Bayan sun gama ta wuce ta
fesa wanka, ta dau gayu na
musamman domin taryar rabin
ran nata.
K'arfe biyu da kwata dai dai
suka iso gidan, da sallamarshi
ya shigo palon babu kowa sai
Mahmoud yaron Hafsat yana
kallon cartoon a MBC3. Da
gudu ya taso ya rungume
Nawap yana cewa
"ga Uncle ga Uncle."
D'aga shi sama Nawap yayi,
yana fadin "my boy, ka zama
babban mutum"
Dariya ya kyalkyale da shi,
"sosai ma, har na kai nursery 2
fa uncle"
"Smart boy" Nawap ya fada
yana dariya, sannan ya sauke
shi, ganin Deedo na saukowa
fuskarta kunshe da wani
murmushi na ban mamaki.
Karasawa yayi inda take tsaye
ta nannade hannayenta, ya
kalleta yace "yan mata na,
yakike?"
"Ina wuni" ta fada, yayin da ya
ansa a daburce, "na same ku
lafia?"
"Lafia lau, ya hanya?"
"Alhamdulillah, ina ta sauri na
zo nayi tozali da abin k'aunata
"
Rufe fuskarta tayi, alamar
kunya, tayi gaba tana cewa
"muje ka ci abinci, dan na san
yanzu haka ko breakfast baka
yi ba"
Bayanta ya biyo yana cewa
"banda abinki waye zai ba
gauro abinci"
Dariya tayi lokacin da suka iso
kan dining table din, sai da ta
rage muryanta, sannan tace
"just two weeks ya rage, ka
daina zama da yunwa in sha
Allah"
Ta juya ta cigaba da serving
dinshi, inda shi kuma yana
murmushi yace "I trust my
baby doll"
Ta kalle shi ta murmusa,
sannan ta mika mashi plate din
abincin, ta wuce kitchen domin
kwaso drinks.
A haka Hafsat ta tarar dasu
yana cin abincin, yayin da
Deedo ke zaune gefenshi suna
tadinsu cikin jin dadi.
Suka gaisa dashi, yana
tambayar
"ina mama small" tace
"dak'yar na lallabata, tana
sama tana bacci."
Sannan ta wuce cikin palon
inda Mahmoud yake a zaune.
Tunda Nawap yazo kullun
suna manne da Deedo, shi ke
kaita skool, sannan ya jirata
office din Dr. Kashim, har sai
ta fito exams, sannan ya dauko
ta su dawo gida kullun, har
zuwa yau da take gamawa.
A hanya take ce mashi
"Ummi ta fada maka da su Yaa
Hafsat zamu tafi?"
"Me zasuyi mana ne in mun
tafi dasu? Me sa Ummi take
mun haka, bata son ina
ke6ewa da matata" ya dan ja
tsaki, ya kara gudun da yake,
yace "ke kuma me kika ce
mata?"
Dariyar da take ta dan
tsagaita, tace "ni har na isa
ince wani abu ne bayan Ummi
ta gama yanke hukunci, lallai
ma"
"Duk ke kika ja mana ai da
kika fada mata"
"Zan bi wani ne ba tare da
sanin Ummi na ba aka fada
maka" tana yi tana kallon
yadda yayi kicin kicin shi dole
ga wanda aka shiga hakkinsa.
"Zaki maimaita ranar da kika
zo hannuna yarinya, dan sai
kinyi wata biyu baki ga Ummin
taki ba" ya fada a dai dai
lokacin da suka iso kofar gida,
ya fara danna horn kamar
wanda ya d'auko majinyaci.
Ita dai dariya kawai take,
yana yin parking ta fito zata
shige, yace "wa kika bar ma
wannan tilin books din naki?"
"Wa fa in ba mijin yar auta
ba" ta shige tana ta dariyar
mugunta.
Yayi kwafa, ya kwashi k'atin-
k'atin din text books din har
guda ukku, shi kanshi sai da
hannuwansa suka k'age, ya
zube mata su a palo, yana
banbami "koma ya ake tana
daukan books din nan, gata dai
abu kamar a karya ta"
Mahmoud yace "uncle kai da
wa kake fada?"
Yace "wannan yar siririyar
auntyn taka mana, ta sanya ni
daukar books masu nauyi"
Yayi dariya, yace "ai idan ta
dauka zasu fadar da ita ne shi
yasa, kai kuma kana da k'arfi
kaga"
Shafa kanshi yayi, ya wuce
kitchen ya dauka robar ruwa,
sannan ya wuce side dinsa.
[24/04 21:45] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA…
108
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
K'arfe goma dai dai na safe,
kowa ya gama shiryawa tsab,
suna zaune a palo suna jiran
fitowar oga Nawap wanda yake
ta faman cika yana batsewa
shi dole an takura masu, za'a
hana su sakewa shi da Deedo.
Karasowa yayi, ya dau wanka
cikin farar gezna, hularshi da
takalminshi har ma da agogo
duk bak'ak'e, yana ta kanshin
Tom Ford Velvet Orchid,
Mahmoud kawai yai ma dariya,
ya kama hannunsa suka fita.
Deedo da Hafsat da suke
kunshe dariya suka kyalkyale,
sannan Deedo ta sa6i mama
small suka fito, yayin da Saude
take kwaso kayan da zasu tafi
dasu tana lodawa a boot.
A gaba suka zauna ita dashi,
sai mama small a hannunta,
yayin da Mahmoud da Hafsat
suke a baya. Haka suka fara
tafiyar kamar kurame, in banda
Mahmoud da mamah da suke
yan surutansu na yara.
* ********
K'arfe d'aya na rana Nawap
yayi parking motarsa a kofar
wani kwarmad'ad'd'an gida
wanda yake da tabbacin tabbas
nan ne gidan Goggo, domin ko
ba zai taba manta gidan da ya
fara ganin mamallakiyar
zuciyarsa ba.
Kallon Deedo yayi, yace
"kamar munyi batan kai
ko?"
"Anya kuwa?" Bari dai in shiga
mu ga"
Ta 6alla murfin motar ta fito,
yayin da shi ma ya bude nashi
kofar ya bita a baya.
Cikin gidan wanda ga
dukkan alamu rabon da ya ga
shara akalla anyi shekara
hud'u, domin ko yadda kasan
kango, haka bola ta samu wuri
ta basar, suka kutsa kansu,
Nawap ya kalle ta
"Bana tunanin akwai dan
Adam din da yake rayuwa a irin
wannan wurin, fito mu shiga
makwabta mu tambaya ko sun
koma wani wuri ne"
Basu ankara ba suka tsinkayi
murya daga cikin dan akurkin
dakin da Deedo take da, wanda
shi kadai yayi saura a cikin
dakunan da suke gidan, domin
kuwa sauran duk sun rufta,
kana iya hango komai daga
inda suke a tsaye.
"Wane dan banzan ne nan?
Iyii? Ko bakwa ji na ne
la'anannu"
Ta fara laluben sandarta,
dakyar ta dafa bango ta mik'e
tsaye, tana bin bangon ba tare
da sanin ta ba ta taka wani
kwano, aiko ba tare da 6ata
lokaci ba ta fadi kasa, ji kake
wani rigijib!!!
Nawap da Deedo da suke
tsaye bakin dakin suka yi
saurin kutsa kai ciki, amma
wani mahaluk'in k'arni tare da
wani gagarumin wari ne suka
yi ma hancinsu sallama nan da
nan suna rige-rige suka yo
waje da gudun bala'i, Nawap
ya rik'e cikinshi wanda yake
murd'a mishi, nan take ya fara
shek'a amai ba k'akk'autawa…
"Allah dai ya tsine muku, wai
su uban waye a nan?" Ta
cigaba da laluben inda ta
wurga sandar, ko Allah zai
taimaketa ta fita ta warci daya
a cikin irin yan iskan yaran da
suke shigowa suna tsokanarta
ko wacce rana.
(Nayi iya kokarina na karasa
labarin nan yau, amma hakan
bai samu ba, I promise yu
zuwa gobe in sha Allah.
Thanks y'all for the love. I love
yu too)
BA’A SHAN
ZUMA…
109-111
BA'A SHAN ZUMA… 109
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Hawaye masu azabar zafi suka
gangaro a fuskar Deedo ganin
halin da kanwar mahaifinta ke
ciki. Hannu tasa ta share, ta
juya tana kallon Nawap wanda
yake goge bakinsa da
handkerchief, karasawa tayi,
gabanshi
"Sannu Yaa Nawap" ta fada
yayin da take waige waige ko
me take nema,
"Kaje waje, bari nayi magana
da ita"
Goggo wadda ta rarrafo ta turo
kanta kofar dakin, tace
"Wai muryar su waye nake
ji nan? Iyii? Ko baza kuyi
magana bane tambadaddu
ya'yan fata, Allah dai ya tsi… "
Nawap ya katseta ta hanyar
cewa,
"Goggo Nawap ne, wannan
kuma Deedo ce, dago ki ganta"
"Deedo? Nawabu? Ku ne? Ko
dai tsinannun ya'yan unguwa
ne suke tsokanata"
Ta fada yayin da ta dago kanta,
ko Allah zai sa ta hango
kyallin wani abu wanda zai
tabbatar mata da cewar su din
ne.
A tare suka toshe bakinsu da
hannu, suna fadin
"innalillahi wa inna ilaihir
raji'un!
Goggo!"
Ganin kwantsa mai kama
da mugunya, har da wasu yan
tsutsotsi suna fita daga idanun
Goggo, idon ya ca6e, ya
cakwale, Allah kadai ya san iya
shekarun da ta dauka tana tare
da wannan azabar.
Lalube ta cigaba da yi, inda
ta jawo 'yar k'afarta guda daya
da tayi mata saura, ta fito da
ita wajen dakin dak'yar,
"'Ya'yan nan ku fada mun
gaskia, Deedo ce wannan a
gaba na da gaske?"
Tasa hannu tana lalube ko
zata samu damar ta6a Deedon.
"Nice Goggo, wai me yake
faruwa da ke ne? Bakya gani
ne ko ya akayi?"
Kuka mai sauti Goggo ta
saki, sai dai kash, kukan babu
ko alamar hawaye, amma duk
wanda ya ganta zai tabbatar
kukan nadama Goggo take
rerawa.
"alhakinku ne yake bibiyata
Deedo, dake da malam Ilu,
wanda bakin cikina yayi
sanadiyyar barin shi duniya, na
shiga ukku ni Batula,"
Abinda Goggo take nanatawa
kenan, yayin da ta dauki
hamnuwanta ta dora bisa kai,
tana kurma ihu kamar
mahaukaciya.
Ihun da Goggo ta kurma,
shi ya jawo hankalin su Hafsat,
da Mal. Labarin makwabcin
Goggo wanda shi kadai ne
mutumen da ya rage wanda ke
taimaka mata a unguwar,
kasancewar kowa ya san bakin
hali da bala'i irin na Goggo,
shi yasa babu mai kallon inda
take, anan inda take a zaune
zata yi kashin ta da fitsari,
haka kuma idan malam
Labaran ya miko mata dan
abinci, anan din dai zata cinye
shi, ba tare da wanke hannu ko
kashin da yake jikinta ba.
Da azama suka yo cikin gidan,
ganin yanayin yadda wurin
yake yasa Hafsat dakatawa,
hannunta rik'e da na Mahmoud,
yayin da Mal. Labaran ya
karasa yana fadin
"Samari daga ina? Lafiya
kuwa?"
"Lafiya lau mal., ina wuni"
Cewar Deedo, inda shi kuma ya
cigaba da kare mata kallo
kamar ya santa.
"Deedo ce" ta fada tana kallon
goggo,
Nan ya fara salati yana
sallallami
"Deedo? Ina kika shiga?
Wanene wannan din shi
kuma?"
Anan suka gaisa da Nawap, yai
mashi bayanin kanshi, mal. Ya
kara da tambayar "kai kuma ina
ka santa?"
Nawap wanda baiyi kasa a
gwiwa ba ya labartawa mal.
Yadda akai ya san Deedo, har
ma da yadda akai ya tafi da ita.
Goggo wadda ta daskare tun
lokacin data tabbatar da Deedo
din dai ce a wurin, ta kara
kurma wani sabon ihun, a
yayin da Mal. Labaran ya
kwashi sabon salati yace
"Eh lallai dole kike shiga
wannan halin Batula, ka ganta
nan" ya fada yana kallon
Nawap tare da nuna Goggo da
yatsa, yace
"Wannan matar bayan tafiyar
Deedo, duk wanda ya
tambayeta ina yarinyar nan
take, ce mashi take ta tafi
yawan karuwanci, ashe ke da
hannunki kika dauki diya kika
bayar, chabdi! Lallai Allah yana
son ki Batula, tunda har ya
baki damar sake ganin Deedo
don neman gafararta"
Cigaba da jinjina kai yayi, ko
a film bai taba jin irin wannan
tsantsan rashin imanin na
Goggo Batula ba.
[26/04 01:21] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 110
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Deedo wadda take shar6ar
kuka domin jin bayanin mal.
Labaran nan da nan taji wata
sabuwar tsanar Goggo ta karyo
mata, ba don kanwar ubanta
bace, da babu wani abu da zai
kara hada su, duk uwar azabar
da ta gana mata bata isheta
ba, har sai da ta zubar mata da
duk wani mutuncinta daga idon
mutanen garin.
Nawap ne ya lallabata har tayi
shiru, sannan ya kai dubansa
ga mal. Labaran wanda har
yanzu bai daina mamakin
makirci da mugun hali irin na
Goggo ba,
"Mal. To ita menene
musabbabin dawowarta haka?
Ina yaranta suke ne basu kula
da ita?"
"Chabdi! Dogon labari
kenan,"
Cewar mal. Labaran, sannan ya
cigaba
"Abinda yayi sanadin
dawowarta haka baya rasa
nasaba da dan ta shehu,
wanda tun yana dan shekara
sha biyar ya zama tataccen
dan daba, inda ya shiga wata
kungiya ta wasu mutane masu
yanka mutun su gudu. Haka ta
faru da shi bayan ya soka ma
wani yaro wuka a ciki, ya gudu
ya bar garin, yan sanda suka
nemeshi suka rasa, har suka
kame ita Batular, inda wani
bawan Allah da bata san ko
wanene ba yayi belin dinta, to
bayan an sako ta daga caji ofis
din ne ta taho gida mota tayi
ciki da ita, wanda hakan yayi
sanadiyyar rasa kafarta guda ta
dama"
Mal. Labaran ya dan
tsagaita, sannan ya dora,
"To ita kuma waccen Hadizar,
babbar 'yar tata kenan, da tana
kula da ita, daga k'arshe sai
abin ya dawo kamar ta dan
samu ta6in hankali, kullun in
banda kuka da kiran shehu
bata da wani aiki, nan zata yi
kashi, tayi fitsari, bata iya
motsawa ko kadan, ana haka
duk Hadizar na taimaka mata,
kwastam, sai aka wayi gari aka
ga Hadiza da katon ciki wanda
babu wanda ya san inda ta yo
shi, kuma ita dai ba aure akai
mata ba, nan fa yaran unguwa
suka dinga jifarta, suna
zaginta, itama daga nan aka
nemeta aka rasa. To ni dai a
ganina kukan rashin ya'yanta,
da kuma iftila"in da ta jefa
mutane, shine yayi sanadiyyar
rasa ganinta, ana haka kowa ya
watse babu ko wanda yake
kallonta, sai fa ni din nan, nima
dan dai kawai in sauke hakkin
makwabtaka, amma in ba haka
ba, babu abinda zai sa na kalli
mai mummunan hali irin na
wannan matar"
Ya karasa maganar, yana
mai nuna ta da yatsarsa.
"Hasbunallahu wa ni'imal
wakil"
Shine abinda Nawap yake
maimaitawa, yayin da yayi
saurin dauke idonsa akan
Goggo, wadda yake jin kamar
ya shaketa ya hada da bango
ta mutu kowa ma ya huta.
"Sai ki nemi yafiyar yarinyar
nan, tunda Allah ya taimaka
miki gata a gabanki a karo na
biyu"
Cewar mal. Labaran kenan
yayin da yake kallon Goggo.
"Na yafe mata ni kam, mal.
Ko yadda Allah ya mayar da ita
ai ya isa ishara gareta, da duk
wani mai hali irin nata, fatan
dai Allah ya yafe mana baki
daya"
Deedo ce take wannan jawabin
a lokacin da take share kwallan
idanunta.
"Amen" duk jama'ar wurin
suka ansa da.
Goggo dai banda wasu
surutai, da wasu yan bige bige
kamar wadda sauro ke cizo
babu abinda takeyi, sai kuma
lokaci zuwa lokaci kaji ta
kurma wani gagarumin ihu,
babu Allah, bare kuma salatin
annabi a bakinta.
Kofar gidan suka fito gaba
dayan su, in banda ita da bata
iya takawa sai dai
rarrafe.
Gaban mota Nawap ya
bude, ya fito da kudi wanda
bansan adadinsu ba, mik'awa
mal. Labaran yayi,
"A taimaka a gyara mata
ginin nan da ya rufta, sannan a
dinga sai mata abinci, inda hali
a samu wanda zai rinka
tsabtacce mata wurin, ni zan
rinka biya in har an samu
wanda zaiyi hakan, mun gode
mal., Allah ya kara girma, ya
kuma baku ladar abinda kuka
yi"
"Amin" ya fada, sannan
sukayi musayar number shi da
Nawap, ya wuce zuwa cikin
gidan shi, inda shi kuma ya kai
kallonsa ga su Deedo da sukai
jugum,
"Sai ku shiga mu wuce"
Babu gardama, duk suka
shige suka dau hanyar
komawa.
Sai da suka shiga Bauchi
sannan suka tsaya, domin
neman abinda zasu ci, anan
Deedo ta kira hally, tai mata
kwatacen gidanta suka je, nan
ta tarar da ita har da dan
yaronta mai shekara daya da
rabi, suna cikin fira take shaida
mata halin da Goggo take ciki,
addu'a dai sukai mata, inda
daga bisani ta fada mata
bikinsu kwana goma masu
zuwa. Hally kuma tai mata
alkawarin zuwa in har Allah
mai kowa mai komai ya bata
iko, sukayi sallama, sannan
suka dau hanyar Kaduna.
[26/04 02:05] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 111
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Har suka iso gida firar da suke
ta irin mutane masu halayya
irinta Goggo ce, Hafsat wadda
abin ya zama sabo a wurinta
tace
"Allah kenan, buwayi gagara
misali, yanzu ji yadda matar
nan ta dawo, ko duniyar da
take ma hadama ta juya mata
baya, suma ya'yan da ta
musguna ma wasu saboda su
sun gudu sun barta, kai Allah
dai ya sa mu cika da kyau da
imani,"
"Amen" suka ansa da shi,
lokacin da suka iso kofar
gidan, ana ta faman kwalla
kiran sallar maghriba.
* *******
Kwana ukku da dawowarsu,
su Ummi suka dawo, inda tayo
siyayya ta ban mamaki, sun
hado mata lefe dai dai
gwargwado, babu karya, babu
kuma karanta a ciki, sai dai
san barka, haka kayayyakin
daki ma sun siyo dai dai
iyawarsu, inda suka karasa
siyen sauran anan gida
Nigeria.
Bayan Ummi ta natsu, ta
huta duk hankalin kowa ya
dawo jikinshi, anan take
tambayar Deedo yadda akai
bata je Ningin ba, ta kara da
cewar
"Ba dai mutumin can ne ya
hure maki kunne ba?"
Ta fada tana kallon Nawap,
Murmushi Deedo tayi, tace "ko
daya Ummi, munje ai"
Nan ta labarta duk abinda ya
faru, bata rage komai ba,
Salati Ummi tayi, sannan ta
kara da "Allah kasa my gama
da duniya lafia"
Suka ansa da amin gaba dayan
su, inda suka d'auko wata firar,
wadda yawanci duk labarin
yadda za'a tsara bikin ne suke.
Biki dai sai matsowa yake,
inda yau rage kwana hud'u a
fara. Kasancewar Deedo bata
da tarkacen kawaye, hakan ya
bata damar kammala duk wani
rabon invitation da zata yi,
wanda dama duk course mates
dinta ne ta gayyato, sai fa yan
mutanen da baza a rasa ba,
wanda suke gaisawa a
makaranta.
Hakan ya bata damar
natsuwa wuri guda, tana
daukar gyara a wurin matar da
Ummi ta dauko takanas, daga
Niger republic. Haka Hafsat ma
ba a barta a baya ba, itama da
nata sinadarin gyaran na
daban, wanda ya kasance
tsakanin ta da Deedo ne, sirrin
kissa da kisisina, da iya rik'e
miji kawai take dora mata,
yayin da Deedo take kwashe su
a kwakwalwarta kamar tana
rubutawa. Domin ko zamanin
nan dai sai da kissar, amma
sai kaga mace a harbutse, ko
magana bata iya ba, sai kuma
idan mijin ta ya kyallo wata
abun ya zama bala'i, a daure a
koyi sirrikan mazan aure
yanuwana.
Rana bata karya, wai sai dai
uwar diya taji kunya! Inji
Hausawa. Haka aka fara bikin
Deedo da Yaa Nawap dinta,
amarya sai kyalli take tasha
dilka, tayi kyau har ta koshi da
shi.
Daga su sai su suke bikin
nasu, dangin Maman ta ne, sai
kuma dangin baban su Nawap,
sai 'yan gayun kawayenta
wanda duka duka basu wuce
mutun sha biyar ba, biki ne
suke hankali kwance ba tare da
hayaniya ba, babu wata bidi"a,
illa kyakkyawar dinner da za
suyi a gobe, sai kuma daurin
aure.
Amarya ce ta fito cikin light
brown din gown mai asalin
kyau, wadda ta dace da kirar
jikinta, yayin da KHADY'S
MAQUILLAGE ta gwangwaje ta
tsararran make up mai daukar
hankali. Tayi kyau dai dai
misali, haka angon ya fito a
cikin danyar farar shaddar
Sheraton, wadda taji lafiyayyan
aiki da light brown din zare,
hularshi da takalmansa, gami
da agogonsa duk light brown
din, sunyi kyau kamar a sace.
Bayan sun shigo hall din Kabir
Gymnasium, inda ya kasance
can ne aka tanada domin
gabatar da dinner, nan fa aka
fara sakin flash, masu video
coverage suma suka cigaba da
dauka, yayin da zaka hango
farin cikin da yake kwance a
fuskar Ummi domin ganin
wannan kyakkyawar rana.
Haka aka cigaba da
rakashewa, ana gwangwajewa
yadda ya kamata, har aka gama
lafia, kowa ya kama gabansa.
Washe gari da misalin k'arfe
1 na rana aka Daura auren Dr.
NAWAP KHAMIS, & FIRDAUSI
KABIR SANI, akan sadaki mafi
daraja, wanda ya ta'allak'a
akan koyarwa ta ma'aiki
(S.A.W).
Bayan daura auren da
misalin karfe shidda na yamma
aka dauki amarya sai gidanta
dake Sultan Road. Komai ya ji,
babu abinda Ummi bata yi ba,
sai kuma fatan zuri'a mai
albarka.
Kwanansu biyu a Kd, sannan
suka tattara suka wuce Abuja,
kasancewar hutun da Nawap
ya dauka ya kare. Rayuwarsu
abin sha'awa, soyayya suke ta
ban mamaki, kowa kokari yake
yaga ya faranta ran dan
uwanshi, dan haka suke zama
na jin dadi da salama.
Satinsu biyu a Abuja su
deedo suka koma hutu, bata da
yadda zata yi, dole ta dawo Kd,
da sabuwar Mercedes-AMG
dinta wadda Nawap ya bata
tukwicin amarci.
BA’A SHAN
ZUMA…
K’ARSHE
BA'A SHAN ZUMA… 112
NA LUBABATU MAITAFSIR
&BENAXIR OMAR
®NWA
Shi da kanshi ya tuko su,
gidansu suka zarce ko da suka
shigo Kd, wanka sukai suka
gabatar da sallar maghriba
wadda tai musu a hanya,
Deedo ta fito cikin wani skinny
long skirt, da yar top dinta,
gashinta, ta tara shi wuri daya
ta daure, kitchen take k'ok'arin
shiga domin ta sama masu
abinci, a dai dai lokacin Nawap
ya fito palon shima cikin blue
din jeans da red din t-shirt,
gabanta ya karaso, ya mika
mata agogon dake hannunsa,
sannan ya miko hannun, yana
kallon ta.
Ansa tayi, tana tura baki tace
"Abinci fa zan girka mana,
kuma ka zo zaka tsaida ni"
Dariyar yadda tayi da bakinta
yayi,
"Gobe kaman haka baza ki
ganni ba, balle har na tsaida
ki"
Ya fada yana langabar da kai,
Itama fuskan tausayin tayi,
tunowar da tayi gobe fa ita
kadai ce; babu yayan ta.
"Yi sauri dauko hijab dinki
muje gaishe da Ummi, can sai
mu samu abinda zamu ci"
Ya fada yana kallon console
mirror din dake makale a palon,
yana gyara collar rigarsa.
"Da gaske Yaa Nawap?" Ta
fada cikin zumudi.
"Zan ce na fasa ko ki wuce
kizo mu tafi"
Da dan gudu ta shige daki tana
fadin "I'm sorry Mon amour",
Bata wani dade ba ta fito
sanye da dogon hijab har
gwiwanta, suka rufe gidan suka
shige mota sai gidan Ummi.
Taji dadin ganinsu sosai, sun
kuma yi sa'a tana zaune a
dining table tana cin abinci,
dan haka ba tare da bata lokaci
ba suka zauna suma, Deedo ta
zuba masu, suka cigaba da ci
suna fira.
Sai wurin goma da rabi,
sannan suka yi mata sallama
suka wuce gida.
A palo suka zauna, firar
yadda zasu yi missing juna
suke ta yi, a haka har sha daya
da rabi, inda Deedo ta fara
hamma, bata ankara ba ta
bingire a wurin ta cigaba da
bacci. Juyowar da Nawap zai
yi ya ganta sai bacci take,
murmushi yayi, don ya zata
baccin karya ne, saboda haka
take mashi, sai ya dauke ta ya
kaita daki sannan ta mik'e.
Shigewa yayi ya gama shirin
baccinsa, ko da ya fito dai a
haka ya tadda ta, dan haka ya
sa6i abinshi suka wuce dakin
baccinsu.
Tun karfe biyar na asuba
suka tashi, wanka suka yi, tare
da alwallah sannan ya ja su
sallah, bayan sun gama suka yi
adduoin da suka saba, Nawap
ya mike ya koma gado, inda ita
kuma ta wuce kitchen ta shirya
breakfast mai sauki, sannan ta
shirya jikinta da jeans wanda
ya matse ta tsaf, ta samo top
dinta mai fadi ta dora, tayi
kyau sosai, sannan ta matsa
inda yake a kwance, lokacin
karfe bakwai dai dai, fuskarsa
take shafawa har ya buda
idonsa,
"7:am har yayi kana bacci, ka
manta akwai aiki yau ne? Nd
flight din karfe takwas zaka bi"
Ya mike tare da salati,
"Ai duk lefinki ne"
Ya fada yana cire kayan jikinsa,
Ta mika masa towel, "je ka
shirya idan ka fito sai kayi
banbanmin" ta fada tana fita
daga dakin.
K'arfe takwas saura suka fito,
jikinta sanye da doguwar
abaya, ta yane kanta da gyalen,
ita ta kaishi har airport, sannan
ta dawo, tana mai cike da kewa
da maraicin mijin ta.
Daga nan ita ma skool ta
wuce domin sun fara lectures
tun satin da ya wuce.
BAYAN SHEKARA HUD'U
Deedo ce ta fito daga babban
asibitin gwamnati na garin
Kaduna, atamfar super wax ce
jikin ta dinkin riga da skirt, sai
dogon hijab dinta, hannunta na
dama sagale da farar riga ta
likitoci (lab coat), yayin da
dayan hannun yake dauke da
jaka, da kuma katon littafin
(text book) mai hoton
kwakwalwar dan Adam a jiki.
Gaban motar ta kirar BMW
M4 ta isa, ta juye tarkacen
hannunta a baya, sannan ta
bude bangaren driver ta shiga
ta bata wuta, ta wuce
hankalinta kwance.
Cikin unguwar rimi ta nufa
dai dai kan alkali road, naga
tayi parking gaban wani asibiti
wanda aka rubuta TAIMAKO
SPECIALIST CLINIC, lab coat
dinta ta buda bayan motar ta
dauka, yayin da ta shige cikin
asibitin kasancewar wayar da
aka mata kan tayi sauri tana da
marassa lafia. Cikin k'warewa
take bin gadajen marassa
lafiyar, a bayanta kuma nurse
ce tana dauke da file na
kowanne patient a wurin.
Gadon wani dan tsoho ta isa,
wanda yake fama da ciwon
zuciya, ta duba file dinshi, ta
juyo da kallonta gare shi
"Baba akwai gwaje gwaje da
zanyi maka, akwai kuma na jini,
sannan kuma zan duba bugun
zuciyarka, amma sai kayi
hakuri fa"
Cikin ciwo tsohon yace
"Kuma duk a nawa zakuyi
wannan aikin? Ni fa wlh ba
kudi ne da ni ba, sai da nace
su kaini na gwamnati, amma
suka kawo ni nan, ni ban san
ya zanyi ba 'yar nan"
Da murmushinta, ta kalle shi
"Kar ka damu Baba, domin
kuwa babban dalilina na bude
asibitin nan ba komai bane, sai
dan na taimakawa marassa hali
irin ka, in sha Allah za ayi
komai, ba kuma tare da ko
sisinka ba"
Ta mik'awa nurse din file
dinshi, sannan ta wuce zuwa
gado na gaba, haka har ta
gama round dinta, ba ita ta bar
asibitin ba sai misalin karfe
biyar na yamma.
[26/04 09:40] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 113
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Tana shiga gidan ta zube a
palo saboda tsabar gajiyar da
ta kwaso, hannuwanshi taji ya
ziro ta kafadarta yana danna
mata su a hankali, lumshe ido
ta fara yi, tana jin tamkar a
mafarki,
"Likita bokan turai" shine
abinda ta ji an fada, wanda
yasa tayi firgigit ta juyar da
kanta tana kallonsa.
"Yaushe a gari?"
Ta fada tana kare mashi kallo,
murmusawa yayi,
"Ko 30 mins banyi da
shigowa ba, na gaji da missing
matata bazan iya daurewa har
sai Friday kafin na ganta ba"
Ya zagayo inda take a zaune
ya zauna a gefenta,
hannuwansa cikin nata.
Bude bakinta zata yi magana
wata kyakkyawar yarinya mai
asalin kama da Nawap, ga dan
banzan wayo, duk da
shekarunta basu wuce biyu ba,
ta rugo da gudu ta fada kanta,
tana shashshekar dariya.
"Mammy sannu da zuwa" ta
fada cikin maganarsu ta yara,
lokacin da ta mik'e ta rungumo
wuyanta, tana mai nuna farin
cikin ganin Mammyn tata.
Sama Deedo ta daga ta,
tana fadin
"Thank you Ummina "
Nawap ya jawosu jikinshi
yace "Ummi har kin manta da
ni ko, dan kinga mammy ko?
Gobe ma zan koma bazan kara
wasa dake ba"
Suka kyalkyale da dariya ita
din da Deedo, yayin da ta
zaunar da ita a tsakaninsu, ta
mika hannu ta rungumo
Nawap, shima haka yasa
hannunsa ya k'ank'amesu yana
jin soyayyar matarshi, da tilon
'yar tasa, har cikin birnin
zuciyarsa.
ALHAMDULILLAH, anan na
kawo karshen wannan labari,
kuskuren da nayi Allah ya
gafarta mana, Allah kuma ya
amfani abinda na fada dai dai,
ya bamu ikon amfani da
darasin da yake ciki.
This is a dedication to a sis
from another mother (FEEDO-
DEEDO) thank you 4 been
there always.
Special thanks to Aysha
Chuchu, Jam33la & Ummu
Ahmad, 4 loving this story like
no one.
Nagode kwarai da hakurinku
akan jinkirin da aka samu kafin
kammaluwar wannan labari. Ku
cigaba da kasancewa tare dani
a labarina na gaba wanda ya
ansa sunan K'ADDARAR
AURENA!
Lubabatu Maitafsir & Benaxir
Omar muke yi maku fatan
alkairi a koda yaushe.
Complied by Princess Aysha Muhammad