Haka minister yadawo Abuja jiki Babu kwari
Iya ce da nabil sukazo har gida wajan baffah Kan mgnar shatuwa iya nazuwa tafashewa baffah da kuka tana ruwan masifa yafito Mata da shatuwa Dan Miss ne yazo yagaya Mata shatuwa tabata Kuma yasan komai har da hajiya Fatima nabil na gefe Yana Jin Dadi tinda iya tasa Baki fole afito Masa da matarsa
Baffah hararar nabil yahauyi yace to kaji Dadi ka fado Mata hankalinka se yakwanta Mara kunya Daman matar taka tana da Rana haka ban saniba ai da cewa kayi baka Santa ko kamanta na tinama to inkai yanzu kana santa itakuma in tace Bata Sanka Naga yanda zakayi Dole ai ka saketa
Kunne nabil yatoshe yace bazan iyaba wlh Babu saki Ni da ita Kuma jikina yabani itama yanzu tana sona Dan Allah ka dawomin da matata baffah wlh ba nabil din da kasani bane da
Baffah yace bani da lokacinka se kutashi mutafi Abuja wajan Fatima tinda yau in Allah Yayarda komai zezo karshe kabar mutane su huta da Kai da kakar taka Wai iya yaushe Kuma nabil yazama jikanki kuma kuka Dena fada
Tace ai yanzu mun shirya Kuma shinake gani azaman shatuwa tinda kun batarmin da shatuwa Kuma shi ne mijinta Ashe Dan Miss Miss na da kirki Haka ban saniba bakaga yanda yake yomin siyaiyaba har kudi yake bani su umaru ma hidima yake Tai musu Ashe yafi ubansa miss miss kirki tasa kuka
Shi nabil yanzu kome iya zatace akansa shi da ubansa baya Jin haushi dariyama take bashi
Baffah da su iya Abuja suka tafi sun Isa lfy minister nagida se ganin baffah da nabil da iya yagani nabil na rime da faggwan kayanta suka shigo
iya Kai tsaye wajan minister taje ta zauna kusa dashi tace to miss miss Allah yadawo Dani Ina shatuwa Ina matar taka Fatima itama Ina Mata kallan me kirki Ashe ka goga Mata mugun halinka ko se wani hararata kake kana zaremin Ido du baze tsorataniba ka fitomin da jikata kawai inma magunan kakeso NASA umaru yatara maka yakawo maka kafito da shatuwa kafin inmaka rashin mutunci
Hajiya Fatima tace yihakuri iya kijira zuwa anjima Zan rakaki inda shatuwa take kici abinci ki huta tukunna kirabu da alhaji Ni da kaina Zan kaiki
yau su Amina zasu dawo gida nanjeria mijinta yagama kwas dinsa har ma kwanaki suka Kara bayan wata shidan da sukayi zokuga murna wajan shatuwa ga kiba tayi ga Kyau takara tadada fari sosai ga turanci tanaji yanzu sosai ga yanzu in anganta bazaace tayi rayuwar kauyeba misalin karfe takwas na dare jirginsu ya iso nanjeria hajiya Fatima ce tatura direba ya dauko Amina da shatuwa Kai tsaye gidan minister aka shige dasu shikuma mijin Amina da yaranta gida suka shige se Amina Taraka shatuwa zata shige gidan nata mijin
Lokacin da suka dawo nabil be dawo daga isilamiyaba iyace da minister da baffah kadai agida shatuwa da taga iya har da kuka iyama kuka tafafa tana mamakin girman shatuwa da kyan da takara iya bakin masifa yamutu se murna ake tayi jikalle tadawo
Tace Allah sarki nabilu Yana Ina yazo yaga shatuwa ta dawo yaro Dan albarka ai ingaya Miki Dan miss miss yajansa yanzu du baya masifar Nan da yakeyi
Takalli Amina kema yannan yar Ina yabanki sallah Zaki kasa alwala Ashe kema kinbi halin Miss Miss har dake asace shatuwa
Kafin Amina Tai mgn Sega nabil yashigo dauke da sallama abakinshi cikin nutsuwa yake tafiya gawani kamshin turaransa da yacika wajan kansa akasa yashigo bema kula da suwaye afalanba shatuwa Ido takura Masa tashi tayi tsaye tana kallanshi Yana dago Kai sukai Ido hudu da juna
Ido suka hau mustsikawa suna dada kallan juna
nabil yace ko dai mafarki nakene ban saniba
Shatuwa itama wajan Amina takoma da sauri tace anty Yaya nabil ne wannan Naga Babu shigar da yakeyi ajikinshi ko sarkar Babu
Dariya dukansu suke musu Amina tace nabil ne shatuwa Kinga yacanja ko
Tace eh anty
Rada akunne Amina takewa shatuwa kardai kimanta da du abinda nagaya Miki kifaja ajinki kafin ki saki jiki dashi Amma Naga ke kanki rawa yake niyar ba da kanki kikeyi ke ko Ina se kin nuna wautarki ta ke rikwan kakace
Kafin shatuwa tayi mgn
Nabil yakaraso wajan shatuwa yasa hannu yatabata yaji dagaske itace ba mafarki yakeba hannu yabude almar tazo shatuwa Amina takalla taga Amina na harararta ai shatuwa Bata da mu da gargadin da Amina take mata da Ido na taja ajinta taje da sauri tafada jikinshi suka rungume juna suna dariya
Nabil yace Aisha ina Kika shiga nake ta nemanki meyasa Kika gujeni kinsan wuyar da nasha akanki kinsan halin da nake ciki saboda rashinki Ina kikaje du tsawan wannan lokacin nake ta nemanki waye yasaceki
Shatuwa tace ba anty Amina bace ta daukeni ta gudu Dani america baffah da mommy ne suka sata ta gudu Dani Wai Dan muna fada Ni da kai yanzuma se da taga nayi fishi da ita na dameta da kuka sannan tadawo Dani har cemata nayi yanzu mungirma mundena fada Ni da Kai Amma anty Amina Bata yardaba har da yimin fada tafashe da kuka
Amina hanu tadora aka tazamo daga Kan kujera ta zauna akasa tace shikenan angudu ba a tsiraba goyan Kaka Kenan akwai wauta daga temako se yazama lefi
Nabil ransa yabaci kallan su amina yafara Yana rungume da shatuwa Yana rarrashinta yace yanzu Ashe Daman du rokwan da nake Tai muku kunsan Inda matata take kukaki ku temakeni ku dawo min da ita se da itama ta dameku tukunna kuka dawo da ita anty Amina meyasa kikai Mana Haka kinsan halin da Dan uwanki yashiga akan hakan da kikayi baffah har da Kai mommy kema haka wlh daga yau Kar Wanda yakara dauke min Mata ba da saniba Allah bazan yardaba yishuru aishata gidanmu zamu tafi yanzu rabu dasu daga yau Kar wanda yakuma zuwa yace kizo kuje wani wajan ba da saninaba karki Kuma yarda kibi kowa kinji
Tace to Kuma ai kace katsani Mata baka sansu Kuma Nima kace baka Sona Ni bazan bika gidan kaba bayan baka Sona Kuma bakasan Mata Ni awajan mommy Zan zauna ko anty Amina ko nabi iya mutafi mazagai tare
Muryar nabil narawa yace haba Aisha kuskurene ko Ada da nake fada rashin sanine Amma yanzu nagane gaskiya wlh yanzu nasan darajar Mata Kuma Ina girmamasu ako Ina suke ta dalilinki nasan darajar Mata aduniya nasan Kuma wacece mace kema wlh Ina sanki Aisha Ina kaunarki bazan iya rayuwa in Babu keba kin Zama wani bangare na jikina karki min Haka Dan Allah ki temakeni kiyarda mu tafi gida yanzu karkisa su baffah suyi Mana dariya daddy da iya kusa Baki ku tayani bawa Aisha bawa
Shatuwa tace Babu ruwansu wannan tsakaninmune Suma ai shedane agabansu kasha fada baka San Mata ba sau dayaba ba sau biyuba
Kwacewa tayi daga jikinshi ta haura sama da gudu tana kuka aminace tabi bayanta da sauri nabil shima binsu zeyi
baffah ne ya hanashi binta yace nabil zauna muyi mgn da Kai Kar kadamu zamu tayaka Bata hakuri zata hakura katsaya yanzu muyi mgn dakai kasan shatuwa na da gaskiya ko tinda kowa yasan akidarka takin du wata mace arayuwarka Kuma daga Kai har ita kunsha fada a gabanmu kun tsani junanku Dan Haka muma muka rabaku muka dauke shatuwa ka Dena ganinta Kuma mu munzata temakwanka mukayi tinda bakasan Mata itama baka Santa Kuma nine jagoran aurama ita tinda itama tana tsoran dokarka takin mata kawai kasaketa mukoma da ita mazagai inda tafi wayo nasamu wani me Santa na auramai
Setin zuciyarshi nabil yadafe da hannu yanamai da numfashi Dakar yace Dan Allah baffah kabar wannan mgnar wlh ko amafarki bazan iya sakin Aisha ba bare da hankalina yanzu ko da tsautsayine da Kuma rashin sani Amma yanzu wlh nadena bazan kumaba Kar ka rabamu muna kaunar junanmu ko itama tana sona tana dai tsoran akidatane na kin Mata Kuma yanzu na Dena itama Kuma wlh Ina Santa in karabamu mutuwa zanyi rayuwata takare kunrasani kenan
kuka yafara kamar wani karamin yaro idanunshi na kakkafewa Yana neman sume musu
Ai minister besan sanda yaganshi gaban nabil yadagoshi Yana jinjigashi Yana Kiran sunanshi karka mutu nabil anbarma shatuwa indai itace farin cikinka shatuwa takace Babu me rabaku Nima Ina tayaka San matarka bazan Bari arabakuba ko da abinda na malkaka aduniya ze Kare Akan abarma shatuwa wlh du Zan bayar in kamutu Ni Kuma yazanyi baffah Dan Allah kayi hakuri kacire mgnar rabuwa tinda yagane gaskiya Nima Kuma nagane gaskiya na baka hakuri Dan Allah kayafe Mana daga Ni har nabil iya kisa Baki za a raba shatuwa da nabil kina kallo kinki cewa komai Fatima kiyiwa baffah mgn zamu rasa danmu shatuwa kizo kiga halin da mijinki yake ciki baffah ze rabaku kizo kice kema kina sanshi Dan Allah kiyi hakuri da du abinda yafaru abaya kiso mijinki
Iya sarkin kuka tace rabu dasu Miss Miss aidu jinshi nake Babu wani rabasu da za a yi ainima Ina da hakki akansu tinda jikokinane wlh bazan Yarda arabasuba Dan Miss Miss tashi kaji nabaka shatuwa har abada takace rabu da usuman ai kana da kirki yanzu Nima Ina sanka saura miss miss Naga shima yadan Fara mutunci tashi kayi hakuri anfasa rabaku Fatima mikomin ruwa mesanyi nabashi yasha ko giyarku ta yanbirni me sanyinnan tsiyayo akofi na duramasa abaki yasha wajan kunfa,kunfar Nan Zaki zubo zatafi rike Masa ciki
Hajiya Fatima tace to iya ikwan Allah ko Yaya se kinsa mutane dariya har da giyar Yan birni me kunfa Kuna shaaninku ke da alhaji kunyi amanku kun lashe kuku kadai su alhaji an saduda anga dangwal zemutu har da bawa shatuwa hakuri tatafi tana dariya
Ruwa me sanyi takawo hade da lemon da iya tace ruwan aka Fara shafamai afuska akabashi wani yasha Yana bude Ido wajan baffah yatashi yaje da rarrafe kamar wani yaro saboda jikinshi Babu kwari yakwanta Akan kafarsa yaishuru Yana Mai da numfashi saboda mgnar ma inyayi kirjinshi ciwo yake Daman Kuma bawata lfyce da Shiba du yawan tinanin shatuwa yasashi rashin lfy
Baffah kansa yahau shafawa da hannu yace Allah yaimaka albarka nabil yanzu na yarda kana san shatuwa Kuma zaka riketa Amana daga Kai har sani yanzu na yarda da ku alhamdulillah burinmu yacika na ganin kun shiryu ka kwantar da hankalinka Ni bazan rabaku da shatuwa ba tinda kana santa gatanan Amana nabaka ita ka riketa hannu binbiyu kabawa marada kunya kanunawa duniya mace Yar gatace awajanka Kuma Mata abin darajawane da girmamawa aduniya da idan kowa dadu wani da namiji kadau matarka kutafi gida Allah yabaku zaman lfy Allah yabaku zuria tagari je kakirata kutafi kayi hakuri da dauke maka Mata da mukayi baka saniba
Murna nabil yafara har da rungume baffah Yana ta godiya minister ma Babu kunya yake tayiwa baffah godiya Yana murna iya se washe Baki ake ana hawaye tana taunar goranta
Amina da tabi shatuwa daki duka takaiwa shatuwa abaya tana dariya tace Ashe kina da hankali kanwata aini nazata shirme zakimin Akan yanda natsara Miki Ashe kina sane adai tausayawa Dan uwana Dan Naga yagama macewa Akan sanki kema Kuma nasan kina san Dan kaninnawa ai da bakibi abinda natsara mikiba da munbata da ke
Shatuwa zatayi mgn Kenan nabil yaturo kofa yashigo kallan Amina yafara yace nifa wlh anty tsoranki nake yanzu tinda Kika sacemin Mata Kuma yanzu tsoran ganinku tare da aisha Zan dinga ji Dan Nagano yanzu kece malamarta itakuma dalibarki to malama ayi hakuri Zan tafi da matata gida tahuta tagaji sosai tanasan hutu duda kinmin lefi Dole nai Miki godiya Yar uwata ngd Allah yabiyaki anty Amina da gudun mawar da Kika bada baffah da mommy sun yimin bayani du abinda yafaru Kuma nagane
Amina nasiha takuma yimusu sosai meratsa jiki tace Ni zantafi kanwata se yaushe ko se naganki
Kai shatuwa ta daga Mata tasa hannu tarufe idanta tana dariya
Amina tace ai nasan amsar da zan samu Kenan awajanki kanwata zuwa gobe zansa akawo Miki kayanyakinki har abincin safe du zansa akawo muku asha soyaiya lfy Ni natafi wajan nawa mijin nabarshi shikadai agida tafice tana dariya
Amina nafita nabil yatako zuwa gaban shatuwa Ido yakura Mata Yana murmushi itakuma Kai ta sunkuyar kasa takasa had a Ido dashi wani kwarjini taga yayi Mata yacika Mata Ido
Yace Aishata babu mgn amaryar nabil jikokin iya ikwan Allah ko bakiyi murnar ganinaba har yanzu fishi kike Dani Baki huceba nasan namiki lefi ranar da zamu rabu Dan Allah kiyi hakuri ko temaka Miki banyiba
Kai tadago tana kallanshi fadawa tayi jikinshi tarungumeshi tafara mgn ahankali tace Ni Babu lefin da kai min ai hakkinkane mijina lefinka dayane zuwa biyu awajena kabini da mugunta ranar baka ragaminba katashi ka tsallakeni bakaji tausayinaba ko temakona bakayiba wannanne kadai yatsayemin araina Dan Haka na dada yarda baka Sona Kuma Dan katsani Mata kai min Haka Kuma bakaga wuyar da nashaba nadade Ina jinya saboda da Kai takara mgnar cikin shagwaba da kukan kissa
Dada birkita nabil tayi lokaci guda yaji yashiga wani Hali mararshi yaji tafara murda Masa saboda yanda take dada shinshige Masa jiki ga shagwabarta dada rudashi take jiyayi kafafunshi bazasu iya tsayawaba janta yayi zuwa Kan gadan dakin suka zube bakinta yakamo yahada da nashi sun Dade ahaka sannan yabarta suna Mai da numfashi Dakar yafusgo mgnar bakinshi yafara mgn
Aisha nidai bazan gaji da Baki hakuriba yanzu tinda Allah yadawo min dake lfy zakiga irin kaunar da Zan nuna Miki da gata da kulawa se kin manta kowa kin kuma yarda nabil masoyinkine na gaskiya kinji amaryata yasumbaci goshinta tashi mutafi gida kihuta kintafi kinbar mijinki da ciwanshi me wahalar dashi kin lasawa mijinki Zuma me Dadi kin dada jefashi agogin bege sefa kinyi hakuri da Ni aisha Dan mijinki jarimine ba rago bane
Ita Bata gane me yake nufiba tana kwance Akan girjinsa se shakar kamshin jikinsa take dagota yayi suka tashi tsaye kansa tahau kalla tana dariya tsalle tayi ta shafo gashin kansa taduba hannunta taga bakomai dariya tasa tace ai nazata bakin fenti kakoma shafawa gashin Kan naka Ashe ainahin gashin kankane yanzu Yaya nabil yabar shigar Mata yadena sa fenti akansa wlh naji Dadi yayana Kuma mijina naji dadin canjawarka kamafi kyau yanzu wlh kamar bakaiba kakoma balarabe mijina yadena shigar Mata da zame wando
Murmushi yayi shima yace ko Ni yanzu wlh shigar Bata burgeni Kuma naji Dadi da denawata yafaranta ran matata aikema kin canja sosai my baby gashi har wannan kwalliyar ta Yan mazagai kin Dena kin koma Yar birni muje gida bacci nakeji kema nasan agajiye kike ga mijinki na neman temakwanki
Hannunta yakama suka sauko kasa suka samu su iya nahira afalo lokacin Amina tashige gida shatuwa se wani sunne Kai take abayan nabil
iya tace au Dan miss miss Daman Kuna ciki tindazu ai munzata kun tafi Kai Dan miss miss ka kwacemin shatuwa kaga ko takaina batayi ta mijinta take
Dariya hajiya Fatima tayi tace ai iya sedai kiyi hakuri nabil yakwace Miki shatuwa mijinta zatabi shatuwa Kuma ta kwacewa alhaji nabil
Dariya minister yayi yace ai nayarda Ni shedane nabil yazama na shatuwa Kuma jikan iya
dariya kowa yasa nabil yace Dan Allah su baffah kuyiwa iya mgn tadena kirana da Dan miss miss daddy Kuma Wai miss miss take kiranshi nace Mata bahaka ake fadaba Taki yarda nace in Bata iya kiraba takirani da ainahin sunana nabil shima din da tatashi Kira se da tabata sunan Wai nabilu se kace wani tsoho kuma iya daga yau sunan matata Aisha kidena kiranta da wata Shatuwa nasoke wannan sunan daga yau
Iya tace ko sannu babana wlh baka isaba Shatuwa take Kuma Haka NASA Mata tin tana yarinya ban,yarda ana kiranta da aishaba kaima in nakiraka nabilu in kaki amsawa wlh Dan miss miss Zan kiraka dashi aikaine kakira kanka da sunan tin ranar da aka kawo Shatuwa gidannan Kuma naji mutane da yawa na kiranka da Dan miss miss shi Kuma ubanka Miss Miss ake kiranshi ko amazagai haka kowa yake cemasa ko bahakaba usuman
Baffah yai dariya yace hakane iya rabu dashi kowa yasanshi da Dan miss miss
Nabil hannun Shatuwa yakama yace zo mutafi Aisha baffah ma yakoma bin raayin iya su daddy se da safe mun tafi gida iya se goben in kinzo dada ganin gidanmu baffah Dan Allah karka tafi ban saniba
Ficewarsu sukayi zuwa gida Shatuwa se sunkuyar da Kai kasa ake ba bakin mgn
Iya tace a lanlai Shatuwa Dan Miss Miss ya fitsareki yakwace,minke da gaske ku ganifa ko akanta ba tadamu zata bishiba murnama Naga tanayi Kuma mun Dade bamu haduba ko tace aguna zata kwana tarufe Ido tabi mijinta ko kunya Babu ko sallama Babu se wani sunsunkuyar da Kai dake kasa kamar taiwa sarki karya zamu hadu gobene to Wai yaushema suka Fara San junansu Miss Miss ko kasani
Kunyace takama minister Dakyar yake mgn du kunyar hajiya Fatima da baffah yakeji yace Nima ban saniba iya loci Daya Naga sun kamu da San junansu musamman nabil kema shedace Kinga irin halin da yashiga da Babu Shatuwa se gashi Shatuwa itama tana San nabil nayi mamaki sosai da Haka yafaru iya Daman inaso nabaki hakuri Akan du abinda yafaru akan auran nabil da Shatuwa da rigingimun da mukayi abaya Dan Allah du amanta da komai yawuce yanzu mun Zama Daya mun koma Yan uwan juna Dan Allah kiyi hakuri Kuma tare zamu koma mazaigai naje har gida mu gaisa da mahaifin Shatuwa da mahaifiyarta nai musu godiya Kuma Suma yadace sozo suga gidan nibil da Shatuwa su samusu albarka baffah kaima bazan gaji da baka hakuriba Akan abinda yafaru abaya Mata tagari Fatima godiyata gareki se Ni dake nabiya Mana kujerar aikin hajji gada,dayanmu har da iyayan Shatuwa da kema iya har da su nabil du tare zamu tafi aikin hajjin bana shine tikwicina na auran nabil da Shatuwa
Godiya suke Kai Masa sosai iya har da kuka tace Allah sarki rayuwa daman akwai ranar da zanje maka Kuma ta dalilin Shatuwa da Dan miss miss nagode Allah yasaka da alheri Miss Miss ka gama,min komai arayuwata ta duniya wlh nahakura Akan abinda yafaru Nima kayi hakuri da abinda yafaru Ashe dai Miss Miss ana da kirki da mutunci ko kaifa ashedai Nima mukaminka na Kiran maguna agwaunati ze min Rana ban saniba gashi har maka kabiya Mana zamuje ai dole naci gaba da taramaka maguna wlh sunanan nasa anware wani kewaye agidan umaru Ina taramasu nasan wasuma yanzu Kan na koma gida sun haihu du se kataho da su in kaje in ka kaiwa gwaunati magunan tabiyaka kudinsu nabar maka Kai anfani da kudinka nakane Ni nabaka Ta fashewa da kuka
Hajiya Fatima da baffah me zasuyi in ba dariyaba shima minister dariya yake tayi
Hajiya Fatima tace iya me abin dariya aikuwa Dole Miss Miss in yaje yataho da magunan da Kika taramasa kije ki kwanta kihuta gobe se zuwa gidan su Shatuwa zaman daki ko kin fasa yimusu zaman daki
Baffah yace Kinga Fatima wlh karki zugota Kinga ta manta Kar azo tafiya tace Baza tatafiba kinsan rigimarta
Tashi kowa yayi zuwa bacci hajiya Fatima nashiga daki minister yabiyo bayanta yashigo dakin se jitayi anrungumota murmushi tayi tace miss miss abokin iya ikwan Allah sirikin Shatuwa uba awajan nabil
Yace hm aini Fatima yanzu bani da bakin mgn wlh kunyarki nakeji da ta baffah ga Shatuwa itama ko ya zata daukeni Fatima Allah yaimiki albarka ke Mata ta garice Kuma uwa tagari kinyi kokarin ganar Dani Akan abubuwa da dama Amma idona yarufe se yanzu Allah yaganar da Ni gaskiya wlh naji dadin yanda Naga nabil yacanja Kuma naji dadin yanda kowa ke yabansa mutane da dama na tarata su yimin godiya Akan abinda nabil yake musu na alheri Nima Naga canji ta yanda yanzu muke mgn dshi yanzu nabil har gaisheni yake har kasa Kuma yanzu Naga du yadena halayansa me kikeso nai Miki Dan na nuna Miki irin Jin dadin da nayi na kokarin doramu ahanya da kikayi kome kikeso ki fada zanmiki kishiya dai Babu ita Dan ke kadaice muradina bani da raayin Kara aure Kuma Ni yanzu mijin tacene ke Kan tacema du nine
Tace mijina Ni Kai nakeso da yarana kune abin Sona fatana Ni dai ka Dore abin haryar gaskiya daga Kai har yaranmu komai na jin dadin duniya ka wadatani dshi rokona Daya ka tayani gyara rayuwar nabil bisa hanya madaidaiciya da sauran Yan uwansa shine rokona agareka
Yace angama uwar gidana Kuma amaryata masoyiyata kome kikace shi zaayi
Dariya tasa tace alhaji Kenan munfa girma da wannan yanzu se saban jini su nabil da Shatuwa jikoki nawa yanzu muke dsu ai tsufa yakamamu
Yace bawani tsufa wlh se in kece Kika tsufa barima kigani
MINISTER yakoroni yahanani ganin komai 🤧🤧😜
Kafin su nabil su karasa gida se da suka ratsa yai Mata siyaiya me yawa yajido Mata Kaya kamar ba gobe daga naci har nasawa daganan gida suka shige motocinsu na tsayawa yaransa suka bude musu kofa suka fito agabansu beji kunyaba yarike Mata hannu dayaga bemasaba karata yayi da jikinsa yarungumeta da hannu daya kamar wani ze kwace Mai ita suka shige cikin gida
Me yaransa zasuyi inba dariyaba sukace oga mafa yabi hanya kuga Wanda kullin ikirarinsa yatsani du wata mace aduniya Amma yanzu shine me rawar jiki Akan mace bama yaso akallemai ita se wani haderai yake Yana wani kakkareta Dan Kar agane Masa Mata abinda yafi bamu dariya matar da aka dauramai ita dakyar akasha faman fada Akan auran Wai yanzu shine yadawo San matarsa itama kuga yanda take ta shinshige Masa sun dawo San junansu ai mu yanzu se godiyar Allah oganmu yadawo mutumin kirki munajin dadin aiki dashi
Daya daga cikinsu yace kunga mukwashi kayannan mushiga da su Kar oga yaji shuru mu batamasa Rai Kuma muma yafita namu hakkin yabamu kudi muyiwa namu matan siyaiya dadane ai oga baze bamuba
Su nabil nashiga falan gidansu daukan Shatuwa yayi kamar wata jaririyaba yai dakinshi da ita Akan gadan dakinsa ya kwantar da ita shima yabita yakwanta kurawa juna Ido sukai suna murmushi Shatuwa kasa daure kanlan da yake Mata tayi tasa hannunta duka biyun tarufe fuskarta dashi tana cigaba da murmushi
hannu nabil yasa yacire Mata hannayanta ya rungumeta yasumbaci lebenta yace karkimin Haka Aisha farin cikina Dan Allah kidena rufemin kyakkyawar fuskarnan Taki kinsan irin kewar da nayi Taki kuwa Aisha ban taba sanin Mata rahamaneba Kuma Ni,imane ku se ranar da nashiga kogin zumarki me tadi da ruda tinani tin daga ranar nagane darajar da kuke dashi awajanmu maza wanna ranar bazan taba mantawa da itaba takafa tarihi Bamba arayuwata Kuma wanna ranar tasani gyara abubuwa dadama arayuwata Kuma kikazo Kika gudu Kika barni kikabar mijinki da ciwanshi da yake damunshi kusan ko da yaushe Dan Allah karki Kara nesa da Ni Dan wlh bazan jureba kitashi muje muyi wanka nifa tare zamuyi kinji yakarasa maganar da shagwaba
Mgnar Amina tatina da take cemata sefa kinyi hakuri da mijinki Dan wlh shagwabanbene tin Yana yaro nasan Kuma yanzu tinda yayi nesa da daddy kece yanzu Wanda yafi kusanci da ke nasan ke ze dawo yiwa shagwaba memakwan ke kadai kina Masa shima yimiki zeyi shawarwarin da ta ringa Bata akanshi tatuna
Iska Taki anhura Mata a ido tadawo daga tinanin da takeyi tace nifa nayi wanka agidan mommy Kan na taho Dan agajiye muka dawo kasa daurewa nayi se da nayi wankana acan kaje kayi ai muna tare wataran nanan
Shuru yayi kome yatina seyai munshari yace to Bari Ni natashi naje nayi ni kadai tashi yayi yahau cire Kayan jikinshi Shatuwa naganin haka tatashi tafice zuwa dakinta da sauri
dariyama shi tama bashi yace yarinya Zama ki Dena Jin kunyata Danni tsarina da matata Babu Yar Jin kunya Dole Nagama ciremiki ita gabadaya Dan wlh cutarmu zatayi musamman Ni
Shatuwa nashiga daki tahau dariya tace Amma Yaya nabil dinnan bayajin kunya Ni mamaki yake tabani kamar bashine masifanfannanba me haderai Kuma Naga da Yana tare da yaransa hade Rai yayi yakoma yanda yake ada muna komowa daga Ni seshi se Kuma yasaki fuskarshi kamar bashiba
Tashi tayi tacanja Kaya tasa na bacci Tai du abinda yadace turaruka kuwa tayi barinsu ajikinta ba a mgn Dan Shatuwa baabociyar kamshice tanasan kamshi sosai ga Amina tinda suka je America Bata denawa Shatuwa gyare gyaren mu na mataba Dan gyaran da taiwa Shatuwa ko Babar Shatuwa se dai haka
tana gamawa kwanciyarta tayi Tai addu'a tatofe jikinta tahau baccinta tayi nisa abacci taji ana shafata ana Mata wasu salo ajiki tatsorata sosai Kara zata saki yai maza yahade bakinsu waje Daya sundade ahaka sannan yabarta
yace matsoraciya ninefa waye ze kwanta akusa da ke in baniba
tsorone yadada kamata yanda taji muryarshi tacanja jikinshi har rawa yake Yana dada hadata da jikinshi kamar za a kwacemai ita tsoro yakuma bata jikinta yahau rawa da tatuno da ranar da Tasha wuya awajansa yanda kadai yai Mata yanzu tasan baze raga mataba yau hawayene yacika Mata Ido tafara mgn da kyar muryarta narawa
tace bacci nakeji Dan Allah kabarni na kwanta nahuta kaje dakinka kaima ka kwanta ai Naga ko Ada da muke agidannan kowa dakin kwanansa da ban
Yace da kikace Aisha Amma Banda yanzu Dan wlh bazan iyaba Ni tsarina Babu raba wajan kwana da matata kitashi muje kisha ko wani abinne me ruwa in ma baza kici abinciba ga kazarkican Naga ko budewa ma bakiyiba bare kici kitashi banaso ki kwanta da yunwa
Cikin shagwabar da batasan tana dashi ba tace Ni banajin yunwa kasan me mommy tabani naci daga dawowata yau har farfesun kaza tabani naci Ni kadai tace Wai ko anty Amina Kar nabawa taci itama tamata nata se da safe kaje ka kwanta tajuyamai bayaya
Murmushi yayi azuciyarshi yace du wayanki Aisha bazan iya barinkiba yau karfin Hali kawai nake tin da naganki ciwan marata yake neman tashi
dakyar yasamu ya lanlabata sukayi nafila yai musu addu'a sosai ta zaman lfy da samun zuri,a tagari Madara me sanyi yabata Tasha dakyar sannan yajata sukaje suka kwanta daganan labari yacanja kala tsakanin nabil da Shatuwa aikuwa tafada Taji awajansa Dan gabadaya yafita hankalinshi Dan azaba jitayi Babu wani bambanci tsakanin ranar farko da tayau dan ta gurzu ahannnunshi tin tana daurewa se da tafara Mai Kuka da magiya sannan yaji tausayinta yabarta Amma ba Wai Dan yagaji da itaba jiyayima gabadaya tafi ranar farko haduwa
hawayene yake tazubo Masa shima a idansa ga wani farin ciki da natsuwa da yakeji azuciyarshi addu'a kuwa tashata awajansa awannan ranar tayarda nabil na Santa sosai Kuma yacanja yanzu yasan darajar mace Dan yanuna Mata gata sosai Wanda Bata taba kawo Haka daga wajansaba wankama shi yai Mata ajikinshi takwana mutsi kadan tayi seya tambayeta menene kome takeso har gari yawaye ranar ko masallaci bejeba agida sukayi sallar asuba tare suka dada komawa bacci
Basu tashiba se da karar wayar kiran Amina tatashesu tace taturo direba yakawo musu abin Kari yabuga kofar su yaji shuru Kuma masu gadi da yaransa sunce sunanan Babu inda sukaje har da tsokanarsa tace ko lfy Baku tashiba ko du gajiyar tafiyace da Shatuwa tayi jiya
wayar nabil yakwashe Yana dariya lokacin Shatuwa tatashi itama se kallan fuskarshi takeyi suna hada Ido dashi Tai maza tarufe idanta sumbatarta yayi yace amaryata takaina kintashi lfy yagajiyar tafiya Yana dariya me zansamu yanzu
Kukan shagwaba tahau yimasa tafada jikinshi tace bayan Kaine kagajiyar da Ni Ni Babu wani abu da zaka samu awajena fishi nake dakai se nakira anty Amina da mommy nakai kararka ka wahalar musu da Ni iya Kuma Naga yanzu kana neman kwacemin ita ko na fadamata bayanka zatabi
Dariya yafara Yana rarrashinta yace yihakuri aishata farin cikina fitilar rayuwata ai in kinyi fishi Dani zanshiga damuwa tuba nake kidince Ni imarki ta iya rudar da mutun yamanta da komai ke ta dabance nagodewa Allah da ban taba hada jiki da wata maceba se ke Kuma insha Allahu kece tafarko kece takarshe ngde Allah da yabani Mata irinki Allah yaiwa baffah albarka da su mommy bazan manta da ranar murnan haihuwata da naje mazagai muka hadu awannan ranar na rike ranar tana da mahimmanci awajena kingama siye rayuwata kinsamar min da Jin dadi da nutsuwar da bantaba jiba arayuwata rufe idanki matata kiga wani abu
Rufewa tayi mukullin mota me tsada yadanka Mata ahannu tare da wata gidan sarkar daham Dan kareriya
Ido tabude taga abinda yasa Mata ahannu kallanshi tatsaya yi tana mamaki takasa ma mgn
Yace kinfi karfin Haka awajena Aisha nadade da sayamiki wannan kyautar se mgnar Fara aikina a asibitin da daddy yaginamin zanfara aiki in mungama cin amarcinmu zan dinga duba bayin Allah Ina temakwansu shima du acikin kyautar da nai mikine da murnar dawowar matata gareni da Jin dadin farin cikin da Kika bani
Shatuwa rasa bakin mgn tayi rungume nabil tayi tana kukan farin ciki tana tamasa ruwan addu'a da gode Masa
Yace ya Isa Haka matar Nabil Bari naje nabudewa Dan Aiken da anty Amina ta turo yakawo Mana abin Kari munbarshi atsaye tin dazu
Soyaiya me tsafta da birgewa nabil da Shatuwa suke gudanarwa atsakaninsu inda suke burge kowa Kuma ake alfahari da su har yawan shakatawa suka tafi cin amarcinmu akasar waje inda suka kwashe wata Daya Acan sannan suka dawo gida suna dawowa ba dadewa nabil yafara aiki asaban asibitin shi da minister yabude Masa Yana aiki sosai Yana temakwan marasa shi mutane na alfahari da shi talakawa nayabansa sosai
Inda lokacin tafiya aikin hajji nayi minister yacika alkawarin da yayi nazuwa aikin hajji da yabiya musu iya ikwan Allah ansha kyauyanci da kokekoke a makka ko Ina za a tana katarin nabil da Shatuwa in iya na wata rigimar ko kauyanci dariya su minister suke Mata sunyi aikin hajji lfy sundawo gida lfy
Basu Dade da dawowaba shatuwa tasamu ciki nabil yayi murna sosai da su minister baffah na alfahari da auran nabil da Shatuwa nabil yasa anrusa gidan iyayan shatuwa anyi musu ginin zamani na masu kudi iya nata gidan daban nabil yagina Mata Yana temakwan Yan garinsu mazagai sosai yanda kowa nagarin mamaki yake yanda nabil yake musu barin kudi Yana temakwan su Kuma baya kyamarsu kawayan shatuwa du Suma anmusu Aure yanzu shatuwa tazama abin alfahari amazagai ko Ina hirarta akeyi ita da nabil ana samusu albarka
Shatuwa taci gaba da karatunta naboko Haka take zuwa da ciki ajikinta inda taci sa,a cikin bame laulayi bane
Finah tananan Akan bakarta na ko tahalin Kaka se nabil yazama mallakinta inda tadau aniyar binbiyar lamuranshi ako Ina yake har Allah yabata sa,a taje har asibitin da yake aiki tafaki idan mutane tashige cikin office dinsa lokacin yafita duba marasa lfy dube dube tafara anahaka wayar nabil Tai Kara yamanta betafi da itaba taga sunan da ke dauke afuskar wayar taga ansa farincikina tana gani tagane matar Nabil ce take kiranshi wani mahaukacin kishine yakamata tana dariyar mugunta tadau Kiran kafin shatuwa tayi mgn
finah tace ke Baki da hankaline da zaki kiramin saurayina awannan lokacin ke mahaukaciyar inace muna holewa Zaki takura mana waikema wacece dazaki dameshi munanan agidan da yagina min muna shakatawar mu kinganmu Nan akwancema yanzu muke bacci yadaukeshi yagama hutawa Dani kinganni akwance Akan fadanden kirjinshi Kai gaskiya my nibil ya iya soyaiya ga zumarshi medadi nabil nawane Ni kadai karki Kara kiranshi ko da Wasa kit takashe Kiran tana dariya yarinya du abinki nasan yau se kin barmin nabil Kuma Dole kice yasakeki
Nabil ne yabude kofar yashigo finah taji tsoro jikinta har rawa yake da ta ganshi fakar idansa tayi ta ajje wayar tahau kukan munafurci har da durkusawa kasa tana rokarshi yatemaka ko aurartane yayi dataga yaki kulata jikinshi tafada tarungumeshi kokarin rabata da jikinshi yafara amma ta cukikiyeshi Taki sakinshi tsawa yake daka mata Yana Mata masifa ko akanta shi tsoranshi Kar wani yashigo yagansu ahaka
Suna wannan halin Shatuwa tashigo arude da tsohon cikinta tana Nishi idanta yayi jajaur saboda kuka Allah ne yakawota lfy ko direba Bata jira yakawo taba dakanta ta tuko mota tazo ganin finah rungume jikin nabil shatuwa tadada yarda da abinda finah tagaya Mata awaya ita Kuma Dan makirci se tadada narkewa jikin nabil tana kukan kissa
shatuwa jitayi kanta na juya Mata silalewa tayi kasa ta sume lokaci guda jini yahau zuba ta kasanta ai nabil rudewa yayi besan sanda yai wurgi da finah ba yasaki wata Kara Yana Kiran sunan shatuwa se da nawaje sukaji da gudu mutane suka shigo Dan ganin meke faruwa aciki har da maaikatan asibitin temakwan gaggawa aka hau Bata aka fice da ita dakin haihuwa dagudu nabil nabiye da su du yarude Yama manta wana temako yadace yabata
yaransama shigowa sukayi dagudu suna ganin halin da ake ciki suka san finah tahada wani makircin tsakanin nabil da Shatuwa kamata sukayi suka Tisa keyarta zuwa waje Daya daga cikin yaransa yace muje mu tsareta har se hankalin oga yakwanta nasan zenemeta Dan akwai sa hannunta akan abinda yafaru
Yaran nabil ne suka Kira hajiya Fatima da Amina suka Gaya Masu shatuwa na nakuda Babu Bata lokaci suka taho zuwa asibitin dauke da Kayan da za a bukata na haihuwa Basu Dade da zuwaba shatuwa ta haihu tasamu Yan uku duka Mata nabil na kanta har tahaihu be yarda namiji ko Daya yakarbi haihuwar matarsaba zokuga murna wajan nabil shatuwa ta haifar Masa Yan uku duka Mata har da kukan murna zuwa yayi yarunggume shatuwa Yana kuka ita kuwa Ido ta rufe ko ganinshi batasan yi itama hawayenne ke fitowa daga idanta
Mejego lfy kalu ta sauka Babu wata matsala angyarata ankaita dakin hutu lokacine sukaga su hajiya Fatima nabil zuwa yayi dagudu yarunggume hajiya Fatima Yana dariya da kuka
Yace mommy Kinga ikwan Allah ko aishata farincikina ta haifarmin yan uku duka Mata asheni bansaniba Mata zan fara Haifa ayarana nafari na nunawa mata tsana cikin rashin sani Allah natuba kakafeni Allah ngd da kabani kyauta Yara Mata har uku
Amina itama Baki yaki rufuwa hajiya Fatima itama haka shatuwa taga gata kamar zasu Mai data ciki Kiran Yan uwa da abokan arziki nabil yahauyi Yana fada musu haihuwar minister da iya sunfi kowa murnar haihuwar minister gidanshi yasa akadawo da mejego da aka sallameta iya gabadaya tadawo gidan minister da Zama tana rainan Yan uku
Shatuwa Taki yiwa nabil mgn du mgnar duniyar da ze Mata bazata amsa maiba nabil yashiga damuwa sosai tin hajiya Fatima Bata gane meyake faruwaba har tagane sharesu tayi saboda mutane se bayan suna zatai musu mgn
Anyi Taran suna nagani nafada nabil da minister sunyi barin kudi asunan Yan uku ba a mgn
Yara sunci sunan hajiya Fatima da Amina da iya ana Kiran me sunan
Amina
ihisan
Me sunan hajiya Fatima ikiram
me sunan iya iman
akayan barka nabil har da lefe yahadowa shatuwa akwati goma shabiyu yace Daman yayi alkawari se ranar da tahaihu in ze hado Kayan barka ze hado da lefen shatuwa amaryar jego ataran suna har da Yan uwan nabil Mata nakasar waje du dunzo Suma sunyi rawar gani Amina yayar mejego da angwan jego ba a mgn Dan tayi bajinta ta kashe kudu sosai wajan hadu Kayan barka hajiya Fatima ma baa mgn baffah akayan barka har da shanu yahado dasu anyi shagalin suna lfy kowa yakoma gidansa lfy iyace tace Bazata komaba se shatuwa tayi arba,in
Nabil ne yasa shatuwa agaba Yana ta rukwanta Yana ta Bata hakuri Yana ranse Mata shi finah ba budurwarsa bace Amma shatuwa Taki yarda ko saurararshi takiyi
hajiya Fatima ce tashigo tace Daman Nima mgn nakeso nayi daku Wai meyake faruwa tsakaninku
Kuka shatuwa tafara Taki mgn nabil ne ya gayawa hajiya Fatima abinda yasani shatuwa tace wlh ba Haka bane mommy Basu labirin yanda sukayi da finah awaya ranar da zata haihu tayi
Ran nabil yabaci sosai yaranshi yakira yace sunemo Masa finah du inda take sukace ai Daman tin ranar da abin yafaru suna tsare da ita zuwa sukayi suka taho da ita har gaban hajiya Fatima da shatuwa da nabil
nabil da Ido yakalli Daya daga cikin yaransa yaciro bingiga yaseta Kan finah dashi Rai nabil yahade yakoma ainahin yanda yake ada yace kiyiwa matata da mahaifiyata abinda yafaru ranar da kikazo office Dina in bahakaba NASA aharbeki wlh
Nan finah jiki nafari tagaya musu gaskiya tace Dan Allah shatuwa da nabil suyi hakuri ita yanzu tadena sanshi Tama tuba gabadaya gida zata koma gaban iyayanta tayi aure Kar suyi Mata komai su barta tasan yanzu nabil yafi karfinta ko da bare yanzu San zuciyane yaja mata Haka
Hajiya Fatima ce tace da yaran nabil kubarta tatafi tinda tagane gaskiya Kuma tafadi gaskiyar abinda yake faruwa Allah yadada shiryata
Haka finah tafita jiki bakwari tana datasani Takoma garinsu
Hajiya Fatima fita tayi tabar nabil da Shatuwa kunyace takama shatuwa tataho tafada jikin nabil suka rungume juna suna dariya yace gaskiya kin wahalar Dani ko murna da godiya Baki barni nanuna mukiba na haifomin Yan uku da kikayi yanzu tinda kin huce se mgnar komawa gidako tinda kingama wanka iyama gobe tace zata koma
Bayan shekara goma shatuwa tagama karatu inda takaranci fannin lfy tazama cikakkiyar Dr tafara aiki a asibitin nabil tare suke zuwa aiki su dawo tare alokacin yaran shatuwa shida bayan haihuwar Yan uku ta haifi maza biyu Mata biyu
Girma yakama nabil da Shatuwa inda su iya baa mgn antsufa sosai da baffah
Rayuwa nabil da Shatuwa suke da iyalinsu cikin kwanciyar hankali da Jin Dadi
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Anan nakawo karshen Dan minister
Abinda yake dedai Allah yabamu ladansa Wanda mukayi kuskure Allah yayafe Mana Allah yasa muyi anfani da abinda ke cikin sakwan
Se Allah yasake hadamu awani saban novel Dina mesuna🤔😜 inda Rai da lfy Allah yahadamu da alheri
Godiya ta musamman ga masoyana a du inda suke Allah yabar kauna