Hannu tasa ta jawo pepeyin jin yana ce mata.
"Kici kije da gudu ki kira Mata, tazo in gaya mata, su Ya Giɗi sun kusa dawowa ta dena kuka, anji lbrin inda suke".
Rufe akoshin tayi kana ta miƙe da sauri tace.
"Da gaske ya Ba'ana an ji inda suke?".
Cikin haɗe fuska yace.
"Na taɓa yimiki ƙarya ne?".
Da sauri ta jujjuya kanta kana tace.
"Bari inje in gaya mata tazo sai inci naman a gida".
Da sauri yace.
"A a jeki kirata, in tazo sai ki tafi da naman, kije kuci keda Ummiy da Bappa da ita ƙawar Mata, ita kuma zan bata nata a nan".
Ai tana jin hakan ta juya ta tafi, da sassarfa.
Tana isa gida, ta kamo hannun Shatu, cikin haki tace.
"Adda Shatu taso, taso muje ya Ba'ana zai gaya miki inda su ya Giɗi suke, yace anji lbrinsu".
Wani irin zabura tayi, hakama Rafi'a dake bakin ƙofar kitchin ɗinsu.
Cikin tarin kaɗuwa tace.
"Ke Junainah, kada kiyi mana ƙarya".
Cikin haki tace.
"Wallahi tallahi, haka yace min zo muje kiji".
Da sauri ta kamo hannun Rafi'a tace.
"Adda Rafi'a kema zo muje tare".
Cikin jin daɗi Rafia tace.
"A a Junainah kuje, Ni kuma kafin ku dawo nayi mana abinda zamuci, da sauri tace.
"A a Adda Rafi'a ki bari kar kiyi girki, Innar ya Ba'ana ta aiko mana gasassun zabbi yanzu zan amso mana su sai muci".
Murmushi tayi kana tace.
"To sai kinzo".
Ita kam Shatu tuni ta fita, ta nufi Garkensu Ba'ana.
Ita kuwa Ummiy ido kawai ta zuba, musu tana son ta kira Shatu ta hanata zuwa amman ta kasa.
Ita kuwa Rafi'a kitchin ɗin ta shiga.
A can garkensu Ba'ana kuwa.
Yana hango Shatu, ya saki wani irin ajiyan zuciya, ido ya zuba mata,
Gaba ɗaya ta rame tayi fiyau da ita, fuskarta tayi jazir alamun yawan kuka, kana, ga kumbura da idanunta sukayi.
Da sauri take tafiya, sai dai tanayin takun a hankali ne, doguwar rigace a jikinta ta atampa, hijabi da ta saka wanda yazo mata har guiwa.
Ta ɗan ja hulan kan hijabin dan ya ɗan kare mata kumburarrun idanunta.
Wani zafi yakeji a ransa, Allah ya sani baya son ganin Shatu cikin damuwa duk ƙaƙantar-ta, yakanyi komai na zalumci, amman baya yi kan Shatu, shi kanshi ya yarda shi tantirine, azzalumi, kuma mugu, hakanan kuma ya yarda so gsky ne kuma so ɗaya ne tak kuma ya sani duniya ta sani yana son Shatu,
yana son sama mata farin ciki a rayuwarta, yana son su rayu tare. Shiyasa yake son rabata da kowa nata wanda suke ƙoƙarin ganin sun hanasu Kasancewa mata da miji.
Wani farin buzu ya shimfiɗa mata a bakin ƴar bukkartasa, tun kafin ta ƙara so.
Tana isowa, murya can ƙasa tace.
"Assalamu alaikum."
Ido ya zubawa fuskarta cikin tausayawa yace.
"Mata ki zauna". Murya a disashe tace.
"Ya Ba'ana ka amsa sallamar mana".
murmushi ya ɗanyi kana yace.
"Mata na amsa bakijini bane".
A hankali ta zauna bisa buzun, cikin sanyi ta lumshe idonta da takeji sun tsastsafo da zafafan hawaye, murya na rawa tace.
"Ya Ba'ana, wai anji lbrin su ya Gaini?".
Matsowa yayi bakin bukkar, ido ya ɗan zubawa fuskarta, sabida lumahe idon da tayi batasan yana kallontaba ganin hawayenta na zubowa ne yashi yin mgna, a hankali yace.
"Mata, kiyi haƙuri, ki kontar da hankalinki, in dai yayunki suna raye, zan nemisu, ko dan farin cikinki, ki bar kuka Mata, bana son ganin hawayenki inajin ƙuna a raina".
Ya ƙarishe mgnar murya can ƙasa.
Cikin rawan murya tace.
"Ya Ba'ana, ya zanyi? Ina zansa raina in ji sanyi, zuciyata tana ƙuna, Yayuna huɗu kab na rasasu lokaci ɗaya, bani da wa wanda zan nuna a faɗin nahiyar nan ince ga wani na a duniyar, babu ya Giɗi, wanda shine tamkar aboki ƙawa aminiya, abokin faɗata abokin dariyana, Babu ya Seyo, yaya mai kamar uwa, sabida yawan tausayinshi da nuna ƙaunarshi gareni, ko uwa iya abinda zata nunawa ɗanta kenan, babu ya Gaini da yake tamkar uba, babusu babu gawansu babu lbrinsu.
An kashe min ya Lado da yake GARKUWA a gareni.
Ya Ba'ana, ya zanyi in banyi kukaba, Ina zan fara nemansu, Ni macece inada rauni, ta ina zan nemosu? An kashe mana Innarmu".
Ta ƙarishe mgnar tana mai kife kanta bisa guiwowinta ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciya, cikin kuka taci gaba da cewa.
"An kashe Inna, sanadin haka Ummiy na ta zama tamkar zautacciya, duk gidan dake cikin Rugar Bani babu gidan da ba'a kashe a ƙalla mutun biyarba a ƙaramin kari, suwaye ne ya Ba'ana, me mukayi musu? Me suke nema damu? Me muka tsare musu? Me laifinmu dan mun kasance Fulani makiyaya?".
Karon forko a rayuwarsa da yaji rauni har ta kaishi ga zubda hawaye, koda yake raunin soyayyace, cikin zubda hawaye murya na rawa yace.
"Mata gani, zan zame miki madadin uwa, uba, yayunki, Inna, zan zame miki Garkuwa, in sha Allah bazan bari ki cutuba, zan bada raina domin kare naki, zan nema miki farinciki da dukkan abinda na mallaka na duniya, zan zame miki adalin miji, Mata ki dena kuka, kiyi haƙuri".
Cikin shessheƙan kuka ta ɗago kanta, ta zuba mishi ido, tabbas kuka yakeyi kamar yadda ta zata, cikin mamaki tace.
"Ya Ba'ana meyasa kake kuka?".
Hannun yasa ya sharce hawayenshi, karon forko a rayuwarsa da yayi abu ya gommace bayiba karo na forko a rayuwarsa da yayi mugunta yaji dana sani kan sace su Gaini. Da yatsarsa manuniya ya nunata, da mamaki tace.
"Nice na saka kuka?". Kanshi ya gyaɗa mata, cikin al'ajab tace.
"Me nayi maka?". Motsowa yayi ta bakin bukkar sosai can cikin sassanyan murya yace.
"Kukanki ne yasani kuka Mata,
farinci bazai samu gurbi a rayuwataba, muddin ke kina cikin ƙunci, dan Allah ki daina kuka,".
A hankali tasa tafin hannunta ta share hawayenta.
Shi kuwa Ba'ana, wani babban kura tanɗu yajo, cikin sanyi ya ajiyeshi gabanta a tsakiyarsu. Cikin sanyi yace.
"Shatu". Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi domin yauce karo na forko rana ta forko a tarihin rayuwarta da taji ya kirata da Shatu, cikin mamaki tace.
"Na'am ya Ba'ana".
Girgiza kanshi yayi kana ya fara fito da wasu sabbin aska cikin zabirar da yanzu ya jawota, a hankali ya ɗago ya kalleta cikin yaƙini yace.
"Shatu, zan faɗa miki abinda, babu wanda ya sani a kaina a duniya, Shatu zan nuna miki abinda duk duniya ban yarda da in nunawa kowaba, sabida ban yarda da kowaba sai ke ɗaya rak Shatu, nasan zuciyarki ciki da woje, ke mai imanice, bazaki taɓa zalumtata ba, bazaki bari a kuma zalum ceniba. Na amince da soyayyarmu, zamu rayu a tare har gaban abadan."
Ido kawai ta iya zuba mishi.
Ganin Junainah ta iso wurin ne, yasashi jawo akoshin gasassun zabbin gabanshi.
Ita kuwa Junainah da sauri ta kuma sa hannu zata jawo akoshin.
Kanshi ya jujjuya mata alamun ta bari.
Cikin kwaɓe fuska da ɗan karen kwaɗayi da yunwar da takeji yana azalzalar ƴaƴan hanjin cikinta tace.
"Yah Ba'ana ka bani mana yunwa nakeji".
Cikin sanyi yace.
"Bazan bayar ba".
Da sauri tasa hannu ta zari akoshin tayi gaba
Shatu ce ta fara kiranta tana.
"Junnu! Junnu!!! Junnuhhh!".
Ina bata kulata bama bare ta juyo.
Shi kuwa Ba'ana ajiyan zuciya yayi tare da mgnar zuci.
"Uhummm ƙuda garin kwaɗayi kya mutu, kwaɗayinki ne zai karki". Kai ya gyaɗa wa Shstu kana ya juyar da kanshi.
Ita kuwa Aysha shiru tayi tabi Junainah da ido.
Shi kuwa Ba'ana cikin sanyi ya wore ƙafafuwan sa,
takalmin roba na sau ciki wato, tashi kabi shanun dake ƙafarsa ya zare.
Sabbin askan ya ɗauka, kana ya fito da wasu ƴan kananun layu guda biyu.
cikin yaƙini yace.
"Shatu, kinga waɗannan layun?".
Kai ta gyaɗa mishi cikin yin kici-kici da fuska.
Jinjina mata kai yayi kana yaci gaba da cewa.
"Wadannan sune, maƙurar, mgnin kariya da zan saka a jikina, zan sasu a gaban idonki, wannan ƙaramar ita zan saka a dundunyar ƙafar dama, itace kuma layar, ƙarfe, mudin wannan laya tana jikina, to wlh babu wani ƙarfe dake kan doron duniya da zai shiga jikina".
Cikin mamaki tace.
"Koda bulet ne!?".
Kanshi ya gyaɗa mata tare da cewa.
"Koda menene, kuwa su wannan sabbin layune, wanda babu makarinsu, sai dai ina na ciresu a jikina,
ita wannan da zan saka a ƙafar hagu, layar zanace.
Duk sihirin mutun bazai karyashiba, zan iya ɓacewa inje ko ina, makarinta abu ɗaya ne!".
A hankali tace.
"To menene makarinta?".
Cikin sauƙe wani nannauyan numfashi yace.
"Idan wata rana dubuna zaicika za'iya kamani, to ammanfa tabbas, zan iya ɓacewa sai dai in ba'a barni na sha ruwaba, amman muddin akabani ruwa nasha zan iya ɓacewa."
Da sauri tace.
"Ya Ba'ana dubunka ya cika kuma, kamar wani mugu ko maiyin mugun abu".
Da sauri ya fizge mgnar da cewa.
"Eh to ai yanzu zan fara fataucin nemo. Suya Yaya Giɗi ne, kinga kuwa, sai yadda hali yayi".
Ajiyan zuciya ta sauƙe kana tace.
"To ita layar ɓatan da ta ƙarfe menene makarinsu?".
Kanshi ya ɗan jingina da bakin bukkar ido ya ɗan zuba mata, kana cikin sanyi yace.
"Uhum makarinta sai in an samu maza tagwaye, da matar da bata al'ada sunyi tuwon sabon geron da za'a shuka a tsakiyar garken fulanin kana tuwon za'ayishi da garin dakan hannune, kuma maza tagwayen sune zasu tuƙa tuwon kana matar da mijinta ya tara da ita batayi wonkan tsarkiba, ta kwashi tuwon , to su kam in naci, tuwon gaba ɗaya sihirin jikina zai karye, in kuma ba haka sai dai ina an tsaga dundunyar ƙafar tawa an ciresune kafin makami ya iya min illa".
Cikin wani irin sanyi tace.
"In sha Allah zaka nemosu lfy ka dawo dasu lfy, zanyi ta addu'a Allah ya baiyanasu."
Kanshi ya tanƙwasar kana a hankali yace.
"Uhum sai daifa Shatu akwai wasu bulalin da aka bani tabbacin zasu worwore duk wani asiri da kafi da nayiwa jikina,
Amman duk da haka bazasu worwore waɗannan layunba, sai dai an bani tabbacin, muddinfa aka dakeni da wannan bulalin zan ji azabar dukan, da zai iya ɗauke raina".
Cikin mutuwar jiki tace.
"Bazama su dakeka ba, Ya Ba'ana".
Kanshi ya mirgina kana, yasa hannu ya ɗauki askarnan, kawai sai ya datsata kan dundunyar ƙafar damanshi,
Da ƙarfi Shatu tasa salati tare da rufe idonta, gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi murya na rawa tace.
"Innalillahi ya Ba'ana zaka kashe kanka".
Cikin harshen fillanci yace.
"Ai bazanji zafinba Mata, bari yanzu in ɗinkesu, buɗe idonki ki gani."
Cike da tsaro tace.
"Bazan iyaba, ina tsoro".
Jin hakane yasa bai kuma ce ta buɗe idonba, har saida ya gama cusa layun kana yasa ƙayar aduwa ya rinƙa hudawa yana ɗinkawa da zaren, gashin bindin shanu, saida ya gama yace ta buɗe idonta.
Cikin tsoron ta zubawa wurin ido, ga jini ya ɓata ko ina,
Sai kuma ta ƙurawa ƙafafuwan ido ganin yana shafa musu man shanu sai wani tafasa wurin yakeyi, cikin mintuna uku duk wurin yayi tib-tib kamar ba shiba.
Cikin tsoro tace.
"Ya Ba'ana, ka dena irin wadannan abubuwa, wallahi shirka ne, tsafine babu kyau! Haramunne."
Ganin yadda ya haɗe fuska ne yasa tace.
"Kayi haƙuri, shiyasa tun forko ina son ince maka ba kyau bana son kana irin wadannan abubuwan".
Murmushi ya ɗanyi kana yace.
"In kin sake min mgnar, bulala ɗaya zan ɗauko cikin bulalin shaɗi na, in zaneki da ita sau ɗaya kiji irin zafin da masu gangancin cewa suna sonki, sukeji a jikinsu."
Cikin tsoro tace.
"Bazan sake bama Ya Ba'ana wadannan, bulalin da kake tsumasu da dafin kunama ai Ni kam na sani bulala ɗaya zakamin zan mutu".
Da sauri yace.
"Azubillah, Mata kada ki sake cewa zaki mutu, domin duk randa kika mutu nima zan mutu, sai dai batun gsky ko Mata, duk mutumin da kikaga ya iya jure bulalin shaɗi na, har ya kai matakin nasara, to wlh ki sani ki shaida, jarumine, irin jaruman da sunyi ƙaranci a duniya."
Hannu tasa ta kange fuska daga wani irin kallo mai cike da so da yake mata,
Tabbas Ba'ana ba barbarene, amman yanada wani irin kyau mai ban mmki, a hankali tace.
"Ya Ba'ana wai da waye kake kamane?".
Cikin murmushin da ya bayyana kyawawan haƙoransa yace.
"Ni da kakata Maman babana nake kama, ita kuma ba kanuribace, fulatamare ce ita".
Cikin sanyi tace.
Murmushi ya ɗanyi kana yace.
Cikin sanyi tace.
"Haba shiyasa mana kake da kyau sosai".
Wani irin kallo ya mata tare da cewa.
"Eyeh ashe Ni kekyawan ne Mata, ke dama shine baki taɓa gaya min ba inji daga bakin wacca nafiso fiye da komai a duniya dan inji daɗi, kin bari sai wasu can keta cemin wai ni kekyawan ne".
Da sauri ta miƙe tare da cewa.
"Sai anjima, Mai kyau ka tashi kaje ka tafi masallacin kaga lokacin sallan jumma'a yazo anata tafiya".
Da murmushi ya rakata. Ita kuwa da haka ta tafi gida, sabida tuni wasu masallatan har sun fara huɗuban sallan jumma'a.
Tana shiga gida ta samu.
Rafi'a, Junainah, Ummiy da Bappa, gaba dayansu a.
Cikin Babban birnin Ɓadamaya, a cikin masarautar Joɗa, kuwa.
Tuni masallacin Lamiɗo Nuruddee, ya cika yayi maƙil da bani adam tako ina zuwa, akeyi.
Masallacin ya cika tab tamkar zai fashe, shiru kakeji babu wani amon sautin ɗan adam dake tashi, sai sautin muryarsa.
Yana tsayene cas kan ƙafafunshi,
Wata dan datsetsiyar, shaddar Super Nour ce a jikinshi wacce take Brown color a ƙalla kuɗinta zai kai dubu ɗari da ashirin, shaddar irin mai mai ɗinnane,
Yayi kauri cikin kayan ko dan yanayin suturar da ya sakane, boxes ce fara ƙal yasa a ciki, sai snglet itama fara ƙal, kana sai Rigar half jomfar yaddan dake jikinshi sai wonɗota, wanda sunyi cib-cib da madaidaicin jikinsa,
Kana sai watta tattausar doguwar al'kyabbar sa, Golding color, sai wani irin sheƙi takeyi, sai hirami fari daja irin mai ɗigo-ɗigo nan, yayi masa sakin manyan Dattawan bai lonƙosashi, ya barshi a zube bisa kafaɗunshi, sai ta gaban goshinsa da ya ɗan matseshi ya bada ɗan tsini dai-dai kan karan hancinsa,
Sai baƙin zagayen daya ɗaura bisa kam hiramin.
Kana sai wasu takalman shi dake can bakin ƙofar shuga masallacin ta ƙofar liman, takalman irin na sarauta ne half cover, wanda suma fari da ɗigon jane.
Yayi wani irin kyau mai ɗaukar hankali haibarsa da kimarsa da dottakunsa sunyiwa fuskarshi ƙawanya, sajen nan nashi yayi lib-lib tamkar anayi wa koren ciyawa bayi, sai wani irin sassanyan ƙamshin turaren OudKareem ɗin sa, dake tashi a jikinsa.
Muryarsace ta cika ko ina na yankin.
Shiru mutanen wurin sukayi kowa na jin, wa'azin yana ratsasu.
Yana Hudbane akan, wuraren da ya dace namiji ya gani a jikin matar da yake neman aurenta,
yana kan hankali, bisa wuce gona da iri da mafiya matasan yanzu keyi, a kan wannan dama da Allah ya basu.
Gyara tsayuwarshi yayi, tare da haɗe hannayenshi wuri ɗaya, ya haɗe bakin al'kyabbar jikinshin. Cikin tattausan lafazi mai ratsa kunne da zuciyar duk mai sauraro da imani yaci gaba da cewa.
"Aure wata muhimmiyar hanya ce, wanda idan aka ƙullashi zai bawa ma'auta daman saduwa, tsakaninsu, ba tare da wata ƙyama ba, kuma ta hakane ma'autan zasu zama sutura ga junansu. Kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa, a Suratul Baƙara aya ta , 187:-
(HUNNA LIBASUN-LAKUM WA, ANTUM LIBASUN-LAKUM). Ma'ana su mata suturane gareku maza, sannan ku maza suturane garesu (Su Matan)."
Gyara zaman al'kyabbar sa yayi tare da kallon tarin dubban al'ummar Annabi dake zaune gabansa, hankalin da nitsuwar kowa na kanshi.
Sai ɗan haskem cameras da yake gilmawa ta kanshi da sauran na kusa dashi, shaidar ana naɗar sautin muryarsa nayin huɗuban. Cikin nitsuwa yaci gaba da cewa.
"Saboda haka, ya zama dole mutun, ya nitsu ya maida hankali ya zaɓi abokiyar zama ta gari da zata zame mishi sutura ya zame mata sutura, wajibine kuma kayiwa kanka da jikinta iyaka har sai an biya sadaki, an kuma ɗaura aure, shaidu sun shaida sannan zaka samu nitsuwa da ita.
Domin shi aure, yana samar da nitsuwa tsakanin ma'auranta. Ɗan Adam bazai samu cikakkiyar nitsuwa a gidansa ba sai in har yanada mata, wacca ya aura. Domin zata ɗebe mishi kewa, ta sa shi ya samu nitsuwar hankalinshi. Saboda zamansu tare, a ƙarƙashin inuwar aure zatayi mishi maganin kaɗaci. Kamar yadda Allah, (A.A.W) ya faɗi a Suratul Rum aya ta 21:-
(WA MIN AYATIHI AN KHALAKA LAKUM MIN ANFUSAKUM AZWAJAN LITASKUNUW ILAIHA WA JA'ALA BAINAKUM, MA WADATAN WA RAHMA INNA FII ZALIKA LA AAYAATIN LIKAUMIN YATAFAKKARUN).
Yana daga cikin ayoyin da Allah mai girma ya halitta mana mataye daga kawunan mu. (Mataye da muke aure da su) domin su sami nitsuwa junanku, sannan kuma ya sa muku soyayya a tsakanin ku tare da Rahma da tausayawa juna. Lallai a cikin wannan al'amari akwai ayoyi abin lura ga jama'a'an da suke masu tunani".
Gaba ɗaya taron al'ummar babu, hayaniya ko motsi shiru kakeji,
Baba Nasiru kuwa, yana dai zaune ne cikin sahun da masallacin amman ji yake tamkar ya shaƙo wuyan Jabeer sai ya kaishi ƙiyama, Baba Bashiru ne dake gefenshi, ya ɗan kalleshi tare da yin ƙasa da murya yace.
"Ya Nasiru ka nitsu mana ka koyi danne abinda ke ranka".
Cikin tarin baƙin ciki yace.
"Haba Bashiru ya zanyi in iya danne abinda ke raina, bayan da kai sani dama duk sauran yan uwanmu, mahaifinmu ko sarautar sarkin ƙofa bai bamuba,
Tunda ya bawa Ya Muhammad, Galadima, yana rasuwa, madadin a maida sarautar Galadima kaina, ko kan Hashim tunda shi ubanshine Galadima, sai ya ɗauki wannan sarautar ya bawa, Jafar shi ɗan rashin adalci."
Murmushi Baba Bashiru yayi tare da cewa.
"To ai kuma dai gashi ya haukace ko? Ina dai yanzu sarautar tafi ƙarfinsa, dole dai ya barta".
Cikin fusata Baba Nasiru yace.
"To ɗaya barta ya haukace ɗin ma, ya maidota ga ƴan ɗakinmu ne, inji, wancan tsohon ya bawa, waishi ya bawa ƙaninshi, ai shima ɗan tsohon sarkine
Sannan kana ganin yadda ya kuma ɗaukar sarautar GARKUWA ya bawa Jabeer, sannan babban tashin hankalin kanaga yau tare suka fito ɗakin labbare dashi wannan munafikin yaro, waishi Sheykh ɗan iska anyi asiri anyi tsafi duk baya kamashi yadda mukeso".
Barrister Kamal ne dake gefensu, yayi ɗan wani guntun tsaki cikin tsuke fuskarsa, da jin haushin yan uwan nashi yace.
"Ya Nasiru kufa, ji tsoron Allah, ku tuna, cikin Masallaci kuke, kuma ba kyau liman na huɗuba ana. Surutu."
Wani irin mugun kallo Baba Bashiru ya watsa mishi tare da cewa.
"To ɗan masu matacciyar zuciya, wa'azin da yakeyi ai tun kan a haifi uwarshi mun sani".
A kufule Barrister Kamal yace.
"Ƙaryane, da kun san abunda ya sani wala Allah da zuciyarku ta tsarkaka".
Shiru yayi tare da fuskantarta Inda limamin take jin yana cewa.
"Halaccin kallon matar da mutun yakeso ya aura.
Haƙiƙa munsan matarka abokiyar rayuwarka ce. Kuma gonarka ce da zakayi shuka a cikinta, sannan kuma gareta zaka samu konciyar hankali. Kuma shi manufar yin aure ya hana kallon wata ko wasu matan wanda ba nakaba da dai makamantansu Irin hakan.
IN KUWA HAKANE TO LALLAI AKWAI BUƘATAR SAI MUTUN YA ƊARJE! YA ZAƁA. Haka kuwa baya yiwuwa sai ka kalleta sosai da sosai. Saboda mahimmancin haka nema shariyar musulunci ta yardar maka da ka kalli wacce kakeso zaka aura da kyau. Don ka tabbatar da wancan abubuwan da aka ambata a sama.
Kuma wannan dama da Shari'a ta bada ta bada shine, a matsayin halasci na wurin mafi yawan malamai, kuma wannan Halascin da akace halasne ya haɗa da cewa. Shin ta yarda ka kalleta, ko bata yardaba, halasne in dai ka kalleta. Kuma wannan hukuncin haka yake a wojen mafiya yawan malamai, sai dai Malikiya, sunce shi hukuncin Halascin ya dogara ne, in ta bashi izinin amma in bata bashi izinin ba to bai halasta ba.
Haka kuma shi wannan hukuncin halascin an samo shine daga, hadisin Abu Huraira (Allah ya ƙara masa yarda) yace, wani mutun ya nemi auren wata mata, ƴar Madina, sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa: "Shin ka kalleta kuwa?". Sai mutumin yace, wa Manzon Allah (S.A.W) "A'a ban kalleta ba". Sai Manzon Allah (S.A.W) yace.
"Tafi ka kalleta, domin mutanen Madina sunada wata illa a idanunsu."
A wata ruwayar kuma da Abu Dauda ya ruwaito.
Daga Jabir Bin Abdullahi cewa: Lallai Manzon Allah (S.A.W) yace.
"Idan ɗayanku zai nemi aure to idan ya sami ikon kallonta wato kallon abin da zai burgeshi zuwa ga aurenta, to ya aikata hakan, (ma'ana ya kalleta) Jabir yace sai na nemi wata mata, daga cikin ƙabilar Banu Salma na kasance ina bibiyanta har sai da naga abin da zai birgeni a aurenta.
Ɗan zagaitawa yayi kana yayi gyaran murya tare da cigaba da cewa.
"To matasanmu na yanzu suna, fakewa da waɗannan hujjojin, suna fakewa da guzuma su harbi karsana, suna fakewa da hadisai suyi haramtaccen kallo, wata sun fake da rama suci ɗanyen gari. Hattara gareku iyayen yara maza da mata, Gargaɗi gareku matasa, bari in tuna sar daku wuraren daya halasta ka kalla a jikin matar da kake son ka aura.
Dangane da inda ya kamata ka kalla, a jikin macen da zaka aura. Malamai sun kasu kan wannan hukuncin, saboda ba su, sami hadisin da ya yi bayani keɓantaccen wuri wanda aka keɓe ko aka ce nanne kawai za'a kalla ba, wannan shi ne musabbabin da suka karkasu kamar haka:
1 Mafiya yawan malamai sun tafi, cewa in mutun yana neman auren mace, yana iya duban fuskarta da tafukan hannunta.
A Duba Fiƙhu wadi Juzu'i na 2. Shafi na 20 sannan kuma a cikin Fiƙhu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24 wasu malamai sun ƙara yin bayani da cewa idan mutum ya dubi fuska mace, zai gane kyawunta, in kuma yadubi Fuskarta zai iya fahimtar cewa, mai ni'imtaccen jiki ne wato mai tattausan fata jiki, ko kuma mata marar ni'iman jiki.
Sheikh imamul Al-Auza'i yana cewa.
"Mai neman aure yana iya kallon wuraren nama dake jikin mace da zai aura.
Duba cikin Fiƙhu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24.
Sheikh imamul Dauda kuwa yana cewa:
Mai neman aure yana iya kallon dukkan jikin matar da zai aura, shima an samu daga Fiƙhu Sunnah Juzu'i na 2 shafi na 24.
Ɗan tsagaitawa yayi tare da ɗago kekyawan tsintsiyar hannunshi ya kalli agogon Daimond dake ɗaure samfarin Gucci,
Ganin lokacin salla ya ƙara tone yasashi yin gyaran murya tare da ci gaba da mgna gaggauce, yace.
" A wata ruwayar kuma da aka samo daga Abudurrazaƙ Umar Sa'idu ɗan Mansur yace,
(Amirul mu'minin) ya nemi auren ƴar Sayyidina Aliyu (R.A) wanda ake kira da Ummul-Kulsum, sai, Aliyu ya ambata masa ƙanƙantarta, sai yace.
Zan turo ita idan ka ganta tayi maka matarka kenan, sai ya aiketa wuri shi. Lokacin da taje sai ya yaye suturar da ya rufe ƙwaurinta.
Sai tace.
(Ba don kai Amirul mu'minin bane da na tsole ko buge idonka, (wato da na mareka) idan muku dubi, wannan in har maganar ya inƙanta to ana iya yin hakan.
Anan kenan in har ka kalleta batayi maka ba, to ka kama bakinka kayi shiru. Kada ka faɗi wata magana wanda zata iya cutar da ita.
In kana ganin kai bata baka sha'awa ba, to tana iya bawa wani sha'awa ya aureta, domin ko wanne icce da ma tsincinsa, kuma abincin wani guban wani.
Allah yasa mu dace, lokacin salla yayi, bari muyi salla sai in Allah ya kaimu sati mai zuwa sai muyi bayani kan halaccin mace ta kalli mijin da zata aura.
Daga nan yayi addu'an kana, ya juya ya fuskanci gabas, tare da tada iƙama bayan yayi addu'an.
Bayan an idar da sallane, suka fito, a jere.
Ta ƙofarsun dai suka shiga, inda duk ahlin masarautar suke bin nan bayi da hadimai da sauran fadawa kusa, duk ta babbar ƙofar suke bi.
Kusan a jere a jere suke tafi.
Kasan cewar zasuyi tafiyar zuwa Rugar Bani ne yasa Mai martaba Lamiɗo ke sauri.
Hakama Sheykh Jabeer, wanda Jalal, Jamil, Jafar, Haroon, Imran, Hashim ke tare dashi,
A hankali ya tsaya jin muryar bappanshi ƙanin Abbanshi Baba Nasiru kenan na ce mishi.
"Kai! Jabeer tsaya".
Tsayawa yayi cak ba tare daya juyo ba,
Suma sauran duk tsayuwa sukayi,
Kusan a tare Baba Nasiru da Baba Bashiru. Suka isosu.
Cikin haɗe fuska Baba Nasiri yace.
"Jabeer, in dai aure kake so ai gwara ka fito fili ka gaya mana, mu bazai gagara ba mu aurar maka koda yar baiwace, tunda shi ubanka zuciyarshi ta mace, baya iya tsinanawa kansa komai."
Da sauri ya rumtse idonshi,
Jalal kuwa wani irin kallo ya watsa bappanun nasu,
Shi kuwa Jabeer shiru yayi bai tanka musuba, Baba Basiru ne ya ne ya bugi kafaɗarshi tare da cewa.
"Kodai kafi ganewa yawon zinace- zinacen daka saba ɗin ne? Kafin burin a barka ba mata, kana zaune ka tsufe a gida ka fake da rigar malumta kana iskanci a cikin tsarkakekkiyar masarauta ko".
Ido ya zuba mishi babu ko kebtawa, ganin haka Baba Basirun ya ɗauke hannunshi dake kan kafaɗarshi.
Dai-dai lokacin kuma Barrister Kamal da Dr Aliyu suka iso wurin.
Suna isa Ya Jafar yayi saurin kamo hannun Ƙanin shi Sheykh Jabeer, ya fara ja da sauri alamun su tafi su bar wurin gaba ɗaya, jikinshi rawa yakeyi.
Ganin hakane Haroon ya kalleshi cikin larabci yacewa Jabeer.
"Ɗan uwana mu tafi".
Barrister Kamal ne ya kalli Jabeer cikin sanyi yace.
"Jabeer jeka, ku tafi kada ka biye musu, tunda sun girma basu san sun girma ba."
Jin hakane yasa Jabeer ya juya ya fara tafiya.
Jalal kuwa wani harara ya watsa musu kana ya juya yabi bayan yayunshi.
Jafar kuwa Jan hannun Jabeer yakeyi a kiɗime gaba ɗaya jikinshi karkarwa yakeyi tamkar mazari.
Ganin haka yasa Jabeer ya jashi ya kaishi sashinsu, ya damƙa hannunshi wa Juwairiyya kana yace mata ta kula dashi, yanzu zai fita shida Lamiɗo.
Jiki a mace Juwairiyya ta mishi fatan a dawo 'lfy.
Ƙarfe biyu da rabi dai-dai suna cikin motoci, wanda a ƙalla sun kai su goma.
Motar forko Waziri ne wanda yake ɗane ga Yayar Lamiɗo.
Sai Galadima, da Wambai,
Ɗaya motar kuma Ɗan iyane da Sallama, da sarkin Dawaki, da sarkin fada,
Sai motar da Lamiɗo ke ciki, shida Garkuwa wato Jabeer sai Haroon sai kuma Hashim da Laminu, ƙanin Hashim wanda duk yaran Gimbiya Saudatu ne matar babban yayansu Habibullah wato Abbansu Jabeer, wanda da shine Galadima. Ɗaya rasune aka bawa Ya Jafar sarautar wanda kwananshi goma da sarautar, komai na rayuwarsu ya sauya.
Sai motar dake binsu wanda Jalal, Jamil, Imran Sulaiman ɗan Barrister Kamal, suke ciki.
Sai sauran motocin fadawa kamaru, Ɗan kazagi, mai yiwa sarki fadanci da kuna dogari mai riƙewa sarki laima, da sarki mota da dai sauransu.
A jere a jere motocin ke tafiya.
Gudu sukeyi mai ɗan yawa sabida ganin yamma ta ƙarato, gashi basu je bama bare su fara shirin dawowa.
Gudu sukeyi, kana fadawansu, rirtiƙe da bulalin dogaye.
Kai tsaye Rugar Bani suka nufa.
Koda suka iso cikin garin Shikan, sunga alamun garin babu lfy, har yanzu dan sai matasan ƙabilar ɓachama da hausawa suketa yawo a garin ko wanne na bawa yankinsu kariya.
Suna isa cikin Rugar Bani.
Gaba ɗaya mutanen Rugar duk inda suka gilma sai a bisu da ido,
Yara maza da mata sunata guduwa suna shiga cikin gidajensu.
Kai tsaye tsakiyar garin suka nufa wanda nanne fadar Arɗo Bani taken kuma lokacin duk manya da yara maza tsoffi da dattawan garin duk suna harabar wurin sabida yau jumma'a duk suna dawowa kiwo da wuri.
Kuma duk a tsakiyar garin suke taruwa sabida bawa garinsu kariya, domin har yanzu suna cike da taraddadin abinda akayi musu.
Kuma ya rigada yanzu an ƙure haƙurinsu sunata shirin ɗaukan fansar rayukan da aka kashe musune. Fiw-fiw haka motocin keta gilma mutane suna wucewa tara da tada ƙura sabida babu kolta a garin sai yashi. Sai sauti da ƙugin mitocin ne ya cika kunnuwan mutanen garin baki ɗayansu.
Motocin na isowa wurin. Gaba ɗaya mutanen Rugar dama baƙin mutanen maƙotansu sauran rugage duk suka miƙe tsaye.
Tare da gya tsayuwarsu, suka gyara riƙon da sukayiwa sanduna su.
Ba tsoro ba fargaba sukayiwa motoci goma nan zobe, suka sasu a tsakiya.
Cikin sauri Sarkin dogarai ya buɗe marfin motar da yake ciki, ya fito tare da zungureriyar bulalarashi. A take kuma Ɗan zagi ma ya fito.
Da sauri duk sauran fadawanma suka firfito kowa da zungureriyar bulalarashi.
Cikin ɗaga murya ɗanzagi yake cewa.
"Ta kawarka lfy Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa, sarki ɗan sarki jikin Sarki,uban sarki kakan sarki. Jama'ar gari sun gaisheka,
Da sauri duk sauran fadawan suka, firfito cikin motar.
Sarƙin motane yazo ya buɗe wa Sarƙi ƙofar.
Dogari kuwa matsowa yayi da sauri ya buɗe wata ƙatuwar laima, gaba ɗaya sukayiwa ƙofar motar labule da mamyan jajayen rigunansu, yayin su duk sawunsu babu takalma, sannan kawu nansu naɗe cikin wasu ƙatti-ƙattin rawanunnuka masu girma babu kunne ko ɗaya a jiki.
Gaba ɗaya mutanen Rugar kuwa, sai ƙara tsuke fuskokinsu sukeyi, cikin jin haushin zuwa sun.
Can cikin motar kuwa Haroon ne saƙale da wayarshi a kunne cikin sanyi yake mgn sabida kada Lamiɗo ya jiyoshi, haka kuwa babu mai jinshi sai Jabeer.
Cikin sanyi ya ɗan kalli Jabeer kana yaci gaba da mgna a hankali yace.
"Umaymah ni dai hankali na ya tashi, da irin wasu mutane da wasu abubuwan da akeyiwa su Jabeer a masarautar su, Umaymah, meyasa bazasu bar musu sarautar da Masarautar tasu gaba ɗaya bane, sai kinga fa yadda Jazlaan dinki ke fuskanta ƙalubale fa."
Cikin wata iriyar murya Umaymah tace.
"Yanzu kuna inane?".
Kanshi ya ɗan jujjuya kana yace.
"Uhum ni ina zan san inda muke, na dai san munzo wata Rugar fulani ce, wai GARKUWAN FULANI nasu ya kawo musu ziyara dan ja-janta musu abinda ya faru, kuma gaba ɗaya mutanen rugar naga sai
Wani irin kallo suke mana kamar dai zasu huce a kanmu ne".
Cikin wani irin tattausan murmushi mai nuna jin daɗi tace.
"Bawa Jazlaan wayar".
A hankali ya miƙa Jabeer wayar tare da cewa.
"Umaymah ce".
Cikin sanyi yace.
"Kace tayi haƙuri sai mun koma zan kirata".
Da sauri ya like mishi wayar a kunne jin tana cewa.
"A a amshi wayar".
Ɗan haɗe fuska yayi kana ya amshi sallamar da tayi mishi.
Kana ya meda kai jikin kujerar murya can ƙasa yace.
"Umaymah, Na gaji tunda muka dawo ban hutaba, yau da sassafe wannan tsohon ya sani shara kamar wani bawanshi haka ya sani na share mishi wannan ɗakin nasu na gado wanda in dan ta nine rusashi za'ayi gashi yanzu kuma ya kwasoni zuwa wata rugar FULANI da duk makamaine a hannunsu, ko wa zasu daka".
Cikin wani irin jin daɗin daya bashi mamaki mai yawa tace.
"Ko kai zasu dakane Jazlaan, Sheykh Jabeer, yasha zana a hannun Fulani".
Cikin sanyi yace.
"Su kashe Ni dai Umaymah, ke kin sani tunda nake a duniya, ba'a taɓa dukana ba, sabida koda iba yaroma ban taɓa yiwa Mama da Ummi laifin da zai kaisu ga yimin dukaba, Abba na kuma baya dukanmu, Umaymah kema baki taɓa koda marina ba, to kuma wa kika ga zai dakeni a faɗin duniyar nan banda ruwan sama".
Murmushi tayi wanda har saida yaji sautin cikin sanyi tace.
"Allah ya tabbatar da al'khairi cikin tafiyar naku, ka dai lura kaine GARKUWAR dole da duk abinda zai cutar da Lamiɗo ko masarautarku ko sunanta dole kai ne zaka zame musu Garkuwa, so dan Allah bana son kayiwa Lamiɗo musu bare gardama a cikin duk abinda zai umarceka".
Cikin sanyi yace.
"To Umaymah, in na koma zamuyi mgna".
Daga nan sukayi sallama, cikin mamaki ya kalli yadda gaba ɗaya manyan hakimai sun firfito, ga Lamiɗo ya fita amman yana tsaye bakin ƙofar motar.
Cikin sauri ya kalli Hashim tare da cewa.
"Hashim Lfy kuwa naga duk suna tsaye, garin basu da abin zamane daza'a karrama baƙi?".
Cikin nitsuwa Hashim yace.
"Uhum cewa sukeyi, wai sun yafe ziyara da ja-jantawar Lamiɗo".
A wojen kuwa, cikin ɗaga sauti Danzagi yace.
"Hattara dai fulani mai ƙasar ne gaba ɗaya, ke tsaye tsakiyar garinku, maza ku bada masauƙi".
Ya ƙarishe mgnar yana jujjuua bulalar hannunshi haka sauran fadawan.
Cikin fillanci ɗan aiken Arɗo Bani ya buɗe murya da ƙarfi cikin harshen fillanci tare da cewa.
"Maza ku bada hanya mai martaba ya iso fadar Arɗo Bani".
Jin haka gaba ɗaya taron al'ummar fulanin suka fara buɗa hanya,
Har gaban rumfar da Arɗo Bani ke ɗauke baƙi, inda aka shimfiɗe wurin da manyan taburmaii kana aka malale manyan kilisai irin namu na fulanin dawa.
Bappa Malam Liman Alhaji Haro Alhaji Umaru, Musu, da kuma Ardo Duno da Arɗo barwa maƙotansu, duk suka mimmiƙe tsaye sai dai gaba dayansu fuskokinsu babu wal-wala, asalima wasun cikinsu jikinsu har ɓari yakeyi, dan fushi da zafin zuciya.
A can cikin ƙauyen Bonon kuwa, Ba'ana da sauran ƙabilum ɓamawam duk suna gaban dodon tsafinsu Bonon ɗin,
Da gudu Maman Ba'ana ta iso wurin cikin Yaren ɓacamancin ta sanar dasu zuwan, sarki Lamiɗo da tawagarsa, jin hakane yasa, Ba'ana ya miƙe jiki na rawa ya nufi rugartasu.
Su kuwa sauran yace in yaje yaga da matsala zai kirasu.
Nan ya tafi su kuma sukaci gaba da dariyar mugunta.
A cikin Rugar Bani kuwa, Bukar Baban Ba'ana ne yayi wata iriyar fitinenneyar murmushi mai cike da mugunta dan son haddasa fitina, ta yadda zai samu masarauta Joɗo da kanta ta shiga matsala.
Kutsawa yayi tayi cikin mutane har ya samu ya shigo gaba-gaba.
Lamiɗo kuwa da tawagarsa taku sukeyi cikin al'farma da ƙasaita.
Su Waziri, Galadima, Wambai, Ɗan iya, ɗan buram, duk suna biye dashi a baya,
Dogari na rike mishi da laima, fadawa kuma na zazzaune a ƙasa, gefe da gefe, Ɗanzagi kuwa muryarsa ce cika wurin baki ɗaya duk da hayaniyar da wurin kedashi.
A hankali Jabeer ya sako sawunshi woje, yana taka ƙafarshi ta dama kan ƙasar garin, yaji zuciyarshi ta buga da azaban ƙarfi har saida ta kaishi da rumtse idonshi tare da ambaton.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
A saman red lips ɗinshi.
da ƙarfi yasa hannunshi ya dafe ƙahon zuciyarshi, tare da kuma maimata.
"Hasbunallahiwani'imanwakil".
Sabida ji yayi tamkar zuciyarshi zata fasa ƙirjinshi ta faɗo ƙasa. Jalal, Jamil, kuwa ido suka zuba mishi, sabida ganin yadda ya rumtse idonshi, sabida suna bakin ƙofar motar, sune ma suka buɗe mishi marfin.
Haroon kuwa da Hashim da Laminu, jira suke ya fita kafin su fita.
Cikin mugun tsana Laminu ya kalli Jabeer ɗin da ya yunƙura ya fita,
zuwa yanzu, wani irin harbawa da tsalle zuciyarshi keyi, wani irin masifeffen fargaba, da kaɗuwa ne suka dirar masa lokaci ɗaya.
A hankali duk suma su Haroon suka fito, a tsakiya sukasa Jabeer kana bayinshi na biye dasu a baya.
A hankali ya gyara tattausan al'kyabbar jikinshi, tare gyara hiramin kanshi ya kange kekyawar fuskarshi.
Takun da yakeyi ne ya ƙarawa shigarsa ta al'farma daraja,
ya fito tamkar balarabe, gaba da baya, kamalarsa da kwarjini shi ya cika dukkan idanun bani adam dake kan doron ƙasar wannan wurin.
Ya Hashimu ne da ya samu ya dawo gida jikinsa da sauƙine, yayi wani irin kabbara mai ratsa zuciya, cikin sanyi yace.
"Ziyararku tayi haske sabida kun zo mana da mai hasken addini a jiki da zuciyarshi".
Ga mamakinshi sai yaji Ɗanzagi na cewa.
"GARKUWA ya amsa Sheykh Jabeer Jikan sarki tsatson sarki gaba da baya".
Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali yake takunda yasa al'kyabbar sa buɗuwa tana bajewa, sabida ɗaga hannunshi da yayi yanai musu sallama irin ta addinin Musulunci.
Mafi akasarin mutanen tafukan hannunshin suka zubawa ido, sabida kai da ganin tafin hannunshi kasan ya gauraye da ni'imar ambaton sunan Allah da rike littafi al'ƙur'ani, da kuma jin daɗin.
Shi kuwa Jabeer ƙara sarƙafe carɓin shi yayi cikin yatsun hannunshi, kana, ya fuskanci gefen hagunshi, ya ɗanga musu hannu tare dayi musu sallamar kamar yadda yayiwa yan gefen damanshi.
A haka har suka isa tsakiyar ƙaton filin.
Inda Lamiɗo da sauran tawagarsa ke zaune.
Bisa fararen kujerun robar da anka jera musu cikin rumfar suka zazzauna.
Bayan sun amsa musu sallamar da sukayi.
Cikin nitsuwa Lamiɗo ya kallesu tare gyara zamanshi.
Muryar Ɗanzagi ce ta karaɗe wurin da cewa.
"Gyara kimtsi. A saurara dai Lamiɗo jikan ɗan Lami Bubayero jikan Lamiɗo Joɗa zaiyi mgna".
Wani irin harara suka watsawa Danzagin, shi kuwa Lamiɗo cikin nitsuwar datattaku tace.
"Da farko dai zan fara da baku haƙurin zalumcin da akayi, muku, Allah ya jiƙan wanda suka rigamu gidan gsky."
Da ƙarfi Ɗanzagi yace.
"Amin". Su kuwa dattawan ido kawai suka zuba mishi.
Shi kuwa Lamiɗo a hankali yaci gaba da cewa.
"Ina mai baku haƙuri da kuma umarnin kada kuce zaku ɗauki mataki domin ramuwa."
Kamar daga sama sukaji Muryar Bakur yana cewa.
"Babu wani sarkin da ya isa ya hanamu ɗaukar fansa sai, Ubangijin daya busa mana, numfarfashi".
Da ƙarfi Wani dogarin ya ɗago zabgegiyar bulalarshi ya zabgawa Bukar.
Wanda saida yayi tsalle ya kurma ihu.
Cikin tsauri Lamiɗo ya ɗagawa duka fadawanshi da hadimanshi da dogara shi hannu alamun kada su sake dukan kowa.
Saura su Waziri kuwa duk shiru sukayi,
Jabeer kuwa, a hankali yaci gaba da tasbihin da yakeyi, sabida danne abinda yakeji zuciyarshi nayi.
Shi kuwa Lamiɗo cikin sanyi ya fara mgna, dan yasan zafin rashin da sukayi ne yasa sukace sai sun rama, a hankali ya kalli fuskokin dattawan da yasan sunje mishi har fadanshi dan neman zaman lfy, cikin kula ya kalli Arɗo Bani tare da cewa.
"Arɗo Bani zaku haƙura, hukuma da masarauta ta bi muku kadun cutar damu da akeyi, ko zaku ɗauki makami dan ramawa?".
Cikin tarin kufula da harzuƙa da kuma son cinma wata gagarumar manufar da ya daɗe yana fatan ya samu da sai yau, fuska a haɗe yace.
"Babu wani wanda zan kuma hana ɗaukan makami,
Dan kare kanshi da ramuwar kisar gillan da akeyi mana."
Cikin tarin Mamaki da al'ajabi Bappa da sauran dattawan suka buɗe baki tare da kallon Ardo Bani, Jabeer ma idon ya buɗe cikin sanyi yace.
"Baba Ardo kayi haƙuri, muyi aiki da al'ƙalami, domin al'ƙalami yafi tokobi, ina nan inata shirin samar da tsaro na musamman kan FULANIN ƙasarmu da nake shugabanta."
Cikin nuna tsantsar fushi da son fusata Lamiɗo Arɗo Bani ya dakawa Jabeer tsawa tare da cewa.
"Kada rufe min baki, meka sani akan Fulani? Me ruwanka damu? Damuwarmu ta shafeka ne? Ina kake sanda ake kashe mana mata, yara, jikoki, mu kanmu bamu tsiraba, in munje mun kai kukanmu a koremu tamkar karnuka, sabida duk baku san darajar fulani ba."
Cikin sauri Ɗanzagi yace.
"Hattara dai Ƙaramin Ardo, wannan sarkine na fulɓe masarautar filɓe ce gaba da bayanta".
Cikin ɗaga Muryar Ardo Bani yace.
"Tafi can baƙin bawa, bawan banza bawan wofi mai ka sani kan fulɓe, meka sani banda bauta da fadanci, masarautar da kuke bautawa bata san menene fulɓe ba".
Cikin sauri Waziri ya yunƙura zaiyi mgna, da sauri Lamiɗo ya dakatar dashi, sabida zuwa yanzu zuciyarshi ta fara tafasa, yaya daga kawowa mutane ziyara dan ja-jantawa suke neman tozarta mushi masarauta. Cikin ɓacin rai ya kalli su Bappa daketa kama hannun Arɗo bani daketa fizge-fizge yana kwaza musu baƙar mgna, cikin fushi yace.
"Masarautar Joɗa ɗince bata fulani ba?".
A harzuƙe Arɗo Bani yace.
"Tabbas dan data fulanice, da an bamu kariya da tsaro, da an duba kukanmu, a kashemu a hanamu ɗaukar fansa, an kuma kasa bamu tsaro. Nan da mukaje ina shi jikan naka da yake matsayin Garkuwan Fulani, yana can ƙasashen woje, da iya dukiyar da ake bashi tsaro da kariya shi rai ɗaya ta kai a kula da fulanin daji dubu a kuma basu tsaro.
Yau kwana uku da kashe mana mutane sai yau zaku ɗebo manyan riguna kuzo mana da batun wai kada mu rama, sara da suka da yanka mana mutane da akeyi,
Kaida kab zuriyar ka da masarauta ka, babu mutun ɗaya da zai iya jurar koda bulalar *(SHAƊI)* ma bare sara da yanka da suka da wuƙa a hakan kuke ganin kanku Fulani".
Cikin tarin zafin ƙuna da tafasar zuciya Waziri yace.
"To me kuke so muyi muku, tun randa akayi abun munzo bamu sameku ba".
A harzuƙe Bukar yace.
"Ƙarya ne babu wanda yazo".
A hankali Jabeer ya buɗe baki da nufin zaiyi mgna sai yaji Lamiɗo na cewa.
"Uhum jinina kuke cewa ba fulaniba, to ko jaririn da aka haifa yau a jikin masarautar Joɗa zai iya jurarar bulalar SHAƊI bare manya ko ɗan baiwa zai iya bare jinina ƴaƴana ko jikokina, ko kun manta masarautar Joɗa ce tushen Shaɗi?".
Cikin son harzuƙa Lamiɗo Arɗo Bani yace.
"A da can baya ba, yanzu kuma da aka san lusarai ake haifa a masarautar inji an haramta shaɗi a masarautar, yau in kun isa fulani ka bada ɗan ka ko jikanka ayi gasar Shaɗi dashi, in ya iya jurewa, to mun yarda mun gamsu ku fulanine ku masarautar Fulani, in kuwa kun kasa fidda goninku to, ku ba masarauta fulɓe bace."
Wani irin karkarwa jikin Lamiɗo ya fara sabida fusata, wai suda masarautarsuce tushen fulɓe a ƙasar, su ake cewa ba fulani ba, har ake kiransu lusarai, Galadima, Waziri, Wambai, Ɗan iya, Ɗan buram, Ɗan Maliki, Sarkin Dawaki.
Gaba ɗaya hankalinsu yayi masifar tashi sabida ganin tsananin fushi da tashin hankalin Sarki Lamiɗo.
Jamil Jalal Haroon kuwa , hankalinsu na kan Jabeer bisa alamun yana cikin wani hali.
Shi kuwa Jabeer bugun da zuciyarshi keyi ne yasa,
Hankalinshi tashi, ƙarfin addu'o'in da yakeyi ne, yashi iya fahimtar abinda suke cewa.
Kamar daga sama kamar cikin mafarki, sukaji murya Lamiɗo na cewa.
"Ga jikana, Jabeer GARKUWAN FULANI, na badashi a matsayin matashi mai yin gasar Shaɗi ku fito da duk gwanin da kukega shine makurar gwayen yankinku. Ayi Shaɗi dashi yadda zaku samu gamsuwar yakai matsayin ya kasance GARKUWAN FULANI".
Tunda ya amɓaci sunan Jabeer, Sarkin Fada yayi wani irin murmushi mai cike da jin daɗin alamun burinshi zai cika.
Hakama Arɗo bani wani irin asirtaccen murmushi yayi.
Jala, Jamil, Haroon, Hashim, Imran, Galadima, kuwa wani irin zazzaro ido sukayi.
Cikin tsananin kaɗuwa da firgicin batun Lamiɗo suka zuba mishi ido.
Bukar kuwa cikin karaji yace.
"Ba'ana Bukar shi zai kara dashi."
Ya ƙarishe mgnar da fatan Ba'ana ya kashe wanda aka kira da Jabeer tunda jikan Lamiɗo ne.
Jabeer kuwa wani irin kallo yayi kakan nashi, irin kallon nan.
Na lallai kam tsohon nan ka haukace, ka zauce, ai bani bakam ko inuwata bazaku kuma gani a garinkuba bare kuyi wannan gwajin dashi.
Ga mamakinsu kab sai sukaji Arɗo Bani na cewa.
"A yau ɗinan kuma Yanzun nan, a kuma nan za'ayi gasar Shaɗi in har kun isa fulani."
Sosai Lamiɗo yaji hakan bai mishi ba dan a zotonshi za'asa ranane ya koma ya shirya Jabeer kafin ayi gasar, to fahimtar ƙuresu suke neman yi, yasashi gyara zamanshi cikin danne fargabanshi na anya Jabeer zai iya jura yace.
"Na Aminc....!
Yau bisa wani uzuri ban samu yin posting da wuriba, kana kuma ba editing a gurguje na watsoshi, bari in nemo PAGE 16 ko zuwa yan da yamma ne.
By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘
*GARKUWA*
PAGE 16
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘
*FREE PAGE SUN ƘARE DAGA WANNAN PAGE 16 DIN IN DAI KIKAGA LITTAFINA GARKUWA BA TARE DA KIM BIYA NA SAKI A GROUP BA TO NA SATANE, DAN ALLAH DA MANZONSA KADA KU FITARMIN DA LITTAFI DAN ALLAH KU BARI IN SAMU KUƊI zuwa makka😂😂😂*
*Littafin GARKUWA na kuɗine dan Allah da Manzonsa kada ki karanta na sata, kada ki watsamin littafi a sata, turo katin MTN na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276 ki biya ki karanta cikin aminci ba tare da haƙƙi naba. Ko kuma ki biya 1k domin shiga Special Group wanda cikin sati biyu rak za'a gama Part 1, da izinin ubangiji kana a shiga 2, turo dubunki ɗaya ta wannan asusun 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidan biyanki ta wannan number 09097853276 in baki da halin biyan dubu ɗaya ko baki da ra'ayi kina iya turo ɗarinki uku kacal da ban tsauwalaba sabida halin rayuwa da muke ciki. Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki sai littafina in dai kin san niyarki ki saya ki fitar da shine in kuma. Har kin sayane to dan Allah da Manzonsa gaya min in baki kuɗinki in cireki a group na, dan Allah🙏🏻 nace badon niba*
"Na Amince!". Cikin tarin mamaki Jalal, Jamil, Imran, Haroon, Hashim, da duk sauran tawagar Lamiɗo suka, zazzaro ido cikin tarin mamaki da al'ajabi, sam basuyi zaton jin haka daga gareshi ba,
Ya Salmanu kuwa wani irin farin cikin mara misaltuwa ne, ya rufewa, domin yana ganin ikon Allah da yake nuna mishi zahirin abinda yake nuna mishi a mafarkansa tsawon kwanakin da yake a gadon asibiti.
Ba'ana kuwa da tun ɗazu ya iso, wani irin ihu yayi mai cike da farin ciki, da jin daɗin yana ganin zaiyi abinda gaba ko kashe mutanen Rugar Bani sukayi gaba ɗaya, masarautar Joɗa bazata kulasuba,
Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi keyi sabida azabar muguntarsa dake tasowa.
Arɗo Bani ma wani murmushi manufa yayi tare da cewa.
"To, ina gwanin naku?".
Cikin karaɗi Ɗanzagi, ya kalli Jabeer tare da cewa.
"Malami ba faɗen Allah, malamai magada annabawa, Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa, GARKUWAN sarki Lamiɗo, jikan sarki, mai martaba Nuruddee. Jarumin Masarautar Joɗa."
Gimtse bakinshi yayi ganin wani irin kallo mai ma'anoni da yawa da Jabeer ke watsa mishi,
Cikin yin ƙasa da murya tare da tsuke fuskarsa, ya ɗan ronƙofo kanshi, kusa da Lamiɗo murya a kausashe yace.
"Wannan tatsuniyar da kukeyi, bafa koyarwan shariya bace".
Da sauri Lamiɗo ya katseshi da cewa.
"Eh amman koyarwar Masarautar Joɗa ce".
Cikin kufula yace.
"Ya ina ce maka Allah kana cemin gadon masarautar Joɗa ce".
Cikin haɗe fuska da ƙasaita Lamiɗo yace.
"Eh ba addini bane, kuma sai an yishi dan gadon masarautar muce".
Kanshi ya kuma motso dashi jikin kakan nashi cikin taɓe fuska yace.
"Okay to ai sai ka tashi, ka tsaya su zaneka ciki da woje".
Cikin kausasa murya Lamiɗo yace.
"Kai ne dai zaka tashi".
Cikin watsawa kakan nashi wani kallo na lallai ma tsohon nan kanka ya kwance yace.
"Ai bani bane sarkin, kaine sarkin ko?".
Cikin faɗa Lamiɗo yace.
"To ko Ubanka bai isa in sashi abu yace bazaiyi ba".
Jin muryar Lamiɗo ta ɗan yi samane, yasa fadawanshi suka miƙe tsaye,
Ware rigunansu sukayi, suka kamgesu da jajayen rugunan nasu, ta yadda babu mai ganinsu,
Cikin haɗe fuska Jabeer yace.
"Yesss shi bazai ƙiba, tunda kai ubanshi ne, Ni kuwa babu wanda zai sani in zauna in bawa wani ƙaton fatar jikina ya zane, kai jimin zancen son zuciya, kai ni kaɗaine jikanka, a duniya, a nanma baga Ya Hashim ba ai shine babban jikanka, zancen gsky na gaji da wannan tirsashe-tirsashen naku, kanada ƴaƴan ai, ka kira ɗaya daga cikin ya'yan ka yazo ya wakil ceka mana, Amman ni dai kam Muhammad Jabeer babu wani tsohon da zanyiwa mubaya'a in tsaya wani gardin makiyayi ya ɗimeni, tunda ba faɗin Allah bane".
Ya ƙarishe mgnar yana yunƙirin tashi tsaye.
Da sauri Galadima yasa hannu ya kamo nashi, fuskar ya kwaɓe tare da komawa zaune yana gyara hiramin kanshi da al'kyabbar jikinshi,
Cikin tausasa harshe Galadima yace.
"Jabeer kafa san ma'anar GARKUWA a masarauta."
Cikin sanyi da ganin kima da darajar dottijon Jabeer ya kwaɓe fuska tare da cewa.
"Nifa shiyasa wannan mulkin bawai sonshi nakeyi ba, sabida wannan tsarabe-tsaraben daba na addiniba, a buwayi mutun dashi, yaya nasan abu ba Allah ne da manzonsa suka wajabta mana shiba, ace in zauna a cutar dani."
Cikin sanyi Waziri ke jujjuya mishi kai a hankali yace.
"Jabeer Garkuwa fa, kake dole ka kare martabar Masarautarmu kana ka nunawa su fulanin da kake Garkuwarsu kai Jarumine".
Rai a ɓace ganin sufa da gske sukeyi, cikin dakiya yace.
"Bana so, ita wannan sarauta ta GARKUWAN FULANI ku bawa duk wanda kukeso, ni ban nemaba dama".
Shiru Haroon yayi dan gskya harga Allah shi wannan abun yazo masa a bazata.
Jalal kuwa cikin haɗe fuska yace.
"Wannan ma ai zancen banza ne,
An bawa Ya Jafar Galadima, ko kwana ashirin baiba a kai, aka birkita masa rayuwa, kana yanzu kun likawa Hamma Jabeer wani GARKUWA kun kwasomu kun kawomu Rugar fulani, wai kuna cewa ayi gasar duka dashi."
Da sauri yayi shiru ganin Jabeer ya ɗaga mishi hannu.
Jamil kuwa tuntuni idonshi ke tsastsafo ruwan hawaye dan gani yake so ake a kashe Hammansu a ƙarar da ƴaƴan ɗakinsu,
Laminu kuwa ɗan Gimbiya Saudatu matar bappansu Sheykh kuma Kani ga Yah Hisham wani irin dariyar jin daɗi yakeyi.
Shi kuwa Lamiɗo, wayarshi ya zaro, Mai alfarma Sarki Jalaluddin ya kira wanda yake kane ga Jabeer. Wanda ya haifi Mamanshi.
Bayan sun gaisane yayi mishi bayanin abinda ke faruwa, jin haka yasa yace ya bawa Jabeer wayar.
A tsakar filin Rugar Bani kuwa, tuni.
Arɗo Bani ya bada dama na suduka yana shekantawa gari cewa.
Ana gamgamin Shaɗi yanzu-yanzu tsakanin Ba'ana da kuma jikan Sarki Nuruddeen.
Tuni an firfito da ganguna anata kaɗe-kaɗe da bushe-bushen sarewa, kana ana buga babban gangan dake tsanar da makotan Rugar Bani sauran rugage alamun za'ayi Shaɗi yanzu.
Kafin kace kobo, Rugar Bani ta cika tayi maƙil da mutane, Maza da mata, matasa da tsoffi, sabida an san duk sanda za'ayi Shaɗi ana bada sanarwar, kwana uku kafin nan to jin wannan na gaggawa kuma da jikan Sarki za'ayi yasa, mutane taruwa, gashi ranar jumma'ace, duk matasan rugogin suna, gida tunda suka dawo sallan jamma'a.
Rugar Bani ta cika tayi maƙil da bani adam, tako wacce kusurwa tsastsafo akeyi kusufa-kusufa.
Jin karan tamɓarin ganganr Shaɗi ne ya ƙara gaiyato mutane harda na cikin garin Shikan, tuni ƙabilun Bonon sun garzayo cikin Rugar Bani.
Bukar kuwa mahaifin Ba'ana shida kanshi yaje, cikin Garkensu ya ɗauko tukunyar tsumin bulalim shaɗin da Ba'ana ke tsumasu da dafin kunamai da sauran sihirurruka, na dodon tsafinsu Bonon.
Matasa majiya karfi ne keta ɗebo ruwa, cikin rijiyoyin garin.
Suna jiƙa taron wurin dandamalin, da za'ayi gasar kaɗe-kaɗen duk sun taru sun cika kunnen kowa.
Jabeer kuwa bugun da zuciyarshi keyi shiyafi komai tada mishi hankali.
A can cikin gidajen Rugar kuwa, duk yan samari da yara sun firfito.
A gidansu Shatu kuwa,
Tunda taji Shelan da Nasuduka yakeyi cewa gasar Shaɗi tsakanin Ba'ana da jikan sarki.
Kuka ta farayi, cikin tashin hankali da kiɗima ta kamo hannun Ummiy da tayi shiru sai ido take binsu dashi, murya na rawa tace.
"Ummiy kijifa, zasuyi ya kashe, wani wanda baijiba bai ganiba, sunfa san illar dake cikin bulalinshi."
Ganin Ummiy dai ba mgna zatayi ba, yasa ta kamo hannun Junainah cikin tsananin tashin hankali tace.
"Junainah ki gudu, kije kicewa Bappa kada ayi gasar nan, Ni dai a bari na haƙura zan auri ya Ba'ana a yadda yake, zan zauna dashi, zanyi ƙoƙarin gyara mishi, rayuwa na gaji, kada a sake cutar da wani a kaina".
Da sauri Rafi'a ta kalleta jin ta kamo hannunta cikin zubda hawaye tace,
"Rafi'a wlh ya Ba'ana zai iya kashe mutun a kaina, da dafin kunamai yake tsuma bulalinshi, da wani tsafin, me ribata ayi ta cutar da mutane a dalilina, babu fa wani mahaluƙin da zai iya cin Ya Ba'ana gasar Shaɗi, babu wanda zai iya jurar azabar bulalinshi fa."
Cikin sauri ta miƙe tare da miƙar da Junainah, sai kuma duk suka koma suka zauna,
Jin muryar maƙocibsu Sarkin aska, yana cewa.
"A a Shatu kada ki tura kowa, kada kuma kije kin tsumayi sakamakon gasar yau in sha Allah zata banbanta da na baya .
Yanzu ma Arɗo Bani ne ya aikoni da in gargaɗeki."
Yana faɗin haka ya juya da sauri ya fita, kana ya nufi wurin gasar.
Da ido suka bishi. Ita kuwa Junainah da sauri ta miƙa ta nufi kitchin ɗin su, tana cewa.
"Yauwa Adda Shatu, barin in kawo mana gasassun zabbin da Ya Ba'ana ya kawo mana muci.
Ɗazu da nace muci Adda Rafi'a ce, tace mujiraki."
Cikin sanyi Rafi'a tace.
"Yauwa Junainah kawo mana, muci yau tunda gari ya waye bamuci komaiba."
Gyara zansu sukayi, kana ta kalli Shatu cikin kula tace.
"Dan Allah Shatu muci abinci, kinga Ummiy ma taƙi cin komai ganin, yadda kiketa kuka tunda kikaji ɓatansu ya Giɗi da rasuwar Ya Lado da Inna."
Cikin zubda hawaye ta gyaɗa mata kai, sabida ita kanta tasan tana jin wani irin masifeffen yunwa, tamkar zai kasheta.
Da sauri Junainah ta nufosu riƙe da akoshin gasassun zabbin da aka zuba dafin macijin a cikin.
A can cikin tsakiyar garin Rugar Bani kuwa.
Tuni su Ba'ana an gama shiryawa zalumci, domin dama ai a ƙa'ida shi zai fara duka,
Yana tsaye sai zagaya filin yake yana zane iska, makaɗa da mabusa nata yi mishi kirari.
A cikin wurin da Fadawa suka kange Lamiɗo da tawagarsa kuwa, anata kai ruwa rana da Sheykh Jabeer,
Cikin kufula, yake cewa Sarki Jalaluddin da suke waya dashi.
"Nifa babbar matsalarta wannan abun da za'ayi ba *Sunna* bace ba kuma *Farilla* bace, ba kuma *Mustahabbibace*, kai ko a babin *Makaruhi* ban taɓa cin karo da wannan banzar al'adar da kukeso in yarda ayita dani ba,
Ina kuma da yaƙini in da zan bajeta a babin musulunci, kai tsaye za'a iya karhantashi, sabida ai cutar da kaine kuma, Musulunci bai yarda mutun ya cutar da kanshi ba, haka kurum kuce wai in tsaya a zaneni, inji shi kanshi kakan Lamiɗon Joɗo da yaji haza a gasar Shaɗin shine ya hana wannan al'adar a masarautarsa sannan yanzu ace za'a saketa a kaina bayan tsawon shekaru 145 ba'ayishi ba, tun zamanin jahiliyan ma an bar abu sai yanzu ku tara abu a kaina, to wallahi bafa zai yiwuba."
Cikin kufula Sarki Jalaluddin yace.
"To ya kakeso ayi ɗan masu ilimi kowa jahiline sai kaine mai ilimi sabida tsabar tsoro da ɗan karen son jiki kana gudun abinda zai taɓa lfyarka shine zakayi ta jawo mana wasu dogin falsafofi, a hir ɗin kafa Jabeer ko uwarka bazan sata abu taimin musuba".
Gaba ɗaya sun hautsuna mishi zuciya,
Ji yadda suketa zageshi, dan kawai yace bazaiyi abinda al'adace ba addiniba sai wani ce mishi suke ko uwarka ko ubanka, bayan sun san baya kuran hakan, rai a ɓace yace.
"Uwata kace ai tunda ita ai ka haifa ba niba ko?, zancen gsky bafa za'ayi wannan abunba, sun daɗe basu ce mana lusaraiba, dolene, sai sun yarda mu fulanine, kai yau nifa ba bafulatani bane.
A kirani da ko wacce ƙabilar ma in anga dama aikin kawai!".
Yana faɗin haka ya katse kiran.
Laminu kuwa da yake cikekken ɗan jarida, tuni yana naɗe komai a faifai jawaban su.
Shi kuwa Sarki Jalaluddin, ido ya zubawa wayar jin jikan nashi ya katse kiran, murmushi yayi, irin nasu na manya, kana da sauri ya kira, Umaymah.
A can Babba birnin Katsina, kuwa Gimbiya Khadijah Umaymah kenan , wacce take matar ɗan Sarkin Tsinako, Kekkyawar mata mai cikar haiba nitsuwa, tana kishinɗe, bisa wata tattausar doguwar kujera, yayinda Hadimanta biyu ke mata tausa.
Jin wayarta na suwane, yasa ta buɗe idanunta dake lumshe, tunda sukayi waya d, ɗan ta Haroon ke gaya mata inda sukaje da ƴaƴan ƴar uwarta mafi soyuwa a rayuwarsu ne, taketa murmushi.
Ganin sunan mahaifinta ne yasa tayi saurin amsa kiran.
Bayan sun gaisane, Sarki Jalaluddin ya ɗanyi murmushi cikin nitsuwa yace.
"Khadijah, kira ɗan ki, ki bashi umarnin bin umarnin mu, domin yana nuna mana ai bamu muka haifeshi ba, bazamu tirsasashi ba".
Cikin tarin girmamawa tace.
"Ranka ya daɗe, me kukeso in bashi umarni a kai nasan bazaiyi min musuba".
Cikin jin daɗi yace.
"Kice dashi ya amince da gasar da za'ayi".
Cikin sauri tace.
"To An gama yanzu kuwa, in sha Allah zaku sameshi mai biyayya a gareku".
Daga nan sukayi sallama,
Kana ta kirashi, sau biyu tana kiranshi baya ɗagawa, sabida kanshi ya ɗau zafi yana ganin za'a tirsasashi ya cutar da kanshi.
Ga wani irin azabebben tsinkewa da zuciyarshi keyi,
Ji yake tamkar zata faso ƙirjinsa ta fito, tayi ta tsalle a doron ƙasa.
Gashi duk tsoffin Masarautarsun sun zagayeshi.
Kowa da abinda ke ce mishi.
Ga uban kiɗen-kiɗen dake hawa mishi kai.
Ita kuwa Umaymah ganin bai amsa kiran bane, yasa ta kira Haroon yana ɗagawa tace.
"Ina Jazlaan bashi wayar".
Da sauri yace.
"To Umaymah uwar Garkuwa gashi nan ido ya raina fata".
Cikin barkwancinta da yaron nata tace.
"Kaci gidanku Haroon Ni ɗana ba ragobane".
Murmushi yayi tare da cewa.
"To mu gani a ƙasa mana Umaymah".
Yana faɗin haka ya miƙa Jabeer wayar wanda yake cewa Lamiɗo.
"Bafa zan yiba, tsohon nan gwara ka miƙe kaje ayi da kai tunda kaine sarkin Masarautar Joɗa, Ni nan babu abinda na sani bayan nonon uwata sai al'ƙur'ani da hadisai, sai likitancin da kuka sani na karanta a dole badon raina yasoba, tun ina yaro kullum Ni a cikin sani dole kuke da tsabar rainin hankali, kaje a jibgeka, Ni kuwa nayi al'ƙawarin zan jinyaceka, Lamiɗo Joɗa."
Ya ƙarishe mgnar yana amsar wayar da Haroon ke miƙo mishi cikin faɗa yace.
"Mitsss wai meye kaketa tura min wannan argar wayar taka ne?".
Cikin mamaki Haroon yace.
"Kan uba Jabeer wayar tawace ma arga, wayar da kuɗi ta sun kai rabin million To inma argace Umaymah ce bisa layi".
Ba tare da ya kara wayar a kunneba yace.
"Hello Umaymah".
Cikin tausayi Jalal yace.
"Hamma Jabeer baka kai wayar kunneba".
Lips ɗinsa ya taune tare da cewa.
"Au, zama su sani yin abu da yawa".
Haroon kuwa mamaki yakeyi domin karo na forko kenan da yaji Jabeer yace Hello a madadin Assalamu alaikum, da shine abinda yakeyi.
Ita kuwa Umaymah tana jin ya kara wayar a kunne shi ya kira sunanta cikin rauni.
Murya a kausashe tace.
"Jabeer".
Da mamaki ya amsa dan sama da shekaru goma sha biyu kenan da Jazlaan take kiranshi, cikin sanyi yace.
"Na'am Umaymah". Cikin bada umarni tace.
"Jabeer ka tashi maza yanzu ka shiga fagen gasar nan ayishi da kai, bana son musu umarnine ba shawara ba".
Cikin sauri ya zaro siraran kyawawan idanunshi,
Dai-dai lokacin kuma Lamiɗo ya miƙe tsaye cikin tashin hankali da kiɗima da firgici da baƙin cikin dakatar da gasar Shaɗi da akayi a masarautarsu ya sani da anayi da Jabeer bazai ƙalubanceshi ba, cikin sanyi yace.
"Zanje za'ayi dani, zan tabbatar da darajar masarautatarmu bata rusheba."
Da ido yabi Dottijon kakan nashi wanda a ƙalla ya kai shekaru 91 a duniya.
Cikin kauda kai yace.
"To Umaymah yadda kikace haka za'ayi amman bari in kira Sheykh Abdulkareem in sanar mishi in ya amince dai zanyi".
Da sauri tace.
"A a ban yafe ka kirashi ba, wato don kasan in ka kirashi zai kira Sitti da Mai alfarma Jalaluddin da Sarki Nuruddeen ya dakatar da duk abinda za'ayin, tunda na san cemishi zakayi ba addini bane, al'adace, to ban yardaba maza tashi".
Ganin Ya Hashim na miƙa masa wayarshi ne yasashi cewa Umaymah.
To cikin sanyi.
Yana amsa wayar da Ya Hashim ya miƙa mishi yaki Muryar, mahaifinshi cikin sanyi da kuma alamun yana kukane yace.
"Jabeer ashe har kayi girman da Lamiɗo zai umarceka da yin abu kaƙi yi mishi mubaya'a,
Ashe har na haifi ɗan da zai ja da mahaifina."
Cikin sanyi da rauni yake jujjuya kai murya na rawa yake cewa.
"A'a Abba, kayi haƙuri kada kayi kuka a kaina."
Bai kulashiba yaci gaba da cewa.
"Jabeer Ashe zuciyarka har tayi tauri da kangarewar da kanaji kana gani za'a daki mahaifina a gaban idonka, bazaka zame mishi GARKUWA ba, Jabeer wannan shine tukuicin tsantsar son da mahaifina keyi muka, wanda har ya jazamin ƙiyayya a wurin yan uwana sunaga ya fifitaku kan sauran jikokinsa Especially ma kai Jabeer komu daya haifa baya nuna mana son da yake nuna maka, shine zaka bari a dakeshi mutun mai shekaru 91 da ɗaya a duniya kai me shekaru 30 bazaka iya zame mishi GARKUWA ba?".
Cikin rauni da ƙunar zuciya, ya miƙe tsaye hannunshi yasa ya kamo na Lamiɗo cikin tarin ƙuna da zafin rai da takaici yace.
"Na Amince, zanyi gasar na yarda, ka koma ka zauna".
Wani irin farin ciki ne ya ziyarci, zuƙatansu gaba ɗaya, sai dai kowa da irin manufar farin cikinsa.
Jin haka yasa fadawan janye labulen da sukayi musu.
Shi kuwa Lamiɗo hannunshi yasa ya kamo hannun Jabeer, cikin tsantsar farin ciki da al'fahari da ƙasaita ya fara taku, suna ratsawa cikin taron.
Kana fadawansu na biye dasu a baya.
Ɗanzagi yana.
"Takawarka lfy Sarki mai daraja Lamiɗo ɗan Lamiɗo jikan Joɗa. Gyara kimtsi".
A haka har suka isa cikin asalin dandamalin da aka jiƙashi jilak da ruwa, sabida hana ƙura wanzuwa.
Gaba ɗaya taron mutanen wurin maza da mata manya da yara, Jabeer suka zubawa ido, sabida duk wanda ya ganshi yaga sahihin Balarabe, mai kamala da nitsuwa, uwa uba kima da haiba, ƙwarjini shi ya cika dukkan idanun magautanshi dake wannan yanki,
yayinda masoyanshi ke taraddadin abinda zai faru.
A tsakiyar filin suka tsaya, hannunsu dake raƙe dana juna Lamiɗo ya ɗaga tare da fuskantarta gabas, kana ya juya yamma, ya kuma juyawa kudu da Arewa, sannan suka dawo tsakiyar filin,
Cikin ƙasaita, yace.
"Ga GARKUWAN FULANI, kuma daga Wannan nasarar da zaiyi a gasar nan,
Zai tabbatar GARKUWAR Masarautar Joɗa, GARKUWA kuma mai ikon zama inda yaso a cikin fada".
Dariya Bukar yayi kana ya ɗaga hannun Ba'ana da yaketa wani abu da ƙirjinshi kamar damisa,
Cikin isa da yaƙini da al'fahari yace.
"Mu kuma ga namu Garkuwan, da muke da tabbacin bai taɓa gasa ya faɗiba".
Sake hannunshi Lamiɗo yayi kana ya juya ya koma ya zauna, cikin rumfar da akayi musu masauƙin.
Al'ƙalin gasar ne yazo tsakiyar taro, kamar ko yaushe, hannun Ba'ana ya kamo, ya ɗaga sama, hakan yasa, gaba ɗaya makiɗa da mabusa suka ƙara sautin kiɗe-kiɗen su, wanda Jabeer ke jinsa har tsakiyar kansa, Allah ya sani, baya son hayani koda dai-dai da ƙwayar zarra ne, ga wani masifeffen fargaba da tsinkewar da zuciyarshi keyi, yanaji tamkar yasa hannunshi ya toshe kunnuwanshi.
Ɗan wani gajeren tsaki yaja sabida Allah ma ya sani baya son kallo, to kuma yanajin yadda idanun mutane ke yawo a jikinshi.
Shi kuwa al'ƙalin gasar, yana sake hannun Ba'ana yazo ya kamo hannun Jabeer,
Da sauri ya juyo ya kalleshi sabida kamo hannunshi da yayi sai yaji tamkar hannun jariri ya kamo dam laushi da taushin fatar, hannun sanyi ƙalau,
girgiza kanshi yayi cikin tausayawa, sabisa, ya za'ayi ace mai wannan taushin hannun fatarsa ta iya jurar azababbun bulali masu masifar zafi.
Ɗaga hannun Jabeer yayi sama.
Yana mai nunawa taron mutanen shi a matsayin dashi za'a gwabza.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, duk abinda akeyi idonshi na cikin ɗan siririn farin galashi mai garai-garai dake liƙe a fuskarshi,
Hannunshi kuma riƙe da carɓinshi, kana bakinshi ambaton sunan Allah.
Cikin tarin mamaki ya kalli,
Al'ƙalin gasar tare dasa hannunshi ya riƙe bakin al'kyabbar jikinshi cikin haɗe fuska yace.
"Me hakan!?". Cikin saurin rusunar da kai Al'ƙalin gasar yace.
"Za'a cire kayan jikin naka ne!".
Cikin tarin mamaki ya zazzaro ido waje, a baiyane yace.
"Akan me kenan, suturar da Allah yayi min a matsayin mulmi, in killace kaina, shine zaku yayemin a cikin dubban dubatan mutane?".
Cikin dakiya Al'ƙalin ya ɗan kalleshi domin kwarjinin Jabeer ya cika masa fuska cikin sanyi yace.
"Allah rene, ƙa'idar gasar ce, ba'ayi da kaya a jikin mutun sai ɗan kamfai, kawai ake bari a jikin mutun".
Cikin kufula da harzuƙa yace.
"To bada niba, Ni nan Muhammad Jabeer wallahi banyi lalacewar da zan tsaya tsirara a gaban jama'a ba".
Yana faɗin haka ya juya a fusashe, zai fita cikin taron.
Ganin hakane yasa Galadima, yayi saurin tasowa, kana Ɗan buram na biye dashi a baya, tareshi sukayi tare da kamo hannunshi.
Da sauri suka juyo suna. Kallon gungun wasu matasa wanda suka kece da dariyar ƙeta cikin hausarsu ta ƙabilu suke cewa.
"To ku ɗan naku ko yadda ake gudanar da gasar ma bai sani bane? Ya zaiyi zaton da wannan shigar tasa za'a dakeshi, to ai ko bulali dubu za'ayi mishi ba jinsu zaiba,
Kai Ɗan kazagi, ka gaya mishi nan ba cikin masallaci bane.
Nan wurin shaɗi ne".
Jiyo hakane ya sa ran dukkan musulman wurin ɓaci.
Sabida sun fahimci kafuraine masuyin wannan zancen.
Galadima kuwa da Ɗan buram sun ɗauka abin wasane, a zatonsu zasu shawo kan Jabeer a sauƙaƙe, amman ina ya tiƙe yace babu wani zinɗiƙin ƙaton da zai sashi ya yaye suturar dake jikinshi.
Dariyar da su Arɗo da sauran mutane keyine ya hautsuna lissafin Lamiɗo.
Cikin harzuƙa ya taso, har kamar zaiyi tuntuɓe ya nufi inda su. Waziri, Wambai, Ɗan buram, Ɗurɓi, Da Galadiman, cikin tashin hankalin alamun akwai wata babbar manufa da Galadima ke son cimmawa cikin lamarin ya riƙe hannun Jabeer tare da cewa.
"Haba Jabeer kai wanne irin mutun ne mai kafiya da taurin kan tsiya, yaya muna binka kana zillawa, muna haɗaka da Allah da Manzonsa amma kana tunzuramu, wallahi da yau sai anyi gasar nan!".
Cikin tsananin ɓacin rai yace.
"In tsaya a tozarta ni kuke so.
Ayimin tijara kukeso, da wanne idon zan kalli al'ummar Annabi da jiki tsirara".
Cikin kufula Waziri yace.
"Waya ce maka tsirarane?".
Murya a sama yace.
"Tsirara ne mana! Tunda sunce wai dagani sai Boxes zan tsaya, ka kuwa san ko Mahaifiyata data haifeni tun ina shekaru shida a duniya bana tsayuwa a gabanta dagani sai ɗan kamfai, tunda nake Mahaifiyata, Mahaifina, Yayuna, Uncles, na Aunty's na, babu wanda ya taɓa dukana, sabida ban cutar dasu da komaiba bare su hukuntani da duka haka kurum rana tsaka kunce in tsaya a dakeni, na yarda, sannan yanzu kuma ace nai tsirara, kai bafa wanda zan yiwa mubaya'a akan hakan..!."
Tas! Yaji sauƙan wani irin gigitaccen mari sai dai babu wanda ya ga sauƙan marin sabida suna tsakiyarsu Waziri ne, kuma sauran mutanen garin duk kowa bayan su Waziri suke iya gani.
A harzuƙe ya ɗago kanshi,
Lamiɗo ne ya gani tsaye a gabanshi.
Jan hannunshi yayi da iya ƙarfin shi na tsufa.
Tsakiyar filin suka koma, cikin fushi yace.
"Galadima zoka cire mishi kayan."
Da sauri Galadima ya motso gabanshi.
Su Waziri kuwa duk suka koma cikin Rufarsu masauƙinsu.
Wani irin tsuma da karkarwa jikin Jabeer ya farayi, tun sanda yaji sauƙan marin.
A take idanunshi nan su kaɗa sunyi wani irin masifeffen juyewa sunyi jazir,
Hatta lips ɗinshi karkarwa sukeyi. Wani irin tarin baƙin cikin da bai taɓa jin irinsa ba a duniya ne, ya lulluɓe masa zuciya.
Koda randa Ya Jafar ɗinsu ya zauce, baiji makamancin wannan ɓakin cikinba.
Ji yakeyi Tamkar ya haɗiyi zuciyarshi ya mace ya bar duniyar kowama ya huta,
Rumtse idonshi yayi da azaban ƙarfi lokacin da yaji, Galadima ya gama komce masaƙalan al'kyabbar jikinshi,
kana ya buɗe shi, yayi ƙasa dashi, har saida ya cire hannayenshi a ciki.
Haroon dake gefensu ya miƙa wa al'kyabbar, kana a hankali ya kuma matsowa gareshi, hannunshi yasa saman kanshi ya ɗage zagayen baƙin abin da yake kan Hiramin, kana yasa hannunshi ya janye hiramin.
Kekyawar fuskarshi ta fito ras, tattausan baƙin gashin kansa dake kwance lib-lib ya baiyana, wanda hakan yasa kaso 70 cikin ɗari na dubban mutanen dake wurin suka zuba ƙwayar idanunsu kanshi, da yawa tasbihi da ta'ajjudin irin kyau da haibar da Allah ma ɗauka kin sarki yayi mishi sukeyi.
Jalal kuwa ji yake tamkar ya rinƙa kurma ihu, Allah yasani baya son abinda zai cutar musu da Hammansun,
Jamil kuwa tuni hawaye yake zubdawa,
Ya Hashim, Imran, Sulaiman, kuwa dukkansu sunkuyar da kawunansu sukayi ƙasa.
Laminu kuwa wani irin masifeffen jin daɗi yakeyi, hakan yasa ya ƙara kutsowa cikin filin hakan ya bashi daman yin viewing da kyau.
Shi kuwa Jabeer tafarfasar da zuciyarshi keyi yayi masifar tsananta lokacin da yaji, Galadima ya zare mishi tattausar rigar shaddar dake jikinshi.
jin yasa hannunshi yana shirin zare mishi singlet ɗin jinshi ne yasashi, ƙara ambaton sunan Allah da sauri-sauri, sabida ji yakeyi tamkar ya buɗe ido ya shaƙo moƙoshin Galadima sai ya sumar dashi, tabbas da ace al'ƙalin gasarne ke cire mishi kaya da tuni ya daku.
Cak ɓari da karkarwan da jikinshi keyi ya bari,
Lokacin da yaji Galadima yasa hannunshi ya kwance zariyar dogon wondon jikinsa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun, Hasbunallahiwani'imanwakil.
Allahumma ajjirni fi musubati!!.."
Ƙasa idawa yayi, jin an saɓule wondon jikinsa yayi ƙasa,
da ƙarfi ya buɗe kwayar idanunshi da suka koma tamkar garwashin wuta. Tafarfasar da jininshi keyi shine abu mafi tartsatsi a rayuwarsa.
Hannunshi Galadima ya jawo da ƙarfi wanda dole yasa ya ɗaga sawunshi ya tsallake wondon ya zama babu komai a jikinshi dagashi sai Boxes wanda Allah yayi mai ɗan tsawone yazo har kusa da guiwarsa saidai a matse yake.
A tsakiyar filin ya tsaidashi kana ya juya ya koma ya zauna kusa da Lamiɗo.
Jalal ne ya sunkuya ya ɗauki wondon da sauri ya miƙa wa, Haroon.
Shi kam Jabeer zuwa yanzu,
Ya sani a duniya ba'a taɓa yi mishi tozarci sama da wannan ba, ji yakeyi a duk faɗin duniya babu garin daya tsana sama da garin Rugar Bani, bai taɓa jin haushi da tsanar wani abu a duniya ba sama da mutanen garin Bani, ji yakeyi ya tsanesu gaba ɗayansu, ya tsani komai nasu, baya so da fata da sha'awan komai nasu.
ƙasar garin ma da yake tsaye a kai ya zuba mata ido ji yake tamkar ya ƙonata ta sauya launi daga farin yashi zuwa baƙin yashi.
A tsakiyar taron kuwa, da sauri al'ƙalin gasar ya jawo hannun Ba'ana da ya zaro wata asirtaciyar bulalar tsamiya, daga cikin randar bulalinshi
sai wani motsi bulalar keyi tamkar tanada rai.
Bayan Jabeer al'ƙalin gasar ya kawoshi. Yana sake hannunshi masu busar al'gaita da sarewa suka farayi da ƙarfin su.
Lokaci ɗaya kuma ranar data take buɗe tarwal ta lumshe.
Mutanen kuwa sai tasowa da ife-ife akeyi. Kallo kuma kab ya dawo kan farar kekyawar fatarshi da kekyawan baƙin tattausan gargasa yayi mishi ƙawanya, iya kyan fatarshi kaɗai ya ishi ɗan adam kallo.
Da ƙarfi Jabeer ya taune lips ɗinshi, yana maiji tamkar zai hudasu sai ambaton sunan Allah yakeyi, babbar yatsar ƙafarshi ta dama yasa yana caka ƙasar garin, kana yatsunshi na hannun kuwa yasa babban yana zagaye kan ƴar manuniyarshi.
A yadda yake jin zafi da ƙuna da baƙin ciki a cikin zuciyarshi ya tabbatar babu wani abu da za'ayi mishi a yanzu yaji zafinsa fiye dashi, to me za'ayi mishi mai zafi sama da tsiraiceshi da akayi.
Ba'ana kuwa cikin dariyar mugunta da sautin amo mara daɗin ji, ya taƙar-kara ya ɗago bulaliyar asirin nan, da iya ƙarfin shi ya zabga mishi ita a tattausar fatar tsakiyar bayanshi.
Da ƙarfi su Jalal kab suka rumtse idanunsu.
Lamiɗo kuwa wani irin kallo yayiwa Jabeer da yayi.
Wani ir.....!
Biya darinki uku kacal domin jin wannan labari har ƙarshe.
Dan Allah da Manzonsa kada ku fitarmin da littafina.
Wannan shafin nakune gaba ɗaya waɗanda suka karanta FREE PAGE🤝🏻😘🥰
By
*GARKUWAR FULANI*