BANAN Page 51-60 (The end)
.
Idan ran Alhaji yayi dubu ya bace kawai yana tunanin hukuncin da xai yankewa wannan mayen talakan karaf suhaim ya juyo dan ya nunama Alhaji ball yana fadin daddy kallo idan sane ya sauka akan Abbansa kawai sai ya fara Abba kaga nashiga jirgin daddy kaima ka shigo a firgice Alhaji ya kalla yaron sannan yace my boy waye Abban naka da hannu ya nuna masa Abba da yake tsaye kamar dutse kunya nadama mamakine suka rufe Alhaji sai yanxu ya lura da kamannin su amma sabi da girman kai irin na masu kudi kawai sai ya nade tabarmab kunya da hauka haba malam ai saikayi mun bayani ban san dankabane Abba ansamu shiga sai washe baki a haba ai ba komai kayi hakuri wlh suhaim bayaji gashi yaxo ya dameka fito mu tafi gida kayi hakuri Alhaji wani shu'umin murmushi yasaki sannan yace aa bakomai ai yaro nakowane amma anan kusa kuke da sauri Abba ya amsa da aa muna xama a dammar ne Alhaji yace ai bansan wajenba dayake nima jiya naxo daga nigeria amma ka shigo na sauke ka sai naga wajen arika xumunci ba musu Abba ya fada motor suka dau hanyan dammar a hanyane Alhaji ya tsaya ya kashema suhaim kudade masu yawan gaske Abba na gwada masa hanya har suka isa garin a kofar gida suka tsaya mutane sai kallon motor sukeyi wasu na lekowa ta katanga burinsu suga wanda xai fito daga motor karaf Abba ya fito tare da wani Alhaji suna magana cikin fara a Alhajin ya gama saukewa yaro tsarabanshi sannan yace to malam Adamu ni xan wuce masaukina amma bayan kwana biyu xan dawo Abba godiya yake xubawa yasa hannu a aljihu dubu goma ya bama Abba shi kuwa har kasa ya duka ya amsa yana xuba godiya. Saida aka xo sauke yaro dan Alhaji ya tafi nan ya suhaim yace bai san maganarba da ker ya yarda shima dan Alhaji yace masa anjima xasuje yawone da gudu ya fada gidan tana gaban madubi tana kwalliya ya fado yana fadi mommy kinga daddy mai jirgi ya sayamun sweet banxa tayi dashi dan tasan shi da xuba a haka Abba ya shigo da kaya niki niki yana ta washe baki tinda taga haka tasan anyi samuwa itama murna ta shigayi saida yasha ruwa sannan yake bata labarin sun kusa yin arxiki haba sai dariya da taji yau mijinta ya kama babban kifi sai yanka, shikuwa Alhaji yaron yashiga ransa kuma yanajin akwai karuwan da xaiyi dasu dan haka tun daga ranar kullum saiyaje ya dauka suhaim sun tafi yawo wata ranama har kwana yakeyi a wajen Alhaji sabi da kwadayi satin Alhaji hudu yayi shirin komawa kasar sa amma sai ya nema Abba ya bishi dan yasama masa abunyi ko yashawara basuyiba suka amince aikuwa suka kamo hanya xuwa kasa Nigeria kasan arxiki da wadata a Abuja suka sauka wata aljannar duniya suka yada xango tunda suka shiga tamfa tsetsen gidan Alhaji Abba yake wara ido yana kallon daula gidan baya faduwa ko ina xagaye yake da masu gadi amma ga mamakin Abba duk girman gidannan ba mace kuma ba iyalin Alhaji bangaran kwanan Alhaji Abba ke aiki shike kulawa da komai kuma bayan shi da alhaji ba wanda ke xuwa wajen rayuwa ta canxa ma su mommy dan abba na tura musu kudi sosai bayan na Abba Alhajima na musu sako cewa na suhaim ne su mommy sai ji da kai su masu kudi shekaran Abba daya a nigeria Alhaji ya basa bangare a gidansa cewa ya dauko su suhaim ba bata lokaci suka nado kaya sai nigeria mutane sai gulma suke wasu na fadin suway ta dace miji wasu kuma nacewa Adamu ya xama dan mafiya da ya saida shegiya ko ya sakota tana wani jida kai ita matan mai kudi haka dai suka gaji suka hakura da munafurcin su duniya sabuwa wajensu Abba dan gaba daya sun canxa Alhaji yana sakar musu shi kuwa suhaim makarantar yaran manya yake xuwa Abba kuwa ya xama jakan Alhaji duk inda xasu tare shine abokin shawaran Alhaji, Alhaji kuku mugune na karshe bashi da imani ko kadan kashe rai ba komai bane a wajenshi muddun xaka shiga harkanshi to lahira xatayi baki baya son gaskiya hakanne yasa yake son Abba dan duk abun dayace to daidaine ba musu yanxu Abba baya kaunar talaka sai masu kudi yana wulakanta kowa ya kora wanda yake so ta xauna Alhaji bai taba aureba sai matan banxa kalakala ya suhaim nada shekara goma mommy ta sama ciki gata kuwa ta gani a wajen Alhaji da Abba da cikinta ya isa haihuwa waje aka fita da ita dan haihuwa wata ranan juma'a ne suna xaune a fallo Alhaji ya kalla Abba nikuwa Adamu akwai wata alfarma da nake nema a wajenka nikuma daga naira daya xuwa milion hansin xan baka da duk abun da kake bukata jin makudan kudi tuni Abba yace haba yaya ai koma miye na mince wlh Alhaji yace nagode ba wata abunake soba face cikin jikin hajiya mace xata haifa to yarinyar nake son ka bani ita har abada ita xan aura itace rufiin asirina da naka dana arxikin mu dan haka kaje kayi shawara da hajiya duk yanda kukayi ka sanar mun amma kasani xan iyayin komai akan saata Abba da gaba daya ya rude sabid jin makudan kudi kai tsaye wajen mommy ya nufa koda ya labarta mata sai cewa tayi yo miye ai mun amince yau ko cewa yayi ka sakeni ya ura ai xamu amince bara yar da amu hafa washagari Abba ya sanar masa yaji dadi kuma sukayi yarjejeniya aka saka hanvnu akotu cewa ya basa.
.
Abba yasaka hannu cewa ya basa auren yarsa sannan ya mallaka masa ita na har abada shike da karfi akanta shima Alhajin ya saka hannu ya bama Abba kudi milion hamsin (jahilci)da comparny guda daya gida da motor nan rayuwa ta xama dai dai shima yanxu Abba na daya daga cikin masu arxiki ita kuma mommy bata da kawaye sai matan manya ta wani kara kyau bayan wata tarane aka haifeni iya gata nagani dan kayan babys kamar hauka Alhaji ya jido komai daga u.s ranar suna aka saka mun khadijat wanda ake kirana Banan tun ina karama nake ganin gata a wajen kowa mun shaku da ya suhaim sosai idan ina kuka xai goyani har nayi barci yana jss 3 ne wata rana yaje school bayan time yayine akaje dakko shi amma sai akace anxo an daukeshi abu kamar wasa ba aganshiba anyi nema har an gaji ba kara min kudi Alhaji ya kasheba wajen neman sa amma har yau ba bayani hakanne yasa duk suka dauka son duniya aka daura mun baxan taba mantawaba wata rana nayi wa Abba laifi lokain ina pri 4, nabi kawata gidansu akaita nemana sai da yanma na dawo Abba ya xaneni nayi kuka harda xaxxabi da Alhaji ya dawo nake gaya masa ya dinga fada harda marin Abba tun daga nan Abba ya fara tunanin anya kuwa basu taffa kuskureba amma lokaci ya kure masa sai dai hakuri ina secondry jss one muka hadu da Ahmad yaron mai aikin gidan su salma ne kawata babanta yake biya masa kudin makaranta mun shaku sosai yana jss 3 yanada kokari sosai a haukan mu wai muna soyayyane idan mun girma xamuyi aure Alhaji ya tafi sudan bayanan inata alla alla ya dawo nagaya masa ranar daya dawo muna wasa nace la daddy inbaka labari yace inajinki baby na ina dariya nagaya masa tashin hankaline ya bayyana a idonsa dama gasu jajaye amma yarinta sai nake cemasa maman ya Ahmad tana bashi danwake ya kawo mun daddy yaushe xaka kaini nagaisheta Abba na wajen amma baice kalaba murmushi Alhaji yayi yauma ai sai muje ko da murna na shirya muka kama hanya a kofar wani gida muka tsaya gidan talakawane sosai da xumudi na tashi xan fita amma ya kulle kofa da lock Abba na xaune a baya shima yana kallon ikon Allah wata motor ne ta parker a wajen wasu samarine suka fito rike da fetir da ashana gani nayi ya danna waya yace ku gama aikin nan da nan suka banka ma gidan wuta ya kama fal gaba daya Abba ya tsorata nikuwa kuka nakeyi ina yinkurin fita amma ina dariya yake sosai kin gani daga yau bake ba wani namiji ke hatta kawa na haramta miki xan kashe kowa akanki ke tawace nikadai gaba daya Abba ya rude dana sani nadama ya farayi amma ba amfani, tundaga ranar muka bar nigeria kuma ina tsoran shi sosai bana kula kowa sabida bana son ya kasheshi saida na kammala secondry nake gaya masa a nigeria xan yi karatu da ker ya yarda naxo kaduna su kuma suna kasar waje gida ya kama mun babba a G R A ya saka matakan tsaro sosai ina karatuna ne amma banda kawa ko aboki wata rana ina tafiya a motor na kawai saina bige wani tsoho makaho nan na kaishi hospital jikin sa yayi tsanani da ker ya far fado na dawo gida hankalina a tashe kullum sainaje na duba shi da jikinsa ya warke amma na barsa a hosptal dan bashi da kowa na nemo wata mata tana kula dashi ina biyanta matan nada kirki wani xuwan Alhaji nake sanar dashi nibana son masu kulawa dani idan ba hakaba xan sha guba in mutu jiki na rawa ya amince ya koresu amma xai rika xuwa koda yaushe na amince bayan sati biyu na nema gida na saya na kwaso su muka dawo shine na aura masa ita na kexama dasu Ammi da Abbi su kansu basu san niko wacece ba amma muna xaman amana munsaba da yan uwan Ammi yanxu abun dake damuna mungano Alhaji ne ya kashe ya suhaim kuma yanxu haka mommy da Abba suna nadaman rayuwarsu amma ba amfani baisan nanba da tuni ya halakasu maganar tafiya kuwa duk sanda su Abba suka xone sai na koma gidana sabida muxauna da su nan ta fashe da kuka yaxanyi da ruyuwata ina cikin hadari gashi na kamu da son ka wlh baxan iya rabuwa da kaiba ya xanyi shima hawaye yakeyi amman sai ya shiga lallashin ta kiyi hakuri ina tare dake har abada baxan barkiba duk rintsi duk wahala yanxu su abba na ina tace suna india amman idan na kammala karatu xasu dawo ayi bikin mu da Alhaji nan da nan gaban shi ya fadi amma sayyace mucigaba da rokon Allah idan kunyi waya dasu mommy suma surika addu a ta numfasa tace to Allah ya bamu sa a yace amin nan aka kira sallah duk suka mike xuwa yin sallah, bayan sun kammala suka gabatar da damuwansu wajen abbi shima yace xai tayasu da addu a washagari ta kira mommy sun dade suna waya tana bata labarin ya sadik da kuma su Abbi taji dadi da ta gane yanxu yarta tasamu mai tsayamata a karshe tace to Banan Allah yasa mu dace kuma ya raba mugu da na gari sannan ya gafarta mana ta amsa da amin mommy na saida safe mommy tace Allah ya kaimu lfy nan sukayi sallama kowa ya kwanta barci tundaga ranan soyayya suke ba kakkautawa idan baya gida to suna manne da waya ita kuwa Amina ta tasa shi gaba ita dai burinta ta mallaki Abubakar gaba daya ta rasa sukuni yau yana office a xaune kawai sayya mike ya nufa wajen sulaiman .
.
da sallama ya shiga office din daga ciki sulaiman ne xaune suna tattaunawa da Amina ganinsu hakan ya basa mamaki kuma hakan ya haifar masa da faduwar gaba komai yasa haka oho ganinshine sulaiman ya fara xabga masa kirari kaga maxa murmushi kawai yayi sannan ya ja kujera ya xauna ko kallo Amina bata isheshiba ganin hakanne ta rausayar da kai cike da kissa tana fadi ina yini oga Abubakar daker ya amsa da lafiya rannan ba annuri ta buda baki kenan xatayi magana wayansa ta dau kara ringing daya ya daga hello babyna am sorry kin kira ina sallah komai tace masa oho gani dai kawai sukayi ya mike haba princess kijira ni ganinan dawowa yanxu i luv u 2 ya kashe wayansa mikewa yayi ya duba sulaiman bara naje gida sulaiman ya kwashe da dariya hala gimbiya tayi kira murmushi yayi sannan ya amsa kasanta yanxu tayi fushi hukuma saida lallashi nan suka tafa ya fice iya bacin rai Amina ta shiga bata san sanda ta fashe da kukaba sulaiman ya dubeta lafiya ta banka masa harara ban saniba ta mike ta fice yaja tsaki banxa kin dade baki tafiba ya cigaba da aikinsa, shikuwa sadik koda ya isa har ta shirya shi kurum take jira fuskannan ta dau make up gonin sha awa yana shigowa ta mike tana bubbuga kafa kai ya sadik tun daxu nake jira har kasa make up dina ya goge Ammine ta bata amsa bana son sha shanci bayanxu kika kammala shiriba ko ruwa baishaba kin tareshi da korafi ta xumbura baki naji nida ba a so bara Abbina ya dawo saina gaya masa idan ya dawo ya dakeni duk aka kwashe da dariya yana dariya yace tuba nake tashi muje Ammi tace baxaka ci abinciba yace no bara na kai princess na dawo ta taba baki a dawo lafiya suka fice suna dariya a motor ta suka tafi amma shike tuki basu faka a ko inaba sai bakin wani dankareran shagon kayan ado na mata sayayya tayi sosai sannan suka fita suna tafiyane Abubakar ya lura da wata motor dake binsu a baya tun daga kantin kawai sai ya juya ya canxa hanya itama motor bayansu takebi gudu sukeyi ba sassautawa har saida suka bar cikin gari gaba daya ta gama tsorata a bakin wata bishiya suka tsaya saka makon buguwa da motor yayi gaba daya sun tsorata a firgece take tambaya lafiya ya buda baki kenan kawai sai ganin motoci guda hudu sun rufa musu baya kafin suyi wani yunkuri an gama xagayesu nan tsoro ya bayyana a idonta fadi take meke faruwane ya sadik su waye wadannan shima bashi da amsar tambayanta dan haka yayi shiru bindiga aka saka musu alaman su tafi kawai ba musu nan sukayi gaba ana binsu har shikin motor sukaja suka tafi anan akabar nata motor tafiya kawai sukeyi amma ba wanda yasan wajen tsayawa saida suka xo get din wani gida sannan suka shiga gidan gaba daya gidan mutane ne a xagaye ba hanyan fita a tsakar gidan akayi parking duk suka fito nan ma tasasu akayi har cikin gidan a tsakiyan falon suka tsaya mutanan suka juya suka tafi daga sama sukaji magana barka da xuwanku ma a bota soyayya duk gabansune ya fadi jin muryan amma sai suka dake sakkowa yayi kasa cike da isa yana wani takama kafin ya iso har gabansu gaba daya Banan ta gama rudewa ganin Alhaji a gabanta bata san sanda ta furta kalmar Daddy ya wanketa da mari a fusace ya fara magana nixaki cuta ki fara soyayya da wani bayan kin dade da sanin ke tawace kuma taura biyu baya taunuwa yau xan kashe masoyin naki ganin marin da Alhajin yayi mata ran sadik ya baci a fusace yace kai malam kai waye da xaka mareta jin wannan muryan ne gaban Alhaji ya fadi yana jin muryan a jikinshi nan ya waigo gareshi shima sadik gabansane ya hau dukan uku uku ganin Alhajin kuku kamar yasan wannan mutumin to a ina kuma baye bai ankaraba yaji saukan mari a xuciye ya daga hannu da niyar ramawa amma kawai sai Banan ta tare ya sadik ka barshi xai kasheka nikuma wlh baxan rayuba sai da kai wani mahaukacin dariya ya sheke dashi yaro yarone to baxaki iya rayuwaba idan na kashe shi to kenan ya xaki kasance idan na kashe wayannan muta nan ya danna wata mabudi kofar ta bude waxa tagani face mommy da Abbanta sunsha dauri mommy tayi kuka har ta gaji da gudu tanufa wajen kofan amma kafin ta isa wajen ya rufa kofan saidai kofan glass ne tana hangosu dukan kofan take tana kuka kar ka kashe su dan Allah nan ya kara kwashewa da dariya yace suma to wadannan fa nan ma ya kara danna wata kofar waxata gani face Ammi da Abbi suma sunsha dauri nan ta kara fashewa da kuka tana fadin kasakesu ba ruwanka dasu mai sukayi makane kaji tsoron Allah magananta ya tunxura Alhaji ya kara gabga mata wani marin saida ta fadi kasa yana fadin aina gaya miki xan kashe kowa akanki kekikaja nina kashe Ahmad da danginsa kuma na kashe suhaim sannan xan kashe wadannan duk kana na aureki xuciya ta diba sadik aikuwa ya kaima Alhaji naushi saida bakin ya fashe xafi ya saka Alhaji sakin ihu nan da nan aka xagayesu suka rirrikeshi Alhaji da baki ke xubda jini yace ku dakeshi sannan ku rufeshi a daya dakin ita kuma ku kaita sama itama ku rufeta sannan ya juya nan suka haushi da duka ita kuwa ihu ta fara tana kuka amma haka suka dagata sai sama da ita.
.
kai tsaye wani daki suka shiga da ita duk wani kayan jin dadi akwai a dakin ajeta sukayi sanan suka fita suka rufe kofan nan ta xube tana kuka mai tsuma xuciyan mai sauraro yau ina amfanin kwadayi gashi tanaji tana gani xata rasa kowa ya xatayi ya Allah ya kawo masu taimakonta daukar wayanta ta fara laluba amma kash ya fadi a waje hanyan shigowa wani sabon kuka ta shiga rerawa ba sassauci shikuwa saida sukayi masa lilis sannan suka daukeshi daya daga cikin dakunan suka wurgashi sannan suka rufe hankalin mommy da Abba ya kai matika wajen tashi kuka sukeyi sosai suna dana sani da bashi da rana shikuwa bangaran Abubakar ya daku dan gaba daya jikinshi ya sake kwance yake numfashi kawai yake iyayi can ya tuna da halin da suke ciki ko ina princess oho kai dole yasan abinyi baxai yuwuba baxai bari wannan tsohon axxalimin ya salwantar masa da babyn saba nan ya yunkura da niyar tashi amma ina ya kasa ya xaiyine ya ceci princess Allah ya kawo musu dauki amin, tsugune yake yana jiran fitowan shashashi amma shiru can ya bayyana yana xabga kirari ina masu neman duniya su bada lahira sun samu ina masu jiran shashashi shugaban yan iska ba tausayi ba tausayawa sannan ya sheke da wata sabuwan dariya sannan ya daure fuska kamar bashiba ya duba Alhajin kuku sannan yace maike tafe dakaine jiki na rawa Alhaji ya fara koro bayani watan boka nafara ganin canji a kasuwancina komai ya kwabe sannan batun ita khadijan tana tare da son wani yaro kuma aduk sanda na duba yaron fargaba na kamani shine nake son naji dalili nan boka shashashi ya kara shekewa da dariya sannan ya duba Alhaji akwai matsala kana cikin duhu gaban alhaji ya fadi nan boka ya fara bayani kamar haka muddun ka bari ta kubce maka to xaka rasa komai duk dukiyan da kake gani xai xama tarihi sannan muddum ka ta kura mata xa a samu matsala maganan yaro kuwa kaje ka biy biya rayuwanka ta baya ina ajiyan daka baro sa baya shike biybiyanka kuma duk abun da kake tunani xan gaya maka fa komai xakayi lokaci ya kure lokacinka kadanne talauci ya kusa lullubeka jin haka Alhaji ya dabarce ka taimaka mun boka ya sheke da dariya hanya dayane muna bukatan danka na jininka xamu sarrafa jininshi yau muke bukatansa idan ba hakaba xaka rasa komai nan da nan ran Alhaji ya gama baci amma boka ya xo masa da rainin hankali a baya shinefa yace karyayi aure bare ya haihu kuma muddun ya haihu talauci xai biyo baya dan haka bara ya kashe dan iska ya huta dariya bokan yakeyi sannan yace kayi kuskure baxan kasuba tunda baka da tunani xakaga karshenka butulu kawai bat ya bace nan tsoro ya rufeshi amma karfin hali yace baka isaba baxanyi talauciba har abada girgixa wajen ya fara nan aka fara xabga masa bulala ihu yake amma ba a barshiba haka aka dinga dukanshi har saida ya haukace yafita a guje amma yana ihu wayyo xasu kasheni yana yaga kayan jikinshi, xaune take tayi kukan har ta gaji idon nan ya kumbura abu biyu ya dameta mutuwan dan uwanta dana Ahmad ta tsana Alhaji kuma Allah ya saka mata shi kuma ya rasa abunyi sai ya tuna da wayanshi nan ya shiga lalubanta can ya tsinnceta ya danna number shek bugu daya ya dauka da sallama Abubakar ya labarta masa komai shek ya ji ba dadi ya tambayeshi yanxu suna ina yace baisaniba nan yace xa asan abunyi nan sukayi sallama number sulaiman ya kira shima ya gaya masa hankalin sa ya tashi ya sanar dashi cewa xaikai maganan wajen yan sanda kuma xasuje company mtn dan su taimaka musu su gane inda Alhaji ya adanasu haka kuwa akayi sun xauna cikin tashin hankali yan sanda suka iso gidan ansha artabu kafin daga bisani suka samu nasaran shiga gidan da ker aka samosu amma duk sun gala baita musamman Abubakar da yasha duka an fito dasu amma banda ita mommy ne tafara tambayan ina yata nan aka haura sama da ker aka gano dakin sannan aka balle kofan aka cetota tana chikin mawuyacin hali amma alhamdulillah tunda duk sun tsira gaba daya gidan Abbi suka nufa anata jajanta ma juna nan mommy suka nema gafara wajen yarsu nan aka yafa juna An gyarama su mommy bangare a gidan Abbi anan xasu xauna shikuma sadik xai koma gidan shek dan ya dawo Nigeria da iyalannshi gaba daya xumunci mai karfine ya wanxu a tsakanin gidajen biyu yayin da sadik suka kara baxa tabarman soyayyansu kowa yasani dan har shek ya xo nemawa dansa aure a wajen Abba kuma ya bashi dan har ankawo gaisuwa da kayan saka rana antsaida magana nan da wata shida idanta kammala karatu komai cikin kwanciyar hankali Abbama yanxu kaya ya xuba a shago yana saidawa kuma Allah ya saka albarka a kasuwanci ba laifi ana samun na rufa asiri yane Abba ya dawo musu da labarin gano Alhaji da jami an tsaro sukayi amma ya haukache kowa yace Allah ya rufa mana asiri nan aka watse kowa yaje ya kwanta suna wayane take sanar masa da haukan Alhaji yaji ba dadi sabida yanxu ya gano cewa Alhajine mahaifinsa na gaskiya ya ganene ta hanyan hoton mum dana dad dinsa duk xalincinsa a,mma baiji dadiba, *JAMSY % HAUWY* [11/7, 11:28 PM] +234 703 259 6585: *BANAN THE END* *EPISODE 111 to 113* Allah sarki abubakar na tausaya maka wannan jarabawa daka tsince kanka aciki ,,amma karka damu ance komi yayi tsanani maganinshi Allah,, bayan yagama cewa Alhajin kuku mahaifinsane kai tsaye police station suka dunguma da kyer akabari suka ga Alhaji ,,innalillahi wa inna illahirrajiun shine kalmar dake fita daga bakin kowannansu musamman abbakar wanda gaba daya hankalinsa idan yayi dubu yatashi ganin halin da mahaifinsa keciki.
.
gabadaya ya yayyage kayan jikinsa saiwani sambatu da ihu yake yana ta fadan maganganu wasu masu ma'ana wani kuma shirme,,,dagudu yaje ya rungume abbannashi yana kuka mai tsima zuciyan mai saurari mu kanmu saida muka zubda hawaye, why dad maiyasa kazabarwa kanka wannan kazamar rayuwar mutum dubu nawa kajefa acikin bakin ciki,,,nagodewa Allah dayayi gaggawar dauke mum dukda nasan rashin mum atare dani bakaramin jefani a bakin ciki bane,,amma hakan yafiyemin nayi imani har mum takoma ga Allah bata fatan tasake yin tozali da kai dalilin bakin cikin daka jefata aciki,,yau ina ranarka take wa gari ya waye ka kasance mai zalintar wasu kana tunani Allah zai barkane yau ga isharanan tun anan duniya kafara gani,,amma hakan bazai sa nagujekaba har duniya ta nade banida sama da kai koda kuwa kai kafi kowa zalinci bazan gusheba wajan roka maka gafarar ubangijiba nan kuka yaci karfinsa,,shikuwa gogannaka tureshi yayi yana wani sosha soshe da dararraku kai kaji shashasha waya gaya maka anama alhajin kuku wayau habawa wane uban kuturu ihuhuhu naci dubu sai ceto saini jikan shashashu hege kaci kutumar ubanka ihuhuhhu.duk wanda ke wajan saida yazubda hawaye bama kamar banan wacce tun zuwansu take aikin kuka ganin masoyinnata habibinta yana xubda hawaye,,dagudu tayi wajansa tariko shi tana cewa yaya sadiq karka damu Allah zai basa lafiya nayi maka alkawarin kasancewa da kai har karshen rayuwata am here for u banan takace har abada,,kallanta yayi u mean so ,,tadan kai mishi bugun wasa a kafada yes mana sai suka fashe da dariya,... Kai tsaye gidan mahaukata aka wuce da Alhajin kuka,,duk ranar wekend yana kaiwa mahaifin nashi visiting,,,haka bai gusheba wajan nemawa abbannasa gafara a wajan surukannasa,, alhamdulillah komi yayi daidai hankalin kowa a kwancene har gashi biki saura kwana biyu kowani bangare ana gudunar da hidindimune shek shiya zamaiwa abbakar waliyi haka tabangaran banan abbane yabada auranta,, rana bata karya saide uwar diya taji kunya a yaune dubbana jama'a suka sheida daurin auran masoyan biyu BANAN % ABUBAK anci ansha anyi haniam marian..muma munsheida dayake bama wuce biki musamman idan batu na rengem ne,,anan saide muce ubangiji yabawa amarya da angonta zaman lfy da hakuri mai jurewa yakore duk wata fitina a zamantakewar auransu ameen amarya da ango sai muce aci amarci lfy sai munzo daukar jariri hahahaha,, Tammattat bihamdulillah,,,dukka duka anan muka kawo muku karshen wannan littafinnamu wanda muka kirkira da basiranmu dafatan kun ilimantu da nishadantu da amfanuwa dashi.mungode sosai da bamu hadin kai dakukayi. Allah yabar kauna.