AUTAR HAJIYA Page 51-60 (The end)
.
Alhmdulillahi dan kuwa yanzu ansamu jituwa tsakanin Fadila da Zainab ```{AutarHajiya}``` yanzu kowace tarage jin haushin 'yar'uwarta,
Saidai fa maganar girki idan fadila tayi, basu iya ci sai dai su d'an yafuta su tashi badan sun 'koshiba, Auta kuwa kalaluwan girki takeyimasu masu dad'in gaske.

Watarana Auta na zaune falo tana kallon wani tsohon Indian film mai suna *(Maharaja)* ta maida hankalinta tsaf kan TV sai jitayi an rufe mata ido ta baya, takama lalube tana dariya, takama hannun da aka rufemata fuska ta ri'ke tana dariya, tana cewa "dan Allah ko waye ayimin afuwa kada ayi wani Abu a film dinnan ban ganiba,
Sakin fuskar tayi ta zagayo ta zauna kusada ita, tana dariya itama Auta dariyar take, takai kallonta ga Fadila tace "Kai sister yanzu abinda kikayimin kin kyauta, kinja an wuce banga wani wurinba, Fadila tayi dariya tace "to ay sai kiyo tariya, cike da nishad'ia Auta ta mi'ko mata remote d'in tana dariya tace "kar6i tariyo min, dan tasan ba maganar tariya tunda ba kaset bane ta sanya.
Fadila tayi dariya tace "ni ban iya wannan tariyar bakedai ki tariyo tinda kece meson kallon, murmushi kawai Auta tayi tacigaba da kallonta.
Fadila tayi dariya tace "ni ban iya wannan tariyar bakedai ki tariyo tinda kece meson kallon, murmushi kawai Auta tayi tacigaba da kallonta.
Kusan Awa d'aya da yan mintoci Fadila na zaune tana taya Auta kallo, saida film d'in ya'kare ana shirin sanyo wani, Auta takai dubanta kan agogon dake manne jikin bangon d'akin taga har 12 ta d'an gota.
.
Auta ta kalli fadila tace girki fa? Kinsan fa rana tayi baki d'ora mana ba, gaskiya ki tashi kada kiyi mana horon yunwa, fadila tayi dariya tace wace ni in horaki da yunwa, kinaso me gidan ya d'aga min yellow card kenan abani hutun sati biyu, Auta tayi dariya tace ayko baze fara ba, kinsan kuwa irin son dayake maki, ai ko hutun kwana biyu baze iya bakiba baranatana sati biyu, dariya sukayi su duka.Bayan shiru ya ratsa na yan wasu mintittika Fadila takai dubanta ga Auta tace "Niko Auta me zaihana murin'ka yin girki tare, ranar girkinki muyi tare nima idan nawa yazo muyi tare.
Auta tayi dariya, tariga tagama d'agowa da fadila, so kawai take tari'ka tayata dan itama tasamu girkinta yayi armashi kamar nata.
.
Tare suka shiga kitchen suka fara girki, farar shinkafa suka dafa me had'e da makaroni, sannan sukayi miya mai rai da lafiya, cikin 'kan'kanin lokaci suka gama suka jera kome kan dining sannan suka gyara kitchen d'in tsaf sukayi moping, kafinnan kowace tawuce d'akinta ta sheka wanka suka fito falo suka zauna zaman jiran me gidansu, sunyi kyau suduka shar dasu abin gwanin ban sha'awa.
Khaleed ne yashigo gidan da sallama suduka suka tashi suka tarbeshi sunayimashi sannu da zuwa, fadila ta kar6i jakar dake hannunsa ta wuce mashi da ita d'akinsa,
Saida yaba Auta lafiyayyen kiss sannan ya wuce d'akinsa, ya tarar har fadila tagama had'a mashi ruwan wanka,
Wanka yashiga, bayan yafito ya sanya kananan kaya marassa nauyi, sannan suka fito suka zauna kan dining, sunfara cin abinci gwanin ban sha'awa sunata fira suna dariya,.
khaleed ya kai dubansa ga Fadila yace waini fadila kodai kema kin Shiga makarntar koyon girkine bansaniba,? Auta tayi saurin tashi ta d'auko filo daga cikin filon kujerun daka zagaye a falon ta mi'koma Fadila tana dariya tace "kar6i sister yimasa waigi kada yafadi ace mune muka kadashi, suduka suka sanya dariya hada kyalkyatawa,
.
Fadila tad'an tsagaita da dariyar datake tace "bawata makaranta nashiga ba illah makarantar sister d'ita gata zaune kusa dakai, ta nuna Auta.
Cike da jin dadi, khaleed yad'aga hannunsa sama, yace "Allah nagodema daka bani mata nagari masu sona masu 'kaunata masu son kasancewata cikin farin ciki koda yaushe, ya kallesu su duka yace Allah yayi maku Albarka suduka suka amsa da "Ameen.
Ranar dai haka suka wuni cikin nushad'i da annushuwa, dan ranar khaleed be fita ko'inaba, saboda jin dad'in zaman gidan dayayi.
*************************
*_BAYAN WATA TAKWAS_*
*************************
*_BAYAN WATA TAKWAS_*
Ahankali take takawa zuwa d'ankin Auta saboda nauyin da cikinta yayimata, tura kyauren d'akin tayi sannan ta shiga da sallama, Auta dake kwance kan kujera 3seater itama da 'katon cikinta, idanunta rufe kamar me bacci, jin shigowar Fadila yasa ta bud'esu takai dubanta gareta, sannan takai dubanta ga cikin Fadila, har cikin ranta take tausayama Fadila yanda take fama da ciki, dan tinda tasamu cukin take ta rashin lafiya, yau zazza6i, gobe ciwon kai, ga kuma rashin 'karfin jiki, babban abin ban tausayin shine tinda Fadila tasamu ciki bata iya cin abincin kirki, ga wani irinkumburi datayi, danma koda yaushe khaleed na kula da lafiyarsu itada Auta.
Duk da itama Auta tana d'an ta6a rashin lafiyar jefi-jefi, amma idan ka kalli fadila sai kace Auta ba ciwo take ba.
Tare suka fito falo suka zauna suna firar duniya, duk rabin firar tasu ta yanda zasu tsara rayuwarsu ne nan gaba, da yanda zasu had'a kan 'ya'yansu sutashi kansu a had'e.
.
Yau Fadila ta tashi da matsanancin ciwon mara da ciwon baya, ga 'kugunta da takeji kamar ze 6are saboda azabar ciwo,
.
Yau Fadila ta tashi da matsanancin ciwon mara da ciwon baya, ga 'kugunta da takeji kamar ze 6are saboda azabar ciwo,
Daga khaleed har Auta sun rud'e sun rasa inda zasusa Kansu, cikin tsananin rud'ewa khaleed yakira Momynsa yasanar da ita halin da fadila take ciki, nan ta umarceshi da sutafi asibiti gatanan zuwa asbitin, tare da taimakon Auta aka kai Fadila mota sai asibiti,
An wuce da ita labour room, nurses sun taru kanta anata faman amma, har 'karfe 3 na rana bata haihuba, lokacin Momyn Fadeela ta iso asibitin cike da tashin hankali, nan ta iske Momyn khaleed sai kai komo take cikin asibitin, kallo d'aya zakayimata ka gane tana cikin tsananin damuwa, khaleed kuwa tagumi yayi yarasa me kemasa dad'i.
Lokacin wayarsa tayi ringing, hannu yasa ya dauka, sunan Auta yagani yana yawo kan screen d'in wayar, da Sauri ya d'auka ya kara a kunneshi, muryar dayaji Auta tana magana da itace ta d'aga mashi hankali, cikin tsananin ciwo take maganar _"kha....khaleed kazo ka taimakeni zan mutu_......
Dai-dai lokacin wayar ta su6uce Daga hannunta, cikin tsananin rud'ewa khaleed yasanar da momynsa abinda ke faruwa, tare suka tafi gidan, da sauri suka shiga bayan sun ajiye motarsu inda yadace.
Dai-dai lokacin wayar ta su6uce Daga hannunta, cikin tsananin rud'ewa khaleed yasanar da momynsa abinda ke faruwa, tare suka tafi gidan, da sauri suka shiga bayan sun ajiye motarsu inda yadace.
Bedroom suka isketa cikin jini male-male, ba Alamar numfashi tattare da ita, Cikin tsananin rud'ewa suka d'auketa suka nufi asibiti, khaleed kuwa banda kyarma ba abinda yakeyi, dan ko tu'kin yinsa kawai yakeyi, amma besan inda kansa yakeba, da taimakon Allah suka isa asibitin, labour room itama aka wuce da ita.
Nan fa likitoci suka taru akanta, amma abin sai du'a,i
Wasa-wasa har karfe shidda na yamma basuji wani dadd'an kabari ba, lokacin kuma Hajiyar Auta ta dad'e da zowa asibitin, zazzaune suke sunyi jugum-jugum Kowa Allah-Allah yake yaji ance d'anshi ya haihu, yayinda khaleed ke cikin matsanancin tashin hankali.

Can gurin 'karfe shida da rabi dictor yafito daga d'akin duk yahad'a gumi, duk illahirin jikinshi ya 6aci da jini, suna ganin fitowarshi sukayimashi caaa, suna tambayarshi "Yaya dai doctor sun haihu kuwa, wata nannauyar ajiyar zuciya likitan yayi sannan yace "ina mijinsu yake?, khaleed yace "gani, biyoni office, Momyn khaleed tace dan Allah doctor kayi mamu bayani anan Kowa yaji halin da suke ciki, ko hankalinmu ya kwanta, nan da kake gani muduka iyayensune, ba wani abu ka fad'i kawai.
Doctor ya share wani gumi daya tsatstsafo mai a goshi, yace " ina farin cikin sanar daku cewa su duka sun haihu, Fadila ta haifi yara biyu mace da namiji, sai kuma Zainab ta haif d'a namiji.
Lokaci guda fuskokinsu suka washe cikin farin ciki suka fara yima Allah godiya,
Sai lokacin likitan yacigaba da magana "amma inaso Ku Sani Allah shi ke badawa kuma shine me kar6ewa a duk lokacin dayaso,
Sai lokacin likitan yacigaba da magana "amma inaso Ku Sani Allah shi ke badawa kuma shine me kar6ewa a duk lokacin dayaso,
.
saboda haka ina me ba'kin cikin sanar daku d'a namijin da aka Haifa ya rasu, kafin daga bisani itama uwarsa tabishi, Allah yafiku sonsu, saboda haka kuyi hakuri addu'a kawai zakuyi masu sai Ku d'auki gawar kuje gida ku shiryasu dan kada akaisu matuary,

```Innalillahiwa'inna,ilaihirrajiun```
Suka furta lokaci guda suka shiga matsanancin tashin hankali, khaleed kuwa jiyayi 'kafafunsa bazasu iya d'aukarsaba zaman dirahan yayi yana zuabar da hawaye, yana cewa "shikenan Zainab kin tafi kiin barni ina zan saka raina, yakama 'kafafun momynshi yari'ke gam yana cewa Momy kicema Auta kada ta mutu ta barni, sosai Momy ta taasayama d'anta ganin yanda yake aurutai marassa kan gado, itama hawayenne suka gangaro kan kumatunta.

Hajiya kau tinda likitan yafad'i rasuwar taji kanta yayimata wani Jim, tana tsaye dafe da kai, kawai sai jinta sukayi 'kasa ta fad'i sumammiya.
Da sauri sukayi kanta, suna salati, nanfa aka shiga wani sabon tashin hankali, dan Hajiya an yayyafa mata ruwa amma ba Alamar numfashi tatare da ita.
Nan aka d'auketa Emergency aka nufa da ita, likitoci ne suka taru dan ganin an ceto rayuwarta, akalla ankai awa biyu kafin asamu numfashinta yafara dawowa.
Nan aka sanar da Baban Auta da baban khaleed abinda ke faruwa asibitin,
lokaci guda suka iso hadda mahaifin fadila, nan aka d'auki gawar jaririn data mahaifiyarshi aka nufi gida dasu, tin daren a kayi masu wanka, aka shiryasu, sukayi kwanan keso.
lokaci guda suka iso hadda mahaifin fadila, nan aka d'auki gawar jaririn data mahaifiyarshi aka nufi gida dasu, tin daren a kayi masu wanka, aka shiryasu, sukayi kwanan keso.
``` Allahu Akbar, kulli nafsin za'ikatul maut" dukkan me rai mamacine```
.
.
Bayan kwana bakwai da rasuwar Fadila, kuma ranar aka rad'ama yaran suna, d'an gurin Auta yaci sunan Baban khaleed, Ana kiransa shaheed, sai kuma babyn Fadila wacce yanzu haka tana hannun Auta ta had'a da yaronta tana shayar dasu, ita kuma sunan Mahaifiyarta aka maida mata *_Fadila_* mashaAllah anyi suna lafiya lau, duk da ba wani taro akayiba, amma 'yan'uwa da abokan arzi'ki sunzo, Auta tasha kyaututtuka ita da baby's daga gurin danginta da dangin khaleed, 'yan'uwan Fadila kuwa sha tara na arzi'ki suka had'oma Auta, abinda yakara d'aga hankalinta tari'ka sharar 'kwalla tana tuna sister d'inta Fadila.
momyn khaleed ce tasamo wata dattijuwar mata wacce zata zauna da Auta dan ta tayata rainon yan biyunta.
***************************
Bayan kwana arba'in su Auta sun gama wanka, suduka suna cikin 'koshin lafiya itada yaranta, sunyi 6ul-6ul dasu yarinayar Fadila kya'kyawa kamarsu d'aya da mamarta, sai dai ta d'auko farin babanta.
shaheed kuwa babansa ya biyo, fari tas dashi, kamar d'an larabawa.
Haka yaran suka taso cikin kulawar iyayensu, dan khaleed kullum idan yataso ayki be'kara fita zama yake suna raino tare.
.
*_BAYAN SHEKARA BAKWAI_*
Wasu kyawawan yara na hango a harabar gidan khaleed suna wasa da ball, cike da nishad'i.
Can kuma sai suka kama rigima bansan kome ya had'asuba, macen ce ta rugo da gudu, tashigo gida, namijin na biye da ita, jikin Auta tafad'a tana cewa "Ammi kice kada ya dakeni,suanan dasuke Kiran Auta dashi kenan _*Ammi*_ Auta ta'kara rungumeta, tace"kai shaheed kada ka doketa, miye ya had'aku? "Ammi wai dan munyi ball naci 3 itakuma taci 1 dan nayi dariya shine ta dokeni ta rugo.
Auta ta rungumoshi jikinta tace yi ha'kuri kaji shaheed d'ina bazata 'karaba.

Ya kalli Fadila wacce ta'kara narkewa jikin Auta yace "kuma yarinya idan kika 'kara saina doddokeki.
Ta kalli Auta tace "ai dai Ammi bazaki bari ya dokeniba ko? Auta tace Bazan bariba mana, aiko Fadila najin haka sai ta kyalkyale da dariya tayima shaheed gwalo, Aiko yabiyota da gudu ze doketa ta ruga tana kiran Ammi... Ammi kice kada ya dokeni, Auta ta tashi tana 'ko'akrin raba rigimar ne khaleed ya shigo da sallama, aiko da gudu suka ruga suka rungumeshi suna fad'in _welcome my daddy_ 'daga Fadila yayi sama yana dariya yace welcome my baby, sannan ya ajiyeta ya d'aga shaheed yace "welcome my dady, sannan suka wuce ciki, nan suka zauna yana tambayarsu karatun dasuke a school suna bashi amsa, dan yaran badai 'ko'kariba,
Auta ce tagabatar masu da abinci, suka zauna sukaci sunata nishad'i, bayan sun gama khaleed yace su shirya zasu fita Unguwa, aiko nan suka kama tsalle suna murna,
Auta ce tagabatar masu da abinci, suka zauna sukaci sunata nishad'i, bayan sun gama khaleed yace su shirya zasu fita Unguwa, aiko nan suka kama tsalle suna murna,
Sun fito cikin shiri, sunyi shar dasu gwanin ban sha'awa Fadila sanye cikin wata had'ad'diyar doguwar riga, milk me zanen Flowers pink, sai takalminta masu tudu suma pink colour, kanta kuwa yasha gyara, kamar na yan indiya, yazubo har bisa 'kafad'unta, shaheed kuwa fararen jacket ya Sanya, sai farin takalmi cover yayi kyau abinsa, haka suka shiga mota gidan Momyn khaleed suka fara zuwa, cike da murna ta tarbesu, tanata ji da yan jikokinta, har daddyn khaleed yadawo suka gaisa sannan suka wuce,...
.
Gidan su fadila suka sauka, da sallama suka shiga gidan, da gudu shaheed ya Fad'a jikin Momyn fadila yana Fad'in momyna gani nazo, cike da fara'a tace "a'a yau megidanne da kansa, to sannu da zuwa, nan suka shigo suka gaggaisa, sunjima anan kafin daga nan su wuce gidan Hajiya.
A gidan Hajiya suka 'karasa wuninsu, sai bayan ishsha'i suka tafi, yaran sunata kewar Hajiya, da Fadila da kyar ta yarda aka tafi da ita wai ita a dole nan zata kwana, saida akayima wayo akan gobe za'a kawota tare da kayanta duka, sannan fa ta yarda aka tafi da ita tanata murna gobe za'a maidota gurin hajiyarta,
Shaheed ya harareta yace, yarinya nima idan aka kaiki nima sai an kaini gurin Hajiyata (Momyn Fadila)
Khaleed yace duka gobe zan kaiku, aiko suka shiga murna.
Khaleed yace duka gobe zan kaiku, aiko suka shiga murna.
*_Anan inso inyi amfani da wannan damar inyi kira ga 'yan mata masu kafewa akan su bazasu auri me mataba, shin bakusan tin kafin kazo duniya Allah yariga ya tsara yanda yakeso rayuwarku yakeso ta kasanceba_
*Kawai ku ro'ki Allah yaza6a maku mafi Alkhairi*
```Alhmdulillahi anan nakawo 'karshen littafina me suna Autar Hajiya,
Ina mi'ka dumbin gaisuwa ga masoyana a duk inda kuke Allah bar 'kauna, nagode```
Ina mi'ka dumbin gaisuwa ga masoyana a duk inda kuke Allah bar 'kauna, nagode```
'