Aysha am so sorry... nasan abunda nayi sam ban kyewta miki ba nagujeki alokacinda kikafi bukatata akusa dake ....zafin rashin babyna yasa namanta cewa ke uwarsa zakifini jin radadin zubewar cikin ....kuma duk laifina ne tunfari Dana yarda da abunda kike kokarin gayamun da duk haka bata faruba...nayi butulci danayi saurin manta soyayyarki agareni da alkawarin danayi cewa zan aureki ....amma yanzu nagane kuskurena kuma inaso ingyara wannan kuskuren by marrying u and changing ur life for good.....
Shocking.........😳
gaba dayansu sunkasa motsi tamkar gumaka haka suka dawo se kallonsu suke kamar idonsu zaifado kasa saboda mamakin kalaman dasuke fita daga bakin AK ....
Uncle jamilu se washe baki yake tamkar Wanda akabiyama hajji jikinshi har tsuma yake saboda farin cikin ganin burinsa yakusa cika
Ita kanta aysha sake dabaki take agaban AK tana kallonsa cike da mamaki danjin zancan nasa tayi tamkar amafarki amma ganin ba alaman wasa atare dashi dakuma damuwar datahango afuskokin su asma'u shiya tabbatar mata dabaisan gaskiyar abunda kefaruwa ba har wasu kwalla kezuba a idonta na farinciki muryanta narawa tace oh allah nagode maka dakadawomun dafarin cikina AK dama ansha gayamaka duk duniyarnan ba Wanda zaisoka sama dani amma kaki yarda dani ka wulakantani lokaci guda ka manta da soyayyarmu saboda kafada tarkon wacce batasan miye so ko tausayi arayuwarta ba ....amma yanzu tunda kadawo gareni komai yawuce let's jus get married and start a new life .....
gyada kai yayi tare da kai hannunsa yadafa kafadanta yana murmushi yace yes baby we will get married kuma nan bada jimawa ba ...zamu manta da duk abunda ya wuce ....musake sabuwar rayuwa ...bazan yarda nasake maimaita kuskuren danayi ba yanzu ashirye nake dana aureki base najira amincewar kowa ba ....aso ko kar aso ni AK zan aureki .... get ready baby u will soon gonna be my wife .....
tsalle tadaka tarungumesa dakarfi tana kyalkyala dariyar farin ciki uncle jamilu nagefe yana tayata jiyake yama fita jindadin abunda yafaru dan tuni yaji duk wata damuwarsa ta kauce fatansa kawai yaga andaura aurennan ko hankalinsa yakuanta ....
Grany nagefe azaune tana kallonsu se murmushin mugunta take tana cije lebe seda ahmad yatabota sannan tayi saurin mikewa tsaye tana fadin ...yo wannan ai zancan banza ne ko kunmanta alkawarin danayi cewa matukar ina raye abidi bazai auri aysha ba to har yanzu ina kan bakata idan har kana son albarkata to dole kanisanci aysha kuma kacire zancan aurenta aranka saboda hakan bazai taba faruwa ba
azabure uncle jamilu yamike tsaye cike datakaici ya nufota yana yarfa hannu cikin kakkausar murya yace haba haba inna meyasa kike mun hakane me aysha ta tsaremaki ....miye aibunta dabazaki so AK ya aureta ba....yanda yake jikanki haka itama jikarki ce so what's the point...ko kiyayyar dakike nuna mun ne tashafeta
"Kiyayya kuma jamilu ....
"Eh kiyayya ....tun ina karami nafahimci cewa kin tsaneni sometimes se ina tunanin kamar bake kika haifeni ba ....kin kware wajan Nina banbanci tsakanina da marigayi kabiru sodayawa nakan nemi Abu awajanki amma sekihanani kibashi .....
saurin dago kai grany tayi tana kallonsa cikin sassanyar murya tace mene.....wannan wane kalan shirmene jamilu ....yakake Abu kamar mara hamkali ....
"Eh naji Mara hankaline ni aidama kullum haka kike fada ....u always says stupid things about me ....komai nayi ban iyaba duk abunda zanmiki bazan birgeki ba amma komai kabiru yayi ....was perfect bayataba laifi awajanki to yanzu abunda kika mun shine zakiwa ya'ta....to kisani bazan daukaba kuma idan har kikanemi shiga rayuwarsu to komai zai iya faruwa
afusace AK yayi yunkurin nufo wurinsa ahmad yayi saurin riko hannunsa yana masa alama da yanatsu .....bawanda yalura dahakan saboda gaba daya hankalinsu nakan jamilu da grany
kallonsa kawai grany keyi tana rike dabaki saboda al'ajabin kalaman jamilu tuni wasu hawaye masu zafi suka wankemata fuska
afusace asma'u tashiga tsakaninsu tana kallon jamilu da jajayen idanuwanta cikin kakkausar murya tace ya isa haka jamilu.....idan baka ragamata amatsayin mahaifiyarka ba karagamata kodan katsira da dan ragowar mutuncin dayarage maka ....you've said enough.... kanata ikrarin bata sonka ta tsaneka .....tafison Abba dadai sauran shirmanaka ....shin kataba tambayar dalilin dayasa take haka .... ayar gajeriyar rayuwarka kataba ganin inda uwa ta tsani danta....nooo .... jamilu bansan yaushe ko wane lokaci kuka dauka tare da Abba ba amma inada tabbacin yana mata abunda ko amafarki baka taba yimata kwatan kwacinsa ba ....akowane lokaci kazo wurinta karba kake ahannunta shin kai kataba bata wani Abu .....abubuwan kuntatawa dakake yimata koda dagaske ta tsaneka to banga laifinta ba she have a right to hate u....
tanakainan tajuya wurin khadeeja tama alama da ido nan take tazo taja hannun grany suka nufi bangarenta seda taga sunshiga sannan tafara takawa ahankali har ta isa inda AK yake tsaye da aysha agefensa fuska adaure tatsaya dap dashi harsuna shakar nunfashin juna cikin murya mai kaman rada tace kabani mamaki....dafari kaki saurarata yanzu kuma kana kallo ana gayama grany magana amma kayi shiru saboda son wata yarufe maka ido...waizakuyi aure ....badai aureba ....kuje kuyi amma kusani badai agidana ba dan haka tun wuri kunemi matsuguni ayanzu natabbata kanada isassun kudinda dazasu isheka gudanar darayuwarku yanda kukeso
baijira yagama jin zancanta ba yawuce bangarensu fuskarsa dauke da damuwa kamar tabi bayansa sekuma tadake tana kallon jamilu tace sekafara shirin aure inafata kanada yan canjin dazaka kashe wurin biki dan kwandalata bazatayi ciwon kaiba ....
tana kainan tawuce bangaren grany koda take ta isko ahmad da khadeeja nabata hakuri amma Sam taki kulasu seda asma'u taje suka taru suna lallashinta
[04/08, 17:27] Hassan Atk: AK napalo azaune yayi jugum yana tunanin maganganun jamilu kana ganin fuskarsa kasan yana cikin bacin rai
Har asma'u tazo kusansa baisani ba seda yaji tadafashi sannan yadago kai ahankali yakalleta suna hada ido tagirgiza mishi kai alamar yadaina damun kansa ....
Kwanciya yayi akan 3sitter yadora kansa saman cinyar asma'u harzuwa lokacin baiyi magana ba kuma jikinsa is very weak
ahankali takai hannunta tana shafa sumar kansa cikin sassanyar murya tace ABI tunanin me kake ....karma kabari maganganun jamilu subata maka rai ....yanzu kake gane asalin waye shi amma ninasan zai iyayin fiye dahaka akan abunda yakeso ..... amma yanzu tunda komai yakusan zuwa karshe just relax OK.....
hannunta yakamo cikin nasa yana dan murzawa ahanakali lokaci guda suna having eye contact dakyar ya iya bude bakinsa yace chitti meyasa zasumun haka.....miye banmusu ba arayuwa....duk abunda sukeso ina kokarin basu ...basu taba Neman Abu awajena na hanasuba kuma bantaba bude baki namusu gori ba akanme suke son cutar dani ....abunda yafi bani haushi wai uncle dina ...yan uwana najini sune suke fatan rabani da farinciki suke kokarin dole se wulakantani ....
gefen fuskarsa tashafo cike da tausayi tace ABI kayi iya abunda zaka iya sauran kuma bawanda zai iyamusu shi se allah ....hakuri zakayi da duk abunda zaka gani agidannan kafin lokacinda zaka kammala abunda kayi niyya ...kanada hali mai kyew kana zaune dasu zuciya daya basu isa su cutar dakaiba ....dazu munyi magana da lawyers zasuyi arranging papers amma kafinnan gobe yakamata muje company munada meeting da companyn Lagos ....
"What....akan wane dalili zamuyi meeting dasu ...
Murmushi tayi tana wasa da button din rigarsa tace ABI Sanin kanka ne munada rashin fahimta atsakaninmu ...kuma hakan bayada wani anfani ....akowane lokaci kayi kokarin yakar mahassadanka da kakkyewan niyya ...nakira meeting dinne dan musamu fahimtar juna kuma mumagance matsalar datake tsakaninmu ....aganina idan har muka hada kai dasu gaba dayanmu zamu anfana kuma zamu samu cigaba aharkar kasuwancinmu ....
Tunda tafara magana ya kafeta da ido ko kiftawa bayayi seda tadan hura masa iska bakinta sannan ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya yakamo hannayanta duka biyu yana murmushi yace chitti wasu lokutan nakan rasa wace kalma zanyi anfani da ita wajan nuna godiyata awurinki ....u come into may life as a stranger ....but now u are my everything... I am who I am b'coz of u ....you are every reason... every hope....and every dream I've ever had ...and no matter what happens to us in the future everyday we are together in the greatest day of my life ...I will always be yours and love u forever ....
Murmushi tayi tana kallon cikin idanuwansa lokaci guda son junansu nakaruwa acikin zukatansu ahankali takai bakinta kan goshinsa tamanna masa kiss tana lumshe ido wasu yan siraran hawayen farinciki suka gangaro daga idonta zuwa fuskansa cikin sassanyar murya tace ABI bana bukatar komai daga wajanka ....soyayyarka agareni kadai ta isheni base kafada ba kwayar idonka kawai nakalla ina hango tsantsar son dakake mani ...if I know what love is, it is b'coz of you ABI ....to the world u may be one person but to me u are more than world itself ....
tashi yayi zaune yana facing dinta da murmushi afuskansa ahankali ya matsa dap da fuskarta yana share mata hawaye cikin wani iron salo mai Jan hankali batayi aune ba taji bakinsa anata atsorace ta zaro ido tanaji wani abu namata yawo tundaga tafin kafarta har tsakiyar kanta ahankali tajanye jikinta tana sunkuy dakai saboda bazata iya hada ido dashiba
shikanshi AK jinsa yayi acikin wani yanayin dabaitaba tsintar Kansa amakamancinsa ba ahankali yadago rinannun idanuwansa yana kallonta cikin wata iriyar murya yace chitti please.... why are u punishing me ....haka zamuci gaba dazama kamar wasu gumaka idan ke bakyaso tonidai gaskiya inaso ....nayi alkawarin sakaki fadin ciki idan har zamuci gaba datafiya ahaka ina ake zancan farin ciki ...
Duka takaimasa aciki tamike tsaye tana daure fuska tace dallah kadaina rashin kunya ba kyew ....
janyo hannunta yayi dakarfi tafado kansa suna kallon juna yace naga alama sena koyamaki yanda zakiyi zaman aure wannan bajintar taki ki ijiyeta agefe ...
"OK kana nufin ban iya soyayya ba kenan....
"Of course ...
Murmushi tayi tana zagayo dahannayanta bayan wuyansa cikin murya mai kamar rada tace u need a kiss right ...
kai yagyada mata yana murmushi yace yes ...can u do that for me ...
murmushi tayi tana kallon cikin idanuwansa dawani irin salo tafara cije lebenta nakasa tana lumshe idanuwa hannunta nayawo akan kuncinsa dabayan wuyansa nan take takashemasa jiki har launin idonsa yacanza se kallonta yake damamakin abunda takemasa
bakinta takai setin kunnensa tadan hura masa iskan nunfashinta cikin rada tace close ur magical eyes suna sani cikin wani yanayi
seyaji radan nata yakara tafitar dahankalinsa ahankali ya lumshe idanuwansa yana sauke nunfashi ahankali har wannan lokacin bakinta nakan kunnensa tana sauke masa nunfashi sannan tajanyo fuskarta tana goga kuncinta akan nasa dan yatsanta takai kan lebensa tana shafawa ahankali....
AK zaune kawai yake amma gaba daya baya duniyar datake jikinsa har tsuma yake gashi koyatsansa dakyar yake iya dagata bakinta takai setin nasa zata masa kiss kenan sukaji ana buga kofa azabure tamike tsaye yayi saurin bude kasallalun idanuwansa yayi yana riko hannunta cikin wata iriyar murya yace chitti please.... Kimanta dasu wallahi kika barni ahaka mutuwa zanyi koda kiss dinne kimun indan rage zafi
Jin Ankara buga kofar yasa ya ware murya cike datakaici yana fadin wayene...
Daga bakin kofar khadeeja tayi dariya tana rike baki tace ohh ohh allah mai iko .... to khadeeja ce dama tafiya zanyi se dasafe....
juyawa asma'u tayi zata tafi yayi saurin mikewa tsaye yana riko hannunta ya janyota jikinsa yana langabe kai yace kibarta ta tafi mana batare da ahmad suke ba aiba bakuwa bace dasekin rakata ...
turasa tayi yafada kan kujera dama jikinsa amace tana dariya tamatso dap dashi cikin sassanyar murya tace kajira wani lokacin ....wannan somin tabi kagani idan lokaci yazo zakaga abunda kwakwalwarka bazata iya daukaba ....bana kunyarka u are my best friend nariga nasaba dakai dan haka kashirya yanzu wasan zai fara....get ready for it....takarashe maganar tana kashemasa ido tajuya dasauri tabar palon ...
kwantar dakansa yayi jikin kujerar yana lumshe ido da murmushi afuskarsa yace danasan zansoki haka daban bata lokacina abayaba ....
Jin anturo kofar yasa yayi saurin dago kansa dan atunaninsa itace ganin aysha atsaye yaji ransa yabace wani takaici da tsanarta ya lullubeda amma yayi saurin boye hakan da kakalo murmushi yana mata alama dahannu yace karaso mana baby ...kamarkwa kinsan tunaninki nake
Murmushi tayi tana karairaya ta karaso wurinsa seda yazauna kusa dashi kamar zata shigemasa jiki cikin siriruwar murya tace sweetheart nifa har yanzu senake ganin kamar badagaske kake zaka aureni ba dan allah idan kasan wasa kakemun kadaina please wallahi zan iya mutuwa idan narasaka ....
kamo hannunta yayi yana kafeta da ido yace baby baki yarda dani bane ko aurenne bakyaso ....tunda Mike nataba yimaki irin wannan wasan .... idan ma wasan ne ai bazanyi agaban su uncle da grany bako ....yanzu kinga kokarin danake shine inkwato dukiyata daga hannun asma'u and everything is going according to my plan ....nagama shirya komai sahannunta kawai zan dauka ...daganan kuma se inyi waje da ita muci duniyarmu da tsinke ....
Dariya tayi cike dafarin ciki tace to yaushene auren nakosa naganni adakinka matsayin matarka daganan zannuna maka tsantsar son danake maka .....
Zare hannunsa yayi daga nata yana mikewa tsaye yace very soon ....kifara shiri kawai ....zan baki yan kudaden dazaki danyi sayayya koda zani biyar ne kafin kudina sushigo hannu....
azbure tamike cike damamki tace what zani biyarfa kace AK ....
"Eh kobazaki iya bane karfa kimanta banada kudi kuma dakunnenki kinji tace ba agidanta zamu zauna ba so senakama haya ga sauran hidindimu taron biki ma na yangida kawai zamuyi ....inyaso daga baya nakarbi dukiyata zamuyi abunda mukeso lefenki ma akasar waje zaki hado dakanki ....yanzu zabi yarage naki idan bazaki iya hakura ahakaba shikenan se afasa auren dama can ansha gayamun kudina kikeso baniba ....yana kainan yamike afusace zaifita tayi saurin rungumosa tabaya tana kuka tace a'a AK dan allah karkamun haka dagaske inasonka kuma ba abunda zaihanani aurenka koda zanrasa kayan dazan saka bazan bari kasake kubucemun ba ashirye nake danazauna dakai koda adokar dajine ....nasan komai mai wucewa ne .....I truly love you AK
Murmushin mugunta yayi yana juyowa ahanakli yajanyeta daga jikinsa yana share mata hawaye yace OK baby dama nagwadaki ne amma nasan kinasona nikuma namiki alkawarin sama maki abunda kike so dazaran andaura auren zanbaki mamaki ....
Washegari dasafe asma'u tashigo dakin cikin shirinta nafita da mug din coffe dinsa ahannunta ahankali takarasa bakin gadon tana kallon AK dake kwance yana baccinsa hankali kuance girgiza kai tayi tana murmushi ta ijiye mug din kan drawer sannan tadawo gefensa tafara Jan kafarsa tana kiran sunansa
Juyawa yayi yagyara kwanciyarsa hade dajan bargo cikin muryan bacci yace chitti please kibarni nadan huta kuana biyu banasamun bacci ....
janye bargon tayi tana cigaba da daddabashi tace tashi mana kamanta munada meeting yau lokaci natafiya ...idan mungama sekadawo kayi baccinka
"kidaga meeting din mana bazan iya tashiba kaina kemun ciwo ga zazzabi nadamuna ...yayi maganar cikin muryan rashin lafiya
saurin karasowa tayi wurin kansa tana taba goshinsa tace amma jikinka bazafi ...Sam bakayi kama damara lafiya ba ...
tura kansa yayi cikin bargo yana fadin dole kifadi haka dan bakisan menakeji ajikina bane
jin tayi shiru yasa yadan leko kansa yaganta wurin drawer tana duba wani Abu murmushi yayi aransa yace lafiyata kalau chitti kawai dai inason inga kina kula danine ....I really like it ...
Ganin zata juyo yayi saurin maida kansa cikin bargon yana sauke nunfashi ahankali irin namarasa lafiya
thermometer tadauko tasaka masa abaki sannan tajuya tadauki wayarta tafara Neman numban doctor...
Ciro thermometer din yayi yana kallo ba alamun zazzabi ajikinsa nan yafara waige waige yana tunanin abunyi murmushi yayi dayahango coffee dinsa agefe yayi saurin tsoma thermometer din aciki sannan yasaka abakinsa
duk abunda yake baisan tana kallonsa tajikin dressing mirror ba seda yagama sannan tajuyo tana kallonsa yayi saurin langabe kai yana lumshe ido ...
Karasowa tayi wurinsa tazare thermometer din tana dubawa ....
Zaro ido tayi tanadafe kirji tace ABI ....109 degrees fever ....this is dangerous... Gaskiya yazama dole ka kuanta asibiti wannan ai yafi karfin gida ...
Ya salam
azabure yamike zaune yana fadin what is the need ...base nazauna a asibiti ba ai ....magani kadai ya isa
"No ABI wannan yafi karfin magani ....it's serious ....
Ganin tana kokarin kiran likitan yayi saurin dauke wayar yana kauda kai yace bawani asibiti ko alluran daza'amun ....ni lafiyata kalau ba abunda yake damuna ....
Murmushi tayi tana zama kusa dashi tace ABI meyasa zakamun karya...office fldinne bakason zuwa ...meyasa tun jiya baka fadamun ba
Girgiza kai yayi yace bahaka bane chitti ....kawai dai inaso kikula danine ...
"saboda haka zakayi missing important meeting... ABI am always with u kanada ko bakada lafiya zan kula dakai amma kabari mugama abubuwan dasuke gabanmu tukunna ....
Kintashi yayi seda takama hannunshi dakyar yamike yana rangaji dakarfi tasa hannayenta tafara turashi yana dariya seda takaishi bathroom tajanyo kofar sannan tadawo tafara gyara dakin kafin yafito tagama tana zaune tana jiransa
Yanafitowa cikin shigarsa ta suite baka yayi kyew matuka batare dayakalli inda takeba yanufi dressing mirror yafeshe jikinsa da turaruka tana zaune tana kallonsa har yagama sannan yajuyo yana kallonta damurmushi afuskansa yace how do I look ....
Gorgeous.... Tafada tana mikewa tsaye takaraso wirinsa tana gyara masa zaman rigar tace kahadu sosai angon aysha ....
tureta yayi daga gabansa yana murmushi yanufi hanyar fita yana fadin kiyita fadi har bakinki yabiki ...nigaba takaini ba baya ba ...kingama sekidaina jamun aji dankinsan bakekadai bace ....
daure fuska tayi tana buga kafa akasa kamar zatayi kuka shikuma yahau mata dariya ganin tanufosa aguje yasa yayi sairin fita daga dakin yana fadin kibiyomun da wayana da makullin mota
suna isa aka fara meeting din kuma sunyishi asa'a domin atake awurin suka magance matsalar dake tsakaninsu kuma suka kara kulla wata hulda atsakaninsu....cike dafarin ciki akatashi taro kowa nayaba karamcin da akamusu .....
Koda suka tashi daga aiki wurinsu Umma suka biya sunjima agidan sunafira har bayan ishsha sannan suka nufi gidan Momy itama suka gaidata tayi farinciki matuka ganin yanda komai yakoma yanda yake da
abotar AK da ahmad se abunda yakaru kowannensu nafarinciki da masoyiyarsa khadeeja tadage sosai dakaratu saboda ahmad yamata alkawarin tana gamawa zaibudemata asibiti takanta kuma dama burinta kenan
hankalin grany ya kwanta yanzu batada wata fargaba kasancewar tasan duk abunda yake faruwa kuma yanda taga AK da asma'u nazamansu cikin so dakauna abun namatukar birgeta .....
Sosai sunkara shakuwa dajuna suna bala'in son junansu soyayyarsu nalunkuwa azukatansu hartakai suna fahimtar abunda dan uwansu kebukata batare dayafurta hakanba ....sedai har wannan lokacin asma'u bata yarda wani abu yashiga tsakaninsu ba sedai tace wannan bashine lokacinda yadace ba tun yana mata magiya har yahakura saboda kasancewa kusa da ita hakan kadaima ya isheshi .... Batare dasanin kowa ba tamaidamasa dukiyarsa bayanda batayiba zata daina aiki amma yahanata
Abangaren aysha da iyayenta kuwa sunzage sunata shirin biki duk da bawani shiri suke ba kasancewar basuda kudi amma sanin cewa daga AK ya aureta sungama arziki hakan yasa basuwani damuba Aunty sadiya tadage se tsuma aysha ake da magunguna kala kala acewarta idan har tayi anfani dasu to bazai kara kula wata maceba aduniyarnan
Abangaren salim Sam yamanta dawata aysha arayuwarsa tunda yaji shiru AK bainemesa ba yasan komai yawuce dan haka ya kwantar dahankalinsa yacigaba da harkokinsa soyayyarsa yake zubawa son ransa dawata cousin dinsa wacce tajima tana sonsa yana wulakantata seda mahaifinsa yanuna Bacin ransa sannan yafara kulata Abu kamar wasa haryayi nisa asonta yanzu bayada wani burin dayawuce ya aureta tuni magabata suka shigo maganar bada bata lokaciba aka fara shirin biki
sedai abunda yabasa mamaki shine seda lokacin bikinsu yagabato aka kara dagashi kuma danisa bakusa ba dayayi magana akace bata kammala karatuba Wanda yasan basuyi haka da iyayanta ba bayanda ya iya dole yahakura dan bayajin zai iya rabuwa da ita ......
komai akasama lokaci to zaizo yanzu bikin AK da aysha yarage sati daya kacal fadin ciki baya boyuwa awurinsu se habaice habaice ake jefamasu asma'u grany ce kawai ke kulasu dan asma'u batada lokacinsu ....su aysha amarya ansha gyara se sheki take duk wata tsohuwar ajiyarsu takare wurin hidimar bikin da dakyar take iya kwatar kudi ahnnun AK daga tafara magana inyace dama yasan kudinsa takeso setayi shiru aranta kwa burinta yananan ba abunda yacanza dazaran ta auresa zata mallakesa da duk abunda yatara sannan takori kowa daga gidan tamallakama iyayenta shikuma tanemi yasaketa takoma wurin salim dinta danshine Wanda takema so nagaskiya ....
tsakanin bashir da Sarah kuwa soyayya mai karfi tashiga tsakaninsu sedai har wannan lokacin batabari yasan tana sonsa ba gudun kar abunda yafaru tsakaninta da ahmad yasake faruwa agareta .....shima kuma abngarensa yana tsoron idan yafurta mata yana sonta yarasa damar kasancewa tare da ita bayanda asma'u batayiba yafadaba amma yaki bawanda yasan dazancan soyayyarsu se grany da asma'u lokacinda tasanar da AK bakaramin farin ciki yayi ba nan take yaji sonta yakara lunkuwa azuciyarsa saboda irin gudummuwa dakuma cigaban datakawo a family dinsa ...she is the best...
Inna ladidi batason auren aysha da AK saboda tasan badan allah takesonsa ba kuma tasan cewa yana aurenta to tasu takare ganin abun dagaske ne yasa bashiri tanufi wurin asma'u bayan sungaisa tasanar da ita cewa aysha kudin AK takeso kome zaifaru kartayarda ya aureta tasan cewa dafari datazo gidan bata sonta kuma basuyi zaman dadiba amma atunaninta itama asma'u kudin AK tagani ta auresa sedaga baya tafahimci mace ce tagari kuma dazuciya daya take zaune dasu shiyasa tazo tagayamata gaskiyar halin aysha
Murmushi asma'u tayi datagama sauraran bayaninta cike da ladabi tace inna ...nasan zakiyi mamaki idan nacemaki nasan asalin wacece aysha sedai kuma nagode matuka dakika fahimceni kuma kikanemi dorani akan hanyar datadace ....kikuantar dahankalinki inna ba abunda zaifaru se abunda allah ya kaddara ....kudai cigaba datayamu da addu'a everything will be fine......
ganin rashin damuwa afiskar asma'u yasa itama hankalinta ya kwanta taci gaba dazuba ido ......
To kuma readers se ince kuci gaba dazuba ido da kunnuwa danjin yanda zata kasance awannan sarkakiyar Wanda sukeson halartar bikin aysha da AK se su tareni a page nagaba Wanda nake tunanin shine nakarshe ko kusada nakarshe insha allah
all tnx to u masoyan wannan littafi sannan inabaku hakurin rashin jina kuana biyu kumun uzuri kuma ina godiya kwarai da kulawar da kuke nunamun inayinku sosai sosai......
Special tnx to u my beloved friend zainab ado and amazing sis sa'ata , Aisha, khady , halimatu,asma'ul husna ,saulawerh and habiba fana , da duk sauran masoya da abokan arziki tnx for ur support....
Se munhadu a page nagaba cikin littafin domin kanwata ........!!!
[15/08, 18:05] Hassan Atk: ba'adau lokaciba AK yafito cikin shigar manyan kaya yayi kyau matuka yana sakkowa kan stairs kallo yakoma kansa kowa yasaki baki yana yaba kyan da allah yamasa nan take maroka suka hau rangada guda antys suka zagayeshi ana likamasa kudi wasu kuma nadaukansa photo
Aysha nadaga gefe azaune tana kallonsa jitake kamar taje tarungumesa saboda tsabar farinciki tanaji tafi kowace ya mace Sa'a datayi nasarar samun hadadde irin wannan amatsayin miji.....
Asma'u nakusan grany azaune tana magana awaya yayinda shikuma yakasa dauke idonsa akanta yanajin sonta nakaruwa azuciyarsa tana dago kai suka hada ido atare suka sakarma juna wani murmushin dasu kadai sukasan ma'anarsa .....
da kyar aka basa hanya Ahmad yaja hannunsa suka fita daidai kofa suka hadu da khadeeja dasarah zasu shigo cike dafarin ciki khadeeja takaraso wurinsu tana fadin wow tsarki yatabbata ga ubangijin daya halicci wannan gayan.....
dariya suka sa gaba daya banda AK da yadaure fuska yana wurga mata harara yace dama nemanki nake... idan kika kara buga mana kofa sena guntule yan yatsun ....
metamaka....Ahmad yafada yana kallon khadeeja ta zunbura baki tana kauda kai
"she always come at the wrong time....
Dariya suka sa gaba daya khadeeja tace kodai kune ba kwa abunku lokacinda yadace ba ....ko nataba zuwa da daddare nabuga muku kofa....takarashe maganar tana murguda baki hade da saitasu dawayarta tafara daukansu photo
tsaye sukayi suna kallonta har tagama daukansu taja hannun Sarah suka Shiga ciki sannan suma suka wuce AK nafadin gaskiya friend kanada aiki ....deeja ai setasama mutum hawanjini ....
Dariya Ahmad yayi yana juyowa yakalli khadeeja yace hawan jinin soyayya ba.... waima yaushe zaku mana aurene....
aysha nazaune da kawayanta azagaye da ita se mita suke mata wai bikinta kamar na yan kauye ba casu ba party ba dinner gaskiya tabadasu basu taba tunanin haka bikinta zaizo ba ....itadai batabi takansu ba dan daban abunda yadameta takashe kunne tana jira taji andaura aure wayarta nagefe sefaman ringing take amma ko kallo bata isheta ba dai cikin kawayanta ce tamiko mata wayar tana fadin aysha dan allah kidauki wayarnan tun safe ake kiranki ...koma waye wallahi baida zuciya da baifasa kiranba ....
tsaki taja tana karban wayar taga sunan salim cike datakaici takashe wayar gaba daya ta tura cikin jaka
Suna nan azaune suka fara juyo hayaniya natashi apalo har tashare daga baya dai dataji abun yayi yawa tafito dan ganin abunda ke faruwa kawayanta nabiye da ita har suka iso palon
Aunty sadiya ce atsaye tana faman zuba ruwan masifa se kunfar baki take anzagayeta ana bata hakuri
Grany nazaune tana kallonta Asma'u na tsaye agefenta taharde hannaye tana murmushi
Cike da mamaki aysha takaraso wurinta tana kwasar babbar rigarta cikin rawar murya tace Momy lafiya....meyafaru....
"Inafa lafiya aysha hau za'acima mutunci ...to munfi karfin wulakanci wallahi ...yau inda AK kotu ce zata rabamu ...ya'ta akuyace dazai mikata bada amincewarta ba ...ko ubanta bai is a yamata wannan cin fuskar ba bareshi ...shi asuwa...
Bata gama rufe bakiba uncle jamilu yashigo palon kamar anjefosa hularsa ahannu yana faman cije lebe idonsa yakada yayi ja kana ganinsa kasan yana cikin tashin hankali rai bace yawuce bangarensa batare dayakalli kowa nawajan ba ....
Dakallo suka bisa har yashige sannan aysha tajuyo tana kallon sadiya cikin rawar murya tace Momy dan allah kigayamun meyake faruwa ne ....AK yafasa aurena ko...shikenan zamcan aurena yasha ruwa ko... yanzu ba'a adaura auren ba kenan...
Kauda kai sadiya tayi tana karkada kafa tace andaura auren aysha sedai bashine ya aureki ba wani daban ya auramiki....
Dimmm aysha taji maganar akunnenta tamkar saukar guduma take jikinta yafara rawa cike da tashin hankali tace Momy wanifa kika ce wayeshi....akan wane dalili zai auramun wani batare dasanina ba ....
"Da salim aka daura miki aure dalilin kuma shinake sonji abakin wa'innan munafukan....takarashe maganar tana nuna grany da Asma'u
Hannu aysha tadora akai tana durkushewa kasa hade dasakin wani kuka mai cin rai take kallo yakoma kanta wasu na tausayinta wasu nagara da akayi haka ganin surutun yayi yawa sadiya taja hannunta suka nufi bangarensu
Suna Shiga tafada jikin uncle jamilu tana fashewa dawani kukan bai hanata ba tacigaba dakukanta danshi kanshi yana bukatar rarrashi seda tayi mai isarta tadago dajajayan idanuwanta tana kallonsa cikin sheshshekar kuka tace dady....everything is over now....my dreams ...my hopes....komai ya ruguje dady....narasa komai...bazan barshiba wallahi senasa zunzubar da hawaye kamar yadda sukasa nayi ...tunda har narasa abunda nakeso to suma dole ne surasa ...senayi ajalinsu....takarashe maganar tana yunkurin mikewa tsaye yayi saurin riko hannunta yazaunar da ita kusa dashi cikin sigar rarrashi yace dakata mana yar baba ....aishi yaki seda dabara ...nafahimci halin da kike ciki amma ai zafi baya kashe kuna ...yanzu kinatso kinuna kamar abun baidameki ba ....kinsan ba abunda yake kashe makiyanmu irin su kuntata mana kuma suganmu muna murmushi ....
"What do u mean dady....kana nufin namanta da abunda suka mun kenan ....shikenan sunci bulus kenan....
Murmushin karfin hali yayi yana cije lebe yace ba abunda nake nufi kenan ba nima kaina bazan yafe abunda yaronnan yamun ba ...seda nagama Tara manyan mutane nashaidamusu AK hausawee zai auri ya'ta bayan sun halarci daurin auren kawai nai sabanin haka....
Mutuncina yazube a idonsu ya kunyatani agaban abokanaina ...yacimun mutunci kuma ya ruguza mun burin danajima ina ginawa yamiki auren wulakanci ....kinaganin zan iya hakura na kyaleshi ....never...I won't spare him...sedai kinsan komai narayuwa idan kabi ahankali zakafi ganin daidai ...ai dasanyin safiya ake kama fara ahannu
Aunty sadiya dake gefe tana sharan kwalla tace wallahi nasan duk aikin matarsa ne da wannan tsohuwar kuma se sunyi nadamar abunda suka aikata yanzu tsakani da allah shikenan aysha tazama matar salim kenan ..yane daukan amarya fa suna kan hanya nidai nafadamusu garama sujuya dan kosunzo ba inda zataje ya'ta ai ba akuya bace ...
Saurin dago kai aysha tayi tana kallonta idonta pa kwalla cikin rawar murya tace Momy zanje...yazama dole naje dan nazama matarsa yanzu amma hakan nayanufin nahakura da abunda akamun ...tunda narasa AK to dolene kowama yarasashi ...wannan alkawarina ne
dayamma akazo daukan amarya kuka Anty sadiya take kamar ranta zaifita da kyar aka banbare aysha ahannunta uncle jamilu dai nadakinsa baifito ba har aka fita da ita tare darakiyar inna ameena se yayar aunty sadiya da kawayanta biyu
daga nesa tahango AK, Ahmad da
Asma'u atsaye suna kallonta cak ta tsaya tana kallonsu itama cike da bakin ciki datakaici idonta sunkada sunyi ja har suntafi sekuma takwace hannunta daga na aunty ameena tanufi inda suke tana share kwallar datazubo mata
Dap da AK ta tsaya tana kallonsa da murmushin mugunta afuskanta tace wow AK kayi kokari....aganinka kayi abun birgewa sedai bakasan cewa ...kakashe maciji ne bakasare kansa ba ...ina mai tabbatar maka dacewa sekayi nadamar abunda kamun...
Murmushi yayi yana kauda kai batare dayace komai ba Ahmad dake gefensa atsaye ya toshe baki yana fadin 🤭 yin shiru shine amasr datafi dacewa da mahaukaci....tana juyowa yayi saurin kauda kai yana daure fuska kamar bashi yayi maganar ba
Dawo dakallonta tayi kan Asma'u tana fadin ke kuma bakar kunama....kinfitar dani daga rayuwar mijinki sekizuba ruwa akasa kisha sedai har yanzu nice dariba saboda Wanda nakeso na aura ...ke kuma sekijira naki sakamon dan bazan taba yafemaki ba...sekinzubar da hawayan bakin ciki da nadama agaban idona Nagani....
Murmushi Asma'u tayi tana girgiza kai tace
Da kin Adana kalamanki maybe suyimaki anfani agidan mijinki ....idan ma kinafadan hakane dan ki tsoratani garama kiyi shiru dan ko agyalena ....nasan kinason salim shiyasa aka auramikishi abunda yakamata kinemi sani shine ..meyasa shiya aureki...wannan kuma ance waka abakin mai ita tafi dadi idan kinje wurinsa se kitambayesa ...kije ke ake jira allah yabada zaman lafiya....
ahmad yakarashe mata maganar dafadin ...dazuri'a tagari ...allah kauda idon makiya da mahassada ...yi nayi bari nabari dai shine zaman aure mazan yanzu hakuri ake dasu..kamusu biyayyar ma yaka kare bare kince zakiyi tsiya seyamaki dan banzan duka yadawo mana dake
Dariya suka sa gaba daya banda aysha da ranta inyayi dubune yabace hawayan datake dannewa tuni suka wankemata fuska murmushi Ahmad yayi yana kallonta yace miye abun kuka amarsu nasiha fah kawai namaki dan natabbata wa'inda yadace sumaki basu samu damar yimaki ba miye laifina dan na'ari bakinsu nacimasu albasa....
juyawa tayi aguje tabar wurin tana rera kukan bakin ciki da takaici tama rasa wani mataki zata dauka akansu dazata huce haushinta
Bayan antafi da amarya kowa ya watse gidan yayi shiru uncle jamilu nazaune apalonsa yajingina kansa da kujera idonsa alumshe yana rike da kwalban mineral ahannunsa yana sha yaji anturo kofa ahankali yadago kai yana kallon AK da Ahmad dake tsaye bakin kofa suna magana kasa kasa Ahmad nakokarin turo AK gaba shikuma yana dojewa suna dago suna hada ido dashi suka natsu wuri guda suna sunkuy dakai ....
Yajima ahaka yana kallonsu kafin da kyar yayi controlling kansa yana kakkalo murmushi yace a'ahh yakuma kuka tsaya daga can sekace wasu baki Ku karaso mana ...
Jiki asanyaye suka karaso wurinsa daga kasa suka zauna bayan sun gaisa AK yadago kai yakallesa sannan yamaida Kansas kasa yana fadin
Uncle dama zuwa nayi nabaka hakuri akan abunda yafaru nasan ban kyautaba amma hakan shine yafi dacewa....aysha da salim suna kaunar junansu kokadan bani takesoba shiyasa naga yafi dacewa da ta'aureshi ...kuskurena daya rashin sanardakai danayi tunda auri amma nayi hakan ne dan nasan idan har kasani to bazakabari nayanke wannan hukuncinba ...kayi hakuri uncle ban aurar da aysha ba seda nayi bincike mai zurfi tundaga kan salim har iyayansa da abokanansa kuma bayada wata matsala abunda yashiga tsakaninsu ma kaddara ce dan bahalinsa bane ....kuma yana kaunarta iyayansa ma sunyi na'am dazancan aurensu insha allahu zatayi rayuwar farin ciki agidansa da albarkarku kawai take bukata ...nikuma kayi hakuri kayafemun ....
Shiru yayi yana kallonsu fuska adaure yanaji kamar yarufesu da duka jin baitankasu ba Ahmad yadago kai ahankali yana murmushin yake yace uncle amana hakuri kasan abun harda yarinta....suna hada ido yawatsamai wata mahaukaciyar harara bashiri yayi kasa da kai yana mamakin bakar zuciya irin ta uncle jamilu
Sunjima ahaka bawanda yace kala secan jamilu yasaki wata nannauyar ajiyar zuciyar daseda tasa suka dago kai atare suna kallonsa yasakar musu murmushi yace bakomai AK nidama baka batamun raiba ...nashiga damuwa ne saboda rashin sanin halin da aysha zata Shiga agidan salim amma yanzu danaji bayaninka na gamsu kuma hankalina ya kuanta dama can aysha kanwarka ce kanada damar dazaka zabamata mijin aure kuma dole ta amince koda bataso bari kuma Wanda dama can saurayinta ne ...fatana dai allah yabasu zaman lafiya ....
Ameen ....suka amsa atare suna mikewa suka fita daga Palin cikin damamakin tarbar dasuka samu daga garesa
suna fita yamike tsaye afusace yabuga kwalbar hannunsa dabango yana huci yayi wurgi daragowar nahannunsa yana dafe kai yace ina bazai yiwu ba....bazan taba yafemaka ba AK ...bazan barka baaaaaa
Suna fita bangaren grany suka nufa acan suka isko Asma'u zaune suna fira
Kusan grany Ahmad yazauna shikuma AK yazauna kusada da Asma'u ahankali yakai hannunsa bayan qugunta tayi saurin bige masa hannu tana hararansa grany tayi murmushi tana girgiza kai tace ya kukayi da kawun naku ne nasan kunsha masifa ko ....
sabanin haka.....AK yafada yana gyara zama yashiga basu labarin yanda sukayi dashi cike da mamaki Asma'u tace what....abunda mamaki anya kwa ba abunda yake boyewa uncle nefa....
Kafin AK yayi magana Ahmad yarigasa dafadin allah yakaiki maka ko akan jakine....nima nayi wannan tunanin ....uncle ba irin mutanen da ake game yanayinsu tafuska bane ....sema kinga kallon danaga yana jefama AK daganan natabbatar da zargina akansa
Tabe baki grany tayi tana mikewa tsaye tace allah dai yafeshi kuma addu'ata bazata fadin kasa ba dayardar allah yanzu dai naga auran wannan ja'irar saura na khadeeja da Sarah kuma ....takarashe maganar tana nufar dakinta
Dakallo suka bita Ahmad nafadin shima kinkusa ganinsa grany kwanan nan dayardar allah
Dariya suka samasa yadaure fuska yana fadin nifa dagaske nake idan Baku shirya ba to mu munshirya koso kike semunfito maku da asalin rashin kunyarmu kunganine ....
dariya Asma'u tayi tana fadin maida wukar surikina ai tunda mungama dawannan matsalar komai yazo karshe insha allah amma ni gaskiya haryanzu magamar uncle jamilu ta tsayamun arai
haka daisukaci gaba da firansu sunkafe akan uncle jamilu baihakura ba shikuma AK yadage akan bawani abu duk dashima aransa yana zargin wani Abu amma bayaso asma'u tasake Shiga wata damuwar shiyasa yanuna rashin yarda dazancan su sedai yayi niyyar saka ido sosai akan duk wani motsin uncle jamilu idan kuma zarginsu yakasance gaskiya to bayajin zai iya yafemasa dole yadau mummunan mataki akansa
[15/08, 18:05] Hassan Atk: 👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
2⃣1⃣5⃣
akuana atashi bawuya wurin allah yau takasance asabar kuma itace ranar daurin auren AK da aysha gidan yacika makil da yan uwa anata hidimar biki amarya taci ado cikin wata doguwar riga tayi kyew matuka ga kawayanta azagaye da ita suna yaba irin kyan datayi .....
khadeeja tazo shiga gidan taci karo da Sarah zasu fita itada bashir cike dafarin ciki Sarah tarungumota tana murmushi tace deeja se yanzu zakizo dafa gidanku zamuje ....
tureta khadeeja tayi tana zunbura baki tace dallah can matsa tundazu fa kenake jira kinbarni acan kinzo kina soyewarki anan ....ina ammah ne itama ina kiran wayarta akashe ....
kallon bashir Sarah tayi sannan takalli khadeeja tace nikaina nemansu nake dazu dasafe naje Yaya yakoroni wai tana bacci kuma kinga yanzu bashir yake gayamun antaru amasallaci shi ake jira ...
dariya bashir yayi yana Sosa kai yace nidai nakosa adaura aurennan naga dramar daza'akwasa mudai zamusha kallo ...
dariya sukasa gaba daya khadeeja taja hannun Sarah suka Shiga ciki shikuma bashir yanufi wurin Ahmad dake dago mai hannu daga nesa ....
AK nazaune abakin gado yana faman rubutu ajikin wata takarda se murmushi yake kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki yayi fari yakara kyew sekara zama yaro yake kamar baya kara shekaru
jin anturo kofar yayi saurin kifa takardar akan ciyarsa yana kallon Asma'u datashifo dakin cikin shirinta tsab tayi kyew bakadan ba tasha sarka yan kunne da warwaro ga light make up afuskanta daya kara fito da asalin kyanta dinkin doguwar riga ne ajikinta yakamata tsab kamar kadauketa kagudu
tana murmushi takaraso wurinsa tana fadin wai mekake jira har yanzu baka shirya ba kaifa akejira ....takarashe maganar tana kai hannu kan takardar yayi saurin boyeta abayansa yana fadin ...yanzu zan shirya kenake jira kihadamun ruwan wanka ...
damamaki take kallonsa tace meyi atakardar ...dabakason ingani ...
nothing .... yafada yana kokarin mikewa tsaye datakardar ahannunsa tayi saurin sa hannayanta biyu ta turasa baya yazauna sannan tazauna akan cinyoyinsa tana zagayo da hannayanta bayan wuyansa cikin murya mai kaman rada tace zaka kabani takardar cikin ruwan sanyi kose nasa karfina nakwata ....
dariya yayi yana kara jimke takardar ahannunsa yazagayo da dayan hannunsa a qugunta yana kafeta da ido yace dazaki sa karfinki ki kuata zanfi kowa farin ciki dan nine dariba coz ur touch was adorable.....
saurin mikewa tayi tana dariya tanufi bayi dan hada masa ruwan wanka har tagama tafito yana zaune inda tabarsa datakardar ahannunsa yana juyawa
janyo hannunta yayi yazaunar da ita kusa dashi yana mikamata takardar yace
chitti duba kiga sunayan ya'yanmu nake fitarwa daga cikin namu ....nasamu suna biyu ABISMA da Maubid ....yakiga idea na ...
kallon talardar tayi tana murmushi tace ABI...suna yana bukatar ma'ana ....miye kuma abisma....inama laifin ABAS ...takarashe maganar tana mikewa tsaye tare kamo hannunsa tamikar dashi
janyota yayi jikinsa yana murmushi yace ohhhh....sunan ne kawai baimiki ba amma kinshirya samun baby kenan....
"stop it ABI kaje kayi wanka lokaci yana tafiya karka ruguza mana shiri
kokarin kwace kanta take amma takasa saboda riko yamata bana wasa ba seda tagaji dan kanta tahakura tayi lamo akirjinsa tana maida nunfashi cikin sassanyar murya tace ABI kana ganin bawata matsala nidai tsoro nakeji .....
hannu yasa yadago dafuskarta yana kallon cikin idanuwanta damurmushi afuskarsa yace don't u trust me....
"I trust u but....
yatsansa yadora akan labbanta yana girgiza kai yace to banason jin komai idan har kina tare dani banada sauran wata fargaba nasan komai yakusan zuwa karshe dayardar allah ......
murmushi tayi tana maida kanta kan kirjinsa tace ina sonka ABI....
"nima ina sonki chitti ....
karan buga kofa ne yakatsemasu nishadinsu atare suka kalli kofar kafin yayi magana khadeeja tace wai ance ana kiran Romeo....
dafe goshi AK yayi yana buga kafa dakasa kamar zaiyi kuka yace ohh ni yazanyi da deeja ne ...bazata taba barinmu muji dadi ba
dariya Asma'u tayi tanufi kofar tana fadin aurar da ita kawai zakayi muhuta .......
[15/08, 18:05] Hassan Atk: Bayan akai aysha dakinta kowa yawatse aka barta ita kadai tana zaune bakin gado har wanann lokacin kuka take duk da tana jiyo motsin mutane daga waje amma bata damu datasan kosuwaye ba
(gidan mai kyau bangare biyu daya Asama daya kuma akasa se Babban palon kasa da kitchen da dining area bangarenta ne asama Palo daya se dakuna biyu da dan karamin kitchen dinta ko ina yasha ado ankayatashi dakaya na alfarma gadonta kawai abun kallo ne tana gaminsa tasan daga company su AK yake harda kujerun palon da komai nabangarenta AK ne yayi )
tana nan zaune har dare yafarayi can bayan sallar isha'i taji anturo kofar ahankali kanta akasa batadago ba natsawon lokaci jin ba alamar motsin mutum yasa tadago kai ahankali tana kallon salim dake tsaye abakin kofar yana kallonta fuska amurtuke tamkar bai taba dariya ba itama daure fuskar tayi tana kauda kai aranta tace duk abunda yakoroka to atsaye ya iskoni dan kome kake ji nafika jinsa ...nakama nafila ne akan nawa
takowa yafarayi cikin dakin har ya iso dap da ita ya tsaya fuska ahade yace urban was yahanaki daukan kirana ...meyasa kika amince da aurena ...wato kinyi kwantai awajan AK asirinki ya Tonu shine ni aka jangwalamun ke ko...
cike da mamaki tadago tana kallonsa fuska adaure tace wane kalan shirmene wanann salim...ni kake gayawa haka...ko shayeshayan dakasabayi ne kaje yauma kayi adaren aurenka ....
Bata karasa maganar ba taji saukan lafiyayyan mari atsorace tadafe kuncinta tana dirowa daga kan gadon tace yau nikamara salim ...adaren farkona zaka dauki hannu kamareni...how dare you ...
afusace yadamko kafadunta yanakafeta da manyan idamuwansa cikin kakkausar murya yace kigode allah kafin kizo na gidan nahuce abunda kamun amma dani kaina bansan iya abunda zammiki ba ....bansan meyasa kika amince da aurenaba amma kisani ...kinyi Babban kuskure aysha... idan ma kina tunanin ina sonki ne then u are mistaken...salim din dakika sani ada bashine nayanzu ba idan nace inajin sonki azuciyata nayi karya....
Saurin dago kai tayi tana kallonsa da jajayan idanuwanta dake zubar da kwalla mamaki datakaici ne bayyane afuskarta bakinta narawa tanaso tayi magana amma takasa furta komai
Gyada kai yayi yanaci gaba dafadin yes...bana kaunarki aysha saboda tuni nasamu wacce tamaye mun gurbinki ....kuma ina mai farin cikin sanar dake cewa tare aka dauramuku aure dani ...yanzu haka tana cikin gidannan amatsayin matata kuma abar sona...yakarashe maganar yanasake mata kafaunta hade da nunata da yatsa yace uma bari namiki kashedi ...idan har kikayi kokarin nuna mana bakin halinki anan to wallahi senamiki abunda zaki mutu kina nadamar Sanina arayuwarki ....yana kainan yajuya afusace yanufi hanyar fita haryakai kofa yaja yatsaya batare daya juyo yakalletaba yace idan kingama kukan asararki sekifito munajiranki kuma idan kika batamana lokaci zanzo dakaina nafito dake hakan kuma bazai miki dadin ba kinfi kowa sanina....
tsaye take kamar gunki tana kallonsa hawaye wani nabin wani haryanzu ganin abun take kamar amafarki yana fita ta durkushe awurin tana sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya sedatayi mai isarta sannan tamike zunbur tawuce bayi tawanko fuskarta tasauka kasa tana cigaba da share kwallar dake zarya akuncinta
zaune ta iskosu kan 3sitter tundaga nesa takafe amaryar da ido bayarinya bace zasuzo sa'anni kota girmi aysha dakadan ba laifi ita kyakkyawace sedai dagani bakaramar wayayya bace dan ko irin yar kunyar nan ta amare babu tazage se zuba shagwaba take yana biyemata suna ganinta suka daure fuska itama daure fuskar tayi tanemi wuri daga gefe tazauna batare datasake kallon inda suke ba
Tajima dazama kafin salim yayi gyaran murya yafara da addu'a dasauran bayanin da kowane mai gidan keyi arana irin wannan sedai ga dukkan alamu dayar amaryar tasa batasan matsalar dake tsakaninsa da aysha ba dan ko abayaninsabai bari tafuskanci wani Abu ba
Juyowayayi yana kallonta cikin sassanyar murya yace hafsat kece uwargida ko banza kingirmi aysha ...kidauketa matsayin kanwarki ...yar uwarki kuma kawarki ...kikama girmanki seta girmamaki ...ke yar uwatace tajini kuma nasan kinasona kamar yadda nakesonki dafatan zaku hada kanku kubani damar tafiyar dagidana yanda yakamata ....bawacce tafi wata acikinku kuduka matana ne kuma ina sonku zaman aurene yakawoku nan bafilin gasa ba dan haka seku natsu kuyi abunda zanyi alfahari daku ...bazan dauki shashanci agidana ba duk wacce tayi laifi to zan hukuntata daidai da laifinta ....
Juyowa yayi yana kallon aysha yacigaba dafadin ke kuma aysha kece Karama kibata girmanta kuzauna lafiya ..banaso naji wasu kananun maganganu natashi atsakaninku ...nasan zaman tare dole wata rana asamu sabani kafin abun yayi girma kusanar dani kar kusake injiyo labarin matsalarku daga waje niyadace Nafi kowa sanin halin da matana suke ciki ...kudaukeni amatsayin abokinku kuma abokin shawararku ....nima zanyi iya bakin kokarina wajan ganin nayi adalci atsakaninku ....zancan girki kuma duk ranar girki dayarku inaso dayar tafito tayata wasu ayyukan komai kuyishi tare danbana bukatar yar aiki agidana sannan idan angama zamu zauna anan muci gaba daya ...idan har kukayi anfani da abunda nafada to insha allahu zamu samu zaman lafiya da fahimtar juna atsakaninmu ...inafata kunfahimceni....
Shiru aysha tayi kanta akasa batace komaiba Hafsat tagyara zama tana kashe murya tace munfahimceka dear kuma insha allahu zamu kiyaye allah yashigemana gaba ...
Murmushi yayi cike dajin dadin furucinta yace yayi kyew haka ake so yanzu se zancan girki kwana nawa nawa kuke so arikayi
dariya hafsat tayi tace gaskiya ni idan nazaba to zanyi sonkai nabarma aysha tayanke mana ....
atare suka juyo suna kallon aysha dasam hankalinta baya Kansu seda salim yakira sunanta sannan tadago ahankali tana kallonsu se alokacin Hafsat taga fuskarta nan take taji jikinta yayi sanyi dan aysha tafita kyau nesa ba kusaba sedai hakan bazai da tayi masa aguywa ba zatayi anfani da tata kwarewar wajan karkato dahankalin mijinsu yadawo kanta
Cikin muryan datasha kuka aysha tace ni....banada...wani zabi...duk abunda kuka yanke yayi
Kamo hannunsa hafsat tayi tana murmushi tace kaga dear mu bamusaniba kawai kayanke mana ...
murmushi yayi yana shafa kai yace OK...bari mugani...kwana daya daya yayi ko...
zunbura baki tayi cikin muryan shagwaba tace kai dear kuana daya gaskiya ba baiyiba ina laifin biyu biyu ma ....
Dariya yayi yana Jan kumatunta yace dama gwadaki nake dakince bakisani ba yanzu bagashi kinfada ba
Juyowa Hafsat tayi tana kallon aysha cikin sigar tsokana tace amarsu kinji abunda mijinki yace ko wai kuana biyu hakan yamiki
mikewa tsaye aysha tayi tana fadin yayi ...nizanje inkwanta seda safenku ....
Damamaki hafast tace ahh yakuma zakitafi bamuci abinci ba
"Kuci kawai nakoshi....takarashe maganar tana hayewa kan stairs
dakallo suka bita har tahaura sama sanann Hafsat tajuyo tana kallon slim tace dear kamar akwai abunda yake damunta ko
Ajiyar zuciya ya sauke yana janyo ledar dake gabansa yace yunwa nakeji yanzu dai muci abinci dasafe mayi magna
aysha nashiga daki tazube abakin kofa tana fashewa dakuka kamar ranta zaifita tajima ahaka kafin tamike xunbur tadauko wayarta takira numban uncle jamilu bugu biyu yadaga kafin yayi magana yajuyo sautin kukanta natashi hankali tashe yamike tsaye yana tambayarta meyafaru
Tanaso tayi magana amma kuka yaci karfinta se fadin take dady zan mutu bazan iya zama anan ba kazo kadaukeni dan allah .....
Duk yanda yaso tanatsu tamai bayani takasa karshema kashe wayar tayi gaba daya tafada kan gado tana cigaba dakukanta
Hankali tashe yafara saga a marwa apalo yana kiran wayarta akashe jiyake kamar yasa ihu aduniya bawanda yatsana yanzu irin AK da Asma'u yasha alwashin se kuntata musu koda kwa zairasa ransa ne seyarabasu dafarin cikinsu .....
AK da Asma'u nazaune apalo suna kallo tadora kafafuwanta kan cinyarsa yana daddana mata suna firansu gwanin sha'awa
Ahankali yakai hannunsa kan mararta yana fadin ya ciwon mara
murmushi tayi tadora hannunta Kannasa tace dasauki yadaina mun
"Gaskiya abunnan yamun shigar sauri yanzu senakara hakurin kuana biyar ....
Duka takaimasa dakafarta aciki tana fadin shiru dallah ...kayi hakurin tsawon lokaci kuana biyar ne zaigagareka ....nidai bawannan yazancan bikinsu ahmad ne
dariya yayi yana Sosa inda tadakeshi yace bikinsu Ahmad kawai harda namu ai nagayamiki komai tare za'ayi shiyasa nace zamuyi komai cikin kuana biyar kinga kafin lokacin wannan maigadin naki yatafi ...se insamu damar kashe boss da zukekiyar amaryata
Pilo tadauko tashiga dukansa yana karewa dahannu suna dariya har tagaji dankanta tafada jikinsa sukaci gaba dafiransu har bacci yadaukesu ahaka....tana kwance akan kirjinsa yarungumota daduka hannayansa biyu suna sauke nunfashinsu atare kana ganinsu kaga asalin masoya
da dadare kafin salim ya kuanta seda yazo yaduba aysha tana bacci ahankali yakaraso bakin gadon yana kallon yanda take faman sauke nunfashi dagani kasan taci kuka bakadan ba durkusawa yayi saitin kanta yana cigaba da kallon kyakkyawar fuskarta har yanzu yana son aysha sedai yazama dole yamata haka dan gudun kartamasa abunda tayi niyyar yima AK duk adacewa yasan dagaske take sonsa amma ance idan kaga gemun dan uwanka Yakama dawuta seka yayyafama naka ruwan sanyi
Ahankali yakai dan yatsansa yashafo hawayen dake makale agefen idonta yajima awurin yana kallonta kafin yamike yagayara mata kuanciyarta hade darufamata bargo sannan yafita bayan yakashe mata wutar dakin
Washe gari dasafe Sarah nazaune apalon masa bashir yazo kusa da ita yazauna bayan sungaisa tafahimci yanason magana da ita ne cikin sassanyar murya tace yadai bashir kamar akwai abunda kakeson gayamun ko
dago dakai yayi yana kallonta cikin rawar murya yace eh ...wato Sarah yakamata ace munsan inda muka sa gaba ...kingafa kullum kara girma muke lokaci tafiya yake ...nagaji da ganinmu ahaka...wato ina nufin yakamata ace kinsan matsayinki awurina ...akwai abunda najima ina boyewa azuciyata wanda naga yakamata ace yanzu kinsan halin danake ciki .....
Farin ciki ne yalullubeta gaba daya ta tattara hankalinta duk tafahimci inda zancansa yadosa amma bata nuna hakan ba saboda tanaso taji wannan Kalmar daga bakinsa wannan ranar zata kasance dai cikin ranakun dabazata taba mantawa dasuba arayuwarta
Jin yayi shiru yasa takallesa damamaki tace Yakuma kayi shiru bashir kafadamun miye wanann dakake boyewa ....
Kauda kai yayi yana cije lebe aransa yace idiot tafasan menake nufi amma takeso tawahalar dani ...yasan tana sonsa amma yarasa dalilindayasa yake shakkar furta mata yana sonta zuciyara se bugawa take dakarfi ita kwa takafesa da ido ko kiftawa batayi sunyi nisa cikin wani yanayi basuma San lokacinda AK da Asma'u sukazo Kansu sukatsaya ba suna kallonsu
Dakyar yatattaro nutsuwara cikin wata iriyar murya yakira sunanta sarah....!!!
seda taji gabanta yafadi ahankali tadago kai tana fadin na'am suna had a ido tayi saurin sunkuy dakai masa tana wasa dazoben yatsarta
Ajiyar xuciya yasauke sannan yafara magana kamar haka ....
Sarah...ban gayamaki abunda keraina bane saboda awaccan lokacin Sam bana gabanki...am just a friend to u...najima ina jin wani yanayi agame dake sedai ayarintata nadauka shakuwace da soyayya irin ta yanuwantaka ...seda girma yafara zomun naga abun karuwa yake baya raguwa ... banada wani buri daywuce naganki atare dani ...farin cikinki kawai nakeson gani koda hakan nanufin bakinciki awajena idan narufe idanuwa na kenake gani ...kullun kece atunanina ...ko bacci nake kece amafarkina ...daga lokacin natabbatar cewa nayi nisa asonki....sedai kash awannan lokacin nafahimci zuciyarki takamu dason wanina.... Sarah tsayawa baki labarin halin danashuga awanccan lokacin bata lokaci ne ....nayi kokarin cire sonki azuciyata amma abun yacutura Sam nakasa controlling kaina akanki duk lokacinda kika matso kusa dani nunfashina nakusan daukewa ... zuciyata tafara bugawa dakarfi ...inason fito da abunda kecikinta amma bakina seyakasa furta koda kalma dayace fatana kawai dazaki kalli kwayar idona awannan lokacin dakinhangi tsantsar son danake maki ....bayan nagama yankewa kinmun nisa arayuwata kwatsam allah yadawomun dake daga lokacin nayi alkawarin bazan kara yin sake ko kubucemunba ...nayanke shawar gayamaki halin danake ciki koda kwa amsarki bazata faranta raina ba ....sarah I love you with all my heart ...body...and soul kuma zancigaba dasonki har bayan raina ...dama daya zaki bani zan kasance abokin rayuwarki nahar abada....
wasu yan siraran hawayan farincikine suka gangaro akan kuncinta cikin muryan kuka tace bashir meyasa kabata lokaci kafin kasanar dani abunda najima inason ji daga gareka najima dafara Sonka bashir bangayamaka bane saboda...ina tsoron abunda yafaru dani abaya yasake faruwa dani akanka ...bazan iya jure hakan ba bashir saboda banajin zan iya cigaba darayuwa batare dakaiba ....ina sonka bashir ...inamaka sonda baki bazai iya furtashi ba I love you so so so much bashir.....
tapin dasukaji anayine yadawo dasu hayyacinsu atare suka dago cike da mamaki suna kallon AK da Asma'u dake tsaye suna faman tapa musu suna dariya kunyace takama sarah tayi kasa dakai tana murmushi bashir kwa ko ajikinsa aguje ya karasa wurin AK ya rungumosa dakarfi yana jijjigashi yace yaya kaji sarah tace tana sona ...tana sona Yaya...oh am so lucky ....
Dariya AK yayi cike dafarin ciki yace kaga komai yazo adaidai tunda kun daidaita kanku se ahada bikinku danasu Ahmad kawai ayisa gaba daya ....
Kara rungumosa bashir yayi yana fadin ohh sweet kill meoooo ..wallahi Yaya munshirya kawai ayi ai munjima dafahimtar juna kuma ni ashirye nake alqur'an koyauma adaura ....
Duka Asma'u takaimasa dajakar hannunta tana fadin kai waiku meyasa bakwada kunyane ko amazan ma gaskiya kudin nadabanne ....
Dariya suka samata taja hannun sarah suka haura sama sukuma suka nufi wurin Ahmad da fara shirye shirye
Uncle jamilu dake tsaye daga Mesa yana kallonsu idonsa yakada yayi ja jikinsa har rawa yake ga wata zufa datawankemasa goshi se cije lebe yana huci aransa yana fadin yazama dole nadauki mataki akanku danbazaku sakani cikin bakin cikiba kuzo kuna farinciki bazan iya jure ganinku haka ba dolene kuma kudandana bakincikin dakuka sakamu nida ya'ta
[19/08, 06:18] Hassan Atk: Har zai juya tafito daga bayi tana kwasar duguwar wedding gown dinta dake Jan kasa .....
tsaye yayi daga bakin kofa yaharde hannaye akirji yana kallonta da murmushi afuskarsa kokadan batasan yana tsaye ba har takoma bakin gadon tana shirin zama tagansa atsaye suna hada ido tasakar masa wani lallausan murmushi dayaji gaba daya tatafi da hankalinsa saboda baitaba ganin tayi kyau irin haka ba kafeta yayi da lumsassun idanuwansa
yanayin kallon dayake mata yasa tayi saurin sadda kanta kasa cikin sassanyar murya tace yanda kakosa wannan ranan tazo bantaba tunanin zaka bata lokaci haka ba harnafara tunanin kiranka awaya ....
dakyar ya iya tattaro kuzarinsa yakarasa cikin dakin yana fadin chitti kowace amarya ana iskota zaune kan gado amma ke ko irin dan lullubin nanma na amare babu....
Zunbura baki tayi tana nufar dressing mirror tace to mutum yanajin fitsari bazaiyiba ....kuma ma aini ba amarya bace
Rungumota yayi tabaya yana shakar kanshin jikinta hade da lumshe ido yace miye banbancinki da amaren ....muma fa seyau zamu fara rayuwar aurenmu ko kinmanta .....
Juyowa tayi tana fuskantarsa da murmushi afuskarta tace to ina tsarabar amarcina ......
Ware hannayensa yayi alamar babu nantake tahade fuska tana turesa daga gabanta tace nikuma indai ba amun irin nakowace amarya ba to sedai kowa yakuana abangarensa dan bazancan amarci......
bata karasaba yayi saurin Shiga gabanta yana fadin dakata mana chitti ....wasafa nake maki nazo dashi yana Palo muje innuna miki ....
dariya tayi tana kama hannunshi suka nufi Palo seda suka biyu da plate da glass cups sannan suka dawo dakin ....
Sallah suka farayi suka mika godiyarsu ga ubangiji da yakawosu wannan lokacin sannan suka zauna anan kasa kamar koyaushe suna cin abinci suna firarsu gwanin sha'awa ...
dadin nama yakaimata karo tace ABI yakamata ace nacanja maka suna ....
Dariya yayi yace da mai nama zaki kirani kome....
"dagaske fa nake kaga kowa yana kiran mijinshi dasuna mai dadi nasoyayya nima zan fara kiranka da sweetheart....
Girgiza kai yayi yana yamutsa fuska yace banason sunan....
"To darling....
"Gara ma nafarkon....
"To yagaka Mine ...nasan tabbas wannan zai maka dadi .....tayi maganar tana washe baki
Mikewa tsaye yayi yanufi bathroom yana fadin am yours amma sunan baimun ba .....
Bin bayansa tayi sukayi brush din atare tanaci gaba dazano mai sunaye amma kowanne seyace badadi har tagaji dan kanta tayi shiru sedai tana tsaye akansa Sam taki yarda tazauna ....
mikewa yayi daga zaunan dayake yana riko hannayanta yace OK fine....naji kizabamun kowane irin sunane ko badadi zan amsa kinji....
dariya tayi tana kallon yanda yalangabe kai tace wasa nakemaka ABI ....you are always my ABI kuma zakaci gaba dazama ahaka har karshen rayuwata ....
Murmushi yayi yana janyota jikinsa suka rungume juna cikin rada yafurta ina sonki chitti ....
Itama cikin rada tafurta nima ina sonka ABI ....
Ahankali yadago dakanta yana kallon kyakkyawar fuskarta idonta alumshe yana kokarin kissing dinta tayi saurin dakatar dashi tana dora tafin hannunta akan lips dinsa
Saurin bude lumsassun idanuwansa yayi yana shirin magana yaji bakinta anasa cike damamaki yazaro ido yana janyo jikinsa daga nata yakafeta da ido yamakasa magana ....
Wani malalacin murmushi tayi tana cije lebenta nakasa tajanyo wuyan rigarsa yazo dap da ita harsuna musayar nunfashi cikin wani irin salo tace kana mamaki ne ....ko kamanta nataba gayamaka idan lokaci yazo zammaka abunda kwakwalwarka zata kasa dauka ....that time has come handsome....
kallonta yake kamar baitaba ganinta ba cike dafarin ciki yasaki yar surprise dariya yana sa hannayansa yaturata baya tafadi reran akan tankamemen gadonsu ....
cwani fitinannan kallo yake binta dashi yana cije lebensa nakasa yacire rigarsa tasama yayi wurgi da ita tsakiyar dakin sannan yabita kan gadon yana rungumota jikinsa dakarfi sukasa dariya mai nuna tsantsar farin cikin dasuke ciki....
wannan Daren yakasance daraen alkhairi mai kunshe da dunbin farin ciki ga duk family dinsu musamman wa'innan ma'auratan dasukafi kowa farin ciki awannan daren saboda shine mafarin rayuwar aurensu mai kunshe da so dakaunar junansu ....
Se mice allah yabasu zaman lafiya da albarkar aure......
Kamar yadda suka tsara sati daya bayan bikinsu suka wuce honeymoon dinsu inda suka zaga kasashe da dama kuma suka samu isashshen lokacin kebewa da junansu inda alakarsu takara karfi soyayya kuma tasamu gindin zama azukatansu....
Daga karshe suka biya masa mai tsarki dan sauke farali inda kowannensu yazage yanemi bukatunsa wurin ubangiji....
Kashin hamsin na addu'ar AK to bai wuce allah yabar mishi asma'unsa ba dakuma haihuwa masu albarka ....
Bayan wani lokaci.....
Haka rayuwa taci gaba datafiya tare dalokaci arzikin AK da Ahmad sedai ace alhmdlillah dan habaka yake bakadan ba sukuma sun dage wajan taimaka ma bayin allah Abba ma tuni AK yakara masa jari kuma allah ya albarkaci kasuwancinsa inda yanzu sedai ya taimakama wani
Hankalin kowa yakwanta saboda
kowannensu na zaune lafiya da abokin zamansa ...
Aysha ce kawai take dan fuskantar matsala daga wurin kishiyarta wato hafsat amma soyayyar da salim kenuna mata yasa abunda yake zuwa mata da sauki ....
Hafsat tasami karuwar da namiji har wannan lokacin aysha kobatan wata bata taba yiba hakan kuma nadaga mata hankali bakadan ba saboda kullun bata rabuwa da habaice habaice daga bakin Hafsat dan tuni tasan dazancan cikin da salim yataba yimata dakuma dalilin zubewarsa maganar duniya ance bata boyuwa ... sedai bawanda yasan halin datake ciki banda Asma'u da AK dan tadaukesu wasu aminanta dabata iya boyemasu sirrinta kuma sukan taimaka mata da shawarwari masu kuantar dahankali ....
Sarah da bashir ma sunsamu karuwar ya mace inda taci sunan Asma'u suna kiranta Malika ....
Khadeeja ma tana dauke da juna biyu haihuwa yau ko gobe zo kaga farin ciki wurin Ahmad ai ko tsinke baya bari tana dauka matukar yana nan ko fita ma bayayi da kyar AK kejansa sufita shima baya jimawa zaidawo yabarosa saboda kokadan hankalinsa baya kwanciya idan baya kusa da ita....
Karatunta hanata yayi dole tadakatar idan tahaihu setaci gaba wani lokacin setasamasa kuka yake barinta tafita ....
Wata safiya ta tashi da nakuda hankali tashe suka nufi asibiti da ita
rsuna isa aka Shiga da ita dakin haihuwa seda aka rirrike Ahmad dan kokarin bin bayanta yake dakyar AK ya lallabashi suka zauna amma yaki barin kofar dakin kuka yake kamar karamin yaro saboda tausayin halin da flying bird dinsa keciki ....
Ba'adau lokaciba su grany da Momy suka iso asibitin lokacin su Umma da inna suna masa mai tsarki basuda labarin halin da ake ciki ...
AK narike da hannun Ahmad yana fadin friend ka kawnatar da hankalinka dayardar allah ba abunda zaisameta lafiya zata haihu kaji....
sarah dake gefe tana sharan kwalla tace yihakuri yaya she will be fine ....
Haka sukaci gaba da kuantar masa dahankali itadai Asma'u tana daga gefe azaune ita tamakasa magana danji take gaba daya tafisu damuwa.....
suna nan zaune sukaji takwala ihu tana kiran Taaaaarzaaaaan ....
Afirgice Ahmad yamike tsaye yana kokarin Sakai cikin dakin AK yayi saurin riko hannunsa juyowa yayi yarungume AK dakarfi cikin muryan kuka yace kanaji ko friend....wahala takesha friend kataimakeni kabarni naje wurinta ...idan wani Abu yasameta bazan yafema kainaba ....
mikewa tsaye grany tayi tana fadin ahmadi kanatsu mana ....kowace macefa haka tayi nakudar nan masu ya'ya goma sha biyu fa suce mekenan ....
Janyo jikinsa yayi daga na AK yana share kwalla yace wallahi daga wannan bazata kara haihuwa ba wannan shine nafarko kuma nakarshe yakarashe maganar yana kara saka kuka su abunma dariya Yakoma basu sedai bahalin yinta saboda yanayin dasuke ciki ....
Suna nan zaune doctor yafito aguje Suka nufesa kowa najefomasa tambaya ganin yayi shiru yasa Ahmad yariko hannunsa hankali tashe yana fadin doctor what happened....please say something ....
Murmushi likitan yayi yana dafa kafadarsa yace congratulation .....matarka tasauka lafiya kunsamu karuwar beautiful princess a family dinku.....
wata wawar runguma AK yakaima ahmad seda suka fadi kasa doctor din yawuce yana fadin to sarkin kuka zaka iya zuwa kaga matarka yanzu ....duk kacikamana asibiti da ihu
gaba daya suka nufi dakin kowa narigan rigan daukan yarinyar
amma kafin su isa tuni AK yayi wata supa ya cafke jinjirar yana jujjuyata cike dafarin ciki yaware murya yana fadin oh my god....she is so... so... so beautiful ....chitti zo kiganta dake take kama....yayi maganar yana nufar Asma'u dake tsaye tana kallonsa cike datausayi aranta tana addu'ar allah yanuna musu nasu kodan taga farincikinsa
dakyar grany takwaci yarinyar ahannunsa sannan kowa yasami damar ganinta ahannunta ....
Cike dafarin ciki Asma'u tadaka tsalle tafada jikin khadeeja suka rungume juna cikin tsananin farin ciki
Sam Ahmad yaki matsawa daga kusan khadeeja seda grany tamasa Jan ido sannan yafita daga dakin badan yasoba ...
Shikam AK duk Wanda yazo barka idan bawanda yasani ba se adauka shine uban yar
ganin rawar kan Ahmad tayi yawa Momy tadauke khadeeja tamaidata gidanta dan tasamu kulawar data dace....
Saboda kaunar da AK kema jinjirar ranar suna kyakkyawar jinjirar taci sunan mahaifiyarsa wato Hafsat sunakiranta Hanan
bayan wani lokaci ....
AK abun tausayi jiyake da Hanan tamkar yarda ya Haifa dacikinsa har tafi shakuwa dashi fiye da Ahmad dan matukar yana gida to tana hannunsa duk dabaitaba Asma'u maganar haihuwa ba amma tasan yana matukar son yara arayuwarsa saboda daki namusamman yaware agidansa yacikasa makil dakayan wasan yara kullun yafita seyadawo da kayan jarirai idan tayi magana yace tanadai yakema babynsa maizuwa
tun tana namishi magana har tagaji tazuba mai ido sedai kullum bakinta baya rabuwa da addu'a tana rokon ubangiji ya arzutatta da haihuwa mai albarka....kuma duk addu'arta seta Santa aysha aciki saboda itama tana fuskantar rashin kuanciyar ahankali agidan mijinta dalilin rashin haihuwarta ....
Allah maji rokon bawa ya arzutta aysha da karuwar ya'mace inda kowa yatayata farinciki daganan bakin Hafsat yamutu suka samu kwanciyar hankali....
Ranar suna yarinya taci sunan grany suna kiranta ameera ....
Kullun AK yasaba idan yadawo gida daga bakin kofa Asma'u kezuwa aguje ta tarbesa amma ranan yashigo har cikin Palo bai ganta ba
Wurgi yayi da jakar hannunsa yanufi kan stairs din yana fadin chitti kina ina ne....gani nadawo fa...
Duk inda yake tunanin ganinta yaduba bai sameta awurin ba har hawana karshe yaduba amma bata ba alamunta
daga karshe ya yanke shawarar lekawa bangaren Ahmad yasan bata wuce wurin khadeeja
yazo daidai dakin babynsa yaji sautin wakar yara natashi ahankali daga ciki
Cak ya tsaya yana kallon dakin nadan lokaci kafin yatura kofar ahankali yashiga ....
Ko ina na dakin agyare tsap gaba daya kayan wasan ansaka kowanne amahallinsa
Wani lallausan murmushi yasaki yana bin ko ina dakallo yakarasa ahankali yake takawa cikin dakin har ya isa bakin dan karamin gadon lilun jariran dake tsakiyar dakin ....
Guywowinsa yakai kasa yana tura gadon ahankali yafara lilu wani dan karamin kwalin gift yagani ijiye akan gadon ....
damamki yake kallon box din danshidai yasan baya cikin siyayyar dayayi ahankali yadauki box din yana waige waige adakin amma ba alamar akwai mutum aciki ....
kamar ya ijiye se kuma yabude box din yana kalllon farar takardar dake ninke aciki
Cike da mamaki yafara warware takardar yana karantawa ....
Result din asma'u ne na asibiti Wanda yanuna tana dauke da............ *juna biyu har natsawon sati takwas*!!!
mamaki.... al'ajabi.... farincike ne suka bayyana lokaci guda afuskar AK hannunsa har rawa yake yana maimata sunan asm'au dayafito baro baro ajikin takardar ....
Jin adafa kafadarsa yadago dasauri yana kallon Asma'u still takardar tana hannunsa baigama yarda cewa ba mafarki yakeba
kallonta yake kamar ya hadiyeta farincikin dayamai yawa yama rasa ta ina zaifara nuna mata farin cikinsa ....wash yan siraran farin cikine suka gangaro akan kuncinsa
murmushi tayi tana kamo hannunsa tadora kan cikinta ahankali tafurta can't you say hello to ur baby......
Rungumota yayi daga durkushe dayake kansa adaidai cikinta yana manna mata kiss yama rasa inda zaisaka ransa
ahankali takai hannu tana shafa sumar kansa idonta alumshe itama hawayen farin cikin take dan ba abunda zasuyi dayawuce godema allah da ya amshi addu'arsu....
Fadar irin farincikin da sukayi aranan bata lokacine dan washe garin ranan gaba daya family din agidan suka wuni duk Wanda yaji labari seyazo dan kawai suga irin farin cikin da AK keciki....
Sosai take samun kulawa daga bangarori da dama grany kullun cikin aikomata da magungunan gargajiya take duk abunda tasan mai juna biyu zata bukata to kafin tanema har an aikomata dashi ....
Inna kam duk bayan kuana biyu setazo gidan dan duba lafiyar jikarta ....
Su khadeeja likita itace ma ke kula dakomai nata kullun se tadubata ko bata zoba AK zaije yataso keyarta gaba tazo tabincikata ....
kowa a family din na tsananin kaunar cikin Asma'u kowa nakokarin jiyamata dadi har so suke tace tana son Abu ....
Su khadeeja aysha da Sarah har fada suke idan tabukaci wani abu kowa setace ita zatayi sedai kafin suzo tuni AK yabiyamata bukatarta .....
kwance tashi ba wuya wajan allah haka sukaci gaba da renon cikin har allah yakaita lokacin haihuwa inda nan akaga rudewa awajan AK saboda duk rigimar da Ahmad yayi to AK yatakashi ya wuce awajan ....
Kasancewar haihuwar tazomata dawahala harseda aka yanke tammahar zata haihu dakanta ana shirin yimata operation kenan allah yasauketa lafiya tasambalo kyakkyawan yaronta mai kama da AK sak kamar antsaga kara
Koda tahaihu AK na masallacin dake cikin asibitin yana zabga addu'a dan tunda akace za'amata operation yabar wajan yanufi masallaci ....
aguje khadeeja tazo tamai albishir baimike tsaye ba seda yayi sajada tagodiya ga ubangiji sannan yafito masallacin aguje yanufi cikin asibitin
gaba daya dakin seda yacika makil da yan uwa da abokan arziki kowa na mamakin kama irinta AK da dansa dan abun sewanda yagani ....
Ranar suna akasha walimar da tatara manyan baki daga wurare daban daban anyi taro sosai inda yaron yaci suna Mus'ab
Haka rayuwa taci gaba da tafiya cike dafarin ciki inda Mus'ab yataso yaro mai farin jini wurin mutane yana wayo kyansa nakara fitowa kamarsa da mahaifinsa kuma nakara bayyana hakan ma yasa suke kiransa da junior bashir ne yasamasa sunan har yabishi kowa yafara kiransa dashi
Hanan tana tsananin son yaron tun yana jinjiri take rigimar agoyamata shi ko makaranta taje seta baiyomasa da tsaraba shima yashaku da ita sosai
*Bayan shekara biyar* .....
Asma'u ce tsaye agefen gado taci adon tsap tana kallon AK dake kuance yana bacci kamar wani karamin yaro ....
Murmushi tayi tafara kokarin tashinshi amma Sam yaki tashi sema janyota yayi tafado kansa yana kokarin rufesu dabargo takwace kanta tana mikewa tsaye takaimasa duka da pilo tana fadin karma katashi wallahi tafiya zanyi dan bazan jirakaba ....
Dakallo yabita yana murmushi har tafita daga dakin sannan yagyara kwanciyarsa yana Jan bargo yaci gaba dabaccinsa .....
tana fita dakinta tanufa tanata masifa ita kadai....
tana tura kofar dakin ta tsaya daga bakin kofar kamar zatayi kuka tana kallon kyakkyawan yaron dake kwance kan gado yana sharan bacci
[19/08, 06:18] Hassan Atk: wata dalleliyar motace tayi parking aharabar gidan
atare aka bude kofofin baya namotar AK yafito se ahmad ma tadayan bangaren sannan driver yaja motar zuwa inda aka tanada dan ijiye motoci....
Bashir kam yajima danufar amaryarsa sedai muce allah yabasu zaman lafiya.....
atare suka jero har sukazo tsakiyar gidan sannan suka juyo suna facing juna da murmushi afuskansu Ahmad yabashi hannu yana fadin fatan alkhairi friend....
murmushi AK yayi yana shafa kai yace kaima haka allah yasa tashin farko kabugu yan biyu kaga aka hada danawa hudu kenan ...
"Ohhh AK kaidai bakada wata matsala datawuce ta yara idan allah yabani nawa ma hada maka zanyi duka karike .....
dariya yayi yana juyawa yanufi bangarensa ahankali Ahmad yakira sunansa
Yanajuyowa yaji yarungemasa dakarfi yana hawaye ....
Rungumesa yayi damamaki yana fadin friend lafiya... meyafaru ....
Janyo jikinsa yayi yana share kwalla yace nothing.... kawai duk lokacinda nakalleka ne se inji inaso narigaka mutuwa dan kona second daya banajin zan iya rayuwa batare dakai ba....
murmushi AK yayi yana rungumosa jikinsa yace ya isa haka Superman....yau ranar farin ciki ce awurinmu baikamata kabata mana ita da wannan tunaninba ......yakarashe maganar yana share kwallar data zubomasa hade dajanye jikinsa daga na Ahmad yanufi bangarensa batare dayasake wata magana ba ....
zaune take abakin gado tanabin dakin dakallo wasu yan siraran hawayen farin ciki nabin kuncinta mamaki take wai yanzu wannan tankamemen gidan nata ne wai itace zaune adaki tana jiran isowar Tarzan dinta amtsayin angonta .....tana cikin wannan tunanin ahmad ya turo kofar dakin yashigo hade dasallama ....
Kanta akasa cikin lullubi idonta alumshe tasauke wata nannauyar ajiyar zuciya sannan tabude baki da kyar ta amsa sallamarsa yajima atsaye yana kallonta kafin yakaraso bakin gadon yazauna kusa da ita yana kai hannu ahankali yadage mayafinta yana kure kyakkyawar fuskarta dakallo .....
ahankali tafara bude idanuwanta har tasaukesu cikin nasa kallon dayakemata yasa tayi saurin kauda fuskarta tana lumshe ido zuciyarta nabugawa dasauri nunfashinta nafita ahankali ....
Hannu yasa yana karkato fuskarta suna facing juna amma still idanuwanta alumshe ....
ahankali yakai bakinsa yamanna mata kiss agoshi yana lumshe idanuwa kafin yajanyota dakarfi yamannata akirjinsa kamar za'a kwacemasa ita cike dafarin ciki yace flying bird senake ganin kamar amafarki wai kinzama matata...I don't even know what to do ....narasa taya zannuna miki farin cikina ....allah nagodema....yakarashe maganar yana kara manneta ajikinsa ....
Saboda rungumar dayamata har muryarta bata fita da kyau dakyar ta iya furta ....Tarzan I like your hug amma nakasa nunfashi da kyau ....
Dariya yayi yana sassauta rungumarsa yace ohh sorry karkiga laifina ....kedin ce ai se inji kamar inmaidaki ciki....
Tashi yayi yana kama hannunta suka nufi bathroom yana tsaye har tayi alwala sannan shima yayi suka dawo dakin ...
Tana tsaye tana kallonsa yashinfida musu dadduma sannan yajasu sallah raka'a biyu kamar yadda sunna ta tanada .....
Suma se muce allah yabasu zaman lafiya da zuri'a tagari....asha amarci lafiya .....
Cike dafarin ciki AK yashiga gidansa dagudu gudu yake hawa kan stairs har ya isa dakinta ....
Yana tura kofar yaga wayam bakowa cike da mamaki yake bin ko ina na dakin dakallo
[19/08, 06:18] Hassan Atk: ahankali takarasa cikin dakin tana hawa kan gadon tafara kokarin tashinsa tana fadin Mus'ab wai baccin kakoma yine...shiyasa nake hanaku cika dare bakuyi bacciba amma bakwaji dasafe kuma kuyita bani wahalar tashinku .....
gyara kwanciyarsa yayi batare da yabude idonsa ba yace mum please.... Yaufa weekend kuma islamiyyar ma seda yamma kidan barni nayi bacci mana .....
Kai tashi dallah baccin ya isa haka....tafada tanaci gaba datashinsa ....
bubbuga kafa yafarayi cikin muryan bacci yana fadin mum to kifara tashin dady tukunna ahima ai baitashiba ....
Dariya tayi tana cimashi sama tace kai kamanta yau zamuje wajan grany ne ....kowa fa zaije harda su Hanan da ameera da duk sauran yara zasuje kanso kowa yayita tambayar junior ne ...
Se alokacin yasaki yabude idonsa yana sakin wani lallausan murmushi yace mum biki za'ayi ne agidan grany....
"Jiya ba naji kuna fita da dady ba yacemaka kaka zaidawo daga Germany ko bakason ganinsa ne ....
cike dafarin ciki yace inaso mana ....amma kibarni indan kara kadan
"Mekenan?
"Baccin ....yafada yana kokarin sake kwanciya tasabashi akafada suna dariya tanufi bayi dashi ....
Cikin sauri sauri tagama shiryashi suna sakkowa kasa daidai nan Ahmad yashigo yana janye da hannun Hanan takara wayau kyanta yafito fili aguje mus'ab yakarasa wurin Ahmad yana rungumesa yace ina kuana uncle....
Cibashi sama ahmad yayi yana dariya yace lafiya kalau my boy ....ya akayi yau katashi dawuri .....
nuna mishi Asma'u yayi dayatsa yace mummy ce ta tasheni wai zamuje gidan grany kaka zaizo daga Germany....
Cike da mamaki Ahmad yace kaka....Germany kuma ....
juyowa mus'ab yayi yana kallon Asma'u da alamar tambaya afuskarshi kafin yayi magana Hanan tace eh mana dady yace mana yau kaka zaidawo daga Germany....
Dariya Ahmad yayi danse alokacin yafahimci inda zancan yadosa yana rike dahannayansu yakaraso cikin palon yana tambaya da AK
Asma'u tace kasan halinahi ai bacci yake kuma Sam yaki yatashi...jiya har karfe biyu suka kai basuyi bacciba ...
haurawa yayi sama yana fadin bari nagwada inga kozaitashi....
Da kwa ka taimakamun...Asma'u tafada tana nufar kitchen dan hadama AK coffee dinsa....
dakarfi Ahmad yatura kofar dakin yana murmushin mugunta yakarasa bakin gadon yafara Jan kafar AK da karfi kamar amafarki yakejin abunda shiyasa ko motsawa baiyiba sema gyara kuanciyarsa dayayi
gefen kansa yakoma yafara jamasa kunne yana rankwashinsa akai...
Cikin magagin bacci AK yace chitti wanann wane kalan tashi kike munne......
dariya Ahmad yayi yana jijjigashi yace kai dallah tashi rana tafito.... har junior yatashi amma kai kana nan kana bacci
Cike damamaki AK yakashe kunne yana sauraronsa batare dayabude idonsa yace chitti meyasami muryanki ne ....ko mura ce takamaki....yakarashe maganar yana janyo Ahmad jikinsa ...
kokarin tashi Ahmad keyi amma dariya tahanasa cikin muryan bacci AK yace mekike ma dariya ne gaskiya mura nan tamiki wawan kamu harta dariyarki ma tacanza .....kinsan meyasa nakasa tashi morning kiss din dabaki min bane yasa baccin yaki Barin idona yanzu kimun se intashi....
yakarashe maganar yana kokarin kamo fuskar Ahmad yaji yatabo saje daidai lokacin mus'ab dake tsaye bakin kofa yakira sunansa dakarfi daaadyyy....
Atsorace yabude idonsa yana ganin Ahmad yasaki yar kara yana turasa baya dakarfi ya tashi zaune yana mutsitstsike idanuwansa dan tuni baccin yakaurace daga idonsa
Aguje Asma'u takarso dakin tana fadin lafiya menene.....
kallonsu take daya bayan daya amma bawanda yakeda niyyar bata amsa cike damamaki takalli Ahmad dake gefe yana kwasar dariya harda rike ciki....tace Ahmad nafasan halinka .... mekamasa ne ...tashin mugunta kamasa ko.....
Kafinyayi magana Mus'ab yarigasa dafadin a'a mummy... Daddy ne yatsokanesa ...
Jan hannunsa Ahmad yayi suka fita ita kuma takarasa wurin Ak tana fadin ABI meya maka ne meyasa kayi ihu katsoratani fa ....
cike datakaici yace chitti meyasa zaki barsa yazo tashina yanzu da nafadi wata maganar agaban Mus'ab fa
Fuskar tausayi tayi tana rungumo kansa tace ohh sorry ABI....bakaine kaki tashiba amma yihakuri bazan kara bari irin haka tafaru ba kaji....
Saurin dagowa yayi yakalleta sannan yamaida kansa daidai cikinta yana fadin wait....chitti kinji abunda naji kuwa....
Mene....tafada tana kashe kunne kozatji abunda yaji....
dirowa yayi daga kan gadon yana kai hannunsa kan cikinta yace motsi fa naji lokacinda kika rungumeni ....kuma irin Wanda nakeji lokacin kinada cikin mus'ab...
cike dafarin ciki tace allah dagaske....dama inason zuwa asibiti saboda najima banga al'adata ba kuma kasan haka yamun cikin mus'ab ko kadan banajin komai ajikina sedai kawai period dina yadauke....
wata kalar dariya yayi mai cike da tsananin farin ciki yana kamo hannayanta cikin rawar murya yace kina nufin ...kenan...oh my god chitti...I can't believe it...allah nagodemaka .....yakarashe maganar yana janyota jikinsa suka rungume juna sunama allah godiya
Kafin sutafi gidan grany seda khadeeja ta auna Asma'u inda result yanuna tana dauke dajuna biyu sunyi farin ciki matuka haka suka rankaya gaba dayansu suka nufi gidan grany dan tarban su uncle jamilu dazasu fito prison shi yaran ke kira dakaka saboda sunsanshi aphoto da mus'ab yadami AK datambayar ina yake shine yace masa agermany yake
Suna isa gidan Hanan da mus'ab suka nufi cikin gidan aguje suna kwalama grany kira
Apalo iskota zaune aguje suka fada jikinta tarungumesu cike dafarinciki tanajin kaunarsu har cikin ranta ....
Nan kowa yafara tsokanar Mus'ab kowa nason magana dashi saboda duk maganar dayayi dariya takebasu gashi gwanin surutu Hanan ce batacika magana ba inkaji firanta to da yane gidansune ko kawayanta wato malika da ameera dan zumuncin da iyayansu keyi yasa yaran suka shaku sosai
amota aunty sadiya banda kuka ba abunda take aysha narungume da ita tana tayata shidai uncle jamilu yayi ahiru dan ba bakin magana kunyar aurikinsa duk tacikasa wato salim da kyarma yayarda yabiyosu dan cewa yayi bazai iya zuwa gidan AK ba ....
Gaa daya sunfita hayyacinsu sunkode sunyi baki ga tsufan dole dasukayi dan uncle jamilu harda furfura kana ganinsu kasan bakaramar azaba suka shaba....
Sunyi farin ciki matuka ganin aysha tayi kyau abunta hankalinta kuance agidan mijinta harda karuwa swgofiya sekemasa daya rike masu yar'su amana ....
Suna isowa gidan gaba daya muatanen gidan yara damanya duk suntaru aharabar gidan ana jiran isowarsa dakyar suka iya fitowa daga motar suna kuka suka fara Neman gafara awurin mutanen gidan
Seda kowa nawurin yazubar musu da kwalla saboda tausayin halin dasuka Shiga yaran dai Sam sunki yarda suje wurinsa mus'ab ne kawai yaje wurinsu saboda shima gwanin tausayine hardashi a yan kukan duk da baisan inda zancan yadosa ba amma ganin kowa nakuka yasa shima yafashe dakuka yana rungume dadynsa
Sunjima awaje kafin suka Shiga cikin gidan ana cigaba damusu sannu abinci kala kala aka Jere musu a dining seda sukayi wanka suka shirya sannan suka pito zuwa dining seda aka zuba musu abinci suka faraci sannan aka basu waje kowa yadawo Palo dan suji dadin cin abincin.....
Duk inda Asma'u tayi AK nabiye da ita dan motsi kanan seyamata sannu...se tsokanarsa Ahmad keyi har kowa dai yagano abunda kefaruwa nanfa aka bude sabon shafin fira ....
bashir ne yafara dauko labarin dramar da Ahmad yayi lokacin haihuear Hanan nanfa kowa yahau yimasa dariya bashiri yayi shiru yanemi acanja firar
ganin baiga Asma'u akusa dashiba yafara cigiyar ta yana tambayar khadeeja kotaganta
dafe goshi tayi tana fadin ohh Yaya shekararku takwas da aure amma kullum cikin cigiyarta kake ....kabarta tasha iska mana ....
Dariya yayi yana shafa kai yace ba laifina bane yayartaki ce ....bana gajiya da ita ...kokadan banason tayi nesa dani duk se inji wani iri.....
Aunty ameena tace kai rabu da ita gara kai ai damijinta dama ba agabanmu akayi bane .....
Dariya akasa gaba daya bashir yace suna dawani Abu wai......aysha takarashe masa dafadin supper glue....
pilo Ahmad yajefa masa yana fadin to anyi shiru miye kuma nadawo dazancan ....
shidai AK tuni yafita Neman rabin ransa agarden yasameta zaune karkashin bishiya ta tasa furanni agaba tana kallo haryazo kusa da ita bata saniba seda yadafa kafadarta sannan tadago dasauri tana kallonsa ....
Kusa da ita yazauna yana fadin tunanin me kike ....
ajiyar zuciya tasauke tana murmushi tace rayuwarmu nake tunawa ABI yamda komai yazo yawuce tamkar amafarki....yanzu gamu ahade wuri guda abunda ko amafarkina bantaba tunanin zangani ba ....
kamo hananyanta yayi yana murmushi yace chitti kece silar haduwarmu anan bansan mezanke cemaki kifahimta ba amma kinkasance tamkar wata uwa agaremu wacce tasanar damu ainahin me ake nufi da yan uwantaka ....wasu lokutan nakan bata lokaci wajan tunanin mezanmiki yasakaki farinciki amma senaga komai zanmiki bazan biyaki kwatankwacin abunda kikamun ba lullun adfu'ata allah yabarmun ke saboda ABI ba komai bane idan ba chitti......ina rokon allah yatashemu karkashin inuwar aure gobe kiyama ....
Kuantar dakanta tayi kan kafadarsa tana saka hannunta anasa cikin sanssanyar murya tace ABI kyawawan halayanka ne suka kamu halin damuke ciki yanzu ....kyakkyawar zuciyarka ita tazamo runfa wa zumuncinmu jajircewarka akan ahalinka kuma shiyasaka tsantsar kauna atsakaninmu ....agaskiya samun irinka ahalin yanzu yanada matukar wahala ...shiyasa kowane lokaci nake alfahari dakai amatsayin miji.... aboki kuma uban ya'yana ina fata kap yaran gidan nan subiyo hali irinnaka ....
Haka sukaci gaba dafirarsu mai matukar birgewa har aka aiko kiransu sannan suka koma ciki akaci gaba dafirar yaushe gamo....
Harsu Umma da inna seda sukazo ranan su nusaiba anzama yan'mata har ana shirin aurar da ita
fa'iz kuma tuni AK yaturashi kasar waje karatu sedai yazo musu hutu
Har lokacin uncle jamilu baibar kukaba yana cigaba darokonsu gafara Mus'ab nagefe duk yahada fuska yana shirin fashewa dakuka danshi sam baigane shine kakan da'ake magana akai ba dan ayanda suka shigo dazu ko za'akasheshi bazai yarda daga Germany suka fitoba duk da yaro ne amma yasan kasar Germany dan basujima da dawowa dagacan ba shida babansa
ahankali yakaraso yana dafa uncle jamilu cikin yar karamar muryarsa mai dadin sauraro yace ....kaima kazo tarban kakan dazaizo daga Germany ne...to meyasa kake kuka....tsaraba kake so....kadaina kuka idan yabani tawa zanbaka kaji....yakarashe magamar yana sharemasa hawaye.....
janyosa yayi jikinsa yana rungumesa dakarfi kwalla nazuba a idonshi har cikin ransa yakejin kaunar yaron cikin rawar murya yace nine... kakanka Mus'ab
Cike damamaki yadago yana kalllon AK dayayi saurin kauda kai yana murmushi
Kowa su yake kallo apalon shidai mus'ab yayi shiru yana kure uncle jamilu da ido nadan lokaci sannan yasakar masa laullausan murmushinsa dake kara fito datsananin kamarsa da AK cike dafarin ciki yace kaka dama Kaine ....amma kaka nacikin photo gashinsa bakine kaikuma naka yayi fari shiyasa banganeka ba ....
dariya akasa gaba daya palon uncle jamilu yaja kumatunsa yana fadin like father like son ....wayanka yafi shekarunka yawa ko
se alokacin sauran yaran suka matso kusansa suna tambaya da tsarabarsu
Shiru yayi yarasa mezai cemasu
bashir yajasu suka nufi bangarensa yana fadin niyabama tsarabarku in ijiyemaku muje kowa nabasa tasa ....
Cike dafarin ciki suka ni bayansa suna tsalle sukuma manyan sukaci gaba dafirarsu ana basu labarin abubuwan dasuka faru bayan tafiyarsu kowa nafadan shirmensa ana dariya .....
Labarin rayuwarsu baida karshe sedai ince ......
Anan nakawo karshen littafin domun kanwata ina fata ya kayatar kuma kunfahimci sakon ayanda yazo muku .....
ina mika dunbin godiyata agareku masoyana aduk inda kuke nagode matuka da addu'arku agareni kuma ina rokon alllah madaukakin sarki dayabiya muku bukatunku na alkhairi