*shafin masoya*
_ba shakka banida bakin godiya gareku masoyana, kan addu’o’I da kwarin guiwa da nake samu a wurinku, haka ina mai baku hakuri kan tsaiko da aka samu na ci gaban wannan littafin na wasu kwanaki, hakan ta faaru ne saboda jarabawa da ke gabana. Ina kallon sakonninku musamman wata ‘yar *ADAMAWA* fullo mai cewa za su min taron dangi idan banyi typing ba, da masu nuna fushinsu musmman wata na nan ‘yar *KANO* da sauransu, duka ina mai baku hakuri, ina kuma so kusan cewa ana tare sosai da soannan._
“ai sarai kasan mu ba makafi ba ne, domin duk fadi tashin da mukayi, ba wanda ka yi wa jagora” Aseeya ta fada cikin tsiwa.
Bayan ya murmusa, ya ce da ita, “ba abin da nake nufi kenan ba, inaso ku duba da kyau, bayan kun ajiye hankulanku wuri daya, ku duba ku ga, wancen icen wanne iri ne”? ya fada a dai dai lokacin da yake kokarin nuna masu icen daga nesa taku dari da talatin daga kan matsattsiyar hanyar da suke tafiya a kai. Gaba daya suka tsaya cak domin ganewa idanuwansu wanne kalar ice yake so su gani, kasancewar da duhun dare, ba ko daya daga cikinsu da ya fahimci, wanne ice ne wannan, ganin haka sai suka karasa zuwa icen domin shaidawa idanuwansu, cikin wofantar da abin, Aseeya ta ce, “ai wannan icen ‘lim’ ne (dogon yaro), me ye kuma alakarsa da fitarmu daga wannan jejin?”
“Haba, ki ajiye hankalinki wuri daya mana, duk walogarar da muka yi a baya ko sau daya kin ci karo da shi icen”
Cikin rashin sanin amsar da za ta bayar ta yi shu kawai
“abokina har yanzu wannan bai fito da bayanin cewa mun fita daga wannan jejin ba, domin ni har yanzu, iya inda idanuwana ke hangowa, ba abinda nake gani face, shirgegen jeji, ta ko’ina na duba kuwa” in ji Abdul
“aboki kenan, ai har gobe, idan kana tafiya a jeji, da zarar ka fara hango icen ‘lim’ kai tsaya ka tabbatar kana kusa da gari”
“mun gode da wannan ilimi da ka karar da mu”
Suka dawo kan hanya suka ci gaba da tafiya, cikin dokin ganin gaskiyar maganar Ameer, suka rasa me za su yi, bakin ciki na har yanzu gari yaki ya zo kusa, ko farin cikin cewa tabbas suna kusa da gari, duk ba wannan ne babban tashin hankali ba, domin a halin ynzu suna kusan karfe biyu ne na dare a tsakiyar jeji.
Tafiya ta yi tafiya, ga shi a yanzu ba mai takalmi a kafafuwansa, domin su Ameer da Fate da aka kama su lokcin masu cin mutane suka swance (cire) musu nasu takalmin, sai faman ketar yashi suke, kasancewar shi ne shimfide a ‘yar matsattsiyar hanyar da suke tafiya a kai wacce iyakarta ta dauki mutum daya, haka suka jero kamar wadanda ke shiga layin jefa kuri’ah, Aseeya ce a gaba, sai Abdul a bayanta, inda Fate take biyarsa, shi kuwa Ameer yana daga baya, suka yi tsit, kamar wadanda mutuwa da gifta ta gabansu, a zuciyoyinsu kuwa, kowa da kalar tunanin da ke zo masa, daga mai kokarin tuno gida, sai mai tunano abubuwan da suka gudana da su, ganin shurun ya yi yawa, Ameer ya yi gyaran murya, sai ya ce da Fate, “idan kin shirya, bari na kawomaki hujjoji kamar yadda kika bukata, amma ga shi ba ~Bible~ a hannunki, ko na kawo kawai”?
Sai lokacin Fate ta duba hannunta taga ashe ba littafinsu mai tsarki a tare da ita, sai ta tsaya chak, dalilin da yaa tsayar da Ameer ke nan, kasancewar shi ne a bayanta, jin ba motsinsu a baya, su Abdul suka waigo, sai suka gan su sun yi cirko-cirko, “me ke damunku?” in ji Aseeya, “bakwa ganin dare ya yi, kuma sauri fa muke yi domin fita a wannan *BAKIN JEJI* ga shi kuna so ku tsaida mu, duk kwanakin da muka yi, kuna nufin baku gaji da kallon jejin ba?”
Fate ce ta karbe zancen, “littafina muka baro baya, kuma ina tunanin wurin masu cin mutanennan ya fadi”
“ah! Tau me kike so kenan yanzu”? inji Aseeya
“mu koma mu dauko mana”
“ke wacce irin mahaukaciya ce? An gaya maki burkutu da giya da kuke sha har su mayar da ku wawaye, kowa ma sha yake yi? Shin ko dai ba tare da ke muke ba a duk wannan fadi tashin cikin wannan jejin? Ina ganin kin rasa hankalinki ne, yanzu da bakinki kike shawarar wai mu koma wurin masu cin mutane? Nasiha daya zanmaki, zan jira ki a nan, sai na nemi wuri na zauna, kafin ki dawo, kin manta gudun awa nawa muka diba kuwa, har kike yunkurin komawa, lallai sai yau na gasgata Hausawa da suke cewa ‘duk wanda Allah ya yankewa Kazar whala, ba shakka dole ya fige ta’ nikam wallahi ba inda zan je, ga Abdul nan dai ko Marubuci nasan shi zai biki”
“rufamin asiri, nan da kike ganina, masifaffiyar yunwa nake ji wallahi, ko abinda ya mayar da ni zuwa cen ai ya isa ya kashe ni, balle wadannan marasa imani, inje su cinye ni danye, a a walla” inji Abdul
Ameeer ya kalle ta, ya ce, “a rayuwa akwai abubuwa da ke faruwa ga mutane, wadanda ba sa da abinda za su iya yi a kai, inaso ki kalla ki gani, da littafinki, da rayuwarki wanne ya fi amafani? Ki duba ki ga, shi littafin za ki iya sayen wani, ita rayuwarki fa? Ki yi hakuri, duk abinda ya kasance kwaya daya, kamar ya kare ne (daga mahifiyata) saura kadan ai, mu koma gida.
Nan ya rarrasheta, ta aminta suka ci gaba da tafiya, sai ya ce da ita, “ga tufka da warwara daga littafinku”
Exodus 4:22 “ *and thou shalt say unto pharaoh, thus saith the lord, Isra’el is my son, even my first born”*
“Kin ga a wannan ayar uabngiji ya kira annabi Yakuba (Isra’el) a matsayin dansa na farko”
Colossians 1:13-17 “mun karanta lokacin da Paul yana kokarin tura later zuwa ga mutanen colosea wani gari ne a Asia ya nuna cewa annabi isah ne dan ubangiji na farko
“Kinga kuwa da tufka da warwara”
“Ga wata tufka da warwara”
“munkaranta a cikin Bible bayan ubangiji ya halicci annabi Adamu, sai ya halicci Hauwa’u daga awazarsa (hakarkarinsa) ta hagu, sai yaa umarce su da su zauna cikin aljanna su ci duk abinda suke so, banda itaciya daya (haka labarin yake har a Qur’ani), a Bible ga yadda abin ya zo
Genesis 2:17 “ *but of the tree of the knowledge of good and evil thou shalt not eat of it, for in the day that you eatest thereof thou shalt surely die.”*
“Kinga anan ubangiji ya ce a ranar da suka ci daga itaciyar, a ranaar zasu mutu. Karanta wannan ayar”
Genesis 5:5 “ *and all the days that Adam lived were nine-hundred and thirty years and he died”*
“Kin ga a wannan ayar an nuna ya rayu har tsawon shekaru 930, wanne ne gaskiya daga ciki?”
“Ga wata tufkar da warwara”
John 3:13 “ *and no man hath ascended up to heaven, but he that came down from heven…”*
“A wannan ayar an nuna ba wanda ya taba tashi zuwa sama karanta wannan”
2kings 2:11 “ *and it came to pass, as thy still went on and talked, that, behold, there appeared a chariot of fire Elijah went up by a whirlwind into heaven”*
“Ga wani Bible dinkuu ya tabbatar cewa ya tashi sama.”
Duka jikinta ya yi sanyi, duk da ba Bible a hannunta, ta tabbatar ba zai karanto ayoyi ba yadda suke ba, saboda ya yi fiye da nawa kuma duka bai kuskure ba.
“Munkaranta a littafinku lokacin a annabi Sulaimanu yana gina fadarsa, ga yadda abin ya zo”
1kings 5:16 ya sanya mutane dubu uku da dari uku(3,300) domin su kula da aikin kawai
A 2chronicles 2:2 mun karanta cewa mutum dubu uku ne da dari shida (3,600)
“Kar ki gaya muna cewa typing error ne, domin lokacin ba da figures ake kidaya ba, wanne ne daidai”?
Haka sai tafiya suke yi yana kokarin zakalomat tufka da warwara har sama da ashirin, ya ce da ita duka wadannan ba komai ba ne kaan hujjarr cewa littafinku ba daga ubangiji ba ne, “me yasa ka fadi haka?” “saboda akwai wasu munanna sifofi da kuka sifanta ubangiji da su, wadanda ya tsarkaka da a sifantashi da ko daya. Ga misali
Isaiah 5:26 “ *and he will lift up an ensign to the nations from far and will hiss unto them from the end of the earth, and behold they shall come with the speed swiftly”*
“Kinji daga littafinku, ubngiji zai fidda sauti irin na mazijai”
Isaiah 7:20 “ *in the same day shall the lord shave with a razor..”*
“Subhanalillahi, kinji ubangiji zai rage gashi a littafinku, wasu abubuwan ba ss faduwa masu karatu kuyi hakuri.
Suka ci gaba da tafiya har suka karaso inda idanuwansu suka fara tozali da ginin gidaje, ai kuwa basusan lokacin da suka diba aguje ba, firar su Fate dole ta tsinke Abdul ne kan gaba wurin gudu, har suka iso daf da wani gari.
Wanne gari ne wannan?
Karshen wahalar kenan ko kuwa wata wahalar ce sabuwa za su fada?
DR. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
2⃣8⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
*Quote of the day*
_he who is not courageous enough to take risks, will accomplish nothing in life_
*shafin masoya*
*_shafin yau naku ne sababbin members na PEN WRITERS ASSOCIATION. Nordin, ‘yar father, Maman twins,Maryam Kummi, Feenert tareda ‘yar autarsu_*
_ina rokon ubangiji da ya karemin ku, ya kuma sa kun shigo wannan rubutun a nasara, ya kuma baku ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi, kuma ku sami lada a kai, ya tsare ku daga rubuta abinda zai jawo maku la’antar ubangiji a gobe kiyama_
*jaje*
_khausar ubangiji ya baki lafiya ya sa kuma kaffara ce, haka Farida Alfijir Allah ya saka wannnan rashin lafiyar cikin ma’auninki. Pen writers ina alfahari da ku irin sosannan_
*jinjina*
_jinjinar ta ki ce ke kadai ‘yar garinmu, Nabeela Dikko, ubangiji ya kara dukaka ki ya bada sa’a a wannan sabon littafi da kika soma_
*tsofaffin members na pen writers ba zan ambaceku ba har dai su o o* lol
Cikin gudunsu suka karaso daf da gidajen wannan kauyen, gari ne da duk da cikin dare ne, suna iya ganin komai kasancewa a lokacin wata ya haskaka ko’ina, gari ne da ba ya da girma sosai, domin a wuni daya sai ka hardace sunayen duka mazauna garin, duk da rashin girman garin, yana da makarantar mataki na farko a boko, duk da azuzuwa guda uku ne kadai, inda sauran dalibai suke karatu a karkashin itace. Suka yi cirko-cirko sai dubann fasali da tsarurukan ginin garin suke, a zuciyoyinsu kuwa farin ciki kamar wadanda aka yi wa bushara da gidan aljanna, ammaa lokaci daya suka kasa bayyaana farin cikin a fuskokinsu, kasancewar iya dubansu ba wanda suka gani, hasalima ba abinda ke taryarsu face kukan kwari sai sautukan karnuka daga nesa, ganin haka sai suka dinga zagayara garin, amm kasancewar lokacin sanyi ne, ba ko mutum daya da suka ci karo da shi koda da sunan barcin waje ne kuwa, hakan ya sa suka dinga zagayar garin har suka zo kan babban titi, ganin haka, suka sake bugewa da sabuwar murna, minti biyar da tsayuwarsu kuwa, mota ta zo taa wuce, a guje, duk da sun tare ta ta hanyar yin alama da hnnu, hakaa motar ta wuce a guje, ganin haka suka ci gaaba da zagayawa, har suka kawo wurin wani karfe a aka daurawa wani falanken katako mai fadi, inda aka rubuta a jikinsa, *DUKUSHI VILLAGE* suka wuce ta wurin, suka sake dawowa cikin garin, suka zauna cikin mkarantar garin da gaba daya azuzuwan ba mai gambu idan ka leka ta ciki kuwa sai kayi zaton fili ne inda ake sallatar sallar idi, domin kuwa gada daya suminti da aka shafe ksan ajin da shi ya tashi, allon bango da ake rubutu da shi kuwa, gaba daya ya dawo fari, ta ydda ko da rubutu aka yi da shi ba yadda za ka iya ganin rubutun, rufin kwanon azuzuwan kuwa, shekaru kusan barkatai da isk ya dauke su y bar su hangham, sama a bude, shiysa duk yadda aka dauko karatu da zarar aka ga alamun hadari, dole a salami yara, head master ba office, takardunsa a waje suke gaba daya kan wani teburi, duka azuzuwannan malami biyu kadai ke karantar da su. Allah ya kawo mana mafita. Suka nemi wuri a tsakiyar makarantar suka kwanta, sai zabgar fira suke yi cikin farin ciki d nishadi, inda suke tsokanar juna kan abubuwa da suka gudana a wannan jejin da suka baro, haka suka ci gaba da fira har inda kunnuwansu suka jiyo musu kiran sallar fari, wannan ya ba su damar halara zuwa inda suka jiyo kiran, ai ko nan suka yi kicibis da ladan, bayan ya kammala kiran sallansa, Ameer ya yi sallama da shi, sai ya yi masa bayanin abinda ya faru d su tun daga farko har karshe, cikin suri ladan ya koma da su gida inda su Fate suka shiga gidan ya gabatar da su wurin matansa, su Abdool kuwa suka dawo masallci domin gabatar da sallah. Suka yi alwla daga gidan ladan sai suka wuce, bayan an ida sallah, mutane sun fara watsewa, ladan ya gurfan gaban mai unguwa ya rada masa wani zance, nan ya waigo ya kalli gefen da su Ameer suke bayan ladan ya nuna masa su ta hanyar ishara da hannu. Zuwa wani lokaci mai unguwa ya fice daga masallacin ladan ya zo ya ce da su Ameer ku zo mu tafi, suka bi ta bayanshi har zuwa gidanshi, inda suka zauna, har zuwa fitowar rana, bayan sun karya kumallo da kunu mai zafi sosai, ladan ya jagorance su, su duka hudu ya zuwa gidan mai unguwa.
A kan hanyarsu ta zuwa ne Aseeya ke ba su Abdul labarin yadda aka yi musu taryar kirki a cikin gida, har da dariyarta wurin gaya musu yadda matan suka dinga kyamar Fate da suka ji ba musulma ba ce. Suka dauke da dariya gaba daya.
Isarsu gidan mai unguwa, suka tarar da fada ta kankama, suka fadi suka yi gaisuwa, mai unguwa ya umarci ladan da ya gabatar da bakin da yake tafe da su, nan ya gabata ya fadi duk abinda ya sani game da su, nan fada ta kicime da surutai cikin mamaki da ta’ajjibi. Mai unguwa ya yi gyaran murya, sai ya soma, “ba shakka a tarihi ba wanda aka taba jin ya shiga wannan jejin kuma ya fito da rayuwarsa, sabod haka fitowar wadannan samarin daga wannan jejin yana kokarin nuna muna wani abu ne, akwai wadanda ubangiji yake so su rayu a cikinsu domin mutane su amfana da rayukansu, akwai wadanda kila ubangiji ya bar su ne domin su gyara wasu kura kurai na rayukansu, mu kuma inaso mu dage da addu’ah mu kuma san cewa ubangiji shi yake da mulki cikakke wanaa ba zai taba gushewa ba, ina magatakarda? Inaso ka sa a buga labarin wadannan yaran a ajiye shi a tarihin wnnan garin, kai kuma ladan, tunda ta hannunka suka zo, ya kamata ka iyar da ladarka, inaso ka je da su ka dora su kan mota domin su koma gidajensu”
Ameer ya soma “ranka ya dade, mun gode da wanan tausayawa da muka samu daga gareka, ba shakka kai shugaba ne wanda ya kamata a duba halayyansa ayi kwaikwaya, zancen komawarmu gida, gaskiya ni tunda har na karaso ta nan, ba zan koma gida ba, abinda nazo yi shi zan karasa Kamba nayi, dama zamana marubuci na shiryawa irin wadannan kalubalen, ina neman alfarmar ranka ya dade da ya bani damaa na wuce zuwa Kamba.”
Cike da mamki, mai unguwa ya kalle shi, si kuma ya mayar a hankalinsa ya zuwa ga sauran abokanin Ameer, sai ya ce da su, “tau kun ji abinda abokin tafiyarku ya ce, me ye ra’ayinku?”
Gaba daya suka nuna suma Kamba za su karasa. Inda Fate ta dora da cewa; “ai ko da sun aminta su koma ni dole na karasa domin na gyara barnar da na yi shekaru ina tafkawa” fadar haka, wani daga cikin fada ya ce, “assha yarinya, mai martaba yana saurarenki” “na kasance mabiyiya addinin kiristanci, munada kungiya da ke shiga kauyuka suna jan ra’ayoyin mutane ganin su kauyawa ne kuma ba sa da ilimi, sai muyi amfani da kyaututuka da kuma ilimin da muke a da shi mu ja hankulansu zuwa namu addini, nasan munyi haka a kauyuka sun fi a kirga, shi ne nake so yanzu a aka tura ni a wani kauyen DOLE KAINA naje a kauyen na gyara wannan barnar”
Gaba daya ‘yan fada suka dauka lokaci daya, “la ilaha illallahu,Muhammadurrasulullahi! Har yanzu wannan danyen aiki yana gudana a wannan kasa ta mu? Lallai zama bai same mu ba, ya kamata maluma ku bazamaa cikin kauyuka ku koyar da addini, ba wai ku zauna a birni ba kuna fadar abinda kuke so domin ku tara mabiya ba……” nan dai mai unguwa ya ja hankulan malamansa sosai, sai ya aika da azo masa da kudi da zai basu domin suyi kudin mota da su.
Wannan na nuna Fate ta musulunta ke nan?
Me zai faru?
DR. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
2⃣9⃣
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
08034840276
*Quote of the day*
_you laugh at me because am different, and I laugh at you because you are all the same_
*Shafin masoya*
_SAUDAT ABDULLAHI ZARIA_ (SAJ)
_BILKISU ALIYU NA YELWA_
_HAFSAT IDRIS_ FULLO
_MISS UMMI_ ABOKIYAR FDANA
_FATEEMAH ZARAH_ MAISON USTAZIYA
_DR. ZAINAB_ ALLAH YA BADA ZAMAN LAFIYA
_IHSAN AHMAD_ AISHA SARKIN RAWA
_BABY_
_SHAMSUDDEEN USMAN_
_ELSANITCS BICHI_
_MARYAM MK_
_HAFSINAT_ SAI MUN ZO ZIYARA A INDIA
_MATAN SHEHI_
_SHEMER QUEEN_
Nan suka koma gaba daya gidan ladan domin su kara kimtsawa, bayan mai unguwa ya hada su da goma ta arziki. Isar su bakin gida wanda rabin ginin gidan, duka ‘Darni’ ne, (inda aka yi amfani da kara musamman na gero aka zagaye Katanga), sai Ladan ya umrce su da su dan jira shi a zaure, ya shiga sai ya fito masu da tabarma, ya ce su jira a dauko musu ruwa daga rijiya domin su tsaftace jikinsu sai su je su hau mota su tafi.
Sai a lokacin suka sami duban yadda jikinsu yake, ita dai Aseeya, sanye take da wani skirt na atamfa mai ratsin shudi da fari-fari sai bakar kala da akayi surki da ita kadan, irin dinkinnnan ne na zamani amma bai kameta sosai ba, shi ya bata damar yin gudu yadda ya kamata da fadi tashin *BAKIN JEJI*, amma hakan bai hanawa skirt din barkewa (yagewa) ba ta gefen gugunta, wanda whight skirt da ke cikin jikinta ya hana aga bayyanar fatar jikin nata, haka farin skirt din yayi dawal-dawal kamar abin da aka fiddo daga bolar gawayi, saman jikinta kuwa rigar skirt din ce, wacce ta sha ado da style na dinki gwanin sha’awa, amma haka ita ma rigar ta yage sosai, da yake lokacin sanyi ne ta saka wata English riga daga kasa, shi ya hana bayyanar jikin nata, gashin kanta mai tsawo kuwa, haka ya yi butuk-butuk kamar wacce aka gino daga rami, kafafuwanta kuwa sunyi kutuf-kutuf kuma sun fashe har jini ya gaji da tsiyaya ya tsaya don kansa, sai kallon kanta take tana murmushin takaici, inda warin jikinta ke kokarin dukan dan siririn hancinnta, sai hawaye suka fito daga fararen idanuwanta. Ganin haka Ameer da ke zaune kan tabarma suna jirn a kawo musu ruwan wanka, ya kalleta cikin tausayi, ya ce; “me kuma kike yiwa kuka? Mu da ubangiji ya tsamo daga masifa ya kawo mu a tafarkin tsira, ai gode masa ya kamata kiyi, ba ki rafka kuka ba, balle ma ai ko a masifa muke dole ne mu gode Allah, ko da kuwa a bakin kura muke” “ba abinda kake tunani ya saka ni kuka ba, kawai na kalli yanayin jikina ne, ji yada na dawo a wulakance a wofance, ashe mutum komai gadararsa da tinkahonsa da zarar ya baro gida shi ba kowa ba ne, ni mutum ce mai ganin kowa ba komai ba a idanuwana, duk massifita, haka kuka hakur da ni kuka taimakaman, ka ga kuwa kunya kadai ta isa ta saka ni kuka’ bayan Ameer ya murmusa, sai ya kalleta, har yanzu kanta a sunkuye, hawaye kuwa, sai rigangar saukowa suke yi daga idanuwanta zuwa lallausan kumatunta. Ya ce; “gyara halayyarki ya kamata ki yi, ba kuka ba”
Numfashin da Abdul ya saka shi ya katse zancen da Ameer ke yi, inda suka mayar da hankulansu ya zuwa wurinshi, shima dai sai kallon jikinsa yake, sanye yake da English wears, bakin jeans ne sai wata long slieve shirt mai kalar maroon, inda rigar ta yi kaca-kaca da dauda kuma ga shi ta yage wurare da dama wurin gudun tsira da rayukansu, wando ya kwshi kasa da kura, amma ba su fito a sarari ba kasancewar baki ne, gaba daya ya fada har idanuwansa sun zazzaro, kafafuwansa kuwa kamar wanda ya buga wasan ball ba takalmi, ya jimu a kwaurinsa inda har yanzu jin bai tsaya ba.
Wannan shi ya baiwa Fate damar duba nata jikin, tana dubawa, ta ji Abdul ya ce, “lallai duniya makaranta ce, ko bakaso dole sai ka dauki darasi”
Da yake ita mun rigaya mun kawo kalar nata dressing a cen cikin littafi, guntun skirt nata ya yage, tun daga ‘yar tsagar da ake yi wa skirt tsakiya ta baya, har ya zuwa mzaunanta a yage yake, wanda kai tsaye kana ganin kamfanta, kasancewar rigartata iya cibiya take kuma arm less ce, idan mai karatu bai manta ba, bata kece ba amma dai ta yi dauda sosai. A jikinta ita ma ta ji rauni sosai.
Ameer kuwa, riga baka ce a jikinsa mai gajeren hannu, sai jeans shudi wanda ya kame jikinsa, ga wata suma da ya bari a kansa wacce tayi burum-burum ba kyan gani, wurare da dama a jikinsa alamun zubar jini ne musamma a hannyensa.
Nan dai suka roki juna gafara, musamman Aseeya daga masifa da ta dinga tsula musu, suka tabbatar da ita da cewa sun yafe mata, suma ta yafe su.
Ganin haka Fate ta kada baki ta ce, “yanzu idan inaso in amshi musulunci ina zanje na karba, kuma nawa zan biya, ko me zanbad”
Nan Aameer ya saki guntun murmushi, sai ya soma; “musulunci shigarsa kyauta ne malama Fate, ba abin da za ki biya, hasalima idan da hali, mu ya kamata mu baki tallafi domin ki ji kwarin guiwar shigarsa, duk da amfi so ki shiga saboda Allah”
“na yi wannan tambayar ne, saboda mu pastors namu suna gaya muna wai kafin mutum ya shiga musulunci sai ya kashe kudade da dama, ya kum sayawa liman rago da makamantansu”
“Kada ki raba dayan biyu, ko dai pastors naku sunmuku karya ne domin su hanaku karbar musulunci, ko kuma sun hadu da bata garin limamai da basusan addini ba, suke karbar kudi ko dabbobi domin shigar da mutane musulunci, wannan halayyar ta karbar dabbobi kafin a shiga musulunci, ita ta haddasa a kudu kafirci ya fi yawa, sai kiji ance a gida sai ambda katon rago kafin a saka mutum daya a musulunci, su kuwa ‘yan mission dag zowarsu sai suka fara raba musu kaya da kudi suna kiransu zuwa addinin kiristanci, kinga kuwa dole su karbi addinin kiristanci inda za a basu kudi da kaya ba musulunci ba inda ake kwace musu dukiya. Wnnan aikin wasu bata gari ne da sam basusan addini ba. Musulunci kyauta ake shigarsa, idan kin shirya karba sai ki fada domin na sanar da ke abinda za ki fada, da bubuwan da za ki kiyayewa.
Tayi dogon numfashi, sai ta kalli, Aseeya wacce dama idanuwanta a kanta suke, sai ta mata alama ta hanyar motsi da kanta, _just do it_ (kawai kiyi) sai ta mayar da hankalinta wurin Ameer, _am ready to accept the religion of Islam_ “Allahu Akbar!” in ji Abdul cikin farin ciki marar misaltuwa. Cikin sauri har da rawar jiki, Ameer ya ce, “duk abinda na fada sai ki fada” ta ce “okay” “ki ce; *ASH-HADU ALLA’ILHA ILLALLAHU, WA ASH-HADU ANNA MUHAMMADARRASULULLAHI* yana fada tana kuskure wurin fada, har sai da ta fada dai dai, sai ya sanar da ita ma’anar abinda ta fada, “abinda kika fada larabci ne, ma’anarsa, *na shaida ba bin bauta da gaskiya sai Allah, kuma na shaida Annabi Muhammadu manzonsa ne* kin aminta da haka?” ta girgiza kanta alamar ta aminta, sai ya ce da ita, “alhamdulillahi you are now a Muslim, bakida wasu zunubai a kanki, sai wadanda za ki aikata nan gaba, za ki kiyaye sallah, zan koyar da ke, haka za ki yi azumi idan lokacinsa ya zo, kafin nan zan koyar da ke wankan shiga musulunci yanzu”
Ya koyar da ita wankan shiga musulunci, ya kuma koyar da ita yadd za ta yi sallah da wasu muhimman abubuwa. Da aka kawo musu ruwa, sai suka fara shiga daya bayan daya suna yin wanka, da suka kammala gaba daya, Ladan ya rakayo su har bakin titi domin su taryi motar da za ta kai su grin *KAMBA*
Bayan Fate ta canja tufafin jikinta, kasncewar sun sanar da Ladan, sai aka kokarta akaa nemo mata tufafi da za taa suturta tsiraicinta.
Dr. ZAIN
*BAKIN JEJI.............*_hanyar kamba_
🐲
_THE DARK FOREST_
3⃣0⃣
_last page_
© *ZAINUDDEEN ZAIN*
® _pen writers association_
✍🏾
~dedicated to: Aseeya Abubakar Imam~
08034840276
*Quote of the day*
_i never admired anothers’s fortune so much that I became dissatisfied with my own_
Atamfar da ta saka ta yi ma ta kyawu sosai, musammaan ma da ta hada da mayafin da aka bata wanda ya rufe jikinta har kusa da kwabrinta, sai kallonta Aseeya ke yi cike da farin ciki, inda farin cikin ya kasa boyuwa har ta nuna a fili ta hanyar rungumeta, “me ya faru kin rungume ni?” “wallahi dadi na ji kin karbi musulunci, da farko na zata ba za ki karba ba, yadda na ga kina kokarin zakalo cewa a kawomaki hujjoji da za su gamsar da ke” “farin cikinne ya sa kika rungumo ni haka? Lallai musulmi kuna son junnku” “ai kuwa, dole ne wannan, domin manzon Allah ya sanar da mu cewa, Imaninmu ba zai cika ba, har sai mun sowa ‘yanuwanmu musulmi abinda muka sowa kawunanmu, haka, ya ce, shi musulmi a wurin musulmi, tamkar gini ne, sashensu shi ke karfafa sashe, haka yadda kikasan jiki haka musulmi yake.” “ban fahimta ba, kamar ya tamkar jiki?” “kinsan idan jiki ya ji ciwo, ba ind ka ji ciwon ne kadai zai ji radadi ba, radadin za ki ji shi ne gaba daya a sauran jikinnaki, haka abin yake” “na fahimta, yanzu dai kamar abinda ke faruwa wuraren da *boko haram* suke kai hari, sai mu musulmin da ke nan, mu dinga jin zafi muja kuma tausaya musu, har mu dinga yi musu addu’ah” “eh! Haka nake nufi”
Suka ci gaba da tafiya, Ladan ne a gaba tare da mazan, inda su kuma suke daga baya suna kwasar firarsu, har suka karaso daf da babban Titi, wanda zai sada ka da garin Kamba, a inda suke sun wuce garin Geza ne kadan, tsayuwarsu, sai Ameer ya ce da Ladan, “Baba, wanne gari ne daga baya”? “garin Geza ke nan” “Geza fa?” ya fada, yana zazzaro idanu.
“me ya faru ne yaro, naga hankalinka ya tashi ga shi yanayinka ya sauya, kasan garin ne”
“ai ko Baba, dole na san garin, daf da mu shigo garin ne, ‘yan fashi suka tare mu har muka shiga wannan jarabawa da ubangiji ya jefa mu. Nasan haka ne, domin lokacin da muka yo kusa da garin driver ya sanar da mu” “ka ko ga garin ba nisa sosai, ko na taka muku, ku gani ko motar taku tana kusa? Ko ba komai, za ku dauko wasu daga muhinmman kayanku” “ai ko Baba, ko da kowa bai koma ba, ni dole na je, rubuce-rubuce na na tsawon shekaru, suna cikin jaka ta, kuma akwai muhinmman takarduna ciki”
“Ameer kenan, ai ko daga garin Adamawa ne zuwa kebbi a kasa, zan tako domin kawai na dauki takarduna da ke cikin jakata” inji Aseeya, nan Ladan ya taka musu. Tinkis-tinkis, har suka zo daf da inda motarsu ta tsaya, abin mamaki, suka tarar da motarsu ba abinda ak taba a ciki, kawai dai an rufe gambun motar, suka bude gambun, kowa ya dauki kayansa, suka tsaya nan har sai da suka sami motar da za ta dauke su zuwa Kamba, suka yi sallama da Ladan suka wuce, shi kuwa ya tattako ya dawo garinsu.
Motar da suka tara, irin a kori kura ce, kuma aka yi daidai da ciki ya cika, sai suka hau ta baya, inda suka zama su shida, kasancewar da mutum biyu a ciki, tare da shanu guda biyu, a haka dai har suk karaso a tashar garin kamba, da aka saukar da su, sai Ameer ya ce da su, su zo su tafi wurin shugaban ‘yan UNION, da suka tafi, sai suka yi masa bayanin abinda ya faru da inda motar take, ya nuna musu ai sunyi neman driver din amma ba su sami wani labaari ba, sai jiya labari ya zo musu cewa an ga motarsa kan hanya, yanzunnan ma muka tura yara domin a dauko ta, kasancewar ba mukulli sai da muka tura sako a BIRNIN KEBBI a karbo dayan daga matarsa, shima ya yi musu goma ta arziki suka fito daga tashaar.
Suka yi bankwana da juna, har da musanyar lambobin waya, duk da a lokacin ba mai waya a hannunsa, kasancewar duka sun fadi wurin gudun ceton rayukansu, amma kowa ya tabbtar cewa zai yi welcome back na layinsa, kowa ya kama gabansa, domin ya gudanar da aikin da ke gbnsa.
Abdul yasa a rayuwarsa, wannan shi ne labari na farko da zai fara rubutu a kai, kuma zai kira labarin da *BAKIN JEJI..* _Hanyar Kamba_
Fate kuwa ta tafi da kudurin rusa kafircin da ta yi shekaru tana ginawa, haka Ameer da Aseeya kowa ya tafi tashi sabgar.
*ALHAMDULILLAHI*
Nan wannnan labarin ya zo karshe, ina mika godiya ga Allah ubangijin talikai da ya bani damar kammala wannan littafin, ina rokonsa da ya kalli wannan littafin ya bani lada da ke cikinsa, ni da duk wanda ya karanta ya amfana da abubuwan da ke ciki kura kurai da na gabtar a ciki ya yafe mani, kar ku manta masoyana, har yanzu kofa a bude take ga duk wanda zai yimin gyara ko bani shawara.
Zan yi amfani da wannan damar na mika godiya ga mahifiyata, ubangiji ya sa aljanna ce makomarta.
Mu hadu a littafina na gaba
*’YAN GUDUN HIJIRA*
_labarin sajida_
Kuka nake yi tun ban far rubutu kan wannan littfin ba, nagode da soyayyarku gare ni.
ZAINUDDEEN ZAIN
DR. ZAIN