"sosai shukrah take jin dadin aikin ta don batada wata
matsala da mijinta tunda yana so, HK batada matsala da *Maryam Anas* don ba
laifi shukrah ta iya aikin ta kuma batada kyashi"
"kasan cewar mutane masu matsalar ido basuda yawa yasa
SHUKRA kullum take tashi a office da wuri hakan yayiwa kowa dadi musamman ma
Safeer a cewar sa gwara Shukrah tayi tarbiyyar yaranta da kanta, bawae don bae yarda
da da tarbiyyar su Mamah bane a a shudae kawae yafi ganewa hakan ne"
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Bayan wata takwas*
Abubuwa da yawa sun faru a rayuwar ma'auratan nn guda
biyu,twins sun girma sunyi wayo sosai don yanzu har suna iya tafiya,magana ma
suna tilastawa Kansu suna dan gwadawa"
"Yau ta kama Saturday kuma kamar yadda suka saba basa
fita week ends saboda haka yau duk suna gida, Safeer na kan one sitter ya daura
Labeeba kan jikinshi yana mata wasa yayinda labeeb ke wasan sa daga kasa kusada
Shukrah ,ita kuwa Shukrah tana zaune ta maida hankalinta kan wani littafi da
take karantawa"
"Safeer ya kalli Shukrah sannan ya kalli labeeb yace
'Sweetheart ' kirawo min Shukrah"
"Labeeb ya dago Kansa ya kalli Daddy'nsa sannan ya
kalli Shukrah wadda batama San me sukeyi ba ya Kara kallon Safeer,Safeer ya
daga
Masa kai,sannan ya Mike yana tafiyarsa irin ta 'yan koyo
yazo gaban SHUKRA ya riko hannunta yana Mata murmushi yace"
"Chuklah Jo Daddy". Yana nuna mata Safeer Wanda ya
dage sai Dariya yake mata, ta turo baki gava ta bata fuska wane zatayi kuka ta
kalleshi"
" Ynx sabida Allah other half Shukrah zaka koya was
yaran nn fada ko,? Dariyar ya tsagaita sannan yace yi hkr yan matana ni bance
yacemiki Shukrah ba shi ya fada"
"Murmushi kawae Shukrah tayi ta mayar da hankalinta kan
book din hannunta don tasan in ta biye masa haushi da takaici zaita tura
mata"
"shirye shiryen bikin Aysher ya kankama tunda next
month za ayi bikin hakan nema yasa Mamah da Hajiyar Haidar suka shirya tsab
suka tafi Cairo donyin siyayyar bikin ,sati biyu kawae sukayi a can suka dawo
inda aka shiga cikin bikin gadan gadan"
"Mutanen Mamah duk sun halarchi bikin kuma sunyi
bajinta ba kadan ba, ciki kuwa harda *Aunty Maryam Ana's* ,sosai Mamah keji da ita don a duniya batada
kamarta duk da kasan cewarta kawace a gurinta amma tamata abinda yan uwanta da
yawa basuyi mata ba,hakan ne yasa ta Kara mata matsayi sosai kuma take alfahari
da ita"
Sunday 23 December 2016 aka daura AUREN *Mahmoud Mustapha da
Aysher Muhammad mai lafiya* Kan sadaki naira dubu hamsin, musalin sha biyu na
rana, sosai Auren ya samu albarkar manya manyan mutanen da suka halarta"
"Karfe takwas da rabi na dare aka kai amarya dakin
ta"
"Rayuwar Safeer da Shukrah rayuwa CE da aka gina ta
cikeda so da kauna,yarda ,amana, karamci dakuma mutunta juna, sosai suke son
junansu sika kuma yarda da Kansu"
"Shukrah a kitchen tana wanke wanke yayinda labeeb da
labeeba suke tayata da barna, Safeer ne ya shigo cikin kitchen din yana Yar
wakar sa da alama dae yana cikin nishadi,karasowa yayi kusada Shukrah ya
nannade hannun rigarsa ya sunkuya yana
tayata daurayewa"
"Other half yaushe za ayiwa twins kani ne sunyi girma
fa yace yana kallon ta cikin ido"
"Dau ke idonta tayi daga kallonsa tana murmushi kasa
kasa sannan tace 'ynx idan nacema inada ciki ae saika rufeni da duka yara wata
goma sha biyu amma ace za a musu k'ani"
"Ware idanunsa yayi sosai a kansa don ta bashi mamaki
sosai be taba tunanin zatace HK ba shi a ganin sa Shukrah tanada hankalin da ko
ciki ta samu bayan ta haihu da wata biyar bazata yi korafi ba, amma sai yaji
Sabanin hk, shiyasa ma yace' Haba Shukrah da girman ki da hankalinki zakice
HK,"
"Dariya tayi don taga kamar abinda tace ya bata ransa
tace' yi hkr Ya Safeer ni ko ynx ma a shirye nake kazo kamin ciki shknn"
"Haka kikace Shukrah?
"Haka nace, meye to ae mu munci dubu sai ceto ya safeer
Shukrah tace tana dariya sosai,daga nn ta kwashe plates din da cups duk ta
jerasu a muhallin su sannan ta dawo ta wanke sink din"
"Shammatar ta Safeer yayi ya dagata cak ya nufi bedroom
da ita yana cewa bakince kinci dubu sai ceto ba,kuma a shirye kike nayi miki
ciki ko,ae ko ynx zan baki triplets
Ma, kan gado ya ajiyeta, itadae Shukrah batada bakin magana
tunda ita ta janyo wa kanta,shafa ta ya fara yi tunda kanta har zuwa kirjinta
duk ya wani susuce dan dan kwana biyun da beyi ba, haka dae yayita romancing
dinta har ya cimma burinsa ae nan ya Kara susucewa donji yayi Shukrah ta zamar
masa sabuwa fill don Shukrah bata wasa da gyara sam nan ya fara Mata surutai
,Shukrah na baki gidana na zoo road, na baki duk wani dukiya Dana mallaka na
baki kaina Shukrah na baki raina gaba daya gani kiyi yanda kikeso dani Shukrah
ki juya ni yadda kike so kinji......
"Da yamma bayan sunyi wanka suna zaune suna hira
Shukrah ta kalleshi ta kyalkyale da dariya ,ya hade rai yana hararar ta don
yasan mugunta ta shirya masa, a kufule yace' meya faru kuma'
"Dariya Shukrah ta cigaba dayi harda rike ciki tana
kallonsa HK kuma tana nunasa da daya hannunta ,haushine ya cika shi ya mike yazo
kusa da ita, Kafin tace zata tashi ta gudu harya riketa ya matseta sosai har
saida tayi Yar Kara ,yace fadamin me yasaki dariya kafin in bata miki rai"
"Sai da takara darawa sannan tace""Shukrah na
baki dukiya ta ,nabaki gidana na baki kaina kiyi yadda kikeso dani ta karashe
tana sake yin dariyar sosai"
"Sake matseta yayi ya hade rai don ya gano abinda take
nufi yace to waye ya fadi hakan?
"Dariya ta kuma yi sannan tace waye to inba Ya Safeer
ba"
."Murmushi ya kuma yi sannan yace nidae sharri kika min
amma zan hkunta ki da daddare,"
Bayan kamar sati uku Shukrah ta Fara ganin canji a jikin ta
don ynx wata kasala CE ke addabar ta ga yawan zazzabi da ciwon kai ga kuma wani
saurin bacci da take data dan jingina sai bacci wani lokacin ma ko girki take
data dan zauna sai bacci,"
"Shukrah CE a kitchen tana dafawa twins indomie don
basa son cin abinci sosai, da zarar sun faracin wani abun da sunci sau uku zuwa
hudu zasu dena ci, ga kuma rigima dasuke damunta dashi Sam basa barinta ta huta
in bacci ma take haka zasuje su hau kanta suna tsalle suna'chuklah ci taci cijo
Daddy ,wani lokacin sai ta hada da duka suke nutsuwa su kyaleta shiyasa ma ta
yanke shawarar yaye su tunda sunyi wayo sosai"
"Tana zuba indomie din ta dawo ta kwanta a kasa Dan
danan kuwa bacci ya kwashe ta zuwa can indomie ta fara kamawa ,Safeer dake
bacci a parlour yaji kauri na Neman halaka shi ga twins sai tari suke suna
kuka, da sauri ya karaso kitchen din kai tsaye gurin gas ya nufa ya kashe
sannan ya dawo gun twins ya daga su yana jijjiga su,duk wannan abinda ake
Shukrah bata sani ba, Haushi ne yasa Safeer fara bubbuga Shukrah yace meye HK
wae yake damunki Shukrah ko ina kika samu sai bacci kin barmin girki yana
konewa yarana sai tari sukeyi amma ke sai baccin ki kike hankali kwance ,kije
kiga doctor mana in cuta kike ya baki magani"
"Taikaici ne ya rufe Shukrah don tasan ko a mafarki
bazata iya mayar masa da magana ba shiyasa ma ta mike ta dau wayarta ta koma
parlour tayi kwanciyar ta sai bacci, sanda Safeer ya futo yaga har ta koma
bacci tsaki kawae yaja ya rike hannun yaransa suka bar Gidan...........
"misalin sha biyu da rabi *Shukrah* ta gama attending
patients NATA,tana zaune shiru kasan cewar bazata tafi gidaba sai 2:00pm bacci
ta fara ji tun tana kokarin hana kanta yi har ta saduda ta kifa kanta a jikin
desk dan danan ko ta fara baccin"
*Aunty Maryam Ana's* taji shukrah shuru don ta saba in dae
ta gama attending patients gurin ta take zuwa suyi hira,hakan ne yasata mikewa
da niyyar dubo Shukrah, sai da ta fara duba Dr.Nuriyya taga tana nn sannan ta
wuce office din Shukrah"
"Da sallamar ta ta karasa office din amma ga mamakin ta
sai taji shiru, tura kofar tayi ta shiga taga Shukrah kwance tanata bacci
abinta, ta karasa jikin desk din tana bugawa, kamar daga sama shukrah taji
bugun ta dago da sauri don ta tsorata
sosai,Ganin Aunty *Maryam Ana's* yasata turo dan bakinta tana shirin yin
kuka"
"Sleeping on duty ko? Good ki sameni a office, zaki
answer query Aunty Maryam Ana's tace tana dariya sannan tayi gaba, Dariyar
itama Shukrah tayi sannan ta dau handkerchief ta goge fuskar ta ta fita ta rufe
office din ta wuce office din Doctor Maryam, a zaune ta sameta tana duba wani
file ta karaso ta zauna a side chair din office din tana kallonta"
"Lazy Doctor daga duba patients basufi 30 ba amma har
kin fara bacci ko,meye matsalar kine wae kwana biyun nn ?Inji Dr.Maryam
Ana's"
"Murnushi Shukrah tayi ta kauda kai don tana gudun
abinda zai je ya dawo, kamar bazatayi magana ba sai can tace' Nima Aunty bansan
meke damuna ba gaba daya banajin dadi, yawan bacci, jiri wani lokacin ma har da
zazzabi nake ta fama dasu a yan kwanakin nn"ta fada cikeda damuwa
"Kin harbo jirgi Shukrah, Allah ya raba lafiya da kaina
zan miki test don INA son sanin watansa nawa Dr.Maryam tace sanda ta taso ta
dawo kusa da Shukrah"
" Result na Test din da akayiwa Shukrah ya nuna tanada
ciki har na tsawon wata biyu da kwana uku, Dr.Maryam Ana's ta kalli Shukrah da
fara'Arta tace sannu Shukrah Allah yasa twins ne ko nasamu amin takwara,
Shukrah ta bata fuska kamar zatayi kuka'Aunty nifa banason cikin nn watan twins
fa Tara, yazanyi dasu fisabilillahi"
"Murmushi Dr Maryam tayi tana kallon Shukrah, tace koda
wasa karna kara jin kince bakyason k'aruwa Shukrah,ko kinsan wani son haihuwa
yake kamar zaiyi hauka amma Allah bai bashi ba,ita haihuwa babbar kyauta ce
bakowa Allah ke bawa ba amma ke kinsamu kice bakya so Shukrah, Allah da kansa
yace yanajin kunyar idon duk Wanda bai azurta da haihuwa ba, haba Shukrah ina
hankalinki ya tafi? Yaranki sunyi girman da ko yanzu zaki iya yaye su, me kike tunani
Shukrah"
"Hakikanin gaskiya maganar Aunty Maryam ta shiga
Shukrah, kuma itama ta sani amma ta share tayi rau -rau da ido kamar zatayi
kuka tace insha Allah koda wasa bazan kuma fadar hakan ba kuma Alhamdulillahi
Allah yana sona shiyasa ya bani haihuwa Allah ka bani ikon tarbiyyantar dasu
kan hanya madai~daiciya"
"Ameen Yar gata na cewar Dr.Maryam sanda take hada
kayanta, atare suka fito da Shukrah Inda take rokon Shukrah tazo da twins
gidanta ran Saturday, Shukrah kuma ta tabbatar mata zasuzo harda Safeer ma ,nan
sukayi sallama kowa ta shiga motar ta suka fice
*MARYAM CLINIC*"
" yau ta kama saturday kuma Kamar yadda Shukrah tayiwa
Dr.Maryam Alkawarin kawo mata ziyara ran Saturday haka suka shirya tsaf gurin
12:00 bayan Shukrah ta gama duk ayyukan
ta suka kama hanyar Gidan Doctor Maryam Ana's, cikin mota Labeeb ya tabo
Shukrah yace 'Chuklah jidan Aunty mayyam jamu ae ko' ,Shukrah ta doke bakinsa
tace wace'''Shukrah'''? ,ae kamar jira yake ya fasa ihu harda fadowa daga kan
sit ya buga kansa kuwa a jikin driver sit ya dinga birgima wane Shukrah Zane
mishi jikinsa tayi,Safeer yayi saurin gangarawa gefen titi yayi parking ya juyo
yanawa Shukrah mugun kallo sannan yace'Wae Shukrah sau nawa zan hanaki dukarmin
yara,ko saboda ban isaba ne yasa bazaki jiba, meyayi miki ma da har ya cancanci
duka daga gareki, sai kace bake kika haife suba komai duka, me zakiji ajikin
yaron nn in kin dakeshi"
"Labeeb ko tunda Daddy'nsa ya Fara magana yayi shuru
kamar yasan me yake cewa sai ya kalli Shukrah ya juyo ya kalli
Safeer,...Shukrah bata iya mayarwa da safeer magana koda kuwa rashin mayar da
maganar zai zamo mata matsala, amma tanajin tausayin Safeer bataso son da yake
yiwa yaransa yasa shi rufe idanunsa ya kuma toshe kunnensa haka kuma ya juyawa
gaskiya baya shiyasa ma yau ta daure tace
"Haba ya
Safeer Dan Allah me yasa wae kai kullum in yaran nn sukayi laifi saika rufe
idonka ka nuna kai bakason ayi musu hukunci,bayan ice tun yana danye ake tan
kwara shi.. Kuma naga ae ba wani Abu nayi masa bige masa baki kawae nayi sabida
ya kirani da sunana ko saboda Ina son su sai ya barsu suyi yadda suke so ?karka
manta fa yaranmu amana ce Allah ya bamu kuma zai tambayemu, me zamu ceda Allah
in ya kasance mun koma gareshi ba tare da mun sasu akan hanya madai daiciya ba,nasan
kafini sani kuma ba fada maka nayiba dan baka sani a a na tuna tarda mune, Amma
dan Allah in na bata maka rai ka yafe min ban Dada da niyyar bata ran kaba
kaji.. Tana kaiwa nan ta Kifa kanta jikin window wasu zafafan hawaye suka fito
Mata a kokaci days kuma tana da tasanin saukin bakin da tayi ita a rayuwar ta
batason wani ma ya bata ran safeer bare ma ita da kanta ta bata"
"Shiru Safeer yayi yana nazarain maganar ta ya tabbatar
da cewa gaskiya ta fada, take yaji ya kara mata matsayi ya kuma Dada tabbatar
wa yayi dacen mace ta gari kuma yaransa sun yi dacen nahaifiya ta gari.. Sonta
yaji yana ratsa duk wata gaba ta jikin sa,ya juyo yana kallon ta har a lokacin
bata dago ba yace cikin zuciyar sa'Ya Allah ga salihar baiwarka nan kayi mata
gafara ka buda mata ka kuma kareta daga sharrin duk wani mai sharri, Karasowar
da sukayi Gidan Doctor Mariam Ana's yasa Shukrah dagowa suka hada ido da Safeer
suka sakarwa juna murmushi ,Safeer ya fito ya bude mata kofar motar ta fito
bayan ta dauko labeeb daga kasa nan inda ya gama rigimarsa yayi bacci"
"Safeer ya rike Mata hannunta yace Other half bacci?
"Murmushi tayi tace wallahi nima bansan inayiba saida motar nn ta tsaya sannan na
farka, Murmushin shima yai sannan suka shigo parlour"
"Da murnar ta tafito ta taresu tana musu ya hanya bayan
sun zauna ne kuma ta tashi ta fara kawo musu drinks, hira sosai sukeyi
Dr.Maryam sai yaba halayen SHUKRA take Safeer yana tayata, yinin ranar a Gidan
sukayi harda Safeer Wanda sallah ce kadai ke fitar dashi a Gidan, don dama can
shi jinin su yafi a haduwa Dana Dr.Maryam duk cikin kawayen Mamah tanaji dashi
kamar danta"
"Sai bayan sallar isha suka bar Gidan,Labeeb
Dan rigima wae anan zai kwana suna tafiya ko barin layin
basuyiba ya dasa kuka wae Sai ta kaishi Chuklah,ae kuwa ba shiri ta Kira su
suka juyo sukadau Dan rigimar su suka wuce gida"
*Bayan wata takwas*
"Cikin *SHUKRAH*ya girma sosai kusan ma yafi na twins
girma abinda ya tashi hankalin Shukrah Knn musamman ma in ta tuna kalar wahalar
da tasha da haihuwar twins har kuka take duk ta Hana kanta sukuni gani take
kamar zata mutu sai ta zauna tayi shiru tana tunani don yanzu ta dena zuwa aiki
tunda cikin ta yakai wata takwas"
"Yau ta kama Saturday amma Shukrah ce kadai a gida sai
Labeeba dake kwance jikin Shukrah shi Safeer yaje Gidan Haiydar shida Labeeb
sun tafi kai Zafeera asibita zata haihu, Kasan cewar Zafeera mai juriya yasa ba
a wani sha fama da ita ba ta haihu cikin kankanin lokaci, ta haifi da namiji
murnaa a gurin Haydar da Safeer kamar me dan danan suka kira Hajiya a waya suka
sanar da ita ,nan itama ta Fara kiran yan uwa a waya cikin kankanin lokaci
asibiti ya cika da jama'a ,a ranar da yamma kuma aka yi discharging dinta tunda
lafiyarsu kalau "
"Washe gari a can Shukrah ta yini yan uwa sai zuwa
Duke,ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Zafeera wato Abdullahi za a dinga
kiransa da little "
Bayan wata biyu ranar wata Friday Shukrah ta tashi da
matsanan cin ciwon Mara har bata iya motsi ko kuka ta kasayi sai hawayene kawae
yake zuba a idanunta ,ga wayarta tana gani takasa dauka ta Kira Safeer
kasancewar bayanan yanacan wajen Gina company dinsa tun safe
DaKyar cikin sa'a Shukrah ta mika hannu ta dauko wayarta
number Safeer tayi dialing, Safeer dake tsaye yaji vibration cikin aljihun sa
yayi saurin dauko wayar yayi picking da sauri ganin Shukrah CE me kiran,
"Hello other half kazo zan mutu kawae Shukrah ta iya
cewa tayi wulli da wayar sakamakon marar ta data juya mata ,rike cikin tayi
tanata juyi a kasa, A bangaren Safeer ma jin shirun da Shukrah tayi yayi mugun
daga masa hankali ko sallama beyiwa haiydar ba yayi ficewar sa da sauri"
"Sanda ya karasa Gidan Shukrah gaba daya ta fita a
hayyacin ta, duk karfin hali irin na Safeer sai da ya goge kwalla ganin irin
halin da shukrah ta shiga ga jini sai zuba yake, ya rasa yadda zaiyi, dakyar ya
tattaro nutsuwar sa ya daga Shukrah cak ba tare da ya damu da jinin dake zuba a
jikin taba, yanasata a mota ya zagaya ya shiga yayi reverse ya fita da gudun
gaske"
"Kai tsaye ya wuce Standard (Asibitin Dr.Mariya
galadanci) cikin sa a ya samu Dr.Zainab zata fita, Zainab ganin halin da
Shukrah take ciki yasata karbar ta tawuce da ita labour room"
"Ba karamin tashin hankali Safeer ya shiga ba ganin
awan shukrah uku cur a labour room amma ta kasa haihuwa ko kuka ta kasa sai
innalillahi wa innailayyi raji'un take fadi ,nan danan ya kira Mamah ya fada
mata sannan ya kira Ammii ma ya sanar da ita, bayan kamar minti goma wata nurse
mai suna Salmah tazo tace masa dole fa sai Shukrah tasha inducing drug saboda
HK yaje ya nemo,ba tare da yasan Inda zai samu ba ya fito duk Air condition din
dake cikin dan karamin hospital din nn amma Safeer ya jike da gumi,kicibus
sukayi da Haiydar Wanda Mamah ta kira ta sanar dashi zancen haihuwar,Haiydar ya
dafa Safeer cikeda tausayawa yace haba Safeer be a man mana duk ka wani rude ka
gigice, cuta ae ba mutuwa bace"
"Dafe kai kawae Safeer yayi don bayason magana ma gaba
daya zuwa can yace inducer zaka samo min Haiydar ,Shukrah tana cikin wani
hali.. Pls help me I can't afford loosing her, I just love her
"Da sauri haydar ya wuce be Dade ba sai gashi da
inducer yaje ya mikawa wani Nurse yace ya kai musu sannan ya dawo gurin Safeer
yana bashi baki,"
"Cikin ikon Allah Shukrah nashan inducer ta nemi ciwo
ta rasa ji tayi kamar zatayi amai, ta kira nurse tace mata
"Amai zanyi
kamani inje toilet"
"Yi aman ki Anan kinji tace mata, kakarin Aman Shukrah
tashiga yi nan danan sai ga baby ta fado ta sa kuka kuwa Shukrah ta koma ta
lafe sai bacci,cikin bacci Shukrah taji bayanta ya wani amsa,ta bude ido a
firgice ta fara kuka jitake kamar zata mutu ga baby tana gani nurse tana
gyarawa, sake sakin ihu tayi sakamakon mararta da bayanta da suka kuma kullewa
tace wayyo Allah ka taimakeni, duk likitocin suka yo kanta, Dr Zainab ta matsa
cikin ta tace Salma zo akwae wani acikin nn da alama, Salma ta karaso da sauri
tarike Shukrah tace yi nishi kinji Shukrah yanzu babyn zai fito, Shukrah ta
marai raice tace vazan iya ba wallahi ni mutuwa zanyi ki kiramin other half
muyi sallama"
"Cikeda tausayi Dr.zainab shiga shafa kan Shukrah,tace
cutafa ba mutuwa bace Shukrah kiyi hkr kiyi nishi ko guda days ne please"
"shukrah bata San sanda ta kankame Dr Zainab ba tayi
wani nishi ae ko sai ga baby nan placenta ta fito, an an aka shiga gyara babyn
cikin kokaci kadan aka jerewa Shukrah twins dinta duk mata, sai anan aka bar
Safeer da haiyar su shigo,Shi Safeer bamaya yin ta Twins shi ta Shukran sa
yakeyi ya karasa da sauri ya rungume ta yana mata sannu, shiko haiydar Twins
yaje ya hade ya rungume yana kissing dinsu nan da nan suka shiga ransa, yashiga
snapping face nasu yana turawa mutane, kafin kice kwabo asibiti ya cika da yan
uwa da abokan arziki, zuwa dare aka yi discharging nasu suka tafi gida "
" Washe gari tun safe mutane suka cika gidan ba masaka
tsinke Safeer ko wanka be samu yayi ba sai gidan Haiydar ya tafi yayi acan,
haka dae gida ya cigaba da cika har ana gobe suna, da sassafe Aunty Maryam Anas
ta aiko da trolleys uku cikeda kayan
babies dana maman babies, da kuma raguna
guda biyu, "
" Ranar suna da asuba safeer ya fadi sunayen da yayi
yaransa huduba da, ta farkon yasamata *Fateema*za a dinga kiranta da ( *Afaf*)
sunan Ammii 'n Shukrah ta biyun kuma *Maryam*( *Anan*) taci sunan Aunty Maryam
Anas, haka aka sha shagalin suna kowa sai murna yake, don har yan uwan su
Shukrah na kd, dana maid, dana Damaturu sai da suka zo, haka yan Adamawa duk
sunzo, Washe gari da yawa suka tafi wasu kuwa sunce sai next week "
" Safeer baya samun ganin Shukrah kwata kwata amma be
damu ba kasan cewar shikansa bashida lokacin kansa don aikin company yayi nisa
sosai kuma akwai bukatar lallai yaje gurin saboda hk kullum inya fita da safe
baya dawowa sai dare "
" Yau sati biyu da haihuwar Shukrah kuma yau aka
kammala ginin company 'n Safeer, Yan uwa duk sun koma sai Shukrah kadae da
twins don labeeba da labeeb an tafi dasu gidan Ammii acewar ta wae basaji zasu
iya buge mata yaranta, wanka tayi ta shirya cikin wani material blue tasa ear
ring pink da bangles pink colour ta shafa powder kawae da lip stick ta daura
pink din karamin veil a kanta ta dauki *AFAF* Tana feeding dinta, safeer ne ya
shigo cikin dakin hannunsa rike da shopping ya ajiye yana mata murmushi ,
karasowa kan gadon yayi ya zauna ya kura musu ido yana jin son su sosai aransa,
dauko *ANAN* Yayi ya daura kan cinyarsa yana shafa gashin daya rufe mata goshin
ta, yace Other half wannan yarinyar tana kama dake duk nafi sonta cikin yaran
nn 4 "
" Dariya Shukrah tayi tana kallon *AFAF*Tace Nikuma
nafison wannan saboda da kai take kama wallahi, murnushi yayi yace mummuna da
ita kuwa sannan ya dauko wayarsa yayi snapping Shukrah a yadda take tana
feeding *AFAF* bata rai tayi wane zata yi kuka tace wallahi banaso me yasa
zakimin hoto a hk, sai wasu sun gani ko, ta zare *AFAF*daga jikinta sannan ta
gyara rigarta ta ajiye ta ta mike da niyyar fita, yayi Saurin ajiye *ANAN* Yazo
ya rungume ta tabaya yace meye nayin fushi kuma, ungo wayar kiyi deleting da
hannunki kinji tawan"
"Karbar wayar tayi tayi deleting pictures din sannan ta
juyo ta rungume shi tayi masa kiss a forehead, Saurin rike fuskarta yayi
yashiga kissing din ko ina na fuskar kafin ya gangaro bakinta yafara tsotsa
kamar wani mayunwaci "
" Yau akayi bikin bude company'n safeer, bikin daya
samu halartar manya manyan mutane yawanci abokan Abbah ne sai ko abokan aikin
Safeer din, *Ahmad da Azeeza* ma sun zo,
zokuga murna gun Shukrah jitake kamar ta goya *Azeeza* ta rasa inda zatasa
kanta sai hidima take da ita, haka aka bude company mai suna *MAI LAFIYA GROUP
OF COMPANY*, haka taro ya watse washe gari kuma aka yi saukar Alqur'ani mai
girma akayi addu ' ar kariya sannan aka tashi"
"Bayan kwana arba' in Shukrah ta koma aikin ta don
miemie ta dawo gidanta da zama ynx tana ss3 sun gama waec suna jiran Neco saboda hk bata zuwa ko ina sai zaman rainon
twins"
"Bayan shekara uku "
An samu nasorori masu yawa a company'n Safeer haka ma
Shukrah tasamu nata nasororin don ynx tayi suna sosai kan kwarewarta a fannin
ido, Mutane da dama Shukrah ta dauki nauyin
musu aiki haka ma glasses kyauta takewa mutane (Nima ita tayi min nawa kyauta),
sosai take samun albarka gurin mutane, haka ma Daddy ya naji da ita yana kuma
alfahari da ita"
Yau Aysher ta haihu, sai dai dan bezo da rai ba, haka aka
sha kuka aka barwa Allah, "
" Yau graduation din su miemee, zo kuga rawar kai sai
da Shukrah Ta mata dinki kala biyar na get together da zasuyi, haka Mamah ma
set uku ta dinka mata"
"6:20pm Miemie ta gama shirin tafiya Get together, riga
tasa body hug pink da jeans blue tayi rolling da pink din veil tasa pink flat
shoe tadau wata pink purse tasha makeup
kamar wata makeup artist maryam tafida ce tayi mata, parlour ta fito ta kalli
Mamah, Mamah yanzu zamu wuce ina car key dinki zanbiya in dauki Amatullah mu
wuce"
"To Allah ya kiyaye hanya, Mamah tace tana mikawa
Miemie car key dinta, kaci bus sukayi da safeer yana kokarin shigo wa karemata
kallo yayi sannan yace 'gidan ubanwa zaki a hk'?, tura baki tayi sannan tace
get together zani, kwada mata lafiyayyen mari yayi yace ke mahaukaciyar inace?
A hk zaki fita ko to wallahi ba inda zaki, har gaban Mamah ya kaita yayi mata
fada yayi mata nasiha sosai har sai da tayi kuka sannan ya wuce ya bar
gidan"
"Labeeb da labeeba ne suka shigo cikin gida da gudu
daga school Shukrah da safeer suna zaune suna hira a parlour suka fado
kansu"
"Labeeb cikeda ihu yace mamy kinsan yau me akayi mana a
skul, Shukrah ta girgiza kai alamar a a, yace wild animal
1.LION
2.TIGER
3.LIZARD
Labeeba tayi Saurin katseshi tace mamy karya yake lizard
reptilian ne, Labeeb da bayason raini ya buge bakinta yace waye makaryachi, ta
bare baki zatayi kuka Safeer yayi Saurin cewa selfie🤳🏻 da sauri
duk suka dawo bayansa ya kashe musu selfie kuwa"
" *ALHAMDULILLAHI*
*ANA NAKAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI INA ROKON ALLAH YA YAFE
MIN DUK WANI KUSKURE DANAYI, READERS IDAN NAMUKU BA DAE DAE BA KUYAFE MIN,
ALLAH YA YAFE MANA GABA DAYA*