Waje ya kafa ya ingizata ya kulle kofan da karfi dan muhibbat ta riga ta kaishi makura...sai a wannan lokacin hajiya mama ta fito kasancewar karar kulle kofan da ya dawo da hankalinta daga tunanin yanda zata bullowa hidimar bikin yaran.
Dariya Amal takeyi sosai dan abin yazama hauka acewarta.
Kai kai meke faruwa ne wai lafiya?
Areef ranshi ya baci yace hajiya mama wlh wata dabbace take shirin shigo mana gida amma munyi maganinta.
Dariya ya bata itama, tace dabba kuma Areef...to Allah ya kyauta, muje inda magana daku ma.
Okey to hajiya mama tamu...wlh da gangan kika dauki mai gadi a gidan nan ashe munada wanda yafi karfin maigadi a gidan tunda har ya iya fada da kuranya...Amal ta fada tanawa Areef gwalo.
Harara ya mayar mata fuskarsa cike da shagwaba.
Am srry ma prince..ta fada can kasa kasa tareda kashe masa ido.
Zama sukayi baki dayansu, inda hajiya mama ta bukaci suyo list din kayan aikin abinci da ake bukata, zata bama baaba wato sabuwar mai aikinta da aka kawo mata ganin Amal takusa tafiya.
Okey hajjaju zamuyo maki list mai kyau tunda hidimar tamu ce munason gayu acikinta...Areef ya fada cikin zakuwa.
Harara hajiya mama ta mayar masa tace kanku dai akeji...ta shige daga ciki.
Areef ya gyara zama yace yauwa princess kinga hidima dai ta kunno kai, so inaso idan kinsamu chance muje ki hada lefenki ko.
Kunya taji ta kamata..ta amsa da oryt ma prince.
*** *** *** *** ***
Ran muhibbat yayi matukar baci,ganin yanda Areef da take mutuwar so amma yayi mata wannan korar karen tareda wulakanta ta agaban Amal, musamman da Amal ta nuna halin ko inkula akan lamarin...tun a lokacin ta saduda inda ta yanke shawarar tattara kayanta ta koma jihar su dan a wannan lokacin babu wani karatu da takeyi face yawan banza....a cewarta.
Ya zama dole na saduda na yiwa kaina fada don son maso wani ba karamar illa yake haifarwa ba, naga tsantsar kauna naga yarda da aminchi, wanda yasa idona ya kulle makanta tayi mani katutu nakasa gane daraja da muhimmanci na AMINTAKA...dake tsakanina da Amal Abdallah AYUD2, kaicho na...ta sake fashewa da kuka inda ta fadi a bakin gadonta ta cigaba da rewa kuka da zubda ruwan hawayen nadama tamkar har azuci...na tabbata yanzu Amal bazata saurareni ba, amma zan bata nan da sati daya kafin na wuce don neman yafiya daga gareta dan nasan halinta ba karamar miskilar mace ba...ta fada a ranta.
Haka ta mike ta dauro alwala dan gabatar da sallah nafila ta nemawa kanta gafara gun ubangijinta akan cin amana da taso yi inda reshe ta juye da mujiya, sannan ta rokawa kanta Allah ya yaye mata son Areef aranta.
Kwanci tashi babu wuya wajen Allah, yau saura kwana takwas bikin Areef da Amal...babu abinda ke wakana a tsakanin masoyan face tsantsar kauna da kulawa da juna, wanda basa son rabuwa koda na minti daya ne.
Areef jingine a jikin mitarsa kirar Hondi baka yana wasa da keys na motan, tattaunawa sukeyi shida abokinsa wato Saleem da sukayi karatun sec sch a ethopia.
Wai groom ina kabaru bride din dan nasan idan naga wata to tabbas zanga zarah.
Hhhh.. Baka rabo da zolaya and kasa mana ido dayawa fa...ya fada yana nunashi kyakkyawar fuskarsa cike da annuri...sunje karbar dinki ita da frnd dinta salma mana.
Kace mun ita da namecy na kawai.
Suka tafa yace guy munada magana sosai muje gida pls.
Haka suka shige mota suna jin kida a hankali har suka isa, dan yau Areef ji yake tamkar an daura auren...lolx
Dinkuna take ta gwadawa sunki karewa saboda yawansu, tana ta yan juye juye a gaban mirro..duk a wannan lokacin batasan prince dinta yana tsaye yana kallonta ba.
Ji yakeyi tamkar yaje ya rungumeta dan jikinsa har tsuma yakeyi.
Rigar jikinta take niyyar cirewa shatin kugunta ya bayyana yayin dukawa ta zare ta kasa.
Karaf a kan idon Areef...yayi saurin runtse idonsa yace ya subhanallah...damn..damn zuciyarsa take bugawa dan ya kwadaitu da Amak dinsa sosai, juyawa yayi zai tafi yaji tamkar an likawa kafarsa magnet yakoma ya tsaya...inda ya sake maido kallonsa gareta...wata wedding gown ce maroon da coffee brown ta saka fitted gown sosai ta karbeta surar jikinta ta dada bayyana babu abinda ya fito bakinsa sai...wow!!! Tareda bude bakinsa cike da mamaki...Amal tayi saurin juyo ta kallesa...kunya ta kamata sosai ta tura kofan dakin dankarfi tareda sa key tana ya salam...yaganni!
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
22
Kuka ta fara rerawa...Princess pls ki bude i wanna talk to u.
Yaya pls ka tafi mu hadu anjima...duk a wannan lokacin tafukan hannayenta suna kan fuskanta dan gani takeyi tamkar yana gabanta.
Yagaji da magiyarsa ya juya ya tafi.
Tunanin yanayin dirin yarinya yayi masa katutu aransa...wanda yasa yakasa zaune ya kasa tsaye...sai kai komo yakeyi a tsakiyar dakin, da haka ya dauki wayansa ya kirata dan jin muryanta
Daga gefenta tajiyo ringing din wayar tata dubawa tayi taga sunan MY PRINCE asaman screen din wayar...babu jinkirtawa ta dauka tareda kangawa a kunnenta...cikin shagwaba hello my king..
Hmmm ai nayi fushi kuma Allah..ya fada yana turo baki tamkar tana ganinsa.
A'a kar muyi haka dakai mana..ta daidaita muryanta da gyara zaman dan rarrashin Mr Right dinta.
To inata magana abuden kofa amma an kasa, da kura ta buyoni saidai ta cinyeni.
Dariya ya bata tace...haba ai nasan ko zaki bazai iya cin naman ma prince ba balle wata kura karamar kwaro..
Murmushi ya sakar mata mai alamar magana...princess yau saura kwana nawa wai.
Haba babynah ka kosa ne?, whyl we are alwez togeda.
Ba wani togeda babe tunda ban kwana da princess of mine ba.
Huh...yau kuma sabuwar rigima ce da kafafunta kenan..ta fada tareda kishingidawa.
Eh naji nidai saura kwana nawa wai...
Saura...hajiya mama ce ta datseta kasancewar kiran da tayi mata.
Baby hajiya mama tana kirana am coming pls...tayi hangin call din tareda mikewa zuwa falon.
Badan ya so hakan ba, dan idan zasu kwana suna waya da Amal bazai taba gajiya ba kasancewar jindadin margic voice din ta...kissing phone din yayi tareda rungumeta ya mirgina gefe daya har bacci yayi awon gaba dashi.
*** *** *** *** ***
Invitations cards ne a zube main falo dana daurin aure dana programs of events anata rubuta sunayen wadanda za a kaiwa, ganin jibi ne daurin auren Amal da Areef.
Gida ya cika yayi makil sai hada hada akeyi tamkar yau ne ranar yinin bikin.
Areef ya shigo baki bude da ledoji a hannunsa yanata yan hange hange dan ya hango princess dinsa amma ina bai ganta ba.
Wayar sa ya fiddo ya juya yana yan latse latse dan lalubo number Amal ya kirata sukayi kicibus a hanya...wani irin kallo ya mayar mata mai kama da i missed yhu yace...from where princess?
Munje lalle ne ango ko bakaso a kumshe maka amaryar taka...salma ta bashi amsa a takaice.. Kasancewar kallon da Areef yayiwa Amal tuni ya narkar da ita a tsaye...huh...seee hot love ooo.
Kayan hannunsa ya mika mata yace kayan da zamu saka anjima ne za ayi kamu ne by 7:00pm kije ki gwana kigani idan sunyi miki, but ya nuna ta da ya tsa yace...ban yarda a gwada a gaban mutane ba, dan baki iya saka kaya ba gaban mutane sai anyi tallan jiki ko?
Baki ta turo tace tohm...yauwa ya amsa mata da shi suka wuce.
_7:00pm(Kamu)_
Ash n black gow ce mai jan kasa sosai tareda veil nata transparent ta gwada rigar ta karbeta sosai sai silver takalmi bawani mai tsini sosai ba kasancewar moderate ce baza a kirata da doguwa ba kuma ba gajera bace ba.
Haka Areef shima yasha boil ash n black combination aikin kansa abin kallo ne, hular kansa mai suna tangaran..kyau iya kyau kam anshashi babu abinda ke tashi sai harkallar kamshin turarukan ango da amarya...haka suka fito zuwa dakin hajiya mama don sanar da ita zasu wuce event.
Kwan kwan kwan..tsohuwa tana ciki...Areef ya fada cike da tsokana..dan kuwa Amal tuni bakinta ya mace.
Dariya hajiya mama tayi tace...ohi dai daga baya kenan...itama sabuwar zata zama tsohuwar ai.
A'a badai yanzu ba kam...yabata amsa.
To ina za aje ne yan shagali kuma ba a gayyacemu ba?, hajiya mama take tambaya tareda kallon Amal kamar bata wajen.
Amalilinah...wannan gayu haka?.
Ta sunkuyar da kanta kasa, Areef ya mayar mata da wani kallo cikin sigar kauna tareda kwarewa a fagen..yace hajiya mama zamu wuce kamu sai mun dawo.
Uhmmn Allah ya shirya ango babu kunya..adawi lafiya a kula mani da Amal dakyau nidai.
Insha Allah ya fada yayin da yake kokarin kamo hannun Amal su fice ta kofan baya.
Saurin fizge hannun tayi tace.. Haba mana ko kamanta gidan a cike yake.
Huh...am srry babe we're late ne kinga saleem yanata kirana shiyasa.
Haka suka fice zuwa wajen motocin dake waje ajere suna jiransu.
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
23
Hall ya cika makil babu masaka tsinke , kida ne ke tashi in a slow motion cikin aji cika da kasaita ango da amarya suka bayyana a wajen...babu abinda sukeyi face cika idon dumbin al ummar da ke wajen.
Kunya kawai Amal takeji.
Haka taron ya tashi gwanin birgewa da ban sha'awa, aka dunguma zuwa gidansu ango da amaryar.
Hajiya mama ce zaune da aminanta wato hajiya zulai da hajiya Aysha wadanda sune na hannun damarta...suna tattaunawa akan yanda shagulgulan ranar suka gudana..
Sallama tayi tareda kunno kai duk da kuwa babu wanda yabata izinin shigowa...ka tsaye cikin dakin ta fada tayi tsaye...wanda da ka ganta kaga rashin kunya a tattare da ita.
Tofa...ke kuma lafiya...ko har kun dawo daga partyn ne?, abinda hajiya mama ta tambaya kenan.
Sannunku hajiya ina yininku...ta fada tana fari da ido tareda buso chewing gum din dake bakinta....wane party kuma hajiya mama ai ni wajenki nazo...muhibbat ta fada kai tsaye.
Toooh...abinda hajiya zulai ta fada kenan tareda kame habar bakinta tana kallon hajiya aysha...lallai kam.
Murmushi hajiya mama tayi tace partyn kawarki mana ko kina nufin bata gayyaceki ba?
Ido ta fiddo waje sannan ta dawo hayyacinta tareda dafe kirjinta...aure Amal zatayi bata fada mun ba???? What a suprise day!..ta fada ciki da mamaki.
Aikuwa dai muhibbat yau ne ranar lallen kawarki Amal da angonta Areef gobe daurin aure in sha Allahu...hajiya mama ta zaro Invitation card dake gefenta ta mika mata.
No...no...no basai na gani ba, nazo ne wajenki kan maganata da Areef.
Ikon Allah...kinada wata magana da Areef ne muhibbat?, Hajiya mama ta tambayeta cike da mamaki...to zauna ina jinki.
Uhm...dattijuwar mace dake mai hankali da sanin ya kamata ace har bakisan akwai wata magana tsakanina da jikanki ba?, ai ba zama ya kawoni ba, Areef yayi mun alkawarin zai aureni kuma yanzu yazo da maganar auren kawata kuma kanwarsa Amal???, kinga an tsokalo tsuliyar dodo kenan.
Salati su hajiya zulai suka kamayi sannan hajiya mama tacigaba da cewa.. To rasa kunya naga abin naki bana hankali bane, Areef tun suna yara suke son junansu, ban taba jinsa da wata yarinya ba sai Amal, saboda haka kifice mun daga gida kafin ranki ya baci!
Taf..taf..takama yin tafi tareda furta wonderful yar tsohuwa...amma kisani ni Muhibbat S. Saulawa yazama dole kuma wajibi ne kibani jikanki na aura in ba haka ba kiga ruwan ikon Allah.
A fusace hajiya mama ta taso kan Muhibbat tana neman dukanta...
Hannu muhibbat ta daga tana niyyar dauke hajiya mama da mari...
Daga bakin kofan falo aka furta karki kuskura ki taba mana kaka banza jahila...muryar Amal tajiyo tana taku daidai ta karaso in da suke...
Juyi tayi cike da isa da kasaita gami da natsuwa ta iso daf da muhibbat...lokacin ta yaye mayafin jikinta da head din kanta tayi wurgi dasu saman kujera, fuskarta babu annuri ko kadan ta je ta dafa kafadun hajiya mama tayi kissing nata tace...we are sorry beloved grany...koma ki zauna...ta zaunar da ita cikin natsuwa.
Ta juya kan muhibbat duk a lokacin hannunta yana a tsaye cak tana kallon wani irin sheki da kyau dasuke walkiya a fuskar Amal da tasha ado ta kin kari...
Muhibbat kinyi kuskure, kin tafka kuskren da zakiyi danasani na har abada...
A daidai lokacin Areef ya ya shigo falon inda bai jira wata wata ba ya isa daf da muhibbat ji kake tas!..tas!!..tas!!...saida yabata mari uku kwarara...sannan yasa hannu ya finciko ta ya wurgar a waje...
Baba idi!..wato mai gadin gidan ya kira sunansa a fusace yace daka yau idan wannan karyar ta kuma zuwa ka barta tashiga gidan nan abakin aikinka.
Ya juya yana huci ya shige cikin gidan.
Kumatunta ta dafe dan tuni bakinta ya mutu...waini muhibbat wannan wace irin jarabace da kaddara suka hau kaina?, me yasa nakasa daurewa nake dauke irin wannan cin mutunci da wadannan mutane sukeyi mani?, meyasa bazan hakura da Areef ba...wayyo ni Allah...ta fashe da kuka mai shiga rai.
Baba idi kuwa tausayin yarinyar yabi ya kamashi...ta zabga uban tagumi yana kallonta.
Huh...sharrin So!
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
24
Haka tagaji da zama bayan ta gama share hawayenta ta kakkabe jikinta tayi gaba fuska duk a kumbure, kasancewar marin da Areef yayi mata.
Shagulgul biki ake tayi inda yau ce ranar daurin aure...ango da amarya sunsha navy blue dresses colour din ta amshesu sosai kasancewarsu fararen fata.
Yau kam Areef tamkar mai tallan close up dan bakinsa yakasa rufewa saboda murna da farin ciki dake tattare a kyakkyawar fuskarsa.
Tsaf ta gama shirinta cikin riga da sket dinki tamkar a jikinta aka zana shi, salma ta kashe mata dauri sai kace goggoro ne a ka dora akanta...ta kalleta tace to yaya?
Amarsu ta ango kisha kyau, dole abani tukuicin gyaraki danayi.
Dariya Amal tayi tace...tukuici salma ai dole ne kidai bari komai ya lafa..
Aww akwai wani tuggu dakike shirin hadawa ko?.
Dariya tasake yi wacce ta bayyana double dimple nata tace...kedai kijira kigani Allah dai yasa mugama taron lafiya.
Ameeen salma tabita dashi, sannan tace amma fa innaga dama Areef bazai ganki yanzu ba Allah saina wasa shi.
Wata yar harara ta mayar mata da ita sannan suka fito main falo, taku takeyi bazar sket din na jan kasa sosai, inda rigar ta kamata ainun kamshin turaruka suka gauraye falon, Inda gogan ya fito daga wajen hajiya sukana shirin fita daurin aure.
Cak numfashin Areef yaso tsayawa ganin yanda Amal dinsa ta canja kamanni takoma tamkar daga wata kasa aka yo odarta.. Wooo hooo hooo!...my princess ya fada tareda fiddo kyawawan idanunsa.
Murmushi tayi inda wushiryarta ta bayyana tace my prince?, tamkar bata gane shi ba dan a ganinta yafita haduwa over...matan dake wajen suka tsaya kallon ikon Allah...salma kuwa a gefe aka barta dan ba asan da ita a wajen ba.
Hannu yasa yakamota tareda rungumeta suna shakar kamshin juna...nan da nan falo ya kaure da guda ana masu kirari.
A daidai lokacin hajiya mama tafito tana tambayar lafiya??...idanunta sune suka bata amsar tambayarta...ganin yanda Areef da Amal suke a makale da juna har tsawon wannan lokacin...
Shiru tayi ta koma tacigaba da sabgarta.
Rada takeyiwa prince din nata wanda koni mai rubutu bansan me take fada masa ba.
Yayinda shima ya mayar mata cikin sigar so da kauna.
Haka suka zame jikinsu tamkar magnet ake neman rabawa...dogon numfashi ya sauke yace bara muje daurin aure mudawo yanzu inda idanunsa suka juye tsantsar kaunar Amal ta bayyana karara acikinsu.
Prince zanje gida nadawo yanzu nida salma...ta fada kasa kasa...no kijira na dawo tare zamuje.
Ya fice jiki babu kwari.
*** *** *** *** ***
An daura auren AREEFULLAH ABDUL'AHAD AYUD1 da AMAL ABDALLAH AYUD2 taro yayi taro inda kusoshin kasar nan suka halarci daurin auren, kasancewar marigari Alh Yusuf 'Doguru aminin jama'a ne.
Farinciki fal a fuskokin family both na iyayen su, hajiya mama burinta yacika anata hada hada da baki...
Inda gidajen amare da angwaye suma su maryam da maimuna ba a barsu a baya ba.
Arfat tashige cikin yan matan amarya tamkar tsararsu kasancewarta zama budurwa.
Da misalin karfe 5:00pm aka dauki amarya zuwa gidanta...gidan da mahaufin Areef yabasu wanda aka gina cikin tsari da baza mashi kayan alatu...Amal kuka takeyi tamkar ranta zai fita duk dan Areef bai barta taje tayiwa mahifiyarta sallama ba...a tunaninsa kuwa tana kukan rabuwa ne da hajiya mamarta da ta shagwabar da ita.
Labulen dakin ya daga tareda hangota cen makure gefen gado tana shashshekar kuka...Sallama yayi masu yace...salma wai ina amaryar cikin tsokana...salma tayi dariya tace ai mun mantota gida sai an koma.
Saurin dago kai tayi ta kalleshi sukayi ido hudu ya mayar mata da gwalo yace...gud nyt salma idan akwai wani abu a sanar dani, dan nima yau agidan zan kwana.
Ya haye sama in da anan ne bangarensa.
Muhibbat tana kwance tamkar mara lafiya, dan jikinta yayi sanyi sosai ganin yanda haryanzu take hasashen maganr hajiya mama da sunan wai Areef da Amal ake hidimar bikinsu...da zata iya tunawa ma da suma zata yi dan ta mance yaushe akace mata daurin aurensu.. Hmmmmm taja dogon numfashi tare da janyi wayarta...data ta kunna danyi chat taragewa kanta zafi...cin karo tayi da pics na bikinsu Amal Areef dana daurin aure wanda sunyi kyau iya kyau...nantake numfashinta ya dauke ta zube kasa babu rai....
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
_I dont dedicate ma pages but i most use da page to nushe ur kumatus wollah VERSMERH~ERLELE(Mrs S. Werkieliey), My Rigimas, his Rigimas, my Babe, his Queen, Allah ya shiryamun ke kirage laziness though it seems like an dauko hanya...i hate yhu babe💗...lolx!_
25
Har gari ya waye muhibbat bata san inda kanta yake ba...kasacewar doguwar suma da tayi.
Taro ya watse, komai anyi shi cikin aminci da lumana gwanin ban sha awa.
Salma ta hada kayanta tabar gidan ango da amarya inda saleem ya dauketa don maida ita gida.
Princess lets pray first pls...Areef ya fada cikin zakuwa inda Amal gabanta keta faduwa, dan ita babu abinda yake tsorata ta irin yanda ake bayarda labarin first nyt tsakanin ango da amarya.
Kinji...yafada tareda yowa kanta ya yaye mata mayafin dake rufe saman kanta..razana tayi tace to prince...cikin shagwaba.
Ido ya kashe mata yace...ko sai na daukeki nayo miki al walan princess?
Uhmmm...ta fada tareda mikewa tsam ta shige toilet din ta dauro al wala ta fito...ya lokacin gashin kanta ya zubo saman gadon bayanta sai walkiya yake yana sheki gwanin ban sha awa.
Baki ya bude...tayi saurin juyowa ta kalleshi jin yayi tsaye bai motsa ba.
Anan ya dawo hayyacinsa dan tuni ya lula wata sabuwar duniya kallon dirin Amal hips ne ke aiki da dukiyar fulani...miyau ya hadiye da karfi..sannan yayi saurin shigewa toilet din.
*** *** *** *** ***
Sun gabatar da sallah nafila kamar yanda addinin islama ya tabadar don yin adduo'i da kuma nuna godiya ga Allah da yanuna masu wannan rana...sannan Areef ya juyo ya jingina guiwoyinsa dana Amal ya kama hannayenta tareda maida kallonsa da hankalinsa gareta.. Tayi saurin sunkuyar dakai kasa.
Amal...ya kira sunanta ya tambayeta...miye banbancin wankan janaba, haila da na biki?
Fuskarsa babu wasa aciki..
Cikin sanyin murya tace yaya...banbancinsu niyya itace ta banbantasu amma duk daya akeyinsu.
Hmmmmm..ya sauke numfashi yacigaba dayi mata yan tambayoyi duk ta bashi amsa, sannan ya zare hannusa daga cikin nata ya dafa saman goshinta ya gabatar da Adduar da ango keyi yayin saduwa da matarsa a daren farko..komai suka gabatar cikin tsafta da yanda koyarwa ta nuna.
Oya muje kici wani abu ko?
Prince am okey...wata irin kunyarsa takeji.
Dariya yakeson yi mata amma yakasa...dan tana dan bashi tausayi, dan ji yakeyi da zai iya da yau bazai kwanta da ita ba amma inaa bazai iya ba yau sai yasan wace ce Amal dinsa.
Hannunta ya kamo ya shiga cire mata hijab din da tayi sallah dashi ya jefa saman gado, ya cire mata rigar jikinta..Amal tafara kukan shagwaba..
Yaya...yaya pls ka tsaya mana.
Bai tsaya saurarta ba sai da ya cire kaf kayan jikinta sannan ya jefa mata towel yace muje mu watsa ruwa sai muje muci abinci ko?.
Ta kudundune fuskarta cikin cinya tana rera kukanta na shagwaba...ni wlh bazanyi wanka da kai ba.
Dariya ya kama yi mata yace habawa yarinya idan ma kinki wlh sai na daukeki naje nayi maki.
Saurin dagowa tayi tana kallonsa cike da mamaki..wai yaushe yaya Areef duk yasan wannan iskancin...hmmm batayi mamaki ba ganin yanda bashida aiki sai kallon indian films inda ake zuba tsantsar soyayya ruwa ruwa..ta fada cikin ranta ta mike ta shige.
Fita yayi yaje bangarensa yanata dariya da annashuwa ya watsa ruwa yasako jallabiya wacce ita kadaice ajikinsa....
Dakin ya turo yasameta ta fito tana shirin saka kayan bacci inda dakin ya gauraye da kanshin turare mai sanyaya zuwa...huh ta mirron jikin wardrobe dinta ta hangoshi tayi saurin dukewa kasa..huh abinda tafi tsana kenan taga namiji da jallabiya kuma yayanta ba halinsa bane yau meke damun yaya Areef wai?, ta tambayi kanta.
My princess nazo na taimaka maki kisaka kayan ne?
Nidai kafita dan Allah...
Yayi dariya yafice yana cije gefen leben bakinsa ya fada idan ma bangani yanzu ba akwai anjima yan matanah...kisameni a diny area yaja kofan.
Baki ta zumbura tace yau nashifa uku da yaya Areef...hmmm ka gama maitanka wlh..ta cigaba dasaka rigar baccinta mai hade da dogon wando pink colour wai ita zasu fiye mata tayi bacci batare da ta takura ba kuma babu mai ganin jikinta...lolx
Hajiya mama gida yayi shiru babu abinda take tunani banda Amalilinta sarkin shagwaba..nidai Allah yasa wannan sarkin zakwadin yabi mani ita a hankali ta fada cikin ranta tare da sauke dogon numfashi..
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
_Alhamdulillah, thank yhu so very much for d warm prayers, Allahu yabar zumunci_
26
Fitowa tayi ta sameshi yafara yagar kazarsa, ta ta tana gefe tana jiranta.
Kamshin turarenta ya doki hancinsa yayi saurin juyowa yana kallon yanda take taku boobs nata suna rawa kasancewar babu abin rikesu face wannan rigar ta jikinta.
Yaa salam...ya fada tareda saurin mikewa tsaye zaiyi kanta kuma wata zuciyar tayi saurin dakatar dashi...karku ma na tsoratar da ita ya fada a ransa.
Kallonsa tasoyi kamar tayi dariya dan abun nashi yafara bata dariya.
Hollandia kadai tasha tabarshi da kazarsa, inda yayi yayi taci takici..hmm idan ma bakici ba zanci yarinya oya lets go to bed.
Ido ta zaro waje tace prince wlh jikina ciwo yakeyi kaje ka kwanta ni nasaba bacci na ni kadai.
Nema take ta raina masa hankali ya sungumeta suka haye sama zuwa bangarenta.
Wayyo Allah na Hajiya mama...Allah sai na fada mata dan Allah yaya ka ajiye ni zanje da kafana..bai dakata ba saida ya direta saman gado yakoma ya kulle duk wata kofa, ya koma zai kashe fitila kenan gabanta yasake faduwa damn!!!...yau nashiga uku na ta fada a fili har yajita.
Sulalewa tayi kasa yazo yacigaba da lalubata baiji komai ba...bed side lamp ya kunna ya hangota ta makure kusada wardrope...huh baby wat are u doin me kikeyi haka ne ya fada a marairaice.
Ni babu komai kawai bazan iya kwana da kai bane, dan Allah kabarni na kwana anan kaji...zatayi kuka ya karaso kusada ita ya zauna...kinga ni mijinki ne, ya kamata mu raya wannan daren kinji kibani aron kanki yau babynah.
Sake narkewa tayi ita dai a'a, da kyar yasamu ya lallabata ta amince suka koma saman gado.
Jikin Areef har rawa yakeyi dan yanda yaji ya kamo dukiyar fulanin Amal tuni hankalinsa yabar jikinsa, anan tafara fita hayyacinta suka cigaba da nunawa juna karshen son da suke wa kansu...inda nikuma na kama gabana dan barinsu suci amarcinsu da hujja kasancewar ba hurumina bane...lolx.
*** *** *** *** ***
Gari ya waye Hajiya mama da yan aikinta guda biyu sunata gyaran gida kasancewar ansha bidiri a gidan, amma tunanin Amal yakasa barinta.
Kai tsaye falo ta nufa ta kirawa wayar mahaifin Areef wato Abdul'ahad, babu jimawa kuwa ya daga tareda sallama.
Yauwa babban mutum kazo ina son ganinka yanzu...sunan da duk yazo mata na girmamawa saraki ko babban mutum takan kira yaran nata dashi.
Okey babu damuwa mama ina zuwa yanzu.
Yauwa...ta kashe wayar tareda zabga uban tagumi.
Abdul'ahad AYUD1 yayi sallama tareda kunno kansa ciki kai tsaye ya sameta tayi zugum, mama lafiya dai?
Ina fa nidai kuzo kukaini nagano Amal dan Allah.
Yaa salam mama yaran dake amarci jiya fa aka gama bikin nan kiyi hakuri a kwana biyu mana.
Harara ta wurga masa ta mike tareda saka hijabinta...muje ka kaini in ganota sai mudawo.
Ohh...mama dan Allah...tayi saurin katse shi da karka kuma banason gardama muje ta shige gaba.
Haka ya bita jiki babu kwari dan shi yasan halin yara yanda suke dokin auren nan agida ma basuji kunya ba inaga ansamesu har gidansu.
Sun isa daf da kofar gidan, mai gadi na niyyar bude masu get AYUD1 ya dakatar dashi da a'a malam barshi iya karmu nan.
Kallon mamaki hajiya mama tayi masa tace...aw saraki nan zaka direni a kofar gida?
Mama dan Allah ki rufamun asiri kishiga kifito ina nan.
Bata saurareshi ba ta fice ta shige ciki.
Barka da zuwa hajiya.. Mai gadi ya fada tareda rusunawa.
Yauwa malam bawale suna ciki ko?
Eh hajiya kamarma basu tashi ba...yana susan keyarsa
Ta juyo ta kallesa.. Basu tashi ba?, yanzu karfe 12:00pm ace basu tashi ba aikin da akace suzo suyi kenan barci?...ta shige ba tareda ta jira amsarsa ba.
Salamu alaikum..Salamu alaikum...taji shiru, samu tayi ta zauna tana kallo.
Kwance take saman kirjinsa anan barci yayi awon gaba da ita bayan kuka da gwawarmayar da suka sha cikin dare.
Gashin kanta yake shafawa tareda kallon kyakkyawar fuskar yarinyar, anan tausayinta ya kamashi kasancewar wani sabon daren dayakeson sake rayawa a yanzu fiye da najiya dan bai gamsu ba...muryar hajiya mama dayaji ta tsinke masa tunaninsa...woooooo ya fada aransa hajiya mama trouble maker!
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
27
A hankali yasoma zame jikinsa daga jikinta amma kam ta kamashi ta rike...princess am coming pls...
Uhmmm..uh... Bata karasa shagwaban ba yace to ga hajiya mama tazo ganinki ya rada mata a kunne tareda cizon gefen kunnen.
'Yar kara tasaki cen ciki sannan tace prince bazan iya tashi ba sai sabon kuka...
Noo pls princess am srry kinji kwanta ina zuwa zan yi mata dabara sai nazo nasaki a ruwan dumi kinji..
A'ahhhh ni bazan yarda ba saina ganta....haka ta fada amma sam ta kasa tashi saboda Areef a daren jiya bai mata sauki ba.
Jallabiya ya zura da boxer ya sauko kasa, inda ya tarad da hajiya mama zaune.
Hajiya mama uwar kuma kaka ga amarya da ango...ya fada cike da zolaya.
Kai ta dago tace kai ar cen wai Areef yaushe zakuyi hankali ne ina Amal din?..ace har yanzu baku tashi barci ba, to da dabaki nazo saidai mujuya kome?
Cool down..sweet granynmu ya zo ya zauna kusa da ita...gud morning hajiya mama ya fada tareda rusunawa.
Uhmmm...ta gyara zama ta fada ciki ciki lafiya...ina Amal nace.
Keyarsa yafara shafawa yace bata tashi bane.
Karya kakeyi...ta fada tareda mikewa zuwa saman up steps din dan ganin halin da take ciki.
No hajiya mama karki fado kibari in ta tashi Allah zan fada mata kinji..ya kama mayafinta yana magiya.
Fizgewa tayi tare da mai da mashi da harara..sannu dan gidan bene da bene to tun kafin in haifi ubanka nake hawan bene Areef...ta wuce ciki..
Amal ce kwance tana nishin azaba wanda har a wannan lokacin radadin zafin aikin Areef bai saketa ba...ji tayi an turo kofan dakin tayi saurin sake kudundunewa
Amal...hajiya mama takira sunanta..bata ansa ba.
Karasowa tayi inda take ta janye blanket din..inda taga jini kaca kaca a bed sheet din ta rafka uban salati sannan ta ajiye hijabinta ta kama Amal tare da taimaka mata ta gyara ta tsaf bayan ta gasa mata jikinta da ruwan dumi.
Duk a wannan lokacin Areef yana falo ido ya raina fata...shi gaskiya hajiya mama ta takurashi miye nata aciki wai.
Haka ta kamo hannun Amal a hankali suke tafiya suka sauko kasa inda tasameshi ya hada kai da guiwa yana yan sake sake...jinta yayi tana sannu kinji Amal.
Amal kuwa kunya ta kamata sosai batason hada ido da kowa kanta a kasa.
To wlh ka kiyayeni kabi mani yarinya a hankali kaji na fada maka, ko zama batayi ba ta fice abinda...tareda fadan sai na sake dawowa.
Dukansu babu wanda yace mata uffan haka ta tafi.
Dagowa yayi ya kalli princess dinshi inda tayi shigar doguwar riga orange ta yafa bakin veil tana sunkuye dai daganin zaman bai mata dadi ba dan tamkar mai jego takejinta.. Haka ya taso ya zauna gabanta cikin marairaicewa yace...my princess kinga abinda hajiya mama tayi mani ko?
Shiru tayi bata ce mashi komai ba.
Princess kin yarda kenan kar nasake shiga gonar da Allah ya halittamun?
Anan ma batace komai ba.
Tashi yayi ya kwantar da kanshi saman cinyarta yace wlh kuka zantayi maki idan bazaki kulani ba
No prince banajin dadi wlh dan Allah kabarni na huta.
Ta fada kamar zata yi kukan.
Uhmmm...okey muje kiyi breakfast tukuna saikiyi barcin.
Haka ya lallabata suka karya, sannan ya kaita dakinta ta kwanta, ya koma bangarensa ya gyara da kansa.
Haka rayuwar aurensu tacigaba da tafiya gwanin ban sha awa...kwatsam mai gadi yayi sallama suna cin abinci yace...yallabai ana sallama.
Wat sallama kuma?..Amal tambaya cike da mamaki ganin lokacin bana yawo bane.
Murmushi Areef yayi baice komai ba
Malam bawale maigadi yace wata matace tana waje.
Wani irin kallo Amal ta watsawa Areef mai tattare da alamar tambaya..yayi saurin kauda kansa yaci gaba da cin abincinsa.
Kace yana zuwa mala bawale...ta fada a takaice fuskarta cike da bacin rai.
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
28
Abin mamaki kafin mai gadi yafice Areef ya mike yabi bayansa...kallonsa ta tsaya tanayi har ya fice..ta mike ta daga labulen falon ta window...damn! Wa zata gani haka bakinta ya furta Muhibbat?!.
Isowarsa kenan tayi saurin mikewa tsaye tana watsa masa wani irin kallo daganin muhibbat da shirinta ta tazo.
Ya akayi ne muhibbat?, ya fada tareda soka hannayensa cikin aljihu.
Farrrr tayi da lulu eyez dinta wanda suka sha kayan makeup a samansu tace...wajenka nazo Areef, ashe kunyi aure da Amal?
Ayya...eh munyi aure kishigo daga ciki mana kugaisa.
Uhmm...ba wannan ya kawoni ba Areef ni kuma ya zakayi dani?
Baiyi mata garda ma ba yace mata...karki damu muna tare ai...ya kashe mata ido
Wani shu'umin murmushi ta saki sannan tace okey number ka fa?
Card nashi ya mika mata sannan yace sai mun hadu ko?
Oryt ta fada ta juya.
Duk a wannan Amal na bakin window tana kallon ikon Allah wanda idonta yakasa gasgata abin da yagani tamkar a mafarki...a guje ta shige dakinta ta fada saman gado tafara rera kuka dan ita bata da abinyi muhibbat taci galaba akan Areef hankalinta ya kwanta.
Tunda ya shigo baibi ta kan ina Amal take ba ya shige dakinsa.. Safa da marwa yakeyi tareda kallon ceilling tunanin muhibbat kuma yayi masa katutu aransa dan yarinyar yau ta tafi da imaninsa..huh ya hura iska mai zafi daga bakinsa...toni ina zan samu number muhibbat nakirata dan musan yanda zamuyi da Amal kar ta ruguza mana budget...abunda yake ta tunani akai kenan.
*** *** *** *** ***
Hajiya mama sun isa gida, inda tunanin Amal ya kamata dan Areef bai mata da sauki ba.. Wannan yaro Allah ya kyauta!, ta fada a ranta.
Rayuwar gidan batayi mata dadi ko kadan ahaka kullum bata da aiki sai kiran Amal a waya tana tambayarta lafiya dai ko, Amal ta ce mata lafiya.
Abdallah ya yanke shawarar yiwa yayansa magana akan Arfat ta dawo gidan hajiya mama da zama saboda debe mata kewa...haka kuwa akayi saidai halin Amal da Arfat ba daya bane ko kadan Arfat batajin magana musamman tara samari dayawan kawayen banza wai ita yar jami'a.
Hajiya mama am back ooo ta fada a fitsarance ta shigewarta.
Kallonta ta tsaya tanayi dan gaskiya akwai aiki wajen lankwasa wannan yarinyar...hmmm ta fada aranta tace habawa badai maryam ce uwarki ba ai baki zubarba wlh.
Ta mike ta shige dakinta da dairly trust dinta da tasaba karantawa tun mijinta yana raye.
Muhibbat ta isa gida murna cike da cikinta tayi wurgi da hand bag dinta ta dauki wayanta tareda danna lambobin Areef kai tsaye ta kira shi bugu daya biyu kuwa aka dauka..
Amal tunda ta dauka bata ce komai ba tana jira taji tace uffan sannan ta wanke ta tas...Muhibbat jin anyi shiru tayi sauri kashewa dan tasan ba Areef bane.
Wanka ya fito yana shirin office Amal tasha gabansa tareda nuna masa number ranta abace tace...Areef me ke kake nufi ne wai?, wacece tazo jiya nemanka, kuma miye hadinka da ita da har zata biyoka gidanka dan dabbanci tayi sallama dakai kafita kana washe mata baki?
Tsayuwa ya gyara yana mata kallon mamaki nine Areef yaukuma Amal?
Tafada in a serious tone dan babu wasa a tare da ita kwarai!!!...ka bani amsar tambayata ko kuma yau fita office ya gagara wlh!
Murmushin mugunta ya saki yace abinda baki isaba kuma kenan yarinya, baju hanya na wuce.
Kama kugunta tayi tace wlh babu inda zakaje Areef, anan yayi wurgi da ita saman gado ya sa kayansa yafice inda yabarta kwance tanata rera kukan takaici kukan bansan matsayina ba.
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
_D Whole page goes to yhu ma peepx..ANEELURV FANZ, EXCELLENT HAUSA WRITERS, HABIEBALUV NOVELS, NOVELLA'S LODGE, NURSES FORUM, D GREAT MINDS, EXPENSIVE LADYZ n odas grps...Thank yhu so very much for d support/encouraging me heart yhu all💕🤝🏼_
29
Haka tagaji ta tashi jiki ba kwari inda tashiga yan aikace aikacen gidan dan tsaftace shi, tanayi tana share hawayenta.
Kofar office din aka bude kai tsaye inda tashiga tana yan lankwashe lankwashe kamar zata karye fuskar tasha make up lukui lukui, tayi sallama cikin siririyar muryarta mai cike da kissa.
Idonsa ya dago yana kallonta baki sake can yayi wani murmushi tareda hadiye miyau ya cire glass din idonsa ya mayar mata da wani murmushi mai tattare da sako...bismillah mana ya nuna mata wurin zama yana kallonta sai bankaro kirji takeyi.
A.c ya mike yakara tareda komawa ya zauna kusa da ita...uhm uhmm Yaya Areef miye haka tafada a shagwabe.
Kyau kikayi mani muhibbat inason mace mai kayan alatu haka da irin wannan bakin naki zaiyi dadi tsotsa ya lakuci hancin ta yana dariya.
Hannu tasa ta rufe fuskarta... Bata ce komai ba.
Uhmmm...muje kirakani cin abinci mana...ya fada yana janyo suit nashi zai saka.
Damn!..gabanta ya fadi..
Ya dai kikayi shiru babe ko bazaki rakani ba?
A'ah...ta fada a razane zan raka ka mana. Am...amma ina ne?
Yadai haka kina tsoron a ganki dani ne?
No kawai banason Amal taganni dakai a yanzu....
Ohhhh ai ba gidanta zamuje ba Hotel zaki rakani sai mudan huta ko?
Haka taji wani sanyi a ranta ta mike tareda janyo necktile nashi ta sumbata saida janbakin ta yafito ajiki...duk a wannan lokacin areef ya rikice bashida burin su tafi dai kawai.
Ficewa sukayi kai tsaye suka nufi hotel dan shakatawarsu.
*** *** *** *** ***
Ta kammala abinci tana jera a diny, kai tsaye wanka ta shiga ta fito ta tsaya tana kallon yanda tsakanin jiya da yau yanda ta rame sosai kamar wacce aka sallamo daga gadon asibiti, uhmmm...murmushin takaici tayi ta shafa mai ta feshe jikin ta ruwan turaruka kala kala inda tasamo doguwar riga ta atamfa tasaka, wanda damuwa ce tattare da ita na rashin gane kan Areef amma hakan baisa ta fasa dukka abubuwan da take masa ba, choge dauri tayi ta kame a falo tana jiran dawowar mijin nata don tarbarshi duk da cewa lokacin dawowarsa ya wuce amma bata gaza ba.
Areef da muhibbat sun shiga sabuwar rayuwa wanda hakan saida yasa areef yayiwa muhibbat dai dai dan saninta diya mace...dadi ya rufeta kamar ta cinyeshi...baby kitashi mu tafi idan kin gama hutawa ko...ya fda jiki babu kwari.
Baby nifa am not certisfy..so ka karamun ko round biyu ne.
Murmushi yayi yace like serious baki gaji dani ba kenan.
Haka nake nufi ai yayanah...ta fada cike da wata irin siga ta yaudara
Bakinta ya cigaba da tsotsewa saida yasake shigarta tsaf sannan ta sake jinta tsam... Uhmmm tayi murmushin keta tace yaya Areef bana gajiya da kai ya za ayi?
Karki damu muna tare ai kullum dan kema ba daga baya ba kin biyani kuma kin koremun kishirwata.
Dadi ya tufeta ta sake rungumeshi tana kissing nashi.
Tare sukayi wanka suka fito suna yiwa junansu wani irin sabon kallo na kauna..ba dan taso ba suka rabu ya wuce gida kai tsaye.
Karar motarsa taji tayi saurin fitowa kamar yanda tasaba tarbarsa bata canja ba...abin mamaki Areef ya daure fuska tamkar yaga makiyarsa.
Murmushi tayi ta kada kanta tace..prince ur wlcm ta karba brief case nashi yace no barshi kawai.
Bata ce komai ba ta koma ciki...
Tun kararsa tayi zata cire masa kayansa yace...no na hutar dake yau...
Idonta kan kiss din dambareren bakin muhibbat shatin janbaki gaban Amal ya fadi tace...Areeef!!!!!...me ne nake gani a necktile naka?
Baya taja tana wlh karya ne idanma idona gizau yakemun yadaina yaya Areef bazaimun haka ba wlh...sai ruwan hawayenta suka fara kwararowa saman kumatunta...tsaye yayi yana kallonta ko ajikinsa shi kallon dayake mata na batakai muhibbat diri ba balle dadi wajen kwanciya..kaicho.
Anan ta sulale kasa tacigaba kuka mai tsuma zuciyar mai sauraronta...ya shigewarsa bathroom zai watso ruwan karya...hmmm!
Urz Aneelurv💕
*^AMINTAKA...^*
_(Labarin Daya k'unshi K'auna, Aminci da yarda)_
*NA*
*ANEESAT ABUBAKAR RIMI*
_Gajeren labari_
_END!_
30
Fitowa yayi har a wannan lokacin tana tsugune tana rera kukan bakin cin, dago kai tayi ta kalleshi inda ta tabbatar da ba bu wani wanka da yayi raina ta yayi...gabanshi tasha tace...Areef meke damunka?, neman mata kakoma yi Areef?, me na rageka dashi a cikin gidan nan Areef?, kana nufin auren sha'awa kayi dani Areef?, ka mance ko wace irin gwagwarmaya muka sha akan shu'umanci na muhibbat?,idan baka sani ba Areef muhibbat bata da lafiya saboda ba yarinya bace mai kamun kai kafi kowa sanin hakan, ko kamance halarci da yarda da na nuna maka nakuma nuna mata?, ko ka manta sanin darajar AMINTAKA...dake tattare a tsakaninmu mu ukun?, Areef ka cuceni kuma zan kira hajiya mama yanzu dan tasan abinda ke faruwa wlh bazaka kasheni ba da sauran kuruciyata...ta karasa maganar tana kuka sosai tashige dakin kusa da dakinta.
Kai ya kada ya fice abinsa babu inda ya zarce sai diny area inda yaje ya cika tunbinsa, anan ya fada kogin danasanin abinda ya aikatawa Amal sam bai kyauta ba...kiran muhibbat ya tsinke tunanin dayakeyi anan ya fara rejecting call nata, nan take jikinsa yayi sanyi ya mike ya nufi wajen Amal..inda yasameta tana tabrera kuka har fuskarta ta kumbure idanuwanta sun kara girma.. Tausayun yarinyar yashiga kamashi.
Dago kai tayi ta kalleshi jin ya shigo a hankali.. Danasani ya bayyana a fuskarsa wanda kuma tasan yabaro bida baya dan ba zata sake aminta dashi ba amatsayin mijin aurenta.
Amal...ya kira sunanta cikin sarkakkiyar murya.
Areef ka rabu dani!..ta dakatar dashi.
Amal ki yafe mani Amal sharrin shaidan ne bazan kuma ba.
Areef ubangijinka zakaje ka nemi afuwarsa baniba dannima baiwace a wajensa.
Amal....
Pls...ta dakatar dashi tareda mikewa zata fice..
Hannunta yajanyo tayi kokarin fizgewa ta kasa...idonta har a wannan lokacin baidaina ambaliyar hawaye ba tace Areef so nake kasakeni zan tafi gidanmu yanzu.
Amal me kike fada ne?, kinsan Allah yana fushi da macen da tanemi saki ga mijinta?,
Na sani kawai bazan iya zama dakai bane ka rabu dani kaje kanemi daidai da kai..
Kasa sakinta yayi...sai ya nemi rungumota ta janye jikinta dan a lokacin Amal kyamatar Areef takeyi sosai...
Mamaki ya rufeshi tamkar ba Amal dinsa ba da tasan darajar So tasan darajar mutum amma yau shi Areef dinta take gudu...anan ya zube kasa yana neman yafiyarta amma ina ta ficewarta.
*** *** *** *** ***
Sallama tayi tasamesu suna tattaunawa akan fidda ranar bikin arfat...iyayensu ne kaf da hajiya mama a falon.
A'ah Amal lafiya kuwa?, Hajiya mama ta tambaya cike da kulawa da damuwar ganin yanda taga Amal ta koma kuma ga kuka tanayi amma babu bakin magana.
Abba inayini dady inayini abinda ta iya cewa kenan.
Lafiya kalau Abdul'ahad ya amsa sannan yace...ya akayine?
Babu komai dady ta fada kanta a sunkuye.
Hmmmm kawai hajiya mama ta fada tareda cewa kai Abdallah kira mani Areef a waya yazo ina kiransa.
Okey mama.
Yayi masa kusan kira hudu amma babu amsa, hakan yasa sukace babu lafiya
Ke Amal meke faruwa nace?!...AYUD1 ysaka mata tsawa dan tafada amma ina tace babu komai
Haka hajiya mama ta yanke hukunci Amal bazata koma ba sai Areef yazo
Areef ne kwance zazzabi ya rufeshi shikadai a cikin gida babu kowa.
Wayarsa nata ruri amma yakasa picking...haka kwana daya biyu babu Amal babu bayaninta yasa ya kokarta ya fita idanunsa jawur ya nufi gidan hajiya mama.
Amal ya samu tana kwace tayi zugum babu abinda takeyi sai yan sake sake dan ita gaskiya bazata yarda takoma gidan Areef ba ko ana ha maza ha mata.. Zancen zuci.
Kai tsaye dakin hajiya mama ya wuce guiwa a sanyaye dan a tunaninsa tagama tona masa asiri...shigarsa keda wuya hajiya mama ta haushi da fada sosai.
Idan kasan muzguna mata zaka dinga yi to ina mai tabbatar maka raba auren zanyi dan bazan lamunta ba...ita a tunaninta yawan kwanciya da ita yakeyi shine yasa Amal bazata iya jure hakan ba ta taho gida.
Kan Areef a kasa baice komai ba anan yafara zubda hawayen dana sani...hajiya mama ayi hakuri bazai sake faruwa ba.
To Allah yasa, sai kaje tana dakinta ku tafi gida.
To nagode...ana tagane cewa kamar ma bashida lfy.
Areef...ta kira sunansa ya juyo, meke damunka ne?
Zazzabi nake hajiya mama.
Ayya...To Allah bada lafiya aje asibiti dai.
To ameeen ya fada ya fice.
Kai tsaye dakin Amal ya nufa yasameta tana kwance tayi shiru...
Sallama yayi ko kallon inda yake batayi ba ta amsa ciki ciki.
Amal ance inzo indaukeki mutafi gida?
Tayi zumbur...ta zauna tace waah...nii???...murmushin rainin hakali tayi masa tace to idan ma mafarki kakeyi to ka farka dan wlh bazanje gidanka ba sai anyi zama mai zaman kansa a tsakanina dakai kuma sai kaje kayo test yauwa!
Amal...ko yanzu na bukaceki zan kwanta dakefa dan haryanzu ke matatace saboda haka kitashi mutafi.
Bazani ba!, ta fada cikeda rashin kunya.
Anan hajiya mama ta fito tajiyo hayaniyarsu inda ta isa ta nemi sasantasu amma inaa Amal takiyarda dan tasan abinda take nufi...
To zankira iyayenku maza sai suzo muji...
Haka su Abdallah da Abdul'ahad da matayensu maimuna da maryam suka zo aka zauna aka tattauna amma Amal taki fada dalilinta na kin komawa gidan Areef.
Ke Amal karki dauki mutane sakarkaru mana to saikin koma kitashi kibi mijinki nace...abinda mahaifinta Abdallah AYUD2 yafada kenan cike da fada duk dan ya razana ta.
Budan bakin Amal sai cewa tayi Abbah saidai kuyi hakuri dan BAKIN ALK'ALAMI ya rika ya bushi....!
TAMMAT BIHAMDULLAH!