Kusan awa biyu sannan khairat tafarka daga baccin daya d'auketa sakamakon Allurar da likitan yayimata, da mummunan fad'uwar gaba tatashi, dan tana zaton ko likitan yagayama Salim watannin cikin nata.
lokacin Kuma drip d'inda aka sanyamata ya 'kare, wannan nurse d'ince tsaye kanta taciremata kanula sannan tafita daga d'akin, ko minti biyu batayiba da fita Salim yashigo khairat na ganinshi tayi wani irin razana tana niyyar saukowa daga Kan gadon, saurin ri'keta Salim yayima yace "Haba khairat miyasa kike haka, kobakisan abunda ke tattare dake bane, yakamata kinutsu kada kijawomin asara Kuma"
Wani irin murmushi jin dad'i khairat tayi koba kome tasan Salim baisan watannin cikintaba, langa6ar da Kai tayi tace "kagayama likita ya sallameni nawarke banison zama asibiti"
"Eh dama yace idan ruwan ya'kare zamu iya tafiya, yanzu kitashi mutafi, Amma Zaki iya hawan mashin d'in kodai insamo mota?"
"A'a bakome zanhau mashin d'in ainaji sau'ki sosai,"
Tashi tayi tana Sanya hijab d'inta Salim d'in na gyaramata, Mama tayo sallama,
Amsawa Salim yayi tareda matsawa nesa kad'an da khairat d'in cikedajin kunyar yanda Mama ta iskesu.
Kallonshi Mama tayi tayi wani guntun murmushi Wanda ita kad'ai tasan ma'anarshi.
Karasawa tayi wurin khairat d'in takama hannunta tana jeramata sannu, itako sai wannan langa6ewa take, ita adole gamai ciki.
Salim ne yace "ai yanzuma zamu wuce gida, Allah ma ya taimaka da mumsha ban-ban tunda muna Shirin tafiya kina zuwa"
"To Alhmdlh, tunda nazo kaje kasamo Mana mai napep saimu hau nida ita, kaikuma saika biyomu a mashin d'in"
"To" kawai Salim yafad'a sannan yahau mashin d'insa yatafi, bayan mintuna goma saigashi yadawo da Mai napep, Mama dake ri'ke da hannun khairat tanata riritata kamar wata jaririya, suka shiga napep d'in Salim yabiya kud'in sannan suka d'auki hanya.
6anagaren Fauziyya kuma, tunda Aunty Safiya tabata wayarta Bata bud'etaba sai yanzu tana zaune tsakiyar gadon d'akinta kad'aici duk ya addabeta, su Walid da Ahmed da walida basunan sunfita Shan ice cream suda dady d'insu.
Wayar ta d'auko ta danna fawa, tana kallo takawo haske tagama loading...... Sannan ta kunnu, Sim yafara updating.... Yana gamawa tareda shigowar sa'konnin Salim, kusan guda bakwai.
Zama Fauziyya tayi tafara duba sa'kon d'aya bayan d'aya.
Na farko dai Yana sanar da ita yadawo gida Yana jiranta d'akinsa, mamakine yakamata data duba lokacin shigowar sa'kon dakuma kwanan watanshi yayi dai-dai da ranar da Salim d'in yarubuta mata takardar Saki, sauran sa'konnin Kuma yanaso tagayamashi inda take, wani sa'kon Kuma rantsuwa yakemata da Allah shifa bai saketaba, a wani massage d'in Kuma Yana ro'konta Alfarma data taimake rayuwarshi duk inda take tagayamashi ko inane zaizo ya sameta.
Fauziyya tana gama karanta sa'konnin tafashe da kuka, wani irin tausayin kansu itada Salim yakamata, wannan wane irin murd'adden Al'marine,
Fitowa tayi daga d'akin tana kuka tanufi d'akin Aunty Safiya, kusan Karo sukayi da ita tana niyyar fitowa daga d'akin.
Kallon Fauziyya tayi wacce duk tabi tarud'e ga hawaye share-share a fuskarta tace "ke lafiya meya faru naganki haka"?
Wayarta tami'kamata tace Aunty Safiya ki karanata wannan sa'konnin Wanda Salim yayimanine duka"
Amsar wayar Aunty Safiya tayi tafara karantawa Fauziyya nakarayimata bayani inda bata ganeba.
Sauke ajiyar Zuciya Aunty Safiya tayi tace, to ikon Allah sai kallo, to tunda yace haka ki kirashi kigayamashi inda kike yazo saumuji 'karin bayani daga wurishi"
"To shikenan Aunty" haka tafad'a ta amshi wayarta takoma d'aki.
Komawa tayi kan gado ta zauna ta tattaro duka nutsuwarta ta lalubo number Salim ta danna Kira, tanata ringing ba'a d'agaba, sai gab da zata tsinke taji and'aga.
Shiru tayi tana share hawaye, tanajiran taji me Salim zaifad'a.
Cikeda mamakin ganin Kiran Fauziyya Salim yafara magana "my wife kece kodai mafarki nake, Ashe dama Zaki iya tafiya kibarni, haba Fauziyya miyayi zafi haka, kome nayimaki baikamata ki hukuntani ta wannan hanyar ba"
Cikin muryar kuka Fauziyya tace "Hubby nice yakamata infad'i haka bakaiba, saboda laifinda ban aikataba kuma banida masaniya akanshi ka sakeni......
Katseta yayi "ki daina furta kalmar saki Fauziyya, wlh tlh bansakekiba, har yanzu har yau har gobe matsayin matata kike saboda nidai nasan ban sakekiba"
Sauke ajiyar Zuciya tayi, dan ita abun yagama d'auremata Kai, to idan Salim yace baisaketaba waye yarubuta takardar saki ya ajiyemata, kawai dai yanaso yayimata yawo da hankali ne....Amma ga rubutunshi 6aro-baro
"Yanzu kina Ina kigayamin plz"
"Hmm Ina Abuja"
"Dama can Kika gudu, Aiko gobe Ina zuwa, danma yanzu yamma yayi sosai, amma gobe inshaAllah asubanci zanyo inzo in d'auki matata"
Murmushi Fauziyya tayi Wanda saida Salim yajiyo sautinshi, shima murmushi yayimata kafin sucigaba da firar missing d'in juna dasukayi.
*Kuyi manage da wannan da bazanyi typing ba sai gobe ganin yanda masoya keta jira yasa nayimaku wannan,*
Mmn khady ce π€Έπ»♀
π *ALMAJIRIN GIDANA* π€¦π»♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* π₯°
*Daga Marubuciyar* π
*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now ππ»
*ALMAJIRIN GIDANA* π
Page 37
*FAN'S ZANGAYAMAKU DALILIN DAYASA JIYA BAKUJINIBA, WLH BACIN RAINE KAWAI, AKWAI WANI BANZA DAKIKI, WAISHI IBRAHIM USMAN BINDIN KAKE KO UBANWA OHO DAI, YANANAN YANA AMFANI DA BASIRAR MU MU MASUYIN LITTAFI KYAUTA, SHIKUMA YANA KWASHEWA YANA SAIDAWA, WAI YABUD'E GROUP BAZAI SAKAKABA SAIKA TURA KATIN 200, KUMA BAWANI LITTAFI BANE NA DABAN YAKE TURAWA SAI NAMU MU MASUYIN FREE, AKA GAYAMAKA IDAN SON KUD'I NE KAFIMUNE, MU BAMUYI NIYYAR SIYARDA LITTAFIN MUBA, BAIKAMATA ACE KAI KANA SIYAR MANA BA, SABODA TSABAR RASHIN KUNYA HAR KIRANKA NAYI TA WAYA WAI DAN IN TABBATAR DUKDA NAGA POST DINDA KAYI NA TALLAR GROUP DIN KAKE KARA JADDADAMIN SAINA TURA KATIN 200 SANNAN KATURAMIN, NIDA LITTAFINA, TO KABUDE KUNNENKA KA SAURARENI DA BABBAR MURYA, WLH KAYI GAGGAWAR DAINA SIYAR MANA DA LITTAFI IDAN KUMA BA HAKABA WLH ZAMUYI MAGANINKA SHEGE ZAUNE GARI BANZA KAWAI, KAJE KANEMI SANA'A DAN WANNAN HAKKIN WASUNE KAKECI, IDAN KUMA KA'KI JI WLH BAKA'KI GANIBA, YAUSHE ZAMU ZAUNA MUYI WAHALAR TYPING DA WAYARMU DA HANNUNMU DA CAHRGE DINMU DA DATARMU SANNAN ACE KUMA WANI YAFIMU CIN GAJIYAR ABUN, BE YIWUWA KURA DASHAN BUGU GARDI DA KWACE KUD'I, DUKDA NASAN IRE IRENKA SUNADA YAWA TO WLH KU GUJI HAKKIN MUTANE KU DAINA, NIDAI NAFAD'A DUK WANDA YA SIYARMIN DA LITTAFI ALLAH YA ISA BANYAFEBA, KUMA KUDIN DAYA AMSA YACI WUTA BAL-BAL* π₯
*Kukuma FAN'S kudaina biyema irin wadannan banzayen, idankuma zaku iya biyan wani 'katon banza kud'i yaturomaku littafin Dana nashiba, Kara muma mu maida na kud'i Kowa yahuta* π€
Khairat Kuma tunda suka dawo gida ta kwanta Kan gado tanata wannan lankwasa, ita gamai ciki, itako Mama sai nan-nan take da ita.
Jitayi tagaji da kwanciyar, wayarta ta d'auko ta dawo falo ta zauna kan kujera tabud'e data tafara chat, Mama na zaune gefe sai jeramata sannu takeyi, Amma saboda tsabar wulakanci batama d'agowa ta kalleta balle Kuma ta amsa.
Kusan minti talatin suna zaune ahaka, khairat sai chat takeyi tana murmushi lokaci zuwa lokaci, kafin tad'ago ta kalli Mama cikin muryar shagwaba tace "Yunwa nakeji, Kuma bazan iya shiga kitchen ba"
Jiki na rawa Mama tace
"Miye kikeso sainashiga na dafa maki, dama ai baikamata ace kinshiga kitchen ba, kamata yayi kizauna kihuta duk wani aiki ki ajiyeshi har Allah ya saukeki lpy"
Murmushin gefen baki khairat tayi tace "ok, tokishiga kitchen kidafamin taliya jallouf kisamin daddawa"
Mi'kewa mama tayi, tanufi kitchen tana fadin "to taliya kikeso, yanzu zandafa maki, Yar Albarka, Allah dai yayimaki Albarka kin kawomana farinciki agida"
Haka mama tashiga kitchen ta ta'kar'kare tafara aiki, minti Sha biyar ta gama dahuwar taliya saiko 'kamshin daddawa ke tashi, zubowa tayi a plate tasako spoon takawo gaban khairat ta ajiye, "to gashi sai ci ko"
Dagowa khairat tayi wacce har yanzu taketa chat d'inta hankali kwance, ta kalli taliyar ta yamutsa fuska.
sannan tace "Mama pork Zaki kawomin banacin taliya da spoon, kamar wata 'yar 'kauye, jiki na kyarma mama tashiga kitchen ta d'auko pork takawo, amsa khairat tayi tasaka cikin taliyar ta d'auko plate d'in takawoshi saitin kirjinta tad'ebo taliyy tana Shirin kaiwa baki, saikuma tawani 6ata fuska, ta maida, ta ajiye plate d'in tace Mama bazan iya cin wannan taliyar ba daddawa yayi yawa, Kuma yanzu banima son taliyar ma d'anwake nakeso"
"D'anwake 'yar nan, badamuwa Bari inyimaki d'anwaken, shiga tayi kitchen ta ta'kar'kare takwaba d'anwake tagama tazubo takwoma khairat, guda d'aya kawai tasaka abaki tafara kakarin amai,
Da sauri mama ta iso gareta tana jeramata sannu, tana tambayarta "kodai bazaki iyacin d'anwakenba?"
Daga Kai khairat tayi tace banason na fulawa, da kinhad'a alabo da wake kinkai ni'ka danaci, Amma Babu kome kabarshi kawai, kiyimin "wainar filawa nakeso"
Jiki na rawa Mama tace "badamuwa ai sai inyimaki, ai kome da dalili akeyinsa, ai bazantaba bari ki wahalaba saboda kinkawomin farinciki arayuwata, nadad'e inason ganin jikana bansamu hakaba saidaga gareki, Allah yayimaki Albarka bari inyimaki wainar fulawar"
Komawa kitchen mama tayi tafara aikin wainar fulawar.
Khairat naganin shigewarta ta kwashe da dariyar mugunta, ganin yanda Mama keta rawar 'kafa akanta wai ita zata samu jika.
Shiko Salim tunda yaji labarin Fauziyya baikarabi takan khairat ba, shirye-shiryen zuwa Abuja kawai yakeyi.
Aranar dai haka Mama ta wuni tana bautama khairat, kamar wata 'yar aikinta, sai dare mama tabar gidan dukta gaji jikinta yayi likis saboda uban aikin datayi, dan Koda tagama girke-girkenta Wanda Babu Wanda khairat taci aciki, saida tashare kitchen d'in tagoge sannan tafito tashare tsakar gidan tayi moping.
*(Ah ni su mama an bautama d'an Sani)* π€£
*Jama'a Wai Baku cigiyar Sani*
Yau itace ranar da Sani ya yanke zaije gidansu Fauziyya yaga halinda take ciki dan tunda tabar gidan Salim bai'kara ganintaba, Yana Kuma Kiran wayarta lokaci zuwa lokaci amma kullum abu d'aya ake gayamashi shine wayar na kashe.
Wanka Sani yad'auka cikin wata fitinanniyar shadda dark blue, yasha hula kalar shaddar, sai takalminshi black, sanifa yafito yayi gwanin kyau ga wani irin turare daya bad'a sai 'kamshi ketashi ajikinshi.
Koda ya isa 'kofar gidansu Fauziyya tsasayawa yayi Yana tunanin yanda zai 6ulloma al'amarin, yakai minti goma 'kofar gidan kafin yayi tamaza yashiga da sallama.
Mamar Fauziyya na zaune kan tabarma tana Shan iskan yammaci, ta amsa sallamar.
Zama yayi kan wata kujera irin ta roba dinnan dake ajiye gefe guda, ya gaida mama cikin ladabi ta amsamashi.
Shiru sukayi nad'an wani lokaci sannan Sani yace "amm Mama dama zuwa nayi mu gaisa da Aunty Fauziyya"
"Allah sarki, Aiko Fauziyya batanan ai tadad'e rabonta da garinnan"
"Ashe batanan to mama Ina tatafi ne?"
"Tana Abuja"
"Abuja" Sani ya mai-maita kalmar cikeda takaicin rashin tako sa'ar dayayi.
"Sai yaushe zata dawo Kuma"
Eh to Nima bansaniba, Amma zata dawo nan bada dad'ewaba inshaAllah"
"To Allah maidota lpy, Amma nace Kota canja layine Naga idan nakira layinta kullum kashe"
"Bata canja layiba shine dai take amfani dashi, ko d'azu muyi waya da ita"
"Owk zankirata, wlh mama banji dad'in abunda yafaru tsakaninta da Salim ba, tunda Fauziyya tabaro gidannan Nima naji duk ya fitarmin Rai"
"To yaza'ayi da 'kaddarar Allah, haka Allah ya kaddara, idan Allah yasa zamansu Bai 'kareba sai kaga an dai-daita"
Gyara zama Sani yayi yace "bani fatan dai-daitawa tsakanin Aunty Fauziyya da Salim, dan wlh Mama Fauziyya zaman ha'kuri kawai takeyi a gidanshi, wannan mutumin ba 'karamin mugu bane Yana muzguna mata kawai dai Allah yasa ita macece mai ha'kuri amma in banda haka da yanzu igoyoyin aurensu duka sun 'kare, gaskiya Fauziyya mace ce wacce samun irinta a wannan zamanin sai an tona"
Tunda Sani yafara magana Mama ke saurareshi ta sauke ajiyar Zuciya tace "to Allah dai yazama bafi Alkhairi"
"Ameen" Sani yafad'a, shiru yaratsa nawani d'an lokaci sannan yatashi yace" nizan wuce"
"To sai anjima"
Lokacin gab da magrib Sani yabaro gidansu Fauziyya, gidan khairat yawuce Kai tsaye zuciyarshi cike da takaicin rashin ganin Fauziyya,
Zaune ya iske khairat falo tana kallon wani Nigerian film, shima Zama yayi kan kujerar dake fuskantarta, kallo tabishi dashi tace "ah Sani wannan d'aukar wanka haka ina zuwa"?
"Ina zuwa kokuma Ina akaje dai" Yabata amsa
"To Ina kaje haka?"
"Ina zanje kau Wanda yawuce gidansu Fauziyya, sai dai Kuma nayi rashin sa'a ashe Fauziyya tunda tabar gidannan tana Abuja"
Wani mugun dad'ine ya mamaye zuciyar khairat, yanzu hankalinta ya kwanta, dama bataso Sani ya auri Fauziyya saboda tana kishinsa, Kuma yanda yake nuna tsantsar soyayyar Fauziyya tabbas idan ya aureta itakuma zai zubata kwandon shara, wani abun farincikin Kuma tayima Salim nisa Kuma da alama baisan inda takeba, kenan ita wannan Abu ita yayima amfani tajefi tsuntsu biyu da dutse daya.
Sani yakatsemasu shirun yace "nifa yunwa nakeji kisamomin abunda zanci, "akwai abinci kusn kala hud'u wane kakeso inkawoma, akwai d'anwake, akwai taliya dafuwar daddawa, akwai wainar fulawa"
Kallo Sani yabita dashi yace "miye ke damunki haka duk Kika zauna kikayi wannan abun"
Dariya khairat tayi tace "banice nayiba wata 'yar aiki nasamu tayita bautamin baji bagani"
"Yar aiki Kuma, yaushe aka kawota gidannan bansaniba"
Dariya khairat takwashe da ita tace "Mamar Salim ai itace sabuwar 'yar aikin dana samu, Dan yau ta bautamin yanda kasan sarki da bawa, Kuma tayi hakane duk dan cikin dake tare dani"
Dariya Sani yayi yace "woooo ke khairat kina wuta Ina binki da fetur, gaskiya ke babbace dole asaramaki, watako kina nufin wannan cikin yazama na Salim"
"Sosaima Kuma wlh bakaga yanda yaketa murnaba"
Kai Amma naji dad'i kice d'ana zai taso cikin so da kulawa, dan Mamar Salim tana masifar son ganin jikanta, shima Kuma Salim d'in yanason ganin d'ansa"
Murmushi khairat tayi tace "yanzu dai fad'i miye zakaci inkawoma"
"Tab ai wlh Babu abunda zanci, bayan kince Mamar Salim ta girka, kawai kishiga kitchen kidafamin ko indomie ne, Kinsan ba abincin Kowa nake iya ciba daga na Fauziyya sai naki"
Tashi khairat tayi tanufi kitchen dan batason ran Sani yabaci Amma in banda haka Babu abunda zaisa tashiga kitchen, mintuna goma Sha biyar tagama hada imdomie da kwai, takawoma Sani yafara dibarshi, saida ya cinye tass yakora da ruwa, sannan ya kalli khairat yace kawomin wainar fulawar inji idan tayi dad'i" Babu yanda khairat ta iya haka tanufi kitchen takawomashi had'eda yaji cikin vowel, amsa yayi yadauki guda ya dangwala yaji yaci, kallon khairat yayi yace "wow Ashe dai wannan matar danike gani haka ta iya wainar fulawa, kinji kuwa yanda tayi dadi" cigaba yayi dacin wainar yanata dankara yaji kamar tsohon maye, haka yatada wainar tass yakuma bi da ruwa.
Fira sukacigaba dayi, sai bayan sallar isha'i Sani yabar gidan dan yasan Salim na gab da dawowa.
Fitar Sani badadewa Salim yashigo gidan hannunsa d'auke da Leda, d'akin khairat yashiga, zaune ya isketa har yanzu film din take kallo, sannu yayimata ta amsa ciki-ciki tana wannan langa6ewa, ledar dake hannunshi yami'kamata amsa tayi tana bud'ewa robar ice cream tagani guda biyu, take miyanta ya tsinke, tabud'e roba d'aya tafarasha, ice cream din yayimata dad'i sosai, kallo Salim yabita dashi azuciyarshi yanajin tsanarta, baisan yanda akayiba har yanzu yakasa jin son khairat, dukda cikinshi datake d'auke dashi, tunda akayimashi albishir din tanada ciki yakeso yakoyama kanshi sonta amma zuciyarshi ta'ki kar6ar tayin dayakemata, uwa uba Kuma dayasamu labarin one love d'insa Fauziyya.
Kallon khairat yayi yace "gobe idan Allah ya kaimu munada wata semina, kifadamin abunda kike bu'kata dan tun asuba zamubar garinnan,
"Ai babu abunda babu, sai dai kud'i zakabada saboda tsaro"
Kud'i ya fiddo Mai yawa daga aljihunsa yami'kamata batareda yace komiba yami'ke zai bar d'akin, har yakai bakin 'kofa tace "Kuma kwana nawa zakuyi?"
"Eh to zadai mutafi sai yanda yakama, amma nasan bazamu wuce kwana biyu ba, kila Kuma yafi haka"
"To Allah ya ya tsare"
"Ameen"
Yafad'a Yana komawa d'akinsa yashiga shirya kayanshi, washe gari da shirinsa yafita ana gama sallar asuba yawuce tasha, golf ce kan layi, saboda haka ba dad'ewa tacika suka d'auki hanya,
*Sai muce Salim Allah kiyaye hanya, dama ance garin masoyi baya nisa Koda yakai bernin sin, yau dai Salim yatafi garin Fauziyya*
π *ALMAJIRIN GIDANA* π€¦π»♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* π₯°
*Daga Marubuciyar* π
*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now ππ»
*ALMAJIRIN GIDANA* π
Page 40
ππ»
*Oyoyo Maman twowins tadawo jama'a kutayani murna, kullum inata cigiya Ina faman Kiran waya bani samu ashe ba lafiya, Allah ubangiji ya'kara lpy, Allah sa zakkar jikine, Allah Kuma yaraya Mana twowins, Allah karo wasu three wins, muzo mukwaso shoki da shaku,shaku, Kai hadama zanku zanyi dan murna*π€£
*Comment d'inki akan littafina Yana matu'kar Sani farinciki, iya wuya muna tare* π€π»
Duk da haka khairat bata ha'kura da Kiran number sani ba, cigaba tayi da Kira.
Sani Kuma Yana ganin Kiran ya'ki dagawa dan gani yake kamar idan yad'aga kome zai iya faruwa, jiyakema kamar idan yad'aga muryar Salim zaiji, dan tun jiya wani mugun tsoron salim yakamatashi.
Khairat gajiya tayi da Kira ta ajiye wayar tahakura,
Sai bayan kusan awa hud'u da Kiran sannan yayi tamaza azuciyarshi yace baridai inkira inji miye yasaka taketa kirana haka, tun farkoma bai kamata in'ki d'agawaba, fad'uwar gaba asarar namiji.
Aiko Yana Kira ringing d'aya khairat tad'aga dama jira take.
"Hello Sani Ina kashiga inata faman kiranka tun d'azu"
"Inafa zanshiga inanan Ina fama da jikina har yanzu bai gama warwarewa ba"
"To ingayamaka akwai labari, kazo gidanan yanzu kagani da idonka"
"Mezan gani? Kawai kigayamin anan dan nanda kwana bakwai bazanzo gidankiba kidai gayamin kawai"
"Kara kazo d'in dai tunda nace kazo, gani yakore ji"
"To shikenan ganinan zuwa, amma wlh idan Naga bawani serious abu bane yasa kika kirani wlh sai rayuka sun 6aci"
"Eh naji kadaizo d'in kagani"
Suna gama wayar Sani ya canja Kaya wurin 'karfe tara da minti goma ya iso gidan, lokacin Salim yariga yatafi wurin aiki.
Sallama yayi, khairat ce ta amsa tayi saurin fitowa daga d'aki.
Wani kallo tayimashi tareda yimashi nuni da d'akin Fauziyya.
Kallon d'akin Sani yayi gabanshi yafad'i cikin murya 'kasa-'kasa yace badai tadawoba"
Murmushi khairat tayi tace "dukta dawowa mai sau'kine sai kaganata zakaga babban abun mamaki"
Fauziyya daga d'aki tanajiyo lokacinda Sani yashigo, fitowa takeso tayi su gaisa, sai dai tana mi'kewa 'kafarta tari'ke takai minti biyar tsaye awurin kafin tasamu tafito.
Sunajin alamun tafiya suduka suka maida kallonsu wurin.
Ganin Fauziyya da 'katon ciki yasa Sani yin Hocking, dan kasa motsi yayi, duka tunaninshi da kome nashi yayi sumar wucin gadi.
Muryar Fauziyya ce tadawo dashi dai-dai "Mal Sani kananan kenan?"
"Eh wlh inanan aunty, yafad'a yana 'ka'karo murmushi kamar Wanda akayima dole.
"Aunty yaushe kikadawo ne?"
"Tunjiya nadawo ai, dayake dare ne"
"Kai Amma nayi matukar farinciki, Allah tsare gaba"
"Ameen Sani nagode, ya maganar wanke-wanke kuma?"
"Kai aunty yaushe rabona da wanke-wanke, idan Kinga nazo gidannan yanzu zuwa nayi kawai mu gaisa"
"Ah Sani kacemin kazama babban yaro, kadaina wanke-wanke, to Allah ya taimaka" tana gama fad'in haka tawuce d'akinta tabarsu.
Kallon Sani khairat tayi tace "kaje kawai zamuyi magana"
Haka Sani yaja 'kafarshi yafita daga gidan Yana layi da tangadi kamar Wanda yashawu, saboda tsabar 6acin rai, Wai yanzu Fauziyya ce da wannan 'katon cikin, to yanzu ta'ina zaya bulloma wannan Al'amarin, haka ya isa gida ya zauna tunani kala-kala cunkushe a kwalwarshi.
Washe gari tun 'karfe takwas na safe Fauziyya da Salim suka fito cikin shiri, zai sauketa asibiti tasake bucking domin zuwa awo, daga Nan zaiwuce wurin aiki.
D'akin khairat yashiga yabata kudin cefane sannan yagayamata zai sauke Fauziyya asibiti.
Nan yake tambayarta "waike yaushe zaki Fara zuwa awo, naga baki ta6ayin maganar Fara zuwa awo ba"
Yamutsa fuska tayi tace "nifa banason zuwa awo, nifa asibiti idanba doleba bason zuwanshi nakeba, ko haihuwar idan Allah yakawomani da sau'ki nafiso inyita d'akina bawanda yaji bawanda yagani, sai dai aganni da babyna kawai"
"Amma Kinsan zuwa awo Yanada matukar muhimmaci gamai ciki, tananne ake gane idan akwai wata matsala Kuma ashawo kanta tun kafin lokacin haihuwa, ana gane ingancin lafiyar jaririn dake cikine ta hanyar zuwa awo, sannan Kuma ana koyama mata yanda zasu raini yaransu bayan sun haihu da yanda zasu kula da lafiyarsu"
"Hmmm zanyi tunani idan naji zan iya zanje, idan kuma bazan iyaba gaskiya bazan wahalar dakaina ba"
Fauziyya tana tsaye tsakar gida tana jiran salim ganin yanda yadad'e d'akin khairat Kuma tana jiyo maganarsu sama-sama yasa taji wani irin kishi, jitake kamar taje ta fiddo Salim daga d'akin, ganin fitowarshi yasa tad'an saki fuskarta dan bataso ya fahimci halinda take ciki.
"Muje ko" yafad'a yayi gaba tabi bayanshi,
Asibitin dai dasuke zuwa nan Salim yakaita, dan suduka Nan sukeda file, kudi yabata yace idan tagama tahau napep takoma gida.
Khairat tana ganin fitar Salim da Fauziyya takira Sani tace tanason ganinshi yanzu,
Gayamata yayi sundanyi wata 'yar tafiya Amma Nanda awa d'aya darabi zai iso,
Zaman jiranshi kawai take tanayi tana kallon agogo lokaci zuwa lokaci, tamatsu yazo suyi magana kafin Fauziyya tadawo gidan.
Yana isowa yawuce d'akin khairat din Kai tsaye, falo suka zauna suka Fara tattauna matsalar su.
Lokacin Fauziyya itama tadawo gidan dan batawani dad'eba a asibitin tagama abunda take.
Tanata sallama taji shuru, sai surutu take jiyowa sama-sama daga d'akin khairat, Jin an ambaci sunanta yasata son jin maganar da akeyi.
Matsawa tayi kusa da window d'in d'akin ta la6e.
Muryar khairat taji tana cewa "ai yanzu cikinta yayi girma maganin zubarda ciki bazai iya yimashi komeba, hanya d'ayace zamubi mukashe abunda ke cikinta shine muhad'a baki da likitan asibitin datake awo, idan taje awo yayimata Allurar dazatasa tahaihu cikin 'kan-kanin lokacin, kaga tunda lokacin haihuwar beyiba koma miye acikin zaizo ba Rai"
"Anya wannan hanyar mai 6illewa ce, bakigani za'a iya samun matsala, idan Kuma likitan ya'ki amincewa fa?"
"Hmm Sani kenan, badai kud'i ke magana ba, zanbashi kud'i masu yawa nasan zai amince da bu'kata ta"
Dafe 'kirji Fauziyya tayi, innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, kawai take mai-maitawa a zuciyarta,
Sauri tayi tafita daga gidan, ta dai-daita nutsuwarta sannan tadawo tasake kwad'a sallama da 'karfi kamar dama yanzu tadawo,
da sauri khairat tafito tana Yan kame-kame "ah kindawo kenan, wlh Nima inanan narasa d'an aike shine nabugama sani waya yazo ya taimaka yayomin cefane"
"Allah sarki" Fauziyya tafad'a tashige d'akinta.
Koda tashiga jikinta duk yayi sanyi, tunani take "Wai abunda taji da gaske ne kokuwa mafarki take, Wai yau khairat da Sani *ALMAJIRIN GIDANA* ake 'ko'akarin had'a kai acutar dani akashe abunda ke cikina, ya subhanallah, menayimaku haka me yayi zafi, ya Allah ka kareni ka tsareni daga sharrin masu sharri.
Ranar haka tawuni sukuku, Salim nadawoawa take har d'akinsa, kallonta yayi yace "Maman twowins andawo ko?"
Harararshi tayi tace "waima twowins nifa d'aya zan haifa, Kai bakasan wahalar haihuwarba shiyasa kakemin fatan twowins"
"Aike naga kinsan wahalarta tunda wannan itace ta bakwai"
Dariya tayi tace "ai dai zanyi d'in Kuma zanji"
Kamota yayi ya zaunarda ita kusadashi yace "zo gayamin ya akayi aaibitin?"
"Ba'ayi komeba Babu ma'aikata Inga zankoma general hospital kawai sai inri'ka awona acan"
"Kinaga babu wata matsala"
"Ba matsala yanda wannan asibitin zasu kula dani suma can haka zasuyimin, kawai dai atayamu addu'a Allah saukemu lafiya, nida amarya bansan waye zaifara Haihuwa ba"
"Ke Zaki Fara bakiga cikinkiba yayi ukkun nata girma"
Dariya sukayi suduka, Fauziyya tace "Allah girman cinnan na damuna" tayi maganar cikin muryar shagwaba.
Kwai-kwayon muryarta Salim yayi yace "Allah girman cikinnan na burgeni nikuma"
Rufe fuskarta tayi da hannu tace "banaso Allah"
Dariya yasamata.
Haka sukacigaba da fira cikin farinciki, harta manta da kudirin khairat da Sani akanta.
_______________________
Satin Fauziyya d'aya da dawowa Salim yasa tashirya yakaita gidan Mamarshi, mamakine ya kamata ganinta datayi da ciki, ba kunya kuma tafara Ina takasa Ina taka aza da ita.
Harda cewa "mahakurci mawadaci, kaga ikon Allah ashe zansamu jikoki har biyu kusan lokaci guda, keda khairat Allah sa ku sauka lafiya, gaskiya naji dad'in wannan abu"
Fauziyya dai murmushi kawai take tana mamakin rashin kunya irinna mamar Salim.
Ranar gidan tawuni sai bayan la'asar Salim yazo ya d'auketa har bakin 'kofa mama tayimasu rakiya tace "ki gaidamin khairat d'in idan nasamu lokaci zanzo har gida in'kara dubaku"
*Bayan watanni hud'u*
Cikin khairat Dana Fauziyya duka yashiga wata tara, khairat cikinta beyi wani girmaba, dan idan ka kalleshi zaka d'auka bai wuce wata shidda zuwa bakwai ba.
yayinda cikin Fauziyya yayi wani mugun girma, zama da kyar tashi da kyar, gawani irin kumburi da 'kafafunta sukayi suntum.
Khairat da Sani dai sunyi iya 'ko'karinsu na ganin sun zubarda cikin Fauziyya Amma abun ya faskara dan Zakaran da Allah yanufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi.
Kulawa sosai Salim yakebasu suduka, Fauziyya Kuma saboda halinda take ciki wata 'kanwar mamar Salim ce tadawo gidan dazama wacce suke Kira Inna Rabi dan tari'ka kula da ita d'akinma Fauziyyar take kwana, Inna rabi macece mai kirki da sanin darajar d'an Adam, ko kad'an halinsu ba d'ayabane dana mamar Salim.
Tana matukar son Fauziyya ganin yanda take girmamata Kuma takemata ladabi.
khairat Kuma bataji dad'in zaman Inna Rabi a gidanba dan gani take kamar antakurata anhanata sakewa, Kuma ga Inna Rabin kamar zatayi sa idon tsiya acewar khairat din.
Sani Kuma dole tasa yahakura ya'kale khairat dan tanunamashi duk wani jin dad'i dole suha'kura dashi har Allah ya sauketa lafiya.
Bahaka Sani yasoba amma ba yanda zeyi dole yahakura ya shafama khairat lalfiya.
Amma sai dai yakasa daurewa dan khairat tariga tasaba mashi bazai iya kwana bakwai batareda ya kusancetaba, saboda haka kullum cikin matsananciyar sha'awa yake.
Zuby ce tafad'o mashi arai wacce tuni takemashi tallar kanta yanacewa akai kasuwa,
Batareda bata lokaciba yaje gidan Zuby yagayamata ya amince da bukatar ta, dama abunda take nema Nan sukacigaba da badalarsu.
Mmn khady ce ππ»
Mmn khady ce ππ»
[10/3, 7:00 PM] Hayat: π *ALMAJIRIN GIDANA* π€¦π»♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* π₯°
*Daga Marubuciyar* π
*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now ππ»
*ALMAJIRIN GIDANA* π
Page 42
*Aha masoya jiyafa Naga ruwan comment, gaskiya naji dad'i sosai banida bakin godiya kawai dai iya wuya..... Comment dinku nasani nishad'i mussamman GROUP din ALMAJIRIN GIDANA NOVEL FANS 1 & 2 dakuma GROUP din ZEE MMN KHADY FAN'S jiya khairat taga ruwan 'yan barka, gaskiya kunyima Sani Kara, Bari muga Yana Fauziyya zai kasance*
*AKAFTA* π€Έπ»♀
Kafin wani lokaci Inna Rabi da Maman Salim da Maman Fauziyya da Salim duka suna asibitin.
Fauziyya Kuma ana lebour kusan awa d'aya tana ciki Amma bataji ciwon komeba shiyasa har yanzu Bata yarda cewa haihuwa zatayiba.
A zuciyarta cewa tace "Niko miyasa wannan narse d'in tayimin haka, haka kawai takawoni nan batareda wani daliliba, tasa duk mutane sunzo to yanzu idankuma ban haihubafa ai naji kunya"
Haka tayita sa'ka da war-wara, tana cikin wannan tunanin taji cikinta yayi wata irin murd'awa lokaci d'aya, tare da wani irin ciwon 'kugu, dafe kugunta tayi tace "washhh, innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Kuma saitaji ciwon ya lafa kusan minti bakwai, saikuma yakuma tasowa haka dai tayitayi kusan awa d'aya, kafin abun ya kankama, yanzu Fauziyya ta tabbatar ma kanta da lallai haihuwa zatayi, dan ciwo takeji sosai, danma Allah yayota macece mai dauriya.
Su Inna Rabi da Maman Fauziyya da Maman Salim da Salim duka suna bakin 'kofar labour room sun kasa zaune sunkasa tsaye, addu'oi kawai sukema Fauziyya Allah sauketa lpy.
Wata nurse ce tafito tace "Ina masu Fauziyya, da sauri mamar Salim jiki na kyarma tace "gamu nan" tareda Isa wurin narse d'in.
"Ku kawo zani Allah ya sauketa lpy, da sauri mama tami'ko sabon fallen zani Wanda suka taho dashi cikin kayan daza'a bu'kata.
Amsa nurse d'in tayi tace "saura guda"
Kallo sukabi nurse d'in dashi.
"Eh saura guda, saboda zani biyu muke bu'kata domin Fauziyya 'yanbiyu ta Haifa mace da namiji"
Ai tana rufe baki Inna Rabi ta ri'ke hanci ta rangad'a wata mashahuriyar gud'a wacce tajawo duka hankalin jama'ar dake wurin.
Ai mamar Salim kuwa tsabar murna rawa tafara takawa tana kwaso shoki, tana wani turo duwawu tana juyi, duka mutanen wurin babu Wanda bai daraba.
Salim dai murmushi kawai yake saki, azahiri amma a zuciyarshi yafi Kowa farinciki, jiyake kamar abarshi yashiga yagano baby's d'inshi da Fauziyyarshi.
Kusan minti talatin sannan akagama gyara Fauziyya da baby's d'inta aka maidosu d'akin hutawa, sannan akaba su mama izinin shiga su ganta.
Ai ana shiga Mamar Salim tayi d'af da baby's d'in duka biyun ta ri'ke tanata kallonsu fuskarta cikeda farinciki, juyowa tayi wurin Fauziyya tana jeramata sannu,
Maman Fauziyya kuwa wurin d'iyarta tanufa tana jeramata sannu tana tambayarta abunda ke damunta, "Babu abunda ke damuna yanzu Mama, nagodema Allah na haihu cikin sau'ki batareda wata matsalaba"
"Alhmdlh" Mama ta fad'i.
"Inna Rabi dake gafe tace "Allah shine abun godiya"
Salim kuwa gefe guda yakoma dan bazai iya komeba indai su mama nanan, sukan had'a Ido shida Fauziyya lokaci zuwa lokaci murmushi yake sakarmata, sannan yayimata Alamar sannu da hannu.
Idan tagani sai dai itama tayi murmushi ta sadda kanta 'kasa.
Mamar Salim ankama baby's anri'ke batada niyyar badawa, saida Inna Rabi tace "Yaya kibada yaran mugansu muma"
Mi'kama Inna Rabi macen tayi tana dariya tace "amshi wannan kishiyace babu abunda zanyi da ita, 'kara inrugumi angona"
Dariya sukayi suduka, Inna Rabi tace "Nima ai nafison angon, waye keson kishiya a duniyar nan"
Mamar Fauziyya tana jinsu Kuma tana kallonsu bata sakamasu baki sai dai tayi murmushi,
Inna Rabi tagama ganin baby sannan tami'kama Mamar Fauziyya, amsa tayi ta kalli 'yan jikokinta wani irin so da 'kaunarsu na shiga zuciyarta, yaran sun d'ebo kamannin mahaifinsu sak, har Kara namijin idanunsa irinna Fauziyya ne, Amma macen kamar Salim yayi kaki babu abunda tabaro nashi.
Yaran kyawawa farare tas, gasu da girmansu kamar ba twowins ba.
Waya mamar Fauziyya tafiddo takira aunty Safiya, bayan sun gaisa mama ta tambayi lafiyar su Walid duka akacemata suna lafiya sannan tace "ganinan asibiti ri'ke da babyn Fauziyya"
Cikin tsananin d'oki da farinciki tace "Mama yaushe Fauziyya ta haihu?"
"Yau yanzuma ba dad'ewa gamunan ma asibiti ri'ke da twowins"
"Twowins Mama" aunty Safiya tafad'i cikin tsananin murna da farinciki, sannan tacigaba da cewa "haba Babu mamaki wannan girman ciki na Fauziyya, Allah ya raya baby's sainazo"
Mamar Fauziyya ce taga rashin dacewar abunda akayi ace har yanzu Salim bai d'auki baby's d'inba Kuma Yana wurin"
Zuwa tayi har inda yake tami'kamashi duka yaran, sannan tayimasu sallama tawuce gida, tunda dai Fauziyya ta haihu lafiya ai 'kara tawuce hakanan.
Salim kuwa yanajin yaran rungume jikinshi yaji farincinsa ya 'karu fiyeda Wanda yake ciki, 'kurama yaran Ido yayi wani irin sonsu da 'kaunarsu nashiga zuciyarshi.
Addu'a yayimasu tare dayimasu hud'uba.
Wurin 'karfe biyu da rabi na rana likita ya sallamesu suka wuce gida cike da farinciki tareda baby d'insu.
Duk abunnan khairat tana gida itada Khalid d'inta batasan wainar da ake toyawa ba.
Tadai San Fauziyya tatafi awo amma batasan ta haihuba.
Sallamar Mamar Salim tajiyo da Inna Rabi, amsa sallamar tayi tafito waje Khalid na goye a bayanta.
Ganin Fauziyya tayi babu ciki ga Mama d'auke da baby Inna Rabi ma d'auke da wani baby d'in.
Kallo kawai tabisu dashi zuciyarta d'auke da tambayoyi barkatai Wanda sai ahankali zatasamu amsar su.
Inna Rabi suna shiga d'aki ta mi'kama Fauziyya babyn dake hannunta tafito domin d'ora ruwan zafi.
Har yanzu khairat na tsaye inda suka barta, kallonta Inna Rabi tayi tace "kije mana ki gano 'yan'biyu Khalid angirma ansamu 'kanne"
Murmushi khairat tayi tace "aini abunne ya d'auremin Kai naga daga zuwa awo andawo da baby's"
"Abun Allah kenan yawuce ya d'aure Kai, kedai shiga kigano Yan tagwaye" Inna Rabi tafad'a ta'kara gaba wurin dafa ruwan zafinta tabar khairat tsaye tama rasa miye zatayi.
D'akin Fauziyya tashiga da sallama ta zauna mama tamikamata Baby's amsa tayi ta zubamasu ido, yaran sun matukar Bata sha'awa, a zuciyarta Kuma jitake inama ace itace Fauziyya, wannan sune 'ya'yan Salim Kuma jininsa ba Khalid ba.
Wasu hawaye ne suka taru suka cikamata Ido, suna niyyar gaganrowa tayi saurin sa hannu tagoge batareda Kowa yalura ba.
Tad'an dad'e d'auke da baby's d'in kafin ta kwantar dasu tawuce d'akinta.
Dama Allah Allah take tadawo d'akin takira Sani tayimashi albishir, koba kome tayi farinciki da haihuwar Fauziyya tasan Sani zai ha'kura da 'kudirin daya d'aukarma kanshi na aurenta, tunda yataba gayamata indai Fauziyya ta haihu to yaha'kura da aurenta.
Kiran wayarshi tayi tanata ringing bai d'agaba lokacin Yana gidan Zuby, suna she'ke ayarsu.
Saida takira yakai sau ukku acikon na hud'unnne zuby dake kwance jikinshi tasa hannu ta d'auko dan 'karar wayar Yana damunta tace "kad'aga Mana khairat ce fa, d'agawa tayi takaramashi a kunne.
"Hello ya akayi?" yafad'a cikin wata irin murya.
Shiru yayi da alama tana Kora mashi bayani ne.
"What"...... Yafad'a da 'karfi tareda tashi zaune yature zuby dake kwance jikinshi yari'ke wayar gam a kunnenshi.
'kuramashi Ido zuby tayi tamatsu yagama wayar taji mike faruwa.
Saida yagama ya ajiye wayar gefe sannan zuby tarungomshi jikinta "miya faru haka baby na, naga dagayin waya kashiga wani yanayi"
"Fauziyya ce ta haihu" yafad'a batareda ya kalli zuby dinba.
"Wayyo dad'i, wani farincikine ya mamaye zuciyar zuby, idan Bata mantaba tatabayima sanin tayin aurenta yace shifa Fauziyya ce kad'ai macenda zai aura, amma yayimata Al'kawarin idan har Fauziyya ta haihu da Salim yaha'kura da aurenta Kuma zai aureta.
______________________________
Tundaga ranar da Fauziyya ta haihu har zuwa yau damuke kwana biyar da Haihuwar mutane keta tururuwar zuwa ganin baby's, kullum gidan cike yake kamar ranar suna.
Salim kuwa yataka muhimmiyar rawa wurin yin kome awadace, kullum za'aci asha kome lpy lao.
_______________________________
Sani dai ya amince da maganar aurenshi da zuby, batareda sanin khairat ba, Dan khairat batama San Yana tare da zuby ba.
Sati d'aya aka tsaida za'ayi aure inda zuby tabashi ma'kudan kud'i yayi hidimar aurenta.
Dan duk wata dukiyar zuby kusan yanzu tana hannun Sani tami'kamashi yanata watayawa abunshi.
*Bayan kwana biyu*
Yau itace ranar sunan 'yan biyun Salim.
Kuma yau Salim yasamu 'karin girma a wurin aikinshi,
Farinciki biyu.
Fauziyya anfito Mai jego, tasha make up, wani tsadadden less tasaka, maroon Mai kwalliyar green da golden, tayi wani fitinannen kyau.
Aunty tun jiya sukazo harda baban Walid, trolley biyu tayoma Fauziyya d'aya kayan twowins daya kayan Fauziyya.
Baban Walid Kuma mijin Aunty Safiya Salim ya baiwa kyautar have million 500k
Gaskiya haihuwar tazomasu da Alkhairi sosai.
Maman Salim dataji labarin irin abun Alkhairi da aka samu murna tayi sosai tace "wannan yara haihuwar ku Alkhairi ce"
Ansha taron suna gidafa yacika ma'kil babu masaka tsinke can na hango tawagar Yan group din ALMAJIRIN GIDANA NOVEL FANS anata cin rangem, bayan angama Kuma aka shiga fagen rawa inda Mrs DJ ke bada tashi gudaummuwar.
Kai nikaina ba'a barni abayaba sunan Fauziyya dole nakwaso shoki ππ»♀π€Έπ»♀
Khairat Kuma tunda ta haihu Babu abunda yashiga tsakaninta da Sani dukda taso hakan amma yabata ha'kuri akan tabari tagama wanka Kuma tagyra kanta sosai.
6angaren Salim kau Yana ba khairat kulawa itada Khalid ammafa babu maganar kashe arna.
Mmn khady ce ππ»
[10/3, 7:00 PM] Hayat: π *ALMAJIRIN GIDANA* π€¦π»♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* π₯°
*Daga Marubuciyar* π
*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now ππ»
*ALMAJIRIN GIDANA* π
Page 41
Bayan wani lokaci, misalin karfe 6 na yamma khairat tana zaune tana yanke farce, taji cikinta yad'an murd'a ahankali, gabantane yayi mummunan fad'uwa dan kusan kullum tunda cikinta yashiga wata na tara sai cikinta yad'an murd'a, gabanta Kuma saiya fad'i saboda ko kad'an bataso tariga Fauziyya haihuwa,
Yau abun ba iri d'aya bane Dana sauran ranakun, dan ciwon cikin 'karuwa yake da kad'an-kad'an.
Haka tayita daurewa tana cijewa, Koda Salim yadawo gidan wurin 'karfe tara na dare bata yarda yagane halinda take cikiba,
Wasa-wasa haka khairat tayita fama da ciwo har 'karfe d'ayan dare tun tanajin ciwon na d'agawa tahuta har bacci-bacci ke d'ibarta kafin yasake motsawa Kuma ta farka, yanzu yadaina dad'ewa daya motsa ko minti biyu ba'ayi yake sake tasowa, magowa tafarayi tsakar d'aki tana burgima, abun ba sau'ki. Takasa zaune takasa tsaye tsakanin falo da bedroom.
Tsakanin 'karfe shidda na yamma zuwa 'karfe shidda nasafe khairat tagama jigatuwa tafita hayyyacinta, dan za'a iya cewa batasan inda kanta yakeba.
Bayan Salim yadawo daga masallacine yashiga d'akinta yatadata tayi sallah dan yasan ba abun mamaki bane bata tashiba har yanzu.
Halinda ya isketa ciki ba 'karamin d'agamashi hankali yayiba, dan falo yayi Karo da ita a yashe ko d'aga kanta Bata iyawa, ga Jini sai faman bin 'kafafunta yake.
"Subhanallah, khairat ya akayi haka? Dama bakida lafiya baki gayamaniba"
Ido kawai take binshi dashi dankuwa babu baki.
Da sauri Salim yanufi d'akin Fauziyya yasanardasu halinda khairat d'in take ciki, Inna Rabi ce tayi saurin zuwa d'akin ta matu'kar tausayama halinda taga khairat d'in.
Kamata tayi takaita toilet tagyaramata jikinta tare da canja mata Kaya, dai-dai lokacin Salim yazo da mota Fauziyya da Inna Rabi suka Kama khairat d'in suka kaita mota tareda Inna Rabi suka tafi asibitin.
Fauziyya Kuma komawa tayi tagyra d'akin khairat d'in duk inda tabata da Jini ta goge, takunna tsintsiyar'kamshi tajawo d'akin sannan takoma nata d'akin, cike da tsananin tausayin khairat, "dama haka ake shan azaba wurin Haihuwa, ya Allah kakawomin tawa da sauki, itama Allah ya sau'ka'ka mata yasa ta haihu lafiya.
Zama Fauziyya tayi tanata tunani jikinta duk yayi sanyi,
Sani ne yashigo gidan, d'akin Fauziyya yanufa ganin d'akin khairat arufe, fitowa Fauziyya tayi tace "Sani Kaine"
"Eh wlh aunty, ina khairat ne"
"Khairat tana asibiti batada lpy, anama sa ran haihuwace"
"Haihuwa?" Sani yafad'i cikeda mamaki da tsoro da fargaba.
"Eh haka nake tunani"
"To Allah dai ya sauketa lpy" Sani yafad'i
"Ameen Sani, ammafa khairat tanajin jiki sosai wlh"
Haka suka d'anyi fira sama-sama, kafin Sanin yabar gidan.
Yana fita Kai tsaye asibitin yanufa, Salim da Inna Rabi ya iske bakin labour room, sai raba idanu suke suna jiran tsammani, zuwansu asibitin kusan mace bakwai ta haihu, Amma khairat har yanzu ba labari.
Wasa-wasa 'har 'karfe shidda na yamma khairat bata haihuba, duk wata dabara daya kamata likitoci suyi sunyi amma abun ya faskara, saboda haka khairat sai an dangano da theater room.
Likitan dakanshi yakira Salim yasanar dashi "a gaskiya matarka tana tsakanin rayuwa da mutuwa, cikin biyu dole ayi d'aya, kodai ayi gaggawar yimata CS aceto rayuwarta data abunda ke cikinta, kokuma ana gaf da rasa ranta itada d'anda ke cikinta, saboda ta galabaita yanzu batada 'karfinda zata iya Haihuwa da kanta, hakama d'anda ke cikinta yagama Shan wahala zai iya rasa ranshi idan aka 'kara Kai wani lokaci"
Cikin tsananin rud'ewa Salim yace "Doctor ayi duk abunda yakamata"
Nantake akaba Salim takarda yasa hannu, cikin 'kan'kanin lokaci akagama shirya kome aka fito da khairat cikin green d'in Kaya Kan gadon da ake tura marar lafiya, tagaban Sani aka wuce operation room da ita, binsu kawai yayi da kallo, yau ce rana ta farko da yaji tausayin khairat ya d'arsu a zuciyarshi.
Fauziyya tana gida hankalinta har yanzu ya'ki kwantawa wayar Salim takira Nan yake sanar da ita C's za'ayima khairat.
Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, shine abunda ta rin'ka mai-maitawa, fatanta Allah ya sauki khairat lpy itakuma Allah yakawomata tata da sauki.
Misalin karfe sha d'ayan dare aka fito da khairat daga theater, Alhmdlh anyi nasarar fiddo santalelen jariri mai Kama da khairat, kyakkyawa dashi zubin larabawa.
Godiya Salim yayima Allah, Nan take yakira Fauziyya yagayamata, tanuna farincinta sosai, sannan yakira mamarshi yagayamata haihuwar, har rawa tataka dan murna, yau tasamu jika, danma dare yayi sosai aida tataho asibitin yanzu, addu'ar samun lafiya tayima khairat itada abunda ta Haifa.
Hajiya Habi maman khairat Mama takira tagayamata haihuwar d'iyarta, Wai kada kaso kaga murna wurinta, ai da wannan daren kasa daurewa tayi saida ta dangano da asibitin taga lafiyar 'yarta da jikanta.
Washe gari tunda safe Fauziyya tashirya zuwa asibitin,
Salim yakaita bayan tahad'a masu kayan breakfast.
Kwance ta iske khairat Kan gado, ga baby kusa da ita abin gwanin birgewa, hannu tasa ta d'auki babyn ta'kuramashi Ido, azuciyarta jitake inama ace itace ri'ke da babynta haka,
Sannu tayima khairat, tayimata yajiki,
Amsawa tayi murya 'kasa-'kasa dan har yanzu tanajin jiki.
Sani ne yashigo d'akin, suduka binshi sukayi da Ido, gaidshesu yayi, Inna Rabi ta amsa, sannan yayimasu yamai jiki, kafin ya jawo kujera ya zauna,
Fauziyya tami'kamashi baby, jiki ba kyarma ya 'karba, zubama jaririn ido yayi Yana sa'ka da war-wara a zuciyarshi, Shima babyn bud'e idanunshi yayi kyar yazubasu Kan Sani.
Khairat Kuma tunda Sani yazo asibitin ya kar6i babyn gabanta ke wani irin mugun fad'uwa, gani take Kamar zaiwuce dashi yace yatafi da d'anshi.
Salim kuwa yasha hidima tundaga ranar da aka kawo Fauziyya asibitin har zuwa yanzu.
Mamar Salim tazo asibitin taga jaririn, sai nan nan take dashi, har tawai tarikayimashi dayana kuka tana wa'ka.
Kai d'an jikalle, jikalle na, waya ta6amin Kai yanzu in d'au 'kota π€£
(Kunjifa su Mama masu jika)
Kwanan khairat ukku asibiti, jikinta ya war-ware aka sallameta,
Kullum gidan Salim cike yake dayan ganin baby, 'kawayen khairat da 'kawayen Hajiya Habi, da mutanen maman Salim sai zuwa ake barka.
Sati na zagayowa akasha shagalin suna, jariri yaci Suna Khalid, shagalin sunafa anyishi ba Kama hannun yaro, dan Salim yasaki bakin Aljihu, mai jego anyi gwanin kyau kamar ba'itabace ta haihu.
*Bayan sati biyu*
Khairat na kwance falo Kan kafet d'in tsakiyar d'akin, Khalid na kwance gabanta yanata yan motse-motsenshi na jarirai, yayi 'kiba gwanin sha'awa ya'kara fari ga sumar kanshi kwance lub, irinta larabawa da fulani.
Sallamar Sani tajiyo, gabanta ya fad'i tayi saurin tashi zaune tad'auki Khalid ta rungumeshi jikinta.
Tana jiyo sanda Sani ya gaida Inna Rabi, Yana Kuma tambayarta ya Khalid, tace "lpy lao suna ciki shida mamarshi"
D'akin Sani yashiga Kai tsaye ya iske khairat ri'ke da Khalid, hannu kawai yami'kamata Alamar takawoshi, ba musu tami'kamashi jikinta na kyarma.
Kallon Khalid Sani keyi yanajin wani irin soda 'kaunarshi nashiga zuciyarshi.
Khairat kuma 'kuramashi Ido tayi, ko kad'an bataso Sani Yana yawan zuwa ganin Khalid, ganitake kamar zai rabata dashi, gashi itama tad'auki son dunyi tad'orama Khalid d'in, jitake kamar idan Sani ya d'aukeshi zai tafi dashi ne.
6angaren Fauziyya har yanzu Babu wani labari har gashi Khalid yakai wata d'aya a duniya, yayi wata irin 'kiba idan ka kalleshi dole ya burgeka kyakkyawa dashi.
________________________________
Yauce ranar zuwa awon Fauziyya saboda haka tun 'karfe takwas na safe tabar gidan zuwa asibiti.
A asibiti kuwa anatayima mata awo har layi yazo Kan Fauziyya, tana hawan gado narse d'in tafara aunata, saita tsaya tace "miye sunanki ma?"
"Sunana Fauziyya"
"Am malama Fauziyya bakijin wani ciwo haka ajikinki?"
"Banajin kome" Fauziyya tafad'a tana kallon narse d'in.
"To Amma Kuma gashi kinfara Labour,"
"Labour kuma, Kai gaskiya badai labour ba, nifa ko ciwon Kai banaji"
Murmushi narse d'in tayi tace "kije labour room kawai",
Murmushi Fauziyya tayi, itafa abun mamaki yake Bata wai taje labour room, bayan tasan ita batajin ciwon kome, Kuma tasan labour fa ba wasa bane barantana taga yanda khairat ta wahala.
Haka dai nurse tamatsa mata sukaje labour room sannan tace yakamata takira wani daga gida dan bazai yiyu ace tahaihu babu Kowa wurintaba.
Haka Fauziyya takira Salim tagayamashi, duk da dai tana kokonton azuciyarta,
Inna Rabi Salim ya d'auka suka nufi asibitin, kafin yazo Kuma takira mamarta itama ba dad'ewa tazo asibitin, mamar Salim ma da sauri tazo asibitin Dan Salim d'in takira yake gayamata Yana asibiti Fauziyya ce zata haihu.
*Munayimaku tallar shahararren man gashi Mai suna ASHKHAD AFRICAN HAIR GROW, man gashine Wanda akahad'a da sinadaran gyaran gashi yanasa tsawon gashi da tsantsi Yana hana karyewar gashi sannan uwa uba Yana fatattakar dandruff daga cikin gashi komen dad'ewarsa,sannan Yana 'kara bakin gashi, wannan man Yanada kyau wlh duk wacce tayi amfani dashi saita Kara nemansa Kuma saitaba 'kawayenta da 'yan'uwanta labari* π©π»π©π» *Hajiya kisiya kiga yanda gashinki zaikoma abin sha'awa ke kanki sai kinji dad'i* π
*Idan Kuna bu'kata serious ku tuntubi wannan no*ππ»
08166169254
Mmn khady ce
[10/3, 7:00 PM] Hayat: π *ALMAJIRIN GIDANA* π€¦π»♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* π₯°
*Daga Marubuciyar* π
*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now ππ»
*ALMAJIRIN GIDANA* π
Page 43
*Saboda Jin dad'in comment dinku nakaramaku wannan*ππ» *BONUS*
Bayan kwana biyu dayin suna Fauziyya na kwance bedroom tana bacci Yan biyu Kuma *Hanif & Hanifa* suna wurin Inna rabi, dan tunda aka haifesu Itace mai kula dasu,
Khairat na tsakar gida tana goye da Khalid tana shanya kayanshi data gama wankewa Kan igiya, Sani yashigo gidan.
Kallonshi khairat tayi tace "gaskiya Sani munyi fushi"
"Fushi Kuma nami"? yafad'a fuskarsa babu alamar fara'a Wanda ganin haka yasa khairat Shan jinin jikinta, Amma saita daure tayi tamaza tace "bakazo ganin two wins ba mana"
"To ai gani nazo yanzu"
Khairat dakanta tashiga d'akin Fauziyya, Inna rabi ta iske falo tare da two wins d'in tace "Inna dama Sani ne yazo ganin baby's"
"To yashigo Mana" Inna Rabi tafad'a tana bin khairat din da kallo...
Fita khairat din tayi minti biyu suka shigo tana gaba Sani na bayanta, Zama sukayi suduka Sani ya gaida Inna Rabi tareda yimata barka, ta amsa cikin fara'a tami'kamashi Hanif yagani sannan ta karbeshi tamaidashi takuma mi'komashi Hanifa.
Ganin yarannan ba 'karamin d'ga hankalin Sani yayiba, Amma ba yanda zeyi yariga yad'aukarma kansa Al'kawarin duk ranarda Fauziyya ta haihu yahakura da ita.
Fauziyya najin shigowar Sani Amma tayi shiru bata fitoba, ita batamaso yazo ganin baby's ba dan batasan da mugun abunda yazoba, Amma koma miye tayi tawakkali ga Allah bata cuci waniba tasan Allah bazai bari wani ya cutar da itaba.
Haka Sani yafita daga d'akin ranshi amatu'kar bace, suna fitowa tsakar gida yami'ka hannu khairat ta sauko Khalid daga baya tami'kamashi, ya rungumeshi jikinshi Yana 'karajin 'kaunarshi azuciyarshi, sannan ya sumbaceshi a goshi kamin ya mi'kamatashi yabar gidan.
*Bayan kwana biyar*
Yau an d'aura auren Sani da Zuby, anyi shagali dai-dai gwar-gwado, ango Kuma yatare gidan amaryarsa, ansha amarci dukda dai dama andad'e dashanye amarcin tun kafin auren.
Bayan sati biyu khairat tagama wanka, yanzu Khalid yanada wata biyu yayi wayo ya 'kara girma, Hanif da Hanifa Kuma sunada wata d'aya, suma sunyi wayo sosai ga wata uwar 'kiba dasukayi Kamar yan wata ukku, kyawunsu ya'kara fitowa Hanif Haskenshi yakara fitowa dan yafi Hanifa haske dama tunda aka haifesu.
Kulawa suke samu sosai daga wurin Salim, baya nuna banbanci duk abunda zai siyo Wanda ya danganci yara guda ukku yake siyowa, haka suma iyayen khairat da Fauziyya Yana kamanta Adalci tsakaninsu wuri d'ayane kawai baya adalci shine har yanzu baya iyaji zai iya kusantar khairat.
Khairat Kuma ha'kurinta yagama 'karewa, saboda haka tun kafin Salim yafita ta tambayeshi zataje gida takaima mama Khalid, bai hanataba saboda haka Yana fita tada'uko waya takira Sani.
Ringing d'aya yad'aga "Hello"
"Hellow Sani kana inane"
"Ina gida ya akayi"
"Plz inaso dan Allah ka taimakamin yau kome kakeyi kabani lokacinka muhad'u gidan Zuby"
Shiru Sani yayi Kamar baiji abunda tafad'aba saida yaji tana fad'in Hello, sannan yace "inaji"
"Ok kaji abunda nafad'a ko"?
"Eh naji amma gaskiya bazanje gidan Zuby ba kawai muje ki Kama mana d'aki a hotel"
"Ok to idan hakan yayima badamuwa sai muhad'u a Al-bustan Hotel, misalin karfe hud'u na yamma Dan Allah kadafa inyita jiranka"
"Indan wannan kada kidamu kinsanni banida African time"
"To shikenan sai mun had'un"
Suna gama waya tashiga wanka tahau shiri, sannan tashiryama Khalid cikin wasu green d'in Kaya Riga da wando na yara yayi kyau sosai.
'karfe hud'u saura minti shabiyar tafita daga gidan, bayan tayima Inna Rabi da Fauziyya sallama akan zataje gidansu.
'karfe hud'u dai-dai napep ya sauketa hotel d'in, batayi minti ukku da zuwaba Sani yazo, tare suka jera har cikin hotel din, khairat takama masu d'aki suka kar6i key din suka wuce.
Suna shiga d'akin khairat batajira wani abuba ta sauke Khalid dake goye bayanta yanata bacci ta kwantar dashi.
Tafara cire kayanta, Sani yanata kallonta, saida tagama kaf tafad'a kanshi tafara kissing d'inshi tako'ina saida tagama cajamashi kwalwa sannan yatashi yacire kayanshi suka fara abunda suka Saba.
Haka suka ida cinye wannan lokaci suna aikata masha'a basu bar hotel d'inba sai 'karfe tara na dare, khairat tawuce gida tana shiga gidan Salim na dawowa.
Shikuma Sani daga hotel d'in gidan amaryashi zuby ya wuce.
Lokacinda yakoma tagama shiryamashi abinci lafiyayye, yazauna yakwashi gara, bayan sungama sunkoma bedroom suka kwanta,
Zuby tanuna tana bu'katarshi amma ya'ki kulata duk yanda takai da kwakwa dole tahakura amma ta dasa ayar tambaya akanshi, tasan kila yau yahad'u da khairat, Dan idanba hakaba tasan Sani kullum sai yayi, amma bawani Abu aidama tare tagansu, wannan ba abun damuwa bane.
Tundaga wannan lokacin Sani yazama tamkar Mai mata biyu, yau khairat gobe zuby.
Zuby tasan da haka amma koda wasa bata ta6a nunama Sani tasaniba,
Khairat dai batasan da wata ala'ka tsakanin Sani da Zuby ba, barantana Kuma tasan sunyi aure.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, yauda gobe asarar mai rai.
*BAYAN SHEKARA BIYU*
Tsarin gidan Salim ya canja baki d'aya, sakamakon cigaba daya samu wurin aiki, kud'i sun zaunamashi sosai,
Baki d'ayan gidan an canja mashi design, kowace anyimata part d'inta
Sai motoci guda biyu da Salim yasiya, daya saboda hidimar gida, d'ayar Kuma Yana fita aiki da ita kokuma wata zuwa unguwa nafita kunya.
part d'in Fauziyya an fidda d'akin Hanif da Hanifa anzubamasu Kaya kome guda biyu abun gwanin birgewa, yaran sunyi wayo sosai idan kagansu zakayi zaton sunfi shekara biyu.
Hakama Khalid ya girma sosai kyakkyawa dashi, fari tas kallo d'aya bazakace bahaushe bane, zakayi zaton irin 'ya'yan larabawa ne.
wata irin sha'kuwa sukayi da Hanif da Hanifa, bacci kad'ai ke rabasu, wani lokacima ko baccin baya rabasu dan wurinsu Hanif yake kwana, domin yafi samun kulawa anan fiyeda wurin khairat.
Hanifa tunda tataso yarinyace Mai shegen wayo da surutun tsiya, Hanif Kuma akwai son 'ya'uwanshi yayinda Khalid ya kasance so silent magana batacika damunsaba, kullum zaka ganshi shiru kamar marar lafiya yanayinsa, idan kaganshi cikin wal-wala to Yana tare da 'yan'uwanshi Hanif da Hanifa.
Khairat tuni tabar tafiya da Khalid unguwa tunda ta yayeshi, nan take barinshi wurin Fauziyya tayi tafiyarta yawon bin hotel itada Sani.
Inna Rabi Kuma ana yaye twowins takoma 'kauye sai dai tana zuwa lokaci zuwa lokaci tana dubasu, dan zamanta gidan Salim ba'karamin sha'kuwa sukayi da Fauziyya ba.
___________________________
Sani zaune tsakiyar carpet dinda ke shinfed'e tsakiyar falon, kulolin abincine gabanshi zuby Kuma tana zaune gefenshi da alama abinci suka gama ci,
Fira suke tabawa kad'an kad'an, cikin firar tasu zuby tasako maganar zuwa garinsu Sani.
"Waini baby yaushe zamuje garinnan naku naga tunda mukayi magana shekaranjiya bakacemin komeba, yakamata ace nasan 'yan'uwanka koda mutum d'ayane kodan abunda nake d'auke dashi, kaga yanzu cikinnan harya shiga wata hud'u baikamata ace na haihu babu danginkaba, Kuma kaga yakamata iyayenka Susan kayi aure tunda kaga basusan da maganar aurenmu ba".
Saida takai aya sannan yace "na mantane ban gayamakiba tun ranar dakikayimin magana natsara yanda zamuyi tafiyar, gobe zamu tafi inshaAllah saboda haka ki shirya mana kome yanda yakamata.
Wani irin dad'i zuby taji Kuma tundaga lokacin tahau Shirin tafiya.
Ranar khairat da Sani suka had'u hotel kamar yanda suka Saba, bayan sunagama she'ke ayarsu yake sanar da ita maganar zuwanshi garinsu, fatan Alkhairi tayimashi sannan tanuna irin missing d'inshi dazatayi, kud'i mai yawa tabashi tace yayima mutanen gida tsaraba.
Washe gari misalin 'karfe takwas na safe suka fito cikin motar zuby zasuyi tafiyar, tun kafin subar garin suka shiga wani 'katon super market zuby tayima iyayen Sani tsaraba saida tacika but da kayan masarufi sannan suka d'au hanya.
Tafiya suke suna labari, cikin so da 'kauna da kulawa da juna hankalinsu kwance, zuby itace ke driving saboda tafi Sani kwarewa dukda Shima ya iya ta koyamashi Amma har yanzu hannunsa bai gama fad'awa ba.
Tunda suka fita gari zuby tafara sharara uban gudu kamar zata tashi sama dan taga titin baida yawan motoci, wata mota take ko'karin wucewa, saiga wata motar tataho da gudu saitin hannunda zata hau, cikin zafin nama ta kauce sai dai akayi rashin sa'a motar takwacemata tanufi daji, 'karshe takaima wani 'katon icce Karo, kafin kace me jini yafara zuba ta wurin 'kafar motar....
Sani da Zuby Kuma duk iya hangenka baka ganinsu cikin motar.
Mmn khady ce ππ»
[10/3, 7:00 PM] Hayat: π *ALMAJIRIN GIDANA* π€¦π»♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* π₯°
*Daga Marubuciyar* π
*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now ππ»
*ALMAJIRIN GIDANA* π
Page 44
*MASU SIYARMIN DA LITTAFI ALLAH YA ISA BAN YAFEBA, KUMA INSHAALLAH KUD'IN BAZAI MAKU ALBARKA BA*
Motar da abun yafaru Kan idonta ce tafara tsayawa kafin wasu motocin duk su tsaya domin taimakon wad'anda sukayi accident d'in.
Kafin ayi wani Abu har police sunzo, nan aka samu aka fiddo Sani Babu Rai tare dashi amma baiji ciwo ko kad'an ba.
Zuby Kuma ansha wahala kafin asamu a fiddota can 'kasan seat itama dai Babu rai amma bataji ciwoba sai Jini dake bin 'kafafunta.
Asibiti aka wuce dasu, kasancewar basuyi nisa dagariba shiyasa aka dawo dasu babban asibitin dake garin, emergency room aka nufa dasu ba Kamar zuby tana matukar bu'katar taimako.
Likitoci ne suka taru akansu domin ceto rayuwarsu, kusan awa biyu kafin asamu numfashin Sani yadawo jikinsa.
Zuby Kuma dama basu dad'e dazuwa asibitin ba ta farfad'o sai dai tayi asarar cikin dake jikinta.
Kwanan Sani da Zuby biyu a asibiti aka sallamesu suka dawo gida, bazaka kallesu kace sunyi wani accident ba, dan babu ko kwarzani a jikinsu, sai dai rashin gudan jininsu dasukayi, Wanda hakan ba'karamin ciwo yayimasuba, bama Kamar Sani Allah yasanyamashi son cikin zuby tun kafin yazo duniya, ashe dai bazai rayu ba, Amma ba yanda zasuyi dole Susama ransu hakuri Allah zai sake basu wani.
Haka suka dangana suka cigaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali.
6anagaren khairat Kuma yau sati biyu kenan da tafiyar Sani kullum saita Kira wayarshi yafi a 'kirga Amma baya shiga, sakamakon 6acewar wayarsa lokacinda sukayi accident, hakan ba 'karamin damunta yakeba saboda haka yau ta yanke shawarar fita ko Allah zaisa taganshi kokuma taji labarinsa.
A waya takira Salim tagayamashi zataje gidan zuby, bai hanataba saboda haka tahau shiri, Khalid sai binta yake yana cewa mama Ina zuwa, Amma ko kallonsa batayiba tacigaba da shirinta.
Cikin wasu fitinannun riga da siket na wani had'adden material blue, sannan tadawo pink din gyale da pink din takalmi da jaka ta Sanya, kalaluwan turare tafeshe jikinta dashi, tafito daga sashenta Khalid sai binta yake Yana fad'in inazuwa, tureshi tayi tace "Kai kada kadameni ko kaga Ina fita dakaine, wuce can katafi wurinsu Hanif kayi wasa"
Sukuku yanufi sashen Fauziyya Yana hawaye, koda yaje baishigaba sai yatsaya 'kofar falon.
Haniface tafito daga falon taganshi, Kama Hannunshi tayi tace "Khalid waye ya bigeka? Momynka ce ko? Taho mutafi mu momynmu bata duka"
Binta yayi suka wuce d'akinsu, suka had'u da Hanif suka Fara wasa, cikin d'an lokaci Khalid ya manta da wani bacin rai.
Khairat kuma tana fita daga gidan Kai tsaye makarantar su sani tanufa gidansu na *ALMAJIRAI* ta tambaya ko yananan,
Nan suka sheda mata ai Sani yafi shekara biyu rabonsa da zama cikin wannan gidan.
Tambaya tayi ko sunsan inda yakoma, sukace gaskiya Basu saniba, da dai abokinsa Basiru nanan daya gayamata domin shine kad'ai yasani.
Haka tabar wurin ranta a dagule dan taso ace taga Sani yau, yanzu Kuma Ina zata nufa.
Napep ta tsaida tashiga bayan tagayamashi inda zai kaita suka d'au hanya.
Sani Kuma Yana tare da Zuby d'inshi dan tunda sukayi accident suka dawo baya fita ko Ina kullum Yana gida.
Zuby Kuma bata gajiya da abunda aka Saba, badare ba rana kullum aikin kenan.
Yauma Kamar kullum kwance suke Kan gado suna Raya saunnah, tunda aure ne sai dai muce raya Sunnah.
Lokacin khairat tashigo gidan tanata faman kwad'a sallama amma shiru ba'a amsaba, Zuby da Sani sunyi nisa sun Lula acikin duniyar ma'aurata.
Gajiya tayi da sallama tashiga falon bataga kowaba, bedroom tanufa batareda wani tunaniba.
Wata irin 'kara tafasa tareda dafe kanta da hannu biyu sakamakon mummunan ganin datayi tsakanin Zuby da Sani.
Baya tayi dagudu tana niyyar barin gidan, da sauri Sani yasa boxer yabiyo bayanta lokacin harta Kai bakin get tana Shirin fita yayi saurin ri'keta "khairat.... khairat.... Kitsaya mana, ki tsaya ki saurareni.
'ko'karin kwace hannunta takeyi tana kuka Kamar ranta zai fita " mezanji Sani ka cuceni ka kasheni da raina, ashe dama zuby kake nema..... innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un"
Wata irin tsawa Sani yadaka mata "ke dallah kirufama mutane baki, kiwuce mushiga daga ciki muyi magana kada kitara mana mutane.
Binshi tayi ciki, zuby Kuma tunda khairat takamasu jikinta ke 6ari tana fad'in "shikenan nashiga ukku na lalace, asirina yagama tonuwa yau nabani na lalace.
Suna shigowa tayi firi-firi da ita Kamar kicemata tak ta ranta ana kare.
Zama Sani yayi kan kujera yacema zuby tami'kamashi rigarshi, jiki na kyarma taje ta d'auko takawomashi yasanya.
Khairat na tsaye tana kallonshi, zuby Kuma ta'ki yarda su had'a Ido da khairat.
Sani ya kalleta yace "ki zauna mana"
"Zama, ai banga ta zamaba cikin wannan 'kazamin gidan, yanzu Sani miye baniyima mena rageka dashi amma bazaka iya ha'kuriba ka danne kwad'ayinka saika 'kara da Zuby, tafad'a tana kuka.
Sannan tacigaba da magana cikin masifa da d'aga murya "Sani kacika munafikin Maci amana, ka cuceni ka cuci rayuwata Allah ya isa kaci amanata.......
"Tassss kakeji ya d'auketa da wani lafiyayye mari, cikin tsananin huci da 6acin rai yace "akwai babbar Maci amana irinki Mai Zina da aure, munafika annamimiya, to Bari kiji in gayamaki zuby ba nemanta nakeba aurenta nayi"
Zaro Ido khairat tayi cikin tsananin firgici tace "Aure.....aurefa kace Sani, zubyn ka aura"
"Tabbas Aure" Sani yafad'a cikin gadara.
Dariya khairat tayi Mai Kama da ta6in hankali tace "to kasani Sani ka auri mutuwarka da kanka, muna zamanmu kaje ka kwaso mana 'kamaya-maya saikutashi mu d'unguma muje asibiti likita yayita aunamu Kamar yadi"
"Mi'kewa tsaye Sani yayi yace "ke dakata khairat bangane inda maganaki ta dosaba.....
Kafin yarufe baki khairat ta kar6e "to Zuby dai 'kanjamau kegaret.......
Kafin ta ida fad'i Sani yaji kanshi na juyamashi yafara gani wani duhu-duhu kawai sai gani sukayi yafad'i sume.
Zuby naganin haka tayo Kan khairat gadan-gadan tacimata kwala, tana fad'in "wlh idan Kika kashemin miji saina kasheki, muguwa."
Itama khairat kwalar Zuby taci tace "gakinan muguwa azzaluma kinsan kinada HIV Kika aureshi danki gogamashi.......
"Na aura d'in ba son abun duniya yakawoshiba, ko kinsan tsakanin aurenmu zuwa yanzu nawa nakashemasa...
"Koma nawa Kika kashemasa Ina ruwana, Nikuma dakika gogamawa ubanme Kika bani"
"Uban mi zanbaki kuwa, sakamakon daya dace dake ne wannan, kina nufin zakiyi bariki ki wanye lapiya, harma kisamu sakamakon samun miji Kamar Salim...
Wani mugun naushi khairat tayima zuby abaki, Nan take ha'korinta guda yacire jini yafara ambaliya.
Itama zuby dukan khairat d'in take, haka sukayita danben bala'i cikin gidan Babu Mai rabasu, ga Sani kwance a sume harta kanshi sukebi suna takawa wurin fad'a.
Kafin kace mi sunyima kawunansu muguwar illah, khairat tafi zuby 'karfi saboda haka zuby tafi jin jiki, sai dai wani mugun cizo da zubyn ta labtama khairat a kafad'a Wanda saida taciro tsokar wurin.
Kayan jikinsu Kuma sun yayyage sunyi fata-fata.
Sani dai Yana kwance rai hannun Allah,
Suma dasuka gaji da damben kowace zubewa tayi tana maida numfashi Babu mai iya tada wani cikinsu.
Azabar ciwon da bakin zuby keyi sakamakon fita da ha'korinta yayi shiyafi kome addabarta, rarrafawa tayi ta d'auko wayarta takira number Alhj Haladu wani abokin tambad'ewarta ne tagayamashi sunanan gida itada mijinta ba lafiya ya taimaka yazo yakaisu asibiti.
Minti ishirin Alhj Haladu ya iso gidan, yayi mamakin yanda yasamesu Kamar wad'anda sukayi wani mummunan had'ari.
Haka ya kwashesu yazuba mota yakaisu general hospital, akace baza'a kar6esuba sai anzo da police,
Ganin suna neman su jazamashi wata fitinar yasa yakaisu wata asibitin kud'i Nan aka kar6esu aka Fara Basu taimakon gaggawa, sannan khairat taro'ki likita dayayimasu awon HIV suduka,
Jininsu aka eba akaje lab, suduka sakamakon d'ayane suna d'auke da cuta Mai karya garkuwar jiki.
Sai dare sannan Sani ya farfado, yaso a sallameshi likita yace gsky baza'a sallameahiba akwai sauran gwaje-gwaje da akeson yimashi, khairat da zuby Kuma tun ranar aka sallamesu,
Khairat tawuce gida cikin tsananin tashin hankali, Wai yanzu itace d'auke da cutar 'kanjamau, Amma Zuby tacika babbar muguwa azzaluma.
Zuby Kuma Zama tayi da niyyar jiyyar Sani, sai dai tunda yaji sakamakon da likita yafad'i na Yanada 'kanjamau yasa yaji wani mugun tsanar zuby muddin Yana ganinta gabanshi zai iya rabata da numfashinta saboda haka korata yayi yace taje gida kawai bayason ganinta.
Hankali tashe zuby tafita daga asibitin cikin tsananin rud'ewa batako kallon gabanta tahau titi tana tafiya kamar wata Zararra by mistake kuwa wata mota tayi ciki da ita, Nan take tace ga garinku Nan.
Allah sarki Zuby anrigamu gidan gaskiya, sai muce Allah ya kyauta namu zuwan.
Mmn khady ce π€Ό♀
[10/3, 7:00 PM] Hayat: π *ALMAJIRIN GIDANA* π€¦π»♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* π₯°
*Daga Marubuciyar* π
*Siyasa ko soyayya*
*Duniya Juyi*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now ππ»
*ALMAJIRIN GIDANA* π
Page 45
ππππππππ
*Kuyi hakuri kunjini shiru kwana biyu hakan yasamu saboda wata Yar 'karamar matsala, bayan haka Kuma zanyi amfani da wannan damar wurin kawo 'karshen wannan labari, Amma kuyi hakuri zan takaita 'karshen labarin saboda wasu 'yan dalilai*
Bayan kwana biyu Sani kwance Kan gadon asibiti Alhmdlh yasamu sauki sosai,
Likitane yashigo d'akin hannunsa d'auke da wasu takardu,bayan sun gaisa da Sani yayimashi ya jiki Sani ya amsa "jiki Alhmdlh Babu abunda ke damuna"
Gyara zaman glass d'in fusakarshi yayi yace "sakamakon gwaje-gwajen damukayi, bayani ganowa damukayi kana d'auke da cutar 'kanjamau, sakamako na biyu Kuma ya nuna bazaka iya 'kara hauhuwa ba sakamakon buguwa dakuma tsananin razana dakayi"
"Me....." Me kake fad'i haka likita, kana nufin yanzu nida Haihuwa har abada"?
"Kwarai kuwa haka sakamakon ya nuna" likitan yafad'a tareda mi'kama Sani takardun sakamakon yafice daga d'akin.
Hankali tashe Sani yabar asibitin 'kafarsa ko takalmi Babu, tafiya yake batareda yasan inda yake saka 'kafarsaba, ikon Allah ne kawai yajaishi gidan Zuby, Yana zuwa ya tarar da mutane dankam 'kofar gidan 'yan zaman makoki, kafin ya isa wurin yaji wani dattijo na fad'in "Allah sarki zubaida anrigamu gidan gaskiya Allah jikanta da rahama" da wannan magan-ganun Sani ya tabbatarba kanshi da mutuwar zuby.
Juyawa yayi yabar wurin batareda yashiga gidanba kokuma yayima wani magana, Babu Kuma Wanda yalura dashi a wurin dukda dama bakowabane ya sanshi.
Shagonsu yanufa wurin Basiru dan yanzu Babu abunda yafi bu'kata sai kud'i, zuwa zaiyi ya 'karbi kud'insa ya tattara yanashi yanashi yaje wurin khairat ya amshi sauran farincikin daya ragemashi a rayuwa wato Khalid yawuce 'kauyensu.
Khairat tana zaune d'akinta cikin kwana biyu duk tabi ta lalace tayi ba'ki, hankalinta yagama tashi,
Ga maganin HIV din data karba asibiti amma batada kwanciyar hankalin dazatasha, dan tunda tadawo daga asibi da maganin da sakamakon gwajin da'akayimata duka tahad'a ta ajiye Kan kujera a falo Tama manta inda ta ajiyesu.
Khalid Yana d'akin Fauziyya wurin su Hanif suna wasa wani Zazzafan zazzabi ya rufeshi har Yana firgita, haniface takira Fauziyya tagwadamata Khalid d'in hankali tashe ta d'aukeshi takaishi d'akin khairat tagayamata bayada lpy, amsarshi kawai khairat tayi ta kwantar dashi dan batada nutsuwar dazata bashi wata kulawa.
Bayan azahar Salim yadawo gida kamar yanda yasaba,
Fauziyya ta gayamashi Khalid fa bayada lafiya Kuma tund'azu nakaishi wurin mamarshi Amma banga tafito takaishi asibiti ba"
'dakin khairat d'in Salim yanufa Dan ganin jikin Khalid d'in.
Yana shiga idonshi ya sauka kan ledar maganin khairat dake kan kujera, har zai wuce saikuma yadawo Yana bud'awa yafara duba magungunan danshi baitaba ganin irinsuba, tunani yafarayi wannan maganin Kuma na miye haka 'kara dubawa yayi ya d'auko takarda Mai d'auke da sunan khairat dakuma sakamakon gwajin HIV tana d'auke dashi.
Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un yafara maimaitawa, da sauri khairat tafito falo Jin yanda Salim ke rafka salati, ganin ledar maganinta gabanshi hannunshi Kuma d'auke da takardar gwajin yasa ta razana tayi hanyar waje.
Da hanzari Salim ya damkota ya wankemata fuska da lafiyayyan mari yace "khairat gayamin gidan ubanwa Kika kwaso wannan cutar?"
Zubewa khairat tayi gabanshi tana kuka, shima Zama yayi kan kujera jikinshi sai 6ari yake.
Wayarshi yafiddo yakira mamarshi yace tazo gida ba lafiya, sannan yakira Hajiya Habi mamar khairat itama yagayamata yanda yagayama mamarshi.
Ba dad'ewa suduka sun halarci taron, Fauziyya mamaki take Wai miye ke faruwa haka taga mamar Salim da mamar khairat sunzo, kodai jikin Khalid ne yayi tsanani, saboda haka itama sashen khairat tanufa Dan taji ko miye.
Ko minti goma dashigowa Fauziyya batayiba Sani yashigo gidan Babu ko sallama yayi wani wurjiga wurjiga kafa ba takalmi, kamar wani Mai tabin hankali.
Yana shigowa kallo yadawo kanshi, shima kallo yabi duka mutanen dake falon sannan yace nagodema Allah Dana iske wannan taron, saboda haka zanyi amafani da wannan damar ingayamaki irin mugun abunda muka d'auki shekara da shekaru muna aikatawa nida khairat.
Nan Sani ya zayyane masu kaf labarinshi tun kafin zuwan khairat gidan har zuwanta har Kuma zuwa lokacinda ake yanzu dayazo amsar d'anshi.
Arazane mamar Salim tace 'kanjamau" innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un Salim Babu dai abunda yashiga tsakaninka da ita"
Murmushi takaici Salim yayi yace "Ina kyautata zaton haka"
Mama tace "maza ka rubuta mata takardar saki yanzu kabata sutafi can su karata tsiyarsu"
Bama saina rubutaba khairat kije na sakeki saki ukku, Kuma kije keda Allah.
Kaikuma Sani kaci amanata kaci amanar matata inshaAllah sai kaga sakamako tun aduniya.
Mamar khairat kuka kawai take sai hakuri takeba mamar Salim.
Mama tace Babu wani hakurin dazanyi ki kwashi gayyar tsiyarki kubarmin gidan d'ana.
Sani Kuma kallon khairat yayi yace kafin kitafi inaso kibani d'ana.
Sai lokacin khairat tatuna da halinda tabar Khalid ciki, da sauri tashiga d'akin.
Wata irin razannaniyar 'kara tasaki domin ganin Khalid datayi Babu Alamar rai tare dashi.
Allah yaraba gardama kenan, Khalid yarigamu gidan gaskiya bayada rabon ganin takaicin rayuwa.
Da sauri Haj Habi tanufi d'akin khairat ta iske tanata fizge kayan jikinta tana wata irin dariya, da alama dai ta haukace.
Sani Kuma Nan aka gayamashi Khalid yamutu, innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un yafad'a baijira wani bayaniba yabar gidan.
Kai tsaye sahgon su yanufa Yana zuwa kuwa ya hango dan-dazon mutane anata zuba ruwa shagon yagama 'konewa 'kurmus.
Yana ganin haka bai Ida karasawa shagonba yayi baya yahau titi Yana tafiya tsakiyar titin, wata katuwar mota tazo tabi ta kanshi, Nan take ya margaya, wannan shine karshen masu cin Amana.
*ALHMDLH ANAN NAKAWO 'KARSHEN WANNAN LITTAFIN, SAIKUMA ALLAH YASAKE HADAMU WANI LOKACIN MAMAN KHADY KEMA MASOYA FATAN ALKHAIRI*
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group
WHATSAPP NO:+2349030159301