Bai samu ganin Khadija ba saboda a lokacin suna sallah, kuma an rufe d'akin da Bilal ke kwance saboda hayaniyar da tayi yawa aka barshi shi kad'ai kafin wani lokaci, fita Usman d'in ya yi yace zai dawo anjima.
A wajen Haseenah ba yanda ta iya dole ta d'an d'auki abin da ta d'auka ta fito ta na kuka ta bar gidan, amma da taje gida kasa fad'an komai ta yi sai tace kawai ta na girki ya same ta yace ta taho gida ya sake ta saki biyu, su kam iyayen take su ka d'ora laifin kan Khadija cewa ita ta shiga ta fita aka sake ta, Haseenah dai komai ba tace ba sai sauraren su, mahaifin ta ne yace zai je ya samu mahaifin Usman d'in dan ba zai d'auki wannan wulak'ancin ba a sako masa 'ya da tsohon ciki, ba ta yi yunk'urin hanawa ba tunda ita kan ta za ta so ta koma d'in, haka ko akayi bayan sallah magriba anyi katari malam ya na gidan mahaifin Haseenah ya sallama ya fito, da ganin shi malam ya tarbe shi yanda ya kamata ya shinfid'a mu su tabarma a waje su ka zauna, nan fa malam *Mussa* ya fad'awa malam abin da ke faruwa, sosai malam ya jinjina ya kuma fad'a mi shi baisan me ke faruwa ba sai yanzu, amma ya yi alk'awarin tuntub'ar Fodio yaji dalilin yin hakan, nan dai ya kwantar masa da hankali suka rabu lafiya, malam kam baiyi k'asa a gwiwa ba wajen kiran Usman yace ya same shi gida, ana idar da sallah isha'i ya k'araso ya samu malam, a cikin gida suka samu waje tare da Hajia suka tattauna sosai sosai, anan ya fad'a mu su cewa "A gaskiya Baba ba zan iya zama da yarinyar nan ba, domin kuwa duk ita ce silar abubuwan da suka dinga faruwa da ni, kawai ku rabu da ita can ta haihu, idan ta haihu zanje na d'auko abinda ta haifa bayan ta shayar da shi dan ba zan iya barin abin da ta haifa a hannunta ba saboda mugun halin ta."
Malam ne yace "Amma duk abin da tayi Fodio bai kamata ka sake ta a wannan halin ba."
Shirun da ya yi yasa Hajia cewa "Koma dai menene ita taja, a gaskiya Hassenah ta bamu mamaki, yarinya sumi-sumi ashe lunbu-lunbu ce macijin k'yaik'ayi, muna ta wa Khadija kallon mai laifi ashe ita ce muguwar."
Murmushin gefen labb'a malam ya yi yace "Ai ni na sani dama *kallon kitse ne ku ke wa rogo*, kawai na zura mu ku ido ne har ita yarinyar ta mu ku ido, in banda hauka irin na ku ma ko gaske ne Khadija ta mallake Usman ai ni a gani na daidai ta yi, domin kuwa in har za mu iya yin magana irin ta jahilai to za mu iya cewa k'ashin arzik'in shi a jikin ta yake, shi ba kyau ba, shi ba hasken fata ba, shi ba kud'i ba a lokacin da ta aure shi, kuga kuwa tana da damar da za ta iya d'aukar kowane mataki dan ya zama na ta."
Cikin sanyin jiki Hajia tace "Gaskiya ne, wallahi sai yanzu na ke jin kunyar ta akan abubuwan da suka faru, daurewa kawai nake ina kallon ta."
Murmushi Usman yayi yace "Hajia ku kwantar da hankalinku in dai Khadija ce na tabbata ba ta kallon ku da wannan abun."
Nan dai suka gama tattaunawarsu kafin ya mu su sallama yace zai tafi asibiti, su kuma dama acan su ka yi sallah magriba, ba su jima da dawowa ba Abban Haseenah ya zo, daga nan asibiti ya nufa ya samu kam kamar ana wata sabga d'akin taf da mutane, Khadija dake zaune kusan Bilal muryar shi ce ta fallasa mi shi yanayin da yake ciki, duk sai taji ba dad'i tausayin shi ya kamata, gaisawa ya yi da mutanen dake d'akin kafin ya isa a gadon Bilal, kafe Khadija ya yi da ido yace "Nana ya mai jikin?"
Saida ta had'e abin da ya tokare mata mak'oshi ta kalle shi da murmushi ta sa hannu ta karb'i k'atuwar ledar hannun shi ta aje gefe tace "Mai jiki gashi nan da sauk'i."
"To Allah ya bashi lafiya." Ya fad'a ya gyara tsayuwarsa, sake d'agowa ta yi ta kalle shi, saida ta k'are masa kallo tace "Babban mutum ka ci abinci kuwa?"
Wani murmushin gefen labb'a kawai ya yi bai bata amsa ba, duk da zuciyarta na raya mata wani abun amma kuma k'wak'walwarta na hasko mata wani abun, kawai anfani tayi da abin da k'walwarta ke hasko mata ta kalle shi ta mik'e tsaye tace "Ina ga mu tafi gida kawai, ga Mama nan za su kwana a wajen shi."
Da mamaki ya kalle ta ya kuma juya ya kalli Mama, mama ce tace "Kuje kawai zan zauna wajen shi, ai ni ce ke daidai dama na tsaya tare da shi tunda d'an gudaliyar mijin ne."
Murmushi su ka yi kafin Usman ya fara fita ita kuma ta had'a kayanta ta same shi a mota, kallonta ya yi yace "Wane gidan zan kai ki?"
Dariya ta yi tana kallon shi tace "Gidan miji na mana, ko ka manta yau ne zan dawo dama?"
Lumshe ido ya yi ya kwantar da kanshi jikin kujerar motar, d'agowa ya yi ya kalle ta yace "Khadija Allah ya miki albarka, kamar kinsan ina buk'atar kulawar ki, Khadija duk duniyar nan ke kad'ai ce macen da ta iyani."
Da murmushi a fuskarta tace "Muje to ka min wanka ka canza min kaya, sannan na sama mana abun da za mu ci sai muyi bacci."
Wata harara ya dallo mata yace "Baccin lafiya? Yau fa kamar amarya ki ke."
Dariya ta sake yi tace "To mu samu muje gidan ko." Tayar da motar ya yi su ka d'auki hanya, saida ya tsaya ya siya musu sandwichs a hanya kafin suka wuce gida, tare suka shiga wanka suka shirya cikin kayan bacci kafin suka d'an sama cikin su sandwich d'in nan, sam Khadija ta manta ma da maganar wata wai Haseenah, hakan yasa ba ta tambaye ta, shiru d'akin ya d'auka saida Khadija ta juyo in da Usman ke kwance, zaune ya ke akan gadon ya tangale bayan shi da pilow damuwa b'aro-b'aro a fuskar shi, tashi ta yi zaune ta matsa kusan shi ta d'ora hannun ta akan k'irjin shi tare da d'ora kanta a kafad'ar shi, gyara mata zaman ya yi ta yanda yake shafar kanta a hankali, cikin taushin murya tace "Bilal ka ke tunani ko?"
Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba sai kuma ya sauke ajiyar zuciya yace "Hakane, muna kwana nesa da Bilal a lokacin da ya kwana gidan su Hajia ko gidan su Mama, amma ban tab'a tunanin akwai ranar da za ta zo ba ina kwance kan gado na cikin sanyi shi kuma ya na kwance a gadon asibiti, ban tab'a tunanin haka ba ko kad'an."
Zunbur ta tashi zaune tana kallon shi tace "Ba ka tab'a tunanin wannan ranar ba? Amma me ya sa? Ko ka manta da mutuwa ne?"
Shiru ya yi ya tsareta da ido, d'orawa tayi da "Abban Bilal, mu gode Allah daya kasance ya na raye mana, da fa ta Allah ta kasance da yanzu ka na kwance akan gadon nan ne shi kuma ya na kwance cikin rami, zanin rufar shi shine k'asa, kaga kuwa sai mu gode Allah a hakan ma."
Murmushi kawai ya yi bai ce mata komai sai kallon ta da yake, matsawa ta yi ta sake lafewa a jikin shi tace "Yau fa dare na ne na farko, kar ka bari tunani da damuwa suyi tasirin hana ka kula da ni da kuma wannan bawan da baisan ma asalin yana da mahaifi ba har yanzu, ka bamu kulawar ka mana na wannan dare, karka damu da Bilal insha Allahu ya na cikin kariyar ubangiji tare da kulawar Mama, zaiji sauk'i."
Dariya ya yi ya matse ta sosai a jikin shi yace "To yanzu me kuke so na fara mu ku, dan dole zansa wannan d'an baban farin ciki yasan cewa yau fa ya shigo hannun shi, amma ina fatan dai kin shirya karb'ar uk'ubata?"
Da mamaki ta kalle shi tace "Ban gane uk'ubar ka ba?" Murmushin mugunta ya mata yace "Nasha wahala sosai kafin ki yarda ki dawo gida na, kin whalar da ni sosai, kin azabtar da ni fiye da tunanin ki, dan haka nima yanzu zan rama a daren nan tunda kin shigo hannu na."
Zabura ta yi ta na neman durkuwo daga kan gadon ya yi saurin rik'o ta yana fad'in "Ai ba ki isa wallahi, ina ki ke tunanin za ki je a daren nan? Daga ni sai ke fa a gidan."
Kukan shagwab'a ta saka mi shi tana zillewa tana fad'in "Allah bar ma gidan ka zanyi, ciki na fa k'arami ne, so ka ke min asarar shi bayan 'yan uwan ka har tsegumi suka fara min saboda ban k'ara haihuwa ba, Allah ni dai ka rabu da ni."
Sosai ya rumgume ta yace "Mak'aryaciya kawai, na fa san komai, cikin ki ya kusa shiga wata shida, a hakanne zan zubar da shi?"
"Ni dai ka sake ni na koma d'aki na kawai tunda mugunta za ka min." Ta fad'a ta na son raba kanta da shi, ya rik'e ta sosai ya rad'a mata a kunne "Na mi ki alk'awarin tafiyar da ke a hankali, abinci kawai zan baku cike da k'aunar ku."
D'ago kai ta yi ta kalle shi tace "Na ga idon ka idan gaskiya ka ke fad'a." Da sauri ya sa tafukan hannayen shi ya rufe fuska ya juya mata baya yace "Um um, ban yarda ba gaskiya."
Cakulkuli ta fara masa ta na fad'in "Ashe ba gaskiya ka fad'a ba, yeee Allah ya tona min kai."
Da irin haka suka tafiyar da daren su cike da kewar juna, bayan komai ya kammala ma alwala su ka yi Usman na gaba ita a bayan shi su ka yi k'iyamun-laili, ana kiran sallah farko ya nufi masallaci ita kuma ta mayar da sallahnta, daga nan kan darduma bacci ya d'auke ta, ko da ya dawo ya ganta d'aukar ta ya yi ya kwantar akan gado, makullin mota ya d'auka ya fita ya samo mu su abin karyawa ya aje kafin ya shirya ya fita zuwa asibiti, duk lokacin Dije na bacci bata farka ba, ya jima a asibiti tare da Mama da malam da Hajia suna ta hira kafin ya baro asibitin, gida ya dawo kai tsaye ya samu Khadija zaune akan teburin cin abinci ta na zubawa za ta ci, k'arasowa ya yi ya zauna yace "Dijangala tame gari, Dije sarkin hutu har an tashi kenan?"
Murmushi kawai ta yi tace "Na tashi, amma kuma saina nemi mijina na rasa in da ya shiga, kad'an ya rage na bayar da sanarwa a gidan radio sau kuma ga ka."
Cikin dariya yace "Allah ya na son ki da rahama shi ya sa ba ki yi asarar kud'in ki ba."
Zaune ta yi ta na aje farantin abincin gaban shi tace "Kuma na yi sa'a miji na ya na iya jiyo bugun zuciya ta daga duk in da yake, hakan ma ya taimaka wajen dawowar ka kusa da ni."
Hannu suka saka tare, kafin ta kai loma bakin ta tace "Wai ina Haseenah ne? Ba za ta fito cin abincin ba?"
Jim ya d'anyi kafin yace "Bata nan." Ba tare da damuwa ba tace "Ok, ko ta tafi asibiti ne awo?"
Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba sai kuma yace "Ta na gidan su." Kallon shi ta yi tace "Gidan su kuma? Lafiya dai ko?"
Cike da jin an takura shi yace "Kai Khadija, ta na gidan su na ce mana, sakin ta na yi."
Dam, taji gaban ta ya fad'i, tabbas tasan ba su yi zaman lafiya da Haseenah ba, kuma ta na kishinta sosai ta na kuma ji haushin irin cutar da ta mata, amma hakan ba shi zaisa ta yi farin ciki da mutuwar auren ta ba, abu d'aya da ta sani shine ita ma mace ce kamar ita, tasan dole wannan kalmar ta girgiza tunanin ta, abun duba kuma anan shine cikin da ke jikin ta, in har za ta iya fad'an gaskiya to duk abin da ta yi ya kamata ace an mata uzuri, dan ko ita ce ba ta san irin damuwar da za ta shiga ba idan aka ce haka ta faru da ita, bare Haseenah da ko wata takwas ba ta yi ba a gidan miji amma ace an sake ta da cikin fari a jiki, a hankali ta kalle shi tace "Amma Abban Bilal zan iya cewa wani abu?"
Ba tare da ya kalle ta ba yace "In dai akan wannan yarinyar ce ba buk'ata, hukunci ne kuma na yanke, zan kula da komai daga yanzu har lokacin da za ta haihu, idan ta haihu kuma ta gama shayar da abin da ta haifa zan d'auko shi na dawo da shi kusa da ni, nasan banda matsala wajen samun wanda zai rik'e shi, ko ke za ki yi min wannan karamcin."
Wani mamakin ne ya sake bayyana a fuskar ta ta na kallon shi, ganin haka ya sa ya mik'e yace "Ni zan fita waje, idan kin gama ki same ni saina aje ki asibiti."
Da kallo kawai ta bishi har ya fita, ji ta yi abincin ya fita a ran ta ita ma sai kawai ta tattara ta shiga da shi madafa, juyewa ta yi a kwano ta fito da shi ta bawa Rabe, godiya ya mata kafin ta samu Usman suka wuce, babu mai magana har suka isa asibiti ya aje ta a bakin k'ofar, saida ta fito ta rufe k'ofar ta kalle shi tace "Allah ya kiyaye hanya, sai ka dawo."
Kallon ta ya yi yace "Ameen, Allah ya sa." Da haka ta shiga ciki shi la ya wuce, sosai ta yi farin cikin ganin Bilal a zaune ya na shan koko mai d'umi, godiya ta yi ga Allah da ya sa yaron ta ya rayu kula har za ka iya cewa ma jikin shi da sauk'i fiy da jiya da ba za ka ce ya na raye ba, sai dai fatan Allah ya k'ara mi shi lafiya mai anfani.
Haka su ka ci gaba da jinyar Bilal cike da kulawa, in da aka d'auke shi daga gidan gaggawa aka mayar da shi cikin asibitin, kullum 'yan uwa su na zirganiya a hanyar asibiti ganin Bilal, Khadija kuma da Usee suna farin ciki idan suka koma gida, har yanzu ba ta sake mi shi maganar Haseenah ba amma abun na damunta sosai, kullum tana auna hakan da kanta ta na ganin idan ita ce ya za ta yi? Ta na so ta sake mi shi magana amma da ta yi magana da Hajia sai tace kawai ta share ta kar ma tasa ran shi ya b'ace akan wata, shi ya sa ta d'anyi shiru amma ba wai ta hak'ura bane, dan abin da take tunani ba kowa bane ke tunanin shi, a haka suka kwashe *sati d'aya* a asibiti.
*Kwana goma sha d'aya* aka sallami Bilal saboda jikin shi ya yi sauk'i sosai cikin hukuncin ubangiji, a lokacin kuma Haseenah rayuwa ta fara gara ta yanda take so...
*Allah ka sa mu dace.*
13/03/2020 à 14:14 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
```Fatan alkairi masoya```
_Bismillahir rahamanir rahim_
*39*
Sabo da jar miya da cin abin da rai ke so ya sa Haseenah ba ta iya cin abincin gidan su, da yake ta na da 'yan kud'in da ta samu hannun Usman sai take anfani da su wajen siyan abin da take so, sannu-sannu kuma sai k'annan ta suka fara d'ora mata raini ta yanda ko aikensu ta yi ba sa zuwa, da k'yar wani lokacin za ta basu kud'i su tafi, wani lokacin kuma sai dai ta tafi da kanta ta siyo dan abu mai galmi da yaji, gaba d'aya a takure take jin kanta a zaman gidan nan, d'akin da suke kwana ita da k'annan su ga zafi ga rashin sarari, yau dai data tashi ta d'auko jakar yan kud'in ta da nufin siyo abin kari sai kud'i suka ce nemi in da ki ka aje, nan ta yi haukan nema amma ba ta gani ba, ta tambaya maman ta kuma tace to ita ina za ta sani, kuma ba kowa gidan sai su duk sauran su na makaranta, dole d'umamen tuwon da aka yi shi ta dank'ara tasha ruwa, ruwa ta kai ta d'auki kwandon sabulu dan yin wanka, amma sabulun sai kad'an ya rage wanda ba zai mata komai ba, cikin jin haushi ta kalli maman ta tace "Mama, wai yanzu shi ma sabulun da na saka saida wani ya d'auka?"
Cikin sanyin hali tsohuwar tace "To Haseenah ba sai ki yi hak'uri ba, da kina gidan ki nan kowa ke wadace da sabulun, sun d'an saba ne da wanka da mai k'amshin shi ya sa da su ka ga naki su ka d'auke."
"To amma Mama ni fa kad'an ne na taho da shi sabulun, yanzu haka ina ga bai wuce uku ba wanda ya yi saura, idan ya k'are sai mu yi ya kenan?" Duk ta yi maganar ne kamar za ta fashe da kuka, a tak'aice tace "Sai ku taru ku hak'ura."
Tsaki ta yi ta shiga d'aki ta d'auko wani ta saka ta shiga ban d'akin, wanka ta yi ta fito ta shirya cikin doguwar riga, tsakar gidan ta fito ta d'auki waya da nufin shiga yanar gizo, sai dai ina babu sadarwar ta k'are kuma babu kud'i a wayar, kallon ta maman ta tayi tace "Haseenah, wai har yanzu mijin ki bai kira ba?"
Cikin takaici tace "Mama bai kira ba, dama ai ba kira na zaiyi ba."
"Kuma ke ba ki tab'a jaraba kiran shi ba ko?" Kallon maman ta tayi tace "Mama taya ni zan kira shi, ai ba d'auka zaiyi ba." Shiru kawai tsohuwar ta yi sai Haseenah da ta shiga duniyar tunani, sai lokacin ma ta tuna da waccen ranar da ya sake ta yace Bilal na asibiti kwance a dalilin ta, to me ya samu Bilal d'in? Ta tambayi kanta, kallon maman ta tayi tace "Mama."
"Um." Ta fad'a ta na kallon ta, cikin taushin murya tace "Mama me zai hana ke da Baba kuje ku dibo jikin Bilal?"
Sake kafe ta da ido ta yi tace " Bilal kuma? D'an Usman d'in?" Ita ma ta na kallon ta tace "Eh mama."
"Dama ba shi da lafiya amma ba ki fad'a ba sai yanzu?" Shiru ta yi ta na sosa kai, tsaki ta yi tace "Allah ya kyauta, Haseenah ko ba ku yi zaman mutumci da matar shi ba ai ina ga dai kya fad'a aje a duba shi ko dan awa Usman kara, ke da shi fa yanzu wata alak'a ce mai k'arfi ta shiga tsakanin ku, ki daina ganin ya sake ki hakan ba shi zai ruguza alak'ar ba."
Da rana bayan Baban su ya shigo mahaifiyar su ta fad'a mi shi ta na so taje ta duba jikin Bilal, da yake dama matar ta fi shi hankali da hangen nesa shi ya sa yaran ma suka fi shakkar uwar akan uban, sai kawai yace ai babu mutumci tsakanin su da Khadija, 'yar su na gida ne saboda ita dan haka babu in da za ta je, nan ta nuna mi shi ba saboda Khadija zata je ba saboda Usman za su je, d'an shi na asibiti kwance ya na da kyau suje ganin shi, ai kuwa bai bari ta tafi ba dan sosai ya rufe ido shi bai yarda ba, haka ta hak'ura ba dan ranta ya mata dad'i ba.
A wajen su Khadija kuma jikin Bilal da dama sosai, suna zaune tare da shi ya d'ora kan shi a k'afafun Mama su na hira, Mama ce tace "Wai ni kam banji motsin abokiyar zaman taki ba, ko bata nan ne?"
Sai lokacin Khadija ta iya tuna bata fad'awa Mama ba, da sauri tace "Kai, Mama ashe baki sani ba ko? Wallahi bata nan gidan tunda na dawo."
Mamaki fa a fuskar Mama tace "Bata gidan, to meya faru? In ce dai lafiya?"
Cike da damuwa Khadija tace "Mama yace sakin ta ya yi, kuma na so yi masa magana amma ya nuna kawai babu ruwa na, sannan na yi magana da Hajia ita ma tace wai na fita harkar ta, sai dai ni gaskiya banji dad'i ba mama saboda ganin halin da take ciki abar a tausaya mata ce."
Cike da jimami Mama tace "Ah sosai ma, komai ai hak'uri ake yi ba a yanke hukunci cikin hushi ba."
Tab'e baki Khadija ta yi tace "Mama kullum tunani na shine idan ni ce ya zanyi? Abun baya min dad'i ko kad'an, amma tunda ya nuna baya so na rabu da sh."
"A'a Khadija." Cewar Mama ta katseta kafin ta d'ora da "Duk da baya so ke ya mata kisan hanyar da za ki shawo kan shi cikin hikima, na sani Khadija kishiya babu dad'i, kuma burin kowace mace ta zauna ita kad'ai a gidan mijin ta, amma ina so ke ki zama ta daban a cikin mata, Khadija idan kika zama silar dawowar ta to kin saka mata alkairi da sharrin da ta mi ki, wannan kuma shine nagarcin addinin ki, yafiya, mantawa, kyautatawa, kinji ko Nana Khadija, ki yi wannan jarumtar ko da baya so, amma idan kinga abun zai zama matsala to sai ki barshi kawai."
Da murmushi tace "Insha Allahu Mama zanyi, nima dama na so tun farko na yi hakan, amma yanzu kin k'ara k'arfafa min gwiwa, tunda ko ba komai sun ruga da sun zama d'aya shi da ita tunda ta na d'auke da cikin shi, rabuwar kuma ba dad'i musamman ita da k'ananan shekaru."
"Gaskiya kam, dan hakan zai iya zama tozarci gare ta da b'ata mata suna."
Cikin nutsuwa Khadija tace "Mama ba lallai ma a kalle ta da laifi ba, ni ba zan fita daga zargi ba tunda dama ana ganin na mallake shi, kinga yanzu za'a ce ni ce na fitar da ita daga gidan, babu wanda zai tuna lokacin da ni na d'auka a na mu gidan gaban iyaye na, nata ne yanzu zai fito fili kowa ya ji."
Cike da gamsuwa mama tace "Gaskiya ne kam, dan ko ansan kin zauna a gidan ma za'a d'auka kishin ki ne ya tura ki gidan, mutum, mutum ai sai Allah."
Murmushi Khadija ta yi tace " *Mutum mugun ice, ya mutu ma fa sai an d'aure shi Mama.*"Dariya Mama ta yi kafin suka ci gaba da tattaunawa.
Washe gari da safe ma daga Haseenah sai maman ta a gidan duk kowa ya tafi harkar gaban shi, rana ta fito sosai Mariya ta shigo d'auke da kaya da alaman sabuwar d'auka ce ta yi, gaisawa su ka yi sosai har ta fara hira da maman ta akan kasuwancin na ta, sun jima nan kafin maman su ta tashi ta shiga d'akin su dan yin wani abun, Haseenah na ganin haka tace "Aunty Mariya, muje d'aki ina son magana da ke."
Cikin rad'a tace "To lafiya dai ko?" Saida ta mik'e ta nufi d'akin tace "Ki zo kiji ke dai."
Mik'ewa ta yi ta na fad'in "To na ji alkairi." Suna shiga bakin katifa suka zauna Haseenah ta tsareta da ido tace "Aunty Mariya, na d'auka abin da ya faru da ni za ki taimaka min wajen ganin na koma gidan Usman, amma ke ko a jikin ki ma sai harkokin gaban ki kike."
Cewar Mariya "To me zanyi in ba harkokin gabana ba, sannan wane irin taimako ki ke buk'ata daga gare ni yanzun?"
A daidai lokacin da Haseenah za ta yi magana a lokacin mahaifiyar su ta fito daga nata d'akin, za ta wuce ne taji Haseenah tace "Ki yi wani abu mana na koma gidan shi, Ko so ki ke na haihu gida?"
Kallonta Mariya ta yi tace "Na yi me? Me ki ke nufi? Wai na sake komawa wajen malam? Sam wallahi ba da ni ba, ai na fad'a mi ki tun ranar Haseenah gaskiya ba zan iya binki mu tsunduma kogin da ki ke neman jefa mu a ciki ba, idan na yi haka to fa nan gaba ba naki auren bane zai mutu har da nawa."
Wani kallo Haseenah ke mata amma ba tace komai ba, d'orawa ta yi da "Kinga k'anwa ta, ki yi hak'uri da abin da ya sameki ki rugumi k'addara, sakin aure ba'a kan ki aka fara ba bare ya k'are kan ki, yanzu idan mu ka ce zamu matsanta sosai to wallahi abubuwa ba za su yi kyau ba, dan ko da an sake juyar mi shi da tunani ya dawo kan ki wallahi ranar da ya sake dawowa hankalin shi a karo na biyu to fa zai sake koroki ne, dan haka abin da yafi kawai ki tuba ga Allah tare da rainon cikin ki har ki haihu, domin Allah fa kin cutar da su sosai, kin raba shi da matar shi, kinsa dangi suna mata kallon marar imani kuma mai laifi, alhalin kuma ke ce mai laifin, ke ba ma dangin shi ba kad'ai har dangin har yanzu suna kallon Khadija a matsayin wacce tasa aka sake ki, alhalin kuma duka mutane *kallon kitse su ke wa rogo*, ke da ake gani ba ruwanki ke ce kuma gubar."
Cikin jin haushi Haseenah tace "Ni ce ma gubar? To idan ni guba ce ke kuma fa? Ai ke ce babbar guba tunda ke ki ka haddasa komai, ina zamana lafiya ban tab'a tunanin wacece matar shi ba, amma ke ki ka zo min da labarin cewa matar shi yar duniya ce ta mallake shi, sannan waya kai ni wajen malam in ba ke ba, wa yake zuwa har gida na ya na karb'o kud'in da ake kaiwa malam d'in? Ai ke ce da kan ki, amma shine yanzu za ki kira ni da guba, to ke ce babbar guba ba ni ba wallahi."
Tab'e baki Mariya ta yi a ran ta tace "Sakarya kawai." A fili kuma cewa ta yi "Wannan kuma ke ta shafa, ni kinga tafiya ta sai anjima." Ta na fad'a ta mik'e za ta fita sai ga mahaifiyar su ta shigo d'akin dan kaf babu abin da bata ji ba, baya ta rumgume hannaye ta na kallonsu cike da haushi kafin tace "Abin da ku ka aikata kenan? Mariya, Haseenah, wannan ita ce tarbiyyar da mu ka baku a gidan nan? Wannan wane irin zubar da mutumci ne? Kenan mutuwar auren ki ba ya da nasaba da kishiyar ki? Haka kawai kinsa muna kallon ta a matsayin mai laifi, to rashin lafiyar da muke tunanin ki na fama da ita fa har da nemo mi ki magani? Ko dai duk k'arya ce ki ke? Dan babu yanda za ayi mata biyu a gidan miji d'aya su zama mushrikai."
Sosa kai Haseenah take cikin rashin abin fad'a sai tsohuwar ce ta k'ara da "Ko ba ki fad'a ba ya nuna ba ki da gaskiya, amma Haseenah taya ki ka iya shirya makirci irin haka? Ko ni da na haife ki ba zanyi abin da ki kai ba."
Kallon Mariya ta yi sama da k'asa tace "Babbar banza, yanzu idan akwai wanda ya kashe mata aure ai bayanki ya ke."
K'asa ta yi da kanta sosai hakan ya sa tsohuwar juyawa ta fita ta barsu, cikin sanyin jiki Mariya ta fita sai Haseenah da ta fashe da kuka, *Asiya* kuma d'akin ta ta koma ta shirya saida ta fito za ta fita ta lek'a d'akin Haseenah tace "Zan fita yanzu, babu kowa a gidan ki fito ki d'ora girkin rana kafin yaran nan su dawo, daga yau kin bar kwanciya a d'aki da sunan wai ki na da ciki a tausaya mi ki, girki da wanke-wanke ya zama na ki."
Ta na fad'a ta fice abin da har zuwa bakin ti-ti ta samu adaidaita ta hau, kai tsaye gidan Khadija ta isa, duk da ba sosai Khadija tasan ba amma dai ta gane ta, sosai ta tarbe ta kamar za ta had'e ta cikin girmamawa, dama kuma in dai ta wannan fannin ne Khadija gwana ce, hakan ya sa ma take da farin jinin al'uma, har d'akin Bilal ta rakata taga jikin shi kafin su ka dawo falo ta zauna, cike da dattako tsohuwar ta kalli Khadija tace " 'Yata Khadija, na zo ne ganin jikin yaron ki da sai jiya na ke jin bai da lafiya, sai kuma abu na biyu na zo na baki hak'uri akan abin da ya faru, 'yar nan wallahi ba mu tab'a tunanin Haseenah za ta iya cutar da wani ba, amma sai yau kuma yanzu na ke jin irin ta'asar da su ka yi ita da 'yar uwar ta daga bakin su, hak'ik'a yau Allah ya wanke ki daga zargin da mu ke mi ki, muna kallon ki a matsayin wacce take hana 'yar mu zaman gidan aure, ashe ba haka bane komai makircin su ne, ashe har zuwa gidan da take ta nuna bata lafiya ba ta son zaman gidan duk k'arya ne, kawai d'ora mi ki laifi ne suke son yi, dan Allah ki yi hak'uri ki yafe mana kinji 'yar albarka."
Khadija da ta yi jim ta na jinjina al'amarin Haseenah, sai yanzu ne take sanin wannan labarin na rashin lafiya, kenan ita ake kallo da wannan laifin ma, murmushi ta yi ta rik'o hannun Asiya tace "Mama, ke fa uwar ce a gare ni, yanda Mama na bata neman gafara na akan duk abin da za ta min to haka ke ma, wallahi na yafe mu ku dukan ku, ni dama ban tab'a rik'e kowa a zuciya ta ba saboda ina so nima Allah ya kalle ni da idon rahama, dan haka ku kwantar da hankalin ku yanzu mun zama d'aya ni da ku, kuma ita rayuwa dama haka take, wanda wautar shi ta fito fili shi ake kamawa da laifi, wanda kuma ya iya takon shi to ko shine mai laifin sai kaga babu mai gani bare ayi magana, kuma ita dama ance *fahimta fuska* ce."
"Hakane kam, Allah ya mi ki albarka, Allah ya sa ki gama da duniya lafiya, Allah ya kare ki daga sharrin abokan zama irin su Haseenah." Sakin hannun ta Khadija ta yi ta mik'e tace "Ni zan tafi, dama ko mahaifinsu bai san na zo ba."
D'aki Khadija ta shiga ta tarkato kaya sabulu da turaruka da turmin atamfa mai kyau, sannan ta had'o da wani k'aton mayafi da ita bai birge ta ba tunda mama ta siyo mata shi daga Dubai, haka ta had'a tsohuwar nan da su ta rakata har k'ofar gida, Rabe da ke zaune tace ya d'aukar mata kayan har saida ta samu adaidaita, Asiya kam a adaidaita har kuka ta yi ganin irin alherin da Khadija ta yi mata, ta na komawa gida ta samu mahaifinsu ya dawo zaune a tsakar gidan, tun bata gama shigowa ba yace "Daga ina ki ke Asiya?"
Kai tsaye tace "Daga gidan Usman."
Da sauri ya kalle ta haka ma Haseenah da ke bakin murhu ta na girki duk ta yi gumi, cikin hushi yace "Yanzu da na ce kar ki jr shine ki ka wanke k'afa ki ka tafi ba da izini na ba? Asiya yaushe ki ka fara yin watsi da maganata? Akan matar da ta kashe ma yar ki aure ne za ki wulak'anta ni haka?"
Abun da bai tab'a faruwa ba shine yau ya faru, cikin d'aga murya tace "A'a malam, kar ka sake ganin laifin ta akan zunubin da 'yarka ce ta aikata shi, wannan yarinyar babu abin da ta aikata, kaga mai laifin nan gaban ka." Ta fad'a ta na nuna Haseenah wacce ta yi k'asa da kan ta, a tausashe yace "Me ki ke nufi da ba ita ce mai laifi ba Haseenah ce?"
Kujerar katako ta janyo ta zauna kusa da shi ta aje jakar hannunta gaban shi, nan ta zayyane mi shi duk abin da taji sun tattauna da kuma zuwanta gidan Khadija yanzu, cikin b'acin rai ya d'auki takalman shi ya tilk'awa Haseenah a baya gashi kam ba ta san da saukar takalman ba, ji ka ke timmm a bayan ta, k'ara ta saki ta dafe baya ganin ya d'auki d'aya takalman ya sa ta shura a guje d'aki, masifa ya dinga zazzagawa takaicin shi kud'in da ya kashe wajen amso mata magani, zagi ya dinga aika mata a d'akin ya na yi ya na kallon kayan da Khadija ta bado.
*Daga ranar* komai ya k'ara canzawa Haseenah, kaf gidan yanzu babu mai kallon ta da mutumci, girki da wanke-wanke ko ga yara a gidan ita ce ke yi, wani lokacin ma mahaifin su har kayan shi ya ke bata ta wanke mi shi, duk a ganinsu horon da za su iya yi mata kenan da zaisa ta shiga hankalinta, wani abu dake damun Haseenah sosai shine rainin da duka k'annan ta suka aza mata, ko kallon su ta yi sai ka ga wata ta kwad'a mata harara, haka kullum take cikin fad'a ita da k'annan ta, ga ciki na ta girma sosai ga kuma rashin kud'i, idan ta tafi awo kad'ai take jin dad'i duk da rashin kud'i ya sa ta canza asibiti, yanzu haka ta na awo ne a asibitin da ke kusa da su asibitin *Ali Chaibu*, a haka ta yi laushi sosai take k'ara nadamar abin da ta yi, gashi Usman ko kiran ta bai tab'a yi ba bai kuma tab'a zuwa ba da sunan ya ganta, ya je sau biyu amma wajen mahaifin ta ya tambayi komai lafiya suka gaisa ya tafi, sai dai duk sati biyu yakan aiko Bilyamin ya kawo mu su kayan abinci da kud'i saboda bebyn shi, har yanzu babu abin da ya rage daga jikin ta na k'iba da ta yi, sai dai fatar ta ta canza sosai ba kamar da ta na gidan ta ba, dan kuwa duk kayan da zai aiko iyayen ta sukan zama na anfanin duka gidan ne, kud'i kuma sai in za ta tafi asibiti ake bata wanda basu taka kara sun karya ba.
Duk lokacin nan da aka d'auka a wajen Khadija ita ma ta matsa lamba sosai kullum maganar Haseenah take wa Usman, ta yi rarrashin duniya ta yi kissar ta yi nisihar amma ya mayar da ita kamar mahaukaciya, akan maganar nan har fad'a su ka yi suka daina magana tsawon kwana uku, saida Bilal ya shirya su kad'ai suka koma magana, amma fa ba ta daina mi shi maganar ba, har tsawa ya mata ya zare mata ido yace idan ta na da zuciya ta daina mi shi maganar Haseenah amma tace ba ta da zuciya in dai akan maganar nan ne, haka kawai take jin zuciyar ta na yin sanyi kullum take son ganin ta dawo gidan ta, ta fad'a mi shi ya sake bata dama ta biyu mana tunda 'yar adam ce ita, amma abun baiyi tasiri ba, har Bilal ta sa ya rok'e shi take yace ya fita a harkar manya ba ruwan shi, izuwa yanzu kanta ya yi zafi akan maganar, hakan ya sa ta samu malam ta kalallame shi sosai, kuma ta yi sa'a ya gamsu da abin da ta fad'a sosai, alk'awari ya mata zan mi shi magana, kuma kamar yanda ya fad'a ya wa Usman magana, amma sai yace shi fa in aka sake matsa mi shi to zai bar mu su garin ita ma Khadijar ta koma gidan su, wannan magana ita tasa malam cewa "A'a Fodio, me ya yi zafi haka, Allah ya huci zuciyar ka, shikenan tunda ba ka so ai."
Cikin b'acin rai yace "Baba Khadija hankali ne bai ishe ta ba, in ba haka ba yarinyar da ta cutar da ita da ni da ku ma amma wai ta dage kai da fata sai an dawo da ita, to tsiyar me za ta mana idan ta dawo?"
Malam dai cewa ya yi "Yi hak'uri to shikenan, zam fad'a mata ta yi hak'uri kawai a bar maganar, Allah ya sa haka shi yafi zama alkairi."
Malam da kan shi yaje har gidan ya fad'awa Khadija dan Allah ta manta da maganar Haseenah ta kula da mijin ta kawai, ba dan haka ta so ba ta nuna shikenan ya wuce, saida malam ya fad'a mata yace idan an sake takura shi fa zai bar gari ne, kai kawai ta gyad'a alamar taji, da dare ko da Usman ya shigo ya na zaune a falon ta tare da Bilal suna kallo Khadija ta fito da kinkimemiyar akwati da cikin ta masha Allah ya fito sosai, saida ta zo gaban shi ta tsaya tace "Malam ni zan tafi gidan mu tunda ka kasa min alfarma d'aya, idan na haihu nima ka zo ka d'auki abin da aka haifa."
D'auke kan shi ya yi daga kallon ta ya na kallon telebijin kamar bai san ta na yi ba, juyawa ta yi da jakar Bilal ya zabura zai tashi Usman ya rik'e shi ya fad'a jikin shi, cikin kunne ya rad'a mi shi "Bari kaga yanda zanyi da ita, ko k'ofar gida ba za ta je ba."
Har ta kai bakin k'ofa amma ba ta ji ana tsayar da ita ba, juyowa ta yi ta kalle shi ta tsaya cak, cikin d'aure fuska ya sa hannu aljihu yace "Kai na manta, zo karb'i kud'in adaidaita mana."
Lalaba aljihu ya ke kafin yace "Hajia banda canji, karb'i makullin mota ta ki tafi da ita gobe zan je na d'auko."
Ya k'arashe maganar da jefa mata makullin gabanta, haushi ne ya kamata sosai ta d'auki makullin ta juya ta fita, a hankali take tafiya da tunanin ko zai zo ya hanata amma shiru, k'wafa ta yi ta juyo da sauri cikin jin haushi ta dawo falon, zaune ta same shi yanda suke hankali kwance suke kallo, da sauri ta k'araso wajen shi ta d'auki akwatin dama ba komai ciki ta jefa mi shi a jiki tana fad'in "Hamago kawai, kenan dama so ka ke na tafi na bar ma ka gidan saboda ka gaji da ni ko? To babu in da zanje wallahi mutu ka raba ni da kai, sai na yi takabarka da yardar Allah."
Tunda ta fara magana Usman ke dariya har da d'aga k'afafu ya na rik'e ciki, d'auke akwarin Bilal ya yi ya shiga d'akin ta da shi, Usman na ganin haka ya fizgota ta fad'a jikin shi ya rumgume ta yace "Ke a haukanki kin d'auka zan zauna hakane har ki bar gidan nan? Ai kafin ki isa gida zansa a sato min ke a dawo da ke."
Cikin kukan shagwab'a ta kalke shi tace "Abban Bilal dan Allah kayi hak'uri ka dawo da ita, wallahi tausayi take bani sosai inna tuna rayuwar da take, wannan ita kad'ai ce alfarmar da na ke nema a gurin ka, ka taimaka ka dawo da ita gidan nan mana ta haihu gidan mijin ta, kullum ina aunata da kaina sai naga idan ni ce ya zanyi ace zan haihu gidan mu, babu dad'i ko kad'an wallahi, dan Allah babban mutum ka taimaka mata kaji, na maka alk'awarin za mu zauna lafiya da yardar Allah."
Tun tana magana ya mayar da kallon shi ga telbijin, saida ta gama ya kalle ta yace "Khadija me ya sa ki ke son takura min akan magana d'aya? Me zaisa ba za ki bar maganar ba tunda har na ce ba na so? Me ta mi ki a rayuwa na alkairi da har ki ke son dawo da ita cikin rayuwar mu?"
Cikin muryar tausayi tace "Wallahi babu komai, na dai fad'a ma ka dalili na kawai, Abban Bilal shekara nawa mu ka d'auka muna neman haihuwa, amma zuwan Haseenah gidan nan sai gashi Allah ya azurtani da nawa cikin nima, watak'ila hakan ya faru ne saboda hak'urin da mu ka yi da kuma tsarkake zuciya ta da na yi wajen zama da ita, ba ka tunanin yanzu idan na sa ka dawo da ita Allah ya sake mana wata rahamar ta hanyar da ba mu yi tsammani ba?"
Ganin ya yi shiru alamun maganganunta na ratsa shi ya sa tace "Za ka iya tuna a cikin karatun da ka ke koya mana kai ka bamu labarin abin da ya faru tsakanin *sayyidi na Abbakar* da *musd'ahu* mai hidima gare su kuma wanda su ke d'aukar nauyin shi, Musd'ahu na d'aya daga cikin wanda suke yayata k'azafin da akawa *Nana Aisha (RA)* cewa ta yi zina, a lokacin da ran sayyidi na Abbakar ya b'aci ya kori Musd'ahu daga gidan shi tare da cewa ba zai sake d'aukar nauyin shi ba, me Allah yace akan haka, Allah ya na son masu yafiya, idan ka yafe kuma sai ka manta da komai, sannan ka k'ara da kyautatawa, to hakanne ya kamata ya faru a yanzu, ka yafe mata gaba d'aya, sannan ka manta da abin da ya faru ka daina tunawa, kyautatawar da za ka mata kuma bai wuce ka dawo da ita d'akin ka ba ta haifi abin da ke cikin ta ba ta kuma raine shi gaban ka, kar kaga ka na keyawa da masoyan ka za su kula maka da d'an da za ta haifa, rik'on yaro sai uwar shi, duk wanda kaga bai rayu da mahaifiyar shi ba dan hakan na mi shi dad'i bane, dan Allah miji na, Usman na Nana, ka saurari matarka mana ka tuna had'uwar ku ta farko da ita da kuma yanda zaman ku ya kasance, saika yanke hukunci."
Shafa kumatun shi ta yi ta d'aga shi zata koma d'aki dan ta bashi damar yin tunani, sumbatar kumatunshi ta yi ta rad'a mi shi a kunne cewa "Kar ka manta Khadija na matuk'ar son ka sosai, kai ne rayuwa ta babban mutum."
Da murmushi kawai ya bita da kallo harta shige d'aki, ya jima nan zaune ya na tunanin abin da ta fad'a mi shi, har ga Allah babu ko k'aunar Haseenah a zuciyar shi bare soyayyarta, amma zai dawo da uta saboda farin cikin Khadija kawai, amma kuma ba yanzu sai ta shiga watan haihuwar ta kad'ai zai dawo da ita, kamar yanda ta sa Khadija zama a gidan su ita ma saita d'and'ana zaman gidan sosai ya ratsata kafin, tashi ya yi ya shiga d'aki saida su ka yi shirin kwanciya kafin ya fad'awa Khadija ya ji zai dawo da ita amma da sharad'i, da sauri tace "Sharad'in me?"
"Zan dawo da ita amma ba yanzu ba, idan hakan ya mi ki to, in kuma bai mi ki ba to abar maganar, sannan zan dawo da ita ne ba dan ina buk'atar zamanta a gida na ba sai dan kin matsa."
Kallonta ya yi yace "Kin yarda?" Da sauri tace "Na yarda Abban Bilal, duk da haka na san ba zaka tauye hakk'in ta ba."
Daga ranar ya samu zaman lafiya Khadija ta daina mi shi magana, haka aka kwashe wasu watannin a lokacin cikin Haseenah ya shiga watan haihuwa, taje asibiti aka bata sati biyu idan bata haihu ba ta koma, a lokacin Khadija da Hajia da Usman da malam suka je gidan su Haseenah biko, abun ya bawa Haseenah kunya sosai ta yanda ta dinga kuka ta na neman gafarar Usman da Khadija, nan iyayen ta ma suka basu hak'uri kafin aka k'ara mata fad'a da nasiha, Khadija da kanta ta tayata had'a kaya dan da tace ma su bari har gobe Khadija tace a'a, tsaf suka had'a kayan suka fito tare da ciki kowace ta na turawa, kayan Usman ya karb'a ya kai mota kafin suka tafi, gida ma saida malam ya sake mu su jan kunne tare da tunatarwa akan zaman aure ibada ne kafin Usman ya mayar da su gida, suna fita Haseenah ta sake fashewa da kuka ta rik'e k'afar Khadija tace "Aunty Khadija ki yi hak'uri ki yafe min dan Allah, wallahi na yi nadamar abin da na aikata."
Kamata Khadija ta yi tace "Haseenah na fad'a mi ki ba komai wallahi, na hak'ura har abada kuma, Allah dai ya k'ara had'a kan mu."
Bilal ne ya fito daga d'aki da riga a hannu ya mik'owa Khadija yace "Mummy taimaka saka min rigar nan, wuyanta matse ni yake."
Da sauri Haseenah ta tara mi shi hannu tace "Kawo na saka ma ka yarima." Bata ya yi ya na kallon mummyn shi a d'ard'ar ya matsa kusa da ita, saida ta saka mi shi ta kalle shi tace "Yarima ka yi hak'uri ka yafewa auntynka kaji, na yi nadamar abin da na yi."
Kallon mummyn shi ya sake yi ta sakar mi shi murmushi hakan ya sa ya rumgume Haseenah yace "Aunty amarya, uwa fa ba ta neman yafiyar 'ya'yan ta."
Kallon shi ta yi tace "To in dai uwa ce ni ai ba aunty ya kamata ka kira ni ba."
Murmushi ya yi sosai ya kalle ta da kunya yace "Mummy." Har zuciya Haseenah taji muryar Bilal ya kira ta da sunan uwa, rumgume shi ta yi take taji wata soyayyar shi ta d'arsu a zuciyar ta, sun jima nan har Usman ya shigo kafin kowa ya nufi na shi d'akin, wani irin sanyi Haseenah taji sai take ji ashe zaman lafiya da wanda Allah ya had'a ka zama da shi dad'i ne da shi, sai taji kamar yau ne aka fara kawota gidan tare da k'udurawa a ranta zata wa Khadija biyayya ko da kuwa za ta zama baiwarta ne hakan ba zai dame ta ba, har ta yi shirin kwanciya Usman ya shigo da doguwar riga yace ta same shi falon Khadija, da to ta amsa mi shi ya fice ko kallon ta baiyi ba, haka ta fito jiki a sanyaye dan tasan yanzu ba mutumcin ta Usman zai gani ba, kuma kamar yanda ya fad'a a gidansu cewa ya fa zo ne saboda Khadija ce ta matsa, to tabbas tasan dawowar nan da ta yi zaman Khadija ne za ta yi, sun samu Khadija zaune da alama su take jira, zaune ya yi kusan Khadija Haseenah kuma cike da kunya ta zauna k'asa, Khadija ce tace ta zauna sama amma tace a'a tafi jin dad'in nan, Usman ne ya gyara murya ya fara magana kamar haka.
"...
15/03/2020 à 23:06 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
_SAMIRA HAROUNA_
*Litattafan marubuciyar*
*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._
*SADAUKARWA GA*
_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*
🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
```Fatan alkairi masoya```
*ALHAMDULILLAH ALA NI'IMATUL ISLAM*
_Bismillahir rahamanir rahim_
*40*
"Haseenah, Allah ya nufa dai akwai sauran zama tsakani na dake, ina fatan abubuwan da suka faru a baya sun koya mi ki wa'azi, Haseenah zan fad'a mi ki wata magana wacce a baya na ke fargaba da shakkun fad'a mi ki, ki yi hak'uri ko da hakan zai b'ata mi ki rai, kinga Khadija da ki ke gani?" Ya fad'a ya na nuna Khadija dake gefen shi, Haseenah dai ta baza kunne ta na saurare, d'orawa da "Ba iya matata ba ce kad'ai, rayuwa ta ce, kuma kin dawo gidan nan ne a dalilin ta, ita ta dage har saida ta ga kin dawo gidan nan, ke na tak'aice mi ki ma har saida ta kai munyi fad'a da ita ko magana ba ma yi saboda ke kawai, Haseenah dan Allah ki tsarkake zuciyarki ku zauna lafiya, Allah kuma ya bani ikon yin adalci a tsakanin ku."
Khadija ce tace "Ameen mijin mu, Abban Bilal da kuma k'annan shi ma su zuwa, mun yarda ka ci gaba da jagorancin mu har zuwa gidan aljanna, mu na da yak'inin ba za mu tab'a yin nadama saboda kai *adalin miji* ne da mu ka yi sa'ar samun shi a wannan zamanin."
Fuskar nan ta Usman kamar gonar audiga haka yake mata murmushi, saida ta kai aya yace "Allah yasa matata, Allah kuma ya sa ba zigani ki ke yi ba dan naga ki na neman fasa min kai."
Dariya ta yi sosai ta mi shi fari da ido tace "A haba dai alaji, ai kasan ba ma haka da kai, duk abin da zai fito daga baki na akan ka gaskiya ne, saima saya wani abun da na ke saboda tsaro."
Kashe mata ido ya yi ita ma kuma haka, Haseenah ta saki baki ta na kallon su, wani zafi taji ya na taso mata a zuciya tare da jin mugun kishi, amma a take ta lumshe ido ta furta a ranta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Allah kasa na fi k'arfin zuciya ta."
Ta na bud'a ido ta kalle su sai taji sanyi tare da jin sauk'in abin da ke ran ta, murmushi ta yi ta na ci gaba da kallon su ta ayyana a ranta in har ta na son zama da Usman dole ta girmama matar shi, sannan ya zama dole ta iya zama da su ta durmiya cikin rayuwar da suke, da k'yar ta mik'e tsaye saboda nauyin da ta yi tace "To sarakan soyayya, ni zan shiga na kwanta, kunsa fa na yi kewar gado na."
Ba Khadija ba har Usman saida ya dara kafin yace "Kenan rayuwar gida babu dad'i ko?"
Turo baki ta d'anyi tace "Babu kam." Jingina ya yi a kujera yace "Dan haka sai kowace ta kama kanta ta, in ba haka ba zan dinga yanka mu ku kati ne ku na tafiya gida ku na hutu."
Kallon shi Khadija ta yi ta kalli Haseenah tace "Idan mutum ya shirya siyan abinci da kwanan kad'aici to ai ko yanzu a shirye muke, dan idan zamu shekara gida ma kaga lafiya lau mu ke kum hankali kwance."
Haseenah ce ta juy tace "Saida safen ku aunty." Da murmushi tace "Allah tashe mu lafiya."
Mik'ewa Usman ya yi yace "Bara na raka ki mai ciki, kar ki je ki zame." Hannun ta ya kama har suk isa falon ta, suna shiga ya saki hannunta har ta shiga uwar d'aka ta kwanta, juyawa ya yi zai fita yace "Ina zuwa."
D'akin Khadija ya je ya mata saida safe kafin ya koma d'akin Haseenah, sam bai wani sakar mata fuska ba har bacci ya d'auke su, dan har ga Allah har yanzu ya na jin haushin ta idan ya tuna baya, kawai babu yanda zaiyi ne Khadija ta tilasta mata ya dawo da ita, kuma tunda ya dawo da ita dole ya sauke hakk'ok'in ta ko kuma ya had'u da fushin ubangiji, Haseenah kuma sam ba ta yi bacci ba saboda sabon ciwon bayan da ya taso mata, tun tana shiru ta na addu'a har ta daddab'a Usman ya farka, nan fa ya rikice saboda ba'a tab'a nak'uda a gaban shi ba, haihuwar Bilal ma baya garin, Khadija ya taso daga bacci ta taimaka mi shi, kayan haihuwar Haseenah na gida ba'a d'auko ba sai Khadija ce ta d'auko nata su ka tafi asibiti da su, saida aka karb'e ta an shiga d'akin haihuwa kad'ai Usman ya kira Hajia ya fad'a mu su, kafin Hajia ta iso Khadija ma ta fara jin bayan ta na d'aurewa tare da rik'ewar mara, a hankali taja baya ta zauna kan bancin da ke wajen, da sauri Usman ya sunkuya ya na kallon ta yace "Ya dai Nana, ko dai kema jikin ne?"
Wani iska ta furzar ta girgiza kai tace "Um um." Sake kafeta ya yi da ido yace "Kin tab'a ba komai?"
"Babu." Ta fad'a ta na huci, kallon tuhuma ya mata yace "Khadija ko dai kema a shigar da ke ciki ne?"
"Ka bar shi kawai, ba buk'ata." Ta fad'a a wahalce, "Kin tabbata?"
Da k'yar tace "Na tabbata." Mik'ewa ya yi yace "Shikenan, amma dan Allah da kinji wani abu ki yi magana tun da wuri."
Komai ba tace ma sa ba har Hajia ta same su tare da malam da ya kawota, kamar dama jiran zuwan Hajia ake sai ko ga wata likita ta fito ta kalli Usman tace "Alhamdulillah ta haihu lafiya, an samu d'iya mace."
"Alhamdulillah." Suka fad'a kusan a tare, nan akayi duk abin da ya kamata wanda suke buk'ata, lokacin dare ya yi sosai Hajia tace Usman ya koma gida da Khadija ita za ta zauna wajen su, ba b'ata lokaci suka kama hanyar gida Khadija sai gyangyad'i take, kallon ta ya yi ya na murmushi yace "Hajia wane suna ki ka zab'a da za'a sawa 'yar ta ki?"
Cikin doguwar hamma tace "Ka tambayi maman ta mana, watak'ila ta na da sunan da take sha'awa ita ma."
Wani kallo ya mata yace "Ta na da wata uwa ce da ta wuce ki a duniyar nan?" Cike da kasala tace "To idan da hali a saka mata *Nana Aisha* kaga idan na haihu nan kusa nima munyi 'yan biyu kenan sai a saka mata *Humaira*."
Cikin murmushi yace "Idan kuma namiji ki ka sake sunkuto min fa." Cikin zolaya tace "Sai ka saka masa *Humair*."
"To amma..." Da sauri ta katse shi tace "Dan Allah ka rabu da ni bacci na ke ji." Dariya ya yi yace "To idan ki ka yi bacci a motar fa?"
Kai tsaye tace "Saika d'auke ni ka kwantar da ni akan gadon ka."
Wani kallo ya mata yace "Me ya sa sai a kan gado na?"
"Saboda ina so haihuwa ta same ni akan gadon." Marairaicewa ya yi yace "Yanzu ku saboda Allah haka za ku had'e min kai ku haihu lokaci d'aya, kenan dole nima sai na yi jego kamar ku."
Dariya Khadija ta dinga shek'awa har da rik'e ciki kafin tace "Ai daidai kenan, kaga kai ma sai ka nemi k'unzugu ka aje saboda tarban jinin bik'i."
Kamar zaiyi kuka yace "Allah ni dai ban yarda ba, babu wani jego da zanyi haka kawai da raina da lafiya ta, dole kisan dubarar da za ki dinga min saboda na gujewa abkawa jego."
Hararan shi ta yi tace "Saboda ni kad'ai ce ke da kai?"
Saida ya kashe mata ido yace "Amma ai ke dabance, ke kad'ai ce ki ka iyani yanda ya kamata, ke ki ka fi kowa sanin abin da na ke so da abin da na ke da buk'ata."
Ba tace komai ba har suka isa gida rabe ya bud'e mu su k'ofa suka shiga, sun samu Bilal na baccin shi kamar yanda suka bar shi, nan suka kwanta suma bacci cike da gajiya, sam Khadija ba ta yi tsammanin gari zai waye ba ta haihu ba saboda abin da take ji, amma sai gashi ta tashi cikin k'arfin jiki, tunda asuba ta had'a kyakyawan abin karin kumallo sannan ta shirya, haka Bilal ma ya shirya Usman ma kafin suka karya na su kumallo abin da basu saba ba kari tunda safiya, asibiti suka tafi sun samu iyayen Haseenah da kuma Mariya, bayan sun gaisa suke mata godiya akan kayan ta da ta bayar Haseenah ta yi aiki da su, nan Usman ya zauna kuda da Haseenah ya kalle ta yace "Mai jego wai wane suna ki ka zab'awa 'yar ta ki ne?"
Kunya ce ta kama Haseenah ta rufe fuska da hijabi, dariya ya yi yace "Ki fad'a mana, dan ni zan iya saka mi ki sunan tsofaffi kamar sunan su Hajia."
Hajia ce tace "Sunan na mu ne na tsofi kenan? To aiko in ka yi wasa sunan Hajiar (mahaifiyar Haseenah) za'a saka mata."
Dariya ya yi ya kalli Hajia a ran shi kuma yace "Asiya." Mahaifiyar Haseenahr ce tace "Ko kuma sunan ki ba, ai yafi nawa."
Na kuma Haseenah ce ta kalli Hajia a ran ta ita ma tace "Allah ya sa kar ya sawa 'yata sunan mahaifiyar shi, *Hawa'u* ai sunan da ne."
Jin dai su na ta cecekuce ya sa tace "Kawai tambayi mahaifiyar ta wane suna ta ke so?" Ta fad'a da nuna Khadija, kallon ta Khadija ta yi tace "Ni kuma?"
"K'warai aunty Khadija, babu wanda ya dace ya saka mata suna bayan ke, a sanadiyar ki ta samu gatan da aka haifeta gidan mahaifin ta, dan haka kawai ki zab'a mata sunan da ya mi ki."
Murmushi Khadija ta yi tace "To shikenan a saka mata Aisha, sai ku tayani addu'a Allah ya sa na haifi mace sai a saka mata Humaira, kunga sun zama 'yan biyu kenan, Aisha da Humaira."
Kowa ya ji dad'in abin da ya faru, haka aka sawa yarinya Aisha tare da sa mata albarka, su kuma aka bisu da addu'a k'ara had'a kan su, nan Usman ya wuce da Bilal makaranta, zuwa k'arfe takwas ko da aka kama aiki aka sallame su, amma ba su bar asibitin ba har sai kusan k'arfe tara kafin Usman ya aiko Bilyamin ya d'auke su, tunda Bilal ya dawo ya ke b'angaren Haseenah ya na lagudar yarinyar, wani iko na ubangiji sai yarinyar ta yi kama da Bilal d'in kamar ciki d'aya suka fito, duk mutanen da ke zuwa wajen Bilal bai bar wajen ba, Khadija ta yi mamaki sosai yaron da ba ya son hayaniya da taron jama'a, amma sai gashi ya wuni zigidir wajen Haseenah har saida yamma lokacin islamiyya ya yi kad'ai ya bar wajen.
Sosai yan uwan Khadija da abokan ta suka mata kara wajen zuwa yi wa Haseenah barka, sai dai Hajia Turai ta rantse ta maya kan ba za ta zo ba sai in Khadija ta haihu, to fa ranar za ta zo gidan ko me zai faru sai dai ya faru, a lokacin kuma Khadija ta nemi da Usman ya mata izini taje ta dawo da Uwani ko dan aikin da ke tunkaro su ta na buk'atar mai taimako, ba musu ya mata izini ta tafi tare da Bilal, ba ta sha wahalar shawo kan su ba saboda dama ba laifin ta bane, nan suka dawo tare da su aka d'ora daga in da aka tsaya.
Sosai Khadija ke kama girmanta wajen ganin ta sauke nauyin da Usman ya d'ora mata, kowace safiya kafin Haseenah ta fito daga wanka za ta samu abin karyawarta yana jiran ta, da rana kuma idan su Mariya su ka zo tare suke aikin rana cikin raha da annashuwa, haka za su dinga cewa ta zauna ta huta za su yi amma sai tace a'a, haka suke girkin rana da na dare tare, kuma sosai suke k'aruwa wajen koyan girkin, dan kwana uku da akayi da haihuwar kullum akwai abin da ake girkawa, a haka aka shiga kwana na hud'u, a lokacin sosai Khadija take jin jikin ta fa ba dad'i amma ta na daurewa ne, yau dai ko da suka gama girkin rana ta shiga d'akin ta ba ta fito ba, saida Uwani taga abin ya fara tsananta ta fito ta nemi taimakon mutane dan su tafi asibiti, Hassana da su Rabi'a na gidan a lokacin su ka taho dan ganin lafiya, d'aki suka same ta kwance sai nishi take ta na ware k'afafun ta saboda tasan haihuwarta kusa take, nan suka duk'ufa aka taimaka mata, leda aka shinfid'a akan gadon suka fara karb'ar haihuwa, ai kuwa ba jimawa sai kan yarinya ya lek'o duniya, suna k'arasa jawo ta sai ta fashe da kukan da ya sa Usman da ya taho hankali tashe lokacin da Bilal ya kira shi ya tsaya cak, rufe fuska ya yi kafin ya bud'e ya na dariya mai kama da kuka, d'aukar Bilal ya yi ya na juyawa da shi cikin farin ciki.
Nan su Hassana su ka fito da yarinyar suka bashi ya karb'a, ya na kallon ta ya ji wata muguwar k'aunar yarinyar saboda sak Khadija ya ke ganin fuskarta, yan uwa fad'an irin bidirin da ake ma b'ata lokaci ne, Khadija dai ga farin jinin mutane gashi haihuwar ta zama biyu, hakan ya sa kullum gidan kamar ranar ake biki, kuma an mayar da bikin rana d'aya ma'ana ranar da Khadija ta haihu, a k'alla mutanen da ke zuwa gidan basa irguwa kuma mafi aksari mutanen Khadija ne, shirye shirye ake sosai in da k'awayen Khadija su ka yi anko har kala biyar saboda farin ciki, kuma babu wanda Usman baiwa Khadija da Haseenah ba, dan ma Khadija ta yi wa kan ta dayawa da bai sani ba, a lokacin kuma Khadija ta tuna da ranar bikin ya yi daidai da zagayowar ranar haihuwar Usman, wanda shekarun su ka kama *arba'in da biyar*, dan haka ta fad'awa k'awayen ta su kaltume cewa ta na so ta mi shi bazata, nan aka fara wani sabon shirin dan bashi mamaki, in da ba kowa ya sani ba daga yan uwan Usman maza da mata, sai yan uwan Khadija da na Haseenah, sai kuma abokan Usman d'in wanda aka gayyata.
*Rana bata k'arya* sai dai uwar d'iya ta ji kunya, yau akayi suna kuma yara sun ci sunan da uwarsu ta zab'a musu wato *Aisha* da *Humaira*, duk girman gidan Usman sai gashi ya kasa d'aukar mutanen da ke wajen har saida aka had'a da wasu runfa har biyu a k'ofar gida, duk wanda ya zo sai yace masha Allah saboda taron jama'ar, kuma kashi uku a cikin hud'u duk na Khadija ne, ita ma kuma hakan ya faru ne sakamakon jimawa da tayi ba ta haihu ba, Usman yayi iya k'ok'arin shi wajen samarwa mutanen abinci da abin sha, inda aka yanka manyan shanu har guda biyu, a b'angaren Khadija kuma shiga kawai take ta na sakewa, duk da Usman ya musu d'inki iri d'aya kuma yawa d'aya amma saida kaltume da Hajia Turai suka sake mata wani d'inki, ita kanta ba ta sani ba sai ana gobe bikin kad'ai suka kawo mata su, yawan taron jama'a ya sa muryar Khadija dishewa ta shak'e ba'a ji saidai ta d'aga hannu kawai.
B'angare d'aya kuma su Kaltume na sama suna gyara wajen da za'a gabatar da walimar dare wacce su ka shirya ma Usee, a haka har dare ya riske su lokacin mutane sun watse sai masu aiki da aka samu suna share gidan, nan fa aka sake sabon shiri in da Khadija ta sake d'aukar wata sabuwar kwalliya wacce ta ci kud'i sosai, Aisha da Humaira ma shiryasu akayi cikin kaya iri d'aya kuma kalar na iyayen su da Bilal, Haseenah da Khadija ma cikin wanda Usman ya d'inka mu su suka saka kala d'aya, nan suka kira Usman a waya wai ya zo gida ba lafiya, a gigice ya tambayi me ya faru? Sai kawai su ka kashe wayar suna dariya, Usman dama walima ya yi sosai shima haka ya tsallako abokan shi ya taho gidan a sukwane, d'akin shi ya nufa ya na shiga ya same su zaune sai hira suke, matsowa ya yi ya na fad'in "Lafiya? me ya faru ne?"
Tare su ka taso Haseenah na cire mi shi hula Khadija kuma riga tace "Ba komai, wanka za ka yi ka yi sabuwar kwalliya."
Duka da mamaki ya kalle su yace "Kwalliya kuma, kamar wata mace? Kwalliyar me?"
Khadija ce ta d'ora mi shi hannu a yatsa tace "Shiiiii, ba magana."
Iska ya furzar yace "Wallahi kun d'auki alhaki na, haka kawai kun tayar min da hankali."
Kallon shi Khadija ta yi cike da shagwab'a tace "Ka yafe mana to." Turo baki ya yi gaba yace "Na k'i d'in."
B'ata rai ta yi ta tisa k'eyar shi ta kalli Haseenah tace "Shiga da shi ciki ki wanke min shi tas, kafin ku fito zan fito mi shi da kaya."
Ba musu suka shiga ban d'aki ta taya shi wanka, ita kuma kaya ta fito mi shi da su kalar na su sai dai ba iri d'aya ba, haka suka fito suka shirya shi kamar wani sarki ko kuma yaro, tsaf su ka yi da su kafin suka fito dan hallara wajen taron wanda a wannan lokacin ya samu halartar manyan bak'in da aka gayyata har daga mak'ota *nigeria* ma, Humaira na hannun Aishatu in da Aisha ke hannun Mariya, haka suka haura sama cikin shiga ta alfarma gwanin birgewa, sai lokacin Usman ya saki baki ya na kallon ikon Allah, tuni hankalin shi ya koma kan wani rubutu da akayi da manyan bak'i aka saka *HAPPY BIRHTDAY GARKUWAR MU*, sunkuyawa ya yi wajen Khadija yace "Aikin ki ne ko?"
Ita ma matso da kanta ta yi tace "Ba ruwa na ni, nima gani kawai na yi."
Tun kafin su isa wajen zamansu Khadija ta hango manyan bak'in da ta gayyata, nima dai baza ido na yi sosai saboda ganin wurin ya cika da mazan hajiyoyi sosai, mamaki ne ya kamani ganin wasu manyan mutane a gefe, haba ai saina bar bin bayan su Khadija na tafi da sauri wani tebur, domin tabbatarwa kaina da gaskiyar abin da na ke gani yasa na k'arasa na tsaya na ce " *Kaussar*." (jarumar littafin *Kaussar*).
Ai kam da sauri ta juyo ta kalle ni, da farin ciki ta mik'e tsaye ta rumgume ni tace "Aunty Meera, ke ce? Me kika zo yi anan?"
Kafin na yi magana daga bayan Kaussar aka ce "Me fa ta zo yi daya wuce d'aukar shegen rahoton nan nata da ta saba yi na jaraba, ko gajiya ba ta yi ta na bi gida-gida ta na wa ma'aurata bin k'wak'waffi."
Wa zan gani in ba *Ahmad* ba, k'ara waro ido na yi saboda ganin ya k'ara k'iba, sai dai ya k'ara haske sosai abinka ga jan buzu kuma balarabe, sai uban k'asumbar nan sai walk'iya take bak'i k'irin, tab'e baki na yi na dalla mi shi harara na ce "Can ta matse ma ka dai, kuma in da ba na d'auko labarin ai da ban d'auko na ku ba."
Shima cikin hararan ta yace "To kin d'auka gata ne ki ka mana, bayan kin gama kalle min mata."
Sama da k'asa na harare shi na ce "Ikon Allah." Kallon Kaussar na yi na ce "Wai yaushe bagwarin mijin nan naki ma ya iya haussa ne haka?"
Dariya Kaussar ta yi ta koma ta zauna kafin tace wani abu yace "Ranar da ki ka zaunar da ni ki ka koya min."
Nuna shi na yi da hannu na ce "Allah ka kiyaye ni ko na sa a k'wace matar ta ka sannan ka koma inda ka fito."
Dariya ya yi wacce ta k'ara bayyanar da tsantsar kyawun shi yace "Bismillah idan kin isa, ke ki na ganin kin isa ki datse wannan auren? To yanzu haka yaro ta baro gida wanda take bawa nono, kinga kuwa ni da ita ba rabuwa sai mutuwa."
Sama da k'asa na sake hararan shi na yi gaba ina kallon Kaussar na ce "Za mu yi magana idan mijin nan na ki ya yi bacci."
Da dariya ya bini da kallo ya na fad'in "Sakaran ina ne ni zanyi bacci a wannan taron, bayan akwai irin su *Najib* (jarumin littafin *D'aukar fansa*)a wurin nan."
Da sauri Kaussar ta rufe mi shi baki saboda su na kusa da su Najib, ni kuma sake ware ido na yi dan naga ina ya ke, ai kam baifi tako hud'u ba na iso ga teburin shi, kallon shi na ke sosai tare da kyawawan matan da su ka saka shi tsakiya su biyu, da murmushi a fuska na ce "Alhaji Najib barka da dare."
Wani mummunan fad'uwa gaba na ya yi saboda kallon da ya watso min kamar kumurci, d'auke kan shi ya yi k'ala baice min ba dan haka na kalli *zarah* na ce "My Zarah sannu ko?"
Da murmushi sosai tace "Sannu aunty Meera, ya ki ke? Me ki ke anan? Ke ma aunty Khadija ta gayyace ki ne?"
"Eh...t..." Ban k'arasa ba Najib yace "Har sai kin tambaye ta me ta ke anan? Gulma mana ta kawo ta, ko kin manta anyi drima a gidan Usee watannin baya da su ka wuce?"
Murmushi kawai Zarah ta yi sai *Yasmine* da tace "Ko da gulma ce ta kawo ta ai kam ta yi anfani, dan nasan akwai dayawa masu irin halin Haseenah wanda za su gyara."
Kashe mata ido na yi na ce "Da kyau tawaje na kin gane, ba zan tsaya b'ata lokaci da wannan mijin na ku ba mai k'aton ciki kamar kun aza mi shi randa."
Da k'arfi ya juyo zaiyi magana Zarah ta rik'e tace "Haba beby ya isa mana, rabu da ita dan Allah."
K'wafa ya yi ya zauna ya na huci, ni kam ko a jiki na sai ma gaba da na yi na bar shi da masifar shi, kamar daga sama na ji na yi karo da k'afar wani, da sauri naja baya ina fad'in "Ayyah sannu ko, yi hak'uri dan Allah ban..."
Bai k'arasa ba saboda ganin *Saif* (jarumin littafin *Ba so bane*) sai dokan uban murmushi yake ya na kallo na, ajiyar zuciya na sauke dan nasan ba matsala, da dai sauran mazan hajjajan ne da ban san me zai faru ba, kafin ya yi magana *Zeinab* tace "Lah aunty Meera ke ce? Me ki ke anan?"
Izuwa yanzu kam na fara gajiya wannan tambayar da kowa ke min ta me ya kawo ni, amma sai na dake na ce "Ni ma na zo bikin Khadija ne."
Da wannan murmushi Saif yace "Ko kuma suma idon ki ka saka mu su ba kamar yanda ki ke wa kowa."
Kallon shi na yi na ce "Haba Saif ya za ka ce haka, kaine fa na ke gani mai hankali a cikin sauran."
Waro ido ya yi yace "Au! Wai ki na nufin sauran duk mahaukata ne?"
Kau da kai na yi na ce "Ka ga ni dai bance ba kar ka ja min sharri."
Juyawa ya yi bayan shi yace " Bara na ga ina zanga aboki na na fad'a mi shi kin ce mahaukata ne su."
Da sauri na bar wajen ina fad'in "Shi ma dai ya lalace kamar sauran, nasan kuma ba zai rasa nasaba da wannan bigaggen *Salman* (jarumin littafin *Auren had'i*) d'..."
Ai dole naja birki domin kuwa karo na yi da Salman d'in, wani kallo ya min yace "Ni ne ma bigaggen?"
Murmushin dole na yi na ce "Ah haba dai, ni na isa na kira ka da bigagge, dama da Saif na ke."
Dafe k'irji ya yi yace "Abokin nawa ne bigagge kenan?"
Zanyi magana naji andafa ni ta baya ance "Aunty Meranmu dan Allah rabu da su, wahalar da ke kawai za su yi."
Baki na.saki saboda ganin *Ummi* ta zama wata babba kuma hamshak'iyar mace, kallon Salman na yi a raina ina raya koya yake ya na iya d'aukar ta ma yanzu? Hum, kallon ta na yi na ce "Ummi na ina 'yan biyu?"
Da murmushi a fuskarta tace "Yan biyu su na wajen su lamama, amma ya na gan ki anan? Me ki ke yi?"
Salman ne ya juya ya zauna kan kujerar da suka tashi ya na fad'in "Me fa zai kawota da ya wuce d'aukar rahoton da ta saba, ta na nan kullum ta k'i canzawa sai tsukewa take, Allah ya sa wayar taki ta fad'i sai mu ga ta tsiya."
Wata dariyar rainin hankali na mi shi na ce "Ka ji malam Salmanu, wato so ka ke na zuma b'ukekiya kamar matar ka, to ni mijina ba ya buk'atar na yi k'iba haka yake son gani na, sannan da ka ke fatan wayata ta fad'i to in fad'a ma ka ta na fad'uwa wallahi sai ka biya ni, in kuma ba haka ba zansa Ummi ta ma bore har sai an sake ma ka tiyata, ai dai ka gane tiyatar da na ke nufi ko?"
Ta fad'a ta na kashe mi shi ido d'aya, baki ya saki ya na kallo na har na wuce na bar shi, saida na b'acewa ganin shi ya kalli Ummi yace "Kuma ke sai kiyi idan ta saki?"
Cike da tabbatarwa tace "Sosai kuwa, me zai hana ni?" Gyad'a kai kawai ya yi ya cije leb'en k'asa, har na wuce na yi saurin dawowa baya cike da tsoro, murza ido na yi ina so na ga wai tabbas shine wanda na ke zato ko kuma dai gizo ne, da mamaki na ce " *Abbas* (jarumin littafin *Sanin masoyi*), ai kam da sauri ya juyo, amma abun mamaki ya na gani na saiya had'e rai ya sake juya min baya, har zan shiga tunanin dalilin da ya sa ya min haka sai kawai na ji andafa ni, juyowa na yi sai kuwa na ga takwarata, cike da farin ciki mu ka rumgume juna ta na fad'in "Takwarata me ki ke anan?"
Raba jikina na yi da nata na sake kallonta ta yi kyau sosai, murmushi na yi na ce "Na zo biki ne ni ma."
Tsaki naji Abbas yaja hakan ya sa mu ka kalle shi a tare, *Sameera* ce tace "Jarumi na lafiya ka ke tsaki?"
Da k'yar yake maganar saboda miskilanci yace "Kinsan ba na son hayaniya, wannan kuma ta tsaya min a kai ta na zuba kamar 'ya'yan kurna."
Tabbas raina ya b'ace yanda Abbas ya nuna ni kamar ya nuna kashi, tab'e baki na yi na ce "Da ace banga lokacin da ka ke wa takwarata 'yar murya ba da sai ka zare min ido, amma tunda har na ga komai to magana ta k'are, wannan shan kunun duk birga ce wallahi."
Kallon Sameera na yi na ce "Takwara idan kun koma gida lafiya ki gaishe min da su Bashir da su Abba da Mama." Da murmushi a fuskar ta tace "Za su ji aunty Meera."
Har zan wuce na ji Abbas yace "Ta na nan har yanzu yanda take kamar za ta fad'i ta na fama da bibiyar rayuwar mutane."
Wucewa na yi na barshi da takwarata tace mi shi "Ba fa na son haka uban yara, duk abin da za ka fad'a mata kamar ni ka ke fad'awa."
Wani kallo kawai ya bita da shi kamar zaiyi bacci, ni kam ina barin nan na shiga neman mutuniya ta, ai kam bansha wahalar ganin ta ba, da gudu na k'arasa na rumgumeta ta baya ina fad'in "Ohhh, my Hajiata."
D'ago kai ta yi ta kalle ni tace "Lah! aunty Meera, ke ce anan? Me ki ka zo yi wurin nan?"
Saida na taushe zuciya ta kafin na ce wani abu *Umar Faruk* (jarumin littafin *Jihadi*) ya fizgoni na yi baya ya na fad'in " Dallah malam sake ta, me ye haka kin wani zo sai kin karya ta."
Ba dan Umar ne ba da sai na mi shi rashin mutumci, amma saina k'yale na ce "To cinye ta zanyi da ka wani taso min haka?"
A tsaurare yace "Ki yi baya ki daina tab'a jikin matata shine kawai abin da na sani."
Rik'e hab'a na yi na ce "Ikon Allah, beby mijin beby, wato wai kai mai kishi ko? To Allah ya kyauta."
"Ya ma kyauta." Ya fad'a ya na kallo na, *Khairat* na kalla na ce "Hajiata ina *Zubaida* ne? kinsan fa fan's sunyi kewarta."
Murmushi ta yi tace "Ta na gida bata jin dad'i ne, kuma ga tsohon ciki da ke jikinta, shi ya sa ta zauna gida tunda tafiya ce mai nisa."
Juyawa na yi na kalli Umar ina dariya, shi kam sai ya had'e rai ya na harare na, saida na fara takawa na ce "Lallai Umar ba dama, wato har yanzu ka na nan ka na tsula tsiyarka, daga wannan ta sauke wannan za ta d'auka, humm."
Juyawa na yi zan wa Khairat magana amma sai Umar ya ciro takalman shi zai jefe ni, da gudu na bar wajen ina dariyar mugunta, kujera na samu na zauna ina sauke numfashi kamar saukar aradu daga gefena aka ce "Aunty Meera ya ki ke?"
Da murmushi na juyo dan na gane mai muryar, da farin ciki na d'aga mu su hannu na ce " *Falmata* (d'aya daga jaruman littafin *Itace k'addarar mu*), lafiya lau, ya ki ke kema?"
"Lafiya lau, me ki ke anan?" Saida na b'ata rai na ce "Abin da ki ke yi."
*Adam* ne yace "Daga tambayar arzik'i malama sai abu ya zama na tsiya."
Hararan shi na yi na ce "Kai ni rufe min baki dallah ban sa da kai ba."
"Ke ni ki ke fad'awa haka?" Ya fad'a a hassale, ni ma a hassalen na fad'a "Eh anyi d'in, me za ka yi?"
Tasowa ya yi ya nufo kaina amma ban gusa daga in da na ke ba, saida ya tsaya gaba na ya nuna ni da yatsa zaiyi magana na ga an rik'e hannunshi daga baya ance "Haba kai kuwa Adam, aunty Meera ce fa, ba ka gae ta bane?"
Sai lokacin na ga mai magana ashe *Marwan* (jarumin littafin *Kawu na ne*) ne, huci ya yi ya sauke hannun shi ya koma mazaunin shi, har ya zauna a kalli Falmata na ce "Fati wai ina d'an uwan ku mahaukaci?"
Cike da jimami tace "Ki bari kawai aunty Meera, har yanzu ya na can babu sauk'i, wallahi duk ya sauya ya zama mahaukacin gaske."
Tab'e baki na yi karo na farko da na ce "Allah ya yaye mi shi, *Fadjimata* kuma Allah ya mata rahama."
"Ameen." Ta fad'a ta na mayar da kallonta gaban ta, sai lokacin na kalli Marwan na ce "Marwan ina aunty na take?"
Da yatsa kawai ya min ishara zuwa bayana, ina juyawa na ga *Wafa'atu* bayana da tulelen cikinta masha Allah, da farin ciki na mik'e na rumgume ta na ce "Aunty Wafa'atu ashe Allah ya nufa."
Ita ma da farin ciki tace " allah ya nufa Meera, addu'ar ki data fan's d'in ki ta same mu har inda muke, gashi yanzu Allah ya sa nima ina d'auke da cikin wata bakwai."
"Kai to Allah ya raba lafiya aunty wafa'atu."
Da "Ameen." Suka amsa su dukan su, sai lokacin Wafa'atu tace min "Amma me ki ke yi anan? Ke ma Khadija ce ta gayyace ki."
Raina ne ya b'ace da tambayar sai kawai na yi gaba na bar su tsaye, ina cikin tafiya naji anyi magana cikin shagwab'a ance "Aunty Meera shine ko ganin mu ma ba kya yi."
Juyowa na yi sai kuwa naga *Raheenat* (jarumar littafin *K'angin rayuwa*) ce, saida na gama kallon mutanen da ke tare da ita, ita da *Sameera* suna manne da juna haka ma *Abdul hakeem* da *Sadiq* suna jone sai tattaunawa suke, matsawa na yi dan mu gaisa amma Abdul hakeem sai cewa ya yi "Ke me ya kawo ki nan?"
Baki bud'e na ce "Abdul hakeem yaushe ka zama haka kuma? A sani na dai ka na da taushin zuciya."
"Sanin baya ki ka min, ai yanzu abin ba sauk'i, dan haka b'ace min da gani kafin ran ki ya b'ace." Yanda ya ke maganar ya sa na tsora ta na juya zan tafi Sameera tace "Haba takwarata, yaushe ki ka zama mai tsoro ne haka har da wannan zai tsorata ki."
Abdul hakeem ne ya kalli Sadiq yace " aboki na ka sa matar nan taka ta yi shiru kafin na fitar mata da jini a baki."
Kallon Sadiq Sameera ta yi tace "To sa na yi shiru d'in, ina jira."
Wuk'i-wuk'i Sadiq ya yi da ido kafin ya kalli Abdul yace "Aboki na ka yi hak'uri, ba zan iya ma ka komai ba gaskiya, wannan matar da ka ke gani ina tsoron bala'in ta."
Wata dariya Sameera da Raheenah su ka yi harda tapa hannu, ni kam dariya na yi na yi kafin na ce "Wai ina yara na ne?"
"Suna gida." Cewar Raheenat, juyawa na yi na ce "Sai anjiman ku."
Kallon Sadiq na yi na ce "Ka gaishe min da bazawarar nan taka."
Waro ido ya yi ya kalle ni ya kalli Sameera, tasowa yayi zai min magana sai kawai takwara ta jawo rigarshi ya koma ya zauna tace "Dan Allah ya toni asirinka shine za ka bud'e mata ido."
Abdul ne ya kalle ni yace "Kedai anyi guba wallahi, to yanzu dad'in me ki ka ji?"
Kallonshi na yi na ce "Ka mantabi guba ce lokacik da ka ke sawa ina rubuta labarin soyayyarka da sabuwar budurwarka."
Kallon shi Raheenat ta yi ,dariya na yi na wuce gaba ina ganin bala'i ya b'arke tsakanin Sadiq da Sameera, Raheenah da Abdul dan fa ita ta yarda bazawara yake nema tunda a ganinta ina bibiyar rayuwar mutane, ta teburin da Adam ke zaune na wuce nan ma cewa na yi ya gaishe da budurwar shi, a tak'aice saida na bi duka ma'auratan d'aya bayan d'aya ina hura mu su wuta, kuma babu wacce ba ta yarda ba saboda ganin ba zan fad'a mu su abinda ba haka bane, kafin ka ce me wajen taron ya fara d'aukar gumi saboda muryoyin dake tashi sama, musamman Kaussar da Khairat da Sameera ta Abbbas, sosai suka rufe ido wai ana cin amanarsu, da dai abin ya k'i sauk'i sai gashi ina niyyar sulalewa na bar wurin na ji ance "Aunty Meera barka."
Ina juyowa da sauri naga teburin cike da jaruman littafin *Aure*, da farin ciki na k'arasa muka gaisa kafin na kalli matan na ce "Ina yaran?"
*Fatima* ce tace "Suna gida aunty Meera."
Sai *Rauda* da tace "Ai sun fara wayo yanzu." Kallon Laure nayi da kanta ke k'asa duk take jin ta a takure, murmushi nayi na ce "Lauratu sarauniyar kunya, to Allah ya mayar da ku gida lafiya, ni na yi gaba wajen nan ba zai zaunu gare ni ba."
"Me ya sa?" Cewar *Iro*, kallon shi na yi kafin na ce wani abu *Siryanu* yace "Akwai bala'in data had'a tunda kaji haka."
*Imam* ne yace "Ko kuma tsokana ba, kasan Meeran mu da tsokana fa, watak'ila akwai wanda ta harzuk'a."
Ban tsaya saurarensu ba na fece ba su ma san da tafiya ta ba sai gani sukayi bana wajen.
😂😂😂😂😂
Ina shirin hawa adaidaita sahu na ji an shak'o hijabina na dawo baya, wazan gani in ba Umar faruk ba da hijabi na a hannu, Saif da Marwan sune masu sanyin ciki sune suka ce ya sake min hijabi tunda ni ma fa ba kara zube ni ke ba ina da aure, saki na ya yi amma Abbas yace "Wallahi ko kije ki fad'a mu su k'arya ki ke ko kuma mu kwana anan mu da ke."
Ahmad ne yace "Ai ba maganar mu kwana anan bane, magana ce ta muje gidanta a matsayin samarinta ma su son ta."
😂 *Ahmad ko bala'i*
Jin haka ya sa na ce su yi hak'uri mu tafi na fad'a mu su gaskiya dan ina son *beby na* ni ma, haka suka tasoni a gaba na zo na fad'a mu su kawai dan raha ne, saida magana ta fara lafawa sai kawai muryar Usman naji yace "Abokai ku taimaka ku tafar min da matar nan dan Allah, dan nima ta d'an fara damu na, sam bata bari mutum ya yi sirri da matarsa."
Murgud'a masa baki na yi na ce " To babu in da zanje sai na k'arashe labarin har k'arshe sannan."
Cikin fad'a Usman yace "To zan gani idan gidanki ne ko nawa."
"Gidanka ne amma babu in da zata je har sai ta k'arasa abin da ta fara." Cewar Khadija, turo baki yayi kamar zaiyi kuka amma bai ce komai ba, nima cewa na yi "Zan tafi yanzu dai saboda na gaji, amma zanyi sammakon zuwa gobe da safe."
Dukansu hannu suka d'aga min suna min bye bye da cewa "Saida safe Meranmu."
Haka na bar wurin cike da kewar *jarumai na* ko ba komai ina jin dad'in zama tare da su, da haka suma su ka ci gaba da walimar su har aka yanka panke dare ya yi sosai kafin Usman ya samawa kowa makwanci mai rai da lafiya ya kwanta dan huta gajiya, haka duka ma'auratan suka kwanta suna soyayyarsu dan har yanzu akwai wanda basu san sun girma ba.
*Asuba ta gari*
Daga lokacin suka fara jego cike da gata da kulawa, a yanzu idan kaga zaman na gidan Usman saiya baka mamaki, duk da har yanzu suna jin kishi amma dai ba kamar baya ba, haka suke tasa Usman gaba su dinga masa k'iriniya shi kuma yana biye musu, rayuwar ta musu dad'i yanzu kuma sun fahimci zama lafiya yafi zama d'an sarki, a haka rayuwa da lokaci ke tafiya girma na k'ara zuwa musu, Haseenah k'iba take tayi abinta saboda kwanciyar hankali da hutu, amma Khadija har yanzu tana nan yanda take bata rage ba bata k'ara ba, a haka sherau su ka je sosai har shekara *goma sha biyar*.
A wannan shekarun abubuwa da dama sun faru masu dad'i da marasa dad'i, daga ciki akwai rasuwar su malam da Hajia, haka ma mamar Khadija ta rasu sakamakon rashin lafiya, haka mahaifin Haseenah ma ya rasu sai maman su wacce tsufa yasa ko yayanta bata ganewa, da haka kusan dukansu suka zama marayu suna kuma kula da junansu sosai, abun farin ciki kuma akwai haihuwa har biyar da Haseenah ta k'ara bayan Aisha, kuma dukansu mata ne sai auta shi kad'ai ne namiji wanda ya ci sunan *Ali* amma suna kiranshi *Khalifa*, kuma wacce yake biwa ita aka wa Khadija kara aka sawa sunan mahaifiyarta *Sadiya* ita ma suna kiranta da *Nawwal*, hakama hajia an mata takwara *Hawa'u* wacce akewa alkunya da *Noor*, sannan daga ciki akwai kammala karatu da bilal ya yi a k'asar *Canada*, amma har yanzu Khadija bata sake haihuwa ba daga Humaira, amma kaf yaran Haseenah ita ke kula da su kamar ita ta haifesu, a haka Bilal ya dawo ya zama cikakken saurayi son kowa k'in wanda rasa, matashin saurayi kyakyawa kuma miskilin yaro mai d'auke da shekaru *ashirin da bakwai*, hakan yasa Usman damka duk ragamar gidan hannu Bilal, a cewar shi aure zai mi shi nan da d'an lokaci kad'an, wannan damar da Bilal ya samu tasa yake juya komai na gidan har iyayen mata, shi ya sa yanzu kullum gidan cikin hayaniya suke saboda Bilal dai baisan yawan surutu, yau ma kamar kusan kullum Aisha da Humaira ne suka shirya dan auwa bikin k'awar su, masha Allah yan matan Khadija kenan, tabbas shak'uwa dake tsakaninsu tasa har suke kama sosai ta fuska da yanayi, sai dai Humaira tafi haske sosai da dogon hanci sannan tafi cikar hallita da kumari, kayan jikinsu ma iri d'aya ne haka suka nufi d'akin Bilal dake sama dan karb'o makullin mota su bawa drebansu ya kaisu, da sallama suka tura k'ofar Humaira ce gaba.
Kwance yake ruf da ciki babu riga a jikinshi sai dogon wando dake d'aure da d'amara (belt), saida suka tsaya kanshi Humaira tace "Yah Bilal makullin mota za ka bamu mun shirya."
Shiru kamar baiji ba, Aisha ce ta kama hannun Humaira tace "Kinga mu fita wallahi bana so ya tashi ya mana tsinannan duka."
Fizge hannunta tayi tace "Ke wallahi kin cika tsoro, kawai saiya doke mu daga wannan maganar."
Kallonshi tayi ta sake cewa "Ya Bilal magana muke fa."
A hankali ya juyo tare da tashi zaune yana kallonsu, saida ya gama kallonsu yace "Ku rufe k'ofar d'akin sai ku zo ku karb'i makullin."
Kallon juna su ka yi saboda sun san me ya ke nufi da abin da ya fad'a, zare ido su ka fara yi kafin ya sake daka musu tsawa yace "Na ce ku rufe k'ofar ko."
Haba wa ai da gufu suka fita suna rige-rige, Allah ne ya saukesu k'asa lafiya basu zama ko ina ba sai falon Usman, kamar an turosu haka suka fad'a d'akin, kowace wajen ta ta uwar ta nufa wacce tasan zata tsaya mata, Humaira wajen Haseenah Aisha wajen Khadija, wata cakuma da Aisha tawa Khadija yasa d'an kwalinta fad'uwa kan kujera hakan ya bayyanar da yar furfurar dake kan ta wacce ba'a ganinta sosai ma, Khadija ce tace "Kai Aisha ho, wannan ba sai ki karyani ba, lafiya me ya faru?"
Haseenah da sai wani k'ara rumgume Humaira take ne tace "Ai da gani ba tambaya kinsan su da wannan yariman mai gida."
Khadija ce tace "Wallahi al'amarin nan ya fara isata fa, gaba d'aya yaron nan ya hana min yarinya sakewa a gida."
"Ai ba laifinshi bane, laifin wanda ya bashi muk'amin ne a gidan." Cewar Usman daya fito daga d'akin shi tare da sauran yaran sunata gurgurar chocolat, hakan ma yayi daidai da shigowar Bilal ya sanyo farar riga wacce ta kamashi, tabbas ko kad'an Bilal baiyi kama da mahaifinshi ba saboda k'irar jikinshi ma ta k'akk'arfan maza ce kusan zaka iya cewa ma kawunshi ne yayi Habeeb, saidai kyawun mahaifiyarshi da yayi kawai da manyan idanunta, belt d'in dake hannunshi ya nad'e ya yo kan Aisha zai tsala mata ta sake shigewa jikin Khadija, Khadija ce tace "Allah ka daketa sai ranka ya b'ace, kaji marar kunya kai, kai baka ji ance ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi ba."
Juyawa yayi ya kalli Humaira hakan yasa Haseenah cewa "Karma ka fara matsowa nan kaji na fad'a maka."
Usman ne yace "Yarima meya faru? Laifin me su ka yi?" Cikin b'acin rai yace "Abba nasha fad'awa yaran nan su daina shigar min d'aki idan ban musu izinin shiga ba,yanzu fa haka kawai suka suka fad'a min d'aki ina kwance ba riga a jiki na."
Khadija ce ta katse da cewa "To shine zaka dake su? Ba sai ka sake musu nasiha ba, kaji sai kace wani gudan babban mutum, yaushe ne aka daina saka maka kaya."
Usman ne yace "Koma yau ne aka daina saka mi shi ai dai an daina saka mi shi saboda ya wuce munzalin, dan haka dole ya hukuntasu tunda sun k'i su san daidai da ba daidai ba."
Kallonshi Khadija tayi ta motsa bakinta hakan yasa Usman yace "Naji ki kamani amma bayan na mik'awa yarima na wannan yaran nan na bayanku."
Wata dariya Haseenah ta yi tace "Kana ganin zaka iya k'watar su a hannun mu ne?"
Wani kallo ya mata yace "Kin manta da k'ashi d'aya ne gareni, bugu d'aya zan mu ku kuji ku a makara."
Dariya Khadija tayi tace "To ina zaka zauna kai kuma?"
"A duniya mana." Ya fad'a ya na zama kusa da su, Haseenah ce tace "Kenan ka fara soyayya a waje bamu sani ba."
Shafa kanshi yayi da ya kusan cika da furfura yace "Ai wasu kyawawan yan mata na samu suka mak'ale min wai ni suke so, kuma na yi alk'awarin aurensu, ai yarima ma zai zama waliyi na."
Dariya suka saka a tare sai Khadija da tace "Komawa baya kenan, to idan zaka je d'aurin auren dai ka shafa gawayi a kanka danka rufe wannan farin abun na kan ka."
Sake shafa kan yayi yace "Alamar arzik'i ne ai, kuma naga kema akwaita a kanki."
Cike da k'aguwa Bilal yace "wai yanzu na zo da matsalata amma ku manta kun shiga sabgar gabanku, Allah ya shirya min ku iyayena, banda kamarku a duniyar nan."
Harya juya zai fita ya tsaya ya nuna su Humaira da yatsa yace "Kuma wallahi babu inda za ku je, na gaji da wannan yawan na ku kullum."
Khadija ce tace "To ni ka ban makullin tawa motar zan fita, ai dai kasan aro ne na baka jiya ko."
Kallon Usman yayi yace "Idan sarki ya bayar da izinin fita sai ku fad'a min zan kawo mu ku."
Cike da jin dad'i Usman ya aika mishi da sumbata yace "Allah ya maka albarka yarona, shi ya sa banda matsala da gidan nan ko bana nan nasan akwai original Usman a gidan, da ni ne da yanzu sun min fari da ido na basu makullan."
Fita yayi daga d'akin sai Usman daya kalli su Aisha yace "Ku kuma ki fito daga nan munafukai kawai, dama da kinga suna raba ido kinsan basu da gaskiya, kuma wallahi ku ka sake shigar masa d'aki ba neman izini da kaina zan hukuntaku."
Cikin turo baki suka sauko suka fita daga d'akin suna kumbura, dan tunda su ka ji Bilal ya rantse sun sa babu inda za su je, suna fita Usman ya kalli tsofaffin nashi yace "Ku shirya da kyau, wannan hutun na k'arshe zan had'a yaran nan da Bilal na aurar da su."
Wata sanyayyar ajiyar zuciya Khadija ta sauke tace "Alhamdulillah, wallahi naji dad'i da wannan maganar, dan duk sanda na kalli yaran sai naji fargaba ya ziyarceni, gashi k'awayen su sun fara aure, sai kaga an fara sakawa yaranka wani tunani na daban alhalin kana tsaye kan tarbiyarsu tsawon lokaci."
Haseenah ce tace "Allah yasa haka shi yafi zama alkairi, amma ka fitar musu da maza ne?"
"Eh to, a tunani na dai da zan had'a Aisha da *Kamal* (babban d'an Murtala) ne."
Humaira kuma sai a had'a ta da *Mujahid* (d'an Issoufou d'an uwan Usman), amma fa sai in basu da wanda suke so, dan ba zamu had'a su da wanda ba sa so ba tunda zamaninmu da nasu ba d'aya ba, da a lokacin yanzu ne aka mana auren da aka yi mana ni da *Dijangala* to na tabbatar ba za su zauna ba."
"Ai ko ni da ga yanzu ne aka had'a ni da kai to da babu abin da zanyi da tsoho." Cewar Khadija kafin ta d'ora da "A gaskiya dukansu sun fad'a min suna da samarinsu har shi Bilal d'in."
Kallonta Usman yayi yace "Kenan duk sun fad'a mi ki nine suka mayar bare."
Gwalo ta mi shi tace "Nifa uwa ce."
Haseenah ce tace "Aunty su wa suka fad'a mi ki suna so?"
Cike da k'asaita tace "Sirri ne tsakani na da yara na."
Tasowa Usman yayi ya bata kunnanshi yace "To fad'a min a kunne naji."
Ai kuwa rad'a mi shi tayi cewa "Bilal ya fad'a min suna soyayya ne da *Ikram* (yar Kaltume), sai Humaira tace suna soyayya da *Kamal* d'in da ka ke son had'a Aisha da shi, sai kuma Aisha tace wani yaro ne mai sunan *Jabir*, d'ane ga Alhaji Abbakar, amma kuma da wata yar matsala."
Kallonta ya yi yace "Matsalar me?" D'orawa ta yi da "Domin kuwa *Miemie* (yar Ashir) tana mutuwar son Bilal, dan har ta fad'a masa ma, kuma yace ba zai iya cewa baya sonta ba saboda tana birge shi sosai."
Dariya usman ya yi sosai kafin yace "Dan haka saiku shirya, yaronku da mata biyu zai fara insha Allah, na yarda da mazantakarshi."
_Tofa fan's wata sabuwa, ga Usman na shirin lak'abawa Bilal mata biyu a lokaci daya, tabbas akwai wasu darussa a cikin labarin rayuwar gidan Bilal, sai dai Meeranku yanzu ta zama lazy wrriter, da zan zo na kawo mu ku d'orawar shi amma ba zan iya ba saboda na gaji yasin._
*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*
*Ina godiya ga Allah da ya nuna min na kammala littafi lafiya kamar yanda na fara, Allah ubangiji kasa a anfana da darasin dake ciki, Allah ka sa mu tsarkake zuciyoyinmu wajen yin kishi mai tsafta, duk wanda suke da abokan zama Allah ka k'ara had'a kansu, wanda basu da kuma Allah ka had'a su da na gari, Allah ka k'ara sanyaya mana zuk'atanmu.*👏👏👏