Harta karasa shigowa falon, bai kuma cewa komai ba sai kllonta da yake yi, yayin da falon ya cika da sautin kukan fauziya, hjy binta zama tayi akan kujera, sai a sannan Mahmud ya iya furta kalman mama, ta daga mai hannu alaman yayi shuru, tace naji komai bana bukatan wani magana, yanzu dai kafin wani bayani ka dawo da matarka, ganin ynda ta daure fuska babu alaman wasa a ciki, yasa yace na dawo da ita, jin haka fauziya dake kukan munafurci ta matsa kusa da hjy binta tana fadin wlh mama nasan nan gaba zai kara saki na, indai akan waccan matar tashi ne, ta nuna salma da gaba daya komai nata ya tsaya cak, sai a sannan hjy binta ta kalli salma, tace mlm ki zauna kin wani tsaya ki kam, salma tayi sauri ta zauna, nan hjy binta ta kalli fauziya dake faman sharara kuka, tace fauziya naji abun daya faru tun daka farko, nayi mamakin da wannan kalman ya fito daka bakin ki, a yau inda bani da wani halaka dake dasai nasa an hukunta ki, domin bazan bari aci zarafin jika naba, ina so daka yau ki sani akan wannan yaron zan iya sabama kowa dan haka ki kiyaye karki kuma aikata wannan kuskuren dan bazan dauka ba, fauziya da mamaki ya cika ta, ta amsa da toh, amma cikin zuciyarta fadi take wlh sai nayi maganinki basai kinga abun da za'a haifa ba, balle ki kirashi jika ba, nan da kwana biyu cikin zai zube sai inga ta tsiya,
Hjy binta ta katse mata tunani da fadin saura ke nazo ne in miki kashedi, salma ta dago dakai cikin tsoro tare da fargaban mai zata fad'a, tace naga take takenki bakya son wannan cikin sai yasa kike wasa dashi, wlh kinji na rantse miki indai wani abu ya sami wannan cikin saina sa an hukunta ki, taci gaba da fadin nasa an kawo masu aiki wanda zasu dinga yi muku abinci, saura kuma ki koresu, indai kikai hakan saina saba miki, daka yau zasu fara abinci a gidan nan har sai kin haiyu, in yaso kyayi duk abinda kika ga dama, salma cikin sanyin murya tace nagode mama, hjy binta tace daina godemin badan ke nayi ba, tace ku bamu waje, nan ita da fauziya suka tashi ko wacce tayi dakinta,
Ta kalli Mahmud wanda gaba daya ya shiga cikin wani hali, sai taga kaman ya rame, lokaci daya taji ya bata tausayi ta tashi ta dawo kujeran da yake, ta kira sunanshi, ya amsa cikin taushin murya, tace banji dadin abun da kayi ba, duk da itama bata kyauta ba, bai kamata ka saketa ba, yar uwarka ce, ko kana so ka bata mana zumunci ne? Yayi saurin cewa a'a mama abubuwan fauziya ne sunyi yawa rashin mutuncin yau daban na gobe daban, tace kayi hakuri kaji, bana so in kara jin ka furta kalman saki a bakin ka, kaima gashi yanzu za'a fara maka haiyuwa ko kana so kaima aima naka ne? Yace mama Allah ne shaida na, bana sakin mace ba tare da hujja ba, tace koma miye daka yau bana so, ka kara hakuri akan komai kaji, yace insha Allah, nan suka dan taba fira na d'a da uwa, sannan ta tashi ta wuce,
Fauziya tana shiga d'aki ta dauki waya ta kira mamanta, tana fad'a mata abunda ya faru, hjy zaliha, tace lallai binta, dole in sake daukan mataki akanta, wato ita idonta ya rufe akan zata sami jika koh, shine har take fad'a miki magana a gaban wannan yar iskan, kar ki damu zan dau mataki, fauziya tace ni yanzu gaba daya ma ya daina zuwa d'aki na, gaba daya ya tare a wajanta, hjy zaliha tace kar ki damu kwanan nan zai dawo wajanki bari cikin ya zube, ai yau saura kwana biyu sati dayan ya cika, kinga in cikin ya zube a nan sai musan yanda za muyi mu xuga binta akan da gangan ta zubar, na tabbata sai tasa an mata wulakanci, daka karshe tasa Mahmud ya saketa, kinga ya dawo naki ke daya sai ynda kika ce, nan fauziya ta saki shewa cikin jin dadi tace kai mama sai yasa nake sonki wlh, hyj zaliha tayi dariya tace zan iya yi miki komai ai dan inga kina farin ciki,.
Wasa2 har sati dayan ya wuce sati biyu, amma cikin na nan, fauziya ta shiga damuwa sosai kullum salma kaman ana kara mata lafiya, ga wani abun bakin ciki hjy binta tana yawan zuwa duba salma, taga ya take ciki, hjy binta ta sauko akan tsanar da tama salma,suna da gida a zone2 wani katon gida, ta sami labarin gidan ya zama na fauziya, ga wani gidan gonan su inda ake had'a su drinks kala2 dasu kaji kifi da sauransu shima ya zama mallakinta ga wasu gida da take dasu guda biyu, a cikin Abuja, nan ta kira Mahmud ta tambaye shi akan mai zaisa yaba fauziya gida da gidan gona bai fad'a mata ba, nn yace wlh bashi ya bata ba, ta kira fauziya tace ya akai ya zama nata, budan bakinta tace ki tambayi danki mana, abun ya bata mamaki, gashi taji labari wajan mutane da dama akan halayen fauziya na bin malamai nan Hjy binta taji ta fitar mata a rai, tace insha Allah zan kara dagewa da addu'a, tun daka lokacin ta fara sakema salma domin ta gano itace mai son danta tsakani da Allah,
Fauziya taje wajan boka akan har yanzu cikin bai zube ba, nan yace mata ai cikin bazai taba fita ba, amma abu daya xa'a mata yaron zaizo bada rai ba, yace inta yarda toh, tace ta amince, yace toh duk sati za'a dinga yima aljanu ynka suna shan jini, a kalla zaki dinga kashe million 5 duk sati, tace babu komai indai za'a kashe dan yaxo bada rai ba, ni burina kawai yaron ya mutu tunda ni har yanzu bani da ciki yama daina kulani, boka ya kwashe da dariya domin yaga zai tatseta yace ki tashi kije sai na jiki, ta tashi ta tafi, boka ya kuma kwashewa da dariya tare da fadin mahaukaciya ni na isa in kashe mutum ne, ko in zubar da ciki, nima sa'a ne inna fada abu ya faru, amma wannan banyi sa'a ba, sai ki kawo kudi inta ci.
Salma taja yarinyar matar nan jikinta inda yarinyar take fad'a mata bara xuka zo Abuja, ita da mamanta wanda take dauke da breast cancer sai a sannan salma ta lura inta shiga dakin tana jin wani wari duk saita dauka ciki ne yasa take ji, yarinyar tace babanta ya rasu wajan shekara biyar kenan dangin shi suka cinye dan abun daya bari, ga cuta na damun mamana anyi na hausa abun ya warke ashe ya lafa ne, daka baya ya kuma tashi anyi na hausan yaki yi, dole muka je asibiti akace sai an yanke nonan, ta yarda aka yanke gashi dayan kuma ya kama, wanda wannan karan taki yarda a yanke, sai dai magani da take tasha, gashi bamu damai bamu sai dai muyi bara mu sami na abinci, wata wacce muke bara ta bata shawaran muzo Abuja zamu iya samun wanda zai dauki nauyinta a dubata a babban asibiti hala ta warke, shine abun daya kawo mu Abuja, muna bara duk inda muka ga kango sai mu kwana abun mu, wata rana na sami labarin mijinki akan yana taimaka ma mutane, wata wacce muke bara ta rakani office dinshi nan muka zauna muna ta jira amma shuru bai fito ba, muka wuce wata rana na kuma komawa ni daya a nan naga ya fito zai shiga mota shida masu bashi kulawa, gaba daya saina kasa zuwa wajanshi, haka naita zuwa amma bana iya yi mishi magana daka karshe masu gadin wajan suka ce kar in kuma zuwa, shine bamu sake haduwa ba saida na ganshi asibiti driver dinshi ya bigeni, salma ta tausaya masu sosai, ta dau alkawarin zata sa Mahmud ya taimake su.
Maryam Obam 😘
ðŸ’ðŸ’ðŸ’KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
85to90
Salma tama Mahmud bayani akan yarinyar da mmnta, shima ya tausaya yace zai sa a kaita asibiti koh Allah zai sa a dace, salma taji dadi tare dayi mai godiya, yayi murmushi yace sai ki fada mata su shirya gobe sai a kaita, nan salma tace toh tare da tashi ya bita da kallo yana murmushi ganin yanda ta tashi tana nishi, ganin yana murmushi yasa ta bishi da ido tare da fadin lafiya? Dariya ya saki mai kara yace babu komai, ta dan bata fuska tace akwai mana ka fadamin plz, tashi yayi yaxo kusa da kunnanta yace I love you, murmushi tayi cikin Jin dadi tace I love you too my dearest husband, sannan ta fita.
Salma ta shiga dakin da sallama, salamatu ta amsa tare da fadin sannu aunty yanzu nake son inzo wajanki inji koh kina son wani abu, salma tayi dariya tare da fadin ina mama? Tace tana bayi, nan salma ta zauna suna ta fira da takwaranta, har mmn ta fito daka bayi, salma tace sannu mm nan tayi murmushi tare da fadin yauwa ya jikin naki? Salma tace da sauki, nan taci gaba da magana gobe da safe zaki shirya zaku asibiti Dr ya duba ki, mmn ta kalli salma da mamaki ya akai tasan bata da lafiya, ko dai taji warin da takeyi ne, salma ta katseta da fadin salma ta fadamin komai, insha Allah zaki warke kuma za'a dace da yardan Allah, mmn tace ngd Allah ya saka da alkairi, da ana samun irinku masu taimako da talaka yaji dadi, Allah ya kara arxiki salma ta amsa da ameen, salamatu tace aunty Allah ya saka miki da gidan aljanna, ina son mmn ita daya ta rage min, ita nake gani inji dadi, ciwon yana damunta sosai, bani da wani Jin dadi, kullum ina kwana da fargaba, Amma a yau zanyi bacci cikin Jin dadi, salma idonta ya ciko da kwalla tace takwara ta insha Allah komai zai wuce babu abunda zai sameta kici gaba da addu'a, sun dan taba fira sannan ta tashi ta nufi gefensu,
Fauxiya gaba daya, ta shiga damuwa komai tayi baya yi, gashi tana ta kashe kudi, harta gidajan da take dashi ta saida, dan dai kawai taga ta sami Mahmud, sannan abun dake cikin salma yaxo bada rai ba, indai taje wajan boka ko nawa yace zata bashi dan dai taga ta sami biyan bukata, Amma kullum kaman ana kara sama Mahmud tsanarta, ga hjy binta itama yanzu ta dawo wajan salma, komai tasa ayi a kanta shima yaki aiki, Amma duk da haka Fauxiya bata saduda ba, ita da mahaifiyarta.
Washe gari da safe, kaman yanda Mahmud yace za'a kai su asibiti, hakan ko akayi, salma tace ya bari suje tare yace a'a baya son tana fita kar wani abu ya sami baby dinshi haka ta hakura, driver ya kaisu Mahmud yace ya tsaya ya musu komai, hakan ko akayi, sunje Dr ya dubata, yaga dayan wajan da aka yanke, sai kuma dayan daya kama, yace dole sai an miki aiki ta wajan gefen breast dinta akwai wani bkin abu daya fito, shima yace za'a yanke shi, tace Dr Idan aka cire zan warke kuwa? Yace insha Allah, nan tace toh ta yarda, yace taxo jibi a mata aikin nan suka tashi suka fita, ita dai salamatu gaba daya hankalinta bai kwanta da wannan aikin ba, sun dawo sunma salma bayani, ta fadama Mahmud ya bama driver kudi yace ya biya komai da komai, kafin jibi din,matar gaba daya ta shiga cikin damuwa, tun da suka dawo babu abunda take sai tagumi da hawaye, salamatu itama ta shiga damuwa, tana ta rarrashi amma sai tace ina ganin kaman bazan tashi ba, yarinyar ta tashi da sauri tana kuka tayi gefen su salma, a nan ta ganta ita da Mahmud a falo, salma ganin yanda ta shigo cikin tashin hankali tana kuka, yasa tace salma lafiya kuwa? Maiya faru? Tace mama,... Ta kasa magana nan salma tace maiya sameta? Mahmud yace muje mu gani, suka fita sukai dakin suka ganta tana ta kuka , salma ta matsa kusa da ita tace mm maiya faru wani abu aka miki? Tayi dan murmushi tace babu ko daya ina ganin kaman wannan ciwon nawa bazan tashi ba, ina tausaya ma yarinyar nan ban san wani hali zata shiga ba, bata da kowa sai ni, salma tace mama ki daina fadin haka cuta fah ba mutuwa bane, tayi murmushi tace hakane ta kama hannun salma tace dan Allah kimin alkawari koda na mutu ban tashi ba ki rike min yarinyar nan,har zuwa sanda za tayi aure, salma ta waiga ta kalli Mahmud ya daga mata kai alaman eh, tace nayi miki alkawari zan riketa amana, balle ma insha Allah zaki tashi, tace ngd Allah ya saka miki da alkairi, salma wani kwalla ya zubo mata ta amsa da ameen, salamatu babu abunda take sai kuka, salma ta rarrasheta tare da fada mata cuta ba mutuwa bane, tayi hakuri,
Kaman yanda Dr yace su koma, haka suka shirya suka tafi, wannan karan harda salma, an kaita dakin theater, nan Dr uku suka shiga, salamatu gaba daya jikinta yayi snyi tana tuna abunda ta fad'a mata jiya, da daddare ko bayan raina inaso ki zauna da wannan baiwar Allah bisa amana ki dauketa tamkar ciki daya kuka fito, sannan ki rike maraicin ki dan Allah kar ki manta ko ke wacece, salma ce ta katse ta tare da dafa ta, tace kiyi hakuri insha Allah zata tashi, Dr sunyi wajan 3hr kafin suka fito ko wanne a sanyaye, salamatu tana ganinsu ta tashi da sauri tana tambaya ya jikin mmnta? Duka suka mata shuru, har salma ta karaso tace Dr ya jikin nata da fatan anyi a sa'a, daya daka cikin Dr din yace hajiya sai dai kuyi hakuri Allah ya mata rasuwa, salamatu ta saki ihu tare da fadiwa kasa sumamma, nan aka dauketa akai emergency da ita, aka bata taimakon gaggawa cikin ikon Allah ta farfado, salma na kusa da ita tace aunty dagaske mmna ta rasu bazan sake ganinta ba, nan salma ta rike mata hannu tana fadin kiyi hakuri duk mai rai mamaci ne, muma lokaci muke jira, yanzu kibar wannan kukan addu'a take bukata, tace aunty ban taba zata mmna zata rasu yanzu ba, mai yasa ni mutuwa bata daukeni ba, salma ta toshe mata baki tare da fadin kar kiyi sabo, salamatu Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, ki mata addu'a Allah ya gafarta mata, a dai2 nan Mahmud ya shigo, gaba daya yarinyar ta bashi tausayi, ya mata gaisuwa tare da mata nasiha daka karshe yace bari su tafi dan a mata sutura, nan salamatu ta sauko tace su wuce tare, taga mahaifiyarta na karshe, hakan ko akayi Dr yace zata iya tafiya, gidan hjy binta suka nufa ga mutane sun taru, an mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya duk wanda yaga salamatu saiya tausaya mata, musamman salma da aka bama amanarta itace yanzu uwa a gareta, saida akai uku suka koma gidansu, Fauxiya ko lekowa ba tayi ba, bayan sun koma aka gyarama salamatu wani daki a gefen su salma, kullum zaka ganta tayi shuru tana tunani salma intaga haka taita mata nasiha,
Cikin salma ya kai wata7 Mahmud kullum inya fita yaga kayan yara saiya siya na mata dana maza, salma inya kawo kayan tayi ta dariya, Fauxiya gaba daya ta fita hayyacinta domin yanzu komai nata ya kare malamanta duk sun cinye kudin, amma duk da haka bata saduda ba, tana ganin za tayi nasara dan ta rasa wannan inta kara mallake Mahmud zata sami wanda ya fishi,. Yayin da salamatu take zama tare da Salma,wata rana suna fira salma take ce mata wai salamatu kina da saurayi kuwa, tayi dan murmushi tace a'a aunty bani da kowa, ni bama na sha'awan saurayi domin maza basu da kirki, amma ke kinyi dace, inda zan sami irin namiji mai halin mijinki dana more, salma tayi shuru tana kallonta, har salamatu ta lura da shurun yayi yawa, sai taji wani iri akan maganan data mata, tace aunty kiyi hakuri inna bata miki rai, salma tayi dariya tace zaki auri mijina......? Cikin zabura salamatu ta dago tana kallonta.......
Maryam Obam😘
ðŸ’ðŸ’ðŸ’KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
90to95
Girgiza mata kai ta fara yi, alaman a'a, salma tace takwara dagaske nake miki, ba wasa ba, sai a sannan salamatu ta sami daman magana tace aunty dan Allah kar ki karamin wannan maganan abune da bazai yiwu ba, bazan iya auran mijinki ba, ko a mafarki balle a zahiri, salma tace kina nufin bakya son shi?? Tace bawai bana son shiba, kodan taimakon da kuka min dole in soshi , balle ma akwai soyayya na musulunci, salma tace toh miye a aibun aurenshi bayan kince kina son namiji mai irin halinshi, salamatu tace haka ne, samun namiji irin shi sai an tona, amma bazan iya auranshi ba dan aunty kinyi katangar karfe a tsakani ko hauka nakeyi bazan taba auran mijin da kika aura ba, salma tace kenan ni bani da ikon in miki zabi? Shuru tayi tana hawaye tace aunty kina dashi, kece uwata kece ubana, kina da iko dani amma..... Ta dakatar da ita tare da fadin tunda ina da iko bana son in kuma ji kince bakya so, ta daga mata kai alaman toh, ta sannan ta tashi dasauri tabar wajan, salma ta bita da ido tare da tausaya mata, tace salamatu wannan shine gatan da zan miki amana abune mai wuya, na amsa amanarki, ban san mijin da zaki kawo ba, inma nace zan xaba miki ban San ya halinshi yake ba, Amma nawa mijin nasan koshi waye, nasan halinshi, nasan bazai cutar dake ba, auran Mahmud shi zaisa in sami kwanciyan hankali muna tare, jin an taba ta tayi firgit ta waiga taga Mahmud ne, ya hura mata ido tare da fadin tunanin mai kikeyi haka? Murmushi tayi tare da fadin yaushe ka shigo? Yace tun dazu nayi wajan 5mnt akanki Amma baki sani ba, kina ta tunani, lafiya kuwa? Tayi Murmushi tare da fadin lafiya dear muje kayi dinner, kai tsaye danning suka nufa, ta tashi zata zuba mai abinci yace ta zauna zai sa dakanshi, dariya tayi tare da zama ya zuba a plate ya dawo kusa da ita, yana bata shima yana ci, har suka koshi, fauziya ce ta shigo cikin fushi sukai ido hudu da Mahmud ga salma a jikinshi tana ta faman yi mishi shagwaba, haushin nata ya kuma karuwa taje ta janyo salma ta tureta salma ta saki kara, Allah yaso akan kujera ta fadi, nan Mahmud ya tashi ya wanke ta damari tare da fadin ke mahaukaciyar inace, tace ta gidanku wannan tso...... Kafin ta karasa ya kuma kwasheta da mari, yace kije na sakeki saki uku, mara tarbiya, ta cakume shi tana fadin wlh baka isa ba, yau ko ni ko kai saina kashe ka sannan in kashe wancan yar iskan da abunda yake cikinta, hjy binta data shigo da kaya niki2 na baby ta kawo ma salma, tazo taji ana rigima ana za'a kashe mata d'a da jika nan ta kira police, suka shigo gidan tace ku kama min ita, fauziya da mamaki tace wlh baki isa ba, ai zan fito sai na kashe ku wlh, nan police suka tasa keyarta sukai gaba da ita, salma gaba daya ta shiga cikin tashin hankali hjy binta ta matsa kusa da ita, tana fadin sannu y'ata bata dai taba kiba ko? Kafin salma tayi magana nan Mahmud ya fara bata labarin farkon abunda ya faru, hjy binta tayi Shuru tare da fadin kayi hakuri duk ni naja maka, na tsani matarka haka kawai ba tare da tamin komai ba,, inata matsa maka kayi aure, gashi na baka yar'uwarka tana kirarin zata kashe mu, hjy binta harda hawaye, tace ma salma dan Allah ki yafe min duk abunda na miki, salma tace mm baki min komai ba, kefa mahaifiyata ce,, komai kika min kin isa ne, ban taba rikeki a raina ba, hjy binta cikin kuka tace ngd Allah ya miki albarka ya saukeki lafiya, salma ta amsa da ameen, Mahmud yau yana cikin farin ciki ya rabu da fauziya zai zauna daka shi sai matarshi, suna ta fira, hjy binta tace ina yar amananki? salma tace tana daki, hjy binta tace Allah sarki, bari inzo in wuce dare yayi, ga kaya can dazu na amso su, nace bari in kawo shine naji wannan bala'in, kayan baby ne masu tsadan gaske, ta tashi, suka rakata har mota sannan suka dawo,yanxu gida ya dawo na salma sunsha love ranan ita da Mahmud duk da ta nuna Mai bai kamata ya saki fauziya har saki uku ba,
Washe gari da safe, suna breakfast, salma ta kalli Mahmud tace ya kamata kaje kasa a saki fauziya, ya bata fuska tare da fadin dan Allah salma kar ki karamin maganan fauziya a nan, tace shikenan bazan kara ba, kayi hakuri plz, yayi Murmushi yace matar da take ikirarin kashe ki, shine har kike tausaya mata, dole sai an hukunta ta, salma dai Shuru Tayi, amma inda za'a nata da an barta da hlinta an saketa, zata hadu da dai2 ita, Indai duniya ce wanda bai zoba ma tana jiranshi balle wanda yake cikinta, Mahmud ya katseta da fadin yau kina da zuwa hspt ki tashi muje, tace toh ta kira salamatu suka fita, bayan ya kaisu asibitin yace bari yaje ya dawo Kafin su gama, tace toh, kai tsaye gidansu yayi nan yaga hjy zaliha tana ta bama hjy binta hakuri akan a saki fauziya, hjy binta tayi banza da ita, ganin Mahmud yasa ta fara fadin dan Allah dana kayi hakuri kasa a saketa, hjy binta tace ai babu ruwanshi a wannan maganan, bai isa yayi komai ba sai yanda nace, hjy zaliha cikin fushi tace shikenan in baki sa an saketa ta dadi ba, zaki sa a saketa ta wuya, ta fita fuuuuu, hjy binta tace ina jiranki, Mahmud ya gaidata ta amsa sannan ya zauna, yace mm ni a nawa ganin da ansa an saketa ko dan xumuncin dake tsakani, hjy binta tace hakane amma ba yanzu ba sai naga abunda zaliha za tayi, yace kar ki biye mata bacin rai yasa ta fadi haka, nan Mahmud ya shawo kanta ta yarda, sannan ta dauki waya ta kira police ta bada umarnin a saketa,Mahmud yace bari ya koma hspt yabar salma acan, tace ita daya dan mai zaka barta, yace ita da wannan yarinyar ne, tace oho toh maza ka koma hala sun gama, ya tashi ya fita.
Fauziya gidansu tayi, hjy zaliha tana falo a zaune, taganta tace fauziya ya akai kika fito, tace haka kawai suka ce inzo in wuce Kuma gidan iyayena zani, kar ince zani gidan Mahmud, hjy zaliha tace bari zanyi maganin su wlh, duk da ya sakeki sai na wulakanta hjy binta ita da danta wlh, fauziya tace ko ke baki haka ba ni sai nayi, matsala ta daya shine banda kudi a hannu ina ganin gidan nan zamu sa a kasuwa, hjy zaliha tace toh ina zamu zauna? Tace haya zamu kama a hankali na siya mana wani amma yanzu ina bukatar kudi, hjy zaliha tace ai kiyi duk abunda ya dace, akwai wani boka a maiduguri dana sami labarinshi ance wlh inya maka aiki Kafin ya karye sai anyi dagaske, fauziya tace toh sai muje can yanzu ki kira dillali ki fada mai gidan nan a kasuwa yake, hjy zaliha tace an gama,
Mahmud suna daki shida salma, ta kalleshi tace dear, ya amsa da na'am, tayi Shuru na wani lokaci, yace ya naji kinyi Shuru inaji, tace inaso kamin wani Abu guda daya, yace salma koma guda dari ne zan miki Indai kina so, tayi Murmushi tare da fadin kayi alkawari yace yes nayi, tace toh dama ina so ne ka auri salamatu, tashi yayi tare da fadin what????...........
Maryam obam😘
ðŸ’ðŸ’ðŸ’KISSA KO MAKIRCI👹👹👹
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
(Mrs nura kuriga)
95to100
Lokaci daya yayi murmushi tare da fadin, wannan wani irin wasa ne salma? Kar ki mata we are not in April fah, balle kice kina fooling dina ne, itama murmushin tayi tare da fadin dear am serious, ba wasa nake ba, ina so ka aur......... Daga mata hannu yayi alaman tayi shuru ya tamke fuska, yace salma daka yau bana son ki karamin wannan maganan indai baso kike kiga fushi naba, tashi tayi tazo kusa dashi tana hawaye tare da rike mai hannu, ganin tana hawaye yasa yaji wani iri, tace dear kayi hakuri ban fadi haka dan in bata maka raiba, ban kuma fadi hakan ba sai da nayi tunani sosai akai, kuma kar ka manta kamin alkawari komai na fada zakamin, yace look salma bawai inaso ayi ta wannan maganan ba, ki bari zan duba mata miji wanda zai aureta kinji, tace Idan ka duba mata miji, shin mai kalan halinka ne? Koh kuma zai iya riketa kaman yanda kai zaka iya,? Yace shuru yayi yana kallonta, Lokaci daya yace salma bari kiji koda ba iri na bane karki manta akwai wanda suka fini, kiyi hakuri kibar wannan maganan plz, shuru tayi tare da matsawa daka kusa dashi ta juya baya tana kuka mai kara kadan, tace wannan ne Karo na farko dana taba nuna ina son abu kaki min, gaba daya jikinshi yayi sanyi, taci gaba da cewa wanda ko a mafarki bazan taba yarda zaka ki abun dani nake so ba, matsowa yayi kusa da ita tare da janyota jikinshi yace salma mai yasa kike son in aureta? Tace Mahmud yarinyar nan amana aka bani ita, kuma ta isa aure, bata da saurayi tace tana son namiji mai hali mai kyau, ni kuma nasan nawa mijin yana da hali mai kyau, sai yasa naga ya dace kai ka aureta, ance imanin dayanku baya cika har sai yaso ma dan'uwanshi abunda yaso ma kansa,Mahmud kai nake so kuma nake ganin nayi dacen miji, dan mai zaisa inki so ka aureta tunda nasan halinka, tace dan Allah ka yarda hakan zai sani farin ciki, yayi shuru har na wajan minti hudu, babu abunda yake kara a dakin sai sautin kukan salma, yayinda yake ji har cikin zuciyarshi, yace shikenan tun da haka kika ce na amince, amma ki sani bazan aureta ba har sai an nemo dangin ta, cikin murmushi tace kar ka damu wannan mai sauki ne, tace ngd Mahmud Allah ya barmu tare ya baka ikon yi mana adalci,.
Fauziya sun saida gidansu, a ranan da aka biya kudin sukai maiduguri wajan sabon boka, Fauziya ji take kaman mota baya sauri, dan ta kosa ta ganta a gabanshi dan tana ganin Idan taje duk wani matsalanta ya tafi kenan, gudu suke zubawa, karan harbi sukaji an fasa musu taya nan motar ta fadi ta fara kundun bala ta tsaya ta cikin daji, har ta tsaya, yan fashin suka karasa motar tana kife da yake suna da yawa sun kai su goma sha biyar, suka fara kokarin daga motar, cikin ikon Allah suka daga ta, yayinda duk yan motan sunji jiki wasu kuma sun mutu, ciki harda Fauziya wanda ta rasu hjy zaliha kuma kafanta daya ya karye ga harshenta ya datse, driver dinma ya rasu da wanda suke gaba, bai fi mutum uku suka rayu ba, nan yan fashin suka dibe duka kayan motar, suka wuce, hjy zaliha ganin fauxiya bata motsi ta tabbatar ta rasu, gashi ita babu daman magana babu baki harshe ya datse da karfe ga karaya a kafa kuka take kaman zararra tana takaici, namiji daya sai mata biyu suka rayu suma duk sunji jiki sai hjy zaliha, nan namijin ya fita dakyar yana tsayar da mota amma kowa yki tsayawa sai wani mai motar albasa ya tsaya, nan ya mishi bayani abun daya faru yana ta salati yace ina sauran? Yace suna ciki, nan yace bari ya karasa gaba kadan akwai gari sai a sanar da sarki, hakan Koh akayi aka kira sarki da mutan gari, da yan sanda aka kwashe wa inda suka mutu, aka kira tashar motar aka sanar domin su kira yan uwansu ita dai fauxiya anan aka birne ta, yayin da wasu yan uwansu sun zo an tafi dagawarsu, hjy zaliha kuma an daure mata kafa, hmm rayuwa kenan hausawa na cewa in zaka gina ramin mugunta gina shi gajere wata kila kai zaka fad'a,hjy zaliha tana gidan mai gari, babu abunda take sai kuka tare da nadama tana fadin na cuceki fauxiya na bata ki dabin malamai kin mutu akan turban, matan maigari in suka ga tana kukan suyi ta tausaya mata,
Hjy binta da Mahmud yayi maganan auren taki yarda tace sam bata amince ba, akan me zai kara aure yama rasa wacce zai aura sai wannan yarinyar da ba'a san kowa nata ba, gwara ka zauna da salma ita daya yafi maka, yace mama salma ce ta matsa min akan in aureta, nan hjy binta tace bana son wasa, ya fad'a mata komai nan tayi shuru tare da fadin lallai salma wannan abun da take shirin yi ban taba gani ba, gaskiya tana da xuciya mai kyau, amma baka san dangin yarinyar ba, yace eh salma tasa anyi bincike akwai wani yayan babanta yace babu komai shiya amince, yanzu turawa kawai za'ayi da komai a daura, tace toh Allah ya tabbatar da alkairi ya amsa da ameen,
Yau salma ta tashi da mugun ciwon mara, saiya tashi ya lafa, Mahmud yana lura da ita, yace suje asibiti taki, sai da kyar da taga ciwon na karuwa, suna zuwa asibiti akace haiyuwa ne, nan aka kaita labour room, Mahmud ya kira hjy binta da hauwa, kusan a tare suka zo, asibitin, salamtu tare dasu salma suka zo, kowa yana rokan Allah ya sauketa lafiya, cikin ikon Allah bata wuce 30mnt ba ta haifo yan uku, maza biyu mace daya, waiyo Allah zo kuga murna wajan Mahmud da hajiya binta, abun ba'a magana, a ranan suka dawo gida basu kwana ba, Mahmud sai kashe kudi yake komai ya bayar yace a siyo shima ya siyo da kanshi, salma tace tana son ran suna a daura auren Mahmud, bata fada mishi ba, ta fadama hjy binta aiko hakan akayi ta tura mutane aka tafi ba tare da sanin Mahmud din ba, balle salamtu ita da bata san komai ba, an kashe naira kaman babu gobe, mazan ansa sunan mahaifin Mahmud el-hassan suna nickname nashi farhan, sai dayan kuma sunan baban salma Muhammad, nickname dinshi anan, sai macen kuma sunan Hjy binta fatima nickname dinta zarah, anci suna an watse har yan daurin aure sun dawo an daura, dama salma ta kira mai lalle ana gobe suna ta musu, kayan dakin fauxiya gaba daya an kwashe akasa sabo, tace salamtu taje tayi wanka ta bata kaya tasa, ta amsa tayi wankan sannan tasa ta fito, ta kaita dakin fauxiya tace ta zauna tana zuwa, Mahmud dake dakinta yana kallon yaranshi yana dariya, tazo itama tayi dariyan tare da kama hannunshi tace suje ya gani, bai musa ba yabi bayanta yaga tayi dakin fauziya din, ganin salamtu a ciki yasa abun ya bashi mamaki, itama kanta salamatu sai da taji faduwan gaba, salma tayi murmushi tare da fadin yau ka zama mijin salamatu itama ta zama matarka an daura muku aure yau, yace salma miye haka, nan ta fada mishi yanda akayi shuru yayi yana kallonta, salamatu kuma kuka takeyi, salma ta kama hannun Mahmud tare da zaunar dashi akan kujeran da salamatu take tace Allah ya baku zaman lafiya sannan ta fita, tana zuwa daki ta fashe da kuka tare da bakin kishi da taji yana taso mata, Lokaci daya ta share hawayen tare da koran shedan ta matsa kusa da yaranta tana kallonsu tana dariya tare da godema Allah,
BAYAN WASU SHEKAR
salma ta kara zama babban mace, ga naira tana juyawa sosai, yanzu tana da yara biyar, ta kara haifan yara biyu maza duka, aka sa musu yusuf da Ibrahim, yayinda salamatu kuma take da yara biyu, mace daya namiji daya, zainab da usman, salma ta kara mallake zuciyar Mahmud da kissa irin nata, ga wani irin girma da salamatu take bata, sai abun da salma tace akeyi a gidan, komai na Mahmud yaso yasa sunanta tace a'a yasa na yaranshi, hakan kuma akayi, hjy zaliha itama Allah ya mata rasuwa bayan tayi jinya mai tsawo taji jiki sosai tare dayin dana sani keya ce,
Hauwa tazo gidan salma ita da yaranta su uku, suna ta fira da salma, hauwa tace wai salma har yau baki fadamin irin naki kissan ba, tayi dariya tace bari in fadamiki ba wasu abu bane masu Wuya kema kin sani sai dai kikiyi, hauwa tace inaji, salma tace hauwa da farko mace ta fara sanin waye mijin ta, tasan miye halinshi, tasan miye yake so miye baya so, babban abu shine kisa ma kanki hakuri, domin shi namiji a koda yaushe yana daukan kanshi sarki matarshi kuma baiwa, yana so Idan ya miki abu duk da shine da laifi ki bashi hakuri ki nuna kece da laifin bashi ba, sannan kuma duk wani hanya da zai sa ke kiyi mishi laifi karki bita, sannan Idan namiji yana fushi kar ki kai mai wata bukata naki kiyi hakuri har sai ya sakko koda kuwa bukatar babba ce, ki ajiyeta a gefe kisan yanda zaki rarrashe shi ya sauko, kar kice ke bai dameki ba tunda a waje aka bata mai rai kema bari ki kara mai wani toh kinga in kikai haka kinja ma kanki matsala, sannan karki dinga yima miji wasa da abinci koda kuwa kina fushi dashi kiyi mishi abinci dan namiji ya tsana yazo gida ya tarar ba'a mai abinci ba, wannan abun zai iya ja muku mugun matsala, sannan ki zama mai tattali da dukiyar miji, sannan Idan yace yana son abu ki nuna kin fishi so indai bai sabama addini ba, kaman ni a lokacin da yace zai kara aure mahaifiyarshi ta matsa mai, nace na amince banyi wani hayaniya ba, kinga a lokacin ji nayi kaman zanyi hauka dan tsabar kishi amma na daure na hakura, inda na tada hankalina na mishi hauka duk da yana sona sai yaji wani kala hala son ya ragu yazo ya fara gayamin magana shikenan na xubar da kimana wani namijin ma saiya sake ka, in kuma ka sami mai surutu saiya fadama amaryan haukn da kikeyi kinga tun kafin ta shigo ta raina ki, shima kin xubar da kimarki a wajanshi, amma da nayi hakuri kinga komai ya wuce, harta fauziya da aka daura mishi wani irin asiri ne ba tayi ba, amma da yake Allah yasan bani da hakki, sai abunta ya koma mata, mata da yawa inda zasu duba zasu ga asiri wlh baya aiki biyayya da iya kissa shike sa namiji ya soki, in kuma Allah ya jarabta mutum asirin yayi kwana arba'in ne fah ya karye, in Allah ya dauki ranki kina wannan aikin mai zaki cema Allah, sannan ko su bokayen zasu ce asiri baya yi sai da biyayya, Idan kikayi tunani tunda sunce haka sai ki duba dan me toh zan kashe kudina a banza, sai kiyi biyayyan kawai ki gani, hauwa tace wlh salma haka ne kinyi gaskiya, amma mai yasa kika karama Mahmud aure toh? Tayi murmushi tace hauwa duniyar guda nawa ce, mata da yawa sun sa bakin kishi akan kishiya inda zaki tara mata dari kice wai akan mai yasa suke kishi da kishiyoyinsu wlh dakyar ki sami guda goma wacce Zata ce ga dalili, kuma fah kar ki manta duniyar ba zama muka zo yiba, zamu mutu mu barta in kin hana mijinki aure Idan kika mutu zaki hanashi yine, ba zaki hanashi ba, gashi kin bata duniyar ki wajan malamai lahirar kuma kije bata samu ba, yanzu dana hada Mahmud da salamatu ba karamin kara daukaka nayi aranshi ba, haka itama yarinyar tana bani girma sosai mai yafi wannan dadi mijinka duk inda ya zauna yace ke yar aljanna ce, ya dinga labarin alherin ki a ko ina, salma tayi shuru tare da cewa kin san wani abu hauwa? Ta girgiza kai alaman a'a? Tace wannan abun da nayi shine kissa wacce babu bokan da zai baki ita, yanzu sai ki fadamin tsakanin KISSA KO MAKIRCI, Wanne yafi, hauwa tace KISSA nima na koya zanje inyi dan in gyara rayuwar gida na suka sa dariya tare da tafawa.... To nima dai anan zan tsaya..
ALHAMDULILLAH
INA MIKA GODIYA GA MASOYA NA, WANDA DA BAZARKU NAKE RAWA ALLAH YABAR KAUNA MASU YIMIN MSG SUNA CEWA BANA REPLY KUYI HAKURI INSHA ALLAH ZAN DUBA SAKON KU ZAN BAKU AMSA NGD
GODIYA TA MUSSAMMAN GA
hajiya nafisa
Amina aliyu
Nana fiddausy
Kawata hibbat
Hassan atk
Ina godiya gareku akan karfafa min giwa da kukeyi ??
MASU SON MAGANA DANI SU NEMENI TA EMAIL DINA KAMAR HAKA: MARYAMALHASSAN206@GMAIL.COM