Farooq kuwa yana fita police station ya tafi
musu bayanin komai da ya faru kuma ya fad'a musu akan zuwan su na yau daddare.
Ai kuwa D.P.O ya bashi mutane mota biyu dan su kama su akan laifin da suke son aika tawa.
Godiya ya mishi sosai sannan ya dawo gida Isyaku ya fad'awa komai dan baya son Husna taji labarin abin.
Isyaku kam gaba d'aya ya tsorata dan kar yaje a garin kafin azo a kamasu su kashe sa hakan ne yace
"Yallabai gaskiya nikam na tsorata da wannan al'amarin ni yanzu zan tafi gida idan Allah ya kaimu gobe sai na dawo."
Shima Farooq abin ma dariya ya bashi dan yaga alamun Isyaku tsoro yake ji sannan yace
"Haba Isyaku ya zaka bani kunya dan Allah gaskiya banyi tsammanin tsoro a tattare da kai ba."
"Kai yallabai wannan al'amarin rai ne kaga kuwa ba'a wasa da shi."
"Kaga fa suma yan anayin sallah'n isha'i zasu zo kowa ya samu wajen b'uya ai sai anyi shiri, kai yanzu abinda nake so kawai kabar k'ofar gidan a bud'e har yan sandan suzo."
Cikin sanyin murya Isyaku yace
"To shikenan yallabai Allah ya tsare mu."
"Yauwa Isyaku haka nake son ji, Ameen ya Allah."
Bayan haka kuma cikin gida ya shiga dan duba jikin Husna.
Tana zaune a parlour tayi wanka tayi kwalliya Yau kam ba laifi tad'an ji saukin jikin ta sosai.
Sallama yayi ta amsa mishi ya shigo yana cewa
"Kai Maman Baby yau Baby ta barki kinyi wa Abban ta kwalliya kenan."
Dariya Husna tayi sannan tace
"Sannu da zuwa."
Yauwa My Angle ya jikin naki?"
"Jiki Alhamdulillah."
"To Allah ya rabaki da Baby na lafiya."
Dariya tayi sannan tace
"Ameen ya Allah,
Amman ya Farooq ya akayi yau kadawo da wuri haka."
"Eh lafiya k'alau kawai inason ganin ki ne."
Murmushin jin dad'i tayi sannan tace
"To na kawo maka abinci?."
"Kai My Angle yau har abinci kikayi mana?
Daman nayi missing girkin ki sosai wallahi,
Amman kuma gaskiya yau ya kamata nabawa Baby kyauta."
Dariya Husna tayi tace
"Kai gaskiya Bata buk'atar wannan kyautar naka."
"Ai kuwa tafi kowa so kedai muje naci abinci sai kiji sauran bayani."
Haka suka ci abinci cikin so da kaunar junan su, Farooq ko kad'an bai nuna gani abu a tattare a fuskan shi ba bare kuma Husna tasan halinda ake ciki.
Yusuf kam shiri yake sosai dan dashi yace za'a tafi gidan Farooq d'in dan yana so ya harbi Farooq da hannun sa.
Haka kuwa duk ya shirya har ya saka kayan da suka bashi da fuskan da zai saka saboda kar a gane shi.
Misalin karfe goma na dare 'yan sanda sukazo suka zagaye gidan Farooq dukan su ko ina sai da suka b'uya sannan suka boye motar su a gaba da gidan saboda kar 'yan fashin su gani.
Ai kuwa misalin Karfe goma sha biyu yan fashi suka zo gidan Farooq har da Yusuf shine yake jagoran su cikin gidan.
Suna zuwa sukayi sa'a k'ofar gidan a bud'e yake hakan ne ya basu daman shiga cikin gidan cikin hanzari.
Isyaku yana d'akin shi zaune dan gaba d'aya ya kasa barci ji yake idan ya kwanta zasujo su kashe sa duk da ga 'yan sanda ta ko ina a gidan.
Suna zuwa direct part d'in Farooq sukayi sauran biyu kuma suka tsaya a wajen Isyaku.
Suna shiga d'akin Isyaku wasu police su biyu sukaje suka kama su.
Suna shiga parlour a zaune suka sami Farooq akan sallaya da alama sallah ya idar yake addu'a.
Suna zuwa suka fara nuna mishi bindiga .
Yusuf ne yaje ya zauna akan kujera ya d'aura kafan shi d'aya akan d'aya sannan yace
"Kai Yau kwanan ka ya kare daman kamar yanda na fad'a maka sai na kashe ka sai na kashe ka ne wallahi bazan ta6a barin ka ka zauna da matar da nake so, tunda kayi taurin kai tu yau lahira zatayi bak"..........
Ganin 'yan sanda sun shigo ne ya hanashi k'arasa maganar da yake yi.
Gaba d'ayan su rikicewa sukayi dan basu tsammanin haka zai faru da su ba.
Ai kuwa gaba d'ayan su aka kama aka kaisu police station.
Yusuf kam sai wani muzurai yake da ido dan kuwa baisan ya akayi haka ya faru ba.
Tunani yake ya akayi Farooq yasan abinda yake shiryawa amman ina ba amsa aka kwashe su.aka kai su station.
Husna da tana cikin d'aki tana barci hayaniyar da tajine yasata tashi.
Gaba d'aya abinda Yusuf yake fad'a taji a kunnen ta ba k'aramin razanata abin yayi ba.
Kukan ta Farooq yaji da sauri ya shiga d'akin dan baisan idonta biyu ba.
Lallamin ta yake sosai amman tak'i yin shiru gaba d'aya Farooq ya fita a hayyacin sa yanda yaga tana kukan har cikin ran shi yake jin kukan ta.
Cikin muryan kuka tace
"Ya Farooq meyesa baka sanar dani wannan abin ba da yanzu wani abu ya sameka ya kake son nayi?" Sai kuma ta fashe da kuka.
Matsowa yayi ya rungume ta sannan yace
"I'm sorry my Angle banason na fad'a miki abinda zai tayar miki da hankali ne, amman nasan duk shirin sa da yake yi mahaifin sa ne ya fad'a mun."
Cikin mamaki Husna tace
"Ya Farooq wanne mahaifin nasa ?"
"Eh mahaifin Yusuf ne ya fad'a mun abinda suke k'ullawa shida mahaifiyar sa."
Nan da nan ya fad'a mata duk abinda Baban Yusuf ya fad'a musu har yanda yayi ya samu aka kama su.
Ba k'aramin dad'i Husna taji ba dan da yanzu an kashe mata miji.
Cewa tayi
"Allah sarki.bawan Allah ashe ba halin su d'aya da d'an nashi ba."
"Wallahi sosai ma Husna ko ni da yake fad'a mun nayi mamaki da bai rufawa d'an sa asiri ba."
"Eh kaga kowa yayi gaskiya Allah yasaka mishi da alkhairi."
Anan dai suka d'anyi hiran su sannan suka kwanta.
Washe gari kuwa aka shigar da su Yusuf kotu Wanda aka yanke musu hukuncin zama a gidan yari na shekara d'aya tare da hukunci mai tsanani.
*Taku har kullum Momyn Musaddiq*📚✍🏻
💞💞💞💞💞💞💞💞
🙆🏻😭 *ABOKIN MIJINA*😭🙆🏻
💞💞💞💞💞💞💞💞
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ*📚✍🏻
````DEDICATED TO MY FANS, no need for long essay you know i💔you💯 one love 💞ana mugun tare irin totally d'in nan``` 😍💞💔❤
*BISBILLAHI RAHMANIR RAHIM WASALLAHU ALAN NABIYYUL KARIM*
*MATAYEN ANNABI TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARESHI.*
*YA AURI MATAYE GOMA SHA D'AYA (11)*
```TA FARKON SU (S) KHADIJA 'YAR KHUWAILID, BAYAN TA YA AURI MATA GUDA GOMA (10) SUNE:
(S)AISHA 'YAR (S) ABUBAKAR
(S) HAFSAT 'YAR (S) UMAR
(S)ZAINAB 'YAR JAHASH
(S) MAIMUNA 'YAR HARIS
(S)SAFIYYA 'YAR HUYAYYI.```
*Biyu sun rasu a wajen sa*
*(S) KHADIJA*
*(S) ZAINAB 'YAR*
*shi kuma ya rasu yabar sauran guda taran (9)*
*KUYANGUNSA*
*Amman kuyangunsa su gudu (4) ne.*
*(S) MARIYATUL-KIBDIYYAH*
*(S) RAIHANATUL-KIBDIYYAH*
*DA WATA KUMA GUDA D'AYA WANDA (S) ZAINAB 'YAR JAHASH TA BASHI KYAUTA.*
*TA HUDU (4) KUMA YA SAMETA NE DAGA WANI SASHIN NA RABATATTU.*
*'YA 'YAYEN ANNABI TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARESHI.*
*'YA 'YANSA MAZA GUDA UKU NE*
*(S) ALKASIM*
*(S) IBRAHIM*
*(S) ABDULLAHI*
*'YA 'YANSA MATA GUDA HUDU*
*(S) FADIMATU*
*(S)ZAINAB*
*(S) RUKAYYA*
*(S) UMMU KHULSUM*
*DUKKAN SU DAGA (S) KHADIJA SUKE SAI (S)* *IBRAHIM SHI DAGA (S)* *MARIYATUL KIBDIYYAH YAKE, WADDA MUKAUKASU YA BASHI ITA KYAUTA.*
🔚 🔚💞
🔚. 🔚💞
🔚. 🔚💞
🔚 🔚💞
*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Page 96~100*
Washe gari kuwa aka shiga da su kotu aka yanke musu hukuncin zama a gidan yari na shekara d'aya tare da horo mai tsanani.
Mahaifiyar Yusuf tayi kuka sosai dan bataso hakan ya faru da tilon d'an ta ba.
Mahaifin Yusuf kuwa cewa yayi
"Komai aka mishi shi yajawa kanshi ai hukuncin ma yayi kad'an da an kara saboda masu irin halin sa sa gyaru."
Farooq jikin shi duk yayi sanyi dan shi yana son Abokin shi tsakani da Allah amman ina Yusuf ba haka ya d'auka ba.
Yusuf kuwa kuka yake sosai yanayin nadamar abinda ya aikata ya cikin kukan shi ne Dauda Wanda shine babban 'yan daban yazo yace da shi
"Haba Maza wallahi ka bani kunya banyi tsammanin haka a tattare da kai ba, yanzu kana nufin dan ankawo ka nan na shekara d'aya shine duk kabi ka damu kanka har kake kuka?
To bari kaji ni da yau zuwana uku kenan kuma ina fita sai naje nayi abinda nayi niya saboda haka ina baka shawarar kar kabari kud'irin ka na kashe Farooq ya fita a rain ka."
Kallon shi Yusuf yayi sannan yace
"Yanzu sau uku kana shiga wannan wajen?"
"Kwarai kuwa kuma ina fita nake cimma burina."
"To yanzu yaushe zamu bar nan har na cimma nawa burin" ya tambaye shi.
"Kai shekara d'aya ne fa ai kamar yau ne saboda haka Abokina kar ka wani cire wannan abin a ran ka."
Murmushi Yusuf yayi sannan yace
"To shikenan nikuwa yanzu na d'aura damarar kashe sa tar da familyn sa."
Shi kuwa Dauda dad'i yaji dan so yake ya d'aura shi wani hanyar.
*BAYAN WATA TAKWAS*
Yau ya kasance asabar Husna ta tashi da labour tun tana d'aurewa har takasa ta sanar da Farooq halinda ake ciki.
Farooq yana ji ya rikice gaba d'aya waya ya d'auka ya kira Mama ya fad'a mata ce mishi tayi ya jirata tana zuwa amman kar ya sanar da mahaifiyar Husna, da to ya amsa mata yaje yasa Husna a gaba yana ta faman yi mata sannu.
Basu wuce minti goma da waya ba sai gata nan tazo cewa tayi
"Farooq d'auko kayan haihuwa mu tafi hospital."
Ai kuwa daman sun had'a kayan su tun ba yau ba alkwatin ya d'auka suka fita sai Aminu Kano hospital daman anan take awu.
Suna zuwa aka shiga da ita kasan cewar haihuwar tazo ta.
Basu wuce 15 minutes ba nurse ta fito d'auke da jariri a hannun ta.
Farooq ne yayi saurin k'arasawa wajen ta yana cewa
"Nurse ta haihu ne?"
Dariya nurse d'in tayi sannan tace
"Gashi kuwa ga Babyn ka mai kama da kai itama Maman Babyn Lafiya ta k'alau" ta k'arasa zance tana murmushi.
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e Farooq sai da yayi sujjada ya godewa Allah sannan ya mik'a hannu dan kar6an Babyn.
Hanashi Nurse d'in tayi tace
"Wannan Babyn mai tsada ce bazan baka ita a haka ba."
"To me kike so ki fad'a mun idan baifi k'arfi na ba zan baki shi."
Dariya tayi ta mik'a mishi tana cewa
"A'a ba komai kawai zolayan ka nake."
"To dan Allah zan iya shiga naganta?"
"A'a ba'a gama gyara ba tukun nan." Tana fad'an haka ta wuce ko koma wajen Husna. "
Hajiya kam tana tsaye tana kallon Farooq abin ma dariya ya bata dan kamar film take kallo take ji.
Sai da yagama yiwa Babyn addu'a sannan ya wuce wajen Maman sa.
"Sai da kaga kallon ta sannan zaka kawo min ita."
Sai a lokacin Farooq yaji kunya magana ba ya mik'a mata Babyn.
A lokacin Farooq ya kira gidan su Husna ya sanar da su wayyo kuzo kuga murna ta ko ina kan nace me mutane sun cika hospital.
Farooq kuwa sai kiran 'yan uwa da Abokan arziki yake yana fad'a musu haihuwar Husna.
3:00 pm aka sallame su suka koma gida cikin farin ciki.
B'angaren Yusuf kuwa ba k'aramin azaba suke shaba duk ya rame yayi bak'i fuskan nan duk gashi dan idan ka ganshi ma bazaka gane shi ba duk ya canza kamanni ga abinci ma sau d'aya ake basu a rana shima ba isarsu yake ba.
Tunda aka saka Yusuf a gidan yari mahaifin sa bai ta6a zuwa ga duba shi ba sai mahaifiyar sa itama lokacin taje duba Yusuf a garin dawowa gida sukayi accident k'afan ta ya karye duk d'aurin da aka mata bayayi har aka hakura aka bari gashi yanzu haka za'a yanke farar amman ba kud'in aiki.
Yusuf yayi nadama sosai yayi da nasanin abin da ya aikata amman yana fara nadama sai Dauda yazo ya canza mishi tunani.
Ai kuwa yana d'aukar maganar Dauda dan ba k'aramin yarda yayi da shi ba.
Haka suke rayuwar su cikin azaba ga aiki duk su sukeyin shi.
Husna kuwa ba k'aramin kulawa take samu ba ta ko wanne b'angare dangin mijinta suna matuk'ar kaunar ta bama da sukaji labarin abinda ya faru a cewar su da wata ce ai tuni Yusuf yaci galaba akan ta.
Haka rayuwar su taci gaba da tafi cikin so da kaunar junan su.
Ranar suna yarinya tace sunan Hajiya Aisha anyi taro sosai dan Wanda bai sani ba cewa zaiyi aure ake.
Da yamma akayi walima wanda Malama Khadija tazo tayi musu wa'azi akan zaman takewar aure.
Washe gari ne za'akai Husna wanka amman ina Farooq yace shi baisan zancen ba dan shi baiyar da Husna taje gida wanka ba.
Akayi-akayi Farooq yabar Husna ta tafi amman yace shi bai yarda ba sai da Hajiya tasa baki sannan ya bari badan ransa ya so ba.
Haka aka d'auki Husna aka tafi da ita wanka amman kullum sai faru yaje sau biyu ko sau uku a rana.
*BAYAN WATA BIYU*
Yau yake su Yusuf zasu fito a gidan yari Yusuf sai Allah Allah yake yaje gida yaga me yahana mahaifiyar sa zuwa d'auka shi.
Ko wannen su yayi shirin tafiya dan duk yawancin su sunada mata harda yara.
Shi kuwa Yusuf bai damu da rayuwar Hafsat ba bare kuma abinda yake cikin ta.
Misalin karfe d'aya na rana aka barsu kowa ga tafi.
Haka kuwa suka rabu bayan Dauda ya zuga Yusuf ya canza mishi tunani.
A zaune ya sameta akan tuburma tayi tagumi tana tunanin wannan rayuwar da take ciki.
Sallama shi da taji ne yasata d'aga kanta da sauri tana kallon shi.
Da sauri ya k'araso inda take yana cewa
"Inna meye ya same ki."
Kuka Inna ta fashe da shi sannan tace
"Yusuf kai ne Ka dawo?"
"Eh nine Inna ki fad'a mun meye ya sani k'afar ki."
Ai kuwa nan da nan Inna ta bashi labarin abinda ya faru da ita da rashin kud'in aikin gashi k'afar ta ru6e.
"Inna yanzu yanke miki k'afa za'ayi?"
Kuka ta sake fashewa da shi sannan tace
"Eh Yusuf idan kuma ba'a yanke ba mutuwa zanyi kuma wallahi bana so na mutu."
"Kiyi hak'uri zanyi abu tunda dai yanzu gani na dawo."
Goge hawayen ta tayi sannan tace
"Kai matar Farooq fa ta haihu yarinyar har tayi wayo."
Gaban Yusuf ne yayi mummunar fad'uwa sannan yace
"Inna yanzu sai da Husna ta haihu?"
"To ya za'ayi da abinda Allah ya k'addara."
Baiyi magana na d'an lokaci sannan yace
"Inna ya labarin Hafsat?"
"Ai Hafsat ta haihu ta haifi 'ya mace sannan yarinyar ta koma yanzu ma naji labarin aure zatayi."
"Aure fa kika ce Inna!
Bayan ban sake ta ba."
"To amman ai ka koreta har ta haihu kaga kuwa ba aure a tsakanin ku."
Tsaki yayi sannan yace
"To ni Inna zan tafi gida sai anjima zan dawo."
"To sai Ka dawo."
Daga nan kuma ya tashi ya fita bai tsaya a ko ba sai gidan sa.
Gidan duk yayi kura duk ya 6aci a haka ya shiga bedroom d'in yayi wanka ya fito ya shirya cikin kanana kaya sannan ya d'auki key motar shi ya fita.
Su Farooq kuwa soyayya suke sha sosai da matar shi ga 'yar su wacce suke kira da Samha hankalin su kwance ba abinda yake damun su.
Yusuf kuwa yana fita wajen wani yaje yace mishi yana so yaje ya cire birkin motar Farooq zai biyashi da kud'i mai yawa.
Ai kuwa nan da nan yaron ya amince daman aikin sa kenan.
Yusuf gidan su ya wuce dan bai sanar da mahaifiyar sa abinda yake kullawa ba.
Farooq ma gidan su yazo dan gaida mahaifiyar sa Bala ya ganshi ya biyo bayan shi.
Buya yayi har sai da Farooq yayi parking motar shi sannan ya fito ya tunkaro inda motar yake.
Lokacin da yazo wajen motar cikicewa dan Yusuf ma anan ya ajiye motar sa kuma duk iri d'aya ne hatta color iri d'aya.
Sai da Bala ya gama karewa motocin kallo sannan yazo ya cire birkin d'ayar motar sannan ya tafi.
Yusuf ya kira a waya yace ya kammala aiki yazo ya biyashi.
Cikin jin dad'i Yusuf ya amsa da to ya tashi yabar Inna ya fita ya hau mota ya tafi.
Sai da Yusuf yahau babbar kwalta ga wata k'atuwar mota tana tunkaro shi ina yayi -yayi yataka birki amman ina babu haka wannan motar tazo ta taka Yusuf.
Ba abinda ake fad'a sai Innalillahi wa inna ilaihi raju'un!
Motar Yusuf tayi rugu-rugu wanda bazakayi tsammanin da mutum a ciki ba.
Haka aka cire Yusuf jikin shi duk jini aka ajiye shi a gefe.
Farooq kuwa ya tashi a gidan su zai dawo gida yaga kamar motar Yusuf ce take ci da wuta, da sauri tayi parking ya k'arasa wajen da gudu abinda idon shi ya gane mishi ne ya razana shi.
Da sauri ya k'arasa inda aka kwantar da Yusuf mutane sai magana suke dan 'yan wajen basu sanshi ba.
Ai kuwa Farooq ana tafiya ya d'auke shi yasa shi a motar sa bai tsaya a ko ina ba sai Hospital.
Yana zuwa aka kar6eshi akayi da shi emergency.
Wani Doctor ne ya fita yace da Farooq yana son ganin sa, haka suka shiga office d'in doctor.
Bayani ya mishi sosai.akan k'afar Yusuf ba zata kara aiki ba sai ba an yake dan tayi rugu-rugu.
Farooq ba k'aramin razana yayi ba dan baiso haka ta faro da abokin sa ba amman ba yanda ya iya haka Allah ya k'addara masa.
Kud'in aikin Farooq ya biya akayi mishi duk wani abinda ake buk'ata Farooq ya biya sannan ya koma ya sanar da Hajiya Aisha.
Itama ta tausayawa Yusuf dan yanzu ya zama abin tausayi.
Haka rayuwar Yusuf ta koma ba k'afafu ya koma zama a kan keke.
Mahaifiyar sa kuwa tanajin labarin accident da d'anta yayi a lokacin hawan jini ya bigeta ta rasu.
*BAYAN SHEKARA D'AYA*
Yusuf na gani akan keken sa zaune yayi tagumi sai faman hawaye yake yayi nadamar duk.abinda ya aika ta.
Gidan Farooq yazo ya nemi gafarar su akan su yafe mishi kuma duk ya sanar da su abinda ya aika ta.
Farooq kuwa ya yafe mishi duk abinda yayi sannan yayiwa Allah godiya da ya shirya Abokinsa.
Haka rayuwar su yaci gaba da tafiya cikin so da kaunar junan su.
Farooq yana taimakawa Yusuf sosai dan yanzu bashida aikin yi sai zama kan keke.
*Alhamdulillah!*
*Alhamdulillah!!*
*Alhamdulillah!!!*
*Alhamdulillah!!!!*
*ALHAMDULILLAH ALLAH NA GODE MAKA DA KABANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN KUSKUREN KE CIKI ALLAH KAYAFE MUN ALKHAIRIN DA KE CIKI ALLAH KA BAMU LADAN SHI*
*MASOYA WANNAN LITTAFI NA GODE DA NUNA KAUNAR KU GARENI NAGODE! NAGODE!! NAGODE!!!*
*SAI KUN SAKE JINA A SABON LITTAFINA MAI SUNA.......*
*Taku har kullum Momyn Musaddiq*📚✍🏻