D'aki ne mai cike da ababen tsoro, tsananin bakin duhun da shi kadai aka bar bil adama da shi, tabbas zai iya rasa ganinsa a duk sadda ya shigo cikin haske. Kururuwa, da wani irin ihu dattijon da ke cikin d'akin ke yi, yayin da a duk lokacin da ya dumfari k'ofar fita, sai ya ga k'ofar ta shafe da bango, tamkar ba'a taba halittarta ba a wurin.
Yayi hakan ya kai sau goma, a k'arshe ya saki wani gagarumin k'ara, mai tsananin sauti, wanda ya ansa kuwwa a gaba d'aya dakin, har ma ya ji tamkar yana girgizawa.
Wani yaro ne ya bayyana gabansa, ya mik'a masa hannu alamar ya taso, ya ko mik'a nashi hannun, cikin yan dakiku, yaron ya fito da shi daga d'akin ma'abocin duhu da ban tsoro. Fuskar yaron da ya ceto shi ya kalla, hawaye ya gani suna sintiri d'aya bayan d'aya, yana fad'in
"Ka taimake ni nima, tamkar yadda Allah ya bani iko na fitar da kai daga halin da kake ciki."
Ya bud'e baki zai yi magana, ya nemi yaron sama ko k'asa ya rasa, a dai-dai lokacin ya farka daga baccinnasa, bakinshi kunshe da salatin Annabi.
Ire iren mafarkan da Mal. Buba ke yi kenan tun daga ranar da yayi shedar karya a kotu, haka kuma ko alama ya kasa samun natsuwa da kwanciyar hankalinsa. Hakan yasa ya yanke shawarar da gari ya waye, zai je ya sanar da Alkalin gaskiyar lamari, a shirye kuma yake ya anshi duk ko wane irin hukunci zai biyo baya.
Washe gari da sassafe ya shirya, ya wuce kotun da ake sauraren shari'ar su Tareeq, bai samu ganin Alkalin ba, sai Registrar ya gani, ya shaida masa abinda ke tafe da shi. Komai registrar bai ce ba, daga k'arshe ya jaddada masa matukar ya shirya fadar gaskiya, to ya dawo ranar da za ayi zama na gaba.
*****
Tsaye yake gaban dogon madubin da ya kan iya kallon tun daga kansa, har kafafunsa, a sa'a guda yana gyara zaman necktie din da ke daure a wuyansa. Grey suit jacket d'insa da ke rataye jikin hanger ya ciro, yana k'ok'arin d'ora shi saman white long sleeve shirt da ke jikinshi, ya hangi yanayin matartasa ta madubin da ke gabansa, da sauri ya juya yana kallonta. Tunda ta fito wanka zaune kawai tayi gaban madubin, ba kuma ta da niyyar motsawa.
Cuff-links dinsa ya k'arasa makalawa, ya taka a hankali ya isa ta bayanta, tare da rankwafo da kansa, ya dora habarsa a kafadarta. Idanunsa ya zuba yana kallonta ta madubin, hakan ya sanya ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, tare da sakin murmushin da ya fi kama da na k'arfin hali.
"What's wrong with you Angela?"
Ya tambaya yana ci gaba da kallonta, bata ce komai ba ta dora hannunta saman nashi da ya zagayo da shi zuwa wuyanta.
"Bana jin zan iya fita yau Ya Sadic."
Ta yi maganar cikin murya mai taushi, ya dube ta da kyau, tabbas iyakar gaskiyarta kenan. Sai dai ya rasa menene dalilin shiru-shirun nan nata. Kusan sati biyu kenan, amma kullun haka take sululu, babu walwala a tare da ita. Yayin da duk irin tambayar da zai mata, ansar dai guda daya ce, 'babu komai.'
Gefen fuskarta ya shafa a hankali yana ci gaba da kallonta.
"Amma kin manta kina da shari'ah yau?"
Ta girgiza kai, alamar bata manta ba.
"Okay, tashi ki shirya please. Success is always with you wifey."
Ya karashe yana mai sumbatar kumatunta, ta murmusa kafin ta daga kanta.
Ganin ta janyo mai zata fara shafawa ya sanya shi mikewa, ya k'arasa saka suit d'in, ya feshe jikinshi da turaruka, ya juya yana dubanta ta madubi. Yanayin kallon da ya ke mata yasa ta fahimci abinda ya ke nufi, ta mik'e jiki babu k'wari, ta isa daf da shi, tare da zagaye hannayenta a bayansa, ta kwantar da kanta saman faffadan kirjinshi.
"Allah ya bada sa'a Ya Sadic."
Ta fad'a a hankali, cikin muryar da ta sanya shi fadawa kogin tunani.
"You really okay?"
Ya tambaya bayan ya d'ago fuskarta, ya saita idanunsa cikinnata.
"I'm fine."
Ta ce da shi, hakan ya sa ya zagaye hannuwansa a bayanta, ya had'e ta da jikinshi tsam-tsam, and not willing to let go.
"I love you Angela."
Ya fad'a a setin kunnenta, sannan ya sake ta ya juya ya d'auki briefcase nasa.
"Allah ya bada sa'an shari'ah. Sai na dawo."
Murmushi tayi mai kayatarwa, ta k'ara da fad'in
"Thank you, nd I love you more."
Daga nan ya wuce zuwa waje, yayin da ta koma saman gado ta zube, zuciyarta sam babu dad'i. Hankalinta na matukar tashi a duk lokacin da ta tuna buk'atar su Alhaji Barau. Sai tayi niyyar ansa tayin da sukai mata, sai kuma fuskar Tareeq ta wanzu a birnin zuciyarta, hakan ke k'ara rikirkita lissafi, har ma da tunaninta. Kusan awa ukku tana zaune a wurin, ko towel din jikinta bata da niyyar cirewa.
Agogon da ke manne da bangon d'akin ta sauke idanunta a kai, karfe tara har da wasu 'yan mintuna, yayin da shari'artasu ta kama karfe goma dai-dai.
Tayi juyi a saman gadon tare da jan blanket, wani irin zazzabi mai zafi ya sauko mata cikin dan k'aramin lokaci.
*****
Tun daga yawan motocin da ke adane a harabar kotun za'a tabbatar da yawan al'ummar da suka halarci shari'ar ta yau, cikin kotun ma ya cika ya batse, har babu wurin zama, Alkali na daga kujerarsa, Barr. Hisham na zaune a bangaren hagu, yayin da Barr. Nasib wanda ke cikin tsananin tashin hankalin tunanin abinda ya dakatar da Jay na zaune a bangaren dama, sai dai lokaci zuwa lokaci, ya kan kai dubansa ga k'ofar shigowa, zuciyarsa na addu'ar Allah ya sa dai lafiya.
Agogon hannunsa ya kalla, karfe goma har da mintuna ashirin. 'Ina Barrister ta tsaya?' Ya kai tambayar ma zuciyarsa, sai dai bashi da mai ansa masa in har ba ita din bace ta bayyana.
"Ya Ilahi.."
Ya fad'a a bayyane, tare da furzar da iska mai matukar zafi.
Cikin tsananin izza, Barr. Hisham ya mik'e,
"My Lord. Ina mai rokon kotu da a cigaba da sauraren shari'ah kawai, dan alamu sun nuna Barr. Jameela is not serious anymore. Nd Justice delay, is definitely justice denied."
A tsanake Alkalin ya kai duba ga agogon da ke daure a hannunsa, ya d'ago tare da gyara zaman gilashinsa yana fad'in
"Sure, but don't you know that, justice rush is justice quash? For that, za'a k'ara mata 'yan mintuna, cuz its better to delay justice than to condemn innocent..."
Bai kai ga rufe bakinsa ba ta fad'o cikin kotun, tamkar wacce aka jefo, tsananin damuwa da tashin hankalin da take ciki, sun bayyana k'arara a saman fuskarta, wanda za'a iya fahimtar hakan ta kallo d'aya.
Cikin gaggawa mai tattare da rashin natsuwa ta isa ta zauna gefen Barr. Nasib, ya rankwafo cikin zak'uwa
"Barrister ya aka yi? Me faru? Ina kika tsaya?"
Ya jera mata tambayoyin, sai dai kafin ta yi yunk'urin bashi ansa, muryar Alkalin ta karad'e kotun, cikin wani irin amo mai k'arfi.
"Where have you been like that? Kinsan kina da shari'ah 10:00 me ya kamata kiyi for God's sake? I'm warning you, nd this is the last time. Okay?"
"I'm sorry My Lord."
Ta fad'a kanta a k'asa, sannan ya ci gaba
"Kin taka sa'a ma, but i was about to stroke the case."
Ya maida dubansa gare su baki d'aya,
"And to y'all, I want to address this. As officers of the law and minister of justice, you should maintain that decorum. So, don't be just like market people kuyi ta objection anyhow. And I expect y'all to assist the court in the task of ensuring justice, protecting human rights and to uphold the rule of law."
Cikin daga murya yayi maganar, da alama ranshi ya matukar baci, ya maida dubansa ga littafin da ke gabansa, a sa'a guda kotun tayi tsit, babu wanda ke koda kwakkwaran motsi.
"As the court pleases.."
Suka fad'a a tare su duka ukun, kafin ya d'ago yana mai ci gaba da cewa
"I almost forget. It has come to my notice that, Mal. Buba, wanda ya bada sheda ta bangaren wadanda ake k'ara ya fad'i false statement, and he's willing to change his statement, so idan yana kusa ya matso gaban kotu."
Wani irin tashin hankali ne yayi dirar mikiya ma zuciyar Barr. Hisham, a sa'a guda aka dinga kallon kallo a tsakanin mutanen da ke zaune a kotun. Shiru Mal. Buba bai bayyana ba, har sai da d'an sandan da ke k'ame bakin k'ofa ya lallak'e, ko Allah zai sa ya ganshi, amma babu shi, babu kuma dalilinsa.
Ganin hakan yasa Alkalin basu dama da su ci gaba daga inda suka tsaya.
Cikin takun girma Barr. Hisham ya mik'e, duk da cewar ba shi da sauran fargaba, domin ya riga ya san sun gama sayen Barr. Jay, har yana ji a jikinshi hakan ne ma ya yi sanadiyyar makararta a zamannasu na yau. Ya murmusa, kafin ya fito gaban kotun, cikin azama ya fara magana, dan kuwa wannan ita ce dama ta k'arshe da yake da akwai, a kuma wannan zaman ne zai san duk yadda zai yi domin ya kubutar da clients dinshi.
"My Lord, ina rokon alfarmar kotu da ta bani dama, domin gabatar da wasu yan tambayoyi ga clients dina."
Girgiza kai Alkalin ya yi, a sa'a guda ya yi nuni mishi da hannunsa, kafin ya k'ara da cewar
"Kotu ta baka dama."
Hannuwansa a aljihu, ya mik'a zuwa bangaren da su Mubee ke tsaye, ya kalle su da fuskarsa ba yabo ba fallasa yayi nuni da Sino.
"Ehhnmm.. Hassan."
Ya d'ago a hankali yana dubansa.
"Zan so ka sanar ma kotu inda kake a ranar laraba ashirin da biyar ga watan December na shekarar da ta gabata"
Shiru Sino ya yi, a lokaci guda ya shafi cikakkar sumarsa da ta mimmike, alamar rashin samun gyara, ya yi k'asa da kansa, kafin ya ansa da
"Gaskiya ba zan iya tunawa ba."
"Kamar ya kenan? Ina magana maka a ranar da ake zargin faruwar al'amarin da ya tara mu a nan, kana ina a ranar?"
"Eh fa, bazan iya tuna inda nike ba gaskiya."
"Ko zan iya sanin dalili?"
Ya d'ago a hankali ya saci kallonsa, sannan ya maida kansa ya fara magana.
"Saboda.. saboda bana cikin hayyacina a gaskiya."
"Baka cikin hayyacinka? Me hakan ke nufi kenan?"
Shiru yayi, idanunsa a k'asa, har sai da ya k'ara maimaita tambayar ya k'ara da fadin
"Ina saurarenka."
"I was drunk."
Ya fad'a a gajerce, har kuma a yanzu kanshi na a k'asa.
"You were drunk."
Ya maimaita da dan murmushi saman labbansa, yana takun kaiwa da kawowa a gaban witness box din da suke ciki. A k'arshe ya k'ara da cewar
"Kafin ka samu kanka a yanayin da ka fad'a, shin zaka iya tuna a inda kake?"
Sai da yayi jim, daga bisani ya ce
"Na san dai mun isa shisha joint tare da abokaina, daga nan babu abinda zan iya tunawa, sai washe gari da na farka na ganni kwance a dakina."
"Abokanka su wa kenan? A ina suke? Kuma a ina kuka had'u da su kafin ku cimma shisha joint din?"
Ya d'ago da kansa, yayi nuni da su Mubee da ke tsaye gefenshi, fuskokinsu sun fita daga hayyacinsu, sunyi baki da wata irin ramar da ta bayyanar da matsanancin halin da suke ciki muraran.
"Sune muke tare da su, kuma fitarmu daga gidan su Mukhee kawai muka zarce can."
"Daga nan kuma baka k'ara ganinsu ba, har sai zuwa wane lokaci?"
"Sai a washe gari muka k'ara haduwa da su."
Murmushi Barr. Hisham ya saki. Ya juya yana mai duban su Mubee tamkar zai furta wani abu, sai kuma ya basar, tare da maida hankalinsa ga Alkalin da gaba d'aya tunaninsa ke kansu.
"My Lord."
Ya fad'a lokacin da ya k'ara takun sawunsa zuwa tsakiyar kotun, ya ci gaba da cewa
"Ta yin la'akari da statement din da d'aya daga cikin clients dina ya bayar, zan so a ce kotu tayi duban tsanaki, ta kuma fahimci cewar a ranar da ake maganar faruwar al'amarin, sam basa ma tare da hankalinsu, abun nufi, basu ma san me ya wakana a ranar ba. Dan haka ina rokon alfarmar kotu, da ta yi duba zuwa ga yanayin da suka tsinci kansu a ranar, ta wanke su daga gagarumin zargin da ake musu."
Ya rissinar da kansa, kafin ya koma mazauninsa.
Alkalin da ya d'ago daga rubutunsa, ya kai duba ta setin da su Jay ke zaune
"Counsel, ko kuna da abun cewa?"
"Yes My Lord."
Ta fada bayan ta mike, labbanta kunshe da murmushin da ya fi kama da na yak'e. Cikin natsuwa ta mik'e, bata ko bi ta kan maganar da Barr. Hisham ya yi ba, ta fito da muffler da ta tabbatar ta su Mubee ce kamar yadda Khamis ya shaida mata, ta iso gaban kotun.
Gaban su Deeni ta k'arasa, ta daga muffler tana duban Mubee wanda shine mamallakinta tana fad'in
"Me zaku ce game da wannan muffler?"
A tare suka d'ago, idanunsu da tamkar zasu fad'o k'asa, hannun Deeni na wata irin kyarma, ba komai yake tunawa ba, sai lokacin da ya daure idanun Tareeq da abun, wanda bai yi tunanin zai kara moruwa da ganinsa zuwa gaba ba. Duk sun gagara furta ko da kalma d'aya.
Kallon tuhuma Alkalin ke jifarsu da shi, ganin yadda suka sha jinin jikinsu, tamkar kazar da aka tsoma a ruwan zafi. Maganar Jay ce ta katse shi daga duban tsanakin da yake musu, ya maida hankalinsa gare ta yana sauraren jawabinta.
"My Lord, mutanen nan da ke tsaye gaban kotu, sunyi amfani da wannan muffler ne wurin daure idanun Tareeq wanda Allah ne kawai ya taimaka yana da rabon gani a gaba, hakan ya tabbatar da cewar muffler din ta su ce, kamar yadda bincikena ya tabbatar mani, an sayi muffler din ne a Dilemma Super Market, shago mai number dari da tamanin da hudu, da ke kan titin Isah Kaita a nan cikin garin Kaduna. Bugu da kari kuma receipt din biyan kudi ya fito 6aro-6aro da sunan Mubarak Garba Bukar rubuce a jiki."
"Objection My Lord."
Barr. Hisham ya fad'a cikin azama, ya mik'e ya fito da tashi muffler a hannu, wacce babu wani abu da ya banbanta ta da wacce ke hannun Jay. Ya kalleta ta k'asar idanunsa, ya jefe ta da wani makirin murmushin da ya k'ara dagula lissafinta.
"Tabbas Mubarak ya sayi muffler a Dilemma Super Market a ranar talatin ga watan September na shekarar da ta gabata, sai dai ba shine zai sa Barrister tayi saurin yanke hukuncin cewar muffler da ke hannunta, mallakarshi ce ba. Domin yanzu haka a tare da ni akwai muffler da shi Mubarak din ya siya, wacce ga dukkan alamu tayi kamanceceniya da wacce Barrister ta gabatar, haka zalika wannan ya nuna cewar wasu ne can na daban suka tafka wannan aika-aikar, da ake tuhumar clients dina."
Ya k'arasa ya mik'a tashi muffler ma Alkalin had'e da duplicate na receipt dinta, mai d'auke da shekara da kuma ranar da aka siye ta. A sa'a guda itama ta mik'a tata, a tare Alkalin yake duban muffler, yana son ya fahimci abinda ya banbanta su, sai dai babu wani banbanci ko da na digo d'aya.
"Da wannan nike rokon wannan kotu mai adalci, da ta fahimci cewa clients dina basu da hannu a abinda ake tuhumarsu, haka kuma bayanan da Barrister ta yi, sun isa su gamsar da kotu cewar wasu ne can na daban suka aikata laifin, yayin da a nan aka tsare bayin Allahn da basu da masaniya a abinda ake tuhumarsu."
"Tabbas mutanen nan da ke tsaye gaban kotu su suka aikata laifin da ake tuhumarsu, kamar yadda Tareeq ya dinga kiran sunayensu a cikin baccinsa, da kuma lokacin da Alkali ya bukaci ganawa da shi."
Ta yi gaggawar katse shi, a sa'a guda ta k'arasa gaban desk dinta, ta fito da wayarta, cikin gaggawa ta bincika recording din da Khamis ya tura mata, ta mik'a shi ga registrar yayi connecting da manyan speakers din da aka tanada domin irin haka, ta yadda kowa da ke cikin kotun zai iya saurarar abinda ke ciki.
Muryar Tareeq d'in ce ta karad'e kotun baki d'aya, haka sunan Mubee tangararam a bakinsa, bayan ya kare ta kuma kunna recording din da tayi a chamber, lokacin da suka kebance da Alkali.
Salati mutanen cikin kotun suka kwasa, a sa'a guda Mal. Buba ya turo kanshi ciki, bai bata lokaci ba ya iso gaban kotun ya tsaya.
"Order.. order.. order in court."
Abinda Alkalin ya ci gaba da maimatawa kenan, har zuwa sadda aka samu daidaituwar surutun mutanen da ke wurin. Registrar ne ya mik'e yayi k'us-k'us ma Alkalin, wanda da alama zuwan Mal. Buba ya ke sanar da shi.
"I don't believe in your recordings Barrister."
Muryar Barr. Hisham Ta sanya su maida hankalinsu gare shi, a sa'ar da ya ci gaba.
"This is just an act, as I said earlier. Dan haka kiyi providing concrete evidences da zaiyi proving clients dina guilty, May be, yeah, may be I'll be convince! Amma wannan, I'm sure sai da kuka shirya ke da yaron da kika kai, sannan kuka yi acting din da kuka yi."
Shiru tayi tana kallon yadda yake magana hankalinsa kwance, gaba d'aya jikinta kyarma yake, zuciyarta tamkar zata tsinke, domin ta gama gabatar da duk wani abu da ta mallaka a yanzu, kuma matsawar wannan damar ta subuce mata, to fa tana ji tana gani tsab za su sha gabanta, su yi winning case din da idan har bata samu biyan bukatarta ba, to kuwa da wuya idan zata ci gaba da ansa sunan Barrister. Dakyar tayi karfin halin had'a kalmomin da bata san ta inda suke zuwan mata ba
"I'm not trying to convince you Barr. Hisham, for that matter, wannan ba huruminka ba ne ba."
Da gama fadar hakan ta ji wani sabon zazzabi ya kuma sauko mata, nan da nan hakoranta suka fara had'e kansu, kyarma take wacce har za'a iya fahimtar hakan ta yadda gaba d'aya jikinta ke motsawa. Jin duk sunyi shiru yasa Alkalin tambayar ko akwai wani mai sauran abun cewa?
Kai kawai Jay ta girgiza, a sa'ar da Hisham ya saki murmushin samun nasara, ya bi ta da wani irin kallon da ya tsananta faduwar gaba da kuma jin sanyinta. Tamkar wacce aka zare ma lakka, haka ta isa ta zauna a gefen Barr. Nasib wanda ya rankwafo yana tambayar lafiya take ko.
Jin muryar Alkalin da ya ce da Mal. Buba ya k'araso gaba, shi ya ja hankalinsu ga maida dubansu gare shi. Ta kasan gilashinsa ya gama kare wa Mal. Buba kallo, a k'arshe yayi nuni masa da witness box, babu bata lokaci ya shige ya tsaya yana ta faman rarraba idanu.
"Kai ne Mal. Buba?"
"Ni ne Yallabai."
"An ce zaka gyara zancenka, haka ne?"
Ya tambaya yana mai ci gaba da kallonshi.
"Haka ne Yallabai."
Ya yi maganar kansa a k'asa.
"Go ahead then."
Duk da ba wai ya fahimci abinda ya fad'a din bane, ya san dai nufinshi ya ci gaba ta yadda ya ga yayi amfani da hannunsa, ya kuma tallabi habarsa ya zuba idanu yana kallonshi.
Daya bayan d'aya Mal. Buba ya fara jawabi, abinda ya fad'i ma yan sanda shi ya kuma maimaitawa a gaban kotun, fuskarsa cike dam da nadama, tare da da na sanin karyar da ya yi a farko.
"Wannan kenan ya nuna jawabin da kayi a baya na k'anzon kurege ne, haka ne?"
"Haka ne Yallabai."
Ya fad'a yana mai k'ank'an da kansa.
"Then, halayyarsu da ka yaba a baya fa? Ya matsayin hakan yake?"
"Wallahi duk shiri ne Yallabai, amma a zahirin gaskiya yaran nan kowa ya san basu da kirki, haka zalika ni shaida ne a irin rashin da'arsu. A lokuta da dama, an sha kawo k'ararsu gida da k'orafin suna lalata 'ya'yan mutane, amma iyayensu su fatattaki wanda suka kawo karar tare da gargadi mai tsoratarwa"
"Amma da girmanka Malam, me sa kayi mana karya da farko? Ka kuma sani sarai yin hakan ya sab'a ma dokar kotun nan. Haka zalika yana da hukuncinshi na daban da zaka ansa."
Alkalin ya yi maganar yana gyara zamansa. Hawayen da Mal. Buba ke taryewa ne suka subuce suka fara zuba, fuskar da ya ke gani a mafarkinshi ita ya kuma gani a idanunsa da ya runtse, yayi gaggawar budewa yana sauraren Alkalin.
Hannunshi ya dora a kai, ya fashe da kuka
"Dan Allah, Dan Annabi ayi hakuri Yallabai. Wallahi bani da yadda zanyi ne, ku gafarta mun dole ce ta saka ni aikata hakan."
Wulakantaccen kallon da Barr. Hisham ya aika masa, shi ya sanya shi nadamar kallon setinshi, ya kauda kanshi da sauri, yana shafe hawayen da suke ambaliya saman dattijuwar fuskarsa.
Bayan shudewar kamar mintina biyu Alkalin na ta faman rubutu, ya d'ago yana kallon yadda Mal. Buba ke zubar da ruwan hawaye. Ya gyara zaman gilashinsa, a sa'a guda ya ji tausayin tsohon ya dira zuciyarsa, hakan ya sanya shi sallamarshi, ya wuce yana ta faman zuba godiya, yayin da shi kuma ya ci gaba.
"Zamu fita hutun takaitaccen lokaci. Idan mun dawo, zamu ci gaba a inda muka tsaya."
Ya k'arashe tare da buga kundin da ke gabansa, ya mik'e, a daidai lokacin da sauran jama'ar cikin kotun suka mik'e baki d'aya.
www.lubabatumaitafsir.com
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
Lubbatu Maitafsir
_Where's Asma'u Mtz, Missy-Missy, Ummy Danfuloti, & Fatima Sani Aminu? This is for you guys. Nd I thank you from the bottom of my heart, for the love you'd towards #DTFBIJ. Let's rock!..._
{22}
Alal hak'ik'a zuwan Mal. Buba ba k'aramin tada hankalin Barr. Hisham da tawagar Alhaji Barau ya yi ba. Ya jefa su a wata duniya ta rudani, tsantsan rikici da tunanin makomar shari'artasu baki d'aya. Jiki babu k'wari suka ci gaba da fitowa daga d'akin sauraren shari'ar. Bangaren da ya ga Jay ta dosa ya tasan ma, cikin d'an lokaci ya cimmata, ya d'an daga muryarsa wacce alamu suka nuna ba k'aramin razanar da ita ya yi ba.
"Tell me you're kidding, about your reaction earlier!"
Muryar da ta tabbatar da mamallakinta ta daki dodon kunnenta, ta haifar mata da faduwar gaba mai tsanani, ta juyo cikin rashin natsuwa tana dubansa. Tsaye yake ya zuba hannayensa a aljihu, ganin ta dakata ya bashi damar fara takawa, cikin tak'ama da tunk'aho, har ya iso inda take tsaye. Murmushin raini ya sakar mata, ya matsa daf da kunnenta ya ce
"Baki isa ki manta da agenda dinmu ba Barrister. Ko kin manta da makuden kudaden da kika danne a account dinki? Kin manta da gidan da yake shirin zama mallakinki? I'm advising you, kada ganganci da rawar kanki ya kaiki ga aikata abinda zaki yi da na sani. For that, in kina da wani kudiri, ki canja takonki kafin mu koma break."
Ya saita idanunsa a nata, yayi smirking ta gefen kumatunsa, ya wuce ya barta a tsaye.
Karkarwa kafafunta suka dauka, a sa'a guda ta tuno maganar mutumen da bata san waye shi ba, wanda ya jaddada mata cewar ya san makarantar yaranta har ma da ajujuwansu. 'Tabbas mutanen nan basa tsoron Allahnsu, haka zalika zasu iya aikata duk abinda suka ambata, koma fiye da haka.'
Tsaye kawai tayi a wurin tana kallon bayansa, har sa'adda ya bace ma ganinta.
Murmushi Barr. Hisham ya ke, har ya iso inda su Alhaji ke jiransa, Prof. Bello ya kalle shi cikin zak'uwa
"Menene abun yi Barrister? Ya kake ganin nasarartamu?"
Bakinsa ya cika da iska ya furzar, ya shafi kwantacciyar sumarsa, a karo guda ya gyara rikon da ya yima gown d'insa, sannan ya fara magana.
"Akwai matsala babba, dan ban taba zaton Barrister nan zata watsa mana k'asa a ido ba. Ban taba tunanin a duniya akwai wanda za'a yi ma alkairin da aka yi mata ya juya bayansa ba. Nd now wannan mutumen ya zo ya rusa gaba d'aya shirinmu."
Ya k'arasa tare da sauke ajiyar zuciya, sannan ya ci gaba.
"But I've an idea, wacce na tabbatar ita ce kadai hanya guda daya da zamu iya winning case din nan."
"Haba Barrister, ka san da haka kuma zaka ke bata lokacinmu, ayi abinda ya kamata mana."
Murmushin ban girma ya zubar, ba tare da bata lokaci ba ya sanar musu da kudurinsa, wanda a nan take, suka aminta da shi.
"Ina zuwa."
Alhaji Barau ya fad'a yana duban sauran mutanen, ya wuce parking lot, yayin da Hisham ya rufa masa baya, har inda motarsa ta ke. Boot ya daga, ya fito da dan k'aramin silver briefcase sai sheki yake, kafin ya maida ya rufe, ya juya yana kallon Hisham, tare da dora akwatin saman motar, ya bud'e da wadataccen murmushi kunshe da fuskarsa.
Dalar Amurika ce cike dam da akwatin, wanda shi kanshi Alhajin ba zai iya tantance adadin yawansu ba, ya kalli Hisham ya ce
"Ka je da su."
Ya rufe case din, ya mik'a masa. Murmushi ya yi, suka sha hannu, yayin da ya ansa ya juya abinsa.
****
"Na gama gabatar da duk wani evidence da ya yi mun saura Khalid, sai dai hankalina ya kasa kwanciya wallahi, jikina yayi sanyi, ina tunanin rashin imani irin na mutanen can."
Barr. Jay ce ke wannan jawabin lokacin da suke takawa tare da Khalid, wanda shi kansa cikin matukar tashin hankali ya ke.
"Amma ya kike ganin yanayin sa'artamu?"
"I can't say Khalid, sai fa abinda muka gani kawai. A yanzu haka maganar da nike maka hankalina baya tare da ni wallahi. Cuz mutanen can, sun wuce duk wani tunanin mai tunani."
Shiru yayi zuciyarsa ta zurfafa a tunanin abinda ya kamata yayi, haka itama tata zuciyar ke zinga da k'ulafucin sanar da shi halin da suka jefa ta, sai dai bata tunanin hakan zai iya basu wata nasarar da basu samu ba tun farko.
Hannunsa ya soka a aljihu inda ya ji lafiyar wayar da yake ta faman ajiya ta Mukhee, 'me ya kamata ya yi?' Ya tambayi kansa, 'ya sanar mata da wannan babban sirrin, ko ko ya jira har su ga inda shari'ar ta kwana?'
"They're after my family."
Ta tsinci harshenta da furtawa, hawaye taf a idanuwanta. Ya juyo da sauri yana dubanta,
"Ban fahimce ki ba."
Ta shafe hawayenta, yayin da ta fara yi masa bayanin komai, a k'arshe ta k'ara da cewar
"Ban san me ya kamata in yi ba Khalid. Ka bani shawara dan Allah."
"Owh Allah!"
Ya fad'a tare da dafe kansa. Ya juyo yana kallonta, har yanzu bata daina sharar k'wallan da ke zubo mata ba.
"It's okay, Allah yana tare da mu, haka kuma zan yarda da duk hukuncin da za'a zartar, na kuma tabbatar babu laifinki a ciki, sai dai ki sani wallahi bazan hak'ura ba, har sai an hukuntar da azzaluman mutanen can, ba zan hak'ura ba, har sai na ga murmushin fuskar Tareeq ya dawo kamar yadda ko wane d'a mai gata yake samu a doron k'asa. Ba kuma zan hak'ura ba, har sai na tabbatar da na cusa bakin ciki a zuciyoyin mutanen da suka jefa firgici a zuciyar yaron da bai ji ba, bai gani ba ko da kuwa hakan na nufin fallasa babban sirrin da na dad'e ina faman boyewa."
Ba tare da wani tunani ba ya fito da wayar Mukhee ya mik'a mata bayan ya bud'e sakonnin da suka yi musaya tsakaninshi da Sino.
"Wannan fa?"
Ta tambaya tana dubansa, a sa'a guda tana mai fito da idanunta waje sakamakon fahimtar inda sakon ya nufa.
"Hasbunallahu wa ni'mal wakeel! Khalid ka ce da ni ba gaskiya idanuna ke gani ba, please tell me this isn't true Khalid, please..."
Ta dago da hawaye shabe-shabe a fuskarta tana dubansa, bai kai ga ansa ko tambaya daya a tambayoyinnata ba, Hajja Fati ta iso inda suken cikin sassarfa da tashin hankali.
"Sannu da aiki Barrister. Ya kike ganin abun? Akwai nasara kuwa?"
Yanayin da tayi maganar ya jefa mamaki da kokonta a zuciyar Barr. Jay, ta d'ago tana kallonta, bayan ta share hawayen, murmushin karfin hali ta dora a saman labbanta, tausayi da jin k'an matar, suka dira a zuciyarta duk a lokaci guda. Kallon k'urilla ta tsaya yi mata, sai a sannan ta lura da canjin da aka samu a kamanninta.
"Alhamdulillah Hajiya."
Shi kawai ta iya furtawa cikin wahalalliyar murya, ta ci gaba
"Sai dai muyi ta addu'a kuma, ni kam nayi duk wani abu da ya kamata ace nayi. But, lafiya na ga fuskanki haka?"
Murmushin yak'e ta saki, ta sa hannu tana tattaba fuskan
"Na dan samu accident ne, Amma da sauki ai."
Kallon reni Khalid ya jefe ta da shi, sai dai yanayin da ya lura tana ciki ya so bashi tausayi da sauri ya kauda kai daga kallonta, ya matsa gefe domin ya samu natsuwar zuciyar da ke addabarsa da tunani kala da kala. Itama juyawa tayi ta fara kiran layin Khamis domin ya kawo mata wayar Sino ta duba, ta tabbatar da abinda idanunta suka gane mata.
***
Zaune ya samu Alkalin hannunsa rik'e da mug mai d'auke da coffee a ciki, ya kai kofin bakinsa ya kurba, a sa'a guda yana duba tarin takardun da ke gabansa. Da sallama ya k'araso ya nema ma kansa mazauni, hakan ya ba Alkalin damar dagowa yana yi masa kallon 'is everything alright?' Sannan ya maida kai ga abinda ya ke yi.
"Ehrrnmm.."
Barr. Hisham ya yi gyaran murya yana tunanin ta ina ya kamata ya fara.
"Is everything okay Barrister?"
Alkalin ya tambaya ba tare da ya d'ago ya dube shi ba.
"Fine Sir. Ina so mu d'an yi magana ne."
Sai a sannan ya ajje mug din, ya d'ago tare da gyara gilashinsa, ya sauke idanunshi cikin na Barr. Hisham yana saurarensa.
Hakan ne ya ba Hisham damar dora briefcase din hannunsa saman teburin alkalin, ya d'auki kafarsa daya, ya dora kan d'aya, labbansa kunshe da kyakkyawan murmushi.
"This is for you Sir."
Ya fad'a bayan ya bud'e akwatin, ya juyar da shi setin Alkalin ta yadda zai iya ganin komai da yake ciki.
Cikin rashin fahimta ya yamutsa fuska yana kallon kudin, a lokaci guda ya sauke dubansa a kan Hisham da ke ta faman blushing.
"What is this for?"
Ya tambaya yana mai yi masa kallon k'urilla da son fahimtar inda yanayinsa ya dosa.
"Ehrrrnmm.. Sir you know..."
Sai kuma yayi shiru.
"Ehnn.. what?"
Ya dake, ya gyara zamansa ya ci gaba
"Ka san yaran nan da ake case dinsu, yaran manyan mutane ne, d'aya a cikinsu d'an gidan Alhaji Barau ne tsohon minister of petroleum."
"And So?"
Ya tambaya tare da yarfa hannu yana kallonshi.
"Ernmm.. shine dama.. dama yace a baka wannan ba yawa ka k'ara mai a mota."
"This is crazy."
Ya fad'a cikin bacin rai.
"Do I look like a fool to you? Ka kuwa san illar abinda kake son jefa kanka? Well, ka tarkata kudadenshi ka mayar masa, nd ka fad'a mishi tankin motata baya buk'atar karin mai. Nd if you really are a lawyer, then ka yi amfani da fasaharka wurin winning case, but not this way. Find your way out Now!"
Ya karashe cikin wata irin tsawa, tare da nuna masa k'ofar fita da hannunsa.
Bai nuna girgiza ko bacin rai ba, haka ya mik'e ya rufe case din, ya balla maballin gaban suit d'inshi, ya d'auki briefcase din, ya rissina, kafin ya fice zuciyarsa na tsananta duka.
Jiki babu k'wari ya k'arasa inda su Alhajin ke tsaye, yanayinshi kawai, ya basu amsar tambayoyin da suke yawo a zukatansu.
"Don't you worry."
Ya fad'a bayan ya mik'a briefcase din ma Alhajin, sannan ya ci gaba
"We're the winners, and that's it."
"Hmmmm.. ni kam ina cikin tashin hankali gaskiya, kila har sai naga inda shari'ar nan ta tsaya, kafin."
Barr. Zainab tayi maganar fuskarta na bayyanar da alhini, sai dai babu wanda ya iya cewa komai, domin duk gaba dayansun cikin rashin natsuwar suke, hatta da Barr. Hisham din wanda yayi k'arfin halin fad'in
"Ya kamata mu wuce ciki."
Ya juya ya kama gabansa, yayin da suma suka kama tasu hanyar dan komawa cikin kotun. Bayan zamansu da kamar mintina biyar, Alkalin ya shigo, hakan ya sa duk aka mik'e, har sai da ya zauna, sannan suka koma mazauninsu.
Bayan kowa ya nitsa, Alkalin ya kuma bada damar ci gaba, Jay wacce har yanzu bata cikin sukuni, ta mik'e tana fad'in
"Ina rokon alfarmar kotu da ta bani dama domin gabatar da shedata ta k'arshe."
Kallonta Barr. Hisham ya yi cikin salo na firgitarwa, a k'asar zuciyarsa yana tunanin me take da shi wanda zata gabatar kuma?
"Kotu ta baki dama."
Da haka ta fito ba tare da ta bi ta kan kallon da Hisham ke watsa mata ba, ta iso gaban kotun, sai a lokacin ta ji wata kwarin gwiwa ta sauko mata cikin dan lokaci.
Wayoyin da ke hannunta guda biyu ta daga, kafin ta fara magana
"Wannan wayar Mukhtar ce, wato Yayan Tareeq, wannan kuma ta abokinshi ce, Hassan Alhaji Barau da ke nan tsaye gaban kotu wacce aka aiko mun daga ofishin yan sanda."
Ta hadiye yawun da ya tokare wuyanta, sannan ta ci gaba.
"A ranar laraba, ashirin da biyar ga watan December na shekarar da ta gabata, da misalin karfe goma dai-dai na dare, Hassan da Mukhtar sun yi musayar sakonni, wanda alamu suka tabbatar da sakoninnasu na da alaka da abinda ya faru da Tareeq a wannan dare. Ina rokon alfarmar kotu data bani dama, domin mu ji abinda sakonnin suka kunsa."
Da hannu Alkalin yayi nuni, alamar kotu ta amince mata. Hakan yasa ta juya ta mik'a wayar Mukhee ma Registrar.
Bai bata lokaci ba, ya gyara tsayuwarsa, a sa'a guda ya fara magana.
"Sino, shine sunan da ke rubuce a jikin number sakon da zan karanta, wanda ya fara da cewar: 'Ya ne? Kaga mun taka sa'a ko? Muna ajje ka gida muka ci karo da Tareeq. An gama komai Baaabaa.' Shi kuma wanda aka tura ma sakon ya mayar da ansa kamar haka: 'ina fatan dai bai gane ku ba?' Sai Sino ya dawo da ansa cewar: 'Hell no, clean job nike fad'a maka.' Mai wayar ya tura sakon smiley mai alamar jinjina, sannan ya k'ara da cewar: 'Zai gane mu ba tsarar yinshi ba ne.' Iyakar abinda ke rubuce a wannan waya ta hannuna kenan."
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!"
Ita ce kalmar da da yawa daga cikin mutanen cikin kotun suke maimaitawa, daga ciki kuwa, hadda Hajja Fati wacce ta juya tana kallon bangaren da Mukhee ke zaune. Kanshi a k'asa bashi da niyyar dagowa, daga haka kuma tana iya hangen tsananin firgici da gagarumin tashin hankalin da zuciyarsa ke ciki.
"Order in court..."
Alkali ya fara maimaitawa kasancewar surutunnasu na neman wuce gona da iri.
Registrar ya mik'e ya isar da wayar ma Alkali, sannan Jay ta ci gaba.
"Ina da tabbacin Hassan ya goge nashi sakonnin ne, sakamakon jin da yayi yan sanda na nemanshi, wannan ya sa ko da aka bincika ta shi wayar, ba'a samu komai ba a akwatin adana sakonninshi."
Ta isar da wayar ga alkali, sannan ta ci gaba.
"My Lord. Da wadannan tarin hujjojin da na gabatar, ina rokon alfarmar wannan kotu mai adalci, da tayi adalcinta ga wanda aka zalunta. Ta bi ma Tareeq hakkinsa, ta hanyar hukunta azzaluman nan da ke tsaye gabanta."
"Objection My Lord."
Barr. Hisham ya fad'a cikin daga murya, ya mik'e daga teburinsa ya fara magana.
"Ta ya ya hankali zai dauki maganar da Barrister ta zo da ita? Haka kawai bamu san hawa ba bamu san sauka ba, sai ta zo mana da maganar wasu sakonnin? My Lord idan mai fadar magana ya kasance wawa, tabbas wanda ke saurare ba zai bi layinshi ba. Ina so kotu ta tuna cewar Mukhtar din da ake magana a nan fa Yayan Tareeq ne uwa d'aya, uba d'aya. Dan haka ya kamata kotu ta yi duba zuwa ga abun, ta kuma fahimci cewar wata lalacewa ce zata sa dan uwan da kuka fito ciki daya ya iya aikata wannan mummunan alkaba'in gare ka? Sam! Wannan ba maganar dauka ba ce, da alama kuma Barrister bata cikin hayyacinta... Dan haka ina neman alfarmar kotu da tayi watsi da wannan shedar ta Barrister Jameela."
Murmushin takaici ta zubar, kafin ya kai aya tayi gaggawar tare shi da cewa,
"Wannan waya dai ta tabbata ta Mukhee, haka zalika wannan dayar mallakar Sino ce, idan kuma har kotu na san ta tabbatar da gaskiyar abinda na gabatar, za'a iya kiran number d'aya daga ciki, ina ga ta haka ne kawai gaskiya zata yi halinta."
Babu gardama Alkalin ya mik'a wayoyin biyu ga registrar, ya kuma umarce shi da yayi kiran layin Sino wanda cikin yan seconds wayar ta dau k'ara, tare da nuna sunan Mukhee baro-baro a jiki.
Murmushin birgewa Jay ta zubar, a sa'a guda jikin Hajja Fati da na Alhaji Badaru har wata tsuma ya ke yi, haka zalika shi kanshi Mukheen, bai taba tunanin rana irin wannan zata zo ba.
"Ina Mukhtar d'in? Is he in court?"
Muryar Alkali ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya tsunduma ya na mai k'ank'an da kai, har sai da ya kuma maimaita tambayar, sannan ya mike jiki babu k'wari, ya iso gaban kotun idanunsa tamkar an soya gyada, sai dai duk wanda ya kalle shi ya san zuciyarsa na cike taf da tsantsan alhini da tashin hankali.
"Kai ne Mukhtar?"
Judge ya tambaya tare da adjusting zamansa.
"Eh ni ne."
Ya bashi ansa kanshi a k'asa. Nuni ya yi mishi da witness box, ya shiga ya tsaya, har yanzu ya gagara d'ago da kanshi.
"Samsung galaxy grand prime, model Sm-G530h, ash in color. Is it your phone?"
Muryar Alkalin ta daki dodon kunnensa, ya d'ago a hankali, ya sauke idanunsa kan wayar da registrar ke mik'a masa, ya ansa ya duba, tare da gyada kai yana fad'in
"Wayata ce, amma ta dad'e da bacewa."
"A ranar yaushe ne ta bace kenan?"
"Uhnmm.. gaskiya bazan iya tuna ranar ba."
"Wadannan sakonnin da ke ciki fa? Zaka iya tuna ranar da ka rubuta su?"
"Ehh? Ni gaskiya bani na rubuta su ba."
"Waye ya rubuta su to?"
"Ni wallahi ban sani ba. Wayar tawa fa ta dade da bacewa."
"Amma ai ka san wanda aka tura ma sakon ba?"
"Eh abokina ne."
"Shi kuma yaron da ake magana a kanshi fa?"
"Kanena ne."
"Then, ka fada ma kotu iyakar gaskiyarka. Menene manufar sakonnin da suke cikin wayarka?"
A razane ya d'ago yana kallon fuskar Alkalin, babu annuri sam, ko alama, sai dai duk da haka bai yi zaton zai iya magana haka cikin daga murya ba. Yan hanjinsa ne suka murda, take zuciyarsa ta tsinke, hawaye masu zafi suka fara shatata daga kwarmin idanunsa.
"Ni wallahi ban ce su yi raping d'insa ba."
Yayi maganar cikin muryar kuka, yana daga hannunsa alamar rantsuwa da iyakar gaskiyarshi.
"Damn it!"
Muryar Barr. Hisham ta ansa kuwwa a cikin kotun, wanda alamu suka nuna bai san sa'ar da maganar ta bayyana a fili ba.
"Me kace suyi mishi then?"
Alkalin ya tambaya yana mai sassauta muryarsa, tare da tallabe habarsa da hannun da bironsa ke rik'e.
Cikin kukan ya fara jawabi,
"Ni kawai.. Ni kawai, nace ne su koya mai hankali, saboda ya raina mu ni da abokaina, duk sadda zai ganmu tare sai yayi abinda zai bata rayukanmu. Amma wallahi ban ce su yi raping d'insa ba. Wallahi ka ji na rantse."
"Laaa ha ila ha Illallahu Muhammadar rasuliLlahi Sallallahu Alaihi wa Sallam."
Ire iren kalmomin da mutanen cikin kotun suke maimaitawa kenan, Alhaji Badaru kam ya kafe idanunsa a kan Mukheen, zufa kawai ke yanko masa ko ta ina.
"Ai dai kai kace mu koya masa hankali."
Muryar Sino ta karad'e kotun, har ma ta disashe surutan da sauran jama'ar suke yi.
Cikin tsananin fushi yayi maganar yana nuni da Mukhee, dan dama tun daga ranar da aka tafi da su ya kullace shi a k'asan zuciyarsa.
"Ai dai ni ban ce kuyi raping nasa ba."
Mukhtar ya fad'a yana kallon setinsu, yayin da kowa ya tsagaita, duk suka mik'a hankulansu ga abinda suke fad'a.
Ganin haka ya sa Barr. Jay ta koma mazauninta, a sa'a guda ta rungume hannayenta tana kallon ikon Allah.
"Ni wallahi ba ruwana. Raka su kawai na san na yi."
Mubee ya fara nashi jawabin shima, yayin da Barr. Hisham ya tallabi kanshi, abun duniya da takaici sun hane shi furta ko da kalma d'aya.
"Order.. order in court."
Alkali ya fara bubbuga kundin gabansa, cikin d'an lokaci aka samu daidaituwar wurin, sannan ya kalle su yana fad'in
"Can someone tell me what's going on here?"
Cikin gaggawa Mubee ya fara magana, ba don komai ba, sai dan ganin reshe na neman juyewa da mujiya, saboda komai a kan idonshi aka yi, matsawar kuma basu yi winning case din ba, to fa yana ji yana gani za'a tusa keyarsa a tura prison. A yadda Ya dandani azabar wurin ta yan kwanakin da ya yi, alal hakika, ba zai so ya kara komawa ba. Asali ma, ko da makiyinsa, ba zai so ya riski kansa a irin wurin ba. Gyaran murya ya yi, a karo guda ya lashi labbansa da suka gama bushewa, sun yi fari fat, tamkar an shafa mai farar kasa, ya kalli Alkalin cikin karkarwa, sannan ya fara magana.
"A ranar laraba ashirin da biyar ga watan December na shekarar da ta gabata, bayan mun fito daga gidan Alhaji Badaru wato mahaifin Tareeq, mun shiga gari muna dan zagayawa muna taba hira, har muka gangaro kan irin rainin da Tareeq ya yi mana mu da yayanshi. A nan ne Mukhtar yake cewa yana neman yaran da zai sa su koya ma Tareeq hankali, yayin da Sino ya ce ya bar komai a hannunsa. Cikin sa'a bayan mun dawo mun sauke Mukhee a gida, sai muka hangi Tareeq yana tafiya, hakan yasa muka yi parking motar, muka fita muka bi bayansa, muka kama shi tare da daure idanunsa, sannan muka saka shi a mota zuwa wani uncompleted building. Ni dai har aka je wurin ban san me za'a yi ba, har sai da naga Sino ya cire wandonsa, ya fad'a mishi. Bayan ya gama ya umarci Deeni shima ya yi. Daga nan muka d'auke shi, muka ajje a gefen gidansu muka kama hanyarmu. Ni wallahi ban mishi komai ba."
"Ba wani, ai dai kaima kabige mishi kafa, ka kwantar da shi sa'adda ya k'i kwanciya."
Deeni ya fad'a cikin sheshshekar kuka yana kallon Mubarak.
"To ai ni taimaka muku ne kawai nayi, naga zai baku wahala. Daga nan na k'ara yi mishi wani abu ne?"
Ya tambaya cikin hayayyak'owa, yana kallon Deenin.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un. Allahumma ajirni fi Musibati, wa akhlifni khairan Minha."
Wadannan ne kalmomin da Barr. Jay ta rink'a nanatawa, wasu k'walla masu zafi da kuma sanyi duk a lokaci guda suka fara ambaliya a fuskarta. Gagarumin kukan da Hajja Fati ta saka, shi ya nemi dagula hankalin sauran jama'ar wurin, hakan yasa judge ya ce a fita da ita, kasancewar yadda take kururuwa, tana kwace jikinta a hannun matan da suka rik'e ta.
Sai da Alkalin yayi da gaske, sannan surutan mutanen ya tsagaita, ya gyara gilashinsa, yana duban tsanaki ga Mubee yana fad'in
"Kai da aka yi wannan duk a gabanka, me sa baka sanar da wani ba? Kuma tun da kaga an daure masa fuska an saka shi a mota ai kasan in ba mugun abu ba, ba abinda zai sa ayi ma mutum haka. Duk da wannan ma, baka hana ba ko ka tambaya, a'a sai ma taya su wurin buge kafarshi. Ko?"
"Ni wallahi ba da niyya na yi ba Yallabai."
"Then, me sa baka fada ba bayan ka fahimci abinda ya faru? Har sai da ka bari yan sanda sun sha wahalar kama ku, muma nan ka zo bata mana lokaci?"
Shiru yayi yana fitar da wasu irin hawaye masu zafi, yana ji a kasan zuciyarsa ina ma zai iya dawo da lokacin baya. Tabbas da shi zai yi azamar sanar ma yan sanda, ya tabbata duk haka da bata faru da shi ba.
Ganin bashi da niyyar magana ya sanya Alkalin girgiza kai cikin takaici, ya juya yana kallon Jay
"Prosecuting counsels ko kuna da sauran abun cewa?"
"No My Lord."
Jay ta yi maganar cike da tsantsan farin cikin da ya kasa boyuwa a saman fuskarta. Ya juya ta bangaren da Hisham ke zaune,
"Does the Defense wants to call further witnesses or have something to add?"
Kanshi a kasa, fuskarsa cike da borin kunya ya shafi tarin sumar da tayi ado a gare shi yana fadin
"No Your Lordship, Defense rest its case."
Tsi-tsit kake jin kotun, babu karan komai, sai yan surutan mutanen da ke tashi k'asa-k'asa, yayin da Alkalin ya dukufa a dogon rubutu mai tsanin tsawo. Barr. Nasib ya rankwafo fuskarsa cike da annashuwa yana yin k'us-k'us ma Barr. Jay, suka murmusa a tare.
Da shudewar wani dogon lokaci Alkalin ya dago tare da daidaita zaman gilashin fuskarsa, yana mai ci gaba da kallon jama'ar da ke zaune gabanshi, ya fara jawabi.
"Having listened to those submissions of the defense counsel, and that of the prosecuting counsel. The prosecuting counsel have been able to proof all evidences of rape against the accused. And they're found guilty as charged. So, today, 13th of March, 2017. I, Hon. Justice A.D Mansoor, zan yanke hukunci tsakanin Director of Public Prosecution da ke k'aran Hassan Alhaji Barau, Mubarak Garba Bukar & Zahraddeen Bello Hassan."
Ya shafi gefen fuskarshi tare da gyara zamansa, sannan ya ci gaba
"This honourable court have pass the judgement as follows: -Hassan da Zahraddeen, kotu ta kama su da laifin Child Sexual Abuse and Rape, wanda ya ke a Section (284) na Penal Code. They're here by sentenced to fourteen (14) years imprisonment, tare da taran nera dubu dari biyar ga kowannensu (500k.)
-Mubarak wanda ya taya su a wurin aikata laifin kotu za ta hukunta shi a kan laifin Abetment da akayi Defining a Section (83) na Penal Code. Therefore, he's sentenced to five (5) years imprisonment.
-As of Mukhtar, wanda shine jagoran komi shima kotu ta kama shi da aikata laifin Abetment wanda yazo a Section (87 & 88) na Penal Code, kamar yanda ya zo a dokance za'a yanke masa hukunci ne dai-dai da wadanda suka aikata, cuz a idon kotu, shine k'wak'walwa mai tunanin, yayin da su kuma criminals din, sune hannuwan da suka aikata (He is the brain and they are the hands). And For abetment, Anything that happens he is liable to it. For that, kotu ta yanke masa hukuncin fourteen (14) years imprisonment tare da taran nera dubu dari biyar dai-dai (500k)."
Sai da ya takaita, sannan ya ci gaba.
"Mal. Buba da ya bada false statement a gaban kotu wanda ya saba ma sashi na (158) sakin layi na (1) na Penal Code, saboda duba da yanayi da halin da ya sanya shi aikata laifin kotu tayi masa sassauci zai biya ta taran kudi naira dubu d'aya (1k). Mai k'ara da wanda ake k'ara, suna da damar daga shari'ah idan hukuncin da kotu ta zartar bai gamshe su ba. I rise!"
Ya k'arashe bayan ya buga gudumarsa, ya mik'e a sa'ar da mutanen da ke zaune duk suka mike suna fad'in
"COOOOOUUUUURRRRRT!!!"
www.lubabatumaitafsir.com
[3/15, 8:12 PM] 🌸Asmart🌸: DUNIYA TA FI BAGARUWA IYA JIMA!
Lubbatu Maitafsir
{23}
Wata irin sowa mai had'e da gunjin kuka, salati da sallallamin jama'a ne ya karad'e gaba d'aya kotun bayan fitar Alkali.
Mukhee, Sino, Deeni, da Mubee kuka suke irin mai tattare da asalin nadama da da na sanin da suka riski yarintarsu a ciki, haka ma iyayensu kaf babu wanda bai zubar da hawaye ba.
Alhaji Badaru kam da alama zautuwa yayi, dan duk wannan bidirin da ake k'ala bai iya furtawa ba, sai dai ya damu zuciyarsa da tambayar 'shin wai yana ina har irin wannan k'iyayyar mai zafi ta wanzu tsakanin ya'yanshi? Yana ina har Mukhtar ya yi lalacewar da yake had'a abokai da 'yan luwadi? Kuma yana ina har tarbiyyar gidanshi ta rugurguje, tayi faduwar warwass, wacce alamu suka tabbatar da gyaruwarta sai ikon Allah!'
"Baba za su ta fi da ni."
Muryar Mukhee cikin zazzafan kuka ita ce ta dawo da Alhajin daga kasurgumin kogin tunanin da ya ambula.
Ya kalle shi, duba na tsanaki, ya kauda kansa, domin a zahiri ya kasa gaskata abinda ke wakana a gaban idanunsa. Haka kuwa yan sanda suka tusa keyarsu, suka fito da su, yayin da wani sabon babin kukan ya k'ara farkewa tsakanin iyayen su Deeni da su d'in kansu. Hajja Fati wacce tun da aka fito da ita take suma tana farfafowa, ta kurma wani gagarumin kuka, tana fad'in
"Ni ce nan na jefa zuri'ata a halin da suka tsinci kansu. Ya Allah! Da wane ido zan kalli yarana?"
Ta mik'e da gudu, ta isa inda Mukhee ya ke ta d'aya hannu, ta d'auke shi da mari, ta k'ara da
"Ka cuce ni ka cuci zuri'armu baki d'aya Mukhtar. Sai dai ba zan yi maka baki ba, Allah ya shiryar da kai, da sauran 'ya'yan musulmi baki d'aya."
Daga haka bata kuma cewa komai ba, ta koma gefe ta duke tana kuka mai matukar d'aci a k'asan zuciya.
Barr. Zainab da Haj. Kareematu ma kukan suke, tamkar su cire idanunsu su jefar, yayin da zuciyoyin iyayennasu maza ke cikin bacin rai da tashin hankali, duk kuma gaba d'ayansu suna rantsuwar d'aga k'aran koda kuwa zai kai zuwa supreme court ne.
Haka suna ji suna gani, aka tura yaran a motar prison, guardrobbers suka rufa musu baya, har suka bace a harabar kotun. Kuka mai tsanani suka kuma fashewa da shi, dak'yar da taimakon Mal. Liman kakan Deeni, ya lallaba su suka shiga mota, suka d'auki hanyar gida.
Khalid wanda farin cikin samun cikar burinshi, da kuma bakin cikin kama Mukhee suka mamaye zuciyarsa, ya kamo Alhaji Badaru, suka fito ya saka shi a mota, sannan ya koma domin fito da Hajja Fati, inda ya ci karo da ita tana neman Zulaiha.
"Zulaiha Khalid. Ina ta nufa? Ban ganta ba."
"Ki kwantar da hankalinki dan Allah, Zulaiha ai ba bata zata yi ba, watak'ila ta wuce gida fa, dan tunda aka fito break din nan ban k'ara ganinta ba."
Ya bata ansa yana mai mik'a mata gyalenta da ta yakice a gefe, ya dora da cewar
"Ki taimaka ki tashi mu je please."
Bata iya cewa da shi komai ba, ta mik'e tana had'a hanya, har suka iso inda motar take, ta shiga baya ta zauna, tare da tallabe kanta da ke matukar sara mata tana ci gaba da rera kukanta. K'aran kiran wayar Alhaji Badaru sosai ya takura mata, a sa'a guda ya gagara ansa wayar shi kuma, har sai da ta katse, aka kuma kira a karo na biyu, sannan ya dauka ya dora a kunnensa ba tare da yace komai ba.
Cikin zakuwar son sanin abinda aka fad'a ta wayar ya zabura yace
"Me ya faru da Hajja Fatin kuma?"
"Ka dai duba ka gani Alhaji."
Aka ce da shi ta cikin wayar, ya kashe a kagauce, ya fara binciken whatsapp dinshi, duk kuwa da ba cikin hayyacinsa ya ke ba.
****
Cikin matsananciyar murna ta fito, yayin da yan jarida da masu d'aukar labarai suka yo mata chaaa, kowa da kalar tambayar da yake jifarta da.
"Me zaki ce game da wannan rana kasancewarki matashiyar barrister wacce ta gagara da Barr. Hisham ta kuma yi mishi mummunan kadi a irin wannan shari'ah mai matukar hadari da ban tsoro?"
Murmushi mai tsada ta zubar, ta juya tare da kai dubanta bangaren da Hisham ke tsaye ya kafe ta da manyan idanunsa da suka canja launi tun a cikin kotun. Ta dawo da dubanta ga matambayan, ta gyara rikon gown dinta ta ci gaba
"Babu abinda zan ce wanda ya wuce Alhamdulillah, domin ba dabarata ba ce, ba kuma wayona ba ne, gaskiya ce ta yi halinta."
"Wace shawara za ki ba iyaye irin na yaron da kika jagoranci shari'arshi? Na ji labarin ba da sa hannunsu maganar ta iso ga alkali ba."
Ta shafi gefen fuskarta, tabbas wannan tambaya ce da koda ba su yi mata ita ba, zata iya siyen shafi a jarida, ta rubuta article domin fadakar da mutane. Ta kalle su cikin sanyin murya ta ci gaba da cewa
"Ina kira ga iyayen yara maza da mata da su saka idanu ainun a kan yaransu, ina kuma shawartarsu da idan har kaddara irin wannan ta fad'a a kan yaransu, to su daina rufe ta, dan yin hakan shi ke k'ara haifar da yawan azzaluman a bayan k'asa. Ina kiran iyaye da babbar murya da su tsaya tsayin daka wurin tarbiyyar yaransu, su kuma rinka fito da irin wannan maganar domin sama ma wadanda aka zalunta din hakkinsu. Su kuma sani cewa, a koda yaushe, mu din nan a shirye muke, dan ganin mun bi ma yaran da aka keta ma haddi hakkinsu. A k'arshe ina rokon Allah ya yaye bakin duhu, firgici da tashin hankalin da aka jefa a zukatan dukkan wasu rape victims da ke kwana su tashi da ciwon abun a kasan zukatansu. Allah ya kare mana zuri'armu, ya kuma shiryar da mu baki d'aya. Thank you."
"Yaushe kike da wata shari'ah nan gaba?"
"Shin Barrister tana da aure?"
Ire iren tambayoyin da suka ci gaba da yi kenan, sai dai bata da lokacinsu, bata kuma tsaya ansa ko da d'aya daga ciki ba, kasancewar Habibinta da ta hanga, wanda murmushinsa ya disashe mata ganin sauran jama'ar gabanta.
Ta tako a tsanake ta iso inda yake jingine da motarta, tana jifarshi da wani sassanya kallo wanda yake sanyaya zuciyarsa a lokuta da dama.
Shima kallonnata yake da murmushi, ba tare da ya ansa gaisuwar da take mishi ba, ya mik'a mata goran ruwan da ke hannunsa yana fad'in
"I'm proud of you JAMEELA! Allah ya k'ara daukaka mun ke."
"Amin amin Ya Sadic."
Ta fada lokacin da wayanta ya d'auki k'ara ta fitar, ta duba da murmushi, ta ansa ta dora a kunnenta tare da fad'in
"I miss you Handsome nawa. Ya aka yi?"
"CONGRATULATIONS MAMMY!...."
Muryar yaranta duk su hudun ta karad'e kunnunwansu, fuskarta na bayyanar da farin ciki ta tambaya
"How do you know I win?"
Jafar ya anshe da fad'in
"Yanzu muka ganki a t.v ai, come home soon Mammy, please."
"I'll Sweetheart. See you guys in a bit."
Ta kashe tana kallon SS da yake ta blushing mai matukar kayatarwa. Ya bud'e mata motan ta shiga, ya zagaya ya shiga nashi bangaren, ya tada motan suka tafi.
*****
Numfashin Alhaji Badaru ne ya fara kaiwa da kawowa sakamakon cin karo video d'in da aka tura masa ta Hajja Fati. A k'asa anyi rubutun da ya matukar ja hankalinshi, mai cike da kalaman batanci da tsinuwa. Ya wurga mata rinannun idanunsa da suka dade da canja launi, tare da dora wayar saman hannunta ya ce
"Wata tsiya nike gani haka Hajja Fati? Ki ce da ni ba gaskiya idanuna ke gani ba dan Allah."
Cikinta ne yayi wata murdawa, dan yanayinsa ya canja mata daga shiru-shirun mijinta, zuwa wani bijimin zakin da zuciyarsa ta kwadaitu da nama bai samu. Haka zalika tunda ta ji ya ambaci sunanta a cikin wayarshi, hankalinta bai kwanta mata ba.
Dai-dai sa'ar da suka iso gida, bai jira Khalid ya tsayar da motar ba, ya fito cikin zafin nama, ya bude bangaren da Hajja Fati ke zaune, ya finciki hannunta, ya fito da ita ya wurgar a k'asa, sannan ya bi ta ya wanka mata lafiyayyen mari har guda biyu.
Bugunta ya fara yi ko ta ina, dakyar Khalid ya iya shiga tsakaninsu, ya koma da baya yana huci yana fad'in
"Ka barni in kashe ta Khalid, ina amfanin zama da fasik'a irin wannan? Kin ci amanata wallahi. Kin cuce ni kin gama da rayuwata!"
Ya juya cikin kunan rai, idanunsa na zubar da hawayen takaici da nadama, ya banka kofar palon ya shiga, yayin da idanunsa suka suka yi tozali da Zulaiha da ke tsaye daga ita sai wata yar ficiciyar rigar da ko gwiwanta bai kai ba, a gefenta wani matashi ne mai shekarun da basu haura nata ba, sai zufa yake, daga shi sai boxers din da ya taimaka wurin rufe tsiraicinshi.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un..."
Bakin Alhaji Badaru ya fara furtawa, bai kai k'arshe ba ya silale ya fad'i a tsakiyar palon.
****
A babban palon gidan Alhaji Barau suka yada zango, ya sauke wayarsa daga kunne bayan ya gama ansawa. Ya juyo yana kallonsu. Bud'e bakinshi zai fara magana, Mal. Liman mahaifin Prof. Bello ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu yana fad'in
"Ya isa haka."
Kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce
"Kamar ya ya isa Malam? Ka tuna rayuwar yaranmu da ke cikin gagarumin hatsari mana. Ta ya za'a ce baza mu bima yara hakkinsu ba? Wallahi bazan iya runtsawa ba, har sai na tabbatar da na kubutar da yarona daga halin da aka jefa shi."
Gyaran murya yayi bayan ya gama saurarenshi, ya d'ago ya sauke dubanshi a kan su duka ukkun sannan ya fara magana.
"Ku ji tsoron Allah duk gaba d'ayanku. Ku tuna idan kun daukaka k'ara kun samu biyan bukatarku, akwai ranar da za'a tsaya gaban Allah, mai iko akan komai, wanda ya ke da masaniyar komai da ya wanzu a bayan k'asa. Haba jama'a, yaran nan fa da bakinsu suka ansa lefinsu, mu gode Allah da shari'ar ta tsaya a haka mana. Da ace kotun musulunci suka kai maganar, kuna tsammanin yarannaku zasu k'ara shakar iskan duniya zuwa yanzu?"
Shirun da suka yi ne ya bashi damar juyawa yana kallon Prof. Bello.
"Kada ka bani kunya mana. Ina tarin iliminka na addini da na bokon da kake tutiya da shi? Ina ka kai tunaninka da har son zuciya ke shirin jefa ka a halaka kana ji kana gani?"
Shiru yayi shima tare da k'ara yin k'asa da kanshi, hakan ya ba shi damar ci gaba
"To bari in tunatar da ku abinda Allah (SWA) ya ce game da mutanen da suke aikata halayyar al'ummar Annabi Loot."
Ya gyara zamansa, ya kuma fuskance su da kyau sannan ya fara da cewa
"Allah Mai Girma da Daukaka a cikin al-Qur'ani yana cewa:
"A lõkacin da Lũɗu ya ce da mutãnensa: "kun kasance kunã jẽ wa alfãsha, wacce bãbu kõwa da ya gabãce ku da ita daga halittu. Hakika kuna jewa maza da sha'awa, maimakon mata wadanda Allah Ya halatta muku. Tabbas kun kasance cikin mutane masu 6anna a doron k'asa." Babu jawabin da ya kasance daga mutanensa face suka ce: "Ka fitar da su daga alk'aryarka, domin tabbas su wasu mutane ne masu da'awar tsarki."
Sai muka tseratar da shi da iyalansa, face matarsa da ta kasance cikin masu wanzuwa.
Kuma muka yi ruwa a kansu da wani irin ruwa mai tsananin azaba, dan haka ku duba yadda alk'iblar ma6annatan ta kasance." Surah al-Araf, aya ta tamanin zuwa tamanin da hudu. (80-84.)
Sannan kuma Ya k'ara cewa:
"Mazaje biyun da suka kasance masu aikata alfasha, to ku cutar da su. Sai dai idan har suka tuba, suka kyautata halayensu, sai ku kauda kai daga gare su. Domin tabbas, Allah Ya kasance mai karbar tuba. Mai rahma, kuma mai jin k'ai." Surah al-Hijr, aya ta saba'in da hudu (74)
Haka kuma Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi yana cewa "duk wanda kuka samu yana aikata luwadi, (halayyar mutanen Annabi Loot), to ku kashe wanda yake yin, da kuma wanda ake yi wa d'in. Wannan hadisi ne sahihi. at-Tirmidhi no.152
A wani hadisin kuma yace "idan namiji ya nemi dan uwansa namiji, ku kira su mazinata, haka idan mace ta nemi yar uwarta mace, suma mazinata ne. Haka kuma a duk lokacin da namiji zai nemi dan uwansa, al'arshin Allah yana girgiza, dan haka ku kashe wanda ya nema din, da kuma wanda ake neman."
Bugu da kari, Abu Dawud ya ruwaito cewar, manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi yana cewa "idan saurayi wanda bai taba aure ba yayi committing sodomy (luwadi) ku jefe shi da duwatsu har sai ya koma ga mahaliccinsa." Abu-Dawud no.4448.
A wani hadisin kuma yace "Duk mutumen da ya aikata luwadi ga dan k'aramin yaron da bai mallaki hankalinsa ba, zai tabbata cikin tsananin kazanta, (janaba) wacce ko da zai tara gaba d'aya ruwan duniyar nan ba zai iya wanke ta ba. Zai kasance cikin fushi, da kuma tsinuwar Allah ta'ala (zai raba shi da ko wanne jin dad'i na duniya da na lahira) sannan kuma ya jefa shi a wutar jahannama, mafi yawaitar azabobi."
Ya numfasa, yana ci gaba da kallonsu
"To ku duba irin alkaba'in da ke tattare da wannan abun, ku kuma tuna cewar yaran nan da fatar bakinsu suka amsa laifinsu, a matsayinku na iyaye, me ya kamata kuyi bayan zubar da hawaye da kuma nema musu gafara da shiriya a wurin Allah? Kuyi tunani da kaifin basira irin ta cikakken dan Adam mana. Ku natsu, ku kuma san me ya kamata kuyi."
Daga haka ya mik'e ya bar musu palon, a lokaci guda zuciyoyinsu suka tsunduma a tarkon nadama da da na sanin rashin bada ingantacciyar tarbiyya ga yaransu. Wanda shine ya jefa su a halin da suka riski kansu.
Masha Allah, Alhamdulillah. A nan Allah (SWA) mai kowa, mai komai, Ya bani ikon kawo k'arshen wannan takaitaccen labari. Kurakuren da na yi a ciki, Allah Ya gafarta, ya kuma sa jama'a su amfana da abinda ke ciki.
For your suggestions, corrections or anything, do not hesitate to contact me via ilubiee3@gmail.com
Firstly, #DTFBIJ is a work of fiction, as I already stated earlier. So, any resemblance to any person, living or dead, is purely coincidental, nd not intentional.
Secondly, I humbly thank you BARR. JAMEELA DANJA, as you're THE SECRET BEHIND DTFBIJ! I really appreciate all the hard work you've done to help me. Words are powerless to express my gratitude, but I'll forever be beholden to you. Please do accept my vehement protestations of gratitude. THANK YOU one more, for always being there whenever i needed you. I'm eternally grateful for everything. Allah ya kawo miji na gari.
To the lovers outta there, I truly appreciates y'all. What would Lubbatu do without you guys? Y'a generosity overwhelms me Wollah. ILY'all to the moon round nd back.
To read the complete story, ku garzaya www.lubabatumaitafsir.com or www.wattpad.com/iLubieee.
Na gode
Na gode
Na gode
Da kaunarku. Lubbatu na kaunarku y'all. Y'a too many to be mentioned!
Sai kun ji ni dauke da wani sabon, wanda ya zo da SABON SALON da ya taka na DTFBIJ. Ku tare ni cikin HAWAYEN ZUCIYATA!
©Lubabatu Maitafsir, 2017.
ASMART