Washe gari tun asuba sun gama shiryawa,lantanace tsugune gaban suhaima tana kuka tana nemn gafarar ta,suhaima tayi tayi ta tashi amman taki Tashi kuka kawai take gaba daya tagama muzanta.
Seda Suhaima takamata ta ɗagata sannan ta tashi,gurin baffa tanufa shima tana kuka tana neman gafararsu.
Suhaima da sauri tanufi gidan maman hanne tace su shirya suma.
Wayyo dadi maman hanne kuka ta rushe dashi.
Ayko ba musu suka kimtsa kayan su.
Ta dawo gida kenan taci karo da Rabiu cikin wata galleliyar mota yana dariya.
Fitowa yayi harda risunawa gurin gaisheta sannan yace.
"Ay jiya minister cash tabani miliyan gomana sabida nine na sanar dasu inda kike,shine naje nasiyo wannan amaryar,kuma ance inshirya,yau zamu keta hazo"ya karasa maganar yana dariya.
Sosai suhaima tayi mamakin yawan kudin da aka saka gaduk wanda ya nemota,murna ta taya rabiu sannan ta shiga gida.
Da kullin kayan lantana taci karo a zaure acikin rigar fulo zaa saudiyya����dariya ce ta kama suhaima amman seta danne.
koda ta shiga cikin gida samu tayi lantana nabada sautun asiyo mata batir da zata dunga sawa a torchlight dinta,in ta isa saudiyya sabida matsalar dauke wuta kaje kaita lalube cikin duhu��������
Suhaima cewa tayi tana dariya.
"wai ke waya fadamiki karamin guri zaki dakike ta wannan digimin,karma akaita da nisa,yanzu gidan me gari ba wuni suke sukwana da wutaba,sabida suna da solar,to shine zaki saudiyya kike tunanin dauke wuta"takarasa zancan tana dariya.
"barnide inje da abuna,kar inzo ina danasani"cewar lantana tana dariya.
Karfe takwas na safe,jiniya ta cika garin,mutane kowa yazo kallo,abun gwanin shaawa.
motar datafi kowacce girma da tsada shureim da suhaima da twins dinsu aciki.
Me bimata baffa lantana innar hanne Da hanne,da habu kanin suhaima da rabiu.
Se sauran motocin jamian tsarone.
ta window lantana ta miko wuyanta,tanawa mutane bye bye.
fadi take.
" hi kenan mun tafi saudiyya zamu mu hya ruwan zan zan"
da kyar baffa yajawota ta zauna sannan aka daga glass din,suka kama hanya mutane se daga musu hannu sukeyi.
karfe tara suka isa airport na kano inda suka tadda me girma gomna yana jiransu acan,daganan sallama sukayi suka nufi cikin jirgi,
Wayyo idanuwan lantana kamar goruba.
Seda aka tamketa da belt sannan taji dama dama.
koda suka iso Abuja seda sukaje fadar shugaban kasa tukuna suka musu godiya sosai .
cike da faraa me girma shugaban kasa Alhaji najibullah Aliyu,yakai dubansa gun su twins yace yana taba kumatunsu.
"Ashe kune kukawa Abba kwari ya gigice yataho nemanku"
Dariya dukansu sukayi,daganan rakiya shugaban kasa yamusu,zuwa airport.
Inda jirgin da shureim yazo aciki yake ajiye yana jiran ranar komawarsa.
Sallama sukayi suka shige ciki,jirgi ya daga dasu zuwa kasa me tsarki.
Abunda su lantana basu saniba tun a airport na kano akabar tarkacen kayan su,torchlight dintace kawai a hannunta,sabida ba aciki tasakaba.
Saukar dare sukayi,inda suka samu tarba daga me mrtaba sarki da kanshi.
Lantana fakar ido tayi ta wurgar da torchlight din,carab akan idon suhaima,cikin dariya suhaima tace.
"Ah ya haka zaki yarda fitilar in aka dauke wutar kumafa?"
Dariya lantana tayi sannan tace,
"bari kedai ay dole na yardar,sabida nakunnata naga bana ganin haskenta shiyasa na yardar,tunda hasken garin yafi nata"
Daganan kai tsaye fada aka wuce da ayarinsu,me martaba sam be lura da su twins dake bacci a hannun innar hanne da hanneba.
Muje zuwa
surbajo for life.
surbajo for life.
����������������
*KANO TO JIDDAH*
����������������
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Gatan surbajo Allah*
*dedicated to zahra bukar*
*57-60*
Sun isa fada se anan sarki yaga su twins,murnar da yayi shida mahaifiyar shureim inaga tafi ta shureim dinma.
Masauki akabasu,lantana tayi tuntube ta fadi yafi so goma sabida tsabar kalle kalle.
Washegari da safe,aka ba su baffa ɓangare guda agidan sarki,da masu ayki,murnar su bazata misaltuba.
Hanne da innarta ko,suhaima cewa tayi gidanta zasu zauna.
Shureim be musaba dazasu tafi suka tafi da su.
Bayan sati guda da dawowarsu aka gudanar da gagarumar walima ta sunan su twins,ba karamin,kyayatarwa tayiba.
Se alokacin suhaima ta tambayi labarin kafilat,rai abace shureim yasanar da ita komai.
Ayko hanashi sakat tayi seda yaje tare da ita aka fito da kafilat din gabadaya tayi baki gwanin ban tausayi.
roƙonsu gafara tayi,dukansu suka yafe mata,sannan suka sata ajirgi ta koma kasarsu cike da dumbin danasani.
mahaifinta, tana dawowa da sati guda ya ɗaura mata aure da dn amininsa.
Shureim yasaka suhaima makaranta sosai take fahimtar komai,su twins sunyi wayo abunsu,gwanin shaawa.
babu me ganin baffa da lantana yaganesu sunyi kyau abunsu,haka su hanne.
Shiko rabiu kusan duk bayan wta biyu se yazo sabida business yakeyi sosai.
So da kauna shureim kullum cikin nunawa suhaima yake ko kadan beson damuwarta abunda takeso akeyi.
Baffa yayi kuka yayi kuka ba adadi na rashin mahaifiyar suhaima araye,shiyasa kullum a harami yake wuni yana mata addua.
Hajji da umarah sunyi ba adadi,rayuwarsu gwanin ban shaawa
Hajiya suhaima anzama babbar mace abun so da kauna agurin shureim.
*ALHAMDULILLAHI*
*ALLAH KAI KAKE IYAMIN BANI NAKEBA*
*DA SANINKA DA YARDARKA NAKEYI*
*ALLAH KA KARENI DAGA SHARRIN DUK WANI ABUN KI AMEEN DON ALFARMAR ANNABI DA AL-QUR'ANI*
*ANAN KANO TO JIDDAH YAZO KARSHE,SE ANJIMANKU*
*SURBAJO CE IYA WUYA AKWAI ALLAH*
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:
+2349030159301