Kuka kawai Ummu takeyi lokacin da ta gama sauraron labarin abinda ya faru, a hankali Ra'eez ya matso ya rungumeta shima yana kukan, gaba d'aya sai suka bama mutanan wajen tausayi sai mutuwar ta dawo masu farko. Da kyar Alhaji Mansur ya lallashe su kafin sukayi shiru.
Ajiyar zuciya Ummu ta sauke tana fad'in Allah yajik'an ka Alhaji Allah ya kai haske kabarinka, hakika bazan tab'a yafema wad'an da suke dasa hannu a mutuwar ka ba, kuma insha Allahu sai sun wulak'anta.
Alhaji Mansur yace kiyi hakuri komai yazo k'arshe, idan suna tunanin sun rufe sirrinsu Allah zai haskasu kowa ya gansu, ina so kisa jarumta aranki domin kije kiga yanda azzalumai zasuji kunya agaban idonki.
Jinjina kai tayi tana goge ido tace dole nasa jarumta kam, kuma zanje har kotun domin na bada sheda akan zaluncin da akayima Malan Sani, domin duk abinda ya faru alokacin ban mance ba.
Murmushi Ra'eez yayi ya rik'o hannunta yana fad'in Ummu ki kwantar da hankalin ki ina nan babu wanda zai sake saka ki zubar da kwalla, kuma zakiga yanda azzalumai zasu wulak'anta. Kanshi ta shafa tana fad'in Allah yasa Ra'eez.
**** ***
Dan Allah ka cire damuwa aranka, bazan bari kayi zaman gidan yari ba koda ace bani da kud'in da zan biya tarar da aka saka maku wallahi zanje naci bashi, dan haka kadena damun kan ka.
Ummah tace mu godema Allah da abun ya tsaya a haka, yau da ace kana dasa hannu a cikin kisan shikenan kaima rayuwar ka acan zata k'are, babu wanda besan k'addara ba, kuma zuciya bata da k'ashi dan haka kadena saka damuwa aranka kaga likita yace jinin ka ya hau.
Ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in dole na damu Nabeel, ka tunafa ko auren farko bakayi ba, kamar yanda wannan abun ya faru ina mai tabbatar maka daga lokacin da ka fara neman aure sai wannan abun ya shafi auren ka, wallahi nayi nadamar abinda na aikata domin nayi maku bakin fenti, taya zan iya fita na kalli mutane, nasan da zaran na fita za'a rik'a nuna ni.
Nabeel yace ni dai bazan damu ba Abbah, damuwata d'aya idan ka kasance acikin damuwa, duk wanda zai nuna mu yaje yayi ta nunawa domin abun kunyar mu mai sauki ne, ina mai tabbatar maka daga nan zuwa litinin za'a mance da labarin ka, domin za'a tono abinda zai girgiza mutane, dan haka kacigaba da neman yafiya awajen Allah, kud'i kuma gobe zanje na kaisu.
Murmushi Abbah yayi yana fad'in nagode Nabeel Allah yayi maka albarka kuma ya baka wad'an da zasuyi maka fiye da haka. Gaba d'aya suka amsa da amin.
*** ***
Washe gari wajen k'arfe goma suka had'u a gidan Alhaji M. Sanda, zaune suke a lambu kowa tashin hankali kwance a fuskarshi.
Mr. Kallah yace hakika muna cikin tashin hankali babba, dama irin wannan ranar nake tsoro, wallahi jiya banyi bacci ba bayan da naji wai an yanke maka hukuncin d'aurin wata ukku agidan yari, sannan Fawwaz d'aurin rai da rai, shiyasa nayi saurin kiran kowa nace mu had'u a nan dan muna da buk'atar tattaunawa kafin litinin saboda shari'ar da za'ayi ta shafemu duka.
Alhaji Barau yace wallahi jiya kwana nayi ina gudawa, banyi baccin kirki ba saboda tashin hankalin da yake gaban mu, gani nake duk kunfini kwanciyar hankali domin nine wanda zan yanke hukunci da zaran an tabbatar da mai laifi.
Alhaji Marusa yace wai an tabbatar da shedar ne? Alhaji Barau yace ai tunda har aka iya samun shedar kisan Fawwaz na tabbata akwai tamu aciki, domin idan baku manta ba alokacin da aka kawo wayar yaron a ciki mukaga duka d'aukar da yayi.
Alhaji Marusa yace muna da sauran lokaci, nasan wannan shedar dole tana hannun Brr. Ra'eez, abinda nake gani mai zai hana mu aika Lucky ya sato mana ita ba shikenan ba.
Mr. Kallah yace kana wasa da wannan lauyen, taya zai bar irin wannan shedar da ta riga ta fito a waje d'aya, kada kamanta yasan abinda yake ciki, idan ma an sace ta wajenshi ina da tabbacin ya tura a wani waje, kawai a samo wata hanyar.
Alhaji Marusa yace bara na kira Lucky naji yanda za'ayi domin ina tsoron yaran can da aka kama idan sukaji duka zasu iya tona komai, kunga idan ma Ra'eez beda wata sheda akan mu sun samu a wajen su.
Waya ya d'auko ya kira Lucky. Bayan sun gaisa yace wai Lucky kasan halin da ake ciki kuwa? Lucky yace na sani mana meye abun damuwa aciki dan kawai an kama Yarana, zuwa anjima zakuji labarin mutuwarsu dan yanzu haka sun kusa shek'awa, maganar shedar da akace an samu ta kisan Fawwaz kuma ina mai tabbatar maku ita kad'ai suka samu a flash d'in, idan kukayi duba da lokacin daya d'auki vedion zakuga be isa ace yaje ya tura a flash ba har ya nufi wajen shugaban kwastam, nafi tunanin tun bayan daya d'auki kisan Fawwaz ya adanashi a flash d'in kuma agidansu ya b'oyeshi, sauran na wayarshi kuma an k'onasu, dan haka kudena damun kanku idan ba haka ba zaku tona kan ku kuma wallahi ba ruwana dan zan iya barin garin gaba d'aya kuma babu wanda zai iya gano inda nake.
Jinjina kai Alhaji Marusa yayi yana fad'in na fahimce ka, mungode sai munyi waya. Kashewa yayi ya kallesu yana fad'in kunji dai abinda yace, dan haka ku kwantar da hankalin ku yaran ma zai gama dasu, ai nasan Lucky beda wasa, kuma nima na aminta da bayaninsa.
Gyara zama Alhaji M. Sanda yayi dan tun d'azu beyi magana ba, kallonsu yayi yana fad'in hankalina ba zai tab'a kwanciya ba matuk'ar ba gani nayi an gama da shari'ar litinin ba, wai meyasa ma acikin mu babu wanda yake hud'd'a da malan tsubbun nan.
Alhaji Barau yace haba dai 'Yallab'ai kai da kan ka, ai wannan sai mutane marasa ilimin boko sune suke irin wannan harkar, dama can ban yarda da irin wannan abubuwan na Iyaye da Kakanni ba, nafi gane nasa majiya k'arfi suyi mani aiki, amma ka tsaya a wajen wani tsugunnan nan mutum kace shine zai maka aiki, idan Kura na maganin zawo tama kanta mana, kai tunda kake ka tab'a ganin Malamun tsubbu cikin kyakkyawan yanayi, shegu kullum suna zaune a bukka ko arami kamar mujiya, kawai ka barshi Lucky ma ya ishe mu da sauran basirar da muke da ita.
Alhaji Marusa yace baka had'u da manya bane shiyasa, idan kana buk'atar aiki babu b'ata lokaci kaje wajen manyan arna a cikin tsaunuka anan sai abinda kaso.
Mr. Kallah yace kudena wannan maganar ta wasu masu tsafi bamu da lokacin yin wannan, kamar yanda Alkali Barau yace aiki ne na marasa ilimin boko nima na goyi bayanshi, muyi amfani da ilimin mu da basirar mu kawai.
Alhaji M. Sanda yace shikenan Allah ya kaimu litinin d'in muga da abinda zasuje, amma fa asanar dasu Adebayo domin suma acikin mu suke. Alhaji Barau yace wannan ba matsala bace duk za'a fad'a masu, kuma nasan ma dole suji hukuncin dana yanke a kotu tunda akwai sunan ka, abinda yafi kawai bakin mu ya zamo d'aya. Gaba d'aya suka ce badamuwa.
Alhaji Marusa yace ni yanzu babban abinda yake damuna rashin kud'in da yake so ya sameni, domin jarina yayi k'asa sosai, a yanzu haka bani da jarin da zan iya shigo da kaya masu yawa dole sai dai na fara da kad'an-kad'an, gashi dama ni ba gwanin sayen kadara bane duka gidajena basu wuce ukku ba agarin nan, biyu haya ake aciki, gaskiya duk b'arayin da suka mani satar nan ban yafe masu ba wallahi kuma sai Allah ya saka mani.
Kauda kai Alhaji Barau yayi yana murmushi a b'oye. Alhaji M. Sanda yace ka kwantar da hankalin ka a kammala wannan matsalar sai asan abunyi. Alhaji Marusa yace shikenan nagode maku.
*****
Bayan sun tafi Alhaji M. Sanda yashigo gida, zaune ya iske Ammi tayi tagumi tana tunani. Zama yayi yana fad'in wannan tunanin babu inda zai kai ki, idan zakije ganin Fawwaz kitashi muje.
Ajiyar zuciya ta sauke tana fad'in yanzu Alhaji hankalin ka har akwance yake da zakace na bar tunani, gudan jinina fa aka yanke ma hukuncin kisa shine zakace na bar damuwa.
Gyara zama yayi yana fad'in kinsan dai baki fini sonshi ba ko? To tunda kika ga na saka hakuri araina kema kisa, domin Fawwaz bazai tab'a wulak'anta ba, da ace yau ratayeshi za'ayi shine hankalina zai tashi, amma zan ganshi a duk lokacin da naso, kuma ni nasan yanda zanyi domin a sama masa kwanciyar hankali a gidan yari domin ina da mutane acan, kuma kinsan babu abinda kud'i basayi, dan haka kitashi muje idan zaki.
**** ***
Ya isa haka Fawwaz kadena kuka babu abinda za'ayi maka, yanzu daga nan zanje naga shugaban gidan Yarin zamuyi magana dashi har wajen kwana dole asake maka, ina zaka iya kwanciya da manyan katti wad'an da suka gawurta awajen aikata laifuka, ko aiki ma bazan bari kayi ba, sannan abinci zansa arika baka wanda kake so kaji.
Kai ya d'aga yana goge idonshi. Ammi tace Fawwaz ka godema Allah da yasa ba kisan lokaci guda za'ayi maka ba, yanzu lokacin da zaka koma ma Allah ne, kaga dai har abada bazaka fita anan ba sai dai a fitar da gawar ka, abinda nakeso da kai ka zama nagari, domin duk wanda yazo gidan yari zai had'u da wad'an da suka fishi komai arashin ji, haka kuma zai had'u da wad'an da yafi, dan haka ina so ka natsu ka koyi darasin rayuwa, kada kace zaka biyema wasu ka lalata rayuwar ka, duk inda aka tara jama'a akwai na banza dana kirki, abinda nakeso da kai kayi kokarin nemo na kirki kayi tarayya dasu, ni dai na yafe maka duk abinda kamun kuma zan cigaba da nema maka shiriya.
Shiru tayi tana goge hawayen da suka zubo mata. Matsawa Fawwaz yayi ya rungumeta yana kuka, kasa daurewa Alhaji yayi shima ya juya yana goge kwalla, soyayya tasa ya jefa d'ansa cikin matsala.
Wani daga cikin ma'aikatan yazo yana fad'in Alhaji lokaci yayi. Kallonshi Alhaji yayi sai yaga da alamu sabon d'auka ne dan duk ma'aikatan wajen girmamashi sukeyi. Kai ya jinjina yana fad'in naji, wucesu yayi yana fad'in kai ka taso kaje ku faskara wancan iccen.
Kuka Fawwaz ya fashe dashi yana fad'in Dady kaji ko, dan Allah kayi wani abu wallahi bazan iya wahala ba, ni gara ma asake mani hukunci arataye ni zaifin mu sauki, kwana d'aya bakaji yanda nakeji ba. Saurin tashi Ammi tayi ta bar wajen tana kuka.
Tashi Alhaji yayi yana fad'in kada ka damu zanyi magana yanzu. Kud'i yasa mashi aljihu yana bin kayan da suke jikinsa na gidan yari da kallo, wai yau 'Dansa ne yake sanye a cikin kayan nan, shida yayi shekara da shekaru yana aiko mutane gidan nan, da masu laifi da marasa laifi yau gashi shima an kawo nashi.
Juyawa yayi yana fad'in sai mun sake dawowa... Barka dai Alhaji Muhammad Sanda. Saurin jiyowa yayi yana kallon dattijon da yake tsaye kusa da Fawwaz. Ido ya tsura mashi sai dai ya kasa gane waye.
Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in dama ai bazaka sheda ni ba, domin ka yanke ma mutane da yawa hukunci zuwa gidan nan ba lallai bane ka iya gane kowa musamman wad'an da sukayi shekaru a gidan, sai dai su daka yanke ma hukuncin har abada bazasu tab'a mance fuskar ka ba.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in bawan Allah duk wanda kagani agidan nan to abinda ya shuka ne yazo girba.
Malan Sani yace sosai kuwa, tunda gashi ma har an fara kawo 'Ya'yanku a gidan, da sannu sauran zasu biyo bayanshi, domin mutanan da sukayi suka agidan nan suna da yawa, lokaci kawai ake jira yayi domin akawo su su girbe shukar su, domin gidannan yana maraba da kowa, mai kud'i ko mulki ko sarauta babu wanda baya d'auka, kuma duk wanda yazo dole ya jeru da sauran mutane.
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke yana fad'in kaga Malan ni bansanka ba haka kawai kazo kana gasa mani magana, Fawwaz kaje ciki zanje wajen shugaban gidan nan.
Juyawa Fawwaz yayi yana goge idonshi, har Alhaji ya juya Malan Sani yace idan baka sanni ba ai kasan Tsohon shugaban kwastma marigayi Alhaji Maiwada, idan har ka tunashi dole ka tuna da direbanshi da ka yanke ma hukunci zuwa gidan nan.
Dammm!!! Gaban Alhaji ya fad'i, saurin jiyowa yayi yana kallon Malan Sani. Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in da sannu zaku maye gurbina yayin da Allah zai d'aukeni naje nacigaba da rayuwa cikin Iyalina. Wucewa yayi yana murmushi.
Jiki a sanyaye Alhaji yaja k'afarsa zuwa ofishin shugaban gidan Yari, har ya isa yana maimaita maganar Malan Sani. A bakin k'ofar ofishin ya tsaya suna gaisawa da masinjan, magana yayi masa akan yana son ganin shugaban wajen.
Masinja yace ai baya gari Alhaji. Kallonshi yayi yana kallon motar mutumin, juyowa yayi yana fad'in amma ai ga motarsa can. Masinja yace ai yau yayi tafiyar bayan yazo nan ya ajeta suka tafi a motar abokinsa. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in shikenan bani lambarsa.
Babu musu Masinja ya bashi, juyawa yayi ya tafi yana masa godiya. Tsaki Masinjan yayi yana fad'in munafukan Allah, a hankali asirin ku zai tonu, shekara nawa kana aiki baka tab'a zuwa gidan nan ba sai yau da aka kawo d'an ka, insha Allahu sai Allah ya toni asirin duk wasu masu zalunci, kun lalata Yara sai abinda sukaga dama sukeyi ba dole surik'a kisan kai ba.
Ciki ya shiga, yana shiga
yace 'Yallab'ai ya tafi. Tsaki 'Yallab'an yayi yana fad'in ai tunda naji yanda shari'ar ta kasance nasan dole sai yazo shiyasa na shirya masa hakan, su sauran da ake kawowa suna rayuwa ba mutane bane, a yanda hukuncinsa yazo aikin wahala zeyi sosai, kaga hakan zai zama darasi akanshi, kuma wallahi zan jama sauran ma'aikatan kunne duk wanda ya amshi cin hanci akan wannan yaron zai iya rasa aikinsa, domin ni ba tsohon shugaba bane babu maganar cin hanci, duk wanda yazo gidan nan dole yayi aiki, wasu ma basu da alifi amma haka suke aiki, sai kuma ace za'a kare masu laifi, koya kirani ba zai samu ba ma.
**** ****
Duk wani shirye-shiryen shiga kotu sun kammala shi, sosai Ummu ta sake a cikin su Mama da Umman Labiba, kuma jikinta yayi sauki sosai, sai damuwar rashin Abbu da take damunta.
Zaune suke a falon gidan su Sameer sunzo duba Adnan, jingina yayi dan jikinsa da sauki sosai. Nabeel yace abokina kajiyo k'amshin lahira fa. Murmushi Adnan yayi yana fad'in ai azabar kishi bata da dad'i, wallahi mutanan nan basu da Imani, wai shikenan an sake su? Rafeek yace taya za'a sake su, ai tunda Alkali yace acigaba da rik'esu har sai an kawo kwakkwarar sheda akansu dole a rikesu, Hamza ma yace suna nan suna shirya yanda zasu kama Ogansu.
Jabeer yace ai wannan Ogan nasu shine babban azzalumi, matuk'ar aka kamashi shikenan komai yazo k'arshe, dan yanda na fahimcesu bazasu tab'a tona asirin junan su ba.
Ra'eez yace Adnan baka da wata hanyar da za'a iya kamashi? Adnan yace gaskiya gidanshi ba cikin gari yake ba, domin wani lokacin idan suna waya ina jin yana fad'a masu su sameshi bayan ruwa, ina kyautata zaton kamar yafi zama acan.
Rafeek yace shikenan zanyi magana da Hamza saboda su san inda zasu farauceshi. Sameer yace wato a kullum ina k'ara godema Allah da yasa shiryata tazo mani tun ina da sauran kwana, hakika zalunci beyi ba, haka zalika aikata b'arna beda amfani, wallahi ayanxu ne nake jina cikekken mutum.
Rafeek yace sai ma kayi aure zaka k'arasa zama cikekken mutum. Dariya sukasa gaba d'aya. Sameer yace ai na kusa nayi auren nan, akwai Hindatu tana d'aya daga cikin matan da na b'atama rayuwa, sai dai ita ba ta hanyar da nakebi na bi da ita ba, anan bayan layin mu take, Iyayenta suna da rufin asiri haka yarinyar akwai natsuwa, tun farkon ganina da ita sai naji ta burgeni, hakan yasa na fara mata magana har muka fara gaisawa, a hankali sai ta fara sona, duk da bata fad'a mani ba amma na fahimci hakan, ni kuma kawai sha'awarta nakeyi, da haka na fara janta jikina, soyayyar da take mun yasa take bin umarni na, da haka har na samu na biya buk'ata ta da ita, tun daga lokacin na dena kulata, lokacin da Iyayenta suka gane abinda nayi mata tasha duka, inda Allah yaso bata d'auki ciki ba, mahaifinta yaso ya tada maganar sai mahaifiyarta tace ya rufa masu asiri yin hakan kamar tona masu asiri ne, dole haka ya hakura, tun Hindatu tana kirana bar na kulleta dole ta hakura dani, shiyasa a lokacin da nace zanbi wad'an da na b'atama rayuwa na basu hakuri naje har gidansu na bama Iyayenta hakuri itama na bata hakuri, cikin sa'a kuma ta yafe mani, tun daga lokacin kawai sai na fara tunaninta, daga baya na fara kiranta, maganar da nake maku yanzu haka soyayyarmu mukesha kuma za'ayi maganar bikin mu.
Tafi sukasa suna dariya. Rafeek yace gaskiya naji dad'in hakan, kuma nasan zaka kula da ita, dama kuma haka ake so, Allah ya baku zaman lafiya. Gaba d'aya suka amsa da amin.
Wayar Rafeek ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Hamza ne, bayan sun gaisa ya fad'a masa mutuwar Yaran Lucky, Rafeek yace shikenan yanzu zan zo. Kashe wayar yayi ya fad'a masu abinda ya faru. Shiru sukayi suna jimamin abun.
Rafeek yace kada ku damu hakan bazai tab'a shedunmu ba, domin su kawai hanyar muce da zata sa mu gano inda Ogansu yake, kuma insha Allahu za'a kamashi. Suka ce Allah yasa.
**** ****
Wai Raheena me yake damunki ne kwana biyu bana ganin ki cikin walwala? Gyara zama tayi tana fad'in Momy haka kawai nakeji kamar bazan samu Ra'eez ba, ada nafi jin zan mallakesa, amma ayanzu zuciyata ta fara tsinkewa, kina gani yaushe rabon da yazo gidan nan, kowane irin aiki yakeyi tunda har muna gari d'aya ai ya kamata ko so d'aya ne ace yana zuwa wajena, idan bezo bama ai akwai waya, wallahi Momy jikina ya fara sanyi.
Hannu Momy tasa ta goge mata hawaye tana fad'in ki kwantar da hankalin ki, tunda har yace maki aiki yakeyi kiyi masa uzuri, kina ganin Alhaji ma yaushe rabon daya zauna muyi fira dashi, da alama wata shari'a zasuyi mai zafi, kinga duka shekaran jiya suka kammala shari'ar yaron gidan Alhaji M. Sanda, yanzu kuma gobe suna da wata shari'ar, shiyasa nima nayi ma Alhaji uzuri saboda nasan yanda aikinsu yake.
Murmushi Raheena tayi tana fad'in Momy kina ganin da sun kammala shari'ar nan zai dawo gare ni? Sosai kuwa, ai ina ganin suna gama wannan shari'ar za'asa maku rana, shima Alhaji lokacin hankalinsa ya kwanta kinga sai ashirya komai, wad'an nan kayan naki idan bakison su kawai zai siyar dasu.
Raheena tace a'a Momy abarsu tukunna. Momy tace shikenan tashi kije kici abinci.
**** ***
*Safiyar litinin a kotu.*
Ur's.
Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
4⃣7️⃣
*High court Lagos*
Cikar kotu ya bama ma'aikatan wajen mamaki, yanda kasan za'ayi wata shari'ar da bata wuce kwana biyu da faruwa ba, wanda yazo da wuri shi ya samu waje.
Bayan da aka gama shiga Alkali ya shigo, bayan ya zauna kowa ya samu waje ya zauna. Kallon mutanan kotun yake yana so yaga kosu Alhaji Kamal sun zo, aikuwa caraf suka had'a ido, mamakin da yayi yau sun k'ara yawa, hakan yasa jikinsa yayi sanyi, gashi su Alhaji Marusa basu zo ba.
Magatakarda ne ya tashi domin karanto shari'ar da za'a gabatar...... *Kamar yanda aka karanta wannan shari'ar a wancan lokacin kafin a shigo da wadda ta gabaceta, hakan yasa aka d'age wannan shari'ar zuwa yau litinin. A yau litinin 18/12/2019 wannan kotu mai albarka zata saurari k'ararraki guda biyu, ta farko itace wadda zuri'ar Alhaji Sambo Jarmai suka shigar akan mutuwar d'ansu mai suna Naseer Sambo Jarmai, wanda aka tsinci gawarsa a shekaru goma sha biyu da suka wuce a ranar wata juma'a da misalin k'arfe 9:00 na dare a bayan gari, hakan yasa Iyayensa suka shigar da k'ara domin suna buk'atar kotu ta bi masu hakkinsu.*
*Shari'a ta biyu itace wadda Iyalan Malan Sani suka shigar, shari'ace tsohuwa wadda akayita a wannan kotun a shekarar 10/5/2008, inda aka yanke ma Malan Sani hukuncin d'aurin rai da rai a gidan yari, shari'a ce data shafi tsohon ma'aikacin Kwastam Alhaji Hamza Maiwada, wanda ake zargin Malan Sani da kasheshi da kuma yunkurin haikema matarsa a matsayinsa na direbansa, Iyalan Malan Sani sun sake dawo da wannan shari'ar baya saboda suna so asake shari'ar dan basu gamsu da hukuncin da kotu ta yanke a shekarun baya ba.*
Mik'ama Alkali takardun yayi kafin ya koma ya zauna. gaba d'aya kotun ta d'auki hayaniya dan basu san da wata shari'ar ba bayan ta Naseer. Alkali kuwa tamkar wanda aka sama shokin, gaba d'aya jikinsa rawa yakeyi yayin da zufa ta fara keto masa, duk yanda yaso ya daure sai da zufar ta sauko masa afuska tamkar wanda aka zuba ma ruwa, kyalle yasa ya goge fuskarshi kafin ya shanye ruwa kofi d'aya.
Bubbuga tebur Alkali yayi hakan yasa akayi shiru. Jarumtarsa ya tattaro kafin yace lauyen da zai gabatar da shari'a bismilla.
Tashi Ra'eez yayi yana gyara zaman farin glass d'insa, sosai yau yayi kyau sai kace zeyi gasar lauyoyi, gaba d'aya mutanan suka bishi da kallo yanda haibarsa ta fito.
Risnawa yayi yana fad'in ya mai shari'a kamar yanda muka fara karanto k'arar Naseer Sambo Jarmai a wancan satin yanzu ma zamu cigaba, duk da yanzu shari'ar ta zama biyu kuma duk nine zan gabatar dasu, amma ayanzu zamu fara gabatar data Naseer.
Kamar yanda na fad'a an samu gawar Naseer a bayan gari, kuma na gabatar ma kotu da bayanin mutuwarsa da 'yan sanda suka rubuta, inda bincike ya nuna cewar ankashe Naseer ta hanyar shakeshi da akayi har ya mutu, kuma wannan kisa da akayi kisa ne da aka shiryashi domin a toshe wata kafa wacce ake zargin Naseer da kok'arin tona wani b'oyayyen sirri, hakan yasa aka kashe shi wajen b'oye wannan sirri.
A cikin sirrin da Naseer ya d'auka akwai wanda aka nuna anan ranar alhamis data wuce inda ya d'auki hoton Fawwaz alokacin da ya yanki Farouk da wuk'a, acikin abokan Fawwaz wani yaga lokacin da Naseer yake d'aukarsu, hakan yasa suka sanar da Mahaifin Fawwaz. Ina so kotu ta bani dama domin na kira Adnan d'aya daga manyana abokan Fawwaz domin yayi mana bayanin yanda komai ya faru...... Ajiyar zuciya mai k'arfi Alkali ya sauke kafin yace kotu ta baka dama.
Adnan ne ya fito yana takawa da kyar dan har yanzu jikinsa beyi kwari ba.
Ra'eez... Kotu zata so taji sunan ka da kuma alak'ar ka da Fawwaz.
Sunana Adnan kuma Fawwaz abokina ne, domin alokacin da mukayi secondary kowa yasan abotar mu saboda mu ukku ne muke tare, duk inda kaga Fawwaz to dole kagan mu nida marigayi Sufwan, abotar mu ta kai har Iyayen mu sun san mu atare.
Ra'eez... Kotu tana buk'atar kayi mata cikekken bayani akan abinda ka sani na kisan Farouk da kuma abinda ya shigo da Naseer cikin maganar.
Adnan.... E to, kamar yanda kowa ya gani a vedion da aka nuna Fawwaz ya kashe Farouk wanda ba kowa bane ya d'auki wannan vedio sai Naseer, kuma Naseer d'an ajin mu ne muna gaisawa dashi, alokacin da Fawwaz ya kashe Farouk bayan munzo muka iske ta'asar da yayi sai hankalin mu ya tashi, kasancewar mu abokai yasa mukayi kokarin rufama Fawwaz asiri, nine na d'auki wauk'ar na jefata a wani rami da ake tara bola, bayan da muka juyo zamu tafi sai na hangi Naseer yana d'aukar mu, sai dai muna jiyowa shi kuma ya bar wajen da gudu.
Bayan da mukaje muka sanar ma Dadyn Fawwaz sai yace kada mu damu, abinda yake so shine kada mu fad'ama kowa yasan yanda zaiji da komai.
Washe gari dana tambayi Fawwaz ya naji ance a bayan gari aka samu gawar Farouk, shine yake fad'a mani Mahaifinsa ya had'a baki da shugaban makarantar aka fitar da ita.
A ranar da za'a kashe Naseer munzo gidan su Fawwaz sai muka iske Dadynsa da bak'i a waje, bayan mun gaisa sai ya bukaci da mu fad'a masu kwatancen gidansu Naseer kuma mu tura masu hotonshi, haka muka bashi muka tura masu hotonshi.
Washe gari sai mutuwar Naseer naji, tabbas na girgiza da mutuwarshi, kuma har gobe ina ganin laifina, domin nine na fad'a cewar ya d'auki vedio, da ban fad'a ba babu yanda za'ayi asan shine, tun daga lokacin na fara janye masu Fawwaz har Allah yasa muka gama kowa ya kama gabansa, ina mai bama Iyayen Naseer hakuri abisa sakarcin da nayi.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in mungode Adnan zaka iya tafiya. Ya mai shari'a wannan shine Adnan abokin Fawwaz, kuma kowa yaji wanda yasa aka kashe Naseer saboda kawai a b'oye gaskiya ina....
Saurin tashi Brr. Bajinta yayi yana fad'in ya mai shari'a ai wannan shedar baki ce kawai Adnan ya bayar, kuma shi kad'ai ne ya bada sheda wanda kowa yasan cewar mutum d'aya baya sheda, domin za'a iya biyanshi yazo ya b'ata Alhaji M. Sanda.
Miyau Alkali ya had'iye dan ya riga daya sadakas, yasan Brr. Bajinta yana kokarin kare Alhaji M. Sanda ne kawai saboda ba komai ya sani ba. Ruwa yasha kafin yace Brr. Ra'eez kotu tana buk'atar cikakkar sheda domin bazata amshi wannan hujjar da aka bayar ba.
Risnawa Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a zan so kotu ta bani dama domin na nuna mata hujjata ta k'arshe wadda zata tabbatar da abinda Adnan ya fad'a gaskiya ne... Kotu ta baka dama.
Tashi Jabeer yayi ya had'a kayan da za'a kunna. Tunda Jabeer ya tashi Alkali yaji cikinsa ya kad'a, zufa kawai take keto masa ta ko ina, gaba d'aya kyallen dayake goge zufar ya jike. Mutane kuwa mamakin yanda hankalin Alkali ya tashi suke dan zuwa yanzu ya kasa b'oye tashin hankalinsa, zaman kanshi a d'osane yake.
Shiru kotun tayi yayin da fuskokin Alhaji Marusa dana Mr. Kallah suka bayyana, sai gefen fuskar Alhaji Barau saboda shi a gefe yake hakan yasa ba'a d'aukoshi duka ba, idan ba wanda yasanshi ba bazai iya shedashi ba, sai kuma bayan Alhaji M. Sanda danshi ya bama mai d'aukar baya.
Muryoyinsu ne suka fara cika kotun, muryar Alhaji Barau itace ta tonashi, domin yana magana wasu suka fahimci shine, sai kuma lokacin da aka fara ambatar sunanshi, haka suka cigaba da sauraron shirin da suke akan kashe Alhaji Maiwada da kuma yanda zasu sa akashe Naseer.
Babban abinda ya k'ara tabbatar da Alhaji Barau ne awajen alokacin da Alhaji M. Sanda yake fad'in *Brr. Barau idan har kayi mani wannan taimakon ina mai tabbatar maka kaine Alkalin gobe*. Zuwa lokacin mutanan kotun kasa jurewa sukayi dole wajen ya d'auki hayaniya, dama kuma d'aukar tazo k'arshe. Hannu Jabeer yasa ya kashe.
Jiyowar da Ra'eez zeyi sai dai yaga wayam a kujerar Alkali domin ya sulale ta kofar da take kusa dashi🤣. Ra'eez besan lokacin da dariya ta kwace masa ba, hannu yasa ya toshe bakinsa yana girgiza kai, ai da mutane suka fahimci abinda yake faruwa sai kotu ta hargitse da dariya tare da surutu.
Duk yanda aka so mutane suyi shiru abun ya faskara, dole sai Magatakarda ne ya hau sama ya buga tebur hakan yasa kowa yayi shiru ya juyo sun d'auka Alkali ne ya dawo. 'Daya daga cikin manyan ma'aikatan kotun ne ya mike yana fad'in an d'age wannan shari'a zuwa lokacin da za'a sanar.
Haka kowa ya fito daga kotun yana fad'ar yanda akayi, 'Yan jarida kuwa sun cika wajen kowa yana son yaji yanda za'ayi, kamar ance su kalli gefe sai ganin 'Yan sanda sukayi sun saka Alhaji Barau a tsakiya suna shirin barin kotun dashi, ai da gudu 'Yan Jarida sukayi wajen, sai dai kafin su kai sai kurar motar suka iske.
Abinda ya faru shine, tun alokacin da hankulan mutane suka raja'a wajen kallon abinda aka kunna hankalin Alkali ya tashi musamman da yaga an hasko hotonsu, tabbas ya tuna da wannan vedion, domin irinshi ne suka kalla a wayar Naseer kuma anan suka konata, ganin beda wata mafita gashi su Mr. Kallah basa wajen hakan yasa ya fakaici idanuwan mutane ya sulale.
Sai dai yana fita su Inspector Hamza suka tareshi, domin sun shiryama hakan, gaba d'aya jikinsa ya d'auki rawa a lokacin da suka kamashi, rokonsu ya farayi akan su barshi ya tafi baya son yaji wannan kunyar, har zasu wuce dashi Hamza yace su jira mutane su fito dan yafison kowa yasan an kamashi. Hakan yasa suka tsaya har sai da aka fara fitowa sannan suka taho dashi.
Tsaye su Alhaji Kamal suke tare da sauran mutanan da yazo dasu. 'Daya daga cikinsu yace lallai Alhaji Kamal maganar ka gaskiya ce shiyasa kace muzo, wallahi na d'auka ba wata babbar shari'a bace, amma meyasa baka fad'a mana komai ba kafin muzo dan nasan kasan da wannan vedion?
Murmushi Alhaji Kamal yayi yana fad'in nafiso ku gani da idon ku. Mutumin yace fad'i gaskiya dai Babban Alkali, kawai kace kasan halin zuciya, kada ka nuna mana asamu wani ya sanar dasu Alhaji Barau kafin muzo.
Alhaji Kamal yace kunga laifi na? Gaba d'aya sukace a'a, ai ana son sirri, kuma hakan da kayi yayi dai-dai, dan haka sai asanar da manyan mu saboda wannan babban abu ne dole sai anyi zama.
Alhaji Kamal yace tun kafin muzo na sanar da Chief Judge, duk da bansanar dashi komai ba amma na fad'a masa ana zargin babban Alkalin kotun nan tare da wasu manya da aikata babban laifi, kuma na sanar dashi za'a gabatar da shari'ar a yau wanda acikinta ne za'a gano komai, kunsa dai mutum baya yanke ma kanshi hukunci, hakan yasa shima Alkalin ya gudu tun kafin a sauke shi, dan haka nasan zuwa yanzu sun kusa isowa dole muyi zama zuwa anjima dan bana so shari'ar nan ta wuce gobe.
***
Wallahi Ra'eez kai mugune, ashe dama ka iya dariyar mugunta, yanzu agaban mutane kasa dariya sai ka tona kan ka. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in ayanzu bana tsoron kowa yasan waye ni, domin komai yazo k'arshe, kuma tsakani da Allah bazan iya rike dariyata ba alokacin shiyasa nayi abuna domin Alhaji Barau yayi abun kunya Alkali da guduwa.
Dariya sukasa gaba d'ayansu. Jabeer yace Allah yaso Raheena da Momynta basa nan da Allah kad'ai yasan halin da zasu tsinci kansu. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in wallahi Jabeer kana son Raheena kawai dai kana b'oyewa ne saboda ni, kuma kasan dai ni ba aurenta zanyi ba.
Tsaki Jabeer yayi yana fad'in wai kai zuciyata kashiga da zaka rik'a fad'ar haka, nifa ba sonta nake ba kawai tausayinta nakeyi. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in kai ma Ra'eez da sa ido kake, tun yaushe Jabeer yake fad'a maka ba sonta yake ba kawai tausayinta yakeyi abarshi ahaka.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana dariya yace an barshi ahaka Yaya, Allah ya kawo masa mai sonshi. Tsaki Jabeer yayi yana fad'in d'ansa ido kawai.
Ra'eez zeyi magana wata matashiyar yarinya tayi masu sallama. Amsawa sukayi suna kallonta yayin da Jabeer ya juya baya yana waya. Gaishe su tayi tana fad'in dan Allah Yaya Sameer nake nema munyi waya yace yana kotu kuma nashigo wayarsa bata shiga.
Ra'eez yace wane Sameer fa? Tace Yayan Adnan wanda yazo bada sheda. Ra'eez yace oho, K'anwarsu ce ke? Kai ta d'aga tana murmushi. Ra'eez yace kuma bamu sanki ba ya sunan ki? *Husnah!* ta bashi amsa.
Ra'eez yace amma dai ba'a nan kike zaune ba ko? Murmushi tayi tace sati na d'aya dana dawo na kammala karatuna a A.b.u zariya. Ra'eez yace masha Allah, na tayaki murna, bara na kira maki shi yanzu na ganshi kila koya zagaya.
Kafin ya bar wajen saiga Sameer ya fito daga baya da alama band'aki yaje. Murmushi ya saki yana fad'in Husna ashe kin iso? Kai ta d'aga tana fad'in na kira ka bata shiga ba. Sameer yace kila network ne.
Juyowa Jabeer yayi yana maida wayar aljihu yace mu tafi idan ka gama surutun naka. Dariya Ra'eez yayi yana fad'in ai fa yau nashiga ukku, sai fushi kake kamar kaine Alhaji Barau.
Dariya sukasa gaba d'ayansu banda Husnah data shagala wajen kallon Jabeer😉. Rafeek yace wallahi Jabeer sai kayi da gaske dan Ra'eez yaga wajen baccin ka.
Harara ya buga ma Ra'eez yana fad'in ka barni dashi Yaya nasan tsiyar da zan masa. Kamoshi Ra'eez yayi yana fad'in haba d'an uwana na kaina, yi hakuri muje, kasan akwai sauran abubuwa agaban mu.
Sameer yace bara na aje Husna gida zanzo. Rafeek yace shikenan nima ofis zan wuce dan dole ayau mu saki wannan labarin, gidan Tv ma nasan zasu haska dan nasan dole akwai wad'an da suka d'auka kasan mutane ba'a iya masu ko yaya ne sai an samu cikin 'Yan jarida sun d'auka.
Sameer yace shikenan Husna muje. Jin shiru yasa suka juyo suna kallonta, ita ko hankalinta yana wajen Jabeer da yayi gaba zuwa wajen motarsu. Hannu Sameer yasa ya mintsinota da sauri ta juyo tana sosa kai.
Ra'eez yace K'anwarmu ki gaida gida ko. Murmushi tayi tana jinjina kai. Gaba Ra'eez yayi yana fad'in Yaya sai munyi waya. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in tunda kana sauri kayi d'aukar magana ba.
Zama cikin motar yayi yana fad'in wai saurin me kake ko sallama dasu Husna bakayi ba bayan kuma kayi kasuwa. Harara ya wurga mashi yana fad'in wallahi Ra'eez kashiga hankalin ka dani, wacece kuma wata Husnah? Kafad'a Ra'eez ya d'age yana fad'in oho, lokacin da ka gama wayar wayace baka tsaida hankalin ka har ka ganta ba.
Murmushi Jabeer yayi yana girgiza kai yace naga alama yau ahaka zaka k'are wajen tsokana, ina su Ummu ko sun wuce? Ra'eez yace suna fitowa Abbah ya tafi dasu kasan kotun ta cika. Jabeer yace ina muka nufa? Ra'eez yace muyi gida dan nasan anjima Kawu Kamal zai nememu dan yace akwai zaman da zasuyi gara muje mu huta.
**** ****
Zaune suke a gidan Alhaji Marusa su ukku suna jiran tsammani, dan tunda sukasan an shiga kotu suka had'u a gidan Alhaji Marusa dan Alhaji M. Sanda ya fad'ama Alhaji Barau da zarar yaga za'a gabatar da shedar data tabbatar suna dasa hannu a kisan Naseer da Alhaji Maiwada yayi kokarin fitowa yazo su gudu tun kafin a kamasu. Sai dai basu san jiran gawar shanu suke ba.
Gyara zama Mr. Kallah yayi yana fad'in nifa hankalina ya kasa kwanciya, tun d'azu nake kiran Brr. Bajinta naji ko an gano wani abu amma wayarsa ma akashe take, da farko tana shiga be d'auka ba, nasan lokacin ko yana cikin kotun, amma yanzu a kashe ma take. (Abinda basu sani ba Brr. Bajinta ma yayi takanshi, dan tunda ya tabbatar da mugayen halinsu ya tsorata, danshi duk tarayyarsu dashi iyaka su sashi yayi shari'ar karya su biyashi amma betab'a sanin su d'in makisa bane, hakan yasa asiri yana tonuwa ya kashe wayarsa dan yace bazai fada masu ba kada su gudu, shiyasa ma ya sanar ma Hamza inda suke.)
Alhaji Marusa yace nima hankalina ya fara tashi, gashi na kira wayar Lucky itama akashe, da alama shima yayi takanshi, ina ganin fa lokaci yayi da kowa zai nemi hanyar tsira, kawai ku tashi mubar garin nan kafin komai ya kwab'e.
Mr. Kallah yace Alhaji Barau fa? Alhaji Marusa yace kai kasanshi, amma wallahi bazan sake mintuna goma awajen nan ba, idan kai zaka tsayashi to ni nayi nan.
Tashi Alhaj M. Sanda yayi yana fad'in jirani Alhaji Marusa. Dole Mr. Kallah ya mik'e jiki a sanyaye yabi bayansu. Suna fitowa suka iske 'yan sanda suna jiransu, ai gaba d'aya sai hankalinsu ya tashi, nan fa suka fara kokarin tserewa, da sauri aka cafkesu akasa mota yayin da 'Yan jaridan da Hamza ya taho dasu suke ta d'aukarsu.
Yayi haka ne domin a watsasu ayau saboda kowa yasan halin da ake ciki, haka suka tafi dasu sai zare ido suke a mota.
Ganin haka gaba d'aya ma'aikatan gidan Alhaji Marusa suka fito domin suyi takansu, sai dai kowa sai da ya kwashi rabonshi kafin yayi gaba.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
4⃣8️⃣
Gaba d'aya gari ya hargitse da labarin abinda ya faru, yayin da 'yan jarida suke ta kok'arin had'a kan labarin da zasu gabatar.
Da misalin k'arfe hud'u su Alhaji Kamal suka shiga taron gaggawa. Manya sun fusata akan wannan abun kunyar da aka jawo ma kungiyar su, dan wannan abun ba k'aramun tab'a Kadar su zeyi ba domin sun san dole sai duniya taji wannan abu. Haka suka gama tattaunawa yayin da suka tsaida wanda zaiyi shari'ar a gobe.
Haka Alhaji Kamal ya sake kunna masu vedion kowa ya gani, tabbas sunji kunyar wannan abu, babu abinda yafi ciwo irin na Malan Sani, shekaru da yawa an kulleshi ba akan hakkinsa ba. Da haka taron ya tashi.
*** ****
Rafeek agaskiya yanzu kam naji dad'in wannan shari'ar daka tado, koba komai silar shari'ar Naseer ta jawo za'a tona asirin mutane da yawa, kamar yanda mutane suka aminta da wannan kotu suna fad'in irin adalcinta ashe dama a cikin duhu muke, Allah ya k'ara tona asirin munafukai.
Rafeek yace amin Baffa, ai yau jinake kamar nayi kuka saboda farin ciki, hakika Allah yana son bayinsa, kuma shi maji rokone, insha Allahu zuwa gobe kowa zaisan matsayinsa.
Ummansu tace nikam ko ba'ayi komai ba zuciyata ta wanke, koba komai duniya tasan waye ya kashe mani Naseer, kuma sun kunyata sai fatan Allah ya kara tona asirinsu. Rafeek yace amin Umma, bara na wuce dama ina wajen aiki naga kiran ku. Baffa yace Allah ya tsare ka. Yace amin.
**** ****
Ya Allah wannan wace irin bak'ar rana ce haka, yanzu Alhaji ne 'yan sanda suka kama har wajen aikinsa saboda tozarci, ina zansa kaina yau, da wane ido zan kalli K'awayena da sauran mutane? Zubewa Raheena tayi jikinta tana kuka.
Dafata Momy tayi tana fad'in wallahi dole kiyi kuka Raheena, mu kam Alhaji ya gama cutar mu, taya zamu iya rayuwa cikin wannan tashin hankalin, ashe dama halin da yake aikatawa kenan ab'oye bamu sani ba? Duk tarin dukiyar nan daya tara mana ta hanyar haram ya tara ta? Kalli wannan uban gida da muke ciki, haba ashe shiyasa Alhaji Marusa ya sayar masa da gidan ashe duk jirgi d'aya ne ya d'ebosu, yanzu gashinan sun kaishi sun baro, meyafi wannan kunya ace kana zaune saman kujera kana shirin yankema wani hukunci sai kuma a nunoka kana cikin masu laifin.
Tashi Raheena tayi tana fad'in wallahi Momy nayi dana sanin shiga yanar gizo ayau, domin ina hawa nayi bakin gani, a group d'in da nake kawai naga an turo hoton Dady a kotu hada vedion shi lokacin daya sulale a kotun, dan bala'i hatta da shedar da aka kunna akotu wallahi an samu wad'an da suka d'auketa, ina hawa face book ma abinda nagani kenan, duk wata kafa ta yanar gizo idan kika shiga maganar su Dady akeyi.
Goge ido Momy tayi tana fad'in bamu da bakin magana kam, abinda nakeso da ke kawai ki kashe wayarki, idan da hali ma kawai ki kulle account d'inki sannan ki karya layin ki hakan zai fi maki kwanciyar hankali, idan yaso lambobin da kike so ki barsu akan wayar dan nima haka zanyi wallahi Raheena bazan iya wannan abun kunyar ba, dole mubar garin nan, gara na koma asalina dama nayi gini na a kano ina shirin zuba 'yan haya wallahi na fasa garin zamu bari.
Raheena tace ya zamuyi da wannan gidan kuma? Waro ido Momy tayi tana fad'in ke yanzu har maganar wata kadara ta Alhaji kikeyi, to ina tabbatar maki sai kotu ta kwace komai nashi dan sai ya biya diyar mutanan da ya kashe, kayan d'akin ki ma zansa azo goben nan a tafi dasu kano, kije ki fara had'a kaya ki da duk wasu abubuwa masu muhimmanci dan wallahi idan masu bincike sukazo bazasu bari mu d'auki komai ba.
Kuka Raheena tasa tana fad'in shikenan yanzu kam nasan Ra'eez yafi k'arfina, dan ko rana aka samana sai ya fasa dan yanzu Dady yayi mana bakin fenti. Momy tace ki kwantar da hankalin ki sai kiga kuma yaji tausayinki tunda yasan ba laifinki bane, dole muje kotu domin ayi komai agaban mu, tashi ki kunna mana Tv nasan yanzu zasu nuna komai.
Aikuwa Raheena tana kunnawa sai ga masu labarin k'arfe takwas na dare. Kowace tasha ka kunna ko gidan radio duk maganar d'aya ce, nuno su Alhaji Marusa ne ya k'ara d'aga masu hankali, shikenan yanzu an had'a kan masu laifi dole a yanke hukunci.
Daga k'arshen labaran aka tabbatar da gobe talata k'arfe goma na safe za'a zartar da hukunci a babbar kotu. Kashewa Momy tayi tana sakin kuka. Masu aikin gidan ne suka shigo jiki asanyaye suna masu jaje.
Tashi Momy tayi tana fad'in bazan bari a cuce ku ba, domin nasan gidan nan ya kusa haramta agaremu, dan haka zan sallame ku zuwa gobe kowa ya tafi ina rokon ku daku yafe mana, bara naje d'akin Alhaji dole nayi maku sallama mai tsoka.
Farin ciki suka kamayi jin abinda Momy tace. Fitowa tayi da wata k'atuwar jaka wadda kud'i ne kawai aciki, haka tasa suka d'auko bakar leda ta bama kowa kud'i masu yawa, kayan Alhaji ta d'auko duk ta raba ma mazan masu aikin, sannan ta d'ebo wasu daga cikin nata dana Raheena ta bama matan, haka sukayi ta godiya kowa ya nufi wajen kwanansa kafin gobe.
Ciki suka shiga suka fara had'a kaya yayin da tayima wani d'an uwanta waya da yake Lagos akan ya taho da motar d'aukar kaya tunda asubar fari zai kai mata kano kafin a kammala shari'ar sai su tafi.
**** ***
Hawaye ne kawai yake zubo ma Ammi bayan data gama kallon labarai, mai aikinta da take gefenta sai hakuri take bata. Ammi tace dole nayi kuka Inno, Alhaji ya gama zalunta ta, ya b'ata mani tarbiyar yarona, ya lalata mani mahaifa, gashi daga k'arshe ya sani jin kunyar duniya, na farko an yanke ma Fawwaz hukuncin kisa, na biyu an kama Alhaji shima nasan hukuncin kisa ne domin rayuka ya kashe, shikenan na tashi a babu, wannan gidan dole na barshi koda bazai shiga cikin diyar da zai biya ba wallahi bazan zauna aciki ba domin komai na ciki haram ne, sisinsa bazan d'auka ba, haka zan tafi garin mu gara idan naje Iyayena su siya mani sutura da kud'insu amma babu abinda zan iya cigaba da amfani dashi domin duk haramun ne.
Inno tace kiyi hakuri Hajiya ai bakisan haramun bane sai yanzu kinga duk abinda kike dashi ya halatta agareki sai idan ya sake baki wani abun ne.
Murmushin takaici Ammi tayi tana fad'in Inno bakinsa girman haram ba, matuk'ar ka kasance kana cin haram kuma kasan haram ne wallahi Allah bazai barka ba agobe kiyama, tabbas ada bansan bakin halin Alhaji ba, nasan dai ma'aikaci ne kuma albashinsa muke ci, amma zuwa yanzu na fahimci ya cakud'a kud'insa da haram domin harkar shigo da haramtattun kaya sukeyi, ban tab'a sanin haka ba sai jiya da nayi bincike a d'akinsa naga wasu takardu, kinga kuwa idan har nacigaba da amfani da kayanshi nima nashiga layin halaka, dan haka ki barni, idan kina son kayana gasu can kije ki had'a dan sallamarki zanyi, sauran kud'ina na banki ma asusun marayu zan kaisu, idan baki son kayan zan mik'asu gidan marayu sadaka.
Inno tace tunda sadaka kika bani ai ba haram bane zan d'ebi wasu sai akai sauran gidan marayu bazan had'e duka ba, gaskiya wannan abu beyi dad'i ba, amma ai zakije kotun gobe ko? Ammi tace badan inaso na mik'a mukullin gidan nan a gareshi ba kuma ya furta mani saki da babu abinda zai sa rana ta fito ta sameni a Lagos, amma dole naje nayi sallama da Fawwaz kuma na amshi sakina.
Inno tace gaskiya zanji babu dad'i, amma Allah yasa haka yafi alkhairi, yama sunan garin ku? Ammi tace Sokoto. Inno tace ikon Allah ashe fa kin tab'a fad'amin wallahi na manta, ai gaskiya garin ku akwai nisa, amma idan da rai wata rana zaki ganni. Ammi tace Allah yasa, kira mani masu gadi su duka.
*** ****
Umar yanzu ya zamuyi, ni wallahi na manta da wannan maganar, tunda na haye saman kujerar Oga shikenan na manta dashi da abubuwan da mukayi, sai cikin satin nan Alhaji Barau yake fad'a mani an fara bincike akan shari'ar da akayi shekarun baya.
Miyau Umar ya had'iye yana fad'in Adebayo wannan shi ake kira ga k'oshi ga kwanan yunwa, muna farin ciki shekaru sun ja an manta da komai ashe abu be wuce ba, kana kallon dai yanda aka kama Alkali a kotu, su Alhaji kuwa har gida aka bisu, taya kake tunanin abun bazai zo kan mu ba, koda ba'a kamma mu yanzu ba idan akaje shari'a gobe dole bincike yazo kan mu.
Adebayo yace wallahi tsoro nakeji, da nasan da wannan abun bazan zo aiki yau ba, gashi aiki ya rik'emu mun kai har dare kada mu fita akama mu, da ace ina da mai a motata daga nan hanyar garin mu zan nemo gara na kwana a ahanya tunda ATM d'ina yana mota bani da matsala, to yanzu idan na tafi an kulle gidan Mai sai na masu jarka kuma ina tsoron na siya da yawa ya bani matsala.
Umar yace kasan abinda za'ayi? Tunda sai gobe k'arfe goma za'a shiga kotu kuma sai an fara shari'a sannan bincike yazo kanmu kawai yau mu kwana cikin shiri, gobe tunda asuba kowa ya kama gabanshi, lokacin da za'a neme mu nasan munyi nisa, dan haka kawai mu tafi. Adebayo yace haka za'ayi Umar kulle ofis d'in mu tafi.
Cak suka tsaya ganin 'yan sanda a gabansu. Tsoro ne ya kamasu gaba d'aya, babu b'ata lokaci suka kamasu suka tafi, motarsu ma sai wasu 'yan sandan ne suka tukasu.
*** ***
Kafin gari ya waye sai da su Hamza suka had'a kan duk wasu masu laifi, sai dai kowa da wajenshi babu wanda yasan an kamo wani sai wad'an da aka nuna a tv, hatta dasu Kwamishna da Dr Aliyu Sani duk an kamasu, sai dai shi kwamishna basu kawoshi ofishinsu ba wani waje suka ajeshi saboda girmamawa.
**** ****
*Tuesday 19/12/2019*
*High court Lagos*
Fad'in cikar da kotun tayi ba abu bane me yuwuwa, domin duk wanda yasan labarin wannan shari'a yasan dole tayi mutane, ko yawan masu d'aukar rahoto ya isa ya cika rabin kotun.
Gaba d'aya ma'aikatan kotun k'arfe bakwai suka halarci kotu saboda dole akwai tsare-tsare, manyan jami'an tsaro ne a harabar kotun su duka suna d'auke da manyan makamai, duk wanda zai shiga kotun dole sai an bincikeshi da abun duba mutane, hanyar maza daban ta mata da ban, sosai abun ya k'ayatar domin sun shirya ma shari'ar saboda sun san ana iya samun wani tashin hankali musamman da shari'ar ta kasance ta manyan mutane.
Lokacin da kotun ta cika dole sai hakuri sauran mutanan sukayi domin jami'an tsaro sun tare hanyar shiga sai dai masu son jin kwakwaf suka tsaya a harabar kotun.
Masu laifi dama da wuri aka kawosu kotun kowa da inda aka ajeshi, kana shiga cikin kotun zaka iske Alkalai ukku zaune asama sai b'angare guda na manyan mutane, yayin da d'ayan b'angaren lauyoyi suke zaune, sai wajen da su Magatakarda suke a zaune, daga wajen zaman mutane kuma duk akwai jami'ai ko wace hanya suna tsaro.
Tsit kake jin kotun dan kowa yasan yau babu wasa, iya mutanan da suke zaune agaba kad'ai ya isa yasa mutum ya natsu, ga kuma jami'ai suna zagaye da bindigu.
Bayan da kowa ya natsu aka umarci da ashigo dasu Alhaji Barau. Idanuwa kawai mutane suka zuba dan gangar jikinsu ta kasa motsi bare ta jawo hayaniya gudun kada suma suyi laifi.
Gaba d'ayansu kawunansu a k'asa suka shigo kotun, Alhaji Barau da aka kamashi yana sanye da kayan aiki zuwa yanzu babu su ajikinshi dan an bashi wata jallabiya yasaka. Haka suka jeru a gefe suna sunnar da kai.
Tashi Magatakarda yayi domin ya karanto shari'ar....
*A yau talata 19/12/2019 wannan kotu mai albarka zata cigaba da sauraron shari'ar da aka fara jiya litinin 18/12/2019, an tsaya a inda Brr. Ra'eez ya gabatar da shedar data tabbatar da wad'an da suka had'a baki wajen kashe Naseer Sambo Jarmai.*
*Sai shari'a ta biyu itace ta Iyalan Malan Sani, inda suke rokon wannan kotu data sake shari'ar da aka gabatar shekaru sha biyu da suka wuce akan mutuwar tsohon shugaban kwastam Alhaji Hamza Maiwada a wannan kotun domin an samu wasu manyan shedu da zasu tabbatar ma kotu ba Malan Sani bane ya aikata laifin da aka yanke masa hukunci akai.*
Risnawa yayi ya mik'ama d'aya daga cikin Alkalan da suke zaune. Bayan da ya gama dubawa ya mik'ama sauran. Na tsakiyar daya kasance shugaba shine ya bama Ra'eez izinin ya cigaba da gabatar da shari'a a inda ya tsaya jiya.
Tashi Ra'eez yayi yana risnawa, ganin bakin fuska yasa ya fara da gabatar da kanshi. Gyara riga yayi yana fad'in ya Mai shari'a ni sunana *BARRISTER RA'EEZ HAMZA MAIWADA, 'DAH GA MARIGAYI SHUGABAN KWASTAM NA LAGOS WATO ALHAJI HAMZA MAIWADA.*
Nine wanda yake kare wad'an da suke k'arar shari'a ta farko data biyu.
Gaba d'ayansu suka d'ago cikin firgici suna kallon Ra'eez, Alhaji Barau yafi kowa girgiza da abinda kunnuwanshi sukaji, tabbas sai yanzu ya gama gano dawa Ra'eez yake kama. Runtse ido yayi yana jin wani irin tashin hankali.
Mutane kuwa duk yanda suka natsu jin abinda Ra'eez ya fad'a dole tasa aka fara kus-kus, domin abun ya basu mamaki.
Raheena da Momy kuwa suman zaune sukayi. Runtse ido Raheena tayi hawaye suna zubo mata, ayanzu kam tasan Ra'eez ya girmema tunanin ta, dama fansa yazo d'auka kenan. Saman cinyar Momy ta kwanta tana kuka. Bubbuga teburin da akayi ne yasa kowa ya shiga hankalinsa.
Gyara tsayuwa Ra'eez yayi yana fad'in, kamar yanda aka gabatar da shedar vedion da aka shirya yanda za'a kashe Naseer a jiya nasan wannan shedar ta tabbatar da wad'an da suka shirya kashe Naseer domin fuskokinsu sun fito yayin da akaji muryoyinsu suna ambatar sunan juna.
Ina so kotu ta bani dama domin na yima mutanan da suke gabanta tambayoyi.... Kotu ta baka dama.
Matsowa yayi kusa da masu laifin yana sakin murmushi.
Alhaji M. Sanda zan fara ta kan ka, duk da fuskar ka bata bayyana a cikin vedion ba amma muryarka ta sheda kai ne, sannan mutane biyu sun tabbatar da cewar kai ne ka bada umarnin aka kashe Naseer, domin duk sauran goya maka baya kawai sukayi, kotu zataso taji daga bakin ka yanda komai ya kasance.
Alhaji M. Sanda... Kanshi a k'asa yace maganar gaskiya duk abinda akaji a ciki haka yake, sai dai kuma mun fad'a ne kawai amma ba mune muka aikata ba, domin mun aje akan zamusa ayi sai kuma aka samu wani ya rigamu aikatawa, dan haka ni bansa a kashe kowa ba.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in Alhaji Barau me zaka iya cewa agame da wannan vedion?
Alhaji Barau... Haka maganar take, kamar yanda Alhaji M. Sanda ya fad'a tabbas mun shirya yanda za'a kashe Naseer saboda a b'oye abinda Fawwaz ya aikata sai kuma wani ya riga mu.
Murmushi Ra'eez yayi kafin ya matsa gaba ya tambayi Alhaji Marusa da Mr. Kallah, sai dai duk amsar d'ayace. Murmushi yayi dama yasan za'ayi haka shi kuma yafiso su k'aryata kafin ya tabbatar masu.
Juyowa yayi yana fad'in ya mai shari'a inaso kotu ta bani dama domin na kira mutumin da akayi hayarshi ya gabatar da wannan kisa.... Kotu ta baka dama.
Kallon k'ofa kawai suke yayin da zufa ta fara keto masu, ji suke kamar su nutse, duk da basu san wanda zai shigo ba amma sun tsorata da murmushin kan fuskar Ra'eez.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
4⃣9⃣
Hannu Mr. Kallah ya d'ora akai ganin anshigo da Lucky, bayansa kuma Dr. Aliyu Sani ne sai Kwamishna Bello kabir wanda duk kunya ta hanashi kallon kowa. Mamaki ne ya cika mutane ganin Kwamishnan 'yan sanda a jerin masu laifi, sai wad'an da suka san Dr. Aliyu suma sunyi mamakin ganinshi.
Lucky ne ya fara fitowa zuwa wajen da ake tsayawa. Matsowa Ra'eez yayi yana fad'in kotu zata so taji sunanka da kuma san'ar ka.
Sunana Adekulle Isnewa, amma anfi kirana da Lucky, sana'ata itace sata sai kuma ana d'aukata nayi aiki a biyani.
Ra'eez... Kamar wane irin aiki kenan?
Lucky... Kamar idan wani yana son ajama wani kunne ko kuma a shekeshi to ina irin wannan aikin a biya ni.
Ra'eez... Shin Lucky ko kasan wad'an nan mutanan?
Lucky... Kallonsu yayi yana sakin murmushi, juyowa yayi yana fad'in sosai kuwa, domin tunda nake harka da mutane ban tab'a harkar da nake jin dad'inta ba kamar harka dasu, zan iya cewa sune Ubayen gidana domin mun dad'e atare musamman Alhaji Marusa dan shine ya nuna masu ni.
Ra'eez... Ko zaka iya fad'ama kotu irin aiyukan da suka saka kayi masu.
Lucky... Gaskiya sun sani aiyuka da yawa, wasu zan iya tunawa wasu kuma bazan iya tunawa ba, dansu basa jin tsoron a kashe kowa matuk'ar zasu samu biyan buk'ata, hatta da junansu ma basu bari ba, domin ko kwanakin baya Alhaji Barau da Mr. Kallah sun sani nayi masu wani aiki akan Alhaji Marusa, duk da shi na sani amma silar kashe mun aboki da yayi yasa na amshi aikinsu.
Ba wani aiki bane sun sakani na kwace kayanshi da yayi odar su masu matuk'ar tsada, sannan na kashe matuk'an motar, ni kuma aikin da nayi mashi na cinna ma babban ma'ajiyarsa wuta kuma duk sun san da haka, wanda silar haka har ya kamu da ciwo.
Dalilin da yasa na fara baka wannan labarin saboda kasan cewar suma zaluntar junansu sukeyi, sai kuma kashe yarana da aka kama wancan satin da nayi a ofishin 'yan sanda kuma na fad'a masu duk sun san da haka.
Wani irin kallon Mamaki Alhaji Marusa yake bin Alhaji Barau da Mr. Kallah dashi, gaba d'aya takaicinsu ya rufeshi, jiyayi beda sauran wata dabara garama ya amsa laifinsa kowa ya rasa.
Ra'eez... To Lucky kotu tana sauraron ka.
Lucky... Acikin aikin da suka saka ni wanda bazan manta ba shine kashe tsohon shugaban Kwastam, sai kuma Naseer wanda ake magana amma shi ba nine na kashe shi ba abokina Peter ne ya kashe shi domin aranar aiki biyu mukayi, mune mukaje har gidan Alhaji Maiwada muka bugi matarsa yayin da muka shak'ama direbansa abun kauda hankali sannan muka saka hannun Matar Alhaji ta yakushi wuyanshi, bayan daya koma gidansa nine na kaima Inspector Bello wato Kwamishnan 'yansan na yanzu jakar da aka samu a gidan Malan Sani had'e da allurar da mukayi ma Alhaji, shine ya sakata a d'akin Malan Sani, sannan Dr. Aliyu shine aka had'a baki dashi wajen tabbatar da Malan Sani akan zargin da ake masa.
Ra'eez... Hannu yasa a aljihu ya ciro kyalle ya goge kwallar data zubo masa, gyara glass d'inshi yayi yana fad'in bayan wannan sai wane aiki kayi masu?
Lucky.... Labarin yanda suka saka kayan Alhaji Marusa a gidan Alhaji Maiwada ya basu wanda akayi shari'a har kotu tasa ya biya Alhaji Marusa makudan kud'i wanda silar haka ya siyar da gidanshi, duk abubuwan dasu Alhaji Marusa suka k'ulla sai da Lucky ya fad'a.
Gaba d'aya kotun tayi shiru ana sauraronshi har ya kammala bada labarin.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in zaka iya tafiya. Inaso kotu ta bani dama domin nayima Kwamishna da Dr. Aliyu tambaya... Kotu ta baka dama.
Dr. Aliyu kaji bayanin da Lucky yayi, shin ko kana da ja akan abinda ya fad'a? Duk'ar da kai Dr yayi dan beda ta cewa, a hankali ya d'ago kai yana fad'in wallahi tsautsayi ne yasa na amshi tayinsu ba halina bane.
Kallon Kwamishna Ra'eez yayi yana fad'in 'Yallab'ai akwai abinda Lucky ya fad'a wanda ba haka yake ba? Sunkuyar da kai yayi yana goge zufar data zubo masa.
Hannu Ra'eez ya tafa yana fad'in ya mai shari'a inaso kotu ta bani dama domin na gabatar da wasu shedu... Kotu ta baka dama.
Flash d'in da suka samu a d'akin Abbu yasa Jabeer ya kunna.... Anan kowa yaga yanda su Alhaji Marusa suka shirya duk wani tuggu akan Alhaji Maiwada, da yanda ake shigo da haramtattun kaya da yanda su Adebayo da Umar suke kulla nasu sharrin har zuwa lokacin da aka cire abinda Malan Hassan yasa a gidan Alhaji Marusa.
Kashewa yayi yana fad'in inaso abani dama domin nayima d'aya daga cikin mutanan da sukayi wannan aikin.... Kotu ta baka dama.
Cike da mamaki suke kallon Abubukar wanda ya zama babban mutum, haka ya tako har gaban kotu.
Ra'eez... Kotu zataso taji sunanka da kuma alak'ar ka da shugaban Kwastam.
Sunana Abubakar Sani, kuma ina d'aya daga cikin ma'aikatan da sukayi aiki tare da Marigayi Alhaji Maiwada, hakika shi mutum ne mai son rike gaskiya da amana, be yarda da cin hanci ko zalunci ba, zuwansa garin nan mun samu cigaba, sai dai wannan gaskiyar tashi itace ta jawo ajalinsa, domin duk abinda aka gani ayanzu haka yake, wasuma ba'a d'aukesu ba, amma tabbas Alhaji Marusa shine yasa aka kashe Malan Hassan tsohon maigadinsa kuma yasa aka rufeshi ba tare da iyalinsa sun sani ba, haka yasa aka wahalar damu nida abokin aikina shima ya mutu Moses saboda muna bayan gaskiya, sannan Mr. Kallah yayi mana canjin wajen aiki kuma suka tsorata mu da kada mu sake dawowa garin nan.
Tunda na bar garin nan ban sake dawowa ba, sai dai mutuwar Malan Hassan ta tsaya mani arai, domin mune silar jefashi cikin halin daya shiga, hakan yasa na kasa daurewa domin anbar Iyalinsa cikin tashin hankali saboda basu san halin da yake ciki ba, haka na dawo garin nan na fad'a masu abinda ya faru.
Sanin bazasu iya komai ba yasa suka sai da d'an gidan da suke ciki suka tattara suka koma garinsu. Tun daga lokacin bansake zuwa garin nan ba, bayan wani lokaci naji aikin kwastam ya faitar mun shine na ajeshi.
Ra'eez... Jinjina kai yayi yana fad'in mungode Alhaji zaka iya tafiya. Inaso kotu ta bani dama domin na gabatar da Matar Alhaji Maiwada... Kotu ta baka dama.
Fitowa Ummu tayi tana share hawayen da suke fuskarta, tabbas yau mutuwar Abbu ta dawo mata sabuwa. Da kallo su Alhaji Barau suka bita kowa jikinsa yana k'ara sanyi.
Ra'eez... Kotu zata so taji sunanki da kuma abinda kika sani akan sharrin da akayima Malan Sani.
Sunana Bilkisu kuma nice matar Alhaji Maiwada, tabbas abinda akace Malan Sani ya aikata k'arya ne, domin aranar yashigo yana kuka, bayan na tambayesa abinda ya faru shine kafin ya fad'a mutanan suka shigo, nice nayi yunkurin bugama wani flask sai shi kuma ya kwad'a mani sanda anan na zube, amma tabbas Malan Sani be aikata abinda aka fad'a ba.
Girgiza kai Ra'eez yayi, duk yanda yaso b'oye hawayenshi sai da suka zubo, gogewa yayi yana fad'in zaki iya tafiya.
Cikin d'aga murya Alhaji Marusa yace ya mai shari'a duk abinda aka gabatar agaban kotu gaskiya ne, gaba d'ayan mu muna dasa hannu a duka laifukan. Shiru yayi yana harararsu Alhaji Barau, dan gara ya fad'i gaskiya kowama akamashi.
Ra'eez kuwa shiru yayi har sai da zuciyarsa tayi dai-dai kafin ya kalli Alkali yana fad'in ya mai shari'a anan na kawo k'arshen duk wata sheda da zata tabbatar da wad'an da suke da hannu akan mutuwar Naseer da Alhaji Maiwada, ina rokon wannan kotu data hukunta masu laifi sannan ta bima Malan Sani hakkinsa na d'aureshi da akayi shekara da shekaru bisa zalunci wanda Alhaji Muhammad Sanda tsohon Alkalin kotun nan ne ya yanke wannan hukunci kuma akan sani ya yanke domin dashi ne aka aiwatar da komai, sannan ta hukunta Kwamishna domin ya bada gudummuwa wajen jama Malan Sani sharri akan saka masa jaka a d'akinsa da yayi, haka zalika ta hukunta Dr. Aliyu domin ya bada sakamakon k'arya wanda biyanshi akayi domin yayi hakan, sai Shugaban Kwastam na yanzu Adebayo da mataimakinsa, suma suna cikin wannan b'arna da akayi. Ina fata wannan kotu mai albarka zata bima Mahaifina hakkinsa bisa kisan zaluncin da akayi masa, kuma... Kasa k'arasawa yayi saboda kukan da yaci k'arfinsa.
Tashi Jabeer yayi ya kamoshi suka zauna dan shima hawaye yakeyi. Gaba d'aya kotun tayi shiru mutane da yawa sai da suka zubarma da Ra'eez hawaye saboda tausayi.
Bayan mintuna Alkalai suka gama duba shedun da aka gabatar, babban cikinsu ne yayi gyaran murya yana fad'in abisa manyan shedun da aka gabatar ma wannan kotu, kotu tayi dogon nazari wanda ta tabbatar da ingancin wad'an nan shedu, dan haka kotu zata yanke hukunci.
Da farko ina mai bakin cikin faruwar wannan al'amari, domin an samu manyan mutane wad'an da mutane suka yarda dasu, suka basu amana da hannu dumumu wajen aikata miyagun laifuka. *Tsohon shugaban Kwastam na k'asa, tsohon Alkalin babbar kotu ta lagos, Alkalin babbar kotu na yanzu, Kwamishnan 'yan sanda na Lagos, babban likita, shugaban Kwastam na yansu alagos da mataimakinsa.*
Wad'an nan mutane dana lissafo gaba d'ayansu manyan mutane ne wad'an da suke kula da dubban mutane a k'asan su, sai dai sunci amanar k'asa, sunci amanar aikinsu, sun had'a kai wajen dakusar da gaskiya, da kunya ace mutumin da yake kwatoma wasu hakkinsu yau shine aka kama da wad'an nan miyagun aiyukan, shigo da miyagun kaya, kisan kai, gaskiya ina mai tsananin jin kunyar wannan al'amari daya faru a k'asata, amma shari'a bazata barsu ba, domin duk matsayin ka bakafi k'arfin hukunci ba, dan haka kotu zata fara zartar da hukunci daga k'asa.
*Adekulle Lucky*... Bisa shedun da suka tabbatar cewar shine yake wannan kisa, da kuma amincewarsa akan laifukansa, bisa kundin tsarin mulki na k'asa k'ark'ashin Penal code shashin kisa, wannan kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya har sai ya mutu.
*Dr. Aliyu Sani*... Abisa hujjar da kotu ta samu da kuma amincewarsa bisa laifin bada shedar k'arya, wannan kotu ta soke lasisin aikinsa, sannan ta yanke masa hukuncin d'aurin wata biyar agidan yari tare da tarar naira million d'aya ga Malan Sani.
*Kwamishna Bello Kabir,* bisa kamashi da hannu dumudumu wajen taimakawa masu laifi, da kuma aikata laifi wajen sakama Malan Sani jaka a gidanshi, wannan kotu ta soke lasisin aikinsa, sannan ta yanke masa hukuncin d'aurin shekara biyu a gidan yari, sannan zai biya Malan Sani tarar naira million d'aya da rabi.
*Shugaban Kwastam Adebayo da Mataimakinsa Umar,* bisa kamasu da akayi wajen k'arba'r cin hanci, taimakama masu aikata laifi, da zaluncin da sukayi ma Alhaji Maiwada wannan kotu ta kwace lasisin aikinsu, sannan ta yanke masu hukuncin d'aurin shekara asirin agidan yari, sannan zasu bada tarar naira million ukku ga iyalan Alhaji Maiwada.
Sai hukunci na k'arshe akan mutuwar Naseer Sambo Jarmai da Alhaji Hamza Maiwada.
Mutane hud'u ne suka had'u wajen bada gudummuwa akan wannan kisa, dan haka kotu zata yanke masu hukunci.
*Alhaji Barau, Alhaji Muhammad Sanda, Alhaji Marusa da Mr. Kallah,* bisa kwararan shedu da aka gabatar ma wannan kotu, da kuma amincewar masu laifi akan laifinsu, kotu ta tabbatar da laifinsu, hakika sunci amanar aikin su, dan haka kotu ta yanke masu hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari tare da horo mai tsanani, Alhaji Marusa zai biya diyar kashe Malan Hassan da yayi ga Iyalansa, sannan su duka zasu biya diyar Naseer da Alhaji Maiwada tare da tara mai yawa ga Malan Sani, domin sun zalunceshi.
Da wannan ne kotu ta kawo k'arshen wannan shari'a, kuma ta wanke Malan Sani daga zargin da ake masa, haka kuma tana buk'atar masu kula da hakkin d'an Adam da su tsaya wajen tabbatar da biyan duk wata tara da aka d'ora akan masu laifi, had'e da sauran jami'an tsaro, sannan za'a sake d'ora sabon Alkali zuwa wani lokaci. Kottt!!!.
Hayaniya ce ta kaure a kotun. 'Yan sanda ne sukayi kok'arin fitar dasu Alhaji Barau dan mutane sai jawosu sukeyi, da kyar aka fitar dasu. Malan Sani kuwa zubewa k'asa yayi yana sujada hawaye suna bin kuncinsa.
Alhaji Mansur ne yaje ya kamoshi, rungumeshi yayi yana kuka. Ra'eez ma sai da yayi sujadar godiya ga Allah, kuka kawai yakeyi domin yau itace ranar farin ciki agareshi domin ya cika burinsa. Rungumeshi Jabeer yayi suna murna, haka suka fito waje.
Suna fita suka tsaya suna kallon fad'a atsakanin su Alhaji Barau. Alhaji Marusa ne ya cakumo wuyan Alhaji Barau yana fad'in tsakani na daku Allah ya isa, shegu ashe dama kune kuka jefani cikin tashin hankali, duk amanar dana baku sai da kuka cuce ni.
Dokeshi Alhaji Barau yayi yana fad'in dalla can azzalumi kawai, waye ya cuce mu idan ba kai ba, mu dukan mu nan kaine silar shigarmu wannan halin ba dan kai ba babu abinda zaisa na aikata wannan abun kunyar, waye ya koya mana kisa.
Haka sukayi ta mayar da kalamai yayin da suka fara fad'a suna tona asirin juna, 'Yan sjarida kuwa sai d'aukarsu sukeyi. Da kyar 'yan sanda suka rabasu.
Takowa Ra'eez yayi har gaban Alhaji Barau yana murmushi. Ido kawai Alhaji barau ya tsura mashi yana sauke numfashi. Raheena da Momy suna gefe sai kuka sukeyi.
Kallonshi Ra'eez yayi yana fad'in ina taya ka murnar samun sabon waje na rayuwa, ina fatan yanzu ka gane komai akaina? Murmushi yayi yana fad'in yau kam zanyi bacci mai dad'i domin karatun da nayi yau ya k'are domin ya biya buk'ata, dama nayi shine saboda ku, tunda naga k'arshen azzalumai Alhamdulillah, Allah shine abun godiya.
Takawa yayi har gaban Raheena, ido kawai ya tsura mata yana kallon yanda take kuka ajikin Momy. Kauda kai yayi dan tausayinta ne ya kamashi. Matsowa su Jabeer dasu Nabeel sukayi wajen.
Momy ce cikin muryar kuka tace Ra'eez bani da bakin magana, ayanzu kam mun fahimci komai, sai dai laifin wani baya shafar wani, ina rokon ka da girman Allah ka yafe mana domin bamu da sa hannu a cikin mutuwar Mahaifinka.
Ra'eez yace bakuyi mani komai ba, dama kuma ban tab'a furta kalmar so ga Raheena ba, hannu yasa ya jawo Rumaisa yana fad'in wannan itace matar da zan aura d'iya ga Malan Sani wanda Mahaifin Raheena yayi sanadiyar zamanshi agidan Yari shekara goma sha biyu, ina fatan bazaku kullace ni ba.
Momy ta kalli Alhaji Barau cikin kuka take fad'in ka gani ko, tun kafin aje ko ina abinda bakin halin ka ya jawo mana, shikenan kaji dad'i zaka tafi ka barmu cikin tsangwama da tsana, domin babu wanda zaiso had'a zuri'a damu, ka cucemu, dan haka garin zamu bari ka bani takardar sakina domin kai yanzu gawa ne.
Hawayen bakin ciki ne suka zubo ma Alhaji Barau, sunkuyar da kai yayi yana jin tsananin nadama atare dashi, zeyi magana sukaga Nabeel yayi gefen su Momy da gudu, yana zuwa Raheena ta fad'a jikinsa a sume, dan tun zuwanshi wajen ya sauke ido akanta ya kasa d'aukewa, duk bidirin da akeyi besani ba dan hankalinsa yana kanta, hakan yasa da yaga alamun zata fad'i yayi wajenta.
Kanta sukayi gaba d'aya, cak Nabeel ya d'auketa Jabeer na gaba sukayi hanyar ofis d'insu da ita.
Ammi ce tasha gaban Alhaji M. Sanda idanuwanta jawur alamun taci kuka, hannu ta mik'a masa tana bashi mukullin gidanshi had'e da biro da takarda.
Kuka yasa yana girgiza mata kai. Daurewa tayi tana fad'in wallahi bazan tab'a yafe maka ba, ka rubuta mani saki na a hanya nake, Fawwaz kuwa ba laifinsa bane, naje wajensa tunda safe kuma naji dad'in yanda na ganshi, domin alamu sun nuna yayi watsi da shawararka, kai da kake kok'arin sama masa gata kaima zakaje ka iskeshi acan, kuma har na mutu zan cigaba dayi masa addu'a, dan haka ina jiran ka.
Zubewa k'asa yayi yana kuka ya riko hannunta yana fad'in kar kimun haka dan Allah, da wanne zanji, idan baki yafe mani ba zan shiga wani hali. Fizge hannunta tayi tana fad'in ina jiranka.
Kai ya jinjina yana fad'in bazan sake zaluntar ki ba, domin nasan yanzu banida amfani agareki, na datse igiyar auren mu, amma dan Allah... Wucewa tayi hakan yasa yayi shiru yana kuka.
Haka 'yan sanda suka tasa su sukayi gaba, jiyowa Alhaji Barau yayi yana fad'in Ra'eez kace ma Momyn Raheena na yanke igiyar auren mu nasan bazata sake zuwa waje na ba, ka dubi girman Allah ga Raheena nan aduba mani lafiyarta.
Kauda kai Ra'eez yayi yana sakin tsaki. Rafeek yace muje muga halin da Raheena take ciki Ra'eez. Goge hawayen idonshi yayi yabi bayan su Rafeek da Sameer hada Husnah da suka shiga wajen su Jabeer.
Mama ce ta rik'e Ummu suka nufi mota saboda yanda jikinta yake rawa, haka Alhaji Mansur yayi sallama dasu Alhaji Kamal akan zaije gidanshi anjima, saboda yanzu zai kai su Ummu gida, tare da Malan Sani suka nufi motar.
Da sauri wasu 'yan jarida suka sha gaban Malan Sani. 'Daya daga cikinsu yace Malan Sani wane irin farin ciki kake ciki akan wannan 'yanci daka samu yau?
Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in yau kam bani da bakin magana sai hamdala awajen Allah, domin wannan nasara da muka samu Allah ne yasa muka sameta.
To me zakace akan wad'an nan azzalumai da suka jefaka cikin wanan tashin hankali? Babu abinda zance masu domin Allah ya fisu, kuma wannan zaman gidan Yari da nayi dama Allah ya rubutoshi acikin K'addarata, Alhamdulillahi nayi godiya ga Allah daya bani ikon cin wannan jarabawa, domin ba k'aramun alkhairi bane Allah ya jarabceka sannan ya baka ikon cin jarabawar, su kuma sai dai nace Allah shine zeyi maganin su.
Zasu sake tambayarsa Alhaji Mansur ya janyeshi yana fad'in sai mu kwana anan. Murmushi yayi ya shiga mota sukayi gida.
Sun dad'e suna zubama Raheena ruwa amma ko motsi batayi ba, cike da tashin Hankali Momy tasa kuka tana fad'in ku taimaka mani kada na rasata dan Allah, jikin Ra'eez ne yayi sanyi ganin halin da Raheena take ciki, da sauri Nabeel da Jabeer suka kai hannu domin d'aukarta, tuni Nabeel ya sureta suka nufo waje domin su kaita asibiti.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
5️⃣0⃣
*Last page*
Kusan mintuna ashirin suna tsaye babu labarin Raheena, Nabeel da Jabeer sun kasa zaune kowa ya tsaya bakin kofar d'akin kamar zai shiga. Ra'eez da yake gefe guda a zaune sai kallonsu yake, duk da shima yana cikin damuwar halin da take ciki amma k'asan ranshi dariyarsu yakeyi dan tuni ya gama harbo jirginsu.
Zama Rafeek yayi kusa dashi yana fad'in wad'an can Romeo's d'in fa? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Yaya kaima ka ganosu kenan? Rafeek yace dama can ai Jabeer yana son Raheena, shi kuwa Nabeel shigar sauri Sonta yayi masa.
Ra'eez yace ga Husnah kuma a gefe. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in abun ai yazo da sauki sai wani yayi hakuri.
Wai Husnah lafiyarki kuwa naga duk baki cikin natsuwarki. Ajiyar zuciya ta sauke tare da d'auke idonta daga kan Jabeer, kallon Sameer tayi tana fad'in Yaya. Sai kuma tayi shiru.
Murmushi yayi yace Jabeer ko? Hannu tasa ta rufe fuskarta. Girgiza kai yayi yana fad'in ai na fahimceki tun jiya, kada ki damu matuk'ar kina sonshi zanyima Ra'eez magana, ke kuma sai kiyi amfani da dabarun ku na mata ki janyoshi. Murmushi tayi tana fad'in nagode Yayana.
Fitowar likita yasa gaba d'aya sukayo kanshi. Ofis ya nufa hakan yasa suka bishi banda Nabeel da yayi saurin shiga wajen Raheena.
Ku kwantar da hankalin ku kawai tashiga cikin damuwa ne shiyasa tayi doguwar suma, amma yanzu komai yayi dai-dai munyi mata allurar bacci saboda zuciyarta ta samu natsuwa.
Ajiyar zuciya Momy ta sauke tana fad'in mungode likita, idan ta farka zata warke ko? Kai ya d'aga yana murmushi, kallon su yayi yana fad'in sai dai tana buk'atar arik'a kwantar mata da hankali idan ba haka ba zata iya had'uwa da hawan jini saboda akwai damuwa a zuciyarta.
Rafeek yace insha Allahu za'a kula likita, yanzu me ake da buk'ata? Takarda ya mik'a masa yana fad'in abiya wad'an nan kud'in zasu bada magungunanta. Amsa yayi suka fita suna masa godiya.
A gefenta suka iske Nabeel ya zuba mata ido, komawa da baya Jabeer yayi ganin abinda yake faruwa. Ra'eez yace Momy zamu wuce sai zuwa anjima idan ta farka zamu dawo kila ma asallameta zuwa anjima.
Momy tace nagode sosai Ra'eez Allah ya baku abinda kuke nema. Gaba d'aya suka amsa da amin. Rafeek yace Alhaji Nabeel muje ko. Kai ya sosa yana fad'in kuje Yaya anjima zan tafi. Murmushi sukayi Sameer yace ai gara ka tsaya kayi jinya. Sallama sukayi masu suka fita.
Suna fitowa suka iske Jabeer saman mota yana latsa waya. Ra'eez ne ya matsa yana fad'in Jabeer ya naga ka fito kuma? Jabeer yace jiran ku nake mu wuce. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Jabeer kada ka kwari kan ka fa.
Kallonshi yayi yana fad'in wai Raheena kake nufi? Kai ya d'aga masa. Saukowa yayi yana fad'in fatana ta samu wanda zai kula da ita idan ta rasaka, kuma Alhamdulillahi ta samu, sai fatan ta amince dashi, kuma nayi murna daya kasance shine.
Hannunsa Ra'eez ya kamo yana fad'in kaine ka santa kuma kaine ya kamata ka kasance da ita, ina maka sha'awar samunta domin nasan wacece Raheena.
Murmushi Jabeer yayi yana fad'in wallahi ko son da nake mata zai iya cutar dani gara ya cutar dani da dai na aureta, bare kuma ni tausayinta yafi yawa a zuciyata, koda ina sonta to kad'an ne, kuma ni bazan iya aurenta ba.
Ra'eez yace dalili? Ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in kaine dalilin, da ace wani ne daban da ban sani ba Raheena take ma irin wannan son to zan iya aurenta kuma na mantar da ita komai na koya mata sona, amma bazan iya aurenta ba bayan tana maka irin wannan son, har bada zuciyata bazata tab'a natsuwa ba, domin koda yaushe muna tare da kai, zaka zo gidana itama zata je gidanka, koda ta mance da kai zuciyata zata cigaba da raya mani tana sonka, kaga kuma shed'an beda gwani zai iya d'arsa wani abu a zuciyata shiyasa kaji nace maka bazan iya aurenta ba, ganin yanda Nabeel ya rikice daya ganta nasan cewar Allah ya kawo mata sauyi, dan haka ina so ka bar wannan maganar anan bana so Nabeel yaji kada wani abu ya tsarga zuciyarsa.
Rungumeshi Ra'eez yayi yana fad'in na fahimceka sosai abokina, kuma ko nine haka zanyi, idan ka amince dani zan iya baka mata? Saurin kallonshi Jabeer yayi. Jinjina masa kai Ra'eez yayi.
Murmushi Jabeer yayi yana fad'in na amince. Sakinsa Ra'eez yayi yasa hannu ya juya fuskarshi zuwa wajen dasu Sameer suke tsaye shida Rafeek, saitin da Husnah take ta zuba mashi ido ya aje fuskarshi.
Murmushi Jabeer ya saki har hak'oransa suka fito, shiru yayi suna kallon juna shida Husnah. Hannu Ra'eez yasa ya kamo hannun Jabeer yana fad'in na baka ita amatsayina na Yayanta.
Dariya Jabeer yasa ya tureshi. Wucewa Ra'eez yayi yana fad'in Yaya muje. K'arasowa sukayi Rafeek yace an gama Maths d'in ko? Kai Ra'eez ya d'aga yana fad'in sauran English. Dariya sukasa gaba d'aya.
*** ***
Lokacin da aka shigar dasu Alhaji Barau wajen da sauran fursunonin suke bayan an basu kayan gidan yari sun saka gaba d'aya mutanan wajen sukayo kansu suka sasu tsakiya.
Yanda kasan zasu rufesu da duka haka suka matse su kowa da abinda yake fad'i yayin da wasu suke masu dariya suna nuna su. Kunya da tsoro ne ya kamasu Alhaji Barau sai b'oye fuskarsu sukeyi.
Wani daga cikin mutanan wanda da ka ganshi kaga rik'ekken marar ji, shine ya matso tsakiya yana fad'in ansutu jama'a. Kowa yayi shiru suna kallonshi.
Takowa yayi kusa dasu Alhaji Barau yana tafa hannu, kallonsu yayi yana fad'in *da d'ina da gobe?*.. Mutane suka amsa gaba d'ayansu da *saurin zuwa.* Murmushi yayi yace *Alhaki?* suka amsa da *Kuikuiyo.*.... *Komin nisan jifa?*... *K'asa zata dawo*... *Idan zaka gina ramin mugunta*?... *Ginashi dai-dai tsawonka*... *NASHIGA BAN 'DAUKA BA?*... *BATA FIDDA 'BARAWO.*
Gaba d'ayansu suka d'auki ihu suna dariya. Hannu ya d'aga hakan yasa akayi shiru. Kallonsu yayi yana fad'in barkan ku da shigowa duniyar mu, gashi dai kun turo mu cikinta ashe dama zaku zo ku iske mu, dan haka ku sani kunzo wajen da za'a mulke ku, domin wannan gida Masarauta ta ce, Mazaje kuna ji? Gaba d'aya suka amsa da E muna ji.
Kallonsu ya sakeyi yana fad'in yau dai Allah ya fidda Baba Sani daga gidan nan yayin da ya maido azzalumai a cikin gidan, saboda haka bana so kowa ya d'aga masu k'afa domin da yawa wannan tsohon macucin Alkalin shine ya kawo mu nan, sai wannan guntun Lauyan wato Barau shine yayi silar aka yanke mana hukunci, daga yau babu sani babu sabo tsakanin mu dasu, dole cikin kwana biyu su gane shayi ruwa ne, domin hukuncinsu horo ne mai tsanani.
Dariya sukasa gaba d'aya yayin da suka sungumesu sama sukayi cikin gidan dasu sai ihu sukeyi. Masu gadi kuwa gefe suka koma suna shan dariya dan sun san basuda yanda zasuyi da su domin Allah ne ya kawo masu azzalumai har gida, hakan yasa kowa ya nufi wajen aikinsa.
Fawwaz da yake gefe guda yana kallon abinda yake faruwa hawaye ne kawai suke zubo masa na takaici, tunda Amminsa tazo masa da labarin d'azu da safe yake cikin damuwa, da kunya ace shida mahaifinsa suna zaune waje guda, dole ma ya rik'a nisantarsa dan ba zai iya zama kusa dashi ba, gara kowa yayi hanyarsa danshi ayanzu ilimin addini yasa agaba domin nasihar Amminsa ta shigeshi.
Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaji an dafashi. Juyowa yayi sai yaga abokinsa ne wanda yake d'aukar karatu a wajensa. Zama yayi yana fad'in Fawwaz na fad'a maka sai kasa jarumta aranka idan ba haka ba ciwon zuciya zai iya kama ka, nasan da ciwo amma haka Allah ya k'addaro maka kayi hakuri kawai. Jinjina kai Fawwaz yayi yana fad'in nagode.
**** ****
Zaune suke afalo bayan da Malan Sani yayi wanka dama yayo aski, kaya sababbi Alhaji Mansur ya bashi ya saka, sosai ya fito yayi kyau duk da alamun tsufa da wahala sun fito masa amma ya canza.
Abdallah yana zaune saman cinyarsa sai shafa kanshi yake yana murmushi, abinci Mama ta zuba masu sai murmushi take kamar amarya.
Gyaran murya Alhaji Mansur yayi yana fad'in muna k'ara mik'a godiya ga Allah daya nuna mana wannan rana, hakika Allah shine mai iko mai juya al'amura yanda yaso.
Kallon Ra'eez yayi yana fad'in sannu da kok'ari Ra'eez, hakika kayi kok'ari kuma ka bada gudummuwa sosai, duk da ka fad'a mani duk ranar daka sauke wannan nauyi zaka aje aikin ka amma ban sani ba ko kana da sha'awar cigaba da aikin.
Saurin girgiza kai Ra'eez yayi yana fad'in wallahi Abbah aikin shari'a ya fitar mun rai, nikam daga yau nagama tsayuwa domin na kare wani, dama saboda haka nayi karatun kuma Alhamdulillahi burina ya cika, takardar aje aikina tana nan na dad'e da rubuta ta kwanan wata kawai zan saka na basu abunsu, nifa na kosa mu bar garin nan ma.
Dariya suka sa gaba d'aya. Ummu tace maganar ka gaskiya ce Ra'eez, koni bazan barka kacigaba da wannan aikin ba, haka kuma jina nake kamar ina zaune asaman k'aya domin garin nan ya fitar mun arai.
Jinjina kai Abbah yayi yana fad'in tsarin mu yana kan hanya d'aya, dama na tambayeshi ne dan ban sani ba ko ya canza ra'ayi, amma tunda kana kan ra'ayin ka shikenan Allah ya albarkaci aikin da kayi, sai mu koma Kano a sama maka wani aikin, amma wane aiki kafi so?
Murmushi Ra'eez yayi
yana fad'in nafi son naganni ina koyawa a jami'a, domin buri na ne, shiyasa ma dana samu aikin nake son na k'aro karatu, dan arayuwata ina son aikin da yake da lokaci, wanda mutum zai iya tsara lokacinsa da kanshi, kuma kowa yasan koyarwa ce kad'ai take da wannan tsarin.
Kai Yaya makarantar 'yan mata kuma zakayi aiki? Rumaisa ta fad'a kamar an tsikareta, hannu tasa ta rufe bakinta ganin a inda tayi maganar. Da sauri ta mik'e tayi waje hakan yasa suka kwashe da dariya.
Umma tace kina da gaskiya 'Diyata, nima na fara tayaki kishi haka kawai zaije cikin 'yan mata yarik'a bud'e murya yana koya masu. Mama tace ai Yarona beda kalle-kalle kusha kurimin ku babu abinda zai faru.
Dariya sukasa Ummu ta duk'ar da kai tana murmushi. Abbah yace tunda dai shine ra'ayinsa zan sama maka, kai ina tabbatar maka wannan shari'ar da kayi zata d'aukaka ka, duk inda ka nemi aiki a fad'in k'asar nan sai ka samu, dan haka mu fara shirin tafiya, Malan Sani gara mu tafi daga baya sai mu dawo asa duk gidajen kasuwa domin mun bar Lagos kenan sai dai muzo da yawo saboda mutanan arziki.
Malan Sani yace duk yanda kace Alhaji haka za'ayi, domin banki kada na kwana alagos ba yau dan wallahi ta fitar mun arai. Abbah yace shikenan zuwa nan da kwana biyu sai mu tafi kafin nan an kammala komai.
Madu ne ya kalli Malan Sani yana fad'in dan Allah Malan Sani ka yafe mani, har yanzu ina jin kunyar shedar dana bayar akan ka wancan lokacin.
Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in wai Madu bazaka dena wannan maganar ba, tun yaushe nace na yafe maka, ko nine fa amatsayin ka wallahi shedar da zan bayar kenan, dan haka komai yawuce.
Abbah yace ai wannan maganar ma abar tada ta, wad'an da suka assasa fitinar ma suna can nasan mutanan gidan Yarin kad'ai sun ishesu, dan haka kowa yayi nagari kansa, ubangiji Allah ya k'ara tsare mana Imanin mu da zuk'atan mu.
Sai magana ta gaba, muna komawa Kano zanyi bikin Yarana dan bazan jira komai ba, ko kuma hada Raheenar zaka had'a? Waro ido Ra'eez yayi yana kallon Abbah da yake kunshe dariya.
Umma tace Allah ya kyauta wallahi Yarona bazai had'a zuri'a da wad'annan mutanan ba. Dariya sukasa Abbah yace dama tsokana ce, babu wata amarya agidan Ra'eez sai Rumaisa ta. Malan Sani yace ai duk yaranka ne duk yanda kayi yayi, Allah yasa alkhairi. Gaba d'aya suka amsa da amin.
*** ***
Maganar ka gaskiya ce Nabeel, dama ka fad'a, zuwa kwana biyu za'a dena labarina, gashi kuma ya tabbata, sai fatan Allah ya yafe mani, dad'in da nakeji yanda Iyayen Farouk suka yafe mani.
Nabeel yace ai Abbah dama na fad'a maka, duk abinda mutum ya aikata akwai wanda ya aikata abinda yafi nashi, Allah dai ya k'ara tsare mu baki d'aya.
Ummansa tace amin Nabeel, ya jikin Raheenar kuma? Kallonsu Abbah yayi yana fad'in wacece kuma Raheena? Duk'ar da kai Nabeel yayi yana murmushi.
Murmushi Abbah yayi yana fad'in to nagane, na samu surika kenan, amma a ina take haka? Sosa kai Nabeel yayi yana fad'in Abbah anan garin take, sai dai zuciyata tana cikin damuwa saboda nasan na d'auko abinda bazaku amince dashi ba, nima wallahi bansan yanda akayi zuciyata ta kamu da sonta ba, domin komai ya faru ne ayau, yanzu hakama daga wajen ta nake tana asibiti bata da lafiya.
Hannunsa Abbah ya kamo yana fad'in bana so kasa aranka ni zan iya tauye maka hakkin ka, fad'a mani wacece ita? Kallon Umma yayi yana fad'in 'Yar gidan Alhaji Barau ce Alkali.
Ajiyar zuciya Umma ta sauke tayi shiru tana kallonsu. Shiru shima Abbah yayi har Nabeel ya fara tsorata da shirunsu, can Abbah ya saki murmushi yana fad'in Allah mai juya al'amura, nine nake tsoron ranar da zaka kawo mani surika arik'a goranta maka abinda Mahaifinka yayi, sai gashi Allah ya k'ulla alak'a tsakanin ka da wacce laifin Mahaifinta ya take na Mahaifin ka so dubu, matuk'ar ita yarinyar tana da hali mai kyau bazan hana ka aurenta ba, domin laifin wani baya shafar wani, Allah ya tabbatar da alkhairi.
Kallon Umma Nabeel yayi yana matse idanu. Hannu tasa ta ja kunnansa tana fad'in amsata kake jira? Kai ya d'aga yana kallonta. Murmushi tayi tace Allah yasa abokiyar rayuwarka kace.
Rungume Umma yayi yana fad'in amin Ummana, nagode sosai, yanzu na samu kwarin guiwar tunkararta da maganar dama amincewar ku nake jira sai dai kutayani da addu'a akwai soyayyar wani a zuciyarta, sanin bazata sameshi ba yasa tashiga cikin wannan halin.
Abbah yace *WAYE NE*? Nabeel yace Brr. Ra'eez ne. Jinjina kai Umma tayi tana fad'in itama ta d'ebo da zafi, koda yake kowama sai yanzu yasan d'an gidan marigayi ne, babu komai, matuk'ar kana sonta kaje ka gwada sa'ar ka. Abbah yace Allah ya baka sa'a. Yace amin.
*** ***
Kwance take ajikin Momy tana kuka, hakuri Momy take ta bata. Raheena tace Momy Dady ya cuceni, ba dan wannan abun daya aikata ba nasan dole na samu Ra'eez, amma kina gani sai dai na hakura dashi, gashima har yana da matar aure, shikenan nasan bazanyi aure ba har na mutu domin Dady ya goga mani bakin fenti.
Shafa kanta Momy tayi tana fad'in zakiyi aure Raheena, domin a yau da kika rasa Ra'eez Allah ya kawo maki wani, abinda nakeso da ke ki daure ki amshe shi, domin idan kika rasashi zaiyi wuya ki sake samun wani, domin shine yazo maki alokacin daya kamata kowa ya gujeki, dan haka ina mai baki shawara daki amshe shi, tunda kika suma yake tare da ke be jima da tafiya ba yace zai dawo, shima abokin Ra'eez ne, sunanshi Nabeel, d'an gidan tsohon shugaban makarantar kings college ne wanda aka yanke ma Mahaifinsa hukunci wan can satin shida Alhaji M. Sanda, yaron kirki ne ina maki sha'awarsa.
Shiru Raheena tayi ta d'ago kai tana kallon Momy, zatayi magana aka turo k'ofa. Nabeel ne dasu Ra'eez suka shigo bakinsu d'auke da sallama.
Saurin duk'ar da kai Raheena tayi dan yanzu kunyar Ra'eez takeji. Momy ce ta amsa masu tana masu sannu da zuwa. Zama sukayi suka gaisheta tare da tambayar mai jiki.
Momy tace gatanan taji sauki likita ma ya sallame mu dama zaman jiranku nakeyi tunda Nabeel yace mujirashi. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in K'anwata babu magana.
'Boye fuskarta tayi tana murmushi. Jabeer yace ko saboda Nabeel ai sai a kallemu. Murmushi Nabeel yayi yana fad'in dan Allah kubarta ta huta. Tashi Ra'eez yayi yana fad'in anbarta mai Raheena, Momy kutashi mu wuce.
'Dago kai Raheena tayi zata kalli Nabeel caraf suka had'a ido, da sauri ta kauda kai tana jin fad'uwar gaba. Haka suka tattara suka wuce gida.
Bayan sun ajesu Ra'eez ya fad'a masu nan da kwana biyu zasu koma Kano da zama. Momy tace muma ai bazamu zauna ba Kanon zamu koma gobe ma.
Ra'eez yace ashe muna kusa, to Allah ya taimaka, na manta Alhaji yace na fad'a maki ya datse igiyar auren ku. Tsaki Momy taja tana fad'in shi ya sani dai, nagode maku, kome kenan zamuyi waya.
Ra'eez yace shikenan. Sallama sukayi masu Nabeel yace nima ina nan. Jabeer yace dama kaji munce kaTaho? Ai gara ka zauna kuyi sallama.
Fita sujayi suna dariya. Suna shiga mota Jabeer yace wai da gaske garin nan zaku bari? Ra'eez yace wallahi kuwa. Jabeer yace aikuwa wallahi tare zamu tafi nima na rubuta takardar aje aiki na. Waro ido Ra'eez yayi yana fad'in yaushe? Jabeer yace tun lokacin da nasan zaka aje naka.
Ra'eez yace su Abbah bazasu barka ba ai. Jabeer yace tuni ma suka amince, da ace mace ce ni ai dole na rabu dasu saboda aure, dan haka sun amince zan koma Kano da zama kuma nima rin aikika zanyi.
Rungumeshi Ra'eez yayi hawayen farin ciki suna sakko masa, bayansa ya dafa yana fad'in nagode d'an uwana, hakika tarayyar mu daga Allah take, na dad'e cikin damuwar rabuwar mu, ashe zamu kasance tare, muje dole nayima su Abbah godiya.
Dariya Jabeer yasa yana fad'in sai dai zuwa anjima yanzu muje ka rakani na shigar da kaina wajen Husnah kaga muna komawa sai asha bikin mu tare. Dariya Ra'eez yasa yana fad'in yanzu kuwa.
*** ***
Kafin dare an gama kammala duk wasu labarai, tun daga gidan tv, gidan radio, yanar gizo, kai duk wata kafa ta yad'a labarai sai da aka yad'a maganar shari'ar su Alhaji Barau.
Ba iya Lagos ko Nijeriya ba, gaba d'aya duniya labarin wannan shari'a ya watsu, duk inda kasan akwai yanar gizo to dole su samu wanann labari.
Mutanan da suka kalli wannan shari'a basa kirguwa domin abune daya tab'a zuk'atan mutane, yayin da wasu suke Allah wadai da halin su Alhaji Barau.
Haka Rafeek sai da ya bada firar da suka tab'ayi da Kwamishna a gidan Tv aka kunna, wanda hakan ya jawo karin surutu awajen mutane, kowa yana fad'in ta bakinsa, yanda Kwamishna yake lailaya zance ta kamar mutumin kirki ashe azzalumi ne.
*** ***
Washe gari wajen k'arfe sha d'aya aka aiko kiran Alhaji Marusa. Koda yazo yayi mamakin wanda ya iske a wajen. Zama yayi jikinsa a sanyaye. Jin shiru anki magana yasa Alhaji Marusa yace Khalil!.
Idanuwa kawai Khalil ya tsura mashi ya kasa magana. Matsowa Alhaji Marusa yayi hawaye suna sauko masa, hannu ya kai zai kamo Khalil yayi saurin kwace hannun sa yana fad'in kada ka tab'ani. Alhaji Marusa yace kayi hakuri Khalil, nasan bani da bakin da zan maka magana amma inaso ka d'auka kaddarace ta sameni.
Tashi Khalil yayi yana fad'in babu wata K'addara Dady, kai ne ka zab'ama kan ka wannan rayuwar, ko haihuwar mu da kayi Allah ne yasa zamu fito duniya, kud'in ka sune Mahaifanmu domin sune suke kula damu ba kai ba, bakasan komai namu ba, baka san tarbiyar mu ba, kawai ka turamu cikin turawa dan kada muzauna akusa da kai mutakura maka, Alhamdulillahi ina k'ara godiya ga Allah daya shirya ni, haka ina bakin ciki da Yaya ya tsinci kasan a irin halin da kake ciki, dama kuma barewa bazatayi gudu d'anta yayi rarrafe ba, bansan abinda kayima Momy kenan ba sai jiya Yaya yake fad'a mani da mukayi waya bayan daya samu aron waya dan yaga abinda ya faru da kai.
Tunda aka kamashi so d'aya bakaje ba, shiyasa ya aiko ni na fad'a maka yana tayaka murnar zaman gidan yari, dalilin zuwana saboda ka fad'a mani inda Momy take naje na nemota domin bazan iya barinta ba, saboda itama bata barmu ba alokacin da baka kula damu.
Cikin kuka Alhaji Marusa yace kayi hakuri Khalil, nasan ban kyauta maku ba, kuma naji dad'i dana ganka cikin kamala, dama kuma Allah yana fitar da rayayye a jikin matacce, bakasan abinda Momynku tayi bane amma zan fad'a maka......
Hawayen bakin ciki ne suka zuboma Khalil daya gama jin abinda ya faru. Alhaji Marusa yace bayan tafiyarta da kwana biyu na samu labarin mutuwarta, ashe barin ta nan abinda saurayinta yayi mata ya jawo mata ciwon zuciya, ciwon kwana biyu zuciyarta ta kumbura ta mutu, kayi hakuri da ban fa....
Saurin tashi Khalil yayi yana fad'in ya isa, ba sai ka k'arasa ba, Allah yajik'anta, nima zan koma inda ka koya mani rayuwa, Alhamdulillahi na had'u da Ubangida nagari mai ilimin addini, duk da kasancewarsa farar fata amma musulmi ne, kuma ya samar mani shedar zama d'an k'asa, yanzu haka bikin mu za'ayi da d'iyarsa, dan haka daga yau ni ba d'an najeriya bane na manta da ita zan rik'e surukaina amatsayin iyayena.
Rikoshi Alhaji Marusa yayi yana fad'in na amince da haka, kuma naji dad'i, amma inaso kaje gidana cikin d'akina zakaga takardun kadarorina ka d'auka gadonka ne duk... Hannu ya d'aga masa yana fad'in kai da kotu ta bayar da dukiyar ka ina kake da wasu kud'i? Ko kana dasu wallahi bazan sake cin sisin ka ba domin dukansu haram ne, nizan wuce, ina rokon ka da ka yafe mani idan na maka badede ba.
Kuka Alhaji Marusa yasa yana kiran Khalil amma ko juyowa beyi ba. Zubewa yayi a wajen yana wani irin kuka. Masu gadi ne sukazo suka korashi ciki.
Haka ya koma wajen da suke fasa duwatsu, yana kuka yana cigaba da aiki, su Alhaji Barau ne suke bashi hakuri suma kukan suke, tausayin kansu ne ya kamasu, acikin kwana daya komai ya canza masu, lallai duniya abun tsoro ce.
*** ***
Duk wata dukiya ta masu laifi sai da jami'an tsaro suka had'a kanta, gidaje da sauran kadarori duk sun had'a takardunsu za'a sasu kasuwa dan sai an fitar da abinda kotu ta yanke idan anyi saura a basu kayansu.
Su Momy tuni suka kama hanyar Kano wanda Nabeel ne ya d'auki nauyin kaisu dan yakasa ya tsare dole sai da Raheena ta saurareshi, hakan yasa yace zai kaisu domin ya gano waje. Itama Raheena tana jinsa aranta dan tana kokarin cire Ra'eez dan tasan ta rasashi, gara ta amshi Nabeel koba komai yanzu ta fara sanin dad'in so saboda ta samu mai sonta ba wanda take so ba, domin za'a kirata aji lafiyarta, sab'anin da itace take kira.
Lokacin da shugaban kula da hakkin wad'an da kotu ta nema da a damk'ama tarar da ta yanke ya buk'aci ganin Malan Sani da Iyayen Naseer, bayan da yayi masu jawabi sai Malan Sani yace gaba d'aya abinda aka bashi a mik'asu gidan marayu dan bazai iya amfani da kayan haram ba, haka ma Baffa yace.
Wannan abu da sukayi bak'aramun burge mutane yayi ba, anan ya fito yasheda ma 'yan jarida komai, su kuma suka shiga rattabawa a labaransu, hakan ya jawo masu d'aukaka da addu'oi a wajen mutane, domin ba kowa bane zai iya tsallake irin wannan dukiya ayanzu.
*** ***
Aje aikin Ra'eez da Jabeer ya tab'a zuk'atan manyansu da sauran mutane, domin sun san sunyi asarar hazikai, tun daga can sama aka aiko da sakon ban hakuri da neman alfarma akan Ra'eez ya koma bakin aikinsa amma yace ayi hak'uri ya gama aikin lauya, duk yanda Alhaji Kamal yaso amma hakan be samu ba dole sai dai sukayi hakuri.
'Yan jarida kowa so yake yayi fira da Ra'eez amma yaki basu had'in kai, da sun tambayesa dalilin aje aikinsa amsar d'aya ce, dama cikar burinsa yake jira kuma ya cika shiyasa ya aje.
Tarin masoyan Ra'eez na garuruwa dama k'asashe basu fad'uwa domin har dena kunna data yayi saboda yawan sako.
*** ***
A ranar da zasu tafi kasancewar jirgin yamma zasubi hakan yasa Alhaji Mansur ya shirya masu taro a harabar gidansu Ra'eez, duk wasu abokan arziki sai da suka zo wannan taron domin su k'ara tayasu murna.
Iyayen Nabeel, Iyayen Sameer, Iyayen Rafeek, Iyayen Jabeer duk sunzo dan sunce zumunci yanzu aka fara.
Anci ansha kuma anyi raha, anan Alhaji Mansur ya tashi yana mik'a godiyarsa abisa goyon baya da kuma had'in kan da suka basu wajen ganin an kammala wannans shari'a, haka yayi ma Iyayen Jabeer godiya da suka amince mashi ya bisu, kuma yayi masu alk'awarin kula dashi kamar yanda zai kula da Ra'eez.
Anan ya kalli Iyayen Sameer yana fad'in ina nema ma 'Dana Jabeer auren Husnah domin inaso da an koma a had'a bikinsu dana Ra'eez. Dariya akasa nan Dadyn Sameer yace ai duk 'ya'yanka ne, dan haka na bama Jabeer Husnah.
Cusa fuska Husnah tayi cikin mayafinta tana sakin murmushi. Dadyn Sameer yace biki biyu zanyi, domin tare za'a had'a dana Sameer.
Abban Nabeel yace ashe kuwa za'ayi babban taro, domin shima Nabeel zan had'a nashi da Raheena, kunga kuwa ya kamata ace an tsaida bikin a waje d'aya.
Alhaji Kamal yace idan haka ne nine zan bada wannan shawarar, tunda mutanan Kano sunfi yawa kuma a cikin mu babu d'an asalin garin nan duk munfi kusa da can wajajen ina gani zamu maida bikin mu a kano, domin kuwa nasan zata d'auke mu.
Tafi akasa gaba d'aya kowa yana fad'in hakan yayi dai-dai. Baffa yace gaskiya naji dad'in wannan zumunci da yaran mu suka had'a, ubangiji Allah ya k'ara k'arfafashi har zuwa jikokin mu da masu zuwa bayansu.
Gaba d'aya aka amsa da amin. Alhaji Mansur yace insha Allahu zamu tsara yanda komai zai kasance, sai dai zamu aro al'ada, inaso bikin ya kasance tamkar na Yarbawa, ma'ana ayi komai arana d'aya atashi, a d'aura aure lokaci guda a wuce wajen cin abinci hada matan, ana gamawa amaren kusa akaisu gidajensu, na nesa kuma washe gari atafi dasu.
Dariya suka sa kowa yace wannan yayi ba sai an tsaya yin wani dogon biki wanda za'a fara tun daga laraba sai lahadi a gama. Bayan sun kammala suka kulle taron da addu'a.
Kowa wajen budurwarsa yawuce domin suyi fira. Jabeer da Husnah tamkar masoyan da suka dad'e, dan Husnah ta iya soyayya, tasan yanda zata sa namiji ya mace akanta ya kuma saba da ita cikin kankanin lokaci, abunka da sabon shiga tuni Jabeer ya zurma har yakusa fin Ra'eez kwarewa.
Kallon juna kawai suke fuskarsu d'auke da murmushi. Rumaisa ce ta fara d'auke idonta tana murmushi. Ra'eez yace komai yayi farko zaiyi k'arshe, kinga yanzu sai muje musha biki babu sauran damuwa ko tunanin shiga kotu. Dariya Rumaisa tasa tana fad'in ai wannan kotu taci mana lokaci.
Ra'eez yace shiyasa ai na zab'i wannan aikin domin nasamu damar kula dake, kinga kema sai kishiga makarantar ki anatse, ko har yanzu kina akan bakarki na bakison karatu? Murmushi tayi tana fad'in yanzu kam nake da sha'awar karatu koda bazanyi aiki ba, dan haka ashirye nake dana fara karatun aikin lafiya.
Tafi yayi mata yana fad'in haka nake son ji, ina matuk'ar son na ganki kina taimakon al'umma, duk da nasan zan baki kulawa amma inaso kema kiyi aiki domin kishiga cikin al'umma kirika sanin rayuwa, Allah ya baki sa'a kuma ya barmu tare. Kallonshi tayi tana fad'in Amin Annur.
***
Tsaye suke a tashar jirgin sama suna jiran akirasu, gaba d'ayansu fuskokinsu d'auke suke da farin ciki, acikin matafiyan hada Madu dan shima yace binsu zeyi, duk wanda yaga wannan zuri'a sai sun burgeshi saboda yanda fuskarsu take d'auke da annashuwa.
Ra'eez kuwa mutane sai zuwa suke suna gaisawa wasu kuma suna d'aukar hoto. Kiran sunaye da aka fara yasa mutane suka barshi.
Murmushi Jabeer yayi yana fad'in kaga angon Rumaisa. Ra'eez yace ga kuma angon Husnah ba, wai ya akayima bata zo rakiya ba? Jabeer yace nine na hanata dan bana so ta sani kuka.
Dariya sukasa gaba d'aya hada su Rafeek, Sameer, Adnan da Nabeel. Rafeek yace ai dama fa ance farin shiga sunfi saurin iya abu, yanzu ko kunyar Yayunta bakaji kake fad'in haka.
Rufe fuska Jabeer yayi yabar wajen yana fad'in na d'auka bakowa ai. Dariya sukasa Adnan yace gara ka fad'a sai dai kuma baka canka dai-dai ba ka ganta can a baya dan kuka tasa mana sai ta biyo mu hakan yasa Yaya yace ta taho.
Jabeer yace Yaya Sameer kai da kan ka? Gira Sameer ya d'aga yana fad'in bana son k'anwata tayi kuka shiyasa na taho da ita, kaje ku k'ara sallama kafin azo kan ka. Ra'eez yace ba sai yaje ba kamar naji an kira sunanshi fa.
Da gudu Jabeer yayi wajenta yana fad'in d'an bakin ciki saboda kasan da Rumaisa za'a tafi ai dole ka fad'i haka, to sai naje. Dariya suka sa. ajiyar zuciya Rafeek ya sauke yana fad'in gaskiya zamuyi kewa, amma bakomai ai Kano da Lagos babu nisa musamman da sauki yazo yanzu, insha Allahu zumuncin mu bazai lalace ba zai d'ore a haka.
Sameer yace Allah yasa. Haka sukayi ta fira har aka kirasu. Sallama sukayi cike da kewa dan Ra'eez sarkin kuka sai da yayishi, suma duk jikinsu yayi sanyi haka suka rabu cike da kewar juna.
Sai da kowa ya gama shiga jirgin kafin jirgi ya d'aga. Hannun Jabeer Ra'eez ya rik'e yana fad'in aiki ya kammala gashi yayi riba tunda ya sama mani babban aboki kuma d'an uwa. Jabeer yace sosai kuwa domin gashi na samu K'ani daga sama.
Harara Ra'eez ya watsa mashi yana fad'in kamanta, ai kasan dai na girmeka. Juyawa Jabeer yayi yana fad'in dan Allah Ummu nida Ra'eez waye babba? Murmushi Ummu tayi tana kok'arin maida kwallar idonta ta kewar mijinta kafin tace kaine babba.
Dariya sukasa hada mutanan da suke kusa dasu. Gwalo Jabeer yayi ma Ra'eez. Murmushi Ra'eez yayi ya rik'e hannun Jabeer, runtse ido yayi yana fad'in daga k'arshe Allah ya bani Yaya nima. Hawaye ne suka sauko masa. Hannu Jabeer yasa ya jawo kanshi ya kwantar a kafad'arsa yana shafa bayansa.
Murmushin farin ciki Alhaji Mansur yayi yana fad'in Allah ya k'ara had'a kanku baki d'aya. Malan Sani da yake gefe yace amin.
*ALHAMDULILLAH*
Nima anan jirgina ya d'aga zuwa Zango daga Lagos😉. Ina mik'a godiyata ga Allah daya bani ikon kammala wannan littafi nawa mai suna *ALKALI NE,* ina rokon Allah ya yafe mani kuskuren da yake ciki, ya kuma bada ikon d'aukar darasin da yake ciki.