.
Muka karasa gindin motar babu magana muna tafe kafada da kafada da muka isa gindin motar ta fuskanceni
yaushe zaka zo? Tambayar tayi matukar girgizani.
Ina kike nufi? Fadila ta dafe kirji cikin razana ta harareni a fusace.
Au baka san zancen ba?
Wane zance? Fadila ta girgiza kai tace shikenan tunda baka sani ba daman babane yace nazo na sameka amma tunda kace baka san komai ba shikenan. Tana gama fadi saita juya cikin fushi ta shige motar.
Shashashan banza sakarai. Wata zuciya tafara yi min kururuwa idan ka bari ta tafi baka lallasheta ba kamar kayi sallama ne da miliyan biyar. Mafarkinka duk ya zama shirme.
Fadila Fadila na kira sunanta cikin gaggawa ta sauke gilashin tagar motar na sunkuya nace.
Kiyi hakuri dan Allah Fadila... Idan kin kula duk ba'a ahankalina nake ba a rude nake... Fadila ta dubeni ta tabe baki sannan tayi tsaki tace.
Yi sauri ka koma gurinta tana can tana kukan kishi kada ta mutu... Gabana yayi das das.
Wa kenane kike nufi? Na tambaya baki bude.
Kafini saninta... Wancan baiwar taka dake jiranka a ofis. Tasawa motarta giya ta firzgeta aguje tabarni anan tsaye ina hangen kurarta.
SAI WATA RANA MILIYAN BIYAR.
Nace da kaina kamar na fashe da kuka koda na nufi ofishina sainaji wani zazzafan zazzabi yana neman rufeni.
.
*********** ****** **********
.
Har sa'ar dana dawo dakin karbar bakin lauriyya tana nan kamar yadda nabarta kanta kife akan teburina na tsaya akanta.
Lauriyya na kira sunanta akwai alamar rawa a muryata. Ta dago kai ta kalleni da wani fatalwan murmushi. Ba sai an fada ba duk wanda ya kalli idanunta yasan taci uban kuka duk kuwa da matukar kokarin datayi wajen share hawaye.
Har ta tafi? Ta tambayeni hannunta rungume a kirjinta.
Ta.... Tafi na fadi muryata na sarkewa.
Mukayi shiru babu wanda ya sake cewa kala har aka kira sallar isha. Sai lauriyya ta mike ta sakala jakarta akafada.
Hilal zan tafi gida... Na danyi shiru na farko saikuma nace Gida? Haka da wurwuri... Ta danyi tsaki sai gabana yafadi tunda nake da ita bata tabayin tsaki a gabana ba.
Banajin dadi ne... Shiyasa nake son tafiya yau da wuri muka dan sake shiru na tsawon lokaci.
Dan dakata to ina da sauran magana dake.. Ta hade fuska.
Maganar me kuma zakayi min na dauka mun gama komai tun dazu? Ga kayan ai acikin jakata. Ta nuna jakar da hannunta.
Duk lokacin daka shirya saika karba in kuma kana so ma yanzu sainaba ajiye ce agurina.
Akwai sauran magana lauriyya... A ina kika samosu? Naji ta rike numfashi cikin kaduwa.
Hilal me kake nufi da a ina na samo su kana nufin kace ni barauniya ce?
Dan girman Allah kada ki bata zancen nan lauriyya ni bahaka nake nufi ba. Ki tuna fa kyauta zakiyimin da kararki ta makudan kudi a iya sanina kuma ban taba ganinki dasu ba kinga kuwa ashe banida laifi danna tambaya.
Ta sunkuyar dakai cikin takaici. Tambayar ta kona mata rai ta daga kai.
Tunda ka dage saika san inda na samesu bari yo na fada ma MIJINA NE ya saya min su.
Mijinki? Ta gyada kai.
Kwarai kuwa baka san na taba aure ba kafin nazo nan garin ba? Nayi ajiyar zuciya.
Ina fatan yanzu ka gamsu. Lauriyya tace sannan ta matso daf dani kusa dani har takai ina iya jinhucinta akan fuskata.
ITACE TA BATA MAKA RAI ?
Na kalleta a rude.
Wa..wa kenan kike nufi? Lauriyya ta dafa kafadata tace.
Nasan daman kafi karfina Hilal na dade ina kwana ina tashi da fargabar cewa watarana sai anzo har ofishin nan an kwace min kai!
Gabana yafadi nayi sauri na dauke hannunta daga kan kafadata.
Lauriyya nataba fada miki kuwa wata kalma kwaya daya?
Wacce kalma ce wannan? Ga mamakina sai naji ina mai kunyar hada idanu da ita.
Adacan Lauriyya ban dauki amatsayin komai ba fiyeda kawai sakatariya na. Nayi sa'a danaga ta kura min idanu kamar zata hadiyeni.
Yau lauriyya na wayi gari duk fadin duniya babu wata 'ya mace datafiki agurina. Lauriyya ta dada matsowa daf dani.
Na Gode Allah Hilal tun ranar dana dora idanuna akanka nake kaunarka.
Zan baki wani labari lauriyya ki saurareni da kunnen basira lauriyya ta dubeni dakyau. Labarin me kuma? Nakama hannunta muka wuce cikin ofishina. Wannan shine karo na farko dana taaba yi mata haka. Na zaunar da lauriyya akusa dani.
Lauriyya jiya da daddare wasu al'amura masu kama da shirin fim sun faru akaina. Abubuwan na da matukar rikirtarwa to ahaka dai ni gama yanke shawara azcuiayata cewa ni dai KE NA ZABA LAURIYYA.
Dan Amina Muhammadu.
Lauriyya tace tana tafa hannu. Ban fahimce ka ba hilal..... Me kake fadi ne kace ni ka zaba ban gane ba.
Me yiwuwa idan nabaki labarin ki fahimce ni ke dai saurara da kyau.
.
Nafara zubo mata labarin al'amarun kyautar jaririn da akayi min tun daga farko har zuwa kan zuwan fadila ofis.
Karfe tara saura kwata nagama bata labarin.
Lauriyya tayi shiru bata ko motsi kamar ruwa ya cinyeta ga mamakina akaro na farko sainaji da gama fada mata labarin damuwa zuciyata ta ragu.
Lauriyya ta mike tsaye tabar kusa dani sannan tafara safa da marwa..
.
Lauriyya ta Mike tsaye tabar kusa dani sannan saita fara safa da marwa acikin ofishin akwai wani yanayi dake fuskanta daya hanani na katse mata hanzari don haka sainayi zamana ina jiran naji ta inda zata bullo inada kwarin gwiwar cewa indai har akwai mafita to lauriyya ce zata kawota na yarda da kwakwalwarta akan hakan.
.
Hilal! Nayi firgigit sa'ar danaji ta kira sunana.
Mecece shawarar Ki akai. Lauriyya ta dawo kusa dani ta zauna sannan tace
Zancen gaskiya Hilal indai kabar miliyan biyar ta wuce ka kayi shashanci. Na zabura cikin kaduwa.
Me kike nufi? Lauriyya tayi dariya miliyan biyar tafi karfin wasa Hilal Amatsayina na mai kaunarka bazan so ka rasa naira miliyan biyar saboda ni ba.
Tunanina ya kure na rasa abin da zance da ita.
Ni shawara ta ta Hilal kaje ka aure ta.
Lauriyya meke damunki ne ta girgiza kai.
Lafiya ta Kalau babu abin da ke damuna ni har kullum babu abin da ke faranta min rai irin cigaban ka
Da miliyan biyar kana iya wa duk Abokan hamayyar nisa.
Lauriyya kibar zancen nan tuni nagama fada miki in har akwai wacce zan aura yanzu a duniya to kece. Idan kuwa na Auri fadila bansan da idon zan Kalle ki ba ta daga kai muka hada idanu tace.
Ko?
Kwarai kuwa na Mike tsaye.
Ko sallah banyi ba yakamata naje nayi sallah lauriyya ta biyo ni Abaya.
Kayi tunani Hilal tunda dai sati daya suka baka amma ni ina ganin gara ka aure ta Hilal.
Ban juyo na kalleta ba sa'ar da take maganar domin na lura ita kanta akwai wani sirri datake kokarin boyewa daga gareni. Wata zuciyar ta ci gaba da yi min kururuwa. Duk kabi ka zama wawa Hilal haka kawai kabari matan zamani suna neman su zauta ka.
Daya kasan yadda take dayar kuwa baka ma san koda tarihin taba.
Zan tafi gida Hilal sai goben lauriyya tace.
Mamakin abin da yasa ta firgicewa haka take sauri sauri ta tafi gida.
Toh shikenan sai goben kenan. Ahaka muka rabu da lauriyya ta tsallake bakin titi tana sauri sauri na bita da kallo cikin mamaki meke faruwa ne? Yanzun nan fa take nuna tsananin kishin ta a gareni take nuna cewa duk duniya ni take kauna lokaci guda kuma tana cewa naje na Auri fadila... Tabbas akwai wani abu murdadde acikin al'amarin.. Bi a hankali dan samari kada ka bari matan zamani su haukata ka a banza nace da kaina....
.
*********** *********** *************
.
Karfe tara da rabi agogon mota ta ya nuna nayi kokari tun sa'ar dana baro ofis na fitar da komai daga cikin zuciyata abunda nafi kauna yanzu a duniya shine isashshen barci domin rabona da barci sa'o'i kusan ashirin da hudu kenan.
Nayi fakin da motar a kofar gidana na rufe gilasan sannan na fito zan kulle kofar kenan sai Naji kamar motsi abayana na juya cikin sauri sainaga wata sura ta fito daga cikin duhu ta nufo inda nake.
Tun dazun nake jiran zuwan ka JARUMIN JARUMAI.
.
BAKWAI 7
.
Da wacce kuma kika zo? Na tambayi fadila lokaci guda kuma na jingina ajikin motar barcin dake idanuna ya zama tarihi a halin yanzu domin tuni nagama fahimtar fadila ta zama kamar tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba.
Nazo maka ne da wani babban labari domin dazun na fahimci wani gani gani kake yi min ka daukeni kamar wata yar iska fadila tace tana tabe baki.
Fadila abin har Yakai da bakaken maganganu.
Yama wuce da haka Hilal duk abin da nake yi ni ba mahaukaciya bace nasan abunda Nakeyi tayi shiru tana maida numfashi
Babana yayi min bayanin duk abubuwan da kuka tattauna dashi jiya banyi mamaki ba sa'ar da nazo ofishin ka naga kana neman ka wulakanta ni ashe tallata maka ni akayi.
Cool down fadila nace da ita rabi da turanci rabi hausa.
Anki ayi cool down din da asama nake ta ci gaba da huci agabana.
Ka dubi da kyau Hilal tun daga sama har kasa kaga makusa ajikina?
Maganganun ta sun fara bani haushi dan haka sainace.
Azahiri dai kam ko shakka babu baki da makusa amma a badini kuma fa...
Ta yamutse fuska.
Abar kaza cikin gashinta Hilal a kare wanne ne ba bare ba ku yanzu yan fim har kuna da bakin da zaku bude kuce wa wani dan iska? Kai yanzun nan Hilal kana tsammanin kai waliyi ne? Yan mata nawa kuka bata a harkar shirin fim
[06:34, 1/31/2018] +234 806 858 0203: ALAKAKAI-25
.
(m) Nazir Adam Salih
.
(c) Yarima Gangariya
.
Yan mata nawa kuka bata a harkar shirin fim?
Kada kice haka fadila ba duka aka taru aka zama daya ba.
Fadila ta zabura cikin fushi kamar zata hau ni da duka
Kasani Hilal na kasance daga cikin dubban yan matan da Allah ya jaraba da son karance karance da kallon Fina finan hausa wannan ne ma tasa duk inda akayi wani gangami na yan shirin fim sainaje gurin ba don komai ba sai kawai don na ganku Abin da baka sani ba shine ba dade da sanin ka abin da yasa ban taba tunkarar ka nayi ma magana ba shine girman kanka musamman ma a lokacin da kake kan ganiyar tashen ka..... Na katse ta.
Fadila duk naji kiyi hakuri don Allah kibar zancen nan mu rabu lafiya Wallahi barci ne a idanuna kamar na fadi nakeji. Tsaho lokaci tana nan tsaye tana ta kokarin dannan bakar zuciyar ta dake ingizota akan dokan danasani.
Dole ne na fada maka tarihina Hilal dole ne na fada maka.
Domin ka daukeni wata tambadaddiyar yar iska bayan kuma dan uwan ku ne dan shirin fim ya batani...... Bazan taba yafe masa ba har abada tafara kuka.
Aure Kam ko zan rasa miji a duniya bazan aure ka ba domin nasan har abada bazaka taba yarda dani ba.
Natafi Hilal ka huta lafiya.... Ta juya aguje ta nufi bayan gidan.
Na bita da gudu gudu adaidai lokacin da take kokarin shigewa mota.
Fadila..... Dan Allah tsaya ki saurare ni ta tsaya cak kafarta daya acikin motar daya kuma awaje.
Babu wani abu kuma da zakace dani Hilal.... Me kake son fada? Zancen naira miliyan biyar?
BAZAKA SAMI KO KWABO BA. tunda ka nuna min cewa kudin kafi so dani tayi tsaki agabana ta tsartar da yawu.
Dubi idanun ka kiri kiri babu tsoro babu kunya.
Kai yanzu har kana da bakin magana?
Aure ne bazan aure ka ba tuni nafadawa mahaifina dazun bayan nabaro ofishin ka..... Jeka ka tsira da mota matsiyaci.
Na yi taku biyu da niyyar kifa mata mari sai wata zuciyar tace dani..
Uhm. Uhm dan samari yi hankali da tangaran.
Fadila ta lura da niyya ta.
Au dukana zakayi? To Bismillah zo doki nayi tsaye kamar gunki duk kwakwalwata a yamutse.
.
Fadila ta shige motarta ta rufe kofar gararam sannan ta fizgi motar ta fice da gudu.
Jikina na rawa na nufi kofar dakina na lalubi dan makullin dakin dake aljihuna sannan nafara kokarin bude kofar sannan ne to wata takarda ta Fado daga jikin kwadon.
Na dubi takardar data Fado akan takalmina da farko na dauka shirme ce amma daga karshe sai zuciyata tace dani Kai duba dai...
INA shiga dakin saina lalubo makunnar lantarkin na kunna lokaci guda kuma na bude takardar dan Sako ne kamar haka.....
.
HILAL.
Me yiwuwa zaka so kasan wanda yayi min ciki zan fada Ma sunan sa domin abin yazama wa'azi a gareka ka kuma yi hankali kada abin da ya faru tsakanina dashi ya faru tsakanin ka da sakatariyar ka na lura ita tafi dacewa ka aura. Sannan wanda yayi min ciki sunan sa (ALHAJIJI)
FADILA.
.
************ ********** *************
.
Ban isa ofishina ba sai kusan karfe goma sha biyu na rana wannan ya samo asali ne sakamakon nannuyan barcin daya daukeni.
Ahanya sa'ar dana nufi ofishina zuciyata cike take da tunane tunanen abubuwan da suka faru a gareni tun daren jiya. A lokacin ne toh.........
.
ME KUMA YAKE SHIRIN FARUWA DA KAI HILAL ?
KA RASA MILIYAN BIYAR
KA RASA TSALELIYAR BUDURWA KAMAR FADILA
.
YANZU KUMA ME KAKE SHIRIN SAKE RASAWA?
.
Ahanya sa'ar dana nufi ofishina zuciyata cike take da tunane tunanen abubuwan da suke ta faruwa a gareni tun a daren jiya. Alokacin ne na yanke shawarar zuwa a ranar nasami mahaifin fadila mu gama kashe magana yanzu kam nagama saduda dacewa nayi sallama da zama miloniya tun da dai na tabbata fadila bazata aure ni ba.
Haka ma yafi kwanciyar hankali akalla ka tsira da mota dan samari.
Toh amma sa'ar da tunanin lauriyya ya Fado min duk sai Naji hankalina ya tashi bansan inane alkiblata ba. Abu daya dai dana dada tabbatarwa da zuciyata tun adaren jiya shine na share su baki daya daga cikin zuciyata domin ita kanta lauriyya na lura akwai wani abu na rashin gaskiya dake tattare da ita.
Ina kokarin fahimtar ko wanne abu ne har har na isa ofishin.
Nayi mamakin da ban ga lauriyya a kofar tana hange hangen ta inda zan bullo ba.
Nasan ga al'ada ko goma na safe nakai banzo ofis ba zan Harare ta tana ta leke leke to ballantana kuma karfe goma sha biyu cikin gaggawa nayi fakin da motar na nufi ofishin cikin sauri gabana ya fadi sa'ar dana shiga gurin karbar bakin banga lauriyya ba nayi tsaye cak a tsakiyar dakin jikina Yabani cewa lallai ba lafiya ba.
LAURIYYA. Nakira sunanta murya a sarkake shiru ta gaida kunnuwana to amma naji kamar motsin mutane acikin ofishina. Nayi taku biyu gaba da niyyar nashiga sai Naji motsin tafiya an nufo dakin saukar bakin.
Sannu ahankali naji takun sawu taf taf taf har ta bayyana idonta sharkaf da hawaye tana ganina saita taho gareni ta fashe da kuka.
Dan Allah Hilal ka yafe ni.... Ka yafe ni Hilal.
Ta sake fashewa da kuka.
Yi Shiru lauriyya menene kum? Kuma meke faruwa? Banyi mamakin jin muryata ko rawa batayi domin Daman tuni jikina Yabani cewa ba lafiya ba lauriyya taci gaba da kuka.
KA yafe ni Hilal yau zamu rabu dakai......
Bazan taba mantawa da abun dakayi min.... Ta sake fashewa da kuka iko sai Allah nace cikin zuciyata.
Wai me ke faruwa ne lauriyya kin ki ki fada min komai sai........ Maganar ta makale a fatar bakina sakamakon wani kwakkwauran motsi danaji acan cikin ofishina.
Na juyo na dubi lauriyya nace.
SU wanene aciki? Ta dubeni a tsorace ta kasa cewa komai adaidai lokacin ne to sauran mutanen dake ofishin suka fito nayi tsaye ina duban su cikin kaduwa.
Mutanen su biyu ne daya namiji ne Kato mai doguwar kasumba yana sanye da shakwara da jamfa da wando na shudiyar shadda kai da ka ganshi kasan akwai kudi zai kai kimanin shekaru hamsin da biyu a duniya dayar kuma mace ce dattijuwa zatayi kimanin shekaru kusan hamsin. Kallo daya nayi nata na gane ta na fahimci ko wacece ita da lauriyya kamar an tsaga kara.
Sannunka da kokari bawan Allah.
Munji duk taimakon dakayi mata. Nayi saroro ina kallon su banida bakin magana matar taci gaba da cewa.
Yau shekara uku kenan muna neman yar banzar yarinyar nan.... Kwana uku ka da daura mata aure ta gudo.
Naji zuciyata ta harba akaro na farko saina kalli lauriyya nace.... KINA NUFIN KICE KINA DA AURE?
Lauriyya ta fashe da kuka sannan ta nuna katon mutumin da dan yatsa tace cikin kuka... Ka ga mijina nan....... Wai wannan katon za'a aura min katon mutumin ya kamo kafadarta ya hankadata waje tsohuwar da nake tsammani mahaifiyata ce tabi su Abaya.
.
Jikina na rawa na rufa musu baya tun kafin na karasa waje na hango wata mota daga can baya Kirar Toyota Coralla mutumin ya tura lauriyya aciki tana ta kuka tuni har yara sun fara taruwa suna kallon fim din. Cikin sauri na karasa gindin motar nace.
Lauriyya..... Allah ya kiyaye kinji Allah taimake ki katon mutumin ya Harare ni alamun tsana karara suka bayyana a fuskar sa ban zarge shi ba ban kuma ga laifinsa ba shekara ta uku tare da matar sa nasan duk duniya babu wanda ya isa ya fitar dani daga zargin sa.
Kaga malam ya isa Jeka kawai abin da kayi da ma ya isa.. Lauriyya ta yunkura acikin motar ta leko da kanta tace.
Watarana zamu sake haduwa Hilal.... Nayi maka alkawari. Nagode Allah ya saka maka.
Mutumin ya tashi motar sannan ya dubi Mahaifiyar lauriyya yace.
GATA DAI YANZU AI MUN GANTA KIN YARDA DAI YANZU BA SAYAR DA ITA NAYI BA KO?
Yana gama fadin haka sai ya sawa motar giya suka harba aguje.
Koda suka tafi sai cincirindon yaran dake kallon diramar suka rufa musu baya aguje suna shewa me yiwuwa da yake sun saba ganin jaruman shirin fim na taruwa agurin sun dauko ko wani sabon fim din aka shirya musu.
.
Kusan mintuna biyar ina nan tsaye sannan sai na juya na nufo cikin ofishina koda na shiga sai Naji shiru kamar makabarta zuciyata tayi kuna bakin ciki da takaici suka lullube Ni hakika rashin lauriyya kusa dani ba karamin rashi bane.
Ba'a dade ba sai Naji kafafuna duk sunyi rauni kamar bazasu iya daukata ba dan haka sai na nufi kujerar da lauriyya take zama a tunani wai ko zata dauke min kewa na zauna a kai ina zama sai Naji duk kasala ta lullube ni dan haka saina dauki kafafuna na dora su akan teburin sannan na lumshe idanuna na fara tunanin matsayina a yanzu.
TA LEKO TA KOMA. Nace da kaina babu Fadila na rasa lauriyya ga shi kuma nayi sallama da zama Miloniya.
Ina Nan zauna sai nafara kiyashin kudaden da ake Bina bashi. Cikin zuciyata a iya sanina ana Bina kudi kusan dubu dari shida da hamsin wani zazzafan gumi yafara sartu akan goshina.
Dole ne nasan duk yanda zanyi na biya su kudin su tun da dai wacce ke tarairayata da kwantar min da hankalin ma an dauke ta.
.
Daga inda nake zaune ina iya hangen sabuwar motar da mahaifin fadila Yabani tana sheki acikin rana nasan banida wani zabi daya wuce na sayar da motar na biya mutane basussukan su zuciyata tayi kuna tuni labari ya ya fara yada duniyar fim cewa na sake shigowa gari domin duk cikin JARUMAI maza babu mai shiga motar da takai tawa a yanzu dan haka sayar da ita ba karamar faduwa bace.
To amma banida zabi. Na lumshe idanuna sannan nace da kaina dan samari Hilal sayar da motar ka biya mutane bashin su ai zama lafiya yafi zama dan sarki ina yanke shawarar sai Naji nafara samun saukin rayuwa cikin zuciyata.
Naji wani dadi ya lullube ni sa'ar dana tuna da cewa motar zatayi tsada idan na sayar da ita dole ne na samu rarar kudin da zanci gaba da juyawa acikin harkar fim.
.
Can kuma sai wani tunani ya Fado min nan da nan na zabura ai kuwa da zan maida duk abubuwan da suka faru akaina tun daga daren shekaran jiya zuwa yau fim. Ba karamar karbuwa zanyi ba murna ta cika ni sai nafara tunanin sunan da ya kamata na sa masa. Sai kuma tunanin wahalar dana sha kafin na jefar da JARIRIN nan tafado min tabbas ALAKAKAI zan Sawa fim din
.
Kwarai kuwa cikin zumudi saina tuma kafata da karfi akan teburin sannan ne to naji wani abu ya Fado daga karkashin teburin. Cikin sauri saina sunkuya na dauka.
JAKA ne ya Fado.
Yawun bakina ya kafe zuciyata tafara harbawa cikin sauri a kwance a tsakar dakin jakar lauriyya ce data kawo min adaren jiya dauke da sarkokin nan masu tsada jikina na rawa na bude jakar.
Suna nan kamar yadda suke suna daukar idanu.
.
Lauriyya!! Nakira sunan ta cikin murna da farin ciki yanzu kam nasan bana bukatar saina sayar da motata dan biyan bashi.
.
Jikina na rawa na Mike tsaye ni kadai kamar mahaukaci nafara juya jakar dake kyalkyali a hannuna kawai sai Naji na fashe da dariya sannan Nace da kaina...
HILAL DAN DUNIYA ALLAH KE SON KA BA MUTANEN DUNIYAR FIM BA..
.
KARSHE.....