Page. 26
Nayi jim sannan na karasa gaban mirror na shafa cream nayi applying powder sannan nayi applying kwalli da lipstick, na zura wata cute arebian gown purple kamar bubu take, na tamke kaina da veil, na juyo nayi tsaye ina kallon bedroom din duk da na shiga gidaje na alfarma naga bedrooms kala-kala amma ban tab'a ganin wanda yayi koda quarter din kyanshi ba, daga gani an zuba naira over, komai na bedroom din abun kallo ne, fitowa nayi na sauko kasa nayi tsaye ina karewa parlourn kallo, tabbas tunda nike ban tab'a ganin mansion mai kyau da girman wannan ba, na wuce kitchen na zage na had'a delicious breakfast na jera komai akan dinning table, nayi tsaye ina kallon stairs, Aaryan ne ya sauko yana sanye da farar jallabiya saida gabana ya yanke ya fad'i, ya karaso ya ja kujera ya zauna na juya nayi serving dinshi before nayi serving kaina sannan naja kujera opposite dashi na zauna, ina having breakfast ina kallonshi saidai har ya gama ya mik'e ya koma sama ban had'a idanu dashi ba, saida na tattara abubuwan da muka b'ata na wuce dasu kitchen na wanke sannan na koma sama na soma bud'e door ina neman bedroom din da yake, ina bud'e wani door na hangoshi kwance yayi relaxing akan kujera idanunsa a lumshe, a hankali na karasa tareda rik'e hannunsa nace,
"Please kayi hakuri...".
Aaryan ya bud'e idanunsa ya kalleni, wani kallo yayi min sannan ya maida idanunsa ya rufe, na dubeshi kamar zanyi kuka, nace,
"Please mana *BA NI DA LAIFI* ai ban san maganar auran tana nan ba shiyasa na kulaka...".
A hankali ya bud'e idanunsa yace,
"Baby wato so kike dole sai kin b'ata min rai, ai na san baki da laifi kuma na san kinyi min halarci, jiya na shigo da farin cikina amma kika b'ata min rai, kin san mey yasa na juya na fita saboda bana san ganinki cikin damuwa...".
Sai kuma ya maida idanunsa ya rufe, fadawa nayi jikinsa ina dukan kirjinsa, yasa dariya yana rikeni ina fizgewa sai kuma ya dafe kirjinsa, na zaro idanu tareda d'agashi, ya kwashe da dariya ya mik'e saidai ji nayi yayi sama dani yana jujjuyawa dani muna dariya sai kuma ya direni akan gado, ya hauro tareda pillow da cinyata, yace,
"Baby hira zamuyi amma idan karfe sha biyu da mintina arba'in tayi kiyi man magana...".
Na gyad'a kai, yace,
"Kin san mey? Lokacin da Yaa Ahmad ya sameni tambayata yayi idan har zuwa wannan lokaci ina sonki sannan ya bani wannan takardar...".
Ya zaro wata takarda ya mik'o min na amsa na bud'e ina dubawa naga ashe takardar da na rubutawa Yaa Ahmad ne, abun mamaki gani da nayi duk wadannan shekaru amma har yanzu kamar sabuwa take, na dubeshi ya cigaba da magana....
"Wannan takardar ya bani sannan yace ya sani ina matuk'ar sonki ya bincika ya samu bani da damuwa, idan har zuwa wannan lokaci ina sonki tou zai bani auranki, ni kuma na amsa da ehh, kin san mey na tambayeshi? Ce mashi nayi ina son sanin komai game dake saboda ina son sanin abubuwa da yawa a game dake, shekarun da suka wuce kinyi kuka saboda ni, bana san ya kasance yanzu kinyi kuka a kaina, tou ya sanar dani komai tun daga yarintarki...".
Da karfi nace,
"Ohhh no...".
Aaryan ya kwashe da dariya sannan yace,
"Ai ba zaulayarki zanyi ba... Yanzu Yaa Ahmad friend dina ne sosai...".
Nace, "Ina Aalima?".
Saida yayi murmushi sosai sannan yace,
"Tunda kikayi aure ban k'ara lafiya ba, na kwanta asibiti a lokutta daban-daban, har abroad Umma ta fitar dani, daga baya na auri Aalima yaronmu daya Yusuf amma muna kiranshi da Abba... Aalima ta tafi Umrah while Abba yana wurin Umma... Adila da Adla suna karatu abroad amma a gidan wani uncle dinmu suke zaune, medicine suke karantawa...".
Mom ce ta fado man a rai, nace,
"Mom fa?".
Yace, "Mom tana nan lafiya lau, kin san mey? Tare da ita aka kai lefe, baku hadu bane...".
Na jawo wayata na kunna mashi recording din call din nan, yana k'arewa yace,
"Ai wannan ba dake yake magana ba, akwai wanda yake magana dashi daban".
Nace, "Hakane sai bayan da mukayi aure yake fad'a man, amma ba kayi man gaisuwa ba".
Aaryan ya dubeni yace,
"Baby tare dani aka rufosu har ranar sadakar ukku saida na halarta... Aallah yayi masu rahama...".
Nace, "Aameen...".
Ya mik'e zaune tareda yi min magana kasa-kasa, na zaro idanu sai kuma yayi min magana a kunne, na rufe idanuna da sauri, ya fashe da dariya tareda jawoni jikinsa yace,
"Uhmmm fad'a min...".
Idanuna a rufe nace,
"No...".
"Ai sai kin fad'a...".
"No...".
Sai kuma na fizge na duro daga saman gadon, shima ya duro ya bini muna zagaye bedroom din yana fadin....
"Kamota, Kamota... Kamota, Kamota...".
Can yayi min kofar rago ya sureni ya jefa akan gado yabi ya danne yana min cakulkulo ina dariya, nace,
"Zan fad'a... Zan fad'a...".
Aaryan ya turo lips yace,
"Miye?".
Saida na rufe idanu sannan nayi mashi rad'a a kunne, ya kalleni ya ware idanu sai kuma yace,
"Ai zan iya... Worry not...".
Na tura kaina a kirjinsa, ya kwashe da dariya sai kuma yace,
"Baby kin san mey?".
A tare muka ce,
"Ina sonki...".
Sai kuma muka kwashe da dariya, kallona yayi yace,
"Mariam na gode sosai da a wancen lokacin kika kasance tare dani other wise bana tunanin zan rayu...".
Da sauri na girgiza kai, yace,
"Shikenan na daina...".
Aaryan ya kalli wall watch ya dafe goshi sai kuma ya sureni yayi bathroom dani it was funny and hilarious, ya daura guntun towel ya nadoni ya fito yana dariya ya ajiyeni akan gado, nace,
"Heartbeat...".
Aaryan yana tsaye a kaina ya karyo wuya yace,
"Miye baby na?".
Na turo baki, ya kama kunnuwansa sannan yace,
"Sorry....".
Nace, "Tou juya...".
Ya juya na mik'e tareda hugging dinsa ta baya na bashi peck a gefen fuska sai kuma na gudu bedroom dina....
Aaryan ya shafa wurin yana murmushi....
Saida nayi applying cream sannan na saka wasu riga da skirt na atamfa, ina zaune gaban mirror ya shigo da wani akwati sak irin na lefena, ya koma, tou nidai ina zaune ina applying makeup ya shigo da akwati guda shidda kuma daga gani set daya ne da akwatu nan lefena, ya lallab'o bayana yayi hugging dina ta baya tareda turo kanshi gefen fuskata yana kallona ta mirror yace,
"Kin san mey? Kinyi kyau...".
Na kalli akwatu nan da ya jera a kusa da na lefena, yace,
"Suma naki ne, guda sha biyu nayi maki sai na ajiye maki wadannan sai idan kin zo in baki da kaina, are you happy?".
Nace, "No...".
Aaryan ya ware idanu, nace,
"I love you so much...".
Yace, "Saboda na baki akwatuna...".
Nace, "A'a saboda kana sona...".
Na mik'e tareda juyowa na zagaye hannuwana a wuyanshi nace,
"Miye?".
Aaryan ya turo lips, nace,
"Inyi maka applying lipstick...".
Yace, "Ohh No...".
Wani abu muka tuno muka kwashe da dariya, nace,
"Kaine...".
Yace, "A'a kece...".
Sai kuma yayi sama dani, muna tare, shine ya jamu sallar zuhr yayi addu'o'i sosai, fita yayi ya dawo da plate, cup, fork da leather, ya zauna tareda juye delicious chicken a cikin plate, nace,
"Tou dai duk wanda yaci shi daya, shi daya zai mutu...".
Yace, "Zo ki ci...".
Nace, "Ehhh zanci amma idan da zuciya daya ka bani...".
Yace, "Indeed....".
Nace, "Kuma kadda kayi min dariya idan nayi katuwar loma...".
A tare muka fashe da dariya, ina yagar kaza ina kallonshi, yace,
"Ki ci abunki...".
Nace, "Maza basu karamar loma...".
Yace, "Ina ruwanki?".
Nace, "Daga magana...".
Yace, "Ehhh kuma idan na kamaki uhmmm".
Saida gabana ya fad'i, saida naci nayi nak na kora da yoghurt sannan nace,
"Garden...".
Na kalleshi naga ya zuba man idanu yana kallona, nace,
"Miye ka zagaya dani inga gidan namu...".
Aaryan ya kunshe dariya yace,
"Alright then, you wish is command my beautiful babie...".
Nace, "Mariam...".
Yace, "Baby...".
Nace, "Mariam...".
Yace, "Baby...".
Nace, "Mariam...".
Yace, "Ni dai babie nace...".
Sai kuma ya mik'e ya sureni, it was indeed funny and hilarious, tou I thought zai fice da ni ne garden amma sai na tsinci kaina a tsakiyar gado, nace,
"Ohhh No...".
Yace, "Ohhh Yes...".
A hankali na bud'e idanuna nayi idanu hudu dashi yana jefata da murmushi, da sauri na maida idanuna na rufe na mik'e zaune ina kukan k'arya, nace,
"Ni ka fita...".
Ji nayi yace,
"In fita in tafi ina?".
Nace, "Koma ina ne, nidai ka fita, ohhh kaje parlour kayi kallo...".
Yace, "Baki son ganina ne?".
Ina dire-dire nace,
"A'a kawai ni ka fita...".
Yace, "Ai babu inda zanje tunda ba ni bane baki son gani, kilbabba ai sadda kikayi...".
Da sauri na toshe kunnuwana, tou ni banji abun da yace ba, ji nayi ya sureni yayi gaba yana taking steps, naji alamar ya bud'e door sai kuma yayi tafiya ya tsaya cak, ina bud'e idanuna ya sakeni cikin bathtub saidai jina nayi cikin ruwa, I feel in fasa ihu, wata sabuwa saida muka fito, a razane na dubeshi nace,
"No...".
Yace, "Please mana...".
Nace, "Wayyo Ummy na...".
Yace, "Wayyo babyna...".
Tou ya zanyi an riga anfi karfina....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest Aaryan fans, Aallah ya albarkaci rayuwarku, wish you all the best....*
*Hope kunyi sallah lafiya baby fans, wish you all the best....*
Page. 27
Second to the last page
A tare muka had'a lunch yana tayani da wasu abubuwan, lallab'owa yayi yai hugging dina ta baya tareda zagaye hannunsa a kuguna, ya turo fuskarshi gefen wuyana yana sauke lumfashi yace,
"I love you so much...".
Na kunshe dariya na tureshi tareda juyawa na pointing dinshi da lidde nace,
"Ina aiki kana hanani, very stubborn...".
Aaryan ya rik'e kunnuwansa yace,
"Sorry Ma...".
A tare muka fashe da dariya....
Bayan sallar isha'i muna zaune muna kallon wani turkish series, nayi pillow da cinyarsa ina shan lollipop, magana yayi min a kunne na ware idanu, yace,
"Yeah ko kuma in kwashe sauran in bada...".
Na turo baki nace,
"Ni bazan yarda ba...".
Shima ya turo baki yace,
"Ni kuma na yarda...".
Nace, "Zamuyi fad'a...".
Yace, "Zamu b'ata...".
Dariya ya bani, can yace,
"Baby ina gashinmu...".
Na mik'e tareda zare kallabin dake saman kaina na warware gammon da nayi gashina ya warware yayi baya, nace,
"Kaga har yanzu yana nan...".
Aaryan yasa hannu yana bin gashin da yatsu yace,
"Aikuwa ya kyauta...".
Kitso guda daya yayi min sannan ya turo min shi a gaba, yace,
"I love it in this way".
Ina shafa kitson nace,
"Amma yayi kyau kuma zaiyi dadin gammo...".
Yace, "No more gammo haka nike son ganinshi...".
Nace, "Ina ka iya kitso? Duk mazan gidanmu babu wanda ya iya kitso saidai suyita jama mutum gashi...".
Yace, "Uhmm a kan twins na iya...".
Nace, "Sun ji dadi...".
Yace, "Kema kinji dadinki brothers dinki suna sonki musamman...".
Nace, "Yaa Ayan...".
Aaryan ya ware idanu yace,
"Nidai dukkaninsu nike nufi...".
Na maida kaina akan cinyarsa nace,
"Kaga ka saka har an wuce wasu wuraren ban gani ba...".
Yace, "Talla suka tafi...".
Wurin karfe goma ya tashi ya kashe kallon ya mik'o min hannu yace,
"Zo muje kiji wani abu...".
Nace, "Saidai ka goyani...".
Aaryan ya ware idanu yace,
"Ai kina da nauyi...".
Nace, "Ai kaima kana da nauyi...".
Aaryan ya ware idanu tareda rufe baki da hannunsa yana kallona sai kuma naji kunya ta kamani nayi kasa da kaina, ya duk'e tareda juya bayansa yace,
"Hau kilbabba...".
Na kwashe da dariya sannan na d'ane bayansa na rikeshi gam, nace,
"Kuma Aallah kadda ka kayar dani or else...".
Zaiyi magana na fasa ihu, yace,
"Na fasa kadda ki fasa min dodon kunne...".
Nace, "Dadai yafi...".
Muka saka dariya, yana taking steps muna dariya ya kashe wuta muka wuce sama, tou saida safe....
Washe gari bayan mun gama breakfast, ya kama hannuna yace,
"Baby zo muje mu sauya kaya muyi tseran keke (bicycle)".
Nace, "Kamar kuwa ka san ina son riding bicycle, lokacin ina yarinya brothers dina suka koya min and...".
Yace, "Ai nasan komai, zamu rink'a motsa jiki, nafi sonki a yadda kike slim bana son kiyi kib'a...".
Dariya ya bani, nace,
"Aiko a da nayi kib'a har tayi min muni... Ahhh don ma yanzu na tashi daga bebilo na koma baby...".
Yace, "Kin san mey? Ina sonki...".
Nace, "Kana da barkwanci...".
Ya ware idanu yace, "Kina da daukar abu da wasa...".
Mukayi dariya yayinda muka tuna farkon haduwarmu, a lokacin da na fara ganinshi, yace,
"Kin san mey? A lokacin da na fara ganinki fuskar Aalima na rink'a gani a saman fuskarki wannan shine ya maido da farin cikina wanda na rasa tun bayan b'acewarta, yanayin dressing dinku, magana da tafiyarku duk iri daya ne, har yanayin jikinku da tsayi daya ne, duk lokacin da na ganki sai fuskarki ta rink'a komawa fuskarta tana dawowa fuskarki... I love Aalima so much and I love you so much...".
Saida gabana ya yanke ya fad'i, na kira sunan Aallah da sauri, muka shiga bedroom ya sureni ya wuce bathroom muna fitowa ya fiddo min wasu kayan sport, trouser then hula kamar ta sanyi, colour vest da rigar sport mai had'e da hula da zip a gabanta, shima ya saka kayan sport, trouser, shirt mai circle neck, da riga mai hula da zip irin wadda ya mik'o min, ya rufe kanshi da hula, nima na shirya tsaf cikin kayan da ya bani tareda kasa da zip, vest dake kasanta tayi appearing, na rufe kaina da hula tareda jawo jelar kitso da yayi min, ya kwanta a kirjina, nayi kyau sosai, looking breathtaking, muka saka takalma muka fice, bicycle (keke) ne guda biyu sabbi dal, na hau ya hau ya kashe mamu selfie, kuma yayi kyau, kwalta dake gefen garden muka ja kekunan, tsere mukayi muna dariya, idan ya wuceni yayi min gwalo, idan na wuceshi inyi mashi gwalo, naji dadi sosai, saida muka gaji sannan muka ajiye kekunan muka wuce ciki mukayi wanka saida mey? Hmmm bari dai inyi shiru, bestiee mai awara ta hanani fad'i, wai dariya kuke bayan idanuna, hhhh lols....
Washe gari tare muka had'a breakfast muka jera akan dinning table muka ci sannan muka tattara abubuwan da muka b'ata muka wuce dasu kitchen muka wankesu, ji nayi ya sureni ya kwantar dani akan doguwar kujera ya turo kanshi akan kirjina na tureshi, yace,
"Baby...".
Nace, "Bacci... Kallo...".
Aaryan ya kalleni yana shafa sumar kanshi sai kuma ya juya ya haye sama jim kadan ya sauko yana sanye da guntun trouser da shirt yayi unbottom wasu daga cikin bottom dinta na sama kuma ba ya da vest, wasu daga cikin peck seven dinsa sukayi appearing, ya rufe idanunsa da black space, the more yake tafowa the more yake appearing more cute, hot and sexy, ya karaso ya zauna kusa dani, na kalleshi the more nike kallonshi the more yake appearing more cute, hot and sexy, kallonshi nike bana koda blinking, yace,
"Miye?".
Nace, "Kadda ka cire glass din...".
Can ya cireshi, nace,
"Please nidai ka maidashi yayi maka kyau...".
Yace, "Saidai idan kin yarda...".
Yayi min rad'a a kunne, na ware idanu nace,
"No....".
Yace, "Nima bazan maida ba...".
Nace, "Please....".
Yace, "A'a....".
Na dubeshi kamar zanyi kuka nace,
"Tou na yarda...".
Smile ya saki ya kanne min ido guda sannan ya maida glass din yayi pillow da cinyata yana kallona ina kallonshi, the more nike kallonshi the more yake appearing more cute, hot and sexy, can ya mik'e ya sureni yayi sama yana taking steps ina kallonshi, tou nayi shiru dai, ai bance komai ba....
Satinmu biyu muna jin dadinmu ya kaini gidansu muka wuni kuma ya kaini gidan Mom, gaskiya naji dadin wannan ziyara sosai, sun nuna min kauna marar adadi, Umma har godiya tayi min akan kalubale da na shanye akan Aaryan, tace,
"Haka zaizo yana kuka yana fad'a min bai jin dadin abun da ake maki saidai bazai iya barin zuwa wurinki ba, wani lokacin ji yake kamar idan bai ganki ba zuciyarshi zata buga, yasha kwana akan cinyata yana kuka ina rarrashinsa, ban da kika cigaba da kulashi da watakila mun rasashi....".
A lokacin ji nayi kamar inyi hawaye, rayuwa kenan yanzu komai ya wuce kamar ba'ayi ba, naso ince mun tafi da Abba saidai na lura Umma tana jin dadin zamanshi shiyasa nayi shiru, daga baya ne mukaje gidanmu har ciki ya shiga nayi mamaki sosai akan yadda naga ya saki jikinsa, ya jima don har abinci yaci sannan ya wuce, da marece Abba yana dawowa yace in shirya in koma gidan mijina, nace shine zaizo ya daukeni, sai bayan sallar isha'i sannan Aaryan ya dawo ya daukeni muka wuce kuma ohhh ashe na daina fad'i saidai inyi sub'utar baki, Mom ta bani expensive car hakanan Umma itama ta bani expensive car, shima ya siya min mota kirar Benz da system kirar kamfanin apple da kuma waya latest version din iPhone tareda iPad, time to time yana min depositing din kudi, tare muke bitar hardarmu, idan tawa ta samu damuwa ya tusani gaba in gyara hakanan idan tashi ta samu damuwa in tusashi gaba ya gyara....
Ranar asabar yana zaune a garden yana karanta news paper yayinda nike kwance nayi pillow da cinyarsa ina kallo a iPad dita, a hankali na zare earpies dake kunnena nace,
"Heartbeat ya labarin Ummu-Abba (Aalima) har yanzu shiru?".
Aaryan ya dubeni yace,
"Wai Aalima?".
Na gyad'a kai, yace,
"Aalima ta wuce london medical checkup daga nan zata wuce Dubai tayi shopping tana sone ta bamu lokaci muyi enjoying amarcimu...".
Nace, "Uhmm... Uhmm...".
Yace, "Kilbabba kamar ba d'azu ta gama min...".
Na ware idanu, yace,
"Tou na fasa bazan fad'i ba, kiyi farin ciki... Aalima jiya nayi waya da ita tana tare dasu Adla...".
Nace, "Aallah sarki twins dinmu Adila da Adla, our greatest doctors to be, ina waya dasu amma ita har yanzu bani da numbarta, ka bani...".
Yace, "Ko jiya saida nace in baki tace a'a tafi son sai ta dawo sannan ku gaisa yadda ya kamata, mu zauna muyi having hilarious moment...".
Saida gabana ya fad'i, wasu lokuttan har mantawa nike da ina da kishiya aw abokiyar zama, koda yake our greatest soffi tace wata ce kishiya wata kuma abokiyar zama ce, wasu ne suka b'atawa wasu suna, sai kiji ana cewa kishiya this and that, maganganu dai daban-daban, duk da na kirkin suna da yawa amma na banzan sunfi kaurin suna, mik'ewa nayi tareda ajiye iPad dina akan table na dauki igiya ina tsallen igiya (after) ina murmushi ko lokacin da nike yarinya ina son tsallen igiya, tun brothers dina suna kad'a min ina yi har na koma ina kad'a abuna da kaina, nifa har kad'a taya nayi kuma nayi wasan dokin icce da jan mota amma cikin gidanmu, ina son buga game a lokacin kuma brothers dina ne suka siya min, tou ina wasa irin na mata amma nafi son na maza, k'awayena sukan ce min idan na sake zan zama ta maza, na kance naji tou miye ai brothers dina duka maza ne, brothers dina suna yawan goyani a baya, wani lokacin har maka wuya suke min, suyi min doki, dukkaninsu sun iya er carafke saboda ina sonta, wasu lokuttan da gangan suke faduwa suna bari ina cinyesu, ina son wasan jirgin leather musamman wanda ake sakawa asaberi, wow, saidai su tadashi kololuwa su bani idan ya samu damuwa tou babu b'ata lokaci zasu sauya min wani....
Ina tsallen igiya ina murmushi a dalilin tunawa da nike da happy moment da na samu tareda brothers dina a lokacin da ina yarinya, the more nike tunawa da wadannan lokuttan the more nike smile more and more.....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak to you all Muslim all over the world, Aallah ya albarkaci rayuwarku, wish you all the best....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 28
Last page
Aaryan ne ya ajiye news paper dake hannunsa yayi taking steps zuwa inda nike tareda rik'e hannuna kallonshi nayi ya kalleni idanu cikin idanu sai kuma ya amshi igiya dake hannuna, muna kallon juna idanu cikin idanu yayinda yake kad'a mamu igiya muna tsalle a tare a lokaci guda, can ya saki igiyar ya sureni yayi ciki, tou an dai hanani fad'i....
Ina enjoying zama tare dashi, yanzu kam matsewata nike in saka guntun skirt, in saka guntun wando, in saka guntuwar gown, tou mey yafi raina ai gidan mijina ne, a wasu lokuttan muna fita tare....
Aalima ta dade abroad sannan ta dawo, har part dinta naje nayi mata sannu da zuwa kuma ta tarbeni da fara'arta....
Aaryan ya had'a mu yayi mamu nasiha tareda raba kwana, tou kwana biyu-biyu zai rinkayi, kowace zatayi girkinta ne amma duk wadda ranar girkinta ya kama ranar jumu'ah tou tare zatayi mu hadu a sashensa muci a tare sannan zamu rink'a fita ziyara, lokacin da zai wuce wurinta da daddare kuka na saka mashi saida ya lallab'ani nayi bacci sannan ya tafi, ina farkawa tsakar dare naji ban ji ni a jikinsa ba, na laluba inda yake kwanciya naji wayam yayinda komai ya dawo min a brain, fashewa nayi da kuka, saida nayi nafila da karatun Alk'ur'ani mai girma sannan na samu na dawo daidai, babu b'ata lokaci bacci mai dadi yayi awon gaba dani....
Da asuba ya lek'o ni hakanan da zai wuce wurin aiki kamar kadda ya tafi har so yayi ya makara, kun san wani abun dariya har uhmm naso inyi mashi ya gudu, aw ashe na daina fad'i koda yake ai ban ambaci suna ba, kuma babu wacce zata iya guessing....
Ina zaune a parlour ina kallo, Aalima ce ta kawo min kaya, ashe komai biyu ta sawo ni da ita hakanan har Ummy tayi ma tsaraba, sai duk naji kunya ta kamani ni da na rinkayin shopping dina ni daya, zama tayi muka sha hira abunmu mukayi having hilarious moment yadda ya kamata daga baya ta koma sashenta, cikin wadannan kwanaki nayi missing Aaryan sosai aiko har henna nayi, idan ya dawo daga aiki zai shigo girkina ya fara kenan wannan itace ka'idar don haka delicious food na girka kuma favourite dinshi kuma bazan fad'a maku girkin ba ballantana wata tayi min snatching, hhhh lols, na jera komai akan dinning table, na cire apro na wanke abubuwan da na b'ata na jerasu sannan na dauraye hannuna na fito na wuce sama na jima cikin kumfa mai kamshi ina wasa dashi sannan na dauraye jikina na daura towel nayi brush before na fito na shirya naci gayu cikin riga da skirt en kanti tareda jawo jelar kitso guda da yayi min ta kwanta akan kirjina kamar dai yadda yake son ganinshi, saida na feshe jikina da perfumes different design sannan na suri veil na zura takalma flat na sauko kasa tareda hakincewa akan doguwar kujera very stylish....
Aaryan ne ya shigo yana sanye da suit yasha zanzaro ga wani cute necktie yana rataye da briefcase a shoulder, he look cute, na saki murmushi tareda mik'ewa na ruga da gudu na d'ane jikinsa yayi sama dani yana jujjuyawa dani muna dariya, ya wuce staircase yana dauke dani, nace,
"Abinci...".
Aaryan ya ware idanu sannan yace,
"Wani abinci kuma? Kilbibi kawai... Ni baby rigimarki ba zata bari inci abinci hankali kwance ba, sai na sakaki bacci sannan kuma idan kin manta tou sai nayi wanka sannan nike cin abinci ko?".
Ya wuce sama yana dauke dani, saida ya kwana biyu sannan ya komawa Aalima, zaman lafiya muke ba ya nuna banbanci a tsakaninmu, yana kwatanta yi mamu adalci saidai dole a wani wurin a samu damuwa, Aalima bata nuna damuwa akan wasu abubuwan, ko ta ya abu zai b'ata mata rai bata nuna damuwa, kau da kai take tana hakuri, har mamakinta nike, tana hakuri kuma bata nuna damuwa koda kuwa ba'ayi mata adalci ba, itace jigon wannan zaman lafiya, koda abu ya siyo mamu sai idan ta bani na zab'a sannan ta dauka, daga baya nace mashi ya rink'a sawo iri daya saidai abun da zaiyi ma fari kyau amma ba zaiyi ma chocolate colour ba, ina kwatanta bata girmanta saidai wasu lokuttan ina kwafsawa ita kuma tana hakuri, wasu lokuttan idan ya wuce wurin aiki ina shiga sashenta musha hira, wani lokacin tana rigani zuwa ko kuma mu hadu a garden, idan kuma yana nan sometimes a sashensa muke haduwa, idan Ummy tazo sai ta fara shiga sashen Aalima sannan ta biyo sashena kuma duk abun da zata kawo min tare take bamu kuma iri daya, little Abba kam ya zama d'an gidan Umma tou yafi zama a can, idan yazo kwanaki yake mamu yana komawa, yana kiran Aalima da Ammi while ni kuma yake kirana da Mami, while yake kiran Aaryan da Abbu, ni kuma ina kiran Aalima da Ammin-Abba, while nike kiran Aaryan da yadda little Abba yake kiranshi sometimes ince heartbeat....
Nadiya tana kawo min ziyara hakanan Affan shima yana zuwa amma brothers dina babu wanda ya tab'a zuwa hakanan Abbanmu, ko lokacin da nike auran late Mahmud tou Yaa Ahmad ne kawai yaje shima sau daya lokacin da yaje ya tafo dani....
Bayan shekara daya da rabi na haihu na haifi baby girl da dare while ita kuma Aalima ta haihu washe gari da safe itama baby girl ta haifa, murna a wurin Aaryan ba'a magana, Aallah kenan yayi maka kyauta ya k'ara, dukkaninsu dashi suke kama sak saidai skin colour dinmu suka biyo, tawa fara ce sol kamar diyar larabawa while ta Aalima take chocolate colour....
Ranar suna yara suka ci sunan Umma da Mom amma muna kiransu Iman da ilham, kamar twins suke....
BAYAN SHEKARU HUDU.
Arziki ya linku, zaman lafiya yana nan, har yanzu ina a baby na ai bana yarda in koma bebilo ba, nayi fresh dani, Aalima tayi maintaining weight dinta kamar yadda nima nayi maintaining weight dina, Aaryan ya k'ara komawa d'an saurayi abunsa, both Yaa Ayan da Yaa Mustapha sunyi aure matansu masu kirki dasu, Affan ya girma, Nadiya ta zama Hajiya, Jalila ta kama kasa tana yawan kawo min ziyara, har yanzu amintarmu tana nan babu abun da ya sauya, bindawa har masters tayi, yanzu haka ita da mijinta basu kasar, both Adila da Adla sunyi aure, kowace cikinsu likita ce kwararra, tou yanzu haka haihuwata ukku, ilham sai en ukku dukkaninsu maza ne, daya Muhammad yake, daya kuma Ahmad while daya yaci sunan mahaifin Aalima, tou muna kiransu da Baffa, Abbu da Malam, tou daga su sai na haifi Habiba wadda taci sunan Ummy yanzu haka shayar da ita nike, muna kiranta little Ummy, Ita kuma Aalima haihuwarta hudu Yusuf (little Abba), Iman, mama (wadda taci sunan mahaifiyar Aalima) then Safeena itace wadda take shayarwa, yaranmu masu kyau, mun had'e kansu don haka kansu a had'e yake, Yusuf (little Abba) yana zaune ne a wurin Umma while ilham da Iman da suke kamar twins suke zaune a sashena, while triple suke a sashen Aalima, baki daya yarana haskena suke biyowa don triple har so sukayi su fini haske mai kyau, while yaran Aalima suke chocolate colour, Mama ce kawai ta biyo skin din mahaifinta wato ita fara ce sol, dukkanin yaran dashi suke kama, little Ummy da Mama ne kawai suke kama damu, Mama fuskar Aalima ta dauko sak saidai fara ce sol kamar mahaifinta while little Ummy take kama dani sak, muna rayuwa cikin farin ciki, mun dagewa yaranmu akan both ilimin addini da na boko, yaranmu sun taso cikin kyakykyawar tarbiyya, idan mutum ya shigo gidan nan babu yadda za'ayi ya gane wannan d'an waccen ne, wannan kuma d'an waccen ne, wannan kam saidai wadanda suka sanmu, Aaryan yana da yara tara, maza hudu, mata biyar, tou ni ina da maza ukku sai kuma mata biyu while Aalima tana da namiji daya da mata ukku....
Alhamdulillah....
The End....
A nan na kawo karshen wannan novel nawa mai suna *BA NI DA LAIFI* kirkirarren labari ne idan yayi daidai da rayuwarku tou akasi ne, a matsayin barka da sallah dinku ne kuma complete document, don haka nima ina jiran barka da sallah na kowace ta kawo nata ku harhado kuma kadda inji shiru, duk wacce take ganin yayi mata kadan da barka da sallah tou ta biya kudinshi naira dari ukku ta account number dina, Ina maraba da gyaranku saidai ku sani a complete ya fito don haka saidai in dauki gyaranku in rik'e amma babu yadda zan gyarashi a novel din tunda complete ya fito....
Ina jiran dogon sharhi....
Kuyi amfani da darussan dake ciki ku watsar da kurakuran da kuka gani, duk wanda wannan novel ya b'atawa rai yayi hakuri, ni nayi ne don nishadantar daku, tou banyi don in b'atawa wani ko wata rai ba....
One luv.....
Happy eid Mubarak to you all....
Our Novels
RUMANA (old edition 2017)
HIJABINKI MUTUNCINKI
BA NI DA LAIFI
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜