"Abinci mai Rai da lafiya suka girka,suka zuzzuba amanyan kololi,suka kai kowani Shashe,bayan sun Hada da lemuka da Ruwan gora,Su maimarta suna dai barayin gadanda suna cin nasu,ayayinda su gadanga suka hade Shida manyan Aminan nashi,Azeema ko dasu Zafira,sai su Anty mardiya da ita da Anty madina,goggo kuwa kunya takeji takasa ci,ummah mai babban daki ita kadai takecin nata,Ummah kuma ita da gimbiya Razeenah,Fasilatu kuwa babu wanda yabi ta kanta don Tunda ta Shiga ciki bata Fito ba,bayi da Fadawa ma ankai musu nasu barayinsu.
Ko kafin yammah tayi lbri ya Mamaye gari tako"ina mutane sai Shigowa suke suna ma goggo barka tare da Murna lokaci daya,wasu gulma ke kawosu,na ganin sarki da ake fadi,don wasu gani suke duk zence ne,aikuwa Maimartaba bai hana kowa ganinshi ba, yace abarsu suyi ta Shigowa yama Fi son hakan,da dare yayi maimartaba Sarkin gombe yaso Sarki Abdulnaseer yakoma masarauta,ammh yanunamai yafiso zamanshi anan,ko banza inda Suwaiba tayi rayuwa ne,ita da gudan jininsa,Shiko Aliyu yaso kebewa da Azeema ammh babu dama,yadda gidan yacika ne yasa sukayi musu sallama suka koma hotel din da suka kama ma Umar daki da safe suka kwana da Safe koda sukadawo suna cikin Shirinsu ne,don Maimartaba yace ayau din zasu kaduna sukuma biya zaria duk atare.
Inna Ramatu kunya da Nadama duk sun kamata,yau dai ga goggo data ke zagi tazama matar sarki,yau ga Aliyu datake yawon Fadin baida Asali Ashe dane,ga Sarki,da mallam lawal yadawo ya isketa tana kuka,ko kallo bata iaheshi ba,saima gyara kwanciya dayayi,yanaji tana kuka tana rokonsa wai ya roki Aliyu don Allah yasa baki Asaki Azeema wlh tayimai alqawarin bazata kara barinta ta aikata wani Abu makamancin Abunda ta aikata ba yana jinta yayi mata banza,saima Juyamata baya dayayi,Aransa yana Fadin bai yarda da Nadamar Ramatu ba haryanzu.
Koda su Aliyu suka dawo sun iske kowa ya Shirya, Nan suka iske Baba Ade tazo, yima goggo barka da kuma taya Aliyu Farincikin Saduwa da mahaifinsa,Hatta da goggo ba"a barta abaya ba ta Shirya tsab da ita,akwatun kayansu aka saka amota ita Azeema tunda zasu dan kwana biyu inji kawu,Su Aliyu ne zasu yi Tafiyar mota zuwa kaduna,su kuma sauran Jirgin maimartaba zasu bi,Gabadaya gidan aka Fito domin Tafiya su Aliyu tuni sun mika hanya Su maimartaba ne tsaye suna bankawana da su mallam lawal,sai ga inna Ramatu ta Fito daga gida da gudu ta zube gaban maimartaba tana kuka,mallam lawal kuwa yana ganinta yafara hararaart maimartaba ne ke tambayanta Meyake Faruwa tana kuka tana Fadamai kamun da Aliyu ya sanya akama Azeeza,Jinjina kai maimarta yayi kafin yace"Ash Abu baiyi kyau ba tashi tashi insha Allahu zan shashi yasa asake yau din nan.."Yake Fada yana kallon Kawu kafin yace"Bala don Allah kiramin Aliyu.."Kawu baiyi gaddama ba ya ciro waya ya kira Aliyu wanda ke gefen Jabir yana driving,Umar da Haisam suna bayan mota,da Azama ya daga kiran kawu yana Fadin"Hello kawu.."Bai yi mgana ba ya mikama Maimartaba wanda yace"Aliyu..."Yafada cikin dattako da mulki,saurin gyara zama yayi yana Fadin"Na"am Abbah,kun taho ne..? Bai bashi amsa ba yace"Yarinyar nan daka sa akama kanwar matarka kakira waya yanzu ka saka asaketa Umarni na baka ba Shawara.."gyada kai Aliyu yayi kafin yace"Angama Ranka ya dade.."Yana fada yana katse kiran,nan take yakira DSP MALEEK KABIR KUMO,sukayi mgana kafin ya bada Umarnin sakin Azeeza,nan sukayi mganar cewa bayan ya dawo yazo nan headquater su,akwai File din da zai cike nan sukayi sallama,jabir ne kawai yasan Abunda Ke Faruwa baiyi mgana ba,ko banza ai Ta horu Shegiyan.
Daganan Fadar maimartaba Sarkin gombe Suka wuce sai da sukayi sallama kafin su isa Airport,dama jirginsu na nan,Suka Shiga suka Lula sararin samaniya,Akaduna suka yada zango Tunkafin su iso mai girma gwanna Jahar kaduna * MALLAM NASIRU AHMED YAR RUFA'I yazo da kanshi ya ya tarbeshi Shida tawaganshi,Sai da sukaje gidan gwannati kafin su wuce gidan kawu,wanda ya kasance Aljannar Duniya nan kowa ya baje,don mamaken gida ne,mai Shashe har guda uku,kowanne ya gaji da haduwa,sai lokacin su Aliyu suka kariso suma,kafin isowasu Aliyu ya amsa waya tafi dari na yan"uwa da abokan Arzuka suna tambayanshi Shin Abunda suka gani gaskiya ne,da eh kadai yake amsawa,sai Barka mutane kemai da tayashi murna,daya gajima kashe wayaryi,Ko!ina na garin gombe jaridu suna ta yawo banda gidajen talabijin din da"akayita watsawa ana nuna Hoton Aliyun dana Maimartaba Sarki Abdulnaseer,Wanda jama"a dadama sunyi matukar mamaki,ciki harda da Ni"ima da iyayanta,mami tana hawaye tana kallon Cp Ahmed Sidi na Iya,wanda yayi Tsuru duk kunya ta kamasa,itako Ni"ima daki tayi dagudu Sauri tana kokarin kiran Muneera dataga ta kirata.
Kunya duk takama Kwamishana,sai zare ido yake,Mirmishi Mami tayi tana Fadin"Ka gani ko? wannan Ranar nake jiyemaka yallabai,kabiyema Sharrin shedan da hudubar dan"uwanka gashi yau kaine,akunya yanzu duk amtsayin kaje kayi gaba da gaba da Sarki,wlh ko haka Allah yabarmu munga sakayyah,Tunda diyar tamu nan harynzu agabanmu kuma tace inba Aliyu bata ba Aure har Abada.."Tana gama Fadin haka tatashi Tafice ta barshi nan yana zufa,lalle al"amarin Allah Kenan,ashe yaron ma yawuce duk Tunaninsu ashe shi din Da ne ga Sarki yanzu haka Shidin yarima ne,Lalle ya tafka kuskure babba ma kuwa.
***************
Azeema ce Tunda yammah tayi take kwance Zuciyarta da gangar jikinta babu wanda suke bukata sai Mijinta gashi kuma gidan yana cike da jama"a,ita yanzu ya zatayi kwance take tarasa mafita,Duk wanda yazo ya ganta kwance sai tace batajin dadi ne,Rasa mafita tayi shiyasa ta aika hibba data aro mata wayar Anty madina,tunda ita tata ta barta Akaduna Tun Sanda Abun nan ya faru,ana kawo mata wayar ta Shige tiolet ta kulle ta lalubo lambar Captain takira wanda suke chan Wani Shashe shida su Jabir yanaganin kiran ya daga ammh kuma sai yaji Shuru anki mgana,sake duba mai kiran yayi kai Tsaye ya Furta.."Pretty..."Yafada yana Tashi saboda su Jabir da suka Tsuramai ido,Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta shagwabe Fuska tace"Bawani pretty,Bayan Tun ranar baka kara nemana ba.."Kanshi yashafa,jin yadda ta kashemai jiki,yace"Ba haka bane pretty kema kinsan dalili aie,ammh koda yaushe kina Raina abar Farincikina.."Mirmishi ta saki tana Fadin"Da gaske..."Tafada tana dariya basar da tambayan yayi yana Fadin"Meke damunki ne,? kowani Abu kike bukatane pretty..? yafada yana Danne dariyansa,Hararan wayan tayi kafin tace"Ni bana bukatar komai..Kai..Kai ne nake son gani.."Tafada tana Rufe fuska,yar dariya yayi yana fadin"Yanzu kuwa zanzo Tunda Service yatashi yanzu an neme ni aie..."Yafada yana rike dariyansa jin ya ganota yasa tayi Saurin katse katse kiran tana dafe kirji kunya duk ya kamata.
Shiko daganan cikin gidan ya Shigo su goggo suna Falo ya gaishesu Rasa inda Azeema take yasa ya kira hibban madina ya tambayeta akunne,Nuna masa sama tayi alamar Tana Upstairs,Sosa kai ya Shiga yi kafin ya mike rike da hibba ya fara Taka Steps,dukkansu nuna sukayi basu gansa ba,kowcce ta dauke kanta,su Zafira suna ankare da yayan nasu,suna danne dariya,Sai da yakawo kofar dakin kana yace ma hibba"Toh maza koma wajen goggo yanzu zan dawo.."Jin haka yasa takoma da gudu tana murna,murda kofar dakin yayi ya Shiga da sallama,tana zaune kan gado,kanta babu dankwali tayi tagumi don bata zata zai zo ba,ganin ya Shigo yasa tadawo natsuwarta harda wani juya baya,Ganin haka yasa yayi Saurin karisawa gareta ya rikota yana Fadin"Am Srry pretty... ba gani ba.."Yafada yana Shinshinar wuyanta,Jin yafara chanzamata yanayi yasa ta saki jikinta itama ta rumgumeshi tana Shakan kamshinsa harda su lumshe,Matseta yayi yana Fadin! I miss u pretty.."Miss u more and more Yayana.."Kamkame juna sukayi kafin sufara sumbatar juna kamar wasu mayunwata,Azeema fa ba dama,domin Ture Captain tayi ya fada gefe tabishi ta danne tana wani kallonsa ta gefen ido,idonsa ta sa hannu ta rufe kafin ta hau zare kayan jikinta bata barshi ya bude ido ba,sai da yaji tana zaremai Rigar Shirt din dake jikinsa,Bai yi gaddama ba ya taimaka mata suka cire duka kayansu blanket ya jamusu suka Shige,Yau Azeema da zafinta take kai Farmaki Shiko yana Neman kare kansa,kafin kace kwabo an lulu barnin da bakowa ke zuwa ba Sai me rabo,.
Tsawon minti talatin kafin su samu Natsuwa Rumgumeta captain yayi yana saka mata albarka domin Duk sanda zai kusanci Azeema ji yake babu bambamci da daren Farko,abunka da mai Shigar ciki tare sukayi wanka kafin yayi wanka tsarki ya fito ya barta itama tayi,kayan jikinsa ya maida,sai lokacin kunya Abunda suka aikata ya Shigeshi yanzu taya zai iya Ratsa mutanen falon ya Fita haka dai ya kukan Kuran Fita,domin alokacin anata kira kiranyen sallar mangariba,Yana Fitowa yaci sa"a babu kowa afalo,sai su hibba suna wasa,Da hanzari ya sauko ya Fice,yana Fitowa yaci karo da su Haisam suma sun Fito zasu masallaci,suna ganinshi suka tsaya suna kallonsa yake yayi musu yana Fadin"Muje mana,ba sallah zaku ba.."Haisam ne yace ahankali"Kayi wanka kuwa..? zaro ido yayi kafin yace",Wankan me? Jabir ne ya duke yana kallon Umar kafin yace"Wankan Janaba mana.."wani dogon tsaki Aliyu yaja yana fadin"Janaban Ubanka,kudai yan iskane idonku na kan Sunnah kuna saka ido,kuka sani ni banda lokacinku kunga tafiyata. "Yafada yanayin gaba,suko suna mai dariya,Umar dake gefe yana dariyan yadda yaya Captain din ya hade rai,wai shi dole tsare gida har sukaje masallaci bai kulasu ba wai shi adole bayasaon Raini,cikinsu maimartaba dasu Kawu ya Shige dasuka mai mgana yace"Gaskiya ya lura zaman dayake acikinsu ma zubar dakaine,a mtsayinshi na magidanci mai mata harda ciki,sukuma amatsayinsu na yara kaskancine,kawai su kama kansu shima yanzu zai chanza taku ne,gwara yafara zama cikin manya Shine mutumcinsa"baki Haisam ya rike yana fadin"Kut..Kai wai ban girmeka ba..?"Wani banzan kallo Gadanga ya jefamai kafin yace"Koda ka girmeni ai baka halliceni ba.."Yafada yana wucewa ya barsu suna zaginsa shida jabir,Aransa yace",Na bar kara zama cikin yara daga yau.."yafada yana yar dariya😜😹
Tun Adaren Aliyu ya samu kiran Ni"ima Tana mai murna,bayan itama harda mahaifiyarta tabamawa mami,wacce ketayashi murna itama amsa musu yayi kafin yayi musu godiya suka yanke kiran,Shuru yayi yana Nazarin wani Abu kafin ya saki ajiyar zuciya yana ayyana Abubuwa dadama.
Washegari suka wuce birnin zaria,A Fadar maimartaba suka yada zango,Maimartaba sarkin zazzau yaji dadin wannan ziyarar ta Sarkin Agadez maimartaba Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,yace dama yaji lbrin zuwansa bai zaci zai zo har Yankinsa ba,An gaisa cikin mutimci sosai kafin wasu jawaban su biyo baya,Maimartaba sarkin zazzau yayi mamaki wai sarki guda ya zauna agarin zaria abaya,lalle Allah mai hikima da kari,su jabir kam sai zagaye masarauta suke,suna fadin"daliin kaza gadangare kansha Ruwan kasko,yau gashi dalilin gadanga sun shiga masarautu dadama,haka su madina ke Fadi,ummah ko baki yaki Rufuwa godema Allah kadai take,domin dalilin goggo sun taka in ba basuyi tsammani ba,daganan Fadar tare da rakiyar Adalin Sarkin zazzazu suka iso anguwan dasu Goggo suka zauna,Allahu akabar Asalin gidansu nan nan kawu ya gyarashi yasaka wasu mutane suna zauna don Allah,saboda su kula da gidan karya lalace,zuwansu gidan yasa Sarki da Suwaiba suka tuna wasu al"amura da suka gabata inda dakinshi yake awanchan karon yanzu wajen ne aka kafa famfo,Maimartaba ya kurama wajen ido,hawaye suna taruwa a idonsa hakama Goggo,mutane anguwa kuwa da lbri ya samesu sunyi matukar mamaki,akwai dattawa dake da rai haryanzu,sai kuma wadanda suka samu lbrin bayan abun ya Faru,basu jima ba suka koma masaurata Tunda Allah ya wanke suwaiba da Da'nta,daganan kaduna suka dawo saboda Shirye Shiryen Tafiya chan Masarautar Tambari buzu ammh bayan An maida Auren goggo.
Kawu da Maimartaba basuyi Shawara dakowa ba,washegari bayan sallaar Jumma"a aka maida Auren goggo da Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,akan sadaki dubu Dari biyar,wanda awajen Daurin harda Maigirma gwannan jahar kaduna,Wanda aka daura amsallacin Sultan bello,Yan mazan ne kadai suke da masaniya sai da suka dawo gida suke Fada,goggo jitayi Abun yayimata wani banbamrakwai daki ta Shige tarufe kanta ganin yaran sun Faramata shakiyanci da Amarsu😛,Gimbiya Fasilatu kam dataji lbri kamar ta mutu takeji ga Danta Shima gabadaya taga baya tsaginta yana manne da dan'uwansa kamar wani zai rabasu,ga gimbiya Razeenah itama ko ajikinta harda ita cikin masu cewa agyara musu goggo,don so suke maimartaba ya rude fa😿Ummah mai babban daki kuwa wani lokacin tafi zama cikin Su Jabir kodon yadda take sakasu dariya,suko su Zafira basu iya saakewa ciikinsu saboda yadda su Haisam da jabir ke damunsu da kallo,Umar ne ya lura har ya shafama Aliyu,dariya takamasa yana fadin"Daz great,karabu dasu lalle wasu yara zasu dawo cemin babban yaya"Yafada yana dariya har ga Allah Abun yayi mishi dadi ko banza zai samu hanyar sakamusu da Abunda sukayi mishi,kuma zumuncinsu zai kara karfi fiye da Da.
Washegari kawu ya umarci Ummah da Goggo da Azeema da Aliyu su tafi gombe su tattara kayan goggo,tayi sallama da mutane saboda jibi zasu tafi chan masarautar Agadez,Gimbiya Razeenah ma tace zata,nan su Zafira sukace suma wlh sui sunje suna makale da princess dinsu,Mota biyu sukayi daya Aliyu ke driving tare dashi Umar,sai baya kuma Ummah da gimbiya Razeenah sai Goggo,dayan motar kuma Haisam da Jabir sai Azeema da Su zafira,wadanda su Jabir suka dinga jansu da zence,itako Azeema sai dai tayi musu mirmishi,suko yan matan basu saba ba duk kunya sukeji,Aliyu ko bini bini ya kira Jabir awaya yana fadin"Subi mai mata da kanne a hankali in ba hakaba ya hana abasu auren"Shuru sukayi suna Tunanin kashinsu ya bushe Tunda yaji lbrin ai sufa sai Abunda suka gani.
Sun isa gombe lafiya,su ummah suka Shiga gidan suka fara hadama goggo kayanta masu amfani,itakuma goggo tafara Shiga makota sallama,suna sallama tana kuka,sune har gidan Baba Ade,wacce itama tayi damara tace wlh da ita za'a Raka goggo masarauta😜goggo ko taji dadi tace ta Shirya su koma kaduna tare,kai goggo mai jama"a ce haka layi yacika,duk gidan data Shiga sai sunyi kwallah rabuwa da goggo Shekaru wajen talati sai yau kwatsam ace za"a rabu,toh basu da yarda zasuyi Tunda yanzu goggo ta wuce da saninsu matar sarki guda,Anan sukejin lbrin dawowar Azeeza goggo taja hannun Azeema suka Shiga cikin gidansu,Wlh da goggo da Azeema da sukaga Azeeza basu iya ganeta ba,saboda yadda tazama wata kamar kwarangwal duk kiban nan bata yanzu ta rame ta lalace tayi baki sai wasu kuraje afuska,ta kode ta lalace tana kwance kan tabarma daga ita sai daure gaba tana wani numfashi ba dadin ji,dukawa Azeema tayi gaban Azeeza tana kallonta tana hawaye take Fadin"Azeeza..Kice kika koma haka meyafaru dake? Inna ramatu dake gefe ne tace tana hawaye"Haka Aka dawomin da ita Azeema,ashe tun kamata da"akayi take rashin lafiya,ciwo ba"asan daga ina yake ba,tunda dai tadawo take kuka da kirjinta sai kuma ciwon kai mai tsanani,tabari muje asibiti,taki bari bansan me take so amata ba.."Kuka share share Inna Ramatu take tana durkushe gabansu goggo tana fadin"Don Allah Azeema da goggo ku taimaka kumin aikin gafara,wlh harda hakkinku ke bibiyanmu,na kyamaceki na wahalar dake,ke kuma goggo nabata miki suna sosai agari na cewa Aliyu bashi da uba gashi yau Allah ya nunamin iyakata,Ga Azeeza itama wlh harda hakkinki Azeema don Allah ki yafemata.."Tafada tana kuka,kamar zata Shide Azeema kuka take tana rike hannun Azeeza wacce ke miko hannu tana so tayi mgana Rikota Azeema tayi tana fadin"Sannu Azeeza Allah yabaki lafiya na yafemiki Duniya da lahira.."Tafada tana hawaye hakama goggo ta riketa tana jadadda yafiyarta,suna nan durkushe sai ga Mallam lawal sun Shigo Shida su gadanga,Shikanshi Aliyu dayaga Halin da Azeeza ke ciki sai da ya kauda kai,jabir ne yafara Fadan meyasa ba"a kaita Asibiti ba,Mallam lawal ya amsa da fadin"Ba inda zan kaita indai da kudina ne,kubarta tana girban Abunda ta Shuka ne.."Goggo ce ta katseshi da Fadin"A"a mallam,kada kace haka itama ya'ce kamar kowa,kuma tayi nadama don Allah ka yafemata"Jin sun saka baki yasa yace ya yafemata,Azeeza na kwance tana kallon Captain Aliyu tana hawaye,domin duk inna tabata lbrin mahaifinsa da duk Abunda yafaru,hawaye take tare da nadamar Abunda ta aikata,gashi yanzu tana ji ajikinta mutuwa zata yi,ammh kuma zata mutu da soyayyar Aliyu aranta domin ba ita ta dorama kanta ba,Aliyu ya Furta yayafemata,ammh fa Susinshi baijin zai iya badawa,Azeema ce tabata Dubu hamsin,wanda cikin kudin da kawu yake bata in yazo take Tarawa,Haisam da tsausayi,shima 50k yaba Inna Ramatu yace akai Azeeza Asibiti Allah yakara lafiya,Shidai jabir da Aliyu sisi basu bada ba,don aransu ma dadi sukeji ko banza anrage mugun iri,sallama sukayi musu suka Fito,inna ramatu har kofar gida kamar zata kwanta musu saboda godiya,nan nema goggo tace su Mallam lawal su tashi su dawo gidanta da zama ta mallaka musu halak malak,in Kawu sun dawo zai sa azo abuge gidan nasu ahade musu da wannan,Hakika mallam lawal yaga karamci,domin nan take maimartaba dake chan yace asanar da mallam lawal An biya musu kujeran makka,shida matarsa ai inna Ramatu harda Faduwa saboda taji Abun abazata ne,oh Duniya yau ga wanda ta wulakanta,sune gatansu Ashe,godiya sukayi ta zubawa kamar ba gobe,goggo ko tayi rabon kudi sosai,haka mutane suka cika bakin motarsu suna Fatan Allah ya kaddara saduwa gimbiya domin dai sun san,cewa kila sai dai kuma a lahira,koda suka bar anguwan haka goggo ke kuka babu wanda ya nemi hanata domin sabo yawuce komai,shikanshi Aliyu da bai cika zama ba, yau yaji Jikinsa yayi sanyi da barin gombe koba komai cibiyarsa ta haihu tana Gomben,ammh kafin sutafi saida ya biya mkrantarsu Azeema sukayi mgana da principal din,cewa Azeema zatayi tafiya,koza"a samu wacce zata cigaba da rubuta mata jarabawan kan tadawo,da hanzari ya amsa mai da za"a samu,kudi mai yawa Aliyu ya bashi sukayi sallama,bayan ya damka mishi Exam card din Azeema wanda yakarba Ahannunta.
Koda suka dawo kwana daya kadai suka kara suna kamallah Sauran Shirye Shirye,Hatta mazajensu Madina sunce dole suma su nemi Yarda awajen aikinsu suma suzo Awuce dasu domin fa dama daya take zuwa arayuwa,goggo ko Ummah ta isheta da kayan gyara itako goggo kunya tana fadin"Umaima wannan Abun kunyar har ina,tsofai tsofai dani,shima fa Maimartaba din ya tsufa don Allah kubarni haka"Ummah tace"haba goggo Shikenan kuma shi Tsoho bayason jin dadi,shima fa yasan dadi,nidai don Allah koda munje chan kisaki jiki,keda maimartaba ku Famshe Riban soyayyarku wanda baku fanshe ba abaya don Allah.."kallonta kawai goggo keyi tana dariya,su madina ko suna taya Ummah Rokon goggo,,Hatta Azeema ba"a barta abaya ba,ta Shige sawun masu son maimartaba ya samu chanjin yanayi😜😂Dole goggo ta yarda tana amsa komai aka bata tana ci,to ya zatayi Allah ya hadata da yaran zamani.
Takowani bangare Shiri yakamkama,Washegari karfe 10:00am na Safe jirginsu yatashi Abirnin tarrayyah Abuja,tunda sai dasuka Koma Fadar gwannati,maimartaba Sarki Abdulnaaeer yayi godiya da Shugaban kasa,kafin su wuce zuwa kasar Niger cikin babban Jirgin da suka zo dashi daga masarauta,Tafiyar data hada mutane dadama,Maimartaba da iyalansa,wadanda suka zo sai su kawu,Ummah,da Su Anty mardiya kowacce da mijinta da yayansu,sai jabir da haisam da Aliyu da Umar,sai goggo da Azeema da Baba Ade,Sune jirgin ya diba zuwa babbar Masarautar Tambari buzu wanda Tuni Lbri ya iske Masarauta cewa maimartaba na bisa hanya Shida duka iyalansa tare da wani Abun mamaki wanda zai bayyanama Masarauta.
_Ina godiya da Addu'o'inku...Ngd Sosai Allah yabar zumunci da zaman Tare..._
*Janafty*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*O Allah, You are the only supreme being worthy of worship, We associate no partners with You and only from You alone we seek for Guidance, Protection and Forgiveness for our sins. Ya Allah save us from the Darkness and Loneliness of the Grave, from the Torments of Hell Fire and finally make Jannatul Firdaus our final abode, Amin. Juma'at Mubarak!*
*Chapter 35*
"Koda Su Aliyu suka isa barrak,sun tararda angama dukkan Training din da za"ayi har anfara Tura sojoji zuwa yanki da ake tashin hankali domin kwantar da tarzoma,suma din sai da suka nemi izini,kafin abarsu su Tafi suna dawowa babu wani tsaiko aka Turasu kowane da bacth dinshi Captain Aliyu An hadashi da wasu sojojin Cameron ne zuwa Maiduguri ayayinda Jabir aka Hadasu da sojojin Chadi,zuwa yobe,shikuma Umar da Sojojin Nageria aka hadasa zuwa Kaduna adajin nan na birnin gwari ma"ana dogon dawa,babu wanda aka hadashi da wanda yasani Tafiya ce ta taimakon kasa da kasa saboda haka babu gudu babu ja da baya,kwana daya sukayi kafin suyi sallama da junasu kowannesu yabi tawagarsu suKa dauki hanya,Dukkansu kowani yatafi da niyar Taimakon kasarsane,dakuma Matakinsa na soja da kuma alqawarin da suka dauka na kare kasa da al'ummah dake cikinta,barikin gabadaya tayi rakwa rakwa gabadaya Rabi da kwatanta duk basu sai wadanda ba"a rasa ba sudin kuma sun kasance suna kasa ne,sosai basu gama sanin wasu dabarun yakin ba.
Ko kafin kace me,Kafafen yada lbrai sun watsa wannan lbrin na Tafiyan wadanan sojojin tare da rokon yan Nageria da su mika godiyarsu ga Kasar Niger da cameron hade da chadi bisa kokarin kawo musu zaman lafiya da tsaro akasarmu ta nageria,haka Aka dinga nuna hotunansu tare da tawagar kowanne,ciki ne da kuma rokon barar addu"ansu garesu na Allah ya basu Nasara suje lafiya su dawo lafiya,Ni"ima taga gwarzonta harda kuka sai da tayi tana mai Addu"ar Allah ya dawo dashi lafiya nan tayi alkawarin duk sallarta sai ta sanyashi ciki,dukkansu sojojin babu wanda yatafi da wata waya ahannunsa sai dai wayar tsaro,wanda zasu dinga mgana da junansu in wani abu yafaru,ko kuma su kira bariki in suna bukatar wani Taimako.
***************
Inna Ramatu da Mallam lawal sun tattara sun koma gidan goggo da zama Duniya sabuwa mai tattare da Farinciki,Inna Ramatu in ta tuna Abunda tayi ta aikatawa ga goggo da Aliyu sai taji kunyan gashi yau tana raban Arzikinsu,Azeeza kuwa bata kowa take ba,sai ta kanta domin Jikinta gabadaya ya rikice shiyasa iyayan nata suka kwasheta suka kaita general hopital inda nan take aka bata gado,tare da wasu gwagwaje,sai gashi gwajin farko angano Azeeza ta dauke da hawan jini,kuma jininta yayi mugun hawa sakamakon ta sakama kanta damuwa,toh tayama Azeeza bazata damu ba,tabiyema Sharrin Shedan da Duniya gabadaya,Sai daga baya take ta Nadama da Danasani,da"ace tayi yaki da zuciyarta bata biyema Rudin Duniya ba da yanzu bata cikin wannan Halin koda Allah bai yayemata soyayyar Yaya captain ba,toh zai yayemata kaso mafi yawa acikinta,kila ma harta samu miji gangariya tayi aurenta bayan tana zaune lafiya da yar"uwarta mai Sonta Adda Azeema,gashi yanzu komai ya lalace duk Burinta babu wanda ya tabbata,Tun Aduniya tafara ganin ishararta inga Randa muka tashi gaban ubangijinmu,ayanzu haka Azeeza tafi kaunar Mutuwa fiye dakomai domin Tasan kotarayu babu amfani ga Rayuwarta domin hatta mahaifinta ya tsaneta,kuma da wani ido zata cigaba da kallon mutane bayan Duniya tagama sanin Duk Abunda ta aikata.
Ammh duka wannan halin data Shiga batabama kowa laifi ba,sai Mahaifiyarta Inna Ramatu,don Tun tasowarta inna bata taba kwabanta ba akan tayi ba daidai ba,kullum goyon bayanta take,koda Abun nan kuwa bamai kyau bane,Inna zata mara mata baya,bata taba koda zaginta domin gyaran Tarbiyanta ba,duk halin data Shiga ayau inna ce Sila domin Baba yana iya bakin kokarinshi wajen basu tarbiya,ammh sakamakon Inna ramatu ya isa gabadaya bata ganin Baba da mutumci,duba Adda Azeema bata da uwa,ammh kalli irin kyawawan dabi"unta da kuma hakurinta da sanyin Halin ta,ammh ita datake uwa ammh bata mori kowanni hali ba sai na mugunta,lalle Rashin Tarbiyama ma wani babban ginshikine sosai ga rayuwa yayanmu na yau da kullum.
Ranar data kwana biyu Asibitin jikin yayi zafi sosai take jin jikinta,Mallam lawal dayazo yana haraman Tafiya Azeeza takirasa da muryan ciwo.."Baba...? tafada tana mika masa hannu,matsowa yayi yana Fadin"gani Azeeza me kike bukata? yafada yana rikemata hannu,runtse ido tayi hawaye suna zubomata tace"Bana bukatar komai sa Yafiyanka baba,hakika na kasance yarinya marajin mgana wacce batabin umarninka ko kadan,ka Furta ka yafemin domin bana ji zaka dawo ka sameni.."Tafada tana kuka sosai,daga inna har mallam lawal jikinsu yayi sanyi Rike hannunta yayi yana fadin"Kiyi Shuru Azeeza kibar Fadin haka mutuwa da rayuwa duk ta Allah ce,mganar yafiya kuma nadade da yafemiki Azeeza Allah yabaki lafiya.."Yafada yana sharemata hawaye,mirmishi take mai har yayi musu sallama ya Fita,inna dake gefe ta rafka tagumi tana Tunanin makomar rayuwarta,Taji Azeeza ta kirata da dan karfi tashi tayi ta isa gareta tana Fadin"Gani Azeeza mekike so? Hannun Inna ta riko tana Fadin"Babu komai Inna,kawai wata wasiyya zan bar miki,koda bayan Raina don Allah inna kada ko bayan kin kara haihuwa kiyimata ko kiyimishi irin tarbiyan dakika bani,ki kasance uwa tagari ga ya"yanki don samun Rabauta ranar gobe kiyama.."Tunda Azeeza Tafara mgana Inna Ramatu ke kuka,tana fadin"Tabbas nazama banzar uwa,na kasance shashasha da na kasance lamba daya wajen Shigarki wannan Halin,Don Allah Azeeza ki yafeni don Allah,wlh na tuba,kuma nayi miki alqawarin zama uwa tagari,tare da zama mace tagari ga Abbanki.."Dukkansu kuka suke bamai lallashin wani Azeeza ce tafara tari mai karfi,inna tana kokarin Tashi taje takira likita Azeeza ta rike hannunta gam tana Fadin"a"a inna karki Tafi,ki tsaya kiyimin kallon karshe don in kika tafi baza ki dawo ki ganni da rai ba.."Inna Ramatu da jikinta yayi sanyi Tafada jikin Azeeza tana kuka,wanda take ta tari tana Numfarfashi,Ganin idonta na kafewa yasa inna Saurin Maimaitamata kalmar Shahada cikin ikon Allah Azeeza ta karba batama karisa ba idonta ya kafe sama jikinta ya saki.
Innalillahi wa"inna Alaihirraju'un,Kullu Nafsin za"ikatul Maut,kowani mai Rai sai ya dandani Dacin Mutuwa,yau dai ga Azeeza ta amsa kiran mahallincinmu Tatafi da duka burinkanta da mafarkanta Allahu akbar Shiyasa akace ka Shuka alheri kodon Watarana bakasan Yaushe zaka mutu ba,Inna Ramatu Kuwa tayi Tawakalli tare da Azeeza ta kwana har sai da Asuba ne ta kira mallam ta sanar dashi,cikin tashin hankali yake kiran sunan Allah,Gabadaya jikinsa yayi sanyi yakara tsorata da rayuwa Fadi yake Aransa Na yafemiki Azeeza Allah ya karbi bakuncinki.
Sai da gari ya waye Mallam Lawal yazo akayi cike cike aka basu Gawan Azeeza suka zo da ita gida,Lokacin mutuwar ta Azeeza tagama zagaye gari kowa sai Fatan dacewa yake mata,Ba"a dauki wani lokaci ba Inna Ramatu da kanta tamata wanka ta Shiryata aka dauketa Akayi mata sallah,Aka tafi da ita zuwa gidanta na gaskiya,Allah sarki Rayuwa kenan komai yayi Farko yana da karshe gashi yau Azeeza an tafi an bar Duniya an kaita an Turbeneta daga ita sai Halinta,sai Fatan muma Allah sa mucika da imani AMEEN.
Mallam lawal ya kira Kawu Bala da kanshi ya sanar dashi Rasuwar Azeeza,salati ya dingayi Abun ya tabashi,haka daya sanar da Ummah itama ta shiga sallallami tana Fadin"Kaji Abun Allah ko,yanzu Duk Abunda tagamayi Ashema ba rayayya bace kai wanda bai bi Allah da manzonsa ba awannan Rayuwar wlh yaji takaichi Allah ya jikanta da Rahama"Kawu ya karba da Ameen da Ameen,Ummah ita takira su Madina ta sanar dasu Rasuwar Azeeza,su kansu Mutuwar ta dakesu,nan sukace in Su Ummahm zasu don Allahu su sanar dasu suma su bisu suma mallam lawal gaisuwa.
Kawu da kanshi ya kira Maimartaba Awaya ya sanar dashi Abunda ke Faruwa,lokacin suna tare da goggo ya mikamata wayar Kawu bala ya sanar da ita Rasuwar Azeeza,mikewa goggo tayi tana Fadin"innalillahi wa'inna Alaihirraju'un Yaya Wata Azeezan? yace"Azeeza dai kanwar Azeema diyar mallam lawal"Dafe kai goggo tayi Tana Fadin"Allahu akbar kabirin ashe Ashe ganin karshe mukayi mata nida Azeema,kai Allah kabamu mutuwar Shahada,Allah ya karbi bakuncinki Azeeza"Kawu da Maimartaba dake zaune suna karbawa da Ameen,
Dauke kwallar data zuboma Goggo maimartaba yayi bayan Kawu ya yanke kiran,Kanta ta dora bisa kafadansa tana Shesshekan kuka,babu shakka mutuwar Azeeza ta daketa,mutuwar matashiyar budurwa ko bakomai Yadda ta dauki Azeema ya'haka tadauki Azeeza,Allah yajikanta da Gafara,hannu maimartaba yasa ya Rumgumo goggo yana buga bayanta alaman lallashi yake Fadin"Shiii..Kibar mata kuka hakan nan,mutuwa fa dole ce gimbiyata,addu"an mu kadai take bukata yanzu plz wipe ur tears"Yafada yana dago Fuskarta,Tirr na kame gefe ina kallon Salon soyayyah manya bansan sanda na saki ihu ba ina Fadin Allah dai ya biya Ranka Shidade😂
Goggo ta dago tana riko hannuwan maimartaba tace"Yallabai na😱😹Bakowa nake Tunani ba sai Azeema kaga fa ga Halin data keci yanzu ya zataji in taji mutuwar kanwarta wacce ita kadai gareta"Ajiyar zuciya maimartaba yayi kafin yace"Hakane karki damu da wannan ki kiramin ita ni dakaina zan sanar da ita.."Yafada yana kallon kwayan idon goggo,wacce tawuce luu,zuwa kirjinsa tana share kwallarta Shiko yayi Saurin tarbanta yana Bubbuga bayanta alamar lallashi domin yakijinin yaga goggo cikin damuwa,Gimbiya Fasilatu data Shigo Turakar maimartaba yanzu,tun da zata Shigo Fadawan bakin Shashen suka sanar da ita Gimbiyar Mata fa tana ciki,saboda haushi ko sauraransu batayi ba,ta Shigo ciki kai tsaye,aiko tayi mugun gani,har tagama Tsayuwarta basu san da kafuwarta ba,kishi ne ya Rufemata ido yasa ta Fice da hanzari tana share kwallah,ahanya taci karo da gimbiya Razeenah ita da bayinta zata shashen Ummah mai babban daki,tana ganinta tayi Saurin daidata fuskarta,wanda ta riga ta makaro tuni ta gnta,sai da sukazo gota juna kana gimbiya Razeenah tace mata"wlh kina wahalar da kanki Fasilatu,kinfi kowa sanin yanzu baki da wani Fada gun maimartaba,dama fa arashin uwa ne akanyi uwar daki,in ma zaki kama kanki ki kama,in kuma zaki cigabane toh bismillah,iskane zai cigaba da Wahalar da mai kayan kara.." Tafada ahankali yadda babu mai jinta sai ita gimbiya Fasilatun,tana gama Fadin haka ta wuce ta barta nan tana cizon yatsa
Goggo da kanta taje har Shashen Azeema ta taho da ita har Turakar maimartaba,in kuka ga Azeema alokacin sai kun mata kuka,saboda yadda ta rame ga cikinta ya fara Fitowa azahirin batu tana Fama da kewar mijinta,gashi ko awaya ba"a samunsu,hakama suma Zafira ma take cikin damuwa,don Safaratu kadai ke waya da Haisam suko su biyun Shuru ne kawai,Maimartaba cikin lallashi da nasiha ya sanar da Azeema rasuwar Azeeza,Tashin hankali wanda ba"a sakamasa Rana,haka Azeema ta mike jikinta na Rawa Tana Fadin"Azeezar ce ta rasu? take Fada kamar ta fita daga hayyacinta goggo ce tayi Saurin mikewa ta rikota ta rumgumeta tana lallashinta,kuka sosai Azeema take tana Tuna Fuskar Azeeza data gani na karshe,Tayi kuka kamar Ranta zai Fita,kome Azeeza tayimata wlh bata taba jin tadaina sonta ba,jininta bata da wata yar"uwa data Fita,haka wuni kuka tana rarrashin kanta ita kadai,maraici ya lullubeta babu uwa babu uba akusa ga rashin miji ga Rashin yar"uwa Duk lokaci daya Haka dai ta rarrashi zuciyarta harta kira Babanta tayimai gaisuwa tace ya bama Inna Ramatu wayar tamata gaisuwa,inna Ramatu najin sallamar Azeema Tafashe da kuka,ai sai itama Azeema tacigaba da nata,saboda yadda suke koke koke ne yasa mallam lawal ya karbe wayan ya kashe saboda ya lura cikinsu ba wacce zata iya mgana alokacin.
*BAYAN WATA UKU*
Lokaci yayi Ta tafiya ayayinda Abubuwa dadama suka Faru ciki harda samun Nasaran dawowar Tawagarsu Umar,tsakaninsu da Tawaagar su Jabir kwana goma ne,Kuma Alhamdulillah an samu nasorori dadama,ansamu Kashe kashen rayuwa wasu sun Raunata gaskiya ammh Tunda ansamu Abunda Ake nema Shikenan.
Iyaye da yan"uwa da abokan arzuka sunyi murna da dawowar ya"yansu lafiya,Jabir da Umar sunyi Farinciki sake haduwa da juna abunda basuyi tsammani ba ballatana Fata,yanzu Fatansu suga dawowar tawagarsu Aliyu wanda ta kasance kusan itace ta karshe bata dawo ba.
Daga chan Masarauta kuwa murna sosai akayi tayi da shagulgula na Dawowar Yarima umar,ammh duka fa zuciyoyo suna cikin Fargaba na Rashin samun wani bayani game dasu Aliyu,ammh an dage da addu"an Allah ya dawo dasu lafiya,Abun da ke Faruwa shine tun watansu daya da tafiya aka daina jin lbrin su kwata kwata awaya balle aji lbrin hadin da suke ciki,an kuma sake Tura wasu sojoji suma dinma dai haryanzu Shuru kake ji Topha Abun fa yafara Zama Abun mgana saboda dai Abun yaci ace in lafiya lafiya Toh sun isa suma su dawo alokacin
Lokacin da Azeema taji lbrin Dawowarsu Umar ammh babu Mijinta aciki sai fa hankali ya tashi rai ya dumguzuma,bata da aiki sai kuka ga cikinta lokacin yashiga watansa na bakwai takara girma da Cika gashi cikin yana da girma sosai,tuni ya Turo gaba kamar cikin wata Tara,sukansu maimartaba karfin hali ne ke tafe dasu ammh fa sun Fara sarewa,Su Umar suna Nageria haryanzu domin ana kokarin Shirya wata tawagan ne zuwa chan maidugurin aje adubo ko lafiya don Shurun yayi yawa.
Kwatsam sai ga wasu daga cikin Tawagansu Aliyun sun dawo ammh babu Aliyu aciki da wasu daga cikin tawagan sojojin su Tara kaf,Sojojinn nageria su hudu,hudun na Cameron ne,kuma kowannensu shugabannunsu suna alfahari dasu sakamakon dukkansu zarata ne kuma jarumai ne,koda suka dawo aka tambayesu ina Sauran yan Tawagansu nan suka bada lbrin cewa wata daya daya wuce yan boko haram sun Farmakesu a sansaninsu dake Sambisa,inda sukayi bata gashi dasu,toh Lokacin an samu rabuwar kan Sojojin,akwai wadanda aka kashe ckin dajin kuma su basuga gawarsu ba,bayan komai ya lafane suka nemi wadandan Sojojin suka rasa ciki kuma harda shugaban Tawagan Nasu Captain Aliyu Tambari buzu,to kuma tun lokacin suka rasa wayoyinsu na mgana zuwa headquater kai tsaye,lokacin da wasu tawagan suka sake zuwa ,sai suka sake sabon Shiri,shine dalilin yin nasaran Cafke yan boko haram har su goma sha bakwai,Sungama duba ko",ina ammh babu gawarwasunsu toh suna kyautata zaton cewa kila sun kamasu ne,sun tafi dasu chan wani waje dabam kuma inda babu wanda ya sani sai su.
Wannan labrin yatadama gwannatin Nageria hankali ba karami ba,Su Umar da sukaji lbrin kuka reras sukayitayi Shida Jabir,basu da karfin gwiwan zuwa da wannan lbrin gida saboda zuciyoyo sun Raunta Ainun,sukansu Karfin Addu"ane ke Tafe dasu,nan da nan Cheif of Staff,yabada sanarwan Shirya jiragen yaki masu dauke da Na"urori zuwa Dajin na Sambisa Domin Ceto Wadanan Sojojin don Kasa bazata barsu su salwanta ba,duk da suna kyautata zaton samun Araye.
*Janafty
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*Chapter 36*
"Washegari Sojojin suka yima Dajin Sambisa tsinke,wannan karon harda manyansu atare, dasu bayan su Umar da Jabir da Sauran wasu jajiratattun Sojojin,Ta jirage ne wadanda ke da Na"irorin Daukan Hoto ta kasa,ma"aikatan dake cikin Helecopter din suna ganin duk wasu kananan Abubuwan dake cikin dajin,ta Na"urorinsu,cikin ikon Allah suka tarar da wani sansani na yan boko haram din acikin chan kuryan Daji,Umarnin yin kasa akabama Jiragen bayan kowani Soja ya saka rigar iska,sun Fara sulalo wa kasa,Mamaya suka yi musu ba Shiri kawai sai dai sukaji tashin harbi kokafin su Fito da Makamansu sunyi musu kwanya harbi kota ko"ina domin Sojojin suna dayawa Suma,nan Fa akaita bata kashi har na tsawon Mintina Talatim kafin sojojin su samu Nasarar kashe wasu ammh duk da haka akwai wadanda suka kara Nausawa dajin,suma acikin Sojojin an samu Wadanda suka Raunata,ammh ba!a samu rasuwar rai ba,nan da nan suka kafa sansani bayan an Fitar da masu Rauninka likitocin cikinsu na basu Taimakon gaggawa.
Cikin katon sansaninsu da Sojoji sukayi watsawatsa dashi aka gano Sauran Sojoji 8 daga cikin wadanda suka bace,suna daure dukkansu da kacha,duk sun rame sun lalace,dukkansu babu riga ajikinsu,ko"ina tabon bulalane da sara alamar dai Suna cikin wata rayuwa,cikin azama aka kwance su aka daukesu zuwa sansanin sojojin domin basu Taimakon gaggawa Major Sadeeq Amfani ne ke Fadin!where iz Captain Aliyu Naseer..'?yake Fada Ahankalinshi take,sai alokacin Sauran Sojojin suka Fahimci babu Aliyu aciki,nan fa hankalu suka Tashi nan da nan akace su Jabir su sake bazama cikin dajin domin sake dubawa kila a dace su ganshi.
Aikuwa hakane ta Faru basuyi nisa ba,suka iske wani sansanin ammh babu kowa aciki,koda suka Farma wajen sai suka tarar da wani mutum Daure daga saman hannayensa da kasa ma an Dauremai kafafu,Shibai kai tsakiya ba,shikuma bai sauko kasa ba,kansa na sunkuye ne jina na zuba ta hanci ta baki,bayan Kafarsa ta dama daure da wani kyalle,ammh haka jini ke zuba awajen,gashi ta kumbura,Tsaye sukayi cak suna bin Mutumin da kallo,Abu daya yasa su ka gane wannan nasu ne,wandon Sojan Nagerian dake jikinsa,wanda yachanza kala saboda jini,Jabir daje tsaye yayi kukan kura yana Fadin"Dude...."Yafada da duka muryansa bude,wanda harsaida Dajin ya amsa,hatta sauran Sojojin dake baya da suka ji suka Biyosu aguje dauke da makamai.
Umar najin haka ya karisa garesa suka rikosa baya Numfashi alamar ma Asume yake,wasu daga cikin Sojojin suka fara Zagaya wajen suna dube dube,wasu kuma suka isa wajen suna kokarin kwance Aliyu,awurin kwancensa ne suka Fahimci yana da karaya biyu Akafadansa ta
dama,bayan kafarsa ta dama ta Dauke da harbin bindiga,ammh an cire harsashinsa,sai kafarsa ta hagu itama tana Dauke da karaya,sai wasu kananun gocewar kashi,kuka reras Su Umar keyi na tsausayin Halin da Aliyu ke ciki,haka suka Daukosa ko"ina na jikinsa ya saki kamar gawa,suna Fito dashi manya sojojin suka karisa garesu da hanzari Jabir ne yake sanar dasu irin Rauninka dake jikinshi,nan da nan Major Sadeeq Amfani yasa su Jabir da Sauran Sojojin su cikon 8 din da kuma wadanda suka jiggata su shiga jirgi tare da Likitocin cikinsu su koma chan Asbitin Federal Ta Abuja,domin basu Taimakon gaggawa,su in sungama tararra komai zasu zo daga baya.
Cikin kankani lokaci aka sakasu cikin jirgin suka lula sararin samaniya,tun acikin jirgin Likitocin sojojin ke bama Aliyu taimakom gaggawa,ammh har zuwa lokacin bai farfado ba,sun dai samu daman warware kafar data keda harbi sukayimata dressing kafin su isa Abuja,shiko Chaif Amry of Staff tun suna chan lbrin ya sameshi cewa an ganosu,nan da nan suka sanar da kafafen yada labarai na Gano wadandan Sojojin dasuka bata ayayin kwantar da tarzoma agarin na maisuguri.
Suna isa Abuja direct asibiti aka wuce dasu,wanda yafi jin jiki Aliyu ne domin Shine baya cikin hayyacinsa,suko Sauran Tun acikin jirgi suka dawo hayyacinsu,Emagency aka shiga dashi domin bashi taimakon gaggawa da kuma daure karayan dake tare dashi,ga kuma harbin bindiga wanda ya dade ajikinsa don ma dai Allah yasa Tun lokacin da Abun Yafaru an cire harsashin.
Lokacin da lbrin kuboto da Sojojin dasuka bata ya zaga Duniya gabadaya Mutane nata murna,ciki harda Ni"ima wanda Tun sadda taji harda captain dinta awanda ake nema,ta Shiga tashin hankali,sai kuka ta addu"ar Allah ya dawo dashi lafiya,jin dawowarsu har saida tayi sujjudan godiya ga Allah,duk da ba"a Fadi Ahalin da suke ciki ba,an dai ce Sun samu Raunika ammh ba na tada hankali ba,suna babban Asibiti dake Abuja suna amsan Taimakon gaggawa.
Kawu Shine kan gaba wajen samun lbrin wayar Umar yakira Shiyake labartamai halin da Aliyu ke ciki hankalinsa ya tashi nan take ya biyo jirgi zuwa Abuja,Shiko Umar suna gama waya da kawu ya kira Maimartaba ya Fadamai Halin da"ake cki..Wai Fadar irin tashin hankalin da Maimartaba ya Shiga Fade bata baki ne,salati kawai yake yana kiran Sunan Allah,lokacin dayake sanar da goggo zaman ya bori tayi hannu bisa kai tana kuka,maimartaba na bata baki,gimbiya Razeenah da Ummah mai babban daki da Baba Ade sai gimbiya Fasilatu kadai sukaji lbrin Abunda ke Faruwa,sai waziri da shamaki wanda maimartaba yabada Umanin ashirya musu Tafiya zuwa Nageria.
Goggo tayi kuka tana Fadin in Aliyu ya mutu ne asanar da ita,ammh maimartaba ya dagemata bai mutu ba da Ranshi,Azeema kuwa babu wanda yake da karfin halin Sanar da ita,saboda yaya lafiyarma kura balle tayi zawo,bata da aiki kullum sai kuka tana Fadin Yaya captain ya mutu ne ba"a san gayamata ne,ga cikinta daya shiga wata na Takwas,yayi girma sosai ta kumbura tako"ina gashi yana neman Rinjiyarta in ka ganta sai ka tsausayamata Saboda yadda ta rame ta lalace kamar ba Azeeman Kaduna ba,Su Zafira na iya bakin kokarinsu na kada Azeema ta damu ammh ina Ita bata su take,kewa tare da zafin ciwon mijinta kadai ya isheta,tayi kuka kamar zata mutu ammh kullum hakuri ake bata,akwai likitar datake duba matan maimartaba ita ke kula da Azeema,duk sati sai tazo ta dubata tare dayi mata Fadan,ta rage saka damuwa aranta don hatsari ne mai tsohon ciki tana da hawan jini,kuma baya kasa kullum saima karuwa dayake,Azeema kallonta kawai take aranta tana Fadin"kaji mata,wato na zauna nayita kwanciyar Hankali mijina ya tafi yaki bai dawo ba,lalle ma wannan kwakwalwarta tatabu toh jinin yayi ta hawa ai badai Ranar sauka sai Muradin Ranta yadawo,Ko Zafira da Jabir ya kira ya sanar da ita Gargadi yayimata na koda wasa karta gayama Azeema,saboda ba"a ce asanar da ita ba.
Washegari Maimartaba da Waziri sai Goggo da Gimbiya Fasilatu Suka nufo kasar Nageria cike da alhini tare da tararradin Halin da zasu iskeshi ciiki,gimbiya Razeenah anbarta ta zauna Da Azeema ita da Baba Ade da Ummah mai babban daki,wanda sukama Azeema karya Da cewa zasu wani bikin masarautar yanki dake gabas dasu ne,kwana biyu zasu suyi dawo,bata damu ba don yanzu Abubuwa dadama basa burge Azeema,ita burinta Allah ya bayyana mata mijinta tare da Fatan Allah ya sauketa lafiya.
Koda kawu Bala ya isa Abuja dakyar aka barsa yaga Aliyu bayan Anfito dashi daga Emegency,wlh sau daya ya kalleshi bai kara ba,saboda yadda yaji kwallah sun tahomai,yanzu Gadangan goggon ne ya dawo haka gabadaya kafafunsa sagale cikin wani karafa,duka kuma nannade da bandeji,bayan Kafadansa shima daure a wuyansa,shima nannade da bandeji domin Shima karaye ne awajen,sai goshinsa wanda shima Wani katon Rauni ne awajen,gabadaya dai Abun Tsausayi,har kuma zuwa lokacin bai Farka ba,tun bayan Farfadowan da yayi lokacin ana Gyaramai Dauri,Kawu waje ya Fita yana Share kwallah,bai dade da zuwa ba,sai ga Haisam,ai Shi yana Shiga ya kame atsaye hannuwansa dafe da kai yana salati su Umar ne suka rikosa ganin yana neman Faduwa fadi yake su Fadamai gaskiya anya Gadanga na raye kuwa,?Sun tabbatar mai dayana raye,kawai dai ya jiki ne.
Sauran Sojojin dasuka dawo hayyacinsu suke bada lbrin Abunda Yafaru Ashe lokacin da yan boko haram din suka kawo masu Farmaki,suka yi ta bata kashi,toh lokacin da aka samu Rabuwa Sojojin acikin daji,harda su Aliyu aciki wanda sakamakon haka suka harbeshi akafarsa ta dama,Faduwa yayi akasa,ammh sai yayi kokarin mikewa,ganin ya kasane yasa ya Fito da karamar wukar dake kugunsa ya yaga daidai inda Harsashin ya Shiga ya saka wuka ya tsaka ya cillo shi waje yana ihu yana komai,saboda azaba,haka ya saka wani kyalle ya Daure wajen,ya mike yana dingishi ya cigaba da gudu yana rike da bindigarsa,ganin bai da wani karfi ne yasa suka mamayesa suka kamasa,suka kuma saka Sauran Sojoji 8 dake tare dashi su Mika kansu ko kuma su kasheshi,toh wannan Shine dalilin dayasa suka Ajiye makamansu suka mika kansu,shine fa suka ijiyesu anan sunata musu Azaba,dama sunce lokaci kawai suke jira dukkansu zasu kashesu,lura da sukayi kamar Aliyu ne Shugabansu yasa suka ware shi dabam suna mai Azaba kala kala,shine fa har yasamu wadanan Karayan da kuma Sauran Rauninka,suna kokarin cinye wa!adinsu na kwana biyun da suka diban musu na zasu nunasu Afaifan Vidiyo,su bada sanarwa cewa ko gwannatin Nageria su sakarmusu mutanesu suma su sakin musu Sojojinsu,in kuma sunki yarda toh suma zasu kashesu Dukkansu,toh Ana cikin hakane Sojojin sukazo suka Farmusu kuma Allah yabasu Nasara.
*****************
Maimartaba basu samu isowa ba sai Washegari,lokacin da suka Shigo cikin asibitin sun tarar da Kawu Bala da Haisam,sai Umar da Jabir,sai wasu Security dake tsaronsu,Yanayin yadda goggo taga kawu tun anan jikinta yayi sanyi kafafuwanta sukayi Nauyi,lura da Halin datake ciki ne,yasa maimarta riko hannunta ya matse alamar Karfin gwiwa kallonsa tayi wasu hawaye na gangaromata,likitocin sunyi complain Majinyacin baya bukatar hayaniya,saboda Baida de da Farkawa ba,ganin kimar Maimartane yasa aka barsu suka Shiga inda Aliyun yake,kai kodaga ganin yanayin dakin,gabadaya glass ne,zaka Fahimci saima Mutum yaji kamshin mutuwa ake kawosa irin wannan Dakin😅,lokacin da suka Shiga Dakin goggo na rabe bayan maimartaba Gimbiya Fasilatu ce kan gaba sai Waziri sai kawu bala dasu Umar,su goggo suna bayansu,Waziri keta salati yana kiran Sunan Allah lokacin dayayi Tozali da Aliyu,itakanta gimbiya Fasilatu da damuwar Abun baiwani dameta ba,sai da tayi baya tana dafe kirji idonta ya kawo kwallah,wani imani yakara Shiganta lokaci daya,yanzu Aliyu ne yakoma haka? ganin haka yasa maimartaba karisawa bakin gadon na Aliyu yana kallonsa da duka idanuwansa waje,Goggo dake bayansa tayi Saurin Rufe bakinta wanda kuka kenan Kwacemata hannu maimartaba ya sanya ya cire gilashinsa mai karamasa karfin ganin,hawaye suka taru acikin idanunsa,har sai da suka kwaranyo bisa hannun Aliyu wanda yake da lafiya,jin sanyin hawayen maimartabane yasa ya motsa hannunsa,lokaci daya da bude kumburarrun idanunsa,dishi dishi yake gani,ammh duk da haka sai da ya gane goggo da maimartaba dake gabansa,bakinsa ne yafara motsi,shiyasa da hanzari goggo ta duke gaban gadon tana Riko hanunnsa take Fadin"gadanga...."Tafada tana kuka kallonta yake,shima hawaye suna zubomai ta gefen ido,dakyar ya Furta"Na"am goggota..."Yafada murya shake,goggo Runtse ido tayi tana Rumgume hannunsa take Fadin"Allah ya Tada kafadunka Gadanga,Allah yabaka lafiya.."Take Fada tana wani kuka,wanda duk wanda ke wajen sai ya tsausayamata,Umar da jabir dake gefe banda Share kwallah babu Abunda sukeyi,Haisam ko waje yakoma don yadda kuka yaci karfinsa,Maimartabane yayi Saurin Ficewa da hanzari,Waziri ya maramai baya Shida Kawu Bala.
Gimbiya Fasilatu da Tsausayin goggo ya cikata ta Durkusa tadafa kafadanta tana Fadin"Ki bar kukan Suwaiba,kuka bazaimana mgani ba,addu"a zamu tayimai Allah ya bashi lafiya.."Goggo na jin haka tamike da hanzari,itama gimbiya Fasilatu ta mike,saboda yadda goggo take jikintama babu karfi saboda kuka,shiyasa kawai Tafada jikin gimbiya Fasilatu takara Fashewa da kuka mai cin rai,itakuma ta riketa tana lallashinta,Aliyu na kwance yana jinsu shima kukan yake,yana so ya tambayi,goggo ina Azeema ta haihu ne?ko haryanzu da Saura ammh kuma bakinsa yayimai Nauyi bazai iya mgana ba
Ashe Fitar su maimartaba sukayi Office din likitan yaje,yace ya Rubuta musu takarda yanzu zasuyi Transfer din Aliyu zuwa wani babban Asibitin kashi dake kasar india New Delhi,nan fa sukace basu san dawannan mganar ba,saboda gwannatin Nageria karkashin Sojojin kasa,ita keda alhakin kula da Aliyu Ahalin yanzu,kuma yana karkashinta babu yarda za"ayi su basu shi su tafi dashi,batare da gwannatin Nageria tasaka hannu ba jin haka yasa nan da nan Akayi waya zuwa ga *BRIG.GEN.S.U KUKA SHEKA* Shiya sanar da maigirma Chief Amry of Staff *LT.GEN.Y.T BURATAI* Abunda ke Faruwa babu Bata lokaci sai ga tawagarsa zuwa Asibitin da Aliyu ke kwance,nan suka hade dasu maimartaba bayan gaisuwa dawani dogon Turanci dole dai gwannatin Nageria ta rarrataba hannu tabasu Yaronsu,ammh sunyi kokarin nuna duk wani taimako da"ake nema suna Shirye suke dasu badashi,domin haryanzu Captain Aliyun yana mtsayin Sojan Nageria,Fatan Alheri ne ya biyo baya tare Da Fatan Allah ya bashi lafiya.
Kawu Bala shiya ta kokari har suka samu Visa zuwa gobe da Safe,shiyasa basu daukeshi daga Asibitin ba,sai Awashegari,bayan sunje hotel sun kwana,karfe 9:30 Jirgin nasu zai tashi ababban Filin jirgin *Nnamadi Azikiwe International Airport Abuja* Motar Asibitin da taimakon wasu likitocin suka daukosa daga Asibitin zuwa Airport din,Abunda zai baka sha"awa dukka masu Fada aji agwannati suna wannan wajen,harda wasu Sojoji wanda suke ta Farate,tare Sarama Shi Aliyun lokacin da"aka Fito da gadon marasa lafiya daga cikin jirgin za"a Daukesa zuwa ciki,yana kwance kamar baya Numfashi sakamakon sunyimai Allurar barci ne wacce zata daukesa har na tsawon awa biyu,bai Farfado ba,har aka Shiga dashi cikin jirgin baisani ba,su Maimartaba Sukabi bayansa,shiga da goggo da gimbiya Fasilatu sai Waziri da kawu Bala,sai Umar da Jabir da Haisam suma ba"a barsu abaya cikin lokaci jirgin da zai yada zango a babban birnin india ya lula sararin samaniya.
_________________
*INDIA*
_NEW DELHI_
""Tun Suna Nageria dama Kawu already yagama mgana da Asibitin ta yanar gizo,sun san da zuwansu,suna sauka sai ga Motar babban Asibitin na *FORTIS HOSPITAL NEW DELHI* Sunzo tare da Manyan likitocinsu sun daukesu,zuwa Asibitin inda nan take babban Likitan kashi wanda Duniya ke Ji dashi *DR KABIR KHAN* Wanda ya kasance musulmi ne gaba da baya,kuma Ba indiye ne ta uwa ta uba,yasa aka Shiga dashi Thearter Room,Tunkafin zuwansu dama Tuni kawu yagama Turamusu dukkan Bayanai game da ciwon nan Aliyu,kuma hatta da kudaden aiki sai da ya Tura musu ta bankinsu dake yanar gizo,Tunda suka shiga dashi basu Fito ba har Tsawon awa biyu shine dalilin Daya su Umar suka bar Asbitin sukaje suka kama musu masauki wanda ke kusa da Asibitin wani kayatattacen hotel suka kama musu, mai Suna _JW MARRIOTT HOTEL NEW DELHI_ Suka kuma kira su kawu awaya suka sanar dasu,sanin ba yanzu za"a Fito da Aliyu ba yasanya dukkansu suka nufi masaukin kowa yayi wanka suka ci abinci kafin sukara dumguma sukoma cikin asibitin,kuma Abun Sha"awa,harda motoar da zata dinga zirga zirga dasu mallakin Asibitin ne,komai nasu cikin tsari.
Suna komawa ba Dadewa sai ga Aliyu an gunguroshi kamar gawa zuwa dakin Hutu,indiyan likitocin kuwa sai bama junasu hannu suke suna ma juna barka da alamun dai aikin da sukayi ansamu Nasara ganin haka yasa,su maimartaba sakin ajiyar zuciya suna mai Hamdala acikin zukatansu.
*Janafty*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
_I dash to whole page 4r My one and only *YAYA*😘 D person of *IBRAHIM* Yaya I.B..Tanque so very much Yaya for ur luv,support and care,Allah ubangiji yabaka Mata tagari wacce zata kula dakai kamar yadda kake kula da *KANWARKA* Ameen_🙏😘
*Chapter..37*
""Dr Kabirkhan Shiya nemi ganawar Sirri da maimartaba dasu Kawu,inda yake sanar dasu cewa aiki yayi kyau masha Allahu,ya sanar dasu lalle gadanga ya Auna arziki domin da"ace an kara daukan wani lokaci da kafarsa inda wacce ke dauke da harbin bindiga sai dai ayanketa,kuma taimako ma na biyu shine sanda harsashin ya Shiga Tunkan yagama huda nama jikinsa,akayi Saurin Fidda dashi shima yabada Taimako sosai wajen Rashin lalacewar kafarsa tasa, kana daga karshe Dr kabirkhan yayaba da Jarumta tare da Dauriya irinta ta Da"nsu Aliyu gadanga,domin ya iya tsawon kwanakin daya dauka da wannan Rauninka ajikinsa tabbas ko acikin Sojojin shi na dabam ne,ammh yanzu haka yana dakin hutu kuma babu wanda zai Shiga inda yake sai nan da kwana biyu lokacin ya Farfado,kuma duka aikin nasa baza"a warwareshi ba,sai nan da wata biyu,lokacin suna saka Ran Insha Allahu komai yazama Tarihi Aliyu zai taka da kafarsa ya Fito daga cikin Asibitin nan yakoma kasarsa da kafarsa
Hakika su Maimartaba Sunji dadin bayanan Dr kabirkhan wanda yayi musu Shi cikin harshen Turanci,godiya sukayita yimishi,shima yana gode musu,kafin su Fito daga office din nasa maikama da aljannah Duniya,Koda suka Fito Abunda ya karanta musu,shi suka karanta ma su goggo dake waje hamdala kowa ya Shigayi Tare da Fatan Allah yasa anyi aikin cikin Nasara,basu koma masauki ba sai chan dare bayan sun leka Aliyu ta cikin glass,din inda gadon dayake kwance yake,gabada kafafunsa suna sagale ne jikin wani karfe,mai aiki da wasu Na"ura,haka hannunsa,shima an sagala shi,jikin wani Abu mai kama da roba,dai dai inda hannun yake anyi wani Filo,yadda hannun yayi bisa,kodaga chan suna hango Fuskarsa yadda tayi Haske,ammh yayi Rama sosai,dukkansu sunji dadin ganinshi domin yafi yadda suka taho dashi,addu"an samun lafiya sukayimai kafin su rankaya zuwa masaukinsu.
Kamar yadda Dr kabirkhan Yafada kwanan Aliyu biyu ya Farfado,kuma Alhamdulillah jikinsa yayi kyau sosai,domin koda likitoci suka gama bincikensu akanshi,suka Fito bayan sun bama su kawu damar Shiga wajensa,ammh banda doguwar mgana,koda suka Shiga sun Tarar da wata Nurse ta tadashi zaune ya jingina bayansa da wani Filo mai kyau da taushi,Yana ganinsu yafara mirmishi alamar Sauki ya samu,Tea mai zafi Nurse din ta hadamai ta mikamai,ya karba da hannunsa mai lafiya,Umar ne ya karisa da hanzari zai karbi Kofin Nurse din ta dakatar dashi kafin tace abarsa yasha da hannunsa saboda inyana motsa wannan hannun nasa,shi zai taimaka wajen Motsa wanchan hannun mai Ciwo,kai ya gyadamata alaman gamsuwa kafin ta Fice ta barsu,nan fa suka zagayesa suna hamdala,goggo ko Kallonsa take hawaye suna taruwa a idonta,girgizamata kai ya hauyi kafin yace"karki kuka goggo,kin manta kece ke man kirari da gadanga kusar yaki,ba gaba da gaba ba ko ta bayan ma karya sukeyi? yafada cikin sanyin murya dariya goggo tayi lokaci daya da mirmishi,Kofin tea din ya mika Umar yana Riko hannun goggo yace,"Toh kuma Shine kike kuka,kinsan baza su iya ba,baza su iya ja da gadanga ba,gadangan goggonsa. ba."Yafada yana Sharemata kwallah,dariya ta kubcema kowa ganin goggo na kuka tana dariya hannunsa ta kamkame tana Fadin!"Tabbas bazasu iya ba,Nasani baza su iya jada gadanga na ba,Allah ya baka lafiya"Da Ameen ya amsa kafin yace"Kawu wai muna wani gari ne,sai naga kamar nan ba Nageria bane,duba ga likitocin da suka zo suka dubani yanzu..?
Maimartaba ne yayi mirmishi yace!"Alhamdulillah Tunda yanzu kadawo hayyacinka,yanzu haka muna babbar birnin india,New Delhi,acikin wani Asibitin kashi.."Gyada kai yayi yana mamakin duk yaushe sukazo nan,kawu ne ya karbe da cewa"kuma kwananmu biyu yau da zuwa,kuma sai yau ka Farfado bayan aikin da"akayi maka Tun bayan zuwanmu.."gyada kai yayi yana bin Su Jabir da Haisam da kallo,wadanda sukayi wani kalan Tsausayi,dariya ta kamashi ya daga hannu yana Fadin"hey ya'n kannena,ban mutu bafa naga kunyi wani kalan Tsausayi ne..",Hararansa Haisam yayi kafin yace!Suwaye kanneka...? kai tsaye yace"Kumana.."Jabir ya yi Saurin Dunkule hannu zai sakamar bisa ciwo,da hanzari Aliyu yace"Kai Dude Don Allah bari wlh kuna gaba dani.."Yafada yana Zaro ido,sauke hannunsa Jabir yayi yana dariya gabadaya su goggo dariyan suke,na ganin diramar su Aliyu,mai hali dai baya chanza halinsa.
Suna Shirin tafiya masauki ne,Aliyu yakira goggo wacce ke Shirin Ficewa dawowa tayi tana Fadin"gani gadanga ko kana bukatar wani Abune? girgiza kai yayi yana Fadin"A'a goggo.."Kallonsa tayi kafin tace'"Toh mene ne? lumshe ido yayi kafin yace",Ammr,nace ba goggo banga Azeema bace ko ba"a zo da ita bane..."?Yar dariya goggo tayi kafin tace"Allah sarki ai nasan zaka tambaya,wlh Azeema na gida,bamu Taho da ita ba,kai batamasan Abunda ke Faruwa dakai ba gaskiya don ni na hana a sanar da ita,tunda aka nemeka aka Rasa,Azeema ta shiga kunci,gashi kuma cikinta ya Tsufa,kaga kuma sanar da ita kamar kara mata damuwa ne.."Dan Ware ido Gadanga yayi kafin yace"Cikin yayi kato ne goggo..? kansa ta dungure kan tace "Ban sani ba in tazo sai ka ganninma idonka..."Washe baki yayi yana Fadin"Da gaske pretty zata zo wajena.."Gyada masa kai tayi kafin tace"Haka nake so,da zarar mun koma zasu zo ita da Gimbiya Razeenah da Baba Ade,Allah barshi sai ta zauna anan har ta haihu,lokacin kuma nasan kai Alhamdulillah kasamu lafiya sai ku tattaro ku dawo gida,ko baiyi ba.."da hanzari Aliyu yace"Hakan ma yayi goggo Allah ya kara girma.."kansa ta Shafa kafin tace"Sai da Safe Allah ya kara Sauki..."Tafada tana fita daga dakin,dayake Asibitin basu da bukatar wani mai jinya,sai dai in daga nesa kukazo,ku kama masauki kuna zuwa kuna ganin majinyacin har ya samu lafiya,ammh ba'a yarda da kwanan Asibiti ba.
Haka ko akayi Sati daya Su maimartaba Sukayi Akasar india kafin su tarrara su koma Niger,Tunda jikin Aliyu Alhamdulillah,kullum yau yakan Fi jiya,Abun mamaki harta hannunsa mai karaya yana iya motashi,hakama kafafunsa,yana iya motsasu,ammh ahankali cikin dabara,Jabir ,da umar kadai aka bari,ammh dukkansu suka koma,daga Niger kawu ya hayo jirgi shida Haisam suka koma Nageria,inda suka kaima su Ummah lbri mai dadi na cigaban da'aka samu game da Ciwon na Aliyu,wanda sai lokacin hankula suka kwanta.
Mganar da goggo ta yanke na zuwan Azeema wajen Mijinta,ta Sanar da maimartaba baiyi gaddama ba ya amince da shawaran goggo,don ko bakomai taga mijinta shima yaga matarsa,ko Allah yasa ta kwantar da Hankalinta ta haihu lafiya,koda goggo ta sanar da ita mganar Tafiya india ammh bata sanar da ita wajen Aliyu zata ba tadai sanar da ita cewa zata tafi ta haihu achan ne,Tura baki Azeema ta hauyi,daganan sai kuka wai ita ba inda zata,ana so tatafi ne,azo da gawan yaya captain abinne Shine asoke ayimata wayau,Fafur fa Azeema tace babu inda zata,dakyar da sa bakin maimartaba ta yarda zataje,nan da nan ko akayi musu Visa,kwanan su Goggo hudu da dawowa sukuma suka tafi ita da Gimbiya Razeenah da Baba Ade,sai Ummah mai babban daki,datace wlh bamai barinta sai taje taga halin da maigidanta ke ciiki,sai su Zafira da Safaratu,wadanda suka sakama Sarki kukan sai sunje sunga Yaya captain suma hankalinsu zai kwanta,mirmishi maimartaba yayi yace duk suyi ta Tafiya Allah ya kaisu lafiya.
Koda suka sauka A babban birnin Delhi,Jabir da Umar su sukazo da motar Asibitin suka daukesu Diret zuwa masauki,Azeema tayi ta kalle kalle tana yabawa da kasar ta india,isarsu masauki ba wuya kowa yayi wanka sukaci abinci suka dan huta kafin Su jabir su ce Su Fito su tafi cikin Asibitin,ita azaton Azeema likita zata gani Shiyaasa,bata nuna wata damuwarta ba.
Umar da Jabir suna gaba sukuma suna biye dasu,har dakin da Aliyu yake suka Tura kofa suka Shiga,yana kishiginde,yana motsa hannunsa babu komai ajikinsa sai boxers,yana ganinsu yashiga washe baki,don Su Jabir basu sanar dashi,gasu zuwa ba,gaisawa sukafarayi suna tambayanshi yajiki yana amsa musu da sauki,Ummah mai babban daki ta shafa kanshi tana Fadin"Megidana gawa taki rami.."Dariya akasa,shima mirmishin yayi kafin yace"Kwarai don sai kin rigani wucewa wlh.."Yafada yana yar dariya Wajen Umar takoma ta dafosa Tana Fadin",Da tsohuwar zuma ake mgani ko Na gaban goshina.."Yarfe hanunta yayi yana Fadin"Tabdijam bawani nan,ai da sabuwar ma anayi,banan kika watsamin kasa a ido ba,nima aje gaba wlh bani so.."Dariya suka samata gabadaya ganin yadda Tayi Da Fuska,Aliyu dai sai waige yake yana Jiran yaga ta ina Azeema zata bullo,lura da hakan Da gimbiya Razeenah tayi itace ta waiga tana Fadin"Wai ina Azeema ta tsaya ne?Batare da ita muka Shigo nan ba..? jin Abunda Gimbiya Razeenah tace ne yasa Aliyu saukar da ajiyar Zuciya,yana lumshe ido.
Zafira ce ta fita waje,sai kawai taga Azeema zaune kan wata kujera ta wani hade rai,saboda duk a tsammaninta wajen likita suka kawota shiyasa tayi Ficewarta tana Tura baki,don yanzu wlh haushi kowama takeji,Zafira ce ta karisa garera tana Fadin"princess dinmu kizo Ummah na kiranki.."Kauda kai tayi kafin Tafara kokarin mikewa Zafira tana taimakamata harta mike,rike da hannunta gam suka Shiga dakin,bata direta ko"ina ba sai gaban godon Yaya Aliyu kafin ta kauce tana Fadin"Jita tanawani Fushi da mutane mufa taimakonki mukayi wajen mijinki dakike begen gani muka kawoki.."Tana Fada tanayin gefe gadanga dake kwance ya bayyana agabanta.
Kallonsa take,shima yana kallonta daga sama har kasa,tana sanye da wata doguwar rigar Abaya baka,sai Gyalen kayanta data nadashi bisa kanta,ga cikinta nan ya turo yayi kato,kamar gobe zai Fito Duniya bayan ta cika tayi Fam,kamar ba Azeema ba,itako kallonsa take cikin Fitan hayyaci,tundaga Samansa har zuwa inda kafafunsa suke asagale,Tsoro ya kamata tayi baya tana sanya duka hannuwanta ta danne bakinta dake rawa da karfi ta Furta.."Ya..Ya..Cap...tain...",Tafada idonta gabadaya awaje,Mirmishi ya sakarmata mai Sauti kafin yace"Na"am pretty..,Nine cijeni kiji ba mafarki kikeyi ba.."Yafada yana mikamata hannunsa mai lafiya,ai da hanzari ta karisa garesa sai jiyayi Ta fadomai kai tsaye hartana bugemai hannun dake da ciwo,gefe yayi da hannun yana Fadin"Wash pretty bi sannu,kinsan yanzu mijin naki yadawo sai allallaba fa"Yake fada yana zagaya bayanta da hanunsa mai lafiya,kuka kawai Tafashemai dashi tana fadin"Yaya captain Ashe zan sake ganinka arayuwata? nazata ka mutu ne su goggo ke boyemin?Bayanta ya Rumgume yana Fadin"Ban mutu ba pretty,sai dai nasha wuyane kawai.."yafada yana yar dariya dago kanta tayi daga kirjinsa tana kallonsa hawaye shabe shabe Afuskarta tace"Har wani tsawon lokaci kadauka kana cikin wannan halin? tafada muryanta na Rawa,Rausayar dakai yayi yana kallonta kafin yace",Bansani ba pretty wlh bansani ba,Abu daya nasani shine nidai na Farfado na ganni anan wajen"Kuri tayi masa da ido,kafin takoma tana bin Raunikansa da kallo,tana hawaye na Tsausayinshi,hannu ta sanya zata taba kafafunsa yayi Saurin rike hannunta yana Fadin"Pretty ciwo ne da zafi.."Yafada Ashagwabe,dariya tayi tana hawaye,tayi Saurin Shammatansa,ta dan ture hannun dayake da ciwo,baya yayi yana Fadin"Wash pretty .."Saurin Fadamai tayi tana fadin"Srry kaji bazan kara ba.."Tafada tana mai dariya hancinta yaja yana Fadin"kinganki ko,so kike kiga kukana ko,toh bazaki gani ba.."Dariya sukayi gabadayansu yana kara rikota,kiss ya sakarmata bisa kai yana Fadin"I miss u Pretty,i miss u like crazy..."Hawayenta suka karu ta dago tana kallon bakinsa,lebenta ta saka anashi tana tsotsa na kusan minti hudu kafin ta cire tana Fadin"Miss u more and more Mijina.."Shima idonshi ya kawo Ruwa da hannunsa mai lafiya yasa ya Fado da ita jikinsa ya rumgumeta kam,duk da tsinin cikin na hanata isa gareshi ammh haka ya matseta yana Sauke ajiyar zuciya,koda suka waiga daki bakowa,ashe tun Rumguman Farko kowa ya Fice batare da wani ya yi Shawara da wani ba😂
"Cikinta yake Shafawa yana Sauke tagawayen ajiyar zuciya kafin ya fizgo mganar"pretty cikin nan yayi kato da yawa,anya ba yan uku bane na baki,kinsa fa ni akwai lafiyan mazantaka ko? dariya takamata,mintsilinsa tayi AGefen ciki ya zille yana dan ihu,yake Fadin"kefa muguwace wlh daga fadar gaskiya sai muguntarki yatashi haka ake jinya dama"Bata dagoba illah kara lafemai datayi tana shafa kirjinsa da hannunta har zuwa nipple dinsa,salon datakemai ne yashashi Saurin rike hannunta yana fadin"pret..ty.."muryansa ta karaya,bata samu zarafin mgana ba illah"Umh..Umh..Umh..Mmmm.."Datake ta cemai,Mirmishi yayi mata yana kara damke hannunta yace"Bari mana pretty kinji,kinga fa halin danake ciki,karki kwantomana kura,wlh ko kin kwantota babu amfanin da zan miki.."Yafada yana cije baki,da Sauri ta dago tana Tura baki tace,"Ni yaushe nace haka...? Saurin Rikota yayi Yana Fadin"wayace kince,nine naji yanayi na chanzawa dat why am srry kinji pretty bazan kara ba.."komawa tayi bisa kirjinsa tana dauke hawayenta,domin data dago ta ganshi Ko"ina sagale sai taji kuka yazomata,kankame juna sukayi tamkar wani zai kwace musu juna,yana rike da ita yake bata lbrin Kafarsa daya harbin bindiga ne,daya kuma karaya ne,sai hannunsa,shima dake da karayan ammh Alhamdulillah ana samun cigaba.
Lalle masu iya mgana sukace Abun namu ne,toh haka tafaru da Aliyu da Azeema,don mantawa sukayi da kowa da komai suna rike da juna,suna hira gefe daya suna shan soyewarsu,har dare dakyar su Ummah mai babban daki suka tara Azeema suka koma masauki,ammh da Farko kuka tafara wai ita ba inda zata wajen Aliyu zata kwana,baki Ummah ta rike tana Fadin"Wai naji yaran zamani,toh in kin kwana,ina zaki kwanta gado dayane dai adakin,kuma yana kwance ko'ina tallabe? ko kallonta batayi ba ta fice tana Tura baki,Aliyu ko baitabajin haushin Rashin kwanan masu jinya ba sai yau,saboda Tafiyar Azeema ranar ko barcin kirki baiyi ba saboda kewa da damuwa,Tun safe ya ke ta kiran Jabir awaya don Allah ya kawo masa prettynsa Jabir sai yayi tsaki ya yanke kiran yana Fadin"wannan gayen Tunda yafara samuwa sai Allah kuma.."daga karshema kashe wayar yayi don yace yana barci bamai tashinsa,itako Azeema tun sallar Asuba bata koma tayi wanka ko karyawa batayi tatafi dakin su Umar tahau kwankwansa musu,Umar ne tafito,tana Neman yin kuka tana rokonsa yazo yarakata cikin Asibitin,ganin zatamai kuka ne yasa ya koma daki ya Shiryo yazo yatafi da ita ko Shiga baiyi ba ya juyo ya dawo yana Fatan Shima Allah yabashi mata wacce zata soshi ta kula dashi kamar Matar Yaya Aliyu.
Gadanga na zaune Yana Tunanin Azeema,ko Shigowanta baijiba,sai kawai yajita ajikinsa ta fadomai tana Fashemai da kuka,rumgumeta yayi ta lallashinta itako Fadi take wlh bazata kara Tafiya anan zata dinga kwana,cikin kunar rai yace"Kwarai da gaske kinanan wlh keda mijinki sai ahanaki kwana dashi,watafi chanchanta tayi jinyata inbake ba,bari likitocin suzo ko susan Abunyi ko kuma su sallameni mukoma gida gabadaya"Yake Fada Ransa bace.
Haka ko akayi Dr kabirkhan na zuwa Aliyu yayi cikiciki da rai ba Annuri,kuma yaki sakin Azeema yana kamkame da ita,Dariya Da sha"awa Abun yabaiwa Dr kabir khan da Sauran likitocin,Yasaketama Adubashi yaki sai Fadi yake,Asan yadda za"ayi dashi ko ayima prettynsa waje ta rinka kwana dashi tana bashi kulawa,ko kuma Shima sallameshi su tafi gida tare,itako Azeema harda dagowa tana Sharbe kwallah,shiko yana lallashinta,Tafi indiyan likitocin suka saka saka musu suna dariya Dr kabirkhan yace cikin Harshen Turanci" Umh very nice LOVE BIRDS..."Yake Fada yana musu Dariya,nan da nan yayi waya daga cikin Asibitin ya bada umarnin kawo wani karamin gado,kafin kace me har an Shigo dashi an kafashi kusa dana Aliyu anyimai Shimfidun alfarma,hardasu blanket da Filo mai kyau kallonsu Dr Khan yayi kafin yace"Is ok ko,mrs Patient ankashe rigimar zamu iya dubashi yanzu?yafada yana dariya tashi tayi tana gyada kai,cikin yar kunya,kuma wai tana wani Share kwallah,suko suna musu dariya kusan fa indiyawa akwai Bama soyayyah muhimmanci,gefe Azeema ta koma har suka gama Duba Aliyu suka fice suNa musu dariya suna tsokanansu da love birds.
Koda su Jabir suka iso,suka iske sabon lbrin baki suka rike,Jabir da bai iya Shuru yace"Wai yau naga bariki umar,yanzu Kaduba gayen nan,duk Wahalan damukayi dashi baitaba nuna damuwarsa ba inzamu koma masauki,ammh yau Azeema tazo harda tada rigiman kota dinga kwana dashi ko asallameshi yadawo gida? hararansa Aliyu yayi yana Fadin",Eh din,to daman ku gardawa dakune zan so ku kwana dani,Allah kyauta kai ni ko yanzu kuka tattara kuka tafi,Ayashe ta gaida Assha ko pretty? yafada yana kallon Azeema,wacce ke kunshe dariya ganin yadda Jabir ke hararansa,Jabir ya yi kuri yana kallonsa kafin yace"Toh ai ba damuwa ba basai ka koremu ba,zamu tafi kuma wlh zaka nemi ni banza mara mutumci kawai.."Dakin ne akasa dariya gabadaya ganin yadda Jabir yaji zafin Abun,Waje yafita yana ta zagin Aliyu shiko hardamai gwallo,Zafirace ta lallaba ta bi bayan Habibitan,Su ummah ko Aliyu sukayita ma Tsiya shiko ko ajikinsa don Abun yanzu ne yayi mai daidai.
Azeema duk da tsohon cikinta bata nuna kiyuwa wajen kula da Megidanta Aliyu,itace bashi abinci,goggemai jiki sabida yaji dadin jikinsa saboda Rashin wanka,akwana hudun da zuwansu garin aka kwance Karayan hannunsa,kuma Alhamdulillah komai yayi kyau masha Allah,sai da kokarin yafara anfani da hannu,wanda wannan aikin Azeema ce,itace keta kokari kan haka kuma yana kokarin motsa hannu,koda daukan Abune na mara karfi,itama Asibitin suna kokarin kula da ita amtsayinta na mai ciki,tunda duk sun saba da likiticin kamar DR khan sun Shaku dashi,inkaga yadda suke hira da Aliyu sai kuce sun shekara aruaru da haduwa ne.
Sati Daya su Gimbiya Razeenah sukayi suka koma,harda Jabir da Umar,Ummah mai babban daki tace ko ba inda zata zata,har sai Azeema ta haihu Aliyu ya warke kana ta biyosu su dawo,saboda itama ta kula dasu,toh ya suka iya dole suka barta sai Gimbiya Razeenah Tabisu suka koma tare,Ita kuma Ummah Dr khan yace ba"a barta ita kadai ahotel ba,gidansa dake cikin Asibitin nan Yakai Ummah mai babban daki,tazauna ita da matarsa mai Suna KAREENA,suna da kirki sosai,duk da Ummah batajin Turanci tana jin labarci,sukuma sun iya saboda sun zauna da larabawa sosai saboda yanayin aikin Shi Dr khan din,itama kuma Azeema aka barta ita da mijinta tana kara kula dashi..
_________________
*BAYAN WATA DAYA*
Sauki tare da cigaba yana samuwa abangaren Aliyu,wanda har an kwance duka aikin da"akayimai akafafunsa,hannunsa kuma Tuni ya yawarke garas,in ka ganshi bazakace yataba samun Rauni ba,Kafafunsa kuwa haryafara koyon Tafiya dasu Duk da tafiyan bata nuna Sosai ba,ammh sakamakon sanduna guda biyu,suna taimakamai Sosai wajen Nunar da Tafiyar nashi,kullum safe da yammah Azeema ke Fitowa dashi suna zagaya Haraban Asibitin,suna tafe suna soyewarsu babu Ruwansu da kowa,Tuni sukebama duk wanda ke asibitin sha'awa ganinsu bakaken Fata,ammh kuma suna mutumta soyayyah da daraja Aure haka,Ba yadda Ummah mai babban daki batayi ba,akan Azeema tadawo tahuta Tunda cikinta ya isa haihuwa ammh fafur taki,wai Tunda lafiyanta kalau ita bazata ta zauna ba,dole ta zura mat ido toh yazatayi Allah ya hadata da yaran zamani.
Awani dare Azeema tatashi da Nakuda,Hankali Aliyu yayi bala"in Tashi ganin halin datake ciki,ko kafin ya danna Madannin kiran likita Azeema tafara Wani irin nishi,ko kafin Nurses din su kariso Azeema tayi wani nishi mai karfi sai ga Kan d'a ya Fito,Allah ya taimake Nurses din suna shigowa Kan Da'n na Fitowa da hanzari suka karisa suka saka hannu suka jawosa,ai basu bar wajen ba,Azeema ta bankare tana salati nishi take mai karfi sai ga wani kan yakara Fito,suka saka hannu suka jawosa,Aliyu dake gefe yahada zufa kota ko'ina yana rike da Azeema,wlh har sai da yayi mata kwallah,ai suna jawoshi,takoma takwanta tana maida numfashi,Ihu suke suna daga ya"yan suna bugasu,nan da nan suka chanyara kuka atare,Azeema dake kwance hannunta kamkame dana gadanga taji cikinta yakara murdawa Nishi take saki tana Fadin"Yaya inaji fa akwai wani acikin cikin?Tafada tana wani nishin mai karfi,Wata nurses ce ta ankare da hanzari ta kariso tana kara ware kafafun Azeema take Fadin"Anoder one..."Take Fadi tana ihu"push oya push..."take Fadamata Azeema ko jitayi kamar zata Shide saboda azaba,dakyar ta iya wani nishi mai karfi,wanda ya Fito da kan Da'n Suka sanya hannu suka jawoshi,suna murna gabadaya dakin ya gauraye da kukan jariran wadanda Nurses din suka dagasu suka zube bisa jikin Azeema suna dariya,jikinsu duk jini ammh haka Azeema ta rikesu tana dariya lokaci daya da kwallah,Aliyu ko kamar yasuma saboda dadi,Dakyar suka koreshi waje suka kwashe mabiyan Azeema suka gyara wajen gefe daya kuma wasu suna kokarin gyaran yaran,duk da asibitin na kashi ne,ammh Nurses din sun san Abunda sukeyi,shiyasa karban haihuwan Azeeman bai basu wahala ba,duk da Abun yazo da Sauki.
Koda gari ya waye sai dai Asibiti ta cika da lbrin Majinyacin Sojan nan da"aka kawo daga Nageri,matarshi tahaifi Tripple,Mata biyu Namiji daya,kuma dukkansu sun zauna amahaifa dayane domin ko Azeema da Aliyu haryanzu sun kasa gane bambamcinsu,duk da kwana sukayi suna kare musu kallo,sun Rumgume yafi sau Biyar suna kara godiya ga Allah daya Basu wannan kyautar,Ummah mai babban daki sai dai Da Safe Dr khan ya sanar da ita haihuwan Azeema,duk da shima baya Asibitin waya akayi masa,jiki narawa suka nufa cikin Asibitin,sai dai suka tarar da Azeema zaune bisa gado tayi Ras da ita kamar ba ita ta haihu ba ga Gadanga a gefe bakin nan kamar zai yage,saboda murna Ummah mai babban daki ita takira Gida ta sanar dasu,gabadaya masarauta ta rude da murna Jikoki uku alokaci daya lalle Allah Abun godiya,Goggo ita ta kira kawu da kanta ta sanar dashi kafin kaceme haihuwan Tripple yazaga Duniya,Haisam na kano yaji lbrin ai sai ya kira jabir yana sanar dashi da zarar komai yayi daidai Aliyu ya dawo gida zasu fadama maimartaba suna so suma ayi bikinsu nan da wani lokaci domin zamowar Aliyu baban yan uku tabbas barazanane ga rayuwarsu😂
kwana biyu da haihuwan Azeema gimbiya Fasilatu da gimbiya Razeenah suka dira a india,murna ba"a mgana,ai gimbiya Fasilatu batayi shawara da kowa ba tayi saranda Taba goggo dama,Domin ta Fahimci tafi karfinta nesa ba kusa,domin tsakaninsu kamar tsakanin sama da kasa ne,duka duka Sati daya suka kara gabadaya aka Rubutama Aliyu gadanga sallama lokacin yana da wata biyu a asibitin,domin yaji sauki sosai koma nace ya warke,domin kafafunsa sun mike da kanshi yake takawa batare da Taimakon sanda ba.
Asibitin sunsha kewa love birds,Azeema da Aliyu ga kuma Tripple masu shiga rai da Ban sha"awa,haka sukayi ta hotuna da likitocin da Nurses,suna bankwana da sabo suka rabu,Azeema harda kwallaar rabuwa ita da Ummah mai babban daki sunji dadin india,sosai Dr khan kuwa sunyi exchanging din Phone number da Aliyu,da cewa da zarar ya shigo Nageria zai nemesa,haka suka rabu da matarsa kareena wacce suka shaku da Azeema da Ummah.
Ranar da suka baro india zuwa Masarautar Tambari buzu,sukowa ana chan ana gudanar da shagulgular murnan dawowar Aliyu da kuma murnan haihuwan yan"uku ,wanda ba"a tabayi ba tun sadda aka gina masarautar,Mutanen Nageria kuwa Sun dade da isa zuwansu Aliyu kawai suke jira,Hatta da jabir wanda yazo Shida Maminsa da Daddynsa,da Haisam ba"a barsu abaya ba domin sunce wlh wannan karon bazasu koma Nageria ba sai da matansu sun gaji suma,suna bukatar gwada karfin mazantakansu😂 wannan karon ma kawu da duka iyalansa,harda su Anty madina sunce wlh suma baza"a barsu abaya ba,tab uwa uba kuma ga shi Sunan yan ukun za"a hadashi ne da bikin gwagwaran biyu Wato Jabir da Haisam,kawu ya roki alfarman kuma Maimartaba baiyi gaddama ba,sakamakon yadda yake cikin Farinciki na dawowar Aliyu,ga kuma wani kyautan daga Allah.
*Ina godiya sosai masoyana ina ganin duka comments dinku daga mabambamta group dadama,bana samun binku daya bayan daya na yi muku reply,saboda ina cikin busy ne ko Typing din ma kokari nake mu kareta mu huta hakanan Shiyasa,ngd sosai kujigaba da hakuri dani Allah ya bar zumunci Ameen*
_*Sisinah Aisha Alto,keda Sahibata Hafsat Hafan ina kai gaisuwa🙋 Alherin Allah ya lullubeku aduk inda kuke*_
*D'IYATA LADINGO GA SAKON JINJINATA👍Allah yayi ma Rayuwarki Albarka can love u less diyar kwarai*
*Janafty*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*Chapter 38*
"Koda suka isa Masarautan, ta dinke babu masaka tsinke,haka aka yayyabe Aliyu da Azeema kamar za"a cinyesu saboda murna da Farinciki,Triple ko sunsha dauka sai da Gimbiya Razeenah ta daukesu ita da Azeema kwacokam zuwa shashenta,inda ta sanya Jakadiya ta saka wata baiwa ta saka mata katuwar gawar da Ruwan zafi ta shiga da Azeema tiolet ta gasata dakyau sosai ita kuma Baba Ade ta wanke yaran tas,aka Shiryasu cikin kayan sanyi masu kyau,aka kaima maimartaba su,shida kawu suka daukesu suka sanya musu albarka,shiko Aliyu bayan gaishe gaishe shashensa ya wuce,shida amininnasa,yasamu yayi wanka yaci abinci ya kwanta domin Hutu,suko Su Zafira da Safaru,suna dawowa goggo ta damkama Anty madina su tace amanar gyarasu na hannunta nan da nan ko tashige dasu Shashen goggo chan kurya domin cika Umarnin goggo,Ummah ko ita dasu gimbiya Fasilatu suna Shashen Azeema suna zaune suna hira cike da Farinciki da Annushuwa,Azeema kuwa tana gama cin abinci suka kulleta cikin daki wai ta kwanta ta huta,tana kwanciya kuma sai barci.
Tako'ina masarauta ta dinke da jama"a daga mabambanta wajeje a kasar Niger,dama kewayanta harda mutanen wasu yanki,domin samun damar amsa gayyatan Da maigirma Sarkin Agadez yayima jama"a na Murna haihuwar jokokinsa har guda uku,tare da Daura Aure tilon ya"yan nasa guda biyu,dole Abun ya Wuce hasashenmu,domin fa ashirya taro ne na azo agani,Hatta da Mallam lawal da Inna Ramatu sai da maimartaba yasaka akayi visa suka taho,domin yace har abada inna Ramatu tana mtsayin mahaifiya ne ga Azeema,sai ga Inna Ramatu zaune cikin masaraurar Tambari buzu rike da ya'yan Azeema,lalle duniya Abun tsoroce kuma hausawa na Fadin Abunda yabaka Dariya watarana Shizai sanya ka kuka,Sai kuma alokacin Aliyu ke jin lbrin Rasuwar Azeeza yaji ba dadi,ammh baiwani nuna damuwarsa ba,kawai yayi jim ne,saboda kada Azeema tace yana murna da Rasuwar yar"uwanta,ammh harga Allah ya manta da wata hallita Azeeza,Fatan dacewa wajen Allah yayimata,ammh akasan Ransa Yana fadin an rage mugun iri.
Daga Nageria Aliyu ya samu waya dadama,ciki harda waya daga Babban headquater su na Abuja,sukayimai ya jiki,bayan nan ya samu waya daga abokan aikinsa dadama,cikin wayar data tsayamai arai itace wayar da Ni"ima tayimai tana kuka,tace tayita nemansa so ba adadi bata sameshi ba sai yanzu,tadamu sosai Allah yasa ya warke babu Abunda ke damunsa,Mirmishi kawai yayi mata kafin ya sanar da ita ya warke yanzu hakama yana Masarauta nan yake sanar da ita haihuwan Azeema,da kuma Aurensu Jabir,Ni"ima taji hawaye sun taho mata tayi Saurin dannewa tana fadin!"Allah ya raya su bisa sunnah Congratulation,"Lokacin datake Fadin haka yana jinta kuka takeyi,sai ya basar yana tambayanta yakamata su Fito da miji ita da muneera Suyi Aure saboda Shine mutumcinsu,Dariyan kuka Ni"ima tayi kafin tace"Muneera zatayi Aure in Allah ya bata miji na gari,mgana na kuma bata don bazan taba yarda na auri wani namiji ba sai mutum daya,in ban sameshi ba,sai da nakoma ga Allah banyi Aure ba.."Saurin katse kiran tayi tana Fashewa da kuka,Aliyu Tunda sukayi waya da Ni'ima ya koma wani Sukuku ranar,saboda kalaman Ni"ima,hakika in yace bayason Ni"ima yayi karya,kuma in yace baya tsausayinta tabbas yasan karya yakeyi,kawai Shi ra"ayin Aurenta ne bayayi,saboda Shi mutum ne,mai zuciya da tsayawa kan Ra"ayinsa tunda yarasa Ni'ima da Farko komai na plan din Aurenta ya Rushe,sai gashi Azeema dabaitaba tsara Rayuwa da ita tazo tazama kaddaransa,gashi yau an wayi gari bayan goggo bai da wata sanyin idaniya daya Wuce Azeema yanamata Sonda baisan iyakarsa ba,saboda kirkinta da sadaukarwanta gareshi,hakadai yayita tunane Tunane har ya kareta baisamu mafita ba.
Ranar Da Azeema ta cika Sati biyu da haihuwa da misalin karfe 10:00am na safiyar Ranar jumma"a Duban mutane da sarakai,suka Shaida auren Haisam da Safaratu sai Jabir da Zafira kan sadaki mafi daraja, afarfajiyar Fadar maimartaba Sarkin Agadez Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,Daurin Auren daya amsa sunansa,wanda ba"a tabayi ba masarauta tacika makil da yan gida da yan waje,busan algaita kadai kakeji da kade kade da raye raye na Masarauta,abinci ko tako"ina kawai afitowa dashi ake,daga cikin masarauta kuma Yau din ne ake Sunan Triples,wadanda suka ci Sunaye masu daraja Daya taci Sunan goggo SUWAIBA ,Dayan kuma FATIMA,Sai Namijin yaci Sunan Maimartaba wato ABDULNASEER,Wanda ada sunan kawu akaso yace,kawun da kanshi yace maimartaba yafishi chanchantan samun takwara da farko,shima inda rai da rabo,mai sunanshi na zuwa,sunsha wanka cikin kayan alfarma,suda Mahaifiyarsu Azeema,wacce ke sanye cikin wani leshi,mai tsada da yarari,kunnuwanta da hannuwanta gabadaya Sanye da zinarai suna daukan ido,Hakama ango karni sanye da shadda fara riga da wondo harda babban Riga Shida aminan nasa,guda biyu duka shiga iri daya sukayi harda cikon Umar na Hudunsu,Ana gama Daura auren suka nufa shashen Aliyu suka gudanar da wata yar kwakwaryan walima,bayan la"asar nayi aka Fito akayi wata kayatattacan kilasa,mai ban Sha"awa Da dadin kallo,haka duka zaratan maza su hudu ke bama doki wuta sunajan limzami,kowa da kowa yafito kallo,harda maimartaba,Amare ma suna gefe,kowacce ita tarike ma mijinta limzaminsa kafin afara kilasan,Hakama Azeema tayima Aliyu gadangan kusar yaki,daga karshe maimartaba da tawagansa suka Rufe kilasa,yau hatta da kawu Bala Da mallam lawal da sun hau dokuna,Atawagan Sarki,itako inna Ramatu Tunda sukazo take Shashen Azeema ta karbi su Ummah ita ke kula da ita da Triple,Tayi nadama sosai in kuka ganta kamar ba ita ba,Abun jin dadinta ma babu wanda ya riketa da Abunda ta aikata kowa amasarautar yana bata girma amatsayinta na Uwa ga Azeema,Gadanga ne dai haryanzu bai saki da ita sosai ba,don shi mutum ne mai Ra"ayin bala'in in baya Ra"ayinka Tun Farko Abu ne mai Wahala yayi Ra"ayinka daga baya,kawai mazayewa yake saboda Uwar mata Azeema,don ya lura Tunda ta haihu takoma masifaffa,mgana kadan sai ta hau Fushi,shiko yanzu Aduniya in akwai Abunda ya tsana to yaga Fushi Afukar pretty yanzu nan zai Rasa natsuwarsa,shiyasa in gaya su Jabir na Rawan kafa kan su Zafira mamaki suke bashi,dariya kawai yake Aransa yana Fadin"Yarinta haryanzu na damun su Jabir,Allah ya kaunda Fitina,tunda daga su Jabir din har Su zafira shegen Rawan kan tsiya😂
Wajen kwana biyu aka Dauka ana gudanar da shagulgula Amasauratar Tambari buzu,saboda jiran Visan su jabir ta Fito,Ranar kwana uku da Daura Aure visan ta Fito sai haraman komawa,Haisam gidanshi na kano zai wuce da Safaratu,itako Zafira cikin Cikin barrak zasu zauna ita da jabir,sai fa alokacin ne koke koke ya tashi suna kuka sun rike gimbiya Razeenah akan su sun Fasa aure,Abun ma dariya yabama Azeema,sai da taje ta kira Aliyu yazo,tsawa daya ya daga musu kowacce ta Shiga natsuwarta.
Goggo ce da Gimbiya Razeenah zasu raka Amare,Ummah mai babban daki tace wazai zauna tab,wlh dole ne aje da ita gwara tayi amfani da lafiyanta kafin karfinta ya kare tazaga duniya😂Sai su Ummah dasu Anty madina da zasu koma,Inna Ramatu dai tana nan sai Azeema tagama wanka sukoma Tare hakama Shima Aliyu ko Shirin Tafiya baiyi ba,su suka raka Amare da angawaye har Filin jirgi,inda suka sha tsiya wajen gadanga yanata musu iskanci yana Fadin"yaga Sai rawan kafa suke,toh ko sau dari zasuyi Arana bazasu taba kamoshi ba,kuma wlh duk wanda yayagamai kanwa da yawa Allah ya isa😂🙉Jabir ya bashi amsa da cewa"Wlh tallhi yage yagema mallam,kai don Ubanka daka yaga kanwar wani wayamaka mgana,kajimin dan iskan Yaya"Dariya Umar ke tayi Shiko Aliyu hade rai yayi yana Fadin'"Yau ga surikin zamani,yanzu ni kake cema Dan"iska ko,ke Zafira zo nan"Yakira zafira wacce ke tare da goggo,ganin haka yasa Umar ya taresa yana Fadin"Allah huci zuciyar magajinmu rabu dasu,ai kowa ya sani ba wani babban Sai Baban yan ukun mu.."jin haka yasa ya washe baki yana Fadin"Allah yaso ku da na kirata nace ko kazo ta matse kafa🙈🙉"..Dukkansu baki suka rike suna kallon Aliyu shiko gwalo yayi musu yana dariya,daga Haisam har jabir binsa sukayi da gudu kowa ya dungule hannu na cin ubanshi yaje ya makale bayan kawu Bala yana Fadin",Kawu ga gansu ko,daga ina musu nasihan hakuri da Kawaici ,saboda dai wanda ya riga ka kwana dole ya rigaka tashi ko mami? yafada yana kallon Mamin Jabir tana Dariya ta amswa da cewa",Hakane Aliyu,babu kuma wanda yakamata yagayamuku gaskiya bayan Shi,yarigaku auren nan,sannan kuma yaya yake agareku Tunda kuna auren kannensa"Suna jin haka sai kawai suka juya suna hararansa,gwalo yake musu yana yar dariya,shi wlh dariya suke bashi in ya kallesu kowani shege ajirace yake da mace🤔Azeema ce tazo ta murdemai kunne ta baya yayi yar kara yana kallonta kafin yace"Pretty mugunta ko? zaki cirema Baban Triplet kunne ko? matse mai gefen ciki tayi tana Fadin"Kabarsu Jabir hakanan don Allah,tunda kai lokacinka babu wanda Yasa maka ido.."Hannuwansa yahada yana Fadin"toh angama Ranki shidade maman yan"uku"Dariya kawai tayimai ta wuce shiko yabita da kallon sha"awa azahirin batu anfara kureshi fa haba,hanya fa ba kyau,tsakani ga Allah yakamata pretty tazo taji dashi Tunkan yafita daga hayyacinsa.
Basu dawo gida ba,sai da sukaga tashin jirginsu,kana suka koma gida cike da kewa,Shashen Azeema ya rage daga Baba Ade sai Gimbiya Razeenah sai Inna Ramatu,hakama Shima Aliyu yaji shuru saboda harda Umar aka tafi zasu koma Asallamesu kafin su biyo jirgin sojojinsu su dawo kasarsu.
**************
Koda suka sauka A Nageria,direct Su goggo kano suka wuce da Safaratu,Awata anguwa mai Suna Tarauni,gidane babban kirarre,sai wanda yagani komai na alatun Rayuwa akwaoshi acikin gidan,babu Abunda zasu nema su rashashi,nan suka kwana sai washegari suka bar kano zuwa kaduna dukkansu,ammh shi kawu tun jiya yakoma kaduna abunshi,da zasu taho sai da goggo ta damkama haisam cheque dinsa na milayan uku,wanda maimartaba yabashi kyauta,tare da albishir din kujeran makka,shida Safaratu,Ummah harda guda da rawa,tana ta godiya balle su madina da sukayi ma Haisam chaa,wai yakowo su ijiyemai kudin,banza dasu yayi,shifa duk ya kosa su watse don wlh arike yake fa😂Karfe 2, da wani abu na Rana suka bar kofar gidan Haisam,suka bar shi daga shi Sai Safaratu sai halinsu sai dai Fatan Allah ya basu zaman lafiya.
Hudu da wani Abu na yammah suka Shiga kaduna direct to barikin Su jabir suka yada zango,shima din dai apartment din na jabir kamar na Aliyu komai ya mallaka,gyare gyare kawai sukayimata da Sauran abubuwa,basu kwana ba,tunda kaduna gidane,dama tuni iyayan jabir suka bi kawu bala,tun jiya suka dawo kaduna abunsu,shima irin kyautar da maimartaba yama Haisam irinta akama Jabir,tare da kujeran makka Shida zafira,Murna kam ba'a mgana basu wani jima sukayimata Abunda yakamata suka barta daga ita sai Halinta kowanne yakoma gidansa,gimbiya Fasilatu da Goggo da ummah mai babban Daki gidan Kawu bala suka sauke gajiyansu sai sungama hutawa ko zasuyi Shirin komawa Niger,saboda atsakanin nan sun yawatu aduniya ba laifi.
Kowani ango awannan daren ya maida amayarsa cikakkiyar mace,Abun ba ragowa ko kadan da alamu dai sunji maza,Ammh dukkansu sun tsinci kansu cikin wani nishadi mara misalatuwa jabir ne yace aransa"Dama Tuni irin wannan Dadin gayen chan ke kwasa,lalle dole yacemana yara,ammh wlh danasan haka aure keda dadi da Rahama da wlh Tun da na balaga zanyi aure,domin na mori Abun da kyau😂kuji fa jabir daga Shiga sau daya yafara sambatu,shidai Umar Tuni ya wuce sansaninsu,ammh shima kasan Ransa yana Cewa ne daya koma kasarsa zai nemi mata yayi aure,shima ai ba Dutse bane.
Sati daya cur su goggo sukayi suna hutawa kafin sukoma kasar Niger,koda suka koma Tuni yan uku sun kara girma da yau kamar ba yan wata daya ba,Fati itace suke cema Afra,sai suwaiba suna kiranta Afiya,sai Namijin suna kirana Anwar,Azeema kuma na cigaba da samun kulawa sosai gimbiya Razeenah na kokarin saka ido akanta kada tayi danyen jego,shiko Aliyu yayi nacin da bin,ko zai samu ya samu Ritsa Azeema ita kadai babu dama,ko gaishesu yazo yi da safe,su Inna Ramatu na wajen da Baba Ade,kuma Abunda ke bashu haushi suki tashi daga wajen,Abun na bakantamai rai Shiyasa kwana biyu yayi musu yaji,da Azeema taga haka sai dauki waya ta kirashi yana dauka ya balbaleta da masifan ta rabu dashi yaji da Abunda ke damunshi kawai ya yanke kiran,itakuma sai ta zuciya kan mene zai mata tsawa haka alhalin yana sane ba laifinta bane,kuma tayaya zata bashi kanta alhalin jiya jiya ne tayi tsarki,kuma ko samun damar zuwa Shashensa bata dashi saboda Baba Ade bata barinta Fita ko'ina suna tare da ita toh ya zatayi,toh dalilin yasa kowa ya Share kowa kenan harsu goggo suka dawo ana gaba,duk da sai su shafe kwana uku basu hadu da juna ba,don ko Su Afiya sai dai ya aiko jakadiya ta daukan mishi su,ko shashen Azeeman bai kallah saboda takara batamai rai saboda ta rainashi ko zuwa ma tabashi hakuri batayi ba,kuma ya sake kiran wayarta tanagani taki dauka,kwafa yayi aransa yana ayyana yadda zaiyi mganinta.
Su goggo basu Rufe sati da dawowa ba Aliyu yace shifa ya shirya zai koma bakin aiki,Abun yaba kowa mamaki,bama kamar goggo,wacce sukayi mgana yace sai Azeema tagama wankan yara sunyi kwari zasu koma tare da ita,da goggo ta tunamai sai ya bata rai yace ya chanza ra"ayi ne intagama wankan tazo daga baya ganin yadda ya mtsane yasa maimartaba ya amince aka neman masa Visa,Shida mallam lawal wanda maimartaba yayi yayi dashi yadawo masarauta su zauna tare yaki,yace abarshi a inda yake saboda yafi sabawa da chan,kuma ko ahaka babu Abunda zaice sai godiya ga Allah,ta sanadin Suwaiba da Azeema bazai kirga alheran daya samu ba,gashi ayau saboda ita zai je kasa mai tsarki lalle Allah ne Abun godiya.
Daga Aliyu sai Mallam lawal suka bi jirgi suka koma,domin goggo tace Inna Ramatu ta zauna,in za'a maida Azeema sai ataho tare da ita,Abun bakinciki Azeema batama san Tafiyar Aliyu ba sai washegarin daya tafi taji suna waya da goggo,lokacin tana bawa Anwar nono wlh dawani bakin ciki ya Turniketa batasan sadda ta ture anwar ba tatashi da gudu ta shige daki tana kuka ba,Baba Ade dake wajen tayi Saurin daukansa tana lallashinshi,tunda fizgoshi daga Nono tayi,Abun yama Azeema ciwo,itako mai tayima yaya captain da zafi haka har zaiyi iya komawa batare data sani ba,wato yanzu bata da wani amfani awajenshi Tunda tana jego,tagama wahalan cikin ya"yansa yanzu ta haifemai toh bata ita yake ba wata zuciya tace wama yasani ko saboda shegiyar Ni"imar nan yakoma,Tuna haka sai da tayi kwallah,bata son haka take kishin mijinta ba,sai Ranar haka ta wuni kuka bata kuma ci abinci ba, yara ko nata kuka ammh kota kansu batabi ba goggo ko ko kanzil batacemata ba domin ta fahimci Fushin na gadangantane dama Tunda taga Tafiya ba Shiri,kuma tun sadda suka dawo bata ganin yana shigowa shashen Azeeman tasan akwai wani Abun,sanin datayi daga Azeemar har gadanga yan buhu da rabi ne bamai gayamata Abunda yafaru Shiyasa takawo ido ta sanya musu kawai,chan ta matse musu shirtartu kawai,yara kuwa Ita ta daukesu ta tafi dasu zuwa Turakar maimartaba tana basu Ruwan zamzam da Dabinon makka,nan da nan ko sukayi Shuru da maimartaba ya tambayi Ina mamansu take tabe baki goggo tayi tana fadin"Yau Fushin d'ankane ya Shafesu ko kallonsu batayi ba Tun safe tana daki tana koken koken banza.."Mirmishinsu na manya Maimartaba yayi yana Fadin"Toh toh kice Abun na manya ne,toh Allah daidatasu,kinga ni yanzu kitashi ki maidama Baba Ade yaran nan,tunda nidai bama Fada ba,kuma bakya Fushi da mijinki,kiyi maza ki kaisu kidawo kiji wata mgana.."Dariya tayi mai tana wani kallonsa kasa kasa tana Fadin"Kai Yallabaina baka tsufa.."Farin gemunsa yashafa yana Fadin',Kinji ki da wata mgana ina Tsufan yake Suwaiba,ai a soyayyarki ban mori komai ba yanzu ne ma nakecin lokacina,kedai yi maza ki dawo ki amsa kiran miji kada ki shiga Fushin mala'iku.."yafada harda kashe mata ido,sauri ta kwasa tana dariya tace "Yanzu kuwa Yallabaina'Tafice Shiko yana binta da kallon kauna.
______________________
Aliyu yana komawa bariki tacika da murna da Farinciki hatta Dinner dare sai da aka hada aka ci aka sha,akayi Rawan Sojoji sunayi suna wakensu,dayake Jabir shida zafira suka daukosa daga filin jirgi,washe gari kuwa har nan barikin Chief Amry of Staff yazo,suka gana da Aliyu akuma nan take ya samu karin girma daga Captain zuwa *MAJOR ALIYU ABDULNASEER TAMBARI BUZU* Yayinda Jabir yatashi daga Captain zuwa *CONOLE JABIR*,dukkan sojojij da suka je wannan kwantar da tarzoman sun samu karin girma,Ranar barikin tarude da murna,kwana sukayi kide kide da wake wake,haka suka taru waje daya suna rawa da waka suna Fadin _Lalle mune soja,dama kunun salala gidan wuya aikin soja dama kunun salala..._Abun sai wanda yagani,Ranar hatta su kawo sunzo ciikin barikin sun tayashi murna,harda su Anty madina dasu Anty mardiya sai Zafira da jabir,wanda wani shagalin sai wani satin A abuja inda anan ne za"a sanyama kowa rank dinshi.
Haka ko akayi A babban headquater su dake Abuja aka sanyama kowa Rank dinshi,wanda kowani gidan talabejin da gidajen radiyoyi,suke yada wannan Abun dake Faruwa life,Cikin masu kallo harda Ni"ima wacce murna ta cikata sosai,nan take ta dauki waya taturama Gadanga sakon taya murna da Fatan alheri,sukuma su maimartaba Atashar CNN suka gani har lokacin da'ake sanyama Aliyu Rank dinshi na zama major,Murna ba"a mgana domin Shima maimartaba biki na musassam ya shirya,sai alokacin Azeema take jin lbrin Tun komawarsa aka karamai girman yanzu taron tabbatarwa ne,Abun yayi mata tsaye arai wato itace mara amfani ko,domin hatta Safaratu da haisam tagani,taga kowa da kowa,ammh ita saboda bata da wani amfani ko bazata jeba agayamata ma ai wani abune,shiyasa bata karisa kallo ba tabar wajen tana dauke hawayen daya zubomata,Anan wajen aka sanar da anyi Transfer din Major Aliyu daga 1 Division Nageria Amry kaduna zuwa Barikinsu na Abuja mai suna *ABACHA BARRAK*...Sai dai kuma yan kaduna sunyi rashi gashi an saba,ammh babu yarda zasuyi Tunda cigabane kamar ma jabir yaji lbri,kuma anan wajen aka karramma Sojojin cameron,da chadi da Niger,bayan Maigirma shugaban kasa ya jaddada godiyarsu garesu,tare da Fatan Alheri,daga karshe gwannatin kasar Nageria tasanar dasu cewa bazata taba mantawa hallarcinsu gareta ba, Allah yabar zumunci,nan da sati daya duka sojojin ,zasu koma kasashensu cike da samun nasara,suma shawagabanninsu sun yaba da kokarin na gwannatin Nageria tare da jajircewa na sojojinta agaskiya tsarin ya burgesu,sun kuma yaba da wannan tsarin gwannatin Nageria nabama mutane tsaro da kare rayuwankan da dukoyoyinsu,sun kuma yi alqawari bada kowacce gudummuwa in bukatar hakan tataso,jawabin daya sanyaya zuciyar yan kasa,sukaji suma yau suna alfahari da kasar su Ta Nageria nan take aka saka Taken Nageria inda kowa ya mike ya kame,yana bin Taken Nagerian daduka muryansu,dayawan sojojin saboda daraja kasa,yadda sukabama Tutar nageria martaba,sunayi suna kwallah😥,Don Allah masu karatu duk wanda yazo daidai wajen nan akaratunsa yatsaya yayi godiya ga Allah(SWA) daya zamo damu daya daga cikin yan kasa Nageria,in zai samu ku gudanar da taken Nageria,nidai nayi nawa kuma na Fada da karfin *AM PROUNDLY TO BE A NAGERIAN*🙋
Haka akatashi taro,kowa yakoma gidansa lafiya,shima Aliyun bai tsaya anan Abujan ba,kaduna yakoma saboda samun damar parking din wasu kayansa,dakuma sallamar Bakinsu,kwana biyun da karin girmansa yasamu ziyara daga Ni"ima da kawarta muneera Abun mamaki harda mami da Cp Ahmed Sidi na iya,saiga Kwamishina yana nemam Dukawa ma Gadanga wai yana rokonsa gafara saurin dago dashi yayi yana fadin"Haba Daddy taya zaka dukamin,nifa kamar dankane,ni wlh haryau a uba nake kallo ka, don Allah bari ni babu Abunda kamin,kuma wlh ban rike ba"Kwamishina yaji dadin kalaman Aliyu har cikin Ransa yana ta godiya,Aliyu har Gidan Jabir ya karisa dasu suka gaisa da kanwarsa zafira inda tarasa inzata kaisu saboda hidima,Ni"ima tatambayi Azeema nan Yake sanar da ita basu dawo ba tana masarauta ammh zasu dawo kwanan nan,Rokonsa tayi don Allah in yana da hoton Triple ya nunamata,nan take yafito dashi ya haskomata,Santinsu Ni"ima tahauyi tana nuna musu Daddy da mami tana fadin"Daddy ku kallesu,suna kama da captain dina'"Kowa yaji Abunda tace itako da iya gaskiyarta take,bata kula da Abunda tace ba haka ta mikama muneera sunata santinsu,Shiko Umar na gefe Shida Jabir,ammh duk motsin da Muneera zatayi a idonshi baisan dalili ba,tunda suka hada ido da yarinyar yaji faduwar gaba itama haka take abangarenta,duk sanda ta dago ido,sai sun hada ido da Umar,tsarguwa tayi da kallon nashi tatashi ta Fito waje shikuma ya biyota da hanzari yana Fadi aransa"oppourtniy comes one in life"Gwara yayi amfani da damarsa kafin ta kubcemai,yana Fita ya ganta jikin motarsu,nan fa ya karisa gareta da gaggawa ya isar ds sakon zuciyarsa muneera can belive itace wannan hadadden gayen ke cewa yana sonta,kuma ma Dan sarki wow..Gaskiya Abunda bata taba tsammani ba,nan da nan tabada kai bori ya hau,nan take sukayi Sharing nombar juna,suna cigaba da Hiransu,suna bama juna lbrin juna,kafin wani lokaci duka zuciyiyon sun yarda da juna,koda su Ni"ima suka Fito nan suka tarar dasu suna zuba hiransu,duk wanda ya gansu sai da ya fahimci wannan ankullah soyayyah mai karfi,Ni"ima Abun yayimata dadi,dama kullum addu"arta Allah yabama muneera miji nagari tayi aure,sai gashi Allah ya bata,kanin gadanga ta yarda ko batada rabon Auren gadanga toh Muneera zata auri kaninsa suyi zumunci na har Abada,Gadanga bai nuna bacin rai ba,saima kallon Ni",imar dayake da tsausayawa,yana yaba halinta na bata hassada da kyashi,ko fada da wani Ni"ima mace ce so simple shidaya zauna da ita shi zai bada lbrinta,cikin mutumci da karramawa suka tafi bayan Ni"ima ta ciko wasu bakaken ledoji da kayan babys dana Azeema tabashi tace abaiwa mejego da Farko kin amsa yayi saida ta nuna bacin ranta kana ya karba,har suka bar haraban gidajen nasu tana dagamai hannu,wlh haka kurum yaji kwallah,yakuma tabbatarma kansa Ni"ima tanayimai So daya ne tak,babu Surki,gida ya Shige dauke da kayan yana mamakin irin Taurin kan Azeema ko Text batayi mai ba,kuma ya tabbatar da taji lbrin komai,umh wlh xata gane bata da wayau ne, don ya lura yanzu pretty bata shakkarsa.
Achan masarauta kuwa Shirya shiryan dawowan Azeema ya kamkama domin wajen kwananta hamsin kenan da haihuwa ta warke tayi garas da ita,kamar ba ita bace mutane uku suka tsagata suka Fito ba,gyara kuwa tashashi kamar ba gobe ita da kanta takejin kewar mijninta yana tasomata ammh tana kokarin dannewa,Su Afiya kuwa sun kara wayau da girma gasu da jiki Tububu kamar ya"yan Turawa,duk wanda ya daukesu bayan son ya jiyesu saboda sha"awa,ana gobe zasu taho Goggo ta kira gadanga ta sanar dashi nan yake sanar da ita su sauka ta Abuja saboda yanzu ma haka yana Abujan ne tun shekaran jiya yabaro kaduna,jin haka yasa goggo kiran Ummah ta sanar da ita,itakuma Ranar da su Azeemar zasu iso Tun safe direba ya wuceta da ita Abujan,Aliyu yazo yayi musu jagora zuwa cikin barikin,wanda kamar ma ba"a Nageria yake ba,ashe na kaduna kauyene,😃Akuma Aranar su Aliyu suka raka rundunar hadakan sojojin camero da chadi da niger,suka hau jirginsu domin komawa kasarsu,ciki kuwa harda Umar,wanda yakoma kasarsa domin cigaba da gudanar da ayyukansu,ammh yace Nigeria tazama gida garesa,Tunda yanzu ma Anan zai dauko mata.
*am srry for d typing error,ban samu damar tacewa ba*
*Janafty*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
_Special Day..!Special person,..!Special birthday..🍢🍡🍧..! *1/1/2020* May dis Day be d begining of Anoder beutifull year 4u...May there be pleasant,suprises...Loads of joy And infinite happiness...Wish u a very Happy birthday *HEARTBEATDADDY*_😘💃💃❤💕💖
*Chapter 39*
""Azeema sun sauka A abuja lafiya,ita da gimbiya Razeenah sai Inna Ramatu kadai sukazo,sai wata baiwa mai Suna Lami,dattijuwace sosai wacce zata dinga taimakama Azeema da kula dasu Anwar,inna Ramatu kuma daga nan Abujan gombe zata wuce wajen mijinta.
Gimbiya Razeenah ita takira gadanga awaya ta sanar dashi saukansu,bai dau lokaci ba sai gashi yazo Filin jirgin na Nnamdi Azikiwe international Airport,koda ya iso,wajen da Azeema yafara tozali ya kalleta ta kalleshi lokaci daya suka dauke kai,kowa naji da kansa,cewa shi aka batamawa saboda haka shiza"a bama hakuri,ko su Anwar hannu Baba lami ya karbesu kafin ya daukosu su rankayo zuwa cikin barikinsu dake Abuja,ko zaman motan baya ta Shige ta hade rai sosai,gimbiya Razeenah ne ta Shiga gidan gaba.
Suna isa suka tarar da kyau da tsari irin na gidajen wajen harsunfi na kaduna ma girma,domin na nan din 3bedroom ne,da kuma falo har guda biyu,bayan katon kichen mai hade da store,kuma ko"ina yaji kayan alfarma babu Abunda ake bukata dama sai kayan da mutum zai saka su kawai zai zo dashi koda suka iso Tuni Ummah tagama gyara ko"ina harta Abinci sai tayi musu,suna zuwa Sallah sukayi kafin su zauna suci Abinci ana hiran Duniya da tambayan Mutanen chan,itako Azeema tunda tayi wanka tashige dayan bedroom din ta kwanta ko kara lekewa batayi ba,su Afiya suna wajen Baba lami,suma sunyi barci Tunda sukaji Ruwan zafi,da kuma nono,shikenan aka daina jin motsinsu,shiko gadanga Tunda yakawo su ya fice bai kara waiwayan gidan ba,saboda bayaso su Raba hali Shida Azeema don yaga take takenta so take yau takureshi har yatankanta.
Basu samu tafiya ba sai washegari da safe Gimbiya Razeenah da Ummah sai inna Ramatu suka rankayo sai kaduna suka bar Azeema da Baba lami da kuma mijinta Aliyu gadanga,daga kaduna ko kwana inna Ramatu batayi ta matsa tana son komawa gombe aranar Shiyasa Kawu Bala yasaka Direba ya kaita dauke da sha tara na arziki data samo daga Masarauta,dakuma wanda Kawu yakara mata,Gimbiya Razeenah dai tanan nan sai ta kwana biyu inji Ummah.
Tunda Su Ummah suka Tafi Azeema tashige bedroom din data zaba amtsauyin nata,takarayin wanka ta Shirya cikin Riga da sikat na Atamfa,wanda suka dauketa sukamata cas dasu,Baba lami na Falo tana Fama dasu Anwar yan Rigima itako kichen tafada domin lokacin har 11 ta gota yakamata tadora musu lunch ko badon Shi ba,don cikinta dana Baba lami.
Farar Shinkafa tadafamusu,saboda babu cefane,dama tazo da Soyayyar miyarta wacce taji kaji aciki,daga Niger wanda goggo da kanta ta soya mata shi,sukaci da ita,suna gama ci ta kwashe Abunda suka bata ta kai kichen ta wanke ta kife ta tsabtace wajen kamar ma batayi girki ba,tadawo Falo ta amshi Afra dake kuka tana Shiga bata Nono,Tagama bata kenan Ta karbi Anwar tana bashi ita kuma Afra baba lami ta sabata,tana dan jijjigata nonon ya kwantamata kada tadawo da ita,sai ga Gadanga yashigo da sallama,Azeema na jin sallamansa ta hade rai,tayi kini kini dashi,Baba lami ce ta zube tana jeramai Sannu da zuwa ya amsa yana mika hannu ya karbi Afra dake hannunta yazauna kusa da Afiya wacce ke kwance tana wutsil wutsil da kafafunta,kumatunta ya latsa yana Fadin"Afi Afi yanmata,kina wasa ne..? yafada yana daga Afra dake hannusa,Baba Lami kuwa Tunda ya amshi Afra ta shige dayan bedroom din da Azeema ta sauketa aciiki
Ta gefen ido yake kallon Azeema,ammh Abun mamaki ko kallo bai isheta ba,balle yasa ran zatacemai sannu da zuwa,itakuma abarayinta ta dojene Tayimai banza,saboda ita ganinta shiyakamata yafaramata sannu da zuwa saboda itace ta sha hanya kafin tazo inda yake,ammh saboda Wulakanci jira yake tamai mgana Shikuma ya tsinkata,aiko tace wlh ya bushe indai itace wlh.
Ganin yadda tawani hade rai kuma ta dauke kaine yasa Shima ya tattarata ya watsar ya cigaba da wasa da ya"yanshi,ganin haka yasa Azeema ta mike tana gyara rigarta kusa dashi taje ta ijiyemai Anwar Tajuya ta Shige daki tana wani Taku,wanda har aran Aliyu yaji wannan Tafiyar,baki ya rike yana binta da kallo wai ma yaushe Azeema takoma hakane? Abun fa mamaki yake bashi,ya"yansa yayi Ta biyemawa yana wasa dasu yana kuma mgana kamar ya samu wasu manya,suko kamar sun sani suyita washe baki suna bangala dariya,yadda bai nemi abinci ba,shiyasa itama batayimai Tayi ba har sai bayan la"asar kana ya bar gidan,bayan ya kira Baba lami ya dankamata su Anwar yayi Ficewarsa.
Koda ya dawo bayan issha'i,ko takan Azeemar bai bi,yayansa kadai ya dauka yayi musu wasa kafin ya mikama Baba lami su,yayi Shigewarsa daya Bedroom din da kayansa ke ciki,itako Azeema tana jin adawowarsa taki Fitowa dama abincin dazu da Rana daya ragu sukayi Dinner dashi,saboda taga alamun bayan ita harta Girkinta ma baya Ra"ayi,shiko Abun ya dameshi na kyaluwan da Azeema tayi dashi,wlh bai zata ba,kuma tana sane itace bata da gaskiya kowa na ganin laifin kowa kenan.
Washegari Tun Safe Azeema tatashi ta tsaftace ko"ina kafin lokacin Tuni Baba Lami ta wankesu Anwar ta shiryasu cikin kayansu na alfarma,ita kuma Azeema harta Fada kichen tana kokarin nema musu breakfast,ganin duk babu cefanan Abinci yasa kawai ta dafa musu macaroni,Suka sake ci da miyar jiya,domin yadda takejin kanta bazata iya bude baki tace yayo mata cefane ba,toh Shi da baya cin abinta yaushe zai yomata cefane,🤔kaji mata kin bashi ne kikaga baici ba?
Wanka tayi cikin Riga da wando na wani pakista,mai kalan pick,yayi mata kyau sosai,sai ta daure gashinta ta baya ta zuboshi ko dankwali bata sanya ba,tafito falo bayan takoma kichen ta sanyo musu macaronin ita da Baba lami ta kawo mata,ita kuma tazauna kan kujera tana tsakuran Abuncin kamar ansata dole,gefe daya kuma hankalinta na bisa talabijin tana kallon wani Shiri A Mbc2,Saiga Aliyu ya Fito sanye da bakar jallabiya alaman yanzu tatashi,gaisuwan Baba lami yake amsawa ammh idonsa na kan Abincin da suke ci,macaroni da miya dasafe kuma? ya tambayi kanshi kafin yakalli Azeema yace"ki Rubuta dukkan Abunda kuke bukata,in na Fiti nayo cefene"In kun tanka Azeema ta tanka,don saima tatashi ta Shige kichen tana wani takun dai dai kamar wata wahainiya,Girgiza kai kawai yayi yakoma daki,yayi wanka ya Shirya ya Fito,ko takanta baibi ba yafice,ammh bayan ya Shiga dakinta ya iske tana tiolet,kan Gadonta ya ijiyemata ledojin kayan da Ni"ima takowa yayi Ficewarsa,sai da Tafito taga kaya akan gado,zazzagewa tayi tana dubawa kafin tayi kwafa,ta maidasu cikin ledojinsu ta ijiyesu nan tashiga harkan gabanta,shiko bai dade da Fita ba sai gashi ya dawo dauke da cefane niki niki,duk Abunda take bukata sai da ya siyomata,Shida Baba lami suka dinga jindan kayan suna kaiwa kichen hakima Azeema na daki tana jinsu taki Fitowa,saima gyara kwanciya datayi Abunta.
Yana gama Shigo dakomai yayi Ficewarsa hatta Baba lami ta Fahimci tsakanin ma"auratan babu zaman lafiya Aranta tana Fatan Allah ya daidaitasu,tana jin Fitarsa tafito da hanzari Taja ledojin daya ijiyemata ta kaimishi daki ta dungurar kan gadonsa tayi Fitowarta kichen Ta fada tana dudduba Abunda ya siyo,nan da nan ta saka masu lalacewa cikin Fridge,sauran kuma ta sakasu cikin ma"adana,bata koma daki ba,ta kunna gas,don yau wlh Tuwon semo takejin ci,shi ta dora da miyar Kubewa danyan,don ta ganta acikin Cefane,don Ta lura ko agidan goggo Bata Rasa danyan Kubewa saboda Yaya captain.
Bata dauki wani lokaci ba,ta kammallah ta mulmule Tuwon aleda ta zubasu cikin wasu sabbin kololin nan kichen din ta bar komai bayan Baba lami ta taimakamata da wanke wanke Tunda su Anwar sun samu barci,ita tabar gyara kichen din,itakuma takoma daki ta Shiga wanka,ta Fito kenan Taji Mganarsa Afalo,yana ma Baba lami Fadan meyasa aka bar Afiya su kadai adaki,hakuri tayi ta bashi,tanaji yayi Fuu ya Shige dakinsa baki tatabe kawai tacigaba da Shafa manta,tagama kenan ta isa gaban Wardrope din ta na neman kayan dazata sanya ya Fado dakin Afusace dauke da lodejin dazu yana Shigowa ya nunota dasu yana Fadin
"Meye haka Pretty naga kin dawomin da kaya? aiko wani Abu ne kya jira nazo ki tambayeni nayi miki bayani..? yafada yana kafeta da ito,banza dashi tayi saima juya masa baya datayi tana Cigaba da Abunda takeyi,wani Abu yazoma Gadanga wuya ya jefar da kayan kan gado,da sauri ya isa gareta sai dai taji an wani Fizgota tatafi kamar zata Fadi,ya riketa da kyau har Suna gogan Numfashin juna,Kallonsa take ammh batayi mgana ba,ganin yadda yake wani Huci,shikadai yace"Ina miki mgana Saboda wulakanci kina min banza..?
Kokarin kwace hannunta take ammh takasa harara ta sakarmai tana Fadin",Ina ce kunne keji ko,don Allah mallam ka cikani"Tafada idonta ya kwallah Tsuramata ido, yayi Fushinsa na Sauka kafin ya sausauta rikon dayayi mata yana Fadin"Ki kwashe kayannan, danaki danasu Afra ne, Ni"ima ta kawo tace na baki.."Yafada yana Sakinta yakama hanya zai Fita ta waigo tana Fadin"Au kace Tsohuwar budurwanka ta kawo,ai dole ta kawo Tunda bayan dawowarka ta maye gurbina,Kaga don tayima abokin Shasha......
"AZEEMA.....""!!!!Aliyu ya katseta da karfi da kuma wata tsawa mai gigitarwa wanda sai da tayi baya jikinta na Rawa,taku yafarayi zuwa gabanta idanuwansa sun chanza launi,kafa daya yadora bisa gado yana kallon Azeema yace"Kinfi sanin Ni"ima ne?kokuwa na riga saninki kafin ita,in inason yin iskanci da ita ai ba sai kin Fada ba,datun Farko da mahaifinta yahani Aurenta dana samarma kaina mafita,yanzu Ni Azeema Saboda Ranin dakimam yakai haka harzaki bude baki kice ina Shanshanci ko? yafada idonsa yana wani juyawa Shuru tayi ta kasa mgana,dauke kafarsa yayi yana Sauke ajiyar zuciya kafin yace
"Koda ina Saurayi ban lalace ba Azeema,kuma saboda Rashin sanin darajan kai narasa lokacin da zan yi Shashanci sai lokacin da kika zama jini da hanta na,kikagama mamaye dukkan Numfashi,bayan kin zamo uwar ya"yana?...Yafada yana nuna kanshi,Kuri yayi mata da ido,ganin yadda yake kallonta ne yasa ta sadda kai tana jin Nadamar Abunda Tafada.
Juyawa yayi zai Fita Yana Fadin"Babu komai Rayuwace..."Yafada yana kokarim Ficewa Saurin Shan gabansa Azeema tayi jikinta duk yayi sanyi,sadda kai tayi kafin tace"Ni ban fada haka har zuciyata ba kawai na fadane Saboda Haushin Ratayen nin dakayi shine kawai Fa.."Tafada idonta na kawo Ruwa,hannunta ya riko kafin yace"cikin ni dake waya Fara rataye wani ehe? nina Fara jan fadan daga baya ban kiraki ba kika kidaga kirana ba? ko ban Nemiki ba? yafada yana kallon kwayan idonta.
Raurau tayi da ido kafin tace'Nima alokacin Haushi naji ka doramin laifin da kasani ba laifina bane.."Matse mata hannu yayi yana Fadin"toh naji ammh kome nayi miki pretty ai ni mijinki ne,yakamata dakika dawo ki girmamani amtsayina na mijinki ammh kiduba yadda kika watsar da Rayuwata why pretty?yafada kamar zai mata kuka,itama kukan ne ya kawomata kawai Sai tafada jikinsa tana Fadin"Nayi kuskure mijina don Allah ka yafemin.."
Rumgumeta Yayi kamkam yana Fadin"Shii..Is ok komai ya Wuce nima kiyafemin kinji.."Yafada yana Shinshinar wuyanta,kamkame juna sukayi kamar wani zai Rabasu Fadi yace"Do u know wht? i miss u So much pretty wlh ko barcin kirki banayi saboda Tunanin kina Fushi dani plz karki kara barina,Rayuwa babu ke tamkar rayuwace babu jinin jiki.."Hawaye suka zuboma Azeema tace"Me too i miss u more,kuma i promise u am not let u down insha Allahu.."Jin haka yasa yadago kanta yayi Saurin dora lebenshi bisa nata yana yimata wani salo,wanda Tuni da dage ta nadeneshi tana mikomai harshenta da hanzari ya kama,yana mata wani Sumbata mai gigita ya"ya mata,kafin kace me,sun Rikita junansu,dama Azeema daga ita sai Tawel,wanda Tuni Aliyu yayi Fatali dashi,cak ya dauketa sai bisa gadonta,anan aka warware komai,Aliyu Tunda ya Shiga birnin Azeema Shikenan ya Susuce Fadi yake"pretty don Allah ki zauna dani,wayyo..""'!Dadi wlh kina Rabuwa dani zan mutu ne..!Sai da Ta rufemai baki sanin basu kadai bane agidan,Itako daman Baba lami tana Falo,tun sadda taji hayaniyarsu ta kwashe yara su Shige daki,aranta tana addu"ar Allah ya daidaita ma"auranta.
Sai da komai ya kamkama bayan Sunyi wanka sun sauya kaya kana Suka Fito falo cin abinci,sunyi Shar dasu gadanga ko bakinsa har kunne,Ranar ma bisa Dining akaci abincin,Shiyasa Baba lami na ganin haka tace ita adaki zataci nata,saboda taga yau ma"auratan babu dama fa,aiko gadanga yaci tuwon nan sosai yana ta zuba santi,suna kammallahwa ta kwashe komai takai kichen,tana dawowa Tashiga dakin Baba lami ta basu Anwar nono,suka sha kafin tayi mata sai da Safe ta Fice,dakinsu ta koma inda uban gayyar ke jiranta tana Shiga ko ya kamata ya kamkame yana wani lumshe ido,datayi mgana sai yace shifa wlh an wahalar dashi dayawa gwara abarshi ya famshe da kyau.
Shikenan zaman ma"auratan ya Daidaita basu kara samun wata mtsala ba,sai ma wani karin so da kaunar juna sukeyi,Ranar da Azeeema tacika sati dadawowa Ranar Gimbiya Razeenah takoma Niger,ammh sai da Ummah ta matsamata ta rakata gidan Jabir taga zafira,murna ba"a mgana kuwa duk da basu dade ba,ammh sunji dadin zuwanta,ai Safaratu dake kano najin lbri takira Ta tana kuka akan wlh itama bata yarda ba sai tazo mata yata iya dole ta Shirya Ummah tarakata taje ta wunin mata,suka rasa ina zasu sanya iyayan nasu saboda farinciki kowacce tayi kiba bulbul Daga gani suna samun kulawa daga mazajensu,bata samu damar komawa wajen su Azeema ba,sai dai sukayi sallama ta waya dasu,suna bata sakon gaisuwa zuwa ga yan gida.
*BAYAN WATA BIYU*
Bayan wata Biyu Da Dawowar Azeema,Tuni su Afiya sunyi wayau sunkara girma kamar ba yan wata hudu ba ita kanta Azeemar tayi kiba takara haske da kyau,to takowani bangare suna samun kulawa,ga kulawar miji kamar ya cinyeta danya bata gasu ga,sunje kaduna sau daya bayan dawowarta,kuma su Haisam da jabir,sun zo Rana daya kowanne da matarsa sun musu kwana daya suka koma,mganar Auren Umar kuwa yazo Nageria sau daya Kawu maimartaba ya wakilta akan mganar babu wata bata lokaci har ansaka Rana Wata biyu yanzu haka biki baifi sati biyu ba ya rage,suna so suyi Shiri gabadaya ne daga chan dukkansu zasu wuce kasa mai Tsarki ne su sauke farali.
Koda Azeema taji lbrin Auren Muneera da Umar bataji komai ba,illah tsausayama Ni'imar datayi domin ko qur'ani zata dafa,Mijinta bayi da Ra"ayin Aurenta yanzu,ammh bata sani ba ko zuwa gaba,domin tataba latsashi akan mganar Ni"ima yayimata Fada sosai yace babu Ruwanta bata fishi sanin Ni"imar ba,daganan takama kanta,bayan an saka Ranar su da Umar,har Abuja sukazo suka wunin mata ita da Ni"ima sai alokacin Azeema tafahimci wacece Ni"ima sam bata da mtsala ko muneera datakeda Rawan kai yanzu duk ta rageshi,Ni"ima Tunda tazo take wahala dasu Afiya da wannan yayi kuka ta sabeshi ta goya,ta dauki wannan Ta hau jijjigawa,ita dai Allah ya Doramata sonsu,Umar da kanshi ya maidasu har gombe da Kayan kwalliyan da Azeema ta hada musu,da farkoma kin karba sukayi sai da tace ko Sun Raina ne?shiyasa suka karba,Shiko Aliyu Tun zuwansu bayan sun gaisa yayi Ficewarsa ko daxasu Tafi Azeema ta kirasa awaya sai cewa yayi Allah kiyaye hanya yanzu zasu Shiga meeting ne,Azeema bata jin Dadin Abunda yayi ba sam wlh duk kunya yakamata,daya dawo sai da tamai mgana banza da ita yayi bai Tankataba Aransa yana fadin"mata masu Duniya yanzu fa daya dawo sai tace yayi laifi kuma oh sudai bamai iya musu sai wanda Ya hallicesu.
Yan Nageria basu Tafi Agadez da wuri ba Sai da Aka Daura auren Umar da Muneera wanda Kawu ya karbomai Aure don maimartaba bai samu zuwa ba,su goggo suna chan suna Shirye Shiryen Zuwan Amarya suko su gadanga sai Awashegari suka dumgumo zuwa Masarauta dashi da jabir da zafira sai Haisam da Safaratu,sai Kawu bala da Ummah,sai Anty madina da Anty mardiya,kowanne da yayansa da mijinta,sai Kawu lawal da inna Ramatu,sai Azeema da ya'n ukunta sai Baba lami,wanda daga chan dukkansu zasu wuce kasa mai tsarki Sai ko Amarya Muneera da angonta Umar,sai Aminiyarta Ni"ima,sai kanwar babanta daya da kuma Yar"uwan mamanta dasu kadai akazo saboda nisa,don itama Amarya da angon dasu za"a Tafi chan Saudiyan.
Koda suka isa Masarautar Tambari buzu ko"ina ya cika da mutane anata Shagulgulan zuwan amarya,kai tsaye Shashen goggo aka kai amarya sai Awashegari ne,aka Kaita Fada jakadiya ta sanyanmata alkayyaban Sarauniyar Tambari buzu ta biyu,maimartaba ya sanyamusu albarka kafin awuce da ita Shashen mahaifiyarsa,bayan anfito da ita daga shashen Gimbiya Razeenah,daganan Ita Gimbiya Fasilatu tabasu kyautan kudi harda zinare,suka rankaya zuwa Babban Shashen na Yarima Umar,wanda lokacin kadan zasu zauna da sun dawo daga kasa mai tsarki zasu tarrara su koma Niamey inda yake aiki.,Duka duka kwana biyu su Ni"ima sukayi suka koma Nageria cike da Abun arziki tare da karramawa irinta masarautar Tambari buzu.
******************
Duka duka Sati biyu ne da zuwansu garin Suka tattara duka Ahalin suka yada zango abirnin madina,harda su Maimartaba da duka matansa guda uku,gaskiiya wannan Tafiya tafiyane mai cike da Nasara,domin sai da suka kwana goma Amadina suna Ziyara kafin su wuce garin makka,inda kowa ya zage Yana ta ibada babu kama hannun yaro,Azeema data ganta gaban ka"aba sai da tayi kuka,haka tayita rokon ma Mahaifiyarta gafara da kuma Azeeza,sai ta rokon ma mijinta fatan nasaran rayuwa dakuma Allah ya rayamata ya"yanta cikin Tafarkin Adinin islama.
Kwanansu goma Sha daya agarin makka,lokacin angama aikin hajji,su maimartaba da matansa da kawu Da ummah da mallam lawal da Baba Ade,da Inna Ramatu,a birnin makka suka bar su Gadanga suka koma gida,domin dukkansu ba gida zasu koma ba,daganan birnin london suka yada zango,sai da sukayi sati kafin su Wuce Canada,nan din sati sukayi kafin daganan su wuce india A birnin New Delhi,sai gasu har gidan Drkhabir khan,wanda Fadan irin murnan da Sukayi Shida matarshi bata baki ne,har cikin asibiti suka shiga zo kuga yadda ake ihun zuwansu love birds,sai hotuna ake dasu ana Daukan Su Afiya wadanda suka kara wayau suka girma,nan ma sai da suka Shafe sati suna yawata gari kafin suyi haraman komawa gida,ta Abuja suka sauka daganan aka Rabu kowa ya nufi inda yafi wayau sudai su gadanga sunzo gida ne,Haisam daganan suka wuce kano Shida Safaratu,sai su jabir dasu Anty madina suka wuce kaduna,Umar da Muneera kuma Tun a India suka rabu su jirgin Niger zasu Shiga sukuma suka Shigo na Nageria.
Bayan dawowansu ba Dadewa Aliyu yaje ya karboma Azeema takardun ta na gama mkranta a gombe yazo yayi mata Rigisteration a BASE UNIVERSTY inda zata karanci PHAMARCY,murna wajen Azeema ba"a mgana Ranar da zatafara zuwa daukan lecture saboda zumudi ko barci batayi ba,gari na wayewa sai ga sabon Suprise,sabuwar motar ta kirar Toyota 306 Aliyu ya dankamata yace Ayi karatu lafiya,Ai Azeema kamar zatayi hauka haka ta makale Aliyu tana kuka tanamai godiya,dama already ta iya mota bayan dawowarsu Abuja,sai ta dinga barin ma Baba lami su Afiya tana tafiya mkranta,inkuma sunada interval a mkrantan takan dawo gida Ta basu nono takoma.
Azeema shiganta mkranta takara wayewa sosai,kuma bata yarda tayi kawa da kowa ba,saboda kashedin Gadanga akanta,tsakaninta dakowa hy hy ne gashi Kwakwalwarta naja kaf Depertment dinsu asan da zamanta mai kokari ce,gata da kamun kai da tsare gida babu Ruwanta da naza,matan ma kwarjini take musu tsoron tanka mata suke,Wani lokacin batajin Tuki da kanta Shiyake kawota yakuma zo ya dauketa Domin preetty tazama shi,shikuma yazama ita,Abunda ke kara sawa yake kara sonta ko mai takeyi bata iya hadashi da Laluransa,shi na musamman ne,domin duk Abunda takeyi dayazo da bukatarsa zata ijiye taji dashi,shiyasa yake kokarin tallafamata tasamu tayi karatun nan saboda shine babban burin Azeema ayanzu.
_Today is a special Day To me_💃💃💃💃
*Janafty*
*ALIYU GADANGA..!*
_(The Story of Young Soldier man)_
*Wattpad:Janafnancy12*
_Mallakar:Janafty💖_
*DEDICATED TO MY MOMMAH...HAUWA S ZARIA(MMN USWAN)*
_Special gift to my Real Dota RAHMA😘Ladingo yar mutan Niger_
*Intelligent Writers Association*✏
*KA'RSHE*.... _END_😥👏🙌✌
*Chapter 40*
""Azeema bata Rufe Shekara da Shiga mkranta ba,Ciki ya bulla ajikinta,lokacin sunyi jarabawar Karshen semister,sun tafi hutu suna Shirin zuwa aji biyu,Inda Allah ya taimaketa Su Afiya shekaransu daya lokacin da wata daya,tuni sun yi girma suna Tafiyansu ko"ina,in ka gansu bazakace Azeema ta haifesu ba,sakamakon basa kama da ita ko kadan,Sai da da Aliyu suke kama,kana ganinsu daga gashin kansu zaka zargi kodai sun hada jini da larabawa ko Buzaye cikin biyu za"ayi daya,balle yadda Su Afiya suka dauko bakin gashin babansu,suna kanana dasu,ammh in Azeema tamusu tsifa ta daure musu da band Abun sai masha Allahu kawai.
Da farko Azeema tayi bori game da cikin jikinta,ta dinga kawoma Aliyu uzirinta,ga yara basu bar shan nono ba ga Kuma karatunta ita yanzu ya zatayi,zama da ita yayi yayita lallashinta dayaga taki yarda sai ya dauketa sukaje wani privet hopital suka samu wata likita,yasanar da ita mtsalansu nan da nan ta Shiga yima Azeema Fadan,ya Allah zai bata kyauta kuma tayimai butulci,tasan Adadin mutanen da suka zauna a inda take,suna mata kuka Allah bai basu haihuwa ba,koko tasan Adadin mutanen dake zaryan awannan hospital din duk dan Allah ya basu haihuwa? Azeema ta girgiza kai Hawaye suna zubomata tacigaba da Fadin"Kuma Shine ke Allah yabaki Kike neman kiyi butulci toh ahir dinki domin sai Allah yabarki da dubaranki,ai yafi ki sanin kina da ya"ya kuma ya zabeki acikin dubu ya baki wannan kyautan,toh tun Wuri ki daga hannu sama ki godemai kada Allah yayi Fushi dake"
jin haka yasa Azeema ta daga hannu hawaye na zuba tana godiya ga Allah,nan likitan ta sausauta takaramata da shawarwarin yadda zata kula da kanta da ya"yanta,Tunda ma taji su Afiyan sukai shekara daya tace ta ciresu anono babu damuwa,Sai acigaba da basu abinci wanda zai cigaba da gina musu jikinsu,magungunar karin lafiya dana karin jini ta Rubuta musu sukayi mata sallama,sai da suka biya phamarcy suka siya magungunar kafin su Wuce gida,Ranar dai Azeema kuka ta Wuni yi,Aliyu na aikin lallashin Tunda aiki ya riga ya sameshi.
Haka Azeema ta cigaba da kula da cikinta sukuma su Afiya Ta ciresu anono ta damkama Baba lami tana cigaba da kula dasu,itama kuma tana Renon Cikinta tana kuma cigaba da karatunta babu wani mtsala domin Aliyu na tsaye kanta ita da ya"yanta,Cikin ikon Allah sai ga Azeema ta haihu kusan lokaci daya da Zafira,Azeema ta haihu yau Zafira ta haihu washegari Kuma duka mata Ranar suna Yar wajen Azeema taci sunan Gimbiya Razeenah,,suna kiranta Sajida,sai yar wajen zafira taci sunan Mahaifiyar Jabir wato khadija suna kiranta Meenal,tsakaninsu da Safaratu kwana goma sha biyar ne ita ta sauka ta haifi danta Namiji wanda yaci sunan kawu Bala,suna kiransa da Sajjad.
*AFTER 5 YEARS*
""Ashekaru biyar da suka gabata Abubuwa dadama sun Faru na Farinciki da akasinsa,na bakinciki Shine Rasuwar Ummah mai babban daki,tare da Rasuwar Baba Ade wadanda suka rigamu gidan gaskiya,Sai dai muyi Fatan Allah ya jikansu Da Gafara Ameen.
Ababen Farinciki kuwa Shine Shekaru biyu dasuka gabata Maimartaba Sarki Abdulnaseer Tambari buzu,yayi murabus daga kan karagan mulki ya nada da'nsa Aliyu Abdulnaseer Tambari,wanda yayi Retire,a aikin Soja,suka tararra shida da duka iyalansa suka dawo Niger da zama lokacin Azeema ta kammallah karatunta sai tazo nan tayi bautar kasarta,Nadin sarauta da sai da aka jadaga kafin Ayishi domin Aliyu Tuburewa yayi Shifa baya bukatar Sarauta yafi bukatar Aikinsa Fiye da komai,ga Umar nan Adorashi shi yabarmai har Abada,Sai da yaga maimartaba yanuna bacin Ransa sosai,kuma su Kawu bala da Mallam lawal suka tayimai Nasiha kafin ya yarda,itako Azeema daga sama taji Abun kamar almara wai Aliyunta zai zama sarki,bata nuna Rashin goyon bayanta ba,saima kara karfafamai gwiwa dataitayi,lokacin ma tana da wani cikin ajikinta,Shi duk damuwarshi daya yasan baza"a barshi yazauna da Azeema ita kadai ba,dayayimata wannan complain kallonsa tayi tana dariya tace"To sai me Ehe,ai wlh bana da wani haufi akan Sadaukina ko yanzu wata ta Shigo na tabbata ni Azeema nayi mata zarrah har Abada,saboda haka karka Damu kanka ga Ni"ima,babu wacce ta dace ka aura sai ita,domin itama masoyiyarkace ta gaskiya nekamar muneera taji lbrim wacce ke Fadin kyawawan Halayyan Azeema domin tana bata girmanta amtsayinta na Matar wan mijinta,ita ma Azeema tana tafiyarta da ita yadda Yakamata.
Sai Ranar Daura aure kana Sarki Aliyu Abdulnaseer Tambari buzu,dashi da tsohon sarki Abdulnaseer tambari buzu,sai ga kanin kwamishina daya hana auren Ni"ima Da farko kunyama tanahashi bada auren akaro na biyu,sai wani ne ya basu Auren,yau ga mahaifin Aliyun dayace sai yazo,toh gashi gabanshi wanda ko daga ido ma yakasayi ya kalleshi bayan Daura Auren kwana daya kawai sukayi Aliyu ya tarraro matarsa suka dawo masarauta,inda ya hadata da Azeema yajata mata kunne,kuma koma baijamata Ni"ima Ta riga data sani Azeema ta mata Zarra,ko goggo Fadan datayi mata kenan Ta girmama Azeema,kowama haka yake Fadi,aiko dole ta girmama Azeema ko taki ko taso,itako Muneera bata zo bikin ba,suna Niemiy, cikinta ya Tsufa yarima Umar ne kadai yazo,shima kwana biyu yayi yakoma Wajen aikinsa.
Ni"ima Ta yarda Azeema ce ke gaba da ita binta take sauda kafa,domin Aliyu ya sanar da ita da Amincewarta ya aurota,so dole ta godemata,ita kuma Azeema ta kama girmanta domin itace Shugaban matan Sarki kuma Sarauniya kwara daya tal mai mulkan zuciyan Aliyu,kowace Ranar datake da kwana zata bi miji Turaka,ammh ita Azeema Aliyu da kanshi yake binta,ita ta hanashi saboda tabashi hadin kai ya kwantanta Adalci.
Ayanzu haka Ni"ima nada diya daya mace mai Suna Umaimah,suna kiranta Ummah,sai Azeema wacce takara bayan Sajida tayi Jabir,sai Bala na karshe wanda suke kira Kawu,Muneera ma ya"yanta biyu Aliyu da Abdulnaseer,sai Jabir dake da uku Haisam kuma biyu haryanzu Safaratu bata kara haihuwa ba,zaman lafiya tare da zumunci yana kara karfi atsakaninsu Inna Ramatu kuwa da Mallam lawal Tuni maimartaba yaci galaba akan Baban Azeema sun dawo masarauta da zama,yau sai ga Inna Ramatu na tsoma biyar tana wanke goma,harta da bayi tana dashi bayan katon Shashen dasuke zaune wanda yaji kayan alfarma.
Su Afiya kuwa sun girma don Suna da shekaru Shidda kenan Aduniya yara ne kanana ammh masu Tunanin manya mgana chakwai babu wanda basayi sun ruga sun saba da Baba lami da Maminsu Ni"ima Shiyasa Azeema in ba wani Abu sukeso ba,basa ma nemanta suna Sheshen Tsohon sarki Abdulnaseeer ko Shashen inna Ramatu ko wajen Ni"ima.,ayanzu haka Azeeema nda katon phamarcy acikin Masarautan wanda Aliyu yasa aka kirkireshi saboda ita da kuma karatunta aka Cikashi da mgunguna,duk Abunda ake bukata konawani mgani zuwa kawai za"ayi A nunamata da kanta zata je ta dauko mganin saboda tariga ta karantu akai.
Shekara Daya da da komawarsu Niger,Siyasa ta kusanto,kawu ya Fito takarar gwannan jahar kaduna cikin ikon Allah kuwa yasamu nasaran Hayewa kujeran gwannan jahar kaduna,ayanzu haka suna gidan gwannnati Abunsu,suna cikin Shekara na biyu kenan akan karagan mulkin.
********************
Sarauniya Azeema ta zauna a kayatattacen Falonta wanda yaji kayan alfarma zaune take Akan wani Tuntu,jikinta sanye da wata alkayabba mai Ruwan zaiba,kallo daya zakamata ka Fahimci tsabar hutu da Mulki tare da jin dadi sun lullube Azeema,tare da wani girma kamar ba yar Shekara 28 aduniya ba,gefenta yar Amananta ne Baba lami,wacce haryanzu suna tare basu rabu Azeema na nan A uwar dakinta
Tuffa takeci Baba lami na gefenta suna mgana kan Wani lokacin achan baya Baba lami na bata lbrin ada ita batasan Tuffa ba,don ita ta aza wani Abu ne dabam,dan dariya Azeema keyi cike da Nishadi,sai ga Anwar ya Shigo da gudu bayanshi Afra ne basu dire ko"ina ba sai jikin Azeema Baba lami ke fadin "A'a megida meye yafaru kuma? wayar hannunsa ya mikama Azeema yana Fadin"Ummi wayarki wlh Tun dazu afra ta dauka tana miki game aciki,kuma Abbu sai kira yake"Karbe wayar Azeema tayi tana kallon Afra dake hararan Anwar,shiko yana mata gwalo,kunnenta ta kamo ta matse tana Fadin"Kin Rainani ko,bakijin mgana ta ko? har yaushe zance kada ki kara daukan min waya ammh bakiji ko,wlh koda wasa kika kara sai nasa sarkin dorina ya zanemin ke,wuce kibani waje.."Tafada tana sakinta,kuka ta fashe dashi ta Fada jikin Baba lami,itako tariketa tana lallashinta tana Fadin"Ke share hawayenki,so kike Maimartaba yace ya fasa auren,kefa matar sarki ce maza share hawayen"Tana Fadar haka ko ta Share hawayenta ta mike tinkis tinkis ta Fice sai Shashen su goggo tana zuwa Ta fada jikin Tsohon sarki Abdulnaseer,tana kuka rikota yayi yana fadin"waye mai tsautsayin daya tabamin ke? matse kwallah tayi tana Fadin ba"Ba Ummi bace ta min Fada ba..",Baki Maimartaba ya rike yana Fadin"a.hhhh babban mgana lalle dole Ummi zata Fuskanci Hukunci kinji share hawayenki kinji amaryata"goggo dake gefe ita da Gimbiya Fasilatu suka tabe baki suna Fadin"Wannan amaryan taka ta Cika shagwaba"cewar goggo,Mele baki Afra tayi kafin tace"Sarkina ka koresu su fita"Dariya maimartaba yayi kafin yace"Angama ranki shi dade..,kutashi ku fita tunda kunji Abunda Amarsu tace",Tashi sukayi dukkansu suna Fadin"Ko bakace ba gaka gata zaka nememu ne"Mirmishi yayi yana Fadin"injiwa Ga Amaryata ni ba wanda zan nema"Yafada yana dariya itako Afra ji'iran Yarinya harda musu gwalo.
achan bangaren Afra na Ficewa wayar Azeema ta sake daukan Tsuwa jin Riging tone din mai kiran kadai sai da ta murmusa,mikewa tayi tsam ta koma cikin bedroom dinta tabar Baba lami suna chasheta ita da Anwar dama dan Rigimar tane,sai ta fada bisa gado kana ta daga kiran Tana Fadin"Allah taimaki maimartaba mai mulkan mutanen agadez..."Mirmishi yasaki mai kayatarwa kafin yace"Kin Fadi jarawabawa pretty,cewa zakiyi maimartaba mai mulkan zuciyar Azeema Shikadai,da'ace kin Fadi haka Tun Farko da kinsamu wata kyauta.."Dariya tayi mai kayatarwa tana Fadin"ko ayanzu ban makara ba bari na gyara maimartabana wanda ke mulki tare da iko azuciyar Azeema ita kadai.."Dariyan Farinciki yayi kafin yace"Maki goma pretty..."Bata Fuska tayi kafin tace"kawai maki goma Yaya captain"saurin katseta yayi da cewa"ba kawai bane preety maki goman dana baki,sunfi maki darin da wani zaici awajen jarabawan Fita daga jami"a,yanzu dai duk ba wannan ba,nayi kewarki kwana biyu ne,wlh ko zaman Fada nakasa yi,shiyasa nace atafi hutun rabin lokaci,shine na samu daman kiranki.."Baki ta rike tana Fadin"a"a Mijina,kafasan sai gobe ne zaka dawo wajena,yau Ni"ima ce keda Turaka,don Allah ka zauna,karfa ka manta akwai hakkin jama"a dadama akanka,bani so ka zama mara adalci agaresu don Allah..."Shuru kawai yayi yana jinta kafin ya sauke ajiyar zuciya yace"Shikenan pretty zanyi Abunda kikace,Ammh wlh bazan boyemiki ba, nidai an cuceni an hadani da aiki ga Sarauta ga karin kwanaki kafin na kasance dake mtseww.."Kawai taji ya yanke kiran,ajiyar zuciya ta sauke tana Tunanin yaushene yaya captain zai rike Sarautar da Allah ya bashi,kullum cikin cewa yake shi an cuceshi anhadashi da aiki,daman ma tana iya bakin kokarinta da batason mai zai yi ba,tashi tayi tsam ta Wuce shashen Ni"ima don batajin dadi tun jiya tana ta fama da amai da zazzabi likita tazo ta gwada ta ta tabbatar da ciki ne da ita
Koda Azeema ta isa shashen Ni"ima chan ta sameta kwance su Jabir nata duduma kanta,shida Sajida,Ummah kuma na gefe tana wasa,Afiya babbar banza ta zaune kan kujera tana ta lissafin banza,domin itace sak mahaifinta kwata kwata bata da yawan Mgana,ko zasu kashe kansu bazata tataba tankasu ba,tsawa Azeema ta bugamata tana Fadin"zan makeki yanzunan,wawiya kawai kina ganin bata da lafiya bazaki iya hanasu damunta ba,ammh kina zaune kamar wata sokuwa.."Narke Fuska Afiya tayi kafin tace"To ni Ummi ya zanyi dasu.."Harara Azeema ta sakarma kafin tace"Maza kwashesu sukai su Shashen momy yanzu"Dakai ta amsa kafin ta mike taja hannun Ummah da Sajida jabir kuma ya bisu abaya,don sunsan hali Azeemar bata musu da wasa saboda taga kaf masarautan babu mai Kwabamusu yara,suna ta Abunda suka ga dama,karisawa tayi ga Ni"ima wacce ke kwance ta zauna agefenta tana Fadin"ya jikin naki Uwar biyu.."Yar dariya Ni"ima tayi kafin tace"Wata uwar biyu nima Ummi wlh bani son cikin duka duka Shekaran Ummah daya fa"Yar dariya Azeema tayi kafin tace"lalle nema Mami,toh Tun Wuri ki maida wannan mganar ki hadiyeta karki bari Maimartana yaji,don ranki sai ya baci,kin manta na sanar dake su Afiya nada Shekara daya na samu cikin Sajida,ki godema Allah bata da Wani rigima kina yayeta ki mikomin ita nan,in zasu tafi nageria hutun karshen Shekara su tafi ma da Ummah da takwaranta don tana nemanta.."Jinjina kai Ni"ima tayi kafin tace" To Shikenan Allah ya kaimu yakuma saukeni lafiya"Da Ameen Azeema ta karba kafin tafara kalle kalle tana Fadin"Mami nifa wlh ina jin kamshin maimartabana,anya baya na nan shashen kuwa.?
mikewa Ni"ima tayi tana Fadin"kema kinsani yanzu haka shashenki yaje bakinan,shine ya biyo sawu,dama ana Cika awa biyu baizo ya ganki ba,ai maimartaba sai yallabiyansa.."Tafada tana yar dariya ita ta ganshi Tun sanda ya Shigo falon,hannu yasaka mata abaki alaman tayi Shuru ya make bayan labule.
yar Dariya Azeema tayi kafin tamike tana Fadin"Au kema kin biyema su goggo ne,To shikenan ni kingama tafiya ta Tunda Abun hakane.."ko taku batayi ba yayi caraf ya dagata sama yana juyi da ita,ihu taso ta saka ya damke mata baki yana dariya kwabe Fuska tayi ta Maki rawaninsa sauko da ita yayi ya rike hannunta yana Fadin"Ke baki da kunya Sarki guda kike duka ko"Hannu ta daga takara makemai kewa tana Fadin"Bakajin mgana ko bance karka fito ba,sai angama zaman fada ba? Tafada tana murde kunnensa dake cikin Rawani,rike hannunta yayi yana Fadin"Wayyo Allah yi hakauri mama Azeema.."Yafada harda matso ido,gabadaya dariya Ni"ima da Azeema suka saka harda tafawa,hararansu yayi kafin ya hade rai yana kallon Ni"ima yace"Dukkanku kallon ku nake,kwana biyun bawacce ke kula dani,ke ya nuna Ni"ima Tunda kikayi ciki shikenan kifara lalaci baki da aiki sai barci da kwanciya,ke kuma ya nuna Azeema,baki da aiki sai yima yara Fada da dukkansu,da anyi mgana sai kice kada abarsu su sangarce,ammh ga aikin mijinki bakya yin ko daya,Allah Zaku sani ne,Aure zan kara dama Sarkin Garin dosso yamin Tayin Diyarsa gimbiya Aisha.."
Azeema ce tayimai wani kallo tana Fadin"au Allah to sai me,Toh Allah kawo ta lafiya ko tazo mungama kwashe romon da sauran wani mazantakan ka sai dai Ta auri saura wlh ko Mami?"Kai Ni"ima ta gyada tana Fadin"Mema zatayi da Tsoho wanda duk baki yacika da goro.."Dukkansu suna mgana ne yana musu wani kallo,sai da suka gama kana ya rike baki yana Fadin"Kutumelisi,ke yanzu nine zaki kallah kice kungama kwashe romon ko? lalle yaron to ko Rabi baku kwasa ba kekuma kina wani narkewa kamar ta Allah ni kikecema bakina duk goro ko? Toh duk na gode da gulmata da kukayi Allah ya kamaku,daga yau duk wacce tazo min Turakata nida ita ce"Yafada yana juyawa har zai Fice ya waigo yana kallon Azeema yace"Ke...."suka dago atare,Nunata yayi yana Fadin"Wuce ki koma Shashenki ko nazo nayi kasa kasa dake.."Tura baki tayi zatayi mgana yafara takowa zuwa gareta saurin Fara tafiya tayi tana kunkuni Ni"ima dake zaune tayi yar dariya tana Fadin"Yauwa tarata kutafi,ni Allah ma yau na yafemiki zuwa turakar Ummi,ban iya Fitinar mijinki,ba daman na dan kwanta sai yace nacika lalaci,kiji dashi har cikina yayi kwari..."Saurin waigowa Azeema tayi tana Fadin"Wa..? No..No yarinya bafa zai sabu ba,ban karba ba kuma bazan karba,nima ai in inada cikin bamai daukemin hakanan nake hakuri so kema ki hakuri gaskiya..."Tafada tana hararan Aliyu dake mirmishi.
Hannuta ya warfo yana Fadin"Ke rabu da ita tama yarda tagama mungode Mamin yara,kamar kinsani dama ta rage kula dani.."Yafada yana Rumgemta kokarin kwace jikinta take,ammh ya riketa kam,itako Ni"ima ganin Abun nasu bana kare bane,sai kawai tatashi ta Shige kuryan dakinta tana kokarin maida hawayenta ta yarda takuma sani Aliyu ba kowa ya biyoba sai Azeema dama ita yazo nema,kullum kafin atashi Fada aganshi sau uku ashashen Azeema,ko agaban waye baya iya boye son da yakemata,sai dai ita Azeemar macece mai tsananin taka tsantsan,saboda Ni"ima in yayi mata wani Abun sai ta basar,ammh ko ajikinta Shiyasa tace tace taji dashi cuz tasan duk mganar dayake ita yake bukata ba ita ba,share hawayenta tayi kafin ta Furta"Alhamdulillah nagodema Allah da tarin Ni"imarsa.."
Haka Aliyu ya tasa Azeema har zuwa Shashenta,suna zuwa taja ta tsaya tana Fadin",haba...Haba wai meyasa kake hakane don Allah..."bata Fuska yayi yana fadin"Kuma Shikenan saboda ita na hana kaina Abunda nakeso,look Azeema ni bani na roketa ba ita gata ya kamata ta barmiki kwananta har ta samu lafiya,to kuma laifi ne don nanuna murnata Afili naga ke matatace kuma kowa yasani kece Fitilar raina,kinga wlh in kika karamin mganar wanchan mata billahil Azim zan iya sakinta takoma garinsu kowama ya huta,haba kinfa dameni dama kin amince in auretane don ki dinga hanani jin dadi dake ehe..."?Yafada yana daka mata tsawa idanunsa sunyi jawur,ganin haka yasa ta zabura tafada jikinsa tana fadin",Wayyo na Tuba,bazan kara ba Allah huci zuciyar Gwarzon Azeema.."Fushinsa ne ke sauka jin yadda take kara kamkamesa,Hannunsa yasa Rumgumeta yana Sauke ajiyar zuciya Wuyanta yake kissing yana Fitar da Numfashi kafin yace"Ya wuce,ammh ki kiyaye,ni banga laifi na anan ba kawai kawai.."Yake fada da alamun haryanzu Abun nacimai Tuwo akwarya.
Dagowa tayi tana Fadin"Toh naji ammh don Allah zan Rokeka alfarma daya..?hade gira yayi kafin yace"Fadi indai bazata hanani jin dadi ba.."ware ido tayi kafin tace"Bazata hanaka ba insha Allahu,dama zance ne don Allah kadaina Satar Fitowa daga fada kana zuwa Shashena,wlh kowa yana kallonka harta bayi da Fadawa suna lura da Abunda kake,kada hakan ya rage maka daraja don Allah kadaina zuwa,In kanason ganina kamin waya sai nazo Turakarka na sameka.."
Wani kallon tara saura kwata yake mata kafin yace"Karma kikara hadani da Allah malama,don wlh bazai samu ba kikama bakinki kawai malama.."Yafada yana sakinta juyawa yayi zai Fice kafin yace"Ki saka ashirya kayan Yaran nan,Gobe in Allah ya yarda Umar zai biyo shida matarsa zai Wuce dasu Nageria suje suyi hutun karshen Shekara gidan Kawu.."Da kai ta amsa kafin tace"Nima dazu mukayi waya da Zafira tace,suma suna nan zuwa hutun karshen Shekara,harda Haisam da Safaru,wacce in tazo bazata koma ba,sai ta haihu.."Dan tsayawa yayi kafin ya waigo yana Fadin"Happy Family kenan can't wait naga Su Dudes an zama iyayan yara"Yafada yana yar dariya,Azeema dake tsaye taga yakara mata kyau batasan sanda ta ruga ta fadamai ba Tana Fadin"Har Abada bazan daina Fadan ni mai sa"a bace..."Dagata yayi sama yana juyi da ita yake Fadin"A"a Pretty bake bace mai SA'A nine mai sa"a dana sameki amtsayin matata kuma uwar ya"yana..."Yafada yana Sauko da ita saitin bakinta ya dora lebenshi yana sakin mata nishi,kamkameshi tayi tana wani lumshe ido,Aliyu ya riga yasan lagonta,bakin kawai ta budemai ya cafki harshenta,yafara kissing dinta in a romantic way,tsayuwa taneman fa gagaransu,ganin zata Fadi ne yasa ya Turata kadan Tafada kan kujera,cikin kwarewa ya bita ya dan Doramata nauyinsa kadan yana kallon Kwayan idonta kafin ya Furta cikin Wani yanayi.." _*PREETY KE TA MUSSAMMANCE...._*.."Yafada kafin ya maida bakinshi cikin nata,suna cigaba Da kissing din juna cikin alamun Fittan hayyaci,Ina ganin haka na Rufe littafina da Birona na juyo ina mirmishi na Fita daga masarautar gabadaya Araina inajin Dole na bar Rayuwar Azeema da Aliyunta hakanan,ina cikin jirgin da zai maidoni Nageria nayi mirmishi nima na Furta.." _MASU KARATU KUMA NA MUSSAMMANE_……'
*ALHAMDULILLAH NIMA MAI RUBUTUN TA MUSSAMMANCE.....*
*Tammat bihamdullah Duka duka Anan Na kawo karshen Littafin ALIYU GADANGA.. !Fata kuskuran dake ciki Allah zai dubi Rauni na ya yafemin,Ladan dana samu Allah ya rabamana tare dani da masu juriyan bin wannan littafin Tun daga Farko har karshensa Ameen*
_Godiya ta mussaman ga kungiyata Daya tamkar da Dubu Wato *INTELLIGENT WRITER"S ASSO* ,Allah yakara hada kanmu gabadaya...Sai godiyata zuwa ga Uwata takaina *HAUWA S ZARIA* tare da Diyata,diyar kwarai irin albarka Wato *RAHMA ABDULNASEER NIGER* LADINGOTA😘Sai ke Sahibata *HAFSART MUSTPAHA* know as HAFNAN,tare da my Sisi of life AISHA ALTO TA😘Bazan Rufe wannan littafin batare dana ambaceku ba,domin kunbani daukkan guduwarku akan wannan littafin domin yazo masu karatu yadda yakamata ina rokon Allah ya saka musu da alherinsa,yakuma bar zumunci,Bazan manta da mika Sakon godiyata ba zuwa gareku ba *HASSAN TANKO* tare dakai *HUSSAIN 80k* Bisa yadda kukayi ta jimarin yada wannan littafin kama daga Fbuk zuwa Whattsop,Ubangiji kadai zai iya biyanku ladan Abunda kukayimin Allah ya biya muku bukatanku na alheri...Sai kuma daga karshe bazan manta dakuba masoyana ba Aduk inda kuke,Hakika naga soyayyah da kauna wacce bata yankewa dalilin wannan littafin,godiya ta mussamman ga wadandan gidajen da sukayi ta jimari tare da hakurin bina Tundaga farko har zuwa yau da zamu karkareta irinsu *JANAF NOVELL 1,2,ALIYU GADANGA FANS 1,2,3,4,ZUMUNTA NOVELLA,TASKAR LITTAFAN HAUSA,AISHA ALTO NOVEL,LADINGO FANS,BENECIAL WRITER'S FANS,INTELLIGENT FANS1,2,HAFNAN NOVELLA,AUFANA TRUE FANS,SIS NAJA'ART NOVELS 1,2,FIKIRAR MARUBUTA,TASKAR MARUBUTA,ZAUREN KAHDIJA CANDY * Daga karshe zan mika sakon Jinjina tare da Lambar yabo da kokari wajen zuba comment zuwa wannan sansani ko nace zaure na *AZEEMAR GADANGA FANS* Bakina yayi kadan na mika kalmar godiyata gareku sai dai nayi muku fatan Allah yabiyaku da alheri yakuma bar zumunci har Abada_
_*Kafin nayi muku sallama gawani Albishir din danake tafe muku dashi....Akwai sabon Novel dina da zai Fita kwananan mai Suna MALIKA MALIK..(Sai na Rama..!)..Yakukaji salon,kunji sunan yagirgiza ku ko? ai daga jin sunan kusan cewa za"a zuba iko, takama girman kai tare da isa,MALIKA MALIK bata son komai sai Rayuwar jin dadi,tataso cikin gata da Dukiya mai yawa,tare da soyayyar mahaifi wanda shikadai gareta..,MALIKA MALIK,Bata ganin kowa da gashi harta ko matar mahaifinta wacce take rokonta bata taba mata kallon arziki ba,MALIKA MALIK bata girmama kowani aiki Aduniyan nan sai kasuwanci,Acikin hakane tayi Ratse ga rayuwar wani dan Saurayi wanda yake ci yasha daga Kakin DAN SANDA,ammh Rana tsaka MALIKA MALIK TA zage kakin Yan sanda tas,wands cin zarafin yayimai ciwo,wanda lokaci daya yaji yana bukatar zama DAN SANDA kodon ya nunama MALIKA MALIK ,Iyakarta sai ya Aureta da aikin yan Sanda yakuma Rataye ta dashi har karshen Rayuwarta YAYI MA KANSHI ALQAWARIN...MALIKA MALIK....(Sai na Rama..!)*_
*Yakukaji Abun,koya wannan badakalan zata kasance duk sai kun biyoni cikin Littafin MALIKA MALIK...Ammh ta hanyar Nunamin soyayyar dakukemin da N200 kachal👌Zaki sha karatunki Tundaga farko har zuwa karshe,ina mai tabbatarmiki bazakiyi Nadama ba,sannan ga wani karin garabasa,HAFSAT HAFNAN,gwanarku marubuciyar FATALWAR MIJINA,HIBBATULLAH,KAICHON SO..,Itama Tazo muku da wani lbrin cikin nata salon mai Taken KISHIN MATA💥Haba ai ku daga jin sunan ma basai na tsawaita mgana ba,kusan Abunda ya kunsa,mata ku matso kusa domin ga dama ta samu ta yarda zaki ga yadda ake kishin ilimi,ta yadda zaki kwace mijinki ta Ruwan sanyi babu boka babu mallam,kiga salon kishin wayayyin mata kiga salon yadda ake Rikita miji,kiga salon yadda zaki samu miji atafin hannunki,chai kada na cika ku da Surutu u we all wach dis in KISHIN MATA,Wanda zaki sha karatunki Shima akan NAIRA 200kachal👌ki amfana da Abubuwan da kudin kima sai da rabonki,ga kuma karin garabasa gamai bukatar Siyan biyu KISHIN MATA DA MALIKA MALIK,zai biya N300 kachal👌ammh gamai bukatar Daya zai biya N200 kachal shima...Karku manta gwanayenku ne TAGWAYEN KAWAYEN MASU ABUN MAMAKI... HAFNAN DA JANAFTY KU SUKE FATAN KUNUNA MUSU SOYAYYARKU AKANSU TA HANYAR FARANTAMUSU WAJEN SIYAN SABBIN LITTAFANSU*