..........Assalamu alaikum.
sallamarsu ya Umar tadaki kunnuwansu Dr jafar daketa kwasar dariya suna tsokanar Hafiz ango.
Kusan atare duk suka juyo, mamaki, al'ajabi, razana duk tasaukar musu alokaci d'aya. Cikin murmushi su ya Umar suke mik'a musu hannu. Haka suka dinga basu hannayen tamkar sokaye.
Tabbas ganin ya Umar cikin shiga ta kamala da dattako ta razanasu, hakama ganin muktar da ya Umar tare yakad'a hantar cikinsu, saikuma ga yazeed ma, towai yaushema yazeed yasamu Umar? Amma ko'a wancan satin yazo majallissa haryake tambayarsu babu labarin Umar dai har yanzu ko?.
Sukuma suka shiga gulmar Umar d'in alokacin.
Amma yaukuma saiga Umar da yazeed, harda Muktar Wanda basu ta6a tunanin yama had'a iri da ya Umar ba.
Sudai su ya Umar ALLAH Sanya alkairi suketa zubawa.
Ya Umar yasauk'e kwayar idonsa cikinta Hafiz, fuskarsa d'aukeda wani murmushin mugunta, angon Lubna kasha k'amshi! ALLAH yasanya alkairi abokina, inatayaka farinciki gsky....
Yana gama fad'ar haka yad'auke idonsa daga kan Hafiz. Sosai jikin Hafiz yayi sanyi, gawata kunyar Umar d'in ta baibayesa. Can ya tsinkayi muryoyin su Umar suna musu sallama zasu tafi. Bai fargaba saida ya hango ya Umar zaune a mazaunin direba, yazeed na gefensa, muktar na baya, duk cikinsu babu mai irin kwatankwacin motarcan......
Dr jafar ne yafara jan tsaki lokacinda motarsu ya Umar ta shillah sukabar wajen.... Mtsoow wai wancan wawan waya bashi motane?.
Salman yaywata dariyar mugunta, yo kaimadai Kasan ta munafikin canne yazeed, kokuma wannan dasuke tare, muktar yake kowama? Mtsoww.
Kabeer yay kwafa yana fad'in aikin banza kawai, Dan anbashi aron kaya da mota, shine zaizo yana mana wata burgar banza. Dabamusan asalin balbelaba, dasai tace mana daga masar take.
Tasi'u dayay shiru yana jinsu, danshi tabbas jikinsa yayi sanyi, cikin sanyin murya ya ce, "kai abokaina, anya kuwa Umar bai warkeba? Idan mumce Aron mota da kaya aka bashi, to kwanciyar hankalin dake tartare dashifa?. Kunga kuwa yanda Umar yayi k'iba da haske? Wlhy fatarsa har wani walk'iya takeyi. Nikamarma yafini k'yan jiki, nidake kwana na tashi a AC.
Zasu hayayyak'oma Tasi'u, alkasim ya dakatar dasu, kai kutsayafa, wlhy maganar Tasi'u gsky ce, tabbas akwai wani Abu ak'asa dangane da Umar.
Hafiz dai yakasa cewa komai. Suma sauran kowa yayi gum yana dogon nazari........
Na ce, " hummm, kowadai yadaka rawar wani, aiya rasa turmin Daka tasa.....
★
Acan kuwa su ya Umar tunda suka tafi suketa shek'a dariya. Cikin dariya Muktar ya ce, "wai kunga idanun Hafiz kuwa, kuru-kuru... Hhhhhhhhhhh!!!.
Suka tuntsure da dariya, yazeed ya ce, ''ai duk mamaki ya kashesu k'ananun 'yan iska kenan. Wani abuma sai sunganka a kasuwa Umar. Hhhh
Ya Umar yay dariya harda dukan sitiyari, wai nifa abinda yabani dariyama shine kallon da Tasi'u da Alkasim sukemin, kaikace yau suka fara ganina. Ina kalon salman harda ta6a gefen rigata yaji wace shadda na saka.
Haka sukaita hira suna dariya, daga nan gidan yazeed suka wuce. A can sukaci abincin rana mairai da lafiya Wanda matar yazeed tadafa, Dan yanzu Alhmdllh ta iya girki, yanda su ya Umar sukaita Santi sai yazeed yaytajin dad'i aransa, lallai shawarar Umar d'in tamasa amfani, danshi ya ce, ''yasakata makarantar koyon girki. Gashi kuma shawararsa tayi musu dad'i su suka, Dan yanzu ko yawan fad'an nan basayi da ita.
Saida sukayi sallar la'asar a masallacin anguwar su yazeed sannan muktar da ya Umar suka taho sukabar yazeed a gidansa.
Da sallama yashigo gidan nasa, ganin takalma reras ak'ofar falon yasashi jan birki, Dan muryoyin mata yake jiyowa dayawa sunata hira da dariya.
Harya juya zai koma saiga inna baito tafito daga band'akin tsak'ar gidan.
A'a Umaru kadawo?.
Eh wlhy inna, ya gidan?, wani biki ake haka?.
Dariya inna baito tayi, ta ce, "a'a su Sa'adatu nefa.
Kallan takalman yakumayi, ya ce, " inna amma naga talkalmane reras, harsu nawane?.
Su 6 ne, fatee, Rafi'a, kaltume (d'iyar inna baito Ce), Sa'adatu, saikuma Saddiqa matar muntari.
O wlhy nama zata wasu bak'ine daban.
Shida inna baito suka shiga.
Saddiqa naganinsa tatashi tana musu sallama, dantasan itama nata mijin ya dawo, gaisawa sukayi da ya Umar tatafi.
Shima ya zauna suka gaggaisa, Anty Sa'a ta ce, "Umar wannan d'aukar wanka haka? Daga ina?.
Shafa kansa yayi yana dariya, idonsa akan Asma'u dake tsiyaya masa ruwan sanyi a cup, ya ce, " Anrty Sa'a d'aurin aure mukaje wlhy."
Tofa, waye yayi aure a irin wannan time d'in haka?.
Ya Umar yakar6i ruwan da Asma'u take mik'o masa, yad'an ta6e bakinsa sannan ya ce, "wani banzane,.... saida ya shanye ruwan sannan yajuyo yana kallon su Anty sa'a dasuka had'a baki wajen fad'in banza kuma!!?.'"
O sorry, wani abokina zance mukufa.
To ALLAH ya sanya lkairi suka fad'a atare.
Ya Umar yamik'e tsaye batareda yace aminba.
Asma'u ta ce, "Abincifa?."
Shiru yayi yashige d'akinsa.
Anty Sa'a ce ta ce, "mata tashi kibishi d'akinsa, waya gaya miki ana tambayar miji yanason Abu acikin mutane? Asma'u nakula sainayi training d'inki gsky akan kula da miji."
Shiru Asma'u tayi tamik'e zuwa d'akin ya Umar, tanata tunane-tunane aranta, ita kanta tana ganin wataran kamar batayin abunda yakamata wa mijinta, to amma tayaya zata gyara? Gsky itama tanason taga suna rayuwa da mijinta kamar yanda akeyi acikin Hausa novels, abin Na birgeta sosai, musamman data kula ya Umar d'an son soyayyane. Itama tanason soyayya, to amma saita rasa yanda zata nunama ya Fharuk d'inta, Dan ita mutumce mai kunyar tsiya, dukda tad'anyi karatunta har zuwa diploma, yakamata kuma ace kanta yawaye, amma matsalar da'aka samu shine harta gama karatunta batada wata k'awa, k'annenta sune k'awayenta, wannan yasa batasan wasu abubuwanba dayakamata mata tanayima mijinta danya zama NATA ita kad'ai.
Kamar yanda Anty Sa'a ta ambata to zata nutsu danta samu training d'in kama ya Umar d'inta ahannu ita kad'ai..........
Tunda tashigo yake binta da kallon mamaki, shin mike damun matar tashine haka? tana tafiya tana tunani?.
Shigowarta takai minti 15 a tsaye, amma alamu sun Nina masa bamata tareda duniyarsu baki d'aya, hankalinta yatafi zuwa wata duniya tadaban. Ya girgiza Kansa tareda tasowa har zuwa Inda take atsaye tana cigaba da sak'a wasik'ar jakuna.
Bata ankaraba saitaji an d'alli bakinta. Cikin Sauri tasaka hannunta tadafe bakin, tareda kai dubanta gamai mata wannan aika aikar haka.
Ya Fharuk ne tsaye agabanta, yacire kayansa dagashi sai best da gakeren wando, ya hard'e hannayensa ak'irji idonsa k'ur akanta.
Ta sauke ajiyar zuciya ahankali sannan takauda kanta.
Ajiyar zuciya ya sauke shima tareda warware hannunsa, Asmah kinada gyara sosai ta hanyar kula dani wlhy, akwai abubuwa masu yawa dakikemin inajin dad'insu dakuma yaba miki.
Akwaikuma masu yawan gsky da idan kikaimin suna 6atami6n rai, nidai asanina mace kullum k'ok'arinta yanakan tarairayar mijintane, ammafa ke agareki Bahaka baneba. Tabbas abinda nagaza samunsa abaya sanda inatareda Lubna nasamesu agareki, harma mafiyansu, saikuma abinda nake samu ga lubna kekuma bakiyiminsu.
Asma'u ni mutumne maison zama da wayayyiyar mace, bawai wayewa ta rashin kunyaba, wayewa irinta zamantakewar aure, nifa a ganina idanhar mace tanason mijinta yazama NATA 100% tofa saita zama Mara kunyar k'arfi da yaji.KeKekuma kunyarki tanad'an cutar damu gsky..
Duk wannan magamar da ya Umar keyi Asma'u natsaye idanunta Na zubar da hawaye, tabbas tasan akwai gazawa a al'amuranta Na kula da mijinta, amma tana buk'atar shawara.
Suduka kowa yayi shiru, ita tana kuka, shikuma yatsura mata idanu yana kallonta, amma yakasa wani yunk'urin lallashinta.
Sunkai tsawon minti 7 ahaka sannan ya Umar Yakama hannunta suka koma bakin gado suka zauna. ganin kukan NATA bamai k'arewa bane yasakashi jawota jikinsa ya rungumeta sosai yana shafa bayanta alamar lallashi, amma uffan baiceba.
Nanma saida sukaja wasu lokuta sannan Asma'u tad'ago tana kallonsa, ya Fharuk Dan ALLAH kayi hak'uri zan gyara, Nima kaina inaji a raina akwai abubuwan danakeyi ba daidaiba, amma rashin nunawarka yasa bana fahimta sosai balle na nemo hanyar gyaran.
Murmushi ya Umar yayi yana kamo hannunta, to yanzun Na nuna da kaina my Asmah, saiki gyara ko? Namiki hakane saboda kar agarin sakakinkifa Na hango wata awaje ta kwace miki ni. Yay maganar cikeda zolaya yana d'age gira sama.
Bakinta ta turo gaba, ni wlhy kabar fad'a, ALLAH banason kishiya.
A indaifa kina sakaci da rik'ona aiko zata kwankwaso miki k'ofa, dama ga d'aki nan inadashi. Jibafa tun kayan danatafi nabarki dasune ajikinki, tunfa na wankan safene, nasan kuma bazaki ciresuba sai wankan barci, amma sanda kina amarya bakyayin wannan kazantan? tundagadai cikin fodeyo kika fara wannan abun, gashinan yanason zame miki jiki.
Shiru tayi tana kallon hannayensa masu laushi da santsi dake rumtse da nata, tasan gsky ya Umar duk yake fad'a mata.
Ganin tayi shiru yad'an girgiza hannunta, kifayi hak'uri badan cin fuska nake fad'a miki hakaba, inaso kigyarane Dan nazama naki kekad'ai da yaranmu my Husna, inasonki dayawa, shiyyasa banason wani Abu yazo yasaka sonnaki yin rauni azuciyata kinji, tunkina 'Yar k'aramarki nake sonki har kika girma.....
Da sauri Asma'u tad'ago tana kallonsa, yamata murmushi, baki yardaba ko?.
Shiru tayi batace komaiba, ya matsa hannunnata, takuma d'agowa tana kallonsa. Muryarsa can k'asan mak'oshi ya ce, "nasan kema kina sona aii, amma kikaita 6oyewa, amma ni tuni naganoki. Ban gaskata hakanba sai aranar da aka sakamin rana da Lubna. to karki damu, yauga Umar fharuq mallakinki ke kad'ai da fodiyonmu. Ammafa idan kika cigaba da sakaci zai samo miki mai tayaki kula dash....
Ai bata bari yak'asa fad'aba tafad'a jikinsa ta k'ank'amesa tareda sakin wani kukan shagwa6a.
Shima saiya rungumeta yana dariya, 'yammata bimin kanki ahankali karki 6allomin ruwa d'inkin yafarke nashi 12. yakamatama nakira Dr Al-Ameen naji yaushe zamuje a kwancene?.
Itadai tana lafe ajikinsa tana shashshekar kuka.
Cikin 'Yar dariya ya ce, ''nasan inda wannan kukan yadosa da abinda kikeso, bara kigani namiki kar asaka uwata awak'a.
d'agota yayi ya manne bakinsu waje d'aya. Tun Asma'u na mutsu-mutsin kwacewa hartayi lif itama tafara bada gunmawarta....
Hummm masu karatu! Wata sa'in muma matafa akwaimu da gulmar tsiya aradu🤔🤪.
♣♣♣.
Tundaga ranar Asma'u da ya Umar suka shirya, yanzukam abubuwan datasan yanaso komai kunyar datakeji haka take dannewa tamasa. ga Anty Sa'a daga gefe tana koyar da ita wasu darussan. hakama inna baito, tunda ta fuskanci Asma'u sokuwace saita d'auki d'ammarar kowa mata yanda zata kula da mijinta.
Ayanzukam shikansa ya Umar yaga canji sosai, farinciki yacika zuciyarsa, wani son Asma'u nak'ara ratsa jijiya da 6argo zuwa jininsa. Shima tattalinta yakeyi sosai. Yakaita asibiti an kunce d'inkin CS d'inta, Dr Al-ameen kuma yabasu shawarar yanda zata kula da kanta batareda samun matsalaba, yakuma bata wasu magunguna.
Har harabar asibitin yarakosu hannunsa d'aukeda fodiyo, yanata yaba k'iba da lafiyar yaron, gashi masha ALLAH k'yak'yk'yawa son kowa k'in Wanda yarasa.
Gaban Dr jafar yafad'i Dan hango su Umar tsaye sunata dariya shida Dr Al-ameen cikeda nishad'i. Ga Asma'u agefensu cikin k'yak'k'yawar shiga ta alfarma, shikansa ya Umar d'in sanye yake da wata d'anyar shadda blue sai maik'o takeyi, tad'inku da d'inkin zamani, ga hularsa k'ube ya Murza mai adon farin zare da ratsin blue. Sai annurin farin ciki da kwanciyar hankali suke fitarwa.
Ganin ya Umar yakar6i Fodiyo daga hannunta Dr Al-ameen, Dr jafar ya ce, "kai, dama matarsa ta haihu?. Dukda sunad'an nesa dashi yana hango k'yak'yk'yawar fuskar fodeyo, da a ka masa kwalliya da milk d'in kayan sanyi na alfarma, ya sauke wata ajiyar zuciya alokacin da ya Umar yabud'ema Asma'u mota tashiga, ya rankwafa ya saka mata fodiyo akan cinya, wannan yarufesu yadawo sukai sallama da Dr Al-ameen shima yashiga motar suka tafi.
Jikinsa har rawa yakeyi yashiga motarsa shima sai majallissa kai rahoto, Dama yatashi daga aiki Dan yamma tayi............
🤣🤣🤣🤣🤣.
*_Amarya Lubna_*
Su Lubna amarya, antare akatafaren gidan data samu gado, Dan tace bazata zauna gida d'aya da matar Hafiz ba, a gidanta zata zauna. Babu musu ya yarda kuwa.
Komai na alfarma tazuba agidan, kud'inta kam bak'aramar girgiza sukayiba, ga 'yan aiki data Loda agidan, kowa da aikinsa, harda masu yimata tausa daban.
Amarci kam itada Hafiz ana dirzarsa, jitake kamar yanzu tayi auren farko.
Tamanta da kowa da komai, komai NATA sai Hafiz.
Shikam tarairaya iya tarairaya yake Nuna mata, matarsama ko lokacinsa bata samu, barema 'ya'yansa da iyayensa. Danginsa kam babu Wanda ke zuwa gidan, Dan Lubna tasaka dokar batason had'in gambiza.
Dayake lalla6ata yakeyi saiya yarda da zancenta, babu kuwa mai zuwa musu gida, shikam aii yazama mijin Hajiya, danko kwayar gero baita6a ajiyewa a gidanba, komai da kud'in Lubna akeyi tunda ta nuna tanadasu. Suci mai k'yau su saka maik'yau, suyi barci amai k'yau, dama su Amrah awajen mom aka barosu dansu d'ebe mata kewa....
*_Suhaima_*
Itadai Suhaima akwai banbanci da Lubna, Dan ita amarcin NATA yazo da gargada.
Ashe Ramadan d'an talakawane lik'is, irindai matasannanne masu son k'arya da burgar tsiya, shine Aron kaya shine na mota, dawannan abubuwan yabige tunanin suhaima harta amince ta auresa, Dama kuma tun awaje suke shek'e ayarsu.
Sai lokacin da'aka kaita taganta awani d'an gida kamar BQ d'in gidansu, aiko ranar kwana sukayi tafka bala'i.
Dole washe gari ya yarda suka koma gidanta data samu agadonta itama.
Hakan yamasa dad'i kuwa, Dan kobabu komai ansamu cigaba, dama wancanma babansane Yakama masa Hayar, Dan Ramadan baya aikin komai sai tsalle-tsallen 'yanmata. Sune samarin shaho na wannan zamanin.
('Yammata sai ayi hattara da samarin shaho, Dan akwai irinsu Ramadan dayawa suna yawo cikin duniya).
*_(((S)))......2018_*
*_Luv you all_*
[1/4, 4:45 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*
*_page→71-72_*
..........Kiyyyyyy!! Yaja wani wawan birki agabansu. duk arikice suke kallonsa, Salman da shima isowarsa kenan yasa k'asan rigarsa yana toshe hancinsa saboda wata k'ura da Dr jafar ya tayar awajen.
Ganin yanda yafito abirkice yasaka sauran mik'ewa gaba d'aya, har sassarfa yakeyi yana had'a k'afa kamar zai kifa Dan k'ok'arin k'arasawa inda suke zaune.
Saidai kuma yana zuwa garesu kallonsu yacanja akala daga gareshi zuwa bayansa, Hafiz da Kabeer hard'an tureshi gefe sukeyi danson kallon abinda suka gani sosai.
Shima sai kawai ya waiga domin bawa idonsa abinci.
Motar ya Umar ce ta tsaya awajen, gaba kad'an da motar Dr jafar. Fitiwarsace taja hankalinsu wajen kallon mamaki agaresu. Shikam koma Inda suke bai kallaba, ya zagaya inda Asma'u take yabud'e mata k'ofar, fodeyo tafik'o masa, yakar6eshi hannu biyu yana murmushi da fad'in yauwa my dear son! Yau kanashan yawo ko?.
Asma'u tafito tana murmushi, yaya shima aii gara yasan gari ko?.
Cikin kallon k'auna ya ce, ''Kodai ke kinaso kiga garin? yafad'a tareda lakace hancinta.
Dariya sukayi gaba d'aya sannan suka jera atare suka nufi ainahin cikin mall d'in, ya Umar na rungume da fodiyo, ga Asma'u a gefensa cikin farinciki.
Su Hafiz kuwa tamkar sokaye haka suka dafama su ya Umar baya da kallo.
Tun a k'ofar wajen masu bud'e k'ofa suka fara rissinawa suna kwasar gaisuwa wajen uban gidansu.
Shikam cikeda fara'a irinta sanin hak'k'in d'an Adam yake amsawa, da nuna musu iyalinsa. Sunajin haka suka rissinawa suna gaida Asma'u itama.
Acikima bata canja zaniba sai rissinawa ma aikatan sukeyi suna kwasar gaisuwa.
Masu siyayya kam sunyi tsai tsaye suna kallonsu ya Umar d'in.
Wasu 'yammatanma harsun k'yasa😉. (Kunsandai rayuwarnan indai kanada 'Yar daud'ar duniya, to yanzu zakaga 'yan mata Na rawar kai akanka). ALLAH yasa mudace.
Da Sauri sadam yataso ya tarbesu, kar6ar fodiyo yayi daga hannun ya Umar tareda gaishesu.
Cikin zolaya Asma'u ta ce, ''lallai Na Rafi'a dolene kuyi Fari kaida ya Harris, Ashe kullum cikin Ac kuke wuni?.
Dariya sadam yayi, kai antymu kin iya Sheri wlhy, amma nidai bazance komaiba harsai kin bani Rafi'a zakiji bakina.
Dayawan mutanen dake gurin saida suka dara, Asma'u ta birge dayawan mutanen wajen, Dan da watace matar mai irin wannan wajen ai da irin shegen mai girman kannan za'ayi, da d'aukar kai, amma jiba yanda take wasa da dariya da ma'aikatan wajen. Dukdadai da alamar sanayya tsakaninta dashi, amma ta birgesu gskiya.
Ya Umar dake musu dariya ya kamo hannunta, kinga my Husna bar shiriritarnan idan kunje gida kwayi, muje kisayi abinda zaki saya mu wuce.
Kallonsa tayi cikin langa6e kai, yaya sayafa? Muda shagonmu?.
Cikin tsokana ya ce, "kema saikin biya aii".
Juyawa tayi tana kallonsu Harris da hankalinsu gaba d'aya yake kan Fodiyo suda wasu ma'aikata, Baki tad'aga zata kira Sadam, ya Umar yasa hannunsa ya toshe bakin. K lafiyarki kuwa? Mizakiyi?.
Kiransu zanyi naji waye ya kafa dokar?.
Cikin dariya ya Umar ya janye hannunta suka shige wani d'an d'aki, Ashe Office d'insane awajen. K'ofar yamaida yarufe yana dariya, kai my Husna ALLAH ya shiryaminke?.
Itama dariyar tayi tanabin ko'ina Na falon da kallon.
Manya-manyan hotunansu guda biyar tagani a kowace kusurwa ta office d'in, itadashi da fodiyo, akowace kusurwa, saikuma asaman tebur d'in an ajiye wani madaidaici itadashi nanma da fodiyo.
Kallonsa tayi, shikuma ya d'aga mata gira yana murmushi.
Itama ta sakar masa da murmushin tareda zuwa ta rungumeshi, hannu biyu ya kar6eta shima ya k'ank'ame kayansa, burinsa kullum yaga Husnarsa cikin farinci, yarinyar data masa hallacci alokacin damutane masu yawa da muhimmanci arayuwarsa suka gujesa, yarinyar dake sonsa Dan ALLAH badan dukiyarsaba, yarinyar data sadaukar daduk wani farincikinta domin NASA ya inganta, yo idanma yagaza Nuna mata k'auna aii yayi butulci mai yawa.....
Asma'u tad'ago tana kallonsa, amma fuskarta tad'an sauya, cikin langa6ewar kai ta ce, "ya amma banga su twins ba?."
Shima fara'arsa ya rage, sannan ya kauda zancen ta hanyar cewa muje yamma nayi karmu kwasarma fodiyo sanyi yazo yana mura.
Komawa tayi takuma k'ank'amesa, yaya kabani amsar tawa tambayar mana.
Wannan ba maganar nan bace, bari saimunje gida.
Baijira amsartaba yafice abainsa.
Itama dolene ta take masa baya Dan tasan halin kayanta sarai.
Ak'ofar office d'in tasameshi yana jiranta, ahankali suketa zagayawa suna d'aukar abinda suke buk'ata, dawanda fodiyo yake buk'ata, harda Hasiya da inna baito dazata koma gobe idan ALLAH ya kaimu.
Sosai suka Lodi abubuwan buk'ata, suna gamawa wani ma'aikaci yazo ya kar6i kayan, wajen kashiya's yaje Harris da sadam suka kar6a akai total.
Amamakin Asma'u saitaga ya Umar yaje yabasu ATM d'insa sun cire kud'in, aranta ta Ce, "Ashe da gsk yaya yakeyi.
Bayan sungama komai tsaf suna shirin fita saiga Yazeed da Muktar sundawo daga wajen aiki, dama haka sukeyi, idan suka dawo saisu lek'o suga yanda komai yake tafiya kafin sutattafi gida.
Juna suka rungume suna murna.
Muktar ya ce, " mutumina kace soyayya kafito?.
Dariya ya Umar yayi tareda fad'in ALLAH yashiryaka Muktar.
Ameen suka fad'a cikin dariya.
Asma'u ta gaidasu da tambayar aikinsu, duk suka amsa cikin fara'a sannan yazeed yakar6i fodiyo yana fad'in kud'an rakamu wani waje mana kaida madam.
Ya Umar ya ce, ''to aja zuga!, ina kuma zaka kaimi? Mudake shirin tafiya gida?.
Kudai kubiyoni kawai.
Haka kuwa suka rankaya suka tafi, Asma'u Na a bayansu.
Ganin inda suka dosa ya Umar yaja tunga. Cikin had'e fiska yazeed da Muktar sukace babu jayayya a tsakaninmu.
Ya Umar baice komaiba yakad'a kai suka cigaba da tafiya har majallissarsu Dr jafar.
Suna ganin sun nufosu kuwa sukayi gum daga sambatun surutun dasukeyi tun d'azun akan ya Umar.
Hannu sukaita basu ana gaisawa, duk jikinsu yayi sanyi, yazeed yamik'a musu fodiyo, to 'yan uwa gafa Usman fodiyo, ankawoshine shida madam domin Susanya albarka awajen dadynsa Umar daya gyara.
Kalan kallon aka fara, salman d'aya kar6i fodiyo yayi murmishin takaici, aransa ya ce, ''gashi k'yak'yk'yawa kuwa.
Asma'u ta ce, "ya gajiyarku ya iyali? Idan bazaku damuba muna gayyatarku walima ta mik'a godiyarmu ga ALLAH akan ni'imomin daya azurtamu aciki, ga d'aya daga cikinan shine gyara mall d'inmu daya dawo kamarma wuta bata cishiba, na biyu shine ku6utar kayan ya Fharuk daga hannun custom, na Uku shine albarkar haihuwar fodiyo da ALLAH ya azurtamu dasamu.
Yanda take magana adake tayi mugun basu mamaki, shikansa ya Umar kallonta yakeyi cikeda al'ajabi da birgewa, baita6a tunanin matar tasa jaruma baceba sai ayau. Dukda dai yasan dama Asma'u akwai tsiwa, amma azatonsa ta daina.
Muktar da yazeed kam bak'aramin birgesu Asma'u tayiba, Dan sai zabga murmushi sukeyi.
Tana gama fad'a kuwa ta ce, " inafatan zaku amsa gayyatarmu, nabarku lfy, yaya idan kun gama INA mota, tajuya cikin takun girma tabar wajan.
Duk binta sukayi da kallon, saikuma kishi yata6a zuciyar ya Umar, dad'an k'arfi ya ce, "malamai kallon ya Isa haka, ko kun manta matar aurece?.
Ajiyar zuciya suka sauke suduka, kowanne yanamai janye idonsa daga kanta.
Yazeed yamik'a hannu ya kar6i fodiyo dahar yanzu yake a hannun Salman, sai wani k'ara k'ank'amesa yakeyi tamkar nasa.. 😉
Yana kar6a suka bar wajen, acikinsu Dr jafar babu Wanda ya iya koda kwakwkwaran tari har su muktar suka kai ga mitar Ya Umar.
Asma'u naciki yazeed yamik'a mata Fodiyo, sannan ya ce, " madam sannu da k'ok'ari, aibansan haka kema kikeba da jarumta.
Dariya sukayi gaba d'aya, ya Umar ya ce, "tab, ai dama Husna matsiwaciyace, Ku kawai takema alkunya, koba hakaba tawan? Yafad'a yana d'aga mata gira.
Harar wasa Asma'u tama ya Umar ta ce, ''bandadai Sheri my boss."
Nanma dariya sukeyi sosai.
Su Tasi'u duk suna kallonsu, kuma azatonsu su sukema dariyar, Dan haka duk jikinsu yakumayin sanyi, wasuma harsum fara nadamar abinda suka aikata ayau.
Ya Umar yatada motar sukayi sallama dasu yazeed suka tafi.
Dayazo saitinsu Dr jafar ma saida yad'aga musu hannu, amma ko tari babu Wanda yayi acikinsu, Dan duk sunyi gum, tundasu ya Umar suka bar wajen babu Wanda ya iya cewa A acikinsu, saidai kallon kallon kawai da zare idanu.
Nikuwa na ce, "hummmm.
__________________________
Ahanya ya Umar da Asma'u sai hirar abinda yafaru sukeyi suna dariya.
Dahaka har suka isa gida. Ya Umar yakwashi ledojin itakuma tasa6i fodiyo suka Shiga.
Afalo suka iske su hasiya da inna baito sunacin tuwo.
Bayan sun musu hannu suka zauna, ya Umar ya ce, " inna yau tuwo akamana?."
Wlhy tuwo nayi Umaru, nidai nagaji dacin shinkafarnan.
Aii wlhy inna kin taimakemu, nikaina bawani damuwa nayi da irin wad'annan abubuwan naiba, nifa aka bani tuwo to anmin dai-dai. Amma su o, e, aii ba'aso, saidai kayan kwad'ayi.
Asma'u datasan da ita yakeyi, ta cuno baki gaba amma batace komaiba.
Ya Umar yace nidai kar aji haushina bankira sunaba dai ko Hasiya?.
Oho dai, aikowa yay zagi akasuwa yasan dawanda yake. Cewar Asma'u tana Barin wajen.
Dariya suka rakata da ita suduka.
Ya Umar ma yamik'e yana fad'in inna bara na rage kayan jikina naje massalaci, danyau zaman cin tuwo zamuyi.
To Umar afito lafiya.
To innarmu, gobe iyanzu munyi kewarki wlhy, dama kiyi zamanki taredamu kawai, zamuyi farinciki wlhy.
'Yar dariya kawai inna baito tayi, ta ce, "a'a Umar, mijinafa?.
Saidai kuma haka inna, amma jimuke kamar karki tafi. Dariya kawai inna baito tayi. shikuma yashige d'akinsa.
*_Lubna_*
Zaune take a k'ataccen falonta, ta mik'e k'afafu gabanta kayan fruit ne da aka yanka k'anana, gefe kuma ga farfesun kaza daya gama had'uwa.
Nikaina 'yar rahotonku saida yawuna ya tsinke😋.
Ahankali takeci tamkar bataso, gefe kuma masu aikintane kemata tausar k'afafunta.
Wayarta dake wringing tamik'a hannu ta d'auka, ganin mai kirannata yasa murmushi fad'ad'a afuskarta.
Hello Hajja Sadiya ykk?.
Daga can aka amsa mata da lfy lau Hajiya lubna, dama kayane suka iso shine nace bara na sanar miki kafin mutane su za6e.
Wani murmushin k'asaita Lubna tayi, tareda danna tsokar nama abakinta, cikin tauna naman ta ce, "OK Hajja sadiya ngd fa, zuwa anjima kad'an zan shigo insha ALLAH, Dan munada biki satin sama.
To shikenan ALLAH ya kaimu lafiya.
Uhum tafad'a tana ajiye wayar batareda ta yankeba.
Kad'an takumacin naman ta tureshi gefe tana yatsine fuska. Bilki akaimin fruit d'innan cikin firij saina dawo zansha. Tayi maganar idonta akan 'Yar aikin dake dama da ita.
Cikin hanzari kuwa bilki mai aiki ta amsa, d'aukatayi tanufi kicin domin cika umarnin madam.
Lubna kuwa d'aki tashiga, aka sake sabon wanka, cikin shiga ta alfarma, saigata tafito rik'eda key n mota, da k'aramar handbag mai azabar kyau. Takun lubna kawai abin kallone, Dan tabbasa 'Yar gayuce ta fad'a da k'ari, komai nata mai ajine🧐.
Motarta tashige sai gidan Hajja sadiya dillaliya, amma mai lasisi, dankuwa kayane Na manyan k'asa take kawowa. babu tambayar miji atsarin Lubna, ayayinda zata anguwa, saidai yazo ya iske bata nan.
Yanzuma tana fita yana shigowa anguwar, yad'anga gilmawar motarta, amma zuciyarsa bata amince itad'in baceba. Saida yashigo harabar gidan ya faka tashi motar sannan yakula babu d'aya daga cikin motocin Lubnar. (Dan kuwa motar Lubna ak'alla takai hud'u agidan, kuma duk Na gararine da nunawa sa'a).
Baice kimaiba yanufi cikin gidan.............
*_(((S))).......2018_*
*_I Love you all my fan's_*
[1/6, 5:08 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*
*_page→73-74_*
..........Babu kowa afalon sai k'arar AC dana TV. Su bilki sunacan kan sauran farfesun da Lubna ta rage sunaci itada saude.
Cikin d'akinta ya k'arasa, ko INA k'al yake, dama a 6angaren tsafta bashida Matsala da Lubna, dukda dai 'yan aiki keyi ba itaba, saman sofa ya kwanta yana k'arema ko INA na d'akin kallo, amma zuciyarsa da tunaninsa nakan ganin da sukaima Umar ayau.
Lallai suma sunsan Umar yagama kama k'asa, kuma kaf d'insu yafisu komai. Dama can yafisu d'in, ayanzuma garashi dayake auren Lubna kud'i sun k'ara zauna masa. To amma aii banasa baneba, dan yamzudai kam Lubna babu abinda bata fishiba, koda kaddarorin data samu a gadonta sun Isa ta keremasa sa'a, shiyyasa yakula take kallon kanta samadashi. Wata kwafa yayi yana kad'a kai, yakula idanfa yatsaya jiran ya huce, tofa rabon wani zai ratsa. Da sauri yatashi zaune, haryanzu yana a duniyar tunani. Tabbas a farko ya auri Lubna ne dansu bak'anta zuciyar Umar. Ammafa ayanzu tunaninsa yafara sauya akalar tafiya wani 6angare. Yatuna da maganar Kabeer alokacin dasuke kulla wazai auri Lubna d'in?.
*_tab wlhy dabadan matana biyuba, kuma ko sati biyu ban k'ullah da k'ara aureba, ga dokar da dady yasamin akan k'aro ta uku, toda wlhy nizan auri Lubna koda Umar zai mutu. Sannan ita kanta saina tatseta tas, dan fak'iriya ta gsk zan maisheta aradu kuwa. Suma aii Tara musu akayi, kunga kuwa nima saina dangwali arzik'i._*
Alokacin Hafiz babu haka kokad'an aransa, da zuciya d'aya ya amsa zai auri Lubna tunda yad'an fisu k'yau da kud'i, kaitsaye zatafi kar6arsa fiye dakiwa a majalissar.
Ya wani mik'e tsaye yana tafa hannaye, _"ni shegiya inji d'an daudu!"_ dazanma kaina sabalula, baijira wani dogon tunaniba yafara bincike ad'akin Lubna, duk wasu muhimman takardu Na filaye da gidaje Na Lubna saida ya lalubesu Tas, k'ananun kawai ya bar mata, yana gama had'awa Yakama hanyar fita, harya kai falo saikuma yadawo, wani tunanine yazo masa, baikamata yakwashe komai lokaci d'ayaba, Dan tabbas zata gane shine.
Saikawai yajuya yamaida komai, takarda d'aya ya d'auka da wasu kud'i 200k daya gani a dirowar gefen gado yafita zuwa gidan Uwargidansa, dama yau itace dashi, yazo yima Lubna sallamane kawai.
Lubna tana zaune dirshen gaban Hajja Safiya, kaya kawai taketa lodama kanta Na garari, Hajja sadiya kam saida dad'i takeji, dama tasan Lubna babu wasa, data saya zata Baka kud'inka, gashi kuma zata yaya dayawa, Dan yanzu batada babbar customer kamar Lubna.
Saida ta Lodi kayan 2millions NATA Na kanta, sannan shima Hafiz ta d'iba masa. (Yo ba ita tataraba, batasan zafinsuba, sanda aka nema tana gado tana barci hankali kwance)😎.
Aledoji Hajja Safiya ta jibga matasu, tasaka 'yan aikinta sukaita kaiwa mota, todama kayan bawani d'inbin yawane dasuba, tunda Na 'yan k'aryane, daga less d'in 300+, sai tanfar 200+, hakama gyale dukna manyanne, barema takalma da jaka, ga yari da kayan kwalli, Dan komai Hajja sadiya saidawa takeyi. Amma dukda haka saida bayan motarta da but suka cika taf, Dan Lubna nason kayan Hajja sadiya, tana siyo kaya masu k'yau da Qualities, gasu designers. Shiyyasa bata k'yashin kashe konawane ta kwashi kaya, dama ga kud'in abanza ana gani.
Sallama sukayi da Hajja Safiya taja mota tatafi, sai gida........
'Yan aikinta ta tura suka kwaso kayan amota, ta kalli bilki amintacciyar mai aikinta kenan, bilki my Sugar yazo gidannan kuwa?.
Eh Anty yazo babu dad'ewama yatafi, inaga yagaji da jiran dawowarkine.
Baki Lubna ta ta6e batareda tace komaiba.
Bilki da sauran 'yan aikin suka fice, itakuma tafad'a bathroom Dan tayi wanka........
___________________________
Safwan kaine ka iya tunawa damu agidannan haka? Kodai 6atankai kayine haka?.
Wata 'Yar dariya Safwan dake gaban mom zaune yayi, mom dama kuna raina wlhy, yanzuma muhimmin abune yakawoni gareku, amma saina k'ara hutawa zamuyi maganar.
To shikenan, ainama godema ALLAH dana ganka yanzuma, jeka huta to, bara nasa ashiryamaka abinci.
To mom, amma yanaji gidan shiru? Inasu baby?.
To ka gujemu ina zakasan mike faruwa agidanku, baby da suhaima sunyi aure, yanzu dagani sai su twins agidan.
Kai yanzunan mom su baby sunyi aure?. Amma banji dad'iba da akayi bananan, ALLAH ya sanya alkairi to. Insha ALLAH dukzanje gidajensu. Matar Ameer fa ta haihu?.
Baki mom tad'an ta6e, ta haihu amma 'yar batazo daraiba.
Ayya my bros ALLAH ya canja damai alkairi, itakuma ALLAH ya jik'anta.
Mom dai batace komaiba, amma mamakin canjawar safwan takeyi sosai, dukya canja mata, ga wata k'iba dayayi ta alamun yanajin dad'i.
Shikam d'akinsa yashige yana wata dariyar mugunta, humm mom dakinsan da shirin danazo gidanan, wlhy datuni kin korani baya, ammafa da ikon ALLAH sainaci nasara akanku.....
😨tofa Safwan dami kazo?.
__________________________
Yanda takeyin komai a kasalance yau kamar mara laka ajiki saita bashi mamaki, dukdadai yasan miya assasa sanyin jikin nata, hakan bai wuce tafiyar da inna baito zatayi yauba.
Itako bama tasan yanayiba, idonta na kan Fodiyo dake shan nono shima yana kallonta.
Inna baito dake kallonsu ta ce, "ALLAH yaronnan kukayi wasa k'iywa zaiyi nan gaba, jibifa ko wata 2 bai cikaba amma yafara sanin fuskar uwarsa.
Asma'u ta duk'ar dakai k'asa saboda kunya. Ya Umar kam dariya yayi, inna aii yafara k'iywarma, kikula indai yana hannunta bakajin kukansa, amma inhar wani ya d'aukesa mintuna kad'an zai fara.
Cikin zaro idanu Asma'u ta ce, ''kai ya Fharuk, Dan ALLAH kadaina fad'a, ALLAH wani yaji saiya d'auka hakane.
Yo da k'arya nakeyi?.
Shiru tayi amma tana hararsa ta gefen ido.
Inna baito dai dariya take musu. Hasiya kam tana school dan suna zana exam na S,s,c,e.
Haka sukaita hirarsu, dukwanda tsokana ta juyo Kansa za'ayi. Har zuwa la'asar da inna baito ta fara shirin tafiya. Yanzu kam hak'urin Asma'u yazo k'arshe, sai hawaye takeyi, daga inna baito har ya Umar dariya suke mata.
Suduka suka shirya har Hasiya data dawo gidan, inna baito sukaima rakkiya har gida da shatara ta arzik'i. Godiya sosai inna baito tamusu sannan sukai mata sallama suka taho cikeda kewarta.
Daganan gidansu ya Umar suka nufa.
Cikin farin ciki mama ta tarbesu, Rafi'a kam kamar ta tashi sama dan farin ciki.
Suna nan zaune anata hira saiga ya Abubakar, kallo d'aya zaka masa kasan abirkice yake, baya cikin nutsuwarsa.
Suduka da kallo suke binsa, bayan an gaggaisa Asma'u ta zame jikinta tabi su Rafi'a dake d'aki suna magana itada Hasiya, inaga sunayine akan Sadam k'anin Muktar.
Mama ta kalli ya Abubakar cikin kulawa sosai, Abubakar mike faruwane haka? Naga tamkar bakada wadatar lfy?.
Idanunsane suka cika da kwallah, yasharesu yana fad'in mama Sakina tagama dani wlhy.
Sakina kuma? Ya Umar da mama suka fad'a atare.
Ya Umar ne yay k'arfin halin fad'in wai Maman Jameela?.
Kansa ya d'aga ahankali.
Mama ta ce, "tomiya kuma had'aku yau?."
Hummm mama dama asheni aikin banza nakeyi, Kullum Sakina cin dunduniyata takeyi, sakina taruguzani, kullum na ajiye kud'ina danufin tari saitabi ta kwashe, ga shagon ya durk'ushe saboda ragad'ar sa datakeyi.
Jiya na had'a kud'i har 1 .5million zanje kasuwa yau shine Sakina ta kwashesu tas, sannan yau dasafe ta titsiyeni saina saketa, hardacewa idan nahaifi cikin uwata na saketa.
Nikuma raina ya6aci na saketa, ni bansan ta kwashe kud'inba saida ta tafi sannan naduba kud'i sukace na d'aukesu Inda na ajiyesu.
Ina k'ok'arin kiranta sainaga wannan takardar awajen data d'auki kud'in. Yafad'a yana mik'ama ya Umar dake kusadashi takardar.
Rubutune d'an kad'an awajen.
↓
_Abubakar bazan iya cigaba da zama dakaiba, Dan kaima nakula *Karayar arzeek'i* na haskoka, gwamma kafin ka durk'ushe kazamemin kaya na kama gabana, nakuma yagi rabona, nidai nayi gaba, 'ya'yanka kuma idan kanaso kazo gidanmu ka kar6a._
Iya abinda ta rubuta kenan, ya Umar yafad'a yana kallon mama dake saurarensa.
Ajiyar zuciya mama ta sauke ta ce, "ALLAH ya k'yauta to."
Cikin ma rairaicewar murya ya Abubakar ya ce, "abinda kawai zakice kenan mama?."
To, mikakeso nace Abubakar? yarinyarnanfa matarkace, abayama nunamin kayi tafini muhinmanci arayuwarka, watsar da kowa da komanka kayi sai sakina. Sai abinda tace shi zakayi, Toni kuwa yanzu miye NAWA?, wanan ai fad'an masoyane.
Kuka Abubakar ya fashe dashi, tamkar wani mace, ya rarrafa gaban mama yana rok'onta gafara da bata hak'uri. Wlhy mama Sharrin shaid'anne dana zuciya, amma tun bayan bikin mufida nayi nadama, Umar Dan Girman ALLAH katayani bawa mamanmu hak'uri, natuba wlhy, kaima ka yafemin abinda namaka, tundaga kan biya maka kud'in asibiti daduk abinda namaka abaya.
Wlhy nayi nadama kunji na rantse muku.
Ya Umarne yataso ya rungumesa, yana fad'in nidai wlhy na yafe maka ya Abubakar, dama can ban rik'eka arainaba.
Ngd Umar, kaidama mai sauk'in kaine, ALLAH yak'arama rayuwarka albarka. Ya nusanta shaid'an daga tsakaninmu.
Ameen ya Umar yafad'a sannan yajuya kan mama yana taya ya Abubakar Neman gafara. Suna cikin haka saiga Abba yadawo.
Yatanbayi ya akayi? Ya Umar yamasa bayanin komai.
Abba ya ce, "kai ALLAH ya k'yauta mana wannan duniya, lallai na tabbata alhakin Umaru ne ke bibiyarmu, Dan ALLAH umaru ka gafarcemu, wlhy yanzu haka Nima cikin iftila'in nake, Dan ALLAH kamana afuw......
Da Sauri ya Umar ya ce, " wlhy Abba na yafe muku, dama can ban rik'eku arainaba.
Kuma nayarda dak'addara k'yak'yk'yawa kokuwa mummuna.
To mungode Umaru, ALLAH yayimaka albarka kaida iyalinka, Yakuma kareku da sharin duk wani mai sharri.
Amen Abba.
Dak'yar suka shawo kan mama ta yafema ya Abubakar, itama ta rok'i gafarar ya Umar d'in, duk ya ce, ''ya yafe musu shikam."
Bayan lafawar komai Abba ya ce, "ai aturama Sakina 'yan Sanda kawai.
Ya Umar ne ya ce, " a'a Abba kubarta, aii duniya makarantace, Wanda baizobama jiransa takeyi. Kubarta taje taci aizasu k'are.
A take anan yayma ya Abubakar alk'awarin kud'i domin yatada jarinsa. Kallonsa sukeyi cikeda mamaki, Dan sunsandai shima bashidashi.
Kallon dayaga suna masane yasakashi yin murmushi, yagyara zamansa sannan ya zayyane musu komai danganeda alkairin yazeed agareshi, dakuma Wanda Alhaji mai kano yamasa shima, har dawowar kayansa Wanda custom suka kama, har bud'e mall d'insa zuwa yanzun.
Rungumeshi ya Abubakar da Abba sukayi, mama kam harda kukan dad'i, murnarsuce tafito dasu Rafi'a.
Nandai akaita mik'a godiya ga ALLAH.
kowa yak'ara Nuna nadamarsa dabama ya Umar hak'uri, akan abubuwan dasukaita faruwa abaya.
Ya ce, "shikam komai ya wuce agareshi.
Ya Abubakar ya d'auki fodiyo shida Abba, sai Albarka suke sakama yaron dabaima San a INA yakeba.
Ya Umar da Asma'u saidai su kalli juna suyi murmushin jin dad'i.
Sai bayan isha'i suka tafi, harda Rafi'a data mak'ale zataje.
Daga nan gidan inna sukaje, itama tayi farincikin ganinsu sosai, musammanma d'an jikanta.
Sunsha hirarsu har baba yadawo akayi dashi, ananma baba ke sanar dasu saurayin Fatee yace zai turo da iyayensa.
Murna sosai sukayi, har Asma'u na tsokanarta.
Oh ni fatee abin dama 'Yar kunshe-kunshece? Yanzu kin sami miji amma ko labari?.
Ayya sorry yaya Asma'u, wlhy bamu wani dad'e da had'uwaba, auren ne kawai yazo lokaci, amma dama inada shirin zuwa nafad'a miki, harnayi kwana biyu.
Oh to shikenan na hak'ura, ALLAH ya Sanya alkairi, yasa ayi damu.
Murmushi kawai fatee tayi, azuciyarta tace amin.
Har goma suna gidan, saida baba ya ce, "su tafi haka nan." 'Sannan sukai musu sallama suka tafi.
Amota ya Umar sunata 'Yar hirarsu shida Asma'u.
Abayama Rafi'a da hasiya sunayin tasu. Fodeyo na hannunsu hardai suka isa gida.......
*_Gidan mom_*
Mom & Safwan..........
🏃♀🏃♀muhad'u gobe idan ALLAH ya kaimu.
*_(((S))).....2018_*
*_I Love you my fan's_*
[1/6, 5:08 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*
*_page→75-76_*
..........Wlhy mom nake gaya miki riba sodai ake samu a harkar, kikalleni yanda na canja, to kud'ine keta shigomin tako ina, shiyyasa naga yadace kuma nazo naji idan kuna buk'ata, dakuyita cinye kud'in abanza aii gara a juya mukusu kuma Ku k'aru. Koya kika gani?.
Ajiyar zuciya mom ta sauke, cikin gyad'a kai ta ce, ''nayarda da maganarka 100% Safwan, kuma Na amince zan bada nawa kud'in, saidai bansan sauran 'yan uwankaba kozasu yarda?.
Zasu yarda mom, Dan zan musu bayani yanda zasu gamsu insha ALLAH.
to shikenan saikayi k'ok'ari, tunda kace sati d'aya kawai zakayi a k'asar.
Insha ALLAH haka nake fata, saboda kasuwar tamu bata buk'atar wasa.
To shikenan, direba saiya kaika gidanjen 'yan uwan naka...............
_________________________
'Yammatana wai har yanzu kewar inna baiton bata sakekibaneba?.
Asma'u dake kwance gefen ya Umar tayi murmushi, yaya kasan ance sabo tirken wawa.
Hakane my Queen, to amma aigani akusadake ko?, yaufa kwanan inna baito hud'u da tafiya, amma kinkasa hak'ura.
Karka damu ahankali zan manta aii.
To ALLAH yasa. Yay maganar yana tashi zaune.
Itama tashi zaune tayi, um bara kaga naje k'ilama fodeyo ya tashi.
Da sauri ya Umar yarik'o hannunta yadawo da ita jikinsa, k bawani fodiyo kinji, natabbata daya tashi dasu Rafi'a sun kawoshi, bagama fatee tana a gidanba.
Kai yaya kallafa agogo, kobabu fodiyo aii akwai had'a breakfast ko?.
Shima su Hasiya zasu had'a, wai bada safennan fodiyon yakoma hannunsuba? Naga taredashi muka kwana.
Shiru tayi batace komai, Dan dama sotake tagudu, tagaji da fitinarsa, jikinta said ciwo yake mata wlhy.
Abu yad'akko a dirowar gefen gadon ya rimtse a hannunsa sannan yamik'a mata hannayen nasa, canki d'aya anan.
Kallonsa Asma'u tayi ta ce, " minene?."
Kedai babu ruwanki dako miye, canki kawai.
Raba idanu Asma'u tafarayi tsakanin hannun haggunsa dana dama, candai ta canki Na dama.
Dariya yayi tareda rungumeta zuwa jikinsa, kinci gari my Queen. 'Yaya maganar yana d'aga mata key d'in mota'.
Da Saudi ta kar6e tana tashi zaune, yaya wannanfa?.
Saida yabata kiss akumatu sannan ya ce, "nakine".
Zumbur tamik'e tana jujjuya key d'in mortar, saikuma tafad'a jikinsa ta rungumesa tana farinciki da godiya agareshi.
Shidai dariya kawai yaketa mata.
Ya Fharuk ni Asma'u nice da mota yau? Wayyo yaya ngd sosai, ALLAH yak'ara bud'i Na alkairi, ya tsareminkai da tsarewarsa, ngd ALLAH ya albarkaci su twins da fodiyo.
Shima rungumeta yayi sosai yana farincikin.
Sundad'e ahaka sannan daga isani tasauka daga adon, yana kiranta amma INA tasheka kaimasu fatee rahoto.
Duk suna zaune agadonta, novel fatee ake karanta musu, saidai kawai sukaji tafad'a tsakkiyarsu tana murna.
Wayyo yaya Asma'u lafiya kuwa? Fatee ta tambaya.
Key d'in mota tashiga d'aga musu tana dariya dafad'in ya Fharuk ya sayamin mota........
Aibata k'arasa fad'aba suka hau ihin murna sums wadda harta taxa fodiyo fake barci.
Ya Umar yana jiyosu, Kansas kawai ya girgiza yana fad'in ALLAH ya shirya..........
________________________
Tab wlhy da ahanya Na ganka bazan yards kai baneba bros.
Dariya Safwan yayi, to aii yanzu agidankine Suhaima.
Wlhy kacanja sosai, danasani Nina turai d'innan nai tafiyata, gashinan tsautsayi yasa Na 6ige da Auden matsiyaci, Wanda baida sisin kwabo said kud'ina dayake ragad'a.
Ban ganeba suhaima mikike nufine?.
Humm Viking bak'in ciki take bashi labarin Wanda ta aura, da k'ayar dayayta shirya mata kafin auren, said a ta aureshi taga babu komai, wlhy dakaga gidamn da'aka fara kaini saika tayani kuma, aiko was he gari dole muka tattaro muka dawo gidannan.
Jinjina kai Safwan yayi ya ce, "ALLAH ya k'yauta to. Nina da dawata shawarar kasuwanci Nazi muku, mom ma harta Nada NATA kud'in saboda ta amince 100%.
Cikin zumud'i Suhaima ta ce, " yimin k'arin bayani akai naji.
Yanda ya tsara mom itama haka ya tsarata, aii babu wani dogon tunani ta ce, "ta amince, Dan da Ramadan yacigaba da cin kud'inta gara tabama Safwan, kuma gashima a in farinciki kasuwanci zasuyi, kud'in zasiyita k'aruwa.
Komai NATA said a ta had'a NASA, takardun kaddarorinta daduk wani abinta Na kud'in, 1million kawai tabarma manta, shima saboda matsalolin yauda kullum dazataimabkanta magani, tunda dai tasan Ramadan babu uwar days ajiye aduniyarnan said masifaffiyar k'arya da fafa.
Safwan yana gama kar6ar komai yamata sallama yatafi akan said sunyi ways kuma.
Yana FIFA ya k'yalk'yace da dariya yana fad'in nasara ta biyu.🤣👌🏼
Daganan said gidan Lubna, it's yatararma bata gidan tafita wajen Niki, yakai away d'ya yana jiranta sannan saigata tadawo.
Itamadai tayi matuk'ar mamakin ganinsa, itama kuma haka ya tsarata Lamar yanda yatsara mom da suhaima.
Itadai ta farko bata aminceba, Dan race saitayi shawara da Hafiz, amma data kanainayeta da dad'in baki, dakuma nuns mata Mayan kud'in suhaima said itama ta aminve, stake an an ta tattaro NASA komai NATA tabashi, it's koma dabatarra suhaima batayiba nabarin wani Abu a hannunta, Dan it a anata ganin Hafiz Na nan.
Nanma komai yahad'a yay gaba, saga nan said gidan Ameer.
Sosai yasamu tarbar mutunci awaken jiddah matar Ameer, sunata hirarsu cikin mutunci Ameer yadawo, rungume juna sukayi shida Safwan saboda farinciki, saida sukayi hira mai tsawo kafin Safwan yasanar dashi abinda yakawoshi k'asar.
Sosai Ameer ya jinjina maganar aransa, baice zai bayarba baikumace bazai badaba. Saida sukadawo saga massalaci sallar la'asar sannan yasamu cikin hikima ya ke6e da matarsa.
Zancen da Safwan yazo dashi yasanar mata, zancen bai wani kwanta acikin zuciyartaba, amma kai tsaye baidace tanuna masa hakaba tunda d'an uwansane.
Ta sauke ajiyar zuciya sannan tace abin farincikine wannan my One, to amma kaga kai kana 'yan kasuwancinka aii, kuma bai kamata karuguzashiba, amma kasamu koda 5million's ne kabashi, lokacin dazai dawo kad'an kuma samin wani Abu saika k'ara NASA ko yakagani?.
Haka yayi wlhy sosai, shiyyasa kullum nake k'ara sonki dear, ALLAH ya barmu tare, yay maganar yana rungumeta.
Ta ce, "nima ina Sonja sosai mijina a in alfaharina.
Cikin sati d'aya Safwan yagama kammala mak'udan kud'ad'en, duk wata kaddara tasu Lubna ya saidata, yahad'a inasa-inasa ya d'age yabar k'asar.🧐
_________________________
Zuwa yanzu ya Umar yafara koyama Asma'u mota, sosai kuma take maida hankali awajen, Dan tafara iyawa babu laifi.
Agefe kuma sunata zabga soyayyarsu.
Ansaka ranar Fatee, yanzuma maganar Rafi'a da Sadam akeyi dansun daidaita Kansu dama. Saikuma Harris ya ce, " shimafa indai Hasiya ta amince ahad'a dasu, Dan yadad'e yana sonta. Yayi shirune saboda bashida abinyi, amma yanzu kam Alhmdllh.
Kowa yayi farinciki da wannan batu, Hasiya kuma ta amince.
Gabad'aya aka had'a saranar itada Rafi'a, sai aka daidaita bikin dana fatee.
Su Asma'u manyan yayye anata shirye-shirye, ya Umar kam tuni ya kammala had'a kayan gadonsu su duka ukun.
Alhmdllh yanzu fodiyo yafara zama abinsa, yaron yayi 6ul-6ul gwanin sha'awa, Asma'u da ya Umar kam soyayya sai abinda yay gaba, yanzu ta iya mota, duk inda takeso zuwa takeyi a abunta.
Ya Abubakar ma shagonshi ya mik'e, Dan ya Umar yabashi jarin dayace. Yaransa kuwa tuni ya kar6osu ya bama mama, takar6a hannu biyu tarik'e Dan yanzu mama tacanja sosai wlhy. Duk abinda 'ya'yanta suka bata takan kar6a da hannu biyu tayi godiya, babu nuna banbanci a tsakaninsu, da Wanda yabata da Wanda bai bataba duk d'ayane awajenta.
Ya Umar yabama Anty Sa'a da Anty Saratu jari suma.
Yahad'a 'yan uwansa yarik'e gam, yazama bishshiya maid'aukeda nauyin kiwa gwargwadon iko.
Yanzu kam koda yaushe yana mall d'insa, shagon k'ofar gida kuwa an samo wani yaro yana kula dashi, ya mallakama Asma'u shi gaba d'aya, kuma Alhmdllh komai yana bunk'asa a shagon.
Abokansa kuwa komai ya sukurkuce musu, suna mamakin dawowar arzeek'in ya Umar, dukda baikoma kamar Daba, amma Alhmdllh, yanzukam sun yard a ya Umar ya keresu tako ina.
Shikam duk sanda yaje mall d'insa zaije wajensu su gaisa, daga gaisuwa babu abinda ke had'asu, idan yatashima zai musu sallama, babu abinda yadameshi dashi.
Dr Jafar yana dana sani da cizon yatsa akan abinda ya aikatama ya Umar, gashi yarasa hanyar dazaibi yarok'i gafararsa, Dan yanzu ya Umar d'in nunawama yakeyi tamkar bai sonsuba.
Ana haka akasha bikinsu Rafi'a da fatee da Hasiya, su ya Umar suntaka rawar gani sosai, sune iyayen amare sune Na angwaye, ansha biki lfy, angina da amare duksun tare agidajemsu.
To ALLAH ya sanya alkairi amen😁.
_________________________
My Husna wai haryanzu jikin NASA?.
Wlhy kuwa ya fharuk, haryanzu akwai zazza6in, gashi fodiyo bayason shan magani, jibifa yanda nake matseahi amma yana zizzilewa, bawani Abu baneba hak'orane kawai.
Ya Umar yad'auki fodiyo daketa kuka saboda maganin da Asma'u tamasa d'ura dashi, rungumesa yayi ajikinsa yana lallashinsa.
Asma'u dake kallonsu ta ce, "ana murmar fara tafiya ciwo yazo ya hana.
Karki damu insha ALLAH zai warke, ALLAH yakawo masa tafiyarmane dawuri, watansafa Tara kenan da haihuwa.
Eh hakane wata tara, tunda yaron mufida watansa 1 kenan da sati biyu, aranar sunan kuwa akecewa watan fodiyo takwas.
Kai yanzu nan har mufida tayi wata 1 da haihu?.
Harma da sati biyu yaya, ALLAH dai yasa mucika da imani, aii duniya na gudu wlhy.
To ALLAH yasa mucika da imani.
Ameen ya rabbi. Kwanannan zakaga cikin su fatee ma wata tafara laulayi.
Dariya ya Umar yayi, to ai abunne babu wuya, wuyartadai a d'aura auren.
Hakane kuma wlhy.
Sunata hirarsu cikin nishad'i.
Can ya Umar ya ce, " af namanta wlhy, amaeyar ya Abubakar mafa babu lafiya, kishirya Dan ALLAH anjima mije mu dubata.
Tofa ko itama cikinne?.
Ina k'yautata zaton haka kam, d'azu nima yake sanar dani damuka had'u a gida.
Ayya ALLAH yak'a lfy, da yamma idan kundawo saimuje.
Humm nikinma tunamin wlhy, su yazeed sunyi zamansu, gashi har 1 saura, kumafa k'arfe biyu za'a fara meeting d'in.....
Sallamar yazeed takatse ya Umar.
Amsawa sukayi.
Sannan Yashigo cikin falon suka gaisa da Asma'u tareda d'n barkwanci da'aka saba.
Saida takawo masa ruwa da zo6o yasa, (Dan bata rabo da zo6o saboda k'aunar da ya Umar me mass).
Babu dad'ewa saiga muktar shima.
Sallama sukayi mata suka tafi.
Bayan tafiyarsu tad'an k'ara gyara gidan, tagoya fodiya tatafi gidan Anty saddiqa dansu d'anyi hira kafin mazajen nasu sudawo...........
7:23pm
Sukayi shirin zuwa asibiti duba matar ya abubakar daya aura kwanakin bata, babu rsuwanta, bakamar sakinaba.
A asibitin sun tararma har an sallamesu, suna shirin tafiya gida, dama mamace awajenta. Bayan and'an gaggaisa da ya jiki suka shirya tsaf.
Sun fito kenan saiga wasu mutane suma sunfito suna kuka d'aukeda gawar d'an uwansu.
Audai su ya Umar suka matsa gefe suna bada hak'uri.
Mamar mamacince k'arshen fitowa, tanata rabzar kuka dafad'in ALLAH ya isa tsakaninmu dake Zainab, kin cucemu, kin kashe mana d'a, zayyan ALLAH ya gafarta maka.
Gaban Asma'u ne yafad'i danjin an ambaci sunan Zayyan.
Kad'an tamatsa kusada gadon da aka turo gawar zayyan za'a saka a mota.
Idanu tazaro sosai waje Dan ganin Zayyan d'inta, cikin rawar murya tace ya Fharuk wlhy Zayyan ne, ALLAH sarki Zayyan, ALLAH ya gafarta maka.
Cak Maman Zayyan tatsaya da kukan datakeyi, hakama sauran 'yan uwan Zayyan duk hankalinsu nakan Asma'u da ya Umar dake lallashinta.
Maman Zayyan tamatso kusadasu, tana fad'in yarinya ina kikasan Zayyan d'ina?.
Cikin kuka Asma'u tamusu bayanin dangan takarta da Zayyan abaya.
Rungumeta Maman Zayyan tayi tana kuka, dabama Asma'u hak'uri, tad'ora dafad'in ai tsinanniyar yarinyar days aura dalilin kwad'ayinsa ita ta manna masa cutar k'anjamau, bai fargaba saida taga yimasa illah, watanmmu biyu kenan a asibitinnan muna jiyya, sai yau ALLAH ya kar6i kayansa.
Zayyan yayi asarar kamilar mace irinki Asma'u, nadad'e ina bak'incikin rashin Aurenki da Zayyan baiyiba dukda ban sankiba. Amma babu yanda zanyi tunda mahaifinsa ya goya masa baya akan auren Zainab, saboda kwad'ayin abin duniya ita 'Yar mai kud'ice.
To dama ance k'uda wajen kwad'ayi yake mutuwa, naga zahiri akan Zayyan kuwa. Ta kuma rushewa da kuka.
Dak'yar su ya Umar suka lalla6eta tashiga mota, Dan tuni ansaka gawar zayyan d'in.
Haka suka tafi sukabar Asma'u na kuka itada mama.
Dak'yar ya Umar ya lallasheta acikin mota.
To ALLAH ya jik'anka Zayyan😭.
*_Lubna_*
Lubna kam abubuwa sun rikice mata, itada Hafiz kullum fad'a harda dabbe, yafita k'arfi, haka zai kamata ya jibga, yazageta tas.
Yanzu batada komai, d'an kud'in daya rage mata sun k'are. Hafiz kuwa bakomai yake iya mataba, Dan yace bazai iya da yanda take cin uban kud'iba.
Wannan dalilin yasa zaman lafiya ya k'aura agidansu, inhar zata nemi Abu yace mata bashidashi to yanzu zasuyi sama kuwa.
Yau danben yakaisu da zagin uwaka ubaka, atake anan Hafiz ya yanka mata Jan kati da saki uku 6aro-6aro ajiki.
Shewa tabuga da fad'in tafi nono fari, itadama tagaji da zama dashi, Dan haka ya tattara inasa-inasa yabar mata gidanta.
Ko'a kwalar rigarsa yakwashe kayansa yabar gidan, dama shimad'in yanzu babu komai, matsalolin lubna sun ida durk'usar dashi. Bashida komai yanzu na azo agani.
Awashe gari lubna tad'aga gidan ta sayar dakomai dake cikinsa. Sutturunta kawai ta d'iba, ta sallami 'yan aikinta. Bilki kawai tabari ta tattara suka koma gidan mom............
*_(((S)))).......2018_*
*_I love you all my fan's_*
[1/6, 5:11 PM] ~🇩 ' 🇯 🇦 🇷 🇭✍: 👩🏻💻.........
💎 *_KARAYAR ARZEEK'I!!_* 💎
*_NA_*
*_Bilyn Abdul_*
*_Sadaukarwa_*
_miss Xoxo na_
_Zarah Bukar_
_Ayusher Muh'd_
*_NIKA'DAI👌🏼 WRITER ASSO.....😜_*
*_page→77-78_*
..........Agidan mom d'imma bawani dad'i baneba, Dan itama komai yak'are, daga ita harsu 'yan biyu duksun fita hayyacinsu, ga ciwon yinwa dake barazanar kamasu.
Tashin hankali goma da ashirin, su 'yan biyu Na ganinta suka fad'a jikinta suna kuka, momy yunwa mukeji sosai.
Rungumesu tayi itama tana kuka tausayi.
Mom tashare hawayenta tana kallon lubna dake rungume da twins, ta ce, "baby kema bak'ya samun number Safwan d'in?."
Humm mom kenan, wlhy ak'alla watana biyu kenan bana samun number sa, anya kuwa Safwan ba cin amanarmu yayiba mom? Ak'alla watan Safwan biyar kenan da tafiya da kud'inmu, amma ko nera d'aya baita6a turo manaba da sunan riba, a lokacinma damuke samun nasa kullum zancensa bai wuce mijirasaba dai.
Gsky mom nafarajin tsoro.
Hummm baby wlhy bake kad'aiba, nikaina a tsoracen nake. Amma lfy naganki da kaya haka?.
Mom Hafiz ya sakeni.
Saki kuma baby? Miyayi zafi haka?.
Mom bar matsiyaci, tunda Safwan yatafi mana da kud'i 'yan kud'in dake hannuna suka k'are Hafiz yafara canjawa, idan Na tambayesa kud'i bazai bani isashsheba, saiyace aibani kad'ai baceba yanada wata matar harda 'ya'ya. nidashi kusan kullum dambe, yoni mom ina ruwana da matarsa ko wasu 'ya'yamsad'in wofi.
Jiya dasafe muntashi ko kayan abinci babu agida sainace yabani kud'i naje nasayo. Shinefa yad'auki 50k yabani, nikuwa uwarmi 50k zatamin, ko a sayen naman gidan bata k'areba. Nace masa sunyi kad'an, shikuma yacemin bashida wasu, haushi yakawoni wuya Na zageshi, shine ya mareni, aikuwa naita danna NASA ashar yabani saki uku.
Ayau Na saida gidan anjima kad'anma zasu turomin kud'ina.
Kuka mom tasaka tana fad'in lalai baby Na k'ara tabbatarwa bakida hankali wlhy, yanzunan saboda kud'in cefane kuka kashe aurenki? To ina motocinki?.
Yo mom run yaushe Na saidasu, d'ya kawai taragemin wadda nake shiga, itama bawani lafiya tacikaba.
Kuka sosai mom takeyi, lubna kam ko'a jikinta, Dan bataga a in kukaba anan. Saga k'arshema 'yayanta tad'iba suka fita. Urban shopping tayo musu mai yawa sannan suka dawo gida.
Turus tayi Dan ganin Suhaima zaune tana rabzar kuka, dukta rame ta lalace, said urban ciki rindimeme.
A sanyaye Lubna tazauna tana fad'in Suhaima kekuma lfy? King a kuwa yanda kuka koma Lamar matar k'auye?.
Kuka Suhaima takuma fashewa dashi tana fad'in badole kiganni hakaba baby, Ramadan ya niyyar kasheni da raina. Kiduba duk alaccin danaima Ramadan arayuwa bai ganiba, dukda nagane bashida komai nayimasa sutura Na zauna dashi. Yau kusan wata biyu kenan yamin wayau da dad'in baki yakar6i 'yan sauran kud'in hannuna way zai fara kasuwance, nikuma daboda yarda danayi dashi Na d'auka Na bashi, Ashe tikitin iskanci da karuwai a hotels yabud'e da kud'in ban saniba. ahankali yabi duk ya said a motocin gidan, Ashe hard a gidan ban saniba. Yau dasafe saiga wad'anda suka sati gidan sunzo wait sun bamu notes nanda gone my kama gabanmu. Ina cikin tararrabi da jiran Ramadan saiga ta karda ya aikomin wai ya sakeni kuma nafara zuwa ganin likita saboda shi an tabbatar NASA yanada HlV😭, Yakima tabbata Nina INA tareda iya, tak'are maganar da rushewa da matsanancin kuka😫.
Data mama har Lubna ma kukan sukeyi, su twin's dai said kallonsu sukeyi da 'yan aikin gidan.
Yau sukam duniya tamusu gwatson k'yanwa🙁. ALLAH yasa mudace ameen.
*_Bayan wash shekaru._*
Abubuwa sun faru dayawan gsk, ciki harda ciwon 6arin jiki data kama mom, sakamakon Nina Safwan da akayi ankamashi da hodar iblis shida wasu abokan kasuwancinsa su takwas. Harma an Yankees musu hucin Lisa ta hangar harbewa, wannan yasa ta yanke jiki ta fad'i awajen, tundaga nan babu wani sashe Na jikinta take mitsi.
Wannanne yasa jinya tazamema Lubna biyu, damage ga Suhaima kwance waken shekara d'aya kenan, tuni ta haihu mace, yarinyarma hartayi wayo, abaya tana shan magani dad'n kukad'ad'en dasuka rage musu, dawanda Ameer take taimaka musu, Dan yanzu shikad'aine mad'an a in hannu acikinsu. Shiyyasa yad'ik'e matarsa GAM, Dan itace sila ta zamowarsa Na gari harya iya rik'ekansa, yanzuma yaransu biyu.
Suhaima tana ganin tasamu lafiya tafara wasa da shan magani, shinefa ciwo ya dirkusar da ita.
'Yan aikinsu kuwa aituni kowa ta gudu ta barsu. Abinci Kansas badan Ameer ba dabasuciba kuwa, duk wata yana k'ok'arin kawo Mayan abinci gidan.
Su 'yan biyu kuwa dasuka zama 'yammata aii saidai add'a kawai, damage dance yaro yana koyine da abinda yagani anayi agidansu, yanzu haka saisu had'a kwana biyu NASA gidan, sunacan yawon gantalinsu.
Kuban tayi kuka harta rasa hawaye. Said yanzu tunanin ya Umar me addabarta,Neman ganinsa takeyi ruwa a jallo amma tarasa hangar hakan........
★★★★★
Su ya Umar kam aii saidai muce Alhmdllh, k'ofofin arzik'i sun kuma bud'ewa tako ina, dagashi har Asma'unsa sun murje sunzama manya ababen Alfahari ga dangi.
Yanzu haka yaransu uku, bayan fodiyo ta haifi mai sunan inna Binta kenan, amma suna kiranta Batul, sai kuma mai sunan ya Umar, wato Umar Fharuk, shima suna kiransa Affan.
Tuni ya canja musu gida mai k'yau da tsari, rayuwarsu sukeyi cikin soyayya da k'aunar juna, ga 'yan 'ya'yansu ababen sha'awa da birgewa, dolene ka gansu su baka sha'awa.
Fatee, Rafi'a, Hasiya duksun haihu, suma anatashan soyayya suda mazajensu.
Hakama 6angarensu inna dash mama, komai Alhmdlh, Anty sa'a da anty Saratu, da mufida sumadai komai normal, kiwa yana cikin kwanciyar hankali.
Abotar yazeed da ya Umar da Muktar kam said abinda yay gaba, sun k'ulle kansu tsam, basa sakeda wata kwafa dazata rusasu, hakama matansu da 'ya'yansu......
★★*★★*★★*★★
Amrah da Afrah na zaune afalon k'asa, duksun baje kayan sweet da samarinsu suka siya musu. Lubna dake zaune agefe tana d'urama mama ruwan tea Dan shine kad'an yake wucewa, shima saida cokali ake d'an zirara mata, lubna dukta lalace tayi bak'i Lamar ba Lubnar nan 'Yar gayuba, tafita hayyacinta sosai, ayanzuma saita had'a kwana hud'u batayi wankaba saboda damuwa da tashin hankali dasukai mata yawa.
Mama ma dake kwance wadda idontane kawai ke aiki, tanata kallonsu Amrah da hira ta kaure a tsakaninsu kowa Na kid'a saurayinta yafi Na 'Yar uwarta.
Da k'yar Suhaima dake kwance gefe ta ce, "Afrah tazo tabata ruwa tasha".
Baki Afrah ta turo gaba tana k'unk'uni, dak'yar tabata ruwan tana yatsina fiska Dan k'yank'yaminta sukeyi yanzu. Hawayene ya ziraro a kumatun Suhaima, tatuna kanta ada, dayanda tayi holewar datafi tasu Amrah. Amma gayanda rayuwarta takoma?.
Lubna ta harari Amrah, itako babu tsoro tarama tana fad'in kijimin momy, minamiki zaki harareni?.
Afrah ta ta6e baki tana danna sweet abaki.
Itadai Lubna batace komaiba.
Saican kamar an tsikari Afrah ta ce, " momy! Yau munga wani abin mamaki wlhy.
Kamar lubna bazata tankaba, saikuma zuwa can ta ce, "nami?."
Humm mall d'in da guys d'inmmu suka kaimu dayagama had'uwa, wlhy momy komai akwai awajen, Raine kawai ba sayarwa, yafa had'u sosai.
Amma kinsan mi muka gani?.
Hoton wani k'yak'yk'yawan mutum shida matarsa da yaransu uku, shine mai wajen, wlhy abin al'ajabi tana masifar kama da Amrah.
K'armin d'ansa kuwa kamar ni nahaifeshi saboda kamar damukeyi. Tab ai kamar ta 6aci.
Amrah ta kar6e zancen dafad'in aii wlhy Afrah har mukazo gida inata tunaninsu. Nidai haka kawai naji ajikina munada dangan taka dash.
Gaban Lubna ne yafad'i.
Da sauri ta ajiye kofin tea d'in datake bama mom, ta ce, ''ya sunansa?."
Ummmm anfa rubuta ajikin pic d'in. Afrah yama? Nikam Na manta.
Da sauri Afrah tace, matardai sunanta Asma'u, shikuma mutumin Umar Fharuk, sai yaranau Usman fodiyo da batul, Affan......
Zumbur Lubna tamik'e tana fad'in kutashi muje Ku nunamin wajen.
Wani kallon sama da k'asa sukai mata, sai kuma suka bushe da dariyar shak'iyanci. Cikin dariyar Amrah ta ce, ''gaba momy ahaka zaki bimu wajen kamar an kwatoki daga bakin kura?.
Inama laifin kid'anyi wanna ki canja kayannan.
ALLAH mom tsamimafa kikeyi, yau kwananki uku bakiyi wankaba, shiyyasa ko kusadake banason zama.
Hawaye suka cikama Lubna ido, wai itace yau 'ya'yanta kekiranta da tana tsami? Lallai rayuwa kenan, ta tababata alhakin Umar kad'ai ya Isa tatsinci kanta fiyema da yanda take ayanzu.
Haka tatafi tayi wanka, sannan tazo suka tafi, suka bar mama da Suhaima agida, Dan harda Habiba d'iyar Suhaima suka tafi.
Hankalin Lubna yatashi sosai daganin hoton ya Umar da Asma'u. Da alama 'ya'yansune taredasu ahoton.
Jiki a sanyaye suka k'arasa indasu Harris da sadam ke zaune.
Bayan Lubna ta gaishesu Dan Amrah da Afrah babu wannan atsarin tarbiyyarsu, NASA Haida kowa, ko gidan Ameer sukaje haka sukeyi. Lubna tafara tambayarsu ko Alhji Umar nan?.
Sudai su Harris kallonsu kawai sukeyi, Dan kokad'n bai gane Lubna ba, shidama Sadam bai santaba, amma idonsa nakan su Amrah daketa taunar cingam k'as-k'as, kamarda Amrsah takeyice da ya Umar tabashi mamaki, hakama Afrah da Affan.
Harris ne yay k'arfin halin fad'in baya nan yaje gida yanzunnan kai yara.
Da sauri Lubna ta ce, "kozaku bamu kwataccen gidan Dan girman ALLAH?.
shiru sukayi suduka, Dan sukam bama su yards dasuba, kowadai yasan yanda rayuwar ta lalace yanzu.
Lubna ta rissina kamar zata duk'a tana k'ara rok'on Harris, Dan itama bata ganeshiba.
Sadam ya ce, ''baiwar ALLAH kekam miyasa kike son ganin ya Umar.
Dak'yar ta iya had'iye yawu ta ce, " ni tsohuwar matarsace, wad'annan kuma 'ya'yansane. Ta nunasu Afrah.
Idanu Amrah da Afrah suka zari, suna fad'in 'ya'yqnsa!!?.
Can kuma Harris tayi wani uban zallo shima yana k'qrema lubna da twins kallon mamaki.
Tabbas alamu dayawa sun nuna gskyar Lubna, musammanma kamainnin Amrah da ya Umar.
Cikin masifa yakirasu waje, ana cikin haka saiga yazeed, yatanbayi abinda ke faruwa Harris yafad'a masa.
Hannu Yazeed yad'aga masa ya ce, "a'a daina korarsu.
Kushiga Mora na kaiku.
Badan Harris yasoba yazeed yad'auki su Lubna amotarsa sai gidan ya Umar.
Afrah dake gaban mota tuni har zuciyarta ta k'yasa yazeed😨🤣.
-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-
Asma'u dake zaune Afalo taci wwalliyarta, gefenta masu aikintane suna zaune sai hira Duke zuba mata tana dariyar. It's babu ruwanta da German kan nan irinna hajiyoyi.
Da gudu fodiyo da Batul suka shigo falon suna kiran Ammi! Ammi!! Mundawo mundawo.
Itama cikin azama tamik'e ta taresu Rana farincikin dawowar 'ya'yanta ababen alfaharint.
Suna cikin murnar saiga ya Umar yashigo d'aukeda Affan ahannu, shima sanye cikin Mayan makaranta.
Shida Affan d'in tahad'a ta rungume tsam ajikinta, shima ya Umar k'yak'yk'yawar tarba yamata tareda manna mata Sumba agoshi.
Affan ya ce, ammi yau antynmu tace Nafi kiwa kokali a class d'inmmu.
Masha ALLAH autana, haka nakeaonji.
Ya Umar ya ce, ''autan lfy hajiyata, idanmma zaki dage ki Dage, autana bai zoba har yanzu, shine zaizama k'anin Affan na tara.
Sosai Asma'u tazaro ido, gaba ya Fharuk rufamin asiri mana, ukunnan ma aii ansha fama kafin suzo.
'Yar dariyar ya Umar tayi, ya ce, "ahaka kuma nake jiran tara nan gaba.
Habadai wasa kakeyi wlhy.
Said a suka zauna sannan yace babu wani wasa da gsk nakeayi.
Shiru tamasa taje takawo masa abinsha, sannan tafara cirema Affan Mayan makarantar.
Suma su fodiyo duksun cire, kowa yama k'ok'arin nuns mata homework d'in da aka basu, sukaji sallamar yazeed.
Yaran kowa ya yard a abinda ke hannunsa suka kwasa da gudu suna fad'in oyoyo dady.
rungumesu yazeed tayi, shima yama fad'in oyoyo yarana.
Ya Umar da Asma'u dai kallonsu kawai sukeyi suna dariya.
Lubna dasu Amrah kam suna baya said kalle-kalle sukeyi agidan.
Saima yanzu su Asma'u suka gansu.
Ko kad'an Asma'u bata gane lubna ba bare su Amrah.
Amma kuma kamar dasukeyi dashi yasakata taura musu idanu.
Shikam ya Umar suna shigowa yaganesu suduka, Dan d'azu yaga Afrah da Amrah a mall d'insa tareda wasu samari biyu. Kuma yaji ajikinsa 'ya'yansane. Har hawaye saida tayi alokacin, yana k'ara yima Lubna ALLAH ya Isa, Dan asanadinsa yaransa suka lalace, shidai bai ta6a Yar kowaba tunyana saurayi bare yanzu.
Amma gawasu suna lalata 'ya'yansa ta dalilin halin ma haifiyarsu.
Yazeed ne yacema su Lubna su zauna.
Duk suka zazzauna.
Asma'u takawo musu abubuwan motsa Baku.
Ran ya Umar a6ace yatashi zaibar falon. Da sauri yazeed yarik'e hannunsa yana fad'in karfa ka manta, a tsakaninmu babu jayayya.
Idon ya Umar yayi jajur saboda 6acin rai, yajuyo yana kallon yazeed, kayi hak'uri d'an uwana, wannan jayayyar tasha banban da wadda bakaso.
No Umar duk d'ayace, Dan ALLAH kayi hak'uri kazauna plss.
Saida ya Umar yay kwafa sannan ya zauna. Amrah da Afrah kam aii tuni sun nutsu, Dan basuga wajen wargiba.
Sudai su fodiyo suna tsaye agefe suna kallon iyayensu.
Lubna ta Haida ya Umar, bai amsa mataba. Bata damuba itama, ta kalli Afrah da Amrah tace augaidashi.
Amamakinta saigashi sun gaidaahi, harma da Asma'u.
Sumad'in bai amsa musuba, saima cikin tsawa ya ce, "Lubna! Miyakawoki gareni? Dawane shiri kuma kikazo yau?.
Tsawar babu Wanda bata razana a falonba, Affan ya k'ank'ame Asma'u yana kuka, Dan basu ta6a ganin baban nasuba a irin wannan yanayinba.
d'aukarsa tayi tana lallashi, fodiyo da Batul ma duksun mak'ale jikin yazeed.
K'asa Lubna tadiro tana kuka da neman gafarar ya Umar.
Ka gafarceni nida iyayena da 'yan uwana Umar, wlhy duniya takoyar damu hankali, munyi nadamar abinda mukaimaka. Umar yanzu bamuda abin jayayya Sakai, dukiyar damuke tak'amar da ita tak'are. Ciwo da bak'in cikin rayuwa sune suka maye gurbin arzeek'inmu.
Umar kayi hak'uri, ga 'ya'yankanan zan maido maka, Dan ALLAH karkace bazaka kar6esuba, Umar wlhy nasan nikaina ina gab da kamuwa da wani ciwonne, rayuwar dasu Amrah da Afrah suka saka kanau kawai ta Isa lafiyata baraza......
Da sauri ya Umar yad'aga mata hannu a hasale, yana fad'in suka saka kamsu, kokuwa kika sakasu ciki. ALLAH shine zaidata van ta6a zina da 'Yar kowaba amma ta sanadinki ga 'ya'yana sunayi. Lubna kin cuceni, kin zalinceni, yama za'ayi Na yafe miki?, kin rabani da 'ya'yana Ashe badan ki kula dasuba? Saidai ki watsa musu rayuwarsu? Wata 'yan kwallah ta taru masa a gefen ido......
Yazeed da Asma'u ne suka saka baki wajen taya Lubna Neman gafara.
Dak'yar ya hak'ura, Afrah da Amrah aukazo suka rungumeshi suna kuka suma. Yauce rana tafarko dasuka gane kuskuren dasukaso tafkawa rayuwarsu, ALLAH ya taimakesu ya tsaresu basuta6a bama wani saurayi kansuba, saidai soyayyar shan minti da romances da samarin sukanyi dasu.
Shima ya Umar rungumesu yayi, yau ga 'ya'yana sundawo gareshi, bayan kwacesu da akayi daga hannunsa Na tsawon shekaru.
Daga nan wajen Asma'u sukazo itama suka rungumeta, basu manta da itaba, suka rungume 'yan kannensu dabasu sansuba.
Lubna sai dad'i takeji, ga hawauenta sunk'i tsayawa, ta rungume su fodiyo itama tanajin dayanzu k'ila itace ta haifesu, amma San zuciya da rud'anin duniya yahana tsaida zuciyarta waje d'aya. Aigatanan a makarantar nadama.......
Anan tabarsu Twins kamar yanda Asma'u ta buk'at.
Aiko hakan yamusu dad'i, saijan 'yan k'annensu sukeyi ajiki, suma dayake sunada saurin sabo harsun saki jiki dasu.
Washe gari, ya Umar yaje har gidansu Lubna d'in yad'auki mom da Suhaima yakaisu asibiti.
Mom sai kuka takeyi, babu bakin magana, hakama Suhaima tanata kuka da Neman gafarar ya Umar, tasanar dashi sune itada mom sukaita zuga Lubna, akan tarabu dashi, run bata aminceba harta amince.
Ya Umar saidai kawai yayi murmushi ya ce, ''ya yafe musu.
*+++++++++++++*.
Cikin wata biyu jikinsu mom da Suhaima yayi k'yau, Dan yanzu mom nad'an iyayin magana kad'an ², dukda dai bata fita sosai, hakama Suhaima alhmdlh, jikin nata yayi, k'yau.
Mom sai sakama Ya Umar albarka takeyi da k'ara Neman gafararsa.
Koda yaushe yakance ya yafe musu.
Asma'u kam bata ta6a gazawa wajen kawo musu abinciba kullum safe da yamma.
Duk sanda Lubna ta gansu dasu da 'yan 'ya'yansu saitayi kuka, da nadama, mai makon Umar yayi baya, kullum saima gaba yake k'arawa. Tagujeshi saboda *,"karayar arzeek'i"_* yau gashi shine yake taimakonsu da dukiyarsa.
Tayi kuka harta godema ALLAH, tayi nadama rayuwarta, shiyyasa akace idanu gemun d'an uwana Yakama da wuta to yayyafama naka ruwan. Idanu kuma ALLAH ya jarabci bawansa badan bata sonshi baneba.
Itakam taga zahiri akan Umar.
Itada 'yan uwanta kam duk ga yanda tasu rayuwarsu tak'are, sun rasa alokacin Dana Umar yadawo.
ALLAH ka shirya zukatanmu, ka ganar damu gsky.
Ni bilynku nace ameen😭.
Alhamdulilahi.
Anan nakawo k'arshen wannan d'an littafi NASA mai suna *_KARAYAR ARZEEK'I_* abinda nafad'a saidai, ALLAH kabani lada, Wanda nati kuskure ALLAH ka yafe mini.
Ina godiya ga d'umbin masoyana, musamman masu bibiyar buk d'innan Na *_karayar arzeek'i_* ngd sosai, ALLAH yabar zuminci, Nina INA k'aunarku da alfahari daku aduk India kuke.
*_Writer's 'yan uwana kuma inata mik'o godiya agareku, ALLAH yabarmu tare, yak'ara dank'on zuminci, ALLAH yak'arama kowa baseeer da hak'urin typing._*
Bilkisa Ibrahim
Bilyn Abdul.
Marubuciyar.
_rashin Sani_
_auren k'addara ko biyayya?._
_k'anwar uwace ko kishiyar uwa?_
_nida aminiyata_
_kukan kurciya_
_sabon al'amari_
_nawaff_
_ban saketa ba_
_Abdul-maleek bobo_
_karayar arzeek'i_
*_Sharhin littatafaina 10 nanan zuwa agareku insha ALLAHU_*
_NGD SOSAI, ALLAH YABAR ZUMINCI._
*_BILYN ABDUL CE._*👌🏼😁
*_(((S))))........2018_*
*_I love you more...._*