Cikin tsananin tashin hankali yake fad'in Musaddiq...Musaddiq kana inane!?Shiru ba amsa yacire wayar ya duba har yanzu a had'e suke,wucewar wasu dak'ik'u Julaibib yana cigaba da kiran sunan shi Musaddiq!Dakyar ya amsa.Kana inane? Musaddiq yamirgina kai cikin ciwo"bazaiyi amfanin kome ba,na san mutuwa zan yi tawa ta riga ta k'are,D'ansarai...kab... ka6uya... k...kak... kaw... wai.Zuciyar Julaibib tasake tsinkewa yafara kuka"na rok'eka da girman ALLAH kafad'a min inda kake zan zo in taimake ka...kai kad'ai karage min d'an uwa na jini a doron duniya!yacigaba da magiya har Musaddiq yabud'e baki dakyar yace"ina wajen masallaci.Wani masallacin? Wanne Musaddiq?
Yayi tambayar a gaggauce jin wayar shi tayi k'ara alamar caji saura kad'an yak'are... Musaddiq ya kasa magana sai nishin azaba yakeyi... Wanne daga cikin masallacin Muss...kafin yak'arasa fad'in sunan difff wayar takashe kanta.Yafurzar da wani huci yana kallan k'onannun k'asusuwan Sudaida sai yaji kukan cakkk...Ya tsaya,yamik'e tsaye yana mata addu'ar dacewa da rahamar Ubangiji"Zaujatiii...ya fad'i sunan yana jijjiga kai"sai ALLAH yahad'a mu a lahira... uwargidata ta duniya da lahirahh!...
Koma wani masallaci ne Insha-ALLAH sai ya gano Musaddiq ya bashi taimakon gaggawa iyakar iyawarshi,zuciyarshi tabushe,wallahil-azim shima sai yayi kisa sai dai idan bai had'u da arne ba;koda zasu kashe shi,yana fita kuwa yaga k'aramar bindiga an kashe wani arne ta fad'i a hannunshi, yad'auka ya lalube aljihunshi yakwashe sauran harsashin yaloda a ciki sannan yafara tafiya cikin sand'a yana bin bango,daga nesa yahango gungunsu sun dumfaro inda yake,a hankali yazame yakwanta a cikin gawarwaki kamar shima mataccen ne.
Suka zo suka wuce suna surutai da yaren Bajju,a d'an abinda yake tsitssinta daga yaren ya fahimci harsashin sune yak'are zasu koma gida su k'ara sabon lodi,dan haka yad'aga bindiga yasaita su daga kwancen ALLAH ya taimakeshi ya harbe guda uku nan take suka zube a k'asa matattu,sauran suka fara gudun ceton rai suna zage-zage a cikin gawarwakin nan akwai wanda bai mutu ba, amma dan abu kazan uban mutum yabari muje muk'ara shiryawa wallahi zai gane da gero ake koko...Julaibib yasake harba bindiga yasamu wani a kai shima ya fad'i yana ihu da kururuwa,sai da yak'ara mishi harsashi biyu sannan ya tashi yabar wajen kafin su dawo,zuciyarshi tana tafarfasa da kalaman wanda ya harbe Sudaida"zan fasa k'ok'on kan matarka...bata sauran amfani a doron duniya"may her gentle soul rest in hell... Julaibib a gaban idanuna sukama Adnan da Sagir yankan rago...ank'ona su Inna a gidajansu... sun kashe su Baba a masallaci...kalaman da suka dinga mishi amsa kuuwa a k'wak'walwarshi kenan.Sai yaji wani k'arfi yasake zuwa mishi.
Yana cikin tafiya yaci karo da gawar Abdul d'in Yaya Karima an daddatsashi abun ba kyan gani,bai tsaya ba dan tsayuwar bata da amfani tunda ya riga ya mutu,su da arnan kuma kowa k'ok'arin kashe kowa yakeyi haka yakeya cin karo da gawarwaki kisan wulak'anci!Julaibib yayi yawon bin masallatai amma baiga Musaddiq ba,a wajen masallacin Malam Murtala yaga wasu mutane guda biyu an sa musu taya sun k'one k'urmusss...ba ta yadda za ayi ka gane ko suwaye wallahi,yaciga da tafiya zuciyarshi na tafarfasa daga baya yaji an harbe shi a kafad'a ashe wasu daga cikin su sun hangoshi... yajuya yana harbinsu shima har sai da harsashi yak'are,yatura bindigar a aljihu yakwanta yana a k'asa cikin mawuyacin hali jini yana zuba.
A wannan rana ta litini kwana akayi ana gumurzu tsakanin musulmai da arna,duk da musulmai masu kayan aiki k'alilan ne amma sunyi k'ok'ari da k'arfin zuciya suma sun kashe arna ba wanda yayi galaba akan wani,kare jini biri jini akayi"ragasss mutuwar kasko.Toh wayewar gari ranar talata kenan kowa ya galabaita ba sauran k'arfi ba kayan aiki,ba abinda mutum zai sa a bakin salati,irinsu Julaibib masu azumi ranar litini babu kome a cikinsu sai abinda sukayi sahur a daren lahadi, ga raunuka a jikin mutane da yake buk'atar taimakon gaggawa amma kayan agajin(first aidbox) tun dare yak'are.Su kuma wad'ancan anata dafa musu abinci da kayan sha na k'arin k'arfi suna zuwa suna cika cikinsu, bayan haka kuma wad'anda akayi gumurzun dare dasu, sai suka dinga komawa gida, wasu matasan na daban suna shiga cikin gari da sababbin kayan aiki.
(Tabbasss ni 'yar Ibrahim Asdilat KD...ganauce, ALLAH yasa inga Annabinmu Muhammad Sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam...yadda naga wannan al'amari ganin idanuna)
Kuma a wannan safiyar ta talata jirgin k'asa yashigo garin musulmai suka fara hamdala ga Ubangiji cewa an kawo musu d'auki...Tabbasss d'auki a kawo ta hanyar k'arama barno dawaki dan k'ungiyarsu (CAN) ce takawo musu k'arin makamai,to a wannan lokacin ne sukama musulmai ainihin kisan k'are dangi, suka tarwatse kome da kowa na garin...musulmai sai kabbara da addu'o'i sukeyi a duwatsu suna harbinsu... amma ko gezau basuyi ba...sarkin yawa ai yafi sarkin k'arfi...Zakara a rataye baya caara;wasu na shiga gidaje sai sunma gida k'ark'af da kayan ciki sannan su banka mishi wuta,haka shaguna da koma inane, shagunan bakin hanya kuma sun kwakkwashe kome amma basu k'ona suba saboda wai anan zasu fara sana'o'insu.
A wannan mawuyacin halin sukayi a rangama da Julaibib yayi matuk'ar galabaita yana numfarfashi,wata Juli ce tanuna shi"yauwa ga shegen da muke ta nema tun jiya,yabisu da kallo idanunshi sun kad'a jawur,dan tsabar rainin wayo da samun waje "kuturu da gad'a a rama.Wai har da mata suna rik'e da wuk'ak'e gayama jini na wuce,wanda za su iya harbi da k'ananan bindigogi sun rik'e,wasu da kokara da gorori, Kauuu...bazato yaji an buga mishi kokara akai"dan abu kazan ubanka you've no respect muna tsaye kaima kana tsaye?
Kaci sa a ba bindiga a hannuna dana fasa k'ok'on kanka,Juli tamik'a mishi na hannunta"ga wannan"yature hannunta"rabu dashi ba yanzu zamu kasheshi ba sai yaci naman ubanshi me dogon gemunnan gashashshe; Now just kneel down,rise up your hands and close your eyes"haka yakai gwiwoyinshi k'asa yayi yadda yace.Wani da yayi tatil da uwar laifi yafara tambayarshi da yanayinsu irin ta mashaya"kai ne D'ansarai Lecturer a Gidan-Waya da nace kasamo ma yata gurbin karatu kace bata da credits d'in da za a d'auketa ko?
Yayi kamar baiji abinda yafad'a ba.Sai yabuga mishi gora a kafad'a"childish monger I'm I not talking to you?Zuciyarshi tak'ara bushewa wallahi shak'a d'aya zai wannan ragowar ruwan burkutun numfashinshi yad'auke har abadan duniya a doron k'asa,sai kawai yamik'e tsaye yana kallanshi cikin idanu"Yes Indeed,I'm D'an Sarai Lecturer in Kaduna State College of Education Gidan-Waya.Wani yazo gabanshi"how dare you baka da kome amma zaka nuna mana zafin kai?Ka san harda wancan tsinanniyar makarantar taka daka bud'e yasa mukayi yak'innan?Dan na san halinka sai kasa wasu daga cikinmu sun zama irinku masu sallah,dama yara nawa kasa suka zama irinku?
To suma duk mun kashe shegu saura kai...bai gama rufe baki ba Julaibib yayi kukan kura ya cafki mak'ogwaranshi,idanunshi suka firfito yafara kakari dakyar suka 6am6areshi,yafad'i gefe yana tari da maida numfashi,sai kuma ya mik'e ya dunfaro shi, yana nunashi da yatsa"yau ka gama kad'ewa har ganyanka wallahi.Julaibib da zuciyarshi tariga ta bushe baiyi wata-wata ba yakai mishi wani irin naushi da k'arfin bala'i a muk'amuk'i ahhh...yayi ihu ya tsuguna kame da wajen dan yaji naushin yadda yakamata,yana zubar da jinin bakinshi sai ga hak'ori biyu a k'asa yasake fasa ihun takaici kaciremin hak'ora?
Julaibib yajijjiga kai zai sake kai mishi wani naushin yaji an bank'areshi ta baya...yayi iya k'ok'arinshi yakwace amma ya kasa dan rik'on kura taga nama suka mishi tamauuu...Idanunshi suka k'ara kad'awa jawur gangar jiki da zuciyarshi mazari sukeyi,wata jijiya ta fito rad'am a gefen goshinshi kamar shatin bulala saboda rik'on da suka mishi me bala'in azaba.
Wanda aka fasama bakin ya goge jinin sannan yamik'e tsaye suna kallan kallo da Julaibib zuciyoyinsu na tafarfasa,har ya kar6i bindigar ya saita kirjinshi dai-dai satin zuciya sai kuma yayi wurgi da ita kaiii...yafad'a cikin k'araji"idan na kasheka one time naji haushin kaina wallahi...yakallesu kuci buhun abu kazan ubanshi yadda zaku iya,yatattaro miyan bakinshi me had'e da jini da kakin majinan da yayi yatofama Julaibib a fuska"filthy bastard.Yatasa matan agaba sukayi tafiyarsu. Aka fara ba Julaibib na jaki ba ji ba gani suna jaddada mishi"ai ko ba makami da hannuma zamu iya kasheka har lahira.
Wayyooo...ALLAH!!!!Julaibib ya daku iya dakuwa sun mishi walmukalifatu da jiki!har ya daina numfashi,suka dinga janshi har zuwa inda wasu tarin gawarwaki suke suka jefashi,anjima zamu gasaku gashin kan saniya ba irin gashin tsire ba,suma suka juya sunata haki da numfarfashi...
Wani sanyine yafara ratsa har 6argonshi kamar wanda a ka ajiyeshi a sararin dusar k'ank'ara ba kaya ajikinshi,ko ina nashi na karkarwa har ya'yan hanji,abinda ya dawo dashi cikin hayyacinshi kenan, dakyar da sid'in goshi ya bud'e idonshi guda d'aya,dan d'ayan ya kumbura suntum fatar idon tayi bak'ink'irin alamar duka da kwanciyar gurbataccen jini,wajen wani irin wari,k'arnin jini da hamami ciwukan dake cikin gawarwakin yakeyi, k'udaje kuma sukace ga sunan yau take sallah a wajen su.Abubuwan da suka faru kafin ya suma suka dawo mishi tiryan-tiryan,wasu zafafan hawaye suka fara zuba daga idonshi me lafiya sharrr... sharrr...
Yafara Istigfari wucewar wasu dak'ik'u kuma ya mirgina kai cikin ciwo"ALLAH kaine mahaliccina! ALLAH ka fini sanin halin k'uncin da nake ciki, kataimakeni.Yayi iyakar iyawarshi ya d'aga hannunshi ya kori mayatattun k'udajen da suka baibaye fuskarshi ga kuma hayaniyarsu amma abun yaci tura, k'afarshi d'aya a karye take hannayen shima haka,zuciyarshi tayi tsananin rauni yana buk'atar taimako, mak'ogwaranshi ya bushe k'amasss kamar ruwa bai ta6a wucewa ta wajen ba,miyau ma dakyar yake tsatstsafowa a bakinshi, yahad'iye wani abu me zafin gaske kamar garwashin wutan da aka barbad'eshi da dakakken barkono d'an munci,kanshi yasara,yafara mishi wani matsanancin ciwo kamar zai rabe gida biyu.A wannan tsananin ya hango gungunsu da jarka,suna zuwa suka bud'e fetur ne a ciki suka fara juyema gawarwakin har dashi sai da suka matsa daga wajen sannan suka harba bindinga tauuu... nan take wuta ta kama wuuuhhh...suma suka juya sukayi tafiyarsu suna wata irin dariya ta rashin hankali da imani.
Wayyo wai ALLAH!Wato idan kaji k'i gudu to Alqur'an sa gudune bai zo ba...shi dai Julaibib bai san ya akayi ba sai gashi ya mik'e...yana barin wajen wuta tabi takan sauran.Yana dafe da bango yana d'ingisa k'afa d'aya me lafiyar dakyar...wani irin jiri ya wulwulashi ya buga da k'asa yadunk'ule yana matagugu,numfashinshi fita ya keyi wani baya shiga, zuciyarshi na mishi suya tana bugawa da k'arfin gaske kamar zata fasa k'irjinshi ta fito!Wucewar wasu yan dak'ik'u sai gashi ya zube a k'asa wanwarrr cikin d'aukewar numfashi difff!
Bayan da k'urar ta lafa manya-manyan matasan arnan da akayi yak'in dasu irinsu Nuhun gidan Diryan,Julius,Shekari da sauransu da sauran su,sune suka dinga tasa k'eyar mata da k'ananan yara zuwa Police Station d'in garin suna musu zagin tsame nama da mugun alkaba'i,su kuma suna biye dasu wasu na kukan zuci,wasu na nasarari,wasu ba uh ba uh uh,haka suke tsallake gawarwaki abun ba kyan gani,kaga gawa ta kumbura ta fashe kayan ciki a waje,awani wajen kuma sun saki aladunsu suna danasha da gawarwakin...Kai ALLAH ka k'ara tsinema arna!dan wata shari'ar billahil-azim sai a lahira!.
Zuwan sojoji da jiniyarsu (siren)da wasu masu kud'in suka hayo kuji fa?Daga wasu garuruwan dan su fitar da yan'uwansu tunda har lokacin basu bud'e hanya ba,haka ake ta zama a Police Station cikin mawuyacin hali,amma wasu daga cikin arnan suna ta kawoma yan uwansu masu sallah abinci da sauran kayan buk'ata.Yayin da wasu bak'in ciki kamar ya kashe su da suka ga maza da yawa na daga musulmai sun fito da ransu da lafiyarsu,sunata mamaki da takaici, to su wad'annan a ina suka 6oya ne a cikin garin da har basu gan suba? Sun manta cewa"zakaran da ALLAH ya nufa da caara toh fa ko ana muzuru ana shaho wallahi sai ya yi.
(Alhaji Umar Millionaire Doka,Wallahil-azim baza mu manta k'ok'arin da kayi na fara turo da sojoji Zonkwa ba har abadan duniya,Ubangiji yasaka maka da mafificin sakamakon shi,yasanya hakan a mizanin kyawawan ayyukanka)
Wannan jiniyar tasa duk wani wanda ALLAH yasa yana da sauran numfashi a doron duniya na daga maza musulmai daya 6uya yafito,nan da nan suka fara d'aukar wad'anda suke kwance cikin mawuyacin hali zuwa asibitocin garin dan a basu taimak'on gaggawa, masu gudun hijira suka fara d'aukar hanya,wasu daga su sai kayan jikinsu dan an k'one kome nasu,wasu kuma ba a k'one ba,masu sauran yan uwa a wasu garuruwan suka shiga kiransu su taimako da mota azo a d'auke su an bud'e hanya...kai rayuwa bata da tabbasss! idan ka san farkon ka,toh baka san k'arshenka,Ubangiji kamana gamdakatar da kyakkyawan k'arshe👏abinda aka tara shekara da shekaru rana d'aya da wuni d'aya an tarwatsashi har abadan duniya sai dai a fara sabon nema daga farko!.
Julaibib yana cikin wad'anda aka kwasa magashiyan zuwa asibitin"Zonkwa Medical Center" Suna kwance a k'asa a d'akin da ake zama kafin aga likita (reception)sai dai tunda aka kawo su ba wanda yakallesu tsakanin likita da ma'aikatan jinya bare susa rai da wani taimakon gaggawa.Wata ma'aikaciyar jinya tashigo tana yarfa musu ruwan bala'i kamar su suka kawo kansu "gwamma ku bud'e kunnuwanku dakyau ku jini ba wanda zamu duba sai ya bamu kud'i,idan ba haka ba to sai dai ku dauwama a haka har ku k'arasa mutuwa,taja dogon tsaki" ku d'in nan kuna da taurin kan tsiya to amma hakan kuma ai yana dakyau tunda kunji a jikinku,sau nawa muna muku hannunka me sanda?bama k'aunarku, bama k'aunar zamanku a garinmu kona sisin kwabo amma naci dambun kuturu kun kafe kai da fata,sai kuma tayi lallausan murmushi"ai gashi mun muku kattt...Kisan mummuk'e.
Tajuya tana cigaba da fad'an kalmomin wulak'anci da tozarci.Julaibib daya sake farfad'owa ya mirgina kai cikin tsananin ciwo da tausayin kai"banda rashin imani a ina mutum yake da wani kud'i a yadda yake d'innan da har zai basu sannan su dubashi!?Tsananin yayi tsanani a gareshi shi kad'ai yasan abinda yakeji a gangar jiki da zuciyarshi sai kuma wanda yashiga mawuyacin hali irin wanda yashiga,suna buk'atar taimako toh sai dai kuma baiga ta inda taimakon zai zoba...sai kuma yayi saurin fad'in.
"ALLAH na tuba,k'udirarka tafi gaban tunanin duk me tunani! Ya Ubangajin sammai da k'assai!Ya Ubangijina na mik'a duk al'amurana gareka! Muryarshi tafara rawa alamar karyewar zuciya💔Ya Ubangijina bani da k'arfi bani da dabara sai abinda kazartai a kaina! Ubangiji ka iya mana! Yamaida idonshi me lafiyar ya rufe dan d'ayan kumburan daya dad'ayi yasa kanshi ya mishi wani irin nauyi kamar an d'ora mishi buhun duwatsu,a hankali yacigaba da maimaita addu'ar"Allahumma lasahla illah maaja'altahu sahlan wa'anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahlan...
Wallahi abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba kwana biyu sunanan a haka kamar yadda wannan ma'aikaciyar jinyar tafad'a mutanan d'akin sai mutuwa suke yi...wari da k'udaje kam ba a magana.Doctor Bode Davis mamallakin asibitin da wasu matasa suka shigo d'akin yana nuna musu"kun gansu sune nake so a fita dasu daga waje muna so a gyara wajen...wani a cikin majinyatan yafara zaginsu"kai Bode ALLAH yak'ara tsine maka albarka,kuma in ALLAH ya yadda kaima sai sun maka abinda suka mana,ka sanni farin sani har family card nake dashi a asibitin nan amma yanzu kace bazaka dubani ka ciremin harsashin dake cinyoyi naba har sai na baka kud'i!
ALLAH yatsinema gamayyar da zaka nemi taimako a wajen wanda kuke gamayyar yak'i taimaka maka a sanda kake tsananin buk'atar haka, tirrr da irinka, wallahi nayi nadamar duk wata mu'amala data ta6a shiga tsakaninmu!Wani yakai mishi kutifo"how dare childish rat...Zai sake kai mishi kutifo Bode yace kyaleshi yaji da abinda yadameshi,in dai kanada kud'i to zamu cire maka,ko da ATM card d'inkane in dai yana aljihunka sai mu d'auka kafad'a mana pin-number mu ciro kud'in muzo mu cire maka.
Yana daga kwancen ya d'ud'd'ura musu zagi sannan yace"gwamma in mutu da in baku ATM d'ina gidan kud'i su rik'e kud'in na bar musu har abadan duniya. Kai bakinka ba zaiyi mutu ba duk da kana kwance sai yadda a kayi da kai? Eh bazai mutu ba ALLAH ya fiku, mutuwata da rayuwata ba ta hannun ko wani kafiri,a hannun ALLAH take tunda gashi nan har yanzu da raina, ai ba a san ranku muke numfashi ba,kuma na rantse da girman ALLAH sai na d'auki fansa,sai na rama abinda kukama Babana da k'anina!
ALLAH dai yabani lafiya zan tafi Maiduguri,na rantse da girman ALLAH duk wanda ya kwanta toh da safe sai dai ku d'auki gawarshi ku rubuta ku ajiye alk'awari ne wannan,idan ko mutum bai mutuba to ya daina baccin dare sai dai in zai dauwama a kwanan zaune dingirgir.Kai! suka daka mishi tsawa"kamana shiru komu k'arasaka.Idan kun fasa k'arasani kuba jikokin Baranzan da Zamburan bane,dan kun kashe ni ai a kwai sauran matasa irina da zasu maye gurbina insha-ALLAH. Basu sake magana ba suka tafi.Suna fita yafara kuka yana numfarfashi,yana cigaba da zagin su...Wucewar wasu dak'ik'u sai ga wasu matasa guda biyu sun zo sun d'auke shi.
Julaibib yabi bayansu da kallo yana zancen zuci"kowace irin azaba zasu sake gana mishi oho!zuciyarshi tak'ara rauni hawaye yafara zubo mishi,ba zato yaji ansa hannu ana share mishi hawayen"kayi hauk'uri ni zan taimakeku,dan banji dad'in abinda aka muku ba sai dai"I have no power da zan hana.Yakalleta da idanshi me lafiyar"ma'aikaciyar jinyace tana sanye da riga da buje farare kanta da k'arin gashi tozon rak'umi guda,yakauda kai... tabbasss shima da yana da k'arfin da zai iya magana to da shima ya d'ud'd'ura mata zagi bayan ya mata dukan mutuwa wallahi.
Tabisu da kallo cikin tausayi"casualties ne rututu all of them ramshackle.Tayi tsaiii...cikin tunani ta yaya zata taimakesu?Sai kuma ta jijjiga kai tana murmushi yes,tayi d'as da yan yatsunta "fad'uwace tazo dai-dai da zama,sai tajuya da sauri tafita.
Julaibib yasake mirgina kai bangaren dama cikin matsanancin ciwo,ga yunwa ta ci ta cinye k'irjinshi ya mishi nauyi,yana tunanin ma ya gamu da gyanbon ciki,numfashinshi yafara fita sama-sama kamar zai d'auke,a cikin zuciyarshi yake fad'in "Qadarullaahi wama sha'a fa'al...a hankali yafara jin wani abu na sukarshi kamar allura a ilahiran jikinshi me zafin gaske wucewar wasu yan dak'ik'u sai numfashin shi ya d'auke yayi doguwar suma.
Bobby!...takira sunan shi a rikice ganin wata shar6e6iyar wuk'a gayama jini na wuce daya fito yana karkad'ata sai walainiya take yi a hasken rana, yana wak'ar shi cikin nishad'i da karsashi:
Into my heart...come into my heart love Jesus...
Come in...to stay...come into my heart love Jesus...
Tajijjiga kai tana amsa mishi da"amennn.Yayi yar dariya"amennnn,fa kikace are you kidding me? Tagirgiza kai"Absolutely no...duk da zuciyarta lugude take yi karfa ya da6a mata wuk'ar a ciki"eh haka nace amennn,mu musulmai ai mun yadda da Annabi Isah Alaihissalam a matsayin d'an aike daga ALLAH,kune dai baku yadda da Annabinmu Muhammad Sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam ba.Tajuya harshe zuwa yaren Bajju.
"Ashyyeaggo(Ina kwana
Yace oh basakut(yi hak'uri) ashe bamu gaisaba
"Ashyllafiya(kin tashi lafiya) yafad'i hakan a gaggauce ya nufi k'ofar gidan zai fita.
Bobby ani yake?(ina zaka)ya tsaya cak sannan yajuyo suna kallan kallo na wucewar wasu dak'ik'u,idanunshi sun kad'a jawur da 6acin rai,takauda kai,yasauke numfashi amma baice kome ba,ita kuma tacigaba da maimaita"ALLAHU-ALLAHU rabbi laa'ushrika bihi shai'a.
Kira yashigo wayarshi yad'aga"kuyi gaba zan biyoku yanzun nan.
Jikinta yak'ara yin sanyi dan ta tabbatar cikin gari zasu sake komawa dan an kawo mishi rahoto d'azu;hausawan daba a k'ona gidajen suba suna ta zuwa suna kwashe kayayyakinsu. Kwallah suka cika idanunta,ta had'a tafukan hannayenta alamar magiya
"Bobby I beg you In the name of Almighty ALLAH karka sake komawa cikin gari.Yaja dogon tsaki yana harararta"ba abinda zai hanani komawa.Yasa hannu zai cire sak'atan k'ofar gidan tasha gabanshi,muryarta tana rawa"haba Bobby wannan wani irin rashin tausayi ne?Me mutanan nan suka muku ne?Haba Bobby kuma fa kuna da yan'uwa a garuruwan da musulmai sune majority while ku kuma minority,yanzu idan sukace suma sai sun rama abinda ku kama yan uwansu na nan yaya za kaji a cikin zuciyarka?
Tacigaba da fad'a mishi kalaman da suka sa jikinshi yayi sanyi,haba Bobby nima bazan so ace an kashe ka batare da kayi laifin kome ba,addinina daban da addininka amma duk da haka you're my cousin,kuma ina son ka,wannan soyayyarce ma tasa nake zuwa in da kuke,hawaye suka zubo mata sharrr...sharrr...Bobby ka mantane
"Kyan a ayyia ni anaatsi kpa shya?(Duk abinda ka shuka to a k'arshe shi zaka gir6e)
" Da anyi wyi yet kasham(me munine ko kyau)
Tafara kuka kasani sarai Bobby biblically ba ace kuma wani addini haka, toh abinda kukeyi kana ganin
Kaza baa chat?(ALLAH yana so)
A hankali ya girgiza kai.Tace to na rok'eka dan girman ALLAH kayi hak'uri kazauna a gida.Ya amsa kai tsaye sai dai idan tare zamu zauna muyita chatting for all day long.Eh na yadda.Yasake kallanta bayan haka za kimin pepper chicken,za kimin pepper soup,da irin wannan hamburger da kuka zi mana dashi da fruit salad yanunata da yatsa"concur?Tajijjiga kai"hundred percent"muje katayani ai wannan abu me sauk'ine k'wace goruba a hannun kuturu.
Alhaji Salim yasaki labulan ganin sun tafi D'akin-girki,yasauke gwauran numfashi cikin dukan zuciya,al'amarin ya ritsa da sune bayan ya kawo Ummi kamar yadda yasaba idan sunyi hutu a makatanta,ko kuma ranakun k'arshen makon da ya samu damar yin hakan,amma baya tafiya yabarta,tare suke yin kwanaki biyu ko uku sannan su koma,jikinshi yayi sanyi sosai, anya zai kuma zuwa Zonkwa bare har yashigo k'auyen Madauci?
Yagirgiza kai"shi dai yazo wannan yanki na k'arshe har abadan duniya,amma idan Ummi tayi aure ta ga za ta cigaba da zumunci da dangin mahaifiyarta toh shi dai bazai hana taba,tunda matar Mazon ALLAH Sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam Safiyya tana zumunci da yan'uwanta na jinsi Yahudawa,wannan bai zama haramun ba.
Yana wannan zancen zucin Rahab tashigo"Baban Ummi.Yad'ago yakalleta ba tare daya amsa ba.Tayi k'asa da murya"Mama ta fitane? Yayad'a kai.Sai ta zauna sannan ta fad'a mishi abinda yake faruwa a asibitin da take aiki"na san zaka taimakesu, mu an hana mu musu kome da tun ranar da aka kawo su dana fara basu taimakon gaggawa.
Jikinshi ya dad'a yin sanyi"nagode Rahab da kika fad'a min wannan maganar Insha-ALLAH zan taimakesu.To kazo muje ka gansu dan kasan ya azayi kafin goben.Yagirgiza kai"bazan fita in bar Ummi da Bobby kad'ai a cikin gidan nan ba.Tayi yar dariya"kana tsoro kar ya soke ya 6arke maka 'ya da wuk'a ne?Tad'an motsa kafad'a"na san ba abinda zai mata amma dan hankalin ka yakwanta barin kira Kuno da Yachat su tayasu zama kafin mu dawo ko? Yagyad'a kai"yauwa yanzu naji dama-dama wai kibiya a cikin idanu.Takama ha6a kuma dai? To anyi ba ayi ba kenan.
Bayan sun idar da sallar magriba Ummi take tambayarshi"Abbana d'azu naga kun fita da Aunt Rahab ina kuka jene?Yakalleta da kulawa "ceton ran wasu bayin ALLAH yan'uwan mu musulmai naje,gobe dasu zamu wuce Kaduna.Bobby yad'aga labulan d'akin "ke Ummi baza kizo muyi hirar bankwana bane ko me?
Tad'anyi murmushi"zuwa kai amma kabari muyi sallar Isha'i.Yasaki labulan yak'arasa shiga cikin d'akin yamik'a mata wata babbar waya samfurin Samsung"to ga wannan idan kun gama you shoud let me know zani Fadiyan Guga ne.Takar6i wayar ranta ba dad'i, a daren litini yashigo da manyan wayoyi sunfi hamsin,da su na'ura me kwakwalwa wai duk tsintar yayi a cikin gari da tarin kud'ad'e a cikin buhu"lallai wata shari'ar sai dai a lahira wallahi!.
Washe gari da sassafe sukayi sallama da kowa suka d'auki hanyar garin gwamma,ko a hanya basu samu wata matsala da jami'an tsaro ba dan kowa ya san abinda yafaru a Zonkwa, idan musulmai ne su jajanta tarebda addu'ar"ALLAH yasa kaffarace,idan kuma arna ne suji dad'in ganin mutanan da suke kwance cikin mawuyacin hali,da da dama da sun k'arasa su da bindiga,wanima gallama Alhajin Salim harara yayi"to wad'annan dai ai kuna 6atama kanku lokaci me wajen kaisu asibiti"repetitive strain injury ne dasu fa ko baku gani bane?Mun gani sai yaya?Alhaji Salim ya tambayeshi.Yamotsa kafad'a yana ta6e baki"they are in coma I don't think they will survive. Alhaji Salim yaja motar ba yare da yace kome ba.
Motarsu tana tsayawa a harabar gidan sauran yaran suka fito da gudu" oyoyo Abbanmu... oyoyo Yaya Umminmu,suka ringume juna cikin farin ciki.Hajiya Bara'atu farar mace,jaruma me k'ok'arin adalci da gaskiya a duk al'amuranta tak'arasa saukowa daga matattakalar benen,fuskarya d'auke da murmushi, Ummi tasaki k'annanta ta rungumeta "Mamanmu nayi kewarki,kullum sai na yi mafarkinki. Tarik'e hannunta suka zauna"nima haka,toh ya fargaba?Ummi takad'a kai"Mamanmu al'amarin ba kyan gani sai ma kinga wad'anda muka kai asibiti mutum a raye amma ya fara ru6ewa tsutsotsi suna fitowa a jikinshi!takama goshinta da hannun dama kwallah sun ciko idanunta "kai! Mamanmu arna basu da imani kona sisin kwabo kuma...sallamar Alhaji Salim daya tsaya gaisawa da mak'otanshi da katseta daga abinda zata fad'a.
"Sannu da zuwa Alhaji.Ya zauna"yauwa sannu da gida ya akaji da yara?Tayi murmushi kawai wanna ta tambayi ya masu jikin?Toh godiyar Ubangiji a kowani hali da yanayi,yakad'a kai amma abin kam ba gyan gani.
Hajiya Bara'atu tama mijin na ta wani kallo dasu biyun suka san ma'anarshi duk da yana cikin damuwa sai da yayi dariya,sauran k'annin Ummi suka shiga tayashi darawa duk da basu san abinda yasashi dariya ba,Ummi ce kawai taga abinda yafaru tace musu "to kiyi shiru Ku fa a wasu lokutan baku da wayau,dan kawai kunga ana dariya sai kuma ku fara?Yaran suka kalleshi"kaima Abbanmu ALLAH sai kayi shiru.Toh nayi shiru ya daina dariyar,sai suma sukayi shiru.
Ummi tamik'e"Mamanmu barinje in watsa ruwa,kuma kuzo muje daga nan kowa yabani labarin abin dad'in da Mamanmu tabashi da bama nan.Suka mik'e Yehhh...wallahi munji dad'i,munje kasuwar baje koli,munje gidan dabbobin daji har munyi selfie da 6auna da giwa da d'awisu kuma hotunan suna wayar Mamanmu tace dama zata nuna muku.Suka bisu da kallo cikin so da k'auna irin ta Iyaye da babu kamarta a wajen kowa sai su d'in har suke shige d'akin Ummi,sai tasama k'ofar mukulli dan kar wani yafito"toh duk ku zauna sai na fito daga wanka zan baku tsarabar dana siyo muku ta d'auko wayarta ta kunna musu wak'ar"Adam wa Hauwa na Ihab Taufiq nan da nan suka fara bin wak'ar.
Mutane goma Alhaji Salim yad'ibo daga Zonkwa tare da d'aukar nauyin kome nasu na magani har zuwa sanda zasu samu sauk'i,sai dai a cikin watanni biyu da zuwan su"44 Nigerian Army Hospital"mutum d'ayane"Julaibib Abdullahi D'ansarai shine ya zama ZAKARAN GWAJIN DAFI.
Sai dai shima a watanni biyun nan sau d'aya rakkin-rak ya farfad'o daga dogon suman da yayi yana kuka da sambatun kiran Bilkisuna,Innarmu, Musaddiq, Zaujatiii... Walida,Sudaida,da sauran sunayen yan'uwa amma wad'annan su yafi kira ko a cikin baccin shi.
Sai kuma yau da yasake farfad'owa sai dai Alhamdulillahi wannan karan cikin hankali yadawo hayyacinshi,a hankali ya bud'e idanunshi yana bin d'akin da kallo,ya gane a gadon asibiti yake kwance, duk in da yasamu karaya an gyara,na hannayen shima sun warke sai dai k'afarce har yanzu da saura, ya maida idanunshi kan Ummi da take zaune nesa dashi tana magana a waya.
Wacece wannan?Ya tambayi kanshi yana kuma k'ok'arin tunano a in da yata6a ganinta sai dai bangaren tunani da adana bayanai na kwakwalwarshi sun bashi tabbacin bai san taba,bai kuma ta6a ganin taba sai yau d'in,abu d'aya da zai iya tunawa shine wata ma'aikaciyar jinya tace zata taimakesu bayan nan kuma k'irjinshi yafara mishi suya sai jin wani abu kamar allura yana tsikarin jikinshi daga nan kuma ya numfashin shi ya d'auke.Idanunshi suka sake kad'awa jawur,yanzu ne yake jin asalin ciwo a jikinshi ko ina yayi tsami.
Kwanakinshi hud'u kenan da dawowa daga hayyacinshi,amma ba wanda yasani saboda yana jin alamar za a shigo zai maida idanunshi ya rufe, yauma jin za a shigo da yamaida idanunshi ya rufe a haka har baccin gaske ya d'auke shi.Sai farkawa yayi yafara jin sheshshek'an kuka ana magana a hankali"kiyi hak'uri Ummi ki bar kukan nan dan banga amfaninshi ba,kar yajawo miki matsala".
Mamanmu ni tausayi yake bani,duk wanda muka zo dasu sun mutu sai shi kad'ai yarage, sannan yanzu duk azabar da yasha an sake karya k'afar wai bata zauna a saiti ba?Takalleta cikin natsuwa"ba kina wajen akayi hoton k'afar ba? Kuma ai kinji bayajin da likitan yayi dan haka ba kome Ummi, ai gwamma ayi abinda ya dace a lokacin da yadace tunda ko an bar k'afar haka to daga baya dolen-dole dai sai an dawo an gyara"ayi agama ai yafi gobe adawo.
Da wannan yawan kukan da kike yi ai gwamma ki dinga mishi addu'a"ALLAH yatashi kafad'a, yasa kaffarace wannnan wahalhalun rayuwar da yake ciki ko?Tagyad'a kai"to amin Mamanmu. Hajiya Bara'atu tayi murmushi"barinje wajen A'isha mu gama maganar kayan danace takawo min sai in zo mu wuce gida yamma na yi.Julaibib yasake tambayar kanshi"su wad'annan su wanene?Sune dai suka kawo shi asibiti suna cigaba da kula dashi ko shakka babu,kullum addu'arshi a garesu"ALLAH yasaka musu da mafificin sakamakonshi ya sanya hakan a mizanin kyawawan ayyukanshi.
"This is my hijab...I will never remove.
Wak'ar Ahmad Bukhatir data sa a matsayin ringtone d'inta tafara tashi,abinda yasa Julaibib yazabura tare da bud'e idanunshi yana kallanta.Itama abin ya bata mamaki,tabbasss da k'afarshi ba a sagale take ba,ba abinda zai hanashi mik'ewa.
Tad'aga wayar da sallama,jikin Julaibib ya dad'a yin sanyi saboda ringtone d'in Sudaida kenan tun saninshi da ita da waya bata ta6a canja waba, haka kuma idan tana cikin nishad'i wak'ar da zaiji tanayi kenan,wanda a wasu lokutan shima ba zato sai yaji yana wak'ar,har rannan yakalleta "Zaujatiii...bakya gajiya da wannan wak'ar,ta masa"eh Yaya D'ansarai ai kalmomin cikin wak'ar ne babu na yarwa,ni duk wak'ok'in Ahmad Bukhatir ina sansu tunda ba harigido, gaskiya da gaskiyace kawai.
Yamaida idanunshi ga kallanta. Tagyad'a kai"na'am Insha-ALLAH,tayi jimmm...tana sauraron abinda ake fad'a daga d'ayan bangaren,wani d'an lallausan murmushi ya su6uce mata gefe da gefenta fuskarta suka lotsa ciki sosai(dimple)sannan tace"fi amanillah...Ilal-liqaa.Tacire wayar a kunnanta tana kallan d'an siririn farin agogon dake d'aure a hannun damarta,tayi rubutu a wayar sannan tasata a jaka.
Tamatsa kusa da gadan da yake kwance tana farin ciki da farkawarshi,cikin muryarta ta natsuwa tace mishi"sannu...ya jikin?Sai kawai idanunta suka kawo ruwa saboda tuno ranar data fara d'ora k'wayar idanunta a kanshi"yana kwance magashiyan wasu sassan jikinshi inda akwai sara da suka naman wajen yayi kore yana fitar da wani ruwa me wari,tsutsotsi yammm...sunata fitowa ta wajen, sai dai yanzu Alhamdulillahi yanata samun sauk'i,ta sauke idanunta akan k'aton d'inkin da aka mishi a kai da kafad'unshi duk sun d'auko warkewa.
Tasake kallan fuskarshi sai taji irin abinda taji a ranar farko ruguzowar wani abu kamar gini a k'ahon zuciyarta,ta kauda kai da sauri,shigowar wasu ma'aikatan jinya guda biyu sanye da kakin soja ya bata tabbacin lokacin bada magani yayi.Tad'an sara musu dan suna aikin su yadda yakamata"aikinku yana kyau"bravo.Sukayi murmushi"Thank you. Tagyad'a kai"you're well come,tajuya tafita a d'akin tare da rufo musu k'ofar a hankali.
Makonni uku bayan nan Julaibib yayi kyan gani fiye da zato saboda yana samun kulawa ta musamman da kuma cimar abinci me inganci da gina jiki,k'afar da aka dad'a gyarawa itama yana d'anyi tattaki da ita amma da taimokon sandunan da yake dogara jikinshi(crotch)a gajiye yashigo d'akin ya had'a zufa kashirban saboda d'an tafiyar da yayi,ya yar da sandunar yana goge zufan fuskarshi,tunani barkatai sun cika k'wak'walwarshi na abubuwan da suka faru, yanajin d'acin mutuwar kamar yanzu yafaru.
Aka turo k'ofar tare da yin sallama. Yad'ago idanunshi da suka kad'a jawur ya amsa sallamar,bai kuma cewa kome ba har Alhaji Salim ya zauna yanata kallan Julaibib d'in cikin tausayi yana ayyane-ayyane a zuci,yasauke numfashi"Qadarullahi wamasha'a fa'al.
Julaibib sai hak'uri dan ALLAH mahaliccinmu ya fika sanin halin da kake ciki,idan ka dogara gareshi zai samar maka da mafita a ragowar rayuwar da zakayi ga kuma tarin lada na maida al'amura gareshi.Nagode Alhaji, kuma bani da bakin da zan gode muku sai dai Ubangiji yasaka muku da irin sakamakon shi,dama kuma ina son sanin kud'ad'en da ka kashe min a asibiti nan.Alhaji Salim yagirgiza kai"ni duk abinda na maka na yi shine dan girman zatin ALLAH a matsayinka na d'an uwana musulmi me buk'atar taimako,ba wai na yi shine idan ka warke ka biyani ba,ni a wajen ALLAH nake neman ladana.
Yagyad'a na sani Alhaji ban kuma man taba,kuma har abadan duniya bazan ta6a mantawa da wannan karamcin na kaba,to amma ina da kud'ad'e da yawa a asusun ajiyata ta gidan kud'i... idanunshi suka sake kad'awa jawur bani da kowa... idan ban baka kud'in ba to me ma zanyi dasune?Wa zan ba?Iyaye da Iyali da sauran yan'uwa ko? Toh duk sun rigamu gidan gaskiya, yakad'a kai cikin alhini da tsananin tausayin kai.
Zuri'ata tatafi abadan,babu me dawowa har a nad'e doron duniya!!!Yad'aga hannayenshi"Ya Ubangijina!ka jikansu, ka gafarta musu!kasasu a cikin shahidan bayinka wad'anda zasu tashi ranar alkiyama jinin jikinsu da aka zubar yana k'amshin turaren almiski.Alhaji Salim yana tayashi da amsawa da"amin amin ya rabbi.
Wucewar wasu dak'ik'u d'akin yayi shiru,Alhaji Salim yakatse shirun ta hanyar kallan Julaibib cikin natsuwa sannan yace"ai ko kai kake da abinda za kayi da kud'i.Julaibib yakalleshi kallan k'arin bayani.Alhaji Salim yajijjiga kai"abinda nake nufi ka samu damar da zakayi sadaka me gudana ga Iyaye da Iyalanka da wad'annan kud'ad'e ladan hakan yacigaba da binsu kamar suna rayene suna aikata aikin alherin da kansu ko kuwa?Julaibib yajijjiga kai yana wani lallausan murmushin da yamanta rabon da yayi hakan, labarin zuciya a fuska ma ana ganin alama,sai yamik'a mishi hannu sukayi musafaba "nagode,nagode kwarai da gaske da wannan tunatarwa taka Alhaji"Jazakallahu khaira-khaira jazaa'ih.
Haka rayuwar Professor Julaibib Abdullahi D'ansarai tacigaba da tafiya Alhaji Salim yana kan hanyar zuwa dubashi kullum ta ALLAH, wasu lokutan kuma har da Iyalanshi,basu ta6a k'osawa ba har zuwa lokacin da likita yaga dacewar ya sallame shi dan ya warke sai d'an abinda ba a rasaba,wanda yau da gobe kuma da bata bar kome ba zata k'arasa warkar dashi.
Alhaji Salim yad'aukeshi suka tafi gidanshi, babban gida kwarai da aka k'awatashi da filawoyin hibiscus da Queen of the night.Wannan gidanane ina fata zaka iya zama a cikinshi,kasan abin talaka sai a hankali,suka fito daga motar sannan yaba Julaibib mukullin d'aki guda d'aya daga cikin d'akuna shida da suke harabar gidan,yasa hannu biyu yakar6a yana ta godiya har Alhaji Salim yad'an dafa kafad'arshi"ba kome wannan ai...yiwa kai ne,ka shiga ka huta, yamik'a mishi hannu sukayi musafaha.Alhaji Salim ya wuce cikin gida.
Julaibib yasa mukulli yabud'e d'akin... wani sanyi da k'amshin turaren d'aki suka daki k'ofofin hancinshi,yad'an lumshe idanunshi,rabon da yaji k'amshi me saukar da natsuwa a ilahirin gangar jiki da sararin zuciya tun Sudaidanshi tana raye, yabud'e idanu yana bin d'akin da kallo kome a kwai baya buk'atar k'arin kome sai tufafin sawa,yakwanta a gadon rigingine yayi matashin kai da hannayenshi tunani barkatai ya cika k'wak'walwarshi a haka har bacci yayi nasarar yin awon gaba dashi.
God'iyar liman ba gudu ba ka ye.
Alamar shiga masallaci cire takalmi.
14 Rajab 1441
8 March 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na ashirin da shida.
A mando sansanin Alhazai(hajji camp)wasu yan gudun hijirar Zonkwa suka yada zango musamman wad'anda basu da takamaiman in da zasu zauna,tabbasss suna samun tallafi to amma kun san k'asar tamu kome kashin dankaline...sune sukayi sama da fad'i da mak'udan kud'ad'en sai d'an abinda ba a rasaba talakwa suka samu,zasu cinye hakkin jama'a su kuma je lahira su biya a in da ba a biyan bashi da tsurar kud'i sai aikin alherin da aka aikata a doron duniya, da tallafin gidauniyar
"D'angote Foundation" ta naira dubu d'ari-d'ari da aka ba mutane dashi suke jalauta rayuwar,Julaibib bai samu ko sisin kwabo ba,kuma hakan bai dame shiba,dan kud'i ba matsalar shi bane,sai dai ma yaba wasu,lokaci zuwa lokaci ya kanje Mando a gaisa da abokan arziki harma yayi ihsani ga wad'anda tasu wahalar tafi ta wasu.
Julaibib ya d'auko wayarshi yana jujjuya ta makonni biyu kenan da siyan wayar tare da yin swap d'in layinshi sai dai har yanzu ya kasa kunnata, sai yayi kamar zai kunna sai kuma ya mayar ya ajiye, yau ma har ya mayar sai ya dad'a d'auko ta yayi jimmm... Sannan ya kunna,tana gama sai tuwa kira ya dinga shigowa ba k'ak'k'autawa"Yad'aga da sallama... kirane daga malamai abokan koyarwa da d'alibai;ya amsa waya sunfi hamsin kai a k'arshe gajiya yayi yasata a jirgi sannan yasamu damar fara karanta sakwanni na ta'aziyya kala-kala,daga nan ya bud'e wata wak'a da aka turo mishi wai Karmataka Studio Kano suka yi wak'ar ta'aziyya shi irin wak'ok'in nan basu dad'ashi da k'asa ba,yafara sauraro sai yaji har da yan'uwanshi yagama jinta har k'arshe,sannan ya kunna d'aya wak'ar sai yaji tsohuwar wakar da Rabi'u Usman Baba kano yayi tun lokacin yak'in Zangon-Kataf bai gama sauraroba,yakashe ya kunna yak'in Zonkwa
"Zonkwa Genocide"anan yake ganin abinda bai gani ba ganin idanun shi...sun maida makarantar daya kashe miliyoyin kud'i wajen ginata filin ALLAH,haka babban masallacin juma'ar garin da aketa kashe mata miliyoyin kud'i wajen zamanar dashi,sai dai basu rusashi gaba d'aya ba,sun rataye k'aton kan allade a gaban masallacin,tarin kwalaben giya kam ba a magana da alama mashaya suka mayar da wajen.
Yajijjiga kai "Manzon ALLAH sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam yayi gaskiya da yace babu amana tsakanin kafirai da musulmai kona sisin kwabo,duk yadda kuke dasu kuwa,taci na ciki wallahi. Sai ya tuno da wata magana da wani ALLAH Magani yata6a fad'a lokacin da yaga anata gudun hijira da ake fad'a a Kaduna"Wai musulmai suna ta tafiya to dawa za suyi yak'i?Ai sai sun dawo sun saki jiki tukuna zasu k'addamar musu... Ilai kuwa gashinan sun gani ganin idanun su.
Yacire wayar a jirgi yafara gwada wasu lambobi amma ba wacce ta shiga,zai sake kira,wani kiran yashigo,ya zubama lambobin idanu anya ban san me wannan layin ba?Har ya katse ya sake shigowa yana gab da katsewa ya d'aga da sallama aka amsa tare da tambayar"dan ALLAH D'ansarai ne me wannan layin?Ya amsa kai tsaye"eh shine.Tace cikin farin ciki ALLAHU AKBAR D'ansarai Bongel ce.Nan suka gaisa tanata mishi ta'aziyya muryarta tayi rauni"mun gwada lambar ka sau shurin masak'i bata ta6a shiga ba,Baban Humaima yaje Zonkwa amma bai samu kowa na kaba,har Mando ni dashi munje amma ba labarin kome"wayyo duniya!lallai wata shari'ar sai dai a lahira.
Julaibib yace dan ALLAH ki turo min lambar Doctor dana Innan Matsirga,yasake famo mata wani miki,cikin kuka tace"baka san abinda yafaru a Matsirga ba D'ansarai?Duk sukayi shiru sai yaji ta katse wayar.Yatallafi kanshi da duka hannayen shi yanajin wani irin yanayi mara dad'i yana tsirga ilahirin gangar jiki da zuciyarshi kamar wanda zai yi zazza6i.To me yafaru a Matsirga?Tambayar daya kasa samo amsarta kenan a k'wak'walwarshi, yad'auki wayar da niyyar sake kiranta sai kuma yaga gwamma yaje ya samu Doctor Manogi ya maida wayar aljihu yasa farar hula zita yafita.
A harabar gidan suka yi kaci6is da Alhaji Salim da Ummi.Ummi tad'ago ta kalli Julaibib wallahi sosai take jin tausayinshi,takad'ai kai cikin jimami"ALLAH sarki kowa da irin tashi k'addarar rubutacciya tun daga Lauhul-mahfus.
Alhaji zani Zari'a ne.Yau d'in nan? Yagyad'a kai"Insha-ALLAH yanzun nan.To ALLAH yatsare,bai damu da sanin abimda zaije yi a Zaria ba. Yakalli Ummi shiga D'akin-shak'atawa ki d'auko min mukullin mota yana nan a hannun doguwar kujera, taje tad'auko Alhaji Salim yakar6a sannan ya mik'a ma Julaibib,sai ya girgiza kai Alhaji kabarshi kawai zan tafi tasha.Yasaka mishi mukullin a aljihun gaban farar rigarshi"motar haya ai lalurace Julaibib,kai kanka za ka fi jin dad'in tafiya a wannan.
Suka yi tafiyarsu suka bar Julaibib, yayi tsayuwar a kawu yafurzar da wani huci, can cikin zuciyarshi yana jinjina halin karamci irin na Alhaji Salim,kullum abincin nan sau uku a rana,idan ma anyi wani abu bayan abinci na ta6akalashe to shima haka za a ciko mishi kwano,shi ko da me zai saka musu bayan addu'ar da yake musu kullum,wani irin tagomashi zai musu?Lallai yaba kyauta tukwuici ko??? Yajijjiga kai"toh shima zai musu abinda baza su manta dashi ba har abadan duniya.
Da wannan tunanin yashiga mota yad'aura belt sannan yatasheta bakinshi na ambaton ALLAH,yana tafiya yana tunanin al'amuran rayuwa me hawa da sauka,me cike da sark'ak'iya,me d'acin da ya zarta na mad'aci a wasu lokutan,me zak'in daya zarta na zuma a wasu lokutan"Dawaamulhal minal mahal (no condition is permanent) ba wani yanayi da yake din din din abadan a doron duniya sai buwayi gagara goyo Ubangijinmu me kowa da kome.
Ya isa Teaching Hospital ya ajiye motar a inda ake ajiye motoci sannnan ya nufi office d'in Doctor Manogi amma yatarar a rufe,wani Likita yafad'a mishi yana Emergency yazauna ya jirashi idan ba sauri yake yiba...Yaciro wayarshi yashiga yanar gizo a kafar sadarwa ta Facebook,sai dai yasha mamaki kwarai da gaske da yaga tarin arnan Zonkwa da suka turo mishi da rok'on gayyata dan su zama abokai,wasu yan gaggawa hannun hagu a romo har sun tura mishi da sak'o ta messenger sai dai bai karanta ko guda d'aya ba ya gogesu yana tsaki"suna da wayau amma in da hankali yake to su basuje wajen ba,basu mayi tunaninshi ba.Masu lambarshi suma sunata mishi magana ta Whatsapp amma bai bi takan suba.
Doctor Garga Ibrahim Manogi yacire farin gilas d'in da yarufe idanunshi yana nuna Julaibib "wa nake gani haka?Sai lokacin Julaibib yad'ago kai yaga Doctor Manogi da yayi wasu yan dak'ik'u kawai yana kallanshi,yamik'e tsaye suka rungume juna "ALLAH me iko Ustazu dama kana raye? Suka saki juna yabud'e musu office suka shiga,nan fa hira ta 6arke na abubuwan da suka faru har Doctor Manogi yabashi labarin abinda yafaru a Matsirga nan d'in ma kisan wulak'anci sukama musulmai wad'anda kwanansu yake gaba sun sha dakyar,sun tasa shanunsu gaba d'aya sun tafi dasu k'auyan kansu,su dai abinda yake hannnun musulmai yana tsone musu idanu,yana hanasu rawar gaban hantsi,sai dai na gaba ya dad'e dayin gaba,kuturwar uwa tilas zama dake,su cinye dukiyar su dawo gidan jiya cin busar doya da magwaro a matsayin abinci,irinsu Innan Bilkisu da sauran yan'uwansu Bongel sun musu yankan rago;a cikinsu Bello ne kawai yasha dakyar,mun dad'e muna fama da k'wak'walwarshi kafin ta dai-daita saboda irin halin firgicin daya shiga.
Amma yanzu Alhamdulillahi ya warke garas,na samo mishi gurbin karatu a Jami'ar Madina yana can,amma ko jiya da mukayi waya wallahi sai da ya tambayeni har yanzu ba a ga wani daya dangance kaba ko mutum d'aya?Julaibib yad'anyi murmushi "Bello kenan,yakar6i lambar wayar shi,sai ya koma gida zai kirashi.Doctor Manogi yakalleshi"ka san ALLAH kawai zagewa za muyi kamar yadda musulman Kafanchan sukayi,duk wanda yasan yana cikin irin wad'annan mutanen to shima yazama cikin shirin ko ta kwana da makaman kare kai"tunda ba kwanciya akafi kare ba,sai dai a fishi da abun rufa.
Haka suka ma musulman Kamatan haka, haka,hakaaaa sai da suka tashi garuruwa goma sha uku,amma dan rashin mutumci da da rashin hankali wasu tsinannu suke iya bud'e baki suce wai musulmai yan ta'addane,kuma gwamnati tanaji tana gani ba a d'auki wani mataki a kan suba,toh gobe ma idan sukaji sha'awar hakan ai basu da fargabar kome dan sun san idan sun kashe musulmai suna jin kamar sun kashe kiyashi ne,kuma da yake bahaushen mutum shima wani k'aton sakarai ne har yasake yadda ya koma garin Zonkwa wai da sunan cin kasuwa...na rasa ina hankali da tunanin wasu daga cikin mu yake.
Sai da sukayi sallar azahar sannan suka tafi gidan Doctor Manogi,shi da Bongel suka dad'a yima juna ta'aziyya,yaba su Humaima kud'i,ran Doctor Manogi da Bongel bai musu dad'i ba saboda kud'in da yawa.Julaibib yad'anyi murmushi"kusa ranku a inuwa yanzu D'ansarai bashi da zuri'a,toh idan ban ba sauran yan'uwa abokan arzik'i na musulmai ba wa zan ba?ALLAH dai yasa tamu k'arshen tayi kyau, jikinsu yayi sanyi,suka amsa da amin.Sukayi sallama yaja motar yatafi,suka bi danjojin motar da kallo har tayi nisa ta6ace ma ganinsu.
Yana zaune a harabar gidan yana alwala Misbahu k'anin Ummi yakawo mishi k'aramin Identification card(ID Card) d'in shine na"Zonkwa Internally Displaced Person daya manta dashi jiya a motar.Nagode ko?Misbahu yayi murmushi sannan yajuya yana fad'in barin d'auko hulata mutafi masallacin.
Shehin malami(Professor)a Jami'ar Usman D'anfodio Sokoto(UDUS)Maimun AbdulQadir ya kawo ma Julaibib ziyara,sun sha hira har sun gaji,tun safe suke tare har bayan sallar la'asar,lokacin ne yake haramar tafiya.Cheque ya rubutama Julaibib na miliyan biyar.Julaibib yagirgiza kai"Professor kar muyi haka dakai mana wannan kud'in to ai ka kwashe kud'in asusun ajiyar takene.
Yagalla mishi harara"idan ma zagina kakeyi a kaikace toh nagode,kuma ka kirani da Maimun kawai.Bazan iya ba Professor;matsayi ai ALLAH yake bayarwa kuma ya baka dan haka dole in baka,bazan k'i kiranka farfesaba.Maimun yace "uhum... wa yaga farfesa ciki fal geron sunday.Sukayi dariya dan sun tuno lokacin.Julaibib yace ai dane,yanzu cikin farfesa cike yake da dajjaja da labanun.Ya ajiye mishi cheque d'in"ba fa zan kar6a ba,na ma gode kwarai da kayi takakkiya kazo in da nake,dan me san kane zai damu da kai har kuma yazo takanas inda kake dan yaganka kuyi zumunci duk da tazarar dake tsakanin mu.
Maimun yakalleshi cikin natsuwa "D'ansarai kar muyi haka dakai mana,wallahi da ina da lambar asusun ajiyarka da sai dai kaji alert. Julaibib kai ai abokin aminci da amana ne,har abadan duniya bazan ta6a mantawa da karamcinku kai da marigayi Musaddiq ba,duk in da zan ba da tarihin rayuwata to tabbasss sai kun fito a ciki.A lokacin da muke karatu a Gidan-Waya na baka wannan labarin yanzu ma zan sake ba ka"tun ina ciki mahaifina yakwanta dama,a haka mahaifiyata ta haifeni tacigaba da kula dani da sauran Yayyina su hud'u duk dani mu biyar,bata samu wani tallafi daga dangin mahaifinmu ko na ta dangin ba,kasancewar suma babu ta musu katutu,duk da haka munfi wasu daga cikinsu duk da mahaifinmu shima ba shi dashi,to amma ALLAH yatarfama garinmu nono gidan da muke ciki na shine ba haya muke yiba,wasu da yawa daga cikinsu kuma haya sukeyi,wasu kuma suna zaune a gidan da aka musu alfarma su zauna har zuwa lokacin da ALLAH ya yassare musu sukayi na su.
Mahaifiyar mu tunda jajayen sawunta take sana'o'i mabambanta ta ajiye maganar aure a gefe ta kuma toshe kunnuwanta ga duk abinda zaije ya dawo na zamanta a haka ga k'uruciya ga rashin aure ba irin sharrin da ba a mataba,ita dai kawai burinta ta inganta rayuwarmu,a haka da taimakon ALLAH dana yan'uwa d'an abinda ba a rasaba ta gangand'a ta aurar da Yayyina matan,muka cigaba da gara rayuwar a yadda tazo ba a yadda muka so tazo mana ba,rannan dai ganin wahalar tayi yawa nace mata ni kawai zan fara bin mota in zama kwandasta idan na iya in samu mota in zama direba.Idanunta suka kawo ruwa tana kallona cikin jarumtacciyar zuciyarta me k'arama mutum juriya da hangen wata rana sai labari.
Maimun ni da mahaifinka ba irin rayuwar da muke so kayi ba kenan,kullum burinmu ace Ya'yanmu sunyi zarra wajen ilmin addini,dan haka kayi d'amara kabani goyon baya dan girman ALLAH karka watsa min k'asa a cikin idanuna,tanuna kanta da yatsanta"madamar ina numfashi a doron duniya to Insha-ALLAH sai ka zama abin kwatance sai anyi alfahari an mori tarin ilminka...
Idanun Maimun suka kad'a yanajin kamar a lokacin ta zaunar dashi tana fad'ama mishi kalaman.Julaibib mun sha wahalar rayuwa,har k'anzon abincin gidajan mak'ota take kankaro mana muzo muci.Kullum kalamanta na k'arfafa gwiwane "Maimun kayi hak'uri wata rana sai labari ba wani yanayi da yake din din din a doron duniya,a haka dakyar da sid'in goshi muka gangand'a na gama secondary,sai da nayi k'wadagon shekara uku sannan na had'a kud'in registration nafara karatu a Gidan-Waya.
wasu lokutan inji kamar in gudu dan bak'ar wuya amma idan natuno da kalaman mahaifiyata sai inji k'warin gwiwa dan na san tanacan tanata k'ok'arin tara min wasu kud'ad'e kafin buk'atarsu ta taso,har zuwa lokacin da kuka shigo makarantar,tamu tazo d'aya kuka fahimci halin da nake ciki kuka taimakeni tun kafin in furta hakan,kuka yadda na dawo d'akinku gaba d'aya da zama inci abincinku,in sa kayan sawanku...da sauransu da sauransu,kun d'auke min abubuwa masu yawa game da karatuna, kuma kuna bani girma a matsayina na d'an Adam bakuyi duba da cewa k'asa nake da kuba.
Mun gama karatu lafiya har na samu koyarwa,D'ansarai kazo ka d'aukeni muka tafi Jami'ar Ahmadu Bello wai ka samo min gurbin karatu...Yakalli Julaibib ban ta6a ganin mutum me irin zuciyar kaba,kai ka biyamin kud'in registration.Da taimakon ALLAH dana mahaifiyata da kai nakai matsayin da nake,toh ta yaya zan manta wannan d'imbun alheran Malam D'ansarai?
Ya share hawayen da yazubo mishi sai dai shi ALLAH baya barin wani dan wani...ina matakin Senior lecturer mahaifiyata itama takwanta dama an gama cin mad'aci za a fara cin zak'in....ALLAH ya jik'anki mahaifiyata da sauran Iyayenmu kaafatan.
Yakalli Julaibib"to dan na baka d'an wannan kud'in da bai wuce kacika matorka da mai ba (full tank)kawanice bazaka kar6a ba?Julaibib yayi yar dariya"D'ansarai ko tayar keke bai dashi bare mota. Babu damuwa motar ma tananan tafe Insha-ALLAH,ka kuma fara shiri dan Umrah na bana da kai zamu tafi muyi azumin ramadana a can.Julaibib yayi godiya sosai sannan yarakoshi wajen mota,anan ma sun 6ata wasu dak'ik'u kafin sukayi musafaha yashiga motar ya zauna direban yaja motar,shi da Maimun suka d'aga hannu suna ma juna adabo.
Miliyoyin kud'ad'e Julaibib ya samu daga abokan arziki da gwammati,dan haka yasai fili babba yasake gina makarantar da tafi ta garin Zonkwa kome da kome gefen makarantar ya gina d'an madaidaicin gida.Ya ajiye aikin koyarwa na duk makarantun da yake zuwa, yadawo makarantarshi daya gina,suna cigaba da koyarwa da wasu malaman daya d'auka.
Alhaji Salim yakalleshi cikin natsuwa bayan sun dawo daga masallaci sallar Isha'i"Julaibib na so kwarai da da matarka ta aure ka tare a gidan ka. Yad'an bud'e idanu dan mamaki"Alhaji aure kuma?Sai yagirgiza kai"zanyi zamana a haka har zuwa lokacin da nima zan daina numfashi a doron duniya.Alhaji Salim yakad'a kai dan shima ya d'an d'and'ana irin abinda Julaibib yake d'and'ana amma ba kamar na Julaibib ba.
Lallai zasu tattauna cikin tsanaki,ai yana da ilmi zai kuma fahimci zama da auren zai fi mishi fiye da yak'arasa rayuwar a haka,tsananin martaba aure irin na bahaushe yasa kome tsufan mutum sai kaga yayi auren koda kuwa irin na butane kamar yadda suke fad'a.
Wata d'aya bayan nan Julaibib yana zaune a D'akin-shakatawar gidan shi yana kallan kwanukan abincin da Misbahu ya ajiye,duk da yabar gidan amma kullum ta ALLAH basa gajiya sau ukun nan sai an kawo mishi abinci, yanzu idan yace a daina kawo mishi bai san yadda zasu fassara al'amarin ba, abu d'aya zaisa a daina kawo mishi wannan abincin shine suga macen aure a gidan,shi kuma bayajin wani aure a ranshi,jiya ma abinda Maimun yagama fad'a mishi kenan wai da yana da 'ya mace da tuni ya aura mishi ita"Julaibib yayi murmushi"haba farfesa gwamma da ALLAH ma yasa baka da ita 'yar tawa zan aura?Ya jijjiga kai"ai hakan shine dai-dai taci karanta ba babbaka.
Ranar Juma'a bayan an sakko daga masallaci Julaibib ya tsaya suna gaisawa da Alhaji Salim,yakalleshi maganar Iyali har yanzu dai shiru bakace kome ba,yad'an shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"zan duba...ko kuma ma dai Alhaji kasamo min yar mutunci a unguwar nan tunda ka dad'e a unguwar ka san yar babban gida.
Alhaji Salim yayi murmushi"fad'uwa tazo dai-dai da zama,yakalli Julaibib "ka bani wuk'a da nama nagode,amma wani hanzari ba guduba idan kuma kaga yarinyar kaji bata kwanta maka ba fa?Ya amsa kai tsaye"zata kwanta min ko yaya take dan na san baza kamin za6en tumin dare ba, zan aureta zan kuma girmamata.
Alhaji Salim yasake kallanshi"yanzu me zakayi a gida?Yad'an motsa kafad'a"bakome.To zo muje gidana akwai maganar da zan fad'a maka suka shiga mota suka tafi.
Sai da suka gama cin abincin rana sannan Alhaji Salim yakalleshi cikin natsuwa"Julaibib zan baka auren 'ya ta Ummi kana son ta?Julaibib yaji wani irin yanayi na girma da nauyin Alhaji Salim,ai wata fuskar ta fi gaban mari har abadan duniya wallahi,Ummi a yadda ya karanceta ai bata da wani aibu tana da natsuwa da hankali,gata da ilmi,kai ko da ace ballagazace a dai irin karamcin da Alhaji Salim yamishi to wallahi ba abinda zai hanashi auren ta "Insha-ALLAH kuma sai ya d'orata a kan hanyar dai-dai bare kuma a kauwamen ta take.Ya amsa cikin girmamawa"to Alhaji nagode ALLAH yasaka da alheri.
Yagyad'a kai"Julaibib ya kamata kasan wacece Ummi da kuma mahaifiyarta.Yayi shiru yana sauraro...Alhaji Salim yabashi labarin aurenshi da Sumayya,'yar data haifa mishi da kuma rasuwarta...Ni tun ranar daka farfad'o na tambayi sunan ka kace min Julaibib na gane ko wanene kai,da irin k'aunar da marigayiya take maka,dan haka Ummi yar wajen Sumayya(Kasham) ce,ita zan baka idan kaga kana sonta.Julaibib yabud'e idanu dan mamaki...zuciya da k'wak'walwarshi bangaren adana bayanai ta koma baya da gudu tana tariyo mishi kome daki-daki tun had'uwarsu ta farko da Kasham a Gidan-Waya ranar da sukaje yin registration... har zuwa ranar data aiko mishi da wasik'a,ruwan zamzam,farin miski da dabinon ajwa da abinda tarubuta mishi"Musha ruwa lafiya...ranar azumin ashura tara ga watan farko na musulunci Muharram...Da abinda ta rubuta a k'arshen wasik'arta
Sumayya Kantiok Donatus(Kasham)
Yayi shiru yana tasbihi a cikin zuciyarshi"ALLAH Alhakimu gwanin iya hakima, ALLAH buwayi gagara misali...Qudirarka da yawa take"ni Julaibib Abdullahi D'ansarai ni zan auri 'yar da Sumayya ta haifa?Lallai ba wanda yasan abinda gobe zata haifar sai ALLAH,dan shi wallahi har ya manta da wata Kasham da Sumayya a rayuwarshi...A hankali mafarkan da ya dinga yi na shekara da shekaru suka dawo mishi wannan mafarki me ban mamaki da yarasa gane ma'anarshi
"Kasham da yake gani cikin shigar kayan fulani idan tayi magana sai kuma yaji muryar Sudaida.
Wannan yana nuna Sudaida matar shice,haka kuma zai auri wata kenan me alak'a da Kasham d'in?Gashi kuwa ya tabbata 'yar data haifa a cikinta...kayan fulanin kuma yana nufin kenan Bafulatana ce?Yajijjiga kai"ko shakka babu tunda Alhaji Salim Iyayenshi Fulanine amma girman birni dan ko Iyayensu basuyi kiwon shanu ba bare kuma su... La'ilaha'illallah.
Sai yasake tuno ranar da Maimun yake fad'a ma Musaddiq mafarkin da yayi"Wai shi da Kasham ne suke kiwon shanu a wani k'aton fili iya ganinka me cike da koren ciyayi"Musaddiq yakyalkyale da dariya"D'ansarai fulani ka koma har matarka take tayaka kiwo saboda tsabar k'auna?A lokacin bai kula suba.Yayi ma Alhaji Salim godiya sosai,amma har yabar gidan bai daina mamakin wannan al'amarin ba.
Bayan tafiyarshi Ummi tashigo d'akin da sallama,ta zauna tana kallanshi"Abbana kace za muyi wata magana idan ka dawo daga masallaci, yana murmushi yace ban manta ba Ummi,ya san yana da yak'ini zata amince,sai yafara mata nasiha akan biyayya ga Ya'ya a wajen Iyayensu wajibine matuk'ar abinda suka zo dashi bai sa6ama shari'ar musulunciba,a hankali kuma yafara kambama halayenta na k'warai, ganin tana ta murmushin jin dad'i,sai ya maida abun zuga"ai na san baza ki bani kunya ba;baza ki watsa min k'asa a cikin idanu ba,ni a duniyar nan ban ta6a ganin yarinya me tsananin biyayya ga mahaifanta ba irinki,nima kinga shi yasa nake miki wata irin k'auna mumaiyiza(ta musamman)
Tagyad'a kai"tabbasss ta yadda Abbanta yana mata k'auna ta musamman d'in dan kome nata na musamman ne wallahi a wajen shi. Cikin d'oki tace"me kake so in maka ne Abbana? Yakalleta cikin kulawa"aure zan miki Ummi,kuma ni da kaina na za6ar miki mijin.Da sauri ta sunkwui da kai dan batayi tsammanin abinda zai fad'a kenan,tanajin wata irin kunya na lull6eta.
Yacigaba da magana "shekaru da yawa da suka wuce ina da labarin shi, mutumin kirkine... kuma nima a yanzu nayi nazarin shi tsafff...naga hakan ganin idanuna,hasashena yana bani zai rik'eki da aminci da amana,burina kullum a kanki Ummi shine kiyi aure,kiyi bautar cikin aure tunda ibadane, ranar alk'iyama ki samu sakamako mafi kyau da daraja,kisamu shiga darul-karamah (aljannah) aljannarma ina miki kwad'ayin samun mad'aukakiya (firdausss)
Yayi shiru yana kallanta"Ummi kiyi magana mana ai ba auren dole zan miki ba,idan kina da za6inki na kuma bincika naga shima mutumin kirkine,toh shi zan aura miki,zan kuma ba wancan hak'uri na san zai fahimceni,tayi k'asa da murya cikin jin nauyinshi"Abbana ina fata in biku in muku biyayya a duk abinda kuka umarceni ko da bana so,zan tilastama kaina so,dan na san baza ku cuceniba,dan nima inaso agaba a bini,na san kuma sai na biku na samu albarkanku,nima zanga da kyau a rayuwata ta gaba.
Yayi lallausan murmushi yana yaba hangen nesan ta"toh kin yadda da za6in Abban naki koda mutumin me gemu da k'asumba cike da furfura kamar na Abbanki?Tasake sunkwui da kai"shi wallahi haka Abba yake magana wasu lokutan sai yaba ka kunya.
Haka rannan yace ma Mamansu wai tana ta wani shashshare shi,to shi gaskiya ya gaji da wannan shariyar,aure zai k'ara kuma sa'ar Ummi zai auro.Ita kuma ta galla mishi harara"dan ALLAH ka auro wacce bata kai Ummi bama.Sai yafara dariya yakalleta"ke Ummi ki zama shaida ai kinji abinda tace ko?Batayi magana ba,sai guduwa d'aki tayi ta barsu,yanzu ma tashi tayi yana kiranta amma bata dawo ba.Alhaji Salim yana da shak'uwa sosai tsakanin shi da Ya'yanshi,dan haka zaiyi wuya yafad'a musu abinda yake so na ayi ko abari kaga basubi umarnin na shiba.
Haiya Bara'atu tak'arasa shigowa"to ai Alhaji wannan al'amari yayi dan shirun budurwa yaddan ta,bazawara kuma sai ta tanka.Tamishi wannan kallan nata dasu biyu suka san ma'anar ta"ko kuwa?Yana dariya ya amsa"ai zancenki ba ja kare ya mutu a juji.
Ranar wata alhamis ba makarantar Islamiyya kuma dama ta gama secondary ana zaman jiran sakamako kafin a d'ora zuwa Jami'a,suna D'akin-girki Alhaji Salim yabisu yana musu sannu da aiki.Suka amsa mishi cikin sakin fuska.Yakalli Ummi "bar kwa6in nan ana sallama dake a waje.Tad'anyi jimmm...Hajiya Bara'atu ta kalleta cikin kulawa"jeki mana Ummi.
Tajuya jikinta a sanyaye tana sanye da riga da zani na atamfar classic,tasa bak'in silifas da hijab tafita,sai dai bata ga kowa ba sai Julaibib,tasha jinin jikinta,ta gaishe shi duk da d'azu tagan shi a hanya da take dawowa daga gidan Alhaji Hafiz kuma ta gaisheshi.Yak'araso in da take tsaye"ai ni nake sallama.
Sai tasunkwui da kai k'asa batace kome ba tana wasa da gefen hijab d'inta"to yaya na miki?nan ma shiru tayi sai yacigaba kinga karfa kiga dan na kwana biyu gemu da k'asumba sun cika fuskata toh na iya soyayya sai na zama tauraronki.Sai kuma yayi shiru yana kallanta ganin har lokacin batace kome ba.Sai yakad'a kai cikim jimamai"Oh D'ansarai marayan ALLAH ba uwa da uba ba sauran dangi da alama baka samu kar6uwa ba dan haka sai ka d'au na Annabawa kawai.Yadda yayi furucin cikin tsananin tausayin kai yasa tad'an d'ago tana murmushi,amma ba shi take kallo kai tsaye ba"Yaya Julaib...ba haka bane ai tunda Abbana ya gamsu da kai bani da ja...shima kallan fuskarta yayi..ALLAH buwayi sai lokacin yake ganin kamanninta da Sumayya har jerarrun hak'oranta farare, da manyan idanunta masu maik'o,wad'annnan sune abinda ta d'auko na ta kai tsaye da kowa zai iya ganewa.Kad'an sukayi hira yamata sallama dan ya lura a takure take.
Watanni uku bayan nan aka d'aura aurensu Alhaji Hafiz yatsaya a matsayin waliyinshi, aka kai amarya gidan mijinta ana musu fatan zaman lafiya. Ummi tashiga bautar gidan aure da duka k'arfi da kuma iyawarta,zaman nasu ba yabo ba fallasa, suna mutunta juna,tana bashi girma a matsayinshi na babba kuma mijinta sama yake da ita,shima yana jin tausayinta amatsayinta na k'arama kuma mace me rauni...
Yasauke gwauron numfashi a sanda k'wak'walwarshi bangaren tunani da adana bayanai tagama tariyo mishi kakaf rayuwarshi daki-daki.
Yauma abinda yasa yamata haka jiya yatafi Gidan-Waya yakwaso kayansu anan yaci karo da kayayyakin Iyalinshi...abinda ya famo mishi wani miki kenan haka ya kwana ranshi ba dad'i... Ummi bata kar zomo ba sai ya bata rataya...yayi huce haushin kaza a kan dami.Yajijjiga kai"gaskiya Ummi bata cancanci haka ba,ai idan d'an kaciya baici kazaba toh tsakani da ALLAH bai kamata kuma yayi baraba...Har lokacin yana jiyo sautin kukanta dan haka ya mik'e dakyar duk da har lokacin kan nashi bai daina ciwo ba.
Ruqayya...tanaji amma tak'i amsawa "haba Ruqayya...sai ya zauna ya gewayeta"Ruqayya Esbeer...ni me laifi ne,laifina kuma babbane...amma na gane kuskurena gani a gabanki na zo ki yafemin...d'ago kanki ki gani na san ke macen albarka ce,baki furta kalamanki ba har sai da kika rasa hanyar bi wajen shawo kan matsalar gidanki,ni d'innan nina tunzira zuciyarki,amma Insha-ALLAH zan kiyaye furucina...ni dai ki taimakeni ki yafemin...ta tari numfashin shi tamik'e zaune tana kallanshi da idanunta da suka kad'a jawur"na yafe maka.
sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u sannan ta cigaba da magana"Julaib...ina tabbatar maka kana d'aya daga cikin bayin da ALLAH yake so Insha-ALLAH idan katuno da jarabawar Annabi Ayuba Alaihissalam"ya kamu da ciwo tsawon lokaci, Ya'yanshi suka dinga mutuwa,duk jama'a suka k'aurace mishi to amma da yayi hak'uri ya mik'a al'amura a wajen Ubangijin mufa?ALLAH mahaliccin mu yace mishi "madallah da wannann bawa nawa me yawan hak'uri da juriya.
Julaib...karage tunanin nan,ka sani wanda duk ya mutu toh ya mutu kenan abadan,babu sauran soyayya da k'auna da zaka nuna mishi face ka yawaita aika mishi da abincin shi(addu'a)idan kana da hali ka mishi sadaka me gudana,toh Julaib...ka musu anata aika musu da ladan kullum ta ALLAH, kaima kullum kana musu addu'a,nima ina musu, Abbana...Mamanmu, kai da d'aukacin al'ummar Manzon ALLAH ga wad'anda suka ga kisan gillan da aka musu,da wad'anda sukaji labari da sauran yan'uwanmu musulmai na garin Jos da Maiduguri da sauran arewacin k'asarnan.
Duk masu ta'addancin nan tun daga duniya zasu fara ganin sakamakonsu,da izinin ALLAH fashewar kwai a saman kwalta za suyi,mutuwar kare a saura.Tad'an kalleshi"dan ALLAH kayi hak'uri ka saki ranki muyi rayuwar aure kamar yadda sauran ma'aurata suke yi cikin nishad'i da karsashi.Yasauke numfashi"Ruqayya ke macen alherice...ALLAH yamiki albarka.Tagyad'a kai"amin,shukran jazilan...Qad uhibbuka...yatari numfashinta kafin ta k'arasa furucinta"hubban jammahhh...sukayi murmushi"to yanzu muje ki bani abincin yunwa nake ji cikina ba kome sai yan hanji.
Bayan ya gama cin abincin yasha magani yad'an huta,sannan tafara mishi bayani a kan gidauniyar"D'ansarai da Me-Lambu Foundation"da suka kafa musamman dan taimakon marayu da zawarawa yan gudun hijirar Zonkwa da ta samar da kud'i me tarin yawa,d'azu bayan tafiyarka masallaci Maman Hasan ta kirani tafad'a min.Baba Alhaji ma (Alhaji Hafiz) ya sake bamu gudummawa kamar yadda yasaba,sai dai wannan karan kayan masarufi muka samu kasancewar watan ramadana yanata matsowa.
Abbana ma zakkarshi ta bana daya fitar d'ungurungum yabamu kud'in,shi tun jiya bayan tafiyarka Gidan-Waya yakira yafad'a min idan ka samu lokaci kaje ka kar6o dan ya kira lambarka bata shiga.Jikinshi yai sanyi "Ruqayya Ubangijine kawai zai saka muku,ina kuma rok'onshi yasaka muku da mafificin sakamakon shi. Yaciro wasu kud'ad'e masu yawa yana mata bayani "wad'annan farfesa Maimun AbdulQadir ne ya aiko dasu.Tagyad'a kai"mungode kwarai ALLAH yasaka mishi.Amin.Bayan la'asar sai inji in kar6o na wajen Alhaji zuwa jibi sai mutafi Mando mu raba musu,tunda kowa kika gani a wajen yana cikin halin ha'ula'i ne.
"Julaib...wai har yanzu gwamnatin jahar nan ba wani tallafi da zata bayar ne? A yanzu dai kam babu amma bamu san a gwamnatin gaba ba tunda wannan ai kinga saura shekara d'aya tak'are tenure,ke dai Ummi Ubangiji yacigaba da rufa mana asiri duniya da lahira wanda yasamu kud'i ko yaya sai yafara sana'a kome k'ank'antarta yacigaba da addu'a ALLAH yasa mishi albarka sai kiga kome ya wuce,ai da rarrafe yaro yake tashi.
Rannan naji a labarai agwam Bajju yana dad'a ba musulman Zonkwa hak'uri akan abinda yafaru wai ba a san ranshi hakan yafaru ba.Julaibib yakad'a kai"rabu dashi ai bakinsu d'aya,in banda haka a ina suka samu wad'annan mugayen makaman? Kud'in baikon da suke bayarwa duk ranar lahadi a majami'unsu bai isa yasiye suba...Gari ne dai an bar musu,ai k'asar ALLAH fad'i gareta,masu murnar sunyi kud'i da kud'in hausawa to yanzu baki gansuba"garin banza dama a farau-farau d'in bamza yake k'arewa.
Ringtone d'in Ummi"This is my hijab...I will never remove.yafara tashi.Rahab ce dan haka ba tare da tayi sallama ba tad'aga.Rahab ta fashe da kuka"Ummi Bobby ne...Me yasa meshi ne haka Aunt? Tayi tambayar da kulawa.Cikin kukan take mata bayani"wai sun tafi Fadan Karshi d'auko akwatin gawa (coffin)na wani abokin su daya mutu, to a hanyarsu ta dawowa motar takama da wuta sun k'one k'urmusss. Ummi tayi jimmm...to me zata cene? Idan batace kome ba tabbasss Aunt Rahab baza taji dad'i ba,Bobby shine babban d'anta,kuma tana son ta,dan ko bata kira taba to ita tana yawan kiranta kusan rabin yaren Bajju ita ta koya mata a cewarta dole ne tayi haka tunda da Kasham tana raye zata koya mata, toh tunda ta mutu ita meye amfanin ta idan bata koya mata ba? Sauran kuma ta koyeshi a gidan Alhaji Hafiz da take zuwa.
Ta tausasa murya"Aunt basakut (kiyi hak'uri)Kuka bazai dawo da Bobby ba"I know it's hurt, but you've to bear it,since you already know that sooner or later each and every one we will go back to our creator...tacigaba da rarrashinta har tayi shiru amma bata yadda ta mishi addu'a ba dan musulunci ya haramta hakan ga duk wanda ya mutu bai yadda da manzancin Manzon ALLAH Sallallahu alaihi wa'ahlihi wasallam ba.Rahab taji dad'in kalaman Ummi sosai "Thank you very much my dear Ummi for this condolence.Sukayi sallama.
Sunyi shirin tafiya Umrah a can zasuyi azumin ramadana,d'aya ga wata kuwa jirginsu ya d'aga zuwa k'asa me tsark'i,garin Manzon ALLAH me safa me marwa,garin dabino da ruwan zamzam... ruwan zamzam me tarin albarka da duk buk'atar da kashashi zata biya Insha-ALLAH.
Dabinon ajwa sukaci da tataccen ruwan inibi da tuffa,bayan angama kiran sallar magriba, shi da Ummi suka kalli juna suna murmushi yad'aga hannayenshi sama dan wannan lokacin amsa addu'a ne kafin a tada sallah"Ya ALLAH bayinka da aka kashe bada hakkin suba a ko ina suke a doron duniya al'ummar Manzon ALLAH! Ubangijinmu albarka wannan rana,albarkan wannan d'aki na ka me alfarma ka yafe musu!Ya Ubangijinmu mahaliccin kowa da kome jinin nan nasu daya zuba a doron k'asa,kasa yazama sanadi na samun d'aukaka da darajarsu!Ya Ubangijinmu kasa hakan yazama sandin shigarsu darul-karamah (Aljannah) Jannatul firdausss al'a'ala.
"Ya Ubangiji!Miyagun da suke ma al'ummar manzonka kisan gillan nan idan wad'anda za su shiryune to ALLAH na rok'ek'a kashiryar dasu, idan kuma 6atattune abadan Ila yaumil k'iyamah... ALLAH! Kai ka haliccemu gaba d'aya, kuma gareka zamu koma gaba d'aya mun bar kome a hannunka kamana maganinsu.Ya Ubangiji! Muda mukayi saura a raye da imani to ka k'ara inganta mana imanin,idan kuma ka tashi kar6an rayukanmu muna maka magiya da sunayenka mafiya kyau,daraja da d'aukaka to ka kar6i rayukan namu muna masu imani,ranar rarrabe tsakanin k'arya da gaskiya, ranar da kud'i da Ya'ya basu da tasiri sai dai wanda yazo da ayyuka nagari...!ALLAH kahad'a fuskokinmu a darul-karamahhh...
Ya ALLAH!me saukar da littafi,me gaggawan sakamako!Ka karya k'ungiyoyin abokan gaba.Ya ALLAH!Ka karyasu,ka girgiza su...!!!
Ummi dake gefenshi itama ta d'aga hannayenta sama tana amsawa da"amin Julaib... aminnn ya rabbi... aminnn... k'arshe.
Kome yayi farko tabbasss yana da k'arshe.Mu Ya'yan Ibrahim Godiya muke ma ALLAH marashin k'arshe daya nufemu yau da kammala rubuta labarin Julaibib Abdullahi D'ansarai ZAKARAN GWAJIN DAFI.
19 Rajab 1441
13 March 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs
Saudat Ibrahim Yahaya😂kisa ranki a inuwa kamar kin mari uwar Soja...Mu Ya'yan Ibrahim zamu rakaki gidan D'ansarai har D'akin-shak'atawa ki zauna kisha bak'in shayi...sai ki tambayeshi baki da baki dan wanga batu🙊gaskiya ba damu ba gaad'a da fatalwa🏃
Muhad'u a sabon littafinmu👇
Dasabon gini...
A Facebook:
Ibrahim's Daughters Novels.
Insha-ALLAH.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!!
Baba Aminu Inuwa Ibrahim(Wambai)
Jiya Alhamis ALLAH yamishi rasuwa...yan uwa kutayamu rok'a mishi gafarar Ubangiji,jinyar da akayi yasa k'arshen wahalar kenan👏😭
ALLAH YAJIK'ANSHI!
ALLAH YABASHI TABBATA!👏
YAU JUMA'A AKA KAISHI GIDANSHI NA GASKIYA... D'AKI A CIKIN K'ASA! SHIKENAN FA RAYUWAR😭
Alhamdulillahi alakullu halin Wa'a'uzu billahi min amali ahalin nar.
Subhanakallahumma wabihamdika ashhadu anla'ila ha'illa'anta astaqfiruka wa'atubu ilaika.