IZINA CE Page 21-25 (The end)
.
Hijab kawai ta d'auka ganin k'arfe bakwai na dare ta dau jakarta tana kuka musty na zaune a kusa da fulawowi ta fito ta tsaya suka k'urawa juna ido da gudu ta fita ko motarta batayi k'ok'arin d'auka ba ta fita tana tafe tana kuka har bakin titi ta shigata samu adedeta sahu ta shiga suna tafiya tana mai kwatance har k'ofar gidansu bayan ta bashi kud'i ta tsaya domin gabanta ke dukan uku- uku me zata cewa iyayenta! kan abinda ya kashe mata aure ya ALLAH ka bani mafita sadakarwa tayi ta shiga tana mai yak'inin zata fuskanci kowane k'alubale tabbas tasan ta tafka babban kuskure Abaya.
Sallama tayi mama da baba da hafiz su zainab dasu Auta kowa nacin abinci suna hira gaban mamane ya fadi tace "wa alaikumussalam" nan kowa ya d"ago ido zubewa shkr tayi awajen tana gursheken kuka maicin rai hafiz yace "ke meye ne? baba yace "uwata maiyya faru? mama tace "kode wani abun ya samu musty" d'agowa tayi ta kallesu "mama ya sakeni" gaban mama da baba ne ya bada dam! runtsie ido maama tayi ta zare hannunta daga cin abincin hafiz yace "meya faru?
.
Tashi tayi ta shiga d'aki baba ya kalli mama "Ana wata ga wata" mama ta tashi ta bita d'akin tace "shkr meya had'aku? shkr dake kuka hardasu majina ta kalli mama "tabbas wanda baijiba bari ba yaji hoho mama duk da na da nayi abinda bai daceba amma abinda nayi yana nan mama na cuci kaina" mama tace "dallah malama ki fad'a mana tabbas naaan kece bakida gaskiya" shkr tace "zan fadi komi mama domin ni yanzu tsoron ALLAH ya dada shigana mama nayi samari kala kala kullum kina bani shawara kina hanani acikinsu na biyewa d'aya munyi soyayya ta rashin hankali abun bai tashi mun illah ba sai yanzu ya dawo ya hanani zaman aure kan sai na dawo mai kullum kirana yana mun barazana mama shine silar kashe min aure nayi dana sani"
Mama kuwa salati ta hau yi "oh ni 'yasu duniya ina zaki damu baka taba sanin cikin yaran zamani duk wayonka sunfika ban Taba sanin zaki biyewa wani shedani ba!"
.
"Mama kaddarace yanzu tabbas labarina zai zamanto IZINAH gamasu irin halina domin su san,irin samarin da zasu na kulawa" baba dake tsaye bakin kofa ya kada kai ALLAH yakyauta yanzu aikinga abinda muke gaya miki ko?
Shkr ta d'ago baba nagani kuma nayi nadama Kuma tazama IZINAH agaren" baba yace "bazan dau wani hukunci akanki ba sai de na cigaba Da nema muku shiriya naji dadin da kika gane gaskiy" mama cikin jimami ta zaunata dafe kai mutuwar aure ba dadi nan duk sukafita akabar shukr na kuka wan nan kenan.
Haris ne zaune da bala suna kalllon k'wallo yace "mutumina fa auren shkr ya mutu" haris yace "ai ranar naji dadi tabbas ni maI sa'a ne" uzaifa ne ya shigo ya zauna ya kaalli Haris yanzu kai Haris seda kai sanadin Auren yariyar nan ?
Haris yace "look man bana son shishshigi" nan uzaifa ya wulla mai hotuna "gashi nan kai bala sai ka gaya mai dalili" bala yace ai bangaya makaba ranr da zan aika da picture dinnan uzaifa ya hanani kai masu zafin ,kai wanda nakai ma dak'yar na k'wata agunsa" Haris ya hade rai "amma kai ajawo ne uzaifa bakayi ba wallahi ka b'atan show amma duk da hakan de naci nasara"
,
Uzaifa yace adai juri zuwa rafi wallhi kajirayi sakamako mugu kawai kaso ka batawa yarinyar mutane life ALLAH yactaimaketa tayi aure shine kake son kashewa" cikin jin haushi ya tashi ya fita.
Bala yace "uzaifa halinsa sai shi" haris yaa girgiza kai "halinsa sai shi"
.
Bangaren shkr kuwa yau satin ta biyu a gida duk ta rame ta fad'a duk ta saka damuwa aranta domin gani take kowa ganin ta yake a yar iska duk ta dawo silent mama na Alwala mardiyya ta shigo gidan ta gaidata dakin shkr ta shiga taganta tana kuka ga hoton musty tana kalla zama tayi gefenta shkr ashe haka abi ya faru banji d'ad'in abinda ya faru ba amma hakan ma alkairi ne agareki domin ALLAH ya gwada imaninki ki daure ki cinye jarabawar nan" shkr tace "nagode" nan ta d'an zauna sukayi hira sosai ta tafi.
Shkr ta shiga kunci ga soyayyar Haris dake cinta .
Abangaren Haris ma duk ya fad'a gashi har yanzu bai huce ba bak'in ciki yayi mai yawa ko sanvcin abinci baya so hakanaan gidan duk yayi k'ura sai De yayi wanka ya fita kawai domin aransa ji yake shkr ta ci amanarsa.
BAYAN WATA BIYU
.
wata biyu kenan, da rabuwar haris da shkr sai asan nan mahaifiyar musty suka samu labari kiran musty tayi taji dalili nan yace kawai shi ya gaji da zama da itane . umma dake zaume kan kujera me daya afalonta tace zancen banza kenan! To na baka izinin ka maido da matarka" amsa mata kawai yayi ya tashi ya tafi .
Shkr kuwa yanzu ta dan yi kiba ta rage damuwar saima yawan azumi datake addua take ALLAH tausasa zuciyar musty ita kanta mama shirUn yayi yawa yau da dare ta samu baba da maganar yace nima wlh abun na damu duk da abinda ya faru dole ya dake shi,gashi har ta kusa gama idda, amma gobe zan neme shi"
.
Washe gari da safe kuwa baba ya nemi mustaph dakyar yazo domin yanajin kunya baba yace "tabbas ammaka lefi amma kayi hkr kamaida matarkaVkuma kayi bincike" musty yace "to baba nagode"
ALLAH MAJI ROKON BAWA
.
Uzaifa dake zaune yana tunani tausayin shkr yakeji tabbas yanzu kome tayi abaya haris ne dole ya nemi mijinta cikin sa a ya je har office din musy ya same shi bayan sun zauna yace "tabbas duk abinda ya faru sa makircin haris ne,kan son daya kewa matarka domin tsohuwar budurwarsa ce amma nasan komi agabana suke hakan duk makirci ne don arabaku"
"musty yace to hotunan fa!" uzaifa yace "duk shima hakan" duk da cewar uzaifa yasan irin soyayyar data gudana tsakanin haris da shkr amma hakan bai sa yace tare sukai ba sai yace duk makircin haris ne nan ya rufawa shkr asiri domin ALLAH yayi gaskiya duk wanda ya rokeshi daya rufamai asiri kome ya aikata zai rufa mai lalle ALLAH ya karbi adduar shkr nan musty yayi mai godiya
.
Byan kamar sati d'aya musty yaje gidan su shkr ya samu baba kan maganar shkr kan yanaso ta koma ya maidata nan baba yaji dadi yayI godia shiga gida yayi yace shkr taje mustu nason ganinta.
jiki asanyaye ta fita tunda ta fita ya k'ura mata ido ganin tayi haske ta rame sunkuyar dakai tayi musty yace "yau na maidake kiyi hkr ki koma ALLAH ya yafemu gaba d'aya" hawaye taji ya zubo mata tasan duk abinda ya faru da ita tabbas gaskiy ce itace sila kuma hotunan duk gaskiy ne amma da yake ALLAH gafurur raheem ne idan kayi lefi ka rok'eshi zai yafemaka in har kayi tuba kuma taubatan nasuhan wanda bazaka koma ga aikatashi ba to har idan kabarwa ALLAH lamarinka zai jib'inceshi ya kawo maka mafita.
.
Tsoron ALLAH ne ya k'ara shigarta ta d'ago ta kalli musty tace "nice da godia" Murmushi yayi mata "yada kuka kuma sorry nayi laifi ko? ashe duk shirin haris ne shiya hada komi seda gaskiy ta fito"
.
Shkr ta share hawaye na tausayin musty nan don tason ba kowane namiji bane za ai hakan ya maida ita amma,kuma duk wansa yasa ALLAH a lamarinsa,ya isar masa yace "gobe zaki koma ko?" harara takai mai "nak'i" nan ta juya ciki yabita da kallo yana murmushi tare da jan motar yayi gaba ta koma ciki aguje tana dariya mama dake kitchen tayi murmushi tana godewa ALLAH domin kullum dare bata bacci tana ta kaiwa ALLAH kukan ta shkr kuwa wani shaukin soyayyar musty ke ratsata ALLAH ALLAH take gobe tayi domin tayi kewar abinta .
Ring taji kiran nusty ya shigo yace "gobe kishirya zan kaiki saloon" tace to "ogana" musty yace "ki cire layin nan gobe zan kawo miki sabo" tace "tam" nan ta cire ta karya bayan ta kwashe nambobin data keso
www.itzays.tk
.
Washegari da safe k'arfe goma musty yazo shkr anshake uwar kwalliya tunda ta fito ya k'ura mata ido dole yana rufe matarsa don tana da kyau shiga tayi yaji wani sanyin kamshi ya bugi hancin sa yace "baby wollahi nik'af zan sai maki kina sawa haba bansan maza na kallonki" murmushi tayi tace yanda kaso haka za'ai mik'a mata sabon layi yayi ta karb'a ta saka a wayarta nan ya kaita gidan saloon yace zaije ya dawo shigar ta keda wuya bata dade ba aka farai mata awa daya da rabi aka gama nan ta kirawo musty yace gashi nan.
.
D'an fitowa tayi saboda yace gashi nan dede kwanr haka ta tsaya kawai ji tayi an mata magana haris ne tsaye yana murmushi tsaki tayi ta juya tana jan hirji dawowa yayi gabanta yana kokarin tab'atata nan ta juya ya janyo mayafinta be aune ba yaji sautin hannun shkr takai mai mari dede lokacin musty ya karaso afusace ya fito yazo ya kama wuyan haris ya kaishi bango yakai mai naushi "karabu da matata wallahi sena d'au mataki akanka" naushi haris yakai mai musty ya goce sai da wasu mutane suka rabasu haris ya shiga mota musty yaja shkur yace "kiyi hkr dole na d'au mataki wallahi" be zarce ko ina ba sai police station yakai report akan abinda Haris ke mai nan ya bada sunan sa ya fadi unguwarsa nan duk ya gama san nan ya maida shkr gida bayan ya kaita ya koma gida ya kwanta ya huta k'arfe uku daidai k'anwar mamarta tamaida ita gidanta.
.
B'angaren haris kuwa karfe 5 na yamma suna k'ofar gida shida wani abokinsa sai tafawa suke motar 'yan sanda ta tsaya suna fitowa suka nunawa haris katin sammaci kan yazo ana nemansa da yayi gardama k'arshe abokin ya bashi baki suka tafi yana zuwa ya tarar da musty a zaune kan kujera suna zaune suna hira da wani dan sanda, suna shiga musty ya aikawa da haris wani banzan kallo nan de aka maida magna musty yace ayi mai iyaka da Haris ya kyale mai mata domin duk abunda ya sameta shine kuma ya sama mata lafy nan aka rubuta arubuce mustY yasa hannu shima Haris ya saka hannu zuciyar sa na tafarfasa hala 'yan sanda sukai mai kashedin duk randa ya kuma se ya kwana gidan maza nan kowa ya kama gabansa
.
Tunda akai wan nan abin Haris ya sama mata lafiya ba yanda yaso haka ya hakura da ita nan kuma ya shiga farautar wasu matan da zai yaudara tunda dama halinsa ne.
yauma da suka dawo daga club suna tafe kida na tashi amotar bala abaya yana dariya wani wawan burki haris yaja ganin waataa zuk'ek'iyar budurwa agaban gefen titi ba wani gardama ya tsaida mota domin tayi mai nan yaa yace "aa yanmata yade? ina zuwa? kallonsaa tayi samada k'asa tayi dariya yace "ko banyi bane? tace "aa kayi mana kamar a landon" lashe leb'e yayi "shigo 'yan mata na kaiki kinga dare yayi" ba musu ta shiga ya figa "ina kikayi? tace "gaba kad'an zan sauka" fuuu haka yake gudu jin hannu yayi a gefen cinyar sa ana tab,a shi ya dago ganin budurwar nan yayi ta kashe mai ido
.
wani murmumahi yayi abin nema ya samu wayarsa ya d'auka ya bata sakan number d'inki ba tantama ta saka mai bala kuwa duk abinda ke faruwa yana daga baya yana ji sunxo dede wurin ya sauketa se munyi waya tace ok
nan tayi wata kwana bala ya dawo gaba haris yace "kaga wata d'anyar bebi na samu dami akala yanzu zan fanshe tada shkr wan nan ma tafi had'uwa" bala yace "gaskiy ba k'arya"
.
Bangaren shkr kuwa hankalinta ya kwaana ta kame mijinta suna zaman su lafiyaa ko fita shkr bata San yi inde ba ya zama sole ba, idanma zata fitan to musty ke kaita wataan ta daya da komawa sai ga ciki murna gun musty ba kama hannun yaro haka suka hau tarairayar cikin da suka dade suna muradi
.
Haris kuwa soyayya tayi nisa shida lubna awaya kullum suna manne yau sukayi zasu had'u nan haris ya mata kwatancen gest house Din babansa domin ba a amfani Dashi k'arfe 5 dede lubna taje ta had'u iya had'uwa tana shiga suka fara watse warsu tun a falo idanuwan harin duk sun k'ank'ance tunk'arfe 5 sai wajen har wuraren asuba na dare san nan suka hakr da juna Haris ya rena kansa gurin lubna yayi mamakin ta tunda suka gama ya kasa tashi itakam k'em ta mik'e da k'yar ya tashi tana dawowa idanuwansa suka sauka akan k'afafu wanta
.
Da sauri ya ja da baya ko ko ko fato wani ihu yasa lubna ta tintsire da dariya ta nuna shi da d'an yatssa take kamar and'aga shi samata sake shi dam ya fad'o ya bugu da k'ugunsa
kuma saka dariya tayi "Haris na dad'e ina neman irinku domin ni ba mutum bace aljana ce ina bin duk namijin dake lalata yaran mutane ina lalata dashi to kaima haka ka fad'o komata karka manta "yan mata wajen goma kayi lalata dasu wasu kuma baka kaida cimma burinka akansu ba" nan ta tashi tayi girgiza ta dawo ainihin suffanta ai yana ganinta ya suma ita kuma ta b'ace.
bashi ya farka ba sai wajen asuba yana tashi yaga gabansa ya kumbura nan ya kirma ihu da k'yar ya kirawo number d'in bala yace yazo ya same shi hakan kuwa k'arfe bakwai na safe yaje ganin halin da yake ciki yasa ya cicci b'esshi yakai mota direct gidansu ya kaishi.
.
BAYAN WATA UKU
.
bayan wata 3 haris ya jigata don ko fitsari baya iyawa ga wani abu dake fito mai yana gadon asibiti sai kuka yake ciwo yaki warkewa ganin hakan yasa aka koma gida ana mai na gargajiya babansa ne ta samo wani malami ganin irin firgitar da yake nan malamin yayi addua yayi mai karatu take birkice yafara wani irin abu malamin ya cewa baban haris "tabbaas ya hadu da aljana kuma sun sadu da aljanar ta saka mai ciwo amma da izinin ALLAH zai warke nan ya bashi rubutu da wasu magunguna cikin ikon ALAH sati d'aya ya fara warwarewa gaban nasa ya rage kumburin saida ya k'ara wata d'aya san nan ya warke tunda ya samu lafiy yazama silent duk ya dena iskanci yadena kula mata balle yayi lalata dasu
se yanzu yayi nadama shima bala ya shiryi domin ya tsorata da yanda haris yayi ganin hakan yasa dadynsa ya samo mai mata akai mai aure tare da aiki a hade ya fara zuwa aiki nutsuwa sosai ta saukar mai ya shiga makaranta ta koyan addini ta manya da daddare domin yaga IZINAH
.
Shkr kuwa summa bar k'asar itada musty domin ya koma yin wani course din a germany wanda zayyo shekara uku acan shiisa ya tafi da shkr
Anan na kawo k'arshen wan nan gajeran littafin nawa inda nayi dede ALLAH ya bamu ladan inda nayi kuskure kuma ALLAH ya yafe mana wasallahu ALA nabiyur kareem
wa ahlhi wa sahbihi ajma'en
Godiya ba adadi ga daukkacin group din da suke bibiyar llittfina sann nan da fans dina masoyana ALLAH ya bar kauna
Fans dina na wattpad ALLAH ya bar kauna
.
Dukkan abinda yayi farko zaiyi karshe yau Allah ya nuna mana karshe *Izinah*
Masha Allah izinah ya fadakar ya ilmantar ya nishadantar Allah ya kara basira daukaka ya kara karfin ido da zakin hanu
Allah ya baki ladan fadakarwa ya yafe miki kurakuraniki
Gsky novel yayi kuma gsky wannan novel din yace sunansa kuma izinah ne ga yan matanmu da zawarawanmu masu soyayyar shan minti gsky muna kuskure sosai, da sosai wlh wasu mazan ba kaunar matan suke ba su matan akwai karamar brain suyi ta biyewa mazan kuma kuskure ne babba daga karshe su hanaka zaman aure, kuma ko basu hana kaba ki dubi babban laifin da kuke aikatawa Al'hali Allah ya hanemu da aekatawa kuma Allah bazai barmu haka ba wlh sai ya jarabcemu gwargwadon abinda muka aekata kamar shkr, Haris ya hanata jin dadin aurenta
One thing da mata masu gane ba tsakaninsu da mazansu su ringa musu rufa2 kuma kuskurene babba tsakaninki da mijinki kuyi zaman amana kuyi sharing damuwarku kuma karki ringa buye masa komai sbd sharrin shaddan kar wata ran kina buye buyenki wani abu ya faru wlh baki da mafuta said Allah kuma in bakya boye masa duk wani tuggu zaki tsallake bi'izinin Allah
.
Kawaye gsky kawaye gubace a rayuwa but ba dukka ba bata garin sunfi yawa, sai kiga kawa bazata baki shawara mai kyau ba sai wadda zata bata miki rayuwa kuma ta zame a hada baki da ita a cuce ki, sunan wadda kika aminta da ita wata kawar kuma tagari ce but kuma bama santa Allah ka ganar damu Allah ka bamu ikon Amfani da abinda muka krnta
Masu irin halin Allah ka ganar dasu su gyara