_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_
*_A RUBUCE TAKE !!!_*
(K'addarata)
*Huguma*
Arewabooks: huguma
Free page 01
Babban falo ne,wanda yake malale da marron din carfet mai taushi da kuma saitin kujeru kalar labulen wadanda suka yiwa falon qawanya,a tsare falon yake,ta yadda duban farko kuma kai tsaye ba zaka dauka falon tsohuwa bane,saboda ya wadata da kayan alatu na rayuwa bakin gwargwado.
Daga tsakiyar falon,mamallakiyar falon ce zaune saman carfet din,babbar macace wadda gashinta mai tsaho da kuma santsi ya fara bayyanar da furfura saman sumarta,kana iya hangen hakan sakamakon gocewar daurin dankwalin dake kanta,fara ce sol har yellow takeyi,tsufanta bai boye kyan siffa da take dashi ba,wanda da alamu ta sameshi ne tun daga zamanin quruciya kawo yau,kana kallonta kasan ba cikakkiyar bahaushiya bace,hakanan kammanninta bana fulani bane.
Daga gabanta kuma wata matar ce da suke diban kamanni da ita,saidai nata shekarun gaba daya ba zasu rufa talatin ba,ita dinma fara ce sol kamar matar dake zaune kusa da ita,wanda kana dubansu zakasan cewa 'ya da uwa ne,yaro ne saman cinyarta tana shayar dashi,dattijuwar mahaifiyar tata kuma tana daga kayan dake gaban nasu
"Duk da kayan sunyi kyau humaira,amma gaskiya nafison wadanda sukafi wadan nan tsada,Banason siyawa widad kaya masu sauqin kudi,gwara masu dan tsada da inganci" mai da dubanta halimatu tayi ga kayan tana sake qare musu kallo duk kuwa da cewa itace ta siyosu da hannunta,kayan irinsu ta siyawa yaranta,ta siyama widad din irinsu ne a nata zaton shine qarshen abinda zatayi ta burge ummu,saita maida dubanta ga dattijuwar
"Ummu,yanzu duk kyan wadan nan kayan basuyi miki ba?" Kai ta girgiza
"Basuyimin ba,kuma tunda nace basuyimin ba ai sai a canzo ko?,tunda dai kudina na saka zan siya,ba kudin wani bane" baki halima ta tabe tana sanya hannunta guda daya tana tattara kayan gefe,zuciyarta cike fal da bacin rai,akwai maganganu da yawa a ranta,amma tasan bata isa ta fadesu ba,yanzu yanzu rai zai iya baci indai akan widad ne
"Kin karba min kudin a wajen yaayan?"
"Yace sai ya dawo zai bayar na ajiye miki" sake baci ranta yayi,wannan karon ta gaza boyewa
"Uhmmm,Allah sarki,to Allah yasa suna da rabon saka ankon" kallonta ummu tayi ba tare da tace mata komai ba,idan da sabo ta saba da irin wadan nan dabi'un,ta rasa me yasa suka gaza fahimtarta,tana ganin son rai ne kawai da son kai irin na dan adam.
"Latifa!" Ummu ta waiwaya bayanta inda qofar kitchen dinta yake ta qwala kira,daga ciki aka amsa sannan mamallakiyar sunan ta fito,wankan tarwada ce,mai matsakaicin jiki,a nutse ta qaraso
"Gani ummu"
"Shiga dakina saman pillow akwai purse dita ki daukomin" amsawa tayi da to sannan ta juya.
Saidai bata ko kai ga isa dakin ba,ihu ya karade gidan cikin wata siririyar murya,ihu ne sosai hade da kuka.
Da sauri Latifa ta dakata da tafiyar,sannan ta waiwayo tana duban ummu,itama ummun ita take kallo,fuskarta cike da tsoro
"Ummu kamar muryar widad fa" kai ta jinjina da sauri
"Haka nake shirin fada nima"
"Yo wace idan ba ita ba?,kaf gidan nan waye yake wannan tabarar idan ba ita ba?" Dauke dubanta ummu tayi daga kan.haliman zuwa ga ladifa,wadda tuni ta fara nufar qofa
"Yawwa,dubamin ita don Allah latifa"
"Yanzu kuwa" ta amsata tana ficewa daga falon.
Yaronta halima ta kwantar a gefe sannan ta miqe itama tabi bayan latifan tana qunquni cikin ranta.
Babbar harabar gida ne wadda ke dauke da interlock shimfide a ko ina,duk da irin girman harabar gidan,jikin kowacce katanga data zagaye gidan dake dauke da sassa sassa guda biyar shukoki ne da.flowers da sukabi bangon gidan suka zame masa ado.
Daga bakin daya daga cikin sassan gidan wasu daga cikin ma'aikatan gidan ke tsaye,daga inda kake kana iya hangota,yarinya ce da duka duka ba zata wuce shekara goma zuwa sha daya a duniya ba,farace sol,irin farin nan me cakude da surkin jaa,ma'abociyar yalwatacciyar suma me santsi data sauko har zuwa bayanta ta kuma bazu har saman kafadunta saboda tsallen da take faman yi tana kuma dage maroon din doguwar rigar dake jikinta,manyan idanunta cike da hawaye da suke saukowa saman kumatunta wasu na zirara har gefan dogon hancinta da ya gauraye da majina da hawayen
"Babu komai fa widad,na gaya miki na cire shi tun dazu" wata mace dake tsaye a gafe sanye da riga da zani na atamfa ta fada tana qoqarin riqe yarinyar.
Dai dai lokacin latifa ta qaraso halima na biye da ita
"Meye haka?,me ya faru?" Yayi tambayar tana nufar widad da keta zabga tsalle da kururuwar kuka
"Tana tsaka da barci a falona bayan sun gama guje gujensu,kawai ina kitchen ni da marka na jiyo ihunta,da nazo sai tace wai kyankyaso ne ya shige mata riga,dana duba sai naga ashe qwaro ne dan qarami,na daukeshi aka fitar dashi,amma tace kyankyaso ne,nayi duban duniya ban ganshi ba" tsaki halima taja
"Iskancin banza da wofi ne da zallar tabara data yi mata yawa,wuce mu tafi kafin na tsitstsinka miki mari" ta fada cikin tsawa
"A'ah dakata a duba matan halima" latifa ta fada tana tsugunna wa gaban widad din,ta dage rigar tata da kyau sannan tace
"Kalli ki gani,babu komai a jikinki" cikin tsoro dubi fararen qafafuwanta,ganin ba komai din kamar yadda latifa ta fada,saita gyada kanta,saidai kuma har yanzu batabar kukan da take ba.
A gaba halima ta sanyata tana ta faman sababi m,wannan ya sake tunzura kukan widad din,har suka isa qofar falon ummu.
"lafiya ko?,me akayi mata?" Ummu ta fada idanuwanta da hankalinta gaba daya yana kan widad,tambayar data yi mata sai ya zamana kamar an tunzura ta,cikin sassarfa ta shige falon,tana kuma isa ta fada jikin ummun tana sake sakin kukan.
"Me kuwa akayi mata banda tsoron banza da wofi da take dashi,wallahi ummu sakalcin yarinyar nan ya fara yawa,haba" halimatu ta fada cikin huci tana neman saman kujera ta zauna kamar zata fashe
"Kin taba gani haka kawai mutum yana kuka ne?,ke me yasa kike haka?"ummu ta fada tana jifanta da harara
"Kyankyaso ne ummu yabi ta jikinta,an cireshi amma ta dauka bai fita ba" latifa data shigo ta sake yima ummu bayani tana dosar kitchen.
Waiwayawa ummun tayi tana jifar halimatu da harara
"To kinji,amma shine zakice kukan banza takeyi?,bayan kinsan widad da tsoro,kinsan kuma halittarta ce a haka?"
"Da sakalci wallahi ummu,haba don Allah,ko nabiha da take qanwarta bata wannan abun sai ita shafaffa da mai"
"To anji,saiki rufawa mutane baki hakanan" ummun ta fada tana maida hankalinta ga widad dake kwance saman cinyarta tana share hawaye
"Sannu kinci abinci?" Kai ta girgiza alamun a'ah
"Anty madina ta zuba mana,sai nayi bacci"
"Shikenan,tashi maza kije latifa ta zuba miki,idan miyar tayi miki yaji ta zuba miki wadda takeyi yanzu tunda naji kamar ta soyu,ki biya bandaki ki wanke fuskarki,bazan sake bari kije ko ina cikin gidan nan ki kwanta bama bare irin haka ta sake faruwa" miqewa widad tayi a hankali ta soma barin wajen,sai data shiga dakin ummun ta wanke fuskarta kamar yadda tace matan,ta cire rigar jikinta saboda jiqewa da tayi ta saka wata,riga da zani ne,da qyar ta iya daura zanin saboda rashin iyawa da rashin sabo sannan ta wuce kitchen wajen latifa.
"Halimatu,banason irin wannan dabi'ar nasha gaya miki,idan baku tausayawa widad ba bai kamata ku sata a gaba ba"
"Nifa ba a gaba na sakata ba ummu,sakalcinta yayi yawa ne,fisabilillahi duk cikin gidan nan wace ake nunawa gatan da kike nuna mata?,ai ba ita kadai bace jika a gidan,sannan ma girma takeyi fa,nan da shekara uku tsaf xa'a iya tayar da batun aurenta,niba tsangwamarta nake ba,so nake naga ta gyara" ido ummu tadan zuba mata na wani lokaci kafin ta janye dubanta daga gareta,ta fuskanci ba zata gane ba
"Allah ya kyauta" kawai ta sake cewa,tasa hannu ta janyo purse din da latifa ta ajjiye mata,ta bude ta fidda 'yan dubu dubu ta lissafa ta miqa mata
"Gashi,ki lissafa ki cire kudin da zaa qara na kayan da zaki canzo din,ragowar ki siya ma yaran sauran abinda ya rage" hannu biyu tasa ta karba tayi mata godiya,duk daba haka taso ba,ta rasa me yasa ummun take kasa dai daita widad da sauran jikokinta.
Sanda ta shiga kitchen zamanta tayi wajen latifa bayan ta zuba mata abinci,tana ci suna hira,sai ka rantse da Allah ba ita ta gama sambada ihun ganin kyankyaso ba,tana ta zubawa latifa surutu ita kuma tana biye da ita,wannan yasa akwai shaquwa sosai tsakaninsu,kusan tana daya daga cikin wadanda basuson kukanta cikin gidan.
Sai data cinye tas sannan ta ajema latifa kwanon ta sauka daga kujerar data hau kai ta zauna
"Kizo ki wanke hannunki mana kafin ki fita" latifa ta waiwaya tana ma widad magana,wadda tuni ta kusa qofa tana sude hannu
"Ina zuwa,zan wanke a wajen anty madina,na manta na baro alawar madarata dazu a can,Allah yasa su faruqu basu shanyemin ba" bata ko sake tsaiwa sauraron latifa ba tayi qofa abunta.
Su uku ne yanzun zaune a falon sabanin dazu,anty halimatu,ummu da kuma wani baqon daban.
Matashin saurayine fari ne shima kamar yadda na lura da kusan mafi yawa na launin fatar jama'ar gidan farare ne,yana da sassalkan gashi mai santsi gami da duhu,kamar yadda sumar qabilar larabawa ko buzaye suke da ita,sanye yake da shadda dinkin zamani da ya zauna masa sosai a jikinsa,kanshi babu hula,hannunsa riqe da wayarsa yana dannawa,gefe daya kuma suna hira da ummu da anty halimatu.
Turus widad tayi tana kallonsa,ta tsareshi da idanu duk da babu wanda ya ankara da fitowarta a cikinsu,dubansa take tana jin wani haushi yana cikata,tsaki taja a hankali don kada su jiyota,sai kuma ta tura baki gaba kamar zata saki kuka.
,juyawa tayi kamar zata koma cikin kitchen din,amma kuma saita sauya shawara,saboda tasan indai ta koma din ummu tasan tana can kuma zata kirata ta fito,abinda bata so din kenan,sai ta dawo tana duban bayan kujerar falon,akwai hanya da zata sadata har qofar falon,don haka ta duqa ta fara tafiya a durqushe ta bayan kujerun,gabanta yanata faduwa,fatanta Allah yasa kada ummu ta ganta.
A hankali ummu ta waiwaya zuwa sashen kujerun,motsi take jiyowa,saita sauke idanunta zuwa qasan kujerun,fararen qafafuwan widad ta hanga,dariya taso subuce mata amma saita danne,ba tare da kowa dake wajen ya ankara da abinda ke faruwa ba tace
"Widad!" Idanunta na kan qofar falon,ba zaka zaci ta ganta ba,cak widad ta tsaya tana zare manyan idanuwanta waje,gabanta yana faduwa,tana jin kamar ta juya ta koma,amma kuma idan tace zata koma din asirinta zai tonu
"Widad,ko bakya jina ne?" Ummu ta sake kiranta tana kallon sashen da alamu suka nuna a nan take a tsaye,saddaqarwa tayi,ta tabbatar ummu ta ganta,don haka sai kawai ta miqe tsaye,fuskarta a daure,ta tattare dan qaramin bakinta ta turoshi gaba,sannan ta fara takowa zuwa inda suke.
Dukkansu suka bita da kallo,halimatu ta tabe baki tana dauke kanta,haushin widad din yana sake kamata,ummu kuwa girgiza kai kawai tayi,cikun zuciyarta tana cewa
"Allah ya kyauta aikin quruciya".
Ta bangarenshi kuwa da kallo ya bita,ya kafeta sosai da idanuwansa,irin kallon da sautari abokansa kan masa dariya,su kuma ce sukam basuga abun kallo ga qwaila kamar widad ba,tun tana tsumman goyonta Allah ya jarabceshi da soyayyarta,har yau kwanan gobe kuma babu abinda ya canza a zuciyarsa game da ita,saidai ita din da baiga alamun koda sakewa dashi tattare da ita ba bare akai ga zancan soyayya,soyayyar da yake da yaqinin bata santa bama,batasan kuma mece ce ita ba,shi yake saka ran ta koya daga gareshi,saidai bata sakewa dashi bare ta bashi wannan damar,tako ina bashi da matsala,yasan zaya sameta za'a bashi ita kamar yadda yake muradi,amma kuma babbar matsalar daga gareta ne.
"Bakiga mutane ba ba zaki gaishesu ba?" Ummu ya fada tana hade fuskarta tsam waje daya,duk yadda takai ga gantanta widad da nuna soyayyarta a gareta,amma bata da sassauci wajen tarbiyya.
Kamar wadda aka sheqawa mari haka ta waiwaya gareshi
"Yaya mahfood ina yini?" Tattausan murmushi ya saki yana kallonta,kanta babu dankwali kamar yadda ya santa,bata qaunar daura dankwali sam
"Lafiya lau widadun ummu,ya makaranta?" Bata amsa masa ba,saita juya ga ummu tana bata rai
"Gani ummu" ummun na shirin miqewa tsaye tace
"Bani nake nemanki ba" saita miqe a abunta tana riqe da hijabinta a hannu
"Muje ki gyaramin wardrobe dita kafin ki wuce gida" ummu ta fada tana yin gaba.
Miqewa halimatu tayi ta saba yaronta a kafada tabi bayan ummun tana cewa
"Har yau ita widad din dana koyawa yadda akeyi bata koya din ba kenan?"
"Nidai ba wannan na tambayeki ba,in zakimin kimin,idan kuma fashin baqin naki zakiyi ki barmin kayana,ko intisar tazo sai tayimin" jin ummun ta fara mita saita tsuke bakinta,tabi bayanta kawai din kawai,sai falon ya rage saura su biyu.
*_DOGUWAR TAFIYA CE,WADDA KE QUNSHE DA TARIN DARUSSA,TAFIYA CE MAI DAUKE DA WANI IRIN SALON KISHI,GOGAYYA CE DA FAFATAWA TSAKANIN MABANBANTAN MATSAYI BIGIRE GAMI DA MATAKI NA RAYUWA_*
*_Ta fita zurfin karatu_*
*_Ta fita yawan shekaru_*
*_Ta fita wayo dabara da siyasa_*
*_GOYON KAKA CE_*
*_SAKALTACCIYA_*
*_ME QANANUN SHEKARU K'WARAI_*
*AKWAI TAZARA MAI TARIN YAWA A TSAKANINSU,KWATANKWACIN SAMA DA QASA*
*AMMA DUK DA HAKA TA CITA DA YAQI*
*GARIN YAYA?*
*_Kin karanta HANGEN DALA?,to ba shakka wannan tafiyar ta fishi zafi darussa da kuma ilimi a cikinta(in sha Allah)_*
*_ku taho kawai muje,kuyi jumurin bibiyata,kamar yadda aka saba har kullum,babu gaggawa cikin tafiyata_*😄✋🏽
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥
0022419171
Maryam sani
Access bank
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*🔥
*_A RUBUCE TAKE!!!_*
(Kaddarata)
*HUGUMA*
Free page 02
*MAAB LUXURY HOME*
*_idan kaji gangami akwai labari_*
*_SABUWAR DUNIYA CE_*
*ALFAHARIN UWAR GIDA*
*FARINCIKIN AMARYA*
*MAIDA TSOHON GIDA SABO*
*DUNIYAR QYALE QYALE*
*KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA*
*_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_*
*nasan zaku tambaya ina ne nan?*
*MAAB LUXURY HOME*
😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya*
*_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_*
*Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu*
*Kayan gado dana parlor*
*Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida*
*Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a*
_adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_
*Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram*
@maabluxuryhome
*Facebook*
@maabluxuryhome
*Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka*
08034631010
*Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝
____________________________
waiwayowa yayi yana dubanta bayan ficewarsu gaba daya,maficin da ummu ta tashi ta bari ne riqe a hannunta tana tsige adon jiki,fuskarta a dinke tsaf,yakanyi.mamakin yadda take masa,kamar wata qatuwar budurwa,ya rasa dalilin da sam bata son su zauna waje guda ko su hadu,saidai har yanzu zuciyarsa na bashi nutsuwar cewa quruciya ce kawai da rashin sanin ciwon kanta,da zarar ta sake hada hankalinta zata fuskanceshi?
"Amma sai yaushe?,lokaci qara quracewa fa yake" zuciyarsa ta gaya masa,sai ya dan gyada kai
"Soon in sha Allah" ya fada yana bawa kansa qwarin gwiwa,qwarin gwiwar da kusan kullum itace madogararsa
"Widad" ya kira sunanta
"Na'am" ta amsa a cunkushe ba tare data kalleshi ba,murmushi yayi
"To kidan kalleni mana?,ummm,ke da zaki zama matata?,so nake ki saki jiki da yayan naki" manyan fararen idanuwanta ta daga tana kallonsa,wani haushi da kuma tsanarsa suka saukar mata,lallai yaaya mahfood ta tabbata dan iska ne,ita yakewa zancen ta zama matarsa?.
Yadda ta zuba masa fararen idanuwan nata sai yaji dadi cikin ransa,don takan jima bata tsaya ta kalleshi ba,wannan ya bashi qwarin gwiwar janyo ledar daya shigo da ita wadda ke shaqe da kayan kwalliya,kasancewar ya santa da son kayan ado da gayu ya tura gabanta
"Ga kayan kwalliya nan 'yammatan ummu,sai ayita shafawa ko?" Dauke idanunta tayi daga kansa ta mayar kan kayan,saita dalla wa kayan harara,ita zaiwa wayo?,ya dauka bata da hankali kenan,haka kawai,bayan ummu tasha gaya mata ko zama tayi kusa namiji ciki zatayi,shine zai wami bata kayan kwalliya?,to bai isa ba,tana gama wannan tunanin ta miqe abinta ta nufi qofa da saurinta.
"Zo mana widad.....widad"ya fara qwala mata kira,gudun kada latifa ko ummu dake daki su jiyo shi,su kuma sanyata dawowa dole saita fella da gudu ta qarasa ficewa,don ta lura shi kadai ne zaifi mata saurin barin sassan.
Bata tsaya ko ina ba sai sassan anty madina,taja birki tana zabga haki,dai dai lokacin da dukka yara yaran gidan da suke da shekaru irin nata ke zaune a falon anty madina,kaf cikin matan gidan ta fisu qarancin shekaru,tana da faran faran da son mutane,tana yawan jansu a jiki gami da biyewa shirmensu,wannan yasa kafatanin yaran gidan kowa ke sonta,yake kuma son zama a sassanta.
Dago kai tayi tana duban widad,muhassana ce kwance a cinyarta diya ga qanwar mahaifin widad tana mata tsifa
"Lafiyarki widad?,irin wannan cin burki haka?" Guri ta samu kusa da khalisa ta zauna tana maida numfashi,sai kuma ta bata rai, idanuwanta sukayi rau rau suka ciko da qwalla
"Yaya mahfood ne"
"Mahfood kuma?,biyoki yayi?" Kai ta girgiza tana turo baki gaba,ita sam sam ma batason maganarsa,yanzu su mahassana zasu fara tsokanarta
"Wai cemin yayi matarsa" tana fadin maganar qwalla na gangaro mata,qaramin murmushi anty madina ta saki,ta rasa wanne irin rashin haduwar jini ne haka tsakaninsu,duk wanda ya kwana ya tashi yasan yadda mahfood din ke qaunar widad,hakanan kowa yasan yadda take gudunsa,bata qaunar hada inuwa dashi
"To banda abinki mene ne don yace miki matarsa iyi widad?,bakiga su zahira ba aure za'ayi musu?,kuma daga su sai ku?" Kafin anty madina ta kammala bayaninta widad din ta saki kuka harda turje qafafu,baki anty madina ta sake tana kallonta gami da jan salati,yayin da su muhassana suma ke kallonta suna dariya
"Tsaya,bakya sonshi ne shi yayan naku?" Kai ta gyada
"Wallahi ni bana sonsa Allah"
"To ya isa,ki share hawayenki,an gama maganar,ba wanda zai baki shi" dif kukan ya tsaya,ta tashi ta zauna dai dai tana goge qwallarta tana kuma hararar su khalisa kan dariyar da suke mata
"In sha Allahu sai su abba sun baku dauda" dariya sosai anty madina ta tuntsire da ita,duk da quruciyarta wani lokaci idan tayi wani abun kamar babba,dauda shike wankin gidan,na kowanne sashe,daga qauye yazo a gidan aka riqeshi
"Bakinki ya sari danyen kashi" khalisa ta fada tana dariya
"Saidai naki bakin" widad ta fada tana sake harararta,dole anty madina ta shiga fadan ta raba,ta kuma janye musu hankalinsu da wani abu na daban.
Qememe taqi komawa sassan ummun,duk da ummun ta aiko latifa har kusan sau uku amma taqi komawa,zatonta mahfood yana nan bai tafi ba,wayo ummun keso tayi mata don ta dawo,har abbanta yazo ya tafi bata koma din ba,son samunta ma tayi kwananta nan wajen anty madina cikinsu farisa,amma kuma tana tsoron kyankyaso,kada yayi mata irin yadda yayi mata daxun,har sai data fara barci sannan latifa tazo ta tafi da ita bayan ta tasheta ta sakata a gaba.
Tana shiga dakin ummu ta haye gadonta taja bargo ta duqunqune sosai harda cusa kanta cikin pillow,tun tana kasa kunne taji shigowar ummu har bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari ummun bata ce komai da ita ba,saidai ta bata ledar kayan kwalliyar tace ta dauketa taje ta adanata,aifa kamar jira take,saita dire cup din da take shan tea dashi ta saki kuka
"Allah ni bana so,banaso ummu" tana turje qafarta a qasa
"Hukumullahu" ummun ta fada a ranta tana zuba mata idanu,wannan abun na widad din kuwa na qare ne?,kullum abu kamar ma sake ci gaba yakeyi?,kafin takai ga sake cewa komai akayi sallama falon,ta dauke kanta daga widad ta maida gareshi taba amsa sallamar.
Babban mutum ne ko ace magidanci,wanda kallo daya zaka masa kasan danta ne daga tsatsonta ya fito,a nutse ya qaraso falon yana kallon widad da fuskarta tayi sharkaf da hawaye
"Ke kuma da baki rabo da rigima me akayi miki?" Ya fadi yana neman wajen zama,baki ummu ta tabe tana girgiza kai
"Don anyi maganar mahfood ne" saita zarce da gaya masa abinda ya faru jiya.
Maida dubansa yayi gareta yana nazartarta na wasu daqiqu,shima kallon quruciyarta yakeyi,yasan ita ke dawainiya da ita,don idan a wani gidanne ko zancan aurar da yayunta da za'a aurar yanzu ba'a fara ba bare ita,to amma haka tsarin yake,a haka kuma dukka suke tafiya
"K'aniyarki" abba ya fada yana tsuke fuska
"Don gidanku mahfood ba babanki bane kike masa irin wannan?,maza tashi ki dauki kayan ki adana su" fuskarta jiqe da hawayen ta miqe ta dauki ledar,sai tayi hanyar fita da ita
"Ina zaki?,nan ne dakinki?" Cikin muryar kuka ta waiwayo
"Anty madina zan kaiwa...."
"Eh itace ke iya jurewa shirmensu ai" ummu ta karba zancan tana qarashewa abba bayani,sai baice komai ba,wannan ya bawa widad damar ficewa.
Tana tafe ita daya tana sharar qwalla,maimakon sassan anty madina,sai tabi siririyar hanyar da zata sadata da parking lot na gidan,tasan can ne babu kowa,don duka samarin gidan masu fita kasuwa kawo yanzu sun fita din,sai su 'yan makarantar da suke shirin komawa ranar litinin,sune daliban da aka yaye daga primary school zasu wuce zuwa qaramar secondry jss one.
Dan bencin da ake ajewa a wajen lokaci lokaci ta haye ta zauna a kai,sai a sannan ta buda ledar tana duba abinda yake ciki,kayan makeup ne sosai irin wadanda takeso,batayi mamaki ba,don uncle mahfood din ya jima da sanin zabinta da kuma duk wani abu da takeso.
Sai data fiddosu tsaf ta qare musu kallo,sai kuma ta tabe baki,motsin da taji daga parking space din ya sanyata fara tattara kayan cikin hanzari,tana gudun ko abba ne ya fito zaya tafi,ta tabbatar idan ya ganta a wajen fada zata sha.
Wanda ta gani a wajen yana niyyar fitowa daga motar tasa ya sanyata sauke ajiyar zuciya,tasan cewa kome zatayi ba kulata zaiyi ba bare ya hanata,don kuwa tsahon tasowarta ta sanshi amma ba zata iya tuna rana daya da magana ta taba shiga tsakaninsu ba.
Kamar yadda ta zata din kuwa,ko a yanzun ma dauke kansa yayi ya soma rufe motarsa sanna ya jefa key din a aljihu ya kuma soma takawa yabar wajen.
Da kallo ta bishi tana tabe baki gami da jifansa da harara,har sai da ya bacewa ganinta sannan ta dauke dubanta daga wajen,a hankali take tattare kayan tana maidawa cikin ledar,qasa qasa take magana ita daya
"Wallahi banaso,bayarwa zanyi,ni ba wani aurensa da zanyi,dan iska kawai" dif maganar tata ta yanke,sai kuma tahau zaro idanu cikin tsoron kada wani ya jita,sai data tabbatar babu motsin kowa sannan ta qarasa kwashe kayanta ta kuma fito.
Isowarta farfajiyar gidan yayi dai dai da budewar gate din gidan,qaramar motar qirar 406 ta danno kai ciki,sai ta dakata daga yunqurin isa sassan anty madinan tabi motar da kallo,sai kuma ta saki murmushi har dimple din dake kwance saman kumatunta hagu da dama ya lotsa,saita cilla da gudu gudu sauri sauri zuw wajen motar,cike da zumudi da kuma murna.
Sanda ta isa daura da motar tuni mamallakiyar motar ta kasheta tana yunqurin fitowa
"Anty dina sannu da zuwa" waiwayawa tayi sashen da widad din take tana niyyar dauko jakarta daga back seat na motar
"Widad rigimammiyar ummu,ya na ganki a gida kuma?" Murmushi tayi tana leqen cikin motar da alama akwai abinda take nema
"Anty secondry zamu tafi fa,muma mun zama manya kin manta?"
"Au anyi haka fa,kice zamu sake samun qarin 'yammata cikin gidan namu....."
"Anty wai ina aysar ne?" Ta tambayeta cikin katsar numfashinta
"Gashi nan a daure" ta fada tana nuna mata shi a kujerar dake kusa da tata cikin baby car seat,zagayawa tayi da hanzari
"Don Allah anty kwantomin shi"
"A'ah widad......ke kanki yaushe ummu ta daina goyaki?, barshi yanzu zan fito na kunceshi" bata rai tayi,wai me yasa kullum suke maidata baya,bayan ita kanta tasan girma take?,to idan ma har yanzu yarinyace ita a wajensu me yasa suke mata zancan uncle mahfood?,dole daga bisani anty dina ta ciro yaron ta miqawa widad shi,sannan suka nufi sassan mahaifiyarta tana ankare da widad din.
"Ke kuma wanne tsautsayin ne ya sanyaki daukar yaronki ki bawa wannan yarinyar?" Cewa momma mahaifiyar anty dina bayan shigarsu babban falon sassan nasu.
Kafin anty dina tace komai widad din ta rigata magana
"Momma Allah na iya fa,gash.i nan ma ni na daukoshi tuyn daga parking space" ta fadatana turo baki,wanda ke sake nuni da zallar quruciyarta,abinda ya sake batawa momma rai,taja tsaki tana miqa hannu gami da yunqurin karbar yaron
"Miqomin shi nan,me kika iya?,yarinyar da ko pant dinta har yanzu batasan ta wanke ba" momma din ta fada tana jifanta da harara,zallar quruciya ya hana widad fahimtar kuma,bugu da qari kuma,akwai wata irin wankakkiyar zuciya da take da ita,ba kasafai ta fiya damuwa da abubuwan da suke faruwa cikin gidan ba,duk da ta soma girma,hankalinta ya fara fahimtar wasu abubuwan
"Allah na fara koya momma"
"Naji,jeki da Allah" ta fada tana sake harararta kamar idanunta zasu fado,sai dauke dubanta daga fuskar momma din tana nufar hanyar kitchen dinta.
Wata tsawa ta kwatsa mata,wadda sai data sanyata ta kusa tuntube da kujerar dake gefanta
"Ina kuma zaki?" Ta fada tana fidda idanu
"Wajen Aafiya zani"
"Kiyi mata me?" Ledar hannunta ta daga tana nuna mata
"Kayan kwalliya na kawo mata ta zaba"
"Uhnnnn,salon kije kisa ta bata aikin dana sakata,to zauna nan har sai ta fito,kada ki shiga ku hadu ayimin shirme" narkewa tayi tana duban momma din,da alama tanason ta roqeta ne ta barta ta shiga,tana kuma tsoron tsawarta,don ba abinda ta tsana sama da tsawa da kuma fada.
"Ki barta mana momma,idan yaso tana shiga saita fito kada ta zauna" dina ke fada qasa qasa,saboda tausayi da widad ta bata,waiwayowa momma tayi ta kalleta tana dan juya aysar a hannu kamar zata masa rawa
"Wannan yarinyar?,tsab zasu iya barnatar min da guri,kuma baka da damar yi maya fada balle duka,tunda tana da uwa a bakin murhu"
"Kiyi haquri momma,yanzu zata fito"
"Naji,amma indai ta shiga din duk barnar da tayimin ke zaki biya"
"Na yarda" sai.anty dina din ta daga kai ta dubeta
"Shiga kikai mata kizo na aikeki sassan anty madina"
"Tohm" ta amsa da zumudinta tana shigewa,deena ta bita da kallo,bata fiya yin fushi ba don mutum ya bata mata ko ya tsangwameta,bata sani ba ko tsabar quruciya ce?,ko sai nan gaba zata fahimta komai idan hankali ya gameta?.
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥
0022419171
Maryam sani
Access bank
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*🔥
*_A RUBUCE TAKE!!!_*
(k'addara ta)
Page 03
*MAAB LUXURY HOME*
*_idan kaji gangami akwai labari_*
*_SABUWAR DUNIYA CE_*
*ALFAHARIN UWAR GIDA*
*FARINCIKIN AMARYA*
*MAIDA TSOHON GIDA SABO*
*DUNIYAR QYALE QYALE*
*KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA*
*_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_*
*nasan zaku tambaya ina ne nan?*
*MAAB LUXURY HOME*
😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya*
*_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_*
*Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu*
*Kayan gado dana parlor*
*Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida*
*Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a*
_adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_
*Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram*
@maabluxuryhome
*Facebook*
@maabluxuryhome
*Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka*
08034631010
*Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝
____________________________
Koda ta shigan bata zauna ba kamar yadda anty deena tace tayi sauri,ta sameta tana yankawa momma albasa,sai zabga gumi taje gami da hawaye,duk da cewa kitchen din kitchen ne irin na zamani,da ya wadatu da iska da manyan windows,dukka a qoqarin momman na koya mata girki,kada ta tashi kamar widad,wadda bata cas bare as a gidan,abinda ya damu wasu cikin gidan,yake kuma basu haushi sosai,suna gajun gatan da ummu ke nunawa widad din yayi yawan da ya kamata ta rageshi ta sanwa wasu cikin jikokinta.
Budewa Aafiya kayan tayi tana cewa
"Zabi duk abinda kikeso a ciki" kanta ta leqa cikin ledar tana cewa
"Ummm,yar gatan ummu,inda nice nace mata ta siyon kayan nan qi zatayi,sai tace naje na tambayi yayuna maza"
"Yaaya mahfood ne nima ya kawomin" daga kai tayi ta kalli widad,dududu itama Aafiyan ba zata wuce sa'ar widad din ba,saidai ta danfi widad din girman jiki kadan
"To me yasa ba zakiyi amfani dasu ba?" Tura baki tayi tana tsuke fuska
"Banaso,ni bana son sa,banason ana min zancensa,ki dauka anty deena zata aikeni" ido ta fidda
"Yaushe tazo?"
"Yanzu" saita ajjiye wuqar tana zura hannu a ledar,ta zabi abinda takeso tana cewa
"Aiko na godde wlh,bari nayi sauri na gamawa momma aikinta na fito" tana dan lila ledar ta fice abinta ba tare data tsaya sauraronta ba,ta samu anty deena a falo,ta bata leda tace ta kaiwa anty madinan,ta amsa ta fice da dan guntun gudunta.
Ta dan samu yaran sassa sassan gidan da dan dama a sashen anty madinan,kasancewarta mai fara'a haba haba dasu da jan kowa a jiki,kowa nata ne,hakanan kowa yana jin dadin xama dasu,bayan sa'anninta masu kamar shekarunta data samu,harda yayyensu da ake dab da bikinsu,kuma suna tare da anty madinan,da alama akwai abinda take koya musu,sauran sa'annin nata suna daga gefe sun buda tasu chamber din.
Bayan ta miqa mata ledar sai ta kalleta
"To wannan dayar kuma fa?"
"Kayan kwalliya ne na kawowa su rafi'ah"
"A ina kika samu kayan kwalliya masu yawa haka?" Basma cikin 'yammatan dake shirin amarcewa ta fada tana dubanta bayan ta dago kanta daga danna wayar da takeyi,kanta tsaye ba kwana kwana ko damuwa tace
"Yaa mahfood ne ya kawomin"
"Shine kuma zaki rabar?" Anty madina ta tambayeta tana bada hankalinta sosai a kanta,kamar zata saki kuka tace
"Banaso anty wallahi,ni banaso"
"Barta don Allah ta rabar,miqomin na zabi nawa" basman ta sake fadi tana miqa hannu,ba wani damuwa tattare da ita ta miqa mata ledar ta qara gaba tana cewa
"Anty basma idan kun gama su na'ima zasu zaba" anty madina data bita da kallo tana kallon zallar quruciya ta saki ajiyar zuciya
"Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi,baaba mahfood dai kam to"
"Uhmmm,wai laifin widad kuke gani?,ni nafi ganin laifin baaba mahfood din ai,kamar maye,yarinya tun tana 'yar tamilo kake faman mata hidima,jikinka da aljihunka basu huta ba,ta fara wayo ta nuna baka so basai ka haqura ba,dui gidan ita dayace 'ya?,ko ita kadai ce jika?" Kai anty madina ta girgiza
"A'ah fa basma,har yanzu widad akwai quruciya tattare da ita,ai ba'asan maci tuwo ba sai miya ta qare"
"Uhmmm,anty madina,yarinyar nan fa daurin gindi ta samu,Allah kuwa,kuma sai yaushe?,bayan mu kadai ne muka haura zuwa SS,mu dinma gashi SS one kawai aure ya tashi,bare su da jikinsu da alama mai saurin girma ne,Allah yasa su gama JS ma"
"Allah ya shiga lamarin" anty madina ta amsa mata
"To Ameen"basman ta fada tana maida kanta ciki ledar,don tuni marwa ummee da nujood suka gama zabar nasu,anty madina nata musu tsiyan girma ya fadi,raqumi ya shanye ruwan 'yan tsaki,su da za'a kawo musu akwati me zasuyi da toshin qanwarsu.
Widad kam bata sake bi takan kayan ba,a nan suka gama gantalewa,duka ta rabar,dan abinda yayi saura ya gangarar dashi anan wajen anty madina,tayi komawarta sassansu.
Sanda ta koma tuni abbanta ya tafi,sai ummu kawai
"Ina kikakai kayan?" Ta tambayeta tana tallafe da kuncinta tana dubanta,maimakon ta amsa saita narke fuska,ta kuma shige cikin kujera abinta ta lafe taba mus mus da baki,juyin duniya ta gaya mata inda takai kayan taqi,dole ga qyaleta,tasan indai cikin gidanne zata ji.
Tun tana zaman likimo har bacci yayi awon gaba da ita,bata tashi ba sai kusan azahar,sanda latifa ta kammala abincin rana,ta kuma tattaro panties da undies din widad din zata wanke.
Sai datayi sallar azahar kamar yadda ummu ta horar da ita,ta karba abinci,saita zagaya baya inda latifan ke mata wankin,ta zauna tana ci suna hira da latifan...
***********
Kamar kowacce safiya a ranakun makaranta,school bus din gidan ke tattara kan duka yaran gidan zuwa makaranta,wanda kusan yawancinsu makaranta daya suke zuwa,wadanda kuma suke mabanbantan makarantu sai ta miqa su sannan ta dawo gidan zuwa lokuttan tashinsu.
Daga can sassan ummu widad ce zaune saman kujera,sanye da sabbin uniform dinta kamar yadda komai nata a ranar yake sabo a matsayinta na dalibar da ta shiga secondry school a ranar,ummu na zaune daga qasan carfet hannunta riqe da plate tana miqawa widad din plantain din ciki
"Maza maza kici kafin 'yan azalzalar nan su biyo sawunki,idan ba haka nayi miki ba haka zaki tafi,yanzun latifa zata kawo miki lunch box dinki" fuska a nake a kuma sakalce take duban ummu
"Wallahi na qoshi ummu,ya isa haka"
"A'ah,qarashe wannan dai" ta fada cikin nuna kulawa,hakanan ba don taso ba ta daga cup din hannunta dake cike da tea tana shanye ragowar na ciki,dai dai lokacin basma ta shigo,sanye take da kayan gida,kasancewar ita din a yanzun sai daina zuwa,saboda kusantowar bikinsu,bawai don sun gama bane,haka al'adar gidan take,alhajin salim mai fata tsoho mai ran qarfe,kaka kuma uba ga ahalin gidan wannan sbine tsarin da ya dora dukka yara da jikokinsa,mutane da yawa 'yan bani na iya da kuma 'yan gaza gani kance
'Gidan me fata ai da wuri suke aurar da yaransu,da sun ga mai kudi sai su cire yarinya daga makaranta,basa ko gamawa,don sunga suna samun masu danshi ne,suma masu kudin da shegen kwadayi,suna ganin kyawawan mata sai su rude' duk da wannan jita jita na dawo musu kunne amma sunyi banza da zantukan mutane,abu daya tsoho kuma dattijon ya sani shine,mutuncin mace dakin mijinta,hakanan duk wadda tayi katari da samun mijin dake da ra'ayin karatu tana ci gaba da karatunta ne cikin dakin mijinta.
"Goyon kaaka,sai a fito ko?,kin tsaida mutane kina bata musu lokaci" ta fadi tana harararta,ganin yadda ummu ta zauna dafa'an tana bata abinci kamar wata yarinyar goye,waiwayowa ummun tayi tana danqara mata harara
"Ke kuma da bake za'ayi tafiyar wa ya sakoki a maganar?"
"Yo fisabilillahi ummu saita makarar da kanta fa makarar da wasu?" Tayi maganar tana miqa hannu gami da fusgar sabuwar school bag din widad din dake ajjiye kusa da ita,kafin su sake cewa komai.muryar dattijon ta ratso falon
"To....to,ya akayi?" Ya fada yana qarasowa a hankali zuwa cikin falon,kafin ya samu waje ya zauna yana dubansu.
Russunawa basma tayi ta gaidashi,dai dai lokacin latifa ta qaraso dauke da lunch box din widad din
"Gashi an gama" ta fadi tana ajewa gabanta
"Ko muje motar na rakaki dashi" latifan ta sake fada tana kuma dauke lunch box din daga gabanta,tabe baki basma tayi sannan tace
"Tabdi!,gigin primary,kina shiga dashi ansan burbushin primary ce,meye hadinki da wani lunch box tsabar sangarta?,Allah latifa ke kike sake taya ummu ana sakalta yarinyar nan" ta qarashe maganar tana hararar widad din
"Wato kedai anyi babbar banza ko?" Alhj salim ya fada yana duban basma
"Allah alhaji bata sanin ta fara girma"
"Wuce ku tafi ga iliya can yana horn" ya fada yana daga musu hannu,sai a sannan widad ta sauko daga kan kujerar,ta maida takalmanta suka fice ummu tana muta addu'ar dawowa lafiya.
Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta tabbatar da fitarsu,ta maida dubanta ga alhj salim din
"Yaran nan sam basu da zurfin hankali,ta yaya zan banzatar da widad ta gaza samun kulawata?,yarinyar da tun tana watanni a duniya mahaifiyarta ta tafi ta barta?,idan ban kula da ita ba waye zai kula da ita?" Murmushi dattijon yayi yana qarashe janye ragowar carbin da ya rage a hannunsa sannan ya ajjiyeshi gefe
"Iya tasu fahimtar kenan,amma duk da haka saboda gudun ci gaba da samun sabani da yadda suke jin haushinta ganin kamar kinfi sonta,kiyi qoqarin boyewa da rage wasu abubuwan"
Dan sunkui da kanta ummu tayi
"In sha Allah" ta amsa masa cike da ladabi,duk da bata da tabbacin yiwuwar hakan.
"Kunun za'a kawo maka ko dumame?"
"A fara kawomin kunun da qosai tukunna" ya amsa mata yana gyara zamanshi sosai saman kujerar,ta yunqura ta miqe zuwa kitchen da kanta,duk da tsufanta hakan bai hanata yi masa tasa hidimar da kanta ba,koda zata bawa latifa tata hidimar tayi mata,amma ta alhajin ita keyi.
Awannin da tayi a makaranta a ranarta gane banbamcin secondry school da primary,sosai makarantar tayi mata dadi,lokacin tashinsu da yayi tun a cikin motar suke hayaniya,labarin sabon aji da kuma sabuwar makaranta
"Don Allah kuyi mana shuru,kun cika mana kunne ha'an" ramziyya wadda take cousin a wajen widad ta fada,ita din gaba take dasu,don a qalla ta basu shekara kusan biyu,ita dinma wannan shekarar ta shiga js three,kuma akwai yiwuwar shekara mai zuwa a karba kudin aurenta kamar 'yan uwanta,dole suka rage hayaniyar,saita maida hankalinta ga iliya driver
"Ko ka wuce damu gidan baaba mahmud?,muga lefen najwa tunda yau babu islamiyya"
"To shikenan,babu laifi" ya amsa mata.
Kicin kicin widad tayi,ko kusa ko alama bata qaunar zuwan gidan nasu,koda hutun makaranta akayi kuwa,gidan ba gurin zuwanta bane,zata iya cewa banda mahaifinta bata da kowa a cikinsa,sai yayanta wanda.ba kasafai kake samunsa cikin gidan ba,yawancin lokutta yana makaranta,duk da yadda mahaifinta ke nacin ta dinga zuwa din amma ummu ta hana,idan ta kama saidai ta wuni ta dawo.
Tun daga harabar gidan matan gidan suka fara jiyi hayaniyarsu,babu wadda ta motsa,don kowacce dan data haifa kadai shine nata,har suka qaraso cikin ainihin babban falon gidan
"A'ah,kada dai kucemin daga makaranta kuke?" Ta tambayesu tana tafa hannuwa cike da yaqe da kuma riya,saboda mai gidan na nan,daga inda yake din kuma zai iya jiyo komai
"Ga alama kuwa umma" najwa dake fitowa daga dakinsu ta fada tana dariya gami da qoqarin daura dankwalinta
"Lefe mukazo gani" widad ta fada tana dan dariya,ganin yau yau umman ta sake mata fuska,ramziyya ta harareta
"Shegen son kallon kayan lefe,caraf ta bada amsa"
"Da gaskiyarta,gaba su za'a kawowa ai" umman ta amsa bayan ta qwalawa me aikinta kira kan ta zubo abinci, murmushi widad tayi maganar tana bata mamaki da dariya,yanzun wataran itama sai a ciko akwatuna da kayan lefe ace nata ne?.
A nan suka ci abincin rana suka kuma baje suka kalli kaya son ransu,alhaji mahmud ya fito a shiryensa,suka hau gaisheshi ya amsa musu cikin fara'a da jin dadin ganin 'ya'yan 'yan uwansa,ya bisu da kyautar dari bibbiyu sababbi,duka harda widad din bai banbantata da kowa ba a cikinsu,sannan ya fice yabar gidan.
"Ni kunzo a dai dai ma,ku taimakamin na fidda kayan da zan kai dinki" ramziyya ce ta dinga tayata zabin,widad na hade mata su waje daya
"Basuyi yawa ba wadan nan kayan anty najwa?, duka zaki kai dinkin?" Inji widad dake zaune daga gefe
"Saina ma qara wasu,kin manta haka amare keyin dinki da yawa?" Kai ta jinjina kawai tana ci gaba da kallonsu,bayan sun gama najwa tace
"Ki kwana anan widad,saiki rakani nakai dinkin,gobe saina maidaki gida".
Cikin murna da zumudi ta amsa da to,ko ba komai zata yita kallon kayan lefen dake burgeta sin ranta,don haka ta baiwa su Aafiya jakarta suka wuce mata gida da ita.
Sanda ummu taji shigowarsu sai tayita sanya idanu taji shigowar widad din amma shuru,har ta gaza daurewa ta aika latifa sassan su marwa ko sassan anty madina ta dubo mata widad din me ta tsaya yi bata shigo taci abinci ta sake wanka ta canza kaya ba.
Da latifa ta dawo mata da batun sun barta gidan baaba mahmud shuru tayi,cikin ranta duka babu dadi,don bataso ko kadan widad din tayi nisa da ita,to amma tasan mawuyacine itama ta yarda ta kwana din,ta tabbatar da wahala bata nema a kawota gida ba.
Sanin hali yafi sanin kama inji hausawa,don kuwa tun bayan sallar magariba bayan sun dawo daga wajen dinkin ta lafe a kujerar falon gidan tana raba idanu,ta cika tayi fam,gida kawai takeson komawa,har umma ta fahimci haka,itama hakan ya mata dadi,don duk randa yarinyar ta kwana a gidan ko yaya ne sai sunga wani abu na bacin rai daga mai gidan dangane da yadda yake nuna mata kulawa
"Rabu da ita umma,kin ganta fa ta fara girma,Allah har qirga dangi naga ta fara,amma.har yanxu bata girma da kwana a bayan ummu ba,yau dai a gidan nan zaki kwana,idan bikin nawa yazo ma ba zaki iya kwana ba kenan?" Itadai batace komai ba har zuwa sanda baaba mahmud ya dawo,tare suka zauna da ita suna cin abinci amma sam taqi sakewa,qarfe takwas na dare ta fara musu hawaye,dole ya tashi driver ya maidata gida
"Maidata,kada ta hanamu barcin dare" cewar abban nata.
Karfe tara saura suka isa gidan,sanda motarsu ta tsaya daidai sanda motar uncle haisam abban su marwa qani ga mahaifinta ta tsaya
"Aah,wa nake gani haka da daren nan kamar widad?" A ladabce drivern ya amsa shi
"Itace,taqi zama ne abba yace a dawo da ita"
"Ikon Allah,to muje ciki" ya fada yana kulle motarsa,sukayi sallama da drivern yabi widad din zuwa sassan iyayensa.
Ummun da kuma alhaji suna falo a zaune,sai a sannan yake cin abincin dare sunadan taba fira sama sama da ummun.
Bataji sallamar widad ba sai fadowarta jikinta data ji,tana shirin dagata sallamar uncle hisham ta biyo baya
"Tare kuke ne?" Ummu ta jefa masa tambayar,yana rage tsahonsa gami da neman wajen zama yace
"A'ah,can na ganta drivern gidan yaaya mahmud ya sauketa"
"Yar nema,shine kike biyo dare kika gudo?,ba zaki qyalemin mata dai ta huta ba kenan?"cewar alhaji yana tsokanarta,daga ummu tayi tana turo baki
"Bakaji dadin gani na ba?,bayan ko cigiyata ma bakayi ba..... shikenan" tayi maganar tana miqewa daga jikin ummu tana wucewa daki
"Ahaf......me kika sani banda takura?". Bata ansa ba har ta isa daki ta tura ta shige abunta,dariya suka saka gaba daya, alhaji ya girgiza kai
"Quruciya me dadi" ya fada a hankali,sai ya maida dubansa ga hisham yana tattara hankalinsa zuwa gareshi.
*_RIGIJI GABJI!_*🔥🔥
*_WANI KAYA SAI AMALE_*🔥🔥🔥
*FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*🔥🔥
*JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA*
*_'YAN BIYAR DIN NAN NE FA_*
*_SARAKAN LABARUN_*
*NISHADI*
*CAKWAKIYA*
*GWAGWARMAYA*
*BARKWANCI*
*TSANTSAR DARASIN RAYUWA*
*TARE DA*
*ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*
*SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*
*KIN SHIRYA MADAM?*
*MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*
*DAUD'AR GORA* Billynabdul
*KI KULANI* Missxoxo
*IDON NERA* Mamuhghee
*RUMBUN K'AYA* hafsat rano
*A RUBUCE TAKE* Huguma
*ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number
09033181070
*MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*
09166221261
*Yan nijer kuwa zasu tuntubi wannan number*
+227 90 16 59 91
*Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾
*HUGUMA*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addara ta)
Page 04
----------------------------------------------------
*MAAB LUXURY HOME*
*_idan kaji gangami akwai labari_*
*_SABUWAR DUNIYA CE_*
*ALFAHARIN UWAR GIDA*
*FARINCIKIN AMARYA*
*MAIDA TSOHON GIDA SABO*
*DUNIYAR QYALE QYALE*
*KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA*
*_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_*
*nasan zaku tambaya ina ne nan?*
*MAAB LUXURY HOME*
😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya*
*_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_*
*Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu*
*Kayan gado dana parlor*
*Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida*
*Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a*
_adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_
*Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram*
@maabluxuryhome
*Facebook*
@maabluxuryhome
*Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka*
08034631010
*Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝
____________________________
*Widad*
Alhaji salim musayyib mai fata shine cikakken sunan,mazaunin maiduguri da wanda aka haifa a can,ya taso ya girma ya kuma yi gwagwarmayar karatunsa dukka acan din,nau'in jinsin nan da mutane ke kira da suna SHUWA_ARAB,saboda asalin iyayensu da kuma kakanninsu dukka ba'a maiduguri aka haifesu ba,ba kuma anan sukayi rayuwarsu ba,rayuwar da sukayi a maidugurin duka duka 'yar taqaitacciya ce,sanadin kasuwanci,asalin tushensu sun fito ne daga qasar mali zuwa yemen,kuma har yanzu danginsa da tushensa suna can gaba daya ko nace mafi yawa daga cikinsu,iyali ga mahaifinsa musayyib suke ta yado a nan,da kuma nashi ahalin shima daya tara.
Matan aurensa biyu dukka 'yan asalin qasarsa wadanda suka hada masa tarin zuri'a da kuma yara masu yawa,dansa na farko da matarsa ta fari wadda ta kasance balarabiyar qasar yemen shine mahmud,wanda yake mahaifi ne ga widad data kasance ruwa biyu,balarabiyar mali kuma bafulatanar usul daga katsina ta gefen mahaifiya,wannan shi ya taru ya bata wani irin sassanyan kyau daya banbanta da kyawun dukka cousin dinta da kuma sauran 'yan uwanta,domin ita daya mahaifiyarta ta haifa ta barta a gidan,sai tarin 'yan uba da kuma cousins da take dasu.
Yanayi na rayuwa da kuma kasuwanci ya maido alhaji salim qasar kano da zama,ya fara tara iyalinsa shima,bayan ya aurar da mahmud arziqinsa ya qara ninkuwa fiye dana da,wanann ya siya manya manyan filaye ya hadesu waje guda,ya kuma yanki wani sashe na gidan ya fara ginin matsugunnin da zai zauna da matansa da kuma yaransa,bayan ya kammala suna gab da tarewa matarsa ta biyu ta rasu,sai mahaifiyar mahmud ce kawai Allah ya qaddara mata zama a gidan.
Mahmud ne kawai ke rayuwa a wajen gidan,girman gidan ya sanya duk yaronsa daya tashi yin aure,za'a fitar masa da tsarin ginin da zai dace da gidan a gina masa ya tare a ciki,wannan yasa sannu a hankali gidan ya zama babban family house dake dauke da sassa sassa guda biyar,kuma kowanne sashe cike yake da albarkar zuri'a wadata da kuma kwanciyar hankali.
Widad ta kasance ta musamman a wajen ummu,saboda ummun ta bude idanu ta gani a matsayin uwa kuma mahaifiya a wajenta,don itace ta raineta tun tana tsumman goyonta har kawo yanzu da shekarunta suke goma sha daya da watanni a duniya.
Soyayyar da ummun itama kewa widad din ta banbamta data kowa,saboda itama tana jinta da matsayi biyu ne a wajenta,d'iya kuma jika,ta manta da raino sanda ta amshi widad da nufin rainonta,don a sannan ta aurar da autarta ma anty halima tuni,kasancewar su din basa zurfafawa karatun boko,kina gama primary ma kika samu miji to tabbas alhaji salim zai bada aurenki ne, matuqar ya yarda da addinin mutum da kuma mutuncinsa,ruwan miji ya barki kici gaba,ruwansa yace a'ah.
Ko kadan rashin uwa bai wani taba widad ba,saboda ta samu dukka kulawa da 'ya ke samu ga mahaifiyarta daga wajen ummu.
Mahfood d'a ne ga baaba maisara,wanda suke 'ya'yan wa da 'ya'yan qani da mahaifin widad,tun kafin ta kawo haka yake nuna yana da interest a kanta,amma ko daya widad din taqi sake masa balle ya samu fuskar da ko hira ta zauna tayi dashi,saboda ita din wata irin mutum ce,tana da wahalar sabo,hakanan idan kanason ganin kazar kazar dinta da hirarta to cikin gidansu ne,musamman sassan ummu ko na anty madina,indai akace maka baqon guri ne zaka tsammaci cikakkiyar magana ma bata iya ta ba.
Abu na biyu tana da masifar tsoron maza,saboda kullum hudubar ummu shine,idan ta sake ta yarda ko hannunta namiji ya kama zatayi ciki,idan kuma ta samu ciki mutuwa zatayi,wannan yasa sam sam bata yarda ko inuwa su hada,bama shi ba,dukka samarin gidan da suke a matsayin yayye a wajenta haka dabi'ar ta take.
_wannan kenan_
*Bayan shekara uku*
Tun daga daren juma'ar da ya kama gobe sallah gaba daya yanayin gari ya canza daga yanayin azumi zuwa yanayin daren sallah,ko ta ina al'ummar musulmi sai hada hada ake,tituna zuwa layuka,gidajen kitso qunshi zuwa shagunan masu dinki ko ina cike yake danqam da jama'a kamar rana.
Haka ce ta kasance gidan alhaji salim musayyib,babban gidan dake dauke da family masu yawa,a dabi'ar gidan babu tsawwalawa,koda salla ce kowanne sashe yana yin kalar girkin da mace ko matan sashen suka tsara yi,saboda kowanne part akwai store da kuma kitchen din su tare da me aikinsu,saidai idan an gama ranar sallah dukka suna zubawa abincin mai dan dama su aike sashen surukarsu hajiya ummu,duk da ita dinma ba zama take ba, takanyi abinci har kusan kala biyu,sabida karbar baquncin jikokinta dama surukanta matan 'ya'yanta maza guda biyar da Allah ya bata,su da 'ya'yansu da kuma 'ya'yan wajen diyarta halimatu,hakanan su kansu jikokin dake cikin gidan suma kusan a nan suke zuwa su karba nata,sukance yafi dadi.
Dai dai lokacin da sassan anty madina yake a cike da yara yaran matan gidan,wanda ake ta faman saka musu qunshin salla daga mai qunshin da ummu da kanta ke daukowa ayi musu,sannan kuma ga me kitso itama tanata kitse musu kansu duk da baiwar suma da yalwar gashi da suke dashi tubarkalla,babban falon da anty madinan ta ware musu saboda irin wannan hidimar a kacame yake.
Daga gefe daya widad ce zaune,tsahon shekaru ukun data qara kyawunta ya sake bayyana muraran,hakanan alamun girma sun fara bayyanar mata,duk da cewa har yanzu gabunta sakarci da kuma wautarta tana nan,cikakkiyar GOYON KAKA,Qunshinta yafi na kowa jan lokaci,saboda ummun tace na musamman za'ayi mata kamar yadda aka saba,masu zumbura baki nayi masu qorafi nayi,to amma kusan idan da sabo an riga an saba,haka sukayi suka gama suka kuma haqura.
"Aafiya ciremin lallen nan" widad ta fada tana yamutsa fuska saboda jimawar da tayi a zaune
"ke kam kin huta,sauranki kitso" afiya ta fada tana matsowa hadi da fara sabule ledar da aka rufa hannun,harara widad ta jefa mata
"Tabdijan,wa za'ayi wa kitson?,Allah ya kiyaye" ta fada tana bata fuska,kitso babban abokin gabarta ne,sam bata qaunarsa,tun daga quruciyarta kawo yau tsaf zata iya irga adadin sau nawa aka taba yi mata kitso,mutane kance saboda tana da suma me kyau ne da tsaho,kusan sumarta ta zarta dukka ta yaran gidan,tamkar zabarta akayi,hakan kuma baya rasa nasaba da gado da tayi ta wajen uwa da uba,don idan ta ware sumarta tana iya saukar mata har tsakiyar gadon bayanta.
Dariya afiya ta saki tana ci gaba da tsokanarta
"Nikam naga lokacin da zaki daina gudun kitso"
"Babu rana"ta amsa mata tana Allah Allah a gama cire mata ta tsallake ta gudu ma daga falon.
"Tubarkalla ma sha Allah 'yammatan ummu,lallai dole mu caji 'yan samari kudi,irin wannan kyau haka?" Anty madina dake shigowa dauke da babban farantin data yanka musu fruit ta fada tana murmushi,cikin yanayi na nuna jin kunya abinda ke nuni da soma girman widad dim ta boye fuskarta tana dariya
"Bafa wasu samari anty Allah"
"Aah fada kike wallahi,kowa fa ya sani" wuf tayi ta tashi saboda yadda sauran 'yan uwanta ke juyowa suna kallonta,wasunsu suna mata dariya ne da gaske har zuciyarsu,yayin da wasunsu kallon hassada qyashi da baqinciki ne suke.jifanta dashi,abu guda daya da bai taba dadata da qasa ba,itakam indai zata jita wajen ummunta to komai lafiya lau,takan manta da dukka wasu qananun abubuwa dake tasowa ko kuma faruwa cikin gidan.
"Ina zaki sauranki kitso ai" anty madina ta fada,sai ta tsaya tana duban anty madina,fuskarta dauke da zallar quruciya ta narke fuska,abinda ke nuna gab take da fara tara hawaye
"Don Allah anty a barshi,nayi bayan sallah" haba ta kama tana kallonta
"Anya widad?,ke wannan sumar bata damunki ne?" Dariyar yadda anty madinan ta saki baki ya kamata
"Ai shikenan,ki biya ta kitchen,ki cewa yalwa ta baki abincin ki kaiwa ma'aruf" sunan da anty madinan ta ambata sai taji kamar tace mata ba zata aiken ba,amma anty madina tafi gaban haka a wajensu,dukkaninsu suna mata kallon babbar yaya, kasancewar dukka manyan yayyansu mata suna gidajen aurensu,a kaf surukan gidan kuma ita dince mai qananun shekarun da suke iya sakewa suke komai tare da ita,itama kuma ta riqesu tamkar qannen nata.
Ba'a son ranta ba ta biya kitchen din ta dauki abincin,ta fito tana dariyar yadda yalwa keta koda kyan qunshin nata,tsakaninta da dukka ma'aikatan gidan qauna ce da soyayya,koda kuwa ba masu aikin sassan nasu ba,idan ka ture wautarta da quruciya da tabara ta goyon kaka,ita din yarinya ce mai matuqar girmama wanda ya girmeta,zaiyi wuya ka sameta da laifin rashin kunya,kai koda laifi akayi cikin gidan da wahala ka samu sunanta a ciki,idan kaji an ambaci sunanta to wata wautar aka tafka,ko kuma ta taba sakalcin nata data saba,wannan ya sanya ummu bata ragawa duk wanda ya tabata,takan ce
"Nasa halin kayata fes,duk wanda yace tayi wani abu idan ma sharri ne zan gane ato,nasan me zata aikata,hakanan kuma nasan abinda ba zata aikata ba".
Har ta isa qofar dakunansu taji hayaniyar mutane a dakin nasa,da alama baqi yayi abokansa,tsaki taja,ta koma da baya cikin takun da basu fi goma ba,ta tsaya dab da motarsa.
Sai data qarewa motar kallo sannan ta matsa kusa da boot din motar ta dora masa abincin a nan,ta kama gabanta hankali kwance ta wuce sassan ummu.
Saidai tana sallama a sassan taji nadamar dawowa sassan ta kamata,babu wanda ya gaya mata yazo gidan,da babu abinda zai sanyata dawowa yanzu,sun riga da sun ganta gaba dayansu,harda na'eema diyar anty halimatu da tazo gidan sallah,saboda haka duk wata dama ta komawa ta qwace mata babu ita,sai taci gaba da takawa cikin falon tana tsuke fuska,hadi da sake gayyato bacin rai saman fuskarta,uwa uba dama ga yunwa dake cin hanjinta,taqi abincin wajen anty madina saboda ba cimarta ta dafa ba,tace sai ta dawo wajen ummunta.
*_RIGIJI GABJI!_*🔥🔥
*_WANI KAYA SAI AMALE_*🔥🔥🔥
*FITATTUN ZAFAFAN DA BABU NA BIYUNSU*🔥🔥
*JERIN GWANON LITATTAFAI ABOKAN TAFIYAR JUNA MASU MABANBANTAN LABARAI DA FASAHA*
*_'YAN BIYAR DIN NAN NE FA_*
*_SARAKAN LABARUN_*
*NISHADI*
*CAKWAKIYA*
*GWAGWARMAYA*
*BARKWANCI*
*TSANTSAR DARASIN RAYUWA*
*TARE DA*
*ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*
*SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*
*KIN SHIRYA MADAM?*
*MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*
*DAUD'AR GORA* Billynabdul
*KI KULANI* Missxoxo
*IDON NERA* Mamuhghee
*RUMBUN K'AYA* hafsat rano
*A RUBUCE TAKE* Huguma
*ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*
0022419171
Maryam
Access bank
Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number
09033181070
*MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*
09166221261
*Yan nijer 🇳🇪🇳🇪kuma zasu tuntubi wannan number*
+227 90 16 59 91
*Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 05
*MAAB LUXURY HOME*
*_idan kaji gangami akwai labari_*
*_SABUWAR DUNIYA CE_*
*ALFAHARIN UWAR GIDA*
*FARINCIKIN AMARYA*
*MAIDA TSOHON GIDA SABO*
*DUNIYAR QYALE QYALE*
*KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA*
*_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_*
*nasan zaku tambaya ina ne nan?*
*MAAB LUXURY HOME*
😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya*
*_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_*
*Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu*
*Kayan gado dana parlor*
*Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida*
*Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a*
_adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_
*Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram*
@maabluxuryhome
*Facebook*
@maabluxuryhome
*Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka*
08034631010
*Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝
____________________________
Idanu ya zuba mata yana kallonta,kullum sake canza masa takeyi,tana dada girma tana kuma sauyawa,yana kuma sake jinta a ransa,a haka ta qaraso wajen,amma ko sau daya taqi kallon sashen da yake zaune ma.
"Ina yini?" Ta gaidashi tana rusunawa kadan,saidai bashi take fuskanta ba,wani sashe na daban take fuskanta
"Lafiya lau widad,ya shirye shiryen sallah?"
"Lafiya" ta amsa masa a cunkushe tana duban ummu
"Ummu yunwa nakeji,me aka dafa?" Abinda ta tsana ummun ta fara yi wato miqewa,da alama zata basu waje kenan,gamin haka sai tayi wuf ta riga ummun miqewa,daga kai tayi ta kalleta
"Ki zauna, na'eema zata kawo miki abincin yanzu" yadda ummu tayi maganar babu wasa saman fuskarta ya sanya ta koma jiki a mace ta zauna tana tara hawaye a idanunta,tana kallonsu suka fice daga falon.
Ajiyar zuciya ummun ta sauke bayan barinta wajen,wanan wanne irin abune haka?,me yake faruwa ne?,har yanzu komai yaqi ya canza tsakaninta da mahfood din?'.
Cikinsu shi da ita ba wanda ya iya cewa komai,har na'eema ta kawo abincin ta ajjiye ta juya ta fice,a hankali yasa hannu ya jawo abincin gabansa sannan yace
"Kamar yunwa naji kince kina ji ko?,matso kici abincin kada ya huce" ko kallonsa batayi ba bare yasa ran zata cin,yayita fama amma qememe tayi biris,dole yaja ledar da yazo da ita zuwa gabansa
"Ga kayan sallah nan,da fatan za'ayi kwalliya me kyau" sosai ya sake quleta,don tana da son kwalliya da gayu sai ya maidata wata qwalamammiya?,bashi da aiki sai kawo mata kayayyaki,yadda taji haushinsa sosai a yau din har taji tana qwarin gwiwar gaya masa abinda bata taba gaya masan ba,daga fararen manyan idanuwanta tayi ta azasu a kansa
"Nifa bana so,banason komai naka,sannan ma ni ba wani auren dangi da zanyi,ni ba yanzu ma zanyi aure ba,don Allah ka rabu dani,ni.....bana sonka" dai dai lokacin da alhaji mahmud salim mahaifinta yayi sallama cikin falon ya kuma sanyo qafafuwansa.
Idanu yake bin widad din dashi,yaji kalamanta guda biyu na qarshe,zallar bacin rai ne kwance akan fuskarsa,ita kanta suna hada ido da abban nata ta sadda kanta qasa gabanta yana tsananta faduwa,mahfood kuwa miqewa yayi yana masa sannu da zuwa
"Zauna mahfood......me naji kina fada widad?" Tsoro da firgici suka hanata yin koda qwaqwqwaran motsi bare ta amsa shi,cikin tsawa ya sake maimaita mata tambayar,saita ida rikicewa gaba daya,ta kuma saki kuka a lokaci guda,saboda sam sam bata saba da irin wannan tsawar ba.
"Dan uwanki kike gayawa bakiso saboda baki da kunya?,wato kin fara girma kenan widad?" Ya fada cikin mugun fada da kuma daga murya,sautin muryar tasa da ya isarwa da ummu saqon akwai abinda ke faruwa a falon,taji kuma ta kasa nutsuwa saboda kama sunan shalelenta da taji anyi,saita yunqura ta miqe tana duban na'eema
"Ki qarasa hada muku kayan waje guda ki maida daya dakin kafin gobe gidan ya sake cika,ina zuwa" ta fada tana takawa a hankali saboda dan ciwon qasa da take fama dashi lokaci lokaci.
Isowarta wajen kadai tafahimci abinda ya faru,fada sosai abban yake zuba mata,da alama ransa ya baci sosai
"Mahfood dan uwanki ne,da kike cewa kuma bakya sonshi gwara ki koya tun wuri,don baki da miji sai shi,shi zaki aura ki jini da kyau" ya fada yana kama kunnensa da hannunsa guda daya
"Tashi ki bani waje" ya fada a tsawace,ta gudu ta miqe tayi hanyar dakinsu fuskarta jiqe da hawaye,saman gadonta ta fada wanda ba kasafai ma take kwana a dakin ba,koda yaushe tana maqale da ummu,a dakinta take kwana,koda tana wajen alhajin to itakam tana dakin nata,haka zata hada duka filallukan dake saman gadon ta qudundune a ciki saboda shegen tsoron da take dashi,bare ma ba kasafai ummun ke barinta ba,wani lokaci ma bata sanin bata dakin idan baccinta yayi nisa ko kuma nauyi.
Kan mahfood a qasa sanda abba ke bashi haquri
"Nasan harda quruciya abba,har yanzu shekararta sha hudu"
"Da kuma sakarci ba"
"Ayi haquri" ya sake fada kansa a qasa,sannan ya miqe yayi musu sallama ya fice daga sassan ummun yace zai shiga cikin gidan su gaisa da sauran mutane.
"Ka dinga bin al'amarin nan a hankali mahmudu,wannan fadan duka ba shine ba" ummu ta fada bayan dukkaninsu sun zauna
"Ummu abunne yake dauren kai,anata cewa quruciya ce,to amma tana sake girma tana sake qinsa?" Kai ummun ta jinjina,ita kanta bataga na meye abba din sai ya matsa har haka ba,shi zumuncin da yakeson a qarfafa a kuma sake qullawar ai ba dole sai ta hanyar hada aure ba,inda akwai wata diyar gareshi wadda tadan tasa kamae widad din ma ita zaifi mata sauqi ya maida alqawarin kanta,bata qaunar wannan rikicin da aketa yi da widad din
"Kasan haduwar jini ne,idan kuma Allah bai sanyata tsakanin bayinsa ba babu yadda za'ayi"
"Haka ne,Allah yayi mana mafita"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" ummun ta amsa masa,sai ya miqa mata babbar jakar da yasa aka shigo da ita,wadda ke shaqe da kayan sallah na mutanen da ya saba yiwa duk shekara,wanda yaran gidanne 'ya'yan qannensa da suke sa'annin widad,wasu kuma qasanta a shekaru,ga kuma nata na musamman ita da widad din da alhaji
"Alhajin baya gida ne?"
"Kasan yau daren sallah,suna can fadar mai martaba,har sai an sanar da ganin wata sannan" kai ya jinjina,don kusan al'adar sa ce duk shekara
"To Allah ya dafa mana" ya amsawa ummun.
Kuka take sosai da hawayen daya fara jiqa pillow din da take kwnace akai,juyin duniya na'eema tayi ta tashi tayi haquri ta dauki abincinta taci amma ko kulata batayi ba,sosai take jin qin mahfood din cikin ranta,ko sau daya bata taba jin tana sonshi ko yana burgeta ba,yana da kirki ta sani,amma ita ba wani magana datayi kama data aure a tsakaninsu da take jin zata yiwu.
Har abbanta ya tafi tana kwance tana kuka,ummu na falon bata motsa ba,duk da na'eema ta gaya mata,bataso taje taga yanayin da take ciki zuciyarta ta karye ta gaza bata qwarin gwiwar yiwa mahaifinta biyayya,wannan yasa tayi zamanta a falo,duk da zuciyar da hankalinta na kanta.
Duk wanda ya shigo nemanta sai tace masa kawai tayi bacci,wasu su zauna suyi hirarrakinsu wasu kuma su wuce,tana nan zaune har qarfe goma na dare,zuwa sannan juriyarta ta qare,sai ta miqe ta shiga dakin da kanta.
Tana kwance rub da ciki har yanzu,saidai ba zaka iya tantance bacci take ko idanuwanta biyu ba,ta qarasa a hankali tasa hannu tana taba kanta gami da kiran sunanta,sheshsheqar data sauke hadi da ajiyar zuciya ya tabbatar mata idanuwanta biyu
"Meye haka wai widad?,tashi mana" ta fadi tana qoqarin dagota ta zaunar da ita,sanda ta kalli fuskarta sai zuciyar ummun tayi rauni,kallon marainiya takewa widad shine dadin abinda yasa batason komai ya sameta mara dadi,yarinyar da batasan dumin uwarta ba?,gaba daya fuskar tata ta tashi ta kuma yi jazur da ita abinka da farar fata
"Kukan kike har yanzu kamar wadda akace mata zata mutu?,tashi ki wanke fuskarki kici abincin naki"
"Ni banaci" ta fada muryarta na rawa hawaye yana sake barke mata,sai kawai ta fada jikin ummun tana sakin sabon kuka,har cikin ranta ummu takejin kukan,sai ta fara lallashinta,da qyar ta ciyo kanta taje ta wanke fuskar ta sanyata a gaba taci abincin,da qyar tayi cokali biyar tace ta qoshi,ummun taso sanyata a gaba su wuce dakinta ta kwana kamar yadda ta saba amma tace anan zata kwana,tunda ga na'eema,sannan Aafiya ma yau a nan zata kwana,dole ta rabu da ita tabar musu dakin bayan ta ja mata kunnen kada ta sake irin wannan kukan,ta kwantar da hankalinta kuma.
*_W A S H E G A R I_*
Kamar yadda suka saba kusan kowa da kowa ake tafiya sallar idi a gidan,akwai wadatar ababen hawa,kowa zai diba iya mutanen da motarsa zata iya dauka,tun sassafe kowanne sashe suke tashi yaran suyita shiri,iyayen kuma suna qoqarin qarasa abincin sallah wanda idan an dawo saga udi za'a dira akai a fara ci da kuma rabo,to hakanma wannan karon ta kasance,har sassan ummun hayaniya ce ke tashi,saidai banda widad dake nannade a bargo,ko motsawa batayi ba bare ta shirya,sunyi sunyi ta tashin amma taqi kula kowa,ummu kuma tunda ta fito da asuba ta tadasu sallah bata kuma fitowa ba,sai alhaji ya gama shirin idinsa.
Karo na biyu latifa fa dawo,wadda itama ta shirya fes da ita cikin dinkin sallarta,duk sallah sai an mata dinki kamar kowanne yaro ko jika dake gidan,dinkinta masu kyau da tsada har kala hudu ko uku
"Widad din ummu,kiyi haquri ki tashi ki shirya,kinga kowa ya gama shiryawa,yanzun nan zakiji an fara tafiya"ta fada cikin lallabawa,bakam tayi kamar bata a wajen,duk iya dabara da hila ta latifa haka tayi ta haqura,daga qarshe dai haka suka tattara suka tafi sallar suka barta.
Bayan ficewarsu ummu ta fito
"Ja'irai,tunda naji shuru nasan sun tafi,kafin su dawo su hana mutun sakat" tayi maganar tana tura qofar dakin,sai idanunta ya sauka kan tudun bargon dake kan gado,cikin ranta zuciyarta ta bata mutum ne,sai ta qarasa tana yaye bargon.
Salati ta saka ganin widad din kwance tana sharbar kuka
"Na shiga uku ni laila?,wai dama baki haqura ba widad?" Hankalin ummun ya tashi sosai,haka ta sanyata a gaba sai data tashi tayi wanka ta kuma zuba mata abincin safe taci,tana gama cin ta koma ta kwanta
"Falo zaki fito ki kwanta,bazan barki ki sake kwanciya ba"
"Ki qyaleni kawai ummu,tunda abba baya sona" ta fada da yanayi na quruciya tana kuma sake sakin kuka,baki ummun ta saki,tana magana kamar wata babba?,duk yadda taso ta fiddota amma taqi sai kwanciya.
Koda aka fara dawowa daga idi tuni gidan ya fara cika da jama'a kamar yadda aka saba duk shekara,jikoki sun fara hallara,kowa fuskarsa da zuciyarsa cike da walwala da kuma farinciki,lokacin sallah lokacine na farinciki,amma wannan shekarar banda widad din,don kuwa duk budurin da akeyi tana kwance a qule a daki,da yake tana da kirki qwarai da son yara qananu,kowa yazo sai yace ina widad,saidai ummun tace bata da lafiya tana daki tana bacci.
Duk yadda jikokinta ke karakaina a falon amma rashin walwala da fitowar widad din sai taji komai ma baya tafiya dai dai,maganar mahfood din taji itama ta soma fita mata a kai,gwara abar zancan,idan yaso a gwada bata wani,duk da abban nata ya gaya mata ita din bata son auren zumunci,to amma maiyuwuwa ta haqura idan aka gwada mata wani indai jininsu yazo daya,da wannan maganar a ranta tayita dakon shigowar alhaji don suyi maganar ita dashi.
Bai samu shigowa gidan ba sai yamma liqis,zuwa lokacin manyan yayyensu maza dake sa mota sun debi yaran gidan da yawa zuwa guraren wasannin sallah da shaqatawa,gidan sai yayi shuru,sai dai daikun yara dake shigowa su fita,har sannan widad din tana daki a kwance,duk da tulin kayan sallar da take dashi bata sanya ko guda daya ba bare ta fito.
Sai data gabatar masa da abinci yaci ya qoshi sannan ta fara magana dashi,yayi shuru yana sauraren ta har ta gama bayananta gaba daya,sannan yayi gyaran murya yana dubanta.......
*_TOFA,TAFIYAR BA'A FARA BA,KO SHIMFIDA BAMU GAMA BA_*
*_INA SAKE TUNA MUKU,IDAN KIN KARANTA HANGEN DALA,TO TABBAS SHAFAR MAI NE,WANNAN TAFIYAR TA FISHI ZAFI AMFANI DA KUMA DARUSSA_*
*_LABARI NE DAYA QUNSHI TSANTSAR KISHI,KAIDI MUGUNTA DA KUMA SIHIRI_*
*_MUGUN TAKU IRIN NA BAQAR KISHIYA_*
*ZALLAR RAYUWAR GIDAJENMU TA GASKE*
*MADARAR SOYAYYA MAI TSUMA ZUCIYA BURGEWA DA BARWA RAYUWA DARASI*
*GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*
0022419171
Maryam sani
ACCESS bank
*Saiku tura shaidar biya ta nan*
+234 903 318 1070
*Masu tura katin waya kuma zasu tuntubi wannan number*
09166221261
*Yan nijer zaku tuntubi wannan number*🇳🇪🇳🇪
+227 90 16 59 91
*Thanks for choosing us*
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 06
"Gaskiya ne,kema kinzo da naki hanzarin,sannan a zahiri cikin musulunci babu auren dole,duk da shi mahmudu yana ganin kamar gata ne zaiyi mata,kuma hakan shine dai dai,to amma kuma duk da haka tana da damar da za'a bata zabi,iyaka idan aka duba ya zamana akwai kuskure ko rashin dacewa a ciki sai a soke lamarin",tana tausayin widad,tasan akwai maqiya da magauta fal cikin rayuwarta,shi ya sanya take a tsaye ga duk wani abu da zaya cutata mata.
Bangaren widad kuwa haka ta yini ta kwana,ummu nata dakon zuwan mahaifinta suyi magana da alhajin,bai shigo gidan ba sai a washegarin da azahar,akayi sa'a alhajin shima yana nan amma yana shirin fita.
Shuru abban yayi sanda alhaji ke masa maganar gami da bashi umarnin janye wancan qudurin nasa
"Alhaji,naso ace an hada abun nan saboda a qarfafa zumunci,sannan yanzun bansan da wanne ido zan kalli isma'il ba(mahaifin mahfood)" murmusawa alhaji yayi
"Akwai dangi da yawa,ba lallai sai mahfood ba tunda jininsu baizo daya ba,kada azo ayi abinda za'a zo daga baya ana dana sanin aikata shi,isma'ila kuwa shi da mahfood din kabar komai a hannuna zan magana dasu" kansa a qasa amma ransa a matuqar bace ya amsawa da alhaji,gami da yi masa godiya da fatan samun qarin shekaru masu albarka da lafiya me dorewa.
Ummu da kanta ta shiga dakin inda widad keta fama kwanciya don yi mata albishir,a kwancen ta sameta,ta janye rufarta tana cewa
"Tashi......ruwa sarkin kwanciya" sake curewa tayi waje daya tana turo baki gaba,don har ta gaji ma da kukan
"Nace ki tashi hakanan, kwanciyar ta isa,maganar aure ce an janyeta an fasa" da sauri ta waiwayo tana kallon ummun gami da jin fitar maganar daga bakinta kamar almara,ko kuma tayi hakanne don ta tashi ta sake?,babanta fa?,wanda baya fadin abu ya canja,wanda baya magana ya sabata,tsayayyen akan duk abinda ya sakawa ransa zai aikatashi,to amma kuma......ummu bata qarya sam sam tasan halinta,fadi da cikawa ce,sannan yadda take qaunarta ta tabbatar ita da alhaji ne suka aikata hakan,sai kawai ta bugo wani tsalle ummu bata ankara ba sai jinta tayi a jikinta ta dane mata wuya cikin madaukakin farinciki.
Murmushi ummu keyi tana jin farinciki cikin ranta itama,tasa hannunta tana banbanreta a jikinta tana cewa
"Zaki qarasani 'yar nema,ashe duka iskanci ne,mitsitsiyarki dake wai kinsan meye auren dole,maza saiki sauka ki shiga bandaki ki wanka ki shirya ki shiga cikin 'yan uwanki" ummu kuwa bata kai qarshen zancan ba ta dire sai bandaki,tayi wankanta sarai,akwai kayan dama da taketa cin burin sakasu,yau kuwa zata gwangwaje kwalliyarta,latifa ta zuba mata abinci taci da kyau,sannan ta tsala kwalliyarta cikin wani lace mai azabar kyau da tsada da ummu ta dinka mata ita kadai,ta zauna ta tsara kwalliyarta dai dai da shekarunta da kuma iyawarta,sai gata ta fito dagwas dagwas gwanin kyau.
A falo ta samu ummu tare da baqin da suka fara zuwa mata yawon sallah,wanda duka 'yan uwa ne da surukai,batulu ce matar baban widad din,haka suke rabawa duk sallah,wata zata fara zuwa gaida ummu dayar ta zauna a gida,washegari ko wata washegarin sai dayar tazo.
Jakarta ummu ta kaba ta zuba mata sababbin kudi 'yan biyar biyar,duk da tasan halin kayarta,qila sai a gama yawon sallar a ci a cinye bata kashesu ba,daga qarshe dasu da wadanda ta samu duka dawo mata dasu zatayi
"Ga barka da sallah ta nan" rungume ummu tayi tana dariya cikin farinciki
"Na gode ummu" sai a sannan ta waiwaya ta rusuna kadan tana gaida batulu.
Can qasan zuciyarta maqare fal da baqinciki da takaicin yarinyar,amma a saman fuskarta kadaran kadaham,tayi qoqarin gyara mood nata ko don ummu dake wajen ta amsa mata
"Yammatan ummu,lafiya lau sai ina?"
"Wajen anty madina zani" ta amsa mata tana yin gaba,duk da qarancin shekarunta,amma kwanyarta na iya tuna wasu abubuwan da suke gudana tsakaninta da matan baban nata,suke kuma kan gudana din,shi yasa dai dai da wuni guda bata marmarin zuwa gidan nasu bare ayi batun kwana,ummu ma ba zata bari ba,koda kuwa babanta yana da muradin hakan.
Kamar ko yaushe chamber ta hadu a sassan anty madina,shigarta wajen kallo ya koma kanta,masu tankwa da yabawa nayi,masu baqinciki suna nasu aikin,ko meye saman fuskarka kusan ta saba dashi,uwa uba ga quruciya da bata sanyata daukan abubuwansu da muhimmanci,fatanta da burinta kawai ta shiga cikin 'yan uwanta ayi mu'amala da ita kamar kowa.
Wunin ranar gaba daya cikin walwala ta yita,sai takejin kamar wadda aka daddaure ayau ta samu 'yanci,sai dare ta dawo sassan umnu,tana gefanta tana bata labarai na abinda suka faru,kowa cikin jikoki na zaune saman carfet suna cin abinci amma ita na nanuqe da ummunta,tare suka ci abinci kafin dare ya miqa su wuce dakin kwanciya.
Sai bayan isha'i a ranar alhj mahmud ya koma gida,har lokacin akwai sauran damuwa da bacin rai a tattare dashi,yayi wanka ya canza kaya,umma dake da girki ya gabatar masa da abinci,sannan ta zauna a gefansa tana sake karantarsa,bakinta cike fal da tambayoyi da kuma son jin qwaqwafi,don tunda ya shigo ta karanci akwai wani abu daya faru.
Ganin shuru yana ta cin abincin baice komai da ita ba,sai ta danyi gyaran murya tana gyara zama
"Amma abbansu fuskarka kamar akwai damuwa,Allah yasa lafiya?" Tsaki yaja yana ajjiye cokalin hannunsa,ya kalleta
"Bari kawai hauwa'u,yarinyar nan ce ta watsamin qasa a idanu,takeson ta kunyatani a dangi"
"Wa fa?" Ta tambaya tana yamutsa fuska,duk da zuciyarta ta gama gaya mata wacece
"Widad mana,qiri qiri yarinyar nan ta fandare taqi mahfood,har sai da alhaji yasa baki a maganar ya dakatar da abun" baki hauwa ta riqe tana sakin salati cikin sake kambama abun,lallai yarinyar shafaffa da mai ce,tana cewa su din akwai yaransu da aka yiwa haka?,kuma suna zaune lafiya lau a gidajensu har kwanan gobe sai tashin zancen
"Yanzu abbansu,lamarin da aka faro zancansa tun yarinyar nan bata cika mutum ba,amma yanzu saboda idanunta sun fara wayewa zata ce bataso?,kuma alhaji shima ya biye mata?,wannan wacce irin tabara ce?,ah to lallai abu ya girmama,billahillazi idan ba'a yi wasa ba gaba sai abinda tace za'a yi mata,idan ba haka ba ran kowa ya baci harda mu iyayenta" fushin abba ne ya motsu sosai akan widad din,kuma dama abinda hauwan keso kenan
"Haba ita din banza?,wallahi bata isa ba,ita ta haifemu ma ashe kenan"
"To tana ganin haka tana faruwa tun yanzu gaba basai abinda taga dama ba?,aure kuma dama ai uba ya isa da diyarsa budurwa ya zaba mata miji,bare wannan da ko minzalin budurwa bata kai ba" shuru yayi yana juya zancan,abun ma sai yanzun yake sake bata masa rai,tabbas bazai barta haka ba,duk da ya sani rayuka zasu iya baci,don ummu ba zata lamunci takura ga widad din ba.
A wannan daren da taimakon zugar hauwa ya kwana cikin tunani,washegari.batulu da hauwan ta bincina mata abinda ke faruwa itama ta dora da tata zugar,sai ya sake hawa sosai
"Banason wannan maganar,ku qyaleni haka" yace dasu daga bisani,ya riga ya gama yanke matakin da zai dauka akan maganar.
Widad kuwa walwalarta takeyi sosai abinta hankali kwancw,tunda ta samu akwa kwance ta daga daurin talala na auren mahfood,bikin sallarta take abunta gaba gadi,koda abbanta yazo gidan bayan kwanki biyu bata kawo komai a ranta ba,batasan cewa yazo da sabon alqawarin bada ita ga ma'aruf,ma'aruf dai,ma'aruf din da kalmar zo na kasheki bata taba shiga tsakaninsu ba,ma'aruf din da tsakaninta dashi saidai ido,saidai bata da labarin wannan alqawarin,domin ummu ta rufe zancan don kada a katseta daga walwalar data samu cikin bikin sallar,ta sakaya zancan bayan ta cewa abba
"Mahmudu ni bazan dakatar dakai ba daga baiwa yarinyarka duk wanda kakeso ba,amma muddin babu haduwar jini ko taji bata sonsa bazan lamunci a kaita inda zafa quntata ba,don ina kallonta ne kamar amana a hannuna,idan tasu tazo daya da ma'aruf zanyi farinciki da hakan,don atika(mahaifiyar ma'aruf,jika ne shi cikin gidan,d'an mace ne)tamkar 'ya take a waje na".
Ci gaba tayi da sabgoginta abinta,ta.maida kanta ga islamiyyar da take zuwa,don tunda aka koma hutu boko bata koma ba,alhaji yace ya isa hakanan,su maida hankalinsu ga islamiyya,ita dasu Aafiya,yayin da zancan bada ita ga ma'aruf ya fara yawo cikin gidan.
Zancan ya zowa anty madina ta bakin mijinta uncle mulhim,ta jinjina lamarin sosai
"Tirqashi" ta fadi,saboda tasan irin rashin jituwar dake tsakaninsu,duk sanda widad ta shigo tana binta da kallo yadda take sabgoginta da alama batasan abinda yake faruwa ba,tana tausayinta itama,tana yarinyarta amma sai abubuwa ke zuwar mata kamar wata babba?.
Bata tashi sani ba sai wata rana suna dawowa daga islamiyya,a hanyarsu ta zuwa gida sun biyo ta wani layi,tun daga nesa suka hangi ma'aruf din yana tahowa shi da wani abokinsa,kunnensa maqale da earpiece suna hira kadan kadan da abokin nasa,kafin su qaraso Aafiya tasa hannu tadan bugi widad,wai tanason mata nuni dashi,saidai ko daya ita widad din bata ma fahimci me take nufi ba har suka qaraso dab dasu.
Aafiya ce ta gaisheshi tana rusunawa,ya amsa mata suka wuce,widad kam da idanu ta bisu har suka wuce din,sai taja tsaki
"Yanzun ya kusa zama angonki ma ba zaku fara magana ba widad?" Wani kallo tayi mata cikin quruciya da sakalci
"Waye angon nawa?,ni ba wanda zan aura na gaya miki ina wajen ummu na,tare zamuyita zama"
"Tabdijan,ni kuwa ana cewa aure za'a yimin zan yarda,bakiga kayan lefen da aka kawowa su anty ramziyya ba?,ga kayan girki da gadajen da aka siya musu masu yawa fa,ke don har yanzu bakije gidajensu ba,baki gani ba gwanin sha'awa,su dafa abinda sukeso,suyi kwanxiyarsu a gadonsu,ba duka ba aike ba fada,ke.....hmmmmm" Aafiya ta fada da alama abun yana burgeta,fuskar widad ta dan sauya zuwa fara'a
"Su ai sun girmemu,ko auren za'ayi mana ba za'a yi mana irin nasu ba" kama baki Aafiya tayi tana fidda ido gami da kallonta
"Inji wa?,wallahi momma tace qila ma mu samu abinda yafi nasu"
"Allah?"
"Wallahi" sai widad din tayi shuru tana jinjina kai,hadi da tuna yawan kayan da aka fitarwa kowacce cikinsu ramziyya daga gidan aka sa amota zuwa jeren gidanta.
Sam ta manta ma da wani zancan ma'aruf,har suka isa gida suna zancan kayan auren,a harabar gidan suka rabu kowa ya shige sassansu.
*RUMBUN K'AYA*🔥
*DAUDAR GORA*🔥
*IDON NERA*🔥
*A RUBUCE TAKE*🔥
*KI KULANI*🔥
*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊
*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*
*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*
*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️
*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥
0022419171
Maryam sani
Access bank.
Shaidar biya tanan👇🏻
09033181070
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*🔥
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 07
Bata fahimci zancan da gasken gaske bane sai da ummu ta fara hadata da walid qaramin dan anty madina yana rakata kaiwa ma'aruf din abincinsa,ta maida wannan aikin na kullum kullum a kanta,a nan ne hankalinta ya fara tashi,duk a qoqarin ummu na kawo kusanci da fahimtar juna a tsakaninsu.
Tun ranar farko kamar tasan manufar yin hakan bata shiga dakin ba,daga bakin qofa ta tura masa ta juyo tayi tafiyarta,hakance taci gaba da kasancewa,duk sanda aka aiketan turawa take daga qofa ta wuce abinta sassan anty madina ko sassan wani daga cikin kawunnanta.
*_RABON ZA'AYI_*
Sun tafi tiryan tiryan da walid kai abincin,tana ta qunci da dacin rai,amma ba zata iya qin zuwa ba,har sun kusa da qofar dakin taji akwai alamun baqo,sai ta koma da baya tana duban walid
"Muje na aje masa akan motarsa,yazo ya dauka" yaron yana biye da ita har gaban motar ma'aruf,ta dora masa abincin sannan suka koma sassan ummu,ta fito ne suna kallon wani cartoon,dama kuma Allah Allah take ta koma ta qarasa kalla.
Da kallon mamaki ummu ta bita sanda ta shiga ganin nan da nan ta dawo
"Har kinkai?"
"eh na kai", ta amsa kai tsaye tana komawa cikin kujera ta lafe hankalinta duka yana kan cartoon din,jim ummu tayi kamar tana tantama,sai kuma ta dauke kanta taci gaba da sabgarta.
Bayan minti goma sai naadir ya shigo ya cewa ummu
"Yaaya ma'aruf yace ba'a gama abincin bane?"
"Wanne abinci kuma bayan wanda aka kai masa,ko qaro musu za'ayi?"
"Anya?,yace dai yunwa yakeji abincin yake jira" waiwayawa ummu tayi ga widad data lafe sosai gabanta na faduwa,amma sai tayi kamar bata a wajen,ta rufe idanunta kamar mai bacci,kallo daya ummu tayi mata tasan ba bacci takeyi ba,sam qarya bata mata kyau,tun dazun ta fahimci akwai lauje cikin nadi a maganarta
"Widad a ina kika aje masa abincin?" Manyan fararen idanunta ta bude kamar zata saki kuka ta bawa ummu amsa
"Yana kan motarsa" baki ummu ta kama tana kallonta
"Kai jama'a" maama batulu ta fada cikin bacin rai,yayin data tsaya tana jiran jin irin fadan da ummu zatayi mata,idan ya kama da duka ma ta doke ta,yarinyar ta tsayewa rayuwarta gaba daya,gata qauna da kulawar da ummun ke bata nata yaran basu samu wannan ba,duk da suna samu dai dai gwargwado daga wajenta,amma ita butulu ba irinta takeso ba
"Yanzu tsabaragen iskanci a aikeki widad kije ki dorawa mutum.abinci saman mota?,ta yaya to zaisan kin kai?,idan wani ya kifar kuma bai sani ba fa?" Ta qarashe maganar tana maida kallonta ga ummu wai ko ummun zata kama mata,amma sai taji tace
"Ubangiji ya shiryeki,wannan quruciyar da shirme da kike fama dasu Allah ya maganta miki" ta juya ga naadir
"Jeka dauka daga kan motarsa ka miqa masa" amsawa yaron yayi ya juya yana ficewa,ita kuwa batulu dole ta kama bakinta jin ummun bata kama mata ba,taso taci gaba da maganar tana sake zuga abin,sai abun ya tsaye mata arai,sosai.haushi ya cikata,yarinya sai nema mata mazan aure ake tana iya shege?,wa tafi goshi?,idan kyau ne yaransu gaba daya babu wanda bashi da dai dai nashi,rashin uwa kuma a kusa ai ba farau kanta ba,dukka yaran dake can gida tare dasu kowanne ba uwar gareshi ba,amma babu wanda ummun ke shagwaba haka kamar widad din,kai hasalima ba wanda ummu ta kama ta riqe sai widad din?.
Da wannan takaicin ta baro gidan,saidai kuma ta qudire a ranta ba zataji takaicin banza ba,don haka da daddare bayan dawowar alhj mahmud ta zauna tayi masa famfo sosai,ta bashi labarin qarya da gaskiya kan abinda ya farun.
Sosai kuwa ya tunxura,ransa ya baci,abun na yarinyar ya fara kaishi bango,zuciyarsa dama yaketa danna,abinda ya faranta ran batulu kenan ta gyara zama
"Diya mace dai 'yar gidan wani ce,gwara a gyara mata zama tun yanzu,sannan idan tace shima ma'aruf bata sonshi kuma bansan wa takeso ba,gashi sai dad'a girma suke,kuma ita din ba wata budurwa ba bare ace akwai irin mijin da take hari,duka duka ma yaushe tasan rayuwa ma?". Shuru kawai yayi yana jinjina kai, tabbas zai dauki mataki,bazai bari yana ji yana gani ba gata ya lalata ba,duka sauran yaran da ake riqo a nan gidan ai ba haka suke ba,idan ma ummu ke daure mata gindi lallai gobe sai ya nuna mata kuskurenta.
Har widad din ta kwanta ummu ta tasheta
"Widad,karki sake aikata abinda kika aikata dazu kinji?,baki gani ma'aruf yayanki ne?,kuma shine zai zama mijinki a nan gaba?" Baki ta sake tana kallon ummu a sakarce,hawaye na shirin fara taruwar mata a idanu
"Miji?,ni wallahi bana sonshi ummu" sai kuka ya kufce mata sosai,ta kuma birkicewa ummun gaba daya
"Samu guri ki kwanta" kawai ummun tace da ita bayan ta gaji da koke kokenta,tana jinta daga kwancen tana jan sheshsheqar kuka har bacci yayi awon gaba da ita,wannan al'amari na widad......to wa take so?,Allah shine mafi sanin gaibu shine amsar da ummu ta bawa kanta daga qarshe,ta rufe idanunta tana fata ko meye zaizo yazo da sauqi.
*W A S H E G A R I*
Tunda ta tashi da fushin zancan ma'aruf ta tashi,ummu tayi tayi ta kulata taqi,ko larifa mutuniyarta yau babu 'yar hirar da suke tsakaninsu,da take zata kwaso undies dinta da uniform ma zata wanke mata nuna mata inda ta zubasu kawai tayi,amma abinka da zuciyar yaro qarfe goma na safe sai ta fito falo ta zauna,ummu na zaune kan one sitter,sai ta koma kan two sitter ta kwanta tana kallo a MBC3,duban sashenta ummu tayi taci gaba yankan farcenta ba tare da tace komai ba,daga nan suna jiyo hayaniyar yaran gidan a farfajiyar gidan,wanda ta tabbatar da ranta fes yake da tuni ta fice,idan ba harabar gidan ba to wajen anty madina.
Sallamar abban nata ya sanyata miqewa ta zauna suna kusan hada baki ta da ummu wajen amsa masa,haka kawai taji gabanta ya fadi,kallo daya tayi masa ta shiga nutsuwarta.
Bai jira sun gama amsa sallamar tasa ba ya qarasa wajen kayan kallon dake falon ya zaro wayar USB dake jin wuta ya nufo widad da ita,baikai ga isa ba kiran sunansa da ummu tayi da qarfi ya dakatar dashi,don tuni ta fahimci abinda yakeson aikatawa,saboda ya taba aikata hakan a baya
"Kayi hauka ne mahmudu?,da raina da lafiyata?,ina zaune a falon zaka shigo ka dauki mabugi ka dakarmin ita?,to daketa nace?,wallahi wallahi kana dukanta saina rama mata,idan kuma kana shakka to bismillah" ummu ta fada ranta a mugun bace,abinda yasa ya yarda wayar hannun nasa kenan,yana qoqarin saita kansa,tare da qoqarin gano rashin dacewar abinda ya aikata din,wannan ya bawa widad damar miqewa da gudu ta isa ga ummun,ta fada jikinta gami da qanqameta tana sakin kuka,abinda ya taba zuciyar ummun,ya kuma saukar mata da tausayin widad din,saita dora hannunta saman kanta tana lallashinta.
Gaban ummun ya qaraso ya russuna yana gaisheta,harara ta jefa masa
"Bana buqatar gaisuwarka" saita zare widad daga jikinta tana umartarta data wuce daki,ta miqe tana sharbar hawaye,sannan cikin kaffa kaffa da mahaifin nata ta gewayeshi ta wuce.
"Kiyi haquri,ni banyi haka don na bata miki rai ba,abinda yarinyar nan takeyi yayi yawa,kowa sai tace bata so?,har a aiketa taje ta dora abinci akan mota?,sa'anta ne shi?,fisabilillahi haka za'a zuba mata idanu?" Duk da taji sallamar halimatu a falon amma hakan bai dakatar da ita daga bashi amsa ba,ta gano daga inda tushen zancan ya fita
"To cewa akayi lallai lallai sai ta sosu?,ko kuma fadar Allah ce?,uwayensu ba sai da kukaji kuna sonsu ba kuka auresu?,to ahir wallahi,a sakar mata mara hakanan,ita kadai kunbi kun sata a gaba?,da kai da masu zigoka din ka gaya musu,wallahi tallahi su fita a idona akan lamarin widad,ba wanda ya haifeta ko yayi wahalarta,saboda haka su kama kansu" qas yayi da kai
"Allah ya bada haquri,ya huci zuciyarki"
"Ameeen" ta amsa a fusace,sai ya miqe,yana son tambaya yaji alhaji yana kusa amma fushinta ya sanya don dole ya juya ya fice, halimatu ta bishi da kallo sannan ta dawo da dubanta ga ummun bayan ta tabe baki
"Allah ya kyauta amma dai ummu ai da kin bari ya hukuntata,icce tun yana danye fa ake tanqwarashi"ta fada tana duban ummu da kyau
"Ya kyauta abinda yafi haka,iccen qaniyarki,duk cikinku wa aka yiwa hakan iyee?" Ganin fadan zai dawo kanta saita zame itama
"Allah ya bada haquri,ni ba haka nake nufi ba".
Wunin ranar kamar an dawo mata da zancan mahfood ne,saboda yadda taga abban nata yazo afujajan kamar yadda yayi mata kan auren mahfood,uwa uba bayan sun kebe ummu ta fara tausarta a hikimance,wannan yasa gaba daya ta shiga damuwa da 'yan koke koke,har sai da alhaji ya fahimta ya kuma bi ba'asi.
To da yake shi dinma mai sauqin kai da fahimta ne sai yace
"Ba ta haka ake bi da yaro ba matuqar anason ya fahimci abu,ta lallashi da siyasa ake binsa,gaba daya al'amarin mahmudu bansan me yake damunsa kan batun yarinyar nan ba"
"Me yake damunsa kuwa banda matansa dake zugoshi?" Kai alhaji ya girgiza
"Allah ya kyauta,amma kedai karki saka haka a ranki,mubi komai a sannu da kuma addu'a,zan sake magana da shi mahmudu din"
"Allah ya rufa asiri"
"To ameen,munyi waya dazu da muhsin,yace ko gobe ko jibi zai shigo garin" dan murmushi ummu ta sake
"Ma sha Allah,ayyukan sunyi sauqi kenan?"
"Eh da alama kam tunda har ya samu sukunin zuwa"
"To Allah ya taimaka,ya ara mana rai"
"Ameen ya hayyu ya qayyumu" alhaji ya amsa mata,sai kuma suka shiga wata hirar ta daban.
*RUMBUN K'AYA*🔥
*DAUDAR GORA*🔥
*IDON NERA*🔥
*A RUBUCE TAKE*🔥
*KI KULANI*🔥
*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊
*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*
*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*
*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️
*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥
0022419171
Maryam sani
Access bank.
Shaidar biya tanan👇🏻
09033181070
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*🔥
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 08
Cikin dakinta take tsaye,sanye da uniform na islamiyya,farin riga da wando da kuma hijab ne,sai baqar abaya da suke dorawa a sama,idan ta saka kayan sai ka dauka ita daya aka kebe aka yi uniform din don ita,tana da wani irin kyau da yasha banban da na yaran gidan dukkansu,innocent face ne da ita,duk da cewar a zahirance din ma bata fiya hayaniya ko rigima ba,bata da abokin fada idan bawai taso ba ko quruciyar ta motsa.
Dukka jakar tata ta zazzage saman gadon tana kwashe tarkacen dake ciki gami da kauda su gefe daya,ta maida alqur'aninta ciki,tana shirin rataya jakar ummu ta leqo
"Kin fasa zuwa islamiyyar ne?" Da fuskarta dake da qarancin walwala ta waiwayo tana dubanta,ssnnan ta buda baki a nutse
"Zani"
"To ai gwara ki hanzarta kada ki makara" ummu ta fada tana sakin labulen gami da juyawa,har cikin ranta bata jin dadin rashin walwalar widad din sam,gaba daya tun ranar ta koma wata sukuku.
Plate takalmanta masu igiya ta daura,baqaqe da suka zauna suka yiwa fararen qafafuwanta kyau,saita fito a dakin,ta yiwa ummu dake zaune a falon sallama sannan ta fito farfajiyar gidan.
Tana tsaka da tunanin ta tsayawa koda Aafiya ne su wuce tare ko kuma tayi tafiyarta hon din mota daga waje ya cika harabar gidan,ba tare da jinkiri ba baba awwa ya miqe ya bude gate din,baqar motar dake daukan idanu da sheqi ta sako kanta zuwa cikin gidan,hankalin widad ya dauku kan motar,kamar taso ta gane motar waye?,tunaninta yazo dai dai sanda baba awwa ya qarasa ga motar bayan ya rufe gate din yana fadin
"Barka dai da sauka,barka da sauka mai gida muhsin" wani murmushi ne ya qwace mata,uncle muhsin?,uncle muhsin ne yazo?,mutumin dake cikin jerin sahun mutanen dake da girma da matsayi a rayuwarta,mutumin dake nuna mata kulawa kamar yadda yaga ummu nayi mata,gaba daya ta sha'afa ma da batun makaranta ta fito,gaba daya hankalinta ya tattara ga uncle muhsin din,wanda ko second daya bata qara a tsaye ba ta nufi inda ya faka motar tasa harda sassarfarta.
Suna tsaka da gaisawa da baaba awwa din ya tsinceta a wajen,bakinta har kunne
"A'ah,yammata sai ina?, islamiyya za'a je?" Farincikinta ya gaza boyuwa,ta gyada kai tana dariya gami da fadin
"Uncle muhsin ka shammaceni,dama zaka zo?"
"Gani kuwa widad,bakiji wajen alhaji ko ummu ba?" Kai ta girgiza still dai tana dariyar.
Kafarta kafarsa suka shige gidan,sai daya fara shiga sassan 'yan uwan nasa suka gaisa,tana biye dashi qafa da qafa,duk da hararar da take samu daga wajensu amma bata damu ba,anty madina ce ma ta tsokaneta
"Batun tafiya makaranta ya tashi kenan?". Dariya widad din tayi,sai uncle muhsin din ya juya ya kalleta
"A'ah,ai ba za'a fasa zuwa makaranta ba saboda zuwa ne,kije ki dawo,ina nan ai" cikin shagwaba ta narke fuska
"Don Allah uncle,yau kadai.....kuma ma lokaci ya wuce,na makara,idan ma naje bulala zaayimin Allah" kai ya jinjina kawai,widad din ta daukeshi da wani matsayi sosai,haka suka wuce sassan ummun tare.
Ina ka saka ina ka ajjiye ummu keyi da dan autan nata,wanda take lelensa kamar kowanne auta a wajen iyayensa,duka su ukun suna falon suna hira,ita widad da kuma uncle muhsin din,sai da ummu ta korata tace ta fidda uniform din daga jikinta tunda taqi makarantar sannan ta miqe da jakarta a hanzarce ta wuce daki.
Dauke dubansa muhsin yayi daga dubanta sanda ta bacewa ganinsa ya maido ga ummu
"Me ya samu widad ne?,ko tayi ciwo baya bayan nan?"
"Me ka gani?" Ummun ta tambayeshi itama
"Ramewa naga tayi,ko girma ne ya kawo hakan?" Kai ummun ta girgiza tana tabe baki
"Batun aurenta ne yaketa zuwa da mishkiloli kawai"
"Aure fa ummu?,widad din?"
"Eh baqon abu ne?,naga kusan duka 'yan bayanta ma haka aka musu" zamansa ya gyara,har cikin ransa bayaso a aikata wannan dabi'a ga widad din,yana jin yarinyar har ransa,saboda baya mancewa da yadda mamarta ta daukeshi a sanda take auren dan uwansa,saboda da shaquwa ne sosai tsakaninsu da ita,ta daukeshi kamar qaramin qaninta
"Amma ummu sunfi widad datawa ai,duka duka ita din shekararta nawa ne?,sha hudu fa?"
"To mahaifinta dai ya tasamma aurar da diyarshi,mahfood ne akayita gwagwarmaya akan lamarinsa tace bataso,muka saka baki ni da alhaji aka ajiye zancansa,ya dauko ma'aruf to yanzu akan batunsa ake,shima din kuma ba so take ba" sosai fuskar uncle muhsin ta sauya
"Amma ummu shikam yaaya meye haka?,tunda bataso duka basai a qyaleta ba?,nawa widad din take?,naga batayi girman da zai daga hankalin kowa ba saboda batayi aure ba ko?"
"Duk yadda nake da iko dashi da ita dole akwai huruminsa na uba daya zama dole na bashi,nidai abu daya na sani bazan bari ayi mata auren dole ba" dan qaramin tsaki yaja abun yana bashi haushi,ko da shi dabi'arsa ta daban ce,bare a yanzun da ya zama riqaqqen dan boko
"Wannan maganar a barta kawai,indan tace taji ta gani tana so ne ma shikenan sai ayi zancan aure,amma ni sha'awar karatu nake mata,karatu nakeso tayi,bari zamu hadu da yayan,ya bani ita kawai mu wuce gida tare"
"Bazan iya baka widad ba,zan maka lamuni dai taje zuwa sanda komai zai lafa" murmushi yayi
"Zahra ta dade tana nacin a bata widad ummu,su kansu su nujood zancansu yaushe zatazo,tunda anyi haka kawai ki haqura ku barmin ita"
"Banyi alqawari ba" ummu ta shaida masa kai tsaye.
Sanda widad din ta dawo falon bayan ta sauya kaya ummu ta shiga ciki ta duba dashishin da za'a girkawa alhajin,har yau har kwanan gobe tsufa jin dadi ko wadata bai hana dattijuwar matar aikin abincin mijinta ba.
Cikin hikima uncle muhsin yake bugun cikin widad kan batun,tuni ta fara share qwalla,sai ya ajjiye spoon din hannunsa
"Kinga share hawayenki,ba wanda zai miki auren dole,dake zan koma ma na kaiki wajensu nujood,ai zaki je ko?" Duk da nisa da ummu shine abu da tafi tsana,amma a yanzun sai takejin shine mafi dacewa,kawai tabi uncle muhsin din,tayi nisa da garin ko abbanta zai haqura da qudurinsa,bata da zabin da ya wuce wannan,don haka ta gyada kai hadi da cewa
"Zanje uncle"
"To shikenan,share hawayen ki bani labarin izifinku nawa yanzu a islamiyya" hira ce ta barke tsakaninsu,harma ta manta da fargabar tafiya tabar ummu,saima zumudin matsawa daga garin,ko banza ta gujewa wani ma'aruf abbanta dama auren da ake shirin qaqaba mata.
Uncle muhsin shine auta ga ummu a maza,daga shi sai halimatu kenan,kuma qani ga abbanta da suke uwa daya uba daya,shi din ba mazaunin kano bane,yanayin aiki ne ya kaishi bauchi,da farko ma kamar bazaije ba,saida ummu ta qarfafa masa gwiwa,ta kuma nuna masa aiki ba inda baya kai mutum,yanzu haka shekararsa kusan goma sha uku da aure,yana da yara hudu,diyarsa ta farko widad ta girmeta da shekara kusan daya,dan boko ne sosai,yana da sauqin kai som mutane da kuma kirki,widad na ji dashi cikin dukka tulin qannen da mahaifinta ke dasu,saboda yadda yake nuna mata kulawa da kuma janta a jiki.
Da kansa uncle muhsin din ya zauna da yayan masa mahmudu,ya sha fama sosai kafin ya gane abinda yake kwatanta masa,don daga bisani dole ummu da alhaji suka sake shiga maganar sannan ya janye qudurin nasa,ba kuma wai don ya haqura da maganar bane gaba daya,wannan ya sake qarfafawa uncle muhsin gwiwar tafiya da widad din
"Taje dai ta huta,amma ban bar muku ita ba,kada ma kazo kace min ga zance ga magana".
Kamar wasa sai ga widad tana murnar tafiya,har ta fara hada kayanta da kanta ma,latifa ita da anty madina sunata dariya
"Ba cinya ba qafar baya,Allah dai yasa a qarke qalau kada ku dawo ranar da kukaje" suke tsokanar uncle muhsin sanda sukaga widad din nata shiri.
Kwana uku kacal ya qara suka tattara sai bauchi,ranar da zata tafin gaba daya 'yan rakiyarsu har bakin motar uncle muhsin din,latifa ke riqon jakarta,tana ta tsokanarta
"Uwar dakina kada dai zama yayi dadi a manta dani" widad dake sanye da atamfarta dinkin doguwar riga tayi dariya tana qwamewa gaban motar uncle din
"Bazan manta dake ba inna latifa,kedai ki zuba ido zakisha tsaraba" dariya ta saki
"To Allah yasa" itama ta amsa tana dariyar,suna dakon uncle muhsin ne,yana rabawa yaran gidan da sukayo masa rakiya kudi,'yan dari dari ne sababbi qar,baya rabo dasu,ya kammala ya dawo cikin motar ya zauna yana sake waina injin motar sosai,ummu ta zagayo ta durqusa tana musu addu'ar sauka lafiya,sannan ta zura hannu saman cinyar widad ta ajjiye mata kudi
"Gashinan,kada kije baqon guri hannunki babu komai" murmushi uncle muhsin yayi bayan ya kalli kudin
"Banda abinki ummu me zatayi da kudi?"
"Ina ruwanka kai dai?" Ta amsa shi,tana gyara yafen mayafin dake saman kanta
"Nidai bance a riqemin yarinya acan ba,aro na baku" ta sake jaddada masa abinda yake ranta,sai yayi dariya kawai yana tayar da motar,dai dai sanda widad kema ummun godiya,duk da itama din batasan amfanin me kudin zasuyi mata ba.
Har motar ta fice daga harabar gidan suna waigen juna ita da ummun
"Zauna sosai kada ki baro kan naki a gida kije bauchi da iya gangar jiki" uncle muhsin ya tsokaneta,sai tayi dariya tana zama sosai din,saidai tun a lokacin taji ta fara kewar gida,taji kamar ta koma,to amma idan ta tuna abinda ta gujewan sai taji dadi,hankalinta kuma yadan kwanta,ko ba komai za'a daina zancan,tana saka ran maganar ma tabi ruwa ta huta.
Suma shirin ficewa a unguwar motar ma'aruf din ta sako kai,uncle muhsin yadan dakata kadan,sai ta lafe sosai ta kwantar da kanta saman cinyoyinta ta yadda bazaya ganta ba,ma'aruf din ya gaidashi sukayi sallama,uncle muhsin yaja motar sukayi gaba yana dariyar widad din cikin ransa,quruciya sai abarta.
*ZAFAFA BIYAR 2023*
IDON NERA Mamuhghee
KI KULANI miss xoxo
A RUBUCE TAKE Huguma
RUMBUN K'AYA Hafsat rano
DAUDAR GORA Billynabdul
Account number
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiki tura shaidar biyanki ga
09033181070
VTU OR MTN RECHARGE CARD
09166221261
AL'UMMAR NIJER SU TUNTUBI WANNAN NUMBER
+227 90 16 59 91
Thanks for choosing us
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 09
Suna tafe a hanya uncle muhsin din yana janta da hira,ta saki jiki sosai sunata hirarsu da yake abokin hirarta ne dama,a nan ya fahimci interest dinta itama game da karatu,da yadda take da kaifin basira,tun suna hirar har suka gaji kowa yayi shuru,saita maida hankalinta ga kallon titi da yadda suke wuce dazuzzuka,can qasan ranta ta dinga jin wata kewa tana shigarta,zuciyarta ta karye,suna dada yiwa kano nisa.
Tun tana iya bin hanya da kallo har baccin ya soma fusgarta,babu jimawa kuwa yayi awon gaba da ita,ta saki jiki sosai tana barcinta abinta.
Bata tashi farkawa ba sai da uncle muhsin ya iso qofar gidanshi ya tsaya yana jiran mai gadi ya bude masa qofa,idanunta ta bude a hankali tana murzasu hadi da budesu da kyau tana qarewa wajen kallo.
Tun a sannan tasan ta shigo baqunta,ta kuma shigo sabon waje,quaters ne dake da qarancin jama'a tare da qarancin gine gine,saidai kuma duka manyan gidaje ne ta wajen,tana nan zaune har ya buda gate din gidan ya dawo ya shigar da motar.
Sanda ya kashe motar waiwayo yayi yana tsokanarta
"Yar qauyen kano yau gata a bauchi" kasa magana tayi saboda kewar ummu data fara shigarta,sai murmushi kawai data saki,dai dai nan matar gidan ta iso.
"Kai kai kai.....abba wa nake gani haka?" Ta fada tana dariya gami da murza bdanunta,saboda baice mata da widad din zasu taho ba
"Wa idanunki suka gani?" Shima ya fada yana dariyar
"Tabdi,wai Allah na,anya kuwa ba gizo idanuwa kemin ba?"
"Shafa kiji dai" ya sake fada yana dariya gami da qoqarin fitowa daga motar yana duban widad din
"Fito mu shiga ciki" yace da ita yana fita daga motar
"Gaskiya na ciri tuta,abba wacce irin addu'a ne ka yiwa ummu ta baka widad?" Ta sake fada tana karbar jakar hannun widad din tare da sake bude mata qofar motar sosai.
Tare suka jera zuwa ciki hadiyya matar uncle muhsin da yaranta ke kira hajjaa nata mamakin zuwan widad din
"Saurin me kike ne?,zakiji komai fa" cewar uncle muhsin.
Tunda suka shiga falon gidan ta gane yaran gidan basa nan,da yake ranar makaranta ce,har dakin yaran hajjaa ta rakata sannan tace da ita
"Ki alwala ki sallah,ki shiga kitchen da abinci ki diba kici,su nujood din sun kusa dawowa,yanzun nan zaki gansu" a nan dakin ta barta ta koma wajen mijinta.
Tun bai gama kintsawa ba ta sashi a gaba,yana shiryawar yana bata labarin dalilin tahowa da widad din,gyara zamanta tayi tana sauke ajiyar zuciya
"Gaskiya abba gwara daka taho da ita,duka duka nawa take da za'a dameta da batun aur,baya ga haka ma naga ko yayyen nata da aka yiwa auren duka sun fita datawa,tunda a qalla suna kaiwa sha bakwai sha takwas,sai ita tun tana 'yar sha hudu?"
"Nafi tunanin farinjinin da yaaya yaga tana da shi ne fiye dana 'yan uwanta ya daga masa hankali yakeso yayi ya kawar da ita,amma gaskiya ni dama nafi mata sha'awar karatu,da zan samu ummu tabarmin ita karatunta zatayi sosai"
"Gaskiya dai abba,Allah yasa ummu ta bari"
"Ba tabbas" ya amsa mata yana zura jallabiyyarsa
"Ki dauko system dita ki sakamin ita a charge,nabar ayyuka da yawa ban kammala ba,inaso na rage kafin gobe" ta amsa masa da to tana miqewa,shi kuma yana fita don zuwa masallaci sallar azahar.
Hankalinta duka yana kan widad tunda ta barta a dakinsu nujood,widad din ba baquwarta bace,tasan yadda take da wahalar sabo da rashin sakin jiki,qilan yanzun tana can zaune a takure,kamar yadda ta zata kuwa haka ta sameta,tayi sallar dai amma tana zaune,cikin dariya tace
"Anya widad za'a zauna mana a bauchin nan kuwa?,taso muje kuci abinci kafin su qaraso,yau sunyi delay ma,Allah yasa ba school bus din tasu ce ta sake basu matsala ba,don haka tayi musu jiya".
Tare suka fito tana biye da ita,a falo suka samu uncle muhsin din,shima shirin cin abincin yake,sai hajjaa ta zuba musu tare,tana daga gefe suna hirar kano da uncle muhsin din,jifa jifa suna sanya widad,har ta fara sakin jiki,da yake daga uncle din har hajjaa mutanenta ne.
Basu ko kai ga gama cin abincin ba sukaji ana taba gate din gidan
"Tohm,ga 'yan makaranta nan"Hajjaa ta fada hayaniyarsu na ratsowa falon tun kafin sukai ga qarasowa.
Tsam widad ta dauke hannunta daga plate din abincin cikin hanzari,kafin sukai ga qarasowa ita ta fita suka hade a farfajiyar gidan.
Cikin murna nujood ta riqeta tana ta ihun murna kamar wadanda wani abu ya sama,banda uncle muhsin sun san abinda ke faruwa babu abinda zai hanasu tsorata,amma sai ya kada kai yana murmushi
"Allah ya shirya,kamar basusan sun fara girma ba"
"Banda abun abba ina hankali a nan,ai saidai aikin quruciya".
A nan falo ranar aka wurgarwa da hajjaa kaya da jakar makaranta,sauqinta daya ranar babu islamiyya ta tabbatar da babu abinda zasu,baga nujood din kawai ba,har duka sauran 'yan uwanta sunji dadin zuwan widad din.
Cikin kwanakin da basu da yawa taji ta qagu ta koma wajen ummunta,duk da cewa gidan yana mata dadi amma sam batason garin,hakanan take,ta fiya baqunta da rashin saurin sabo,abu daya ne yake sanyawa taji komawar ta fitar mata a ka,batun ma'aruf da kuma mahfood da taji rannan uncle muhsin suna zancan da hajjaa hadiyya sunayi cewar har yanzun bai haqura ba,yace idan Allah yayi rabonsa ce shikenan.
Zumbura baki tayi gaba ba tare data baiwa zancan muhimmanci ba,duk da qarancin shekarunta amma ta fuskanci zallar nacin da mahfood ke dashi,ta rasa da wanne suna ya dace ta kirashi,takan kirashi da maye a ranta,taja tsaki ta dauki marker din zanen da tazo dauka suna wani zane ita da nujood ta fice zuwa farfajiyar gidan inda suka sanya kujeru suka zauna.
*******
Baqar mota ce wuluk qirar BMW take ratsawa a hankali ta saman titin,daga cikinta tana dauke ne da mutane uku,dukkansu sanye suke da police uniform (kakin d'an sanda,matuqin motar akkauran dan sanda ne baqi dake hakimce a mazaunin driver yana sarrafa sitiyarin motar cike da qwarewa,yayin da wanda ke zaune a gefansa ya kasance siriri sosai,hakanan kuma dogo ne,duk da cewa a zaune yake zaka fahimci hakan.
Na ukun nasu kuwa yana zaune daga bayan motar,tashin farko zaka iya kiranshi da matashi,don duka duka shekarunsa na haihuwa ba zasu haura talatin da biyar ba,mara hasken fata ne da zaka iya kiransa sa chocolate color,irin fatar dake da tsada da kuma daukan hankali,saboda yadda take a kwance kadai zai nuna maka zallar jin dadin da ma'abocin fatar ke samu.
Yana da matsakaicin tsaho,wanda inda ace siriri ne kai tsaye zaka iya kiransa da dogo,saidai murjewar jikinsa ta shanye tsahon nasa ta sanyashi a sahun matsaikatan maza,manyan idanu gareshi masu daukan hankali,girmansu bai hanasu lumshewa ba a duk sanda yaso hakan,kamar yadda yake da wasu irin lips kai kace na mace ne.
Sosai uniform din suka zauna masa a jiki,kai kace saboda jikin nasa aka qerasu,qafafunsa da yayi crossing nasu socks ce kawai,boots dinsa na aje gefan qafafun nasa.
Duk da hirarrakin da mutum biyun dake gaban motar sukeyi shi sam ko sau daya bai tsoma musu baki ba,hasalima tafin hannunsa ne shimfide saman fuskarsa kamar mai wani tunani,abinda kuma zai iya hanaka ganin ainihin fuskar tasa sosai kenan,sai kyakkyawan agogon Rolex dake daure a tsintsiyar hannunsa.
Yanayin zaman da yayi kamar na mutumin daya gaji tubus,sam zaka zaci baya cikin motar ne,duk da hirar da sukeyi din ta shafi aikinsu,dukansu cikin zuciyoyinsu suna muradin ya sanya baki,saidai sunsan abune mawuyaci,shi yasa cikinsu ma babu wanda ya sanya rai da hakan suka ci gaba da hirarsu ba tare da sun daga sauti yadda zasu dameshi ba.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana zame hannun nasa daga saman fuskar tasa,kyakkyawar zagayayyar fuskarsa dake cike da wani irin kwarjini gami da haiba ta bayyana,ya dan bude idanunsa kadan da nauyin gajiya ya cikasu.
"Samuel" ya furta cikin muryarsa dake da kauri da nauyi
"Yes sir" mamallakin sunan wanda shike tuqin motar ya amsa a ladabce
"Ka saukeni gidan hajiya tukunna"
"Consider it done sir" ya sake amsa masa cikin nuna qarfin bin umarnin sa.
Kafin wani a cikinsu ya sake cewa wani abu wayar dake tsakanin seat din gaba guda biyu ta dauki tsuwwa,mutumin dake zaune a kujerar dake zaman banza ne ya miqa hannu yana dubawa,kana yadan waiwayo kadan dai dai sanda yake qoqarin maida boot din qafarsa
"Sir,dan jaridar nan ne" shuru kamar bazai amsa ba,da alama ba ma'abocin son magana bane,sai kuma yace
"Ka katse kiran ka tura masa saqo,gobe qarfe biyu su sameni a zone one"
"Yes sir" shima ya amsa yana juyawa cikin qoqarin idar da umarninsa.
Dai dai sanda ya gama sanya takalman yana gyara zamansa motar ta soma gangarawa cikin unguwarsu,sai ya juya gefansa yana daukar tarkacensa dake zube akan seat din gami da maida hularsa saman kansa yana dakon motar ta isa qofar gidan.
*ZAFAFA BIYAR 2023*
IDON NERA Mamuhghee
KI KULANI miss xoxo
A RUBUCE TAKE Huguma
RUMBUN K'AYA Hafsat rano
DAUDAR GORA Billynabdul
Account number
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiki tura shaidar biyanki ga
09033181070
VTU OR MTN RECHARGE CARD
09166221261
AL'UMMAR NIJER SU TUNTUBI WANNAN NUMBER
+227 90 16 59 91
Thanks for choosing us
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 10
K'ofar wani madaidaicin gida mai fenti ruwan toka da qaramin gate ruwan madara motar ta tsaya,ya sanya hannunsa cike da nutsuwar nan tasa dake zmaa mabudin nasara ga dukka aikin da ya sanya a gaba zai buda motar,saidai kafin yakai ga aiwatar da hakan Samuel ya rigashi,ya kalleshi yadan kau da kai sannan yace
"Thank you Samuel,you can go,zan koma gida da kaina" kai ya girgiza
"No oga,zamu jiraka,daga nan station zamu koma,babu wani aiki da zamuyi kuma". Baice masa komai ba ya sauka daga motar ya nufi gidan yana takawa cikin tafiya ta tsayayyun maza.
Da sallama ya tura qofar ya shiga,yar farfajiyar gidan babu kowa saidai qal take,fes kamar babu wanda ke rayuwa cikin gidan bare ya bata ba,yana hango takalma daga qofar falon,wanda zaka fara taka wata qaramae baranda kafin ka cimma falon,sai yaci gaba da takawa har ya isa baranda yana maimaita sallamar sa,hadi da yunqurin zame takalman qafarsa kafin yakai ga shiga falon
"A'ah qaraso da takalmanka abinka" daga can cikin falon aka fadi,sai ya miqe murmushi daga qasan zuciyarsa na kubce masa,har ta hangoshi kenan,duk da shi bai hangota ba,ya yaye labulen yana sanya kansa ciki tare da jaddada sallamarsa.
Daga can saman kujera mai cin mutum biyu take a zaune,babbar macace wadda aqalla ta doshi shekara sittin,zaune sanye da atamfa dinkin riga da zani,kanta lullube da kallabi mai santsi irin na asalin tsaffi a qasar hausa.kyakkyawae bafulatanar bauchi,wadda bata qi dibar komai nasu ba,illa hasken fata,bata cika fari sosai ba irin wanda akasan fulani dashi ba,fuskarta na nuna zallar kamala da nutsuwa da kuma mutuntaka irin ta cikakken dan adam.
"Wa'alaikumus salam,maraba...yanzu kake tafe?"tayi tambayar tana gyara zamanta cikin kujerun
"Eh hajiya" ya amsa mata dai dai sanda take duban 'yar budurwar dake kwance cikin kujera
"Tashi ki bashi waje" tun kafin ma hajiyar takai qarshen maganarta ta soma yunqurin tashi tana lalubar dan kwalinta daya fita,cikin sauri ta fara gaidashi
"Ina yini uncle"
"Lafiya lau" ya amsa mata yana zama cikin wata kujerar ta daban,bayan ya dan ture kayan da suke kai
"Shiga kitchen ki samo masa ruwa"
"Tom" ta amsa tana ficewa daga falon.
Sai a sannan ta tattara hankalinta a kansa,cike da girmamawa ya zamo qasa yana gaidata,ta amsa masa cikin kulawa da kuma qauna
"Alhmdlh.....ashe kun dawo"
"Shigowata bauchi kenan nace bari na fara zuwa na gaidaki" ya amsa mata yana komawa mazauninsa
"Ma sha Allah,Allah yayi jagora"
"Yayi hajiya,saidai fatan Allah ya dada yi mana,duk abinda akaje yi din Allah ya dafa mana an samu nasara" murmushi ya wadaci fuskarta,duk sanda zaiyi tafiya irin wannan sai ya shaida mata abinda zaije yi din,duk da cewa kusan komai din da zaiyi ma cikin rayuwarsa ita yake fara sanarwa,ita yake fara shawarta,takan tsaya tuquru da addu'a koda bai nema addu'arta ba,domin kuwa shi din na dabanne a zuciyarta,yana da wata irin tarin biyyaya me wahalar samuwa ga yaran yanzu.
"alhamdulillah, alhamdulillah,Allah abun godiya,to Allah yaci gaba da kula mana da rayuwarku"
"Ameeen ya hayyu ya qayyumu hajiya" ya amsata yana sake cire hular kansa kamar tana damunsa ne ya ajjiye a gefansa yana duban tarin kayanta dake ajjiye
"Ya akayi maisara ya kawo miki kayanki haka babu guga?" Dan duban kayan tayi
"To wallahi dai bana ce ba,kamar dai kallon qwallo suka tafi" fuska yadan tsuke
"Qwallon me?,idan bazaya iya aikinsa yadda ya kamata ba sai yayi magana" murmushi hajiya ta saki,shikam akan dukkan abinda ya shafeta baya wasa dashi,baya bada uzuri,hakanan baya daga qafa
"Yana qoqari ai,kasan su da son qwallo,kuma yau da gobe ma sai Allah" shuru yayi ya sanya hannu yana karbar cup din da muneera take miqo masa mai cike da ruwa.
Sai da ya shanye ruwan sannan ya dubi hajiyan
"Saura kwana nawa ne bikin gidan kawu hassan?"
"Na zaci zaka leqa ma,yana gida kamar bai fita ba yau"
"Sai idan na dawo,na yiwa auwal magana zai fidda kudin gudunmawar nan,zai kawo miki sai a bashi"
"To to madallah,Allah yayi albarka,ya qara budi"
"Ameen ameen" ya amsa mata yana sanya hannunsa a aljihun uniform dinsa ya fiddo kudi ya ajjiye mata yana cewa
"Zan dan huta gobe,may be bazan fito ba"
"Baka gajiya abbas?" Murmushi kawai ya saki ba tare da yace komai ba,baijin zai gaji da yiwa hajiyan tashi hidima bakin ransa,domin baya da kamarta a fadin duniya
"Allah yayi albarka"
"Ameen ameeen"
"A gaida gida,a gaidamin kishiyoyin nawa" kamar tace kwana biyu sunqi gidan sai kuma ta fasa fadin hakan,ita din mutum ce mai son zaman lafiya,batason rigima sam,saidai a duk sanda ka qureta bata da dadi.
A bakin mota ya samu su Samuel sunata hirarrakinsu,kafin ya iso ya bude masa qofar motar ya shiga,sannan suka zagaya suka shiga suma ya tada motar suka bar layin.
Duka duka tafiyar minti talatin da 'yan kai motar ta sake sanya signal sannan suka shiga wani madaidaicin titi mai burji,wanda zai sakada da ainihin unguwar da suka nufi shiga.
Basuyi tafiya me yawa ba motar ta fara slow,da alama sun cimma inda suka nufa,ba jimawa ta faka qofar wani madaidaicin gida.
Daga girman gate din gidan zaka fahimci girman gidan,idan nace girma bawai ina nufin girma na sosai ba,saidai kana gani kasan yalwataccen gini ne daga ciki,hakanan ya qawatu ga idanun me kallo,yana dauke da tsayayyun katanku masu tsaho da qarko,wadanda ke dauke da fenti ruwan madara har jikin gate din,wanda aka yiwa ratsin zaiba(gold) a jiki.
Wannan karon kafin su bude masa ya rigasu budewar,ya zuro qafafunsa dake saye cikin baqin boot zuwa waje yana duban gaban gidan sannan ya sanyo gangar jikinsa zuwa waje
"Thanks Samuel" yace dasu bayan yadan waiwaya da kyau
"You deserve it sir"ya fada yana saluting nashi cikin girmamawa,jinjina kansa kawai yayi yana nan tsaye har suka tada motar suka fara barin gaban gidan,sannan ya qarasa a hankali yasa hannu yana knocking.
Daga ciki wata kakkaurar murya ta bayyana ana tambayar waye,bai bada amsa ba har zuwa sanda mai tsaron gidan ya bude qofar,da sauri yaja da baya cikin matuqar girmamawa yana masa sannu da zuwa
"Yauwa sule,mun sameku lafiya?"
"Lafiya lau oga"
"Ma sha Allah" ya furta yana takawa zuwa cikin gidan,hannunsa guda daya saye a aljihun wandon uniform dinsa,daya hannun kuma riqe da hular tasa.
A hankali yake takawa zuwa cikin gidan yana nazartar yanayin gidan,daga farfajiyar gidan ko ina fes yake cikin hankali da nutsuwarsa,duk da bashi da tabbacin abinda zai tarar a ciki amma hankalinsa ya dan kwanta kadan,yaci gaba da takawa cikin taku na qaqqarfan namiji wanda horon aikin damara ke yawo cikin jiki da kuma jininsa.
Qofar falon ya murza,yayi sa'a ya sameta a bude,sai ya tura yana sanya kai ciki,bakinsa dauke da sallama.
Kamar jira akeyi,yara biyun dake wasa a falon saman dan keken wasan yara suka waiwayo zuwa gareshi,babbar me wayon wadda ke tura qanwarta ta saki keken da mugun gudu ta nufeshi
"Abba....abba!" Take fada cikin daga murya dake cakude da sautin zallar farinciki,yayin da daya yarinyar keta kiciniyar saukowa daga kan keken itama don ta iso gareshi.
Wani qawataccen murmushi ne ya subuce masa,ya duqa a hankali yana jiran isowar yarinyar,tana qarasowa ya dauketa caraf yana sanyata cikin jikinsa,saidai kuma me?..... janyeta yayi da sauri yana duban kayan jikinta sakamakon qarnin da baisan na meye ba daya daki hancinsa,ya sauke idanunsa kan gaban rigar yarinyar,rigar da idan bai manta ba naira dubu shida ya sanya ya siyeta kafin tafiyarsa wannan aikin,kwanaki goma baya da suke wuce kenan.
Jirwaye ne na abubuwa kala daban daban a gaban rigar,wanda shi kansa bazai tantance na meye ba,ya dauke idanunsa ya maida kan fuskar yarinyar dake dauke da jirwayen busassun hawaye,kafin yayi magana yaji ana jan hannunsa hade da gwaranci,sai ya mayar da kallonsa kanta,tana tsaye a gabansa tana ta babbaka masa dariya,da alama akwai abinda takeson gaya masa cikin gwarancin nata,sai ya miqa hannu daga tsugunen da yake ya dauketa cak yana azata saman cinyarsa,saidai ita din ma babu sauqi,tsami ko kuma warin pampers dinta ne ya kaima hancinsa ziyara,ya miqa hannu yana taba pampers din,sai ya jishi a cike,tausayin yarinyar ya kamashi,take kuma ranshi ya baci
"Abba,ka siyo man teddy din?" Kumatunta ya kama yana qoqarin hadiye fushinsa,abinda kusan ya zame masa jiki koda yaushe
"Mimi teddy,bari na huta tukunna" bai sake jiran komai ba ya sanya hannu ya sunkuci yaran duka su biyun,sunata zuba masa shirmensu yana biye musu ya doshi sassanshi dasu,don bazai iya sake zama a wannan sashen ba a yadda idanuwansa suka ganshi a hargitse kamar an shekara ba'ayi masa shara ba.
Sashe ne daya tsaru matuqa cikin kalolin light blue da fari,tun daga babban falonsa dake manne da window size da hotunansa da yawancinsu cikin uniform dinsa ne na police zuwa bedroom dinsa wanda aka zubawa kayan gado masu matuqar kyau da tsari.
Yayi zaton zai samu sassauci a sashen nasa,tunda yabar key ya kuma buqaci a gyara masa,amma sai ya samu waje shima sammakal,sauqin daya ne baikai jagalewar can ba,ya hadiye wani abu mai tauri yana sauke yaran gefan gadonsa,sannan ya fara cire uniform din nasa,ya rage daga shi sai wata farar shirt mara nauyi ko kadan mai gajeran hannu,wanda hakan ya bayyana cikar zati da siffar jikinsa,muscles tako ina dake nuni da siffar qarfi da kuma yanayi na motsa jiki da daga qarfe da yakeyi a kowanne lokaci,wandon jikinsa ya fidda ya rage iya boxer,sannan ya shige toilet dinsa ya hada ruwa mai dumi sosai ya dawo dakin ya fidda musu kayan jikinsu ya wuce toilet din dasu ya sanyasu a bathtub.
Fes yayi musu wanka dukka su biyun har gashin kansu,sunata qyalqyala dariya hadi da cikashi da duminsu,shi kuma yana ta biye musu,dukka a qoqarinsu na hadiye damuwa da kuma bacin ransa,bayan ya gama ya sanya kayan daya cire musun a leda ya jefa a dustbin,duk da kudin da ya sanya ya siyesu,mutum ne shi mai tsananin tsafta hadi da tsantsami,don hakan baima san ta ina zai fara tsaftace kayan ba,don haka ya gwammace yayi musu hakan.
Anan dakin ya shafa musu mai ya gyara musu gashinsu,sannan ya buda jakar da yazo da ita,a duk sanda yayi wata tafiya indai dama ta samu baya gajiya da yiwa iyalinsa tsaraba,ya fidda wasu gown na wani cotton material iri daya guda biyu ya sanya musu,sannan ya feshe jikinsu da turare.
Murna suke abinsu kawai,walwalarsu ta dadu saboda yadda sukaji jikinsu yayi musu dadi,ransa a bace ya daga kai yana duban agogon bango,a qalla ya kusa minti talatin da shigowa,amma batasan ya dawo din ba,abar ta tashi ma,yaran data bari a parlor fa?,haka take tafiya ta qyale yaran qofa a bude kusan awa guda ba tare data leqa su ko ta bibiyi halin da suke ciki ba?.