*Asalin labarin...*
*Alh Sulaiman Goni* mahaifin *zahra* yakasan ce haifaffen garin Maiduguri ne, yayin da rawuwarshi take kano gurin uncle dinsa..acan yay primary yay secondary har jamiar sa acan yayi. Yafara aiki a karkashin company nin uncle dinsa, yayinda shine manager a company nin saboda hazakarsa sa kwazonsa...wata rana yazirci i'ya yensa a borno Allah yasa yay gamda katar da *Fatima Zahra* yarinya mai hankali da natsuwa..tunda yakalketa soyayyarta ta kamashi lokaci guda yaji baya iya rayuwa inbada i'taba. Baiyi kasa a gwiwa ba yasanar da i'yayenshi, ba bata lokaci mahaifin Sulaiman yaje dakanshi gurin abban Fatima da maganar. Dama aka bashi dayaje in Allah yasa suka fahimci junansu falillahil handih..
Cikin kankanin lokaci kuwa tsarka kekkiyar soyayya mai tsafta ta shiga tsakanin Sulaiman da Fatima. Bab'ata lokaci kuwa magana ta i'sa gurin manya acikin wata shida aka gama komai aka yanke biki wata daya. Biki budiri rabar bikin Fatima da Sulaiman anyi shagali an zubda naira domin kuwa akawta ta dangin amarya da dangin ango kowa yanajin shima wani ne sosea akayi barin kud'i. Bayan la'asar dangin amarya suka shirya akatafi da i'ta gidanta dake garin *KANO* bayan nasihu datasha gun 'iyayenta da 'yan uwa. Kwanan su biyu suka dawo akabar amarya daga i'ta sai angonta. Aurensu nada wata shida yatafi karin karatu, ,,,,cikin shekara uku dukiyar ta harzuga yakoma business tsakanin kasashen waje zuwa nig. Bayan aurensu da shekaru biyar..shiru2 bazancen haihuwa,, sunje asibiti andubasu domin suna tunanin ko akwai wani matsalane amma babu..tun suna damuwa har suka share da lamarin ..haka sukaci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali.
*Alh Omar Matawalle* shine mahaifin *Yazid* tare da matarshi *Haj Aisha* dukansu 'yan garin kano ne. Alh umar yakasanci masha hurin mai kudi haka babban dan siyasane..sunyi aure da Aisha tun kammala secondary school dinta suna zamansu na lpy. Shekaransu d'aya da aure Allah yaba ta haihuwa ta haifi d'a namiji mai kama da ubansa sak! Karkuso kuga murna a family nnan ranar suna yaro yaci suna *Yazid* sunan mahaifin Aisha ...anyi shagali naira tayi kuka ranar sunan.
Abotar Alh Sulaiman Goni da Alh Omar Matawalle tafarane ranar wata litinin agurin wani occasion na 'yan siyasa yayinda aka gayyaci manya manyan ma'aikatan gwannata..tundaga nan aminci yashiga tsakanin su, yayinda yazama hatta matansu sunzama aminan juna kamar *Dangin juna* haka suka zama.
*Alh Usaman Dala* wato daddy n zuby yakasamce bakano, mutum mai tsanani akan boko! Yana bata muhinmmacin sosea a rayuwarshi..shi prof. Ne, kuma babban doc. ne..sananne ne sannan kuma attajiri ne.
*Suwaiba* wato *Momy* tareda kawarta aminyar ta Wato *Hajara (mama)*. sun kasance 'yan *barya*, karamar hukamar a jahar kano.
.sanannu ne sosea garin bawanda bai sansu ba gurin rashin kamun kai, da biye biyen maza..bankad'anci...da shige2.
Suwaiba ta kasance i'ta kadaice gurin 'iyayenta , talakawa ne sosea gasu da son abun duniya.. Mahaifiyar suwaiba ta kwarance gurin bin malamai da bokaye..gashi bawai abin Duniya garesuba amma tana zuwa gun malamai kawai don mallake mijinta.
In kasan Suwaiba to kasan hajara don hanta da jini suke tif da taya. Ranar wata talata, ranar alh usman dala ya ziyarci wani kauye dake kusa da *barya* motarshi ta b'aci a hanyar dadowa, kamar daga sama suka hamgo wani hadadden matashi, Suwaiba da hajara ne ke tahowa.. Jiki na rawa cikin rige2 sukayo gunsa. Gaisheshi sukayi ya amsa ba yabo ba fallasa donshi baison harka yan qauye. Ruwa yace sukawo mishi suwaiba cikin azama takoma cikin gari ta daibo masa ruyawa..kudi mai uban yawa yabasu yaja motarsa yatafi.. Tun daganan Suwaiba da mahaifiyarta suka samai kohon zuk'a, da bokaye da malamai saida suka jawo usman ya haukace akan son Suwaiba. Cikin karamin lokaci akayi auren aka kaita kano dangin usman bason auren sukeba amma bayadda suka i'ya gannin dan uwan nasu zai iya rabuwa dasu akan maganar. Hajara kam kamar ta mutu don bakin ciki tanaji tana gani haka aka aurar da suwai a birni..domin 'iyayenta bamasu son abun duniya bane, mutanene masu saukin rayuwa masu godema duk abinda Allah yabasu.. A haka wani daga cikin samarin kauyen lauwali yaro mai hankali da sanyi yafito yace yana son hajara murna agun iyayenta baa maga domin burinsu baiwuce itama tatafi dakin mijin taba. Hajara kamar takashe lauwali domin bata sonsa, mahaifin lawwali abokin mahaifin ta ne don haka cikin kankanin lokaci akayi bikin. Ranar da a'akai hajara dan madaidaicin gidanta..(domin lawwali yanada sana'arsa) hanashi shiga dakinta tai tarufe kofa sai
a soro yakwana ... Auren hajara nada wata hudu tasamu ciki , karkaga bala'i gun hajara "ita bazata haihu da talaka matsiyaciba" ..garaba dai kala2 bawanda bataiba tasha yunkurin zubda cikin amma Allah baiyiba saida ta haifeshi. Ranar suna yaro yaci sunan "Muhammed sani* anace dashi *Arman wanda Haj. Suwaiba ta nada nasa don (kasan abinka da 'yan birni wayayyu) .
Haj. Suwaiba shiru2 har shekara biyar ba ciki ba labarinsa, yayinda ta danne zuciyar mijin da asiri don haka ko damuwa bayayi saidai danginsa suma hasukayi suka hakura. Ashekara na shidane Allah yabata ciki karkuga tarairaya da kulawa agun Alh usman dayake bata. Ranar da Hajiya suwaiba tahaihu Alh.usman kamar zai cinyeta don kauna da i'ta da abinda ta haifa, ranar suna jaririya taci suna *Zubaida* anyi shagali kuma anyi barin kudi ranar. *Zubaida* nada shekara hudu aka sata nursery yayinda *fauxiyya* (yarinyar da hajara ta haifa bayan haihuwar arman da shekaru hudu) keda shekaru shidda a duniya shikuma arman nada shekaru goma.
Lawwali yana cikin tashin hankali da masifa domin kuwa masifar yau daban tagobe daban da hajara ke masa, ahaka harya kamuda hawan jini da ciwon zuciya kullum yana kwance gida ba lpy gaya bawata kyakkyawar kulawa .. Ana cikin hakane Allah yamai rasuwa saida muce Allah yaji kanshi. Hajara kam abun bai dametaba ko a jikinta don daman kamar kaya yazame mata,, yanzu kwa tayada kwallon mangoro tahuta da kud'a. Bayan tagama takabane tashirya ziyara ta musamman zata kaima kawarta, aminiyar ta *Haj Suwaiba* a kano. Bakaramin mamaki taiba ganin irin daular da kawarta ke ciki. "Uuhm!...rayuwa kenan! Yanzu suwaiba kece cikin wannan daular!?." Farr suwaiba tayi "hmm kedai bari ..duniya kam nasameta." "To sumu kuma haka zamu kare da zani daya kenan." "Aa, kikwantar da hankalin ki, tunda yanzu bakida aure kwai abinyu." Zabura hajara tayi tamatso daf ta i'ta "ayya menene fada min." "Akwai wani abokin Alh., sunanshi *Alh Sulaiman Goni*, yanada mata daya kuma bai taba haihuwaba. Zakije gidan a matayin naiman taimako su taimaka subaki aiki koda share2 ne, idan anyi sa'a sunbaki daganan kuma saimusan abinyi." Wani tsallen farinciki hajara tayi tarungume kawarta hards dan hawayenta "ngde kawata, ngde ngde..Allah yabarman ke."
*👄hαвíєвαh luv👄*
[3/26, 1:04 PM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝.....57/58*
_Writing by_
*👄Habieba Luv👄*
_Editing by_
*💅Sadnaf💅*
💝💝💝💝💝💝💝💝💝
A gidan haj suwaiba hajara ta kwana, sakamakon mijin bainan yaje Australia wani aiki.
Washe gari sassafe suwaiba ta tadata tamata kwatancen gidan alh Sulaiman Goni.. 'Ya'yanta kwa ta d'iba kagansu kamar almajire suka tafi.
Dai2 anwangale get din gidan hajara ta karoso tazo shiga . dakatar da i'ta mai gadin yayi yahana shiga, taburewa hajara tace saita shiga. Hayaniyarsu ne yajawo hankalin alh yace mai gadin ya barta . tana isa gaban alh tafashe da kuka tashiga baahi labarin karya da gaskiya. "Alh don Allah katai makamin koda aikin share share ne kabani." Sosea tausayinta yakamashi coz shi mutumne mai tausai. Iso yamata harcikin falon Haj Fatima yanuna maguri tazauna yaran suka zauna gefen ta. Ciki yashiga yakira Haj Fatima suka fito tare. Tunda Haj Fatima suka hada i'do da hajara gabanta yay wani mummunan bugawa, hakanan taji bata mataba.
Har kasa hajara tasauka ta gaida Haj Fatima ta amsa adan sake..kamar yadda hajara tafadama alh haka shima tashaidawa Haj Fatima,, ita taji tausayinta sosea ko dan marayun yaran dake gurinta. "To Hajiya shine nayanke shawarar zaabata aiki girki, inyasa sai abata wancan dakin." Yay nuni dawani daki dake gefen store. "Ba laifi hakan yayi..Allah yasa alkhairi zamanmu." "Amin."
Hajara harda dan kukanta tana godiya. Fita alh yayi yatafi office.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya suwaiba sa hajara kullum suna kam magani don suga sunjawo hankalin alh Sulaiman.
Wata rana Hajiya Fatima tafita unguwa, alh yadawo da rana cin abinci..kwalliya sosea hajara tayi tabuga dauri tashafa turaren da boka yabata tahada abinci takaima alh. Yana zauna a garden kan wani lallausan rug yayi matashin kai da wani haddaden tropillow .. Tundaga nesa yake kallonta ko kiftawa babu, lokaci daya wani tunani yazo ransa. Dasallama tashiga gurin ta ijeye tryn tayi saving nashi tatashi tafi.
Tun daga ranar alh yafata jin yana son aurenta, suma kuwa basu tsayaba cigaba suke da aikinsu.
Bayan wata daya, alhaji Sulaiman da kansa yasamu hajara yafada mata abinda ke ranshi, shawara tace zatayi yabata lokaci. Aminiyarta takaima maganar sukayi shawarwarinsu takoma.. Wasa2 hajara da alh soyayya suke a boye cikin gida, maganar aure ya kankama yabata sadakinta ranar jumaa aka daura aure. Sai ranar auren Haj Fatima taji labarin. Tayi kuka harta godema Allah .
Washe gari da safe har karfe takwas Haj Fatima taji shiru ba alaman breakfast, dakanta taje dakin hajara amma bata isketaba sai yaranta dasuke bacci.. Fita tayi taje ta daura break. Karfe goma dai2 saiga alh da amarya sun jero suna nufo dining, tsananin mamaki yakama Haj Fatima.. "Wannan wani irin cin amana ne."
Alh gabatar da hajara yayi wa Haj Fatima.. Bata i'ya cewa komai ba haka bataci wani abun kirkiba tatashi takoma bedroom nata.
Tundaga lokacin komai nagidan ya canza hajara itace tagaban gashi komai i'ta, watanta biyu tasamu ciki karkaga farinciki agun Alh ..lokaci daya Haj Fatima tazama bora..komai sai Hajiya hajara don wata daya da aure suka tafi maka itada mijinta.
Su arman kwa sunzama yan gida shida fauxy sai abinda sukaga dama suke.
Ranar da hajara ta haihu karkuga murna gurin alh Sulaiman kamar zai cinye jaririyar, ranar suna yarinya taci suna *Farida* su hajara ankara kame gida sai yadda sukayi dashi.
*Zubaida*, yarinyar Haj suwaiba, takasance mai harka da kawaye masu rawar kai, gasude yara don awannan lokacin suna js1 amma basuda labari sai na aure.. Tun daga nan aure tashiga ran zubaida batada wani buri daya wuce tana kammala secondary tayi aure.
Farida nada shara biyar lokaci daya Allah yabama Haj Fatima ciki..zokafa bakin ciki gun hajara, ba yadda batayi da bokaye da malamai akan cikin yazube amma Allah baiyiba.
Ranar wata jumaa Haj Fatima tafara nakuda, alh Sulaiman yana kaita asibiti ta haihu ta haifi yarinyarta mace kyakkyawa mai kama da laraba. Lokaci daya alh Sulaiman yaji kaunar yarinyar yashigesa, yaji duk duniya ba abinda yakeso sama da i'ta.
Ranar suna jaririya taci suna *FATIMA ZAHRA* anyi shagali naira tayi kuka. Tun lokacin da hajara ta fahinci akwai so mai tsanani tsakanin alh Sulaiman da zahra ta kudiri niyyar rabasu.
Zarah yarinyar tataso da wani kalar da bi'ar bayyan tsaraicinta, batada kunya kwata2 batajin kunya fidda tsaraicin ..shiga irinta yahudawa shine dabiarta ..akwaita da tsiwa bata barin ta kwana ..ba yadda mahaifiyar ta batayi akan ganin ta sanza halayyarta amma abun ya faska , tun abun baya damunta harya fara damunta coz yarinyar girma takeyi abin nakara shiga ranta.
Lokacin da zarah tagama primary tashiga secondary tayi wani Abu waishi ruruwan samari..samari kala2 zaka gani tareda zahra, tun daga nan akefara zargidan da bin maza . abin yana matukar kona ran mahaifiyarta, yanzu abbanta baiwani damu da i'taba don hajara ta gama samishi tsanarta .
Hantarar da alh Sulaiman yakema Haj Fatima yasa takamu da hawan jini, yauda lpy gobe ba lpy.
Wata rana zarah tadawo daga unguwa wani saurayi yasauke a mota carab akan idon mama..wanda haka duk yan gidan suke kiranta.
Falon alh tatafi tasanar dashi cewa taga zahra da wani saurayi suna iskanci a mota.
Afusace yafito yazo yasamesu zaune falo ruwan masifa yafara saikema Haj Fatima da zahra hakan ya taddasa ciwonta yatashi tafadi, a gigice zahra tayo kanta tana jijjigata tana kuka.
Kwananta biyu a asibiti Allah yay mata cikawa, bakaramin kuka zahra tashaba don mamarta kadai ke sonta gidan. Bayadda yan uwan Haj Fatima basuyiba akan abasu zahra amma abbanta yaki haka suka hakura suka barta.
Arman tatashi cikin gata a gun alh Sulaiman, don kamar dancikinsa haka yake kallon sa. Arman yatashi da budadden idon akwaisa da son mata suma kuma suna biyemasa coz yaron akwai kudi.
Lokacin da zubaida takare secondary school tasamu momynta da maganar aure takeso ita bazata tafi jamia ba sai intayi aure. Koda Momy tasamu daddy zubaida da maganar fir yaki wai dole satagama jamia. Itama taburewa tayi tace sai aure, dagyar da dabara sukaja hankalinta ta hakura tace zatayi..amma ita kadai tasan abinda take shiryawa!.
Rayuwat zahra tana cikin kunci bata samun farin ciki, abbanta baya nuna damuwa da i'ta, ga hantarar da ake mata gun yan gidansu, ga maganar duniya da kallon da ake mata Wanda azahirance ba haka yakeba.
Agun mutum daya take samun farinciki gurin *Haj Aisha* wato mami..i'ta kadai tarike amana ba yadda batayi da abban zahra akan yabata itaba bayan rasuwar maman ta amma taki.
*Yazid* yazama matashin saurayi mai jini a jika, wayayye dan boko.. Maiji da kansa..ga kyau..yagama karatunshi a London yadawo nig. Yayinda yacigaba da kulada kafanonin mahaifinshi..(wanda Allah yay masa rasuwa tunshekaru biyar dasuka wuce)
Yazid ba abinda yatsana kamar zahra don ko gidansu taje ranar yini zaiyi a daki kokuma yabar gidan..haka i'tama ba kaunar kallonsa takeba.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya yayinda zubaida tasa rawuwarta cikin kazanta coz batada wani eaki daya wuce bin maza....
Wannan kenan
*Cigaban labari...*
*👄Habiebah Luv👄*
[3/27, 8:07 PM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝....59/60*
_wrítíng вч_
*👄hαвíєвαh luv👄*
_єdítíng вч_
*💅ѕαdnαf💅*
💝💝💝💝💝💝💝💝💝
*Cigaban labarin.......*
*Y* usuf suna fita baizarce da zahra ko i'naba sai
*HB SPECIALIS HOSPITAL*, dama already yama frnd dinshi Dr Idriss magana..
Ba b'ata lokaci wata babbar likita *Aunty yagana* ta duba zahra sosea ta tausaya mata don sai anyi mata dinki, cikin 1h aka gama mata dressing tasamu bacci. magunguna aka rubuta Yusuf dakanshi yafita pharmacy yasawo.
"Yanzu Dr bazai yiyu muyi tafiyanba kenan? Dole saita kwana?." "Gaskiya saita kwana, coz kasan dinki karamin mistake mutum yayi yakan i'ya warewa..so saita kwana muga yanda abin zaiyi zuwa gaben." Iska mai zafi Yusuf ya furzar,,"OK..alright.. Badanuwa..Allah yakaimu."
Abangaren yazid ko ranar bai i'ya tsinana komai ba, hatta masjid bai'ia zuwaba sai agida yarinka salla yana addua yana kuka shabe2 harda majina, i'donsa duk sun kumbura haka fuskarsa daka ganshi kasan yana cikin mawuyacin hali, gashi soyake yaji gidan mami ko zaid'anji sanyi a ransa amma baisan dawani i'do zai kalleta ba.
Yana zaune kan praying mat ya gabatar da sallar isha kenan yajiyo buge 2 a dakin da zuby ke ciki, saida yay adduoinsa da tasbihai kafin yatashi cikin bacin rea yabude yashiga. Dakin bakinkirin kamar ba'a hallici haske ciki ba, torchlight din wayarsa ya kunna ya dalle mata ido.
Zuby gaba daya tafita hayyacinta..fuskanta dukkya kunbura yay jaa ga fuskan shike da dry tears bakinta a rufe da bandage sai sure2 takeyi. Yazid yana karasawa gurin ya danko gashin kanta yad'ago fuskanta hadi da saukemata wani lafiyayyen mari..saida tashid'e takusa suma. fizge bandage din bakinta yayi yadaka mata tsawa "dan boruobanki menene?." Jiki na bari muryanta na rawa tace "wllh yunwa... nakeji." "Don uwarki ubanki yakawo abinci ne?." Girgiza kai tayi tana hawaye " ni sa'an ubanki ko sa'an uwarki dazakimin nodding, oya open ur mouth n telk...dan kan uwarki."
"Don Allah.. Kayi hakuri,,...wllh baikawoba..amma kataimaka min plss..ko kamaidani gidanm.." Wani Marin yakara sauke mata "ke a jakantarki kina tunanin zakici bulus ne?, kinzo kin lalata min rayuwa ,kin rabani da kowa nawa kinrabani da farin ciki na *matata* tareda mahaifiyata ..kin kawomin sauran wasu katin banza... " shiru yayi yahad'e kansa da bango yanajin zuciyarshi kamar zata kone don zafin datake masa.
Yafi minta ashirin a haka kafin yafita daga dakin yarufo kofar. Wani kuka maicin rai zuby tafashe dashi tana regretting rayuwanta na baya..
Yazid yana fita yashiga mota yatafi wani can unguwar talakawa. wani almajiri yagani yafito daga wani gida hanunshi rike da roba... Parking yayi gefe yafito yanufi gun yaro. "Almajiri.." Alama yay mishi da hanu yazo, bamusu yaron yazo gurin yazid. "Mene cikin robarnan?." "Abinci ne ciki.." Yafada yana bude robar.. baya yazid yay yana toshe hanci "meye wanna?" Yafada yana pointing robar.. "Tuwone..miyan kuka." "Plss..rufeshi." Rufewa yayi yatsaya yana kollon yazid.. "Kaga , kabani wannan tuwon inbaka dubu daya kasai abinci.." Tunkafin yazid yagama fada yaron yace "eh..wllh nayarda." Yafada yana mika mishi robar. Kin amsa yazid yayi sai yaron yanaimo leda awani provision shop yasa aciki kana yakarba yabashi kudin yatafi. Restaurant yawuce yay takeaway kafin yatafi gida. Afalon ya ijiye dayan ledan dayan kuma yashiga dakin da zuby take ciki. A inda yabarta haka ya sameta, kujera ya jawo yazauna gabanta yaciro abincin ledan ya ijiye gabanta tare budewa .. .wani uban warin daddawane tabugi hanci zuby tai saurin kauda kanta gefe.
"Kee maye kakayi hakan?." "Plss don Allah bana i'yacin wannan , indai a nine wllh nakoshi." "Toda kina tunanin a ubanki nakawowa?." Nandai shiru tayi batace komai ba ..
"Oya bude baki.." Kin budewa tayi ganin zai zabga mata mari yasa tabude ya turamata loma baki. Da kyar ta'iya hadiyewa tana hawaye.."wllh inbaki hadiye wannan kukanba sainashi uwarki." Yay maganar ba'alamar wasa ..dif tahad'iye kukan tanaci kamar tayi amai. Yazid kwa cikin mugunta yake kara dannamata loma, saida yaga tana kokarin amai sannan ya kyaleta.
"Zanyi salla.." Tafada cikin sanyi murya. Mugun kallo ya watsa mata "munafika kawai..zan kunceki kiyi salla, amma kina idawa zan maidaki daure.." "To"
Kunceta yayi yafita tareda sama kofar key.
Abangaren Hajiya Momy kuwa tana komawa gida tawuce bedroom nata tasaki wani dan marayan kuka.."nashiga ukuna halina yabi 'yata ,yaa Allah kayafemana Allah natuba...kuka tarinkayi tana surutai masu maana da maras, ranar ko ruwa batasa bakintaba lokaci kankani harta fad'a tafita hayya cinta. Damuwanta daya Daddy n zuby batasan how can explain to him ba, meyema zata ce masa 'yarsa *KARUWA CE!* innalillahiwainnailaihirrajiun.
Haka shima yazid ko abincin daya siya restaurant bai'ya ciba, kwana yayi yana sallah yana rokon Allah daya sanyaya zuciyar matarshi da mami don su tausaya mai.
****
Washe gari...
Karfe shida Yusuf yad'auki hanyar Maiduguri bayan sallama da akabasu don yanzu dasauki don ko zafinma kadan takeji. A natse Yusuf ke driven duk wani motsin zahra akan idon sa, motsi kadan ya tambayeta meke damunta.. Daga karshe dai sit ya kwantar mata takwanta bacci yay gaba da i'ta.
Ba'ita ta farkaba saida sukayi shigo cikin maiduguri , tafiyan minti arbain takawosu bakin wani babban gida wanda girmansa yakusa cinye layin dukda girmansa. Horn yay maigadi yabude masa get yashiga....
A 1get yay parking natse yafito yabude ma zahra kofa, a hankali ta saukar da beautiful white leg dinta tafito . a hankali suke takawa saboda kafar zahra, dayan get din akabude musu suka shiga . suna zaune cikin wata haddadiyar rumfa akan rug gakuma fruit gefe cikin wani madaidaicin basket... Da sauri aunty tataso ganin Yusuf da zahra don cayayi zashi lag wani aiki. Dukansu suka taso sukayo gurinsu. Cikin mamaki aunty ke kallon zarah gaba dayanta da yadda take tafiya a bude "what's happening Yusuf!?, where did u get her? Kaida kaje lag..kafada min man." "Its long story aunty just take her in.. Kama hanunta aunty tayi suka shiga ciki su twins sukabi bayansu shikuma Yusuf yawuce part dinshi.
Ganin condition din da zahra ke ciki yasa aunty direct tawuce da ita toilet ta had'a mata ruwan zafi mai gishiri tashiga gasata, sai ta tabbata tayi sannan tahada mata ruwan wanka tafito. Dakinsu su twins taje ta dauko mata normal wear da panta/ bra taje kitchen tahad'o mata lunch mai lafiya tadawo dakin. Time din zahra tafito daga wanka tana zaune kan dressing chair tana shafa lotion..k'ura mata i'do aunty tayi nakusan mimti goma harsaida tajuyo kana tadauke idonta " ga kaya nan kisa." Tafada tana mika mata .amsa tayi tasa batare da tasa bra dinba don nipple dinta tunda yazid ya tumurmushe su basubar zafiba, fant tasa tadawo gefen aunty tazauna . "ZAHRA!." Dagowa tayi takalleta batare datace komaiba "meyasa bakison bayyana min damuwarki?, ko baki daukeni kamar mahaifiyarki ba?." K'asa tayi da kanta batace komaiba.
kama kanta aunty tayi tayi parking dinsa tajanyo wani karamin glass centre table ta daura abincin kai, dakanta tai feeding din zahra saida ta tabbata takoshi sannan ta kyaleta .."ki kwanta kiyi babbici don nasan kingaji, in kin tashi gawaya kikirani sai na had'a maki ruwan zafiko." "To" aje mata wayar tayi kan site drawer tajamata kofa tafito, Batafi minti gomaba bacci ya d'auke ta.
Aunty bedroom dinta tatafi tazauna bakin gado tana nazarin Abubuwa dadama. Su twins suna zaune falo shiru kowa da ntunanin dayake ranshisallamar da labaran yayine duk tadawo dasu ,kaya yake shigowa dashi niki2 manyan Leda's sunfi ashirin. Yusuf ne yashigo dayan hannunsa zube cikin aljihun wandon sa dayan kuma makullin mota. "Where is aunty?." Ya tambaye su. "She's in bedroom.." "Oya go and call her." Tashi salima tayi tanufi bedroom din. Ba'adad'e ba saigata da Aunty, zama tayi kan sofa ta zubama Yusuf idonu tanajiran jin more information... "Aunty ga kayan zahra nasawa, sai kujera mata a closet wad'annan atamfofin Kuna sai akai gundinki.Kallonsa Aunty tatsayayi "Yusuf kafad'amin abinda nakeson ji man...." Dan shafa lallausan gashin kanta yayi yashiga bama aunty duk labarin abinda yafaru wanda yaji yazid yafad'a har kwana a hospital din dasukayi bai b'oyeba..
Nodding kai kawai aunty tashiga yi tareda furta " ZARAH! yama haka?, yayi kyau!."
*👄hαвíєвαh luv👄*
[3/28, 10:40 AM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝.....61/62*
_Writing by_
*👄habiebah luv👄*
_Editing by_
*💅Sadnaf💅*
_Dis page goes to u *Official Sa'adatu D/tsafe,* may Allah guide u and Protect u... Together with u *Lainat🐒* hrt u dear ❤😍._
💝💝💝💝💝💝💝💝💝
Yazid yakasa samun sukuni a rayuwarshi kullum yana cikin tunani, acikin kwana biyu dukya fice hankalinsa yarame yayi baki ga ciwon zuciyar dake dan tab'ashi! . yana zaune kan praying mat yagabatar da sallar asuba yajawo wayarshi yay dailing no. Din mami. Tanakan tadduma tana azkhar wayanta nagefen takawo haske alamun kira yashigo, ganin sunan only son dinnata yasa tak'i dagawa harta katse..sau biyar yana kira amma ko day'a bata dagaba , tanajin tausayin rayuwar da yazid keciki, amma dole take dannen wa don tanuna mishi kuskuren sa. Ganin taki dagawa yasa yakifa kanta da gado yasaki wani kukan huce takaici.. Saida yay mai i'sarsa yatashi yawanko fuskanshi a bathroom yadawo yazauna bakin gado yashiga wani duniyar tunanin. "Yanzu bansan taya zanfara tunkarar mami da maganar zahra ba, inje ince inaso tadayo bayan duk walakancin dana mata..innalillahiwainnailaihirrajiun.. Rire kansa dake saramasa yayi yafada gado. Zubaida tana cikin dakinta wanda dasafiya dadare duk dayane aciki don bala'in duhunsa , tana rakube angle din dakin tahada kai da gwiwa tana sharar hawaye " yaa rabbi kayafemin laifin danayi baya, Allah natuba ubangiji kayafemin kabani ikonyin wata rayuwa mai amfani..." Kukane yaci karfinta tanayi harda shashshek'a. Yazid baizo yabud'e taba yay shirinsa cikin kananan kaya yatafi gidan mami. A Maiduguri kuwa zahra ta warke tafiyanta yadawo dai2 batada wani damuwa yanzu don 'yangidan suna i'ya kokarin su ganin sun kwashe mata dukwani damuwa.. Misalin karfe shad'aya dukkan su suna zaune garden hanun zahra rikeda iPhone din da Yusuf yasai mata sai ganin pix dindasuyi jiya dasuka fita takeyi..sosea duk sunyi kyau, har mamakin kanta take cikin kwana biyu tagyaru tayi wani fresh gadan kiban datayi. "Aunty!" Zahra takira sunanta, "what's happen aunty's daughter?." "aunty nifa yaa yazid yasakeni don bazan k'ara komawa kano ba , har abadah!." Dai2 shigowar Yusuf gurin kenan "yeah kinfadi dai2, nima abinda yasa tun farko banyi wannan maganarba saboda kene, don bansan ko kinason mijinkiba.." Danturo baki gaba tayi "Allah yasauwak'e, damani tun farko bana sonshi..don yanzu kawai yasakeni bankara zama dashi." "Ehh wllh Sis harki koma, irin wannan rashin mutuncinma dayake maki , ea wllh inda nice tunfarko maba zanzauna ba.." Salma tai maganar tana bala'i kamar yanzu abin yake faruwa. Aunty dai tana jinsu batace musu kalaba. "Kinji aunty! Kifadama abba saiyama alwalansa magana!." "Naji Zahra!. "
***
Yazid nashiga falon mami yazube kasa gabanta yasaki wani marayan kuka, kamar wani karamin yaro hakayake harda ajiyan zuciya. Mami ko daga kai batayi ta kalleshiba, amma a kasan ranta jitake kamar ta janyoshi jikinta ta rarrashesa. "Mami don Allah ki yafemin nasan nayi kuskure a baya amma wllh arashin sanine mami...mami kikulani kozanji dadi a raina.. Plss mami ubangijima dakansa yana yafiya.." Tashi tayi zata tafi yarike kafarta yana kara fashewa dawani kukan "free my leg yazid inbaso kake inyi mugun sabamaka ba!." "Mami.... Wani dan banzan tsawa tadaka masa bashiri yacikata, yazube gurin yana burgima. Mami shigewa bedroom dinta tayi tanaji itama kamar tarusa ihun kozataji sanyi ranta. Yafi awa biyu yana kwance Gurin yana kuka daga karshe yatashi yafita ko gani maikyau baiyi. Ikon Allah ne kadai yakai yazid gida lpy don idanuwansa rufewa sukeyi zuciyarshi namasa nauyi kamar andaura mata dutsi ga sarawan da kansa kiyi. Yana parking ko rufe motan baiba yashiga ciki kaitsaye yashige dakinsa yakwanta. Abukamar wasa yakejin zuciyarshi kamar ana mata barin wuta, sosea takemasa wani balin ciwo dabata taba yimasaba .. Rike kirjinsa yayi yana kokarin tashi amma yakasa saimawani duhu da jiri daya fara gani. Wani razanan nen ihu yasaki wanda duk gidan yadauka, dai2 nan mortar faruq ta'ida parking yafito a razane jin ihun yashiga ciki. A hankali idonsa ke rufewa harya gama rufewa ruff tareda tsayawar munfashin sa. A hargitse faruq yashigo dakin yanufi inda yahango yazid kwance yashiga kiran sunansa tareda jijjigashi , ganin abun basauki yasashi fitowa yakira maigadi suka sashi a mota sai hospital. Likitoti biyarne kan yazid, faruq dawasu colleagues dinsa..sunfi awa uku kansa suna masa eaki , dagyar suka samu numfashinsa yadawo. Fitowa dashi akayi aka kaishi dakin dabakowa..coz abun baya bukartar hayaniya. Yana kwance idonsa rufe dakaga irin baccin dayake kasan na wahalane, faruq nazaune bakin gadon kan kujera hanunsa rike da waya yana kiran layin mami.
Bugu biyu tadaga tare dayin sallama "i nayini mami." "Lpy lau faruq ya aiki? Kwana biyu shiru kamar bakanan.." "Wllh mami inanan eaki yay min yawa." "Ayya to Allah yabada sa'a." "Amin" danjim yayi yarasa ta'inda zaifara fadawa mami , candai yanisa yace "am mami dama yazid ne baida lpy yana hospital dinmu...." Zumbur tamike tsaye "what yazid! Yanzufa yafita daga nan!...OK i'm coming right now." Daga haka takatse kiran. Mayafinta da handbag tadauka tafita driver yakaita. Can gefe da inda sukayi parking ta hango faruq da'alama zuwanta yake jira, yana hangota yataho shiya tama jagora har dakin da yazid yake. Sosea taji wani mogun tausayinsa yadirar mata tana ganin da laifinta ma cikin wannan damuwar daya shiga. "Mami plss have a sit .." Zama tayi still idonta nakanshi. Gyaran murya faruq yayi yafara magana a hankali yanda bazai tada yazid daga baccin dayake . "mami, kinsan abunda kedamun yazid!?." Girgaza maikai tayi batare datace komaiba "Heart attack!. Mami yazid yana dab da kamuwa da ciwon zuciya mai tsananin gaske ..mami kamata yayi kimanta da abinda yariga yafaru kija yazid jikinki hakanne zaibashi confidence na tunkarar sauran yakin dake gabanshi! Mami akwai kalubale dayawa agaban yazid akan ZAHRA! Mami yazid yakamu dason zahra, damuwar rashinta ne ya jefashi cikin wannan hali dayake ciki..plss mami kitausaya nasa, kiyafe mishi..."
Mami jitake kamar tai hawaye kozataji saukin zafin da zuciyarta keyi. "Faruq, inama yazid hakane don yagane kuskuren dayayi , faruq kai kanka kasan irin son danake ma yazid, duk duniya banida kowa daya wucesa. Faruq!."
Dagokai yayi yakalli mami da i'donta yacika da kwalla "faruq ciwon zuciya shiyayi agalin abban yazid, faruq banaso inrasa yazid kamar yanda narasa mahaifinsa.." Shiru tayi tasanadin hawaye dataji yana zuba mata, dasauri faruq yaciro handkerchief yatare hawayen "mami karki damu, insha Allah ba'abinda zaisameshi ..zai warke da yardar Allah. Adduarki dakuma kulawarki yake bukata."
Bayan kwana uku yazid yaji dama2 aka sallamosu suka dawo gida. Kulawa ta musamman mami kebashi kamar wani jariri haka tamaidasa, bata barinshi yazauna shikadai saboda karyayi tunani inkaga mami tabar gun yazid to saidai in bacci yayi.
Bayan sati daya..
Suna zaune a falo shida mami yadaura kansa bisa cinyarta tana shafa masa sumar kansa tana bashi labari sai dariya yake. "Ni yazid amaryarka ina takane?." Saida gabansa ya fadi donshi yagama mantawa dawata zubaida, bata fuska yayi yace "tana gida!." "Which house!? ." mami takara tambayarshi "my!." "Yayi kyau!."
Shirune yabiyo baya yazid yafada dunyar tunani "karfa yarinyarnan tamutu nabarta daure daki ba abinci..." Ringing din wayar mami ne yakatse mar tunani, sunan aunty n zahra ne ya bayyana kan screen din...
*👄habiebah luv👄*
[3/28, 8:40 PM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝........63/64*
_Writing by_
*👄habiebah luv👄*
_Ending by_
*💅Sadnaf💅*
_Where re u my guyz?, *Muhi🖤,Kaltumee,daddy' gal,teemarhcuties, my Ngleruma😍,Teema❤,Amina aa,Dr thaudat,🅱k,sa'adeeya,fatima&hasina,💋Aisha bichi💋, sadiya👠,khairati,queen supy*....nd other.. Don u re many can't mention all..dis page is for yours donjin dad'inku..😍_
💝💝💝💝💝💝💝💝💝
duk sai mami taji bata kyautaba, don ita yadace takira. Aunty kuwa zahra ne tasata gaba da kuka dale sai ance akawo mata takardanta, aunty tayi2 da'ita tabari abba yadawo daga tafiyan dayiya sai shi yayi magana amma taki har abinci tadaina ci.
Asanyeya mami tadaga tai sallama, bayan sun gama gaisawa mami take tambayan zahra "zahra tanan lpy ..." Yazid yanaji an ambaci sunan zahra yazabura yamike zaiyi magana mami balla masa harara, natsuwa yayi yasauke kansa kasa. Aunty gagara ma mami maganar tayi don tana matukar jin nauyin ta..gaya sunyi zaman mutunci da 'yar uwarta sam hakan baidace ba..ahaka sukayi salama.
Yusuf da ransa yay matukar baci yafita daga dakin kamar maishirin tashi sama, itama zahra dakinta tawuce tana buga kafa ..aunty kam da i'do tabisu tana rasa abun cewa.
"Mami , ZAHRA!?." "Eh..aunty nta ne takirani.." Mami don Allah kiban no din kinji.." Batakai ga bashiba wayar yazid din tashiga ringing. New number ne dakamar bazai dagaba saikuma yadaga.. Daga dayan bangaren akace "Yeah am YUSUF ALKHALI ! Zahra's broda, kai gaggawar eako ma zahra da takardar saki! ...don bazata dawo gidanka ba ..hop u get me right!?." Yazid dayaji kamar ana saukar masa da ruwar wuta cikin kunnasa yadake yace "okey, alright.. I'll do dat..just give a little time i'll come over nd give her divorce paper!. Tabe baki Yusuf yayi yakatse kiran.
" meye kake cewa yazid!?. " shafa fuskan mami yayi, "mami karki damu, kawai kimin addua gobe zantafi borno...insha Allah zandowo maki da zahra nki.." Hawaye tagani nasauka a idonsa . hawayen tashiga goge masa tajawosa jakinta tana pitting bayansa .."karka damu my boy, everything will be okey soon.." "Insha Allah mami."
Bayan yayi sallar isha baidawo gidan mami ba, gidansa yawuce don yaga zuby ko ta mutu koda saura..ahanya yakira faruq yake sanar dashi suhadu a gidansa..don yasan dole zubaida tana bukatar likita a lokacin. Kusan atare suka isa, direct dakinda take ciki suka shiga. Touch light din wayarsa ya haska dakin , zuby suka hango kwance yashe2 kamar gawa ko numfashi babu. Cikin azama faruq yakarasa yafara bata taimakon gaggawa, shiko yazid baiwani damuwa daga karshema falon yakoma. Yafi minti talatin dakin kafin yafito yashiga kitchen yahada mata shayi mai kauri yadafa indomie yahado mata da snacks da drinks saida yacika wani katon try da abinci kafin yawuce dakin..yazid ko ko kallonshi baiba sai danna waya dayake.
Kamar mayya haka zubaida tarinka tura abinci tanaci tana kwarewa, faruq nazaune gefebta duk tausayinta yacikashi "rayuwa kenan wai zubaida ce wannan..." Saida taji takoshi sannan tafashe mishi dakuka maiban tausayi. "Plss Dr kataimaka min..dan Allah kamaidani gida.. Natuba wllh..bazan sakeba.." Furuq jiyake kamar yay mata kuka don iyaka tausayi tabashi. "It's okey, ya isa insha Allah zan maidaki gida, amma ba yauba..kibari sai gobe." Gyada mishi kai tayi.."ngde." Fuska a daure yazid yashigo "tashi mutafi.." Tashi faruq yayi suka fita amma bai rufe dakinba, kafar falo kawai yarufe. Zubaida tadanji dadi tafito falo tazauna tana tunanin rayuwa.
Washe gari...
Dawuri yazid yashirya yama mami sallama don 10flight dinsu zai tashi, addua sosea mami tamishi har airport tarakashi saida taga tashin jirgin kafin tadawo gida.
Shadaya suka isa , can nesa ya hango *Ajibt* wani friend dinshi dama already yasanar dashi zuwansa kuma gidansu zai sauka. Hugging din juna sukayi suna mai farin ciki, at d end dai mota suka shiga sukatafi. Wow nace time din da'a wangale get din gidan. gidane na bugawa a jarida don yahadu harshe. Mahaifin ajibt mai kudine sosea dan siyasa ne. Saida suka biya yazid ya gaida umman ajibt sannan suka wuce part dinshi.
"Kai man yanaga duk kafita daga yazid dinka?." Furzar da iska mai zafi yazid yayi ya koroma ajibt abinda ke damunsa. Sosea ya tausayama yazid "man harka damu insha Allah komai zai dai2 ta ,zan taimaka maka.
Wanka yazid yayi yasa kananan kaya yafito falo suka zauna da ajibt suna tattauna yanda zasujema zahra. daga bangaren Umma tasa akakawo musu lafiyayyen lunch, saida sukaci suka koshi sannan yazid yace" man yanzufa zamu je." Harara ajibt ya balla masa "saimuje din ea, kabari sai gobe man amma daga zuwa , ko hutu babu.." "Kaga nibansan wulakanci, aikasan ba hutu nazoba kawai inzaka rakani kazo muje.." Bayanda ajibt ya i'ya haka yatashi suka tafi.
"Yazid dama nan gidan ne?, ae gidan abokin Daddy ne!." Gyada kai yazid yayi "abun zaizo mana dad'an sauki kenan!." Basusha wani wahalan shiga gidanba don maigadin yashaida yazid, kuma dama yasan ajibt sometimes akan eakoashi gidan. parking sukayi suka fito akabud'e masu dayan get din suka shiga.
Sanye takeda wani doguwar pink riga 'yar kanti , ta matseta sosea tafidda mata da shep dinta ga boos dinta suncika rigar kamar zasu fito. Tayi rolling da milk din vail, tasa hell hill milk mai adon stones kamar yadda yake gaban rigarta ma stones masu kyau jere. Tana zaune cikin wani rumfa mai zagaye da flawers gaba daya attention dinta nakan wayar ta datake charting kuma da'alamu yanai mata dadi.
Tunda daga nesa yazuba mata mayun idonsa yana kallonta, gani yake kamar ba i'ta..tayi wani irin kyau na musamman sai shining take gawani kiba datayi . har i'sa gurin batasan ya i'sa ba, wayar hanunta yarike tareda had'awa da beautiful fingers dinta. Dagowa tayi tana kallonsa don duk a tunaninta Yusuf, razana tayi tamike tana binshi dawani irin kallo wanda bansan nameba..shima kallonta yake kamar lakacin yafara kallonta "ZAHRA!." Yafada cikin wani murya. Gagara cewa komai tayi sai gaban dake balain faduwa..shima dakewa kawai yake amma wani irin faduwar gaba yakeyi. Pls say something man.." Still batace komaiba kuma idonta nakansa .. ganin taki magane yamatso kusanta yana kokarin riketa, dai-dai shigowar Yusuf kenan ya hango yazid nakokarin rikota "stop malam don't ever touch her!!!." Cikin d'aga murya yay maganar. Karasowa gurin yayi yana watsama yazid wani disguise looking. "Meye kake kokarin yi haka, bayan yanzu ba marka bace!." Shima yazid din wani kallo yawatsa masa "kila kaika datse mana aurenko!?." "I think divorce paper kakawo mata!?." Wani murmushin rainin hankali yazid yasaki "tsakanin aurena da zahra basaki ciki..I want u to know dat nazo tafiya da matata ne!." "Kayi kad'an! Baka i'saba dole kasaketa..at dat time nikeda i'ko da ZAHRA! ba kaiba!. so dole sai yadda nayi..kaikafa buga game din amma nikeda ikon tsaidashi.. dis is just to beginning!.. Yanzu akafara kick din!.."
"Haka kace!?." "Haka nafad'a!." "Muzuba mugani zanga wazaiyi wining!" Murmushin gefe Yusuf yasaki "U shall see!." Daga haka yaja hanun zahra sukayi ciki. Serere akabar yazid gun yama rasa abunyi, jiki a matukar sanyaye yaja kafarsa da kyar yashiga mota ajibt yaja sukabar gidan.
*👄habiebah luv👄*
[3/29, 11:25 AM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝.......65/66*
_Writing by_
*👄habiebah Luv👄*
_Editing by_
*💅Sadnaf💅*
_Kuyi hakuri da wannan bayawa...don banjin dadi..._
💝💝💝💝💝💝💝💝💝
Runtsa idonsa yayi dak'arfi yanajin zuciyarshi kamar zata fito..."meye wannan Yusuf din kenufi ne!?." Ganin bazai iya samo amsarba yasa yabude idonsa dasuka dawo kamar gaushi don jaa yasauke kan ajibt wanda shima kallonsa yake. Dafa kafadanshi ajibt yayi "kakwantar da hankalinka frnd insha Allah komai zai dawo dai2..kuma kasan me?." Kai yazid yagirgiza batare dayace komai ba. "In dis week daddy will come back from Cairo kaga saikawai mufada mishi dakansa zaije yama abban su Yusuf din magana.." "Gud idea frnd ngde Allah yasaka..." "Noo ..u deserved it ea.." Key ajibt yama motar suka fita daga gidan .
Kusan cin karo sukayi da aunty dake bakin kofar falo kusan duk abinda sukayi a idonta, fuska a matukar daure take kallon Yusuf.. "Shige ciki.." Tafada zahra jiki a sanyaye tawuce kamar wanda kwai yafashema a ciki haka take tafiya , gaba daya takasa gane condition din datake ciki. "YUSUF!." Aunty takira sunanshi bayan sunkara sa falon sun zauna , sauke kansa k'asa yayi batare daya amsaba "kanakishin zahra ne!." Kamar saukar aradu haka yakejin maganar aunty. "I'm asking u nd u keep silent.." Dagowa yayi yakalleta still he can't say anything.. " U can go..tunda kazama kurma.." Da kyar ya'i d'aga kafarsa yafita gaba daya tunaninsa ya cakub'e. Tashi aunty tayi tashiga dakin zahra, gamamakinta hangota tayi kwanshe gado tana hararar hawaye..gada daya tausayinta ne yakama aunty , tarasa gane gaskiyar ta tanason mijin tane koya?." , gakuma wani lamari datake ganowa kamar zahra nada ciki.. Karasawa tayi tad'agota ta rumgumeta tana pitting bayanta "kiyi shiru daughter, its okey.." Tsit tayi sai ajiyan zuciya datake saukewa . "ZAHRA!." "Naam aunty" har kiboyemin komai, take me as ur mother fad'amin kinason yazid ne!?, kinason komawa gidanshi..!?." Zabura tayi tad'ago saikuma tamaida kanta tasaki kuka. "Aunty ni basonsa nakeba, kawai dai yaban tausayi ne ...." Tafad'a cikin kuka..."to ya'isa, shikenan..kiyi shiru." Lallashinta tarinkayi harsaida tai bacci. Tsayawa kallon tayi nakusan minti goma tana kissima abubuwa a ranta, daga karshe fita takoma bedroom dinta.
Yazid nazaune kan gado gabanshi da system yana dannawa, shikuma ajibt nakwance yana waya. Bayan yagama wayarsa ya dago yana kallon yazid , seriously yafara mishi magana "kagani Dr ne ko Yazid!?." Dagowa yayi yana kallonsa da mamaki "ca akwai maka bansaniba!?." "To alhmdllh tunda kasani..as my observation nagano matarka! ZAHRA! Nada ciki!." Wani uban zabura yazid yayi yajuyo yana kallon shi. "Ajibt CIKI!?." "Yeah,sure ciki!." Rasa gane condition din da ke ciki nayi, kamar wanda aka zabura yatashi yadauki makullin mota yay hanyar fita, fixgoshi ajibt yayi yana watsa masa wani kallon. "What are u trying to do?." "Bansaniba, dalla sakeni ..zanje in dauko matata ne ta haihu a gurine..inkuma sunce bazata biyoniba sai sucire cikin suban abina!, tunda ninayi!." Wani mugun dariya ajibt yasheke da "wato ance matarka nada ciki harka samu abin gadarako?, to wllh kamaida hankalinka inkace zakai masu wautar 'yan fari duka zasuk'i badata..gara kabi a sannu.
Dawowa yayi yazauna yana sosa geya, wani irin farin ciki yakeji mara misaltuwa wanda baitaba jiba!.
Kano...
Karfe goma faruq yashigo gidan yazid , da spirykey yatoho yabode falon yashiga . time Zubaida nasaune kasa tabuga uban tagumi , karasowa yayi yazauna gefenta sai a lokacin taji mutum, a razane tadago tana kallon shi tayi tunanin yazid ne saikuma taga faruq ne. Kallon dataga yakemane yasa tasauke kanta kasa " tashi inkaiki gida.." Kamar jira takekuwa tamika tai hanyar waje.. Murmushi furuq yayi yabi bayanta...rufe falon yayi yashiga motar dama zuby kam tuni tashige. A haka suka isa harcikin gidansu yakaita , tunda akashigo idonta yafara tara kwalla, godiya sosea tamishi tashige ciki da gudu tana sakin wani kuka. Tausayinta yagama cikishi saida yaga shigewarta kana yaja motarshi yafito.
Momy tana zaune falo ga abinci gaban takasa ci gaya tabuga wani uban tagumi . kamar daga sama take jiyo kukan zubaida , idonta takai kan kofa dai2 isonwan zubaida kenan.. wani irin super momy tayi ta rungume zubaida suka saki wani irin kuka....
*👄habiebah Luv👄*
[3/31, 11:56 AM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝.....67/68*
_Writing by_
*👄habiebah Luv👄*
_Editing by_
*💅Sadnaf💅*
_Dis page is 4 u 🌹Ayshah🌹, tnku for diffusion my book._
💝💝💝💝💝💝💝💝💝
Duka kuka suka rinkayi bamai rarrashin wani, saida sukayi mai isarsu sannan momy takama hanun zubaida suka shiga bedroom. Zaunarta tayi bakin gado i'tama tazauna takurama zubyn i'do. K'asa tai dakanta tanajin kunyar mahaifiyar tata..."plss momy..gor give me.. Nayi nadama abinda nai, ya rabbi kayafemin, kabini akonyin aikin alkhairi asauran rayuwa ta data rege...am regretted.. " wani kukanne yakara kufce mata tashige jikn momy.. Kiyi shiru daughter, is okey..dis is our destiny wannan kaddarar tamuce baki daya bataki kekadai ba..ya rabbi kayafe mana baki daya.. wannan abinda na suke nake girba..." Itama momy kukan tafashe dashi tana kara rungumeta.. "Yanzu momy daddy yasani ne?." "Baida masani, kuma babban abinda ke damuna bansa how can explain to him ba..bansani ba daughter ko wani abin zamuyi creating mufada mishi?." "Nooo momy!, noo! Don't tell him lie, tell him d truth... wannan maganar tafi karfin wasa bai kamata abuye masa ba.." Tafada cikin shashshek'a. Haka suka yini suna kuka bawanda ya'iya rarrashin wani, dakyar wani zubin momy ke rarrashinta , don i'tama kukan take.
Farida duk ta lallace tayi baki gaba daya tarame tafice hayyacinta, kullum tana shikin kuka tana nadamar biyema hisham datayi tabashi kanta ya lalata mata rayuwa yaguda yabarta. Yau kamar kullum tana zaune garden tahade kai da gwiwa tana kuka "hisham kacuceni , ka yaudareni, kagudu kabarni ka lalatani..bazan taba yafe makaba..macuci.." Kuka tarinka yi tana surutai, sai da tai mai i'sarta kafin taje bakin fanfo tawanke fuskanta tawuce falon mama. Dai2 shigarta fauxy tafito daga dakinta taci gayu sai taku take tana girgiza. Mama dake zaune falo idonta akan fauxy tace " kai Allah dai yanuna mana bakinku keda nabil , ranar za'ayi shagali, zamu jijjige.." Tintsirewa da dariya fauxy tayi "kai mama wai zaku jijjige..ea yanzu kun tsufa." "Inafa tsufa, ea yanda kikejin kanki haka nakejina agun abbanku...kedai Allah yanuna mana ranar." "To amin mama, ni zanje gurin my nabil." "Kigaidashi, kije mamanshi na gaidashi.." To mama zaiji." Ficewa tayi daga falon tana baza duwawu, mama ta fallawa farida harara.."dalla tashi kishige ciki kullum kina zaman gida bakida mashinshini..mai bakin jini kawai." Dagudu farida tashige bedroom dinta tafada gado tareda sakin wani kuka maiban tausayi. Kamar kullum sai da yagama kissing dinta kafin yad'ago jajayen idonsa yana kallonta .plss baby aunguwa zaki rakani..." Yafada numfashinsa na sama da kasa .. "Wani unguwa kuma baby.." "Gidan yayar momyne, kullum saita tambayeki..tace inkawo ki..plss don't say noo.." Wani dadi fauxy taji tunkan tashiga har family sunfara tambayarta.. "OK ..to muje.." "To baby kije kigawa mama.." "Noo karka damu , ba'abinda zatace." Wuta yay ma motar suka fita daga gidan. Saida sukeyi tafiyan kusa 1h kafin suka i'so bakin wani gida. Gidane mai kyau nagani nafada..horn nabil yayi maigadi yabude mai get. Gidan shiru kamar bakowa ciki. "Bismilla baby,,,mushiga.." Yafada yana shigewa gaba. Abakin falon suka tsaya ya danna doorbell amma shiru sunkusan kai minti biyar gurin amma ba'alaman za'a bude "baby mushiga kawai maybe basakusa." Shiga sukayi fauxy tazauna shikum yay upstair. Baidad'eba ya sauko hannunshi rike da ruwan faro .."baby kigafa auntyn batanan nakirata tace makofta tashiga yanzu zata dawo.." Yafada yana ganin reaction dinta.. "OK badamuwa, mujirata." Wasa yafara da i'ta sosea wannan karon abin yafi na kullum,don saida nabil yasamu nasarar shigarta. Tureta yayi, ya hankad'a ta gefe yana watsa mata wani mugun kallo.
"Damake 'yar iskace Fauziyya!?, damake ba cikekkiyar budurwa ceba!, Allah yatona maki asiri..gara da Allah yasa ban aureki ba..dama kinje kingama bada kanki awasu 'yan iskan shiyasa bakida matsala kona tabaki..karuwa kawai..harki kara nunawa ko a hanyane kinsanni..kuma bazan aureki ba ...get out!!!." Yadoka mata wata uwar tsawa.. Jikina rawa tana hawaye tace "don Allah nabil kayi hakuri,, wllh insonka..karkamin haka..plss natuba sharrin shaidan ne..amma zan gyara.." " before I open m eyes kificemin...inba hakaba saina kasheki!." Jinkisa yasa tatashi tad'aibi kayanta hanu tafice tana kuka. Sai a balcony tasa kayan ta sannan tafita . abakin titi tasamu abin hawa, har kofar gida yakaita tabishi kudinshi tashige..bakowa falo don haka dakinta tawuce tasa key tashiga kuka tana tunanin yanda akayi lokaci daya abubuwa suka dagule mata.
Borno...yazid cikin farinciki yakasance wannan ranar, kwana yayi yana salla yana godema Allah.. Kuma yana rokon Allah daya sassauta zuciyan zahra tatausaya masa tadawo. Bayan sunyi breakfast yazid yadauki makullim mota baikobi takan ajibt ba yafice wani babban mall mai suna *S MATA SHOPPING MALL* . siyayya yayi sosea na kayan kwadayi, saida yacika manyan leda biyu sannan yakoma gida. Afalo yatarda ajibt zaune yana danna waya, wani dariya ne yazoma ajibt daya ganshi da leda.."aa malam yazid mijin zahra daga i'na haka ko gayyata babu.." B'ata fuska yazid yayi "kaga bansan wulakanci, inzaka rakani katashi kashirya don nima shiryawa zanyi... " daga nan yashige bedroom. Dariya ajibt yarinka yi saida yayi mai i'sarsa kafin yatashi yashiga shiryawa. Karfe shabiyu dai2 suka gama shirinsu sukama Umma sallama suka kama hanyar gidan *Alh Alkhali.*
Wannan karon harcikin falon aunty su yazid suka shiga,
Duk suna zaune aunty na karanta wani newspaper su zahra kuma nazaune sunsa laptop gaba suna kallon pics.
"Assalamu alykum." Sallamarsu tasa aunty duban bakin kofa, fara'arta ta fadada ta amsa "sannunku da zuwa,,,kukaraso man." Saida sukayi nailing suka gaida aunty kafin suka zaune. "Ajibt ya ummanka ?." "Lpy lau aunty, tace agaisheki." "To ina amsawa, salma kawo musu ruwa man." Tashi tayi ta gaidasu kana tawuce kitchen . zahra kam tunda taji muryar yazid gabanta ke faduwa sosea2, da gyar ta'iya bude baki tace "ina..yininku..." Murya narawa. takara sa, ajibt ne kadai ya amsa don yazid garara amsawa yayi sai ido daya kafeta dashi.wani irin kyau dayafi ko yaushe taimasa, sai shining take gawani uban fari datakara da kibar datayi. Gaba daya zaman gurin ya i'sheta tatakura sosea gashi bata i'yajin kafarta zata dauketa tabar gurin, itadai burinta sutashi sutafi.
Salma da katon try tafito daga kitchen, baked chicken meatballs ne ciki da pizza with chorizo, avocado and goatcheese, sai hot drinks. Tunda tafito ajibt kebinta da i'do hakanan yaji ta burgeshi, wani dan medium centre table ta janyo ta i'jiye kai. "Sunnuko!." Ajibt yafad'a yana mata murmushi mai kyau. "Yawwa!." Bawani yunwa sukejiba amma don gulma saida suka kusa cinyewa (sunji delicious). Sunfi awa biyu gidan daga bisani sukama aunty sallama .."to aunty mu zamu wuce.." "Har zaku tafi ajibt, to kagaidamin da ummanka.." Har ajibt yakai bakin kafo yazid yananan idonsa nakan zahra da i'ta kuma duk attention dinta nakan system din gabanta.. "Kaga malam inba yanzu zaka tafiba nizan wuce.." Gaba daya kunya yakamashi yajuyo yana dan sosa kai yama aunty sallama suka wuce.. Haryaje bakin kofa ajibt kuma yafita yajuyo sai kuma suka tad'a ido da aunty , kasa yayi dakai yana shafawa..juyawa yakarayi zaifita still ay kara juyowa. Murmushi aunty tayi tace "is there anything!?." "Um..aunty dama..nace..dan Allah..inason magana..da i'ta.." Yayi maganar cikin kinkina. Gyada mishi kai kawai tayi, dasauri yafice yba gurin ajibt. Harara ya galla masa "kaje kayi zamanka dalla kasani jira.." "Kai bawannan ba
,yanzu kajirani mota zanyi magana da gimbiyata ne tananan fitowa." Tsuka ajibt yaja yay shigewarsa mota shikuma yadawo gurin wani rumfa yazauna yana jiran fitowan ta.
"ZAHRA.." "Naam aunty.." "Tashi kije zakuyi magana da yazid!." Dasauri tad'ago tana kallon aunty don ita duk da bataji mesuka ceba.."aunty injefa kikace, kumama ni bawani magana dazai fad'amin.." "Nace kitashi kije.." "Aunty.... Daga mata hanutayi " shotup, don't say anything.. " gaba daya ranta baiso hakaba , tashi tayi tayafa wani karamin gyele akan doguwar rigan atampan dake jikin ta tafice. Bata karasa gurin dayake ba tatsaya can wani guri tajuya mishi baya, murmushi yayi yatako har inda take yana kallon eyeball dinta. "Princess..!" Da mamaki tad'ago tana kallon sa saikuma tasauke kanta don kwarjini daya mata. "Plss FATIMA! Say something.. Plss inji muryanki..abaya nayi kuskure nazalunceki amma kiyi hakuri da duk abinda yafaru, kitaimaka kidawo muzauna innuna maki irinson danake maki..plss ko dan babyna dake jikin ki !." A mujun razane tad'ago tana kallon sa, sai a sannan ta'iya furta "BABY!!!?." "Yess Fatima, akwai jinina dake yawo a cikinki! " yafada yana kaiwa hanu cikin tareda shafawa!. "Hey! ." Yusuf yafada da karfin gaske. Karasowa gurin yay ya wullar da hanun yazid dake kan cikinta " meye hakan? Hargida zakazo kanama mutane iskanci!?." "Hy malam cooldown , ina duba lafiyan babyna dake cikinta ne!." Kara tamke fuska yayi yana jefama masa banzan kallo "inma baka cikin hankalinka to garama kadawo, don bawani ciki ajikin zahra..kuma gidanka ne dabazata komaba!." " Dolene takoma ta haifamin yarona don bazan barta da cikina jikinta tacigaba dazama nanba..hop kafahim ceni?." "ZAHRA!." Yusuf yakirata ba'alama wasa, "inaso kifad'a mishi da bakinki cewa bazaki komaba!." Kirjinta ne yay wani mugun bugawa ruwa yafara taruwa idonta. Same with him shima kirjin nasa bugawa yake yanajin Yusuf yafara fin karfinsa.. "Say it.." Yadaka mata tsawa, cikin rawar murya tace "ban komawa gidanka yaa yazid..!" Kamar ansauke masa guduma a kirji haka yaji saukan maganar.. Zayyi magana Yusuf yaja hanunta sukabar wurin. I'donsane yaciko da kwalla kanshi na balain juya masa kawai maganar zahra ne yake masa suwwa cikin kunnen sa da kwakwalwarsa.."bankomawa gidanka..." Hawaye kawai yaji yana sauko mai. Ajibt dake cikin mota yana ganin duk abinda ke faruwa yafito yakamata hanunsa yasashi mota suka wuce gida.
Zahra kam suna shiga falo ta fizge hanunta daga na Yusuf tashige dakinta tasa key tafada gado tana kuka!. Mike kafada yayi dai2 zaifita yaji muryan aunty "YUSUF zonan!." Juyawa yayi yaganta tsaye bakin stairs tahad'e rea sosea saida gaban Yusuf yafad'i .. A hankali yataka zuwa gurin "gani aunty" yafada a hankali. "Karka kara shiga tsakanin yazid da zahra!, mata da miji ba'ashiga tsakaninsu watara kai zasu bama kunya...kuma meye amfanin sakinma in anyishi tunda har Allah yakawo rabo a tsakini, yazid yayi laifi kuma yagane laifinsa easai a barshi haka..plss kabar shi haka.." Cikin sanyi yad'ago yana kallonta,"aunty nima bawai ina abunnan don wani manufa bane, inayi don inkwata mata 'yanci ne.." "To shikenan hakan yayi kyau kaje Allah yaymaka albarka." "Amin aunty na , ngde."
Suna komawa gida yazid yashige bedroom yafada gado yana kuka kamar karamin yaro. "Haba yazid meye kake yi haka!, saikace ba namiji ba kazo kana kuka akan mace.." Dukda kukan dayake bai hanashi hararan ajibt ba "nayi kuka akan mace, don bakasan irin son danake mataba ne saisa kake fadan haka , wllh mutuwa ma zan'iya akanta..plss zahra don't leave me I can't stay without u......plss come back closer to me.." Kuka yarinka yi kamar yaro, ajibt yayi rarrashin harya gaji yabarshi.
Yau Thursday ranar da abban ajibt zai dawo, karfe biyu guide dinsa sukaje daukoshi a airport. Bayan yahuta yayi wanka yaci abinci su yazid sukaje mishi sannu da dawowa, gaisawa sukayi da yazid da fara arsa "when did u come yazid?." ,"since 5days back abba." "Ina maminka" "Abba tana nan lpy.. Tace agaida ka.." "To yayi kyau...amma yanaga dukka sanza kazama wani irin?." Yazid dakaman jira yake yafashe da kuka "suhanAllah..what's happen.. Fadamin meye yake faruwa?." Yazid bai boyeba ya zayyanewa abba komai tundaga aurensu.. "Kakwantar da hankalinka, insha Allah komai zaizo karshe soon, dakaina zanje gurin Alh anjuma kajiko?" "To abba ngde Allah yakara girma.." Fita sukayi ajibt na mishi dariya.
*👄habiebah Luv👄*
[4/2, 12:58 PM] 👄hαвєвαh luv👄: *💝KARUWA CE💝....69/70*
*END....*
I’m waiting,hoping and wishing for the time when we can be together again. I miss you so much my *FANS*😭.
_Writing by_
*👄habiebah Luv👄*
_Editing by_
*💅Sadnaf💅*
💝💝💝💝💝💝💝💝💝
Misalin karfe 9:30pm abban ajibt yadawo daga gidan Alh Alkhali, fuska ba walwala yafito daga mota bayan wani guide dinshi yabude mashi kofa. Yazid da ajibt kuwa suna zaune compound suna jiran dawowan abba, tunda yazid yaga yanayinsa ba dadi gabansa ke dukan uku2 lokaci daya idonsa yafara tara ruwa. Kallon ajibt yayi wanda shi idonsa na kanshi "frnd Allah yasa bawani matsala aka samuba, don naga mood dinshi is so bad.." Yazid yafada muryanshi na cracking. Dan bubbuga kafadanshi ajibt yayi "be strong mana man,, insha Allah everything will be alright..ka kwantar da hankakinka." Tashi sukayi sukabi bayan abba bayan yashiga part dinshi. A falo suka sameshi zaune yayi crossing legs yana kadasu. Nan kasa suka zauna suka gaidashi batare da ya amsa ba yafara magana. "YAZID!." Abba yakira sunanshi da babbar murya. Nan take jikin yazid yakara sanyi kwalla nataruwa idonsa don yasan babu nasara a wannan lamarin, cikin sanyin murya ya amsa kansa na kasa. "Kasaurareni da kyau, kabar ZAHRA! , kakyalesu nan da shekara daya mugani..suda kansu zasu naimeka. Harka kara zuwa inda take muzuba musu ido.." Tunda abba yafara magana hawaye yafara saukoma yazid yanaji kamar ruwan wuta ake zuba masa jikinsa.."shikenan nashiga uku.." Abinda kawai yake fada ransa. "Kanajina ko!?." "Eh..ab...ba.." Gud..u can go..." Dakyar ya i'ya Jan kafarsa yafita daga dakin , suna fita yafashe dawani irin kuka yafada jikin ajibt. "Shknn na shiga uku frnd ..mutuwa zanyi wllh...wllh zanmutu..ya Allah help me.." Kamar karamin yaro haka yazage yana kuka. Dakyar yajashi daki yazaunar shi yana bashi hakuri,,amma ko saurarunshi bayayi. "Nikam rayuwa ta tazo karshe ajibt... Don Allah ko bayan reana ka naimamin yafiya gurin zahra don Allah... Bazan iya rayuwa ba'itaba..I can't.." Lokaci daya zazzabi mai zafin gaske yarufe shi , bakaramin tausayi yabama ajibt ba..injection yay masa yasamishi ruwa nantake yasamu bacci.
A week later... Yazid yagama fita hayyacinsa yarame yayi baki duk ya lallace duk wanda yasan shi da yakalleshi yanzu dakyar zai ganeshi, kana kallon shi kasan yana cikin bala'i . yana zaune falo ya buga uban tagumi yana matsar kwalla, ajibt nazaune gefen yana kallonsa.. "Frnd nikan yau zanje gurin zahra, in mata koda kallon karshe kafin in mutu...don nasan rayuwa ta tazo karshe.." Yakare maganar hawaye daya nabin daya fuskanshi. Gagara cewa komai ajibt yayi don baisan mezeciba. Tashi yayi yay wanka yashirya cikin kananan kaya, dukda raman da yayi amma kyansa nanan inda yake..makullin mota yadauka yafice daga dakin. Tunda yashiga layin gabansa ke bala'in faduwa lokaci daya sanyi ya shigesa.
A waje yay parking yafito yay knocking mai gadi yabude yashiga..kamar wanda kwai yafashewa ciki haka yake takawa, a compound yagano Yusuf zaune kan rest bench yayi crossing legs hanunshi rike da jarida yana karantawa.. Lokaci daya maganar Yusuf yadawo mishi.."yanzu nike da iko da zahra bakaiba..dole sai yadda nayi.." Hawaye yaji nasauka a face dinshi don yasan yayi wauta ..dayabi Yusuf a sannu da duk abin baikai hakaba..dakyar yaja kafarsa yakarasa gurin da Yusuf kezaune yay nilling tareda kama 2legs dinshi yana hawaye.. "Broda! Kataimaka min dan Allah.. Kabani zahra nasan nayi kuskure amma nobody above a mistake.. Ubangijin muna masa laifi kuma yayafa mana inmun rokesa..don Allah kugafar ceni gaba daya ..nagane laifina plss kubani matata ..." Kuka yazid keyi tsakani da Allah harda majina, tunda yafara maganar Yusuf ke kallonsa da mamaki..shidai yasan abban ajibt yazo gurin abban su kuma angama magana akan zata koma ..toko meye yanzu?..oho.." "It's okey..ya'isa, yanzu katashi kaje gobe zan naimeka.." Kara rike kafanshi yayi yana masa godiya kamar zai ari baki.. "Bakomai katashi takaje.." Harya fara tafiya Yusuf yabishi da i'do yana mamakin yanda duk yafita kamanninsa, dawowa yazid yayi yace "don Allah broda inason ganinta.." Batare da yace kamaiba yacire wayarshi yay dailing no din zahra , few minute later saigata tafito sanye da Arabian gown kana kallonta kaga wanda hankalinsa kwance cikin hutu.. Idonsa kyem akanta ko kiftawa babu.. "Kitsaya zakuyi magana..." Yusuf yafada tareda mikewa yabar gurin.
Kamo hanunta yayi yarike cikin nasa hawayensa nazuba kai..dagowa tayi tana kallon sa eyeball to eyeball tausayinsa na ratsata, i'ta kanta tasan yasha wahalan rayuwa akan ta. "FATIMA!." Taji yakira sunanta, bata i'ya amsa mishi ba sai idonta data sauke kasa.. "Abunda nai makine yakebina, ya hanani samun sukuni a rayuwa..kiyafemin kidawo gareni ..in nuna maki yanda dake sonki..zan muna maki gatan daba kowace mace kesamuba..zaki alfahari dani amatsayin miji.. Plss FATIMA for give me..."yakasa controlling kansa hawaye kawai yakeyi sosea yana shashshek'a . " it's okey yaa yazid.. Kabar kuka, nayafe maka ..nadade da yafemaka yaa yazid.. " baisan lokacin da ya rungumota jikinsa ba ya furta mata "I LOVE U." Cikin kunnanta, zame jikinta tayi tai cikin gida da gudu.." Farin cikin da yazid ya tsinci kansa cikin wannan lokacin bazai misaltuba.
Bayan sati...ansa komawan zahra nanda sati biyu , gyara aunty tana ana mata..cikin lokaci kankani zahra tazamo tauraruwa..su yazid kai sairawa yake yafadama mami duk abinda ke faruwa.. Gyara tasa akafarayi agidan yazid na musamman. Ranar asabar yazid yazo tafiya da matarshi , sosea aka sasu gaba akamusu nasiha har airport su Yusuf suka rakasu saida jirginsu yatashi kafin suka koma gida.Karfe biyu suka sauka international airport dama already mami tatura masu driver batareda bata lokaciba suka shiga suka wuce gida. Farin cikin da Mami ke ciki bazai faduba kamar zata cinye zahra sai nan nan take da i'ta , part din Yazid tasa aka gyara musu kafin agama masu gyaran gidansu. Har karfe goma suna zaune falon mami sunata hira...yazid yagama kaguwa sutashi sutafi part dinshi. "Mami bacci nakeji.." Yafada yana hamman karya.. "To ea saika tashi katafi..kona rikeka?.." Murmushi zahra tayi tadago tana kallon yazid dashima idonsa yana kanta.. Lakwabar da kai yayi a hankali yace "plss mana wife!." Juya mishi ido tayi tareda yamishi kwalo tana dariya kasa2 . har karfe shadaya suna zaune saida mami tafara gyangyadi kafin taimasu sallama tace suma suje sukwanta. Mami tana shigewa bedroom yazid ya dauki zahra cidak kamar wata baby doll suka tafi .
Washe gari.. Karfe tara suka gama shirinsu suka tafo part din mami..itama sauko wanta kenan suka wuce dinning yin break.
A bangaren su zubaida kuwa ranarda daddynta yadawo ranar momy tafada masa duk abinda yafaru, bakaramin kuka suka shaba dukansu kamar lokacin abin yafaru. Daddy n yafi ganin abin laifinsa ne don saida tafito tasanar dasu cewa tanason aure amma boko tarufe mashi ido yagagara ganewa..naiman yafiyanta sukayi suna kuka i'tama tanema yafiyansi. Daddy n ta dakansa yaje gurin yazid ya naimi takardar zubaida bamusu kuwa yabashi dama ko baizoba zai aika musu. Yanzu zubaida tazama mutuniyar kirki tayi watsi daduk rayuwanta na baya takama Allah kullum tana cikin istigfari. Bayan tagama iddane faruq yafara biyowa tabayan gida, bamusu tabasi hadin kai suka fara soyayya cikin tsafta donshima faruq yatuba da duk iskancin dayake.
A gidan mama kuwa komai ya cabe mata domin kuwa fauxy ciki gareta..farida ta natsu takama Allah baruwan ta da harkar kowa gidan kullum tana cikin tuba da abinda ta aekata. Ranar wata talata abba yadawo daga abroad , tashin hankali daya shiga lakacinda yaga fauxy da ciki baa magana..wuta ya bude masu akan ko tasamo wanda yay mata cikin ya aureta ko yakoresu daga gidan shi..kuka sukarinka yi ita da mama suna rokanshi da kyar ya kyalesu.Wata rana farida nazaune compound din gidan su kamar daga sama ta hango hisham yazo ya durkusa gabanta yana kuka yan naiman yafiyar ta..yafemashi tayi itama kuma yace yanzu zai aureta, dakanta tafadama abban su akan family hisham zasu kawo kudin aure.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya su zahra sunkoma gidan su ,,, son da yazid yake nuna mata kuwa ba misali don kullum suna nanike da juna yanajin lafiyar babynshi..
Faruq da zubaida kuwa an daura musu aure yayinda suka tare a katafaren gidan faruq son dasuke nunama juna kuwa baa magana. Anyi auren farida da hisham yayinda arman shima ya dawo hanyar Allah yanaimi aure akabashi yanzu ansa auren nanda wata daya.. Mama itama tagane laifin datayi baya , tana kuka taje gurin abban tana naiman yafiyarsa ,cikin ikon Allah kuwa yayafe mata yarungumi 'yarsa zahra da duk wani abunasa yanzu da sunanta yake yinshi..don kuwa soyayyarta sabuwa tadawo agareshi yana tunawa da mahaifiyarta. Fauxy kam wani dattijon Alh mai mata uku tasamu ya aureta suna can abuja abinsu.
Zahra tazama 'yar gata tako'ina abbanta baya sati baizo gidanta ba susha hiransu suci abinci harda yazid sanna yatafi.
Borno..Yusuf yakoma Spain bakin aikinsa yayinda yasamu wata 'yar can ya aura suna zaune lpy ba maijin kansu..anyi auren twins a borno yayinda gida yazama shiru daga aunty sai mijinta. Ajibt ma yayi aurensa amma a abuja suke da zama don can yake aiki.
Bayan wata shida..
Zahra da mijinta uban 'ya'yanta abin alfaharinta wato yazid nagani tareda beautiful kindz dinsu guda biyu mace da namiji sunsha kwalli sunje park suna rest..sai magrib suka koma gida already me aikinsu tai musu girki ta gyara ko i'na. wanka sukayi sukayi salla kafin suka fito yin dinner. Bayan anyi sallar isha zahra ta karama *Amir da Amira* wanka takaisu dakinsu tareda Nanny dinsu. Wanka itama tayi tashafa turaruka masu matukar dadi tasaka wani sexy nighty gown tatafi dakin yazid. Saida tabiya kitchen tahada mashi coffee kafin tadawo a hankali tatura kofar tashiga. Yana zaune bakin gado dagashi sai boxer laptop na gabanshi yana wani eaki. Kamshi turarenta ne yasanar mishi da zuwanta, ture laptop din yayi yazuba tama idon. Karban try din yayi ya keeping a side yajawota jikinshi yana shafa gashin kanta. "Babyna 'yar aljannah sai yanzu?, tun dazufa nake jiranki..yau inaso musamu wani baby kinga su amir kullum saisunce suna son small baby.." Yafada yana shafa cikinta. Ture mishi hanu tayi.."plss kabar wannan kasha coffee nan karya huce.." Noke wuya yayi kamar karamin yaro.. "Nikam naki...kenake so.."yafada yana lalumanta, Kashe wutan dakin yayi yamatseta yana mata cakulkuli..dariya taringayi kamar zata shide shima yana tayatayata..saida yaga zata shide sannan ya kyaleta yacire mata rigan baccinta yaja musu bargo.
*ALHAMDULILLAH*
Nan nakawo karshen wannan book mai suna *KARUWA CE..*, kurakuran danayi ciki Allah kayafemin ..
Masoya abin alfahari ..ina alfahari daku masoyana iduk inda kuke..alkhairin Allah yakasance tare daku.
Inamika gaisuwa ta musaman gareku:,
💅Sadnaf💅
Khaleesat haiydar
Zuwairat nuhu
Axland
Khadija bb
Classic amrah
Khadija candy
Real khady
Muhi
My best Anfa
BieBie dee
Kaltumee
Lainat
Daddy's gal
Amin Aa
Ngileruma
Sadiya
Teema... Nd others..
Saimun hadu a sabon book dina nagaba wanda insha Allah zakujishi soon..
*👄habiebah Luv👄*