*CHAPTER Twenty Eight*
________🎓Yana tura ƙofan Halwa tabuɗe idanun ta, dama tun ɗazu bata yi barci ba tunani ya cika mata zuciya
Jin ya nufo wajen gadon sai tasake Rufe idanun ta tana sauraron bugun zuciyar ta dake sake hauhawa
Ajiyan zuciya yasauke lokacin da ya'iso bakin gadon yasami waje yazauna, fuskarta yake kallo kasancewar Facing ɗin sa take yi kuma da hasken lantarki da yakunna shigowar sa, yasan ba barci take yi ba don haka yace
"Tashi zaune muyi magana".
Runtse idanuwan ta tasake yi, sai kuma ahankali taware su kan bayan sa da yajuya mata, tashi tayi tazauna tana sake jawo bargon jikin ta duk da ba wai ta saka kayan barcin me nuna tsiraici bane, sai dai kasancewar yanda yalafe a jikin ta ana ganin komi, gashi kuma rigan iyakan ƙasan gwiwan ta yatsaya
Shima gyara zaman sa yayi sosai yana fuskantan ta
Kanta a ƙasa tana jiran abinda zai biyo baya, sai dai shiru yaƙi yin magana, ita kuma ta kasa ɗago kai bare ta kalle sa sabida tasan idanun sa na kanta
Zuba mata idanu kawai yayi yana kallon ta, jujjuya maganar da yake son furta mata yake yi a zuciyar sa, sai da ya ɗan ja lokaci kafin yafesar da numfashi yabuɗe baki yasoma magana
"Halwa". Yakira sunan ta a hankali
"Na'am". Ta'amsa masa batare da ta ɗago kanta ba
Hannayen sa yahaɗe waje ɗaya kafin yace "Da farko dai ina so in baki haƙuri agame da zamantakewar da mukayi abaya, sabida yanda na nuna miki halin ko in kula a matsayin ki na Matata, duk da ba wai nayi hakan a son Raina bane, har a cikin zuciyata ina jin zafin abubuwan da nayi miki, don Allah idan na ɓata miki ki yafe min yanzu ina so mu gyara zaman auren mu ne shiyasa nake so mu soma fahimtar juna a yanzu ɗin".
Lumshe idanuwan ta tayi hawayen da suka soma sintiri a fuskarta tun soma maganar sa suka ci gaba da tsiyaya, wani irin sanyi ne yake ratsa ta har cikin zuciyarta, har a yanzu ɗin ma bata ɗago kanta ba tace dashi
"Yaya Khalil wlh baka yi min komi ba, idan ma har kayi min to na yafe maka domin ban taɓa kallon ka matsayin me cuta min ba".
Tattausan hannayen ta yariƙo cikin nasa wanda sai da yasaka suka ji tsigan jikin su ya tashi, domin hakan ba wai ya taɓa faruwa bane dasu, fatar jikin junan su be taɓa haɗuwa waje ɗaya ba
Sauke ajiyan zuciya yayi yana ƙara damƙe hannayen nata, idanun sa kafe akanta duk da ba wai kallon sa take yi ba, sannan yasoma magana
"Duk da bansan cewa kina sona ko baki sona ba but ina me neman alfarma ki bani dama a cikin zuciyar ki, Ni kuma zan koya miki ƙaunata sannan nayi miki alƙwari zan faranta miki da iyawa ta, sannan duk abinda ke faruwa naji komi wajen Dad".
Shiru yayi yana jan numfashi sabida jin wani kishi ya turniƙe shi tunawa da wani banza shi yasoma ɓata wa Halwan sa rayuwa, ɗan daidaita muryan sa yayi yace
"Ina so in ƙwato miki haƙƙin ki wajen tsinannen mutumin da yaruguza miki rayuwa".
Yanda yayi maganar cikin wani irin murya da dole ne kagane tsananin kishin sa, duk da kuwa ya daure sosai wajen dai-dai ta muryan nasa, hakan yasa taɗago kai akaro na farko tazuba masa idanu, bata yi tunanin wai ko wannan maganar yake son faɗa ba koda yace mata yaji komi wajen Dad, cikin sanyin murya tace
"A'a Yaya Khalil abinda yawuce ya rigada ya wuce, duk da ada Ina da burin ɗaukan fansa amma yanzu tuni na cire hakan a raina, Husna yanzu ta zama mallakin Saleema na bata ita har abada.."
Katse ta yayi da faɗin "duk da haka dole ne na ƙwato miki haƙƙin ki, Ni lauya ne ke kuma Matata ce, taya kike tunanin zan iya barin wanda yataɓa yin ma Matata Fyaɗe batare da na ɗau mataki ba? Ba wai mayar masa da Husna za'a yi ba but dole ne Kotu ta yanke masa hukuncin abinda yayi, na rigada na gama bincike a kansa zuwa kwana biyu da yardan Allah zan miƙa Case ɗin kotu".
Wani irin farin ciki me haɗe da kuka ne suka taho mata, ko kaɗan ta kasa ɗauke idanun ta akansa, sai dai ta matse bakin ta gamm ta hana kukan nata fitowa illa hawayen dake ƙara sintiri saman fuskarta tare da murmushin farin ciki dake gudana
Kazalika shima kallon nata yake yi, yayinda yasauya riƙon da yayi wa hannayen ta yana murza mata su a hankali yana jin ƙaunarta na ƙara shiga zuciyar sa tare da ƙara girma sosai, yana son yafaɗa mata sirrin dake ransa sai dai kuma baya son yasanar da ita da baki illa a aikace, don haka yabata umarnin tamiƙe tasauko su gabatar da Sallah kamar yanda ko wanne ma'aurata suke yi
Hakan kuwa yafaru, ita tasoma yin alwalan tafito tasanya Hijab tazauna zaman jiran sa
Shi kuma sai da yayi wanka sannan yafito da alwalan sa, doguwar riga kawai yazira suka ta da Sallah, har suka idar yayi musu dogon addu'a inda daga nan kuma yafice zuwa kichen yaɗauko Plates da Spoon yasake kazan da Saleema taba shi, sai da yagama dai-dai ta komi sannan yayi wa Halwa magana akan tasauko su ci, don ita tuni ta haye kan gado tana lissafi cikin zuciyarta, tayi mamaki da ganin abinda ke gaban sa wanda hakan yatabbatar mata ya shirya ma daren, duk da ko kaɗan bata ji ƙamshin ba sa'ilin da yake sake wa illa motsin leda da take ta faman ji kuma bata yi tunanin dashi yazo ba
Babu musu tasauko duk da bata jin yunwa, amma kuma zuciyarta bata ba ta shawaran musa masa ba ko dan faranta masa da take son Yi, domin kuwa ta ɗau alƙawari faranta masa sosai a daren nan ta yanda zata nuna masa godiyar ta a duk kan komi da yayi mata kuma yana shirin sake mata wajen ƙwato mata haƙkin ta
Bata wani ci ba, shima haka ɗin, ita ta tattare komi zata kai kichen yadakatar da ita yakwasa yamayar
Kafin yadawo har ta shiga ta wanke bakin ta, yana shigowa tana fitowa sai tanufi kan gado tahaye
Shima ɗin Toilet ɗin yashiga, babu jimawa yafito yanufi gaban mirror, anan yagama shafe-shafen sa tamkar wani mace, sai da yabi ko ina nasa da turaruka kafin yakashe wutan yanufi kan gado ya haye...
A wannan dare Khalil da Halwa sun raya sa ne cike da farin ciki da annashuwa, tare da soyayya me tsayawa a rai ga duk kanin su, wanda tuni ko wannen su ya sanar da ɗan uwansa sirrin dake cikin ransa batare da sun an kare ba, har gabanin asuba kafin suka yi barci manne da juna tamkar zasu maida junan su ciki. 🤦🏻♀️🙄
*****
Washe gari a makare suka tashi dukan su, don lokacin ƙarfe 07:38am. Ne, Sallah suka gabatar a gurguje, suna idarwa Halwa tasake nannaɗe wa akan gadon don barci ne sosai a idanun ta tunda basu samu sun yi ishashshe jiya ba
Khalil kuwa shirin Office yayi a gaugauce Cuz lokaci ya ƙure masa, gashi babu daman zama agida tunda yana tsaka da soma wani Shari'a ne aiki yayi masa yawa sosai
Koda yagama shiryawa wajen gadon yanufa yasakar wa Halwa kiss a kumatu sannan yaƙara mata a goshin ta, yashafa kanta yana murmushi ganin yanda take yamutsa fuska tana gyara kwanciyarta,
Sosai idan tana yamutsa fuska take masa kyau ainun, ya kula hakan ya zame mata ɗabi'a ko da yaushe sai tayi
Gyara mata Bargon yayi yasake rufe ta yafice dasauri riƙe da briafcase ɗin sa, ɗakin Saleema yashiga sai dai babu ita ciki, har Toilet ya leƙa be ganta ba don haka yafito Direct yanufi kichen
Tana ciki kuwa tana haɗa musu Breakfast, daga ita sai doguwar riga iya cinya da gajeren wando baƙaƙe, sai hula me raga-raga shima baƙi tasaka a kanta, kasancewarta fara sai kayan sukai mata kyau suka sake haskata sosai
Ƙamshin turaren sa shi yasanar da ita zuwan sa, juyowa tayi dai-dai lokacin da ya'iso gaban ta idanuwan su suka haɗe waje ɗaya yayinda suka sakar wa juna murmushi
Ita tasoma gaishe sa, ya'amsa mata cikin fara'a yana janyo ta jikin sa, sannan yatambayi lafiyan ta da yanda tatashi
Murmushi tayi cike da tsananin ƙaunar sa aranta ta'amsa masa da "alhmadulillah Mijina, da fatan ƴar uwata tana ƙoshin lafiya?"
Sai da ya ɗan ja numfashi idanun sa na kanta yace "Lafiya ƙalau tatashi, but yanzu ta koma barci ne".
Narke fuska tayi tace "amma kuma baka yi Breakfast ba zaka tafi?"
"No sauri nake yi ina da aiki a Office in naje zan yi a can, ki kula min da kanki, Allah yamiki albarka".
Yamatso da bakin sa yasakar mata kiss a libs ɗin ta, har ya janye bakin sa sai kuma yamaida yahaɗe bakin su yayi socking na tsawon sokonni biyar kafin yajanye bakin sa, idanun sa yazuba mata yana kallon ta yayinda talumshe nata idon cike da tsananin shauƙi
"I Love You so much". Yafaɗa ahankali still yana kallon ta
Buɗe idanun ta tayi suka shige cikin nasa, yau ne ranan farko da ta iya juran kallon cikin idanun sa har na tsawon wasu mintuna batare da ta janye ba, tsantsan farin ciki ne yacika ta har takasa motsawa bare tasauke idanun nata har tafurta wani kalma
Murmushin sa me kyau yasaki yana saka hannu yaja hancin ta domin sosai yagane bata cikin tunanin ta a lokacin
Ɗan ƙifƙifta idanuwan ta tayi kafin tace "I Love You too My husband".
Sai kuma takau da kai tana murmusawa
Hannun sa yaɗago yakalli agogo kafin yasake kallon ta yasakar mata Peck a goshi yace "na tafi Byeee ki kula kinji".
Gyaɗa masa kai tayi sai kuma tace "Allah yatsare yadawo da kai lafiya".
"Ameen". Ya'amsa ta yana juyawa yafice dasauri
Ta daɗe tsaye a wajen tun fitan sa batare da tayi yunƙurin yin wani abu ba, in banda murmushi babu abinda take sakar wa, sai da tagaji don kanta kafin tajuya ga Ruwan zafin da take tafasawa, lokacin tuni ya tausa har ya gaji, dasauri tazuba citta da kanumfari a ciki, sai tasaka Lipton taƙara ruwa don ya gama ƙonewa, rufewa tayi taci gaba da sauran aiyukan ta
Cikin mintuna ƙalilan tagama komi sannan takwashe takai kan dainning, daga nan ɗaki tawuce tasillo wanka tashirya cikin jan atamfa me ratsin ruwan hanta, ɗinkin doguwar riga me hannun fanka, sosai rigan tabuɗe daga ƙasa kuma tayi mata kyau ainun, sai taɗaura ɗankwalin normal tayi Light makeup da yaƙara fito da ita sosai
Parlour tanufa da waya a kunne suna gaisawa da Ummi da takira ta.
Bata daɗe da zama ba itama Halwa tafito, har tayi wanka ta shirya cikin ƙananun kaya 🍑Baby Peach colourn riga da Skert, rigan me santsi ne da dogon hannu da aka saka bottles, tana da coller sannan kuma shara-shara ne domin har farar Vest ɗin da tasaka a ciki ana gani, skert ɗin kuma me Robber ne me ƙaramin tsagu ta baya dack peach colour, sai tasaka baƙin ɗankwali taɗaure kanta tare da zagaye gashin ta da ta taufke a tsakiyar kai
Masha Allah tayi kyau sosai duk da bata yi kwalliya ba, sai dai ta saka Powder da kazal a idanun ta, fuskarta sai fitar da annuri yake yi tana ƙyallin amarci, kallo ɗaya kayi mata zaka san tana cikin farin ciki da walwalan da yakasa ɓoyuwa a face ɗin ta.
Lokacin da ta'iso Saleema ta gama wayan takalle ta tana murmushi tace "Ƴar uwa kinyi kyau sosai wlh, wannan ƙamshi da kike yi haka kowa yaganki ya ga Amarya?"
Dariya Halwa tayi lokacin da tasami wuri kusa da ita tazauna tana faɗin "kai Sister ban da sharri".
"Wlh dagaske nake yi, baki ga sai shaining kike yi ba, halan baki kalli madubi bane?" Saleema tasake faɗa tana tsatstsare ta da idanu ta sigan tsokana
Hararan ta Halwa tayi tace "Uhm to Ni dai ban gani ba gaskiya".
Saleema tace "to ina ga idanun ki ne, amma dai bari Barrister yadawo sai ya bambance mana gaskiya, yanzu tashi muje mu yi Breakfast dama yanzu nake Shirin kiran ki".
Tashi suka yi suka nufi wajen dainning ɗin inda Halwa tuni ta sauya hiran nasu.
Da rana da Khalil yadawo be jima ba yasake fita, sabida yace musu akwai abinda zai je yayi ba zai dawo ba sai dare, don haka su kaɗai suka zauna suka buɗe shafta suna ta hira
Da yamma sai ga Larai ta kawo Husna da Ahmad, Murna wajen Saleema kamar me, tsaban murna har rawa ta dinga yi tana shilla Ahmad tana cafewa shi kuma yana wangale mata wawulan bakin sa
Ai itama Husna sai tasaka mata kuka akan ba'a ɗaga ta ba
Me su Halwa zasu yi ita da Larai in ba dariya ba, sai suka koma tonon Saleema ɗin ganin yanda take ta nishi daƙyar taɗaga Husna dake mata kukan taɓara tana cewa "ita be ishe ta ba a ƙara ɗaga ta" yarinyan sai uban wayau kamar me
Shi dai Ahmad tunda aka kwantar dashi kan kujera wasan shi yaci gaba da yi don be san ma me suke yi ba
Basu bar Larai ta tafi ba sai da takai musu har magriba sannan tawuce gida.
[1/19, 6:29 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Twenty Nine*
________🎓 *ONE WEEK AGO*
Suna zazzaune akan dainning table suna yin breakfast wayan Haris tayi ƙara, sai da yakai Cofin shayin sa baki yakurɓa kafin yakalli wayan, ganin sunan Dady yafito ɓaro-ɓaro sai yayi saurin ajiye Cup ɗin yana kai hannu yaɗauki wayan tare da yin peacking yana karawa a kunne
"Aslm alaikum Dady.."
"Eh Dady ban fita ba but yanzu zan fita".
"Ok to".
Cire wayan yayi daga kunnen sa yaɗau tissue yana share bakin sa, be ce komi ba sai da yamiƙe yajanye kujeran da yatashi sannan ya dube su yace
"Ni zan wuce but bazan dawo ba yau sai zuwa dare insha Allahu sabida akwai inda zan je".
Miƙe wa Zubaida tayi don ta rakasa, yayinda Fahima tayi masa adawo lafiya tana ci gaba da breakfast ɗin ta
Har bakin ƙofan Parlour takai sa kafin tamiƙa masa briafcase ɗin sa suka yi sallama yafice
Mota yahau sai Family House ɗin su domin amsa kiran Dady da yayi masa.
Bayan ya shiga da motan sa tanƙamemen gidan nasu wanda yakasance me tsananin kyau da burge wa, duk da iyayen sa kaɗai ne agidan ada, but a yanzu Daddyn nasa ya dawo da ƙannin sa biyu da iyalan su suna zaune agidan, kasancewar su kaɗai Allah yaba ma iyayen su that's why mahaifin Haris ke ji dasu sosai, shiyasa da yadena siyasa a yanzu sai yagina wannan tanƙamemen gidan kuma yayi musu umarnin dawowa kowanne da nasa Part ɗin.
Fitowa yayi a motan yanufi cikin gidan, koda yashiga parlour'n; Daddyn sa ne da Mamyn sa zaune cikin damuwa, shi kansa Haris da yashigo ya tabbatar ba lafiya ba ganin yanda sukai tsamo-tsamo fuska duk babu walwala, gaishe su yayi suka amsa masa
Dady ne yadube sa fuskan sa da damuwa yace, "Haris".
"Na'am Dady". Ya'amsa masa ahankali yana kallon sa
Numfashi yaja kafin yace, "wacece Halwa?"
Wani irin bugawa gaban Haris yayi jin sunan Halwan, still sake tsatstsare Dadyn da idanu yayi ya kasa furta komi
"Kayi shiru ina magana?"
"Alhaji na fa faɗa maka kamar yarinyan nan ce da yayi haukan son ta har yakwanta a Hospital". Cewar Mamy idanun ta na kan Dadyn
Jinjina kansa Daddy yayi kafin yaɗauki Envelope ɗin dake kusa dashi yamiƙa wa Haris batare da yace uffan ba
Hannu na rawa Haris yasaka hannu kamar zai amsa sai kuma yatsai da hannun nasa yana cewa "Dady menene?"
"Abun da ka shuka ne yake son bibiyan ka Harisu, ashe dama Ciki kayi wa ƴar mutane har da rabon ɗiya atsakanin ku? To ka amsa gashi nan sun maka ka a kotu domin ƙwato mata haƙƙin ta".
Amsar Envelope ɗin yayi yaciro yasoma warware wa, sai da yagama karanta abinda ke ciki kafin yakalli Dad idanun sa cike fal da hawaye, ba komi yasaka shi shiga wannan yanayin ba sai famo masa gyambon da akayi, hakan na nufin cewa da rabon yasake ganin Halwa a rayuwarsa?
Murmushi yasaki me haɗe da hawaye, gaba ɗaya tsaban farin ciki ya kasa yin magana
Sai da Mamy tace, "Haris kayi magana mana kayi shiru, shin cikin ka ne ko kuwa?"
Cikin zumuɗi yakalli iyayen nashi yace "Wlh nawa ne, yarinyan da nake ta nema shekara da shekaru yau sai gata zan same ta cikin sauƙi, don Allah Dady kafaɗa min aina take yanzu inje inga ɗiyata, ina son ganin ta Dady har yanzu ina ƙaunar Halwa araina, Please Dady kashige min gaba wajen nema min auren ta, na yarda Wlh zan aure ta in dai sabida hakan ne zasu kai Ni kotu".
Baki sake suke bin Haris da kallo ganin yanda yakoma kamar zautacce
"To kai ban da abun ka ina zan ga yarinyan tunda ba ita ce tazo takawo takardan ba? daga kotu aka aiko don haka sai mu jira zuwa nan da Monday ɗin kamar yanda aka rubuto, yanzu abinda zaka yi kaje wajen Brr. Musbahu kuyi magana Idan nadawo zuwa gobe sai mu san abun yi".
Marairaice fuska Haris yayi yace, "Dady please asan yanda za'a yi anemo gidan da suke wlh bazan iya zama har zuwa Monday kafin in gansu ba".
Mamy tace, "To ya kake so ayi ne Haris? Kabari mana zuwa goben kamar yanda Daddyn ka yafaɗa, Ni kaina tun kafin naga yarinyan naji ƙaunar ta araina, wlh Ni farin ciki nayi gwara da suka miƙa case ɗin Court adawo mana da Jikar mu kusa damu tunda cikin naka ne".
Washe baki Haris yayi yace, "Ai Mamy nasan da cikin tun sanda iyayen ta suka kore ta, kuma na neme ta but ban same ta ba SHINE SILAN ciwo na".
Girgiza kansa Dady yayi yace "na ga alamu ko kunyan mu baka ji Haris, don baka ji nace zan hukunta ka ba ko?"
Sunkuyar da kansa yayi yana sosa ƙeya fuskar sa cike da murmushi Mamy ma na taya sa
"To je ka wajen aiki lokaci na ƙure wa, amma kasamu ku haɗu da Brr. Musbahu kaji ko?"
"To Dady". Haris ya'amsa masa yana miƙe wa tsaye
Sallama yayi musu yafice dasauri yana duba agogon hannun sa.
Maida idanun sa ga Mamy yayi yana cewa "kin gani ko? Abinda muka ja wa kan mu kenan silan sangarta yaron nan, da yanzu ban dena siyasa ba shikenan haka za'a ɓata min suna".
"To ya zamu yi Alhaji? yaro ne ka haife sa yanzu baka haifi halin sa ba, Ni ina ga ko da bamu sangarta sa ba dama zanen ƙaddaran sa ne haka, gashi abinda muka rasa muna fatan samu ashe da rabon zamu samu, wlh Ni har na ɗebe tsammani akan zan ga yaran Haris".
Murmushi Dady yayi yace "ban da abun ki duka-duka nawa Haris ɗin yake don be samu haihuwa ba har yanzu zaki cire tsammani? Ni ina ga saboda saka ran da muka yi ne shiyasa muke ƙosa wa, tunda dama matar sa ta taɓa ɓari bare muyi tunanin shine me matsalan, yanzu tunda yace "har yanzu yana ƙaunar yarinyan" kinga sai mu aura masa ita tazauna da ƴar ta, kin ga haɗo min kayana in tafi kar inyi late".
"To shikenan Alhaji Allah yasa mu dace dai". Tayi maganar tana miƙe wa don bin umarnin sa.
**** **** **** ***** *****
Abun zai baku sha'awa zaman Halwa da Saleema, sun ɗau kansu tamkar ba Kishiyoyin juna ba, kamar yanda kuka san suna zaune a baya haka yanzu ɗin ma suka ci gaba da zama da junan su, su kansu suna manta cewa Miji ɗaya suke aure bare har suyi kishin juna, ƙaunar da suke wa juna ƙauna ce ta tsakani da Allah
Shi kansa Khalil yana matuƙar alfahari dasu da jindaɗin kasancewar su mata a gare shi ganin yanda suka haɗa kansu fiye da Da, komi tare suke yi basu banbanta komi a tsakanin su, baza ka taɓa gane wanene me girki ba sai idan dare yayi wajen kwana, shine Khalil zai shiga ɗakin wacce take dashi, gyaran gida, girki, komi da komi tare suke yi, zaman su sai son BARKA, sai dai muyi musu fatan ɗaurewa ahaka. 😅
Yau ma Halwa ce tatambayi Khalil ɗin zuwa gidan su, domin tayi ƙudurin zuwa musamman don ganin Mama da kuma Zainab ƙawar ta, akoda yaushe suna ranta shiyasa yau tatambaye shi
Khalil be yi mata musu ba ya amince, duk da yaso yabi su sai dai aiki sunyi masa yawa, ga cases da yake dasu ciki kuwa har da nata, yanzu be da lokacin zama agidan ma
Saleema cewa tayi zata bi ta don haka suka yi shiri tare, kaya iri ɗaya suka saka, Jan Material Less ɗinkin riga da Skert, har da Gyalen da suka saka White colour da takalmin ƙafafun su iri ɗaya ne
Tubarakallah Masha ALLAH sun yi kyau matuƙa, kallo ɗaya kayi musu zaka san hankalin su akwance yake, in banda ƙyalli da ɗaukan ido babu abinda suke yi
Kasancewar yau Saturday Husna bata je school ba don haka har dasu aka shirya cikin kayan su masu tsananin tsada wanda yayi musu kyau ainun, duk wanda yaga yaran sai sun bashi sha'awa
Saleema da kanta tayi musu dreving, Halwa tazauna gefen su tana riƙe da Ahmad, yayinda Husna take zaune a baya.
Tunda suka shiga anguwan nasu Halwa take baza idanu tana kallon lungu da tsaƙo na cikin anguwan cike da tunano rayuwan ta na baya, har sanda suka kai ƙofar gidan su, gidan da tayi rayuwa aciki tare da sauyawan ƙaddaran ta
Numfashi tasauke lokacin da Saleema tatsai da motan dai-dai ƙofar gidan, fitowa suka yi gaba ɗaya yayinda Saleeman taɗauki Husna dake ta faman tsalle-tsalle
Gidan suka nufa suka shiga ciki da sallama
Wata matashiyar yarinya ne zaune tana haɗa lagwani a risho ta'amsa musu sa'ilin da taɗago kanta tana kallon su
Su ma dai kallon ta suke yi, yayinda Halwa taɗauke kanta daga gare ta tana bin gidan da kallo, gaba ɗaya an sauya gidan da sabbin abubuwa, musamman face_face da akayi wa gidan da kuma penti da akayi wa ko ina na gidan wanda ada babu shi..
Maganar budurwan ce tadawo da Halwa cikin tunanin ta tamaida idanun ta kanta, but aranta kuma tana mamakin wacece yarinyan don ita tasan ba cikin dangin su take ba bare kuma na Baba
"Ko dai matar Yaya Nura ne?" Tatambayi kanta aranta
"Ku shigo mana kun tsaya anan". Budurwan tayi maganar lokacin da tamiƙe tana share hannayen ta ajikin zanin ta
Shigowa suka yi suka nufo ɗakin da tanuna musu wanda ada ya kasance na Baba ne, shiga suka yi da sallama budurwan na biye dasu, sai da suka zauna tukun tasake fita tashiga ɗaya ɗakin, babu jimawa sai gata da ƙaton Jug cike da ruwa aciki, ajiye musu tayi tana faɗin
"Bismillan ku".
Babu wanda yayi ƙoƙarin ɗauka yasha a cikin su illa haɗa baki da suka yi wajen cewa "alhmadulillah mun gode".
Yayinda Halwa taƙara da faɗin "don Allah baiwar Allah wajen Mama muka zo".
"Mama kuma? Ai babu Mama gidan nan gaskiya, ko dai Aunty Zulaiha?" Yarinyan tafaɗa idanun ta akan Halwa
Girgiza mata kai tayi tace, "ina nufin masu gidan nan na asali, but kin san yaya Nura amma?"
Shiru yarinyan tayi tana tunani, sai kuma tagirgiza kanta tace, "a'a gaskiya sai dai kunyi ɓatan kai ne, nan daga Ni sai Auntyna da Mijin ta muke zaune anan ɗin, kuma shi sunan sa Aƙilu ne ba Nura ba, babu wasu kuma dake gidan nan, amma dai abinda nasani Mijin Aunty Zulaiha siyan gidan yayi, to ban sani ba ko waɗanda kike neman su ne suka tashi kenan?".
Murmushin yaƙe Halwa tayi bata iya cewa komi ba
Ganin haka yasa Saleema tace, "to don Allah ko kinsan inda suka koma?"
"Wlh ban sani ba".
"To shikenan bari mu tafi mun gode". Cewar Saleema tana miƙe wa tsaye
Itama Halwa tashi tayi suka fito waje, takalman su suka saka suka yo wajen gidan
"To yanzu ina zamu je?" Saleema tayi tambayar time ɗin da suka iso jikin motan su
Kallon ta Halwa tayi fuskarta da alamun damuwa tace, "wlh ban sani ba, Allah yasa ba wani abun bane yafaru dasu wlh hankali na ya matuƙar tashi, Nasan babu yanda za'a yi su siyar da gidan su in dai ba wani abu bane ke faruwa".
"A'a ki dena faɗar haka, babu komi insha Allahu ki cire komi aranki kinji ko?"
Murmushi Halwa kawai tayi tana sake rungume Ahmad dake hannun ta
Saleema tace, "To ko dai zamu tambayi maƙota ne?"
"A'a muje gidan su Zainab Nasan zamu ji komi acan idan ma wani abu ya faru ne".
Motan suka shiga suka nufi gidan su Zainab da babu nisa da nan ɗin, Saleema nayin parcking suka fito suka shiga gidan suna doka sallama tun daga zauren gidan
Umma na cikin ɗaki ta'amsa musu sallaman tana fitowa, duk da ta kalle su but bata gane Halwa ciki ba illa maraba da tayi musu tace musu "su shigo daga ciki".
Sai da suka zauna taba su ruwa sannan suka gaishe ta
Ta'amsa cikin fara'a tana sake duban su
"Sai dai ban gane ku ba wlh, ko dai wajen Zainab kuka zo?"
Murmushi Halwa tayi tace, "laa umma Halwa ce fa, baki gane Ni ba?"
Sake kallon ta da kyau Umma tayi sai kuma tace, "oh ikon Allah Halwa kece? Wlh ban gane ki ba ko kaɗan gaba ɗaya kin sauya min, Allah Sarki ashe da rabon zamu ganki?".
Still Murmushi Halwa take yi, tasake gaishe da Umman
Ta'amsa mata cike da fara'a tana bin ta da idanu
"ALLAH Sarki tamkar ba ke ba abin ki, waɗannan yaran naki ne?" Umma tayi maganar tana kallon Husna da talafe a jikin Halwan, yayinda Ahmad ke kan cinyan ta shima kwance
"A'a Umma ga mahaifiyar su nan". Halwa tayi maganar tana nuna Saleema
Jinjina kanta Umma tayi tace "Masha Allah to Allah ya raya su ta farkin Gaskiya".
"Ameen Umma, Ina Zainab ko bata nan ne?"
"Ai Zainab tayi aure kusan watanni bakwai kenan".
Halwa cikin tsantsan farin ciki tace, "Umma yanzu Zainab tayi aure ashe? Allah Sarki ashe bazan ga auren ƙawata ba?"
Umma na murmusawa tace, "ai kam Zainab tayi aure, ai dayake babu nisa da nan ɗin da gidan ta, sai in saka yara ma sukai ki idan zaki je".
"To umma amma naje gida ban ga su Mama ba, ko wani abun ya faru ne?"
Umma tace, "ai su Mama sun tashi tuni, ai ba anan anguwan ma suke zaune ba, Nura ya sai musu sabon gida, ashe baki sani ba?"
Murmushi Halwa tayi tana gyaɗa mata kai, kafin kuma tace, "eh umma ban sani ba wlh".
"To kin tafi can Gombe kin ɓoye ba dole ba, ina ga kema har auren kinyi bamu da labari ko?" Umma tafaɗa cike da fara'a
Still Murmushi Halwa tayi bata ba ta amsa ba
Sai Saleema ce taba ta amsa da "Eh umma itama tayi aure ai".
"Allah Sarki to Allah ya sanya alkhairi, bari inje maƙota in Kira yaro sai yakai ku gidan Zainab ɗin". Umma taƙarishe maganar tana tashi tafice.
[1/20, 4:52 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Thirty*
________🎓 A ƙofar gidan da Zainab take aure Saleema tafaka motar ta ta kamar yanda yaron da Umma tahaɗo su dashi yace musu, fitowa suka yi tare da sallaman yaron suka shiga cikin gidan, sallama suka yi duk kan su wanda yajawo fitowar Mahaifiyar Aliyu daga ɗaki
Amsa musu tayi cikin fara'a tare da musu maraba
Halwa ce tayi mata bayanin wajen Zainab suka zo
"Allah Sarki, to ku shiga tana nan ai, ku bi tanan ne ga hanyan sasan ta nan, sannun ku da zuwa". Still tayi maganar cike da fara'a tana sake musu sannu
Inda tanuna musu nan suka shiga, a bakin ƙofar ɗakin suka yi sallama
Zainab dake zaune a tsakar ɗakin ta, ta baje ƙafafuwa da ɗan ƙaramin cikin ta da be wuce watanni huɗu ba, yanzu ne ma yake shirin shiga na biyar ɗin, dayake ta taɓa yin ɓari, yanzun ma salat take yanka wa tana so tayi kwaɗon shi taci
Jin sallaman su yasanya tatsai da yankan tana ɗago kai ta'amsa musu tare da basu iznin shigowa
Shigowar kuwa suka yi Halwa ce a gaba
Hakan yasa Zainab tasauke idanun ta kan Halwa ɗin duk da bata gama gane ta ba, sai tawaro idanu tana son gasgata gizau ɗin da idanun ta ke mata
Lokacin tuni sun gama shigowa, yayinda Halwa kuwa kallon ta kawai take yi tana zuba murmushi, a take anan wani irin farin ciki yamamaye ta sakamakon ganin Aminiyarta wacce suka fi kowa shaƙuwa tun ƙuruciya, babu abinda ke raba su akoda yaushe har tasowar su, sai gashi rana tsaka sun rabu wanda basu sake ganin juna ba tsawon shekaru kusan biyar
"Halwa". Zainab tafaɗa da rawan baki still itama tana bin ta da idanu batare da ta motsa daga inda take zaune ba
"Zainab ɗina". Halwa itama tafaɗa ahankali idanun ta na kawo ruwan hawaye
Ai tuni Zainab ta yunƙura tamiƙe cikin tsananin murna ta nufo ta tarungume tana sake kiran sunan ta batare da ta furta wani kalman ba, kuka suka fashe dashi na tsananin kewar juna da farin ciki.
Saleema da tuni ta nemi waje ta zauna, Ahmad na hannun ta dayake tun shigowar su ta'amshe shi, kallon su kawai take yi cike da tsantsan tausayin su, kasancewar ta me rauni itama tuni ta soma hawaye batare da ta san tana yi ba
Sun daɗe rungume da juna suna ta sambatu da nuna kewar da sukai wa junan su, kafin kuma suka saki juna suka sami waje suka zauna, bakin su gaba ɗaya yaƙi rufuwa Cuz farin cikin da suke ji a yau ɗin
"Wlh bansan da bakin da zan iya nuna murnan da nake ciki ba da ganin ki Halwa, nayi kewar ki nayi kewar ki fiye da yanda kike tunani, tun ina saka ran dawowar ki har sai da kika saka nacire rai da ganin ki, nayi kewar ki wlh". Zainab taƙarike maganar nata tana me share ƙwallan da yacika mata idanu
Murmushi Halwa tayi tace "kiyi haƙuri Ƙawata, kina raina bazan taɓa manta wa dake ba, naso zuwa a lokuta da dama sai dai Allah be nufa haɗuwar mu ba sai yanzu".
Hannu Zainab tasake saka wa tashare hawayen ta, sai kuma takalli Saleema dake kallon su har yanzu ta kasa cewa uffan
Hakan yasa Halwa tace "Sunan ta Saleema, ƴar uwata da tamaye mini gurbin ki, da ba don ita ba ban san ya rayuwata zata koma ba, ita ce tamaye min farin cikina dana rasa abaya.."
"Haba ke kuwa kiyi shiru mana mu gaisa". Cewar Saleema tana katse mata maganar ta
Baki a washe Zainab tagaishe ta duk da kuwa Saleeman ba wai ta basu tserayan shekaru bane, da shekara ɗaya ta girme musu
Cikin fara'a Saleeman ta'amsa cike da ƙaunar Zainab ɗin aranta
Sai da suka gama gaishe-gaishen nasu har Zainab ɗin tatashi takawo musu drinks, Ahmed ta'amsa daga hannun Saleema takoma tazauna tana faɗin
"Kema ƴar lukuta zo nan wajena".
Husna dake maƙale jikin kujera tana jan igiyoyin kwalliyan da akayi, tataho dasauri ganin Saleema ita take kallo, dayake yarinya ce me shegen wayau ga son mutane
Ɗaukan ta Zainab tayi taɗaura saman kujeran tana cewa "Yauwa ƴan mata na, ya sunan ki?"
"Husna". Tafaɗa tana jujjuya jikin ta cikin wasa
Kallon Husnan tayi da kyau, sai taɗago tana duban Halwa tana murmusawa tace "wlh sak irin ku ɗaya, daga gani yarinyan nan taki ce, ashe kema kinyi aure?"
Dariya kawai Halwa tayi batare da tace komi ba
Saleema ce taba ta amsa da "Eh".
"Allah Sarki rayuwa kenan, ashe babu rabon muga auren juna, amma mun gode Allah tunda Allah ya haɗa mu da ran mu da lafiya".
Sai kuma takalli Ahmad tace "kai kuma ya sunan ka ɗan kyakykyawa?"
Husna ce taba ta amsa da faɗin "cunan sa Ahmad, amma kincan mene Aunty Mamy take ce mici?" ( Tana nufin Halwa)
"A'a sai kin faɗa?" Zainab tafaɗa tana shafa mata kai
"Tana ce mici Amadidi".
Dariya suka yi ban da Halwa da tayi murmushi kaɗai kana tace
"To Sarkin surutu faɗi ba'a tambaye ki ba".
"A'a ki ƙyale ta tayi surutun ta, ai duk surutun ta baza ta kai ki ba na sani". Cewar Zainab tana dariya
Yayinda Saleema ke taya ta, ɗan barkwanci suka taɓa na tuna baya kafin Zainab ɗin tace
"Wlh na shiga damuwa lokacin da su Mama suka faɗa min kin bi Dangin mahaifin ki Gombe, ban san meyasa naka sa yarda cewa wani abun ne yafaru dake ba, domin Ni dai har ga Allah nasan baza ki taɓa tafiya batare da kin sanar min ba".
Murmushin takaici Halwa tasaki tuno da abinda yafaru da ita a shekarun baya, sai dai ko kaɗan baza ta taɓa iya ɓoyewa Zainab sirrin ta ba, ita ɗin Aminiyarta ta ce wacce suka shaƙu matuƙa, kuma ta san ko babu komi zata taya ta jimamin abinda yafaru da ita, don haka tagyara zaman ta tasoma bata labarin komi da komi tun tafiyan ta har zuwa yanzu, abinda ta ɓoye mata kaɗai shine haihuwar Ahmad, don ko kaɗan bata kawo shi a zancen ta ba
Sai da Zainab ta dinga share hawaye sabida tausayin ƙawarta
"Ashe abun da yafaru dake kenan? Meyasaka su Mama suka aikata miki hakan? Dama akwai ranan da zata zo su guje ki? Waɗannan wasu irin mutane ne masu baƙin hali marasa yarda da ƙaddaran Allah, tirrrr da su wlh, tun farko shiyasaka zuciyata takasa amince wa da abinda suka faɗa mana".
Numfashi Halwa taja kana tace "Ni har yanzu ban ga laifin su ba Zainab, abinda nasani kawai shine Yaya Nura da yaƙi faɗa musu gaskiya, na tabbata wlh da ya sanar musu dole zasu yarda, har yanzu na kasa manta kalaman da Yaya Nura ya faɗa min aranan, bayan komi a gaban sa yafaru, shin meyasa ya aikata min hakan? shine abinda nake so in sani".
"Ya kuwa zaki sani tunda maci amana ne shi, idan be faɗa musu gaskiya ba su basu san ƙaddara bane? Ko kuwa basu fi kowa sanin halin ki bane? Dama sun yi ne da gayya don su kore ki sai gashi Allah yasa baza ki taɓa muzanta ba, wlh sun bani mamaki ko a mafarki bazan taɓa yarda zasu iya juya miki baya ba".
Haka Zainab ta dinga faɗa kamar zata ari baki, sai zagin su take yi musamman ma Nura da tafi tsanar sa a yanzu, bata dena ba sai da tayi ta gaji don kanta
Anan ne Halwa take faɗa mata tana son zuwa inda suka koma tagan su, gashi sun fito Umma bata faɗa musu ba bare su san gidan
Zainab ce mata tayi "ai Ni wlh ko na sani bazan faɗa miki ba balle ma ban sani ba, me zaki je kiyi musu tunda su suka kore ki? Wlh kar ki soma ki je tunda sun kore ki; ki bar su har abada".
Sai anan Saleema tasaka musu baki
"A'a hakan be kamata ba, su ɗin dolen ta ne kuma makusantan ta, kar ki manta Ƙanwar mahaifiyar ta ce, ko babu komi taci darajan ta, insha Allahu zamu je ko ba yau ba, kuma duk abinda suka yi su da Allah ne ba mu da hurumin ɗaukan mataki".
Ita dai Zainab taɓe baki tayi bata sake tanka zancen ba, sai ma sauya wa da tayi nan da nan suka ɓarke da hira, daga ƙarshe Zainab ɗin tatashi don yin musu girki, amma basu bar ta ba don tare suka shiga kichen ɗin gaba ɗayan su suka yi girkin, koda zasu ci ma a Plate ɗaya suka ci cike da nishaɗi.
Sai yamma sakaliya sannan suka baro gidan Zainab, yayinda itama tayi musu alƙawarin zuwa nan ba da jima wa ba, duk da dama Halwa ta faɗa mata zasu shiga Kotu jibi, kuma tayi mata alƙawarin zata saka Aliyu ya kawo ta Court ɗin, domin baza ayi babu ita ba.
***** ***** ****** ******
*MONDAY*
Tun ƙarfe 07:00am. Brr. Khalil yafice a gidan.
Su kuma su Halwa sai wajen ƙarfe 09:00am. Suka gama shiryawa, dayake sai ƙarfe Goma ne za'a shiga court ɗin
Husna tuni an shirya ta drever ya tafi da ita school, shi kuma Ahmad tare dashi zasu tafi yana hannun Saleema, sai da suka shiga mota ne sannan Halwa ta'amshe shi tunda Saleema ce zata tuƙa su
Direct gidan su Khalil suka wuce, saboda zasu taho tare da su Mom ne
Lokacin da suka je ba wani zama suka yi ba Mom tafito suka tafi, tunda dama ita kaɗai zata bi su, yau Monday Nazeefa na school, shima Dad yana da aiki don haka bazai samu zuwa ba
Kafin goma sun isa court ɗin, acan suka haɗu da Ummi har da Zainab da tayi musu alƙawarin zuwa
Abun mamaki kuma har da Mama da Baba da Nura a wajen, duk da Halwa bata gan su ba, su ma ɗin basu gan ta ba, amma su sun zo ne kasancewar Nura yace musu za shi ana Shari'a da uban gidan shi, shi ne Baba yace "be kamata su zauna agida ba dole su je, ko don martaba uban gidan sa tunda yayi musu halarci, a sanadiyar sa ɗan su ya sami kuɗi sosai, sannan basu da masaniyar komi akan Halwa ce wacce za'a yi Shari'an da ita
Nan kuwa basu sani ba, Haris ne yasaka shi tilas yazo, kuma yace "idan be zo ba zai iya tona masa asiri, don haka gwara yazo yaga me zai faru, be san cewa Haris wayau yayi masa ba don ya rigada ya shirya amsa duk wani tuhuma da ake musu sabida samun ƴarsa, sannan kuma ko hakan zai sa Halwa ta yafe masa har ta aure sa.
Lokacin da suka isa Halwa aka bari a baya, tana rungume da Ahmad tana shirin fitowa sai ganin Haris tayi a gaban ta
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Tafaɗa a fili sa'ilin da tayi tozali dashi
Gaban ta ne yayi matsanancin faɗuwa, sai dai bata nuna firgitan ta a fili ba, ta kai duban ta gare shi fuskarta a ɗaure tamkar bata taɓa sanin sa ba, tana shirin sake yunƙura wa tafito taji muryan sa ya daki dodon kunnen ta
"Halwa ashe zamu sake haɗuwa? Nasan bani da bakin da zan roƙe ki; ki yafe min, but duk da haka ina neman afuwar ki, wlh nayi nadaman abunda..."
"Kai da Allah dakata min". Takatse sa da faɗin hakan tana me banka masa harara tamkar zata maƙure sa dan baƙin cikin ganin sa da jin muryan sa
"Ka ɓace min agaba ko in maka wulaƙacin da sai kayi nadaman zuwan ka duniya".
Shi kansa Haris yayi mamakin furucin nata da yanda tafaɗa cikin tsananin fushi tamkar ba Halwan da ya sani ba abaya, duk da dama ta sauya masa sosai amma hakan be sa ya kasa gane ta ba, kuma yasan irin hakan take masa magana domin dai bata sauya ba a yanda ya santa
Yana shirin sake magana
taja ƙofar da ƙarfi ta rufe kanta aciki, domin dai babu yanda za'a yi tabar wajen dole sai ya matsa, ita kuma baza ta iya juran sake jin maganar sa ba, ta matuƙar tsanar sa fiye da kowa a duniya
Hannun sa ya kai zai ƙwanƙwasa Glasses Motan, sai jin murya daga bayan sa yayi, wanda ya dakatar dashi daga abinda yayi ninya
"Malam don Allah kayi haƙuri ka bar nan wajen, Halwa yanzu matar wani ne baka da hurumin da zaka iya mata magana kaji ko?". Cewar Saleema dake tsaye gefe tana kallon duk abinda suke yi tun ɗazu
Shima dai kallon ta yayi tamkar sakarai, babu abinda ke kai kawo a zuciyar sa sai ce masa da tayi "Halwa matar wani ne". "Kenan tayi aure?" Ya tambayi kansa batare da zai iya samun amsar ba
Be sake motsawa ba, tamkar gunki ya zama sabida ba ƙaramin taɓa sa maganar yayi ba, har be san ma a wani yanayi yake ciki ba
"Excuse me zan wuce". Tayi maganar tana kallon sa ganin be da ninyan jirga wa
Ɗan ja baya yayi kaɗan ya matsa mata kamar wanda be da jini a jiki
Buɗe ƙofan tayi ta'amshi Ahmad daga hannun Halwa, sannan tayi mata maganar tafito
Ko kallo be ishe ta ba sanda tafito, gaba kawai tayi tabar Saleema na rufe ƙofan kafin tabiyo bayan ta
Idanu kawai ya kafa ma bayan ta hawaye na sintiri a face ɗin sa.
[1/20, 5:15 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH```
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Thirty One*
________🎓 Kafin Shari'an su Halwa akwai Shari'an da Khalil ya soma yi
Na wani yaro ne da yayi wa ƴar aikin gidan su fyaɗe, tun wajen watanni uku da soma Shari'ar sai yau ne ake shirin ƙarƙare shi
Kasancewar uban yaron me kuɗin gaske ne, tun a zaman farko da yaga Khalil na shirin yin nasara akan su, shi ne sanadin da ya samo ƴan daba suka je suka harbe shi, sun so su kashe sa ne gaba ɗaya sai Allah be basu Sa'a ba
Lokacin da Alh. Sheƙau (kar ku ce da Sheƙau ɗin sambisa nake yi fa lolx 🤪) ya basu aikin; to ya bar ƙasan ma gaba ɗaya shi da ɗan sa tunda ya samu beli, ƴan daban kuma da suka yi aikin sun tabbatar masa Khalil ya mutu duk da kuwa su ma daga baya suke jin yana da rai, sun so su sake komawa asibitin su kashe sa but a time ɗin akwai jami'an tsaro, to sai suka yi wa Alh. Sheƙau bayanin cewa sun wulla Khalil barzahu, don haka ya biya su kuɗin su sukai gaba a bin su
Sai kwanaki biyun nan suka dawo ƙasan sabida a yau ɗin za'a koma kotu a yanke hukuncin ƙarshe, sun saki jiki babu abinda zai faru tunda an kashe musu Khalil, duk da a time ɗin har da Brr. Tahir ya taya shi shari'ar, amma sun fi so su ga bayan Khalil tunda shine yadage sai ya amsar wa yarinyan haƙkin ta.
Yau kuma da aka shiga kotu sai hankalin su yayi mummunan tashi ganin Khalil a raye be mutu ba
Shi kuwa Khalil murmushi kawai yayi yana bin su da kallo, don shi tuni ya gane Alh. Sheƙau ne ya saka a kashe shi, be faɗa ma kowa bane don baya son maganar tayi tsawo, duk da kuwa yana da hanyan da zai sa a hukunta Alh. Sheƙau komin girman sa a ƙasan kuwa, tunda yana da gwamnati a hannu, but be yi hakan ba ya ƙyale su tunda dama zargi yake yi, amma yau da ya gansu sai ya tabbatar da zargin sa
Be damu kansa ba kawai Shari'an ya gabatar, kuma cikin ikon Allah ya ƙwato wa yarinyan haƙƙin ta, inda aka yanke wa Yaron Alh. Sheƙau hukuncin zaman gidan yari na shekara 8 sakamakon kama sa da yin wa yarinya fyaɗe, kuma babu Beli, sannan kuma dole zai bada kuɗi dubu ɗari cif don nema mata magani.
Hakan ya faranta ran mutane matuƙa, ya saka wasu kuka da hawayen su sabida tsaban farin ciki, da yawan su kuma hakan ya taɓa faruwa da yaran su, sai dai rashin samun wanda zai taimake su ba sa iya ƙwato wa ƴar su haƙƙin ta, amma kuma wannan hukuncin da aka yanke wa mutum ɗaya ya sa zuciyoyin su fari da wanke duk wani tabo da ƙuncin dake cin su
Kowa sai sanya wa Khalil albarka yake yi, tare da addu'ar gamawa da duniya lafiya, gaskiya yayi na mijin ƙoƙari, kuma samun irin su a duniyar mu masu jajircewa wajen tsayawa tsayin daka don hukunta masu laifin fyaɗe, hakan zai saka a rage yawaitan su a duniyar mu, idan suka ga ana musu hukunci to dole zasu dena abinda suke yi
Sai dai kuma matsalan al'umman mu suna jin tsoron su fito da irin wannan maganar su bayyana wa mutane don ƙwato wa ƴar su haƙƙin ta, suna ganin tamkar sun tona wa kansu asiri ne, kuma hakan zai ja musu tsangwama a wajen mutane, wannan dalilin yasaka suke ɓoye wa har a kasa hukunta masu laifin fyaɗe, su kuma hakan ke saka wa suna ci gaba da aikata laifin tunda babu abinda ake iya musu.
Don Allah mata duk wanda hakan ya faru da ita, ya jajirce wajen ƙwato wa kansa haƙƙi, iyaye su ma su dage su tabbatar an hukunta wanda ya aikata ɗin, hakan na taimaka wa sosai wajen rage yawaitan laifukan, Allah ya ƙara tsare mu da zuri'armu baki ɗaya Ameen.
Daga wanann Shari'an ne aka shiga na su Halwa, alokacin ne Halwa da su Mama suka ga juna, sai dai babu halin magana tunda Alƙali na ciki
Shima Nura ya ganta, sai dai ita bata ganshi ba, mamaki sosai ya cika sa ganin yanda ta sauya gaba ɗaya tamkar ba ita ba, tsananin kyan da tayi masa ma ya kasa ɗauke idanu akanta, yanayin canjin rayuwan da ta samu duk da su ma suna da rufin asiri sosai, amma kuma yanzu tana cikin daula ne dole kaga sauyawan Halwa, ga ta dama tun farko tana da kyan ta da dirin jiki, but yanzu komi nata ya sake canja wa tayi kyau matuƙa, skin ɗin ta tuni ya sake haske tare da wani irin fresh, Kai da gani kasan babu wahala a rayuwan ta, jin daɗi da kwanciyar hankali ya zauna mata, bare uwa uba tana tsaka da cin amarcin ta ne, ƙyallin amarci da Albarkan aure ya sake fito da ita.🥶😫
Koda Khalil ya tashi ya gabatar da kansa a matsayin Lauyan dake kare wacce ta kawo ƙara, komawa yayi ya zauna
Sai dai su Haris basu da lauya, domin tuni Haris yace "be buƙatar lauya a halin yanzu, ya yarda zai amsa laifin sa sannan a bashi ƴar sa". Don haka ya ga babu amfanin ya samu Lauyan ma
Dadyn sa da Mamy basu ji daɗi ba, amma babu yanda zasu iya tunda yace "zai amsa laifin sa".
Brr. Khalil ne ya miƙe yafito gaban kotun bayan ya nemi iznin magana da Halwa
Fitowa tayi tatsaya a inda aka tanada don tsayawar masu amsa tambayoyi
Khalil ya tambaye ta sunan ta da sunan mahaifin ta, sannan kuma ya buƙaci ta ba ma kotu Labarin asalin abinda yafaru a ranan da mummunan ƙaddaran yafaru da ita
Tiryan-tiryan tasoma faɗa wa kotu abinda yafaru
Tsit kotun tayi ana sauraron ta, tuni masu saurin kuka da tausayi sun soma zub da hawaye, sabida sosai abinda yafaru da Halwan ya matuƙar basu tausayi
Ita kanta tana ba da labarin ne tana kuka, sabida yanda take jin ƙunci da baƙin ciki a zuciyar ta tamkar lokacin da ake keta mata haddi ne
Zina tabo ne babba ga duk wanda ya tsinci kansa a halin; dole ne ya koka, musamman waɗanda akayi musu ta ƙarfi, su kansu masu aikata wa da za su gane illa da girman laifin da suke yi, wlh wlh da har su mutu baza su dena kuka ba saboda tsoron haɗuwar su da ALLAH😭, ya Allah ka kare mu da kariyan ka, bamu da wayau ko dabara ya Allah ka kare mana zuri'armu daga faɗa wa mummunan makoma. 🙏🏼
Har sanda ta dasa Aya tana shashsheƙan kuka
Khalil kallon ta kawai yake yi cike da tsantsan tausayi tare da tarin ƙaunar ta a ransa, ji yake yi tamkar yajawo kayan sa yarungume ta ya rarrashi abin sa, amma kuma babu hali 🤠, don haka yaja numfashi yana lashe bushashshen laɓɓan sa, cike da sanyin murya yace mata "taje ta zauna". Sannan ya juya ya fuskanci Alƙali ya nemi iznin ganin Haris
Fitowa yayi ya tsaya inda Halwa ta tashi
Khalil kallon sa yake yi tamkar ya kama sa ya maƙure shege😃, sai dai babu hali, don haka ya murtuke fuska yasoma masa tambayoyi
Babu abinda Haris ya musa a tuhuman da ake masa, sai ma ƙara wa da yayi da abinda basu sani ba, ya faɗa musu komi da yanda ya nemi taimako wajen Nura.
Tirƙashi! nan ake yin ta fa, ai nan da nan kotu ta hargitse saboda jin bayanan Haris, waɗanda suka san Nura kuwa kamar su: Mama, Baba Zainab Halwa, da su Saleema, daskare wa suka yi sabida tsantsan mamaki da Al'ajabi
Halwa bata iya ko motsi ba, don ba ta tunanin kunnen ta ya jiye mata dai-dai, shiyasa tabi Nuran da kallo wanda tuni Khalil ya buƙaci ganin sa, zuba masa ido kawai tayi tana sauraron abinda zai fito daga bakin sa
Lumshe idanuwan ta tayi da suka cika da hawaye, ko kaɗan baza ta iya juran abinda yake faɗa ɗin ba, don haka tasaka hannun ta biyu ta toshe kunnuwan ta tana fashe wa da kuka me tsananin sauti
Duk mutanen wajen sai da suka kallo ta, sosai ta basu tausayi wasu har da zubar mata da hawaye
Ita kanta Saleema dake kusa da ita hawayen take zubar wa, tasaka hannu tariƙo mata nata hannayen, cikin rawan murya tasoma rarrashin ta
Halwa bata dena kukan ba, sai ma ɗaura kanta da tayi saman cinyoyin ta tasoma rerawa kamar zata shiɗe, babu abinda zuciyarta ke maimaita mata sai sunan Nura, taya hakan ma zai faru? Taya ɗan uwanta masoyin ta, wanda tafi yarda da shi a baya fiye da kowa, shine zai yi sanadin shigar ta wannan halin, meyasa? Me tayi masa?
Guduma Alƙali yabuga don hayaniyar kotun tayi yawa, tsit kake ji an yi duk da kuwa har yanzu Halwa bata dena kukan ba, amma kuma ba'a ji acikin kotun sai can wajen su
Khalil bayani ya sake yiwa kotu kafin yakoma wajen zaman sa ya zauna
Sai da Alƙali yayi rubuce-rubucen sa kafin ya ɗago yasoma yanke hukunci, hukuncin ɗaya ne aka yanke musu daga shi Nuran har Haris, domin dai basu da maraba tunda duk laifi ɗaya suka aikata, don haka an yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na shekara 8 batare da beli ba, sannan kuma dole Haris zai biya kuɗin rainon masa ɗiya da akayi, kuma bashi da damar amsar ɗiyar sa sai idan mahaifiyar sa ta amince.
Sosai iyayen Nura suke kuka sabida abinda suka ji, tabbas yau suna nadaman abunda suka yiwa Halwa, shin da wani ido zasu kalle ta? Sun kore ta sabida gudun zubewar mutuncin su, ashe ɗan su shine SILAR KOMAI, Mama tafi kowa shiga tashin hankali, tana ganin tafi Nura ma laifi, domin abinda ta aikata wa ɗiyar ƴar uwanta yafi na Nura muni, shin ina hankalin ta yaje ne a lokacin da har ta manta wacece Halwa a wajen ta?
Suna ji suna gani aka tasa su Nura, amma ko kallon inda yake ba suyi ba, suna ji da ƙuncin dake ransu.
Halwa kuwa sabida shiga ruɗu da kukan da take yi, tuni numfashin ta ya rabu da gangan jikin ta, ta kasa jure abinda taji, ta rasa taya ma zata ɗaura abun akan mizani, shin dama akwai ɗan uwa irin haka da zai iya cutar da ƙanwar sa sabida kuɗi?
Hankalin Khalil da su Ummi ya tashi sosai, musamman ma Saleema, ai nan da nan Khalil ya ɗauke ta ya fice da ita suka take masa baya, mutane sai kallon su suke yi kowa da tunanin da yake yi aransa
Asibiti Direct aka wuce da ita, domin a cikin su babu wanda yayi tunanin zuba mata ruwa ko zata iya farfaɗowa.
𝗕𝗔𝗬𝗔𝗡 𝗦𝗛𝗨𝗗𝗘𝗪𝗔𝗥 𝗔𝗪𝗔𝗡𝗡𝗜 *2*
Tuni su Halwa sun koma gida, sai dai har alokacin sun kasa gane kanta, abinda Nura yayi mata ya matuƙar saka ta a Shock, kuka kawai take yi ta kasa yin shiru
Khalil da Saleema in banda zaman rarrashi babu abinda suka zauna yi
Sukuku ta koma, gaba ɗaya ta dena walwala, to idan ɗan uwanka yayi maka haka, wanene ma bazai maka ba? Nura ya cuce ta, duk tsanar da take yi wa Haris, sai taji gaba ɗaya ma ya gushe ya koma kan Nura, tsantsan tsanar sa ne ya ɗarsu a ranta, ji take yi ta tsane sa fiye da mutuwar ta, kuma ba ta tunanin zata iya yafe masa har ta koma ga mahaliccin ta.
Bayan kwana biyu sai ga su Mama da Baba sun zo har gida neman gafarar Halwa, kuka suke yi suna roƙon ta, yayinda itama take nata kukan tare da rungume Mama, tabbas tayi kewar iyayen nata fiye da zaton me karatu, taya zata ƙi yafe musu bayan su ne iyayen da tabuɗe idanu tagan ta tare da su? Bata taɓa kallon wasu a iyayen ta ba sai su, su ne tatashi tasani; su ne kuma suka raine ta, ko waɗanda suka haife ta bata jin su kamar su
Shiyasa tanuna farin cikin ta da ganin su, ko babu komi iyayen ta sun dawo gare ta, shekaru kusan biyar basa tare, gaskiya tayi kewar su matuƙa, kuma ko kaɗan bata kalle su da abinda ɗan su yayi mata ba.
Mama kuwa kunya da dana-sanin abinda suka aikata mata yasa ta kasa kallon Halwan, gashi sabida son zuciyar su sun aikata babban kuskure, sai dai Allah ya yafe musu.
.
𝑇𝑜 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑟𝑎𝑏𝑎 𝑚𝑢 𝑑𝑎 𝑚𝑎𝑠𝑢 ℎ𝑎𝑙𝑖 𝑖𝑟𝑖𝑛 𝑛𝑎 𝑠𝑢 𝑀𝑎𝑚𝑎, 𝑠𝑎𝑏𝑖𝑑𝑎 𝑘𝑎𝑑𝑑𝑎𝑟𝑎 𝑦𝑎 𝑓𝑎𝑑𝑎 𝑤𝑎 '𝑦𝑎𝑟 𝑠𝑢 𝑠𝑎𝑖 𝑠𝑢ka 𝑚𝑎𝑛𝑡𝑎 𝑑𝑎 ℎ𝑎𝑘𝑎𝑛 𝑠ℎ𝑖𝑛𝑒 𝑘𝑎𝑑𝑑𝑎𝑟𝑎𝑛 𝑡𝑎, 𝑠𝑎𝑖 𝑠𝑢ka 𝑘𝑜𝑟𝑒 𝑡𝑎, 𝑘𝑜𝑑𝑎 𝑚𝑎 𝑑𝑎 𝑔𝑎𝑛𝑔𝑎𝑟 𝑡𝑎 𝑎𝑖𝑘𝑎𝑡𝑎 ℎ𝑎𝑘𝑎𝑛 𝑏𝑒 𝑘𝑎𝑚𝑎𝑡𝑎 𝑠𝑢 𝑘𝑜𝑟𝑎 𝑡𝑎 𝑏𝑎, 𝑑𝑜𝑚𝑖𝑛 ℎ𝑎𝑘𝑎𝑛 𝑏𝑎𝑏𝑏𝑎𝑛 𝑘𝑢𝑠𝑘𝑢𝑟𝑒 𝑛𝑒, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑘𝑦𝑎𝑢𝑡𝑎.
[1/20, 5:29 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
𝐁𝐀𝐑𝐑𝐈𝐒𝐓𝐄𝐑 𝐈𝐁𝐑𝐀𝐇𝐈𝐌 𝐊𝐇𝐀𝐋𝐈𝐋
♠️
𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔:✍️ 𝐵𝑦
𝐍𝐚𝐟𝐢𝐬𝐚𝐭 𝐈𝐬𝐦𝐚'𝐢𝐥
(𝐹𝑒𝑒𝑛𝑎ℎ 𝐽𝑖𝑘𝑎𝑟 𝐿𝑎𝑤𝑎𝑙 𝐺𝑜𝑚𝑎)
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
\𝗙.𝗪.𝗔📚/
𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷! 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷!! 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷!!!
𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑛𝑎 𝑔𝑜𝑑𝑒 𝑚𝑎𝑘𝑎 𝑑𝑎 𝑘𝑎 𝑏𝑎𝑛𝑖 𝑑𝑎𝑚𝑎𝑟 𝑟𝑢𝑏𝑢𝑡𝑎 𝑤𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑙𝑖𝑡𝑡𝑎𝑓𝑖𝑛 𝐵𝑟𝑟. 𝐼𝑏𝑟𝑎ℎ𝑖𝑚 𝐾ℎ𝑎𝑙𝑖𝑙, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑏𝑎𝑛𝑖 𝑖𝑘𝑜𝑛 𝑟𝑢𝑏𝑢𝑡𝑎 𝑎𝑏𝑖𝑛 𝑑𝑎 𝑧𝑎𝑖 𝑎𝑚𝑓𝑎𝑛𝑖 𝐴𝑙'𝑢𝑚𝑚𝑎𝑛 𝑚𝑢, 𝑘𝑢𝑠𝑘𝑢𝑟𝑒𝑛 𝑑𝑎 𝑧𝑎𝑛 𝑦𝑖 𝑎𝑐𝑖𝑘𝑖 𝑘𝑢𝑚𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑦𝑎𝑓𝑒 𝑚𝑖𝑛 𝐴𝑚𝑖𝑛 🤲 𝑦𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ.
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 ƴ𝑎𝑛 𝑢𝑤𝑎𝑛𝑎 𝑚𝑢𝑠𝑢𝑙𝑚𝑎𝑖 𝑏𝑎𝑘𝑖 ɗ𝑎𝑦𝑎.
𝗕𝗢𝗢𝗞 𝗧𝗪𝗢
.
_______________________________
𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 𝗧𝗵𝗶𝗿𝘁𝘆 𝗧𝘄𝗼
________🎓 Bayan sati Uku da faruwan abun Hutun su Halwa ya ƙare, ta koma school yanzu bata cika zaman gida ba, tunda yanzu sauran su ɗan watanni ne su ƙarashe, karatu suke yi sosai.
Sai ga Zainab wani ranan asabar ta kawo musu ziyara, ai kuwa sun yi farin ciki matuƙa, ranan wuni suka yi hira har yamma kafin Aliyu yazo ya ɗauke ta, sun rabu cike da kewar juna
Washe gari kuma sai ga iyayen Haris sun zo wai ganin Husna, tare da matan Haris ɗin da wasu makusanta cikin Familyn su, duk da kuwa da yawan su ganin ƙwaƙwaf suka zo yi
Tarba me kyau Halwa da Saleema suka yi musu
Tunda suka zo Mamy da Daddy suka naniƙe Husna ko sakin ta sun ƙi yi, dayake har ciki Daddy yashiga, ƙaunar yarinyan sosai yashige su, yanzu basu da abunda suke tunawa sai ita, tunda yanzu ɗan su yana magarƙama, har hawaye Mamy take share wa idan ta kalli Husnan, tana jin soyayyar yarinyan sosai aranta duk da kasancewar ta shegiya, amma su suna son ta a matsayin jikar su
Sun roƙi Halwa taba su ita su tafi da ita, amma firr Halwan taƙi, sai ma faɗa musu tayi ta kyautar da ita yanzu, don haka su yi haƙuri
Babu yanda zasu yi haka suka haƙura, sai dai sun sake neman alfarman zasu riƙa ɗaukan ta tana musu hutu.
Da zasu tafi Daddy ya ajiye masu kuɗi me yawan gaske, duk da Halwa taƙi amsa, sai Khalil ne yace "ta'amsa" tukun ta amsa.
Bayan kwana biyu kuma sai ga Mamy ta sake dawowa da kaya niƙi-niƙi, wai ta kawo ma Husna ne, har da Ahmad sai da takawo mishi nashi
Ranan ma Halwa tana school daga ita har Husnan, sai Saleema da Khalil ne da shima dawowan sa kenan, sun amshi kayan tare da yin mata Godiya
Ƙin tafiya tayi, har sanda aka dawo da Husna ta ganta kafin tatafi.
Rayuwa taci gaba da tafiya da daɗi babu daɗi, gashi har su Halwa sun rubuta Exams ɗin su ta ƙarshe, yanzu kuma sai jiran result.
**** ***** ***** ****
Itama Nazeefa a wannan shekaran ne tagama Secondary School ɗin ta, koda result ɗin ta yafito sai Dad yatambaye ta Aure ko karatu? Ita kuma tace masa karatu take so taci gaba, tunda har yanzu soyayyar Khalil ne aranta bata taɓa tsayawa da kowa ba, ko da tace auren take so ba ta da wanda zata iya fitar wa, kuma ba ta jin ma zata iya aure yanzu idan har ba ta cire soyayyan Khalil bane aranta, duk da tayi iyakan ƙoƙarin ta amma ta kasa manta sa, don haka ta samu Dad tafaɗa masa tana son tayi school ɗin nata ne ba'a state ɗin nan ba, ko ba komi tasan idan tayi nesa dashi zata manta shi
Dad be yi musu ba kuwa, yace mata ta zaɓa inda take so
A.B.U Zaria ta zaɓa don nan ne yafi mata, duk da kuwa bata san school ɗin ba, amma yanda take jin labarin sa tasan ba ƙaramin makaranta bane tunda yayi fice a ƙasar Nigeria.
Dad sai da yatara Sameer da Khalil ya faɗa musu komi don jin shawaran su, nan Khalil yaba da shawaran akai ta Abroad tayi acan, cikin su babu wanda yanemi ja da maganar nasa tunda suna ganin shine yakawo ta gidan, don haka shi yafi iko da ita fiye da kowa, Mom CE ma tanemi ta hana, amma kuma ganin Nazeefan tana murna sai tasaka albarka kawai ta ɓame bakin ta
Ƙasan Sudan Nazeefa ta zaɓa, domin tafi son fannin Islamic shi za ta karanta, su ma su Dad sai hakan yayi musu daɗi.
Cikin ikon Allah aka fara mata shirye-shiryen tafiyan ta, Sameer ne akan komi har sai da komi ɗin ya kammala, sai kuma tafiyan ta nan da ɗan watanni kaɗan.
*** **** **** ******* ****
Yau su Halwa sun tashi da farin cikin haihuwar Hakima ne, wajen ƙarfe 10:00am. Suka shirya suka tafi gidan Sameer ɗin
A lokacin ma tuni ƴan uwan Hakiman sun soma zuwa, kasancewar agida ta haihu, kuma lafiyan ta lau da ita da Babyn ta, wannan karon ma namiji ta haifa
"Masha Allah". Abin da su Saleema suke ta faɗa kenan da suka ga yaron, sak Sameer basu da maraba, dayake shima Aamir ɗin Dadyn nasa yabiyo, sai yaron ya koma tamkar Aamir sanda yake ƙarami ( na kula jinin su shi da Khalil ƙarfi ne dashi lolx🥴)
A can suka wuni suna ta hira, Abida ma ta shige cikin su ana tayi da ita, dayake yanzu ta ajiye batun soyyayyar Khalil agefe bare tayi kishi dasu, yanzu ma haka har ta fitar da mijin aure acikin waɗanda suke zuwa wajen ta, tunda tasan wanda take so ɗin ba samun sa zata yi ba, shiyasa tayi wa kanta faɗa, wata biyu masu zuwa zasu sha biki
Har yanzu tana zaune agidan Hakiman ne, tunda iyayen su sun rasu, shine Hakima ta ɗauke ta, kuma Sameer cewa yayi shine zai mata auren.
Sai dare Khalil yazo ya wuce dasu.
To rayuwa dai haka taci gaba da tafiya, zaman su Halwa sai son BARKA, babu ruwan su da faɗa ko kishin juna, sun zama tamkar ƴan uwan juna ba kishi ne ya haɗa su ba, komi tare suke yi, shi kansa Khalil yana alfahari da samun su matsayin matan sa, babu abinda zai ce wa Allah sai godiya, farin ciki kullum sake wanzuwa yake yi agidan sa, ko wacce cikin su yana matuƙar ƙaunar ta kuma yana jin ta arai da magudanan jinin sa, babu ma wanda zai iya tantance wacce yafi so, sai dai shi Khalil ɗin yana ji aran sa yafi ƙaunar Halwa, a ganin sa fa. 🤣
An yi suna lafiya an gama lafiya, yaron yaci sunan mahaifin Hakima, Abdulrahman, zasu ringa ce masa Haneef.
𝐀𝐅𝐓𝐄𝐑 𝐎𝐍𝐄 𝐘𝐄𝐀𝐑 𝐀𝐆𝐎.
A wannan shekaran abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da zamowar Halwa cikakkiyar Lauya, yau ta amshi certificate ɗin ta
Ko wani masoyin ta yau yana taya ta farin ciki
Don haka Khalil shi da kansa ya shirya mata gagaruman walima don faranta mata
Kasancewar yanzu yayi sabon gini, zasu tashi a anguwan da suke zaune, ya tsara musu babban gida wanda ya ninka wanda suke ciki a yanzu, ko wacce da nata Part ɗin, sai dai kuma haɗe yake da babban Parlourn na su gaba ɗaya
Saura kwana biyu su tare don haka ake ta faman shirye-shirye babu kama hannun yaro, tunda abun ya haɗe musu biyu ne, ga Waliman taya Halwa zama Barrister, ga kuma Waliman koma wa sabon gida.
Babu abinda zasu ɗauka na tsohon gidan su, komi sabo aka sanya agidan
Mom ita ta ɗaukar musu me gyaran jiki, don tana so su fito sosai, har gida ake bin su ana musu komi, an zana musu lalli me tsananin kyau, sai aka yarfa musu kitso wanda ya sake fito dasu ainun, idan ka gansu sai ka ɗauka sabbin amare ne, sabida duk abinda ake ma Amare ƴan gata an yi musu.
A ranan tarewan suka koma can sabon gidan nasu, tare da ƴan uwa na kusa
Zuwa ƙarfe 04:00 gidan ya cika maƙil da jama'a, su Mama da Baba ma duk sun hallara gidan, iyayen Haris ma sun zo, Zainab da ƙanwar Mijin ta har da mahaifiyar sa da Umman ta ma duk sun zo, su Zaituna ma sai da suka zo mata kara
Ana fara taron su Halwa suka fito, duk kansu sun sha kyau cikin Milk ɗin Material me tsananin tsada, doguwar riga aka yi musu fitet gown, sai akayi kwalliya da ston masu ƙyalli, an yi musu Light makeup da ya ƙawata fuskar su, takalmin su da gyalen da suka yi Rolling duka kalan baƙi ne, sun yi kyau Masha Allah, ba ma zaka iya tantance wacce tafi ba a cikin su
Ƙaramin cikin Halwa ya fito ɗass yayi mata kyau matuƙa, ga haske da tasake yi sosai sabida cikin
Haka Husna da Ahmad su ma an shirya su, tubarakallah Masha Allah kowa ya gansu sai sun burge sa
Mamy tunda ta hangi Husna ta ɗauke ta tana ta nan-nan da ita.
An gudanar da taro lafiya an gama lafiya, kowa ya tafi da tarin ɗumbin kyaututtukan da aka raba
Sai dai aka bar ma su aiki da gyara gidan
Su ma su Saleema ciki suka shige, suka ɗaura alwala saboda kiran sallan magriba da aka yi, sallah suka yi suka cire kayan jikin su suka sauya da wani atamfa me ruwan kuka da ratsin ja da baƙi, ɗinkin riga da skert ne iri ɗaya komi da komi, parlour suka fito suka zauna suna hiran Waliman cike da nishaɗi
Husna da Ahmad tuni barci ya ɗauke su, Dattijuwar matar da suka ɗauka me aikin su, ita tayi musu wanka ta shirya su a kayan barcin su ta kai su ɗakin su.
Sai da aka kira sallan isha'i kafin suka tashi suka je suka gabatar suka sake dawowa.
Shima Khalil ɗin be dawo cikin gidan ba sai da yayi sallan isha'i sannan ya shigo.
.
𝚙𝚕𝚣 𝚜𝚑𝚊𝚛𝚎 𝚊𝚗𝚍 𝚟𝚘𝚝𝚒𝚗𝚐
[1/21, 1:38 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
𝐁𝐀𝐑𝐑𝐈𝐒𝐓𝐄𝐑 𝐈𝐁𝐑𝐀𝐇𝐈𝐌 𝐊𝐇𝐀𝐋𝐈𝐋
♠️
𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔:✍️ 𝐵𝑦
𝐍𝐚𝐟𝐢𝐬𝐚𝐭 𝐈𝐬𝐦𝐚'𝐢𝐥
(𝐹𝑒𝑒𝑛𝑎ℎ 𝐽𝑖𝑘𝑎𝑟 𝐿𝑎𝑤𝑎𝑙 𝐺𝑜𝑚𝑎)
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
𝐅𝐄𝐄𝐍𝐀𝐇 𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑'𝐒 𝐀𝐒𝐒𝐎📖
®Ɗ𝚊𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚖𝚔𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝙳𝚞𝚋𝚞💪✓
𝗝𝗜𝗞𝗔𝗥 𝗟𝗔𝗪𝗔𝗟𝗜 𝗖𝗘✍️
𝗪𝗮𝘁𝘁𝗽𝗮𝗱: 𝗨𝗺𝗺𝘂𝗗𝗮𝗵𝗶𝗿𝗮𝗵👈
\𝗙.𝗪.𝗔📚/
𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷! 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷!! 𝙰𝙻𝙷𝙰𝙼𝙳𝚄𝙻𝙸𝙻𝙻𝙰𝙷!!!
𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑛𝑎 𝑔𝑜𝑑𝑒 𝑚𝑎𝑘𝑎 𝑑𝑎 𝑘𝑎 𝑏𝑎𝑛𝑖 𝑑𝑎𝑚𝑎𝑟 𝑟𝑢𝑏𝑢𝑡𝑎 𝑤𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑙𝑖𝑡𝑡𝑎𝑓𝑖𝑛 𝐵𝑟𝑟. 𝐼𝑏𝑟𝑎ℎ𝑖𝑚 𝐾ℎ𝑎𝑙𝑖𝑙, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑏𝑎𝑛𝑖 𝑖𝑘𝑜𝑛 𝑟𝑢𝑏𝑢𝑡𝑎 𝑎𝑏𝑖𝑛 𝑑𝑎 𝑧𝑎𝑖 𝑎𝑚𝑓𝑎𝑛𝑖 𝐴𝑙'𝑢𝑚𝑚𝑎𝑛 𝑚𝑢, 𝑘𝑢𝑠𝑘𝑢𝑟𝑒𝑛 𝑑𝑎 𝑧𝑎𝑛 𝑦𝑖 𝑎𝑐𝑖𝑘𝑖 𝑘𝑢𝑚𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑘𝑎 𝑦𝑎𝑓𝑒 𝑚𝑖𝑛 𝐴𝑚𝑖𝑛 🤲 𝑦𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ.
𝗦𝗔𝗗𝗔𝗨𝗞𝗔𝗥𝗪𝗔
𝑁𝑎 𝑠𝑎𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑟 𝑔𝑎 ƴ𝑎𝑛 𝑢𝑤𝑎𝑛𝑎 𝑚𝑢𝑠𝑢𝑙𝑚𝑎𝑖 𝑏𝑎𝑘𝑖 ɗ𝑎𝑦𝑎.
𝗕𝗢𝗢𝗞 𝗧𝗪𝗢
.
_______________________________
𝗖𝗛𝗔𝗣𝗧𝗘𝗥 𝗧𝗵𝗶𝗿𝘁𝘆 𝗧𝗵𝗿𝗲𝗲
________🎓 Kallon su yayi duk kan su kafin ya lumshe idanun sa ya buɗe yana zuba murmushi, hannun sa ya saka acikin aljihun sa ya ciro Keeys kana ya kalle su, batare da yace uffan ba, yaja hannayen su ko wacce ya saka mata keey ɗin, be bari sun yi magana ba yace da su
"Keey ɗin mota ce, kyauta na a gare ku".
Duk kan su ɗago keey ɗin suka yi suna murmushi cike da farin ciki, kafin kuma su rungume sa cikin tsagwaron murna suka soma masa godiya, Halwa har da hawayen ta
Hannu yasaka kawai yana shafa kansu kana yace, "to ku tashi muje ku ga motan ko".
Babu musu suka tashi suka fice, ai kuwa motocin sun bala'in burge su, ga su masu tsada ne daga gani, na Saleema green CE, ita kuma na Halwa fara, sai da duk kan su suka shiga ciki suka dudduba sai santi suke yi, duk da Saleema ba yau ta saba yin mota ba, but kyautar mijin nata sosai ya faranta mata, kuma ji take yi kamar ma bata taɓa yin mota ba sai akan wannan
Shi Khalil ma dariya sukai ta bashi, ganin abun nasu yaƙi ci yaƙi cinye wa sai murnan santi suke masa, sai da ya ja hannun su suka yo ciki sannan suka haƙura.
Dayake ranan a ɗakin Halwa yake, ai kuwa ranan yaga gata, sosai ta zage ta faranta masa rai
Shi kansa yasan yau ya samu tukuici.
Washe gari ma haka masu zuwa taya su murna sukai ta shigowa, musamman waɗanda suke cikin anguwan, da yamma kuma suka je nuna wa su Ummi motan nasu, Saleema ita ta tuƙa nata, shi kuma Khalil ya tuƙo na Halwa, tana zaune a gefen sa, sun jima agidan har magriba kafin su wuce gidan su Khalil ɗin, can kuwa sai wajen sha ɗayan dare suka baro gidan.
Tun daga ranan kuma sai Khalil yake fita da Halwa koya mata motan, idan be samu time ba tare suke fita da Saleema tana koya mata, ahaka har aka shafe tsawon watanni biyu lokacin ta ƙware sosai, gashi ta soma aiki, duk da wajen aikin su ɗaya da Khalil, wani lokacin tare suke zuwa, bare ma yanzu da cikin ta yashiga watanni shida, so be barin ta tana tuƙi sosai, tare suke tafiya.
Itama Saleema ya buɗe mata Chamis, a shagunan dake bakin layin anguwan su anan ya kama mata hayan ɗaya, duk idan zata tafi tare da Ahmad take tafiya, duk da yanzu yayi wayo sosai babu inda ba ya yawata wa da ƙafan sa, har magana ya soma, amma ba ta barin sa agida, sosai take ƙaunar yaron koda yaushe yana liƙe da ita, shiyasa ma har ƙyuya yake dashi, don be cika yarda da kowa ba sai ita.
Yau ɗin kasancewar Asabar ne gaba ɗaya a cikin su babu wanda ya fita, suna zaune a Parlour duk kan su
Khalil da Halwa suna zaune a ƙasa sun yi baja-baja da takardu, shi ke aikin ita kuma tana taya sa, yayinda Saleema ke kwance saman dogon kujera, ta ɗaura Ahmad a jikin ta dake barci, idanun ta a lumshe suke, jefi-jefi suke ɗan taɓa hira, Husna na can gefen dainning table da kayan wasan ta, ta baza su sai yi take yi tana surutun ta.
Sosa kanta Halwa tayi da hannun da take riƙe da Bairo, sai kuma ta ɗan juya kai ta kalli Saleema tace mata "sis Wai yau naji ki so slowly ne, ko wani abun na damun ki?"
Ɗan buɗe idanun ta tayi kaɗan kafin ta saki murmushi tace, "a'a babu abinda ke damuna, yau dai kasala nake ji wlh".
Khalil dake faman aiki a Lapton yana jin su be saka musu baki ba, ahaka suka ci gaba da zaman, sai dai zuwa lokacin Saleema ta dena saka musu baki gaba ɗaya, numfashi kawai take sauke wa a hankali tana sake ƙanƙame Ahmad dake jikin ta, kwana biyu kenan da zuciyarta take mata zugi duk ta hana ta sukuni, sai dai bata ba da ƙofan da za'a gane wani abun na damun ta ba, don ba ta son ta tayar musu da hankali, sai ta mayar da hankalin ta kan shan maganin ta, sai dai yau gaba ɗaya jikin ta ya matsa mata tunda bata sha ba, har soma kumbura tayi wanda in ba kayi mata kallon ƙurilla ba; ba lallai kagane hakan ba
Ci je leɓen ta tayi ahankali, kafin ta buɗe idanuwan ta da zuwa yanzu sun sauya kala, sun koma kore-kore, miƙe wa take ƙoƙarin yi jikin ta na rawa tana son zame Ahmad dake kanta
Ɗago kai Halwa tayi ta kalle ta, sai kuma tayi saurin faɗin "sis meke damun ki ne wai? Lafiyan ki ƙalau kuwa?"
Sai alokacin shima Khalil yaɗago kai jin tambayan da Halwa take mata, da alamun ruɗu a muryan ta, shima dai saurin tambayar Saleeman yasoma yi ganin yanda duk ta sauya lokaci ɗaya, gashi jikin ta sai rawa yake yi tana faman cije baki, miƙe wa yayi ya koma kan kujeran yana tallabo ta yasake cewa "lafiya kuwa meke damun ki? Ko wani waje na miki ciwo ne?"
Murmushi tayi tana lumshe idanun ta kafin tace, "ban sha magani na bane yau, shine zan tashi in ɗauk.."
Be bari ta dasa Aya ba yakatse ta da faɗin "ya salam! Meyasa to? Wannan ganganci ne ai".
Sai yaja tsaki yana faɗin "nima bansan me ya hau kaina ba yau ɗin ban tambaye ki ba, tun safe ma baki sha ba ko?"
Gyaɗa masa kai tayi kawai
Kallon Halwa yayi ransa duk babu daɗi yace, "je ki ɗauko min maganin".
Dasauri tatashi tana zare hannun ta da tariƙe na Saleeman, ɗakin ta tawuce ta ɗauko magani ta kawo masa, sai ta koma ta ɗauko ruwa cikin Fridge tasake dawowa ta miƙa masa
Shi da kansa ya bata, sannan yace ta kwanta ta huta, idan anjima jikin babu daɗi sai su nufi asibiti
Halwan ɗaukan Ahmad tayi tamayar dashi ɗaki, don Saleeman ta samu sake wa akan kujeran.
Gaba ɗaya sauran wunin ranan sai suka yi a rashin walwala, musamman ma Halwa da duk motsin ta yana kan Saleeman, gwara-gwara Khalil ya fita gab da magriba, kuma be dawo gidan ba sai da akayi isha'i.
Ita kuma Halwa taliya ta girka musu me sauƙi bayan ta idar da sallan magriba, zuwa lokacin ne Saleema ta tashi, duk hankalin Halwa kacokan yana kan ta sai tambayar ta take yi ko akwai inda yake mata ciwo? Komi ita take mata
To dayake dama jikin dasauƙi, ita dai Saleema sai dai tabi ta da murmushi duk da har yanzu zuciyar ta be dena zugi da radaɗin da yake mata ba, har sanda Khalil ɗin yashigo gidan shima ya hau tambayan ta, sai dai yaji daɗin ganin ta wasai da lafiyan ta, don har hira suka koma suna yi, nan ne hankalin su ya ɗan kwanta.
Washe gari Sunday har yamma Saleema lafiyan ta ƙalau, domin a ranan ma tafi samun lafiya fiye da jiya, sai dai da dare jiki yaƙi daɗi dole suka dangana ga asibiti.
Duk wani makusantan su tun a daren tuni yaji labarin rashin lafiyan ta, su Ummi duk sun hallara asibitin hankalin su duk a tashe, musamman yanda suka ga likitocin sai kai komo suke yi a ɗakin da aka kwantar da Saleeman, kuma sun ƙi ce musu uffan bare su san meke wakana.
Zuwa goman dare, lokacin wajen awanni uku da shigar da saleema sannan likitan ta ya nemi ganin su, gaba ɗaya suka ɗunguma wajen su, doctor ɗin be musu wata ƙwaƙƙwaran bayani ba, illa kwantar musu da hankali da yayi, sannan ya faɗa musu baza su samu ganin ta ba har sai gobe.
Zuwa lokacin Halwa tasha kuka kamar zata ƙarar da hawayen ta, da zasu tafi gida cewa tayi babu inda zata je, daƙyar su Ummi suka lallaɓa ta suka koma gida har Khalil ɗin aka bar Ummi ita kaɗai, tunda su ma su Abba duk sun dawo, kowa ya tafi da fargaba a halin da Saleema take ciki.
Zuwa washe gari tuni duk sun hallara, har lokacin dai babu wani labari daga wajen doctors, sai daga baya tukun Doctorn ya nemi gana wa dasu, dalla-dalla yayi musu bayani
Zuciyarta ta rigada ta gama kumbura har ta kai matakin da dole sai dai ko ayi mata Theater da gaggawa a cire mata a sauya mata, ko kuma tarasa ranta domin ya daina aiki gaba ɗaya
Babu wanda be girgiza ba da jin wannan zance, amma ya suka iya da ikon Allah?
Tuni anyi cuku-cukun yanda za'a samu ayi mata aikin a cikin kwana biyu, Abroad za a fitar da ita
Sai dai kuma Allah shi yafi su ƙaunar ta, a kwana na uku ranan da ake saka ran tafiya da ita, a ranan Allah ya amshi abun sa, Saleema ta amsa kiran Allah batare da ta sake shaƙan numfashin duniya ba, tunda tun lokacin da aka kawo ta komi na jikin ta ya dena aiki sai da na'ura.
Musalta muku yanda Familyn nan suka shiga ɓata lokaci ne, domin dai alƙalami na bazai iya muku bayanin tashin hankali da ruɗun da suka kasance ba, tun a asibitin ma Halwa da Ummi suka zube ƙasa a sume, shi kansa Khalil sai da jiri ya ɗibe sa aka kwantar dashi, ga dai shi idanun sa biyu sai dai komi nasa ya dena motsi har sai da yayi kusan awanni biyu ahaka, (ma'ana yayi suman Ido buɗe ne) sosai mutuwar ta shige sa, tabbas kuka rahma ne ga bawan da yashiga ruɗin rayuwa, sai dai Khalil ya kasa samun hawayen da zai zubar don yaji daɗi da salama a zuciyar sa, wannan dalili ne yasaka zuciyar sa tayi masa nauyi fiye da tunanin mutum, be iya ma buɗe baki yayi magana kawai ya zama tamkar status ne
Itama Ummi an yi Sa'a ta farka tun a time ɗin, shi kam Abba dauriya kawai ya ara ya yafa wa kansa, but duk da haka sai da yayi ta sharan hawaye sabida ya kasa jurewa.
Halwa dai bata farka ba har aka kai Saleema gidan ta na gaskiya, mugun hawa jinin ta yayi, kasancewar tana da hawan jini tun lokacin cikin Ahmad da aka harbi Khalil, bata farka ba sai a washe gari, sai dai duk wanda yake ɗakin a lokacin dole ne ya zubar da hawaye sabida tausayin ta, sai da Nurse suka yi mata alluran barci kafin suka samu sukuni, Dattijuwa me aikin su ita aka bari a wajen ta, tunda duk sun tafi gida karɓan gaisuwa
Sai a daren ranan ne Khalil yasha kukan sa ma'ishi, tare da raya daren don nema wa Saleema gafara wajen Allah Sarki, a zaune ya kwana a ranan, kuma koda safe be samu yayi barci ba ya tafi asibiti ganin lafiyan Halwa, bata farka ba alokacin, sai ya nufi gidan su Saleema inda anan ne ake karɓan gaisuwa.
Sai da yamma ne aka faɗa musu ta farka, dole suka ɗunguma zuwa wajen ta
A kwana biyu kawai ta fita hayyacin ta, ga ciki da take fama dashi, gashi kuma ba'a son masu irin laluran ta da tashin hankali, amma ya aka iya, sai dai kwantar mata da hankali kawai da suke tayi tare da mata nasiha me ratsa zuciya, da kuma nuna mata yin tawakkali ga duk wani ƙaddara da yasame mu, Mom CE me ƙarfin halin mata wannan maganan, don ita Ummi ma tana gida ba da ita aka zo ba
Sai dai Halwa ta kasa barin kukan, domin ko tayi yunƙurin dena wa, da zaran ta tuna Saleema ce ta rasu sai kukan ta yadawo sabo, an yi rarrashin duniya taƙi yin shiru, dole suka zuba wa sarautar Allah ido, duk idan kukan nata ya dawo yi take yi kawai babu me tsayar da ita, sai idan ta gaji don kanta sai tayi shiru anjima ta sake dasa wa, gaba ɗaya duk ta ya mutse ta saka wa kanta ciwo na ƙarfi da yaji, domin dai sai da tayi wajen sati ɗaya a asibitin kafin a sallame ta, ga hawan jinin ta da yaƙi sauka, likitoci sun yi mata maganar hakan zai iya shafan lafiyan ta da abinda ke cikin ta amma taƙi sauraron su.
Tunda suka koma gida ma babu lafiya, haka rayuwan taci gaba da Gara mata yau ciwo gobe lafiya, Khalil haka yake fama da ita ko kaɗan ba ya gajiya da mata hidima, duk wani farin ciki dake gidan nan nasu yanzu babu, rasa Saleema cikin rayuwan su ba ƙaramin giɓi yay musu ba, idan kashiga gidan sai dai kaji shiru ko motsin kirki ba sa yi
Su Husna sai dai me aikin su ke kula dasu, ita take musu komi.
Daga baya ma Mom zuwa tayi ta tafi da Halwan gidan ta, tunda sosai take jin jiki, kullum cikin ciwo take
Shima Khalil can yake wuni idan ya je aiki ya dawo, aikin ma ba kullum yake zuwa ba, saboda shima har yanzu ya kasa dawo da kuzarin sa, ya kasa manta Saleema a ransa, baya iya taɓuka komi.
Ahaka rayuwan taci gaba da tafiya har sanda cikin Halwa ya shiga watan haihuwa, lokacin ma tuni tana asibiti saboda yanda takoma sai kun tausaya mata, gaba ɗaya ta kumbure tayi suntum kamar ba ita ba, cikin yayi girma sosai har ba ta iya ma tafiya
Lokacin da tasoma naƙuda an ma fid da ran zata iya rayuwa, domin kwanan ta biyu tana a halin ciwon naƙuda, gashi hawan jinin ta yayi mugun hawa
Likitoci sun yi iya yin su amma ta kasa haihuwa da kanta, tunda jinin ta ya kai matakin da baza ta iya haihuwan ba, kuma komi zai iya faruwa da ita
Ganin idan taci gaba da zama ahaka zata iya rasa ranta dole aka shirya yin mata CS, ahaka aka shigar da ita ɗakin Theater bata ma san a inda kanta yake ba.
Khalil yasha kuka sabida tausayin matar sa, daƙyar ma ya iya saka hannu da za'a yi mata CS ɗin, dole Sameer da Brr. Tahir sukai ta tausan sa suna ba sa baki, su ma duk hankalin su a tashe, kowa yayi jugun ana jiran abinda hali zai yi.
Alhmadulillah an samu nasaran ciro wa Halwa yara biyu duk ka maza, kuma duk ka yaran suna a cikin ƙoshin lafiya, sai dai Mahaifiyar su ne da akayi zaton ta mutu ma, sai da likitocin suka yi iya yin su kafin suka gane tana da rai, Oxgyen suka saka mata sannan suka fito da yaran suka yi musu albishir da samun ƙaruwar twins
Sun yi murna sosai duk da suna cikin damuwa da halin da aka sanar musu Halwa na ciki, Khalil kawai aka bari ma yashiga wajen ta
Tunda ya shiga idanun sa na kanta, hawaye ne kawai suke kwaranya a saman kuncin sa, yana saka hannu yana share wa cike da raunin zuciya, ganin yanda Halwan nasa ta koma tamkar ba ita ba, har wani baƙi tayi sabida tsaban rame wa, tamkar ba ita ce wacce ta kumbura tayi himm ba, amma yanzu lokaci ɗaya ta zabge tamkar ba ita ba
A hankali ya taka ya isa gaban gadon, a ƙasa ya ajiye gwiwowin sa yana tura hannun sa cikin tafin hannun ta da aka saka mata Drip, damƙe hannun yayi sosai kafin ya ɗaura kansa saman cikin ta yana ci gaba da hawaye, hawayen tausayin ta, gaba ɗaya zuciyar sa ta gama rauni, bazai iya juran itama ya rasa ta ba, taya zai iya rayuwa idan ta tafi?
Ɗago kansa yayi yana kallon fuskarta, cikin sanyin murya yace, "Ina ƙaunar ki Halwa, don Allah.. kar ki tafi kema ki bar Ni, wlh idan na rasa ku duka zuciyata bugawa zata yi, don Allah kiyi haƙuri ki tashi, ki tashi mu raini ƴaƴan mu da Allah yayi mana kyautan su, kinji ki tashi don ALLAH.."
Dole yayi shiru sabida kukan da yataho masa, sai ya sake ɗaura kansa saman jikin ta yana ci gaba da tsiyayar da hawaye, sosai yake ji a jikin sa itama zata tafi ne
Yanda hawayen sa ke zuba ajikin ta hakan yasa take jin sanyin har cikin fatar ta, wannan dalilin ne yasa tafarka a time ɗin, idanuwan ta kaɗai ta buɗe tana bin ɗakin da kallo, tsawon sokonni kafin tagane akwai mutum kusa da ita, sai kuma daga baya ta fahimci Khalil ne, hakan yasa taɗago ɗayan hannun ta ahankali ta aza a kansa
Cakk ya tsai da kukan nasa yana ɗago kai dasaurin sa, nan idanun sa suka faɗa cikin nata da suka ƙanƙance suke a lumshe, daƙyar ma take iya buɗe su sabida halin ciwo
Be san sanda ya washe baki ba yana ta faɗin Alhamadulillah...
𝗧𝗢 𝗯𝗲 𝗰𝗼𝗻𝘁𝗶𝗻𝘂𝗲..✍️
_Nima ALHMADULILLAH anan na kawo karshen book ɗin 𝐁𝐑𝐑. 𝐈𝐁𝐑𝐀𝐇𝐈𝐌 𝐊𝐇𝐀𝐋𝐈𝐋, abun da na rubuta daidai Allah ya amfanar damu, kuskuren da nayi kuma Allah ya yafe min._ 𝑎𝑚𝑖𝑛
𝐼𝑛𝑎 𝑚𝑎 𝑚𝑎𝑠𝑜𝑦𝑎𝑛𝑎 𝑓𝑎𝑡𝑎𝑛 𝑎𝑙𝑘ℎ𝑎𝑖𝑟𝑖, 𝑠𝑎𝑘𝑜𝑛 𝑘𝑢 𝑚𝑎𝑠𝑜𝑦𝑎 𝑦𝑎 𝑖𝑠𝑜 𝑔𝑎𝑟𝑒 𝑛𝑖 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑏𝑎𝑟 𝑧𝑢𝑚𝑢𝑛𝑐𝑖 𝑛𝑎 𝑔𝑜𝑑𝑒 𝑘𝑤𝑎𝑟𝑎𝑖
𝐽𝑖𝑛𝑗𝑖𝑛𝑎 𝑎𝑔𝑎𝑟𝑒 𝑘𝑖 𝐒𝐇𝐔𝐆𝐀𝐁𝐀 𝐒𝐀𝐅𝐍𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔 𝐉𝐀𝐖𝐀𝐁𝐈, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑘𝑎𝑟𝑎 𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑘𝑎 𝑘𝑖, 𝑦𝑎 𝑘𝑎𝑟𝑒 𝑘𝑖 𝑎 𝑑𝑢𝑘 𝑖𝑛𝑑𝑎 𝑘𝑖𝑘𝑒, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎𝑠𝑎 𝑘𝑖 𝑓𝑖 ℎ𝑎𝑘𝑎, 𝑓𝑎𝑡𝑎𝑛 𝑎𝑙𝑘ℎ𝑎𝑖𝑟𝑖 𝑘𝑎𝑤𝑎𝑖 𝑧𝑎𝑚𝑢 𝑟𝑖𝑘𝑎 𝑚𝑖𝑘𝑖 ℎ𝑎𝑟 𝑚𝑢 𝑘𝑜𝑚𝑎 𝑔𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑏𝑎 𝑘𝑢𝐧𝑔𝑖𝑦𝑎𝑟 𝑘𝑖 𝑛𝑎 𝐏𝐞𝐫𝐟𝐞𝐜𝐭 𝐖𝐫𝐢𝐭𝐞𝐫'𝐬 𝑛𝑎𝑠𝑎𝑟𝑎, 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑠𝑎𝑘𝑒 𝑑𝑎𝑢𝑘𝑎𝑘𝑎 𝑠𝑎 𝑓𝑖𝑦𝑒 𝑑𝑎 𝑛𝑎 𝑦𝑎𝑛𝑧𝑢 𝑎𝑚𝑖𝑛.
𝑩𝒊𝒔𝒔𝒂𝒍𝒂𝒎 𝒎𝒂𝒔𝒐𝒚𝒂🤝, 𝒌𝒖 𝒕𝒔𝒖𝒎𝒂𝒚𝒆 𝒏𝒊 𝒂 𝒔𝒂𝒃𝒐𝒏 𝒃𝒐𝒐𝒌 𝒅𝒊𝒏𝒂 𝐑𝐀𝐔𝐃𝐇𝐀 𝒏𝒂𝒏 𝒃𝒂 𝒅𝒂 𝒋𝒊𝒎𝒂 𝒘𝒂 𝒃𝒂. 🥰😍👌
𝐉𝐢𝐤𝐚𝐫 𝐋𝐚𝐰𝐚𝐥𝐢 𝐜𝐞 𝐭𝐚𝐤𝐮 𝐦𝐞 𝐤𝐚𝐮𝐧𝐚𝐫 𝐤𝐮...❤️ 𝕃𝕠𝕧𝕖 𝕪𝕠𝕦 𝕗𝕒𝕟𝕤.