Tun da jirgi ya ɗaga daga Qahɗaanie bai tsaya ko ina ba sai Leonardo da Vinci international Airport Wanda aka fi sani da fiumicino Airport da ke birnin Rome, can kusa da kudanci Kasar.. Sun iske motoci na jiran su daga ofishin jakadancin Qahɗaanie, nan su ka isa su ka bada shedan isowarsu sannan nan ma aka basu kuɗi daga mai martaba sannan aka tura wa'inda zasu raka su lardin Milan.
Jirgin sojin Qahɗaanie ya sake ɗaga su daga fiumicino airport zuwa Malpensa airport da ke birnin Milan inda a nan su ka iske Stefano Angelo yana jiran su. Anan AbdulHaleem ya sallami duk wani ɗan rakiya don bai ma son a san inda za su sauka. Nan fa su ka so su yi gardama don mai martaba ya umurce su da su tabbata sun ga gidan da danshi zai sauka sannan a aje wasu daga cikin hukumomin tsaro a wajen don kula da shi. Amma AbdulHaleem ya tuɓure ya ce babu wanda zai bi shi, ya gode da karamci kuma ya bar Qahɗaanie kenan har abada.
Labarin nan ya girgiza mai martaba don kuwa ba su bar filin jirgin ba sai da su ka kira shi a waya su ka faɗa masu. Yaji takaicin bakin zuciya irin ta AbdulHaleem amma Ace ana nuna masa gabas yana shi kudu zai fuskanta. Bai ce komai ba sannan bai nuna a fuska ba sai ya cigaba da zancen da su ke da yan majalisa.
Faisal Musayyib, ɗaya daga cikin sojojin da su ka rako su AbdulHaleem, kuma idon Ummu Hafsa ne ya sa waya ya kira ta bayan ya ɓoye kan shi.
"Allah ja zamanin uwar sarkin gobe, ai kam dai zance ya tabbata, ya fusata ya aiko ma mai martaba zantuttuka marasa daɗi a cewarsa shi ba zai sake dawowa Qahɗaanie ba, ina ga lokacin dawo da AbdulHaseeb yayi don ya kasance kusa da mai martaba" ya faɗi cikin murna da farin ciki.
"faɗi abin da kake so Goron Albishir na aika ma iyalinka"
"Ummu duk abin da kika bada ina farin ciki, amma ina so a ba ni shugaban rundunar tsaro ta daular Qahɗaanie" yace don shi kanshi burin sa kenan. Don tun da ya taka mukamin manjo general yake Harin wannan mukamin.
"toh Faisal za'a kwatanta, na gode Allah ya muku albarka" tace tana murmusawa.
Faisal Musayyib jinin masarautar Qahɗaanie ne sannan kuma miji ga er Ummu Hafsa ta huɗu, wato Maimuna. Tun bayan aurensu ya shiga sojin Daular Qahɗaanie, kasancewar sa jinin masarauta bayan naɗa sarki Abdoul Jabbar ne ya maida shi karkashin masu kula da masarauta (Royal guards). Aminci da kuma kallon ɗa da sarki ke masa yasa mai martaba ya sa shi jagorantar tafiyar AbdulHaleem saboda hankalinsa bai bashi ba, ya san ana iya kashe masa ɗa yana ji yana gani.
***
Adjetey na zaune ranshi duk ba daɗi, yana ji da Aamir alhamzie, sannan wani banza na neman ya kassara masa, ko ba komai zaman sa a Masar ya koyi larabci, yanzu ya san ko bai karanta shari'a ba zai iya kwatar ma Alhamzie duk wani yanci ba tare da an cuce shi ba.
Wayar sa ya ɗauka ya sake kiran Aamir,
" Ubana da ya fi kowa" ya ce yana dariya
"ka na cike da albarka, naji sauki sosai, an cire harsashin don a kafa ya harbe ni" yace yana dariya
"MaashaAllah! Zan dawo nan kusa, ya kamata mu haɗa kai da ishmalie mu kwace Qahɗaanie, ko AbdulHaseeb ba zai yi sarautan ba" ya ce cikin kufula
"Ai ance ɗan iskan ya gudu, da ya jira mun gwada karfi da shi amma tun da uban sa na girmama ni kuma yana girmama zumunci za mu ɗaga musu kafa,, amma za mu buɗe namu daular a sannu sai mu ci su da yaki" yace yana so ya hana adjetey zuwa don ya san in ba su bari ya samu ilimin ba, ba za su wani samu nasara yanda su ke so ba.
"Abba ka bani dama in nuna kwanji na, ka yi hakuri in dawo. Sarauta ai ba sai da ilimin shari'a ba, mu karfi da yaji za mu kwata. Ka amince min kawai" ya ce yana mai magiya yana nuna masa yanzu da zafi zafi akan bugi karfe. Har sai da ya amince sannan ya aje wayar. Nan ne Zubaida ta shigo da cikin ta da ya tsufa, in akwai abin da adjetey ke so yana bayan matarsa da abin da ke cikin ta. Rungumo ta yayi ya zaunar a Saman cinyarsa. Sannan ya ce da ita
"kwana biyu na kasa gane kanki me ke damun ki" ya ce mata cikin rada.
"Ammie ce, sati biyu kenan ban ji daga gareta ba, kace su Fatima sun bar Qahɗaanie amma kuma ba ta kira ta bamu labari ba, sati biyu fa, ko dai mutuwa tayi" tace cikin hawaye. Hakan ya sa ya ji tausayinta don shi ya toshe lambar Ammie daga wayar ta. Ciro wayar sa yayi ya kira ta bugu uku ta ɗauka
"Ina kuma shige Zubaida" tace muryar ta na rawa
"Mun yi tafiya ne Ammie" ya faɗi, Zubaida ta sa ido tana kallon da ya sharara. Sai ya rufe mata baki ta hanyar sa mata wayar a baki.
"Ammie na yi kewar ki" Zubaida ta faɗi,
"kin san kuwa Ramlatie na hannun ɗan yan kan kai ne, mijinta shan jini yake yai arziki, Abbie kuma ya sake ni" tace tana sakin kuka, don da fari ta yi tunanin sharrin su fatima ne, sai da ta koma gida yayanta ya sa bincike nan duk hotunan Nasiruddeen ya fito a matsayin ɗan fashi. Sai kuma inda ya fito a matsayin ɗaya daga cikin member na wani club a Ghana wacce ake zargin masu shan jini. Nan dangin ta su ka sa ta gaba da sunan mai siyar da ya'ya saboda son abin duniya.
"ai ko ni ma ɗin ɗan fashi ne, don in kisa ne ba zan iya sanin adadin mutanen da na kashe ba, yanzu ya kenan" Adjetey ya faɗi yana mai katse wayar. Hajiya Amina kuwa suma tayi a wajen don Tsabagen tsorata da tayi.
Ashe ba yawa, da naji hannu na ya fara zafi se nayi tunanin ya kai 5k words ashe ko 2k bai yi ba. Anyway zan kokarta na muku gobe
Insha'Allah.
Ina jin daɗin comments ɗinku, kar ku
gaji, ku yi comment ku yi voting ku
gayyato ahlinku da aminanku.
Shin akwai wani gyara da kuka gani,
ku na iya gyara min ta safiyyahjibril@gmail.com ko kuma
sako ta nan.
Nagode
Ummu-Abdoul
Add Vote
Mahaifiyarta ce ta zo wucewa ta same ta kwance a sume, ruwa ta samu ta watsa mata nan ta farka a firgice. Sanin da tayi abin da ke damun ta ya sa ta cewa " Ai Amina ba ki ga komai ba, ai duk wanda yace bakar tukunya ɗiya ce toh ya goya ta da farar zani" mtswww ta karasa cikin jan tsaki. Kuka sosai Ammie ta saki, shike nan ta yi asarar ya'yanta dama su kenan Allah ya bata kuma ta aurar da su ido rufe. Sai da ta ci kukan ta ma ishi sannan ta mike ta fita da niyyar zuwa ta samu Alhaji Yahuza don ta roke shi ya taya ta neman ya'yanta. Haka ta ke zuba tafiya har ta iso ofishin sa, faɗi ma sakatarensa cewa ita ɗin matarsa ce ya sa ya barta ta shiga.
"Abbie don Allah ka taimaka min, ka maida auren mu wallahi ba zaka sake samu na da matsala ba" tace tana kamo kafarsa. Janye kafarsa yayi ya cigaba da rubutu ita kuwa kuka take ranta ɗaya. Ganin kukan yaki ci ya ki cinyewa ne ya tashi ya iso gareta
"Zan maida ki ɗakin ki in har za ki kwato min ya'ya na daga hannun miyagu. In kin yi haka a yanzu ma sai in maida ki don baki kammala idda ba" yace murmushi kwance a fuskarsa, wani murdawa da cikin ta yayi sai da ta zabura ta kalle shi a firgice.
"Kai ne karfi na Abbie, ka da ka min haka, wallahi ina cikin nadama da dana sani, ka yi min aikin gafara ka taimaka min" tace cikin kuka, kwarai ya so ya fara tausaya mata, amma sai ya basar ya nemi cilla zuciyar sa wani gun daban saboda kada ya tausaya mata.
"Haba Amina, ni ne nan shege mai hana aure mai haiqe ma ya'yansa" ya ce yana mai jin zafi a ransa. Bai kara uffan akai ba ya ɗaga hannu ya nuna mata hanyar kofa, ba ta Musa ba ta gyara fuskarta da hawaye ya kwanta mata ta fice jiki babu kwari. Zuciyar ta na aunowa kamar zata fashe sai ta fasa. Allah cikin ikon sa ne ya kaita gida lafiya don kuwa idon rufe ta ke tafiya.
***
A can Misra kuwa, mutuwar tsaye Zubaida ta yi a wajen, Jin kalaman Abdullahinta ga Ammienta. Shi kuma sai da ya furta sannan ya tuna ai tana zaune a wajen sannan duniya in da akwai abin da Allah ya jarabce shi da so toh Zubaida ce da abin da ke cikin ta, ganin irin daskarewan da tayi ya sa shi ɗan firgita. Ruwa ya ɗebo ya watsa mata, firgigit ta tashi tana zazzare idanu. Lumshe ido ta sake yi nan duk abin da ya faru minti biyar da su ka wuce su ka dawo mata, muryar mahaifiyarta da na mijinta ke mata tsuwa kowanne daga ciki na maimaita abinda kunnuwan ta su ka jiye mata.
'anya ba mafarki nake ba' zuciyar ta ya raya mata hakan amma ganin mijinta zaune da waya a hannu ya sa ta gaskata cewa anyi hakan.
"ke yanzu kin yarda anyi hakan kenan? Ai kawai na faɗa mata ne don na ga alamun an fara cin nasara a kanta, so ake a raba mu fa. Ban san me ya sa za ta yarda da" yace mata cikin rada bayan ya rungume ta tsam a jikin sa kamar yana tsoron rasa ta.
"Amma kuma ai ka san mahaifiyata ce ko" tace tana mai share hawaye da kuma samun zuciyar ta na washewa
"Ki yi hakuri, zan kira na bata hakuri" yace yana manne bakinsa akan nata hakan ya sa ta yin shiru. Cikin salonsa ya mantar da ita damuwar da ke tattare da ita su Lula duniyar da su kaɗai su ka san da shi.
Yinin ranar shi yayi komai na gidan tun daga girki har zuwa shara da komai, daidai da abinci shi ya ciyar da ita a baki yana yi yana kalamance ta, hakan ya sa ta kara so da kaunar mijinta sannan ta qara amincewa babu wacce ta kai ta dacen miji. Sai da ya tabbatar da ta yi barci sannan ya jawo kwamfutar sa ya shiga yanar gizo. Bincike yake akan dabarun da zai fishe shi don shi dai ya ɗauki alwashi ko zai sadaukar da rayuwar sa sau dubu ne sai ya ga bayan Qahɗaanie, don a ce wasa babu abin da zai taɓa Alhamzie ya sa ido ya barshi.
Am so sorry dear ones, wallahi na kasa typing ne, duk na ɗauko system don na yi typing se in kasa.
Akwai whatapp grp ga mai ra'ayin shiga, don zumunci. Mata zalla, WhatsApp me on 08157284163.
BAYAN SHEKARU HUDU
Matashiyar mata ce zaune, kallo ɗaya zaka mata ka san ta haura shekaru talatin da biyu a duniya, a fakaice zaka rantse babu wanda ya kaita farin ciki amma nace ma kallon kwayar idonta zai haska ma mai kallo damuwa a cikin idanunta.
A zahirance talabijin take kallo amma hankalinta gaba ɗaya ya tafi wata uwa duniya wanda hakan ba zai rasa alaka da damuwar da idanunta ke nunawa ba.
"Haba! Kashe kanki kike son yi? Nayi sallama yafi a kirga amma gaba daya baki doron duniyar nan, na gaji da wannan ɗabi'a fa" ya ce cikin faɗa, yana shirin barin wajen yaji an ambaci sunan da dole ya sa ya dawo ya maida kallo ga tashar Aljazira da ta bari kunne
"Daular Qahɗaanie na fama da gagarimin barazana don maganar da ake yi yanzu yan ta'addar Ishmalie sun yi nasarar kwace gwamnatin Daular, ita dai daular Qahɗaanie daula ce da Larabawa su ka kafa shi kusan shekaru dubu daya da su ka wuce, amma chuɗanya da su ka yi da mutanen yammacin Afirka musamman Hausawa ya sa Al'adun su ya gauraye ya zama ga dai shi nan. A yayin da ake ɗauko wannan rahoton ba'a san inda iyalan masarauta su ke ba bayan mutuwar uwargidan mai martaba da aka kashe yayin musayar wuta tsakanin yan ta'adda da sojojin Qahɗaanie..
Su dai ishmalie su na da'awar su kaɗai ke da ɗarikar musulunci na gaskiya yayin da sauran ke kan ɗarika mai cike da son rai da kwaskwarima, su na da littafin su na gaskiya wanda ba qur'ani ba sannan ba su yarda da ko wane hadisi ba don kuwa a cewarsu an sa son rai a ciki... " bai iya kai wa karshe ba ya kashe talebijin ɗin, da dinsa ɗaya yaran sun janye uwarsu da bai san ya zai yi da ita ba.
" Lokacin ɗaukan fansa yayi" ya faɗi a bayyane yana mai jawo na'urar sa mai kwakwalwa ya haɗa da yanar gizo ya shiga wani wajen da shekaru huɗu kenan rabon da ya garzaya cike da burin ba'a canza lambobin sirrin ba. Bai sha wuya ba sai ga shi yana hango masarauta. Mutanen da ke zagaye da ita ɗauke da manyan makamai, tun daga kan bindigogi da tankokin yaki wanda na sojojin Qahɗaanie ne amma kuma wa'inda ke sakaye da wajen wasu mutane ne daban.
"Yaa Mugithu Agithnie" ya faɗi yana furzar da iska. Wasu lambobi ya sake latsawa nan ya hango majalisa tare da wani baqin mutum zaune akan karaga, a shekaru ba za su wuce tsararraki ba amma kuma da gani gwani ne a ta'addanci. Waya aka miko masa nan ya amsa ya kara a kunne, sai ta abin yayi don ya ji yo maganganunsa amma bai ji sosai.
"Haba zuby, ki kula min da yara na, na faɗa miki jihadi mu ke yi, sannan na sa an fitar da Ammie Kasar waje, shi kuma Abbie ya na haɗe da tsohon sarki. Ni haɗin kanki nake nema Qahɗaanie nan da kwana goma za mu chanza masa suna da tuta. Ina sonki da yawa ki kula da yaran" yace yana jefa sumba a iska.
Zuciyar sa na bashi ko wanene wannan yana da alaka da matarsa amma ba ya son ya yarda, chan dabara ta faɗo masa, tashi yayi tsam ya nufi ɗaki wajen matar sa.
"Zan je Qahɗaanie, amma ni kaɗai, in mai martaba ya yafe min sai in dawo in ɗauke ku. Babu abin da nake so sama da farin cikin ki, ki kara hakuri, Abbie da kowa na cikin kwanciyar hankali kin ji. Ya ce yana shafo cikin ta da ya ɗan tasa. Bata ce komai ba sai murmushi don kuwa wata ɗaya kenan da ta fara mafarki da iyayensu da yan uwansu, tun lokacin ta sa rigima akan su koma Kasar su ta gado duk kuwa da cewa ta fi mijin nata amfana da birnin Milan ta Kasar Italiya.
***
Tun bayan rabuwan su da sojojin da su kai musu rakiya, da ɗaukan su da Stefano Angelo yayi bai tsaya da su ko ina ba sai Corso Venezia anguwa ce na manyan masu kuɗi wanda ya kunci abubuwa na ban girma da jin daɗin rayuwa. AbdulHaleem ya so ya gardama amma sai Stefano ya nuna masa zaman sa anan shine daidai, hakan kuma zai basshi ikon samun abin da yake burin samu saboda akwai wani shugaban mafia Fronteno clemenza da ke zaune a nan wajen kuma yana son ya maida shi ubangidan AbdulHaleem.
Sai da su ka dauki kwanaki su na zagaye gari inda duk su ka mace da son Kasar ba ma Milan city kaɗai ba. Gini ne na alfarma inda da gani anyi ɓarna dukiya wajen sarrafa wannan gine-ginen. Su na ganin wajajen su na qara godiya ga Allah AbdulHaleem na cike da burin son maida Qahɗaanie fiye da haka nan.
Ranar farko sun fara da manyan wajen kasuwanci ne inda su ka fara Via Montenapoleone Wani sashi na Quadrilatero d’Oro
Via Montenapoleone ba da mahimmanci sosai a fannin kasuwanci, don kuwa ana iya ce mata masaukin tsadaddun kaya kamar su Gucci, Prada da Valentino. Sannan ana samun kaya yan kanti da hadaddun kayan da aka yi su da fatu, za'a iya cewa nan ne ma mafi a'ala a wannan fannen, ana samun kayayyakin Bottega Veneta, Salvatore Ferragamo and Fendi hakan ya sa ake kallon wajen a kasuwa da ake samun kayan fatu masu lamba ɗaya (world class leather product)
Daga can sai su ka garzaya Corso di
Porta Ticinese
Tana zuwa wajen zuwa ta London ya faɗo mata a rai don kuwa gani yayi ya mata kama da Portobello Road saboda kayan data gani da su ke zarra (unique clothing) , daga nan sun je Corso Vittorio Emanuele
IIwanda ke kusa da Piazza del Duomo city square a tsakiyar Milan city, a nan ta ga shagunan Zara, H&M, Mango da Bershka .
Sun je Corso Buenos Aires, Nan sai da tayi kwalla don tunawa da tayi da Abbie, lokacin da su ka je Paris don wajen exactly Oxford Street da ke London da kuma avenue din des Champs-Élysées da ke birnin Paris.
Ranar a gajiye ya su ka isa gida bayan sun tabbatar da sun siya duk abin da zasu bukata da kuma wasu abubuwa da su ka san zai amfane su.
Washe gari su na fita su ka sake zagaye gari sun je wajajen kamar su : (hotuna yafi ko 😀)
Add Vote
Haka su ka cigaba da zagaye har su ka gama ganin gari sannan Stefano ya samu ya haɗa shi da Don clemenza.
***
Duk wani gata da mace za ta nema toh Fatimah ta samu wajen AbdulHaleem, don baya jira ta nema kafin ya bata duk kuwa da takan ji zafin raba ta da dangin ta da yayi da yanke duk wani hanyar zumunci da su.
Ko da cikin ta ya cika wata tara, daina fita ko ina yayi yana manne da ita don kada haihuwa ta zo musu yana nesa da ita. Allah cikin ikon sa kuwa ranar da naquda ta zo basu ɓata lokaci ba Allah ya sauke ta lafiya in da ta haifi yan uku duka mata.
Haihuwan da ta yi ya sa Don clemenza ya ce su dawo cikin gidan shi don matarsa Martina clemenza ta kula da Fatima. AbdulHaleem bai mu sa ba don ya yarda da amincin su duk da kasancewarsu maabota littafi yan ɗarikan katolika, ba su yarda su aikata wani abin da zai taɓa amincin da wani ya basu ba. Don clemenza ya yarda da amana ya yarda da abota sannan duk runtsi baya manta alkhairi.
Haɗuwar sa da AbdulHaleem ya gwada shi ya fi a kirga tun daga kan kuɗi har mata, kuma AbdulHaleem ɗin ya tsallake, a nan ya kara yarda da zancen wani ɗan uwanshi Solozo da ya ce masa babu mutanen da su ka kai musulmi Amana saboda su addinin su ta koyar da su hakan, toh duk wanda ya gani da akasin haka toh ya saɓa ma abin da addininsu ya zo masu da shi.
***
Sun koma gidan Don kuma Fatima na samun kula kamar yanda ta san in da gidan Abbie ta je za ta samu ko ma fiye da hakan.
Ranar suna Don da kanshi ya shirya musu k'warya k'waryan liyafa, ya gayyaci abokan arziki da yan uwansa gida ya cika makil, abu ɗaya yayi don ya burge AbdulHaleem shine tsaftace liyafar, duk wani abu da ya jibinci giya ko haram a musulunci bai bari an kawo wajen ba. Yara su ka ci sunan Hafsah, Maryam da Aisha. Saboda sunan iyayensu mata da kuma sunan uwar muminai Aisha RA. Rayuwar su na tafiya gunin sha'awa yaran na girma suna canza kamanni.
Don ya kasance maabocin shan giya, kuma maabocin ba da labari yayin da AbdulHaleem ya kasance gwani a sauraro da kuma fahimtar labari. A zamansa da Don ne ya fahimci kurakuransa wajen qaddamar da mulki. A nan ya fahimci ba ragwanci ke sa mahaifinsa yin shiru yayin da aka nemi taka shi ba, a nan ya fahimci ba'a tsoratar da mutum da kalamai don a ci galabansa sai dai ayi gaba da gaba ko kuma a yi kisan mummuke wanda na karshen ya ke ragon salo.
Don na bashi labarin yanda mafiya kan ci yaki a kasar Italiya, yanda ake daraja mafiya fiye da wani hukuma da yanda su ma su ke kwantar ma talakawa hakkin su matukar talakawa sun mika wuya sun nuna mafiya ta fi hukuma daraja.
"A da duk yankin nan babu wanda aka raina sama da ni" Don ya ce da AbdulHaleem wata rana bayan ya cika cikinsa tatil da giya. Sai da ya kwankwada sannan ya cigaba da faɗin
"lokacin akwai wani shege nan, takamar sa kullum duk abin da wani zai aiwatar se ya bashi da ga cikin riba, wata rana kawai se ya tsare ni wai zaitun ɗin da na ke siyarwa dole sai na bashi kashi talatin cikin dari na riba na, lokacin kwata kwata jarin bai wuce lira dubu goma ba, ka san ba'a koma euro ba, in ban manta ba sai a shekarar 1999 aka maida shi euro daga Italian Lira. Ban Musa masa banna bashi abin da yake bukata a bainar jama'a amma na riga shi isa gidan sa na aika shi lahira, shi ne mutum na farko da na fara kashewa, ban faɗi ma kowa ba amma kawai se na tsinci kaina mutane na bani wani irin girma na musamman.
Bayan kwana biyu wani yayi ma kawar matata fyade, lokacin ita ba ta yi aure ba, ta zo gare ni tana kuka cike da bakin ciki na ce mata za ta iya aurensa tace min eh nace toh an gama.. In faɗa maka gayyatar sa nayi gida na nace da shi
Add Vote
Get the App
BA GIRIN-GIRIN...
by Ummu-abdoul
YOU ARE READING
MYSTERY / THRILLER
BAN YARDA A YI COPYING DAGA NAN ZUWA KO INA BA, YIN HAKAN SHIGA HAKKIN MALLAKA NE ANA IYA
arabs despera
19 : Girbi
Start from the beginning
Yan Uku @ 3yrs
***
A Qahɗaanie kuwa tun bayan tafiyar su Fatima da rashin jin su hankula su ka tashi, musamman na mai martaba, take ya yi Dana sanin korar sa da yayi. Addu'a su ke Allah ya bayyana su har zuwa lokacin da Abbie ya samu hotunan yan uku. Da murna ya garzaya fada ya sanar ma mai martaba tare da nuna masa hotunan.
Farin cikin da ahlin gidan su ka shiga ba'a magana take mai martaba ya haɗa gagarumin liyafa ya ciyar da talakawa irin abin da ya ci a ranar, gidajen talabijin da jarida suka ɗauki hotunan yara anan nuna wa.
Abin da ya ba Ummu Hafsa haushi a wannan shine faɗin da yan jarida keyi na " Yarima mai jiran gado ya samu qaruwa" ga hotunan yara ga na su da su Fatima lokacin bikin su. Hakan ya sa ta kai ma Alhamzie ziyara, kasancewar ta ɗauke kafa daga zuwa don a tunanin su tun da AbdulHaleem korarre ne a fada toh tabbas AbdulHaseeb ne sarki, hakan ya sa tayi sanyi ba ta san shi ahamzie yana can yana shirye shiryensa ne da yan kungiyar ISMAALIE.
Bayan sun gaisa ta ke mika masa jaridar da ta riko masa don shi ma ya gani. Bakin ciki ya cika masa zuciya don Sam bai yi tunanin AbdulHaleem na da rai ba don shi ya aika a kashe shi kuma an dawo masa da hotunan gawar da aka ce a AbdulHaleem ɗin ne.
"kina so ki ce min yana da rai har ya samu qaruwa ba ma ɗaya ba har uku? Adjetey ya dawo min da tabbacin ya kashe shi ni kuma ban taɓa aika shi ya dawo min da abin da kunnuwa za su yi takaicin sauraro ba" yace yana huci kamar macijin da ya hadiye miliyan talatin da shida😂😂😂.
"Toh shi ne abin ji ai, abin takaicin an kasa gane Kasar da su ke, don naji kamar mai martaba na faɗin suna Saudiyya ne, ni ban ma san ya za'a yi ba" tace itama hankali a tashe
" Ba damuwa dama akwai shirin da mu ke yi, za mu aiwatar nan ba da jimawa ba, ka da ki damu, komai zai tafi yanda muke so" ya ce yana dariyar mugunta.
***
Daga nan su ka fara aiwatar da da'awa a anguwannin da ke wajen Qahɗaanie, nan su ka fara halatta mu su wasu daga cikin haramun, su na fatawar sau uku mutum zai yi sallah a rana, da safe, da rana a haɗa azahar da la'asar, sai magriba da isha'i ma a tare za a yi. Azumi ba wajibi ba ne kawai mutum ya rike istigfari, da dai sauran fatawowi na shagala. A take su ka samu mabiya mara son yin ibada.
Ko da labari ya iske mai martaba, gayyatar su yayi su ka zauna, nan ya musu wa'azi ya nuna musu illar abin da su ke yi, sannan ya ja musu kunne akan baya son abin ya sake tasowa in ba haka ba zai hukunta su. Daga haka sai su ka fara ɓoye kansu, a hankali kuma su ka cigaba cin mutane suna samun mabiya saboda kyaututtuka da su ke samu daga ISMAALIE.
A cikin shekara biyu sun samu mabiya daga jami'an tsaro anan su ka tara makamai ba tare da Sarki ya ankara ba, sai da suka kwashe duk wani makami mai amfani sai suka sa ma maadinan makamai wuta cikin dare. Wannan abin ya tayar da hankalin mai martaba, AbdulHaseeb da abdulbaar ne su ke bashi baki da nuna masa zasu jagoranci siyo wasu makamai.
Fara sata, fyade da fashi da ake yi ya sa zaman Qahɗaanie ya fara gagaran yan daulan, nan sarki ya shirya ma duk wani yayan sa da iyalansu tafiya zuwa Kasar Sudan in da shugaban Kasar ya tabbatar masu da samun tsaro zuwa wani lokaci. Bayan tafiyar su kuma ya fara tsara ma yakar ISMAALIE don ya san abu na farko da za su yi masa shine kashe masa yan uwa shi ya sa ya nema masu mafaka.
An share shekaru biyu ana fafatawa, an rasa rayuka da dama daga yan ISMAALIE har mutanen daula. Duk yanda aka so a kamo Alhamzie bayan an tabbatar da yana da hannu a wannan ta'addanci abin ya faskara saboda mafaka da aka ce ya samu a wata kasa.
***
Bayan nasara da masarautar Qahɗaanie ta ba da shelar ta samu tare da kashe manyan yan ta'adda ne, kungiyar ta'addanci ta ISMAALIE ta aiko da wasikar sulhu tare da mika wuya ga sarki mai adalci don ya musu hukunci cikin tausayawa. Kwarai sarki Abdul-Jabbar yayi farin ciki ya sanar ma duniya nasarar da ya samu sannan ya amince ma yan ta'ada akan su hadu a gidan masarautar garin.
Ranar haɗuwar ta zo sarki ya tare su a ɗakin majalisa daga shi sai magatakardansa sai wakili daga sojin daular da kuma yan jarida.
Bayan sun zauna ne ne suna cikin magana wayar mai martaba tayi kara, in da aka sanar masa da tashin bama bamai guda uku a cikin babban kasuwar daular, sannan kuma ana wulakanta mata da su ke kasuwan. Dago kansa da zai yi sai ya bindigogi hudu a saitin kansa, tare da tasa kanshi zuwa da umurtan sauran da su biyo su in ba haka ba za su harbe mai martaba. Babu musu su ka bi su zuwa wani lungu can da ba'a san da shi ba. Ummu Hafsa ce taga Gilmawansu nan ta saki ihu hakan ya sa ɗaya daga cikin yan ta'addan sakin mata harsashi a ciki wanda yayi sanadin mutuwar ta.
Add
FYADE; SAKACIN IYAYE
Safiyyah Ummu-Abdoul
Safiyyahjibril@gmail.com
Yanda rayuwa ke tafiya, da wuya a wayi gari, rana ta fito ta faɗi ba tare da an ji labarin fyade ba daga kusa ko daga nesa. Kullum al'umma ba su da aikin yi sai tsine ma masu aikata wannan mugun aikin ba tare da an ɗauki mataki akan su ba. Hakan ya sa abin ya girmama har ya tashi daga munzalin yi ma yara mata fyade ya koma ga yan maza.
Abin ya munana har ya kai ga samari ma ba su tsira ba don shaqa musu kayan maye ake don a ci galaba akan su. Duk wannan na faruwa ne saboda sakacin iyaye.
Yanzu a duniyar da muke ciki babu wani gata da ɗa musulmi ke da shi sama da azkar musamman wa'inda manzo SAW ya ambace su da kariya. Maimakon iyaye su maida hankali wajen koya ma ya'yan su azkar ɗin nan sai aka maida hankali wajen sama musu ababen more rayuwa.
Yin azkar din fita gida na sa mutum ya zauna karkashin kulawar Allah har ya koma gida, ga addu'ar kamar haka BISMILLAHI TAWAKKALTU ALAL LAAHI WALA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH... ALLAHUMMA INNIE AUZU BIKA AN ADILLA AU UDALLA, AU AZILLA, AU UZALLA, AU AZLIMA AU UZLAMA AU AJHALA AU YUJHALA ALAYYA.
Addu'a ce mai sauki, duk yaron da zai iya haddace waka toh lallai zai iya haddace ko kashi na farko na addu'ar ne. Saboda haka wajibi ne ga iyaye da su koyar da Yaransu wannan addu'a.
Faɗin LAA ILAHA ILLA ALLAHU WAHDAHU LAA SHARIKALAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADEER sau 100 safiya da maraice na kare mutum daga dukkan sharri. Minti nawa zai ɗauke mu, mu zauna da iyalinmu mu yi shi da sauran adduoi safiya da maraice, yafi zaman kallon film da sauransu.
Abu na karshe, tofa musu Ayoyin Kur'ani a gaban su ba shine addu'ar kariya ba, ko tofashi a ruwa ayi musu tsarki duk wannan hanyar kaskantar da Kur'ani ne. Addu'ar da annabi ya bar mana don karanta ma ya'ya domin kariya shine U'EEZUKUMAA BI KALIMATILLAHIT-TAAMMAAT MIN KULLI SHAIDANIN WA HAAMMAAT WA MIN KULLI A'ININ LAAMMAAT.
Ubangiji Allah ya bamu ikon sauke hakkokin da suka rataya a wuyan mu, ya bamu ikon tarbiyyantar da ya'yanmu. Aameen YA RABBI.
17/02/2018
Add Vote
Afuwan Afuwan for the long silence. Manage this, love u ol.
This page is urs @Reine_Gh thnx for d cover
Ummu-Abdoul 😍😘💕💞
Cikin kwana biyu ya kammala duk wani shiri da ya kamata yayi, duk wata motsi na Qahɗaanie yana sane da shi, abin mamaki bai ga mahaifinsa ba balle iyayensa mata, hankalinsa in yayi dubu toh ya tashi, ya ba kansa laifi ya fi a qirga don gani yake da ya turje ya ki barin gari da tabbas hakan bai kai ga faruwa ba.
"Azeezatie, Habibty, Nisfie ukhra!" Ya ce yana kwanciya a gefen ta matsawa tayi zuwa quryan gado. Tun da ya faɗa mata jirginsa zata tashi karfe sha biyu na daren ranar ta ke kuka. Tun tana yi a ɓoye har ta bayyanar, yaran su ka sata a gaba su na tambaya. Da fari ya share ta sai kuma zuciyar ta gagara hakura da sauraron amon kukanta.
"Da kin adana kukan ki zuwa lokacin da sakon mutuwa ta zata riske ki, Qahɗaanie zan je kuma mijin yar uwarki ya amshe fada, kasancewar dan ta'adda ne" ya fadi mata kai tsaye don ya san lallaɓa ta ba zai sa tayi shiru ba amma hangen fitina ya fi maido mata da hankali.
"shi ne sai yanzu zaka faɗa min, awanni uku sukai saura jirgin ka ya tashi zuwa ga halaka" tace masa tana mikewa a firgice
"Kin san de ba ke kaɗai ba ce ko, in wani abin ya samu baby na sai kotu ta raba mu" yace yana ɗaga mata gira.
"wai yaushe za ka shiryu ne, mugun fata ka ke jefawa Qahɗaanie ko" tace tana dukan shi da filo. Dariya ya sa mata sannan ya kamo ta zuwa jikin shi. Saitin kunnen ta ya je ya ce
"Ya'yana za su iya zama marayu a kowane lokaci daga yanzu, ki shirya kawai a kowane lokaci za ki iya shiga halin takaba"
"AbdulHaleeeeeem!" Ta faɗi cikin kuka don kwanyarta ya gagara iya hango hakan na faruwa da su. Rungume shi tayi tsam kamar ta komar da shi ciki.
"kar ka tafi ka ji" tace masa cikin rada
" Ki zama mai dauriya, ke ce karfi na in kin yi kasa wa zai ta da ni. Addu'a nake so ki min, in ban je ba, Abbie, Ummie, Mamie, Ammie, mai martaba, Qalbi, AbdulHaseeb duk su na cikin hatsari. Ummu hafsa ta rasu, mutane sun yi gudun Hijira, rayuka sun salwanta kin ga kenan gaba ɗaya babu wani gata sama da Allah sai kuma ni da za'a samu nasara daga Allah ta hanya ta. Ki zama mai karfi da tsayayyar zuciya, ki zama jaruma ki zama mai yawan addua" sannu a hankali kalaman sa su ka saukar mata da natsuwa sosai, hakan ya sa ta kara yin alfahari da mijinta tare da jinjinawa kokarin sa.
Nafilfiloli su ka yi na neman nasara sannan ya kama hanyar zuwa filin jirgi cikin rakiyar Santonio amintaccen direban Don clemenza. Bayan tafiyar su Don da kansa ya ɗauke su zuwa gidan shi don samun cikakken tsaro duk da ya san mutan Kasar Sun san su a matsayin ahlin sa.
***
Washe gari da karfe hudu na maraice AbdulHaleem ya sauka a filin jirgin Kasar Ghana. Maimakon ya nufi ofishin jakadancin Qahɗaanie da ke Accra kamar yanda ya bayyana kansa da fasfo mai nuna daga masarauta ya ke. Se ya karya jiki ya shige gari kamar ba Bako ba.
Gidan abinci ya fara isa ya ci, sannan
ya nemi wajen buga waya na kuɗi ya sanar da su fatima isarsa Ghana tare da mata sallama don ya san samun nasara daga gare shi ne kaɗai zai jiyar da ita muryar sa. Sun yi dogon hira yayi magana da yan uku sannan su ka yi sallama. Daga nan ya kira Don ya sanar masa babu abin da yake faɗa masa se "ka yi amfani da hankali sannan ka san rayuwar Mahaifin ka na hannun ka, saboda haka babu tsoro a cikin lissafinka, ko zaka ga mutuwa toh ka tabbatar da ka yaqe shi" Don ya maimaita yafi sau a kirga har su ka yi sallama.
Map dinsa ya ciro ya dudduba sannan ya koma filin jirgin in da ya samu yan tasi ya dunqula masa euro dubu biyu ya kwatanta masa in da zai kai shi. Ganin yawan kudin ya sa bai Musa ba don ya san zai kudanye ne sailin da zai juya kudin zuwa cedi. Tafiya su ke su na hira har su ka dumfaro koramar da ta raba Ghana da Qahɗaanie ta gefen gabas, sannan ya sauka ya masa sallama. Har AbdulHaleem zai wu ce direban nan ya kira shi.
"Ka san in da kake shirin dumfara ana rikici sosai, da zaka bi shawara ko wanene naka ke daular ka yi hakuri mu je gidana zuwa lokacin da komai zai lafa" kallon sa AbdulHaleem yayi kamar ba zai yi magana ba sai ya ce
"Nasaran Qahɗaanie na tare da ni da ikon Allah, ni.." bai kai ga karasawa ba ya jiyo munfashi da kukan yaro nan su ka isa wajen, wata mata zaune da dan ta ɗan shekara huɗu tana numfashi daga ji na wahala ne, ɗaukan ta AbdulHaleem yayi ya sa a motar mutumin ya ce su koma.
Garin da ke kusa da Acra su ka shiga nan su ka nemi asibiti aka mika matar nan.
"Ga amana na bar maka, zan dawo da yardan Allah in amshe su, jininta na Qahɗaanie ne amma duk ka ji sanarwan mutuwar Yarima AbdulHaleem, in ka ji labarin zaman lafiya a Qahɗaanie ka mika ta ga duk wanda ka samu, mu je ka kaini in da mu ka yi alkawari" yace yana mikewa haɗe da bashi wani kudin da bai san yawansu ba, ya ce "ga wani amanar tun da ka san ko ni wanene cin amanata na daidai da rusa daula da zama sanadin rayuwar musulmi"
Suna tafi direban na tunani da tausayi haɗe da sha'awar AbdulHaleem, can dai ya ce masa
"ka rike HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL" Zaka zama mai nasara. Kar ka karaya nasara ta ka ce da yardan Allah. Sunana Sufyan Marwan in ka zo filin jirgin Acra za'a kawo ka har gida na" girgiza kai AbdulHaleem yayi alamun gamuwa sannan su ka cigaba da tafiya.
Rungume AbdulHaleem yayi cikin jinjina da nuna karfin guiwa sannan su ka rabu.
Iyo yayi zuwa inda bishiya ya kwanto ya dane ta reshen da ya kwanto. Haka yayi ta bin rassa har ya kai ga inda ya ke tunanin nan ne hanyar, ƙkasa ta rufe wajen haka ya fara sharewa har ya kai ga marfin. Yatsarsa ya ɗaura a wajen da ya ke kamar mabudi nan take ya motsa. Farin ciki fal a cikinsa don tsoronsa a ce sun yanke hanyar sadarwan fada.
Haske ne ta bango nan ya bi matakalar da ya gani ya rufe kofar. Tafiya yake har ya kai ga karshen matakalar, nan ya iske farfajiyar fili ne da motoci guda biyu ajiye, farin ciki ya yi haɗe da gode ma Allah da ya bashi fasahar yin hanyar tsaro ta karkashin kasa.
Bai yi tsammanin motocin za su yi aiki ba amma yana da yaqini akan kamfanin da ya ba aikin sarrafa motar, nan ya gwada mai mazaunin mutum ɗaya da ke ajiye ya shiga ya tayar.
Tafiya ce mai tsawo kafin ya isa Fada don duk da rashin barci da kuma tafiya dodar sai da ya share awa takwas kafin ya isa mabulla a fada. Kofar shiga ya haɗe ne da bangon tsaro na fada wanda duk shi ya tsara hakan. Babu abin da yake ambata sai Hasbunallahu wa ni'imal wakeel da Alhamdulillah. Don shi lokacin da ya fitar da tsarin bai taɓa zaton zai yi aiki a kusa ba, yayi ne kawai don daular su ta yi daidai da zamani.
Kamar yanda ya shiga bai yi wahalar fita ba sai dai yana manne jikin bango yana kallon harabar cikin masarauta kasancewar wanda ke ciki zai ga na waje shi kuma wanda ke wajen bango zai yi tunanin fenti ne mai kyalli. Tafiya yake ta cikin bango yana zagaye har ya kai in da yaga ya dace ya fita, sai tin ɗakin ummansa ne, nan ya san akwai abin da ya ajiye da babu wanda ya sani daga shi sai mai martaba, kuma shi ke isar da jan lantarki (shocking) ga kujerar karaga.
Yana isa ya jawo, ɗakin ummunsa na fitar da kamshin sa kamar kullum, gadon ta a shirye kamar yadda ya taso ya saba gani. Take ya shiga cikin matsanancin damuwa don ba ya son ya tuna cewa wani abin ya same su.
***
Jawo karamar akwati yayi ya buɗe nan ya latsa wasu lambobi ya aika da sako, sako ya dawo masa. Take fuskar talabijin ya bayyana inda majalisan mai martaba ya bayyana, bakin mutumin nan ne zaune a kan karaga tsirara ya sanya fuskar mace yarinya a tsakanin cinyarsa yayin da a gefe yan mata ne kanana da gani ana shirin barnata musu rayuwa ne. Bakin ciki ya cika AbdulHaleem take ya danna makunin shocking ɗin nan, ya tsaya sako ya fara isa.
Adjetey na zaune da yarinyar farko cikin saba'in din da ya sa a kamo masa budare don ya fara more rayuwar mulki kenan AbdulHaleem ya isa. Can daga gefe mai martaba ne daure da wasu daga cikin manyan yan majalisa ciki har da Abbie don su shaida danyen aikin da zai yi. Addu'a su ke a ransu don ba su yanke kauna daga rahaman Allah ba.
Karar da mai martaba ya jiyo na ɗaukan sako daga daya daga cikin makunin tsaro da shi da AbdulHaleem kaɗai su ka san da zaman su ne ya sa shi murmushi.
"Shege tsoho ya san daɗi, Aamir kaɗai ke da hurumin shiga farin ciki a wannan yanayi" wani gardi ya faɗi yana neman kai ma mai martaba mari amma ya fasa. Hakan yayi daidai da fara shocking da kujerar ta fara, takan ɗauki lokaci ne saboda katakan da su ka rinjaye karafan kujerar.
Shi bai yi tunanin shocking bane da farko ya ɗauka daɗin da yarinyar ke shayar da shi ne ya sa shi jin wannan a jikin sa. Sai da hannun sa ya makale a jikin karfen fulawar kujerar.
Nan sauran jikin sa ya ɗauka, ihu yake yana ku taimaka min, amma duk wanda ya isa wajen shocking din wajen wurin ke ɗaga shi ya kayar.
AbdulHaleem na kallo daga ɗaki yana kyakyata dariya chan ya tuna ai yana da sauran aiki a gabansa. Kashewa yayi ya aje, don ya san lallai ya jigata.
'ka fitar da mahaifanka farko sai ka tun kare makiya' wata sashi na zuciyar sa ta tuna masa. Lambobin jami'an tsaro ya kira in da su na chan su na tunanin kwato masarauta daga hannun adjetey.
***
AbdulHaseeb ne ya ɗaga don hankalinsa a tashe, ga mahaifiyarsa kwance a asibiti rai a hannun Allah ga mahaifinsa ba'a san inda yake ba ga shi kanshi ISMAALIE sun ba da sanarwan duk wanda ya kai musu shi ko a mace ne za su ba shi kyauta mai tsoka, hakan ya sa ya makale a hedkwatar sojoji amma kuma yana makale Kusa da tangarahu.
"AbdulHaleem Abdul-Jabbar ke magana daga masarautan Qahɗaanie" ya faɗi kai tsaye
Ba don AbdulHaseeb ya shaidi muryar dan uwansa ba da zai ce karya ce so ake a yaudare su.
"Nisfie yaushe ka Shigo, ina Mahaifin mu" ya ce a ruɗe
"ina cikin masarauta yanzu ina bukatar jami'ai don in fitar da iyayenmu daga gidan nan, a turo runduna ta kofar dawaki, zan san yanda za'a yi a fitar da su ta nan amma a zama cikin shiri" ya faɗi yana tafiya cikin sanɗo don isa in da kwamfutar sa ya nuna akwai taron mutane a ciki.
mention a usermention a user
mention a usermention a user
Add Vote
Ziyarar Mutuwa
Safiyyah Ummu-Abdoul
Safiyyahjibril@gmail.com
A Yan kwanakin nan mutuwa ta kawo ziyara ga abokai na a shafin yanar gizo ta Facebook. Sati uku kenan da wuya na shiga shafin ban ci karo da sakon mutuwar aboki (friend) ba ko abokin aboki (mutual friend) ba, ni kuma Allah ya min saran shiga shafin mamaci don in ji tausayin kaina da tunanin wata rana hakan zai kasance a shafi na.
A wannan ziyarar ne nake ganin abin da yafi sakon mutuwar ɗaga min hankali don kuwa ina iske mamaci ya/ta yi posting abu yan kwanaki tsakanin ta/sa da mutuwar. Kenan ba'a sanin cewa za'a mace ɗin don da ana sani da tabbas firgici da tsoro ba zai bari mutum ya samu sukunin yin postin ba. Wasu ma za tsakanin post ɗin su da mutuwar su yan awanni ne kawai ko mintoci.
Jiya da dare mu ke maganar rashin lafiyar mahaifiyar kawar mu shamsiyya yusha'u ni da qawata Aisha yareema ashe lokacin da muke wannan hiran bakin sun iso gare ta ko suna shirin zuwa gareta. Mutuwar ta taɓa ni sosai. Muna fatan jinyar ta zama kaffara gareta.
Yan uwa hakika ba abin da ya kai mutuwa darasi, sannan mutuwar abokin Facebook darasi ne ga duk wani mai shafi a Facebook don abin da ya kamata mu yi tunani akai shine in su sun mutu bayan sun yi post ɗin alkhairi da za'a dinga gani ana aika musu lada saboda qaruwa, mu kuma da muka sa gulma da cin naman mutane da talla da zunubin wasu, da yi ma juna bakin ciki da hassada da duk wani mugun abu a social media in muka mutu muna aikata hakan fa?
Auno mala'ikan ɗaukan rai ya ziyarce ka/ki yayin da hannayenki ke typing zagi ko tsinuwa ga shugabanni? Ko ki./ka na Can kana gulma da cin nama ko Ace mutum na chan shafukan batsa ko ko ko...
Yan uwa mu kiyaye gaɓɓanmu daga aikata haramun domin za su bada sheda ranar da baki ba zai iya magana ba.
Allah ya jikan mamatanmu ya kai Rahma ga makwancin su ya sa su kasance cikin Raudha min riyaadil Janna. Mu kuma ya sa mu is ko su a sa'a.
Ummu-Abdoul
24th February 2018
5:11pm Nigeria
Add Vote
shamuSYY accept my condolence please, Allah jikan ummah ya sada ta da rahma. Sisters pls pray for her mum.
Ku kara hakuri da er boko, kuma zance na Allah am a lazy type, ga abubuwa da dama a gaba na. Ur prayers needed.
😍😘😘😘😘😘
Ganin yanda ɗakin ke tsare ya so ya ba shi tsoro, jikin wani lungu ya maqale a tsorace.
'Kasan ba'a banza na ɗora ka akan
karati da tokwando ba sai don ka san
yanda zaka kwaci kanka, kuma
musamman daga Kasar China na
hayo su toh kar ka bani kunya ko a
bayan ido na, ko bayan kasa ya rufe
ido na' kalaman don Clemenza ya faɗo masa a rai take wasu kwarin guiwa da bai san da su ba suka taso masa tun daga tafin kafarsa. Hakan ya sa ya tuna da ajiyar da ke jikin wondonsa na ciki. Rabuwarsa da direban taxi ya saka ta a wandon kafin ya ajiye sauran kayansu a wani kogon bishiya.
Bindiga ce, Don ya masa kyautar sa da zai baro, tana iya harbin abin da ke da tsawon mile ɗari in dai an seta shi da kyau. Sannan ba ta da kara, tana ɗaukan harsashi sannan tana ɗaukan nakiya duka biyu Don ya cika masa shi ya ce iya taimakon da zai iya masa yanzu kenan.
'Ka san mafi yawan yan ta'adda bindiga kawai ce karfin su, ba su da karfin yin faɗa da jikkunan su, saboda haka a duk sanda ka haɗu da su nema hanyar raba su da bindigogin su Shike nan ka ci nasara matakin farko a kansu' cewar yogn Chen mai koyar da shi karate. Yana tuna hakan ya daidaita bindigar sa ga mutanen da ke zaune a bakin kofar kowannensu ya sakar musu harsashi, kafin su ankare da zuwan halsashin kowannensu ya samu isowar nashi cikin kirji. Tim su ka faɗi nan sauran da ke tsaye a gefe su ka yi sauri don barin wajen domin kuwa labarin shocking din Adjetey ya is ko su, a wata majiyar ma cewa ake ya suma an fice da shi daga fada don samun magani.
"Aljanu ne a fadan, ka san mu a kasarmu aljanu na taimakawa masarauta" cewar ɗaya daga cikinsu da ya fito daga yankin arewacin Nijeriya, ta yana gizo ya hadu da wani dan ismaalie a hankali daga abota su ka janye shi zuwa ga ta'addanci.
Kalamansa ya sa da yawansu tsorata, har su ka juya sai wasu karfafa daga yankin Kasar ibo sa su ka ɗauki aniyar ganin wannan aljani. AbdulHaleem na ganin tahowarsu ya sake sakin harsashi wanda bai sauka a ko ina ba sai cikin cikin ɗaya da ga ciki, take ya sheme a kasa. Dayan na ganin haka ya tsaya cak, ya gudu ko ya tsaya. Hakan ya sa AbdulHaleem fitowa ya dunkare shi ba tare da tsoro ko shakka ba.
Daga idon da yayi ya ga AbdulHaleem take zawo ya nemi kucce masa, don kuwa tabbas wannan ne hoton da ke zagaye da falon Alhamzie da sunan ɗan sarki da su ka kashe, kenan Aljanun ma Fatalwa ne, bai dawo daga duniyar tunani ba yaji saukar naushi a fuskar sa don sai da kumatun ya lotse, wani sabon naushin ne ya sauka nan ya fara kuka wiwiwiw faɗi yake
"ka yi min rai in fita, ba zan sake dawowa ba" karamar wukar da Mr Chen ya bashi ya zaro daga in da ya aje ya so ka ma mutumin a cinya. Wukar na shiga cinyar sa yana sakin ihu, hakan ya sa AbdulHaleem ya sakar masa kuma. Faɗin da yayi yana gurnanin azaba, AbdulHaleem ya dunfari ɗakin, buɗewa ke da wuya ya iske yan ta'adda uku suna mashaa da wasu tsofaffi, ma'aikata a fada. Take ya tsorata kada Ace mutanen nan sun yi da iyayensa.
"Kai ma dauki ɗaya, yanzu muka fara don mu sha romon dukkansu kafin a tada mu" daya ya faɗi ba tare da ya juyo ba ganin irin tsorata da matan su ka yi ganin AbdulHaleem.
Bindigogin da su ka ajiye ya kwashe ya damka ma mahaifiyarsa kana ya jawo mai maganar cikinsu ya daɓa masa wuka a mazakutarsa, ya yasar da shi gefe.
Sauran ba su ankara ba sai da yayi ma na biyun wanda shi sakin ihu yayi da ya ji azaban. Ba kamar na farko ba da ya kasa motsi saboda tsananin azaba. Ihun na biyun ya sa na uku tashi a firgice yana lalubo bindigar sa ganin babu ya Mike yana mazurai.
"wanene kai, don kazan kazan ka har zaka shigo nan, ka kawo kanka ajalinka" yace yana fiffiga kamar zai iya wani abin. Isa gareshi AbdulHaleem yayi bai masa wani gargadi ba ya soka masa wukar a cinya, azaban da ya ji ya sa ya nemi guduwa amma kafan ya hana hakan ya sa ya janye jiki gefe. Bin sa yayi ya masa abin da yayi ma sauran nan shi ma ya bi saura wajen jin azaba da zubar jini.
Sake waya yayi zuwa hedkwatar sojin Qahɗaanie inda aka tabbatar masa da zuwan jirgi mai saukar angulu a inda ya bada umurni. Nan ya jagora ci matan da ke ɗakin zuwa kofar yamma in da jirgi ke jiran su. Sai da ya tabbatar da tashin su sannan yayi yunkurin komawa don ya fuskanci sauran da ke gaban gidan.
'malam ga matar ka ga ya'ya kada ka yi yunkurin raba su da gatansu' wani sashi na zuciyar sa ya ankarar da shi amma ya cije ya dage. Saman gini ya nufa, yana tafe yana Hasbunallahu wa ni'imal wakeel don ya san bai da wani gata sai na mai duka. Ko da ya isa nan ya samu an ajiye na'urar harsashi da in aka saki zai yi kaca-kaca da wanda aka harbawa.
"Duk wanda baya fatan mahaifiyarsa ta yi sabon naquda ya sallama kansa, masarauta za ta yanta shi cike da kyatuttuka da aikin yi" ya faɗi ta lasifika din da ke makale da wannan tankin. Wasu maballai ya latsa take harsashi ya sauka a kan wasu yan ta'adda ya na kallon yanda su ka tarwatse. Babu shiri su ka fara gudu don tsira da ransu suna hayewa kan hillux hillux din da ke harabar wajen suna guduwa. Ganin haka ya sa AbdulHaleem ya sake sakin harsashi nan wasu suka kara zubewa, don burin sa ya rage yawan yan ta'addan.
'ina mai martaba' shine tambayar da ta hana masa latsa botirin a karo na bakwai nan ya juya da sauri zuwa ga hanyar da zai sada shi ga cikin majalisa
Add Vote
Faɗin wahalan da Adjetey ya ji a dalilin shocking ɗin nan ma ɓata lokaci ne, umurni ya bayar aka miko masa jallabiyarsa ya sanya ta ya nemi ta shi. Nan ya ji kafafunsa na maido masa da shocking ɗin da ya ji. Kwanciya yayi warwas a wajen yana mike kafafunsa ko zai samu sa'ida.
Bai gama mai da karfinsa ba sai jin ihun wasu ya yi, sai ga wasu a guje suna haki
"Yaa Naqib, wallahi aljanu sun bayyana da ga can gefen, sakin harsashi su ke, mutanenmu na chan kwance a mace" haka su ke faɗi wani na faɗi wani na caɓewa. Wani tsoro ne ya ziyarci Adjetey don bai taɓa tunanin haka ba da ya shiryo ma zuwan su.
"Ai yanzu ma suka illa ta Naqib, yanzu haka ga shi nan magashiyan, ai gara na mutu da na haukace" mai sai ta bindiga ga mai martaba ya faɗi yana ajiye bindiga ya ari ta kare, nan wasu su ka biyo sawu sun fito kenan su ka shige jirgin su mai tashin angulu da ya ke a harabar fada. Adjetey na fitowa shima ya faɗa, tare da ba da umurnin tashi nan su ka tashi suka bar masu gadin fada a cikinsu.
***
Bayan fitar su mai martaba ya kalli waziri ya ce " AbdulHaleem ne ya iso, babu wani aljani a fadan nan don a kafa daular nan akan ɗarikan sunnar annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, ka ga kenan babu yanda za'a ayi shirka ta shigo daular nan" nan fa su ka fara faɗin albarkacin bakunansu duk da cewa da yawa a cikin su a tsorace su ke.
alkyabba mai martaba ya cire don ya rufe yarinyar da su ka ma tsiraici. Su na haka su ka jiyou muryar AbdulHaleem yana ba da shela, hamdala mai martaba yayi ta yi, zuciyar sa na haske da farin cikin samun nasara.
Tun daga bakin kofa ya tari AbdulHaleem, dudduba shi yake don ya tabbatar da lafiyar sa., sai da ya Kalle shi tsaf sannan ya rungume shi yana mai shi masa albarka. Bin iyayen yayi daya bayan daya suna dafa kansa su na shi masa albarka. Sannan su ka dunguma zuwa kewaye fada bayan AbdulHaleem ya bada sanarwan a turo musu dakarun sojojin Qahɗaanie.
"Hakika na yarda duk ta'addancin da ya zarce awa ashirin da huɗu to gwamnati na da ra'ayi akai ko kuma gwamnati ta gaza" cewan mai martaba yana kara rungume AbdulHaleem a karo na ba adadi.
"Baka da ra'ayi kuma baka Gaza ba, kawai de tunanin ka ne irin na bayin Allah wa'inda a lokacin su ta'addancin bai hayayyafa ba. Amma a zamanin nan yanda aka fitar da na'urorin tsaro haka ake bayyana mutane zuwa ga ta'addanci.Shi yasa lokacin nan na sauya tsarin fada" ya faɗi yana kyafta ma mai martaba ido, nan su ka sa dariya.
***
Yini uku aka ɗauka wajen gyara fada tare da yi masa sabon fenti. Sauran na'urorin da aka illata kuma AbdulHaleem ya hana a taɓa su don bai yarda wani ɗan Qahɗaanie ya san da zaman su ba. Sai a sannan aka dawo da matan gida sannan a lokacin ne mai martaba ya samu labarin Ummu Hafsa na kwance ne a gadon asibiti ba ta mutu a kamar yanda suka faɗa masa.
Anyi jana'iza duk wa'inda su ka rasu, fili guda mai martaba ya ware ya zama makabartan duk wanda ya rasu a dalilin Ismaalie. Sannan aka fara gina gidajen da su ka salwanta a kwanakin firgici sannan mai martaba ya koma fada. A lokacin ne ya bada daman zama da yan jarida kamar su BBC, aljazeera da sauransu in da ya faɗa ma duniya cigaban da aka samu.
"an ce yan kungiyar Ismaalie sun koma dajin Asad, shin wani yunkuri kake don fitar da su daga daular na ka gaba daya" ɗan jarida ya tambaya wanda hakan ya sa mai martaba tunawa da su.
Shi tun da aka samu nasara sai yake gani kamar gaba ɗaya babu su a daular. Gudun ɓata ma kansa suna da martaba ya sa shi yin murmushi ya ce
" wannan ba wani babban matsala bane don kuwa muna shiri ne don so muke mu kauda burbushin su gaba ɗaya daga Qahɗaanie, sun samu mafaka ne daga wasu yan daulan, mun san da su kuma za mu fara yanke musu hukunci nan ba da jimawa ba" ya bada amsa, haka su ka cigaba da tambaya yana basu amsa, yayin da ake nuna su kai tsaye a manyan tashoshin talebijin na duniya.
Ya samu sakonnin taya murna da sambarka daga shugabanni kasashe zuwa ga sarakunan daulolin Larabawa da sauran su.
***
Sai da aka yi sati sannan AbdulHaleem ya kai ziyara gidan Abbie, sai a lokacin ya tuna bai kira Fatimansa ba. Karkada kai yayi don ya san a cike take da shi.
Ya kira Don de tun a kwanakin nasara, in da yayi masa godiya haɗe da bayani kana ya nemi alfarma Don ya sama ma masa wa'inda za su gyara musu fada da ma ita kanta daula don ta danyi shigen kasashe ma su cigaba.
Bayan sun gaisa da Abbie nan ya masa faɗa sosai, ya nuna masa kuskuren da su ka ɗauka na rashin kira ko waiwayen gida. Din mutuwa ba ta zuwa da shela in ta tashi se bayan ta ɗauki wanda yake rabon ta kafin a san da ziyarar ta. Bai kasa da guiwa ba ya nemi gafaran Abbie sannan ya latsa lambobin Fatima ya kira. Ringing biyu ta ɗauka bata amsa sallaman sa ba ta hau masifa
"ni wallahi ban san mijin da na ce na aura ba, shi de ko yaushe burin sa ne a gaban sa da ya sa gaba baya ko waiwaye. Toh malam dusar ka ta bushe ka bada himma zuwa kwashewa, tom" ta ce tana murguda baki, shi kuma dariya yake don ya sa ta a murya ne (handsfree) ne ga iyayenta duka zaune.
"Hala firgicin bai sake ka bane kake ta dariya don anya na lafiya ne" tace a kufule.
"wai rayuwar da kuke yi kenan miji ba abakin komai ba, wani irin iya shege ne faɗin ma miji magana" cewa Ummie don ita abin bai bata dariya ba kamar yanda sauran su ka tiqe su na yi. Muryar Ummie da taji yasa ta kiran sunan da karfin ta cikin murna. Sai duk su ka sa dariya. Gaisawa tayi da kowa da aka kawo wajen Abbie cewa tayi sai dai video call, nan su ka jona Skype su ka fara. Murna a wajen su ba'a magana. Ya'yan ta zaunar da su tana nuna musu dangin su.
"Abbie tun da an samu lafiya za mu zo ko, don ni na gaji da rashin ku" tace cikin shagwaba. Ya'yan duk sai suka maimaita hakan ya ba Abbie dariya. Haka de su ka yi sallama ba tare da ya bata a sa.
***
Tafe yake cikin nishadi don magana da ya yi da iyalin sa. Tafe yake mutane na jinjina masa don yabawa da su ka yi da kokarin sa wajen dawo masu da zaman lafiya.
A kofar shiga majalisa ya ci karo da AbdulHaseeb da Abdul Baar, rungume su yayi cikin farin ciki don tun da ya dawo bai sa su a Ido ba don duk su biyun na cikin dakarun sojin Qahɗaanie.
"ka yafe min AbdulHaleem, in ba haka ba rayuwa ta zata zama matsala. Na cuce ka sau ba adadi don kawai na gaji mai martaba, yanzu na kara tabbatar da cewa kafi ni cancantar sarauta, ka fi ni a komi ni ba komai bane sai mai cike da son kanshi" ya karasa yana mai rushewa da kuka. ha'an Nisfie kuka ba na jarumai ba ne, an halicce mu ne don mu yi kuskure shi ya sa baa yi mu mala'iku ko annabawa ba, kada ka damu zo mu karasa cikin gida.
Sun fara da sashin Umma Hafsa in da ta ke jinya tun bayan dawowarta daga asibiti, kwance su ka iske ta idanunta a rufe amma kuma hawaye na zuba daga idanunta. Zuciyarta yayi baki kirin kamar wanda aka babbaka saboda haushi, takaici da kiyayyar Abdulhaleem da ya mamaye ta. Ranta ya qara 6aci jin shigowar su. Ta ya za’a yi tana ji tana gani nasara ya hau kan Abdulhaleem duk shirin da su ka yi masa, sannan don cin Amana kuma kawunta Saifullahi ya shirya hanyar da za’a kasha ta. Wasu zafafan hawaye su ka gangaro mata don tana ganin in ba hakan ta yi ba ba za ta ji salama ba a ranta.
AbdulHaseeb da ya san dalilin hawayenta ji yayi ina kasa za ta bud’e duk su shige ko sa huta, a da yayi abu cikin son raid a kuma zuga irin na mahaifiyarsa amma tun day a fahimci Alhamzie amfani da su kawai ya ke don ya cimma wata manufa ta sat a daban ya sallama ma bakin nufinsu na son yayi mulki ko ana ha maza ha mata amma lokacin ya qure masa a sannan. Ko a jiya da ya shigo d’akin mahaifiyar ta sa , ya so ta fahimce shi amma inaa gani take tuba a yanzu kamar mutum ne ya na ganin nasara sannan ya janye nema.
“Ko bayan raina ban yarda ka bar ma AbdulHaleem kujeran Mulki ba, duk fitinar da ke tattare da kujeran kar ka damu ko da kuwa kowa zai mutu ne a bar ka a raye” tace masa bilhakki har cikin ranta hakan ne. shi ya sa da ya ga hawayenta zuciyar sat a bashi ganin Abdulhaleem da tayi ne duk da kuwa cewa idanunta a rufe yake hakan bai hana ta fahimtar kasancewarsa a wajen ba.
Hannu Abdulhaleem ya sa ya yana share mata hawayen,amma ji ta ke kamar an d’aura mata gawayi saboda tsananin kiyayyarsa da take ji a ranta. “LAA BA’ASA DUHURAN INSHA’ALLAH" y ace mata yana share mata hawayen, tausayinta yake ji don ba zai manta labarin da Don ya bas hi ba na irin azaban da ke tattare da harsashi kasancewar an taba masa shi ya sa ko makiyinsa ne ya fi so ya kasha shit a guba bat a harsashi ba tun da aka ta6a harba masa ita.
“Ka bar Ummu ka zo mu karasa ciki, harda tausayinmu ya sa Ummu hawaye, tana bukatar kadaici” Abdulhaseeb ya ce don ya samu su fita kafin ta kwafsa masa. Ba musu suka fita bas u tsaya ko ina ba sai d’akin Ummu Maryam. Zaune take tana tilawar Al-Qur’ani, tayi farinciki ainun da ganin d’anta don tun day a dawo bas u ke6e ba, bata so ganin sa da AbdulHaseeb ba don in akwai wanda ba ta yarda da shi ba yanzu Abdulhaseeb ne don kuwa ta sha kama shi yana fad’in kalaman 6atanci akanta ko akan Abdulhaleem duk kuwa bai ta6a sauya mata ta fannin biyayya ko kyautatawa ba. Hakan ya sa ita ma ba ta ta6a nuna masa ta ji ko sau d’aya ba.
Anti A’azu Naasi alaiyya,
Anti Ahabbu naasi ilayya
Ummi anti hayatie
Anti Noorie
Anti Qalbie
Uhubbuki bi killo diqqatin min qalbie
Abdulhaleem yace yana rerawa kamar wak’a , kusa da ita ya zauna yana mai kwanciya a gefen kafad’unta. Dariya tayi tana mintsilinsa nan take yayi tsalle yana mai ja da baya.
“Qalbie ba ki ma yi kewata ba, hmm ni kam nayi wallahi kullum sai mun yi hiranki da yara” yace yaka rungume ta. Ajiye Qur’ani tayi ta kale shi ta ce
“Ai kai ka auru kawai mallam, tun da nab aka d’iyata shike nan kamanta alkhairi, haba mallam a dinga tuna alkhairi” nan duk su ka sa dariya. AbdulBaar ne ya shigo hakan ya hana Abdulhaleem fadin zancen da ya yi niyya don bai ga alamun nadama daga AbdulBaar ba sai ma kwantaccen bak’inciki da idanunsa ke fitarwa. Hira su ka cigaba da yin a kan rayuwa ba tare da sun firta wani abu dangane da inda Abdulhaleem yake ba ko kuma abin day a faru a masaruta bayan ba shi. Can dai ya jawo kwamfutar d’akin ya bud’e shafin Skype ya kira Fatima, fatansa dai tana kusa don su gaisa da Ummu.
Yaran ne su ka fito a akwatin kwamfutar, Humaira wato Aisha itace mai maganar bayan ganin mahaifinsu das u kayi “Papa quando torni” Tace cikin halshen italiya wato Papa Yaushe zaka dawo.
“Gadan inshaAllah” ya ce hakan da yayi na musu nufi da larabci za su yi Magana. Abdulbaar kuwa burinsa ya san garin da su ke hakan ya sa shi haddace torni don ya fita ya tambayi yaren wani gari ne hakan.
“wannan ne maman Papa ?” cewar Hanan wato Hafsah kenan tana nuna Ummu da ke zaune tana murmushi
“Laa ke ce kika haifi Papa, kina da kyau sosai ina sonki “ inji Hibbatullah wato Maryam. Nan farin ciki ya cika Ummu Maryam, wai ita aka Haifa ma ya’ya har uku. Hawayen farinciki ne ya zubo mata don kuwa Allah kenan mai baiwa, ya bata d’aya sai ya bata nafila har uku .
“Ba ku fada mata sunayenku ba” Abdulhaleem ya ce, “kunga Ammou Abdulhaseeb da Ammou AbdulBaar da ke hotunan nan kun tuna” yace yana jawo su don su gansu
“Laa papa wannan ne mai cin abin yan Nijeriya d’innan a hoto” su ka fad’I suna nuna AbdulBaar saboda wani hoto day a zauna ya na shan Faten da makocinsu a amerika ya basu san das u ke can.
Fitowar Fatima ya sa Abdulbaar mutuwar zaune, duk da tana cikin mayafi hakan ba zai hana mutum gane cikin da ta ke d’auke dashi ba, gaida ummu ta yi kana ta gaida sauran , kokallon mijinta ba tayi ba don cike ta ke dashi, yanzu ma ihun yaran ya sa ta tasowa don ta gaida uwar mijinta.
“wainnan anya zan bari Mai Martaba ya gansu kuwa, wannan fi’ili da su keda shi ai sai su kwace min miji na” tace ma Fatima cikin dariya
“Ai fa Ummu kin ga kin tashi a amarya kenan kuma fa, don yara na kyawawa ne” cewar Abdulhaseeb.
“Haba Ummu wainnan munanan ne kike fad’uwan gaba akansu, ai uwata ce Amarya har gaban Abada” Fatima tace tana murmushi
“Ummu kinji ko, Allah yi mata wa’azi matar da ke kiran mijinta mummuna, da ni fa take don ta san jinni na ya fi karfi akan su” dariya duk su kayi, su ka danyi hira kadan sannan su ka yi sallama. Anan d’akin Ummu maryam su ka cigaba har aka yi kiran sallah, sannan su ka sauka don bada farali, daga nan su ka shiga majalisa wajen mai martaba.
Sun iske sun a karanta wasikar shugaban Kasan Ghana ne, hakan ya tuna ma Abdulhaleem ajiyar da yayi a Ghana. Bayan sun gaisa da mai martaba ne ya nemi izinin zuwa Ghana don akwai wacce ke can da zai taho da ita Qahd’aanie.
‘ai ko in Fatima ce sai dai ayi biyu babu don ba zan hakura ba, wannan mace mai cike da kayan dad’i ne zan bar ma wani, hmmn’ AbdulBaar ya fadi a cikin ransa bayan ya saurari Mai martaba ya shirya yanda tafiyar Abdulhaleem zai kasnce cike da tsaro.
DA YAU AKA ‘DAURA AUREN ZAINAB MUHAMMAD (XIESOBA) AMMA ALLAH BAI SO HAKAN BA, YA ‘DAUKE RAYUWARTA A LOKACIN DA TAKE TSAKA DA CIKA BURIKANTA..
UBANGIJI ALLAH YA JADDADA RAHMA A GARETA YA SANYA TANA CIKIN DAUSAYIN ALJANNA .
SISTERS KU KARA HAKURI DA NI PLEASE, NAYI ALMOST 6K WORDS ASHE BAI SAVING BA, HAKAN YA SA NA JI KAMAR NA AJE BGGB. NONE THE LESS WILL TRY AND UPDATE SOON INSHA’ALLAH.
LOVE YOU ALL…
Karfe bakwai na safe jirgin su ya tashi daga babban filin jirgin Qahɗaanie, AbdulHaleem ne kawai sai wasu amintattun sojoji da mai martaba da kansa ya zaɓo su ne su ka tafi. Tafiyar awa uku su ka sauka birnin Accra in da sojoji da jami'an tsaro daga ofishin jakadancin Qahɗaanie su ka nemi gwamnati ta basu ne su ka iske su na jiran su da motoci. Bayan sun gaisa ne AbdulHaleem ya nemi su karasa wajen da yan tasi ke zama don ya duba wani. Ya kai nan ya na shirin tambayar Sufyan Marwan kawai ya ji an rungumo shi ta baya. Cike da farin ciki Sufyan ya ce
"Kaga ikon Allah ko, da ma na san nasara ba na su bane" ya karasa yana mai kara rungume shi.
"Alhamdulillah! Abu ya zo da sauki fiye da yanda mu ka zata. Ka san tun rabuwan mu nake ambatar HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL kuma na ga ijaba don ba yi na bane yin Allah ne ne" AbdulHaleem ya faɗi cike da murna. Kallon yan rakiyan yayi yace su biyo bayan su don shi a motar Sufyan zai karasa. Ba su yi masa musu ba sai ma qara shirya kansu da su ka yi wasu na gaba wasu na baya su ka bar filin jirgin inda ba su zame ko ina ba sai gidan Sufyan.
"Mai girma sarkin gobe ko rundunar nan za su tsaya daga nan ne kai mu shiga ciki?" Sufyan ya tambaya, hakan ya sa AbdulHaleem ya tsaya ya yi masu magana take su ka Kewaye gidan don kowanne daga cikin su na mamakin haɗin yarima mai jiran gado da dan tasi.
Bayan sun shiga ciki ne, falonsa dan madaidaici sannan su ka kara gaisawa, ya shiga cikin gida ya zo masa da abin motsa baki sannan Iyalinsa su ka fito su ka gaida shi. Kwarai AbdulHaleem ya ji daɗin wannan karamcin da kauna da Sufyan ke masa.
"ina ajiyata" ya faɗi yana murmushi.
"Ajiyar ka na nan ta ji sauki kwarai amma tana cikin hatsari, bakinta ba ya iya furta komai tun da lafiya ya samu take zubar kwalla, abu ɗaya ta ke rubuta min Wanda na ke tunanin in ba mahaifi ba toh tabbas makusanci ne a gareta, ka ganshi nan" ya ce yana mai mika ma sa takardan.
"Nemi Alhaji Yahuza Bello Qahɗaanie" ya Karanta a bayyane. Wani Yahuza Bello ba dai surikinsa ba, take ya firgita ya d'ago kai da sauri yana kallon Sufyan.
"ka fito min da ita in ganta mana" yace masa a ɗan firgice
"BA fitowar ne matsala ba, gwamnati na neman ta wanted, ban san laifin da ta yi ba amma an saka makudan dukiya ga wanda ya bayyana ta a cewarsu yar shugaban majalisar wakilai ne, abin da ya sa ban mika ta ba, bambancin addini da ke tsakanin su biyun" Sufyan ya faɗi kamar yana raɗa.
"toh ko cikin gidan zan shiga nima ne dai, ka san de ba zan yi zuwan banza ba ko" AbdulHaleem ya fadi yana mai kokarin Saita kanshi kar ya kwafsa don ranshi ya ɗan fara ɓaci.
" zan so haka don ban yarda da jami'an da gwamnati ta turo maka ba, kada su zama Silar Ajali" yace yana masa Jagora, a kofar shiga wani ɗaki ne ya iske yaro kamar humaira, nan gaban saya kara faɗi kada hasashensa ya zama gaskiya.
"Ya sunanka" ya ce da shi yana mai shafa masa kai,
"Ahmad, za ka sa mommy na ta min magana ta dena kuka?" yace yana kallon AbdulHaleem.
"ba ka gane shi ba ko, shine yaron D kukansa ya ja hankalinmu, ashe yunwa ce ta sa yayi kama da karamin yaro, inaga zai yi shekaru hudu fa" Sufyan ya ce, sama sama AbdulHaleem ke jinsa don ya cike da rudani. Ganin bai amsa ba ya sashi yin sallama da shiga dakin, AbdulHaleem ma ya bi shi, wacce ya gani tabbas ita ya ke zato.
"Ramlat" ya fadi muryar sa na rawa. Mikewa tayi da sauri ta nufe shi kamar za ta rungume sai kuma ta tsaya, tsugunawa tayi ta saki sabon kuka, babu abin da take bukata sama da taji an rungume ta ana bata hakuri, so take ta faɗi matsalan ta ga wanda zai fahimce ta, so take a ce mata tayi gagganci ayi mata fada sosai, sai gashi Allah ya kawo mata wanda bakin ciki da cigaban sa ya kaita ga fadawa halin da take ciki a matsayin wanda shi ne kawai zai taimaka mata.
"Zan samu niqabi anan kusa, ko da kuwa a fita a siyo ne?" AbdulHaleem yace yana mai tambayar Sufyan wanda kallon su yake cike da mamaki.
"kanwata tace, aure ya kawo ta garin nan, aka aiko mana da sakon rasuwan ta" yace ganin kallon da Sufyan ke bin su da shi.
"Maman zahra kan yi amfani da shi zuwa islamiyya, toh sai ta yi amfani da shi" ya ce yana mai mik'ewa. Ɗauko niqab din yayi ya ba ta, har a lokacin kuka ta ke yi mai tsuma zuciya. Mik'a mata yayi ta amsa ta sanya, AbdulHaleem bai ce komai ba ya juya ya fita, Sufyan ya biyo shi rike da Ahmad ita kuma ta shiga ta yi musu Sallama aka rabu ana kewa.
"Ka nemi gidan siyarwa ka siya ka koma cikin sirri, zaman ka a nan akwai hatsari" AbdulHaleem yace yana mai mik'a Masa wasu dolloli da bai san yawansu ba. Sufyan bai so ya amsa ba amma kallon da AbdulHaleem ya masa na rokon ya amsa ne ya amsa sannan su ka fita.
Wa'inda ke waje sun yi mamakin ganin AbdulHaleem da yaro da kuma mace sanye da niqabi. Nan yan gulma a cikinsu su ka fara kallon kallo yayin da wasu su ka basar. Bai ce musu komai ba ya isa ga motar sa nan ne aka bude masa, Ramlat ta fara shiga sai Ahmad kafin shi ya shiga.
Babu wanda ya maganta cikinsu har su ka isa filin jirgi, nan su ka shiga jirgi sai daular Musulunci Qahɗaanie. Sai da la'asar jirgin su ya sauka a Qahɗaanie nan din ma mota ce ke jiranye s wajen don Tafiya masarauta.
***
Labari ya riga su isa don jakadan Qahɗaanie ya kira mai martaba ya fadi masa aure AbdulHaleem fa yayi a Ghana kuma har da rabo, don dai shi kam shaida ne a yaya mata Fatima ta haifa masa. Ko da mai martaba ya ji shiru yayi bayan ya sallami jakada. A sanina AbdulHaleem ba zai taɓa aure ba da izinin sa ba duk kuwa rashin tabbas na ɗan yau amma ya hakura ya jira zuwan sa.
Haka wajen Ummu Maryam da gidan su Fatima duk tsegumin ya is ko su amma sai su ka fi Ta'allaka da cewa Fatima ce dama Ghana ya ajiye ta kenan.
Daga kallon da ake jifan shi da ya san wani magana ta shigo masarauta hakan ya sa ya wuce da zubaida ɗakin Ummu Maryam ya kuma umurce ta da kar ta yarda a ga fuskanta. Sannan ya wuce majalisa inda ya iske wajen makil da mutane kamar jira ake a ji daga gare shi, ga yan jarida da ma'aikatan gidan jarida kamar su aljazeera da sai sauran su. Hankalinsa ya tashi don Kuwa ya san bayyana Ramlat yanzu kamar zuba fetir ne a wutan da ke ci balbal.
Bayan ya kai gaisuwa ya samu wajen Zama kamar kullum ba tare da ya furta komai ba kamar yanda mutane su ka so yayi.
"mai martaba an samu ɓarkewan gobara a Hilaalu Qamar, mutane fiye da 100 sun rasa rayukansu kuma har gobe ba'a san Silar ta ba" cewar wani ɗan sanda da ya shigo yana haki.
Karkade kai AbdulHaleem yayi don ya san ba kowa ke da alhakin wannan abin ba sai ISMAALIE, ya san shirun sa su ka yi wani shiri ne na daban.
"A shirya mana tafiya zuwa wajen yanzu, sannan a haska komi ga mutanen gari" AbdulHaleem ya faɗi yana mai cijewa. Sarki ya girgiza kai alamun nuna jinjina, hakan ya sa su ka fita zuwa wajen. Tafiyar minti talatin su ka yi zuwa wajen. Cincirindo mutane ne ana tsamo gawawaki da wa'inda ke da sauran ransu amma sun jikkata sosai.
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun" kawai AbdulHaleem ke fadi don bai taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba. Tare ya shiga cikin yan kwana kwana ana kauda gawawaki ana saka wa'inda ke d rai cikin motar asibiti. Suna yi suna duba fuskokin gawawakin da ba su qone kurmus ba, don gane mamatan. Anan su ka tsinci wasu gawawaki guda biyu a kusa da juna kafafun su ne kawai ya ƙone, AbdulHaleem ya kalle su ya kara nan kawai zuciyar sa bata bashi ba, nan ya sa aka ɗauke su hotuna sannan ya sa aka haɗa su da sauran.
Sai da su ka sallace su sannan su ka birne su gaba daya, sheikh Yusuf ya musu wa'azi mai shiga zuciya duk ana mai nunawa live a dukkan tashoshin talebijin, hakan ya kara ma AbdulHaleem daraja da Martaba a idon duniya
Manage this..
Love u all 💞💕😘😍
Add Vote
Happy birthday, sweetie. May you always believe in yourself and follow your bliss, wherever it takes you! Wishing you a birthday as beautiful and bright as you, dearest daughter! Have an incredibly wonderful birthday, our sweet little angel Hafsa (Haneefa)
Sai da aka kwana uku ana makoki, da su AbdulHaleem da sauran manyan masarauta, a cikin kwana ukun nan AbdulHaleem baya ko runtsawa, kokari yake ya gano su waye mamallakin wannan fuskan ta wata na'ura da ya samo daga Amerika wanda aikinsa tantance sassan jikin dan adam ne, wannan na'ura in aka sanya ko da hoton Yatsa ne zata aika hoton yana gizo in da zata dauko hoton da yatsan nan ke ciki da inda hoton yake. Sai da yayi kwana uku kafin ya samu aka samo masa hotuna guda goma na mutanen nan biyu kusan duk hotunan a tare su ke ɗauka. Har ya cire rai ya fara tunanin zargin su kawai yake kila kasuwanci ya kawo su kasancewa Hilaalu Qamar na da babban kasuwa da ake zuwa cin ta da ga fadin duniya. Sai ya ga an sa masa next, wato da sauran bincike kenan, bai yi qasa a guiwa ba ya latsa nan ya samu abin da yake so. Wato wasu hotuna ne nasu tare da manyan yan ta'adda, majalisar ɗinkin duniya ta sanya binciken su. Buɗewa yayi da kyau nan ya karanta takaitaccen tarihin su.
Daya daga cikinsu Joseph Jones dan asalin Nairobi ne, a kasa sai aka ambace shi da zama dan bindiga, shi kuma na biyu Yasser Musa dan Kasar Somaliya ne, shi aka ambace shi da laifin ta'addanci, nan takaici ya cika AbdulHaleem wato in musulmi zai fitar da sanda ya daki wani toh ta'addanci me amma in wanda ba musulmi ba zai yi wani aiki da ya shafi kisa toh tabbas shi din ko dan bindiga ne ko kuma mashayi.
Cigaba da bincike yayi har ya samo wani hoto na su da ya fito sosai a nan ya adana hoton ya ajiye kwamfutar. Daga nan ya aika ma jami'an tsaro da kuma yan jarida don a fada ma duniya wa'inda su ka aikata wannan ta'asan sannan ya yi kira ga saura da su guji fadawa tarkon su. Hakan ya kawo cecekuce, yan siyasa na duniya da manazarta suna kara jinjina ma masarautar Qahɗaanie na amfani da hanyoyin zamani wajen magance ta'addanci.
Yan kungiyar ISMAALIE kuma hakan ya sanya masu tsoro da dan firgici don jin kalaman masarauta akan tsatsauran hukuncin da za'a masu in an kama su, sannan ga kyauta ta musamman ga wa'inda su kayi saranda. Wannan ya sanya su shirya taron gaggawa a gidan Amir Alhamzie Wanda ya dawo Zangon Qahɗaanie ba tare da sanin kowa ba sai su yan kungiya.
"Wai ni ban gane ba, mun dawo Qahɗaanie baka barni na je ga Ammie ba, kullum kana hanyar fita, kai ba soja ba amma duk wani nau'i na bindiga kawo maka ake, me kake yi da su" zubaida ta tambaya cikin fushi, ta rasa gane sana'ar mijinta sannan an kawo ta wani gida an garkame.
"Kinga yanzu ina da taro, kar ki ɓata min lokaci. Kar ki damu ba abin da ya sami dangankinki, Ramlat ce ma de ake kan nema wata shida kenan ita da yaron ta su ka gudu. Wacce ba ta iya hakuri m Ibadan aure ba ta ya za ta yi nasara gobe kiyama" yace yana ratsewa ta gefen ta ya na mai ficewa haɗe da garkame qofa kamar yanda yake mata.
Zama tayi daɓas a wajen tana tunani in har Ramlat za ta gudu toh cikin biyu akwai ɗaya, walau su na magana da Fatima ta yaudare ta ko kuma da gaske mijin nata na da wani dodo a kwabat. Shiru tayi tana tunani itama ga ta nan dai, kwanaki an ce Qahɗaanie na cike da hatsari da karancin tsaro, amma ita gidanta babu wani abu makamancin haka. Sai dai kuma kalaman mijinta a ko da yaushe na 'mun kusa mulkan Qahɗaanie, na kusa zama sarkin Qahɗaanie' ya faɗi mata hakan ya fi sau a kirga amma bata taɓa yin ma kalaman fashin baqi ba se yanzu.
Tashi ta yi zuwa dakin sa, tana mai addu'ar bai kulle ba, don ba kasafai ya ke kullewa ba tun bayan da ya sa Allah ya isa in ta shiga ba tare da izininsa ba. Ajiye yaron da ta ke goye da shi tayi gefen yayansa dan shekara huɗu sa rabi sannan ta je. Durowowi ta fara bincika anan ta ga abin mamaki, bindiga, kwaroron roba, guru, layu, wayoyin cable da dai sauran abubuwan ta'addanci kamar su wukake girma girma.
Haka ta cigaba da bincike nan ta ci karo da jaridan da aka manna manyan yan ta'addan Afirka, sai ga hoton mijinta a matsayin Adjetey ba Abdallah da ta sani ba, kuma a matsayin mataccen ɗan fashi D gwamnatin Kasar Ghana tace ta hallaka saboda laifin fashi. Ko da ta ga kwanan watan nan ta Shiga tashin hankali Saboda tserar wata daya ne da lokacin bikin su.
Tunawa tayi da zancen Fatima da take faɗi mata aibun auren wanda ba ta sani ba, bata san inda ya fito ba kawai don ta matsu ta yi aure. Kuka ta fara kamar ranta zai fita amma sai tunanin hakan ba shine mafita ba, ya sa ta samun kwarin guiwa don samun cin ma nasara.
***
Ramlat tun bayan isarta dakin Ummu maryam ta ke cikin dar-dar, amma kuma ganin yanda Ummu ta amshe ta ya sa ta sakin jiki, gobaran da aka yi ya sa ba'a bi ta kanta ba, sai da aka gama makoki. AbdulHaleem neman Mahaifin ta da mahaifiyar ta yayi sannan mai martaba da kuma Ummu nan su ka hadu a dakin sirri na masarauta kafin ya aika ma zuwan ta da na yaron.
"Ramlatie!" Hajiya Amina tace tana rungume er ta cike da hawaye.
"Na san kai alkhairi ne, mun gode Allah ya saka da alkhairi" ta faɗi tana shasshafa er ta. Maganar sai ya ba Alhaji Yahuza dariya, wato sharrin da take kira ne yau ta kira da alkhairi. Isa ga Mahaifin ta tayi shima rungume ta yayi sannan ya sumbaci goshinta . Sai da su ka gama murna AbdulHaleem ya faɗa masu inda ya haɗu da ita, da kuma amanar ta da ya bari a hannun Sufyan.
"Zan wuce da ita wajen Fatima saboda tana cikin hatsari" ya kammala da faɗin haka.
"ban yi shekara ba na fahimci sana'ar miji na ba komi bane sai shan jini da kungiyar asiri, duk yanda na so na tuntuɓe ku na kasa sai daga baya na aika ma ukhty Fatima sakon text daga wayar wata matar shugaban sa. Ni dai na san na goge text din amma ba'a yi sati biyu ba ya dawo ya min dukan kawo wuka wai na faɗi a gidanmu yana shan jini, wacce na tura mawa sun bar Qahɗaanie kuma a satin za'a je a kashe mijinta.
Tun da ga ranar sau 1 ake bani abinci, sannan in ya tashi nema na baya min ta inda aka halatta, haka zai qulle ni ya gama abin da yake da shirin yi. Haihuwan Ahmad ya sa nayi tunanin zai raga min amma maimakon haka sai abun ma ya karu. Ana cikin haka mijin zubaida ya zo gidan mu, anan ya ke fada min da hannun sa ya kashe mijin ukhty Fatima, inyi ladabi irin na zubaida in ci moriyar rayuwar duniya. Nan fa na nemi yafiyan miji na muka zauna lafiya, a lokacin na samu saida har ya ke ganin na miqa wuya ya fara bari na zuwa kasuwa da asibiti amma shi ma da masu tsaro na.
Bayan shekaru hudu ne wata rana na samu maganin barci na zuba musu a lemun abarba da kwakwa, nan su ka sha su ka fara barci. A haka na gudu na bar gidan ba tare da sun sani ba. Rashin sanin wajen zuwa ya sa mu ka isa dajin da aka tsinto mu, ina ga mun yi kusan wata shida a wajen ko fiye don kuwa tun abin da na qullo mana ya kare muna samun kayan marmari har mu ka kai ga cin ciyayi har mu ka koma shan rawu" ta faɗi tana zubar da kwalla. Haka duk wanda ya ke zaune sai da zuciyar sa ta motsa don tausayin ta.
"ina ga zuwa Anjima da maraice za mu wuce, na bar iyali na da juna biyu duk da na san Don zai kula da ita amma tana bukatata" ya ce yana kwanto ma mai martaba.
" malam ba za ka tafi da ya'ya na biyu garin da ba mu sani ba" cewan Ummu Maryam
"Italiya fa nace zani, ban bar wajen ba, ina can duk da ina tunanin komawa Mauritius" ya faɗi yana dariya.
***
Jirgin su na tashi Ammie ta daga waya ta kira Adjetey, da murna take ce masa yanzu jirgin su Ramlatie ya tashi da mijin Fatima ai shine ya tsinto ta, ai yace daga Italiya zasu koma Mauritius.
"Mauritania dai ko, ni ban taɓa jin kasa haka ba, ai ko haska yace kila ya faɗi ne don ya shashantar da mu ne" ta bada amsa.
"ai gara da ya ta fi da ita, shegen mijinta ya je ya ci kanshi, wallahi ya ci amana since shi yasa nace miki da farko na sha sharri ce kawai" ya fadi yana nuna farin ciki. Zubaida da ke zaune a wajen ji tayi kamar ta shiga cikin wayar ta nakaɗa ma Ammie duka.
Add Vote
double update Is an angel's birthday. ..
Ko da ya gama wayar ya fara bata labari ji kawai tayi ta kara tsanar sa, wanda zai iya nuna farin ciki akan abin da ta yi imani zuciyar sa na cike da bakin ciki toh ta tabbatar abubuwa da ya kasance yana ɓoye mata yana cutar da shi da yawa su ke. Bata dawo daga duniyar mamaki ba sai taji yana faɗin
"Banza an baka amanar yarinya ka cinye, Allah ya kubutar da ita ga ta anan AbdulHaleem ya dawo da ita, ya kuma..." bai kai aya ba ta fisge wayar ta buga a kasa, firgigit yayi yana kallon ta
" a matsayin adjetey kake magana ko Abdullah?" Ta ce tana mai tsallakewa ta wuce ta barshi baki a hangame. Tunani yake ya akayi ta san wannan sunan ko kuma dai ta samu mai kawo mata tsegumi ne, amma kuma ko da yaushe rufe ya ke barinta. Tashi yayi don neman hanyar yin waya don kuwa dole yayi ma tufkar hanci.
***
A gajiya su ka isa Milan city, Ramla sai Kalle Kalle take don Tsabagen kyau da ta iske, a da tayi tunanin kyau na Qahɗaanie saboda ganin yanda ya ninka Ghana a kyau se yanzu take ganin Afirka ba komai bane cikin ta sai dauɗa. Tun tashin duniya uffan bai ce mata ba, har su ka isa Milan city, anan ne su ka iske su Fatima a wajen jiran passenger.
Turus Fatima ta tsaya tana kallon mijin ta rike da yaro mai kama da Yaranta, sai dai shi baqi ne, a daga bayansa kuma mace cikin niqabi.
Daurewa tayi ta isa gareshi, bayan ya ɗaga yaran yana sumbatar su.
"Papa wanene wannan handsome din" humaira tace tana shafa fuskar sa.
"ɗan uwanku ne sunan sa Ahmad. Ahmad ga yayyin ka" yace yana haɗa hannuwansu.
"muna da tafiyar mintuna kafin isar mu gida fa" fatima tace zuciyar ta na kuna, ko ta ina zata fara ne ma wai itace da kishiya. Bai ce mata komai ba har su ka isa mota, ya shiga mazaunin direba ya zauna hakan ya sa zama baya tana kumbure kumbure. Kallon ta yayi ya girgiza kai, bai ce komai ba su ka. Cigaba da tafiya, ita dai Ramla bata dage niqab ba saboda umurnin da ya bata kenan.
Suna isa gida ya d'auki kayan Ramlat ya shiga da shi gida, su kuma su ka biyo sawunsa, yaran ko kula da su ba su yi ba sai wasan su su ke.
Sai da su ka shiga cikin gida sannan ya ce ma Ramla ta daga niqab ɗin.
"Ramlatie" tace tana mai ja da baya, "Amma kun ɗauki alhaki don kila jini na ya kai 300" ta ce tana rungume ta.
"Ai Kiris in fashe da dariya, nace Ukhty da kishi take" nan su ka sa dariya su duka. Shi kuma AbdulHaleem ya haɗe rai kamar bai san suna yi ba. Tashi yayi ya shige dakinsa har da sa makulli.
"kamar fa yayi fushi ne" Ramla ta ce tana kallon er uwarta.
"manta da shi, zo muje ki yi wanka kinji" Fatima ta faɗi tana mai mikewa.
***
Kwana su kayi suna hira, sun sha kukansu yayin da Ramlat ke ɓata labarin rayuwar aurenta,
"Ai Ukhty na ɗauki darasi, gaggawa a aure ba shi ne jin daɗin auren ba, Hmmmn na ga rayuwa ni yanzu ban ma san makoman aure na ba" ta ce tana share hawaye.
Add Vote
"ai kin san kowa da kalar kaddaran sa, mutum kan zama sanadi ne kawai. Ba don kiji haushi ba, sai da na kusa talatin amma kuma wallahi se dai irin faɗan nan, amma kam ban san bakin cikin aure ba" fatima tace tana tausaya ma kanwarta
"ai Ukhty zubaida ce abin tausayi, mijinta ashe ɗan fashi ne, wai a Ghana an san an kashe shi ashe fitar da shi aka yi sai ya samu masauki a Zangon Qahɗaanie" tace tana karkada kai.
"toh Allah sa baya cikin ISMAALIE don ni tsoron su nake. Oh ni 'ya su, Ammie kuma na, zaune hankalin ta kwance" cewa Fatima
"Ukhty wallahi tunani na kenan, iyaye na da aiki a gabansu, son abin duniya na sawa ba sa wani maida hankali wajen sauke hakkin su. Allah dai ya bamu sa'a"
"Aameen Ramlatie kina jin kiran sallah kuwa, Taɓ lallai mun raba dare, bari in je in lallaɓa sarkin gobe" Fatima tace suna dariya.
***
Ko da ta isa ta iske shi zaune saman darduma yana karatun alkurani. Zama tayi gefen sa har ya kai karshen suratul Maryam, yana shirin fara basmala na suratul ɗaha ta amshi qur'anin.
Banza yai mata ya cigaba da istigfari, a bayyane tana jinsa. Kamo hanunsa tayi ta daura asaman cikinta hakan ya sa ya kallo ta yana mai kara haɗe rai
"kin san lokacin ibada ne yanzu ko, don an kira sallan farko" ya ce cikin dakewa.
"wani Ibadan na ke sonka da shi, kira'arka da na ji ya tayar min da kwadayin ka" ta rada masa cikin kunne. Duniya in akwai abin da ya ke so ta nuna tana muradinsa hakan na kara masa son ta da begenta a cikin ransa.. Amma duk da haka ya dake bai dai motsa ba sannan bai taimaka mata ba ita kuma bata kyale shi ba.
Bata wani sha wahala ba ya kasa jurewa ba shiri ya bada kai..
***
Tun da suka koma AbdulHaleem ke shirye shirye komawar su Mauritius saboda ya san rayuwar sa da na iyalinsa na cikin hatsari, hakan ya sa ya nemi Don da ya bashi jirgin sa mai tashin angulu
su ka isa Republic of Mauritius (French: République de Maurice) , sun fara sauka a babban birnin Kasar wato Port Louis, da Niyyar yin sati ɗaya don su ga garin da ake kira da Aljannar duniya. Mauritius kamar kasa ce a cikin Afirka sannan itace Kasar da ta raba Afirka da Asia, zagaye take da ruwa (island) fiye da kashi hamsin da ahlin Kasar yan addinin hindu ne, kashi 13 ne kawai musulmi amma hakan bai hana musu daraja musulunci ba.
Bayan sun share mako suna ganin gari sannan su kayi kaura zuwa THE ST REGIS MAURITIUS Resort
, wanda ya ke Kewaye da ruwa, ga wajajen shakatawa. Anan su ka kara gode ma Allah da ni'imar da yayi musu don kuwa hatta shi AbdulHaleem bai taɓa sanin da wani kasa Mauritius ba balle abin da ta kunsa sai da yake Qahɗaanie yana bincike ya gano ta cikin map din duniya.
Add Vote
Suna zaune a cikin resort amma Tunaninsa na Qahɗaanie, tun bayan da labari ya iso shi akan an sace matar Galadima da Ummu Hafsat wacce ba ta daɗe da warwarewa ba, an sace su ne a cikin asibiti Ummu Hafsa ta je don kara duba lafiyan ta, sannan ga wasu yara kanana da aka sace ana sakin ma masarauta gawawaki ɗaya bayan ɗaya. Latso tauraron dan adam ɗin da aka jefa Qahɗaanie ya yi, Ya sanya lambobin sirri take ta haska masa daular. A hankali ya ke bin sawun da yake tunanin nan ne mabuyar yan ta'adda yana yi yana aika ma sojin Qahɗaanie da sako (signals) su kuma a can suna amfani da shi wajen bincike. Hankalinsa ya dauku ya tuna da ai suna fitar da fayafayen video, bai wahala ba sheikh Google ya samar masa wanda aka turo karshe. Nan ya shiga ciki ya fara lalube yana dubo lambobin internet da aka sa wajen shigar da bidiyon.
***
Tun bayan warkewan Ummu Hafsa ta ke karɓan magani daga likitan masarauta. Tayi kyau abin ta amma ko da yaushe burin ta fita, hakan ya sa ta haɗa baki da likita akan za ta je asibiti don wasu gwajin. Hakan ya sa mai martaba ya haɗa ta da matar Galadima don kula da ita.
Sun kammala da likita sun fito ofishin kenan ta ji bindiga a kunnen ta.
"wuce mu tafi" suka daka mudu tsawa hakan yasa su ka bi su ba tare da gardama ba, ba ta kofar da su ka shigo aka bi da su wani wajen. Bakin mota mai rufaffen Baya (van) aka shigar da su.
Shigar mutan Kasar ke yi kenan
Tafiya ake da su kamar za su bar gari, ihu da kabbara kawai su ke yi suna harba bindiga sama, hakan ya kara ruda cikin Ummu hafsa, gani take kawai mutuwa zata yi. Ta ina zata fara, me ya sa sai ita ne ko da yaushe a saninta ko a jiya Ummu Maryam ta je unguwa kuma ta koma gida lafiya lau.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" ta faɗi dan da kyar. Tunawa da tayi da kalaman AbdulHaseeb ya sa ta barkewa da kuka, ta ina za ta fara?
"Ummu ki tuba tun kafin Dana sani ya zo miki a kurarraren lokaci, babu abin da zai daga masarautanmu yanzu sai ni da AbdulHaleem, haɗin kanmu shine zaman lafiyan mu da al'umma gaba ɗaya, a da mun bi kururuwan iblis amma ina ga lokacin tuba bai kure mana ba ko" ya fadi yana fice mata daga dakin saboda irin kallon da ta ke jifan shi da shi.
'kaico na' ta faɗi tana mai kara sakin hawaye kamar famfo a zaria.
"Ummu Laa tahzan, innallaha ma'ana" cewar matar Galadima tana mai share mata hawaye.
Can cikin daji aka kaisu, ginin tenti ne da tamfolin aka yi du bukka bukka, cikin daya aka cusa su sannan ana sanya wasu kiran samudawa su ka kewaye su ta yanda ko suna da karfin gudu ba za su iya ba.
***
Ko da sakon batan su ya iske masarauta hankula ya tashi, don ganin an sace uwar gidan mai martaba ai kowa ma bai cikin tsaro. Ganin an kwana an tashi an sake kwana an tashi babu bayanin su ya kara tayar da hankalin mutane, duk in da ka shiga zancen kenan, mutane na kara ɓuya a cikin gidajen su, masallatai su ka ɗauki qunuti da sauran addu'oi don samun agaji daga mai duka.
Sai da aka yi kwana huɗu sannan mai martaba ya tara yan jarida don ya aika ma mutanen sa kalaman sa duk da kuwa kasancewar sa cikin rudu da tashin hankali.
"Yaa ku al'ummata, ina muku gaisuwa irin ta yan aljanna Assalamu Alaikum warahmatullah..." Ya fara faɗi bayan ya zauna, sannan yai shiru yana haska duk wani mai kallon sa da murmushi.
"Hakika na san muna cikin rudani saboda bacewan iyayen gari guda biyu kwana hudu da su ka wuce, ni rudani na ba don bacewan su bane, halin da kuke neman jefa kawunan ku ne tashin hankali na, rayuwar al'umma ta ya fi min mahimmanci akan na daya daga cikin iyali na, sannan tsoro ke sa a ci galaba akan gwani. Abin da nake so da ku shine mu haɗa karfi da karfe mu ga mun yaki ɓata gari ma su son ganin karshen daular mu, mu tona asirin duk wani mugu da ke ɓoye a cikin mu sannan mu cigaba da addu'a tare da gyara halayyanmu. Allah na tare da mai hakuri mai yawan bauta masa" ya fadi a karshe yana mai yi musu sallama.
Kalaman mai martaba ya dawo ma da yawa da suka yanke kauna kuzarinsu da kuma wani karfin son ganin sun samu nasara.
Sai da akayi sati da sace su labarin ya iske AbdulHaleem yana Mauritius lokacin, tun da ya ji yake kokarin san kamo inda suke ta hanyar tauraron dan adam da yanar gizo.
"Wai mun zo nan ɗin ma ba zan mori miji na ba, ka aje kwamfutar nan ka saurare ni" fatima ta ce tana jan kafafunsa.
Add Vote
ohhh Azeezaty, nourie" yace yana jan hancin ta ganin ya fara samo abin da yake nema.
Zama tayi gefen sa tana kallon yanda y a ke abu se kace wasan aljanu.
'wai wannan da kwamfutar ya karanta ba gina makamashin nukiliya ba da se Allah' ta faɗi tana murmushi ganin baiwan da Allah ya ma mijinta.
Ya kai gaf dazai kai wajen da ya tabbatar da nan ne sansanin yan ta'addan ne sakon ya rufe sai wata wasika da ya shigo. Cikin jin haushi ya buɗe yana tsaki
'Shiga wannan don yin hiran bidiyo da wakilin mu" ya gani rubuce, bai yi kasa a guiwa ba ya shiga link ɗin inda cikin kankanin lokaci ya iske shi a shafin.
Turawa uku ne su ka bayyana kowannensu sanye da tufafin kare hakkin bil adama.
"Muna maka barka da maraice, muna godiya da amsa gayyatar mu" su ka faɗi, girgiza kansa yayi don ya matsu ya ji rainin hankalin da su ke shirin karanto masa.
"Muna daga cikin masu kare hakkin dan adam ne na majalisan dinkin duniya, mun yaba da kokarin ka na son fitar da ta'addanci daga yankin Qahɗaanie, amma ka san dai su ma mutane ne kuma su na da ikon yin rayuwa kamar kowane ɗan Adam, akwai kudade da majalisa zata dinga biyan Qahɗaanie duk shekara matukar za ku kauda kanku daga harkan ta'addancin da ake a yankin ku, da wannan kudin za ku iya kai daular ku zuwa ga wata mataki mai dorewa tare da samun taimako daga wajen mu. Sai dai rashin ɗaukan shawara zai iya sa ka cikin matsalan cin zarafi ɗan Adam" su ka faɗi suna saurarensa.
"Su kuma al'ummanmu da ake kashewa kullum fa su kuma ba su da gata kenan" ya tambaya a kufule
"Ai su ɗin ba kungiya bace, sannan kowa baya wuce wa'adinsa, saboda haka nake shawartan ka da tsaya a matsayin ka kar ka zaqe da yawa" su na gama faɗi su ka ɗauke. Ko da ya koma ya cigaba da tracking waincan nan ya iske komi wayam.
"Dama an faɗi, turawan nan na da hannu a ta'addancin da ake da sunan Musulunci" ya faɗi cikin tashin hankali. Se a lokacin ya tuna Fatima ta shigo ko a yaushe ta fita bai ma sani ba.
Ji yayi zaman Mauritius din ya fice masa a rai, babu abin da ya ke so. Kamar ya koma Kasar sa ta gado, ya fito ya yaki yan ta'adda har sai sun zama tarihi.
***
Washe garin wayar AbdulHaleem aka sako duk wani da yan Ismaalie su ka sace, maza da mata wasu da ciki wasu a nakashe abin dai babu daɗin ji.
Sarki yai murna da dawowarsu su sannan ya kara bada shela duk wani dan ta'adda ya aje makami sa ya zo masarauta zata ba shi aikin yi don in ya bari masarauta ta kamo shi toh ya sani hukuncin sa kisa ne.
Wannan hukuncin ya zama kanun labarin duk wani kamfanin rediyo ko jarida, wasu na jinjina masa yayin da wasu ke ganin ya tsaurara amma shi bai bi ta kan kowannensu ba ya cigaba da hidimominsa.
***
An shafe wata shida babu wani tarzoma da ya sake tashi a daular Musulunci Qahɗaanie, mutane sun cigaba da lamuran su kamar ba'a yi ba, an manta da wasu Ismaalie saboda tunanin sun zama tarihi, kwatsam sai aka wayi gari da tashin bomb a masallacin kusa da jami'a. Inda aka samu rashin rayuka da dama.
Hankalin mai martaba ya tashi don bai taɓa tunanin mutanen nan na nan ba. An sallaci mamata an kai su gidajen su na gaskiya sannan aka yi makokin kwana uku.
Ana cikin makokin ne AbdulHaleem ya sauka da iyalinsa da Ramlat da Ahmad dinta. Sun iso mutane na ta farin ciki saboda a bayyane su ka dawo.
"MaashaAllah, AbdulHaleem ne da yara biyar, kai ya kamata mu yunkura munyi aure muma" cewan AbdulBaar yana mai rike da yaran da Fatima ta haifa a Mauritius yan biyu masu kama da mahaifinsu. Haka su kai ta santinsu tun bayan isowarsu.
"Ai se hamdala kam, ka san duk abin da aka ce maka ba yin mutum bane na Allah ne shi ya ke yin sa a lokacin da ya so ga wanda ya so. Dubi auren nan nasu da irin sheɗancin da muka saka kanmu a ciki amma da ya ke Allah ya riga ya tsara hakan zai faru ba gashi nan ka ji su tsit ba, sai albarka da su ke tayi" AbdulHaseeb ya fadi yana mai jin Dana sani a tattare da shi. Baya gajiya da nadaman abin da ya faru a baya, sannan baya gajiya da ba kanshi laifi akan duk wani tashin hankali da su ka fuskanta a daular Qahɗaanie.
***
AbdulHaleem da shirin sa ya dawo, bai faɗi ma kowa ba cikin dare ya je ya birne duk abin da ya kunso ya dawo da shi. Sannan ya koma gida abin sa.
"Ai duk wanda ya taimaka wajen rufa ma mai ɓarnar asiri toh shima yana daga cikin masu ɓarnar" ya ke ta faɗi ma kanshi duk lokacin da tunanin wa'inda ba su da hannu da abin zai shafa ya faɗo ma sa a rai.
***
Tun bayan da ya tabbatar da mabuyar yan ta'adda a Qahɗaanie ya zauna ya shirya ma su yanda zai karar da manyan su yanda hakan zai ɓatar da kananan. Da haka ya kulla abota da daya daga cikin su ta hanyar shafin Twitter. Anan ya dinga sanin sirrin su har ya san shirin da su ke da niyyar yi na kona sarauta sai a koma damurkadiyya a Qahɗaanie. Tun daga lokacin ya kara kaimi a shirin sa cikin sirri har ya kai ga shuka nukiliya a yau da ya tabbatar da suna cikin shirin yin taro da mutanen su zasu hallara ciki kuwa har da Saifullahi Alhamzie.
***
Karfe sha biyu na dare nakiyar da ya shuka su ka fashe, nan gaba daya gari ya dauka. Mutane sun rufe kunnuwansu don a tunanin su girgizan kasa ne ya faru a Qahɗaanie. Hayaki da kara ke karade ko ina yayin da ɗakin taron Ismaalie ya banke kurmus ba tare da ko ɗaya daga cikin su ya fita ba.
Sai da garin Allah ya waye sannan aka ga in da aka samu tashin nakiya, nan take masarauta ta fitar da sun shigo da nakiyoyi ne don su hallaka Al'umman Qahɗaanie sai abin ya tashi musu.
AbdulHaleem ya bayar da shedu cikin wa'inda ya biya kudi akan suna cikin Ismaalie amma su an tura su gadin matan su ne. Duniya kwarai ta girgiza da wannan balle da aka samu kusoshin wasu kasashe a cikin mamata.
Salam
Ku kara hakuri da ni pls, ba haka na so ba amma kuma haka abin ya zo. Please ku sanya ni a cikin addu'aoi ku. Ina son ku ina kaunar ku fi SABILILLAH...
Kila na baku wani Anjima
Bayan wasu shekaru masu tsawo...
"Papa ka ganta ko, wai nace zan zani wajen Ummu tana cewa princess ba sa fita, ni de a kaini ko wajen Ummu ko wajen Abbie" faɗin yarinya yar shekara huɗu.
"kin manta alkawarin ki da abbun ki, ɗazu fa su ka zo da ummi ko kin manta" yace yana gyara gilashin idon sa. Shiru tayi kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta sa kuka. Ya rasa me zai mata ta yi shiru, rigiman ta ya fi na sauran ya'yan da Allah ya musu ga shi ta faɗo gidan farfesa ina ka fito littafi ina za ki littafi.
Safiyyah kenan er su ta takwas, bayan yan uku Allah ya azurta su da biyu maza Muhammad da Mahmood, Fatima ta sake yan biyu kuma maza Mus'ab da Musayyib sai auta Safiyyah.
Tun bayan dawowarsu Qahɗaanie abubuwa su ka cigaba da lafawa, tsiararun yan ta'adda da su ka yi saura su ka tsere daga yankin saboda hukunci mai tsauri da ake ɗaukan masu.
A cikin wannan ne Zubaida ta samu ta tsero gida bayan duk ya'yan da ta haifa sun rasu a dalilin tashin nakiya. Da fari Abbie ya ki amsar ta saboda a cewan sa itama er ta'adda ce, haka aka dauke ta zuwa fada bayan kuka babu abin da take yi ita da ammi.
"Ban san miji na dan ta'adda bane sai bayan sa su ka kwace fada, sun kasance suna karanta Ayoyin qur'ani da fassara da yayi daidai da ra'ayin su tare da alkawarin ni'ima ga wa'inda su ka yi taaddanci.
Tun da ya fahimci na fara d'ago shi ya yanke min fita, duk yanda na so da na gudu na kasa da ga karshe ya min alkawarin in na yi yunkurin guduwa sai ya kashe Abbie" ta faɗi cikin shessheka lokacin da mai martaba ya tsareta da tambaya.
"ban ki ko wane hukunci daga gare ku ba, yin gaggawa a al'amura ko da yaushe tudun Dana sani ya ke sauke mutum. Ban nemi zaɓin Allah ba a aure a tunani na wayau da dabara ke kai mutum ga aure wanda bai yi ba kuma yin kansa ne ba wai lokaci bane.
Sai da lokaci ya kure min sannan na san BA GIRIN-GIRIN BA ne abin tayi mai. Ga ukhty Fatima wa zai ce ta taɓa dadewa ba aure, duk wani jin daɗi da mace ke nema a gidan miji ta samu fiye da haka, kaico na" ta faɗi tana fashewa da wani sabon kuka.
Jikin wa'inda ke wajen duk yayi sanyi, wasu na tausayin ta wasu na tunanin na su makoman.
"BA komai ke kai mutane ga gaggawa akan abin da ya jibinci aure ba sai daukansa da ake gasa ba ibada ba, don kowa da na shi tsarin rayuwa, sannan hassada ba abin da ya ke karawa se ci baya.
In ka ce baka yi aure ba, saoinka sun yi, saoinka nawa ke gadajen asibiti sannan nawa ke gidan mahaukata?
In ka ce baka da kuɗi kannen ka na dashi wasu suna can suna kokuwa da numfashi don su samu su rayu kamar kai.
In kana tunanin kai ka fi wani kayi aure shi bai yi ba, kila kullum sai ka zubar da hawaye saboda bakin ciki da kake samu a gidan auren shi yana can hankalin sa kwance.
In kana ganin ka fi wani dukiya ne kake masa dagawa toh a duniyar nan ma mutane nawa su ka san da kai.
In kuwa ka ce hassada da kyashi da bakin ciki ne zaka sa a gaba toh tabbas kyashin nan, hassadan nan ko bakin cikin nan shi zai zama. Ajalin ka.
A rayuwar nan fa yanzu kawai kake da shi, jiya ya wuce babu amfanin dawo da shi, sannan ba ka da tabbas din kaiwa anjima balle ka tsaya fada akan gobe" mai martaba ya fadi yana mai sallaman kowa.
***
Rayuwar su ta cigaba da tafiya sannu a hankali, komi na tafiya daidai misali, Fatima ta koma bakin aikin ta, Ramlat ta koma makaranta inda AbdulHaseeb ya kasa kai da kafa bai da mata sai Ramlat. Zubaida kuma ta koma gida gaban su Abbie.
Nasarori su ka dinga samun su tun bayan auren AbdulHaseeb da Ramlat. Sannu a hankali Fatima ta taka matakin farfesa duk yanda masarauta ta so ta aje aikin ta ki don a cewar ta Mafarkin Mahaifin ta ne dole ta cika masa shi.
***
Daular Musulunci Qahɗaanie ta kara samun cigaba, in da komai nata na tafiya daidai da zamani. Kwanciyar hankali da zaman lafiya ya wanzu sosai a daular. Ilimin kimiyya da kere-kere ya zama abin da ke kara ɗaga daular.
Mulkin daular ta koma hannun yarima AbdulHaleem duk da mai martaba na nan a matsayin sa na sarkin Qahɗaanie. AbdulHaseeb na kula da rundunar sojin Qahɗaanie. AbdulBaar ya koma neman ilimin addini har ya taka matakin malanta saboda ganin sa hidiman da zai ma addini ne kawai zai jawo masa Rahma wajen Ubangiji.
***
Kukan da Safiyyah ta saki ne ya dawo da AbdulHaleem daga duniyar tunanin da ya shiga. Cikin masu yi musu hidima ya kira aka ɗauke ta don ya san ba zata barshi ya natsu ya gama shirya cigaban da ya samo na amfani da karan masara wajen fitar da takin noma da yake so a gwada a damina mai zuwa.
Ana fita da ita farfesa Fatima ta shigo tana mai rungume mijinta ta baya.
"o'ooo ina ta mamakin inda Safiyyah ta koyo rigima ashe dai..." bata bari ya kai karshe ba ta mantar da shi duniyar da su ke ciki
Alhamdulillah....
Banso ya kare anan ba but wani dalili ya sa dole na cire more than 5 chapters don kawai mu kammala a yau.
Ba a son raina bane but may b a gaba in da rai da lafiya kuma Allah Ya so zan dawo na gyara.
In kun lura ko comments bana bi yanzu kun ga hakan kadai ya isa sheda cewa ina wani yanayi..
Kun san ina sonku ko💞💕 wannan na har abada ne.
Tana iya yiwuwa ba zaku kara ji na ba har se wata shekara, tana iya yiwuwa kuma ku ji ni bayan Ramadan. Amma ko ma dai menene ina rokon duk wanda na ɓata ma wa da ta/ya yafe min.
Allah sada mu da alkhairi
Safiyyah Ummu-Abdoul
Safiyyahjibril@gmail.com
08157284163
Add Vote