FAREEDA ABDALLAH*
*Shimfid'a*
Nigeria k'asa ce mai albarka, wacce Allah ya albarkace ta da tarin albarkatu, musamman irinna noma da kiwo, ga ma'adanai a k'ark'ashin k'asa, ga albarka ta man fetur da ake hak'owa a ko wane lokaci.
Amma mutanen cikinta musamman 'yan siyasan zamani, sun kafa mata mummunar tarihi, musamman na cin hanci da rashawa, da k'wace, da zamba cikin aminci, ga k'yashi da hassada da ya yiwa al'ummar cikin k'asar katutu a zuciya.
Ga rashin samun shuwagabanni na gari da zasu tsaya tsayin daka su gyara k'asar yanda har zata kai tana gogayya da ko wacce k'asa a fadin duniya.
Amma fa dukda wannan mummunar tarihi nata haryau talakawan cikinta basu fidda tsammani ba, ako wane lokaci suna yiwa kansu kyakkyawar fatan Allah ya basu shuwagabanni na gari, wad'anda zasu tsaya su rungumi k'asar da hannu bibiyu, su share musu hawaye.
Wannan fata nasu gaba d'aya sun tattara sun d'orashi akan jam'iyyar DPP, mai alamar share hawaye, musamman ga d'an takarar shugabancin k'asarta, Alhaji Abdullahi mutumin kirki, wanda a tarihin siyasarsa ya sami kyakkyawar shaida, na jajurcewa akan gaskiya, da k'ok'arin kauda cin hanci da rashawa.
Shiyasa suka fito k'wansu da k'wark'watarsu, don sake sabunta katin za6unansu, kamar yanda gwamnatin kasar tayi umarni ga duk wanda ya kai shekara goma sha takwas, zuwa sama da haka.
Layi ne dod'ar a ko wace mazab'a, na maza daban na mata daban, dukda ranar da ake k'walawa hakan baisa sun gajiya ba, share gumi suke suna tsaye a layin, ba abinda yake tada su saidai idan an kira sallah, suje su sauke farali su dawo su ci gaba da tsayuwa.
A wannan lokacin tabbas sun jajurce, Chanjin suke buk'ata, sun gaji! sun gaji matuk'a gaya, addu'a suke ta ko wane fanni, da coci da masallaci, Allah ya dafa musu su sami Chanjin gwamnati mai albarka.
"Wash... Allah... Nah.."
Amatullahi da take tsaye a tsakiyar layin mata 'yan uwanta ta fad'i haka dak'yar, lokaci guda ta durk'ushe zuwa k"asa, tana cije baki, wata masokiya ce ta soke ta tun daga gadon bayanta har zuwa mararta.
"Ya dai Amatu? Ko haihuwar ce?"
Wacce take tsaye a bayanta ta tambayeta haka, fuskarta na bayyana tsananin tausayi, bayan ta dafa kafad'unta.
"Hadiza,.. Ji nake kamar bayana zai 6alle, kama ni mu shiga gidansu Aunty Lami inyi fitsari"
Ta fadi haka dak'yar, tana ciccije baki, alamun ita kad'ai tasan azabar da take ciki.
Nan take wasu mata suka taimaka wajen rike ta, aka shiga da ita gidan dake makwaftaka da gurin sabunta katin za6en.
Da shigarsu kuwa haihuwar ta taho gadan-gadan, ko kafin ma ayi yunkurin zuwa asibiti faya ta fashe, kan d'a ya kunno kai.
Nan take mata suka taimaka mata har ta haifo sankacecen yaronta namiji, jajir dashi, kamar an tsaga kara shi da mahaifinshi.
Cikin jinin Amatullahi ta rungume shi, sannan ta fashe da kuka, bayan ta tuna da Mahaifinshi.
"Yaro na ka fad'o duniya a lokacin k'unci da hargitsi, ga kuma damuwa da wahalhalu, mahaifinka yaci burin a haife ka ya jiyar dakai dad'i, amma Allah bai nufa ba, sakamakon wadannan azzaluman da suka yi garkuwa da shi, Ni Amatullahi naga ta kaina, naga mutuwa, ni kam me zance da wadannan azzaluman? Tsakaninmu da su sai sakayyar Allah..."
Fashewa da mahaukacin kuka ta sake yi sannan ta rungume yaron da yake ta callara kuka, tamkar ya fahimci me take cewa.
Matan da suke gurin kuwa sai share hawaye suke yi, cike da matsananciyar tausayin su.
Cikin kankanin lokaci aka gyara ta ita da jinjirin, sannan ta koma gurin katin za6en aka sabunta mata, bayan an d'aga mata k'afa saboda yanayin da take ciki na jego, sannan ta nufi gida.
*BABI NA DAYA*
Dukda girma da kayatuwar dakin taron, su goma sha biyu ne a ciki, suna zaune a rukuni guda.
Kallo daya za'a yiwa fuskokinsu a fahimci tsananin tashin hankali da damuwar da suke ciki, bayan hucin iskar AC, baka jin karar komai sai na gwama numfarfashin da suke yi cike da damuwa.
"Ba zai yiwa ba... Ba zai taba yiwuwa ba... Siyasar da muka dauki tsawon shekaru goma sha shida muna gina ta lokaci daya wani can ya rusa mana ita.. Wannan abu ne da bazai taba yiwuwa ba.
Mune Gangar jikin siyasar kasar nan, dan haka dole sai wanda muka so zai yi mulki a kasar nan, dole abi mu, dole abi duk abinda muke so, talakawa basu da yanda zasu yi damu a kasar nan, mune muke sawa ayi ko da ba'a so, kuma mune muke sakawa a bari ko da kuwa duk al'ummar kasarnan suna so"
Honorable Alhassan ne yake fadin haka cike da hargagi, muryarsa na bayyana tsantsar damuwar da zuciyarsa take ciki.
"Ka kwantar da hankalin ka Honorable Alhassan, kai matsalata da kai gajen hakuri.."
General Danladi ya fadi haka yana murmushi, tareda murza gashin bakinsa yana jujjuya kwala-kwalan idanunsa a kansu, kai kace babu wani abu da yake damunsa.
Zuru sukai mishi suna kallonshi, gaba daya sun zaku suji me zai fada, domin sun dade da sallama mishi, shi din kwararre ne a iya kulla tuggu da makirci, aduk lokacin da wani abu ya nemi kawo musu cikas a harkokin siyasarsu to shine mai kawo musu mafita, in anbi daga-daga na kurya kasha kashi.
"A wannan lokacin tabbas Alhaji Abdullahi mutumin kirki zaiyi mulkin kasar nan!!"
"Me ne..?!!!"
Suka hada baki gurin fadin haka a rude, tamkar basu fahimci me yake nufi ba, gaba- dayansu sun kwana da sanin cewa matukar Alhaji Abdullahi mai inkiya mutumin kirki ya samu nasarar darewa kujerar shugabancin kasarnan kashinsu ya bushe.
Ba ta abinda suke samu suke yi ba, ta abinda suka tara suke yi, sunsanshi da shegen bin kwakwkwafi, da son komai za'ayi ayi gaskiya, bayan ya toshe duk wani hanyar cuwa-cuwansu to abinda suka tara ma sai yayi musu binciken kwakwaf akan ya akai suka tara, gaba-daya busassun kashi ne dankare a duwawunsu.
Nan take suka fara tsiyayar da gumi, irinsu Honorable Alhassan kuwa tuni cikinsu ya fara murdawa.
"Alhaji Abdullahi zai mulki kasar nan a wannan lokacin tabbas! Domin Dodanniya ta tabbatar min da haka. Duk wanda ya nemi kawo cikas kuwa to za'a yi babu shi, ina nufin fa saidai uwarsa ta haifi wani"
General Danladi ya sake fadin haka yana mai basu tabbaci, a wannan lokacin mummunar fuskarsa a jagule, damalmale da matsananciyar damuwa.
"To Yanzu menene mafita?"
Sanata Ishaku ya tambayi haka da matsananciyar damuwa a fuskarsa.
"A wannan lokacin fa muna fuskantar barazana ta ko wane bangare, ga barazanar Alhaji Abdullahi, ga barazanar rushewar jam'iyyarmu mai alamar asusu, ga barazanar matasan nan marasa kunya, wadanda suka bullo ta ko wane fanni suna Jan hankalin mutane akan kar su sake yarda damu"
Inspector general na 'yan sanda Inuwa ne yake fadin haka.
Shiru suka yi na tsawon wasu dakiku, kowa yana tunanin mafitar da zata bulle dashi.
"Yauwa..! Ina da shawara"
Gaba daya suka zuba mishi ido suna saurarenshi
"Alhaji Abdullahi mutumin kirki a wannan lokacin mulki yake nema ido rufe, kuma shi mutum ne mai saurin yarda, tun kafin jam'iyyarmu mai alamar asusu ta kife damu ya kamata muyi gangamin komawa Jam'iyyarsu mai alamar share hawaye, muyi gangami mu goya mishi baya har ya cimma gaci.
Su kuwa talakawa sun riga sunyi amannar cewa tabbas idan ya hau zai share musu hawaye, kuma suna ganin duk wanda yake jam'iyyarsa mutumin kirki ne, da wannan damar zamuyi amfani mu koma kan kujerun mu, su talakawa sun dauki jam'iyyar DPP a matsayin CHANJI, mu kuma mun dauketa a matsayin DAMA.
Kai kuma Your Excellency ka tsaya a jam'iyyar OPP mai alamar asusu, ka tabbatar ka wawashe duk abinda yayi saura a lalitar kasar nan kafin lokacin fad'inka yayi.
Su kuma Matasan nan 'yan siyasa, da matasan Addini zamu dankwafar dasu a bai-bai, zamu rufe bakunansu ko da ta hanyar aurar musu da 'ya'yanmu ne..."
"Ina... Bazai yiwu ba General, bazai taba yiwuwa in aurar da diya ta ga wani banzan matashin d'an siyasa ba.
Muyi musu shigo-shigo ba zurfi kamar yanda muka saba, sai sun gama amincewa damu sai mu ninke su a bai-bai.
Su kuwa TALAKAWA.. Daman kaji ne, da mun watsa musu tsaba zasu fito su tsattsaga"
Wata muguwar dariya suka kwashe da ita gaba-dayansu, a zuciyarsu suna masu gamsuwa da shawarwarin da suka yi.
"DPP... CHANCE...! DPP... CHANCE...!! DPP... CHANCE...!!!"
Sannan suka daga kofunan lemu suka buga wa junansu suna fadin "cheers.."
Suka fara kwankwada suna kyakyata mahaukaciyar dariya.
[02/03 12:45 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!!*
*Fareedah Abdallah*
*2)*
Yanda yake ta kai-kawo a tsakiyar falon kamar mai yin safa da marwa shi ya k'ara bayyana tsananin tashin hankalin da yake ciki.
Babbar yatsarsa ya sanya ya sharce wata zazzafar gumi da take tsiyaya mishi a goshi, dukda sassanyar sanyin AC da ya wadaci lungu da sako na babbar falon.
A karo na barkatai ya sake warto d'aya daga cikin wayoyinshi da yai watsi dasu a kan d'aya daga cikin kujerun falon, wata lamba ya lalubo ya danna kira, sannan ya kara a kunnenshi, nan take kiran ya shiga, ya fara ringing alamun samun wanda yake nema a wayar.
Murmushi ya sake alamun fara samun kwanciyar hankali, karo na talatin da takwas kenan yana kiran lambar na'ura tana sanar dashi wayar a kashe take, sai a yanzu yayi nasara kiran ya shiga.
"Halllooooo..."
A ka furta daga can bangaren cikin muryar k'wayancewa.
"Hello... Hello... Killer kana jina...?"
Ya tambaya daga bangarensa muryarsa har tana hard'ewa tsabar damuwar da yake ciki.
Tsawon dakiku goma sannan aka amsa daga can bangaren
"Ina jinka Honorable.. Ya harkoki...?"
"Killer..? Kana ina ne?"
Ya sake tambaya ba tare da ya amsa tambayar da aka mishi ba.
"Ina rami Honorable.. Na nisance ka ne kamar yanda ka bukata.."
Aka sake amsawa da k'yar daga can bangaren, ana magana ana ciccijewa, alamun mai maganar a buge yake, mankas yayi da kayan maye da suke gusar da hankalin d'an Adam.
"Ka saurareni da kyau Killer, an samu matsala.
'Yan sanda sun samu nasarar kama Usher, bisa ga dukkan alamu kuma a shirye yake ya fad'i gaskiya, shiyasa nake so kabi duk hanyar da zaka bi ka kashe shi, Ka kashe shi Killer..! bana bukatar ya sake kwana guda a duniyar nan. Idan ka aikata hakan tabbas zaka dawo kan matsayin sa, sannan zan k'ara maka da kyautar naira miliyan goma.. Da dank'areriyar mota, kuma zan baka 'yanci fiye da yanda kake tsammani..."
'Kit' kiran ya katse ba tare da ya gama maganganunshi ba.
Wata wawuyar murmushi ya sake, domin yana da tabbacin Killer ya gama jin duk abinda yake muradi.
Hurgi yayi da wayar gefe d'aya ba tare da ya duba tsadarta ba, sannan yayi wata mugun sufa ya dira akan kujera yayi d'ai-d'ai, tunawa da yayi matsalarsa ta kusa zuwa k'arshe yasa shi barkewa da wata mahaukaciyar dariya.
Ya san Killer bazai ta6a bashi fad'uwa ba, domin ba wannan ne karo na farko da ya saka shi aiki mai mugun hatsari ba, kuma ya ci nasara, ba tare da yabar wata kafa da asirinsu zai iya tonuwa ba.
A can bangaren Killer kuwa kallo yabi wayar dashi, da ya fahimci ta mutu ne sanadiyyar rashin caji yasa ya aje ta gefe guda, wata wawuyar mik'a yayi yana jin tsananin farin ciki a zuciyarsa.
'K'as.. K'as.. K'us..' Karar da kasusuwan baya da na hannunshi suka bada kenan.
Ya dad'e yana jiran wannan ranar, domin ba tun yanzu ba yake tsananin jin haushin Usher, wanda daga zuwanshi gurin Honorable ya k'wace mishi muk'amin da ya shekara goma yana aiki a wulak'ance kafin ya samu.
Shegen yaro ne Usher, ga d'an banzan kwakwalwa da basira, shiyasa a cikin shekara d'aya da rabi ya zarce kowa a gurin Honorable Lado.
K'wafa yayi, sannan ya cije gefen bakinsa na dama, a zuciyarsa yake tanadin kalolin azabar da zai ganawa Usher kafin ya shek'a shi garin da ba'a dawowa.. Wata muguwar dariya mai barazanar fasa dodon kunne ya fashe da ita, tsawon mintuna uku yana k'yak'yatawa, sannan ya yunk'ura ya mike zaune, daga bisani ya mik'e ya fice daga Kogon dutsen, hannu biyu yasa ya kare ranar da ta haske mishi fuska, kwananshi biyu kenan yana cikin Kogon, ba abinda yake yi sai bankawa cikinshi hayak'i da kayan maye, ba sallah ba salati.
**** **** ****
Tun daga nesa rugugin jiniyar motocin 'yan sandan ya mamaye kan titin da zata sada mutum da asibitin Barau Dikko da ke cikin garin Kaduna.
'Yan jarida suna tsaye cirko-cirko suna jiran k'arasowar motocin, motoci hud'u ne na 'yan sandan, suna fakawa daya daga cikin 'yan sanda ya fito da sauri ya k'arasa ya bud'ewa Kwamishinan 'yan sandan K'ofa.
Yana sa kafarsa a waje cincirindon 'yan jarida suka yanyame shi tamkar tarin k'uda je kowa da irin tambayar da yake jefo masa.
"Yallabai wane bayani zaka yi mana akan wannan mai safarar miyagun k'wayoyin da kuka kama??"
Kusan dukkansu wannan tambayar suke ta maimaitawa suna binshi da sassarfa hannayensu rik'e da abin magana, a hannayen wasu kuma manyan wayoyi.
Su kuwa 'yan sanda sai ture su suke samarwa da kwamishina hanyar shiga cikin asibitin.
"Yallabai... Yallabai... Dan Allah ka bamu bayani ko da ba yawa Yallabai..."
Bai ko juyo ya kalle su ba har ya dangana da cikin asibitin, su kuma 'yan sanda suka kare k'ofar dan kar 'yan jarida su shiga, wasu 'yan sandan kuma suka bishi a baya da sassarfa.
Duk inda ya ratsa kallonshi ake yi, Dakakke kuma tsayayyen jarumin 'Dan sanda ne wanda kallon Idanunshi kad'ai ke kad'a hanjin 'yan ta'adda da masu aikata miyagun laifuka.
Yana isa cikin reception d'in asibitin yaja ya tsaya ya k'urawa makeken talabijin d'in da yake manne a jikin bango ido, yana saurarar labarun duniyar da ake karantawa a daidai wannan lokacin.
"An kama shararren mai saida miyagun k'wayoyin nan wanda aka fi sani da Usher, 'Yan sanda sunyi iya bakin kokarinsu sun sami nasarar kama mai saidawa mutane kwayoyin sun sakaye shi.
A inda sam bazai samu nasarar gudu ba balle har yayi nasarar tserar da rayuwarsa.
Usher mai safarar miyagun kwayoyi, a jiya ne dai aka samu nasarar damk'eshi bayan bata-kashin da ya gudana tsakaninsa da 'yan sanda.
Wanda a sanadin haka har suka harbeshi a kafa, a yanzu dai yana asibitin Barau Dikko ana jinyarsa, inda 'yan sanda suke jiran farfadowarsa dan su sami muhimmin bayanai daga bakinshi..."
Da sassarfa ya wuce kai tsaye zuwa 6oyayyen d'akin da aka kwantar da mai laifin ba tare da ya tsaya sauraren k'arashen labaran ba.
"Dan Allah ku kula dashi ina zuwa.."
Abinda likitan ya cewa 'yan sanda fiye da goma da suke tsaye cirko-cirko rike da makamai a k'ofar d'akin kenan.
Ganin k'arasowar Kwamishinan yasa likitan juyawa cikin d'akin suka rufa mishi baya.
Yana kwance tamkar matacce, an mak'ala mishi injin taimakawa gurin yin numfashi, ga k'afarshi guda nannad'e da bandeji, ba zaka taba tsammani yana numfashi ba sai ka ta6a kirjinsa daidai saitin zuciyarsa.
"Barka dai likita, ya jikin nasa?"
Abinda Kwamishinan ya fara tambayarsa kenan bayan sun isa babban ofishin likitan.
"Eh to da sauki dai, a ko wane lokaci daga yanzu zai iya farfad'owa. Bugun zuciyarsa yana tafiya yanda ya kamata"
Gyad'a kai yayi alamar gamsuwa, sannan ya fito daga cikin d'akin likitan yana biye dashi a baya
"Ka kula dashi, Inaso ka ci gaba da kulawa dashi, domin shi d'in da kake gani ba k'aramin mai hatsari bane, zan fad'awa jami'an mu su ci gaba da bada kulawa mai tsanani a kanshi, domin a sashin mu muna matukar neman bayani daga bakinshi.
'Usher' Fitinanne kuma hatsabibin mai safarar miyagun k'wayoyi, sau ashirin da tara muna harin kama shi amma sai ya samu hanyar tserewa, sai jiya Allah ya bamu sa'a a kanshi"
"An gama Yallabai"
Likitan ya amsa cike da gamsuwa, a zuciyarsa yana jinjina k'ok'ari da hazak'ar 'yan sandan, musamman ma Kwashina Sunusi Isa.
"Kana ji Jocob?"
Kwamishinan ya maida hankalinshi kan d'aya daga cikin 'yan sandan da suke tsaye a kusa dashi.
"Eh Yallabai"
Jocob d'in ya amsa da sauri.
"Ka kula dashi, ka kula da duk wani motsi nashi da shige da fice, karka kuskura ka bar kowa ya shiga gurinshi idan ba likita ba, idan nace kowa to ina nufin ko ma waye, komai girman matsayi da shahararsa"
Ya k'arasa maganar cikin sigar zazzafar gargad'i da Jan kunne.
"An gama Yallabai"
Ya amsa da hanzari, ya sara masa cike da
kwarewa.
Gyad'a kanshi yayi alamar gamsuwa ya nufi hanyar ficewa daga asibitin gaba-daya, duk inda ya wuce 'yan sanda ne suke sara masa sannan su bi shi a baya da sauri.
[04/03 10:10 PM] fareedah: *BARA A KUFAI*
*Fareedah ABDALLAH*
*3)*
Babu abinda yake tashi a cikin kangon sai hayak'in sigarin da suke ta bankawa cikin su, idanuwansu sunyi jajur! babu ko kyan gani, baki da hancinsu hayaki kawai yake fitarwa. Sai zare ido suke kamar zasu ci babu!
"Kai Baba ya ne...? Tuntuni wannan gayen sai 6ata mana time yake yi...? Ko da sauran bayani ne a gurinka ka bani in afa? Na k'osa kwarai inji ni ina lilawa a duniyar cikin gajimare"
Daya daga cikinsu ya tambayi dayan yana zare ido.
"Ba wani bayani Baba.. K'ark'af nake tun jiya.. Shegiyar abar ce indai ba kawo mana ita yayi ba bamu cika samunta da sauk'i ba. K'ara ta6o mana shi a waya muji miye bayani"
Ya amsa da muryar k'wayancewa, yana hurga idanu lungu da sak'o a cikin kangon ko zai tsinci Tsohuwar ajiya.
Ringing d'in wayar daya daga cikinsu ne ya dauke musu hankali daga surutun da suke yi, hannu ya zura a aljihu ya dauko wayar, karamar Nokia ce, an daure sama da k'asanta da robali
"Ka ga 'Dan shegiyar ce yake kira na"
Ya fad'a yana kallon d'ayan sannan ya danna ma6allin amsa kiran, ya kara a kunnenshi.
"Kb kuna ina ne? Kuzo yanzun nan Honorable ya bada kayan aiki, tun d'azu nake neman ka a waya bai shiga ba..."
"Wayyihuhuhu...!! Aha! Aha!! Figo, ga mu nan fasowa, Allah ya taimaki mai taimako Honorable, sai yayi ko garin ba kowa.."
Katse wayar akai daga can 6angaren ba tare da an jira ya k'arasa kirari da sowar murnar da yake yi ba.
Nan take yaja hannun abokin sa Muver suka nufi mahad'arsu inda suke had'uwa idan irin wannan ta taso musu.
Matasa ne su goma sha biyu, wad'anda da ace sunyi amfani da damarsu da yanzu suna makaranta, ko kuma suna gurin koyon sana'o'insu.
Amma ga sunan a zube, babu abinda suke tsinanawa kansu ballantana su amfanar da al'ummar k'asar su, a kullum saidai su sami kayan maye su sha su bugu, sannan su ci gaba da jagaliyar siyasa.
Manyan kwalaye uku ne a gaban shugabansu Figo, shak'e suke da kayayyakin maye, masu matuk'ar illah ga lafiyar d'an Adam, a gefe guda kuma wani kwalin ne a ajiye, shi kuma cike yake da bandir bandir na foster, sai kuma Bana manya manya har guda goma acan gefe guda, masu d'auke da maka-makan hotunan Honorable Habu, dan takarar gwamnan jihar Kaduna, a jam'iyyar DPP, mai alamar share hawaye.
Figo ne ya fara koro musu bayani, da yake shine kaman shugaba a cikinsu, duk wani aiki ta hannunshi suke samu.
"Honorable ya bada kayan aiki, sannan kuma ya k'ara mana da kudi masu yawa har naira dubu uku..."
"Yeeee.... Sai Honorable ko garin ba kowa"
Gaba d'ayansu suka fashe da ihun murna, suna fad'in haka, fuskokinsu yalwace da matsananciyar fara'a da annashuwa.
Saida ya dakata suka gama shewa da hargowar su sannan ya ci gaba da cewa
"Yace mu fara ta6awa, wannan somin ta6i ne, akwai lagwada da romon da zamu shar6a idan za6e ya matso.
Bukatar shi yau mubi dare mu manna wad'annan fastocin nashi aduk wani lungu da sak'o na cikin garin nan, su kuma wad'annan Banan ya bada sunayen manyan guraren da zamu kakkafa su, dan haka daga yanzu zuwa dare mu ci gaba da holewa, zuwa sha biyu zamu fara aiki"
Wani ihun suka k'ara fashewa dashi suna tafawa a tsakaninsu.
Shi kuwa Figo nan take ya farke kwalayen ya fara rarraba musu kayan mayen, yana k'ara musu da sabuwar d'ari biyu mik'akkiya
"Sai Oga... Allah ya taya ma Honorable"
Abinda kowa yake fad'a kenan idan ya amshi kayan mayen da kud'in, fuskarsu na bayyana zallar farin cikin da zukatansu suke ciki.
Wata kwalba guda ce ta rage Figo ya d'ago yana tambayar wa zai ba, da sauri Kb yakai hannu, Tsula ma yakai hannu zai fisge, nan take kwalbar ta fadi ta fashe.
A zuciye Kb ya d'ago yana watsa masa wata muguwar harara, daman basa shiri, akan dole suke zaune guri daya.
"Kai dan uwar babanka saboda ba'kinciki zan amsa shine ka buge ka fasa? Saboda tsohuwa bata baka tarbiyya ba ko..?"
Ai kafin ya rufe baki Tsula ya cakume shi da dambe, nan take suka fara bud'awa, suna ba hammata iska kamar zasu kashe juna, dambe suke da dukkanin k'arfinsu, kowa yana neman makasan d'an uwansa.
Nan take sauran suka fara sowwa da ihu suna musu wak'a had'e da tafi duk lokaci d'aya.
"Ku chasu arna ku chasu... Ku chasu ba mai raba ku..."
Ganin Tsula ya zaro wuk'a yana k'ok'arin ya soki Kb yasa Figo ya shiga tsakiyarsu yana antaya musu maguzawan zagi, Muver ma ya rike Kb yana fad"in
"Yawa kake abokina... Ka share kawai... Zamu had'u dashi a k'ark'ashin kwata"
Da k'yar aka raba su kowa yana huci da maida numfashi, nan take Figo ya sallamesu da cewar kowa yaje yayi caji, su had'u da misalin k'arfe goma sha biyu na dare.
**** ****
Yara ne kyawawa farare tas! Mace da namiji, kai da ganinsu ba sai an fada maka tagwaye bane.
Suna cikin guje-gujensu a gurin wasansu suka jiyo horn din mota daga kofar gidan, ganin mai gadi ya wangale get din gidan an shigo da motar yasa suka fara ihu da hargowa suna fadin
"Oyoyo.. Daddy.. Oyoyo.. Daddy.."
Yana Fitowa daga cikin motar suka nufi gurinshi a guje, shima fuskarshi dauke da murmushi yake kallon yanda suke rige-rigen isowa gurinshi, suna karasowa ya hadasu ya daukesu duk su biyun, sannan ya rungumesu a kirjinsa yana juyi dasu a tsakar gidan, nan take suka fara kyalkyata dariya cike da murnar jin dadin dawowarsa.
Cikin gidan ya nufa dasu suna sa6e a kafadunshi, yana tambayar su ina Mominsu?
"Taya ciki, tace muje muyi waca kal mu dame ta, wai jata cilya maka delicious"
Yaron namiji wanda ga dukkan alamu shine babba ya amsa da haka, maganarsa cike da tsamin baki irinna yara.
"Daddy ina tsalaba ta?"
'Yar macen ta tambaya tana shafa suman kan mahaifinta.
"Tsarabarku na nan Ummita, na siyo muku da yawa har sai kun ture ke da Abee"
"Yeee... Godiya muke Daddy"
Suka amsa da sowar murna.
Da sallama a bakinshi ya sanya kafarshi cikin falon, daddad'an kamshin turaren wutan da ya bugi hancinshi yasa ya shaki iskar sosai sannan ya lumshe ido, yana budewa yayi arba da ita cikin kyakkyawan shiga tsaye a bangaren Dining table tana shirya abinci.
"Oyoyo Daddy.."
Ta fadi haka da tattausar muryarta, tana haskeshi da kyakkyawar murmushinta.
Martanin murmushinta ya mayar mata, sannan ya sauke su Ummita kasa, ya ci gaba da kallon yanda take karasowa gare shi cike da rangwada da rausaya, tamkar reshen bishiyar da iskar damina take kad'awa.
Tana karasowa gare shi a slow motion tayi masauki a kirjinsa, tsawon lokaci yana rungume da ita sannan ta zare jikinta a hankali, kan kujerun falon taja hannunsa ta zaunar dashi, shi kuma ya bita tamkar rakumi da akala.
Kasa ta tsuguna ta zare mishi takalman kafarsa, sannan ta zare mishi safa, ta mike cike da rausaya takai ma'ajiyarsu ta ajiye, sannan ta koma gareshi tana kara mishi barka da zuwa.
Lura da yayi su Abee sun koma gurin wasansu yasa ya jata kan cinyoyinshi ya zaunar da ita, sannan ya kwaye rigarta yasa kanshi daidai cikinta yana fadin
"Hi Sweet hearts na dawo, ya kake? Kwana uku ina missing dinka, harma dakyar nake iya barci saboda rashinka, oya fada min, kayi kewa ta?"
Kamar d'an dake cikin yasan me yake faruwa, take yayi motsi daga dama zuwa hagu.
Da murmushi ya dago kanshi yana kallonta, itama murmushin take zuciyarta dauke da zallar farinciki.
"Kinji Ardo ma yace yayi kewa ta, ke ma fada min yanda kika yi missing dina?"
Dariya tayi sannan ta hada bakinta da nashi, ta fara aika mishi wasu zafafan sakonni masu wuyar fassarawa, nan take ya cafke harshenta kamar mayunwacin zaki, dan man bakin da ta goga a la66anta saida ya tsotse shi tsab, kasancewarta ba ma'abociyar sanya jambaki ba.
Dakyar ta kwaci kanta tana maida numfashi, shagwabe fuska tayi, cikin muryar shagwaba tace
"Daddy kaga ka goge min kwalliya ta.."
Ta fada tana shafo la66anta, ta kwa6a fuskarta kamar zatai kuka.
Yatsarshi yasa yana zagaye dan kyakkyawan bakin nata dashi yace
"Baby indai wannan kwalliyar ne karki damu, muje yanzu in sake miki wata, har wanka ma zan sake miki kinji Baby na?"
"A'ah! Ni dai naki wayan!"
Ta fada tana make kafadarta, kamar wata karamar yarinya.
Dariya yayi, ita kam a hankali ta mike daga jikinsa, taja hannunsa tace
"Daddy muje kayi wanka saika ci abinci"
"Tam! An gama Babyna"
Dariya sukayi gaba-daya, sannan ya rike ta a gefen kafadunsa suka nufi dakinsa.
Ita ta tayashi ya rage kayan jikinsa, ta shiga cikin bayi ta hada mishi ruwan wankan, bayan ta zuba turarukan wanka kala-kala.
Kafin ya fito wanka ta nunke kayan da ya cire ta adana su inda ya dace, sannan ta fito mishi da kananan kaya na shan iska ta feshe su da turare.
Yana Fitowa ta amshi tawul din hannunshi tana taya shi goge ruwan jikinshi, ita ta goge shi tsaf sannan ta taya shi shiryawa.
[04/03 10:37 PM] fareedah: *BARA A KUFAI*
*Fareedah ABDALLAH*
*3)*
Babu abinda yake tashi a cikin kangon sai hayak'in sigarin da suke ta bankawa cikin su, idanuwansu sunyi jajur! babu ko kyan gani, baki da hancinsu hayaki kawai yake fitarwa. Sai zare ido suke kamar zasu ci babu!
"Kai Baba ya ne...? Tuntuni wannan gayen sai 6ata mana time yake yi...? Ko da sauran bayani ne a gurinka ka bani in afa? Na k'osa kwarai inji ni ina lilawa a duniyar cikin gajimare"
Daya daga cikinsu ya tambayi dayan yana zare ido.
"Ba wani bayani Baba.. K'ark'af nake tun jiya.. Shegiyar abar ce indai ba kawo mana ita yayi ba bamu cika samunta da sauk'i ba. K'ara ta6o mana shi a waya muji miye bayani"
Ya amsa da muryar k'wayancewa, yana hurga idanu lungu da sak'o a cikin kangon ko zai tsinci Tsohuwar ajiya.
Ringing d'in wayar daya daga cikinsu ne ya dauke musu hankali daga surutun da suke yi, hannu ya zura a aljihu ya dauko wayar, karamar Nokia ce, an daure sama da k'asanta da robali
"Ka ga 'Dan shegiyar ce yake kira na"
Ya fad'a yana kallon d'ayan sannan ya danna ma6allin amsa kiran, ya kara a kunnenshi.
"Kb kuna ina ne? Kuzo yanzun nan Honorable ya bada kayan aiki, tun d'azu nake neman ka a waya bai shiga ba..."
"Wayyihuhuhu...!! Aha! Aha!! Figo, ga mu nan fasowa, Allah ya taimaki mai taimako Honorable, sai yayi ko garin ba kowa.."
Katse wayar akai daga can 6angaren ba tare da an jira ya k'arasa kirari da sowar murnar da yake yi ba.
Nan take yaja hannun abokin sa Muver suka nufi mahad'arsu inda suke had'uwa idan irin wannan ta taso musu.
Matasa ne su goma sha biyu, wad'anda da ace sunyi amfani da damarsu da yanzu suna makaranta, ko kuma suna gurin koyon sana'o'insu.
Amma ga sunan a zube, babu abinda suke tsinanawa kansu ballantana su amfanar da al'ummar k'asar su, a kullum saidai su sami kayan maye su sha su bugu, sannan su ci gaba da jagaliyar siyasa.
Manyan kwalaye uku ne a gaban shugabansu Figo, shak'e suke da kayayyakin maye, masu matuk'ar illah ga lafiyar d'an Adam, a gefe guda kuma wani kwalin ne a ajiye, shi kuma cike yake da bandir bandir na foster, sai kuma Bana manya manya har guda goma acan gefe guda, masu d'auke da maka-makan hotunan Honorable Habu, dan takarar gwamnan jihar Kaduna, a jam'iyyar DPP, mai alamar share hawaye.
Figo ne ya fara koro musu bayani, da yake shine kaman shugaba a cikinsu, duk wani aiki ta hannunshi suke samu.
"Honorable ya bada kayan aiki, sannan kuma ya k'ara mana da kudi masu yawa har naira dubu uku..."
"Yeeee.... Sai Honorable ko garin ba kowa"
Gaba d'ayansu suka fashe da ihun murna, suna fad'in haka, fuskokinsu yalwace da matsananciyar fara'a da annashuwa.
Saida ya dakata suka gama shewa da hargowar su sannan ya ci gaba da cewa
"Yace mu fara ta6awa, wannan somin ta6i ne, akwai lagwada da romon da zamu shar6a idan za6e ya matso.
Bukatar shi yau mubi dare mu manna wad'annan fastocin nashi aduk wani lungu da sak'o na cikin garin nan, su kuma wad'annan Banan ya bada sunayen manyan guraren da zamu kakkafa su, dan haka daga yanzu zuwa dare mu ci gaba da holewa, zuwa sha biyu zamu fara aiki"
Wani ihun suka k'ara fashewa dashi suna tafawa a tsakaninsu.
Shi kuwa Figo nan take ya farke kwalayen ya fara rarraba musu kayan mayen, yana k'ara musu da sabuwar d'ari biyu mik'akkiya
"Sai Oga... Allah ya taya ma Honorable"
Abinda kowa yake fad'a kenan idan ya amshi kayan mayen da kud'in, fuskarsu na bayyana zallar farin cikin da zukatansu suke ciki.
Wata kwalba guda ce ta rage Figo ya d'ago yana tambayar wa zai ba, da sauri Kb yakai hannu, Tsula ma yakai hannu zai fisge, nan take kwalbar ta fadi ta fashe.
A zuciye Kb ya d'ago yana watsa masa wata muguwar harara, daman basa shiri, akan dole suke zaune guri daya.
"Kai dan uwar babanka saboda ba'kinciki zan amsa shine ka buge ka fasa? Saboda tsohuwa bata baka tarbiyya ba ko..?"
Ai kafin ya rufe baki Tsula ya cakume shi da dambe, nan take suka fara bud'awa, suna ba hammata iska kamar zasu kashe juna, dambe suke da dukkanin k'arfinsu, kowa yana neman makasan d'an uwansa.
Nan take sauran suka fara sowwa da ihu suna musu wak'a had'e da tafi duk lokaci d'aya.
"Ku chasu arna ku chasu... Ku chasu ba mai raba ku..."
Ganin Tsula ya zaro wuk'a yana k'ok'arin ya soki Kb yasa Figo ya shiga tsakiyarsu yana antaya musu maguzawan zagi, Muver ma ya rike Kb yana fad"in
"Yawa kake abokina... Ka share kawai... Zamu had'u dashi a k'ark'ashin kwata"
Da k'yar aka raba su kowa yana huci da maida numfashi, nan take Figo ya sallamesu da cewar kowa yaje yayi caji, su had'u da misalin k'arfe goma sha biyu na dare.
**** ****
Yara ne kyawawa farare tas! Mace da namiji, kai da ganinsu ba sai an fada maka tagwaye bane.
Suna cikin guje-gujensu a gurin wasansu suka jiyo horn din mota daga kofar gidan, ganin mai gadi ya wangale get din gidan an shigo da motar yasa suka fara ihu da hargowa suna fadin
"Oyoyo.. Daddy.. Oyoyo.. Daddy.."
Yana Fitowa daga cikin motar suka nufi gurinshi a guje, shima fuskarshi dauke da murmushi yake kallon yanda suke rige-rigen isowa gurinshi, suna karasowa ya hadasu ya daukesu duk su biyun, sannan ya rungumesu a kirjinsa yana juyi dasu a tsakar gidan, nan take suka fara kyalkyata dariya cike da murnar jin dadin dawowarsa.
Cikin gidan ya nufa dasu suna sa6e a kafadunshi, yana tambayar su ina Mominsu?
"Taya ciki, tace muje muyi waca kal mu dame ta, wai jata cilya maka delicious"
Yaron namiji wanda ga dukkan alamu shine babba ya amsa da haka, maganarsa cike da tsamin baki irinna yara.
"Daddy ina tsalaba ta?"
'Yar macen ta tambaya tana shafa suman kan mahaifinta.
"Tsarabarku na nan Ummita, na siyo muku da yawa har sai kun ture ke da Abee"
"Yeee... Godiya muke Daddy"
Suka amsa da sowar murna.
Da sallama a bakinshi ya sanya kafarshi cikin falon, daddad'an kamshin turaren wutan da ya bugi hancinshi yasa ya shaki iskar sosai sannan ya lumshe ido, yana budewa yayi arba da ita cikin kyakkyawan shiga tsaye a bangaren Dining table tana shirya abinci.
"Oyoyo Daddy.."
Ta fadi haka da tattausar muryarta, tana haskeshi da kyakkyawar murmushinta.
Martanin murmushinta ya mayar mata, sannan ya sauke su Ummita kasa, ya ci gaba da kallon yanda take karasowa gare shi cike da rangwada da rausaya, tamkar reshen bishiyar da iskar damina take kad'awa.
Tana karasowa gare shi a slow motion tayi masauki a kirjinsa, tsawon lokaci yana rungume da ita sannan ta zare jikinta a hankali, kan kujerun falon taja hannunsa ta zaunar dashi, shi kuma ya bita tamkar rakumi da akala.
Kasa ta tsuguna ta zare mishi takalman kafarsa, sannan ta zare mishi safa, ta mike cike da rausaya takai ma'ajiyarsu ta ajiye, sannan ta koma gareshi tana kara mishi barka da zuwa.
Lura da yayi su Abee sun koma gurin wasansu yasa ya jata kan cinyoyinshi ya zaunar da ita, sannan ya kwaye rigarta yasa kanshi daidai cikinta yana fadin
"Hi Sweet hearts na dawo, ya kake? Kwana uku ina missing dinka, harma dakyar nake iya barci saboda rashinka, oya fada min, kayi kewa ta?"
Kamar d'an dake cikin yasan me yake faruwa, take yayi motsi daga dama zuwa hagu.
Da murmushi ya dago kanshi yana kallonta, itama murmushin take zuciyarta dauke da zallar farinciki.
"Kinji Ardo ma yace yayi kewa ta, ke ma fada min yanda kika yi missing dina?"
Dariya tayi sannan ta hada bakinta da nashi, ta fara aika mishi wasu zafafan sakonni masu wuyar fassarawa, nan take ya cafke harshenta kamar mayunwacin zaki, dan man bakin da ta goga a la66anta saida ya tsotse shi tsab, kasancewarta ba ma'abociyar sanya jambaki ba.
Dakyar ta kwaci kanta tana maida numfashi, shagwabe fuska tayi, cikin muryar shagwaba tace
"Daddy kaga ka goge min kwalliya ta.."
Ta fada tana shafo la66anta, ta kwa6a fuskarta kamar zatai kuka.
Yatsarshi yasa yana zagaye dan kyakkyawan bakin nata dashi yace
"Baby indai wannan kwalliyar ne karki damu, muje yanzu in sake miki wata, har wanka ma zan sake miki kinji Baby na?"
"A'ah! Ni dai naki wayan!"
Ta fada tana make kafadarta, kamar wata karamar yarinya.
Dariya yayi, ita kam a hankali ta mike daga jikinsa, taja hannunsa tace
"Daddy muje kayi wanka saika ci abinci"
"Tam! An gama Babyna"
Dariya sukayi gaba-daya, sannan ya rike ta a gefen kafadunsa suka nufi dakinsa.
Ita ta tayashi ya rage kayan jikinsa, ta shiga cikin bayi ta hada mishi ruwan wankan, bayan ta zuba turarukan wanka kala-kala.
Kafin ya fito wanka ta nunke kayan da ya cire ta adana su inda ya dace, sannan ta fito mishi da kananan kaya na shan iska ta feshe su da turare.
Yana Fitowa ta amshi tawul din hannunshi tana taya shi goge ruwan jikinshi, ita ta goge shi tsaf sannan ta taya shi shiryawa.
[05/03 11:36 PM] fareedah: *BARA A KUFAI*
*Fareedah Abdallah*
*4)*
"Kunyi waya da Aunty Yasmin kuwa? Tun safe take ta damuna da kira, wai ta kasa samunki a waya, kewarsu Abee ya dame ta"
Ya tambayeta haka yana rike da hannunta, lokacin da suka nufi falo.
"Eh munyi waya da ita, har ma sun gaisa da su Ummitan.
Ai ta fada min zuwa sati na sama zasu dawo"
"Eh haka tace min. Allah ya dawo dasu lafiya"
"Ameen"
Ta amsa kai tsaye, da tattausan murmushi a fuskarta.
Kujerar dining ta janyo ta zaunar dashi, ta bude mishi kulolin abincin tana kara yalwata fuskarta da murmushi.
Daddad'an k'amshin kalolin girke-girken da suka bigi hancinshi yasa shi lumshe idanu, yaja numfashi ya shaki kamshin sosai. Ya bude idanu ya zuba a kanta yana jifanta da murmushi a daidai lokacin da ta fara zuba masa dambun shinkafan da ya wadatu da ganye da cabeji da busasshen kifi. Ko da gani a ido kawai zaiyi matukar dad'i.
Kasancewarsa ma'abocin son girke-girken gargajiya yasa aduk ranar girkinta tana k'ure basirarta gurin k'ayata kalolin girkin gargajiya dan ta burgeshi dashi.
A gefenshi ta zauna tana bashi a baki, idan yaci saiya karbi cokalin ya bata taci, suna ci suna had'awa da daddad'an kunun zak'in da ta had'a mishi, yana ta santi da yaba abincin, ita ko sai dariyar jin dadi take yi a haka har suka k'oshi.
Ta zuba mishi farfesun kayan ciki yaci kad'an yace ya koshi.
Hannunshi taja kamar rakumi da akala tayi mishi mazauni a kujerun falon, t.v ta kunna mishi ta koma ta gyara gurin da suka ci abincin tsaf!
Tana kwance tayi matashin kai da cinyarshi, shi kuma yana shafa gashin kanta da yake ta fidda daddad'an kamshi, suna kallon labaran duniya.
".... A jiya ne karkashin jagorancin Kwamishinan 'yan sandan jihar nan aka sami nasarar kama fitaccen mai safarar miyagun kwayoyin nan Usher.
Wanda yanzu haka yake kwance a asibitin Barau Dikko saboda harbin da akayi mishi a kafa a kokarinshi na tserewa..."
"Oh my god!!"
Abdul'ahad ya fadi haka bayan ya buga goshinshi da tafin hannu sannan ya kama kanshi da hannu biyu, fuskarsa na bayyana Tsananin damuwa.
Da mamaki take kallonshi, sannan ta yunkura ta mike zaune, ta dafa kafadarsa alamun son kwantar masa da hankali.
"Me ya faru Daddy?"
Ta tambayeshi da damuwa a fuskarta, ganin lokaci daya ya canza ya shiga yanayin damuwa.
"Baby ina takaicin yanda Kwamishina yake aiki tamkar wani sabon shiga a aikin dan sanda, shi a rayuwarshi bai iya boye abubuwa masu muhimmanci ba, wannan mai laifin da kike ji ba safarar miyagun kwayoyi kawai yake yi ba, yana cikin kungiyoyi da dama na masu garkuwa da mutane, kuma tsohon dan jagaliyar siyasa ne, idan zancen kama shi ya fito fili har 'yan jarida suka yayata to bai kamata asan asibitin da yake ba.
Domin shi din wasu daga cikin manya a kasarnan yake yiwa aiki, shiyasa munsha shirya zamu kai mishi hari amma sai ya kubce, ko yanzu da aka kama shi ina mai tabbatar miki zasu iya yin komai dan ganin asirinsu bai tonu ba, idan ta kama ma zasu iya saka wa a kashe shi"
Idanu ta zaro gaba daya, cike da tsoro da mamaki tace
"A kashe shi fa kace Daddy?"
Dan murmushin takaici yayi yace
"Kwarai kuwa Baby, ai kasar nan namu da kike gani sai addu'a, duk wasu manyan laifuka da ake yi da kike ji ko gani in kika bibiyi asalinsa akwai sa hannun wasu manyan kasarnan a ciki, shiyasa al'amarin sai ki ganshi a cukurkude, duk yanda za'a so kawo gyara daga kasa tunda can saman a gurbace suke gyaran bazai taba yiwuwa ba.
Shiyasa duk wani mai kishin kasarnan yake so Alhaji Abdullahi ya samu nasarar darewa kujerar shugabancin kasarnan, domin ko bai gyara komai ba to zai tsaida barnar, mu kuma fata muke 6arnar ta tsaya. Daga baya sai gyara ya biyo"
"Amma Daddy ina ga ai da sakawa zasu yi a sake shi, bawai su saka a kashe shi ba"
Ta fadi haka muryarta a sanyaye da tagumi hannu bibiyu.
"Kinsan waye Usher kuwa? To babban mai laifi ne, girman laifukansa ya kai duk wanda ya nemi saka baki a maganarshi to tabbas shima za'a diga masa alamar tambaya, shiyasa zasu saka a kashe shi tun kafin ma ya tona musu asiri"
"Tabdijam!! Allah sarki.."
"Tausayi?"
Ya tambayeta da mamaki a fuskarsa.
Daga kanta tayi alamar 'eh'
"Tausayin wa? Commissioner ko ni mataimakinsa?"
Hararar wasa tayi masa ta amsa da
"Tausayin iyayen da suka haifi Usher musamman mahaifiyarsa. Ya Allah ka shirya mana zuri'a"
"Ameen, addu'ar kenan Baby"
Hannunsa ya mika ya dauko wayarsa ya danna kira wa Kwamishinan, ringing uku a na hudu ya daga kiran.
"Hello Abdul'ahad"
Ya fada daga can bangaren.
"Yes sir!"
Ya amsa yana sara mishi tamkar yana gabanshi, bai jira cewarshi ba ya ci gaba da cewa
"Congratulation Sir"
Dariyar jin dadi yayi daga can bangaren, cike da alfahari ya amsa da
"Thank u Abdul, ka dawo kenan?"
"Eh sir, na dawo dazunnan, sai nake ganin news din a TV"
"Wallahi kuwa, a wannan lokacin dai mun samu nasarar damk'eshi bayan bata-kashin da muka yi dashi lokacin da yake kokarin gudawa"
"Congratulation once again Sir"
"Thank u"
"Amma Sir baka tunanin akwai matsala a inda aka ajiye shi? Kasan fa wadanda yake wa aiki suna iya turowa a kashe shi, don kar ya tona musu asiri..."
"No.. Hakan bazai taba yiwuwa ba, mun sanya tsaro mai tsanani a kanshi, kuma nayi umarnin kar abar kowa ya shiga gurinshi.
Amma tunda ka kawo wannan shawarar zuwa gobe sai mu canza mishi maboya"
"Ok Sir! Allah ya kaimu goben"
Da haka sukayi sallama ya katse wayar.
Kallonta yayi sukai murmushi gaba-daya, sannan ya mike ya fita harabar gidan ya shigo da Ummita da Abee, ganin magrib ta kawo jiki.
Wanka Momynsu Aysha tayi musu sannan ta sakawa Abee jallabiya tayi mishi alwala yabi babanshi zuwa masallaci, ita kuma sukayi nasu sallar a gida ita da Ummita.
(Iyalan Mataimakin Kwamishinan 'yan sanda kenan Abdul'ahad, jaruman Littafin A DALILIN 'DA NAMIJI na fareedah Abdallah)
[06/03 11:36 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!*
*Fareedah Abdallah*
*5)*
Hankalinshi a kwance ya bude kofar Ofis din, sannan ya sanya kanshi ciki, had'eda maida kofar ya rufe.
Yana juyowa yayi arba da hancin bindiga a saitin goshinshi, nan take ya fara rawar d'ari saboda tsabar tsorata da firgiji, idanunsa a warwaje, hanjin cikinsa suka taru suka dunkule waje guda kamar zai saki kashi a tsaye, dakyar yake jan numfashi dan razana, ya d'aga hannunsa duk biyu alamar mik'a wuya da sallamawa.
Gabjejen kato ne yayi saitin kwakwalwarshi da hancin bindiga, idanun k'aton jajur, babu alamun tausayawa ko kad'an! da alamun kiris yake jira ya sakar mishi harsashi a kanshi, da ya wulkita Idanunshi kan kujerar zamanshi na Ofis din kuwa wani gabjejen k'aton ya sake arba dashi a zaune yana wasa da hancin bindiga, ya d'aga kafafunshi duk biyu ya d'ora su akan teburin gaban kujerar, kayayyakin amfanin da suke kai kuwa anyi watsi da su a k'asan Ofis din.
"Kai likita.. Kar ka 6ata mana lokaci.. 'Dakin da aka kwantar da Usher zaka shigar dani, amma kafin sannan ina so ka kalli nan"
Nan take ya d'auko waya a aljihunsa, ya kunna mishi wani vidio sannan ya danna play.
Tsabar tsorata yasa Dr. Habeeb ya fara sakin fitsari a wando, iyalanshi ne gaba d'aya anyi musu daurin huhun-goro.
Ga wasu gabza-gabzan mutane nan zagaye dasu, kuma ko wannensu rike da bindiga, su kuwa iyalan nashi sai kuka suke yi, gwanin ban tausayi.
'Yar karamar yarinyarshi Zahra tana kwance magashiyan a kasa kamar bata da rai.
Matarshi abar kaunarshi daya daga cikinsu ya damk'i gashin kanta da k'arfi, magana take cikin mawuyacin hali da jin azabar dank'an da aka yiwa gashin ta.
"Dr.. ka taimake mu dan Allah... ka basu duk abinda suke nema su rabu damu... ka ceci rayuwarmu pls... kaga Zahra ma kamar ta mutu..."
Fuskar babban d'anshi Ahmad dan shekara goma sha uku aka hasko, yana cikin matukar galabaita, baya ko iya daga kanshi sama, an bank'reshi ta baya an d'aure hannuwanshi da igiyar daure shanu, gurin sashin d'aurin sai jini yake fitarwa.
"Zamu sake su idan muka samu nasarar fitar da Usher daga cikin asibitin nan! Dan haka minti goma ke gare ka ka samar mana da hanya mafi sauk'i na fitar dashi, ammafa idan har ka damu da iyalanka. Idan kuwa baka damu dasu ba.."
Ya d'aga kafad'unsa alamun rashin damuwa ya ci gaba da cewa
"Kana iya mana gardama ko kuma ka k'i nuna mana inda ka 6oye Usher. Kana so in fada maka irin kisan da zan maka?"
Wani kakkauran miyau ya hadiye 'muk'ut' jikinshi babu inda baya kad'awa, ya jik'e da gumi sharkaf. Idanunsa na zube akan wanda ke zaune kan kujerarshi hankali kwance, yana ci gaba da wasa da bakin bindigarsa.
*****
"Dr barka da dare, wanene wannan kuma?"
Inspecter Jocob ya tambayesu a lokacin da Dr Habeeb suke kokarin shiga d'akin da aka kwantar da Usher shi da wannan gabjejen mutumin, shima yana sanye da farar riga irinta likitoci.
Matuk'ar jarumta yayi gurin saisaita muryarshi bayan ya tuno halin da iyalansa suke ciki, sannan ya sanya murmushin yak'e a fuskarsa yace
"Oh! wannan? Dr. Mansur kenan, shi zai karbi aikin daren nan, shi yasa zan nuna mishi komai kafin in tafi gida"
"Ok no problem"
Ya amsa da haka sannan ya koma gurin zamansa ya ci gaba da game din da yake yi a wayarsa.
"Good job Dr."
Ya fad'i hakan bayan sun shiga d'akin muryarsa kasa-kasa.
Shammatar likitan yayi ya makure shi a bango ya toshe mishi baki, sannan ya shak'a mishi hodar iblis a hancinshi, yaja sosai kuwa saboda Tsananin tsoro, minti kadan ya tafi lauu... Ya rike Shi dan kar yayi faduwar da zai ankarar da 'yan sandan da suke waje abinda yake faruwa.
Windon d'akin ya duba sai yaga irin mai bud'ewar nan ne, wanda ake yinsu saboda tsaro, yanda ko da gobara ya kama daga ciki za'a iya bud'ewa a fice ta windo.
Da wannan damar yayi amfani ya fice da Usher dake kwance kamar matacce, bayan ya zazzare duk wasu 'karafa da aka jona mishi.
Minti goma tsakani wasu motoci guda biyu suka shigo cikin asibitin, Killer ne da tawagarsa, sunyi mummunar shiga ta bak'ak'en kaya sun rufe rabin fuskokinsu. Kallo daya za'ayi musu a gano tsantsar rashin imani a tattare dasu. Hannayensu rike da muggan makamai.
Killer yana rike da babban bindiga A.k 47 tsirararta. Burinshi idanshi idanun Usher ya aikashi garin da ba'a dawowa.
Suna shiga reception biyu daga cikinsu suka shak'e mai bada kati bayan sun nuna mishi bindiga
"Dakin da aka kwantar da Usher zaka nuna mana"
Killer ya tambayeshi bayan ya zaro mishi idanuwa kamar zai cinye shi danye.
Dakyar ya iya d'aga hannu yayi musu nuni da cikin asibitin, domin mugun shak'ar da sukayi mishi bazai iya magana ba.
'Daid'aikun mutanen da suke zaune a gurin kuwa tuni suka fara guje-guje suna neman mafaka dan su tserar da rayuwarsu.
Ba ta su yake ba dan haka suka nufi cikin asibitin suna k'ara gyara rikon makamansu, suna wangale duk dakin da suka yi arba dashi.
A daidai wannan lokacin ne kuma Inspecter Jocob ya ankara da abinda ke faruwa bayan yaji shirun yayi yawa su Dr. Habeeb basu fito daga dakin ba, yana bud'e K'ofa yayi arba da likitan watse a gefe d'aya, da sauri yakai Idanunshi kan gadon da aka kwantar da Usher.
Wayam ba shi ba alamunshi sai k'arafan da aka jona mishi a zube gefe daya, kuma ba dayan likitan da aka kira shi da Dr. Mansur.
Windo ya gani a bude hakan shi ya ankarar dashi abinda ya faru, da sauri ya fita waje ya sanar da sauran 'yan sandan sannan ya dawo ya dira ta windon don yabi sawunsu, domin ga dukkan alamu basuyi nisa ba.
Farar rigar likitoci ya tsinta gaba da dakin kadan, ya dauka kenan sai yaji harbin bindiga ta cikin asibitin, nan take ya juya cikin asibitin a guje yana kara gyara rikon bindigarshi.
Killer sunyi nasarar gano dakin da aka kwantar da Usher, amma ganin 'yan sanda a kofar dakin yasa suka bude wuta, nan take aka fara musayar wuta da harbe-harbe.
Da tsiya Killer ya samu nasarar shiga dakin, amma wayam baiga Usher ba, sai likita a kwance a kasa, takaici da bakin cikin rashin samun Usher yasa ya sakarwa Dr. Habeeb harbi guda, a daidai lokacin Inspecter Jocob ya sawo kai cikin dakin.
Da matsiyacin gudu Killer yayi wani wawan tsalle ya fice ta windo, Jocob kuwa ya bude mishi wuta, harma ya samu nasarar samunshi a hannu, kamar walkiya ya bace a cikin fulawoyi da duhun dare yana dafe da hannunsa, katanga ya kama ya haye, sannan yayi tsalle ya dire ta baya cikin mawuyacin hali, domin hannunsa sai zubda jini yake yi.
****
Yana samun nasarar haurawa da Usher ta katangar suka saka shi a motarsu, wacce suka aje ta can bayan asibitin, take suka figeta da wani matsiyacin gudu suka harba kan titi, tamkar masu gudun ceton rai.
"Hello.. Eh komai ya kammala, ku kyale su ku samfe, mu hadu a joint"
Dariya sukayi shi da dayan da yake tuka motar, sannan suka tafa.
Lokaci guda suka juya kujerun baya na motar suna kallon Usher, wanda har zuwa wannan lokacin baisan inda kanshi yake ba.
Suna cikin gudu tayar motarsu ta fashe, zaro ido sukayi a tsorace, karo na farko kenan da hankalinsu ya tashi, gashi basu da safayar taya, kafin suyi tunanin tsaida motar tayar ta fice fit! Nan take motar ta fara watangaririya dasu a kan titi, daga bisani kuma tayi juyin masa sau biyu kofar baya ta bude akai watsi da Usher can bangaren titin, kanshi yayi mugun buguwa da wani murgujejen dutse. shima na bangaren mai zaman banza aka watsar dashi can gefe guda ba tare da yasan inda kanshi yake ba, shi kuwa mai tuka motar saboda ya sanya belt duk juyin masar da motar take yi bata watsar dashi ba, saidai ya dad'e da fita daga hayyacinshi, take motar ta fara ci da wuta.
Karfe goma sha biyu na dare ne a lokacin, babu motoci masu zirga-zirga, sai daidaiku, idan mota daya ta wuce ana daukan lokaci kafin wata motar ta sake giftawa.
"Ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba..."
Kb ya fadi haka cike da tsoro a fuska da muryarsa, lokacin da yaji yayi tuntube da wani abu har yana neman kifawa, taga-taga yayi kamar zai kifa amma yayi karfin halin tsayawa daidai, sannan ya haska da tocilar hannunshi mai masifar haske.
"Kai Baba... Kaga abinda na gani kuwa...?" Ya fadi haka yana haskawa Muver mutumin da yake kwance a kasa magashiyyan.
"Wannan ai mara lafiya ne Kb, kaga kafarsa ma nannad'e take da bandeji"
Wani mugun tsaki yaja, sannan ya zungure shi da kafarsa, cike da masifa yace
"Amma kai mugun wawa ne, baka da lafiyar ma saboda kaci kafar kare dole sai ka fito yawo? To idan ka gama hutawar ka kwashe tsamin jikinka ka koma gida.
Baba zo mu ware mu bashi guri"
Kb ya fadi haka yana tangadi, hannunsa rike da kofi cike da koko, wanda suke shafawa a bayan poster sannan su manna a bangon gidajen jama'a.
Shi kuma Muver hannunsa dauke da damin poster da suke mannawa.
"Haba Kb.. Bai kamata muyi haka ba, ka ga fa kamar ma ba a hayyacinsa yake ba, zo muyi a tara kawai mu watsa shi can gidan, da alamar ma nanne gidansu"
Ya fadi haka yana nuna wani gida da yake can nesa kadan da inda suke tsaye.
Nan take suka kama shi kai da kafa suna ta tangadi kamar zasu kife, saboda duk su biyun a buge suke, dakyar suka karasa kofar gidan, suna tura kyauren gidan kuwa ya bude, sukai watsi dashi a tsakar gidan sannan suka fice.
[07/03 9:46 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!!*
*Fareedah Abdallah*
*6)*
*TUNA BAYA*
Daga yanda yake tafe jikinsa a matuk'ar sanyaye, fuskarsa cunkushe da damuwa ya tabbatarwa da Mahaifiyarsa yau ma ba'a dace ba, da matukar tausayi take kallonsa.
Kan tabarmar da ke shinfide a kofar dakin ya zube jagwab ya watsar da takardun hannunsa gefe guda, ya tallabe kansa da hannu bibiyu.
Murmushi tayi k'okarin wadata fuskarta dan kwantar masa da hankali.
"Kamaluddeen?"
Ta kira sunanshi muryarta a tausashe.
"Na'am Umma"
Ya amsa kanshi a kasa, muryarsa har rawa take saboda tsabar damuwar da zuciyarsa take ciki, ga kuma mugun gajiyar da ya kwaso.
"'Dago fuskarka ka kalleni mana d'an Umma?"
Idanunshi ciccike da kwallah ya dago yana kallonta. Murmushi ta sake sakar masa ta sake gyara zamanta a kusa dashi.
"Kar6i ruwa kasha"
Ta mika mishi babban kofin roba cike da ruwa mai sanyi wanda ta debo a randar kasar da ke ajiye a kofar d'akin.
Hannu bibiyu yasa ya kar6a yayi bismillah ya kafa kai ya fara kwankwad'a, kad'an ya rage sannan ya aje kofin gefe guda.
Mik'ewa tayi ta shiga dan tsukikin kicin din da yake tsakar gida ta zubo mishi faten tsaki a farantin roba, ta sako mishi cokali a gefe.
Hannu baka hannu kwarya ya ringa Kai loma, daman da Tsananin yinwa ya koma gidan.
Saida taga ya natsu yayi hamdala ta kalleshi da kulawa.
"Yau ma ba'a dace ba ko?"
Saida ya had'iye wani dunk'ulallen miyau na tsabar bakin ciki da takaici, hana idonshi barci yayi ya tashi tun bayan sallar asubah ya fice neman aikin, saboda tun satin da ya wuce ma'aikatar suke ta sanarwar neman ma'aikata masu irin matakin karatunshi, amma da yaje ko interview din da suka ce zasu yi ma basu yi ba, saida rana ya gama kod'asu tun safe har Karfe uku, sannan aka sanar dasu suyi hakuri har an rufe d'aukan ma'aikatan. Karin bakin cikinsa shine pure water na naira goma kawai ya saya a take ya shanye, baida ko sisi da zai sayi abinci.
"Wallahi Umma ba'a dace ba, yanzu a kasar nan in kinga ka samu aiki to saidai in kai wani ne ko kuma dan wani, idan biyun nan basu samu ba to ya kasance ka san wani ko kuma ka san wanda yasan wani mai hanyar samun aikin. Amma in ba haka ba bazaka taba samun aiki ba duk kyan takardunka.
Muna tsaye a gurin fa sai lek'owa ake ana kiran sunayen wad'anda suke da k'afa a gurin, mu kuma da bamu da hanya ko oho, saida rana ya gama gasa mu sannan aka sallame mu da cewar an gama d'aukar ma'aikatan"
"Babu komai Kamaluddeen, lokaci ne, watarana sai labari in Allah ya yarda"
Ta fada muryarta a tausashe, da salon kwantar mishi da hankali.
Amma fa zuciyarta cike take da matsananciyar damuwa.
"Allah yasa haka Umma"
Ya fad'a yana k'ara jin kwarin gwiwa a zuciya da gangar jikinsa.
"Ameen"
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu, kowa da irin tunanin da yake yi a zuciyarsa.
Umma kam har idanunta sun fara tara kwallah, babu wanda ta tuna sai marigayi Malam Ahmad, mahaifin Kamaluddeen, wanda ya rasu shekara d'aya da ya wuce.
A lokacin rayuwarsa shi yayi ta fafutuka ya buga nan ya buga can har Allah yasa Kamal ya kusa kammala karatunshi.
Sunsha jik'a garin rogo su sha babu suga saboda a biya kud'in makarantar Kamaluddeen, idan ta zauna tana mitar yanda karatun yake jan kud'i da cinye duk d'an tattalin arzikinsu saidai ya kalleta yayi murmushi.
Bai cika tankata ba saidai idan yaji mitar tak'i k'arewa sai yace
"Kiyi hakuri Hajara, wata rana sai labari, wannan karatun da kike gani kina rainawa shi kadai ne gatan da zan nunawa Kamal, Yanzu wani lokaci ne da Ubangiji ya Kawo mu matukar baka da ilimi to a komai zaka zama koma baya, masu ilimi dasu ake damawa a komai na kasar nan"
Idan taji haka sai hankalinta ya kwanta, harma tayi murmushi tace
"Toh Malam, Allah ya k'ara maka k'warin gwiwa, Ubangiji Allah ya bada sa'a"
"Ameen Hajara, shiyasa a kullum nake kara k'aunarki"
Sai suyi murmushi gaba-daya, zukatansu cike da kaunar juna.
Inda Allah ya k'ara taimakonsu kuma Kamaluddeen din Guru ne a gurin karatu, daga fannin boko har islamiyya, yana da masifar naci akan duk abinda yasa gaba, ko a makarantarsu saidai ace shi d'an talakawa ne, baya shiga irinna manyan gayu, amma idan a fagen kwakwalwa ne da wuya a samu na biyunshi a kaf department dinsu. Da yawa-yawan dalibai abokan karatunshi maza da mata idan wani abu ya shige musu duhu shi suke nema ya musu k'arin bayani yanda zasu fahimta sosai, har wani inkiya suke mishi
*Second lecturer* ya iya Karin bayani sosai yanda kusan kowa a cikinsu zai fahimci darasin. Shiyasa da yawansu suke taimaka mishi ba tare da ya nima ba, wasu abubuwan idan aka nemi su saya kafin ma ya sanar da iyayenshi zasu sai mishi, akwai lokacin da wani daga cikin abokan karatunshi ya biya mishi kudin registration. A haka dai har Allah yasa ya gama karatunshi.
Yana daf da kammala karatu Allah ya dauki rayuwar mahaifinshi, daga jinyan kwana biyu.
Sunji mutuwarnan ba kad'an ba, dukda rashi na talauci da Allah ya jarrabi Malam Ahmad tsayayyen Uba ne kuma bango abin jingina.
Umma Hajara kam har kwanciya rashin lafiya sai da tayi. Ga zumunci da ya zama abinda ya zama a wannan zamani da muke ciki.
Babu mai waiwayar iyalan mamaci sai dai idan yabar abin duniya.
Haka nan da dad'i babu dad'i ci gaba da gudanar da rayuwarsu su uku, cikin rufin asiri da taimakon Ubangiji.
Mahaifiyarsa, shi Kamaluddeen, sai kanwarsa Fatima.
Da buge-buge har ya kammala karatunsa, Ummansa takance
"Wannan karatun burin mahaifinka ne Kamaluddeen, da yaddar Allah bazan ta6a gajiyawa ba"
Ya gama karatun da sakamako mai matuk'ar kyau, suna murnan wahalarsu ta kusa zuwa karshe ashe wasa sabon girki, duk inda ake tunanin neman aiki yak'i samuwa, a kullum cikin yawo da takardunsa yake daga wannan ma'aikata zuwa wancan Ofis amma aiki yak'i samuwa.
Duk inda yaji ana neman ma'aikata to da asussuba zai buga sammako ko da kuwa baida kudin mota duk nisan guri zai taka a k'afa, amma saidai ya gama bilayinshi ya koma gida.
Ba kuma fa wai dan takardunshi basu kai a dauke shi aikin bane, kawai dan baisan wani babba ba, kuma shi ba dan wani babba bane.
Yanda kuma zumunci ya lalace a wannan zamanin namu yasa daga dangin babanshi da dangin Mahaifiyarsa duk suka tsame hannu akansu, saboda ansan ubansu ya mutu baibar komai ba, basu tsira da komai sai k'aramin gidan da suke ciki ginin k'asa, mai d'auke da d'kauna guda uku. Uwar d'aki da falo guda daya sai kuma d'aki daya a tsakar gidan. 'Dan tsukikin kicin mai kama da akurkin kaji da kuma k'aramin ban daki mai d'auke da masai da gurin wanka duk a ciki daya.
Shiyasa kowa yake tunanin duk wanda ya dauke su ma wahala zai k'arawa kanshi. Da wanki da surfen hannu da Umma take yi a gida suke gudanar da rayuwarsu. Sai kuma kulle- kullen kuka da ku6ewa.
"Umma Fatima bata dawo bane?"
Ya tambaye ta ganin yanda tayi nisa a duniyar tunani.
"Tana islamiya, amma nasan duk inda take yanzu tana hanyar dawowa..."
Bata gama aje numfashin maganarta ba Fatiman tayi sallama ta shigo gidan hankalinta a tashe, da gudu ta nufi gurin Ummanta ta rungume ta, sannan ta fashe da kuka.
Hankalinsu ne ya dugunzuma gaba d'aya, Kamal ya birkitota daga jikin uwar zuwa jikinshi, yana jijjiga ta yake tambayarta
"Keh Fatima! Kalle ni nan!! Me ya faru!!? Waye ya taba ki?"
"Yaya... Yaya... Ka shiga tsakanina da d'an gidan Chairman Ado... kusan kullum idan zan dawo makaranta sayya ringa tare ni yana min maganganun banza... Wai inzo dakinshi zai bani kudi... Yau shine yace min indai banzo dakinshi da daddare ba zai zo ya sace ni.."
Wani mahaukacin mari ya dauke ta dashi, sannan ya fara zazzaga mata bala'i yana cewa
"Dan Ubanki tuntuni shine baki fada min ba? Zo muje inga uban da ya tsaya mishi a garin nan"
Hannunta yaja suka fice daga gidan, Ummansu tana kwallah musu kira ko sauraranta bayyi ba.
Ba wani nisa bane tsakanin gidansu da gidan ciyaman din, layi biyu ne a tsakaninsu, haka yake janta sauri-sauri gudu-gudu har suka isa kofar tangamemen get din gidan.
Tunda yaga maza yan maula wadanda zuciyarsu ta gama mutuwa a kofar gidan suna alwalar sallar magrib ya tabbatar mishi Ciyaman din yana nan.
Ganin karamin kofar get din gidan a bude yasa yaja hannunta suka shige cikin harabar gidan, suna shiga Ciyaman din yana Fitowa, da alamun masallaci zashi.
Kallon-kallo ne ya gudana a tsakaninsu har na tsawon wasu dakiku, Kamaluddeen tunanin farkon zuwanshi gidan yake yi, a lokacin da sakamakon jarabawarsu ta fito, Ciyaman ne farkon wanda ya fara kaiwa takardun da kwarin gwiwarshi na tunanin zai taimaka mishi, duba da yanda takardun sukai kyau.
[09/03 4:00 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!!*
*Fareedah Abdallah*
*7)*
Tsawon lokaci Ciyaman yana duba takardun makarantar, layi-layi yake bi yana duba kyakkyawan sakamakon, Lokaci daya fuskarsa ta had'e gabas da yamma.
Kamal ko yanda yaga mummunar fuskar chairman ta kara damalmalewa da 6acin rai yasa jikinshi yayi sanyi, lokaci d'aya yayi fuskar tausayi kamar zai fashe da kuka. A zuciyarsa yake ta addu'ar Allah ya dube shi ya dora shi akan Chairman yayi mishi hanyar samun aiki.
Tsawon wasu dakiku kamar bazai tanka ba can ya d'ago ya kalleshi a yatsine
"Ba laifi.. Ka d'an ta6uka. Amma abinda nake so in tabbatar maka shine in dai aikin gwamnati kake bukata da wad'annan takardun naka zaka dad'e baka samu ba, domin basu yi kyan da ake bukata ba..."
A razane ya d"ago da fuskarshi yana kallonshi, baki da hanci bud'e, mamaki kwarai yake yi a zuciyarsa, aduk department dinsu shine yazo na d'aya da mafi kyakkyawan sakamako, amma kuma ace takardunshi basuyi kyan da zai samu aiki ba? Wane irin kyau ake bukata bayan wannan?
Bai damu da kallon da yake mishi ba ya ci gaba da watsa mishi duk maganganun da suka zo bakinshi na gwalewa da sace gwiwar Kamal, ya karya lagon duk wani kwarin gwiwa da alfaharin samun kyakkyawan sakamakon da yake ji a ransh. Tuni idanun Kamal sun cicciko da hawaye, kanshi na k'asa, yana k'ok'arin had'iye wani dunk'ulen abu da ya tsaya mishi a mak'oshi.
"Karka damu fa, iya zallar gaskiyar magana ce wannan nake fad'a maka.
Amma zanyi maka wata alfarma..
saboda hakkin makwaftakan da yake tsakaninmu da kuma matausaya da naga kana dashi, zan iya baka aiki idan kana so"
Da sauri ya shanye duk wani damuwa da bacin ransa jin da yayi zai samu aiki yace
"Godiya nake Honorable, ko wane irin aiki ne zanyi, ni dai bukata ta in samu aikin. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, ubangiji ya jikan mahaifa"
"Ok! Ameen. Ba wani aiki bane mai wahala, zan sai maka waya ta naira dubu goma, wacce zaka ringa hawa media kana tallata ni, da yabon irin k'ok'arin da nake yi akan mutane. Kaima dai shaida ne akan haka.
Da tuttura hotunan irin aikin da nake yi a k'aramar hukumar nan.
Idan naga aikinka yana kyau zan ringa biyanka naira dubu biyar duk k'arshen wata, amma fa nima nawa aikin shigen aikin gwamnati ne, sai kayi wata biyar kana min aiki a wata na shida zan fara biyanka"
Tsabar ba'kin ciki da takaici yasa jikinshi ya fara tsuma, zuciyarsa cike da matsanancin 6acin rai da bak'in ciki, hannu kawai iya mi'ka mishi alamun ya bashi takardunshi, domin a yanda yake jin zuciyarsa idan ya k'ara zaman minti biyu zai iya kaiwa Ciyaman din naushi.
Kallo daya Chairman yayi mishi ya fahimci manufarsa, dan haka ya mika mishi takardun ba tare da ya kara tankawa ba.
Yana kar6ar takardun ya nad'e su yayi musu riko mai kyau, alamun suna da matuk'ar muhimmanci a gurinshi.
Tsaye ya mik'e kamar bazai tanka ba, sai kuma ya kalleshi ranshi a matukar 6ace yace
"Na gode da wannan aiki naka mai matukar daraja da muhimmanci, amma kayi makuwa.. Domin wannan aikin ba da ni ya dace ba, da wannan da'ki'kin d'an naka Ado ya dace, wanda saboda tsabar dak'ik'ancinsa har yau ya gagara gama Diploma"
Yana gama fad'in haka ya kara gyara rikon takardunshi yayi hanyar ficewa daga falon.
Yana ji Ciyaman din yana d'ura mishi ashar, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Karshen kalmar da kunnenshi ya jiyo a daidai lokacin da yake gab da ficewa daga gidan shi ne
"Matsiyaci ko a tandun mai za'a saka shi haka zai fito k'amas, yaje a haka zai kare a wahalce"
"Yauma d'iban albarka kazo kayi min har gida?"
Ciyaman ya katse mishi tunaninshi bayan ya had'e girar sama da kasa yai murtuk!
Hannu ya d'aga mishi yana watsa mishi mummunan kallo mai cike da tsana.
"Dakata Malam! Yau ba neman aiki nazo ba, kashaidi nazo yi maka akan bunsurun d'anka Ado.
Ina fada maka da kakkausar murya ka ja mishi kunne.
Idan yana tare yaran mutane yayi musu fyad'e ya kwana lafiya to hawainiyarsa ta kiyayi rama ta, domin wannan yarinyar da kake gani ba kamar sauran yara marasa galihu bane.
Wallahi tallahi idan ya sake shiga gonar k'anwata saina yi masa mummunan lahanin da bazai kara marmarin tare wata yarinya a hanya ba. Mata-maza zan maidashi yanda har gaban abada bazai k'ara moruwa ba!
Wannan shine kashe di na farko kuma na karshe, zan gani idan ka bashi tarbiyya ta kwarai"
Wani wawan tsaki yaja ya tofar da kakkauran miyau a tsakar gidan. Yaja hannun Fatima sukai hanyar fita daga gidan.
Wasu 'yan sanda su biyu da suke gadin Ciyaman din sun yunk'ura zasu damk'eshi Ciyaman ya dakatar dasu, bayan Kamaluddeen yabi da kallo har suka 6acewa ganinsa, murmushi yayi zuciyarsa cike da miyagun sake-sake. Ya kad'a kai ya fice daga gidan ya nufi masallacin kofar gidansa.
Har lokacin basu tada sallar ba suna jiranshi, domin matuk'ar yana gari kuma yana gida to duk dad'ewar da zaiyi bai fito sallah ba a masallacin ba'a tada sallah sai an jira shi.
Ko bayan komawarsu gida Ummansu rufe shi tayi da fada, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, ranta yayi mummunar baci da abinda yayi.
Kanshi na k'asa, sai faman bata hakuri yake yi, sai daga karshe ta sassauta murya ta koma yi mishi nasiha, tana gargadinshi akan wannan saurin fushin da d'aukar abu da zafi, shi saurin fushi babu abinda yake haifarwa sai dana-sani.
******
Tsawon sati guda Ado bai sake yunk'urin tare Fatima a hanyar dawowarta daga makarantar islamiya ba, da alamun kashedin tsohonshi ya shige shi. A tunanin Kamal kenan.
Duk tsawon satin Kamaluddeen shi yake raka ta islamiya da boko, sannan idan an kusa tashi zaije makarantar har a tashi su dawo tare, ganin Ado bai sake tare ta ba yasa hankalinshi ya kwanta.
Har tsawon sati biyu babu wani abu da ya faru, dan haka ya sakankance ya ci gaba da bilayin neman aiki ita kuma ta ci gaba da zuwa makaranta.
A rana ta goma sha bakwai ne da ya kama ranar wata asabar, Fatima ta tafi islamiya da karfe biyu na rana, ana tashinsu karfe shida na yamma ne amma har aka kira sallar magrib bata koma gida ba.
Da farko basu damu sosai ba, amma ganin har an idar da sallar magriba duhu ya fara shigowa misalin karfe shida da minti hamsin hankalinsu ya fara tashi sosai, a d'imauce ya tafi makarantar amma bai tararda kowa ba, makarantar ma a kulle take.
Gidan malamin su Fatiman ya tafi hankalinshi a tashe yana tambayarsa ina Fatima? Abin mamaki da d'aure Kai tabbatar mishi yayi a wannan ranar ma sam Fatima bata je islamiya ba.
Da mugun tashin hankali ya sake bin hanyar daga makarantar zuwa gidansu ko zai ganta, saboda tsabar rud'ewa ma ya manta fatimar mutum ce kuma babbar budurwa, domin sai kallon k'asa yake yi tamkar zai tsince ta.
Yana isa gidan ya iske Ummansu itama hankalinta a mugun tashe, harta fara kuka, ta sake tabbatar mishi Fatiman bata dawo ba.
Kofar gida ya fita ya tsaya yai shiru cikin tunani, hannayensa zube a aljihu, tunani yake ina zaije ya nemi Fatiman?
Ita sam ba yarinya ce mai yawace- yawace ba, kuma ita ba mai irin tara kawayen nan bane balle yace ko ta biya gidan wata kawarta, kuma basu shak'u da danginsu ba balle yace ko can taje.
"To ina zata je???"
Ya tambayi kansa a fili.
Tunanin da ya fad'o mishi a zuciya ne yasa ya girgiza kanshi da karfi, da wani matsiyacin gudu ya nufi gidan kamar mahaukaci, a lokacin har an idar da sallar isha'i shi kuwa ko magrib baiyi ba.
Yana zuwa ya fara buga kofar gidan da karfi, duk wanda yaji bugun zai tabbatar babu lafiya.
[10/03 10:58 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!*
*Fareedah Abdallah*
*8)*
Kusan duk iyalan gidan sun fito harabar gidan don ganin mahaukacin da yake yi musu wannan mugun bugun, har da shi kanshi mai gidan. Tafasa kawai yake yi yana jiran fuskar wanda zai bayyana, yanzunnan ya shiga cikin gida dan ya samu ya huta amma matsiyatan 'yan maulan nan baza su barshi ya huta ba.
Tunanin da yake yi kenan a zuciyarsa.
Maigadi yana bud'e gidan ya fad'a ciki a guje kamar wanda aka jefo, kansu ya nufa gadan-gadan.
Idanunsa cikin na Ado ya kai mishi wata wawan raruma ya watsar dashi a kasa, kanshi yayi da naushi ta ko ina, cikin mintina da basu gaza biyu ba ya hada mishi jini da majina. Duk yanda mai gadi da chairman suke k'ok'arin kwatar Ado a hannunsa sun kasa
"Ina k'anwata..? Dan ubanka ina ka kaimin k'anwata...? Ka fito min da k'anwata kafin in Kashe ka a gurin nan...!"
Ihu yake yi kamar mahaukaci yana maimaita wad'annan kalaman, hannuwansa duk biyu yasa ya shak'e shi kamar zai kashe shi.
Ado sai k'ok'arin k'watar kanshi yake yi, domin ba k'aramin shak'a yayi mishi ba.
Duk abinda Chairman ya rarumo buga wa Kamaluddeen yake yana fadin
"Dan Ubanka sakar shi, sake min d'ana ko ka 'kare rayuwarka a gidan yari"
Kamal ko gezau baiyi ba, saima k'ara shak'e Ado yake yi idanunsa sun kad'a sunyi jajur! Ga dukkan alamu bashi cikin hayyacinsa.
Mahaifiyar Kamal da k'anwarsa sai kuka suke yi, dukda dare ne gidan har ya fara tara mutane.
Baiji isowar 'yan sanda ba sai kawai yaji hancin bindigogi a saitin kanshi
"You are under arrest"
Abinda d'aya daga cikin 'yan sandan ya fad'a mishi kenan suna k'okarin banbare hannunshi daga wuyan Ado.
"Yauwa Officer, kunzo a daidai, ku tafi dashi, mahaukaci ne.
Wannan shine karo na biyu da yazo gidannan yana min barazana da kisa.
Sati biyu da suka wuce yazo yana min barazanar sai yaga k'arshe na, yau kuma yazo yana k'ok'arin Kashe min d'a, kuma yana k'ok'arin k'ala masa sharrin ya sace masa k'anwa, bayan kuma yau tun safe Ado yana gida, baida lafiya ma tun shekaran jiya ba fita yake yi ba"
Yana gama fad'in haka yaja hannun Ado da 'yan sanda suka k'waceshi dak'yar yayi cikin gidan dashi, Hajiya da k'anwar Ado suka rufa musu baya.
'Yan sandan kuma suka tasa k'eyar Kamaluddeen suka tafi dashi a motarsu.
Daya bayan daya jama'ar da suka taru a gidan suka ringa watsewa har suka fice gaba d'aya.
Sai hum-hum-hum suke yi da zancen, dan da yawa daga cikinsu sun san Kamal, kuma Sun shaide shi yaro ne mai nutsuwa da rashin shiga shirgin da babu ruwansa, ga girmama na gaba, tsakaninsa da kowa mutunci ne, shiyasa suke ta mamakin abinda Chairman ya fad'awa 'yan Sandan a kansa
*****
Yusuf abokin Kamaluddeen shi yaje yana fada mata abinda ya faru, saboda yaga lokacin da Kamaluddeen din yabi hanya da gudu zuwa gidan Ciyaman, shi kuma ya bishi yana tambayarshi abinda yake faruwa, amma bai saurare shi ba.
Akan Idanunshi komai ya faru, har wucewar da akayi da Kamal din, shiyasa yaje ya sanar da ita.
Hankalinta ne ya k'ara d'ugunzuma, take numfashinta ya fara sama da k'asa, dama lafiya bai ishe ta ba.
Dame zata ji?
Kuka kuwa tayi shi kamar ba gobe,
"Oh ni Hajara, wannan wane irin masifa ne? An nemi Fatima an rasa shi kuma Kamaluddeen 'yan sanda sun kulle shi, ya Allah ka Kawo min 'dauki.."
Tana gama fad'in haka saita sake fashewa da kuka, ta ba matan makwaftan da suka shigo jajantawa gaba d'aya tausayi, sai share hawaye suke yi, suna fad'a mata kalaman kwantar da hankali.
Yusuf da wasu daga cikin abokansu ne suka ringa bi lungu da sak'o tun daga hanyar makarantar zuwa gidan suna neman Fatiman, amma har dare ya tsala basu sami nasarar ganinta ba. Ko wanda zaice yaga wucewarta a ranar ma basu samu ba.
Dole suka hak'ura zuwa safe su dasa daga inda suka tsaya.
Da d'ai d'ai Matan makwafta suka fice daga gidan suka barta cikin mawuyacin hali. A wannan ranar sam barci baiga idanun Umma Hajara ba.
Nafilfili take yi tana rokon Allah ya bata ikon cinye wannan nannauyar jarabawar, tana addu'ar tana kuka da majina, tayi raka'o'i sunfi talatin, tsabar damuwa da tashin hankali bata ko sanin surorin da take karantawa.
Washe gari ana idar da sallar asubahi ta nufi gidan Chairman, taje a dai-dai lokacin da ya tura k'ofar gidan shi zai shiga ciki bayan dawowarsa daga masallaci.
"Ranka ya dade barka da asubah.." ta furta da rawar murya, wasu sabbin hawaye suna sake zubowa wasu na korar wasu.
A d'age ya kalleta kamar hankali bai ishe ta ba, d'an nesa da ita yayi a tsorace, ya kalli mai gadi yaga yana kusa dashi kad'an.
"Lafiya kuwa?"
Ya tambaye ta da d'ari-dari.
K'asa ta zube a gabanshi kamar mai neman gafara, ta had'a hannu biyu alamar rok'o ta fara magana cikin kuka.
"Ni ce mahaifiyar Kamal. Yaron da kasa 'yan sanda suka kama jiya da daddare...
Dan Allah Dan Annabi SAW ka taimake ni kasa a sakomin yaro na, wallahi su biyu kawai na mallaka a duniya.. mahaifinsu ya dad'e da rasuwa ya barmin su marayu...
Abinda ya maka ba halinshi bane yana cikin zafi da radadin rashin k'anwarsa ne.. Dan Allah kasa a sako shi nayi maka alk'awarin ko kofar gidannan bazai sake zuwa ba balle har ya shiga harkarka"
Tana gama fadin haka ta fashe da kuka, kamar zata kwanta ya taka bayanta tsabar rok'o da kaskantar da Kai.
Hura hanci ya fara yi yana cika yana batsewa, kamar bazaiyi magana ba, kanshi na girma yana kara kumbura tsabar ji da Kai da ganin eh shi fa ya isa.
"Tabbas yaronki yana shaye-shaye, Amma ina tunanin ke baki da labari. A duk sanda zai zo gidannan a buge yake zuwa min, yaita min hauka iri-iri.
Na dad'e fa ina hakuri dashi, in banda ma ni din ina da tausayi da jin k'ai da tuni nasa anyi maganinshi.
Amma tunda kinzo da kanki zan yafe mishi"
Da sauri ta dago tana zabga godiya da addu'a da fatan alkhairi a gare shi.
Kanshi ne ya kara kumbura, cikin izza yace
"Ki tafi gida, zan duba al'amarinki. A ko wane lokaci zaki iya ganin danki ya dawo gida"
Yana gama fadin haka ya shige cikin gidan, mai gadi ya maida kofar get din bam ya rufe, suka barta a gurin tsugune.
******
"Amma Alhaji baka tunanin Ado ya aikata laifin da ake tuhumarsa dashi?"
Mahaifiyar Ado ta tari Chairman da zancen a lokacin da ya shiga cikin falon. Dan sama-sama taji muryar Umma Hajara tana rokonsa yasa a sakar mata d'anta.
Daure fuska yayi tamau alamun ba wasa.
"Me yasa kika ce haka?"
Ya tambaye ta a tsaitsaye, ba tare da yaba maganar wata muhimmanci ba.
Ita ma had'e nata fuskan tayi murtuk! Dukda ita ta haifi Kamal ta dad'e da sanin wasu daga cikin tsiyatakun da yake aikatawa.
A kullum nasiha da fad'a take mishi, amma ako wane lokaci mahaifinsa goyon bayanshi yake yi. Kuma shi yake k'ara lalata shi ta hanyar sakar mishi manyan kud'ad'e wad'anda suka fi karfin bukatunshi.
Kuma ranarda Kamal yaje gidan yayi kashaidi a fita hanyar kanwarsa ta samu labarin duk abinda ya faru ta bakin mai aikinta. Har ma ta jawa Ado kunne a kebance ba tare da sanin mahaifinsa ba, amma ga dukkan alamu baiji ba.
"Tsawon kwana biyun nan Kai kanka kasan Ado baya dawowa gida da wuri, kuma ko jiya da aka wuce da yaron nan station Ado bai dawo gidannan ba sai daf da asubah. Ina yake zuwa?"
"Hotel na kama masa dan yaje ya huta daga hayaniyar da yaron nan ya haifar masa. Kina da matsala ne da hakan?"
Ya tambayeta yana watsa mata mugun kallo. A zuciyarsa tunani yake yi bacin ita ta haifi su Ado da tuni ya dad'e da rabuwa da ita.
Girgiza kai tayi alamun rashin gamsuwa da abinda yace
"Alhaji ni dai a kullum ina fada maka akwai ranar kin dillanci. Ka kiyayi ranar da Ubangiji zai tsayarda Kai yana tuhumarka akan amanar da ya dank'a maka"
Tana gama fadin haka ta shige bangarenta ta barshi a tsaye.
Shiru yayi yana tunanin maganganunta a ransa, can kuma ya watsar da komai ya haye sama zuwa bangarensa.
******
Ajiyar zuciya taita saukewa akai akai har ta isa gida, a zuciyarta take tunanin rabin damuwarta ya ragu, tunda za'a sako Kamaluddeen.
Abu fa kamar wasa k'aramar magana tana neman zama babba, saida aka shafe kwanaki biyu ana neman Fatima amma ba'a ganta ba.
Kuma har wannan lokacin Kamal bai koma gida ba, dangin Mahaifiyarsa da dangin mahaifinsa sun had'u sunje station d'in amma sam 'yan sanda sun hana belinshi, a cewarsu wannan babban case ne, dole sai kotu ta shiga tsakani.
Suna ta jelar zuwa gidan Chairman kuma dan su sake bashi hakuri yasa a sake shi basa samunshi, ance kwananshi biyu bashi a garin, amma ana saka ran dawowarshi gobe.
Zuwa wannan lokacin Umma Hajara ta karasa ficewa daga hayyacinta, dangin mijinta da nata dangin da basu damu da ita ba saboda talauci a kullum suna gidan suna rarrashinta.
A washegarin kwana na uku ne suka wayi gari da wani mummunar tashin hankali, Fatima aka tsinta yashe a kofar gidansu da asubah, a cikin halin mutu kwakwai! rai kwakwai! anyi kaca-kaca da matantakanta, cike da rashin imani da rashin tausayi.
Tsananin tashin hankali da d'imuwa yasa zuciyar Umma Hajara ya bugawa, take ta yanke jiki ta fad'i wanwar kusa da Fatima.
Nan take aka kwashe su gaba d'aya zuwa asibiti.
Masu raunin zuciya a cikin makwafta sai kuka suke yi, zuciyar wasu kuma sake cika tayi da tsoron Allah suna k'ara imani dashi, yanda cikin kwanaki k'alilan ya jarrabi iyalan gidan da fitinu iri-iri.
Minti talatin da zuwansu Allah ya kar6i rayuwar Umma Hajara.
Ita kuwa Fatima kokawa kawai take da numfashinta, dan bata san inda kanta yake ba, likitoci hud'u ne suka rufu a kanta suna k'ok'arin ceto rayuwarta.
A daidai wannan lokacin ne kuma Chairman yaga dama ya bada umarnin a saki Kamaluddeen, bayan 'yan sanda sun mishi laga-laga, had'e da kwakkwaran Jan kunne, da zazzafar gargadi.
Cikin kwanaki ukun nan yayi baki, ya rame, ya fita daga nutsuwarshi. Hankalinshi naga Fatima da Ummanshi, addu'a yake Allah yasa anga Fatima.
Yana isa gida ya tararda wannan mummunar labarin, wani jiki da ya kwashe shi dakyar yayi taga-taga ya dafa bango, ya kasa kuka ko kad'an. Duk yanda Yusuf yaso su shiga gidansu yaci abinci yayi wanka k'i yayi, dan haka suka nufi asibitin da rakiyar Yusuf din.
Suna shiga cikin reception a asibitin ya had'u da k'anin Ummansu da wan babansu, suna tsaye zuciyoyinsu a jagule, fuskarsu d'auke da mugun tashin hankali, sharar kwallah kawai suke yi.
Suna ganinsa suka k'arasa gare shi a sanyaye, fuskarsu cike da matukar tausayinsa.
Kallonsu kawai yake yi, yana k'ok'arin tattaro duk wani dauriya da juriyar zuciya ya makawa kansa.
"Ya jikin nasu?"
Yayi karfin halin tambayar su bayan ya lura sun kasa ce mishi komai.
Hannunshi kawai k'anin Ummansu ya kama suka nufi ofishin babbar likitan, tana hakimce akan kujera, hannunta d'auke da wasu takardu tana dubawa.
"Shine wannan likita"
Abinda kawu Mustapha yace mata kenan ya saki hannunsa yayi waje, bayan ya ja musu k'ofar ofishin ya kulle ta waje.
[11/03 11:11 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!!*
*Fareedah Abdallah*
*9)*
"Likita ya.. ya.. Jikin.. Nasu..?"
Ya fad'a da rawar murya, ko zama ya kasa yi, yana tsaye k'ik'am a gaban teburin likitan.
A hankali dattijuwar likktan ta d'ago fararen idanunta da suke 6oye cikin farin gilashi ta kalleshi, kallo ne mai cike da tausayawa.
"Ya sunanka?"
Ta tambaye shi a tausashe.
"Kama..ludd..een"
Ya amsa tambayarta a rarraba, ba amsar da yaso ji ba kenan, so yake yaji halin da mahaifiya da kanwarsa suke ciki, dan kirjinsa sai bugawa yake yi.
"Malam Kamal zauna mana?"
Ta sake fadin haka tana nuna mishi kujeran da yake fuskantarta alamun ya zauna a kai.
A d'ofane ya zauna kamar mai cutan basir. Gaba daya idanu da hankalinshi suna zube a kanta.
"Ya kake da marassa lafiyar nan?"
"Mahaifiyata da k'anwata"
Ya amsa a k'agauce. Ya k'osa kwarai yaji a wane hali suke ciki ne?
"Kamal ina fatan kasan muhimmancin yarda da kaddara ko?"
Saida ya hadiye wani miyau mai kauri, zuciyarsa cike da matsanancin fargaba da tsoro ya daga Kai alamar 'eh'.
"Da kyau Malam Kamal, nasan kasan yarda da kaddara mai kyau da mara kyau na daga cikin rukunan imani..."
"Dr. Dan girman Allah ki fada min sun rasu ko?"
Shiru tayi tana tunanin ta yanda zata fada masa rasuwar mahaifiyarsa da kuma halin da kanwarsa take ciki. Sai kawai tayi shahada tace
"Kayi hakuri Kamal, Allah yayiwa Mahaifiyarka rasuwa d'azunnan"
Runtse ido yayi da karfi saboda wata masokiya data taso daga kasan hakarkarinsa ta cake shi a kirji. Kimanin minti uku kafin ya iya bude jajayen idanunsa ya zuba su a kanta.
"Fatima fa?"
Ya tambaye ta dakyar kamar mai koyon magana
"Mu je!"
Ta fadi haka bayan ta mike tsaye daga mazauninta. Dakin da aka kwantar da Fatima suka nufa.
Shi kam Allah ne kadai ya kaishi dakin lafiya, Sam baya cikin nutsuwarsa. Kiris ya rage ya gwabza karo da wasu ma'aikatan jinya mata biyu sai suka dare suka bashi hanya.
Gado daya ne a dakin da aka kwantar da ita, a hankali ya ringa takawa har ya isa gaban gadon da take kwance kamar matacciya.
Yanda aka yi mata kaca-kaca da fuska ne ya fara d'aga mishi hankali, fuskarta duk jini, wasu guraren duk sun kumbura, kanta nannad'e da bandeji, idan ba tsananin sani kai mata ba baza ka shaida ta ba, da yake an sa zanin gado an lullube ta tun daga kafafunta har zuwa saman kirjinta.
Runtse idanunsa yayi yana tsananin jin tausayinta a zuciyarsa. Juyawa yayi ya fuskanci likitar, alamun neman karin bayani akan halin da take ciki.
"Kwanaki uku aka d'auka ana yi mata fyad'e ana karawa, ta rasa jini da yawa, shi ya k'ara taimakawa gurin fitar da ita a hayyacinta.
Ga dukkan alamu wad'anda suka yi mata wannan d'anyen aikin a buge suke, dan sunyi mata kaca-kaca da matantakanta, yanda ko ta rayu to ta samu nakasu na har abada a rayuwarta.
Tsawon kwana ke gare ta shiyasa har yanzu take a raye...!"
Hannu kawai ya iya d'agawa ya dakatar da likitan, alamun baison ji, zuciyarsa bugawa kawai take 'fafafat' jijiyoyin kansa sun taso rud'u-rud'u.
Tsawon wasu dak'ik'u yayi shiru kamar wanda aka zarewa laka, a sanyaye ya taka har zuwa gaban gadon da take kwance, ya duka a daidai kanta yana kallonta. Hannu yasa ya d'an yaye rufar da akayi mata har zuwa cikinta, sannan ya kamo hannunta ya rike tsam a hannunta.
A hankali ya fara magana a daidai saitin kunnenta
"Fati... Fatin Yaya Kamal, kiyi hakuri kinji..? Zanyi miki wannan tambayar ne domin kada wadanda suka aikata miki wannan tozarcin su k'ara aikatawa ga kowa ce 'ya mace.
Ina so in hukunta wadanda suka aikata miki haka hukunci mafi muni da tsanani akan wadanda suke lalata yaran mutane.
Nasan kina matukar jin jiki... Amma ki daure... Dan Allah... Ki fada min.. Su waye!? Su waye..!!?? Su wanene suka aikata miki haka!!!???"
Nan take taja wani nannuyar numfashi tun daga cikinta har zuwa kirjinta, wasu zafafan hawaye suka silalo daga gefe da gefen idanuwanta, ta damk'e hannunshi da yake cikin nata da karfi, ta fara k'ok'arin magana cikin mawuyacin hali, numfashinta yana k'asa yana sama
"Ya..ya.. Su..su A..do...dah ah..boh..kan...sa..."
Maganar ce ta katse ta fara jan numfashi da karfi, ta ja sau hudu ranta ya fice daga gangar jikinta, domin yana ta jiran taja na biyar amma shiru, sai likitan ne ta matso tana goge hawaye cike da tsananin tausayin wadannan 'yan uwan, taja zanin gadon da aka rufa mata har saman kanta.
Kallonta yake kamar wani wawa yana neman karin bayani, ta girgiza mishi kai, alamun sai hakuri. Fatima lokaci yayi.
A wannan rana Kamaluddeen yaga tashin hankalin da bai taba gani ba a rayuwarsa, ga gawar mahaifiyarsa mai matukar jin tausayinsa da kaunarsa, wacce duk tsumi da tattali da tanadinta a kanshi ne da tilon kanwarsa.
A gefe guda kuma ga gawar k'anwarsa mafi soyuwa a gare shi.
Nan take zuciyarsa ta fara halarto mishi wasu dad'ad'an hirarraki da suka gudanar da ita kwanaki kadan da suka wuce.
*Yaya Idan ka fara aiki kasan me nake so ka siya min?* wata rana suna hira da fatima take tambayarsa.
Dariya yayi yace
" *A'a saikin fad'a fatima*
Itama sai tayi dariya tace
" *So nake ka sai min camera in ringa daukarku hoto Kai da Umma, hotunan Baba kuma ka Kai a Wanke min manya in kafa a daki kullum in ringa kallonku.. kasan nafi kaunarku fiye da kowa a duniya...*
Kafadarsa da Kawu Mustafa ya dafa ne ya dawo dashi cikin hayyacinsa. Ya ba mutane matukar mamaki, domin kuwa dashi akayi komai na jana'izarsu, har aka kaisu makwancinsu na gaskiya.
Da aka dawo gurin Zaman makoki ma yana zaune a gurin cikin abokansa, amma ya zama wani shiru.. Kallon mutane kawai yake yi, in za'a yini ana mishi magana baya amsawa, ko abinci mai nauyi baya iya ci, idan aka matsa masa da nasiha ne sai yace a kawo mishi ruwan lipton yasha, haka har akayi kwanaki bakwai, sannan aka watse.
Kanin Ummansu da Yayan Babanshi sun umarci ya tattaro kayanshi ya koma gidan d'aya daga cikinsu da zama, sai kawai ya bisu da 'To' wacce bata karya wuya, amma ya kudiri niyyar ci gaba da zamanshi a gidan su.
Ranarda aka watse yafi minti talatin yana zaune a kofar dakin Umma yana rusa kuka, komai da komai na gidan yana nan a mazauninshi, amma rashin wadannan rayukan guda biyu yasa gidan ko kadan baya mishi dad'i.
*******
Tsawon wata guda kenan da rasuwarsu, ya rame yayi baki, ya kara lalacewa, gaba daya rayuwarshi ya zamo tamkar wani mara amfani, ya zamo shi kad'ai. Baya shiga harkar kowa.
Sallah da ya zama wajibi da wasu abubuwa masu muhimmanci kawai ke fitar dashi daga gidansu, sai yayi kwana uku bayyi wanka ba, mutanen unguwa sai tausaya mishi suke yi, lokaci zuwa lokaci sukan kira shi suyi mishi nasiha, da Jan hankali akan rungumar k'addara kyakkyawa da mummuna.
Godiya yake musu kawai, ya kad'a kanshi ya shiga gida.
A 6oye kuwa zazzafar bincike yake yi akan Ado d'an gidan Ciyaman, kama daga guraren da yake yawan zuwa, abokansa, 'yan matansa, club d'in da yake zuwa, hatta kalar giyan da yake sha babu abinda bai binciko ba.
Kuma ya gama komai na target dinshi, lokaci kawai yake jira.
A ranar da Umma da Fatima suka cika kwanaki arba'in da rasuwa a wannan ranar ne ya shirya fara d'aukar fansarshi, ana idar da sallar magrib ya sallo wanka ya shirya yayiwa Club d'in da Ado yake yawan zuwa duk daren duniya tsinke.
Akan Idanunshi Ado ya isa cikin Club d'in.
Yarinyar Adon ya nema suka tsadance ya biyata sannan ya bata wasu kwayoyi guda biyar yace ta zuba mishi a cikin giyarshi.
Fari tayi da idanunta tana karkada jiki
"Ina fatan dai ba Kashe shi zaka yi ba?"
Ta tambaye shi, zaro idanu yayi sannan yace
"Haba dai, wani irin kisa? Abokina ne fa tun na yarinta, sabani muka samu shiyasa nake so inyi amfani da wannan damar, idan yasha ya fara barci sai in dauke shi muje gidanmu dashi, idan ya farka sai in bashi hakuri mu sasanta"
Gyad'a kanta tayi alamar gamsuwa, sannan ta nufi gurin Adon tana lank'wasa da karairaya da jijjiga tamkar zata karye.
Akan idonshi ta zubawa Ado kwayoyin a cikin kofin giyarshi, sannan ta kafa mishi a baki ya shanye tas!
Wani mugun murmushi yayi sannan ya cije gefen bakinshi na dama alamun mugunta, Fitowa yayi daga maboyarshi ya nufi gurin Adon, yana zuwa ya bashi hannu suka tafa, da yake a buge yake bai gane shi ba sam.
"Baba yah, mu fasa ne?"
Ya tambaye shi da irin muryar bugaggu.
"Eh mu fasa kawai Ba..Ba.."
Ya amsa dakyar yana lumshe idanu.
Tallabar shi yayi a kafadarsa suka nufi motan Adon, a kujeran mai zaman banza ya zaunar dashi, sannan yasa hannunshi a aljihunshi ya dauki makullin motar, ya zagaya mazaunin direba yaja motar suka bar gurin, bayan ya d'agawa yarinyar hannu alamar sai wani lokacin, sannan yayi mata alamar jinjina da babbar yatsarsa.
[12/03 8:34 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!!*
*10)*
Ma6oyar da ya dad'e da tanada a wata sabuwar unguwa inda babu mutane domin wannan ranar kawai yakai Adon ya d'aureshi tamau, wani mugun d'auri yayi masa irin na huhun goro, ya d'aure mishi baki tamau, yasa babban gam ya k'ara nad'e mishi baki yanda ko ya dawo cikin hayyacinsa bazai iya ihu ba.
Hannyensa ya bank'aresu ta baya yasa igiya ya dauresu ya zagaya da igiyar ta cikinsa ya k'ara d'aureshi gam!
Wayar Adon ya dauko a aljihun wandonsa, ya dangwala yatsar Adon ta bude ya shiga gurin ai ka sak'o.
Ciyaman ya aikawa sak'o kamar haka
" *Dad ko ban samu dawowa gida tsakanin gobe da jibi ba karku damu, mun danyi nisan kiwo ne, zan dawo gobe da yamma ko jibi. I luv u Dad*"
Yana tura sakon ya kashe wayar gaba d'aya ya jefata a aljihunshi, ya fice daga gurin yaje ya kai motar ma6oyar da ya tanadar mata, inda baza'a taba tsammanin tana gurin ba.
Sai karfe goma sha biyu da rabi na dare ya samu ya koma gida.
A wannan ranar yayi barcin da ya dad'e baiyi irinsa ba tun rasuwar Umma da Fatima, har ya kusa makara sallar asubahi, ana idar da sallar ya sami dattawan Unguwar bayan sun fito sallah ya sanar dasu zaiyi tafiya zuwa Kaduna a ranar.
Akwai wani Kamfani da suka turo mishi da sakon yakai takardunshi na neman aiki.
Fatan alkhairi suka yi mishi da addu'ar Allah ya tsare hanya.
Yaje ya samu dangin Babanshi da na Ummansa suma ya sanar musu da hakan, addu'a sukayi mishi da nasihar ya rike kanshi, sannan suka kawo d'an kudi suka bashi da cewar ya k'ara na mota.
Godiya yayi sosai sannan ya koma gida ya hada kayanshi kala uku a cikin jaka, yana daf da ficewa daga gidan kiran wayar Dr. Zainab ya shigo cikin wayarsa.
A ladabce ya gaishe ta bayan ya dauki wayar, girmanta yake gani ba kad'an ba. Tun bayan rasuwarsu Umma take tausaya mishi, shiyasa take taimaka mishi da wasu abubuwan ba tare da ya tambaye ta ba, sau biyu tana kiranshi zuwa asibiti tayi mishi kyautar dubu biyar.
Ita ce ta fara bijiro mishi da maganar ya kamata su shigar da Chairman da Ado k'ara kotu ta bi musu hakkinsu.
A lokacin da take mishi maganar ce mata yayi su jinkirta zuwa lokacin da su Umma zasu cika kwanaki arba'in da rasuwa.
Shiyasa yanzu ta kira shi dan taji shawarar da ya yanke ita kuma tasan hanyar da zasu bullowa al'amarin.
"Kamal ya k'arin hakuri?"
Ta tambayeshi daga can bangarenta.
"Hakuri Alhamdulillahi. Nagode Dr. Allah ya saka miki da alkhairi"
"Ameen. Na kira ka ne inji zaka 6ullo asibitin ne yau? Ya kamata muyi ho66asa fa, kwanaki yana ta k'ara yawa. Akwai wata aminiya ta Barrister Safiyya da mukai maganar case din da ita. Ita ce zata tsayawa Fatima a kotu"
Wasu hawaye ne suke neman zubo mishi yayi k'umaji ya had'iye su, tunanin irin mutuwar da Fatima tayi ba karamin kunar zuciya yake saka shi ba. Guri ya nema ya zauna cikin nutsuwa ya fara mata magana
"Dr. Ni kam gaskiya in dan ta ni ne ki janye daga kudurin shigar da Ado k'ara"
"Saboda me?"
Ta tambayeshi da sauri.
"Dr. Ki tuna wanda shari'ar nan ta sha fa mana, dan gidan Chairman ne fa na karamar hukumar nan. Kuma Ado shine d'a mafi soyuwa a gurinshi, Kinga kuwa Koda zaiyi yawo tsirara sai ya fitar da danshi daga duk wani zargi. Ni kuma kinsan ba kudi ne dani ba.
Kuma bani da wata kwakkwarar hujja bayan abinda Fatima ta fada min akan Ado, kinga kuwa bayan bukatar kudi ana bukatar kwararan hujjoji kafin a samu nasara a shari'ar nan. Kuma yanda wasu daga cikin lauyoyi da alkalai suke gurbace a kasar nan saye su kawai zaiyi a saki d'ansa ni kuma in kwana a ciki"
Shiru tayi tana jujjuya maganganunsa a zuciyarta, tabbas maganarsa abar dubawa ce, amma bai kamata suyi kas a gwiwa ba. Akwai kwararan hujjojin fyaden da akayi ma Fatima a hannunta, kuma ta yarda da kwarewar Barrister Safiyya akan aikinta.
"Kamal ka sakawa ranka kwarin gwiwa, mu ke da Gaskiya in Allah ya yarda nasara tana 6angarenmu.
Kamata yayi ka shi go asibiti anjima mu karasa magana"
"Zan shigo amma saina dawo kaduna"
Ya fada mata kamar yanda ya fad'awa dattawan unguwarsu.
Fatan alkhairi tayi mishi ta nemi ya je ya karbi kudin mota kafin ya wuce.
Amsa mata yayi da zai biyo amma ba dan zai biya asibitin ba, yayi godiya suka yi sallama.
Kulle gidan yayi ya dauki jakar kamashi ya fice daga unguwar gaba daya.
Bai nufi Kangon da ya boye Adon ba sai da duhun dare ya shiga, yaje ya tarar dashi duk ya jigata ya fita a hayyacinsa, yayi kashi yayi fitsari duk a gurin.
Mugun murmushi ya sakar masa sannan ya aje jakarsa a gefe ya k'arasa kusa dashi, hannunsa yasa ya d'ago kanshi suka had'a idanu yace
"Ina fatan ka gane ni??"
A tsorace Adon yake kallonsa yana jujjuya kai, domin babu bakin magana
"To idan ma ka manta ni bari in tuna maka, ni ne dai Kamal, dodon nan naka wanda ya kusa kaika lahira a gaban idanun mahaifinka, wanda kuka dauke kanwarsa Fatima, kukai mata fyade mafi muni, sannan kuka lalata rayuwarta har ya zama sanadiyyar rayuwarta..."
Cije baki yayi zuciyarsa na kuna, domin sam baya san tunawa.
Wani k'aton dutse ya d'auko ya ajiye a gefe sannan ya fara k'ok'arin cire ma Adon wando yana fad'in,
"Dama na fad'awa Ubanka, duk ranar da ka sake shiga hanyar k'anwata tabbas saina maida kai Mata-maza, amma da yake shi dabba ne ya d'auka da wasa nake yi"
Jikin Adon ne ya fara karkarwa saboda tsananin tsorata, nan take zuciyarsa ta fara raya masa yanda akayi suka sace Fatima.
*Yarinyar ta dad'e tana daukar hankalin sa, ya biyo mata ta lallami da alkawarin kudade amma taki bashi hadin kai. Shiyasa suka shirya yanda zasu sato ta shi da abokansa. Ko da suka sace ta gidan gonar mahaifinsa ya kaita, ko kafin ya far mata saida wani abokinsa ya bashi maganin kara karfin maza, su uku suka sha shi da abokansa, sannan suka sha giya suka bugu kafin su far mata. Shi ya fara keta mata rigar mutunci, bayan sun daure hannu da bakinta abokansa suka bank'are masa kafafunta... Duk tsawon kwanaki ukun da tayi a gurinsu a kanta suke sauke duk gajiyar da suka debo...tun tana iya kuka da idanunta har ta koma bata iya komai sai ajiyar zuciya, sai numfashi da take iya ja a wahalce. Tsoron kar ta mutu a gurinsu yasa suka dauke ta cikin dare suka watsar da ita a kofar gidansu. Suka kara gaba zuciyoyinsu cike da nishad'i, ko d'ar babu wanda yaji a zuciyarsa.*
"Yauwa ka tuna ba?"
Kamal ya tambayeshi wasu zafafan hawaye suna zirarowa daga idanunsa.
Girgiza kai yake yi alamun A'a, yayi hakuri, amma ko sauraranshi Kamaluddeen bayyi ba, ya kamo abin fitsarinsa cike da rashin tausayi ya fara dandak'e ta da dutse.
Tsabar azaba da tsananin wahala yasa Ado sumewa, gashi babu bakin ihu, ansa tsumma an cushe bakin sannan aka maida gam aka nad'e, suman da yayi yasa Kamaluddeen ya kyaleshi har saiya farfad'o, domin so yake duk azabar da zai gana masa ya kasance idonshi biyu, so yake ya d'and'ani azaba fiye da yanda suka azabtar da k'anwarsa, ko tausayi ya fara Kawo mishi ziyarar bazata sai yayi saurin halartowa da zuciyarsa irin yanda sukai kaca-kaca da k'anwarsa, take saiya nemi tausayin ya rasa.
Tsawon kwanaki biyu da yini guda yana azabtar dashi, zuwa wannan lokacin ya suma sau goma sha tara.
Ya dandak'e abin fitsarinshi tsab! Sannan ya samu rodi mai tsatsa ya ringa tura mishi a takashinsa, duk tura rodi daya sai Ado ya suma saboda tsananin azaba da rad'ad'i, saida ha galabaitar dashi gaba-d'aya, ko ya suma ya farfad'o ma bashi da banbanci da sumammen, sannan yayi hurgi da rodin gefe guda, ya zauna yana maida numfashi, kallon Adon yake yi zuciyarsa cike da muguwar tsanarsa, ji yake har yanzu bai mishi rabin azabar da suka yiwa Fatima ba.
'Yar karamar wuka mai shegen kaifi ya d'auko a cikin kayansa, yayi masa kwaya-kwayan zane a fuskarsa irinna gobirawa.
A wannan lokacin Ado ya zama mutu-kwakwai rai kwakwai, saboda tsabar azabar da ya gana masa, ya tabbatar da wuya ya rayu ko da ya rayu ma zai rayu ne a wahalce da kuma tsananin jinya, har sai ya gwammaci mutuwa akan rayuwarsa.
Had'a kayanshi yayi ya kara gaba, zuciyarsa fes! Kaduna ya nufa kamar yanda yayi alkawari, bayan ya d'auko wayar Ado ya turawa Ciyaman sak'on kwatancen inda zasu sami Adon, da kwatancen inda zasu d'auki motarsa, sannan ya zare layin wayar ya karya ta.
Yana isa Kaduna yaje kasuwa ya nemi masana waya ya bada wayar aka goge komai da yake kanta, sannan ya saida ita ya amshi kudin, da yake waya ce irinta masu gata a lokacin.
Wani abokinsa da sukayi karatu tare ya nema yaje gidansu, yace ya shigo Kaduna ne shiyasa ya neme shi dan su gaisa, shi abokin nasa da yake yana da kafa har ya samu aiki.
Abokin nasa mai suna Ibrahim yaji dadin zuwansa kuwa, domin bai manta irin taimakon da Kamaluddeen din yayi masa a lokacin da suke karatu ba, shiyasa ya rike shi saida yayi mishi kwana biyu.
Sun zagaye garin Kaduna sosai, Kamal yaji dad'in wannan ziyara, har kumari yayi, yai shar dashi, domin a yanzu cikin kashi dari na damuwarsa sittin ya ragu, sai abinda baza'a rasa ba.
Kwananshi hudu da barin gida sannan ya nufi Kano, da kyakkyawar albishir d'in da Ibrahim yayi masa, na cewar ya dawo da takardunshi nan da sati biyu, in sha Allah zai mishi hanyar samun aiki.
[13/03 11:20 PM] fareedah: *BARA A KUFAI*
*11)*
A lokacin da sak'on ya iske shi baya garin Kano, yayi sammakon zuwa Kaduna a ranar, shiyasa ya kira wayar DPO hankalinshi a tashe yayi masa forwarding din sakon.
Bayan awa daya Hajiya Kaltume mahaifiyar Ado ta kira shi tana kuka, tana sanar dashi duk inda yake yayi gaggawar dawowa, Allah yayi wa Ado rasuwa.
Ai bai tsaya yin abinda ya kaishi kadunan ba ya kira direbansa, a d'ari biyu suka juya Kano, sai zafgawa direbar masifar yai sauri yake yi, Allah ne ya taimake su suka isa lafiya.
Asibitin da yake suka wuce kai tsaye, tun kafin motar ta daidaita tsayuwa ya bude murfin k'ofar ya fice, ya nufi cikin asibitin kamar zai kifa k'asa saboda sauri.
Yana shiga yayi arba da DPO a tsaye shi da wasu 'yan sanda guda biyu yana musu bayani. Gurinshi ya nufa kai tsaye jikinsa ba inda baya kyarma.
"Honorable barka da dawowa"
DPO ya fad'i haka yana mika mishi hannu dan su gaisa.
"Ina d'ana yake? Kaini ofishin likitan da yake kula dashi"
Suna shiga ofishin shi kuma likitan yana kokarin fitowa, amma ganinsu yasa ya koma cikin Ofis din
"Ya jikin d'ana?"
Ya tambaya bayan ya kwalalowa likitan idanu, ko zama ya kasa yi.
"Sai hak'uri Honorable, Allah yayi mishi rasuwa d'azunnan"
Likitan ya fad'a cike da tausasa murya.
"Me yayi sanadin mutuwarsa?"
Ya sake tambaya cike da karfin hali, hankalinsa a mugun tashe, k'iris yake jira ya fashe da kuka.
"Kisan gillah akayi mishi, an yayyaka mishi fuska da wuk'a, kuma da alamun anyi kwanaki biyu zuwa uku ana gana mishi azaba, dan wasu raunukan a jikinshi sunyi awa ashirin da hud'u ko ma fiye da hakan.
Kuma tun yana da rai, anyi amfani da dutse gurin dandatse mazantakarsa, sannan aka samu rodi aka ringa tura masa a duburarsa.."
Nan take jikinshi ya fara kyarma, runtse Idanunshi yayi da karfi yana jin Saukar maganganun likitan a cikin kwakwalwarsa, tsawon lokaci yana a wannan halin, kamar ma bazai iya magana ba.
"Muje inga gawarsa"
Ya fad'a cikin karfin hali, sannan ya nufi hanyar ficewa daga Ofis din da sassarfa, zuciyarsa na suya da tafarfasa.
A kofar d'akin da gawar yake, ya tararda Hajiya Kaltume da Zahra karamar 'yarsa, kanwar Ado sun had'a kawunansu da bango sai rusa kuka suke yi, Zahra tana ganin shi ta k'arasa da gudu ta rungume shi, ta sake fashe wa kuka
"Daddy... Sun kashe mana Yaya..."
Runtse idanu yayi ya karkata bakinshi bangare daya kamar zai tashi aljanu, jin kalmar an kashe Ado, d'a mafi soyuwa a zuciyarsa wani matsanancin bakin ciki da takaici yake saka shi, bakinsa sai rawa yake yi.
Janye ta yayi daga jikinshi, ba tareda ya iya furta mata komai ba yabi bayan likitan zuwa cikin d'akin.
Wani d'an k'aramin mahaukaci ya zame musu lokacin da yayi arba da gawar Ado.
"Wayyo.. Wayyo... wayyo Allah na... Ado wa yayi maka haka? Wallahi saina kashe ko waye, ko da kuwa duk abinda na mallaka zai k'are... Dan Allah ka tashi.. Ado.. Ado.."
DPO ne yaje da sauri ya rirrik'e shi ganin yanda yake ta wujijjiga gawar yana neman fad'o dashi daga gadon asibitin.
Da k'yar aka samu ya natsa ya ciccike wasu takardu, sannan aka basu gawar suka tafi da ita gida.
Ko kafin a sallaci gawar Adon sambatu kawai yake yi, manyan abokansa suna ta mishi nasiha da kalamai na kwantar da hankali.
Dukda munanan halayen Adon da yayi tambari a Unguwar, gawarsa ta tara mutane masu matukar yawa, ba don komai ba sai don Babanshi yana da k'unban susa, kuma ana sa ran za'a k'ona hannu gurin zaman makokin.
Wannan Zamani namu kam sai addu'a, banbancin jama'ar da gawar mai kudi take tarawa daban yake da na talaka, shi talaka ansan sai dai a sallace shi don Allah, ko an dawo babu abinda za'a samu.
Shi kuwa mai kudi ana ganin zaman makokin nan da za'ayi an huta da cefanen abinci, kyakkyawar ci da sha duk za'a samu a cikin kwanakin. Ya Allah ka shirye mu.
Ana dawowa mak'abartar kuwa aka fara firfito da manyan kuloli na abinci, da ruwar roba da lemu kala daban daban, nan take aka fara rububi hannu baka hannu kwarya, duk yawan mutanen nan saida suka ci suka ture, domin kafin wannan kulan ya kare za'a sake fito da wani kular.
A can cikin gida kuwa Chairman yana cikin matsanancin hali, ya gama hak'ik'ancewa wannan fitsararren yaron Kamaluddeen shine ya kashe mishi d'a, domin kuwa yayi ikirarin muddin ya ta6a kanwarshi sayya maida shi mata-maza.
A karo na biyu kuma ya sake tabbatar mishi muddin wani abu ya samu k'anwarshi to saiya kashe shi, ya samu labarin rasuwar yarinyar da rasuwar Mahaifiyarsa tun a wancan lokacin, da farko yayi tsammanin yaron zai dauki wani mataki, amma sai yaga har an cinye kwanaki talatin yaron baiyi wani motsi ba, shiyasa ma ya sakankance.
Ashe kwanton 6auna yaron yayi mishi. Lallai ya kamata ya koya mishi hankali, tabbas zaisan ya ta6o tsuliyar dodo. Sai a wannan lokacin wani kuka mai tsananin k'arfi ya taho masa, dan haka ya d'ora hunnu akai ya fashe da kuka da hawaye shar kaman an bude fanfo.
[14/03 9:54 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!!*
*12)*
Tun bayan dawowarsu daga makabarta yayi wa DPO umarnin duk inda Kamal yake lallai a kamo shi a gark'ame shi, domin shi ke da alhakin kashe mishi d'a, kamar yanda suke dashi rubuce a cikin file dinsu a wancan lokacin da yasa suka kama yaron.
Shigowar DPO cikin falon shi ya katse mishi kuka da tunanin da yake yi, ya d'ago da jajayen idanunshi yana kallonshi, sai sauke ajiyar zuciya da jan majina yake kamar k'aramin yaro, har DPO ya nemi guri ya zauna idanunshi kyar a kansa.
"Yallabai!! Duk inda muke tunanin zamu samu yaron nan fa munje bamu same shi ba, amsa d'aya muke samu daga gurin 'yan layin nasu, wai ya tafi Kaduna tun kwanaki biyar da suka wuce.."
"Karya ne.."
Ya katse shi da murya mai cike da hargagi.
"6oye shi sukayi dan sunsan dole zan sa a kamo shi, DPO duk inda ya shiga ina bukatar ku nemo minshi, kisa mafi muni nake so inyi mishi, dole sai ya d'and'ani irin azabar da ya ganawa Ado kafin ya mutu, zaisan ya tabo wa kanshi balbalin bala'i"
Ya k'arasa fad'in haka bakinshi na kumfa, saboda tsananin fusata, zuciyarsa k'una kawai take yi, baik'i ya rufe ido ya bud'e yaga Kamal a gabanshi ba, tabbas da saiya mutsutstsuke shi kamar wulak'antaccen k'waro.
"Yallabai wannan karon akwai matsala fa"
DPO ya fad'i haka yana murza gashin bakinsa. Bai jira cewarsa ba ya ci gaba da cewa.
"Ko da muka je nemanshi matasan layinsu taso mana suka yi kamar zasu cinye mu d'anye, suna fad'in lallai idan muka kama shi sai sun k'ona gidan ka sannan su k'ona ka da ranka, saidai duk abinda hukuma zata yi tayi musu"
Zaro idanu yayi yana kallonshi, babu abinda ya tsorata shi irin cewar da akayi za'a k'ona shi da ranshi, shi da yake burin daga Chairman ya fito takarar d'an majalisar jiha idan aka k'ona shi ya mutu a ina zaiyi takarar?
"Yanzu miye mafita DPO? Domin bana so yaron nan ya k'ara ko kwana daya a raye ba tare da na turashi inda ya aika Ado ba"
Wani mugun murmushi yayi yana tand'e gefen baki irinna miyagun 'yan sandan da suka saba kar6ar cin hanci.
"Mafitar guda biyu ce Yallabai, ta farko shine ka shigar da yaron k'ara kotu kana tuhumarsa da kashe maka d'anka.."
"Ina daya mafitar? Dukda nasan idan na shigar dashi k'ara duk tsawon lokacin da shari'ar zai dauka nine mai nasara Amma bana bukatar zuwa kotu, duk harka ce ta bata lokaci. Nafi so tsakanin yau da gobe in d'auki matakin da dace"
"Mafita ta biyu zata tabbata ne matuk'ar zaka saki kud'i Yallabai"
"Kamar nawa ake bukata?"
Ya tambaye shi ba tare da wata shakka ba.
"Ko Miliyan biyu biyu ka bada sai ayi maneji da ita Yallabai"
"Zan k'ara maka da dubu dari biyar akan miliyan biyun, matuk'ar ka kawo min gawar yaron nan Kamal"
"Ni kuma zan tabbatar aikin ka ya tafi yanda kake buk'ata, sannan zanyi da takatsantsan yanda ba za'a ta6a gane da hannunka a cikin kisar shi ba, balle har siyasarka ta ta6u a gurin abokan hamaiya"
"Good point DPO, ka tuna min.
Bana bukatar 'yan uwanshi su sami ko da gawarshi ne, kai ko labarin kashe shi ma bana so su samu domin babban abin zargi a gurinsu ni ne. Ina so kayi mishi kisan wulak'anci, mafi munin wulak'anci, sannan ka 6atar dashi, inda ko kusa bazasu ta6a samunshi ko labarinshi ba. Su kasance kullum cikin dakon dawowarshi ba tare da sun san ya tafi kenan har abada ba.
Kaga idan kayi haka babu ta yanda za'ayi su zarge ni, balle har su yayata 'yan adawa su sami abin yarfe a gare ni"
"Ka sa a zuciyarka aikinka ya kammala Yallabai"
Jinjina kai yayi, ya saki wani mugun murmushi, sai a wannan lokacin yaji sauk'in damuwarsa.
A take ya rubutawa DPO cheque na naira miliyan daya da rabi, sannan yayi mishi alk'awarin aiki yana kammala aikin zai bashi cikon miliyan d'aya.
Da haka suka rabu, ya tashi ya fito gurin abokansa da suke Zaman kar6ar gaisuwa a d'akin ganawa da bakinshi.
********