WASHE GARI:
Kiran sallar asubah ne yasashi bude ido, ahankali yazare jikinshi daga natah, sannan yamayar da bargon ya rufeta, se da yayi wanka sannan yayi alwala yawuce masallaci.
Har yadawo bata tashiba, sede yafahimci idonta biyu, ahankali yakaraso bakin gadon yadagota yamannata akirjinshi yarungume.
Magana yafarayi cike da tsantsar kauna, nagode sosai Yasmeen, kin karemin mutuncinki na diyamace, Allah yamiki albarka, fatana kizama uwar ya'yana, na kasance tare da ke har alahira.
Cike da rarrashi yacigaba da cewa kiyi hakuri ki daure, ina ne yake miki ciwo yanzu? Wani irin kunyarshi takeji, domin ko ido bataso suhada.
Hannunta yakamo domin zuwa bathroom, amma kuma se yaga ta tsaya cak, wani irin zogine yataso matah ajikinta, ashagwabe tafashe da kuka.
Tunin yafahimci hakan, saboda haka betsaya bata lokaci ba cancak yadauketa yashige bathroom, se da yagasa matah jikinta sosai sannan yayi matah wanka, yace kiyi alwala ko.
Tana idar da sallah takwanta awajen, murmushi kawai yayi, don yasan yau dole ne yasha shagwaba, pillow yasaka musu sannan ya janyota jikinshi sukafara kwasar bacci.
Se kusan karfe goma 10:00am wasu daga cikin ma'aikatan Mr Adnaf dakenan cikin gari suka'iso da abin karyawa (breakfast).
Fu'ad ne yamusu waya sukawo musu (order), nanfa take batare da bata lokaci ba, chips and egg ne da soyayyen plantains da kuma pepper sourp din kifi.
Cikin kananan kaya tashirya brown and milk color riga da wando na English West, tayi kyau ga shi kuma dede jikinta, parking din gashinta tayi wanda ya sauko matah 'akafadarta, bata wani bata lokaci ba awajen kwalliya, simple makeup tayi.
Akunyace takaraso inda yake zaune sannan ta durkusa ta gaishe shi, sanye yake cikin yar' karamar riga da wando iya gwiywa na English West, yayi kyau sosai acikin kayan tamkar wani bature.
Ido yatsura matah yana kallonta, takara yimishi kyau sosai, gashi kayan sun karbi jikinta sosai, hannunta yakamo ya janyota jikinshi tare da zaunar da ita akan cinyar shi.
Ahankali yakai bakinshi dede kunnenta yafarayin magana, kinbani wahala sosai rabin raina, da narasaki da bansan irin halin dazan shigaba, saboda ina matukar kaunarki Yasmeen, I love u so much yace ayayin da yamanna matah kiss awuyanta.
Dakyar ta'iya bude bakinta tafara magana, saboda tsananin kunyarshi datakeji tace Yaya don Allah kayi hakuri, nima nadade dafara sonka, ban fahimci hakan bane tun da wuri, se kuma na dinga hukunta kaina da kebewa guri daya, batare danasan nakamu da soyayyarka ba.
Cikin sanyin muryarta tacigaba da cewa tun ranar da kadawo daga U.S, haduwarmu awannan ranar naji wani abu, wanda kuma nakasa fahimtar ko menene, se yanzu na fahimci soyayyar Yaya Abnee shakuwace kawai tayi yawa atsakaninmu, wallahi Yaya bansan ina sonka ba se da kayi two days ban gankaba, na shiga tashin hankali sosai danaga Abba yana shirin rabani da kai, ayayin datah karasa maganarta tare da dora kanta akan kirjinshi.
Murmushi yayi donjin dadin kalaman nata tare da kara rungumeta akirjinshi! Ayayin datacigaba da cewa, I love u yayana! I still love u and I wll love u forever.
Cike da farinciki yakara rungumeta tare dayin kissing natah agoshi! Yace muje toh muyi breakfast, babu komai 'kanwata.
Hannunshi takamo cikin rausaya suka'isa dining room dinsu domin yin breakfast.
BAYAN WATA GOMA:
Tafe take dakyar saboda girman cikin dake jikinta, ayayin da tafito daga kitchen, Fu'ad na hango acan gyefen parlourn yana tayata shirya musu wajen cin abinci.
Jin datayine kafarta tarike yahanata cigaba da tafiyar, wani irin ciwon marane me radadi yataso matah, wanda yayi sanadiyar zubewar cups din dake hannunta.
Cikin hanzari yakaraso inda take durkushe! Salati takeyi cikin tashin hankali, cikin yan' minutes tafara fita hayyacinta, ahanzarce ya dauketa yasa a motor, se asibitin Dr Sadik.
Batare da bata lokaci ba akashiga da ita labor room (dakin aihuwa), Fu'ad kam yashiga damuwa sosai kuma ya tausaya matah matuka, ganin yanda tagalabaita.
Awaya yakirasu Ammi yasanar dasu, befi mintuna arba'in ba (40 minutes) nahango watah nurse takaraso inda Fu'ad ke tsaye.
Yanayin danagan shine ya tabbatarmin da cewa Yasmeen tasauka lafiya, kan kice me har su Husna sun'iso tare da Ramatu me aiki dauke da su flask da kayan abinci.
Su Halee kuma nahango man'yan kawaye tare da Ummansu, nima nabisu zuwa dakin da'aka fito da mejegon tare da abinda ta haifa.
Fu'ad muka tarar rungume da jariri, wani kuma nagani ahannun mejegon, hakan yasanar dani cewar yara biyu ta haifa, abinka da jinin Fulani gabadaya se kuma kunya takamata, shi kanshi Fu'ad yaji kunya yanda muka shigo mukasameshi rungume da baby, musamman dayaga Umman su Halee, dole ana gaisawa ya mikawa Husna jaririn badon yasoba yafice.
Husna kam se murna ake, anyi ya'ya, Umman su Halee ce tadiba matah abincin da sukazo dashi, nanfa tasakata agaba se datayi kyat.
Pepper sourp din zabbi ne wanda yaji kayan yaji dana kamshi, se kuma tuwon semo da miyar agusi da tea datah hada matah.
Dr Sadik ne yashigo asibitin tare da Mufidar shi rungume suke da yaronsu gwanin ban sha'awa har yayi wayo, tunin damah Fu'ad yabugamar waya yasanar dashi haihuwar.
Nanfa yadubasu da jariran, ganin suna cikin koshin lafiya yabasu sallama, nanfa aka dunguma zuwa gida.
Tunin har 'anbugawa mutanen Adamawa dana Taraba waya ansanar dasu haihuwar, Husna aka bari da Ramatu me'aiki anan gidan mejegon.
WASHE GARI:
Tun da sassafe Inna Hafsatu mahaifiyar Abnee tare da Muhseena kanwar su Fu'ad suka kamo hanyar zuwa Gombe, domin Abba yace base andaukota wani wankan gida ba, hakan yasa Baba Iro turo Inna Hafsatu ta zauna da masu jegon.
Yara kam se sam barka, gabadayansu maza, gasu kyawawan gaske, kamar su kuma daya, domin ba'a'iya ban ban tasu.
Fu'ad kam farin ciki fal, ko da yaushe yana nan rike dasu ko fita bayayi idan yadawo daga office, kullun yana gida.
Haka Inna Hafsatu ta dinga yimar tsiya, wai kasar turawa ta batashi, yazama kamar ba dan' Fulani ba, domin ba'asan bafillatani da haka ba.
Ranar suna yara sunci sunar Abba da kuma Baban su Fu'ad! Usman da Muhammadu, ana kiransu da (Naufal da Nawaf).
Yara sunsha gata kam tako'ina, musamman awajen Fu'ad da kuma Abba, anyi bikin suna nakece reni, irin kuma na masu akwai wanda yasamu halarta mutane da damah.
Canfa na hango wasu daga cikin members din MRS YARIMA HAUSA NOVELS GROUP, Suna ta parking motors aharabar gidan, lallai ana zumunci kam, sede muce Allah yakara zumunci da kaunar juna, musamman irin su Sister Huraira Taraba da Sister Asma'u Sokoto (Mrs Suleiman) da Mrs Kabeer Sokoto, Allah yabar zumunci.
Bayan suna Abnee yazo yaga twin's (Naufal da Nawaf), kasancewar baya garin akayi aihuwar, sede Fu'ad yakirashi awaya ya sanar dashi, kuma yahadasu da mejegon sun gaisa.
Ananfa suka hada kansu da Muhseena kanwar Fu'ad, kullun Abnee yana hanyar gidansu Fu'ad, saboda Muhseena.
Se bayan arba'in tukun Inna Hafsatu takoma Adamawa, Fu'ad da Abba sunyi matah shatara ta arziki har ma da ita mejegon.
Muhseena kam dan dole aka bar birnin Bubayero, domin hutunsu na makaranta yakare, shima Abnee beso tafiyar masoyiyar tashi ba.
Bayan anwatse Ammi tazo taga yan' jikokinta, abinka da Fulani gidan kunya, Fu'ad da kanshi yaroki Ammi akabasu aron Ramatu me'aiki, saboda tadinga yimusu reno da yan'aikace aikace, ganin yanda Yasmeen din tafi sabawa da aikinta, ita kuma Ammi aka samo matah watah me'aikin ta zauna tare da su.
RAYUWA MEDADI:
Rayuwa medadi ne cike da kwanciyar hankali tacigaba da tafiya agidan Fu'ad da Yasmeen, tare da yan' yaransu Naufal da Nawaf.
Watannin twin's uku da haihuwa Yasmeen ta kammala karatunta na digiri, sede tun datah gama Fu'ad yahanata yin aiki, domin shi gani yake kawai zata wahalar da kantane, tunda babu abin da tarasa.
Itama kuma Yasmeen din bata daga hankalinta ba, ganin babu wani abin datake nema tarasa agidan mijin natah, hakan yasakata tattara takardunta ta'ajiye agyefe ta rungumi aurenta hannu biyu.
Bikin aminiyartace Halee yataso, sati biyu kuma tsakani dana Abnee da Muhseena, nanfa sukafara hidimar biki manyan kawaye, Fu'ad kam sefaman likemata yake, dashi akaje komai na bikin.
Ana kuma gama bikin Halee sukanufi Adamawa, anan akasha shagalin bikin Abnee da Muhseena, Yasmeen 'ana nan 'ana kuma can, abinka da auren dangi tuwona maina.
Su Ammi ma duk Adamawa suka taho gabadayan su, seda akagama biki suka biyo bayan motor amare zuwa Gombe, twin's kam Yasmeen bata ko ganinsu se sunji yunwa.
Suna shan nono kuma ankoma dasu, saboda basu da wani kyiwa, hakan yakara bata damar shan shagalin biki.
Angama biki acan Adamawa, sannan suka dauko amarya zuwa gidanta dake birnin Bubayero, dake unguwar Abuja Quarters.
Abnee shima Abba ne yagina mishi gidan da zasu zauna kamar na Fu'ad, komai na ginin iri daya da gidansu Fu'ad, kuma yayiwa amarya kayan aure (lefe) yace shima Abnee base yayi.
Anan gidan Ammi tashirya musu walima kayatatce, wanda yasamu halartan manyan malaman addini da damah, nanfa sukayi lectures sosai akan zaman takewar aure, sannan akaci aka sha, angoge wuya.
BAYAN WANI LOKACI:
Zaune take a parlour tana kallon TV, ayayin da Naufal da Nawaf suke zaune akan kekensu suke wasa, Fu'ad ne yashigo parlourn batare datasani ba.
Bayan kujerar da take zaune yazagayo, tare da zuro hannunshi dede kan wuyanta, atsorace ta dago kai sukayi four eye! Cikin yanayin shagwaba tace Honey welcomes, har ka bani tsoro fa.
Fuskarta yatallabo yana cewa Ohhhh! sorry my sweetheart tare dayin kissing natah agyefen kumatunta, bakinshi yakai dede bakinta yafara batah salon kiss irin nashi.
Shide ko da yaushe ganinta yake tamkar yau suka fara rayuwar aure, kamar ba ita ta aifi yara biyu alokaci daya ba.
Abangaren Yasmeen kuwa tana matukar mamakin yanda akoda yaushe Fu'ad yana mar marinta, tamkar wata sabuwar amarya, gaskiya dole mace takula da kanta matukar tanason taga mijinta yana riritata tace aranta.
Adda Fanna babu abinda zance se godiya, kinyimin dukkan gata a aurena, kece kika gyarani, ajiyar zuciya tayi ayayin datah tuno jegonta! Tabbas Inna Hafsatu kema kintaka rawar gani agareni, domin kece kika gyarani da sirrikan magunguna irin na Fulani har na tsawon kwana talatin, nagode sosai.
Jin datayine yakai hannunshi kan kirjinta yasakata yin ajiyar zuciya daga tunanin datah keyi.
Yadade yana batah salon kiss cike da kwarewa irin nashi, sannan itama tafara mayar mishi da martani.
Se da suka dade suna nunawa junansu soyayya cike da kauna sannan ya kamo hannunta sukanufi harabar gidan nasu.
Kyawawan idanuwanta masu daukan hankali ta zuba mishi! Kallonshi take medauke da sirrika iri-iri, wanda kuma yake kara sashi ya rude 'aduk lokacin datah mishi irin wannan kallon.
Ganin sun nufi inda watah motor take ajiye sabuwa fil yabata mamaki! Cike da murna ta kalleshi tace Honey kacanja motor ne? Gaskiya motor nan tahadu sosai tasake cewa cike da farin ciki, hannunta yakamo har jikin motor, motor ce kirar MATRYX yabude wajen zaman driver yace shiga mugani my baby.
Cike da doki tashiga ta zauna tare da yaba motor da kuma samishi albarka, sannan tayi mishi addu'ah taneman tsari da sharrin karfe.
Ga mamakinta setaga ya ciro key din motor yamika matah yana cewa takice motor babyna, farin cikine ya lullubeta! Wanda yasakata rungumeshi tana kwalla me cike da murna.
Gabadaya tarasa ta'inda zatafara yimar godiya! Cikin nutsuwa tallabo fuskarshi tare da yin kissing nashi abaki, cikin sanyin muryarta me cike da yanga tafara magana.
Ido yatsura matah yana kallonta, nagode sosai rabin raina tace, ba ni da watah kalmar da zanyi amfani dashi domin yima godiya, ako da yaushe cikin sakani farinciki kake, nide burina nacigaba dayima biyayya da saka farinciki nima har 'iya karshen rayuwata.
Fuskarta ya tallabo suna kallon junansu yace kinfi haka awajena my baby, saboda haka kar ki damu dayimin godiya, ayayin da ya karasa maganarshi tare da manna matah kiss agoshi.
Cike da yanayi irin ta kauna yacigaba da cewa ke ta dabance babyna, ke tawace, ni kuma naki ne, I love u! Domin da ke NADACE! cike da jin dadin kalaman shi itama tace, I love u too! Nadade dasanin cewa da kai NADACE Yaya Fu'ad, ayayin da su ka sakarwa junansu murmushi tare da rungumar junansu suka koma cikin gida cike da kaunar juna.
ALHAMDULILLAH!!!!
Muhadu asabon littafina mai suna NI DA ASWAD!! taku har kullum Suwaiba Moh'd Gombe (Mrs yarima).
FATAN ALKHAIRI:
Fatan alkhairi ga dukkannin members na MRS YARIMA HAUSA NOVELS GROUP Allah yakara daukaka ameen.
GAISUWA GAREKU CIKIN UMMANA:
Dafatan kuna lafiya da duk kan iyalanku
Sister Mami (Ummu Amna)
Sister Hauwa (Maman Adnan)
Note
DA WA NADACE?
Alhamdulillah! Nasamu damar kammala wannan dan littafin NASA mai suna DA WA NADACE? Wannan labarin kuma ba gaskiya bane, kagaggenen labarine, ina kuma gargadin masu satar fasaha, ban yafewa duk wacce tayi ko yayi amfani da wani bangare na littafina ba, ina kuma rubutune domin jan hankali da kuma tunatarwa, fadakarwa bawai don neman sunaba, AKIYAYE.
MASU KARATU:
Masu karatu nagode sosai da yabawarku gareni, ina matukar jinjina muku kwarai, naga sakonninku, wanda sukenan gida 9ja da na kasashen ketare, nagode sosai da kaunar ku agareni, ina kuma mika ta'aziyata ga sister Husna Sudan na rashin Aunty dinta datayi! Allah ya jikanta da rahma ameen.
LOKACIN RUBUTU
From
1/3/2013
5/4/2013