Amsard yace",mekenan haka?
Fayal tace"abinda kakeso mana nafada kayi tunani zaka gane".
Amsard yace"aa nidai kimin bayani".
Fayal tace"toh 1 mean i.
4 mean love. 3 mean you.
Kaga in aka hada i love you kenan'.
Amsard yace"wooooooooow!
Nakasa rufe baki bansan yadda kalmar nan take da dadiba sai yau
Gaskiya naji dadi kuma nagode sarauniyata".
Fayal tace"uhummm toh nima sai kafadamin".
Amsard yace"toh ai nawa me sauki ne indai wannan kalmarce har sai kingaji daji dan haka
*I LOVE YOU I LOVE YOU I LOVE YOU*
Sai da yafada sau uku da karfi sannan fayal tace"wAyyo Allah kunnenah zai fasamin kunne jama'a akawo agaji".
Amsard yasa dariya taredacewa"i love you baby princess".
Fayal ma tayi dariya sannan tace"toh dai Allah yashiryamin kai".
Amsard yace"Ameeeen matar".
Fayal tace"au har nazama matar?
Amsard yace"eh mana ai har andaura asama saura nakasa". Fayal tace"a lallai ne ango".
Amsard yace"yauwa amaryar mukwana lafiya ".
Fayal tace"owk byeee
Misss you".
Amsard yace"miss you too".
Sukayi sallamah cikin nishadi da begen juna.
Fayal bata kwanta barci ba sai da tatashi amnah domin sanarmata abinda ke faruwa.
Fayal tace"amnah amnah amnah kitashi".
Amnah tace"uhumm fayal menene?.
Fayal tace"tashi kizauna muyi magana".
Amnah ta tashi tareda cewa"toh inaji".
Fayal tace"wai afadawa su dady da momy yan uwan amsard dasuzo jibi".
Amnah tace"woow harkinsa nadaina jin barci dagaske?
Fayal tace"ehmna dagaske nake miki".
Amnah tace"gaskiya naji dadi da safe ni zan farawa momy albishir ".
Fayal tace"umm to mukwanta sai da safe ".
Amnah tace"owk byee amaryar mu".
Fayal tace"kyaji dashi dai".
Amnah ta yi murmushi sannan ta kwanta .
Abangaren amsard kuwa suna gama waya da fayal yaje yadauro alolah domin yin lafilah.
Ya roki Allah dayasa alkairy ne haduwarsa da aurensa da fayal.
Sai da ya idar yagabatar sa addu"o insa sannan yakwanta barcinsa.
Washe gari
*PAGE*50
--------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Washe gari tunda safe Alhaji ya fito ya kira hajiya momy yace " Kishirya zamuje gidan Alhaji babba".
Tace "to Alhaji" tashiga ciki ta kimtsa sannan ta fito suka fita.
Ashe duk abun nan da ake amsard yana jinsu yanata murna azuciyarsa. Suna fita shima ya fito falo ya zauna dan yakira fayal.
Kafin ya fito da wayarsa naji tana ringing yana fiddo ta yaga princess ce nan yaji wani sanyi aransa, ya daga tareda fadin.
" Aminci, karamci, halacci da mutunci sukara tabbata agareki ya saraunmiyar kyawawa" Saida fayal taji wani sanyi batasan lokacin data lumshe idoba.
Tace " tareda kai habebe na. Fatan rabin raina ya tashi cikin koshin lfy "
Amsard yace " ina lfy kanwata daman yanzu nake shirin kiranki"
Fayal tace" ai naji hakan azuciyata shiyasa nace bari narigaka"
Amsard yace" gaskiyane Masoyiyata Ammanfa yau kin dan ban mamaki"
Fayal tace "uhum uhum yayana menayi uhum "
Amsard yace" uhum uhum kalamanki sukaban mamaki ashe kanwar tawa gwanace a kalaman soyayya "
Fayal tace " uhum yayana ai soyayyarka ce tasani nazama haka domin banma san yanda akai naji ina furtasuba"
Amsard yace" Lallai kanwata kice naci gari? ".
Fayal tace "sosaima."
Amsard yace " gaskiya naji dadi babyna."
Ahaka sukayi sallama zuciyar kowa cike da shaukin kaunar junansu.
A bangaren su Alhaji da hajiya momy kuwa. Sun isa gidan Alhaji babba. Sunkuwa yi sa'a Alhaji babba baifitaba. S Suna shiga Alhaji babba yataso da murna yace " Alhaji kaine yau agudanmu ba ko waya Allah dai yasa lfy"
Alhaji yace " wlh kuwa Alhaji ai abundake tace damu yafi qarfin waya"
Alhaji babba yace" to to zauna zauna Allah yasa lafiya"
Alhaji yace" wannan tafiyar ta dankace Alhaji. Nazone mu tattauna don danka amsard yasamu mata"
Alhaji babba yace " Alhamdulillah kai amman gaskiya nayi murna sosai kace amsard angirma kai masha Allah "
Alhaji yace " to yanzu halinda ake cikima so nake muje neman auren nasa a jigawane, yaushe kake ganin yakamata muje"
Alhaji babba yace "ai ba abun jinkiri nan gobe goben nan zamuje insha Allah. Asanar dasu kawai"
Ahaka sukayi bankwana akan gobe insha Allah zasuje jigawa neman auren amsard.
A bangaren usman kuwa yana isa gida. Ya yi sallama Amina ta taso da gudu tatarbesa cikin murna tace "honey katafi kabarni inata zullumi fatan kadawo lfy."
Usman yace " lfy kalau uwargidana nazo miki da Albishir abokina ankusa angwabcewa. Kuma Dadynsa yabani sabuwar mota hajiya momy kuma tabani one million boron Albishir."
Amina tace" kai Alhamdulillah gaskiya nima naji dadi matuqa kace su yaya amsard ankusa zama ango".
A bangaren su fayal kuwa. Dasafe amnah tatashi tacewa momy "yau inada Albishir da zan baku keda Dady."
Momy tace "Kaii harkinsa nafarajin dadi dagaji Alkhairi ne. To fadamin"
Amnah tace" noooo mommy sai mun je yin breakfast zakiji "
Momy tace " to shikenan "
Bayan su momy da amnah sungama hada kayan breakfast. Momy takira Alhaji suzo an shirya breakfast.
Sun zo an zazzauna amman fayal bata fitoba dady yace "wai ina fayal dita? " Amnah tace "tana daki."
Dady yace" jeki kiramin ita tazo mu karya"
Amnah tace "to dady"
Amnah tatashi tanufi dakinsu tana zuwa tatarar da fayal sai dariya take tana wayarta da amsard.
Amnah ta kalleta tace" ohni su fayal har an zama yan gari a birnin love. Toki taso muje dady nakira muyi breakfast "
Fayal tace " to ganinan zuwa. "
Tai sallama da amsard tatashi suka tafi. Suna shiga ta zauna inda tasaba zama akan dining set ta gaishe da dady da momy.
Suka amsa cikin farin ciki. Dady yace" ina kika shige ne ko barci ake? "
Fayal tace"a a dady kawai ina zaunene. " tafada tana kallan Amnah tana mata alamar tayi shiru karta tonata. Amnah tai shiru kawai tana murmushi.
Kusan mintuna 10 dafara cin abincisu sai amnah tace " dady da momy albishirinku".
Sukace" goro atare suna dariya"
fayal najin haka tai zunbur tamike ta ruga ciki tana rufe fuska domin tasan me Amnah zata fada. dukkansu suka fashe da dariya.
Amnah tace" dady zakuyi baqi gobe "
Dady da mumy sukace" baki kuma Suwa zasu zo mana?"
Amnah tace "dady su Abban amsard ne zasu zo neman auren Fayal"
Dukkansu cikin farinciki sukace "Alhamdulillahi kaiii masha Allah. Allah yakawomu lokaci Kaii gaskiya munji dadi"
Momy tatashi dagudu tashiga ciki tana kiran fayal fayal zozo manaaa 'yataaaaaaa.
*PAGE* 51
------------------------------------------------------------------------
Fayal tana shiga daki ta kwanta .
Momy nashigowa taga fayal akwance.
Momy tace"ah wai kwantawa kikayine aibakiga ta kwanciyaba tunda dai kinsan gobe muna da baki ko?.
Fayal ta girgiza kai alamar eh.
Momy tace"toh kuzo keda amnah kushiga kasuwa kusiyo duk abinda kukasan da"abukata domin bana son aikan auwalu shirme yamasa yawa".
Fayal tace"toh momy".
Sannan tashi tashiga toilet tayi wanka amnah ma tazo tayi.
Batare da bata lokaci dukanninsu suka shirya sannan suka nufi market domin cefane.
Sunyi cefane sose wanda ko wani gidan bikinma ba ayinsa.
Sai misalin karfe 4 suka dawo gida .
Suna shiga momy suka tarar ta kira momyn amnah suna magana akan zuwansu amsard.
Dagudu fayal takarasa gun momy tare dafadin"wayyo momyna mun gaji wallahi".
Momy tacewa momyn amnah"kingama ka ya"yan naki sun dawo ".
Momyn amnah tace"toh ageshemin da amare kuma ahuta gajiya sai goben ko".
Momy "tayi dariya sannan tace"owk amare dasuji eh sai goben kizo da huri fa".
Momyn amnah tace"insha Allah".
Anan sukayi sallamah
Momy ta kalle fayal da amnah tace"a lallai kungaji dan naga har wani baki kuka kara" .
Fayal tace"uhym ba amnah bace take ta siyan kayayyaki " .
Amnah tace"ehdin ai hakanma bamu gama ba komawa zamuyi"
Fayal tayi dariya sannan tace"ai ynzu kam kinyi kadan yarinya".
Momy tace"um ba surutu ba kutashi kuyi wanka sai kuyi sallah maza azo afara rage aiki".
Amnah tace"owk momynmu".
Dukansu sukatashi .
Kowa yayi wanka sannan sukayi sallah aka dukufa wajen aiki.
Abangaren amsard kuwa sai farinciki yake .
Hjy momy kuwa tasashi agaba sai tsokanarsa take shiko amsard baki ba abin magana ba sai dai yayi murmushi.
*washe gari*
Da huri su Alhaji babba suka shirya shida amininsa domin zuwa jigawa.
Fayal suna kichin sai aiki suke sai ga kiran prince yashigo ai tuni fayal tazura daki da gudu"
Momy tace"toh Allah dai yakyauta wataranma kuma agabanmu za ayi ko kunya ba aji ba tunda yanzu ma anfara yin wayar".
Amnah tasa dariya sannan tace"momy kenan".
Sunata aikinsu suna fira sai ga momyn amnah ma ta isa akacigaba da aiki.
Fayal tana zuwa daki ta amsa wayar tare da fadin"Assalam alaika".
Amsard yace"wa'alaiki salam .
Fayal tace"good morning honey".
Amsard yace"morning my princess.
Fatan ranar nan tamiki kyau kamar yadda fuskarki take".
Fayal tace"da ikon Allah mijin kirki
Da fatan dake da"azo domin ina bukatar ganin kyakkayawar fuskar sarkinah".
Amsard yace"uhumm bayan sunce baza azo dani ba uhumm ni kuka ma zanyi".
Fayal tace"uhummm haba sarkina karkayi kuka kayi hakuri kaji kasan me kyau baya kuka".
Amsard yace"uhummm ni a"a sai nayi fah'.
Fayal tace"uhummm uymmm toh muyi tare uhummmm uhummmmm".
Amsard yace"wayyo rufamin asiri sarauniyata karkiyi kuka ai inwani ne ma yazubarmin da hawayenki sai na zubarme da idonma gaba daya".
Fayal tace"toh promise bazakayi kukan ba".
Amsard yace"i promised sarauniyata.
Fayal tace"tanx my sarki.
Alhaji yasa sahala takira amsard tazo tasami amsard nawaya tace"yaya alhaji yana kiranka".
Amsard yamata alama da hannu da nufin yana zuwa.
Amsard yacewa"fayal byeee sarauniyata alhaji nakirana".
Fayal tace"owk byeeee miss you take care".
Amsard yana zuwa alhaji yacemasa gasu alhaji babbanan sun iso kazo kai zakayi musu jagora zuwa jigawan.
Amsard yaji dadin jin hankan sose amman haka yaboye azuciyarsa gudun kar ace yayi rashin abin.
Abangaren fayal kuwa suna gama waya taje kichin aiko ta tarar momyn amnah ta iso.
Momyn amnah tasa fayal agaba sai tsokanarta take.
Fayal kuwa takasa magana gashi amnah da momy sai dariya suke mata.
*PAGE* 52.
-------------------------------------------------------------------------
Amsard ne ke tuka su
Sunyi nisa atafiya sannan yashiha gidan mai domin kara me amotar alokacin ne yama usman text cewa"muna hanya fa dani akazo inmun kusa dan ma magana muhadu agidan su fayal din".
Alokacin daya tura text dai dai da gama sa man da ake hakan yasa suka cigaba da tafiya su Alhaji babba kuwa sai hirarsu suke amota .
Insuka ma amsard magana sai dai yayi murmushi in nabada amsa ne sai yabAsu.
Su momy sun kammala kome hakan yasa sukaje suka kara wanka kowa yaci gaye sannan suka fara shirya abincin acikin flas da dish.
Adai dai wannan lokacin su amsard suka iso .
Usman ma ya iso domin amsard yakara masa text din.
Usman ne yafara shiga yasanar wa da dady sun iso dama shima dady yakira dadyn amnah suna xaune jira kawai su amsard su iso hakan yasa yace"a madallah kushigo mana ".
Su Alhaji babba suka shigo sunyi gesuwa ta mutunci sose da dady kamar sun san juna hakam ba karamin dadi yamusu ba .
Bayan sun gesa ne dady yasa akaturo amnah .
Amnah tana zuwa yace "yauwa damuyi maganene kikai shi bakwon nako dayan falon kwa gesa achan".
Amnah tace"to tare da fadin muje to".
Amsard da usman suka bita tashiga dasu falo.
Sannan ta koma ta sanarwa da momy akan akai musu abinci.
Amnah tace"momy fayal takai wani karamin falo ni dan kai na dady .
Momy tace"owk".
Aka kira fayal takai abinci .
Fayal tace"uhumm momy nifa kunya nkeji".
Momy tace"a basu sanki ba ma".
Fayal tafara shagwaba aiko momyn amnah tace"maza dauka kikai amnah kema dau naki.
Ba musu dukansu suka dauka domin sun san halin momyn amnah atsaye take.
Abangaren su alhaji kuwa
Alhaji babba yanemawa amsard auren fayal kuma dadyn amnah yabasu tare tabbacin ba bata lokaci za ayi bikin.
Sunyi farinciki sose ana cikin hakane amnah takawo musu abinci suka fara ci cikin nishadi.
Fayal tana zuwa kawai taga abin mamaki wai amsard ne zau ne dan ita ko ganin usman m batayi ba.
Ta sake baki kawai tana kallonsu.
Amsard sai murmushi yake mata.
Usman yace"yadai amaryar mu ki karaso mana.".
Sai alokacin fayal tagane ashe ba amsard vane kadai.
Tayi murmushi tare da ajiye basket din abincin.
Sannan tazauna tana fadin"sannun ku dazuwa".
Usman yace"yauwa amaryar mu".
Fayal ta ce"ina hininku".
Amsard yayi sauryn cewa lafiya lau" .
Usman yace"kai mallam adai bary na amsa ko?
Amsard yace"aa barni mallam gwara na amsa abina".
Fayal tace"uhumm wato da kacemin barakazo ba ko?.
Amsard yayi murmushi sannnan yace",ai surprise nakeso namiki neh".
Fayal tace"ysssn zakayi bayani amman dai ga abinci kufara ci".
Fayal ta zuba musu abincin tare da musu bismillah.
Usman yace"toh nidai akwoshe nake uwargida tacikamin ciki da abinci.
Fayal tace"haba dai kaci mana banda fulako fah'.
Usman yayi dariya sannan yace"ai kigodewa Allah akwoshe nake da sai nacinye abincin nan duka.
Fayal tayi dariys tare da fadin lallai kam.
Amsard yace"uhumm nito kizo muci ".
Fayal tace aa nifa nakwoshi.
Amsard yace",uhummm uhummm ni wallahi sai kinzo danci".
Fayal tace"uhymm ni aa kaci".
Usman yabude baki tare da fadin"laaaaaa agaban nawa?
Toh bara nabarku .
Amsard da fayal suka sheke da dariya atare .
Domin sun sunmanta ma dashi awajen.
Niko nace kwaga masoyan asa....
Amsard yace"au mallam daman kana nan nsh"
Usman yace"ai baka tuna dani ba kam.
Ahaka sukata zolayar juna har sukaci abincin.
Su alhaji sun tsayar da auren nan da karshen wata .
Sukayi sallama tare dasaawa akira musu amsard da usman dasu koma gida.
Fayal tunda taji maganar tafiya tafara shagwaba akan amsard ba zai tafi ba.
Usman yace"yoooo kwana nawane?
Ai munkusa hutawa da wamnan shagwabar".
Dakyar amsard yalallaba fayal ta hakura.
*oh su fayal anzama yar love*
Suka rabu cikin farinciki da begen juna.
*PAGE* 53.
------------------------------------------------------------------------
Su amsard suka kama hanyar komawa jigawa.
Ita kuwa fayal tana komawa momy amnah tasa ta agaba tana da anki zuwa amma tunda akaje aka hango ango an labe.
Fayal takasa zama dan kunya.
Ahaka rayuwarsu fayal da amsard takasance arana sai suyi waya sau goma ko fima .
Yau yakasance saura kwana biyu biki.
Dan haka gobe sa lalle kuma za ayi kamu.
Amsard tuni ya iso jigawa gidan usman ita kuwa AmeenAh tuni takoma gidan su fayal domin shirye shirye da hike fayal bata da wasu kawaye Ameenah da Amnah ne sai kuma kawayen amnah na skul da suka gaiyata.
Washe gari
Anata chukuchukun biki
Lokacin tafiya kamu yayi.
Fayal tasaka jan doguwar riga tare da golden din rosil da takalmi tare da pos dinta.
Sukuwa kawayen amarya golden din kaya suka da jan dan kwali.
Amsard ma jan kaya yasa tare da golden din takalmi da hula.
Abokanansama golden din kaya sukasa
Agaskiya abin nasu yatsaru ba sai nabata lokaci wajen muku bayani ba.
Anfara kamu lafiya sannan akasa fayal a lalle tare da amsard .
Ankira amsard da fayal suyi rawa fayal ta kame kam
Shiko amsard yabawa mutane mamaki.
Yadunga tikar rawa sai vedio akemasa wasu kuma na masa manni.
Ahaka aka kammala cikin farinciki.
Washe gari yakasance daurin aure dan haka dun bun mutane sun sheda aure fayal da amsard.
************
Rayuwa suke cikin farin ciki da zaman lafiya tare da annashuwa.
Kowa yana kyautatawa juna akullum suna gundun bacin ran junan su .
Anacikin haka fayal tasamu ciki.
Tasamu kulawa agurin amsard kamar yadawo da cikin jikinsa yake.
Ita kuwa fayal ansamu damar shagwaba sai wadda ta karu.
Anacikin haka fayal ta haihu lafiya tasamu yarta mace.
Wace akasamata sunan hjy momyn amsard
Ana kiranta da *ASHNAH*
*ALHAMDULILA NAN NAKAWO KARSHEN LITTAFINA MAI TAKEN 'BABU RUWAN SO' BANSAN IYA YAWON GODIYA DA ZAN NUNAMA D'UNBIN MASOYANA BA, NAGODE KWARAI DASO DA KAUNAR DA KUKA NUNA MA LITTAFINAN, ALLAH YABARMU TARE........**THANKS ALOT ALL MY FANS.....LOVE YOU SOOOOO MUCH*💋*Godiya ta musamman ga duk 'yan group d'ina, dakuma 'yan uwana writers nagode sosai Allah yasaka da alkairi da zumunci da san da kuka nunamin.*_*Jinjina Gareku ' yan Zamani Writer's Association nagode kwarai Allah ya kara d'aukaka*_My fans sai kunjini a sabon novel d'ina nan gaba me taken *KUCHAKAR KISHIYA*
*Ur"s preety xayeesherth*💖