Bayan sallar maghrib aliyu ya dawo ya daukie dije suka karasa gidah, bayan isarsu dije tai wanka ta fitoh tana d'aure da towel a kirjinta aliyu ya rungumeta ta bayah
"Deejah wea yaushe zaki haifamin yara ne"?
Murmushi tai masa
"My lion, nifa bana son haihuwa gskya"
Kissing d'inta ya shiga yayi sosai wnda yasa ta narkemasa gabad'aya a jikinshi, daukanta yay ya direta akan gado tare da kashe light d'in dakin.
Washe garin ranar bayan aliyu ya fitoh, dije na zaune kan kujera tana shaan water melon (kan_kana) sea ga nazee ta shigo gidan.
"Ayya ke khdy nan ne dkinki"?
Murmushi tai mata
"Eh nazee nan ne mana, ynxn dea ya ake ciki"?
Murmushi nazee tai
"Khdy muslim ya fad'amin komai kuma yace in bki hkuri wlh baisan ke matar aure ce ba, amma yace nana ta gidanku ta sakashi"
Ajiyan zuciya dije ta sauke
"Amma wlh muslim yaci amanata, ban yafe masa ba nana"
Dafata nazee tai
"Kada ki damu zan ga wanda zai hana in saa a bata kashi a garin nan Khdy, sea nasa anyi mata wulaqanci na fitar hankali"
Murmushi dije tai mai dauke da tears
"Ki kyaleta Allah yana bayan mai gskya, ynxn kinga Allah ya rufamin asiri, ngd sosai nazee kinji"?
Murmushi tai mata tukkuna sukai sallama.
Misalin karfe 8pm, dije ce zaune akan kujera ta d'ora kanta akan cinyar aliyu, yayinda hannunshi ke kan gashinta yana wasa dashi, tashi tai ta zabura tai toilet tai amai, binta aliyu yay da bayah
"Lpy? Mai ke damunki"?
Haki ta shiga yi sosai
"My lion wlh kasala nake ji kwanakin nan kuma ina yawan amai"
Murmushi yay yace oyah tashi muje nan gurin family Dr dinmu, tashi tai bayan ta kimtsa jikinta ta bi bayanshi, suna zuwa kuwa aka fara dubata, bayan d'an lokaci Dr din yace
"Dije nada juna 2"
Murna da murmushi a gurin aliyu abun sea wanda ya gani, haka suka dawo gidah dije rai a 6ace
"My lion nifa bana son haihuwar nan"
Hannunta ya kama ya rike
"Khdy bana son ki zama haka, ina so inga jinina dan Allah ki deana cewa haka"
Baki ta turu
"Naji"
```BAYAN WATA 3```
Dije cikinta ya k'ara mata kyau sosai, rayuwa suke ita da aliyu cikin jin dadi da nishadi abun sea wanda yagani.
Yau ranar ta kama litanin, haka aliyu ya shirya y fitah zuwa gurin da ake kai masu kayah. Manyan kaya yasa farar shadda da komai fari, kamshi kawea yakeyi.
Kusa da dije yaje ya zaunah dake cin gwaba, hannu yasa ya shafa cikinta
"Khdy saura wata nawa ne ki haihu Eyye?
Fuskarta ta shagwa6'e
"My lion ka barni hka tun safe kake abu d'aya har ynxn"?
Kiss ya manna mata a kumatu
"Ke d'ince ai ta daban, I love u"
"Tashi muje in kaiki gidah kapin in dawo"
Riga ta dauko dogowa ta saka da dogon wando wnda yake iya kwabrinta, ta saka hijab dinta suka kama hanya bayan yayiwa kowa na gidan sallama.
Hanya ykama ya fitah yayinda dije ta haura d'kinshi, ummi da mame kowanne a cikinsu yana d'akinshi.
Bayan kamar minti 10 haka dije ta fitah dga d'kin tabi ta gaban d'kin nana.
Waya taji tanayi
"Da fatar dea zaka saka poison d'in yau?
Murmushi tai ta kashe wayan ta rike a hannunta
"Yau aliyu sea lahira! Dan ni bana barin bashi haka"
Jin haka da dije tai yasa ta fitah da gudu a gidan, ta kira nazee tace
"Tazo plzz" ta kuma zayyana mata komai akai.
Kasancewar hanyr da nisa kapin akai gurin nasu.
Taxi ta tara dea2 tym din nazee ta karaso
"Look! Khdy ki koma gidah ni zan tafie kinga cikine dake"
Cikin muryan kuka ta dubie nazee
"Nazee mutumin da kike magana akai fa mijina ne, muje dea"
Hanya suka kama ta tafiya a tsakiyan hanyan wasu mutane da suka rufe fuskokinsu da max (hulan fuska) suka taresu, wasu irin karta majiya karfie, dije da nazee suka finciko dga cikin napep din.
D'ya d d'aga hannu da gora zai watsawa dije a jiki nazee tai kururuwa ta rufeta da jikinta ta had'e hannayenta 2 guri d'ayah
"Dan Allan kuyi hkuri, cikine da ita kada ku daketa dan Allah ku dakeni, dan darajar Allah"
Daria suka kyalkyale dashi
"Ke hajiya jaye nan ki wuce danmu itace target d'inmu kinji ko"?
Kuka nazee ta k'ara fahsewa dashi lokacin da suka jaa hannuntah
"Dije murya na rawa ta kare cikinta ta maida dubanta ga nazee
"Nazee for god sake ki taimaki mijina kada ki bari yasha drinks d'in nan dan Allah, Ki taimaki mijina kada ki damu dani"
Nazee kai ta girgizah
"Bazan barki nan ba dije, ina tare dake"
Dije hawayenta suka cigaba da bin kumatunta
"Nazee dan Allah ki taimakamin, rayuwar mijina na cikin hatsari, yana tsakanin rayuwa da mutuwa"..
®Kausar Luv💞
[11/15, 7:17 PM] Kausar~Luv: [8/23, 6:45 AM] Kausar Luv💞: ```ALIYU_HAYDAR```
Page ((76)) to ((78))
```©Kausar M Hassan```
Wata irin tsawa aka daka mata wanda yasa nazee ranta cikin na kare a gaba ta had'u da mai napep din da gudu suka kama hanya.
D'ayan mutumin ya fara nufar dije, daga xaune ta fara jaa da baya2 tana kuka tana kare cikinta, cikin muryan kuka ta hau furta
"Mai nai maku ne dan Allah? Maisa zaku kasheni ne? nifa matar aure ce, kuma inada ciki dan Allah ku kyaleni dan Allah"
Wata irin darian mugunta sukai su 2 d'in, wanda yasa dije mirginawa ta tashi tsaye ta fara gudu tana waigen bayah, suma suka rufa mata bayah. Tana gudu suna gudu haka har suka sata a tsakiyah. Jikinta duk ya bad'e da kura...
Nazee na isa dea2 inda dije ta fadamata ta sauka dga napep d'in, da gudu2 ta fad'a babban store din tana haki tana karie.
Shafi'u taci karo dashi a bakin kopa, numfashinta sama2 yake fitah
"Dan Allah aliyu nake nema mijin Khdy"
Shafi'u yay mata jagorah gurin aliyu, tana isa kuwa an kawo masa drink na pineapple cikin glass cup ya dauka kenan zai kafa a baki nazee ta ka6e cup din ta hau bashi labarin da dije ta fadamata ta kuma sanar dashi halin data barta da kuma inda ta barta.
"Oh, no!"
ya fad'a tare da buga table din dake gabanshi ya tashi ya fitoh yayinda shafi'u ya damkie wannan ma'ikacin nasu ya kulle shi a d'aki yabi bayan su aliyu.
Koda suka kawo gurin kwance suka tarar da dije a gefen hanya, da gudu aliyu ya isa gareta ya daukie kanta ya d'ora akan cinyarshi.
"KHADEEJAH" ya kira sunanta tare da jijjigata, a hnkli ta bud'e idanunta, cikin sanyin murya mai cike da rauni ta furta
"Na godewa Allah dayasa kana nan lpy qlw, yaa aliyu ka yafemin ni mutuwa zanyi, ka yafemin! Ina sonka sosai".
Jini ne ya fara biyowa ta kafafunta wanda ya kara sa aliyu cikin tashin hnkli, da sauri ya sungumeta sukai asibiti a emergency aka diretah.
Dga nazee har aliyu kowanne a cikinsu hanklinshi a tashe yake, aliyu ya kasa zama ya kasa tsayi.
Kusan minti talatin, suna tsaye a haka kapin nan likiti ya fitoh yace
"Cikin dake jikin matarka ya zubie, kuma ta samu rauni amma da sauki ynxn zamu dubatah.
Wasu irin hawaye suka zuba mashi a ido, yana mai kallon dkin da aka sakatah.
Hka aka kammala komai kapin nan yay gidah, yayinda nazee ta tsyaa tare da itah.
Sanar dasu yay abunda ya faru duka kapin nan suka d'unguma zuwa asibitin..
[8/23, 6:54 AM] Kausar Luv💞: ```ALIYU_HAYDAR```
Page ((79)) to ((80))
```©Kausar M Hassan```
```BAYAN SATI BIYU```
Dije ce zaune akan kujeran d'akin ummi ta kurawa TV ido duk da hnklinta ba'a nan yake ba. Aliyu ne kwance a d'akinshi ya d'ora hannunshi ya rufe idanunshi abunda ke dawo masa a rai shine maganar dije lokacin da take cemashi bata son haihuwah
"Kenan ita ta had'a wannan dan ta zubar da cikin dake jikintah"?
Tashi yay kaman wanda aka tsikara yay dkin ummi kusa da ita yaje ya tsaya ya tabata hakan yasa ta maida dubanta gareshi tare da sakar mashi murmushi.
Shi kuwa d'aure fuska yay kaman wanda bai tab'a daria ba a duniya ba.
"Wato Khdja sea da kika zubar da cikin nan ko"?
Ido ta bishi dasu
"My lion ya zaka fadie hka?
Ya zan zubar da cikina kumah"?
"To aike kika fadamin ciwan bakya son haihuwa"
Kuka ta fashe dashi
"Haba yaa aliyu sea kace wadda batada imani dan Allah kada kace bka san halina b"
"Ya ISA"!
Ya daka mata tsawa
"Idan har bada niyya kikai baa, maisa baki kirani a waya kin sanar dani ba? Ko ki fad'awa mame, ummi, da kuma abbi"? Sboda ke gaki d great ideal wife ko"?
Wallahi kin matuqar bani mamaki, amma bkomai ni zan rabu dake tunda bkya son hada jini dani"
Karaf sea a kunnen mame dake kokarin shigowa d'akin,
Cikin 6acin rai ta furta
"Kul wallahi! Kada ka soma kai bakada hankli ne"?
"Mame ki tmbyeta gata nan ba ita ta fadamin bata son haihuwa ba"
Ummi dake kuryan d'akinta ta fitoh
"Aliyu mai yake faruwa"?
Nan take ya zayyana mata komai
Ummi ta kuwa baiwa aliyu gskya, yayinda mame tabi side d'in dije.
Fitah yay zuwa dki ya harhadou kayanshi cikin jaaka, ya dau biro da takarda yay rubutu akai ya mayar ya rufe, ya dawo dkin.
Kusa da ita ya tsaya ya dubieta
"Tunda mame ta hanani rabuwa dake to ni zan bar kasar dama tafiya zanyi, ungo!"
Ya miqa mata takardan.
Hannun dje na rawa ta kar6a takardan.
Ta fashe da kuka, ta kai kasa ta rike masa kafafu
"Dan Allah yaa aliyu kayi hkuri kada kamin haka, rayuwa batace haka ba, kaji tsoron Allah"
Kafanshi ya fincike daga rikon da dije tai mata, fashewa da kuka ta kumayi
"Yaa aliyu! "Yaa aliyu! "Ya aliyu!... Dije ta hau kiranshi tana kuka.
Ina! ko juyowa baiba kawea ya fice dga gidan, yayinda dije ta zube kasa ta cigaba da kukanta.
Mame tasa hannu ta kar6a takardan ta rikata suka fitah dakin, bayan d'an lokaci dije ta sauka dga kukan da takeyi
Mame ta miqa mata takardan tare da furta
"Kar6a takardan nan ki ajiyeta a wani guri mai kyau kada ki sake ki budeta"
Hawayenta ta share ta kar6a takardan, a cikin zuciyanta take furta
"Namiji kudan zuma, ruwan mad'aci, hakika sea yau na yarda da batun baba, amma aliyu kaci amanata, bazan ta6a yafemaka ba"
Aliyu kuwa daga nan airport ya nupah, ticket ya siya ya wuce kasar London..
```BAYAN SATI 2```
Dije ce kwance akan kujera ta jingina kanta akai, kanta babu ko d'an kwali, rigar sanyi mame
tasa ta rufe mata jikinta dashi saboda ana d'an sanyi, Kamar wadda aka ta6a ta tashi xaune. Cikin rawar murya tace
"Mame yaa aliyu ya dawo ne"?
Mame zaunawa tai kusa da itah ta dafa kafad'anta
"Khdja bai dawo ba halan kinyi mafarkinshi ne"?
Kai ta girgizah mata da idanunta da suka zurma
"Mame naji kamshin shine"
Dubawan da zatai taga rigan sanyin shi ce a jikinta,
Tausayinta ya kama mame sosai ta janyouta jikinta ta rungumetah
"Kiyi hkuri khdja na tabbata in shaa Allah wata rana zai dawo ya kuma gane gskya"...
Kwantawa tai jikin mame ta cigaba da hawaye, a cikin zuciyanta take furta
"Yau itace yaa aliyu kewa haka"? Yana karyata ta, kwata2 yama manta da babin rayuwan wata dije"
Haka aka share kusan wata 2 babu aliyu babu labarinshi, dije ramewa take sosai na rashin jin dumin mijinta a tare da itah.
Yau ranar ta kama litanin dije ce zaune a falo, nazee ta shigo gidan.
"Khdy ina mijinki"?
Murmushin yaki tai
"Yayi tafiya ne nazee amma ya kusa dawowa"
Sun jima a gidan suna fira kapin nan tai mata sallama ta fitah....
To yaa aliyun ma zai dawo kuwa?🤔
"Original butulu, kaji sunanka.
Kai wasu maza babu amana😏
®Kausar Luv💞
[11/15, 7:17 PM] Kausar~Luv: [8/24, 8:29 AM] Kausar Luv💞: ```ALIYU_HAYDAR```
Page ((81)) to ((83))
```©Kausar M Hassan```
```BAYAN SHEKARU 3```
"Islam!!! Bakajin magana ko"?
Gudu takeyi suna zagayen kujera, yana b'oya, dkyar ta samu ta rikeshi ta daukeshi ta manna mishi kiss a kumatu.
"Khdy"
Nazee ta ambaci sunanta
Juyawa tai da dara_daran idanunta tai murmushi
"nazee amarya yr shagali"
Murmushi tai mata
"Maman Islam kenan, yaron nan kamar su d'aya da babanshi ko"?
Murmushi tai
"Sosai ma, bara in dauko maki tsarabanki"
Tashi tai ta wuce dki ta dawo kasa ta mika mata wata jaka.
Kar6a nazee tai, tai gdya.
Sun dea d'an jima suna firah kapin nan nazee tai mata sallama akan hanyarta ta shigowa gidan ta had'u da aliyu_haydar. Wanda y bar gida shekaru 3 kenan cib a yau..
Ga dije da d'an_d'a d'an kimanin shekaru 3, to y akai hka? Ya lamarin yake ne"?
Muje zuwa zamujie komai dea in shaa Allah.
Shigowa yay ciki, cike da daukie da murnar ganin iyayenshi, kai tsaye dakinshi ya nupah, kasancewar babu kowa a falon harta ma'aikatan gidan duk suna kuryar gidan. Key yasa a jiki sea yajishi a bud'e hakan yasa ya murd'a kopan d'akin.
Bud'ewan da yay sukai ido 2 da dije wadda ta cire kayanta ta d'aura towel iya cinyarta tana yarfie gashin kanta. Dije ta qara kiba yar dea2, hips dinta sun qara cika, ta kara kyau da wayewa sosai.
Idanunshi ya rumtsie gam, saboda wani irin abu dayakeje yanai masa yawou a jiki, a hnkli ya kara bud'esu, ya maida kopan dkin ya tura da kapanshi ya karasa kusa da itah da baya2 ta fara jaa ya matseta da bangon d'akin yana k'are mata kallo, bakinshi ya kai nata ya had'e ya fara tsotsa, dkyar ta iya tsaida numfashinta ta tureshi ta d'ago idanunta da sukayi jajir suka cika da kwallah masu zafin gaske
Humm zazzafan hawaye kenan.
"Kada ka kara wallahi aliyu ni ba matarka bace, ka manta ka sakeni"?
Idanunshi yay narai2 dasu
"Yaushe na sakeki? Kiyi hkuri ki saurari baya nina dan Allah"
Bayanta ta juya mashi
"Look! Pls ka kyaleni bana son ganin fuskanka aliyu"
Matsawa yay kusa da itah ya d'ora hannayenshi akan kafad'anta
Da sauri ta bangaje hannayenshi dga kafad'anta
"Ka kyaleni aliyu bana sonka! na tsaneka!"
Hannunshi ya d'ora ya d'ago fuskanta, cikin muryan kuka ya hau yin magana
"Khdja look in to my eyes and tell me dat u don't love me"
Juyar da kanta tai gefe ta fara cizon le6enta
"Ki fada'amin kinji plzz ki amsani"
Zubewa tai kasa gefen gadon, ta cigaba da zubar da kwallah
"I don't love u"
Ta furta a sanyaye.
Shima rufa mata baya yay
"Dan Allah Khdja kada ki hukuntani ta hakan, nifa mijinki ne har ynxn na kuma har abada"
Idanunta ta saukar kasa
"Aliyu ka kyaleni, bana son ganinka"
Hannunshi ya d'aura kan lips d'inta tare da hugging d'inta sosai ya shiga lalubarta.
🤔Oh maza ba kunya, kagama yimata abunda ranka yakeso ynxn kuma ka dawo kana wani binta....
[8/24, 8:35 AM] Kausar Luv💞: ```ALIYU_HAYDAR```
Page ((84)) to ((85))
```©Kausar M Hassan```
Da dabara ya kwantar da ita kasah ya shiga yimata wasu irin salo na daban, gabad'aya ya gama fitar da ita hayyacinta.
Wani karfie taji yazo mata wanda ya bata damar tureshi ta tashi tai maza tai toilet ta kulle tana sauke ajiyan zuciyah. Wani irin numfashi yaja ya sauke tare da fitah dkin zuwa falo, a falon ya tarar da mame da kuma ummi had'ie da abbi. Kowannensu ido ya bishi dasu musamman mame ganinshi da tai y fitoh dkinshi.
Ummi ce ta fara magana
"Oyoyo d'an ummi yau an waiwayo gida kenan"?
Murmushi yay mata ya karasa kusa da ita ya zaunah
"Ummi nayi missing dinku sosai"
Ko kallon banza mame batai masah ba, hakan yasa ya tashi ya matsa kusa da itah
"Mame ina wuni"?
"Lpy"
Ta fad'a a takaice ta tashi ta wuce ta bar falon.
"Aliyu"
Abbi ya kira sunanshi
"A cikin shekarun nan 3 ina ka tafie ne"?
Nan ya xauna ya fayyacewa abbi komai, abbi yay murmushi
"Amma kasan baka kyauta bako? Ka tafie ka bar matarka a nan"
K'iya ya sosa
"Abbi wallahi sharrin shaid'anne da kuma fushin zuciyah"
Ummi ta tari numfashinsu
"Shin tunda dea Allah yasa ya dawo lpy ai sai a manta komai"
Sun d'an jima a hka yayinda aliyu hnklinshi ke gurin mame, dan yasan tabbas ya 6ata mata rai matuqa.
Yunkurawa yay dga zaman da yay zai tashi. Jin ana kiran sunan "kaka" yasa ya koma ya dakata.
Waigawa yay suka had'a ido d yaron dayasha shadda fara, an gyara masa sumar kanshi, kamshin turarenshi na white diamond. Ga kamar su nan d'aya da aliyu kai da ganinshi kasan jininshi ne Bul2 dashi. Da gudu2 ya haye cinyar abbi
"Grand pa, hw r u today"?
Hancinshi abbi yaja
"D'an bature kenan, ina ice cream d'in nawa"?
Hannu y dora a goshi tare da fad'in
Oops! Kaga mum ta shanye d'ayan saura wannan"
Sun jima suna wasan jika da kaka, aliyu dea duk yana kallonsu.
Islam dake zaune kan cinyan abbi ya taso ya tashi ya tattako zuwa ga aliyu daya saki baki yana kallonshi.
Cikin yar muryanshi mai dadi ya furta
"Who are you"?
Aliyu bayyi mamakin tmbyr ba
"Kaima waye"?
Murmushi Islam yay
"Am Islam"
Aliyu ya dubie ummi
"Ummi wannan d'ana ne ko"?
Kai ummi ta d'aga mashi, aliyu ya rungume islam sosai
"Ina sonka ma boi ina sonka yarona"
Kwace jikinshi islam yay
"Why are hugging me so tight"
Ya maida dubanshi ga ummi
"Big grand ma plz who is he"?
Kallon kallo suka fara
"Babanka ne"
"No grand ma"
Aliyu tashi yay ya riqe hannunshi
"Can't you see that, muna kama? The same nose, eyes, talk and everything"?
Dea2 lokacin dije ke karasowa gurin sanye cikin farin rigah iya cinya da dogon wando baki, ta d'aura d'ankwali fari mai kyau da kyalli. Kamshin humran data shafa na tashi. Haka ta fice ta gaban aliyu.
Islam da gudu yay gurinta yay hugging d'intah
"Mum wannan yace wai shine babana"
Kallon aliyu tai da idanunta da suka d'an chnza kala.
Cikin muryan kuka ya fara jijjigata
"Plzz mum, shine babana"?
A hnkli ta bud'e bakinta jiki a sanyaye tace...
®Kausar Luv💞
[11/15, 7:17 PM] Kausar~Luv: [8/25, 11:22 AM] Kausar Luv💞: ```ALIYU_HAYDAR```
Page ((86)) to ((88))
```©Kausar M Hassan```
"Eh, Islam shine babanka"
Wata irin ajiyan zuciya aliyu ya sauke tare da riko hannun islam, Islam kuwa idanu y bishi dasu.
"Muje in baka labari my son"
D'aukanshi yay tsam suka kama hanyan zuwa d'kinshi, yayinda dije tai tsaye tana kallonshi cike da mamaki.
"Khadeejah"
Ummi ta kira sunanta.
idanunta ta d'aga ta kalleta
"Zo ki zauna"
A hnkli ta zukunna ta zaunah kusa da ummi.
Nasiha ummi tai ta mata mai shiga jiki, kapin nan tace ta tashi ta kira mata Islam zasu fitah.
Akan hanyarta ta hawa upstairs d'in taci karo da Nana, ko kallon inda take dije batai ba, ta karasa kopar d'akin ta bud'e.
Kamar mai koyon magana ta furta
"Islam grand maa d'inka na kira"
D'agowa yay dga kwanciyar d sukai shida aliyu ya wintsilo dga kan gadon da gudu2 ya fitah dkin. Da sauri ta juya bayanta zata fitah aliyu y kira sunanta, hakan yasa taja ta tsaya chack.
Tashi yay ya matsa kusa da ita ya dubieta
"Khadeejah dan Allah ki yafemin, wallahi sharrin shaid'anne, ashe bayan tafiyana kin haihu"?
Ido cikin ido ta kalleshi cikin tsawan murya tace
"Aliyu na haihu bayan tafiyarka, kasani islam d'anka ne a shari'ance amma nice matsayin mahaifiyarshi kuma nice matsayin mahaifinshi saboda hka na haramtaka maka mu'amala da d'ana saboda baka san wahalan shiba, ni nasha wahalanshi in d'ayah, ni na raineshi ba tare da wanda yake ikirarin cewan shine mahaifinshi ba"
Ta dakata ta share kwallan da suka kwararo mata a ido ta cigaba da cewa
"Ka tafie ka barni a lokacin da nafie buqatarka a cikin rayuwana, ka nuna cewa baka yarda daniba, to mai zaka fadamin kuma ynxn"? Bana son jin komai dga gareka"! Ta ra6a ta gabanshi ta wuce.
Shikam aliyu mamaki yake wea shine yau dije ke fad'awa wad'an nan irin kalaman.
*BAYAN AWA 6*
Aliyu ya kasa zama ya kasa tsaye hakan yasa ya tafie d'akin mame dke zaune akan kujera tana sauraren karatun al_qur'ani mai girma. Kan gowowinshi ya tsuguna ya dubieta, cikin sanyin murya yace
"Mame dan Allah ki d'aga ido ki dubieni, ki yafemin laifina. Mame na tuba"
Kallonshi tai
"Aliyu ai bani ka 6atawa ba, kasan wadda ka 6atawa, aliyu haka ka tafie ka bar matarka har tsawon shekaru 3, ynxn data rasu ya zakayi"? Kodayake ai ka saketa ma na manta"
Tashi mame tai ta wuce kuryanta ta maido kopan ta kulle, kanshi ya daka ya tashi ya wuce dkin ummi. Akan sallaya ya tarar da ita tana kokarin tashi.
Zaunawa yay kusa da ita.
"Ummi wea ya akai Khadeejah ta haihu bayan kuma an tabbatar da cewa cikinta ya zube"?
Ummi ta gyara zamanta
"Wato bayan tafiyanka da sati 3, sea yanayinta ya fara chnzawa hakan yasa muka dauketa zuwa asibiti, da aka bincika ne likita ya tabbatar mana da cewa cikine da itah , amma yayi zuba saboda hka zai maida wattannin da yay kapin nan zata haihu in shaa Allah"
Ummi ta dafa kafad'anshi
"Aliyu Khadeejah tasha wahala, Idan ka ganta kai da kanka bazaka d'auka zatayi rai ba, ka nema gafararnta dan Allah"
Kai ya d'aga mata, ya tashi ya fice, a falo ya hangota cikin atamfa riga da skit, tasha kyau sosai, tana wasa itada islam.
Sea daria suke yana hugging dinta, da alama shagwa6a yake matah.
Kai tsaye dakinshi ya nupah ya zaunah.
Misalin karfe 9pm. Dije ce zaune akan gefen gadon mame, mame ta kalleta
"Khadeejah tashi ki kwanta, kinji"?
Tashi tai ta wuce kan gado ta kwanta tare da islam, yayinda aliyu keta faman jin haushin kanshi, shifa wlh yana son jin dumin matanshi a tare dashi.
Kasa kwanciya yay hakan yasa ya lalla6a ya sauko dga gidan saman, zuwa d'akin mame. A hnkli ya bud'e dakin ya shigah, kasancewar babban dakine akuy d'akuna a ciki, kamar an sanar dashi inda take ya bud'e da fitilan wayanshi daya kunnah.
Kwance suke ta d:ora hannunta akan jikin islam, ta saka kayan bacci, rigar iya cinyarta, ta saka safan kafa.
Hannu yasa ya fara shafarta, ya kurawa kirjinta ido, gasu tsam2 kaman bata haihu ba, hannu ya d'ora akai ya fara shafasu. Hakan yasa ta bud'e idonta, zatai magana, aliyu yasa tafukan hannayenshi akan bakinta yana kallonta, wani irin wawan cizo ta sakar mashi wnda yasashi sakin hannun nashi.
"Tashi ka fitah ko in kira mame wallahi"
Kasancewar yasan idan mame tazo bazaijie da dadi ba yasashi fitah dkin. A daddafe ya kwana a d'kin saboda yanda ya shiga cikin wani irin yanayi da tausayin matarshi...
[8/25, 11:23 AM] Kausar Luv💞: ```ALIYU_HAYDAR```
Page ((89)) to ((90))
```©kausar M Hassan```
Washe garin ranar, bayan dije ta shiryawa islam tsaf domin zuwa makaranta
(Nursery school) har mota ta rakashi tukkuna ta koma d'akin mame tai wanka ta shirya, cikin Arabs wears, dubawan da zatai tagan babu yan kunnenta ko d'aya duk sua dakin aliyu. Wani dan karamin tsaki taja kapin nan ta kama hanyar zuwa dakin, kai tsaye ta bud'e ta shiga, direct loca ta nupa ta hau dibansu tana zubawa a wata jaka, ta baya taji an rungumeta ana shinshinar ta kaman wata aba, dkyar ta iya samu ta saita kanta da karfi ta juya
"Wea malam lpy ne dan Allah? Sea wani bina kake kaman wadda aka mallaka maka"?
Murmushi yay
"To ai ke matata, by d way ma ina xaki tafie"?
"Meye naka a ciki? Zn tafie inda raina yakeso"
ta karasa maganar da saka yan kunnenta ta fitoh, kasa jurewa yay y biyotah bayah tana tafiya yana mata magana amma ko kanzil batace dashi ba, haka har suka isa dakin mame.
Ganin tai banza dashi yasa ya fincikota
"Wea Khadeejah badake nake magana ba"?
Idanunta ta d'aga ta dubieshi
"Najika mana, to gidan kawata zan tafie ko akuy damuwa ne"?
Hijab dinta ta dauka ta daukie key, da alama na mota ne, ta kama hanya binta yay har gate
"Wea khadeejah bakida hnkline? da aurena zaki fitah akanki ba tare da kin sanar daniba"?
Hararanshi tai
"Sannu mijina dan Allah kai ko kunya bakaji ba"?
Ta karasa maganar ta bude motanta blue, E.O.D ta shiga gate man ya bude mata kopa ta fitah.
Wani irn tarnakie da wata irn tanzuma ta kama aliyu, yana mai jin haushin kanshi.
```Bayan awa 5```
Khadeejah ta dawo gidan, kai tsaye dakinta dake cikin dakin mame ta nupah, ikon Allah! Aliyu ne zaune akan kujera ya harde kafafu
"Wea ina kikajie ne"?
Kallonshi tai tare da yun murmushi
"Allah sarki, kaga fa gurin wani buki na tafie, kanwar saurayina ke aure fa"
Wani wawan mari ya aikamata
"Ke mallakina ce, ke tawa ce! Kina nan a raina, ke matata ce!. Kada ki kuskura ki kara min maganar wani d'an iska a nan"
D'an murmushin yaki tai ta dubieshi da hawaye sha6e2 a fuskanta
"Matarka"? Taka ce?
Ta yaya"?
Murmushi aliyu yay
"oh yah! nagane lallai kin manta koni waye ko"?
Tashi yay ya maida kopan ya kulle , kasancewar ummi da mame duk suna kuryan gidan.
Dawowa yay ya cire rigarshi, ya fincikota ido cikin ido ya dubeta
"Yau zaki fahimci hakan"
Riganta ya fara kokarin rabata da itah, ya shiga kokarin nuna mata shi zakine, sumba ya rika aikamata ta ko ina, ya yarfata kan gadon d'kin. Da baya2 ta fara jaa.
"Aliyu kaji tsoron Allah, wallahi kada ka sa6awa Allah niba matarka bace"
Ko ta kanta baibi ya hau gadon ya fara kokarin cimma burinshi akantah.
Sea da ya tabbatar data saduda tukkuna yay bayah.
"Ni ban sakeki ba dije, kin kuwa duba takardan dana baki"?
A hnkli ta tashi ta maida riganta da hijab dintah, ta tashi ta bude loca ta zaro paper tace
"Gata aliyu, wannan itace takardan da kabani'
Takardan ya amsa ya bude, ya miqa mata
"Ki karba ki karanta"
Amsa tai a hnkli ta dubieshi sannan ta maida dubanta ga paper d'in, ta fra karantawa
Ga abunda ke ciki
```My Muhibbaty, kiyi hkuri akan abunda nai maki nayi hakane a bisa wani dalili, ina sonki, komai dad'ewan da zanyi dan Allah kada kimin mummunan fahimtah, I love u, ina sonki Khadeejah"```
Idanunta ta d'ago ta dubieshi, Aliyu ido cike da kwallah ya hau bata bayanin
"Dije daama tafiya zanyi harta wad'an nan shekarun, na d'auka zan iya tafiya in barki cikin dad'in rai, sea na kasa wannan shine dalilin dayasa nai hka"
Ya nisa ya cigaba da cewa
"Ni nasan kina sona dije, kuma har yau har gobe"
Aliyu ya rage tsayenshi dea2 gowowinshi yace
"Khadeejah! On my kneels, dan Allah kiyi hakuri, kimin hakuri plzzz"
"Kinyi hakurin"?
®Kausar Luv💞
[11/15, 7:18 PM] Kausar~Luv: [8/27, 2:14 PM] Kausar Luv💞: ```ALIYU_HAYDAR```
Page ((91)) to ((93))
```©Kausar M Hassan```
Idanunta ta rumtse tukkuna ta d'agosu tare da zubewa kasa dirshan, cikin muryan kuka ta fara cewa
"Yaa aliyu wannan ba dalili bane, amma kasani nayi hakuri saboda nasan kana sona kuma kana kaunatah, amma dan Allah kada ka karamin irin hka"
Shima kasan ya durkusa ya zaunah yasa hannunshi ya share mata hawayen dake sauka a fuskanta
"Matata naji kuma nasan nayi laipie sosai"
Le6enta ta cije tace
"Bakasan ya nai rayuwa babu kai ba, bakasan iya kukan da naiba, na d'auka na 6atawa mafi alkhairin namijin dana sani a duniya rayuwa, na rika d'aurawa kaina laipie"
Rungumeta aliyu yay
"Bakimin komai ba matata, ina sonki ina kaunarki har cikin zuciyatah"
Tashi yay yace
"Muje in fadawa mame dalilina"
Babu gardama ta tashi tabishi suka karasa kuryan gidan chaan inda mame da ummi, aliyu ya fayyace masu komai ya kuma baiwa kowa hakuri. Mame dkyar ta sauka, haka suka wuni a ranar cikin farin ciki sosai.
Misalin karfe _10:00pm_ Aliyu ne kwance a d'akinshi ya kasa kwanciyah, tsananin buqatar dayakeyiwa dije ta kara tsanantah, musamman ace mutum irinshi mai yawan desire. Hakan yasa ya tashi ya shiga d'kin mame cikin sand'a ya nupie inda dije take. Sa'ah ya taka islam baya nan, da alama yna hannun mame.
Kallonta ya tsaya yanayi irin yanda take bacci hankli kwance, gefenta ya zauna ya d'ora hannunshi akan goshinta ya shafa, ya shafa gashin kanta, kamar wadda zata farka sea ta d'an motsa ta kara juya kwanciyarta. Aliyu yay murmushi a cikin zuciyanshi ya furta
"Hali na nan bai chnza ba, ana bacci ana juye2"
Gefe ya hau y kwanta ya shigar da itah a cikin jikinshi, ya fara wasa da itah, wanda yasata bud'e idonta tsam. Zatai magana ya rufe bakinshi da nata, kiss yay mata mai kyau kapin nan ya dakatah da idanunshi da sukayi jajir yace
"Khdja dan Allah ki taimakeni"
Murmushi tai kad'an
"My lion nifa bacci nakeji, dan Allah ka kyaleni"
A kunne ya rad'amata
"Har ynxn fushi kike dni ko"?
Kai ta girgizah mashi
"To plzz ko wasa ne nidea plzz, ki biyoni muje dakina"
Hannu tasa a baki
"Haba bawan Allah idan mame ta tashi bata ganni ba fa"?
Murmushi yay
"Sea tace kinyi gurin mijinki ko"
Batada option wanda ya wuce ta tashi tabi bayanshi, suka karasa d'akin, wani irin murmushi yay lokacin da yake maida kopan dkin ya rufeh.
A wannan daren sunyi wasa sosai kapin nan ya barta. Bata yarda takai asuba a dakin ba, saboda gudun had'a ido da mame.
Washe garin ranar mame ta hada masu kayansu harda na islam. Wea su koma gidansu, amma gidan da abbi ya siyawa aliyu.
Itadea dije batace komai ba, ummi ce ta hadamata kaya naji da gani, haka misalin karfe 8pm mame tace su wuce.
Islam shikam ya rike abbi wea ba zea bisu ba, dije tai2 kiranshi amma yaki, haka suka fitah driver ya saukesu gidan dake bayan layain ya juyo, aliyu ya daukie kaya ya shigah. Tsayawa fadamaku kyau da tsarin gidan wani sabon 6ata lokacine. A ranar aliyu bai bar dije ba sea daya samar wa kanshi natsuwa, ita kuwa tasha wahala matuqa ainun, amma duk da haka bata nuna ba.
Washe garin ranar bayan sunyi sallar asuba dije ta tashi tai wanka ta saka English wears riga da wando, gashin kanta ta d'aure da ribom, duk hakn da tai aliyu na bacci, ta had'a masu breakfast ta daura kan dining, tukunnah ta dawo kusa da aliyun tasa hannu ta shafa fuskanshi har sau 3 tukkuna ya bud'e idanunshi, wanda sukai tozali da dije.
Wani irin lallausan murmushi ta sakar mashi mai d'auke da wani irin sako na ina kaunarka. Maida mata da murmushin yay.
Cikin yar karamar muryanta tace
"My lion Muje ko"?
Kai kawea ya iya d'aga mata ta tashi ta wuce, yabita da kallo shima din y tashi.
A gurguje yay wanka yay brush ya fitoh sukai breakfast.
Bayan sun kammala dije tace
"Yaa aliyu yau bazakajie ko inaba "?
Murmushi yay
"Sea dea idan zaki koreni to, amma nikam yau ina gidah"
Murmushi tai ta miqe zuwa kan dogowan kujera shima d'in binta yay suka zauna akai sunata firansu irinta masoyah.
Misalin karfe 4pm sea ga kiran nazee a wayan dije. D'auka tai ta karaa kunne
"Amarya yar shagali"
Nazee tai daria
"Wai nikam yaushe zaki deana kirana da amarya? Cemaki nai aure zanyi"?
Murmushi dije tai
"Wallahi aure da dadi nazee bazaki ganebane sea kinyi, ynxn dea zan kiraki letter, kinsan baban islam ya dawo babu jimawa ana wayah"
Sallama sukai abunsu.
_2weeks letter_
Aliyu ne zaune akan kujera
"Maman islam wea har ynxn baki shirya bane"?
Da sauri2 ta fitoh da d'an kunne a hannu
"My lion kasan fa shirin mata, akuy mu da nawa amma ynxn kam ai na shirya"
Murmushi yay
"Muje kinsan halin shafi'u ynxn nan zaice wea na shanyashi"
Gyalenta ta saka babba, inda tai shigarta in pink tayi matuqar kyau sosai. Nan suka kama hanya, akan hanyarsu ta zuwa gidansu shaf'iu sukaga wani sabon guri da aka bud'e. Aliyu yay parking
"Ina zuwa"
"OK"
Ta fad'a tare dayin murmushi.
Motan aliyu ya bud'e ya fitah, yayinda dije ta daukie wayanta ta fara game.
[8/27, 2:32 PM] Kausar Luv💞: ```ALIYU_HAYDAR```
Page ((94)) to ((95))
```©Kausar M Hassan```
Dushie2 na fara hangowa hakan yasa nasa hannuna, na nurza idanuna
_Guess who?_
Muslim?
Ni kausar na fad'a lokacin dana hangenshi cikin wata irin motah ta alfarma, yasha kana nan kayah, parking yay dea2 inda aliyu yay parking, bud'e motan yay ya fitah, d'ago idanunshi da zayyi yay tozali da dije.
Glass d'in dake fuskanshi ya cire ya kara dubanta dkyau, wani feeling yaji a zuciyanshi wanda y kasa gane kona meye.
Wayanshi ya d'auka ya shiga images, hotonan dayasa aka d'aukesu ne a ciki, wani d'an guntun murmushi yay kawea ya wuce ciki.
Zai shiga aliyu na fitowa, sukai karo, hakuri suka baiwa juna kapin nan aliyu ya fitoh ya dawo motah suka karasa gidansu shafi'uh, a chaan suka wuni, har Maman shi ke cewa gashi nan yaki aure. Dije tace zata bashi matah, suka kuwa ajiye akan hakan.
Basu suka dawo gidah ba sea kusan karfe 9pm, dan har gidan Nafisa suka je.
Koda suka iso aliyu ya shiga da motanshi, suka fitah tare. A kopar gidan suka tarar da wani envelope, d'auka aliyu
"Kowa ya ajiye oho"?
Ciki suka shiga kowanne yay wanka, suka chnza kaya zuwa na bacci suka dawo falo. Bayan sun dawo dije tai kitchen had'uwa Aliyu lipton.
Aliyu ya daukie envelope d'in nan ya bud'e! Wanda ba komai bane a ciki face hoto nan muslim da dije wanda aka d'auka kimanin shekaru 4 da suka wuce.
Shiru aliyu yay baice komai ba kasancewar dije na kitchen tana had'u masa Lipton. Haka har ta fitoh ta tarar dashi a gurin, cup din dake hannunta ta ajiye a kasa ta kar6a pics d'in ta fara dubawah, take wasu hawaye suka kwararo mata a ido. Har kasa ta rage tsayenta ta fara magana
"My lion! Dan Allah kayi hakuri, wallahi wannan photo nan da kake gani bansan an d'auka ba"
"Kaimin rai kada ka gujeni dan Allah....
Hannu ya d'aga mata alaman ta dakata
"Khadeejah bkya buqatar neman gafarata, hakika rayuwata ta 6ace, amma ni nayarda dake 100% saboda hka ki deana wannan kukan kinji? Amma bani labari ya akayi hakan ta faru"?
Nan take ta tashi zaune ta fara bashi bayanin yanda abubuwa suka faru, ji yay kaman yay tsuntsu ya iske Nana ya kasheta saboda ta kaishi makoura.
Hannunshi dije ta rike
"Kayi hakuri! Kada kace da ita komai, in shaa Allah watarana sea labari"
Hotonan ya kalla ya dubieta
"Tashi muje mu kona wannan dmn mu cigaba da shiga cikin sabuwan rayuwanmu da zamu gina"
Murmushi tai ta bishi.
Bayan sun dawo falo ya zauna akan carpet, dije ta d'ora kanta akan jikinshi.
"My lion"
"Muhibbaty"
"Ka kuwa san na shiga jami'ah"?
D'an murmushi yay
"Kema kinsan tunda mai tsare gidah ya dawo babu wata jam'ah da zaki tafie"
Hannunshi ta rike
"Shikenan ai tunda baka so, Ina fatan Allah ya bamu zaman lpy mai d'orewa"
"Amin matata"
_1month letter_
Dije ce zaune tna kallon tashar saudi sunnah. Aliyu na gefenta yana kallonta. Yunkurawa tai ta tashi dn kiran da ake mata a wayah, tashin da zatayi sea amai, da hanzari ya d'auketa ya kaita toilet ya wanke mata jikinta ya dawo da ita, family Dr dinsu ya kira a wayah yazo, bayan y dubuta yace
"Congrat ur wife ix pregnant"
Wasu kaya sea amali akace, daria aliyu yay mai d'auke da hamdala ga Allah.
®Kausar Luv💞
[11/15, 7:18 PM] Kausar~Luv: [8/28, 1:00 PM] Kausar Luv💞: ```ALIYU_HAYDAR```
Page ((96)) to ((98))
```©Kausar M Hassan```
Bayan fitar dr, aliyu yace
"Bara in kira waya in sanarwa dasu abbi"
Tasowa tai dga kwanciyar da tai akan cinyarshi
"A'a! My lion ka barshi dan Allah idan lokaci yay sea ka fad'amasu kaga dea abubuwan da suka faru a wanchn karon Allah ma dea yay islam sea yazo duniyah da bamu ganshi ba, gashi anty Nana har ynxn hali bai chnxa ba"
Murmushi yay mata
"Ba damuwa matata yanda kike so haka za'ayi ai, Allah yaasa ki haifo min mace kinga nima sea a rika kirana da suruki watarana"
Daria tai
"Wallahi my lion ka fiye abun daria, ynxn dea kaga Zuma nake son shaa wallahi"
Kiss ya manna mata a kumata
"Ina zuwa ynxn zan dawo da itah"
Tashi yay ya fitah a cikin uwar ranar nan ya shiga mota. Bai jima sosai ba ya dawo da itah, nan inda ya fitah ya bar dije nan ya dawo ya tarar da ita. Zuman ya bud'e da sauri2
"Tashi kada babayna yace babanshi yayi masa rowah"
Fuska dije ta yatsine
"My lion nifa bana son zuma, ice cream nakeso"
Kai ya girgizah ya tashi ya ajiye zuman ya kara fitah, kasancewar akauy inda ake siyarwa nan kusa ya siyo ya dawo dashi, a kitchen ya tarar tana kokarin kunna gas, da sauri ya janyouta
"Kar6a! Dan Allah yi maza kisha"
D'an murmushi tai
"My lion kasa a fridge ni ynxn kuma kawea farar indomie nakeson ci"
Ajiyan ziciya ya sauke
"Kai wannan cikin zaka wahalar da babanka ko"?
Murmushi tai masa
"Nidea taimaka ka dafamin"
Hannuwan rigarsa ya fara nan_nad'ewa
"Angama my wife, amma Allah na dafashi sea kinciyeshi tas"
Murmushi tai ta koma falo tare da ice cream d'in a hannunta ta saka a fridge, chaan ta dauko zumanta ta fara shaa, haka ya kammala ya kawo mata ta fara ci kamar wadda bata ta6a Ciba. Tas! Ta cinye kayarta harsa sudin kwano
"Gskya my lion ka iya abunci dga yau kai zaka rika dafamin"
Murmushi yay mata
"Nidea taso kiji"
Ganin ta warwashe akan kujera yasa ya d'auketa ya wuce next room da ita ya kullu kopan d'akin.
Washe garin ranar
"Islam ne keta faman kiriniya, shida abbi, ala dole fa shi sea ankaishi yaga mum dinshi.
"Sallaman dasu dije sukai ne ya dakatar dashi dga shagwa6ar dayakeyi. Da gudu ya isa gareta ya rungumeta
"Mum I missed you"
Kan kujera suka zaunah suka fara firah, ummi ce ta lura da yanayin dije ya chnza babu ko tantama ta lura cikine da itah.
_9months letter_
Dije ce zaune akan kujeran falo, ummi da mame na gefe, cikinta yayi mata kyau sosai ya kara mata kyau. Aliyu ne ya shigo gidan shida islam, kusa da dije ya zaunah
"Kar6a Dr yace a baki"
Ledan ta kar6a ta bud'e
"Tohm ngd"
Kasancewar a gidan ta komah saboda ta samu kula mai yawa, bayan kwana 2 da faruwar wannan al'amari dije ta fara labour. Kasancewar a d'akin ummi take hakan ya baiwa aliyu damar jiyo zancen da ake dga d'kin. Da sauri ya fitoh zuwa d'akin, a durkushe ya tarar da dije ta cije le6enta. Yama rud'e irin yanda yaga tana zufah, da alama ciwon da takejie ya wuce misali.
Hannunta ya rike
"Dija sorry, be strong! Kada kiyi kuka"
Kusan daria dije tasoyi amma ta cije ta dakeshi a kirji
"Ka wuce ka bani guri wallahi, ka kyaleni"
Waiyh! Ta rike bayanta
"Hannunshi ya d'ora kan bayan nata
"Sorry in matsa maki ne"?
Ummi tsaye tai tana kallonshi, ganin baida niyyan fitah yasa ta korashi waje ta maida kopan ta kulle.
Waiyh! Haihuwa kenan, mai wahala, wallahi duk wanda bai girmama mahaifiyarshi ba to hakika yayi babbar hasara, uwa ta dabance, ita ta daukie cikinka, ta haifeka, a gurin haihuwar nan Allah kad'ai ne masani akan ko zata iya rayuwa ko kuma mutuwa, Amma ta daure bayan ta haifeka ta cigaba da kula dakai.
```Ya Allah! Addu'ah nake Allah! Ya Allah ka jiqan iyayenmu kamar yanda suka jiqanmu muna yara, ka bamu ikon yi masu biyayya```
Bayan gumurzu da akasha Allah ya baiwa dije haihuwa, inda ta sankota yarinyarta mai kama da itah.
Ummi komai da ake buqata tayishi kapin nan ta bud'e d'akin, abun mamaki mame da abbi, aliyu. Kai abun mamaki hardasu nana.
Murna suka rikayi sosai, kowanne a cikinsu shidea a bashi yarinya ya d'auka. Aliyu kowa kai ya kunna a cikin d'akin, ummi ta janyoushi
"Gidanku nace, tsaya nan sea gobe zaka ganta"
Daria sukai dukansu, abbi ya fara kar6anta ya sakamata albarka tukkuna aka baiwa mame, bayan ta d'auka zata maidawa ummi, Nana tace
"Mame kibani itah"
Aliyu kaman zai hana amma sai y kyale. Kar6anta tai tayi mata add'ah kapin nan ta baiwa aliyu itah.
[8/28, 1:00 PM] Kausar Luv💞: ```ALIYU_HAYDAR```
Page ((99)) to ((100))
```©Kausar M Hassan```
Kar6anta yay yayi mata addu'ah kapin nan aka maidata gun ummi, a wannan daren dai dije tare da ummi ta kwana, washe gari sukajie asibiti aka dubata bayan nn aka kira a waya aka sanarwa su innah, murna sosai sukai tare dayin addu'ah.
Su nazee da shafi'uh sune zuwa kullum kan hanya, bayan sati d'aya akai bukin suna yarinya taci sunan *fatima*. Haka dea suka cigaba da zama a gidan, dije ta koma d'akin ummi yayinda aliyu da islam keta rayuwa a d'akinshi.
_BAYAN KWANA 40_
Su dije da aliyu, islam da kuma jinjira Fatima suka shirya zuwa kauyensu dije, a chan fa isalm ya zagie ya koma kaman ya saba, wasanshi yakeyi abunshi, inna ta hadawa dije kayan gyara kusan ma a chaan suka wuni.
Rayuwa nata tafiya, aliyu da dije sun koma gidansu. Yarinyar su nata girma.
Yau ranar ta kama lahadi, dije ce zaune bayan tayiwa fatima wanka ta shiryata kamshin turarenta na tashi, dea2 lokacin aliyu da shafi'u suka shigo gidan.
Kan kujera suka zaunah, dije ta tashi ta kawo masu ruwa masu sanyi kasancewar ana d'an zafi, kar6a aliyu yay
"Nagode matata"
"Ur wlcm my lion"
Shafi'u bayan yasha ruwan ya dubie dije
"Khadeejah har yau dea sunan aliyu nan baki chnza masa wani ba"
Daria tai kad'an
"Haba shaf'iu ai wannan sunan har mutuwa , yana nan sunanshi my lion"
"Yauwa yama batun matar da kikace zaki bani gashi har shekara ta kusan shud'ewa"?
Murmushi dije tai
"Kana son nazee"?
Zama ya gyara
"So ma kai wallahi, ni ai tun ranar da accident d'in nan ya sameki na ganta kuma na fara sonta wallahi, kada in zama tazoru banyi aure ba"
Daria dga aliyu har dije sukah saa.
Sallama sukajie wadda ba kowa bace face nazee, nan fa dije ta amsa ta janyou hannunta suka zaunah batai kasa a guiwa ba ta fara yimata bayani ta kuma sanar da ita akan shafi'u ta gabatar dasu, nan akai komai aka kammala.
_BAYAN SATI 2_
A gida suka hadu su duka harda nafisat, a falo suka baje suna firah abunsu. Nanace ta fitoh a hnkli dga dakinta ta zauna kasa ta dubie mame.
"Mame dan Allah kiyi hakuri akan abunda na aikatamaki"
Murmushi mame tai
"Babu komai nana ai komai ya wuce meye ma amfanin tadou da maganar data wuce"?
Juyawa Nana tai ga ummi
"Ummi kema kiyi hakuri dan Allah"
Murmushi ummi tai
"Nana bkomai ai, ke jininace ina sonki har a rayuwana saboda haka ki deana bani hakuri haka, ba sonki ne banayi ba tun chaan dama, halinki ne kawea bana so"
"Ngd ummi"
Juyawa tai ga Aliyu zatai magana aliyu ya tari numfashinta
"Bkomai Allah ya yafemana, dama haka akeso idan mutum yay kuskure to ya gane yayi kuskuren, kuma kin gane sbd hka babu komai Allah yay mana jagora"
Kowa a falon murna yayi sosai, babu wanda ya rike nana a rai, saboda sun san rayuwan d'an adam babu inda bata kaishi sannan rayuwa kowacce iri ce tana buqatar uzuri.
Bayan wata 2 akai komai aka kammala akan auren shafi'u da nazee. Ya rage saura sati d'aya d'aya. Haka Allah y kaimu ranar bukin auren, akai shagali cikin harkar girma. Komai dea cikin wal_wala akaishi. Dije itace keyin komai a 6angaren amarya dea2 da second d'aya dije bta manta da cewa ita matar aure ce ba, kai harta su nana da nafisa su ummi sunje wannan shagali, a gurin bukin nema wani abokin kasuwancin su aliyu mai suna mansoor wanda ke xaune a saudi Arabia, d'an kimanin shekaru 55, yaga nana kuma yace yana sonta da aure. Ba'ayi kasa a guiwa ba akai komai bayan anyi buki da sati d'aya suka wuce Kingdom of Saudi Arabia.
_Bayan sati 3_
Aliyu na zaune yana wasa da Fatima, dea2 lokacin misalin karfe 8pm na dare, Dije ta fitoh dga d'akinta tai wanka ta fitoh ta sanya rigar baccinta iya cinya red in colour, tayi mata kyau sosai ta ko ina kamshi ke tashi a tare da itah.
"My lion plzz gyara min zaren rigan nan"
Murmushi yay
"Kinga fatima ma tai bacci ki shinfiedieta"
Kar6anta tai ta wuce da ita d'aki ta shinfiedieta a cikin gadonta ta dawo.
Gashinta ta janye
"Yauwa samin plz"
Maimakon yasa sea ya zare gabad'aya yasa hannunshi ya janyoutah, kamshin jikinta ya shaqa
"Deeja kinyi kyau"
Kiss ya shiga aikamata ta ko ina wanda yasata narkewa kasa shima ya rufa mata bayah...
®Kausar Luv💞
[11/15, 7:18 PM] Kausar~Luv: ```ALIYU HAYDAR```
*FINAL EPISODE*
```©Kausar M Hassan```
*BAYAN SHEKARU 5*
Babban gidan Alh shuraihu, ilahirin kafatarin iyalinshi suna ciki, Abbi da kanshi, ummi, mame, aliyu, nana, Nafisa, isalm, dije, Fatima, da kuma Muhammad d'an d'an Nafisa Wanda ya girma.
Kai hardasu shafi'u da nazee duk suna falon, da "Yar su yar shekara 3 mai suna sadiya, fira suke sosai falon ko ina daria kakejie.
Dije a cikin zuciyanta take furta
"Rayuwata ta zama haske, samun miji da "yan uwan mijina masu k'aunata, duk da nasha gwagwarmaya a rayuwana, amma hakan baisan na sare ba, ga family d'ina masu kaunata. Hakika aure b yana nupin rushewar tsohon family dinka bane, yana nupin gina wani sabo a cikin soyayya! Kauna da kuma aminci".
Murmushi tai lokacin da tagan isalm yana wasa da sadiya, cikin ranta ta kara furta
"Allah gatan bawa, ya Allah ka zaama gatana"
Da dare misalin karfe 9pm, dije ce ta fitoh dga kuryan dkinta, kan kujera ta kwanta. Dea2 lokacin aliyu ya fitoh dga dakinshi, rungumeta yay dga kwancen
"Khadeejah kin zama garkuwa agreni wadda ta zama haske a cikin rayuwana, ina sonki sosai kinji"
Murmushi tai masa ta manna masa kiss a baki
"Nima hka mijina, ka kadea nakeso, kazama tare dani a kodayaushe"
Murmushi yay
"Alkawari ne wannan matata"
Fuskanshi ta had'e da nata
"Ngd my lion"
Kissing d'inta ya shigayi sosai, dkyar ta d'anja da baya
"My lion kai baka gajiya ne"?
D'an dakatawa yay
"Ina sonki ne wallah, idan kuma kina so sea in karo mata in hutar dake"
Jawoshi tai ta rungumeshi
"Wallahi a'a yi yanda kake so my lion, kishiya? Chaab! Allah ya tsare nikam bana son kishiya"
Murmushi yay mata sosai ya manna mata kiss a kumatu mai kyau.
"My lion I love you"
"I love you tew"
Hancinta yaja kad'an yace
"My dream girl"..
Dariya suka saa dukansu tare da rungume juna.
A hka suka cigaba da rayuwa cikin farin ciki da kaunar juna
ALHAMDULILLAH!!!!!
A nan wannan labarin yazo karshe ina fatar masu karatu kun samu darussa, nishad'i a ciki.
+2347067465637
Wannan littafi na ALIYU_HAYDAR.
Sadaukarwa ne gareki
```DEEJAH ABDULLAHI DUKAMAJE (Dream girl)```
Group members d'ina na facebook da whtsapp duk ina sonku ina kaunarku sosai.
Duk wanda yay posting wannan labari dga wannan group zuwa wannan. Da wanda nasani da wanda bansani ba ina cewa
"Tnx 2u all"
Bazan manta daku ba.
Ummi Aysha Ibrahim khalil.
Aisha Muhammad Maman Shakur ( the one and only)
Fertyma Usman (Pherty)
Fido sodangi.
Futhalkhair
Rash kardam
Phatee Lamin
Ummu haibat
Kai dama sauransu duk na gaisheku.
Da wannan nake cewa Ina sonku sosai...
Masoyana a duk inda kuke a fadin duniya ina sonku sosai ina kaunarku, ni mutum ce kamar kowa kowanne dan Adam ajizi ne, idan nayi kuskure a yi hkuri dani a yafemin.
Plzz ina cigiyar books d'ina
KECE JININA UMMI AYSHA
HALEEMATU_SADEEYAH
SAI BANGO YA TSAGE
KAINE SANADI
LABARIN KHADEEJAH.
TSAKAA MAI WUYAA.
Plz duk wanda keda ya taimaka min dashi ta wanchan number d'in nawa da na bayar..
I love you All.....😘😍
Kausar Taku ce kuma nawane, Allah ya sada fuskokinmu a aljanna firdausi amin....
Mzzzzzzz you guys.