Sunday, September 13, 2020
BA DON SHI BA Page 21 to 30
Share this
BA DON SHI BA Page 11 to 20
Share this
Wednesday, August 28, 2019
BA DAN SHI BA Page 31 to 40 (The end)
Jefa kafar ta kawai take ba tare da tasan inda take nufa a da gidan maman salaha tayi niyyar zuwa amma yanxu saboda takaici da bakin cikin da take ciki yasa ta fasa kuma bata da niyyar komawa gida tana tunanin zuci tana share zazzafan hawayen da ke kwaranyo mata wai ita yau ake kira da karuwar gida kuma a gaban ta tabbas tasan ana zagin ta amma bata taba jin zafi irin na yau ba.
tsayawa tunanin ta yayi cak ganin wata tsohuwa kwance kamar mara lafiya a gefen titi ga yara na ta jifan ta wasu kuma suna watsa mata ruwa.
karasa tayi da sauri ta kori yaran yaran a wajen domin lokaci daya taji tausayin matar ya kamata.
bata nuna tana kyamar ta haka ta tallabo kanta wanda yake kamar tarin kudaje saboda dattin sa ko tsakar ba'a gani kayan jikin ta duk sun yafe kafar ta ko takalmu babu kana kallon ta kasan mahaukaciya ce.
tallabo kanta tayi jikin ta zafi rau sai rawar sanyi take sai da *Jiddah* ta zubar da hawaye saboda tausayi.
kirqm mansu take shirin yi a waya sai kuma ta tuna ai tabar wayar a gida dakyar taja,matar gefen wani gida sannan tace"mamah ki jira ni anan yanxun nan zan dawo bata jira amsar ta ta juya da sauri ta koma gida.
duk basa nan ba bata lokaci ta dauko wayar ta ta kunna number diin mansur ta fara dialing ta fada inda zai sameta abinka da me nema a duhu ba musu ya amsa da sauri.
yqndq tabar ta haka ta tarar da ita anan kwqnce kudaje sau bin ta suke saboda daudar dake jikin ta tausayin tane ya kara kamata.
tanq zaune haka sai ga mansur ya iso ganin ta da yayi a firgice haka yasa shi tambayar ta ko lafiya.
bayani take masa fuksa daure tana fada masa asibiti zasu kai wannqn baiwar ALLAHn ganin da yayi ba wasa a fuskar ta yasa shi amsawa da tow ba don ranshi ya so ba dan banda wari ba abinda wari ba abinda ke tashi jikin matar.
suna sakata a bayan mota suka nufi asibiti da sauri aka amshesu gado aka bata a aminity aka gama komai aka daura mata drip ba wqni abu bane ke damun illah yunwa abinda likitan ya gama fada musu kenan.
tayi alkawarin ba zata kara bari hakan ta faru ba tana jin matar a jikin ta kamar jinin ta kuma tqna tausayin ta matuka.
wuni curr tayi a asibitin sai yamma tayi niyyar tafiya gidah,saboda asibitin baa kwqna.
sai da ta tabbatar tabar komai da za'a bukata sannan ta tafi.
*BAYAN SATI BIYU*
A yanzu kam sai dai muce ALHAMDULILLAH jikin Anty yayi sauki sunan da Jiddah ke kiran ta dashi kenan domin kuwa yanzu fess take ba abunda ta rasa da kudin take mata komai.
amma yanzu an tabbatar da mahaukaciya ce hakan bai hana jiddah kaunar ta dan har ta gane ta wani bin zatayi hauka da ihu amma da zarae Jiddah taxo shikenan komau zai lafa.
duk wannan abinda ake inna asabe bata dq labari hankalin na gun Rabi dake kwanxe ba lafiya kuma an rasa me yake damun ta yanzu indo ce ke tashen iskanci shiyyasa inna bata lura ba.
antyn jiddah taji sauki saboda haka likitoci suka ce a kaita gidan mahaukata tayi na'am da hakan kuma.
daga nan asibitin suka wuce an gama komai an bata kaya dakyar aka raba su da jiddah itama kuka take dakyar aka lallaba suka rabu ita kuma ta wuce gidah.
*Ur's princes deejer*
[18/03, 14:42] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
WE HERE TO EDUCATED,MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS.
✨✨ *BA DON SHIBA* ✨✨
*Story $ Written*
*By*
*KHADIJA AHMAD*
*Princes deeja💝*
*Wow!I must say thanks to all my fans,U guys are awesome,ur comment give the urge to write more and more to u,I wish u enjoy and learn so many thing in dis novel don't forget that I luv u every and each one of u guys MIE LUV U💝*
*Page* 1⃣0⃣1⃣
Kwanci tashi ba wuyq a wajen ALLAH yanku kimanin 5month kenan Jiddah ke tare da Antyn ta duk wani kudi da take samu a kqn ta suke karewa domin asibitin mahaukatan da ta kai ta mai matukar tsada ne kowqne lokaci cikin tambayar ta kudi suke ita bata gajiya haka zata bada.
jiki kam yayi sauki sosai domin yanxu bata ihu sai dai ta rinka surutai ita kadai amma kuma tsaff take kamar ba mai tqbin hankali ba.
Sauri sauri take shiri saboda zuwan su nyt party kuma duk dare tana son taje taga antyn tah kwana2 bata jeba.
fitowq tayi domin fita daga gidan amma haladu ya tare mata hanya yana binta da wqni mayen dan shigar dake jikin ta marqbar ta da tsirara kadan ce.
cikin muryar shi da ta koma ta en maye ya fara magana"ke yarinyar gaskiya kina raina min sense kwarantsi ga kaya a cikin gidan mu amma sai naje waje na biya ya fada yana shafo kafadun ta.
hankada shi baya tayi sannan ta fara surfa masa masifa amma gaskiya kai dabba ne a dabbobin ma bunsuru ni kanwar ka kake wa irin wannan maganar saboda akuyanci gaskiya sai yanxu na kara yadda kai din babbab jahili....Ai bata karasa ba taji saukar mari a kuncin ta kuma ta tabbatar ba haladu bane.
inna asabe ce hannu rike da zani tun sanda haladu ya mata magana take sauraran su batayi niyyar fitowa ba sai da taji zagin dq Jiddah ta masa cikin hargowq ta fara magaba"kina karuwa er iska har a nemeki kina cim fuska to wqni dare ne jemage bai gani meye baa sani akanki keda matacciyar uwarki ai gado kikayi a wajen ta itama har tabar duniya karuwqn ci ne sana'ar ta kafin ta mutu har guduwq tayi yawon karuwan ci a cqn duniya aka jiyo labarin mutuwar ta.
kinga ko kece babbar er akuya kai kuma haladu kwantar da hankalinka badai wannan jikin nata kake so ba to kamar ka samu ne indae ina gidan nan wuce muje.
tunda ta rike kunci har cin mutuncin da ta mata kanta na sunkuye hawaye masu zafi na gangaro mata zuciyar ta kamar ta tarwatse saboda bakin ciki.
fita tayi a gidan ta hau napep asibiti ta wuce tqna jin kiran mqnsur amma taki picking domin a hqlin da ta ke ciki babu wqnda zata iya saurara.
ta same ta tqna bacci cikin kwqnciyar hankali abinda ya dan sanyaya mata rai kenan itamq kwqnciya tayi a bayqnta tayi shiru tqna tunanin rauuwar yanda ta koma amma kuma duk sanda taji tana son daina wa sai ta kasa to,meyasa tun lokacin da Rabi ta fara ciwo likitoci sun tabbatar HIV ne da ita ga kuma ciwon sanyi da yayi mata mugun kamu duk wanda take harka dasu bai ma zuwa wajenta duk sun guje ta tunanin da take idan da akanta haka ya faru itama haka zasu guje ta tana wannan tunqnin har bacci ya dauke ta.
haka rayuwq take tafiya Jiddah ta dena kwana a gidah tun randa haladu randa haladu ya kulle mata kofa lallai sai tq bashi hadin kai dakyar ta samu ta mai wayo ta gudu dan innah asabe yanxu hankalin tq na gun Rabi da har jikin ta bai sauki.
yanxu asibiti tqke kwqna tare da antynta sai watq rqna kuma gidan mansu ko daya daga cikin samarin ta.
Rayuwa tq mika inna asabe har yanzu tana fama da jikin Rabi ga indo yanxu ta fitsare itama bata kwqna a gidqn haladu sai ya ga dqma daga ita sai Rabi Asiya ce kawai ba ruwqn ta itqce ke taya jinyar duk tabi ta rame kamar ba asabe ba.
*********************
*2 years later*
Cikin farin ciki ya ke sakkowa daga matalar jirgin fuskar sa cike da annushuwa ya kara kyau ya goge fatarsa glowing take alamun hutu ya zauna ya koma handsome guy wanda samun irin su ke wuya *AMMAR* kenan bayqn shude 5 years da yayi a kasar india yau gashi ya dawo zuciyar sa cike da bege da kaunar son ganin Jiddah dama burin shi kenan kuma yayi alkawarin gurin ta zai fara nufa.
*tofahhhhhh ku biyoni domin jin yadda zata kasance domin kuwa koni naji tsoron dawowar ammar*
*Ur's princess deeja* 💝
[25/03, 17:33] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
WE HERE TO EDUCATED,MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS,
✨✨ *BA DON SHIBA*✨✨
*Story & Written*
*By*
*KHADIJA AHMAD*
*Princes deeja*
*Page* 1⃣0⃣2⃣
*LAST PAGE*
Tsaki yaja me cike da takaici ganin,har yanxu drivern bai karaso ba gaba daya ya rasa inda zai sa kanshi babbab burin shi shine yaje yaga jiddah.
yana cikin,wannan,tunanin sai ga drivern ya karaso bai tsaya jin ta bakin sa ya shige motar tafiya sassauka sukayi sai gasu sun shigo cikin unguwar ganin yayi drivern na nufar hanyar gidan su da sauri ya katseshi tare da fadin banan zamuyi ba kwatqnce ya rinka mai sai gasu a kofar gidan su Jiddah.
Wani farin ciki ne ya lullubeshi ji yake tamkar yau ammai,bushara da gidan aljannah.
shiru kofar gidan,ba kowa har zai shiga ciki sai kuma yaga wata tsaleliyar mota tayi parking a kofar gidan fasa shiga cikin,gidan yayi dan yasan daya daga cikin en iskan yaran nan ne..
tunanin shi ya tsaya cak ganin wata kyakkyawar budurwa ta fito daga cikin motar jikin ta sanye da wasu irin kaya wqnda ko a wadanda ba musulmai ba sai cikakken mara kunya zai sa su.
shima wanda ya sauke ta ya fito tare da riko hannun ta yana fadain"baby yanxun a gida zaki kwqna pls ki bani 2daz mana saboda ke na tsallakr duk abinda nakeyi nazo amma kwqna 1 kika min.
cike da yauki ta fara magana kamar bata so uhmm nifa a hakan ina ganin nayi maka kokari amma ka raina shikenan sai kuma next tym yanxu zan shige.
shiru yayi bai kara magana kudi ya dauko wanda basan iyakar su ya zuba mata a jaka kamo hannun ta yayi ya kai,mata kiss sannan ya shige mota sao da ta ga ya wuce ta jiyo domim shiga.
Abinda tayi arba dasji ne lokaci daya yasa jakar ta faduwq duk kudin ciki suka zube jikin ta ya fara sai,hawaye kamar an bude famfo.
tun da fara zuciyar shi ke bashi wqni abu amma ya karyata hakan sai da ta waigo ya tabbatar da zargin da zuciyarshi ke gaya mishi.
duk da ta canxa amma hakan bai hana shi gane tq a kallo daya.
ita kam tunda ta tsugunna a wajen take kuka bata taba tsammanin *AMMAR* zai dawo a wannan lokacin ba.
karasowa yayi inda take ya tsugunna ya kamo habar ta abin mamaki shima kukan yake kamar ba Ammar da ta sani jarumin namiji ba.
A kasan zuciyar sa ji yakeyi kamar zata fashe wai *Jiddah* ce ta koma haka.
da sauri,ya mike ya shige mota dan idan ya cigaba zama anan zuciyar shi zata iya tarwatsewa.
Mikewq tayi ta shige gidah tana kuka mai cin rai.
A bangaren *AMMAR* kuwa duk wani abu da Abban shi ya tanada na dawowar sa babu wqnda ya kalla kuma ya tambeye shi yace ba komae.
Nura ya kira a waya cikin 5mnt sao gashi ya iso yanayin da yaga Ammar abin ya tada mai hankali idan yayi jaa duk jiyoyin kanshi sun tashi kallo daya zaka masa kasan yana cikin tashin hankali.
Tambayar nura yaui akan halin da yaga jiddah a ciki tun yaushe hakan ya soma faruwa.
tass Nura ya labarta masa komae.
Tabbasa akwai wani abu a kasa bayin kanta bane ya tabbata akwai sa hannun inna asabe a ciki.
Gidan maman salaha yace nura ya rakashi.
da murnar tq ta tarbeshi tare da kawo masu ruwq da drinks.
Itama tqmbaya ya mata akan jiddah nan ta kwashe komai ta fada masa.
tausayin jiddah da kuma soyayyar ta suka dawo mai sabuwq filll.
cikin bacin rai ya fara,magana"nayi alkawarin dui inda magani yake sai na nemo shi sai jiddah ta dawo kamar daa har sai tafi daa insha allah.
cikin hanxari maman salaha ke bashi labafin wani mai magani,da ya shahara wajen karya sihiri.
cikin murna yake tambayar ta wani gari yake.
ai ba nisa a zaria yake unguwar ban xaxxau.
hamdala yayi sannan ya mike suka mata sallama.
gisan su jiddah suka nufa bai tsaya neman ixini ba ya shige gidan kamar daga sama inna asqbe ta ganshi cikin kaduwa ta mike ta shige daki.
dakin jiddah ya nufa kwance ya sameta tana aikin kuka kanta duk ya yamutse idon yayi jaa.
karasa yayi kusa da ita ya zauna sannam ya fara lallashin ta.
sai,da ta yi,shiru sannan yace ta hada kayanta zata je gidan maman salaha.
ba abinda ya bari ta dauka dan yaga duk kayan bana arziki hijabi ne guda daya ta saka sannan suka fita.
inna asabe na kallon su ta window qmma ba halin magana.
tasan tunda wqnnan tsinannen yaron ya dawo tofaj komai nata sai ya lalace.
hijab ta zara sai gidan,muguwar kawar tq ta fada mata duk abinda ke faruwq.
basu tsaya bata tym suka nufi gidan boka na kan tudu.
fada mata yake tayi sakaci domin kuwa idan har yaron nan yana nan tofahh aikin bazai ciba.
wqni kullin magani ya bata sannan yace a tabbatar yaci maganin to bakin shi zai kulle ita kuma jiddah a tabbatar ta taka tofahh sai tayi yawo tsirara.
kudin suka bashi suja fito suna murnar mota suka shiga suna kara firan mugun abunsu.
basu ankara ba sai ji,sukayi drivern yana salati cikin kaduwa suka kalli gaban motar.
wata tanka ce ta nufo su gadan gadan mutane ma sai salati suke takan su wannan motar tabi.
a take muguwar kawar inna asabe ta mutu.
ita kam ana cirotq a motar a sume aka samera kafafuwqn ta duk cixge driven ma a sume yake asibito a kayi dasu ita kuma gawar aka sa a mutuware.
A gidan maman salaha ta kwana washe gari da sanyin safiya ammar ya iso suma sun gama shiryawa ita sao jiddah bata san inda zaa je binsu,kawai take.
sun isa lafiya inda malamin yana kallon aJiddah yasan meke faruwa da ita.
tana hada ido dashi ta hade rai.
daki ya shiga ya dakko wani abu ba tayi xato ba ci tayi kawai an watsa mata abu,mai radadi a jiki.
ihu tayi wanda duk sai da gidan ya amsa.
cigaba yayi da zuba mata ruwan yana kuma karanto addu'a yana tofah mata.
wani abu ya dauko ya turo mata a hanci birgima ta farayi tana ihuu ammar tana kuma fuxgefuxge ammar malam ta kira ya riketa sannan yasa wata igiya ya daure mata kafa da hannaye.
sannan ya cigaba da zuba mata wannan ruwan addu'an.
sai suka ji wahala sannan suka fara magana wai turo su akayi su sata yawon karuwan ci amma sunyi alkawarin zasu fita ya dena kona su haka.
sai daya kara galabaitar dasu sannan suka fada masa wadda tayi aikin.
wqnnan abun ya kara turq mata a hanci a take ta rinka jero atisshawa.
bacci ne ya dauke ta a take.
hamdala sukayi gaba daya sannan malam ya basu wasu magunguna wani a shafa wani kuma a tayi wqnka.
sai da tq kwashe 2hr tana bacci sannan ta farka da salati a bakin ta.
kallon su take daya bayan daya idon ta ne sauka a kan ammar mamaki ne ya kamata to yaushe ya dawo.
tunanin ta ya katse sanda,maman salaha ta riko ta ta mikar da ita tsaye.
gidan maman salaha suka nufa sai tym,take tambayar ta meya faru taga ammar yaushe ya dawo.
bata fada mata sai ruwan wanka ta hada mata sannan ta xuba maganin a ciki.
tana fitowq ta bata oil ta shafa sannan ta kwanta.
inna asabe ana can asibiti sanda ta farka taga kafafunta duk babu su sumewa tayi gashi an kira yaranta duk ba wanda yazo.
da kwatancen data musu aka kawo ta har gida a lokacin ne tayi kuka kamar ranta zai fita gata kwance ga rabi kwance indo kuma ra tafi yawon ta haladi kam dama sai tayi sato bata ganshi ba asiya ce kawai mai taimakonta.
rayuwa ta juya mata baya ji take dama mutuw tayi ta huta.
farkawar jiddah daga bacci ya dadae da shigowar ammr gidan.
tunani takeyi na rayuwar da ta yi a baya gani take kamar a mafarki.
sai da taci abinci sannan ammar da,maman salaha suka mayar mata da abinda ya faru ashe ba,mafarki bane kuka takeyi sosai wanda hakan ke kona zuciyar Aammar da kuma kara jin tsanar inna asabe a ransa.
dakyar suka lallashe ta yi shiru sannan ya fada musu halin da inna asabe ke ciki.
duk da haka sun tausaya mata.
mikewa tayi da sauri wanda hakan ya fadar musu da gaba sai yanxu ta tuno da antyn ta.
fada musu tayi da sauri ammar yace suje dama,da mota yazo.
suna zuwq aka barsu suka shiga dan sunsan jiddah.
duk da bata cikin hankalin ta murna take sosai da ganin jiddah.
abinda ya daure musu kai shine ganin tsantsan kamar da matar sukeyi da jiddah.
ganin haka yasa ammar ya nemi sallama dan zuciyar shi ta bashi akwai wani abu,a kasa.
maman salaha tamai magana da su biya suga inna asabe dan dai yana ganin girman ta ne amma da ba inda zashi.
sun tsaya a kofar gidan inda jiddah ta kafe ba zata shiga ba dakyar suka lallaba ta riko hannun a antyn ta suka shiga.
inna asabe kwqnce abin tausayi kafar ta wqni mugunyan ruwa take fitar wa me wari.
duk ta lalace tayi baki.
duk sun tausaya mata sai daga baya jiddah ta shigo antyn tah na bayanta.
ae inna asabe na ganin antyn jiddah ta zabura tare da fadin"fadin *Fateema* a tare duka suka zube hankalin su ya tashi matuka jiddah kuka tasa ta nufi antyntah.
ruwa ammar ya dibo ya zuba musu inna asabe na farkawa ta fara na shiga 3 damsa boka yace duk randa nagan ki asirin kaina zai dawo wayoohhh ta fada tana cixge gashin kanta gashi ba halin tafiya surutai kawai takeyi tana tona ma kanta asiri.
ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bude idon ta akan jiddah ta dara dora idanun ta sannan juya wqdda ta gani yasa ta mike zaune abinda taji tana fada ne yasa ta kallon su jiddah a yanzu kam kowq ya fahimci inda maganar inna asabe ta dosa.
mamaki sukeyi wai wannan matar itace mahaifiyar jiddah rungume juna sukayi suna murna kowannen su yana kuka me tsuma zuciyar me saurare.
inna asabe jam har yanxu bakin ta beyyi shiru ba abinda ta aikata tun farko har yanxu take fada musu.
duk sunyi tirr da ita sannan suka mike dqn tafiya zuciyar kowa tayi sanyi najin abinda inna asqbe ta aikata.
washe gari dukan su zamfara suka nufa har da ammar kowa yaga fateema sai yayi mamakin ganinta musamman mahaifiyar ta ammar ya barsu ya dawo gisa shida maman salaha cike da kewar jiddah dan yanxi kam duk sun san sirrin zucciyar su.
sai a lokacin Ammar ya fada mahaifin shi duk abinda ke faruwa sannan ya roki alfarmara nema masa auren Jiddah.
mahaifinsa yayi matukar farin ciki cikin kankanin lokacin akayi komai aka gama wata 3 aka sa.
koda yaushe yana hanyar zamfara komae ya gani sao yace zaima jiddah kyai ya siya ya aje mata.
kudi ya zauna masa ya kara fresh .
itama jiddah ta yi kyau ita da antyn ta sun kara fresh rayuwa ta musu dadi.
lokaci baya jira saidai a jirashi gashi har anfara hidimar bikin ammar da jiddah walima kawai akayi sai ranar jumaa aka daure baa tsaya bata lokaci ba aka dauki amarya sai kaduna unguwar kinkinau gida hadadde wanda ske kira da aljannar duniya jiddah tayi kuka sosae domin zaman da sukayi sa mahaifiyat ta sunyi wata irin shakuwa.
a haka ammar ya shigo ya same ta ita kadai duk sun watse lallahshin ta yayi sannan suka dauro alwala sallaj sukayi rakaa 2 suna mai gode ma allah da ya nuna mmusu wqnnan rana mai mai cike da da farin ciki.
zama sike mao cike da so da kauna ammar yana nuna ma jiddah tsantsar soyayya ita kuma tana matikar kulawa dashi a haka zaman su ya ya kasance cike da da farin ciki.
*BAYAN SHEKARA 2*
Rayuwa ta mika a yanxu jidda yaran ta 2 mace da namuji daya sunan mahafinta ya ci muhammad suna kiran shi affan sai ta macen sunan mahaifiar ammar asmau suna kiran ta iftihal rayuwa suke me dadi su da yayn su.
inna asabe kuwa tana cikin hauka gashi ba kafa komai anan take yinshi rabi kam tuni a ALLAH ya daiki kayan shi ita kuma indo tana nan tana fama ciwon aids asiya ce kawai mai lafyar a yanxu kam imna asabe tayi nadama kullum sai da ta fita bara haka take han jiki ta fita har bakin masi tsokana nayi masi jifa nayi *ALLAH YA MANA KYAKKYAWAN KARSHE*
*ALHAMDULILLAH anan na kawo karshen novel dina kuskuren dake cike allah ya yafe min SAI MUN HADU A CIIGABN NOVEL DINA 🌸BARAUNIYA CE🌸🌸*
GODIYA TARE DA GAESUWA TA MUSAMMAN GARESU en *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION ZAMANAWA HADIN KANMU ABIN ALHARINMU*
NA GAESHEKI
*Real shaxee*
*Nasmat*
*Zeesa*
*King boy dan luv*
*Kawata layuxa*
*JABAKA*
*xayeesharyt*
*sisi*
duk ina muku fatan alkaeri hrt u so much
*Urs princes deeja*