ALJANA CE KO MUTUM Page 41-50
.
suka hada ido da nawwar kowannan su ya zaro ido waje, yayi saurin sake gyalen tare da mike wa tsaye, yana ja da bays, itama saurin tashi tayi tana murxa idanuwanta shin mafarki takeyi ko da gaske ne .
har sai da ya Isa bakin kofa zai fita yaja burki ya tsaya, yayin da zuciyar shi ke harbawa, ya juyo don kara gasgata abunda ya gani, still dai nawwaran ce ba wata ba.
yashiga tunani me kanwarsa take nufi ne, tana nufin sameeratu ce kyautar data mashi? sameera data zuba mawa nawwar ido takasa magana itama azuciyarta, tunanini take, anata zaton nawwar abokin mijinta ne Yusuf.
.
cikin murya sassanya sameeratu tace yaya nawwar, ya juyo da dubanshi gareta, tare da kara so wa wajenta, hawaye na zuba a idanunshi, yana mata wani irin shu'umin kallo na soyayya, yayin da itama haka.
takara cewa yaya nawwar kaya fe min nayi kuskuren daya zame min Dana sani, nakin amsar soyayyarka, alokacin son Yusuf ya rufe min idona, bana ganin kowa sai shi, sai da akasa mana ranar aure, sannan hankalina ya dawo gareka, gashi yau Yusuf shine matsayin mijin Dana aura takara fashewa da kuka.
nawwar najin haka yaji jiri na son dibanshi zai fadi kenan, ta taho da sauri cikin kidima ta tareshi ya zauna bakin gado ya dafa kanshi da hannayen shi, yana salati" yace sameeratu lokaci ya kuri narasaki har abada, tace kayi hakuri nawwar nice da wannan kaicon don xuciyata tana tare da kai, baxan taba manta ka ba Nima sai ta fashe da kuka.
ya matse wani hawaye mai radadi tare da cewa narasaki har abada nawwara, ji sukayi ance hamman dina Baka rasata ba hasalima kun kasance a inuwa daya wato mata da miji.
gaba ki dayan su suka tashi don kallon mai magana, Mimi ce ke karasowa cikin dakin, yayin da Yusuf da awwal da khadija da zainab suka shigo" cikin murmushi, Yusuf yace kaji masoyan asali Mimi tace aikuwa.
.
nawwar yace Mimi mekike nufi, tace hamman nah ina nufin aunty sameera matar kace itace kyautar Dana maka, nawwara ta kalli Yusuf don Neman Karin bayani.
tace Yusuf kafahimtar dani abunda naji, yace nawwar abunda kikaji gsky ce da nawwar aka daura miki aure, ta kara kallon khadija da zainab suma suka Daga mata kai alamun haka ne.
nawwar da nawwara kamar sun hada baki sukace atare, tayaya hakan ta faru, awwal yace yanxu Mimi zata fada muku.
Mimi ta soma magana tace, hamman in baka manta va lokacin da aka kwantar da kai a asibiti na maka alkwarin insha allahu sai ka auri nawwara, to tunda ga lokacin nadauki aniyar nemo nawwara, SBD bana son in rasaka, da haka naje nasamu Dr awwal nafada mishi kudirina , shima ya aminta.
takanas mukaje kano dashi, alokacin ma ana shirye shiryen bikin nawwara da Yusuf, lokacin ZANU shiga gdan sai muka ga zainab da khadija, muka gabatar musu da kanmu da abunda ke tafe damu, sun nuna farin cikin su sosai.
kuma sun Samar mana nawwara bata son auren da Yusuf, muka rasa ya zamuyi mutunkari Yusuf da maganar, ashe Yusuf dan makarantar su yaya sulaiman ne kuma abokinshi ne, to shine nasanar masa, shikuma yafada mawa Yusuf cikin sauki Yusuf ya amince, SBD amintar dake tsakanin su da yaya sulaiman, daganan kuma muka dunguma wajan abbban nawwara muka sanar mishi.
shima yayi murna dajin wannan labarin , Yusuf yace kar asanar ma nawwwara sai dai kawai taganta da nawwar, Nima haka nace kar asanar mawa nawwar, sai Mami kadai da Abban mu, to kunji yadda akayi.
nawwar ya rungume yar autar su yana thank you my sister, Ashe haka kike sona daya, lallai na jinjina miki Allah ubangiji y baki miji mafi alkhairi, kowa yace amin.
itako tace Allah ya bani Yusuf hamman nah, nawwar yace mene cikin dariya sulaiman yace AI Yusuf ke sonta.
itako nawwara tana jikin khadija tana kukan murna da Allah ya nuna mata wannan rana, gaba ki dayansu suka fito falo don su Mimi zasu koma GDA, nawwara da nawwara sai Satan kallon juna suke.
khadija taci Mimi AI nikam binku zanyi don idan na kwana gdannan zan kwashi kayan haushi SBD nasan za agurji soyayya gara nayi can, bakiga ma yadda nawwara ke harara ta va, alamun bata son inkwana don karna takura su, sameeratu takai ma khadija duka.
Yusuf ya ijye musu gazan amare da su drinks yace amarya da ango mun barku lafiya, so Ku nuna mawa duniya kunfi *king* *laisu* da *rumana* na takaddan *kutausaya* *min* iya soyayya dukkan su suka kwashe da dariya.
bayan tafiyan su nawwar ya janyo nawwara cikin jikinshi ya rungumeta yana ma Allah godiya daganin wannan ranar, bayan sunci sunsha sun gabatar da sallan da akeyi, tare da addu'oi, daganan kuma sai zance ya canxa salo, inda suka Lula duniyar ma'aurata, ina ganin haka nayi waje abini don kunya, amma nabar hjya seeema, zasu gano muku.
kubiyoni agaba donjin wani soyayya zata kasance agdan ma'auratan nan.
.
su Mimi sun Isa gda tare da ba mawa Mami labarin yadda suka baro su hamman din, Mami taji dadi sosai kuma tayi musu addu'an fatan zaman lafiya da dorewa.
Mimi tace Mami ina aunty sauda, Mami tace AI tun lokacin da aka kawota, ta kwanta SBD gajiyan biki, hakane kam gashi sunsha hanya.
ASUBA TA GARI.
.
nawwar ne yatashi Daga bacci don yin alwala SBD zuwa masallaci, ya tsura mawa nawwara ido"" yana kallonta, yayi murmushi tare da shafo gefen fuskarta.
bayan tafiyar shine itama ta tashi donyin wanka sannan tazo tayi sallah, bayan ta idar tafara karatun alqur'ani, lokacin kuma nawwar ya dawo masallaci.
ya yaba da hazakarta, don da ka take karantawa, bayan ta gamane ta juyo sukayi ido hudu dashi ta sunkuyar da kanta kasa tana gaisheshi, ya amsa mata cikin murmushi, tare dace wa y gajiyan biki da sabon wuri kuma, tace gajiya kam tabi gado.
yace masha Allah haka akeso, yace nawwara ki saki jikin ki dani ni mijinki ne mai kaunar ki, in Allah y yarda bazan taba barin wani abu y same kiba , nan suka fayya ce mawa junan su irintarin son da sukeyi wa juna, daganan kuma suka koma bacci" sai wajajen karfe Tara suka tashi, ya wuce bangaran sa don ya shirya.
.
itama tashiga wanka bayan ta fito ta tsara adonta mai kyau cikin atamfa , tana cikin shirya wane taji hayaniya a falo, su khadija ne suke hamman tsiya Mimi tace ango kasha kamshi, irin wannan kwalliya haka, sai kace za aje gasar kyau,, lallai aunty mu ta iya shirya ka"" suka kwashe da dariya" dai dai lokacin nawwara tafito.
duk suka zuba mata idanuwa Mimi ce takara sa ta rungumeta tare da cewa barka da safiya auntyn mu, yauwa Mimi iyayen surutu, tundaga daki nakejin muryanki kina ma angona tsiya.
khadija tace a lallai nawwara har kin samu bakin magana, zainab tace aunty khady ba dole ba, zama da masoyi dadine dashi fa,, Mimi tace hakane kam, suka bushe da dariya.
Mimi tace ga breakfast dinku nan Mami tace mukawo muku, nawwar yace AI yanxu nake son dama muje wajan mamin don taga amaryata"" ya janyota jikinci tare dacewa muje muyi breakfast, suko su khady zuba musu ido sukayi cikin sha'awa.
bayan sun gama suka dunguma can gdan Mami tayi murnan ganin nawwara kuma rayaba da ita'. tayi musu nasihohi masu ratsa jiki, aunty saudama tayi musu.
bayan wata uku dayin bikin sameeratu akayi na khadija, alokacin ne nawwara taje ganin GDA , SBD tund tayi aure bataje ba sai da bikin khadija ya tashi, tare da sulaiman da Mimi sukaje, shi sulaiman zuwanshi da biyu yayi SBD zainab kanwar nawwara.
.
lokacin nawwara da cikin wata biyu ajikinta, iyayenta sunyi murnan ganinta, don takara kyau alamun hankalinta akwance,, SBD nawwar na tattalinta suna gurje soyayya, daidai da girkima shi yake mata, ga Mimi kuma nataya ta wasu ayyukan SBD gata da akanuna mata.
bayan wasu yan watanni nawwara ta haifo santalelen danta mai kama da babanshi, kar kuso kuga murna wajen Mami kamar zata cinye yaron, anti suna Inda yaro yaci suna Ahmad ana kiranshi da (usaimin).
suna samun kula, bayan sunyi arba'in ne akayi bikin Mimi da dan ustaz Yusuf da anso a hada dana sulaiman waje daya, ska fasa SBD hidiman zayyi yawa.
nawwara ta sake yin JAM na state uni dake Kaduna wato Kasu inda zata karanta Islamic studies, cikin sauki tasamu masugunni a Kasu, tafara karatun ta cikin sa'a, arzikin mijinta bunkasa take.
usaimin awajen Mami yake zama SBD makarantar nawwara, anxo anyi bikin zainab da sulaiman , abun gwanin ban sha'awa .
akwana atashi bawuya wajan Allah
shekaran auren su nawwar 6, yau weekend duk suna gd babu aiki tare da yaran su guda biyu Ahmad (usaimin) sai maimuntu (mubina) , duk suna zaune afalo ana hira, nawwara ta kwanta acinyar nawwar, yayin da shi kuma yana mata susa akai, mubina tace, daddyna kana cirewa mummy kwarkwata ne dukkan su suka kwashe da dariya, nawwara tace, mubina a ina kika San kwarkwata?
tace mummy awajen Hjy kaka wai nace ma Hjy kaka tabani dan kwalinta na daura sai tace min baza ta bani ba wai ina da kwarkwata a gashine, ta karashe maganan cikin shagwaban kuka.
usaimin ya kwashe da dariya, yace hakane mana kina dashi, nan da nan tafara ihun kuka tana daddy kaga yaya usaimin ko, ya turekan nawwara y janyo mubina jikin shi yana lallashinta, bawwara tace lallai kam SBD wannan sha gwababbiyar zaka tureni bara ka gani, aiko tadare jikinshi, shima usaimin ya taho duk suka zauna jikin nawwara suka rungumeshi suna dariya yace I love you all.
TAMMAT ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFIN ALJANA CE KO MUTUM,