawan waya da maza, kullun aka tashi daga skul sai tayi AP da namiji kuma manyan yara take tarayya dasu.
Da haka har muka kammala SS 1 zamu shiga SS 2, bayan an dawo hutu ne muka fara ganin sauyi daga Kerry, saboda kullun tazo sai ta bimu one by one ta bamu hannu mun gaisa har da su Iby kamar yanda taga muna yi dasu. Wani lokacin har fira take k'ok'arin jana dashi saboda ta kula duk na fisu sauk'in hali.
Bayan sati biyu da dawowa hutu ne ta tare ni wai tana so ta shiga group d'in mu, dana fad'awa su Reesha yace "ai an riga da an rufe shiga k'ungiyar mu, wasu ma suna so amma mun hana su shiga" Iby ya katse shi da cewa "kai guy yarinyar nan fa big gal ce, wallahi tunda ta yarda duk wani jiji da kanta ta nemi mu saka ta is good kawai a saka ta d'in, sauran wanda suka nema mutun hud'u ne ko uku suma sai a saka su, kaga mun cika 20 kenan daga nan sai mu rufe d'aukar kowa, koya kuka ce?"
Mu duka muka had'a baki mukace "hakan yayi"
Reesha yace "to shikenan ayi hakan"
Washe gari na shaida ma Kerry komai, taji dad'i sosai ta kuma bayyana min hakan, bayan anyi break tayi introducing kanta a wurin mu muma muka mata namu, tun daga nan ta shiga cikin mu har ya zamo kamar ma itake leading namu, har Reesha sai abunda Kerry ta fad'a yake ji saboda kusan komai itace take mana, idan wani party za'ayi itake d'aukar nauyin komai na party'n, ko abinci muka daina siye sai ita take siya mana.
Wani lokacin ma idan muka rasa idea'n k'aryar da zamuyi a gida mu fita itace take fad'a mana yanda zamuyi dan duk ta fimu k'walwa.
Haka rayuwar mu taci gaba da kasancewa, amma a koda yaushe ina yawan neman gafarar Allah saboda ina cin amanar ummanah, duk lokacin da zan fita sai tace min inji tsoron Allah, haka kuma aduk lokacin da na mata k'arya naje wani wuri nakan tuno da furucin ta, lokaci d'aya naji bana son rayuwar da nake ciki, na tsani kaina a doron k'asa. Wannan fitar da mukayi ta k'arshe ma sai da nace baxanje ba amma Afnan tace inhar banje ba sai ta tona min asirin abubuwan da nake yi a wurin ummanah, tsananin tsoron ummah da nake yasa na bata hak'uri banda yanda zanyi dole sai da na bisu, wannan shine asalin k'ungiyar *AREWA STARS"* Ta k'arisa maganar tana kuka sosai cike da nadama.
*Amrah nd Rerbeeart sk novels📚*
[1:06pm, 20/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
DOWNLOAD MORE NOVELS FROM http://hausabooks.com.ng
Page 36-40
Duka iyayen sunyi shiru sun ma rasa abunda zasu fad'a, yaran kuwa in banda kuka babu abun da suke yi ga azabar ciwo da ta addabe su, ga DJ da MC ance baza'a iya raba su ba dole sai d'aya ya rasa rayuwar sa.
MD ma shike nan ya rasa k'afar sa d'aya ya zama gurgu.
_(Allah sarki! Haka rayuwar take, ba'a gama halittar d'an adam ba har sai lokacin daya kwanta damar sa, wallahi wannan rayuwar abun tsoro ce, yanzu zaka ganka da lafiya kuma yanxu xaka iya rasa ta, yanxu kike da k'afa yanzu Allah yana iya yin yanda yaso da k'afar, haka kuma zaki ganki lafiya lau da idon ki Allah zai iya sawa ki rasa idon a lokaci d'aya, wallahi ko wannan ya ishe mu ishara akan muji tsoron Allah, mutuwa bata alerting idan zataxo, wallahi wannan labarin dana rubuta kusan abubuwan da suke faruwa kenan da gaske, muna fita daga gidaje ama iyaye k'aryar xa'aje wani wuri amma inda za'aje d'in daban yake, shin bamu gudun Allah ya zare mana rayuwar mu a inda mukaje d'in? Kar ku manta cewa manzon tsira Allah ya k'ara masa aminci yace "za'a tada mumini akan abunda ya mutu yana aikatawa" shin zamuso a tashe mu muna aikata alfasha? Duk abunda muke aikatawa fa Allah yana ganin mu, idan a tunanin mu ai mun ma iyayen mu k'arya bazasu tab'a gane wa ba tou ko mun manta cewa akwai RAQIB DA ATIB? wanda ranar k'iyama zasu bada shaidar abunda duk muka aikata, mun manta cewa k'afafuwan mu zasu bada labarin inda muka taka mukaje dasu? Mun manta cewa hannuwan mu zasu bada labarin abun da muka tab'a dasu? Mun manta da cewa bakin mu zai bada labarin abunda aka fad'i dashi ko akayi dashi? Mun manta da cewa ido zai bada labarin abun da aka kalla dashi? Mun manta da cewa ba'ayiwa Allah dabarah, baki d'aya rayuwar yanzu tarbiyyar yaran mu ta tab'arb'are, na kirkin mu k'alilan ne, wallahi muji tsoron Allah, mu dage yiwa kan mu da iyalan mu adduo'i'n shiriya, wallahi zaman kabari kanshi abun tsoro ne, zaman kad'aici kenan, barin ace tsayuwar k'iyama, ranar da wayon ka da dabarar ka bazai amfane ka da komai ba, ranar da uwa da uba ba tamu suke ba kowa ta kan sa yake, Ya Allah kasa mu cika da imani, Allah ka shiryar mana da duk wanda suka b'ata)._
Da kuka da komai Dad da Mom suna ji suna gani aka d'auki Kerry bayan an d'ad'd'aure ta aka nufi psychiatric (asibitin mahaukata) da ita.
```Bayan wata daya.```
Duk wata k'asa da suke tunanin idan sun kai Kerry zata samu lafiya sunje amma abun babu sauk'i, kud'i kawai suke kashewa amma abu yaci turah, daga k'arshe dai haka suka hak'ura suka dawo da ita Nigeria a asibitin mahaukata saboda xama da ita bazai tab'a yiwuwa ba, duka take sosai ga surutai marasa ma'ana da take yi tana fad'in "ai duk laifin ku ne, kune baku bani tarbiyyar kirki ba, inda kun kula dani da tarbiyyar kirki ai da komai bai same ni ba" sai kuma ta fashe da kuka, hakan yasa kawai suka hak'ura suka miyar da ita asibitin.
Su kuwa su Afnan abu babu sauk'i, ciwon ana magani amma kamar bayi ake ba, kulkun k'ara rub'ewa yake yana wari, Momy tace ta fiddo miji a mata aure amma duk a samarin ta wanda tama magana a waya da murna zasu amince, amma da zarar sunxo sukaga yanda take ga wari tana yi sai su tafi bazata sake ganin su ba, kullun cikin damuwa take.
Samir kuwa ya warke sosai dan shi kad'ai ne ma ya warke, amma abun haushi da takaici shine bashi da mazakunta, bazai tab'a auruwa ba har abada, in ma yayi auren babu macen da zata iya zama dashi.
*Amrah nd Rerbee'art sk novels📚*
[11:14am, 4/11/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
DOWNLOAD MORE NOVELS FROM http://hausabooks.com.ng
Page 36
*```KARSHE```*
💓💓💓
haka dai rayuwar taci gaba da tab'arb'are masu, raunukan su sai k'ara rub'ewa suke abun k'yama da tausayi, Ummy banda wari babu abunda takeyi, ko Mamin ta ta daina shiga d'akin da take, in ma abinci zata kai mata sai dai ta ajiye daga bakin k'ofa ta rarraho ta d'auka.
Afnan kuwa Momy ta aika da hoton ta masallatai ayi tallar ta, nan da nan kuwa aka fara rububin ta, amma da mamaki duk wanda yazo yaga fuskar ta da yanda take sai ya tafiyar sa.
Kamar kullum Momy ce zaune ta buga tagumi ta tsurawa Afnan ido tana kallon ta cike da tausayi, sallamah akayi Momy tayi saurin amsawa tana kallon mai shigowa, Dady ne ta gani hannun shi rik'e da Affan sanye da Uniforms alamar daga makaranta ya d'auko shi,
"Oyoyo momy na" ya fad'a tare da isowa wurin Momy.
"Sannu da dawowa Alhaji" ta fad'a bayan ta rungume Affan a cinyar ta tana cire masa safar k'afa.
"Momy wai yaushe Yaya Afnan zata warke ne?",
D'an murmushin yak'e ta mashi kafin tace "insha Allahu zata samu lafiya yaro na, ka ringa saka ta a addu'ah kaji?",
Kai ya d'aga cike da tausayin 'yar uwar sa.
"Assalamu alaikum" akayi sallamah,
Dady ya amsa da "wa alaikumussalam, Mati ya akayi ne?",
"Yallab'ai kayi bak'o",
"Bak'o? Waye ne?",
"Wani gurgu ne yallab'ai, yace ayi masa sallamah da kai",
"Gurgu? To kace ina zuwa".
Kallon shi ya miyar ga Momy yace "Maman Afnan barin fita inga mai nema na".
Bayan ya fita ya samu wani gurgu ne ya mik'a masa hannu suka gaisa,
"Bawan Allah meke tafe da kai?" Dady ya fad'a yana kallon gurgun mai ido d'aya.
"Sunana Sani, dama yallab'ai naga wani hoto ne a masallacin da nake aiki, so ina da ra'ayin auren yarinyar indai babu damuwa"
Shiru Dady yayi ya k'are masa kallo sosai sannan yace "ehh to! Nidai a wuri na babu damuwa, amma ka shigo mu shiga ciki idan yarinyar taji tana son ka sai ayi binciken komai sannan a d'aura aure".
Murmushi yayi sannan yabi bayan Dady daya fara shigewa cikin gida.
Bayan sun shiga ciki ya gaishe da Momy cikin girmamawa itama ta amsa masa da sakin fuska.
Dady yayi ma Momy bayanin abunda yake tafe dashi kai tsaye momy ta goyi bayan abun,
Afnan ma dake kwance take ta amince dashi duk da yanda yake d'in.
*****
Shirye shirye sosai suka kankama na bikin Sani gurgu da Afnan, duk da ba wani abu za'ayi ba walima ce kawai za'ayi.
Ranar jumu'ah aka d'aura auren su amarya ta tare a babban gidan ta da Dady'n ta ya mallaka mata ita da mijin ta.
Feenat kuwa taci gaba da zuwa makarantar ta har sun fara zana jarabawar k'arshe ta sakandire.
Kerry kuma har yanzu abun shiru babu sauk'i, gashi kuma sun k'i zuwa wurin malamai duk da shawarar hakan da ake basu.
*AREWA STARS* dai a haka suka k'are da tab'arb'ararriyar rayuwa, wannan ishara ce ga masu hali irin nasu, masu yawan zuwa party ba tare da iyayen su sun sani ba, ina fatan wannan gajeren labarin zai zama fad'akarwa ga al'ummah musulmai har ma da wanda ba musulman ba.
ALHAMDULILLAH!!! DOWNLOAD MORE NOVELS FROM http://hausabooks.com.ng
Duk abunda yayi farko zayyi k'arshe, muna godiya ga Allah mai kowa mai komai da ya bamu ikon kammala wannan labarin namu, kurakuran dake cikin labarin Allah ya yafe mana,inda muka yi daidai kuma Allah ya bamu ladar.
Muna godiya ga masoyan mu da suka bibiyi labarin har ya kaiga k'arshe irin su:-
```Rukayya Auwal,```
```Faty KK```
```Husnah Ibrahim,```
```Aysha Khalil,```
```Amman Suraj```
Da da da da, lissafo ku ba abune mai sauk'i ba, sai dai muce muna k'aunar ku akoda yaushe, kuci gaba da kasancewa damu a littattafan mu na gaba.
Jinjina, fatan alkhairi, godiya su tabbata ga K'ungiya mai albarka *```NAGARTA WRITERS ASSOCIATION```* Allah ya bar zumunci ya k'ara had'a kawunan mu amin.
```ZARAH~B~B``` *godiya da jinjina mai tarin yawa a gare ki, kin nuna mana soyayya kuma kina kan nuna mana ita, Allah yabar mu tare ya k'ara miki baseerah.*
All groups members and admins na group d'in da muke muna gaishe ku, tsayawa lissafo ku ba abune mai sauk'i ba, sai dai mu maku godiya da bibiyar labarinmu da kukayi.
'Yan uwan mu writers muna godiya a gare ku, Allah ya raba mu da sharrin mahassada da mak'iya.
Amrah and Rabi'atu sk novels group mun gaishe ku da babbar murya, Allah ya barmu tare ameen.
Kuci gaba da kasnacewa dani Amrah a cikin novel d'ina mai suna *UMMU HAYDAR* idan na kammala exam insha Allahu.
Amratu A Mashi and Rabiatu Sk msh
AKA
Amrah da Rerbee'art
ke cewa mu huta lafiya.